SADAUKI OMAR COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SADAUKI OMAR COMPLETE

SADAUKI OMAR COMPLETE

- - Post a Comment

 SADAUKI OMAR COMPLETE Tsit! Gurin yayi duka suna mamakin futowar wannan magana daga bakinsa wacce basu ta'ba tsammaninta ba.Sarki yace."Omar ko zaka fad'ama na dalilin ka na 'kin dawowa cikin mu ko kana fushi damu ne." Kansa a'kasa yace."Bazan ta'ba fushi daku ba har abada ranka ya dad'e  babu wanda na sani a rayuwata sama daku hakanan kunyi min duk abunda iyaye kewa 'yayan su kun dauke ni a matsayin danku Saboda haka tsakanina daku babu fushi ko wani kulli na daban kawai  bana jin zan sake zama cikin gidanan saboda wasu dalilai na wanda na barwa kaina su ina fatan wannan magana tawa bata 'bata ranku ba idan na 'bata muku rai to ina neman afuwarku ku gafarce ni.''


Sarki!! Yayi gyaran murya a nutse yace."Ba tun yau ba na san Halin Omar da magana d'aya gami da tsayayya kan abunda ya fad'a ni nasan akwai hujjar da ta sanya ka bujirewa bukatarmu ko wannan ya ishe mu mu gane cewar kai d'in jarumin namiji ne wanda ke tsaye kan iyalinsa tabbas na jinjina maka da har kayi nasarar kashe maciji mai girma irin wannan saboda haka baza mu takura maka ba domin bamu san manufarka ba, duk inda zakaje da aysha kaje amanarka ce kamar yanda kafad'a kuma ina kara tabbatar maka da cewar sai yanzu nake alfahari da wannan auran naku sosai dole duk wani uba nagari wanda yasan abunda yake yayi sha'awar yarshi ta auri namiji tsayayyaye mai tsayuwa kan iyalinsa da kare lafiyarsu Omar!! Wannan masarauta mai cike da dumbin tarihi tana alfahari dakai har abada."


Omar ya d'ago kansa yana murmushi yace."Allah ya taimake ka nima ina alfahari da kasantuwa ta a tare daku Ubangiji Allah ya 'kara daukaka wannan masarauta mai cikakken tarihi."


Duka suka amsa da ameeen, Umarulfaru'k."!! Shi kanshi Galadima yanzu duk wani haushi da kishin Omar din ya daina ji wannam jihadin da yayi na kashe maciji ya ishi kowa ishara a cikinsu duka sun tabbatar da cewar zai rike a aysha bakin rai bakin fama kamar yanda ya fad'a musu.


Nan yake sanar musu da cewar ya nemi aiki kuma ya samu da izinin Allah zai fara kwana biyu masu zuwa." Sarki yayi ta sanya masa albarka da fad'in "Insha Allah zai sanya ayi masa saukar a'lkur'ani me girma.


To duka albarka suka sanya masa banda faisal dake cika yana batsewa yaso dawowar su gidan ko don ya cigaba da cunguna masa shi dai yana tsananin kishi da irin baiwar da Allah yayi ma Omar din.


Falani da Omar a palon ta suna hira cikin sakewa gami da wata irin kauna da suke ma junansu Falani tace" A gaskiya Omar naji dad'in aikin daka samu ina yi maka fatan alkairi har karshen rayuwarka amma ina neman wata alfarma a gurinka." Yace."Mama ki fad'i ko wace alfarma ce insha Allah idan ina da iko zanyi miki ita."Tace."Tunda dai haka ta kasance nace mai zai hana na sauya muku gurin zama daga wanda kuke zaune sai ku dawo da zama cikin daya daga cikin gidajena dake unguwar *Kurawa* Hankalina ya tashi da faruwar wannan lamari."


Yace."Mama babu abunda zai sake faruwa da izinin ubangiji ki kwantar da hankalin ki insha Allahu zamana cikin wannan gidan ba zaiyi tsayi ba saboda ina sanya ran company da nake wa aiki zasu mallaka min gurin zama  kusa dasu ina ganin nan da wani lokaci magana zata 'kare, Wannan abun da ya faru sam ban so kuka ji ba saboda ba abune na dadi ba idan wani ya fahimci al'amarin cikin kyakyawar siga wani bazai fahimta ba ban ta'ba tunanin aysha zata fad'i maganar ba kowa yaji.""A'a Omar wannan lamari ne wanda ya cancani kowa ya sani duk wani masoyinku dole ya jajanta al'amarin ha'kika da nasan har yanzu unguwar ba tara mutane ba babu abunda zai sanya ni nace kaje ka zauna cikinta rabona da zuwa inga gidan shekaru shida kenan tunda aka gama gina gidan naje na gani na sanya albarka a ciki to tun sannan na dam'ka makkullin gidan  gurin mao unguwa kaji dalili da ya sanya dukanin wannan al'amari ya afku." Yace.''Haka maganar ki take mama amma kar ki manta duk wanda ya yarda da Allah ya kuma mi'ka lamuransa a gareshi to babu shakka yana tare da kariyarsa Saboda haka ina so duk wata fargaba da take damunki ki cire ta daga ranki Mama insha Allahu Allah zai tsare miki Omar a duk inda yake."


Murmushi tayi ta d'ora hannunta akansa tana fad'in"Insha Allah Omar kana tare da alkairai da nasarori a rayuwarka." Murmushi yayi  Yace."Mama ina Amanata ne. na kwana biyu ban ganta ba Mama na sha kewar ku da yawa"!? 'Yar dariya tayi tace"Safara'u manya kenan Tana cikin daki kwana biyu haka take takure kanta kullum cikin 'kananun hawaye har sai da nagaji na titsiyeta ina tambayarta shine tace min wai kai take tunani."!


Omar ya sanya dariya ya shafa sumarsa shi kanshi kwana biyu yayi missing din Safa sarkin dariya yayi missing din dariyarta da jerarruk kananun ha'koranta da yake masifar so."


Fulani tace.''Bari in sanya a kira maka ita nasan dai kome ke damunta zata fad'a maka tunda dai kaine abokinta." Ya saki murmushi a nutse yace."Kwarai kuwa mama aboki dan uwana nake gurin Safa ina jinta kamar wacce muke ciki daya da ita yanayin yanda ta tsinci rayuwarta na bani tausayi."'Kwarai kuwa shiyasa nake tausaya mata nima kullum addu'a ta shine Allah ya bata miji nagari wanda zai duba maraicin ta."Jakadiya ta sanya ta kira Safara'u ta shigo cikin doguwar abaya ire-iren kayanta kenan ta yane kanta da karamin mayafi mai kananun dutsina....Tana ganin Omar ta washe bakinta aikuwa duka jerarrun ha'koranta farare tas!! suka bayyana Omar ya ji wani irin yarrrrr! a jikinsa duk sanda Safara'u zatayi irin wannan dariyar a gabanshi sai yaji kamar ya kama bakin ta ya tsotsa."Wayyo Sadaukina! Yaushe kazo ne."!! ? Tafada tana me 'karasowa inda suke Mama Fulani tace." Ko kunya baki ji ka Safara'u yaushe rabon da inga kinyi irin wannan dariyar."Ta rufe fuskarta da mayafi tana fad'in"Kai Mama."!Dariya tayi tace"Ai ba karya nayi miki na kullum kina sinke a daki kina kananun hawaye da tunani Sadauki gashi yanzu ko kunyw kina washe baki don kin ganshi."


Cike da kunya take boye kanta cikin mayafi still tana dariyar tana le'ken Omar din,  Shima mirmushi yake mata yana so mama ta barsu su kad'ai ya kalli dadashin Safara'u san ransa.


Mama ta mike tana fad'in''Bari in barku kuyi hirar zumunci Omar ka tabbatar da ta fad'a maka dukanin damuwarta.


Yace.''Insha Allahu Mama.'' Tana futa ta bud'e fuskarta tana kyalkyala dariya sai kallonsa take Omar ya shiririce gurin kallonta sai shafa sajen fuskarsa yake.


Yace."Shin wai meye abun dariya ne ke komai dariya ba kya gajiya ne? Ko kuma kin hango wani abu a jikina wanda ya baki dariya."Tsagaitawa tayi tana fad'in"Ba dole inyi dariya da murna ba yau na ganka Allah kuwa kwanaki uku da bana ganin ga ni kadai nasan halin da na shiga."!! Cikin shagwaba take maganarGirarasa guda ya d'aga mata yana kanne mata ido daya cikin wata iriyar siga yace."Me yasa kika damu dani da yawa ne."!?


"Saboda ina son.....Sai tayi shiru kuma ta kasa 'karasawa." Fuskarta ta rufe da mayafinta tana yar dariya duk da ta rufe fuskarta bai hanashi hango kwawan ha'koranta ba Yace."Ki bude fuskarki kiyi min bayani hummm!! Yau kuma ni ake jin kunya.''? Da murmushi a fuskarsa yake maganar.Bud'e fuskarta tayi tana wasa da hannunta yace."Safa manyan gari Mama tace kina kuka duk kin damu ko zaki iya fad'amin abunda ya sanya kike kuka da sanya wa kanki damuwa."

Post a Comment for "SADAUKI OMAR COMPLETE "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...