SIRADIN RAYUWA CHAPTER 10 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 10   BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 10 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

- - Post a Comment

 SIRADIN RAYUWA CHAPTER 10

 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA


Ajjiye wayar tayi tanajin wani daci da zallar rashin adalci cikin lamarin gaba daya,a iya sanin data yiwa fulani aishan macace mai tausayi jin qai da kuma kyan hali,batasan meya sauyata haka lokaci daya ba,tayi mamakin yadda tabari BURI gami da ALWASHIN watsa aniyar maqiya yakeson sauya halayya da dabi'arta,ta dauki buri mai tsaho da girma akan azeez fiye da yadda aka santa,duk da cewa dama can mutum ce mai son 'ya'ya,amma duk da haka tana da kyakkyawar halayya da dabi'a wadda ta siya mata soyayya mai girma a zukatan al'umma,sai gashi yanzun tana wasu abubuwa da suke baiwa sodangi mamaki,halayyar da sam tasan ba tata bace,rashin adalci,rashin tausayi da kuma nuna halin ko in kula akan kowa face diyoyin cikinta,indai hakane kuwa maqiya sun cucuta,dafin magauta ya ratsata,ya mata kuma tasiri da har yafidda kyakkyawar halayya daga cikin jininta ya sauya mata wata.      Kamar yadda ta zata din kuwa babu wanda ya kalla abincin ma a cikinsu har ita kanta,kusan kowa zuciyarsa babu dadi,duk da cewa wani abu yau ya bata mamaki,ta gaza karantar yanayin da zuciyar bilkisu ke ciki a yau,farinciki ko akasin haka?,wani irin emotion take gani kwance saman fuskarta data gaza tantance a wanne bigire zata ajjiyeshi?.      Kamar kazar sa qwai ya fashewa a ciki take shiryawa,ita kanta batasan a wanne matsayi ruhi da zuciyarta suke ciki ba,abinda ta sani kawai shine,ta tashi da qwarin gwiwa bayan ta raba dare tana tunani tare da qoqarin samarwa kanta mafita,ta sanyawa kanta wani yaqini da jarumtar amsar duk wani nau'in rayuwa da zata tunkareta.       Tana shiryawa idanuwanta na sauka sashe bisa sashe na dakin,tana tuna dukkan yadda rayuwarta ta wakana cikin gidan tsahon shekara guda,ta runtse idonta lokacin da tunaninta yakawo ranar daya amshi mutuncinta,take dukkan wani qwarin gwiwa data tattarowa kanta ta tarwatse,saita sulale a wajen saman gwiwoyinta tana rufe fuskarta da tafukan hannunta,tana jin wani irin abu yana tasowa daga qirjinta can cikin zuciyarta,ambaton sunan Allah tasoma yi,wanda hakan ya taimaka mata ta daidaita tunaninta,saita miqe a hankali,tazauna gefan gadon,ta nutsu nadan wani lokaci sannan taci gaba da shirinta.       Sanda take sanya kaya take kuma agogo wanda yake nuna mata mintuna ashirin kacal suka rage su fita daga gidan zuwa filin sauka da tashin jiragen sama don konawarta tushenta,qarar qararrawa taji da alama akwai mai buqatar shigowa gidan,dukka saita tattara hankalinta,har zuwa sanda taji.mama sodangi ta bude qofar,muryar wata mata taji wadda bata santa ba,saidai tana iya jiyo kiran sunanta da mama sodangi tayi da ladingo,daga haka bata kuma jin komai ba saita qara hanzari ta kammala shirinta gaba daya.       Sake duban agogo tayi,minti goma ya rage musu,tana dauke idanunta ana turo qofar dakin,mama sodangi ce,idanunta kan bilkisu,cikin wani irin yanayi daya dasawa bilkisu fargaba da faduwar gaba,wadda ta sanya ta gaza ci gaba da kallon maman,ta sadda kanta qasa,har zuwa sanda ta qaraso inda bilkisun ke tsaye.       Kamar wadda batasan meya shigo da ita dakin ba ta tsaya tana duban bilkisu,a hankali ta lalubo hannunta ta sanya takardar,hakan ya sanya ta daga kai tana dubanta,kai mama sodangi tasoma girgixa mata,idan ta lura dakyau ma kamar qwalla ce cike a idanunta,dukkansu babu wanda ya iya cewa da dan uwanshi komai aka sake shigowa dakin,sallamar ladingo ta karade dakin,maimakon mama sodangin ta amsa,sai kawai tasaki hannun bilkisun ta juya da sauri tafice daga dakin,ita kuma ta rakata da ido har ta bacewa ganinta,sai a lokacin ta ankara magana ladingo ke mata,ganin alamun bata ji ba yasanyata maimaitawa

"Idan babu damuwa zan soma debe kayanki na fita dasu,driver yazo za'a saka cikin mota" bata iya cewa da ita komai ba,don ji take kamar bakinta bai taba magana ba bare tasan ta yaya zata amsa mata,qafafunta tamkar lawashi saboda rashin qwari,tana jinta kamar mai tafiya a wata duniya ta daban tasoma nufar qofa don barin dakin ba tare data waiwaya tasake duban dakin ba,ba tare data tsaya ta duba ko akwai abinda ya kamata ta dauka ba,babu komai cikin hannunta sai takardar datake da tabbacin ko ba'a gaya mata ta meye ba tasan ta meye,har takai falo sannan taji kamar qafafun nata ba zasu iya qarasawa da ita waje ba,don haka ta lalubi kujera tazauna donta ragewa kanta nauyin da taji dukka gabban jikinta sun mata.      Kamar a inuwa taga shigowar wasu matasa,wanda da alama ma'aikata ne,kamar a inuwar taga ana fidda dukka kayan gado da aka qawata dakin dasu,eh kamar inuwa zata ce,tunda hankalinta bai jikinta bare ta tantance inuwa ne ko zahiri ne.


       Tamkar mutum mutimi haka take zaune cikin falon gidan,daga kunnuwanta har idanuwanta basa iya ganin komai,basa kuma gane kome face mai rayuwarta ta gaba zata haifar mata.      Hannunta na dama dunqule yake da takardar data zamto tamkar wani mubudi ne na rayuwarta ta gaba,takarda ce da saqon dake ciki take jinsa daidai da saqon ranar mutuwarta,riqonta kawai zafi yake mata tun daga tafin hannunta har zuwa qwaqwalwa da zuciyarta,yakuma zarce zuwa ilahirin jikinta gaba daya.     Duk da cewa tana tsammanin zuwan ranar,duk da cewa tasan cewa lallai lallai komai daren dadewa irin wannan ranar tana tafe,takuma shirya zuwanta tun daga ranar da aka soma lissafin kasantuwar kwanakin har zuwa randa zata risketa,saidai batasan me yasa ba,meye dalilin data tabata har haka ba,batasan meye dalilin da jikinta da zuciyarta suka girgiza har haka ba,sabone?,ko kuwa tunanin me gobenta zata haifar mata ne?,meye matsayinta meye sakamakon rayuwarta?,wanne sabon shafin zata bude?      Karo na qarshe ladingo tafito tafito da akwatinta da take jin shine abu na qarshe a cikin dakin data mallaka,ta qarasa inda take aje musu kayansu shima ta ajeshi,ta qarasa gaban bilkisu ta tsaya cikin rusunawa

"An gama fitar da komai,ance jirgin qarfe sha biyu zamu bi,yanzu haka mai motar dazai daukemu zuwa filin jirgin yana kan hanya...."       Qwaqwalwarta tajiyo wani sashe na maganarta,saidai bata fahinta duka ba,cikin jimla guda ta tattara maganartata,qwaqwalwarta ta sake aika mata da saqon

"Tafiya zakuyi,zaku koma nigeria,zaki kuma cikin gidanku".      Tamkar wadda ake bawa umarni sai kawai tamiqe,cikin qarfin hali tasanya hannu tagyara zaman qaramin hijabinta,kana tasoma takawa a hankali kamar mai tafiya saman qayoyin da aka shimfidawa hanyarta tayi hanyar bedroom din daya zama shine matattarar dukka wani tarihi nata.      Idan ka kalleta a sannan zaka iya rantsewa tashigo dakinne tana son fayyace da ainihin qasar wanne waje aka gina dakin saboda yadda takebin kowacce kusurwa ta dakin da kallo sama zuwa qasa da kallo har na tsahon wasu daqiqu.       Sauke idanunta tayi awani sashe can na dakin,tasoma takawa a hankali kamar wadda maganadisu yake janta zuwa arean,tasa hannu tasoma shafa wajen,yana yawan tsaiwa a wajen duk da cewa cikin duhu take ganinsa,yana son wajen sosai duk da bata taba ganinsa muraran ba,saita sake matsawa da jikinta wajen,ta lumshe idanunta tana shaqar daddadan qamshin da wajen yake fitarwa,tabbas qamshinsa ne,abinda duk cikin rayuwar datayi mai kama da mafarki tafi riqewa,saikuma qaqqarfar ajiyar zuciya wadda tasaka dukkan gabbanta suka saki,hawayen da uta kanta batasan na meye ba suka ziraro daga idonta guda daya.      Kamar wadda aka tsikara tajuya da sauri tanufi qofar ficewa daga dakin,dakin da zuwa yanzu yakoma zallar kangonshi babu komai ciki tamkar wasu rayuka basu taba wanzuwa a ciki ba,batasan inda kayan suka koma ba tunda dama ba mallakinta bane.      Girgiza kanta take dasauri tana gayawa kanta,tabbas bata tsira da komai ba,babu abinda ta tsira dashi koda kuwa hoton fuskarsa ta zahiri ne face ragowar qamshinsa daya barwa hancinta da qwaqwalwarta tabonsa.       Cak ta tsaya tana duban gabanta,kana ta duqa a hankali takai hannunta tadauki zoben daya dauki hankalinta qwarai,zobene da tasha ganinsa a yatsunsa,abun guda daya tak datake iya banbance dangane da duk wani abu daya shafeshi,cikin sauri tadauki zoben ta damqe a hannunta kana cikin sassarfa tafice daga dakin ta zarce da ficewa daga gidanma gaba daya don tanaji cewa izuwa yanzu itama ya kamata ta yanke dukka sauran abinda yayi saura.        Tanajin ladingo na mata magana saidai bata ko tsaya ba bare ta waiwayo ta dubeta,fatanta shine ta raba kanta da komai daya wanzu a shekara guda,ta yanke dukkan wani abu dake da alaqa da shekarar........      **********    *****   ********       Tana zaune daga guri na musamman da aka tanada saboda xaman baqi,daga gefanta kuma maimartaba ne sarkin qasar kaisa,daga hannunshi da nata hannun yaransu kowanne zaune a mazauninsa,dukkaninsu sun bada hankalinsu dari bisa dari kan taron da ake gudanarwa,farinciki ya lullube zuciyar kowannensu na ganin yadda dansu kuma yayansu yaketa karbar lambobin yabo da girmamawa kala daban daban.       Kamar yadda a tsarin shiga kyan halitta,kwarjini da kuma wata irin ginshira tasa ya fita daban da sauran daliban,hakanan ma ta fannin hazaqarsa suna gamida shahararsa cikin makarantar,farinjininsa daga wajen malamai har zuwa dalibai.       Fuskar fulani aisha tamkar gonar auduga,zuciyarta fes kamar dutsen qanqara,har hakan ya gaza boyuwa ya bayyana saman fuskarta,jerarrun fararen haqoranta irin na azeez sun bayyana kansu saboda irin murmushin da takeyi,ko iya yanzu ta tabbatar da cewa azeez din yayi zarra,yakuma fara taka irin matakin da takeso ya taka,tauraruwarsa ta haska ta danne ta kowa,sunansa ya shahara yakuma fantsama ko ina,inama ace adama tazo wajen batayi qaryar bata jin dadi ba?,koda yake koda adama batazo ba,ta tabbatar afra zata bata labarin dukkan abinda ke faruwa,uwa uba akwai waya a hannunta tana nadar komai.       Wasu qwallar farinciki ne suka so fitowa daga idanuwanta a lokacin da aka buqaci mahaifinsa ya taso makaranta zata girmamashi saboda irin gudunmawar daya bayar,da kuma kyakyyawan misali daya baiwa dalibai,hakanan yasa makarantar tasake samun daukaka da suna,bayan maimartaba ya isa wajen sai azeez din ya nemi alfarmar mahaifiyarsa ta taso,sosai ta dinga jin farinciki,tana jin cewa taqi kadan ya rage burinta ya gama cika.      Awa biyu cur akayi kwashe ana gabatar da taron kafin a kammala,har yanzu farinciki yaqi barin zuciyarta,cikin sigar xolaya mai martaba ya dubi fulani aisha

"Ke ko 'yar karan nan ma babu,kinga fuskarki kuwa kamar gonar qanqara?" Cikin dan jin nauyinsa tadan sunne kai kadan tana dariya qasa qasa kana tace

"Bazan iya boye farinciki na ba,don abdul'azeez bai bamu kunya ba,yayi dukkan abinda yakawoshi qasar nan,harma fiye da abinda muka zata" kai.ya jinjina shima yana sake jin dadi,alfahari da tilon dan nashi namiji yana ratsashi.       Daga mazaunin dalibai maza kuwa kamal ne zaune kamar ruwa ya cishi,duk wani motsi na azeez din yana kan idanunshi,jin zuciyarsa yake kamar zata babbake ganin yadda yaketa samun lambobin yabo daga bakunan malamai kala kala,ya tabbatar wannan labarin bamai dadi bane akunnen mahaifiyarsa,ya rasa kuma meye hana fulani adama zuwa wajen,bayan mom ta shaida mishi tana qasar,kuma zata zo.       Can wani sashen kuma daga rukunin mazaunin daliban dai minal ce zaune,ita dinma idanunta hankalinta da tuaninta yana ga azeez din,wani daci take ji cikin ranta da zuciyarta na yadda tayi loosing oppurtunity dinta,na yadda ta rasa azeez din,duk da ta taki babbar sa'a da bai sake tada case din ba,bai kuma sake nemanta kobi ta kanta ba,duk da cewa a hakan tana boye kanta daga gareshi,kada wataran su hadu ya tuna allura ta tono garma,wai shin me zatayi azeez ya sota kamar yadda take buri?.      "Guy din nan ya gama haduwa,komai yaji,Allah ya masa komai" ta tsincin furucin na fitowa daga bakin wasu 'yammata dake zaune gefanta,saita waiwaya tana dubansu,ji tayi wani abu ya tokareta,kamar ta miqe ta shaqesu ganin yadda suke binsa da kallo duk inda ya motsa kamar wasu tsaffin mayu,dole ta janye idanunta daga kansu tana jan tsaki mai qarfi a fili,wanda sai daya sanya qawarta ta waiwayo tana dubanta gamida tambayarta,saidai bata bata amsar komai ba.      Lokacin tashi nayi kamar yadda aka tsara a rubuce aka qarqare komai,a nan dalibai suka soma musayar adress da lambobin waya gamida daukar hotuna a tsakaninsu.      Haka ce ta faru ga azeez,mutanen dake son daukar hoto dashi....musayar lambar waya da amsar adress suna da yawa,harda 'yan shishshigi,harda wadanda shi bai taba hulda dasu ba,iya mutanen da suke selective a wajensa ya tsaya sukayi wadan nan abubuwan ya qara gaba wajen da motocinsu ke fake ya barsu a wajen.       Me martaba ne cikin motar,sai ammi a ciki,sauran duka suna wata mota ta daban,yana shiga maimartaba ya dubeshi cikin murmushi

"Wadan can mutanen da suka jiraka fa?" Sai daya waiwaya ya dubesu ta window sannan cikin girmamawa yace

"Allah ya taimakeka.....na gama sallamarsu" murmushi kawai yayi ba tare daya sake cewa komai ba,ya riga da yasan hali xanen dutse,har yanzu halayyarsa tana nan a jininsa,tun zamanin shekaru qananu har yanuzu da aka doshi shekara ta ashirin da shida.       Lokacin da drivern ya tada motar suka fara tafiya mai.martaba yayi gyaran murya,kana cikin sautin muryarshi dake nuna tsantsar hikima,dattijantaka da kuma kamala yace

"Babu shakka duk baiwar da dan adam yaga ubangijinsa yayi masa....yayi masa itane bawai don yafi kowa ba,a'ah,yayi masa itane saboda shi din mabuwayin sarki ne,yakanyi abinda yaso a sanda yaso a kuma lokacin da yaso,dukkan wata baiwa a rayuwa tamkar jarrabawa ce ga bawa,yakan iya cinyeta,yakan iya kuma afkawa zuwa ga halaka idan baiyi takatsantsan ba,abdul'azeez...,zuwa yanzu girma ya soma hawa kanka,tunda gashi har ka soma aje wani mataki na karatu,shekarunka kuma sun bar ashirin da biyar sun soma tsalle zuwa da shida,ina fatan zaka zama mai nutsuwa da nazari a duk yanayi matsayi ko matakin daka samu kanka,ka zama cikakken mutum mai kamala da adalci,sannan kuma adali a duk wani sha'aninsa,hakan zai baka dama ta gina inga tacciyar rayuwa,ka samu iyali na qwarai,ka auri matar da bazata zalunceka ba kamar yadda kaima ya haramta ka zalunceta,wannan shine matakin rayuwarka ta gaba" hakanan yaji wani irin yanayi ya shigeshi,cikin girmamawa ya furta

"In sha Allahu".      Murmushi fulani aisha tayi tana qoqarin danne yanayin data shiga

"Allah ya taimakeka nasihar tun yanzu?,da ka bari ai mun qarasa gida kun huta tukunna sai kuyi xama na musamman" dubanta yayi shima yana murmushi

"Kinsan hausawa sukace da zafi zafi akan bugi qarfe,kuma kowacce magana akwai muhallin daya dace ayita" kai ta jinjina kawai tana kau da kanta gefe,sai takejin kamar wata qusa ya kafa mata.     Tans jinsu suna magana jifa jifa da azeez din har suka qaraso gidan,wanda babu kowa ciki sai fulani adama da fafur ya qirqiri ciwon qarya,saboda baqinciki da bacin rai mai martaban da kanshi ya tako zuwa bikin,saboda tsantsar soyayya d kulawar da yakewa azeez din kenan?.Sosai ta ware idanunta da sukayi nauyi tana kallon qasar datayi shekara guda cif ba tare data rayu a ciki ba,ta cikin motar take bin ko ina da kallo,motar da take ciki ita qwal daya,daga ita sai wannan matar da taji an kira da ladingo,tun sanda suka sauko daga jirgi ba zata iya cewa ga inda su mama sodangi da rakiya sukayi ba,ta lura da haka,amma batace komai ba,hakanan bata buda baki da niyyar tambaya ba,wataqila yana cikin tsarinsu,wataqila dukka cikin irin nasu adalcin kenan.       Kamar wadda ta warke daga makanta haka ta dinga bin qofar gidan nasu da kallo,gidan da shigarta daya kwanakinta biyu tal a ciki,gidan da take da tabbacin kowanne irin daukan hankali xaiyi an samar dashi ne bisa cinikin mutuncinta da akayi

"Mun iso" muryar driver dake gaban motar ta ratsa dodon kunnenta,ba tare data waiwaya ta dubi kowa cikinsu,ko tabi takan kayanta dake cikin motar ba ta,ta sanya hannunta ta bude motar ta xura qafafunta tafito.       Duk da cewa dare ne,duk da cewa bata gama sanin kan gidan nasu ba,amma hakan bai hanata gane qofar shiga gidan ba,ta tura ta cikin qarfin hali ta bude ta kutsa kanta ciki.      Bata manta hanyar falon nasu ba don haka taci gaba da kutsa kai,bata dakata ba sai data isa qofar shiga falon,sai a sannan taji duk wani rauni nata ya dawo,sai a sannan fargabar yadda zata tadda 'yan uwanta ya fado mata,sai a sannan fargaba da tsoron irin rayuwar da zata gudanar ta dawo mata,ta sanya hannunta kamar wadda zata kama maciji ko qadangare ta yaye labulen nasu.       Hannatu tasoma hangowa zaune cikin falon qasan tiles din dake malale a falon,gefanta umaima ce da amina,hajara na kwance saman cinyar hannatun,da alamu kallo suke,don basu lura da labulen da aka daga ba.      Daga gefe saman kujera kuma wata matace zaune,itama.kallon take,a qalla zata doshi shekara talatin da takwas,qafarta daya saman daya,lokaci lokaci tana latsa wayar dake riqe a hannunta.      Wasu hawaye taji masu dumi sun ciko mata idanu,ko yaya suka rayu tsahon lokacin?,ko yaya sukaji lokacin da babu ita?,ko yaya rayuwa ta kasance musu?.       "Ta ina ake shiga?" Taji an fada daga bayanta,data waiwaya sai taga ladingo ce janye da akwatunanta,maida idanunta tayi cikin falon,ta qara taku ta saka qafafunta a ciki,bakinta dauke da sallama wadda take fitowa da qyar.      Dukkaninsu kamar an jona musu schoking suka daga kansu kusan lokaci guda,hakanan miqewarsu cikin tsananin mamaki wanda lokaci qanqani ya juye zuwa zallar farinciki,kana suka fara rige rigen isowa gareta,duqawa tayi a gabansu ta hadesu gaba daya zuwa jikinta,suka saki kuka kusan lokaci daya.      "Meye haka lafiya?" Matar dake zaune saman kujerar ta miqe tana tambaya gami da binsu da kallo,fuskarta akwai alamun rashin sanin wacece bilkisun,babu wanda ya iya tanka mata a cikinsu saboda kukan da sukeyi,ladingo ce ga dubeta ta soma gaidata,ta amsa tana son jin qarin bayani,kafin suce komai umma katti ta shigo falon

"Ke hannatu,kukan me kukeyi haka?,kuda waye kuma?" Cak ta tsaya ganin bilkisu duqe a gabansu,ta waro ido tana cewa

"Mai gado?,saukar yaushe?,yaushe kika zo?" Kai kawai ta daga ta kalli umma kattin,sai taga ta sauya sosai,ba kamar lokacin data barsu ba,maganar ladingo ce tayi kutse cikin tambayoyin da take jerowa bilkisun

"Ko xamu samu damar ganin mai gidan?" Tace da umma katti,don ta fuskanci kamar ita tafi wayewa da gidan akan wadda ta taras a falon.      Duban ladingo tayi ta gyada kai

"Eh bari ayi masa magana" daga haka ta juya zuwa wata qofa,tana tafe tana waiwayowa tana sake duban bilkisun harta shige.        A falonsa ta sameshi yana zaune yana zuba lomar tuwon shinkafar da ladi tayi da take girkinta ne umma kattin tashiga,har ladin ta daga kai xatayi masifa sai kuma saqon datazo dashi ya sanyata yin shuru

"Kazo ga maigado ta dawo" hakanan yaji wani faduwar gaba ta saukar masa,taste din abincin ya canza masa

"Na shiga uku,tofa" ya furta a sarari kuma a hankali,itadai umma kattin gaba tayi takoma zuwa falon don ta kashe qwarqwatar idanunta,taga meye zai faru,cikin yatsina fuska ladi tace

"Wai dama da gaske shekara dayar zatayi su dawo da ita?" Waiwayawa yayi.ya dubeta ba tare daya gane ma'anar tambayar tata ba,sannan ya miqe kawai yana goge hannunsa ya dauki hularsa dake gefe yadurfafi falon.        Yana shiga sautin kukansu yasoma sauka a kunnensa,saiya hada rai ya tsaya a kansu yana dubansu

"Wanne irin shashashanci ne wannan?,meye haka ke me gado?,ba zaku godewa Allah ba daya hada fuskokinku saiku xauna kuna kukan banxa dana wofi?" Janye jikinsu suka fara suna qoqarin tsaida kukan nasu,saidai ita bilkisun nata hawayen sunqi daina zuba.       Cikin girmamawa ladingo ta gaidashi sannan tasoma magana

"An umarceni dana danaganata da mahaifinta,kamar yadda akayi yarjejeniya bayan shekaru guda,to lokaci yayi,saboda haka gata nan kamar yadda fulani ta umarceni,shaidarta tana hannunta,dukkan abinda suka mallaka mata gasunan sun zama nata,tun daga lefe dukiyar aure dama komai da komai,hakanan sun bata dama,daga nan zuwa shekara guda duk abinda take da buqata a matsayin sallamarta ta qarshe ta fadi dukka adadin za'a bata....saidai fulani tace na tunasar daku yankewar alaqa ta har abada....." Wani abu ya soki zuciyar bilkisun da har ta gaza daurewa ta dubi ladingo,duban da yasa bata iya qarashe bayaninta ba,har abada kuma komai lalacewa ubanta ubanta ne,wato xallar rashin adalci,wulaqanci da kuma qarfa qarfan har yakai matakin da za'a dinga aikama mahaifinta gargadi ta hanyar 'yar aike kuma baiwa?,duk da cewa shiya siyama kansa koma meye,amma abun yasoma yiwa kunnuwanta muni.      Tsam ta miqe tana riqe da hannun aminatu da umaima,qasa qasa tace

"Kaini dakinku" da saurinsu sukayi gaba tana biye dasu,har zuwa dakin data zauna wancan karon lokacin da ake yinin bikinta,shine babu abinda ya sauya a ciki,saidai atsaftace yake hakanan komai yana shirye bisa tsari da doka,tasan za'a rina,dama bata taba tsammatar qazanta daga wajensu ba,saboda ta yadda da irin hoton data yi musu ma zallar tsafta da nutsuwa,saita qarasa zubewa anan tana sakin wani sabon kukan suna tayata,don suma bai ishesu ba,hannatu ce kawai bata biyi bayansu ba,wanda bata lura ba,har sai zuwa lokacin da zuciyarta ta gaya mata kukan ya isa haka,don bashi da wanu magani,face sake sanya qannan nata da zaiyi suma cikin wata damuwar,dole ta yiwa kanta waigi,ta goge nata hawayen ta lallashesu,kana ta shiga bandakinsu ta daura alwala ko zataji sanyi cikin zuciyarta.      Tana fitowa daga bandakin hannatun na shigowa janye da akwatunanta,saita dauke kanta don ko ganin akwatunan su kansu batason yi takoma kusa da amintu ta zauna tana kallon yarinyar tana dan murmushi duk cikin qarfin hali,tadan qara girma da wayo sabanin sanda ta tafi.      Hannatu ce ta qaraso ta dora mata wani abu dake nannade saman cinyarta tare da qaramar jakarta,saita kalli abun da alamun tambaya

"Kudinki ne da suka baki daga can,matar da kuka shigo tare ta baiwa baba,yace nakine bazai karba ba,baba ladi nata qoqarin sanyashi ya karba har tana yunqurin amsa nina karbo....karkiqi amsa don Allah yaaya,haqqinki ne,nakine bana wani ba,wanda akaci a baya ya isa,Allah ya amfana,idan ma kikace ba zaki karba ba babu abinda zai sauya,su zasu amsa su kuma murqushesu suci gaba da rayuwarsu ba tare da komai ya faru ba" idanunta taf da qwallar data samu ta tsayar take duban hannatun,tun daga yanayin jiki da kalamanta sun nuna hannatun bata da bace,hankali ya soma gameta,ba shakka ta sauya qwarai,ko nauyin daya hau wuyanta bayan tata tafiyar ne yasa hankalin yayi hanzarin zuwa mata haka lokaci guda?duk da dama tazarar shekara biyu rak ta bata,roqon datayi mata da qoqarin amso saqon da tayi tun daga falon,idan tace ba zata karba ba kamar ta watsa mata qasa a ido ne,don haka cikin hikima tace da ita

"Ganinsu ne banason yi hannatu" da sauri ta daukesu daga kan cinyarta

"Bazan takura miki ba yaaya,amma zanta ajjiye miki su har sanda kike da buqatarsu" ta qarashe maganar tana miqewa zuwa cupboard dinsu ta bude can sama ma'ajiyar kayanta ta cusa su sosai.       sai a sannan ta soma duban dakin loko da saqo,karon farko hauwa'u ta fado mata

"Ina kulu ta,ita kadai ce ban gani ba?" Ta ai qarshen tambayar tana maida idanunta ga hannatu,sai taga yanayin fuskarta ya sauya sanda take dawowa mazauninta data tashi,jin bata amsa mata ba saita sake duban sauran,suma dai kamar hannatun kowa fuskarsa ta nuna zallar damuwa,gabanta yayi mummunar faduwa,zuciyarta ta qiyasta mata wani mummunan abun ya samu hauwa'un suka boye basu gaya mata ba,cikin rawar murya tace da hannatu

"Hannatu,meya sameta baku gayamin ba?" Kai ta girgiza tana duban bilkisu

"Yan uwan mamanta sunxo sun tafi da ita"

"Ya Allahu" ta fada tana dafe kanta,wataqila rabuwarsu da hauwa'u kenan har abada taxo?,yan uwan mamanta?,yan uwan maman nata da sai afi shekara biyar ba'asan inda suke ba?

"Yaaya,hauwau na kuka tana cewa ba zata bisu ba sai yaaya maigado ta dawo,sai kin dawo kin sata a makaranta yadda kika ce,saikin dawo ta ganki amma haka suka dauketa,sunyi dauki ba dadi da baba,amma suka nuna mishi halinsu na fulani,saboda da zafinsu da shirinsu sukazo,tana kuka muna kuka haka suka jata suka tafi,kiran sunanki kawai take,munfi sati bama iya cin abinci,munfi sati muna mafarkinta,daga qarshe dole muka haqura saboda babu yadda zamuyi,amma kullum sai munyi zancanta,har yau muna kewarta,ko da kika ganmu xaune a falo ma zancanta muka gamayi kenan,sai gaki kin shigo".       Wani sabon tashin hankalin taji ya rufto mata,ji take kamar jininta ya hau,hauwa'unta,yarinyar da duk cikin qannenta taficin buri akan tazo ta ganta,saboda tasan tafi kowa qulafucinta,kukan dai da bataso tayi shiya sake dawo mata,don bata da wata hanya ta huce takaicinta da baqinciki idan ba kukan ba.


*****   *****   ******   *****
      Tun a mexico ammi fulani aisha ta shirya masa walima ta musamman,wanda tasamu halartar familynshi na kusa sosai,musamman dangin mamamshi daga mali,har safwa ma wannan karon sai data zo,da tarin kyaututtukanta na murnar tayashi karatunsa,wanda ita saura shekara guda ta rage mata ta kammala nata karatun,walima me kyau da qayatarwa akayi,kusan kwanakin duka cikin sabga yake,sai washegarin randa aka kammala walimar sannan yasamu huta,ya kulle kanshi a daki ya kashe dukka wayoyinshi.       Saidai tun baccin baiyi nisa ba yasoma mafarkai,hakan ya tilasta masa tashi,yayi addu'a ya gyara kwanciyarsa,saidai baccin ya gaza sake samuwa kwata kwata,haka dole yanaji yana gani yaci gaba da juyo saman gadon,daga qarshe ma wanka yayi yasake ficewa,duk da hutun da yake da buqata.


******    *****   *****   *****     Tana zaune daga gefan gadon hauwa'u wanda a yanzu ya zama nata tun bayan dawowarta gidan,saboda taqi nata dakin kamar dai wancan karon,sanye take da rigar bacci doguwa mai dan kauri,sai wani qaramin dan kwali data rufe kanta dashi.      Misalin bakwai da rabi ne na safe,dukka yaran na zaune a gabanta sanye da unifoarm suna karyawa,wanda ruwan tea ne da bread,zata iya cewa a yadda tasan rayuwar gidansu a da,yaran sun samu 'yanci da sauyi kaso sittin cikin dari maimakon daa,a yanzu akwai abinci a gidan dai dai gwargwado,safe rana da dare,babu zaman yunwa,hakanan baban nasu ya qoqarta sakasu a makarantar boko mai sauqin kudi,dama already ta barsu suna zuwa islamiyya,kuma basu fasa zuwa ba har kawo yau,basa yawo cikin tsumma kamar yadda sukeyi a baya,saidai kuma kusan babu mai kulawa da rayuwarsu,ba'a tsangwamesu ba tsangwama mai yawa kamar baya ba,hakanan babu mai tattalinsu kamar yadda suke dai a baya,umma katti ta kama yaranta sune a gabanta yadda dai rayuwar take a baya,mama ladi da amaryar da bilkisun tazo ta taras ya rangado wadda taji suna kira da anty sukam ta mijinsu suke ko ince ta kansu,domin a zahiri kowacce na nuna mishi tattali ne,yayin da kuma a badini kowaccen kanta da rayuwarta take qoqarin ginawa,suna hangen dan abun hannun malam bilyan,sannan kuma suna hasashe da lissafin basu haihu dashi ba,basu da kowa dashi,to ba shakka idan ta tashi barewa dasu zata bare.        Tana zaune tana dubansu suna 'yan hayaniyarsu har suka gama,hannatu ta kada kansu don wucewa makaranta,ta laluba jakarta don basu dan abun kashewa saidai babu komai a ciki,saita buraci inama ace tana da wani abu da zata basun dazai sake yawan farincikinsu,hakanan ta musu fatan dawowa lafiya suka amsa cikin cikin walwala suka fice,don wannan rayuwar da suke ciki gani suke sun samu dukkan komai,tunda basu saba irinta ba,a baya sun rayu babi ci sha suttura ko muhalli mai kyau daga mahaifinsu,a yanzu kuwa dukka sun samu,don haka a nasu ganin basu rasa komai ba.

     Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana binsu da kallo,ta jima zaune a inda suka barta tana tariyar rayuwa da abubuwan dake cikinta,anty zuhriyya?,ina take?,ina tayi?,tayi nisa da ita nisa mai yawa,irin nisan da bata zata ko tsammata ba,har yanzu mafarkin da tayi da ita daren jiya yana nan maqale a ranta,makwafi ce ta mahaifiyarta wadda bata da tamkarta,tunda dangin nasu sun mata nisan da bazata iya zuwa muhallin da suke ba,su din kuma sun manta da cewa dan uwansu ya aurar da diyarsa aqasar harta haifi diya itama ko kuwa yaya?,mahaifiya tabbas mahaifiya wani jigo ne na rayuwa,babban bango ce kuma majingina,wanda duk mutumin daya rasata ba shakka dole yayi kuka,kuka kuma da bazai yanke ba sai ranar da taka ta sameka.


       Kamar wani hankali aka qara mata game da muhimmamcin mahaifiya,ta tabbatar da cewa koda mahaifinta yafi qarfin mahaifuyarta,koda tana raye aka mata wannan auren na qarfa qarfa,tabbas bayan ta dawo ba zata fuskanci rayuwar data soma fuskanta cikin gidan ba a yanzu.


       Na farko sabuwar amaryar babanta wadda ta gama karantar tsaf kishi take da ita,na biyu daga umma katti har mama ladi duk da cewa ta dade da sanin yadda suka dauketa,amma ta tsammaci yanzun komai zai canza,albarkacin albarkacinta da kowaccensu take ci a yanzu,saidai wani irin mu'amala ce tsakaninsu,idan sun ganta ta gaidasu su amsa,idan basu ganta ba babu mai nemanta ko cigiyarta,koda zata wuni ta kwana cikin daki ba tare data leqo ba,qannenta sune sanyin idaniyarta,abokan hirarta,akwai abubuwa da yawa da suke cunkushe a zuciyarta suke damunta suna dagula lissafinta,wanda tsahon sati biyu da dawowarta harta soma ramewa,baya ga rashin abubuwan more rayuwa yadda tasamesu a baya dakyau wanda yanzun duka sun janye,babu wanda yadamu da yanayin abincin da zataci a gyarashi saboda taste din bakinta ya canza,babu wanda yadamu daya bata kudin sabulun wanka kona wanki,idan an bayarma tona qannenta ne,su kansu basu gama wadata yadda ya kamata ace sun wadata ba,saidai wannan din bata sani ba,shin daga mahaifinsu ne ko daga matansa wakilansa wadanda abun yake biyowa ta hannayensu?,duka bata sani ba,saidai dukka wannan ba damuwarta bane,kome tasamu tana ci,kome yazo.hannunta tana amfani dashi,tunda tasan rayuwar da tayi abaya gaibu ce,wadda tayi dai dai da mafarki.


      Komai zai biyo baya ko xai sameta tana da tabbacin rashin mahaifiya nada kaso mai tsoka da kuma muhimmiyar rawa da yake takawa wajen tsintar kanta a kowanne yanayi ma da take ciki,da tana da mahaifiya ko babu komai tana da kafadar da zata jingina tayi kuka,tana da muhallin da zata fadi damurta a fuskanceta,koda ba za'a yaye mata damuwar ba,za'a tallafa mata da addu'a,tana da wajen da za'a tambayeta me ya dameta?,me take da buqata,amma yanzu fa da babu uwar?,saidai tayita cinye damuwarta ita daya,ko tayita magana da 'yan uwanta data tabbatar babu lallai su fahimta abinda take nufi.


       Sai datayi wanka,tasamu kaya ta saka tana duba yawan kayanta dake da buqatar wanki amma babu sabulun da zata wanke din,batason taba na qannen nata,saboda su dinma bawai wadatar dasu yayi ba.


     A hankali take takawa zuwa kitchen din gidan,ga duk wanda yasanta kallo guda zai mata ya karanci tana cikin damuwa qwarai,akwai tarin damuwa cunkushe a ranta,babu kowa ciki dama shan ruwan shayi ya kawota,don haka tasamu kofi ta diba,duk da tanajin yadda wasu lokutta ake kyarar qannenta idan suka taba kofin daya daga cikinsu,ta dauki salar biredi dake ajjiye harta soma shan iska,wanda ta tabbatar nata ne,don kusan koda yaushe itace ta qarshe a yin breakfast a gidan,babu kuma wanda ya damu da ita bare ya killace mata.


       A tsaye takeshan shayin,lokacin ne anty tashgo kitchen din,da alamu ita keda girki a ranar,fuka a gintse,tana ta ciccin magani da harare harare,da qyar ta amsa gaisuwa bilkisun kamar wadda aka yiwa dole,sannan tasoma hada girkin rana,wanda da wurwuri takan gama duk ran girkinta,ruwan mutum yaci ruwanshi ya barshi,tasha jin suna fada da abokiyar yin nata mama ladi akan hakan,da yake ita mutunce maison abinci mai dadi,umma katti kanja gefe ta tafa hannu tace itakam 'yar kallo ce,hakanan ko anqi ko anso itace uwar gida kuma babu yadda aka iya da ita.


      "Wato ke babu abinda kika iya tsinanawa mutane,saidai idan an tuqa a baki" taji anty tana fada sanda take dauraye kofin da ta gama shan ruwan shayin,dakatawa tayi tana duban antyn cikin mamaki,don bata gane me take fada ba sam,aiki dai tasan cewa kafin qannenta su fita su suke share falon gidan da baranda tas to bata musu horon ganda ba,itake shiga kitchen ta gyara musu shi fes kullum kwanan duniya ta wanke dukka kwanukan ciki,don tasan babu lallai yaran suyi yafita yadda ya kamata,kuma ita din shaida ce,daga zuwanta gidan zuwa yau kitchen din har wani qara haske yayi akan nada,hakanan duk sanda suka gama cin abinci xata tattara kwanukan tasake wankewa,don ba kasafai ma suke kwana da wanke wanke ba yanzu tun sanda tazo,to batasan wanne aiki takeso ba kuma sama da hakan,kafin tace komai ta yaba mata maganar data tsaya mata fiye da tsammani
"Dama illar zama da gansamemiyar bazawara kenan,tana maka kallon biri kana mata kallon ayaba,idanu sun gama budewa ta gama sanin komai,kai wala'alla ko kwanan aure kayi da ubanta saita gane,mtsewee Allah ya sawwaqa" idanunta ta lumshe gaba daya tana jin wani tashin hankali na rufto mata,sunan Allah tasoma ambata don ya kawo mata agaji,tana jin wani irin zafi yana ratsa zuciyarta,ta maida kofin muhallinsa da qyar sannan ta lalubi qofar fita.


      Da qyar takai kanta daki,ta samu qasan tiles din tayi zaman dirshan tana yin filla filla da maganganun antyn,sai taji suna mata wani irin ciwo,wanda daga qarshe sai da suka danganata da zub da hawaye,kalmar bazawa ta sanyata sakr maida kanta cikin duniyar tunani,duk sanda zata daga kai ta kalli fuskarta a madubi sai wannan sunan ya fado mata,ba shakka sunanta ne,sai taji wani irin rauni da tashin hankali sun baibayeta,ba shakka duk wanda ya santa zai kuma ce wani abu akanta saiya laqaba mata wannan sunan,duk wanda yazo da niyyar aurenta sai an alaqantata da wannan sunan,mafi muni ma a cikinsu idan an tambayeta wayeshi din wanda ta aura?,bata da cikakkiya kuma tartibiyar amsa akan haka.


      Cikin kwanakin lafazan da antin ta dinga aike mata kenan,wadanda suka zama tamkar guba a zuciyarta,suka tarwatsa duk wani zaman lafiya da salamarta,suka dinga damunta gamida sanyata cikin wata iriyar matsananciyar damuwa,wadda ta bayyana har a gangar jikinta baya ga zuciya.


      Abun mamaki sai taga mama ladi itama tabi sahu,ya zamana sun sakata a gaba batare da tasan meta tsare musu ba,duk ranar Allah daga fitowarta zuwa faduwarta cikin kuka da qunci take,hakan yasa cikin lokaci qanqani dukkan wani kyau da kumari datazo dashi yayi nashi waje.


       A gefe guda kuma wani irin matsananciyar tsanar masarautar kaisa da ahalinta suka saukar mata,tasan koma meye duk wani hali da take ciki a yanzu sune sila kuma ummul aba'isin din komai,komai lalacewar uba uba ne,amma banda haka da zata iya cewa mahaifinta shine mutum na biyu daya zama sila kuma yake da alhakin komai,cikin qaramin lokaci ta sake tsanar komai ma,ciki harda rayuwarta.

********    *****   ********

"Ya Allah!" Ya fada da sauri lokacin da yake tashi daga shimfidarsa,yaxauna sosai saman gadon dafe da goshinsa.


    Ya jima zaune a haka yana maida numfashi da sauri da sauri,sa'an nan ya zuro qafafunsa yasauko,saida yasoma kunna qwan lantarkin dakin,haske ya gauraye ko ina,sa'annan ya durfafi bandakin dake cikin dakin.


       Sosai yadinga watsawa fuskarshi ruwa,mafarkin da yayi yanzu sakanni qalilan da suka shude yana dawo masa tar cikin kwanyarsa,tamkar yanxu yakeyinsa,muryarta da fuskarta na gilmawa cikin idanunsa.


      Ya jima sosai a haka,sannan daga bisani ya daura alwala,a hankali ya ciri towel yana goge ruwan jikinsa,yana kuma dawowa zuwa cikin dakin,saman gadon ya sake komawa ya kwanta,saidai wannan karon rigingine yayi bayan ya tokare bayansa da filo,lokaci zuwa lokaci yana sauke ajiyar zuciya.


       A daren ko kadan bacci bai sake xiyartar idanuwansa ba,yanaji yana gani hakanan yayi asarar daren,bai samu runtsawa ba har sai da ya bada faralin sallar asuba,sannan wani gajeran bacci yayi awon gaba dashi.

***********


      Cikin girmamawa dukka barorin dake sassan nata suke xubewa suna miqa mishi gaisuwa,saidai ko sashen da suke baya duba bare akai ga amsawa,takawa yake zuwa cikin sassan nata cike da wani irin kwarjini da cika idanu,saidai kallo daya zakayi masa ka fahimci akwai rashin kuxari da walwala a tattare dashi,musamman ga mutumin da yasan wayeshi.


      Bai tsaya ba hakanan baiyi jira anyi masa iso ba,har sai daya dangane da falon da mahaifiyarsa ke zaune tana ganawa da baqi,shigowarsa ya tashi dukka wani baqo dake wajen yafice ya basu guri,saiya samu qasan kilishin da take zaune akai yaja daya daga cikin lausasan tumtum na alfarma da aka qawata wajen ya jingina qafarshi,a ladabce yasoma gaidata.


       Idanunta qur a kanshi ta amsa mishi,kana ta jefa masa tambayar dake kai kawo cikin ranta,sati guda kenan daya gabata
"Lafiya qalau kuwa kake yarima?" Dubanta yadanyi kana yayi qas da kanshi,ya shafa wuyanshi zuwa habarshi sannan ya amsa
"Lafiya ammi"
"Amma meya haifar da rashin kuzari da alamun damuwa saman fuskarka cikin satin nan gaba daya?" Shuru ya danyi kamar me neman dalilin daya sanyashi hakan,kusan hakan ne,donshi kansa baisan wacce iriyar amsa zai bata ba,wacce amsa ce kuma ta dace da tambayarta,saiya dan ja tsaki,yana tsammanin kawai shi da kanshi yakeson takura kanshi,ko kuma dan qaramin sabo ne daya gitta ba tare daya sani ba yakeson masa kutse cikin rayuwarshi,amma anya kuwa?,wanne irin sabo ne haka cikin a wannin rayuwarsu da idan aka curesu a haduwa biyu zuwa uku kacal basu gaza awa daya da rabi ba zuwa biyu
"Bana samun ishshen baccine kwana biyu....kuma ina tsammanin gajiya ce,dana gama warwarewa komai zai koma dai dai" tashi tayi sosai ta zauna,sabanin dazu da take a kashingide,fargaba tana shigarta na kada ace daga dawowarsa wani mugun abu na shirin samunsa daga magauta
"Wacce iriyar gajiyace da zata hanaka bacci haka har tsahon mako guda?,anya abdul'azeez?,idan akwai wani abu daban da kakeji ka gayamin tun komai baiyi nisa ba,tun ba'a ci galaba a kanka ba" kanshi ya girgixa yana son tabbatar mata da cewa babu komai
"Babu komai ammi,i wil b okay"shuru ta danyi,sannan ta gyada kai
"Allah yasa".


        "Dazu mai martaba ya aika sassanka nima na aika,maisara ya isar da saqon kana bacci,anyi rasuwa ne a gidan dan maje,yaso kuje jana'iza tare amma bai sameka ba....,inaga yana da kyau idan ka fita daga nan ka nemeshi kaji daga bakinsa,idan yana da ra'ayin zuwanka saika shirya ka bishi,ya kamata irin wadan nan abubuwan ka dinga kiyayewa saboda gobenka,kada ka manta,gobe kaine kan matsayin da yake kai a yanzu,shi yasa yakeso ka zamana a gefansa"
"In sha Allah" ya amsa mata,ba tare da yasan wanne irin feeling ne ke cikin zuciyarsa ba game da maganar.


         Dai dai lokacin sumaira ta qaraso falon,wadda tayi shirinta na komawa makaranta,kafin ta zauna azeez din ya umarceta ta hada mishi abinci,ta hada masa komai ta aje gabansa sannan ta qarasa wajen ammi suka gama maganarsu sukayi sallama ta wuce.


      Bata fi mintuna goma da tafiya ba afnan ta qaraso falon,rungume take da litattafanta ta iso gaban ammi tazube littafan gamida zama sosai a gabanta bayan ta salube jakarta kamar zata shige cinyarta,cike da shagwaba take fidda safarta,idanun azeez da bata ankara da wanzuwarsa a falon ba yana kanta,ba kasafai yake maka magana ba idan kana abinda baya so,yawanci yafi sanya maka idanu harsai sanda idanunka suka ankara dashi
"Wannan karatun akwai wuya ammi....wallahi kamar na gudu" murmushi kawai ammin ta saki kana ta dubeta
"Dadi ne yayi miki yawa auta....mutum nawa ne suke neman dama irin taki amma basu samu ba?" Shuru tayi na dan sakannin da basu wuce uku ba kana ta gyada kai
"Gaskiyane fa ammi,har kin tunamin da BILKISU" kanshi ya daga da hanzari jin afnan ta ambaci irin sunan,sunan da baisan me yasa ya fara zaune masa cikin kwanyarsa da tuninsa ba,ba tare data lura dashi bs taci gaba
"Tana da qoqari sosai ammi,gasar karatu muke da ita,duk da bamu saba ko shaqu da ita ba....amma kowa yasan mayyar karatu ce,burinta a rayuwa tayi karatu....Allah sarki bilkisu,rana daya babanta ya cireta daga makarantar,yayi mata auren dole....."
"Har yanzu baki manta ba afnan,har yau?" Ammi ta fada,wanda sai a sannan ta tuna afnan din ta taba zuwa mata da qorafin akai.maganar zuwa ga mai.martaba,duban ammi tayi,fuskarta na nuna alamun alhini
"Bazan manta ba ammi,bansan tana da kirki ba nayita gaba da fada da ita,ba ruwanta ammi,innocent kamar bilkisu amma aka hanata cika burinta"
"Gskiyar yayanku da wani lokaci baku shiri saboda dan banzan surutu,idan kin gama saiki tashi ki wuce ciki" langabe kai tayi tana duban ammin,tana shirin sake magana suka hada idanu dashi,ya balla mata harara data sanya bakinta ya rufu gam,tayi gaba da sauri zata wuce
"Saiki turo uwani ta kwashe miki su,kada kisoma zuwamin anjima kina min cigiyar littafanki ina tsaka da hutawa"
"Zoki kwashe" ya fada cikin kaushin murya,ba shiri ta dawo ta tattara litattafanta tayi gaba,ya saki siririn tsaki
"Silly girl,litattafanma sai an kwashe miki an kai miki saboda tsabar sangarta,saina rage dukka barorin dake sashen nan na maida ayyukan kanku" itadai bata da bakin magana ta qara wuta tawuce nasu bangaren,ammi itama naji batace komai ba,sai murmushi kawai datayi,tun ya qarami haka Allah ya halicceshinda wani irin girma cikin zuciya da jikinsa,amma ya manta shima komai hadimaine suke masa?,saita kada kai kawai tana sake sakin murmushi qasan ranta tana binsu da addu'a.

      A duban farko idan kayi masa,zaka tsammaci wani ciwon ne yake damunsa,saboda yadda yaketa safa da marwa cikin dakinsa,daga wancan bangon zuwa wannan,lokaci lokaci yakan sanya hannunsa saman sumarshi ya shafi kansa,yanajin qwaqwalwarsa tana matuqar daukar dumi da caji.


      "Why?,me yasa?,me yasa?,me yasa ta kasa barin tunani da qwalqwawarsa?,me yasa tun bayan nan bai taba kwanciya peafully ba ya tashi haka?,me yasa duk wani motsi nashi second ko minti saita ratsa ta ciki ta tuna mishi da kanta?,yana tsammanin komai is over kuma komai ya wuce,amma baisan me yasa wannan ya kasa wucewa ba,me yasa wannan memory din ya kasa shafewa ba.


        A hankali ya maida akalarsa zuwa bandakinsa,ya tsaya gaban famfo ya watsawa fuskarsa ruwa mai sayi sosai,har sai dayaji zuciyarsa na kwanciya,sannan ya jawo daya daga cikin qananun towel din dake jere raras ya goge fuskarsa da kyau ya wurgashi gefe ya fito.


       Yana shirin komawa yazauna don ya ragewa kansa kai da kawon da yake kamar sojan dake fareti yaji ana knocikin qofar dakin nasa,ko waye ma yasan wani makusancinsa ne kuma mai muhimmamci,tunda har ya ratsa dukka falukan ya qaraso bedroom dinsa,don haka yana daga tsayen ya bada damar a shigo.


      Abdulrashid ne,wanda shima cikin satin ya kammala nashi karatun ya dawo qasarsa garinsa kaisa,idanunshi saman azeez yana dubanshi bakinsa dauke da sallama,saiya waiwayo shima yana dubanshin lokaci guda kuma yana amsa sallamar.


      "Ya na ganka haka ko shiryawa bakayi ba?" Kanshi ya daga yaduba lokaci sannan yaja qaramin tsaki,ya soma takowa bakin gado inda abdulrashid ya yiwa kansa mazauni
"Nayita kiranka kafin na shigo ina wajen ammi,itama ta kiraka amma no answer....."
"Bacci nayi" ya amsa mishi a taqaice yana miqa hannu ya janyo wayarsa dake gefan filon daya tashi akai,abdulrashid ya bishi da kallo sanda yake buda wayar yana duba miscal din dake ciki
"Ammi ta gayamin cikin kwanakin nan kamar kana cikin damuwa?....what's going on?" Ya tambayeshi still yana kallonshi,saidai shi hankalinsa na bisa waya,miscal dinsa dana ammi ya soma tararwa,saina wani abokin karatunsa sannan na safwa,yakuma sakin tsaki kana ya maida wayar ya aje,banda ya mata alqawarin zuwa yau din,baijin akwai abinda zai fiddashi,hakanan yakejinshi cikin mode din da baison magana da kowa
"Just thirty minutes,yanzu zan shirya" ya fadi a maimakon ya amsa mishi tambayarsa yana nufar bandakin,sake dai binsa yayi da kallon,ba shakka akwai abinda yake damun nashi,duk da dama tsabar miskilancinsa yasa idan baku dade ba ko baka karanci yanayinsa ba zaka tsammaci ko yaushe cikin damuwar yake.


       Sai daya shafe kusana wanni guda sannan yasoma shiryawa cikin wani tattausan yadi mai kyau da tsada,wanda yabi lafiyayyar fatarsa ya kwanta dakyau,yana cikin fesa turare abdul yasake masa tambayar,saidai baice mishi uffan ba,alamun dake nuna baida sha'awar su tattauna kenan,sai daya gama sa'annan suka fito gaba daya.


      Abdul dinne ke tuqa motar,tuqi yake cikin nutsuwa,saboda shikam yanayin garin ya masa dadi sosai,saidai shurun dake cikin motar yayi yawa,a hankali yace
"Zuwanka kenan fa na farko tunda ka dawo,babu wani abu da za'a kai mata" tsaki yakuma ja sannan yace
"Share kawai letter".bagarar dashi abdul din yayi yaci gaba da tuqinsa.


      Ba'a jima ba dai still yakuma sakin wani tsakin,abdul.ya taka burki da qarfi uana dubanshi cikin bala'i bala'i
"Kaga malam,bafa zaka zo ka sanyani a gaba da tsaki ba hakanan babu gaira babu dalili,ban maka uban komai ba,ban kuma san meke damunka ba". A maimakon ya amsa mishi saiya bude murfin motar da wani irin hanzari ya fice kawai yana buga mishi qofar,binsa yayi da kallo baki bude,tsahon minti biyu ya tuna suna saman titi ne ashe bawani parking din arziqi yayi ba,don haka ya balle murfin motar ya biyo bayanshi.


      Saman motar ya sameshi zaune abinsa dafa'an,kamar ya manta suma saman titi ne,ga motocin dake zuwa wucewa sunata saka musu haske dake nuna wrong parking sukayi,kuma koda yaushe zasu iya hada goslow ma
"me kake haka?,baka gani saman titi muke?" Wani kallo ya masa,kana ya dauke kansa baice masa komai ba
"Oh god" abdul ya fada a ranshi,baison wannan side din na azeez,indai yasoma haka to 'yan taurin hade da uban miskilancin suna kusa kenan,zaka sha wuya idan ya taurare.


        Waiwayawa yayi yadubi titin,da gaske sun fara hada cunkuson ababen hawa da yawancinsu suka soma zuba uban horn,ya dawo da kallonshi kansa
"Ka gani ko?,pls ka sauko mu wuce muna sake bata lokaci anan" sai da yayi kamar bazai magana ba sannan yace
"U better keepquite,kar ka sake damuna"
"Naji" ya amsa mishi a kaurare yana jifansa da harara,wani kallo shima yayi masa sannan ya sauko yakoma cikin motar.


       Kansa jingine da kujera idanunsa a lumshe,yanajin sanda ya tashi motar suka soma yin gaba,bayajin koda yaje wajen safwa zai iya tabuka abun arziqi,may be ma ya qare da nuna mata halinsa,don haka yace
"Maidani gida" kallonsa yayi sannan yadauke kai yaci gaba da tuqinsa
"Kai din banza,baka isa ba Allah,minti biyar yayi yawa mu isa,ka sanya mata kuma rai,sannan yanzu kace na maidaka gida" jin abinda yace ya sanyashi yin shuru bai sake cewa komai ba har suka isa.


          Ta juya ta kalli kanta a madubi sau babu adadi,ita da me aikinsu ne wadda taketa biye mata,kwalliyar data kira takanas akazo har gida aka mata take dubawa,yau ranar ta kusamman ce,karon farko tunda ya dawo zaizo wajenta
"Halima inane baiyi ba don Allah?"murmushi tayi
"Ai tako ina kwalliya tayi,ina da tabbacin shi kansa idan ya ganki yau saita Allah,saiya susuce fiye da yadda kike tsammani" dadi ya kamata,tayi dan tsalle gami da ihu tana mata godiya,dai dai lokacin da mahaifiyarta ta leqo dakin.


        Tsaki taja ganin irin quruciyar da safwa ke yi,ita kuma halima na tayata
"Bansan se yaushe xaki gama girma ba safww,saiki fito kije suna jiranki a falon baqi" daga haka ta saki labulen ta juya,tana jiyo kwakwazonta da muryarta,dama tasan za'a rina hakan zata faru,saita saki murmushi tana addu'ar Allah dai ya nuna mata ranar auren tilon diyar tata da muradin ranta abdul'azeez.


      Sai data sanya masu aikinsu suka kai komai sannan ta qara gyaggyarawa ta fito,a qofar falon ma ta kusa minti uku tana dudduba inda baiyi na,sa'an nan ta daga labulen dakin ta shiga.


       Akan azeez din idanuwanta soka fara sauka,wani sanyin dadinya saukar mata,ason ranta idan itace zata so ya taso.da sauri ne ya iskota,kana su rungume juna kamar yadda turawa kanyi a duk sanda sukaga abun sonsu da suka dade basu ganshi ba,saidai ita din bata samu haka ba,amma idan ta lura dakyau kallonta yake ta qasan idanu,wato miskilancinsa bazai barshi ya bude dukkanin idanunsa ya kalleta sosai ba.


      Sam shi ba wannan bane cikin kwanyarshi,idanunsa da zuciyarsa ne bijiro masa da ita kamar yadda take masa lokaci zuwa lokaci,sai yake ganin fuskarta gefan ta safwa har tazo ta zauna.


       Kusan rabin hirar da abdul suka yita,ya karanci damuwa qarara saman fuskar safwa saboda yadda ta ciwa ranar da lokacin buri,don haka saya miqe ya zagaya ta bayanshi ya sunkuya dai dai kunnensa cikin rada
"Don't be a silly pls....bai kamata ba,kayi abinda ya kamata" sai ya daki kafadarsa sannan ya qara gaba ya fice.


      Ci gaba sukayi da kallon juna kawai shuru yana sake ratsa dakin,sai data gaji sannan ta saki ajiyar zuciya,ta taso zuwa kujerar da yake kai a hankali idanunta a kanshi,tana jin kamar taje ta rungumeshi cikin jikinya,saidai bata manta da sharadin daya sanya mata ba kafin ya iso,don kada ma tayi yunqurin aikatawa.


     Hannun kujerar da yake kai ta xauna,hakan ya kawo kusaci sosai tsakaninsu,cikin sanyin murya da shagwaba tace
"My prince" shanyayyun idanunshi dake sakr narkar da ita a soyayyarshi ya daga ya kalleta dasu,ya kafeta kuma dasu yana ci gaba da kallonta,itama kallonshi take,ta daga hannunta a hankali xata shafi idanun nasa,sai kuma ta tuna warning dinsa,don haka tayi saurin janye hannun nata  da sauri
"Gaba daya ka ciremin zumudin zuwanka dana kwana inayi,idan wani laifi nayi maka pls prince ka gayamin..." Wani murmushi ya saki na gefan baki yana kada kai
"Babu wani abu....just bana jin dadi ne...." Ya qarashe maganar yana miqewa idonsa still a kanta
"Zan dawo wani lokaci" ya fadi yana tattakawa a hankali harya fice daga falon,daga inda take xaune ta bishi da kallo kawai,tana jin idanunta na tara qwalla,me yasa zai mata haka?,saita miqe cikin sassarfa tayi cikin gida tana gab da rushewa da kuka.


       A harabar gidan yasamu abdulrashid tsaye jikin motar yana amsa waya,baice masa komai ba ya bude gidan baya ya shige maimakon gaba,galala ya bishi da kallo yana sauke wayar daga kunnensa,tsahon minti biyar yaji baice masa komai ba,kamar ma bai cikin motar,don haka saiyayi sallama da wanda yake wayar ya maida aljihunsa,yabude kawai ya shiga ya tada ita shima still bai cewa azeez din komai ba.


********  ***""""***  *******


      Ƙarfe biyar da mintuna ne na yammacin ranar,zaune take saman abun sallarta wanda tunda tayi sallar azahar kusan take kai bata tashi ba,kiran sallar la'asar ne kawai ya tadata,ta ajjiye qur'anin hannunta tashiga bandaki ta daura alwala tayi sallar la'asar din,ko data idar qur'anin tasake dauka taci gaba da karatunta,don a yanzun indai tana ita kadai cikin dakin shine babban abokin hirarta,cikinta babu komai,tun shayin safe data samu ta kukkurba a tsaitsaye cikin qannenta,don batason ta fita daban cin abincin tayi karo da mama ladi ko anty wani ya samu maganar dazai gaya mata wadda zata sake dagula lissafinta.


      Jin yadda hanjinta ke murdawa saboda yunwa ya sanyata aje qur'anin gefe,sannan ta miqe a nutse ta taka ta fice zuwa kitchen.


       Kamar baquwa ko barauniya haka take takawa cikin sanda,don bata fatan ta tadda kowa a ciki,addu'arta ta karbu,babu kowa din kuwa,ta samu plate ta bude tukunya ta xuba dafadukan shinkafar da akayi a matsayin abincin rans,ta saka spoon ta fara tsakura,don gaba daya cin nata tamkar na yara haka yake,cikin nata ba wani babban space ne dashi ba.


       Gabanta yayi mummunar faduwa sanda take kai lomar abincin bakinta saboda jiyo muryar anty tana shigowa kitchen din,faduwar gaban data sanyata qwarewa,saita saki cokalin tahau tari tana dafe qirjinta.


      Dubanta anty tahau yi sanda ta qaraso tana tabe baki,sannan taja dogon tsaki
"Qaryar banza qaryar wofi,dama kin lallabo kina satar abinci babu cas ba as ba dole alhaki ya sakaki ki qware ba,jarababbiya kawai....ni wallahi bansan me yasa ubanki ma ya zuba miki ido kike ci gaba da xama tsakanin matan babanki ba,bayan babu abinda baki sani ba,mu dake yanzu duka sammakal" munanan maganganun da basu dace ba taci gaba da fada,wadanda suka haddasa tsaiwar tarin cak ba tare da tasha ruwa ba,sai kuma zafafan hawaye suka biyo gurbinsu.


       Kai ta kada ta juya da niyyar bar mata kitchen din saiga mama ladi itama ta sako kai,tun daga bakin qofar kitchen din ta tsinci meke faruwa,itama saita dora nata
"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" ta furta wasu sabbin hawaye da har suka sanya bata ganin gabanta sosai suka kwaranyo mata,taci gaba da tafiya kawai taba laluben hanya,amma hakan baisa sun rabu da ita sun qyaleta ba,saima leqowa da mama ladi tayi ta kitchen din ta dora
"Wato muna magana ga shashashai kina ci gaba da tafiya ko?,da yake babu uwarki ciki mu duka bamu haifeki ba,koda yake tunda kika yi mana uwar takima haka zaki.mata tsaf kuwa,tunda kin balaga kinsan namiji kinsan dadinsa kamar yadda muka sani,kinga kuwa dole kiga ai kanmu daya,daya daga cikin illolin xama da bazawara kenan,muna fada malam yana ganin ba haka ba,to yau zaizo,ni ko shi a cikin gidan nan,kwana biyu sai anyi magana ya wani ce jinin maimunatu ce ke,ina ruwanmu da wata maimuna,shi ya santa,da can baisan hakan ba sai yanzu"


       Sosai kalaman suka mata girma a qwaqwalwarta,duk da haka bata fasa daga qafarta ba,burinta daya ta isa dakinsu kunnuwanta su tserewa muna nan kalaman da mama ladi da taci gaba da tsaiwa tana jifanta dasu,me ya kawo zancan mahaifiyarta a wannan maganar?,baiwar Allahr da batasan me yake faruwa ba?,batasan da wanzuwarsu ba?,ta jima kwance cikin kushewarta cikin salama shine yanzun zasu ambatota cikin haukan kishinsu da batasan meye manufar yinsa ba?,shin wai sun manta cewa itace sila na dukka wannan daula da suke ciki?,ko iya haka bata cancanci samun dagin qafa ba daga garesu?,tana jin qirjinta na mata wata irin suya,tana jin wani irin xafi cikin qirjinta,numfashinta kamar an dora mata dutse a qirjinta yana son ya fara yi mata nauyi.....


       Kamar daga sama,kamar cikin daya daga cikin mafarkan data saba yi,kamar al'amara kamar shifcin gixo sai taji sallama daga bakin qofarsu,sallamar data dauke dukkan wani kuka da take gursheqen yinsa cak! Tashi guda!,kwatankwacin yadda ruwan sama ke daukewa lokaci daya.


       Cikin hanxari ta waiwaya,ta waiwaya dinne bawai donta yarda da sautin muryar data ji ta wadda zuciyarta ta dauki shekara da shekatu tana begen sake gani bane,ta waiwaya badon ta yarda da qaryar da kunnuwanta ke mata ba,ta waiwaya ne kawai don taga wacece mai irin muryar halitta mafi soyuwa a wajenta,muryar anty zuhriyya,anty zuhriyyarta,matar da take kallonta a matsayin mahaifiyarta.


       Fes idanunta suka sauka a kanta,komai dadewar zamani,komai shudewar lokaci,hakanan komai sauyawar zamani batajin wannan fuskar kamanninta zasu bace daga idanunta,ba mai irin muryar anty zuhriyyar bace,anty zuhriyyar ce da kanta,tsaye daga farkon farkon falon tana dan sake duban falon da alamun tantamar inda take,sanye cikin wani leshi da aka yiwa dinkin doguwar riga wadda ta fito da kyau gayu da tsarinta,hadi da girma dake nuna shekarunta sun fara sauyawa zuwa na babbar mace,bawai babbar macen data tsufa ba,aah,babbar macen da ilimi kudi da wayewa suka sake bayyana aihin wacece ita.


       Dukka lebanta na sama da qasa rawa suke,kunnuwanta sun toshe ta daina jin abinda mama ladi ke fada,idanunta kadai sune kewa anty zuhriyya kallo irin na qurill,tana tsoron kada ta bace mata kamar yadda take zuwa mata a mafarki sannan da zarar ta farka ta bace mata.


       Duk da idanu da take binta dasu amma bakinta ya kasa furta kowacce kalma,bude baki tayi da niyyar sake yin sallama cikin falon idanunta karaf suka sauka kan bilkisun dake tsaye ta kuma kafeta da idanu
"Dauhgter!"
"Anty!" Suka ambaci sunan juna kusan a tare,kana kowanne ya durfafi dan uwansa da sauri sauri,saidai kafin bilkisun ta isa ga anty zuhriyyar tuni ta sulale a wajen,tana shirin kaiwa qasa anty zuhuriyya ta tallafota jikinta,a take ganinta yasoma daukewa tafara gani dishi dishi,hakanan jinta ya soma yin low,abu daya zuwa biyu ta iya jin muryar mama ladi,sai muryar anty zuhriyya data iya banbance abinda tace saboda tana jikinya ne
"Ke kuma wacece?" Sai muryar anty zuhuriyyan still data sake fada cikin tsawa
"Ahir kada ki sake ambatan sunan maimunatu,don linxami yafi qarfin bakin kaza!" Daga haka taji antyn na sake janta jikinta,daga wannan bata sake ji ko gane ko meye yake faruwa ba jinta da ganinta suka ida daukewa gaba daya......tayi rolling dashi tabi bayan rakiya suka fice  ³⁷

Post a Comment for "SIRADIN RAYUWA CHAPTER 10 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...