RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

- - Post a Comment

 

RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO


Wannan ma littafi ne da zamu dinga kawo muku shi a wannan website namu kudai ku kasance damu a koda yaushe Www.bankinhausanovels.com.ng 

KADUNA 


Da yammacin ranar Alhamis ne, Allah ya yalwata garin na Kaduna da ruwan sama. Hakan ya jawo boyewar jama’a da dama domin fakewa ruwan. Ruwane ake tsugawa mai Karfi kamar zai fasa saman kwanukan jama’a. Cikin hukuncin na Rabbi, wanda ya saukar da ruwan ba tare da wayonmu ko dabararmu ba, ya tsaida abin shi cak! Cikin lokaci Kalilan. Hakan ya sa jama’ar da ke Boye suka fara firfitowa kowa na KoKarin kama gabansa, domin gab ake da kiran Isha’i. A irin wannan yanayin da za ka ci nasarar leKa dakunan jama’a za ka tsinci kowannen su a Kundudune cikin rigar sanyi, ko kuma bargo. Marasa Karfi kuwa, irin almajirai da sauran su, suna Kudundune a lungu ko kuma cikin zannuwa. 


Alhaji Lukman ne zaune a mazaunin direba, yana tafiya a natse bisa shimfidaddiyar kwalta, fuskarsa babu alamun gajiya ko kuma Kosawa da irin cinkoson motocin da ya ci karo da su kafin, ya sami daman hawa saman gada. Hakan ya dasa masa tunani kala-kala a cikin 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Zuciyarsa. A wannan karon zuciyarsa ta gama karaya, har ya soma jin ya gaji da yadda hanyar ba ta motsawa. Babu abinda yake hange a yanzu kamar gidansa da ke cikin rukunin gidajen na Unguwar Rimi. Yana son watsa ruwa, haka ba . ya son isha’i ta riske su a hanyar. 


Duban agogon cikin motarsa ya yi wanda , yake nuna masa Karfe bakwai da rabi. A _ zuciyarsa ya ce, ya makaro. Cunkoson ababen hawan suna ci gaba da yawaita ne daga saman gadan, hakan ya sa ya dan waiwayo ya dubr * dansa Sultan da ke kallon gefen titi hankalinsa kwance.. Ta madubi ya dubi matarsa Hajiya * Salma, ita ma dai idanunta suna kafe a cikin jarida. 


Ya sake mayar da hankalinsa a kan kwaltar yana duban yadda kowa ke sauri domin isa ga muhallinsa. Ganin yawan cunkoson ya fi yawa ne daga saman gadar, yasa ya sauya ra’ayinsa, wajen sauka Kasa ya bi ta Kasan gada. Wanda yake hango tarin sauki fiye da tsayuwarsa a inda bai san lokacin isarsa gida ba. 


Hajiya Salma da ke hakimce a baya, ta dago daga karatun Jaridar da take yi, idanunta Www.bankinhausanovels.com.ng 

 manne da farin gilashi, tana duban yadda Maigidanta ya sauya hanya, hakan ke tabbatar masu dole sai sun je Mando kafin su yi kwana. Babban dansu mai shekaru goma sha biyar a’ duniya yana ci gaba da watsa idanunsa a bisa titin kamar mai son tuna wani abu. A cikin zuciyarsa kuwa ji yake kamar a dauwama a cikin irin wannan yanayin, kasancewarsa mutum mai tsananin son damina. Yanayin da ke sa shi farin ciki fiye da kowanne irin yanayi.

Tun bayan fitowarsu daga Jaji, gidan. mahaifiyar Abbansa, suka shiga mota, babu wanda ya furta ko da kalma daya. Kowa da irin . sake-saKen da yake yi, kasancewar ita zuctya ba a raba ta da yawan tunane-tunane, duk da shirme yafi yawa a cikin dukkan tunanin. Haka tsarin su yake, ba su damu da dole sai sun yi surutu ba, idan kuwa za su yi sai ya kasance mai ma’ana ne, kasancewarsu ‘yan boko masu ji da kansu. Ko cikin gidan su ka shiga za ka sami gidan su shiru kamar babu kowa a cikinsa. Sau tari idan sun shiga za ka sami gidan shiru kamar babu kowa, shi ya sa da zarar masu surutu sun kawo ziyara gidan, suke tattara surutunsu, su ajiye tsakar gida. Suna fitowa suke nada gammo su dauki abinsu. Domin ko ka yi babu mai ba ka cikakkiyar amsa. Sau tari masu surutun cikin dangi suna fitowa daga gidan suke fara tsinewa bakin hali da son korar bako da Karfi da yaji irin na gidan Alhaji Lukman. 

Sultan ya dan dubi mahaifinsa, kamar zai basar, sai kuma ya ce, “Abba idan ka sami wuri ka tsaya kusa da tashar motocin can, zan sha kayan marmari sannan ina jin fitsari, zan je in yi,” Yana maganar yana yamutsa fuska kamar wanda akai wa dole sai ya yi. 

Hajiya Salma ta dago tana duban danta, “Sultan ka bari mu Karasa gida mana. Ba ka san ana daukar ciwuka wajen tsuguno a irin nan wajen ba ne?” ta yi maganar tana sake zura idanunta a kansa cikin kulawa. 

Idanunsa ya sake watsawa a bisa titin, yana nazarin har yaushe cunkoso zai ragu su isa gidan? Girgiza kansa kawai ya yi ba tare da ya ce uffan ba, ya dawo da kallonsa ga mahaifinsa da ya sami wuri ya tsaida motar. Gorar ruwa ya dauka ya fice daga motar. Idanu yake rarrabawa 

yana neman inda ya kamata ya yi fitsarin. Wurin 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

ya jagalgale da yawa, don haka ya dinga jin Kyama ya kasa ajiye Kafafunsa yadda ya kamata. Lalacewar wurin ya darsa masa danasanin fitowarsa, amma kuma yadda yake jin fitsarin ba zai iya haKura ya koma ba. Bayan wata Katuwar mota ya samu ya zaga, sannan ya yi abinda ya kawo shi, ya mike hannunsa riKe da ragowar gorar ruwan yana son fita ya wanke Kafafunsa. Numfarfashin da yake ji sama-sama kamar akwai wani abu a kusa da shi, ya sa ya dan dakata da tafiyar da yake yi, tare da kasa kunnensa sosai Yadda yake jin numfarfashin yana Karuwa, ya sa Kafafunsa suka kama rawa-. Tsananin tsoro ya shige shi. Don haka ya yi tsalle gefe guda yana zare idanu. Ji ya yi kamar an sawa Kafafunsa dabaibayi. Ji ya yi kamar Kafafun sun gaza daukarsa. A hankali yake jiyo sautinta, “A taimake ni! Ruwa! Ruwa! Zan mutu.” Cikin Karfin hali da son ganin mene ne ya daga kafarsa daya ya sake daga dayar ya nufi wurin da sautin ke ratsa kunnuwansa. Gumi ke. — tsattsafo masa kamar ba shi ba ne ke jin sanyi. Duk yadda ya so ya yi Karfin halin tunkarar 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

shiga wurin da yake jin sautin abin ya faskara. Da baya da baya ya koma yana sake waige kamar mai neman wani abu. Wani ya hango daga shi sai singlet da buta a hannu, rudanin da ya shiga ya hana shi mamakin yadda ake kwada sanyi, amma kuma babu riga a jikinsa. Da sauri ya bi bayansa, “Malam! Ina jin Kara a kusa da babbar motar can, don Allah zo ka duba ka gani. : . 


Mutumin ya zabga masa harara, “Kai! Me kake yi a nan? Idan ba ka wuce ba, za ka ci mutan gidanku.” Ya sa kai da nufin tafiya Sultan ya sha gabansa, “Don Allah ka zo ka gani.” Tsayawa ya yi yana Kare wa Sultan kallo cikin duhun, kafin ya ce, “Mutum ce a wurin sai kuma me kake son ji?” Mutumin da ya yi shayeshayensa ya baiwa Sultan amsa cikin Kufula a kan bata masa lokaci da yake neman yi. 


Sultan ya zazzaro idanu alamun firgici. “Mutum? To me yake yi a wannan wurin? Ku ce ya tashi wani abu zai same shi.” Sultan ya jero wadannan kalaman cikin kidimewa. Da alamun Sultan ya fara kai mutumin bango idan aka yi la’akari da kallon banzan da yake aika masa. 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

| Gyara tsayuwarsa ya yi ya ce, “Kai yaron nan akwai shegen naci, kamar irin kafiran farkon nan. Eh mutum! Mutum din ma mai numfashi. Ba namiji bane mace ce, Saudatu ce, take yaudarar jama’a da Hijabi sai ga cikin shege. Ko da yake arniya ce, ta shigo mana musulunci da masifa. A nan Kasan motar take kwana. Kila ma nakuda take yi, don yau kwananta biyu kenan ban ganta ba. Da a can take kwana aka koro ta.” Ya nuna wani wuri da hannu, wanda babu komai a gun Sal tayoyin babbar mota. 

Tunda yake magana Sultan ya kafe shi da idanu ta hasken motocin da ke wucewa, suna hasko su. Sai dai kafin ya ankare ya sake samo tambayar da zai yi masa har mutumin ya wuce abinsa, yana auna wa Sultan zagi. Numfarfashin da ya sake jin ya Ziyarci kunnuwansa, ya kanainaye zuciyarsa da wani irin tausayl. Damuwa ce manne a zuciyarsa. 

Wannan karon da rashin tsoro ya doshi Karkashin motar, wanda ga dukkan alamu motar ta jima da tashi aiki. Kai tsaye ya rankwafa-ya ~ shige. Ruwan saman da aka yi ya sami 

makwanci a KarKashin motar, 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

 “Sannu Anti. Anti me kike son in kawo maki? Don Allah Anti kiyi min magana kin ji?” Wasu hawaye suka sake tsinke masa, wasu suna korar wasu. Cikin hukuncin Allah aka hasko hasken fitila, wanda ya ba Sultan daman kallon fuskarta. Hawaye ne kwance a bisa fuskar. Idanunta a rufe. Bude idanun ta yi , ta zubawa Sultan, tana kallon yadda hawaye suka bata masa gaban riga. idanun ta mayar ta rufe. Ganin yadda take kuka yasa ya sake Kankameta yana kuka sosal. 

Tunda yake bai taba ganin babba yana kuka ba, sai a kan Saudat. “Anti ki yi hakuri ki daina kuka. Ki yi addu’a ne Anti don Allah.” 

Cikin sautin muryar marasa lafiya ya ji muryarta tana magana, “Na gode, na gode. Ku taimakeni ku raba ni da nan za a kasheni ne.Ina son ko ban rayu ba, abinda ke cikin cikina ya rayu, domin dasawa wanda ya kawo ni nan, bakin ciki da tabon da ba zai taba gogewa a tarihin zuri’arsu ba. In gaya maka wani abu, da kuma littafi ka tafi da shi ka miKawa wani babba, wanda zai iya taimaka min wajen yada labarin nan? Ka yi alKawarin ko bayan raina za ka taimake ni ka tona asirin wanda ya sa jefa rayuwata a cikin masifa? Kayi alKawarin za ka Kwatowa dan da zan Haifa ‘yancin sa?” 

Kwakwalwar Sultan ta yi karama da sauraren wannan kalaman na Saudat. Kukansa ya Karu ya gyada kansa ba tare da dogon nazari ba, alamun ya amince. Yana son yin magana a lokacin da ta mika hannu take nuna masa wani Boyayyen buhu a sakale, wani mutum ya fizgo shi da Karfin tsiya, kan Saudat din ya koma gefe. A gaban Abbansa suka tsaya a lokacin da yake jin muryarsa yana cewa, “Kada ka ji masa ciwo mana malam!”’ 

Sultan ya fizge da Karfin tsiya daga irin rikon da mutumin ya yi masa ya zube a gaban mahaifinsa a bisa guiwowinsa ba tare da ya damu da cabalbalin wurin ba. “Abba ka taimake ni kada ta mutu. Abba ku bar ni in je inji abinda za ta gaya min. Abba za ta mutu idan muka tafi.” 

Abban ya kai kallo ga Hajiya Salma, wanda dukkansu mamakin Sultan din ne ya rufe su. Kafin su yi magana mutumin da ya finciko shi daga gun Saudat ya fara magana, “Alhaji ka kama yaron nan naka ku bar wurin nan. Yarinyar nan cikin shege ta yi, saboda rashin kamun kai 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

ko da kuwa daki daya kuke kwana. Zai kasance akwai jahilci a cikin jama’a da suke tunanin H.1.V zai shafi makusancinka. Na gode.” Kallo ya bi shi da shi har ya isa ga matarsa ya ja suka wuce. 

Lokaci bayan lokaci yana jin dirar kukan yaronsa har tsakiyar kansa. Amma kuma babu wanda ya iya Kara cewa komai. A haka suka Karasa gidan, ‘yan Kannensa su biyu, Hafsat da Haidar suka taso da gudu daga hannun Mairo mai aikinsu, kai tsaye gurin Sultan suka nufa. Ya shafi kansu kawai ya wuce ciki. Duk: suka bi jikinsa da kallo, sannan suka dubi Abbansu suka ce, “Abba me ya sami Yaya Sultan jikinsa ya lalace? Ya fadi a kwata ne?” 

A nan ma babu wanda ya ce masu komai. Shi kuwa yana shiga ya fada bandaki ya yi wanka da alwala ya fito ya shimfida darduma ya gabatar da Sallarsa, a nan kan daddumar ya yi barci, tare da sa hannunsa a matsayin matashin kai. 

“Umma! Umma!! Abba!!! Innalillahi wa inna ilaihirraji’un. Me ta yi maku? A’a don Allah ku bar min Antina kada ku kashe ta.” 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A guje suka shigo dakin suna girgiza shi. Cikin tashin hankali da gigicewa ya tashi da Karfinsa ya ture su ya yi hanyar waje da gudun gaske. Cikin sa’a mahaifin ya kamo shi ya rungume shi a Kirjinsa yana shafar bayansa, “Ka natsu Sultan ni ne mahaifinka. Ka natsu ka ji? Mene ne?” 

Cikin hawaye masu yawa da ke sauka daga kwarmin idanunsa, “Abb... Abba..” 

Ajiyar zuciya ya saki da Karfi, kamar wenda zai hadiyi zuciya. “Abba idan bamu je mun taimaki Anti Saudat ba, nima zan tafi can da nisa inda ba zaku ganni ba.” Cikin jin zafin kalaman yaron kamar ya watsa mata ruwan zafi, ta Karaso har gaban Alhaji Lukman ta finciko yaron ta dauke shi da mari har sau biyu, kafin ta kai hannu ta buge masa baki tana huci. “Dan ubanka zo ka kwashe kayanka ka bar min gida shashashan yaro. Har kayi girman da Za ka fara’ sa min ciwon kai Sultan? Duk cikin mutane ka rasa wacce za ka ce a taimaketa sai karuwa? Mazinaciya? Tubabbiya? Wacce iyayenta suka guje ta? Bare mu haduwar Kaddarar fitsari? Uwa uba mai dauke da cutar da kaf zuri’arku sai tabi Www.bankinhausanovels.com.ng  ta kashe daya bayan daya. Na ji a jikina matsala ce ke shirin tunkarar mu shi ya sa na hanaka zuwa fitsarin nan, kayi min kunnen shegu.” 

Ran Alhaji Lukman ya kai matuKa a baci, ya dinga dubanta kamar bai taba ganinta ba. “Akan matsalar nan zaki dukar min yaro? Ke kin fi Karfin Allah ya jarabceki ne? Ko kuwa har kin gama tsara abubuwan da za su faru da ke a gidan duniya ne? Har kin gama tsara komawarki gare shi? Kina da yara mata kike tsinewa na wasu? Daman kina tunanin zaki dauwama a duniyar ne?  zamu mutu, ta hanyar da Allah ya tsara mana a cikin littafinsa. Sultan yana dafe da Kuncinsa ya Karaso kusa da Abbansa ya ce, “Abba, Anti.” Sunkuyawa ya yi ya rungume yaron, “Ka yi hakuri Sultan, zuwa gobe sai mu Je mu dauko ta. Ka ga yanzu Karfe goman dare.” 

Sultan ya girgiza kai, “A’a Abba idan ba mu je yau ba, za ta mutu ni kuma bana son ta mutu.” Murmushi ya yi “Yadda kace haka za a yi Sultan. Amma ina son ka sa a ranka, kowani , Www.bankinhausanovels.com.ng  rai sai ya dandani dacin mutuwar nan. Ba mu Zo domin mu zauna a duniyar ba. Ta so mu je.”

Hajiya Salma, da taji gabanta ya fadi, ta fice daga dakin ranta a matuKar bace. Tun kafin ya fara tuki ya kira ‘yan sanda ya yi masu bayani tare da kwatanta masu wurin yana son su riga shi zuwa. Yana kashe wayar ya kira Asibiti, ya ce yana buKatar motarsu tare da kwatanta masu wurin. Sultan dai sai kallon fitilun gefen titunan yake yi ransa a jagule. ba kamar dazu ba, da yake jin nishadi. Gani yake kamar mahaifinsa baya sauri. Duban yaron ya yi bayan ya murza sitiyarin ya sha kwana, “Sultan, ka yi min murmushi mana. Ka ganka kuwa? Gabadaya fushi baya yi maka kyau, sai ka koma sak! Hajiya Gwaggo.” 

Kallon mahaifinsa ya yi idanunsa cike da hawaye, “Abba sai andauko anti.” Lallai tunda yau ya kasa samun fara’ar yaronsa, ya san abin da gaske ne. Shi kansa yana jin kwatankwacin abinda yaronsa ke ji. 

Tunda suka yi fakin Sultan ke bin motar ‘yan sandan zuwa motar asibitin da kallo. Gaba daya ya kasa sauka sai da mahaifinsa ya yi masa 

Www.bankinhausanovels.com.ng magana. Shi kansa Alhajin yadda ya kula da kamar hankalin ‘yan sandan a tashe ya isa ya gamsar da shi akwai matsala. A tare suka iso suna mai sake kafe su da idanu. Daya daga cikin su ya Karaso hannunsa rike da wayar sadarwa, “Alhaji muna isowa muka hadu da tashin hankali. Baiwar Allahn da ka kwatanta mana ita ga ta can kwance cikin jini, wasu marasa imani sun sassare ta har Allah ya yi mata cikawa. Mun iso dai-dai sun gama ta’asar. Mun yi iya bakin Kokarinmu mu kama su, amma hakan ya gagara-. Tarasu.” 

Sultan da jikinsa yake kyarma, ya durKushe Kasa yana wani irin kuka, “Ant Saudat!! Me za ki gaya min?” Iya abinda bakinsa da ke karkarwa ya iya furtawa kenan. Sauran maganar ta maKale a makoshinsa. Kuka ya tokare masa ya hana su fitowa, Alhaji Lukman ya lumshe idanunsa, “Ya Salam!” 

Hawaye suka cika masa idanu, yasa hannu ya sharce. Jikinsa ya yi matuKar sanyi, “Allah ya jikanki.” . 

Sultan ya mike cikin kuka ya isa kan gawar da ke shimfide da Katon cikinta a gaba. 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Duban ‘yan sandan ya yi yana ganin su dishidishi. Har sun kammala daukar hotunanta da kuma rubuce-rubuce. Idanu ya zuba mata har zuwa yatsunta da ke ‘dauke da wani zobe mai kyau. Kurawa hannun ido ya yi. Ya sa nasa hannun ya rike ta, yana jin kamar numfashin zai dauke. A hankali ya :zare zoben da ke hannunta ya mayar cikin aljihunisa. 

‘Yan sandan sun so su raba shi da gawar, Abban ya dakatar da su, “Ku bar shi ya rage radadin da ke damunsa, tun dazu yake mana magiyar mu je mu dauko ta ashe mutuwa za ta yi .” Kwalla ta ziruro masa daga idanunsa, ya girgiza kai kawai. A dai-dai lokacin kiran Hajiya Salma ta shigo wayarsa. Ya ji duk ya tsaneta. Ya tabbata duk namijin da ya ce zai biye wa shawarar wata macen sai ta kaishi ta baro. Dauka ya yi ya sa a kunne yana magana cikin rawar murya, “Baiwar Allan da take miko hannu take bukatar taimako kika hana, saboda dalilin kin tsani zina, kin tsani mai dauke da cuta, kin tsani wacce ta tuba ta koma addininki. Wadanda suka fi ki tsanar wadannan abubuwan sun kashe ta sun kawar da ita daga duniyar gaba daya.” Sauke 


Shin me zai faru? Kudai kuci gaba da bibiyar mu Www.bankinhausanovels.com.ng 

Post a Comment for "RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 1 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...