SIRADIN RAYUWA CHAPTER 18 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 18   BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 18 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

- - Post a Comment

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 18

 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMAKyakkyawar budurwa ce zaune gefan gadon kara sanye da kayan saqi,kyakkyawar fuskar hauwa'unta data sha yabawa tana qissima girmanta,ba shakka hauwa'u ce,saboda babu wani sauyi da zai saka ta kasa gane fuskar daya daga cikin 'yan uwanta,musamman hauwa'un da kullum take kwana ta kuma tashi da begen son ganinta.       Batasan ta kirayi sunanta ba sai da taga mutanen dake cikin bukkar dukka sun waiwayo suna kallonta,har ita hauwa'un da kanta ke kallon qasa a dazun,miqewa taga tayi daga bakin gadon karan tana fiddo idanu

"Yaaya maigado!" Ta fada da sauri kana cikin wani mugun gudu tayo inda take,ba bata lokaci ta fada jikin bilkisun suka rungume juna,lokaci daya kuma suka fashe da kuka,wanda ya janyo hankalin na kusa dana nesa,suka tattaru a wajen suka tsaya carko carko suna kallon sarautar ubangiji.       Daidai lokacin da anty zuhriyya da kanta ke ratso wajen saboda dadewar da taga bilkisun ta danyi,gashi suna son wucewa,sai tsoro kuma ya kamata na yadda ta barta ta shigo wajen ita kadai,gashi bilkisun tabar wayarta a mota,don haka ta shigo da kanta dubata.      Itama tsaiwa tayi tabi sahun 'yan kallo don batasan meya faru ba,ganin sunata yaren fulatanci a tsakaninsu an rasa me musu magana sai ta matso

"Ke daughter meye hakan?,daga cewa zaki sayi madara saikizo ki samu waje ki tsaya?" Kanta ta dago fuskarta ta jiqe da hawaye,tana riqe da hannun hauwa'u daketa kallon bilkisun kamar zata bace mata tace

"Anty hauwa'una ce,kuluwa ta" hakan data fadi yasa ta fahimci komai,sai a sannan hauwa'un ta waiwaya dubi dattijuwar da suka fito daga bukkar tare tayi mata magana mara tsaho da yaran fullanci,taji dai ta fadi sunanta dana babansu malam bilya,sai tsohuwar ta dubesu tana murmushi

"Ma sha Allahu,ai sai kuyi bayani,don sam bamu ganeku ba,ke ɓingel,bamu abun zama" ta gayawa budurwar da suka fara haduwa da bilkisu,saita juya da sauri ta shige bukkar.  *_BAYAN WASU MINTUNA_*
      Hauwa'un na zauna gefan bilkisu kamar zata haye cinyarta,labari take bata na yadda tayi kewarsu,da yadda tasha wahala kafin ta sake a nan din,duk da ta samu kulawa sosai anan fiye da nasu gidan,hakanan a hannun kakar tasu wadda ta gansu tare take,wadda ita ke riqesu ita da qanwarta da mamar tasu ta haifa a gidan data sake aure,ta auri bafulatani jinsinta,yanzu haka suna tare dashi da yaransu biyar harda wannan da ake kira da bingel.


.      "Nayi kewarku yaaya kamar me musamman ke ke dana saka rai da dawowarki,kullum ina cikin lissafin kwanakin da suka rage kidawo,ki cikamin alqawarin karatu da kikayi mana,katsam sukazo suka tafi dani bayan sunyi baram baram da baba,yanzu haka yaya maganar aurena ake da shehu,ni kuma bana sonshi yaya karatu nakeso har yanzu" ta qarasa maganar kuka na qwace mata.      Zancan auren ya taba bilkisu da anty zuhriyyan kanta,kai bilkisun ta kada

"A'ah bazai yiwu ba,ki daina kuka kulu na,babu me miki aure yanzu sai idan kece kika ce kinaso,aurenma na dole....ki kwantar da hankalinki,kinga mun taho da yara,amma gobe zan dawo,zanga dukkan wanda ya kamata na gani,zaki koma can gida cikin 'yan uwanki,kuma in sha Allahu zaki karatu yadda kikeso" murmushi ya kubcewa hauwan duk da hawayen dake saman fuskarta

"Zaki iya daukar nauyina yaaya?,duk da naga kin zama 'yar gayu sosai,kin canza daga yaya maigadonki kin zama kamar wata baturiya?" Murmushi tayi tana tuna yawan albashin da a yanzu take dauka

"Karki damu,harda bingel ma idan kinaso zan hada da ita" idanu ta fiddo 

"Allah yaaya?"

"Da gaske nake miki kulu" shuru ta danyi sannan tace

"Amma ina tunanin koni dinma su yelwa barasu yarda ki sake daukata ki maidani gida ba sabida abinda ya faru tsakaninsu da baba,da irin riqon da suka samu labari yayimin,bare su hada miki harda bingel,kuma na sani burinmu nida bingel daya itama karatu takeso kamarni" 

"Karki damu,daren yau kita addu'a,zasu fahimta in sha Allah" tayi maganar tana miqewa tare da amsarwa anty zuhriyya yaron hannunta,ta leqa su yelwa sukayi sallama ta shaida musu zata dawo gobe tanason magana dasu.      Har can bakin titin hauwa da bingel sukayi musu rakiya,tana riqe da hannun amatu da abdul kamar ta hadiyesu,tana jin qaunar yaran har ranta kamar yadda mamarsu ke sonta itama,tanata santin kyansu kamar kada su rabu.      Ko cikin mota hirar hauwa'u suka dinga yi ita da anty zuhriyya,ranar gaba daya da abinda ta kwana cikin ranta,washegari ta dauki najwa da amatu suka rakata rugarsu hauwa'u,daidai sanda tasan suna dawowa daga kiwo.      Ba qaramar gwagwarmaya tasha ba kafin su amince zata dauki hauwa'u,su kuma fasa aurar da ita ga wanda sukayi niyya da farko,don harta fidda rai ta haqura kafin su amince,amma bisa sharuddan zasu dinga zuwa ganinta duk sanda sukaga dama,hakanan itama zata dinga ziyartarsu duk sanda buqatar hakan ta taso,amma sam sunqi su bata bingel,babu musu ta amince,don tasan a yanzu dai babu wata sauran matsala,don baban nasu ba nada bane,ya sauya qwarai,kuma a yanzu bashi da abokiyar shawarar data wuce ita,ta saka a ranta zatasan yadda zata ja ra'ayinsu anan gaba su bata bingel dinma,tunda suka bata hauwa'un a yanzu.     Anan suka tsara zasu wuce kano nan da kwanaki ukun da suka rage musu a ringim,randa zasu tafin zasu biyo su dauketa saisu wuce,akan haka suka rabu. ¶¶¶¶¶¶¶   ¶¶¶¶  ¶¶¶¶¶    Bata taba zato ko tunanin duniya zata mata qunci da baqi ba irin na wannan lokacin,bata taba tunani ko tsammanin akwai ranar da zatazo fara'ar mai martaba tayi mata wuyar gani ba,bata taba wassafawa a ranta irin wannan lokaci zaizo ba,dukkan wani abu bai mata taste a baki,kamar yadda babu wani abu dake burgeta sam a yanzun,idan ka qare mata kallo zakaga rama ta fara bayyana akan fuskarta.     Tun daga randa suka kebe da azeez dukkan wani walwala da sakin fuska qauna da kulawa dake tsakaninsu yayi qaura,abu mafi daga hankalima yadda yayi mata shuru,har yau baice mata uffan ba,bai kuma tada maganar ba kamar ma ba'ayi komai ba,kamar ba abinda ya faru,koda taje turakarsa da sunan kwana takan zauna kamar wata baquwar amarya a gareshi,tsakaninau babu wata hulda koda ta cikakkiyar magana dake hadasu,sai maganar data zama dole.      Ayanzun takai maqura,shirunsa kullum sake kasheta yake alhalin tana raye,tafison yayi fada,tafison ya dauki mataki akanta,tafison hukunci akan shirunsa amma yaqi tankawa ko yace komai.       *_AZEEZ_*     Daga nashi bangaren shima kusan hakan take,yanata kasa kunne da zuba idanu mai martaba yace wani abu,yanata saka kunne yaji kira daga gareshi,saidai har yau shuru maqatau malam yaci shirwa,babu alamun ma zaiyi wani zama dashi ko ya nemeshi.      Hakan yayi masifar daga masa hankali gami da qara masa damuwa mai yawa,saboda dukkan wani burinsa ya azashi ga mai martaba,ya danganta samun mafitarsa daga wajensa,saidai da alama tunaninsa ya saba,failure tana shirin samunsa,shi kuma sam baishiryawa hakan ba.     Kewar yaransa tana masifar damunsa,yana da buqatar sanyata cikin idanunsa koda zaginsa zatayi,ya tabbatar zai samu wani relief ko yaya yake,to amma bayason yaje mata alhalin baisan wanne hukunci mai martaba ya yanke ba,bayason ya aikata abinda yaci karo da shiri ko tsarinsa,duk da dukkan wani fatansa na samun matsera daga gareshi yanzu ya fara kwaranyewa,daga baya yaji dukkan haquri da juriyarsa ta qare,ya shirya kawai yayi nufin zuwa jigawa ya gansu.      Sanda ya shirya ya nemi ganin fulani bai samu ganinta ba,rabonsa da ganin nata tun randa ya bayyanawa mai martaba komai,haka ya wuce jigawa bayan ya barwa afnan sallahu,wadda binsu kawai take da idanu,tana jiran taga yadda lamarin zai qarke,amma koma meye batajin wannan zata zuba idanu rayuwar qawarta ta tasake tashi a tutar babu,tana jin har cikin ranta zata shiga wannan lamarin a wannan karon koda ammin zatayi fushi da ita itama.       .      Yammacine lis ya isa garin na jigawa tarin Allah,garin yayi luf luf saboda haramar shigowa da damina keyi,wanda ake saka ran wannan karon za'ayi azumin ramadan ne a cikinta.       Dai dai lokacin bilkisu na xaune a falon hajiya suna hirarsu abinsu,ana ya gobe zasu wuce kaisa,hajiyan na bata labarin yadda mata sukayi xaman aure azamanin daa da yadda suka bi mazansu,da kuma yadda suma mazan suka riqe iyalinsu da kyau kuma suka kyautata musu,bilkisu nata mamakin abun,daga qofar part din hajiyan su amatu ke wasansu abinsu saman kekuna.      Sallamar daya daga cikin ma'aikatan gidan qofar sassan hajiyan yaja hankalinsu

"Isa shigo mana" hajiya tace tana sake miqe qafofinta dake mata ciwo,ba musu ya shigo,ya duqa cikin girmamawa

"Hajiya maman 'yan biyu ce tayi baqo" ya fada fuskarsa cike da fara'a,sai itama hajiyan ta washe baki

"Malam isa,ya naga kanata washe bakine,ko ta samu ne?" Da yake hajiyan akwai barkwanci,babu ruwanta sam bata da matsala,saiya sanya dariya

"Ai hajiya baqonne baqon alkhairi ne" murmushi tayi tana cewa

"Alhamdulillahi....aimu haka mukeso,to yayi kyau,ka bude mishi dakin baqi maza,zan aiko yarinye ta kawo masa ruwa"

"To hajiya" ya fada yana juyawa da hanzari

"Hajiya bansan waye ba,bansan akwai wanda na sani daya san gidan nan ba"  cikin nuna halin ko in kula da batunta tace

"Baqo ai duk inda yake rahamane,tunda ba maciyin naman mutane bane ai ba abun gudu bane,don baki sanshi ba yanzu tun kafin ki fita sai kice masa ba zakije ba ko ya koma ko kuwa yaya mai gado?,haba bilki aiba halin dattako bane" sai tayi shuru ta sadda kanta qasa,Allah ya sani hakanan takeji fargaba gamida mamakin wanne baqo zatayi a garin da take a matsayin baquwa,ba fita take ba,ba wani gu take zuwa ba,idanma wanine ya ganta ya biyota a ina?,kuma yaushe?,yana daya daga cikin abubuwan da yasa batason zuwa nigeria,ta tabbatar da cewa zata takura ne da zaryar manema,hakan kuma zai zama kamar tunzurine ga magabatanta,zasu sake damuwa ne da sanyata a gaba kan maganar aure,wanda ita kuma sam bata shiryawa hakan ba.       Tanaji hajiyan ta saka yarinye mai aikinta ta hada ruwa da lemuka harda dambun kaza ta fita kaiwa,daidai sannan hajiyan ta sake cewa

"Tashi ki daure ki leqa" bata musa ba ta miqe jiki a salube,ta shiga daki ta dauki wani mayafinta me kauri ta yafa sannan ta fito.      Tana fitowa yarinye na qoqarin komawa sassan hajiyan,data kalleta itama fuskarta a washe fiye da dazu,batace da ita komai ba ta wuce itama yarinyen saita wuce da saurinta kuwa.        Zata giftasu amatu taji kukan amatun,saita tsaya ta qarasa wajen tana tambayarta meya faru,ashe bigewa tayi da keken ta kurje hannunta,ta kama hannun ta duba,sai taga kujewar ba wani mai yawa bane rakine irin na amatu,wanke mata wajen tayi da ruwa tace taje wajen hajiya akwai robb ta shafa mata tabarsu a nan ta wuce.        Shaqar farko data yiwa iskar dake kai kawo bakin qofar falon taji gabanta ya yanke ya fadi,qamshi wani turare daya zama sananne a wajenta ke tashi,saidai kuma tako ta ina zuciyarta na gaya mata babu ta yadda wanda ta sani asalin mamallakin turaren ya iya riskarta a nan,don haka saita dake zuciyarta ta shiga cikin.      Idanunta basa iya ganin kowa a dakin,saidai kuma hancinta na jiye mata qamshin sosai fiye da daxu,kamar ma mai turaren na gab da ita.      Data gama dube dubenta bata ga kowa ba saita juya da niyyar ficewa ta koma inda ta fito,karab sukayi gware,taja baya da sauri numfashinta na niyyar qwace mata,sai data daidaitashi sannan takai dubanta gareshi.       Yana tsaye bayanta dab da ita harde da hannayensa ya zuba mata idanu yana qare mata kallo,ranta ya baci ganin yadda yake binta da kallo kamar ya samu majigi,taja dogon tsakin daya sanyashi dawowa hayyacinsa,saita durfafi qofa da hanzari zata fice.         Ina!,ta riga data makaro,don kuwa tuni yakai mata tattausar cafka,yayi kuwa nasarar danqota,ba tare da bata lokaci ba ya janyota zuwa cikin jikinsa ya lullubeta da kyakkyawan yalwataccen qirjinsa ta hanyar runguma.       Ajiyar zuciya yaketa saukewa ajejjere kamar wanda ya farfado daga dogon suma,sam bai damu da hayaniya dukan qirji da qoqarin tureshin da taketa famanyi ba,duk sanda ya saki ajiyar zuciyar yanakanji qirjinsa ya rage nauyi,duk sanda ya tuna itace rungume a qirjinsa sai yaji kamar bashi da wani sauran matsala a rayuwarshi,saida yayi mai isarsa,har cikin ruhinshi yaji cewa ya gamsu sannan ya sassauta riqon da yayi matan yana duban tsakiyar qwayar idanunta.     "Sai yaushe princess,har sai yaushe sannan xaki bani dama?,dama guda daya da nake buqata daga gurinki,wadda zata iya bani lokaci da zan warware miki komai" ya fada da wata iriyar lallausar murya dake cike da bege wanda ya taba sassan jiki zuwa ruhi,cikin fusata dai da qoqarin qwace kanta har yanzu tace dashi

"Baka da wannan damar,ba kuma zaka samu ba,ka sakeni nace ka sakeni!" Ta fada a tsawace,sake riqonta yayi sosai fiye da dazun,kai kace ce masa tayi riqeni,sosai ta fahimci cewa da gaske yake bazai saketa din ba,saboda haka tace

"Ba yaranka kakeson gani ba?,su kazo gani?,to sakeni na turo maka su" ta fada a fadace sosai,saiya saki wani irin lallausan murmushi dakan wuce da zuciyar 'yammata lokaci guda,ya kuma girgixa kai

"Ba yarana kadai ba,harke ina da buqata,ina da buqatar ganinki,ina da buqatar zama dake,ina da buqatar rayuwa dake,kafin sannan kuma ina buqatar tattaunawa dake,wanda tattaunawar ita zata kawo makomar rayuwar yaranmu"

"Makoma!,makoma kace?,makomar banza da wofi?,ku baku tuna ba?,bakuyi tunanin cewa ina makomarsu ba?,yaya makomarsu zata kasance,su waye zasu zama,duka sai yanzu kake wannan maganar?,ni bakuyi tunanin tawa makomar ba,saboda ba uwace ta haifeni ba,nidin ba mutum bace?,me zan koma me zaya sameni dukka baku damu ba!,ka sakeni malam" ta qarashe maganar launin fuskarta yana sauyawa,hakanan fushinta na qara fitowa qarara har cikin idanunta.     Wani riqo yayi mata sosai yana dan girgizata

"Na yarda bilqess,na yarda da komai kika ce an miko an mikin,kuma ya cancan ci kiyi komai din matuqar zaki huce,amma ki fuskaceni da farko mana".      So take ya fuskanceta kamar yadda yakeso ta fuskanci shi,amma ta lura babu niyya ko alamun hakan tattare dashi,kuka kuma take da buqatar yi saboda yadda takeji zuciyarta na cunkushe mata tare da tuna mata wasu abubuwa masu nauyi da suka taba wanzuwa tsakaninsu,don haka saita sulale ta tsakanin hannayensa tayi qasa kawai,kana ta fice daga tsakiyarshi ta miqe kuma tayi gaba da sauri.        Tana fita daga dakin sukayi kacibus da yarinye

"Maman 'yan biyu,hajiya tace ya shigo su gaisa mana" bata tanka ta ba face gaba da tayi abinta,tana da tabbacin taje ta bawa hajiyan labarin cewa ga babansu amatu ne,don duk wanda ya ganshin basai ya tambayeta ba yake gane wayeshi.      Da kallo yarinye ta bita harta bace tana tunanin kodai bata jita ba,sai kawai ita din tayi gaba zuwa falon don ta sanar masa.      Yana tsaye idanunshi a rufe ya daga kanshi yana kallon sama,ya zuba hannayensa dukka cikin aljihunsa,da alama wani tunani yake me cin rai yaji sallamarta,saiya buda idanunsa a hankali ya zubesu akanta,ta duqa cikin girmamawa,kwarjininsa na dukanta 

"Hajiya tace ka qaraso ciki ku gaisa" a nutse ya gyada kanshi,hakanan yaji abun ya masa dadi,don haka babu musu,tanayin gaba yabi bayanta.       A hankali yake takawa yana tattauna zancan cikin ranshi,baiga wasu alamu dake nuna sakkowarta ba ko kadan,yana jin zaiyi qundumbala ne kawai ya sake tunkarar mai martaba,yayi masa dukkan hukuncin da zaiyi masa matuqar zai gyaro lamarin ta dawo cikin rayuwarsa ita da yaransa.     A bakin sassan ya samesun kuwa suna wasansu,saidai amatu na langabe zaune waje daya tun ciwon dazu,dukkaninsu sun ganeshi,kusan tare suka nufoshi kamar yadda shima ya nufesu cikin farinciki,yana jin wani dadi yana ratsashi,gaba dayansu ya rungumesu cikin jikinsa yana kissing dinsu,yayin da kowannensu ya soma cikashi da surutu yana son mishi hira.   Ko daya baiji nauyin da suke dashi ba ya daukesu cak,daya a hannun dama daya a hannun hagu haka ya nufi sashen hajiya dasu amatu na nuna mishi ciwonta a shagwabe,ya kuwa biye mata yana sakw zuzuta ciwon,badon nuna gwaninta ko wani abuba,a'ah,har cikin ranshi yakejin ciwon shima kamar a jikinsa yake a haka suka qarasa sashen,yace bari su fito zaya kaita asibiti.


     Cikin jin dadi hajiya ta tarbeshi,shima ya gaidata cikin girmamawa,kai bakace shine wannan azeez din ba d'a ga sarkin kaisa kuma shahararren dan kasuwa na duniya ba.      Babu yadda hajiyan batayi da bilkisu ba ta fito amma taqiya,data aika yarinye saita cema hajiyan kanta ke ciwo,shi yasan kwanan zancen,don haka bai tsawwala da yawa ba yace zai wuce yakai amatu clinic a wanke mata ciwo,kama baki hajiya tayi sannan tace

"Saboda taya bera bari wannan dan ciwon za'a kai ta ganin likita,rakine kawai irin nata,shi yasa kishinsu ya kasa daidaituwa da kishiyarta" wato mama mahaifiyar abbaa.      Murmushi kawai yayi,ya fuskanci tsohuwar tana da yawan barkwanci da raha,hakan sai yaji yayi masa

"Zamuje mu dawo hajiya,wataqil yana mata zugi ne" hajiyan na musu tsiya haka suka fice.     Suna fitowa harabar gidan abba da mahaifinsa dr maisara suna shigowa gidan,da qafa suka shigo da alama sun faka motarsu ne a wajen gidan,duk yadda akai kuma ba zasu jima ba zasu sake fita ne.      Dukkansu idanunsu akan azeez,ga abbaa tuni ya fahimci komai ganinsa dauke da yaran,ga kuma kama ta zahiri nan dake bayyana kanta,yayin da dr maisara ke kallonshi cikin mamakin kamannin da yake gani zahiri game dashi da kuma yaran.     Sun cimmashi don haka ya qarasa garesu suka gaisa kana ya koma inda yaran suke.      Dukkansu yaran ya zuba cikin lafiyayyar motarsa,ya tada ya fice daga gidan.       Yawo sukayi sosai dasu bayan anwakewa amatu ciwon,manyan wuraren shaqatawa dake garin,saida kowannensu ya gaji tubus sannan suka dawo gida.       Ciki dukkansu suka shiga harda su abdul din,don tuni amatu ta soma gyangyadi saboda gajiya,saiya haye saman motarshi kawai ya zauna shuru yana kallon sararin samaniya wadda ta cika da taurari da kuma farin wata daya kai rabi saboda tuni kwanakinsa sunyi nisa,sam sai yaji baison barin qofar gidan,kamar ya dawwama anan,har zuwa sanda zatace ta yafe masa.      Shuru anguwar,cikin layinma gaba daya shi daya ne zaune,har zuwa sanda wata mota ta shigo layin da full light dinta,amma data matso dab dashi sai aka rage hasken motar.      Saida suka giftashi sannan ya gane su waye a ciki,bai damu ba yaci gaba da zamanshi har suka shige cikin gidan.      "Wannan yaron waye?,kamar nasan fuskarshi" dr maisara ya tambayi abbaa sanda yake qoqarin faka motar

"Zaka iya saninsa,sanannen dan kasuwa ne,sannan kuma babansu amatu ne,tsohon mijin bilkisun zuhriyya"

"Eh qwarai,amma ina fata lafiya ko?"

"Nafi zaton bikon matarsa yake,saboda zuhriyya ta soma yimin maganar,to bamu gama ba wannan tafiyar ta taso"

"Haka ake bikon?" Dr maisara ya fada yana duban abbaa,shima abban saiya kalleshi don bai fahimci me yake nufi ba,duk da yasan mahaifin nasa baisan komai kan auren bilkisun na baya ba

"Eh...to ai banga wani support da kuke bashi ba,kada kacemin daga kai har zuhriyyan goyon bayan diyarku kuke?" Ya san mahaifin nasa sarai,yasan dattakonshi sak irin na mahaifiyarsa fatsima,babu abinda sukaqi jini irin lalacewar aure,dole ya yiwa mahaifin nasa bayani,idan ba haka ba yanzun dukkan laifin zai koma kansu.     A nutse yaw warwarewa mahaifin nasa bakin gwargwadon abinda yasani yakuma san zai fahimta,shuru dr maisara yayi yana jinjina lamarin,kana ya sauke nannauyar ajiyar zuciya

"Tabbas ko shakka bana yi,sarki abdallah baida masaniya kan faruwar hakan,bada kuma yawunsa aka aikata komai ba,na sanshi tun kafin ya zama sarki,nasan halayensa sarai,amma wannan magana ce dake da buqatar nazari....zamuyi magana in sha Allahu,bai kamata a qyale lamarin haka ba"

"To baba,Allah ya tashemu lafiya"

"Amin" ya amsa yana yunqurin fita.    Har ya sanya qafarsa waje sai kuma ya waiwayo

"Kar a kuma hanashi ganin yaranshi,domin su babu ruwansu dama duk abinda ya faru,kuma suna da haqqi saman wuyanshi na mahaifinsu"

"Tuni dama zuhriyya take turasu idan yazo,in sha Allah kuma za'a ci gaba da hakan" daga wannan dr maisara ya fice yana jujjuya batun cikin ranshi.    Koda abbaa yafito sashen hajiya ya nufa,don yau duka bai samu ya shiga ya gaidata ba.     Daidai lokacin da bilkisu anty zuhriyya da hajiya ke zaune dukka a falon hajiyar,amatu na kwance saman cinyar bilkisun.      .      Magana hajiyan take cikin siyasa akan abdul'azeez din,yadda take ka kirkinsa da cikar kamalarsa,saidai sam bilkisu jin maganar take kamar ta dora hannu aka tayita zunduma ihu,kamar tacewa hajiya tayi shuru,amma hakanan ta haqura ta rufe bakinta tayi mata kawaici.      Bayan sun gama gaisawa da abbaa ne yace

"Yaron nan yarima muka samu nida baba zaune qofar gida saman mota,baba ke fadan an hanashi ganin yara ne,daga yau yace kada a kuma hanashi ganinsu duk sadda yazo"

"Shine dai dai ai,ina ruwan yara da rigimarsu" hajiya ta cafe zancan

"Ai dama ba'a hanashi ba abbaa" anty zuhriyya ta amsa tana kallonshi

"Ni wallahi da zaku nuna halin dattako,da yazo koma meye an zauna an sulhunta,darajar mace fa dakin mijinta,darajar 'ya'ya gidan ubansu,sam agolanci baida dadi,duk yadda za'a kula da yaro kuwa".       Tsam bilkisu ta miqe tana saba amatu a kafadarta,sabida zancan bai zauna mata ba,sam sam ba irin aurenta akewa wannan gatan na zaman sulhu ba,hasalima batajin hajiya tasan ainihin yadda auren da rabuwar ta kasance,shi yasa ta fadi hakan,tadai san sanda aka sakota da cikinsu amatu,saita wuce kawai dakinta,hajiyan ta bita da kallo harta bace sannan ta dubi anty zuhriyya

"Kada su sake ku biyewa shirmenta,shi aure rai gareshi,koda kashe juna kukayi aka dawo idan da rabo sai an koma,mutuwar aure na jawo tozartar yara da tabarbarewar al'umma matuqar ba'a kwai wani qaqqwaqwaran dalili da zai janyo hakan ba"

"Hakane" abbaa ya fada daga nan ya mata sallama ya wuce,anty zuhriyya ta miqe ta biyo bayanshi.   ¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶      Tun randa abun ya wakana tsakanin fulani adama fulani saratu da hajja fauziyya suka kasa zaune suka kasa tsaye,kowanne yanason sanin ainihin abinda ya wakana,yana son yasan ainihin labarin,shin da gaske matarshi ce?,idan matarshi ce yaushe akayi auren?,maimartaba ne ya daura masa auren yakuma boye ku kuwa?,dukka har yanzu babu wanda yasan taqamaimen asalin maganar,gashi mai martaba gaba daya ya musu dif,kai kace babu wani zance irin hakan daya taba faruwa cikin masarautar,gaba daya ya shiga sha'aninsa da sabgoginsa,ko a fuska basuga wata alama ta komai ba tattare dashi,har gwara fulani aisha sun samu labarin ta fada yanayin damuwa,amma banda wannan itama basu samu komai ba basu kuma samu wani bayani ba sabanin hakan.      Ta gefan kamal shima hankalinsa na a tashe ne,kalmar matata ce din da azeez ya fada na neman tarwatsa shirinsa,indai ya tabbata kenan tilas ya haqura da ita?,ya sake rasata kenan duk burin da yaci a kanta ya tarwatse?,wannan tunanin shima ya saka masa damuwa,ya kuma hanashi sakat.


 

    ¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶      Kamar yadda a cikin wadan nan lokuttan suka koma shi da ita kamar wasu baqin juna,misalin qarfe goma na safiya,tana tsaye daga gefansa yana shiryawa cikin irin suturar da yake sakawa idan zaiyi zaman fada.      A lokuttan baya itake tayashi shiryawa,ta qware tsaf ta wannan fannin fiye da kowacce mace cikin matanshi,wani lokaci har bai ganin kyan shigarshi idan ba ita ta tayashi shiryawar ba,saidai a yanzun dare daya ya soke wannan,duk lokacin data yunqura zata tallafa mishi yakan dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu,tun tana qoqarin gwadawa harta haqura,daya daga cikin horon da yake mata kenan wanda ke matuqar ci mata rai,shekaru kusan arba'in komai laifin da zata masa bai taba yi mata abu makamancin haka ba.       Yanzun ma tana tsaye ya gama shiryawa,da sauri ta dauki cup dinsa na tatacciyar madarar shanu data tafasa masa da citta da kununfari ta miqa masa,saidai kamar kullum yauma hannu ya daga mata kawai,kana ya soma takawa zai fice.        Kasa jurewa tayi,yau haqurinta da dakiyarta sun qare,saita saki kofin madarar ya tarwatse a nan wanda hakan ya sanyashi juyowa,har a jikinsa yaji fashewar abun da yadda take tsallakesu,amma saiya dake ya basar,itama bata damu da wannan ba ta tsallake cikin hanzari ta isa inda yake.      Hannayensa ta kama gam cikin nata,sai kawai ta fashe da kuka,baice mata uffan ba,kamar yadda bai dakatar da ita ba har sai datayi mai isarta

"Duk hukuncin da zakayimin ka yimin don Allah,amma banason wannan shurun,wannan halin ko inkula din don Allah" a shashance yace

"Wanne laifi kikayi kuma?,kinyi wani abune dama?" Kuka ta kuma saki tana girgiza kai

"Kada kace haka don Allah,kada kace haka".       Duk yadda yaso ture tausayinta daga ranshi amma hakan yaci tura,bazai iya tuna sanda ya ganta tana kuka haka ba,duk da hakan ya riga ya qudirta dole ya hukuntata yadda zataji a jikinta,bai taba tunanin zata tafka ta'asa mai girma haka ba,don bashi ba ba yarima ba,yarinyar data aikatawa abun,yanason ta gamsu a karan kanta ta cutar da ita,yanason ta gamsu cewa ya kamata ta nemeta,ya kamata ta nemi afuwarta,shi kansa yariman yana da laifi cikin abun,kuma koshi din bazai qyaleshi ba,saiya hukuntashi daidai da laifinsa

"a'ah,meye na damuwa kuma?,bayan kin aikata abinda ya dace ne?,kin isa kiyi shawara da kanki fa kuma ki yanke hukunci tunda shekarunki sunkai,kuma komai ya tafi daidai,meye na damuwa kuma?".     Shuru tayi tana sheshsheqar kuka,sai ya zame hannunsa kawai yayi gaba yana juyo sautin kukanta,duk da yadda zuciyarsa ke masa nauyi dajin kukan nata.       Yana saka qafarshi falonshi ya tadda fulani adama zaune gefen kujera,ta caba ado sosai har abun yaso bashi mamaki.       Tana ganin fitowarsa ta miqe cikin girmamawa tana sakin murmushi

"Allah ya baka yawan rai,Allah ya tsare mana kai,ya qara lafiya da nisan kwana,barka da fitowa takawa" ta fada cikin daga murya,don tana da masaniyar aisha na cikin dakin,murmushi ya saka cikin sarauta,yana daga tsaye don baison ya zauna ta bata mishi lokaci

"Ya akayi adama?"

"Barka da warhaka"

"Barka kadai,kun tashi lafiya?"

"Lafiya qalau ranka ya dade,zuwa nayi dama in gaisheka,jiya da yau duka bamu samu ganinka ba,gashi ka barmu cikin alhini kwana biyu"

"Lafiya alhmdlh....alhinin me fa?" Sosai ta sauya fuskarta ta maida kalar jimami,kanta a qasa ta girgizashi

"Abinda ya faru da yarimanmu,kullum cikin zullumi muke kwana,muna fata Allah yasa ba wani abu mara kyau ya aikata ba,gashi babu wanda ka yiwa cikakken bayani a cikinmu Allah ya baka nasara" kanshi ya dauke don ya jima da soma karantar adaman,musamman lokacin daya matsa bincike kan daga wannw saqo hotunan suke fitowa,sai suka lura sunfi fitowa daga nahiyar da fulani adaman take,saiya soma takawa yana yin gaba kafin ya bata amsa

"Awwnnn....ashe....na mance ma wani abu ya faru,kuyu baccinku dakyau ku daina tunani,ba wani big issue bane ba,kusa a ranku kaman ba'ayi ba"

"Amma muna buqatar qarin bayanin da zai kwantar mana da hankali,ko 'yar uwarka bakaga yadda ta damu ba" saiya juyo yana dubanta

"Kije ki musu bayanin dana miki,inaga ga ishi kowa a cikinsu"

"In sha Allahu ranka ya dade" ta fada tana sunkui da idanunta ganin yadda ya tsareta da ido,daga haka ya juya ya fita cikin jama'arsa.       Da baya da baya fulani aisha ta koma ta zauna bayan ta gama jin duk abinda ya wakana tsakanin fulani adama da me martaba,hannunta tasa tana toshe bakinta da kuka keson qwace mata karo na biyu a ranar yau,duk da taurin rai da dakiyarta,a haka kamar yayi fushi da ita,amma kuma a fakaice ta wani bangaren yana qoqarin lulluba asirinta,tabbas talk sani tsakaninta dashi wata irin soyayya ce min indillahi tun quruciya,bata taba kuma zaton qiyayyar su adaman a kanta takai har hakan ba,tasan suna sone suji komai,su samu abunda zasu qarasa tarwatsa ta,saita dafe kanta da hannu biyu tana ambaton sunan Allah.


      Ranar ya jima sosai a fada,wanda kafin ya tashi yasa aka shaidawa mama sodangi yana buqatar ganinta bayan zaman fada.       Zama sukayi daga shi sai ita,ba tare da sanin kowa ba,ya samu dukkan bayanan da yake da buqata kafin ya sallameta,yayi shuru abun na sake qona mishi rai,aisha ta mishi ba zata,ta kuma bashi mamaki,badon Allah ya tsare ba shi kadai yasan yawa da girman abinda zai faru,a hakanma yana ji a jikinsa tsarewarsa ce ta kawo lamarin ya tsaya iya haka,ya miqe ya shige ciki yana sake wassafa hukunci da qarshe da zai yanke kan lamarin.    ¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶      Bayan ya tabbatar da tahowarta qasar kaisa a ranar,saiya sauya akalar motarshi zuwa masaukinsa,ya dauki dukkan abinda zai dauka shima ya nufi qasar kaisa,ya nufeta da qarfin gwiwa da tarin karsashin zuwa ya samu mai martaba kanshi tsaye,ya gaji da wannan walagigin haka,ya gaji da yadda take wajigashi tana wasa da hankalinsa duk yadda taso,yana da buqatar ayita ta qare kawai.          Sanda ya isa bai nemi kowa ba,hakanan bai shiga masarauta ba kai tsaye,hakanan ya samu kanshi da ra'ayin sauka a village(wani gida ne nashi da aka yiwa gini na musamman,gini irin na qauye na gargajiya saidai kuma a zamanance,dukkan abinda ke cikin gidan na gargajiya ne,hatta da dakuna na bukka ne,saidai kuma ciyawar da turakunan da akayi amfani dasu a zamanance ne,hakanan katangun duka na qasa ne bulon qasa ne,saidai lailayayye sosai wanda kana gani kasan an zamanantar dashi,hakan kitchen din dake cikin gidan,kwanukan girki na qasa,kwanukan abunci na akushi ne,gadon qarfe mai rumfa amma na zamani,kawai qoramu da aka gyara wajen,kai kace ire iren na qauye ne,akwai randuna na qasa na ruwa mafitai tabarmin kaba da sauransu,duk da awani wajen tiles akayi aka saka carfet,sannan dole ta sanya aka saka ac saboda sake qawata wajen da bada nishadin xama.      Gidane daya dauki hankali matuqa saboda yadda aka tsarashi,afnan na bala'in son gidan tun lokacin da aka kammalashi,saidai tasan babu fuska bare tace zataje,gidane na musamman a wajen maishi shi karan kanshi,yanayin wajen na qawatar dashi,saboda yadda ya cika da tsirrai da shuke shuke da ko yaushe sukan sanya gidan ya kasance luf luf cikin sanyi da qamshin qasa mai dadi,yawan tsirran ya gayyato tsuntsaye kala kala,wadanda suka kama bishiyoyin gidan kowacce na rera salon nata kukan ko waqar,idan ka shiga gidan kaida kanka kasan na musamman ne.        Ya jima zaune a daya daga cikin falukan gidan bayan ya rage kayan jikinsa,saiya jawo wayarsa ya soma neman layin safwa,saboda kwana biyu gaba daya baida nutsuwar kiranta,hakanan itama baiga nata kiran ba,bai sani ba tana kaisa din ko ta qara gaba yadda ta saba,a halin yanzun yana da buqarta kusa dashi koda ba zata tsinana masa komai ba,amma a qalla zai dinga jin motsin mutum.     Sam sam sai wayar tata taqi shiga,ya gwada kusan sau uku amma ana gaya mishi layin a kashe yake,yayi mamaki qwarai,saiya gwada ta mamanta itama taqi tafiya,don haka ya sauya shawara yayi kiran afnan.       "Barka da warhaka yaya...." Ta fada cikin nuna girmamawa

"Yauwa....ko safwa tayi magana daku zata wani wajene?" Mamaki saiya cikata,itakam tana mamakin aure irin nasu,safwa ko yaushe jinta take kamar qaramar yarinya,ta kasa gane ainihin ma'anar aure,ta kasa gane cewa ta girma,saita yita yin abu kamar yau aka haifeta,shima ta nashi fannin ya rungumi kasuwancinsa gaban komai,ibadarsa ce kawai yake sakawa gaban kasuwanci,sam kamar zaman auren nasu bai dameshi ba

"Am asking you kinma mutane shuru?" Ya fada a dan fadace,da alama ranshin a bace yake

"Bandai sani ba,amma dai ganina na qarshe da ita....tazo wajen ammi bata sami ganinta ba,tace na gaya mata zata yiwa daddynta rakiya zashi yearly cheakup dinsa" daga haka bai sake jiran jin komai daga bakinta ba ya katse kiran.        Sai yaji ranshi ya baci sosai wannan karon,ya kamata ya dauki mataki hakanan,aure ba abun wasa bane,hakanan shiba lusarin namiji bane,bazai zauna mace ta soma haihuwa dashi ba amma har yau sakarya bace,batasan ciwon kanta batasan ma'anar zaman aure ba,atleast koda zata bai kamata ta wuce haka ziqau kaman ita ke zaman kanta ba,tunda matsalolin nan suka sanyashi gaba bai sakata a idonshi ba,amma yasan ya tsare dukkan wani haqqinta.      Idanunsa na alumshe yana wassafa matsalolinsa guda biyu wata sassanyar busar sarewar sarauta ta ratsa falon,alamun anason magana dashi,idanunsa na a rufen ya bada umarni a shigo din,daya daga cikin amintattun bahi na musamman da ya saka aka turo mishi suke kula da gida ya bayyana,cikin shiga ta musamman,kaman yadda yake kamar sutura ga duk wanda ke aiki cikin village

"Allah ya taimakeka,ya baka yawan rai.....yallabai abdulrashid ne yake neman iso" da hannu still dai ba tare daya buda idanunsa ba ya mishi nuni daya barshi ya shigo.      Sallamar abdulrashid ita ta sanyashi bude idanunsa,ya zuba mishi idanu kamar yadda shima ya zuba masa nasa idanun yana kallonshi harya samu waje ya zauna.       Tashi abdul'azeez yayi sosai ya zauna har yanzun idanunsa kan abdulrashid daya lura yana masa kallon qurilla,ya buda baki zaiyi magana dariyar da abdulrashid ya sanya ita ta katseshi daga fadin abinda yayi niyya,cikin mamaki yake duban abdulrashid,daga baya daya lura akwai shaqiyanci cikin dariyar tasa,sai kawai ya sake maida idanunsa ya kulle,ya kuma koma ya kwanta kamar yadda yake a dazun,har yayi dariyarsa ya qoshi don kansa sannan ya soma magana

"Mai firgitarwa yau shi ake firgitarwa?,lallai dara taci gida,inama zanga dukka matan da kake zame musu xaki idan sun ganka,jikinsu ke tsuma saboda kwarjininka,soyayyarka ke hanasu bacci da sukuni,suke kasa kallon fuskarka,yau suzo....ga wata yarinya guda daya ta birkita maka tunani...ta hana rayuwarka sukuni,ta hanaka sakat....ban taba zaton kai rago bane yarima sai yanzu,ban tsammaci cewa kai rago bane sai akan bilkisu,kaga yadda ka birkice ka hautsine?,idan na gani da kyau ma kamar ramewa naga kayi hakane?",ya qarashe ta sigar tambaya.       Sai daya kai aya sannan azeez ya bude dukka idanunsa akan abdulrashid,cikin tattausan muryarsan nan da lafuzzansa masu kama da ana jera masa su yace

"Ragon maza nake akanta,hakanan banda wayo ko wata fikira indai akanta ne,jarumi nake kuma zaki tsakanin maza 'yan uwana,mai furgita duk yarinyar data nemi shiga gonata ko hurumina ba tare da yarda ko amincewata ba" saiya tashi ya zauna sosai bayan yakai qarshen xancan,idanunsa da suka jajjanye duka akan abdulrashid,hannunshi daya ya dora saman qirjinsa bayan ya dunquleshi,daidai saitin zuciyarsa

"Kasan me nakeji anan abdulrashid?,kasan kullum da yadda nake bacci?,kasan yadda zuciyata ke zugi?,amma sam taqi fahimtar haka,taqi ta bani dama,taqi ta gane cewa bayaga mahaifiyata itace mace ta biyu da nake tsananin so da qauna,macen da bazan iya sake jure rashinta ba,me yasa ba zata fahimta ba?" Ya fada a hankali launin qwayar idanunsa na sauyawa.      Nannauyar ajiyar zuciya abdulrashid ya saki,tausayin azeez din yaji yana shigarsa,lallai dukkan abinda zai saka azeez din ya zauna yaba tona asirin zuciyarsa haka ba qarami bane,tunda suke tsahon tasowarsu tare,bai taba ganin yana yiwa wani abu irin wannan son ba,jarumine na gasken gaske,lallai ya cancanci a tausaya mishi.     Bai ankara ba yaga ya miqe

"Zanje na samu me martaba,koda zaiyi gunduwa gunduwa da namana na roqeshi ya saita lamarin,shirunsa din nan abdul nasan yana nufin abubuwa ne da dama....ina zuwa" ya fada yana shigewa ciki inda zai sadashi da 'yar qoramar da aka tanada saboda wanka wadda tayi shige da swimming pool amma a gargajiyance.    ¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶      Yayi mamaki lokacin daya ganshi cikin hakimai a fada,ya saje cikinsu cikin ire iren shigarsu shima,saidai ya dake ya kuma nuna kamar bai ganshi din ba.      Duk tsahon awannin da aka dauka din yana nan tare dasu bai motsa ba,har zuwa sanda aka gaman zaman,sarki ya miqe yayi ciki yana biye dashi,sauran 'yan majalisar sarki suma kowa ya wuce uzurin gabanshi.        Daga shi sai me martaba ya rage,har zuwa lokacin yana biye dashi ba tare da yace komai ba.       Waiwayowa yayi sanda yake niyyar shigewa turakarsa,suka hada idanu da azeez,a ranar sai yaji mahaifin nasa ya masa kwarjini matuqa kamar sauran mutane,saiya sadda kanshi qasa

"Lafiya dai ko?,inason na shiga ciki na huta" me martaba ya fada yana duban azeez din,duk da yasan da walakin goro a miya.       Zubewa yayi nan gabanshi saman gwiwoyinsa,cikin sanyi da matuqar nadama ya soma neman alfarma a wajensa gameda lamarin bilkisun,tare da alqawarin amsar dukka hukuncin da yace ya yanke a kanshi.       Shuru ya masa har ya kammala sannan yayi gyaran murya

"Saboda ni ka daukeni qaramin mutum ko?,bayan mutuncina da kuka gama zubdawa da saidawa a idanun al'ummata yanxun kakeso na sake zuwa na ɓarar da sauran da hannuna?,ai abdul'azeez ta inda aka hau ta nan ake sauka...kaje ka samu uwarka yadda kuka qulla ku warware,kasan kana sonta amma ka bari akayi wannan barnar da kai?"

"Afuwarka da yafiyarka nake nema,ba don ni ba,kodon albarkacin 'yan biyun dake tsakaninmu"

"Yan biyu!" Mai martaba ya furta ba tare daya shirya ba,ya kuma sake fadin

"Kana nufin akwai zuriyya tsakaninku?" Kai ya gyada yana sake tabbatar masa,shuru me martaba yayi bayan ya lalubi kujera ya zauna,kyawawan mintuna biyar bai iya cewa komai ba,daga bisani ya miqe bai cewa azeez komai ba ya wuce ciki ya barshi a nan.        Daren ranar gaba daya sarki abdallah ya qarar dashi ne wajen nazari da kuma neman mafita wadd zata zama adalci sulhu kuma alkhairi a gareshi da ahalinsa.       Jikinsa ya bashi tabbas wannan lamarin jarrabawarshi daga ubangijinsa,ya jarrabeshi kan macen da tafiso cikin matansa,da yaron da yafiso cikin yaransa,duk da tarin qoqarin adalci da biyewar da yake,hakan ya sanya daga shi sai ubangijinsa ne kawai sukasan da wannan sirrin.       Kwanaki biyu ya dauka qwarara dukkan bincikensa ya kammala a asirce,duk abibda azeez din ya fadi babu qarya a cikinsa,hakan ya kawo masa sassauci kan hukunci da matakin da yayi niyyar dauka a kansa.
       A kwana na ukun bai samu sassauci ba sai daya ganshi kan hanyar gidan malam bilyaminu da kanshi ba aike ba,cikin mota qwaya daya mai baqaqen gilashi,dagashi sai amintattunsa mutum uku,cikin salo na bad da kama,don baka isa kace sarkin kaisa bane a motar.*GIDAN MALAM BILYAMIN*      Tub dawowarsu kaisa din ya zamana kusan kullum yaran na wajen malam bilya,da hauwa'u wadda har kukan dadi mlm bilyamin din yayi da dawowarta cikin 'yan uwanta,domin yayi cigiyar yayi neman har ya gaji ya haqura,albarka babu irin wadda bai shiwa bilkisu ba,don a yanxun kusan yaranshi har mazan kusan suna gabanshi,su mazan biyu daga cikinsu suke kula mishi da shagunansa,tunda a yanzun shi babu damar fita kamar daa,jikin yaqi dadi,ciwo yaqi barinsa,yau da lafiya gobe babu.       Sau tari yakan zauna ya zubda hawayensa idan yaga yadda Allah yayi dashi,wato duk abinda kaga Allah ya hanaka mai yiwuwa akwai hikimarsa cikin hakan,me yiwuwa ya baka wani abun madadinsa wanda kai bakasan da hakan ba.         A da yana kukan talauci da babu,yana ganin Allah ya hanashi dukiya,ashe ya masa musayarta ne da cikakkiyar lafiya,daga baya ya amshe lafiyar ya barshi da kudin,wanda kudin gashinan sun gaza siya masa lafiyar,ga kudin da zaici duk abinda yakeso,zai saka duk suturar da yakeso amma rashin cikakkiyar kafiya duka ya hana wannan,saidai ya kalla iyalansa da kuma wasu a waje suci,ashe babu arziqin da yakai na lafiya.       Cikin wannan jimamin da alhinin ya kama mama ladida sabuwar amaryarsa sun hada kai suna kitsa yadda zasu masa gagarumar sata,saboda a cewarsu idan ya mutu ba zasu tsira da komai ba bayaga tuminin takaba,umma katti da 'ya'yansa su zasu wawashe komai.      Wannan ma ya tashi hankalinsa qwarai,ya dinga kuka bayan ya sallami kowaccensu da saki bibbiyu,saiya dinga tuno rayuwarsa da maimunatu mahaifiyar bikisu,ta fishi kyau,ta fishi nasaba ta fishi dukiya,amma ta yarda,ta zabi ta rayu dashi badon yana da komai koya mallaki komai ba,ta ajjiye dukkan wasu qualities nata,ta haqura da rayuwar gidanshi,harta mutu bai ajewa ba bai bawa wani ajiya ba barema ta saka rai,sai gashi yanzu wadanda ya tsincesu sama taka suna neman kassarashi ta sandin dukiyar da aka samu ta hanyar diyar maimunatu,dukiyar da ita maimunatun bata dandana ba.       Ashe duk tsiya duk masifa matar babu ba qashin yardawa bace,sabida tunda suke da umma katti bata taba yunqurin gwada hakan a gareshi ba,itadai barta da masifarta da bala'inta,son yaranta ta hana na wani,da nuna mishi yatsa,amma babu wannan mugun qullin a ranta,ranar yayi kusa sosai ya kuma yi nadama,tare da godewa Allah da yaketa haska masa gaskiya tunda sauran lokacinsa.       To a yau din ma kamar sauran ranakun,da kanshi yayi kiran bilkisun yace ta kawo mishi 'yan biyu,ta shirya da kanta,yaran kuwa suma sunata murna,don ba qaramin son zuwa gidan suke ba,saboda yadda kowa ke nan nan dasu,ta shiryasu sosai,tayi musu adon shadda ash,wadda abba ne ya dinka musu su biyu kawai.      Itakam babu abinda zata cewa Allah sai godiya,kowa son yaran yake,nuna musu qauna da kulawa yake.       Da kanta ta kawosu,ta zauna suka sha hira da malam bilya din,sannan ta shiga ciki wajen 'yan uwanta suka sha hirarsu suma bayan ta gaida umma katti.      Hirarsu suke gwanin sha'awa,duk sanda ta daga kai ta kalli yan uwannata taga yadda rayuwa ta musu kyau hakan na sake faranta mata,a yanzun haka zancan auren auren hannatu ma akeyi.      Awa biyu kawai tayi tatafi tabarosu acan,tasan akwai masu kawosu gida,idanma sun kwana duka ba damuwa,don tasan mawuyacine su qyalesu su dawo a yau din.       Bata rufa awa guda da tafiya ba motar maimartaba ta iso layin,a daidai qofar gidan suka faka,yasamu tabbaci yana nan,saboda a yadda aka bincika masa ba kasafai yakan fita din ba kamar yadda muka sani.


        Su biyu ne rak cikin falon,daga shi sai maimartaba,wanda ko a mafarki malam bilya bai tsammaci zuwanshi har cikin gidanshi ba.     A hankali maimartaba ya sauke ajiyar zuciya kana ya miqawa malam bilya hannu,hannun ya kalla kana ya kalli maimartaba,ya sakar masa murmushi gamida bashi qwarin gwiwa,hakan ya sanya malam bilyan miqa masa hannu sukayi musabaha yana tambayarsa iyali.      Shuru na sakanni ya biyo baya,sannan mai martaba ya soma magana cikin nutsuwa

"Da farko malam bilyaminu....banason ka kalleni da idanun sarki,inason ka kalleni da idanun uba ga mijin 'yarka,sa'annan kuma suruki a wajenka,inaso muyi magana takai tsaye,kowa ya fadi abinda ke zuciyarsa,banason kaji nauyina ko kayimin alfarma" saiya dan tsagaita yana duban malam bilyan sannan ya dora.        "Dani dakai dukkan munsan abinda ya wakana tsakanin yaranmu shekara bakwai baya basai anyi bita ba,saidai nidin shekaru bakwai da suka shude,sun shude ne ba tare da nasan wannan lamarin ba,wanda kuma bansan da wanzuwar tashi ba sai cikin shekarar nan,a shekararnan dinma cikin satin nan,da fari ina mai baka haquri a madadina matata da dana akan wasa da akayi da rayuwar diyarka,tabbas anyi maku abu mafi muni,zalunci cikakke wanda dukkan dan adam din da aka yiwa an cutatawa rayuwarsa,nayi matuqar girgiza dajin labarin da yadda aka wofantar da jinina da yake tattare da diyarka,wanda a yanzun Allah ya rayasu....inajin nauyin magana ta gaba da zan furta,amma kuma dana zauna nayi dogon nazari akai sai naga shine mafita a rayuwar ƴaƴanmugaba daya nida kai da kuma jikokinmu"saiya tsagaita yana sauke numfashi sannan ya dora

"Cikin labarin daya bani ya tabbatar min yarinyar na a matsayin matarsa ne har yau,da farko ban yarda ba na kuma qaryata,saboda ba lamari bane da hankali zaiyi saurin dauka ko ayi amfani dashi ba,amma daga bisani daya gayamin shaidun daya maida matar tasa a gabansu,saina tabbatar da ingancinsu da kuma adalcinsu,amma duk da hakanan ban tsaya a nan ba,sai dana kira kowannensu na tabbatar da cewa haka maganar yake,wanda daya daga cikinsu tana kamar a matsayin uwa a wajensa ne....alfarmar da nake nema a nan ayimin itace,bilkisu ta koma dakinta a matsayin matar abdul'azeez,bayan na tabbatar da nagartar halayenta daga bakin wadda ta zauna da ita,hakan ya alamta min tana daga cikin sahun mata na gari daya kamata a riqe da kyau,rabuwa da ita tamkar tafka wata hasara ce mai girma,hakanan ko babu wannan an cutatar da rayuwarta,babban adalcin da zanyi a yanzu a damar da Allah ya bani shine ta sake komawa a matsayin matarshi,wanda duniya duka zata shaida,shaidawar da a baya bata shaida din ba".       Ba qaramin burgeshi sarki abdallah yayi ba,bai taba zato ko tsammatar haka ba,labarin adalcinsa da sauqin kansa ashe ragewa ake?,inama ace dukka shugabanninmu zasu kasance kamar haka?,inama a ce na sama zai kasance mai tausayi da adalciwa na qasa kamar haka?,tabbas da duniya ta zauna lafiya,da mun rabu da tarin matsaloli da suke addabarmu a yau,ba shakka ya koyi tarin darasi a yau daga sarki abdallahn,wanda yake zaune tare dashi babu wani shamaki,da ace wani zaya shigo baha ga suttutar jikinsa kuma baisan fuskarshi ba.....babu abinda zai hana yace ba sarki bane wannan.      Ajiyar zuciya shima malam bilya ya saki,yana jin kunyar kanshi da kanshi,kowanne uba na gari yakan kauda son zuciyarsa ashe ya zabawa zuri'ar da Allah ya nashi nagartaccen abu da yasan shi dasu zasu kubuta har a gaban Allah,tabbas wannan babban darasine daya sake samu a yau

"Dukkan abinda ka fada na jisu na kuma fahimta,saidai komai bai gudana ba saida gudunmawata da goyon baya na,bawai sunsa qarfi bane sun dauki 'yar,saidai kwadayina da son tara abun duniyata da dukka shi ya janyo hakan,ba shakka nayi nadama,nayi nadama mara iyaka kuma ina kan yinta,ta yadda na dauki yarinya mafi biyayya cikin iyalina na sadaukar da rayuwarta da mutuncinta,yarinyar data fito daga mace mafi soyuwa,nagartacciyar mace daya tamkar da dubu,matar da har yau ban maida kamarta ba,amma kwadayin samun dukiya duka ya rufemin idanu yasa na manta wannan"

"Idan akwai abinda ya kamata ace raina ya baci guda daya ne,ina namen afuwa,naji baqinciki naci kuma alwashin cewa.....daga ranar da aka kore cikin dake jikin maigado,bakai ba....koma waye zayaxo da sunan sunaso daga baya,koma waye yazo da sunan zuri'arsa ne bai isa ya amshesu ba,ciki kuwa harda hukuma.....kai din mutum ne mai girma kuma adali,wanda na tabbatar dama can baka da masaniyar wannan kitimurmurar,zuwanka wannan waje a irin wannan yanayin ya sake tabbatar da kai din waye,na yafe iya haqqina,amma akwai abu daya..." Saiya dakata shima yana gyara zamanshi.        "Daga wancan lokacin dana gane kurena,na gane gangancin da karan tsayen da na yiwa rayuwarta,saina dauki alqawari akaran kaina,sa'annan na dauki alqawari tsakanina da ubangiji na cewa....bazan sake yanke hukunci irin wannan cikin rayuwarta ba har na koma ga Allah ba tare da amincewa ko lamuncewarta ba,bazan sake yanke hukunci irin wannan kan rayuwar duka yarana ba,koda yara maza bare matan....saboda haka,a yanzu bani data cewa,sai abinda ta zaba a karan kanta" murmushi mai martaba yayi yana jinjina kai

"Ai koda ka amince surukina bazan taba yarda a zartas da komai ba saita amince da kanta,saboda dukkaninmu nida kai ba haqqinmu bane ba nata ne,sannan koda ta yardan bazan taba nemawa abdul'azees ko mahaifiyarsa sassauci ko dukka hukuncin da taso yanke musu ba,matuqar dai ta amshi alfarmata shikenan,sauran hukunci duka nata ne,yanzu wannan magana ta rage tsakanina da 'yata ne,naka ido kawai"murmushi malam bilya shima ya saki,yana jin dadin yadda ya maida bilkisu 'yarsa sosai kamar azeez din,yana niyyar cewa wani abu amatur rahman da abdulrahman suka shigo da gudu abdul din yana biye da ita,da alama wani abu ne ya hadasu.      Tunda suka shigo gaba daya suka tafi da hankalin me martaban,numfashinsa ya tsaya cak na wucin gadi,ya zuba musu idanu babu ko qiftawa yana kallon hukuncin ubangiji,sak abdul'azeez dinsa.       Kabbara yake a zuciyarsa yana sake kadaita Allah,iya yaran kawai sun isa su zama ishara garesu,sun isa su bayyanawa kowa cewa wani babban lamarine can dama da Allah ya boye a tarayyar bilkisu da abdul'azeez din.      Yana zaune ya kasa magana har malam bilya ya raba gaddamar,sannan ya kalli me martaba fuskarsa qunshe da murmushi

"Wadan nan yaran kadai sun zama wani farinciki da garkuwa na zuciyata,su kadai idan na kalla nakan tabbatarwa kaina lallai alqawari Allah na haihuwarsu ne ya tabbata....amatu kuje ga kakanku can ku gaidashi" ya fada yana dagasu daga jikinsa.      Idanu suka tsura masa,sannan suka juya suka kalli junansu suka kuma kalli malam bilya,sannan suka maida dubansu again ga maimartaba da yaketa jifansu da murmushi,ya qagu yaji dumin jikokinsa,kamar ya janyosu zuwa jikinsa saboda tsabar zaquwa.      "Ku qaraso mana taurarin masarautar kaisa" ya samu kanshida furtawa tsabar tsananin farincikin da yakeji cikin zuciyarsa,sashe daya na zuciyarsa kuma yana jin takaici da kuma kaico na ba cikin masarautar aka haife musu suba,saidai duk da haka yana miqa godiya ga ubangiji me dumbin yawa daya sanya suka fito daga tsaftataccen tsatso,hanya ta gari,sunnar ma'aiki S A W ba haihuwar titi ba

"Ammi zata mana fada,rannan ta kusa zane abdul,sabida yayi irin abun kanka a kansa" duka shuru sukayi,suba yara bane,sun fahinci me yarinyar keson fada,sai maimartaba ya saki murmushi yana shafa nadin dake kanshin

"Idan na cire zakuzo?,kuma ba zatayi fadan ba?" Dukkansu suka gyada kansu,saiya sanya hannunshi biyu yana nufin cirewar.      Da sauri malam bilya ya dakatar dashi

"Karka biye musu ranka ya dade.....ke amatu,abdul....ku qarasa maza ku gaidashi,ni nace muku ai,don haka ba zatayi fada ba"      Dukkansu luf sukayi q irjinsa tamkar sun jima da saninsa,ba shakka jini ba wasa bae,sai yaji idanunsa suna son cikowa da qwalla,yau ga yaran abdul'azeez dinsa a jikinsa,jinin azeez dinsa,lallai Allah da girma yake.    Ya dan jima da yaran har sai da yaga sun saki jikinsu dashi,sannan ya musu kyauta mai yawa,ya kuma wuce gida da alqawarin zuwa yaga bilkisu da kanshi.     ¶¶¶¶¶  ¶¶¶¶  ¶¶¶¶¶¶    Dukkan abinda me martaba keyi babu wanda ya sani,hakanan ya nemi anty zuhriyya da abbaa da kanshi ya gana dasu.      Nauyinsa girma da kuma shekarunsa suka hana anty zuhriyya tuburewa,mutum ne shi mai fahimta da saurin gano mutum,ya fuskanci a bacin rai take,hakanan taci alwashi sosai kan abinda akayi musun,saboda haka ya saki murmushi

"Bazan hanaki daukan dukkan matakin da kike gani ya dace ba,matakin da kike ganin shine zaisa ki huce....duk da mantawa zaiyi wahala,saboda anyi muku dukkan abunda ya cancanci dan adam yayi fushi akai,wanda koda nine akaiwa bazan qyale ba....amma ni alfarma daya nake nema shine,a maidamin surukata tare da yaranta,ta koma cikin ahalina,duk duniya kowa yasan cewa itadin ta zama familyn marigayi sarki mu'az kaisa,jikokina susan asalinsu,hakanan aurensu yaci gaba...bayaga haka bana buqatar komai daga haka".      Ita dinma kamar shigen abinda malam bilya ya fada haka ta amsawa maimartaba cikin girmamawa

"Allah ya taimakeka....indai wannan alfarma ce mudai mun maka,adalcinka yafi gaban ka nemi abu aqiyi maka,saidai.....bilkisu marainiya ce,hakanan mun mata alqawarin cewa zata yanke dukkan hukuncin da yayi mata babu mai tursasata,saboda duk qalubalen rayuwarta ta fuskanceshi ita kadai ba tare da munsan me ta gani ba,don haka muma kuke roqon alfarmar cewa,zamu barta ta yanke dukkan hukuncin da taso" kai yake jinjinawa cike da gamsuwa

"Maganarku da hukuncinku yayi daidai,matuqar muka shigo da tursasawa cikin lamarin bamuyi adalci ba sam,hakanan ba lallai mu samu abinda muke nema ba....,a yanzun haka na baro ayyuka da yawa a fada,amma zan dawo da kaina rana ta daban na ganta muyi magana".      Ko bayan tafiyarsa zancan suka rinqa tattaunawa a tsakaninsu,sam bawan Allahn bai dauki mulkin da yake dashi a bakin komai ba,ya dauki rayuwa da sauqi qwarai da gaske,ko a mafarki basu taba kawo cewa zaiyi tattaki har cikin gidansu ba saboda diyarsu,basu taba zatan zai nema wata alfarma ba daga gurinsu,duba da irun girma matsayi da martaba da yake da ita.      Saidai duk da wannan babu abinda ya rage haushin fulani a zuciyar anty zuhriyyan,da kuma alwashin da taci a kanta na nuna mata kurenta koda sau daya ne tak cikin rayuwarta,tabbas saita aiwatar da wannan,saboda ta san itace kanwa uwar gami,kuma ummul'aba'isin na faruwar komai     Cikinsu babu wanda yayi zancan da bilkisu,itama kuma batasan meke wakana ba,tasan dai a ranar anyi baqi a gidan,kuma da alama manyan mutane ne,daga haka bata fahimta komai ba,kuma bata tamnaya ba,sabida dama tambayar abinda bai shafeta din ba ba dabi'arta bace.*ABDUL_AZEEZ*      Duk da abinda mai martaba yayi masa na nuna halin ko inkula,da kuma korar da yayi masa hakan bai sanya ya haqura ba,ya sake iskeshi a dakin hutawarsa,bayan ya gama wani xama na musamman da dukka hakiman dake qasarsa.      Da kallo me martaba ya bishi,yana karantar sauyi qarara tattare dashi,ga duk wanda ya sanshi duba daya zai masa ya tabbatar da cewa lallai abdul'azeez din ya sauya,hakanan akwai abinda ke yunqurin kawo masa tarnaqi a rayuwarsa.     Bai dakata ba har sai daya isa gabanshi a lokacin da yake kashingide,ya zube bisa dukka gwiwoyinsa a gabansa kanshi a qasa

"Na sake kawo kaina Allah ya taimakeka,na sani cewa nidin me tarin laifi ne a wajenka,hakanan na cancanci dukkan wani hukunci daga wajenka,amma ina roqon yafiya da gafararka da kume neman alfarmarka kan ka shiga lamarina" ajiyar zuciya ya sauke a boye,yana mamakin yadda duk sanda zaiyi magana saiya tattarawa kanshi dukka laifin ya aza saman wuyanshi,sam baya ambata ma sunan mahaifiyarsa a ciki,kamar shi kadai ya aiwatar da abun,yanajin tausayinsa amma yana ganin bai kai stage din dazai janye horonshi haka tunda wuri ba shida uwarsa,cikin tsare gida irin wanda yakanyi lokaci zuwa lokaci,musamman idan yana shari'ar data bata masa a rai a fada yace

"Banga amfanin zuwa ka nemi yafiyata ba,bayan bani kuka zalunta ba,mai ciwo daban mai neman magani daban?,kuma ma da kake fadin na shiga case dinka azeez ashe ina da qima da mutunci har haka?,ai na zaci nidin ba kowa bane,hakanan bani da wata rawar da zan taka cikin rayuwarka,banason na sake jin komai daga bakinka,ka tashi ka nemi yafiwa wanda kuka batawa,don ni babu abinda xan iya yi maka".       Yafi kowa sanin cewa shidin kaifi daya ne,idan yayi gaba mawuyacine ya dawo baya,daya daga cikin halayen daya gada kenan daga gareshi,don haka gwiwa a sake ya miqe ya soma takawa a hanakali hannayensa goye a bayansa,fulani aisha tayi saurin komawa da baya kafin ya risketa,zuciyarta na wata irin quna,saita fasa shigowa,ta koma izuwa sashenta,tabbas dole tasan abunyi,basu taba samun sabani koda shigen wannan ba tsakaninta da maimartaba,bare abdul'azeez da yake lelensa,ya kamata ta farka,ta kuma lalubi abunyi.      Babu wanda ta kula koda barorinta da suka zube suna ta faman yi mata barka da dawowa,hakanan afanan data samu zaune a falo tana karatu,itama afnan bata ce komai ba,sai binta da kallo da tayi harta shige dakinta,ta dauke kai afnan ta maida ga littafinta,saidai kuma itama zuciyarta ta fada kogin tunani.      Kai tsaye ta tsaya a gaban mudubin dakinta,kanta take qarewa kallo sosai,ba zata iya tuna wani abu daya taba damun rayuwarta ya sanyata rama haka ba irin wannan lamarin,ra hasaso azeez a idanunta,ta kuma hasaso sanda yake zube gaban maimartaba yaba masa magiya,amma yayi burus dadhi,kwatankwacin yadda yake mata itama,ta sima gajiya,ta sima kaiwa maqura,wai shin ma me zai hanata ta tunkari yarinyar ayi me gaba daya?,me zaisa ba zata sake bin wata hanyar ba,ta jarraba koda kome zai daidaita?,da wannan tunanin ta samu relief,ta kuma zauna tana tsara yadda zata gabatar da komai.¶¶¶¶¶¶¶    ¶¶¶¶¶   ¶¶¶¶¶


     Kalaman da memartaba ya gaya masa,sai yaji kamar yana bashi izinin ya sake yin dukkan me yiwuwa ne ya nemi yardar bilkisu,hakan ya sanya a washegari ya kuma shiryawa kamar kullum shi daya tak,bayan ya dakatar dakkan 'yan rakiyarsa ya nufi gidan anty zuhriyya.      Sanda take fitowa daga gidan da niyyar zuwa gidansu zata dauko su amatu da suka kwana a can,daga nan kuma ta biya ta gidan biki ta su taho tare da anty zuhriyya,wadda dukkansu yau suna gidan wunin biki daga ita sai mai gadi a gidan,a lokacin ne shima ya faka motarsa,ya kuma fito yana kulleta sukayi kacibus.      Cak ta tsaya ba tare data iya koda qara taku guda ba,yayin da shima ya tsaya daga rufe motar da yakeyi,idanunshi fes bisa kanta,zuciyarsa na wani irin bugu garwaye da wani matsanancin sonta da yaji yana taso masa.      Tayi masifar kyau cikin shigar da tayi,babu wanda zai kalleta bai sake kallonta ba,saboda yadda tayi fresh,kana kuma kallonta zata tabbatarwa kanka ruwa biyu ce,chaculet colour din fatarta ta sake fita sosai ta qara haske,wanda sauran kadan ka kirata da fara idan ta shiga jinsin wasu masu choculet colour skin din.     Takowa yasoma yi yana burin ya cimmata a inda take tsayen,saidai tun kafin ya qaraso din ta kuma ciki da sauri kamar wadda taga dodonta.     Koda ta buda falonma bata tsaya a nan ba,sai data dangana da bedroom dinta,sannan ta samu kujerar madubi ta zauna tana maida numfashi,takaici ya kamata,tana ta murnar kwana biyu bai zuwa,ko yayi zuciya ne ya dauke qafa,sai kuma yau gashi katsaham,sai taja tsaki tana dora jakarta saman madubin bayan ta ciro wayarta.     Koda ya tafin bq zata fita yanzu ba,saita tabbatar da yayi nisa da unguwarsu,don haka ta kira number hauwa'u,ta sabuwar wayar data siya mata,tace kada suji shuru,sai zuwa anjima zata shigo,sannan ta kashe ta kira anty zuhriyya itama tace sai rana ta qara yin sanyi sannan zata zo,ta kashe wayar tana jan tsaki gami da dora wayar saman madubi,sai kawai ta miqe ta zare takalman qafarta,ta kuma ware rolling din kanta,take gashinta da yasha gyara yake qyallin ya bayyana,doguwar rigar jikinta data fidda shape dinta sosai daga sama ta sake qara mata kyau,saita haye saman gadonta tayi ruf da ciki bayan ta runtse idanunta,tana addu'ar Allah yasa yabar qofar gidan da wuri.      A qalla wajen minti goma tana a haka,ta soma gajiya da kwanciyar,ta sake gyara kwanciyar tata zuwa rigingine tana jan tsaki,gami da soma qunquni saboda takaicin bata mata lokaci da yayi,kamar a mafarki ta hangi kamar inuwar mutum wanda hakan ya razanata,ya kuma sanyata bude idanunta da sauri.      Ji tayi zuciyarta na neman faso qirjinta ta fito sanda idanunta suka hango matashi,tsaye bakin qofar shigowa dakin,ya jingina da qofar bayan ya budeta,ya harde hannayensa duka a qirji,bayan yaui crossinh qafafunsa,tamkar mai shirin daukan hoto.     Zumbur ta miqe cikin razana,tare da mamakin yadda ya iya ratso harabar gidan,ya qaraso har falon gidan,ya kuma riski dakinta,duk da cewa ba abun mamaki bane tunda babu kowa cikin gidan,amma babban abun mamakin shine,girman qarfin halinsa da har ya iya hakan.      Kasa magana tayi,sai wani zama da tayi tsakiyar gadon bayan itama ta zuba mishi idanu,kamar dabbar dajin da aka kawowa farmaki tana jira taga motsin wanda yakeso ya farmaketan.      Minti guda kafin ya saki hannayen nasa,sannan ya soma takowa cikin dakin,wanda hakan ya sanya itama ta soma motsawa sannan ta fara magana cikin hayaniya,duk da a cike take da tsoro

"Karka soma shigomin daki,ka fitarma mutane daga gida malam,nan gidan matan aure ne,don me zaka shigo musu gida babu izininsu?".    Bai kulata ba,illa gadon daya durfafa idanunshi a kanta,yana qarewa shigar jikinta kallo,wani shauqi daya jima baiji irinsa ba na neman tasiri cikin ranshi.    Karar wayarta dake saman madubi ya dakatar dashi,dukkansu suka dubi wayar lokaci daya,saiya sauya akalarsa zuwa inda wayar take

"Karka tabamin waya mana,meye hakan?" Ta fada da sauri cikin jin haushi,bai juyo ba bare ya tanka,yasa hannu ya dauki wayar yana duba me kiran.     Dr adam ne,tuni ya gane waye,saboda number waje dake nuna daga qasar da aka kira,wani abu yaji ya soki ranshi,sai yayi rejecting kiran.     Yana qoqarin maida wayar yaga sms saman screen din wayar,da sunan ASSADIQU,ya latsa kai tsaye ya sadar da kanshi ga akwatunan saqonninta


_gimbiyar duka kyawawan duniya,banason na cika damun wannan kyakkyawan ruhin mai cike da aminci,amma ina buqatar a tabbarmin da zuwan nawa,yayi ba matsala?_     Idanunsa ya runtse na wasu sakanni,yanaji taba sake bashi umarnin ya ajemata waya,sai kawai ya kashe wayar gaba daya ya sanyata cikin aljihunsa,sannan ya juyo yaci gaba da nufar gadon da take

"Wai kurma ne kai,bakajin me nake cewa?gidan matan aure ka shigo musu baka nemi izni ba" Ta sake fada cikin tsiwa.      Bai amsata ba har sai daya qaraso bakin gadon,ya kuma zauna a gafensa a nutse,sannan cikin narkakkiyar muryarsa yace

"Na sani,kuma nima tawa matar auren nazo  

⁶⁹Post a Comment for "SIRADIN RAYUWA CHAPTER 18 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...