RAUDHA CHAPTER 9 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RAUDHA CHAPTER 9

RAUDHA CHAPTER 9

- - Post a Comment

 RAUDHA CHAPTER 9

Biri da wando ta saka me santsi Light orange, ƙasan wandon me fela ne sosai, sai ta saka top fari iya gwiwar ta, me kwalliyan stones, sannan sai ta naɗa blue ɗin ɗankwali a kanta, wanda ya fito mata da gashin ta ta ƙasan ƙeya, Light makeup tayi da ya fito da tsantsan kyawun ta, kai Masha Allah duk wanda ya ga RAUDHA wannan lokacin bazai so ya ɗauke idanun sa ba, ta haɗu iya haɗuwa sai wanda ya gani, takalmin da ta saka me tsinin gaske ne cover me igiya, kalan Light blue da farin Socks a ciki, sai tashin ƙamshi take yi irin turaren nan na Arabian+


Ramcy dake zaune saman sofan ɗakin ta, sakin baki tayi tana kallon ta


Sai da RAUDHA ta matso kusa da ita, ta sanya hannun ta ta shafa fuskar ta tana murmusawa. Sannan a time ɗin Ramcy ta rufe bakin ta bayan ta dawo da tunanin ta jikin ta


"What happened Besty?"


Gwauron numfashi Ramcy ta sauke kafin tace, "ban san me zan ce bane wlh Besty, haɗuwar ki yayi yawa. Masha Allah gaskiya ki gode Allah".


Murmushin ta me kyau ta saki kafin ta lumshe ido ahankali ta furta, "Shukran Lak, linazhab".


Da ido Ramcy tayi mata magana, "wai what?"


"Let's go".


Miƙe wa Ramcy tayi tana gyara zaman gyalen ta, itama tayi shiga ne cikin baƙin yadi me santsi, ɗinkin doguwar riga, duk da kasancewar ta baƙa but sosai tayi kyau matuƙa, kasancewar an yi wa rigan ado da jan zare sai Stones, kuma tayi amfani da jan ɗankwali ne sai farin gyale.

      Fita suka yi, inda tuni an gama taruwa su kaɗai ake jira a wajen. A hanya suka haɗu da Farida ta zo kiran su, sai suka tafi tare, itama kanta sai ya ba kwalliyan RAUDHAN take yi


Ita kuwa sai murmushi take saki me fid da sihirtaccen kyawun ta, tana takun nan nata ɗai-ɗai me ban sha'awa, kasancewar bata yafa gyale ba, shiyasa duk inda jikin ta ya juya ana ganin komi ta yanda take sarrafa jikin ta.


      Tun doso wan su wajen sai idanun mutane kawai ya koma kanta, hakan yasa wasu da hankalin su be kai kanta ba, sai duk suka kallo wajen


Tana tsakiyar Farida da Ramcy ne, suna taho wa wajen


Nan da nan aka soma tafi sabida sanar wan da MC ke yi na zuwan ta, nan ya soma koɗa ta yana kambama ta


Ita kuwa idanuwan ta na kan su Daddy da ta hange su, su ma suna mata murmushi, Suhaib har da ɗaga mata babban yatsan sa alamun tayi zam-zam. ita kuwa ta saki murmushin nan da ke ƙara wa fuskar ta kyawu.

"Kai man juyo ka ga wata halitta don Allah". Cewar Sharif da yayi maganar a hankali kusa da kunnen Zulain dake waya ya karkace kai


Juyo wa yayi kuwa, yana shirin hararan sa sai idon sa suka sauka kan RAUDHA dake tafiya zuwa wajen zaman ta, take anan komi nasa ya tsaya illa idanun sa da ya lumshe ya sake buɗe wa akanta, yana son tabbatar wa kansa itan ce ko kuwa?. Maganar Sharif ya sake dawo da shi hayyacin sa


"Ni wlh da na san S. Makamashi yana da ƙanwa irin wannan, ai da tuni ita na nema, me zai kai Ni zuwa waje gida be ƙoshi ba".


Shiru Zulain yayi don hankalin sa be gama dawo wa kan Sharif ba, bare ya tantance me yake faɗa, idanun sa ƙyam akan RAUDHA har ta zauna ta yanda yanzu yake ganin fuskar ta sosai. A take ya saki wani irin ajiyan zuciya yana sake lumshe ido


A tare Sharif da Mom ɗin sa da suke waya, suka je ho masa tambaya the same


Buɗe idanun sa yayi yana kallon Sharif da ya tsaya kallon sa shima, sai kuma yayi saurin kara wayan a kunnen sa sosai yana faɗin, "Mom zan kira ki letter please". Ya Yi saurin katse wayan be jira cewar ta ba, nan ya sake mayar da idanun sa kan RAUDHA gaba ɗaya ya mayar da hankalin sa gare ta, sosai yaji daɗin ganin ta da baki ma bazai iya furta wa ba, har wani sakin murmushi yake yi batare da ya sani ba


Sharif dake faman kallon sa baki sake, ya jinjina kansa ya ce, "cab ɗijam.. Kar dai har ta sace maka zuciya daga kallon farko?"


Zulain be kalle sa ba don ba ya son abunda zai gilma ga kallon kyakykyawar nan, amma kuma sai ya ɓata fuska yana kumbura shi irin maganar Sharif ɗin fa ya fara isar sa


Murmushi kawai Sharif yayi be ce komi ba, ya mayar da hankalin sa shima ga abinda ake yi.

      A lokacin RAUDHA ta miƙe ne tana speech da muryan ta me daɗi da ya karaɗe wajen. Sosai duk mahalukin dake wajen ya mayar da hankalin sa gare ta cike da sha'awa. Har ta gama aka soma mata tafi Raf.. Raf... Raf


Sannan sai Suhaib ya amsa ya sake ma kowa godiya tare da yaba wa ƙanwar sa, da nuna irin tsantsan ƙaunar da yake mata. daga nan kuma Daddy ne ya amsa shima ya soma yabon ta sosai, da abun mamakin da ta ba su, tare da nuna wa mutane tsantsan alfaharin da yake yi da ɗiyar sa


Haka ake ta tafa wa cike da tsananin burge su da suka yi, don sosai iyalan suka burge kowa. Haka dai aka ci gaba da gudanar da partyn cike da sha'awa, inda daga baya MC ya kira RAUDHA domin ta taka


Murmushi kawai ta soma zuba wa, domin har yanzu ƙaunar ta da rawa yana nan, sai dai yanzu ba kamar da ba, duk da a yanzu ta koyo irin rawan larabawa ne, ko tana yi zaka ka bata cika yin irin na nan ba saboda ya zame mata jiki na larabawan. Tashi tayi ta fita ta soma taka wa a hankali tana dariya bakin ta ya ƙi rufuwa


Nan Suhaib ya taso ya soma taya ta


Yanda yake rawan ne sai da ya ba kowa dariya, sai tafi ake musu


Ita RAUDHA ta saka a sauya musu, don ta kasa yi sosai sabida waƙar Hausa ce, sai ta ce a saka mata na Laraba wa, ai nan ta soma taka wa irin nasu sosai, sai shima Suhaib ya biye mata suna yi tare, har da riƙe hannu irin na laraba wa yanda suke yi


Sosai yanzu ɗin Suhaib yafi ba wa kowa dariya, kowa ka gani wajen nishaɗi yake yi.

     Lumshe idanu Zulain yayi saboda tsantsan wani farin ciki da yake ziyartan sa, sosai yarinyan ta matuƙar burge sa fiye da tunanin mutum, nan da nan ya ji soyayyar ta me tsananin ƙarfi ya kama sa. Har wani buga tagumi yayi da hannu biyu yana bin ta da kallo.


     While sauran samarin, abokan Suhaib duk haka ne a wajen su, kowa fatan sa ya dace da mallakan kyakykyawar balarabiyyan nan.

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


     Wata farar mota ce ta shigo cikin gidan a wannan lokacin, ahankali motan take tafiya har zuwa inda akayi parcking motoci, kamar mintuna biyu da tsayuwar motan aka buɗe ƙofan, sai dai wanda ke ciki be fito ba, illa ziro fararen ƙafafuwan sa dake cikin baƙin sandal Shoes da yayi waje


Daga inda yake duk da akwai tazara sosai da inda ake partyn, amma kuma hakan be sa tattausan waƙar larabawan dake tashi a wajen kasa ratsa masa kunnuwa ba, take anan ya lumshe idanun sa cike da jin daɗin waƙan, kamar shuɗewar mintuna biyar ya buɗe su yana aza idanun sa kan wayan sa dake saman cinyan sa, ɗauka yayi ya soma dubo Numban Suhaib da yayi masa serving da Dude yayi kira


While Suhaib na filin rawa yana tiƙan rawa tare da RAUDHA, sai yaji wayan sa na ruri, dasauri ya saki hannun ta yana zira wa cikin aljihu ya ciro wayan, ganin sunan Dude a screen ɗin wayan na yawo, sai nan da nan fara'an sa ya ƙaru, matsawa yayi gefe yana answer call ɗin ya kara a kunne, "Dude".


"Surprise! Gani a cikin gidan ku".


Waro ido Suhaib yayi, "haba don Allah".


Murmushi yayi shi kuma yace, "ka zo ka gani, ina nan wajen parcking space". Daga haka ya katse wayan


Da sauri Suhaib yayi hanyar barin wajen


Inda RAUDHA ta kira sunan sa


Juyo wa yayi yana kallon ta. Ta ɗage masa gira akan "ina zai je?"


Nuna mata yayi da hannu wai "yanzu zai dawo".


Ta marairaice fuska kafin ta juya ta nufi wajen zaman ta. A lokacin ne aka soma bata kyaututtuka.


            🌐🌐🌐


       Suhaib na isa wajen parcking space, Rayyan dake mota ya fito yana rufe wa. Rungume juna suka yi cike da tsananin murna, kafin kuma su saki juna suna cafe hannayen su ko wanne baki a washe


"Dude wlh ka shammace Ni, nayi tunanin ba yanzu zaka dawo ba".


Murmushi Rayyan yayi yace, "dama wannan week ɗin zan shigo, but sai naga dacewar shigowa yau ɗin tunda naga yau ce ranan ƙanwar ta mu, sai in Taya ta murna".


Dariya Suhaib ya saki yana ƙara ba shi hannu suka cafe yace, "gaskiya ka kyauta, Daddy zai yi farin ciki da zuwan ka, to ya Uncle da Ammee, da su Faruk?"


"Alhmadulillah duk suna gaishe ku, akwai babban surprise ma, but bazan sanar maka ba sai muna gaban Daddy".


Murmushi Suhaib yayi yace, "ok mu je to, mun tsaya a nan".


Jan hannun sa yayi suka nufi cikin gidan. Har sun kusa ƙarisa wa wajen taron sai wayan Rayyan tayi ƙara, ogan sa ke kiran sa don haka yace ma Suhaib "yayi gaba zai zo". Wayan ya ɗauka suka soma magana. Daga inda yake yana hango taron mutanen, inda fitilu masu haske suka haske wajen, kasancewar duhun magriba ta gabato, a time ɗin ma shirin tashi suke yi.


      Yana gama wayan sai ya nufi wajen, a time ɗin har wasu sun soma barin wajen sabida an gama.


     Tuni itama RAUDHA taja hannun Ramcy sun shige gida.


     While su Daddy sun tsaya suna sallama da mutane.


    Ƙarisawa Rayyan yayi wajen Suhaib.


            🌐🌐🌐


     Kai tsaye ɗakin RAUDHA dake sama suka wuce, anan suka zube kan kujera kowa na faɗan gajiyan da ya sha, sai kuma Ramcy ta tashi tana faɗin, "oh na bar su Aunty Nafeesa a waje, kuma sun ce min tafiya za su yi, ina zuwa bari inje".


RAUDHA tace, "miƙo min wayan ki, but kar su tafi yanzu zan sauko sai mu gaisa, in yaso drever ya mayar da su, but ke nan zaki kwana ko?"


Dariya Ramcy tayi tana zaro ido, "No ai nima tafiya zan yi zuwa anjima kaɗan, sabida Baba na gari kuma sai da yayi min gargaɗin in dawo, ina tunanin ma zamu tafi tare kawai da su ne".


"Ok mu je to sai mu yi sallama". cewar RAUDHA tana miƙe wa tare da wayan ta dana Ramcy dake hannun ta


Ramcy kuma ɗaukar jakan ta tayi suka fice.

     RAUDHA tafiya take yi tana latsa wayoyin, kasancewar tana son tura pictures and videos ɗin da Ramcy tayi mata ne a wayan ta, kuma tana son tura wa *Ƙalby* a yanzu ɗin.


    Sai da suka fita waje, kafin suka haɗu da su Amarya da Aunty Nafeesa suna shirin shigowa


Anan RAUDHA tayi musu godiya sosai, inda tasaka masu aiki suka kwaso musu kayan party ɗin. har wajen motan da za'a tafi da su ta raka su, kasancewar gaba ɗaya an gama watse wa, wasu sun wuce masallaci.


       Su sun shiga mota, ita kuma ta tsaya da Ramcy suna ɗan Surutu, har sanda ta gama tura wa kafin ta miƙa mata wayan. Sai da ta jira suka tafi tana ɗaga musu hannu kafin ta juyo cikin gidan. Da ɗan tazara tafiyan, ahankali take taka wa tana latsa wayan ta, inda take karanta text ɗin da Ƙalbyn ta ya turo mata, tana sakin murmushi cike da nishaɗi, har sanda ta iso cikin gidan, ta hau Lifter ya wuce da ita sama. ɗakin ta takoma ta shiga Toilet tayi wanka kafin ta ɗauro alwala, kayan ta ta saka farar less mara nauyi tamkar yadi, doguwar riga akayi mata fitet amma me guntun hannu, sai ta tufke gashin ta ta saka hula Robber ja, ta ɗaura Hijab tayi Sallah, sai da ta gama ta cire ta ɗauki wayan ta tafito parlour'n sama, anan ta haɗu da Farida da yaran ta tana buɗe musu Chocolates suna sha


"My guys how far?" RAUDHA tayi maganar tana murmushi bayan da ta ƙariso wajen su


Nan suka tashi suka nufo ta, sai ta soma ba ma Abdul hannu suka cafe, sai kuma ta miƙa wa Haneep da ya miƙo mata nasa yana dariya da zilalar da yawu


Murmushi tayi ta saka nata hannun cikin nasa, sannan ta sumbaci goshin sa ta ce, "My Daddy , I love you so much".


Washe baki yayi cike da murna, cikin muryan sa da ba ya fita maganar sosai ya ce, "I lobi u Baby".


Shima wai yayi irin na Suhaib da yake kiran ta Baby


Sai suka saka mishi dariya daga ita har Farida dake kallon su


"Wow My Daddy wa ya koya maka faɗan suna na?"

Abdul yayi saurin cewa, "Aunty ai yaji Daddy na faɗa miki ne, kuma yanzu yace mu kira ki, sai ya ce miki i love You Baby, shi ne shima ya faɗa, but be iya sanar da ke sauran ba".


Murmushi RAUDHA tayi ta shafa kan Abdul tana faɗin, "kai kuma me wayau ga shi ka faɗa".


Ya washe baki yana tsalle


Still murmushin tayi; tayi musu peck a kumatu, sanan ta shafa kansu, ta miƙe tana kallon Farida tace, "Aunty bari in zo".


Tashi za su yi su bi ta, sai Farida ta riƙe su tana ce musu "su zo ta gama ɓare musu biscuits and Chocolates ɗin".

    RAUDHA tuni ta bar wurin, ta Steps ta nufi ƙasa, a hawa na biyu ta tsaya ta shiga parlour'n don duba Daddy, don tasan baza su wuce suna nan ba dukan su. Tana shiga wani ƙamshi ya doki hancin ta, lumshe ido tayi tana buɗe wa, tabbas kamar ta taɓa sanin me turaren nan, kamar ta taɓa jin sa a wani waje, amma aina? Wurga idanu ta soma yi cikin parlour'n. Can ta hangi mutum saman kujera, sai dai bayan sa take hanga tunda kujeran da ya zauna a kai ya juya wa ƙofa baya ne


Kamar ta wuce sai kuma wani zuciyan nata ya bata umarnin zuwa ta ga ko waye, domin dai tana ji a ranta ta san koma waye ne, kuma farin sani tunda turaren sa ya tabbatar mata da hakan, amma kuma ta kasa tuna inda ta sani. Takowa tayi ta nufo wajen


Kasancewar bata da takalmi a ƙafafuwan ta sai Socks, shiyasa Rayyan be San da zuwan ta ba, ya ƙuƙe sai kallon zafafan hotunan ta da ta turo masa yake yi, yana zuba murmushi

Gab ta kusa isa wajen, inda ƙiris ya rage ta hangi abinda yake yi a wayan, sai ya juyo da sauri, sabida ajikin sa sai da yaji kamar da mutum a wajen, kuma take yaji ƙamshin turaren ta ya bugi hancin sa.


    Haɗa idon da suka yi, sai ta tsaya cakkk tana bin sa da kallo, ƙure sa da idanu kawai tayi ta kasa tunanin komi


Haka zalika shima idanun ya zuba mata, yana kallon ta cike da tsantsan ƙauna a idanun nasa, tare da tsatsan kewar ta gami da muradin ta cikin ransa. Komi nata ya sauya fiye da Da, ta sake girma da tsananin kyau.Yanda take jin wani iri da kallon ƙwayar idanun sa, hakan yasa tayi saurin ɗauke kai daga kallon sa, a lokaci ɗaya ta taɓe baki don bata yi tunanin shi ɗin zata gani ba, tun barin ta Abuja rabon ta da shi, sabida koda ya zo Hospital gaishe ta sanda tana jinya, ba ta sanin kowa. Sosai ya sauya mata fiye da tunanin ta, ba don ta sanshi sosai ba baza ta iya gane sa ba, ya sake ƙiba da ya ƙara masa kyau matuƙa, ga haske da ya sake wanda kowa ya kalle sa zai san hutu ya zauna masa, ya sha aski da yayi masa kyau ya sake fito da shi, kasancewar ba hula a kansa, yana sanye cikin faran gezna shara-shara, har Singlet ɗin da ya saka a ciki ana gani. Yanzu bata san meyasa ba, kaso sittin a cikin ɗari na daga tsanar da tayi masa a baya, yanzu kuma sai taji babu shi, ya ragu sosai.+


   Juya wa tayi zata bar wajen, sai ta tsinkayi muryan sa da yasa ta sake tsaya wa cakk, zuciyarta ta na wani irin bugawa da ƙarfi, sakamakon sunan da ya kira ta da shi. Dasauri ta juyo tana kallon sa


Shima idanun sa akanta suke, sai ya saki murmushi ya sake cewa, "pretty babu gaisuwa?"


Waro idanuwan ta waje tayi, sosai zuciyar ta take tsananin bugawa a yanzu ɗin, domin kuwa the same sunan da Ƙalby ɗin ta yake kiran ta da shi ne, ita in ba ma makuwa tayi ba, muryan sa na mata shige da muryan sa. Ji take yi tamkar tace ya sake maimaita sunan, sai kuma tayi dauriya tana kau da idanun ta daga kallon sa, ta sake juya wa tayi hanyar ɗakin Daddy.


     Da kallo Ray ya bi ta da shi, yasan sarai abinda ke cikin ranta, don haka tuni ya saki murmushi zuciyar sa cike da farin ciki.

     Har ta kusa ƙule wa, sai Suhaib da ya shigo yanzu ya kira sunan ta. juyo wa tayi tana kallon sa, sai kuma ta tako tana faɗin, "Yaya ina kuka shiga, ina neman ku? An ce kaima kana nema na".


"Eh Baby, dama Dude ne ya zo musamman don taya ki murna, shine na ce bari in Kira ki ku gaisa. Dude ga Baby ɗin; ko kun gaisa?" Suhaib ya sauya akalan tambayar nasa ga Rayyan yana kallon sa

"Yaya mun gaisa". RAUDHA tayi saurin faɗar maganar idanun ta kan Suhaib tana murmushi, tana juya wayan hannun ta


Murmushi shima yayi ya ce, "ok mu je mu zauna to, yanzu Daddy zai shigo ya sauka downstairs raka baƙin da yayi ne".


Gyaɗa kanta tayi, suka nufi inda Rayyan ke zaune, Suhaib ya zauna gefen sa, ita kuma ta zauna can kujeran dake kallon nasu, zata yi magana kenan taji shigowar message a wayan ta, ɗagowa tayi tana karanta wa

         _"Pretty kin Yi matuƙar kyau fiye da ko yaushe, har kin saka naji na ƙosa na mallake ki a matsayin matata, wlh pretty ina son ki, ƙaunar ki zai zauta Ni, ji nake yi kullum kamar ana ƙara min wutan ƙaunar ki a raina, I love You so Much my pretty"._


     Murmushi kawai take zuba wa, sabida sosai message ɗin yayi mata daɗi. Itama sai ta soma typing don mayar masa da reply.


      Ray dake hira da Suhaib, hankalin sa na gare ta, ta ƙasan ido yake kallon ta, ta yanda babu wanda zai fahimci yana kallon ta.         Tun tafiyan ta ƙasar Madina, hankalin Rayyan ya tashi matuƙa, gani yake yi gaba ɗaya ya gama rasa ta, shi da yake burin da zaran ta samu lafiya, ya bayyana mata ƙaunar da yake mata, sai gashi wai zata tafi karatu, hakan ya saka sa damuwa tsantsa. Haka ya danne wa ransa yaci gaba da al'amuran sa, sai dai ya rasa ta ya ya zai samu gana wa da ita ko da ta waya ne kamar yanda yake tura mata saƙo, tunda tuni ta dena amfani da wayan ta, anan Abuja ma ta bar shi, kuma da ta tashi tafiya sai dai aka siya mata wani, ga shi ba shi da Numban ta, ya rasa ya zai yi ya samu, ba ya son tambayan Suhaib kar ya zargi wani abu.

     Ahaka dai Allah ya basa Sa'a, inda watarana suna zaune suna hira da Suhaib ɗin, ya ce "ya ara masa wayan sa zai tura wani abu" to anan ne ya lalubo Numban ta na can yayi saurin kofe wa.

      Tun daga ranan Ya samu damar waya da ita, da fari text ya soma tura mata, ita kuma lokacin da ta gani, ta sha mamaki kasancewar yayi mata bayanin shine Masoyin ta da ke tura mata text a baya. Ta so ta share sa, sai kuma mamakin abun ya ƙi barin ta, tambayan da ta soma masa, "shin aina ya ƙara samun Numban ta? Kuma taya ya san ba ta ƙasar Nigeria?"


Shi kuma be bayyana mata komi ba, sai ya ce mata "duk inda take a faɗin duniya, idan har yana numfashi, to tabbas sai ya lalubo ta, ƙaunar da yake mata ya wuce tunanin ta".


Hakan sai ya saka ta shiga tunani tsantsa, tana tunanin shin wanene shi? Aina ya santa? Tunani kala-kala take yi a kansa. Kuma tun daga ranan bata sake mishi reply ba, duk da kuwa tana karanta saƙon sa, sosai yake saka ta tunani duk idan ta gama karanta saƙon sa, sabida kalaman sa ba ƙaramin taɓa mata zuciya yake yi ba, da haka ya soma kiran ta wai "yana son jin muryan ta". Tun bata ɗauka, har dai ta soma ɗauka, inda ta sha mamaki, domin kuwa muryan sa sak yayi mata kama da wanda ta sani, sai dai ta rasa aina? Koda wasa bata taɓa kawo cewa Captain Rayyan bane, to taya ma zata yi tunanin hakan bayan ta san ba sa shiri, ya tsane ta itama ta tsane shi, ita ta manta da shi ma tuni.

     Haka rayuwan taci gaba, inda Rayyan be ƙasa a gwiwa ba wajen yin nasaran sace zuciyar RAUDHA, sai dai fa ya sha matuƙar wahala, domin sai da ya dage da gaske, da jure duk wani wulaƙanci nata kafin yaci nasara, don da farko ma har block ɗin sa ta koma take yi, sai ya sauya sim ya sake neman ta. Sosai take mamakin naci irin na mutumin da bata ma sanshi ba.


     Kusan shekaru biyu da zuwan ta ƙasan, sannan ta amince ta karɓi soyayyar shi, don tuni ta saba dashi fiye da tunanin mutum, tabbas RAUDHA tana da wuyan sha'ani, babu wanda yake iya shiga jikin ta ta daɗi, tana da wuyan sabo, idan kuma ta saba da kai, tana baka yardan ta ne ɗari bisa ɗari, idan tace tana sonka, to tana son ka ne har cikin zuciyar ta.

  Sun saba sosai matuƙa, koda yaushe suna tare maƙale a waya ko a chart, idan tana school zata ijiye duk wani soyayyar sa a gefe, shima haka idan yana aiki be cika takura mata ba, ahaka dai rayuwan taci gaba, inda sosai RAUDHA ta tsunduma a soyayyar Rayyan batare da ta san waye shi ba, kuma bata taɓa tambayan sa don ta sani ba, ba wai don ba ta son sani ba, a'a, sai don shi be bayyana mata kansa ba, ita kuma jan aji da miskilanci irin nata, ya hana ta tambayan sa, musamman ya buɗe sabon account na facebook suke charting, ko su yi a WhatsApp da Numban sa personal, Wanda don ita kaɗai yake amfani da shi, ko kuma su yi ta inbox message.


      Haka rayuwan taci gaba da gudana, har sanda ya nemi ta tura masa hotunan ta, sabida yana matuƙar kewar ta yana son ganin ta. Anan ne tayi masa maganar itama tana son sanin shi, tana nufin ya faɗa mata komi a kan sa. Amma sai yayi mata daɗin baki inda ya ƙi yin mata duk abinda ta buƙata. Ita dai ta tura masa pictures ɗin ta, kuma bata sake tambayan sa ba tunda ta lura ba ya son ya nuna mata kanshi ne, har ga Allah ta yarda dashi ɗari bisa ɗari, kuma tana ƙaunar sa, ta saka a ranta ko waye shi zata iya auran sa. Dama akace duk wanda be taɓa soyayya ba, idan har ya tashi yi ba ya ɗaukar ta da wasa, tabbas haka ne a wajen RAUDHA, domin mahaukacin so take yi wa Rayyan, gaba ɗaya ta ɗau yardan ta ta ba shi, a cikin duk wanda ya san ta babu wanda be san labarin sa ba, su Daddy tuni sun san da irin ƙaunar da take mishi, sun buƙaci ganin sa amma sai tace musu watarana zasu gansa kamar yanda shima yake sanar mata, itama hakan ta sanar musu, sunan sa kawai ta gaya musu, inda yace mata sunan sa Muhammad. Yayi mata alƙawari duk sanda ta gama karatun ta, idan ta dawo Nigeria za su haɗu.


         🌐🌐🌐


     Shigowar Daddy ya saka RAUDHA ta ɗago kai tana kallon sa, sai kuma ta ajiye wayan tana tashi ta nufe sa tana kiran sunan sa


Tarban ta yayi yana murmushi, inda ya shafa kanta ya riƙe hannun ta suka dawo suka zauna a inda ta tashi


Anan Rayyan ya gaishe shi, ya amsa cike da fara'a yana tambayan sa aiki kafin ya ce, "nayi mamaki, wai yaushe ka shigo ƙasar?"

Dayake tuni an sake musu sauyin wajen aiki, dama shekara uku za su yi a Abuja, sai su dawo Kaduna inda anan ne dama yake aikin sa, to sun samu hutu sai ya tafi ƙasar su Bayelsa, sai yau ya dawo, kuma ya hana kansa sukuni sai da ya shigo Zaria don ganin muradin ransa.


    "Daddy yau na shigo".


Jinjina kansa Daddy yayi yace, "Weldon Captain kana ƙoƙari wlh, ya mutanen gida, ɗazu muna magana da Mahaifinka sai kuma muka katse akan ana jiran sa, zamu yi waya anjima, kuma ka ga hidima ya mantar dani ban sake kira ba, shima be kira ba".


Murmushi Rayyan yayi yace, "lafiya ƙalau suke, amm. Uncle babban surprise ne da shi, duk da ban yi tunanin zai sanar maka ba, ya bari zuwa Friday, Coz ranan Saturday za su shigo gaba ɗaya".


"Haba dai? Are You serious?" Daddy ya faɗa cikin fara'a


"Yes Daddy".


Take anan shi da Suhaib suka nuna matuƙar farin cikin su


Ita dai RAUDHA tana jin su bata ce uffan ba, sai faman taɓe baki take yi tana kallon Rayyan da shima ke kallon ta ta ƙasan ido


"Baby kina ji Uncle ɗin ku zai zo, baki taya Ni farin ciki ba?"


Yaƙe tayi tace, "Daddy I'm so happy, Allah ya kawo su lafiya".


"Emeen Baby".


Hira suka ci gaba da yi. Inda RAUDHA ta bar su tana ta faman latsa wayan ta, don bata san ma me suke cewa ba.


        Sai ga Farida itama ta shigo ta zauna cikin su, lokacin su Abdul duk sun barci.

     Ba su tashi ba sai da aka kira isha'i.


     Bayan sun dawo suka yi dinner a parlour'n ƙasa, inda Rayyan yace musu zai wuce, don shi be damu da tafiyan dare ba, kasancewar sa jami'in tsaro


But Sam Daddy ya ƙi barin sa, dole yace masa sai ya kwana, in yaso washe gari sai ya tafi da wuri


Be musa masa ba kuwa, anan ɗin ya kwana, washe gari zuwa ƙarfe 08:30am. Yayi sallama da su ya tafi, ya so ganin RAUDHA sai dai be samu dama ba, domin dai tana can tana barci, kuma ba ya kyautata zaton zata iya tashi yanzu don yasan halin ta sosai.


     Sai ƙarfe 12:40am ta farka kuwa.


     Zuwa dare su ma su Suhaib suka wuce Abuja, inda suka bi jirgi.Washe gari ƙarfe 11:00am. RAUDHA ta tashi, bakin ta kawai ta wanke ta ɗauraye fuska ta fito Parlour, part ɗin Daddy ta wuce, sai dai bata same shi ba, sai ta tambayi ɗaya daga cikin ma'aikatan dake gyara Part ɗin, suka ce mata "ya fita ne"+


Ɗakin ta ta koma ta ɗauki waya ta kira sa, nan yake sanar mata "ya fita, but bazai daɗe ba zai dawo". Sake fitowa tayi da wayan a hannun ta, inda ta kira ɗaya a cikin masu aikin ta bata umarnin kawo mata Breakfast ɗin ta saman


Bata jima ba kuwa ta haɗo mata


zama tayi saman dainning tana ci tana latsa wayan ta. Kamar shuɗewar mintuna ashirin sai wata acikin masu aikin ta shigo take sanar mata tayi baƙi. maimaita kalman baƙin tayi a fili, idanun ta kan ƴar aikin, sai kuma tace, "su wane ne?"


"Ranki ya daɗe wasu samari ne su biyu".


Shiru RAUDHA ta sake yi zuciyarta cike da mamaki, kafin kuma tace, "ok CE musu su jira Ni, ki sauke su parlour'n ƙasa".


"To ranki ya daɗe". Tayi maganar cikin girmamawa tana juya wa don isar da saƙon ta


RAUDHA ci gaba tayi da harkan ta, tamkar bata san jiran ta ake yi ba, sai da ta ɓata time kafin ta miƙe tsaye, wayan ta ta ɗaga tayi Selfie 🤳 tana turo baki gaba, sannan sai ta shiga WhatsApp ta tura wa Rayyan, a ƙasan ta rubuta, "Good morning Ƙalby, I Love you xoxoxo" ta saka emojis na love ta tura masa".


Murmushi tayi kafin ta kama hanyan barin parlour'n, ko kaɗan bata yi tunanin sauya kayan jikin ta ba, tana sanye cikin kayan barci riga da wando masu santsi, kalan ruwan Powder, wandon Three qwater ne amma burgujeje tamkar skert, sai rigan ɗan shimi me hannun vest da kwalliyan bakin leshi a gaban, kanta da baƙin hula me raga-raga, ƙafanta kuma babu takalmi sai Socks


Duk da yanzu ba ta fita da irin shigan nan, amma har yanzu bata dena yin sa ba in dai a gida ne.


     Lifter ta hau ya kai ta ƙasa. Tana sauka ta shiga cikin parlour'n


Zulain da Sharif dake zaune, suka hange ta tana nufo su, sai gaba ɗayan su suka ƙura mata idanu, ko wanne a ransa yana yaba tsantsan kyan da Allah yayi mata, gaba ɗayan su ganin dirin jikin ta sai da ya tafi da duk natsuwar su. har ta iso wajen ta zauna kan sofan dake kallon su, ta ɗaura ƙafan ta ɗaya kan ɗaya tana bin su da ido, amma su gaba ɗaya hankalin su ya fita jikin su

Itama sai da ta gama ƙare musu  kallo, musamman Zulain ganin sa da tayi Bature, duk da kasancewar sa ba fari ba, domin ko kama ƙafan hasken ta be yi ba, amma kuma gashin kanshi fari ne irin na turawa, da ganin shi dai kasan Bature ne shi. Taɓe baki tayi kafin tace, "ku ne kuke nema na?"


Sai a time ɗin suka dawo hayyacin su, yayinda duka suka yi murmushi, Zulain na shirin magana wayan ta ta soma ƙara


Ɗago wayan tayi tana kallo, sai ta saki murmushi tana peacking Call ɗin ta kara a kunne, sai a time ɗin ne ta kalle su ta ɗaga musu hannu alamun tana zuwa, "Hello Ƙalby". Tafaɗa still tana murmusawa


Daga Zulain har Sharif kallon ta kawai suke yi, babu wanda yake jin abinda take faɗa kasancewar ta juya harshe zuwa larabci ganin suna kallon ta. Zulain in ban da Hello ɗin da tace ba ya jin komi, haka shima Sharif, gwara shima Ƙalby ɗin da ta faɗa ya gane me take nufi, a ransa ya ce, "lallai kam! wannan yarinya anya ba mu kawo kan mu inda za'a wulaƙanta mu ba?" (A raina na ce da sauƙi dai Sharif, da abaya kazo ina tunanin baza a baka wurin zama ba bare a kalle ka na arziƙi, ko ba haka ba Fans?🤣)


Duk abinda take yi sosai take ƙara shigan zuciyan Zulain, be taɓa ganin yarinyan da ta burge shi irin ta ba, duk da kasancewar sa bature amma wayewar ta sosai ya burge sa, ba ta da maraba da su. Be dena tunanin ba har sanda ta gama wayan


Ta kalle su tana faɗin, "afuwan na tsai da ku ko? I'm sorry".


"No problem Cuty, girman ki ne ai". Zulain ya faɗa yana murmushi


Itama murmushin tayi idanun ta akansa tace, "ok me ke tafe da ku?"


"Soyayya". Cewar Zulain still yana murmusawa


Ɗan waro ido tayi, sai dai bata kai ga magana ba yaci gaba da faɗa mata yanda ya kamu da tsananin ƙaunar ta, ko kaɗan babu ɓoye-ɓoye a lamarin shi, tunda dama su turawa ba kunya suka cika ba


Har ya dire maganar shi RAUDHA kallon shi take yi, a rayuwan da tayi a Madina ta samu mutanen da suka sha sanar mata suna ƙaunar ta, sai dai yanda ta ƙi ba su dama ne, yasa dole suka haƙura. tuni Ƙalby ɗin ta ya sace mata zuciya, kuma ba ta tunanin koda da wasa zata iya haɗa soyayyar shi da wani, duk da tana ganin waɗanda suka burge ta matuƙa, musamman ma yanzu Zulain ɗin nan, sosai taji a ranta yayi mata, ya haɗa komi ne wanda ɗiya mace idan ta ganshi dole ta so shi...


    Shigowar Daddy da sallaman shi, shi ne ya katse musu gaba ɗaya tunanin su, wanda Zulain da Sharif sun tsaya ne su ji amsar da zata ba su, yayinda ita kuma ta faɗa kogin tunani


Miƙe wa gaba ɗaya suka yi har RAUDHA, su Sharif suna masa sannu da zuwa


Sai a time ɗin ne ma ya gane su, nan da nan ya washe baki yana faɗin, "a'ahh ku ne ashe? Sharif and Zulain ko?"


Murmushi suka yi suna amsa mishi da "Eh".


"To ku zauna mana, Sannun ku da zuwa".


Zama suka yi kamar yanda ya ba su umarni, shima ya zauna akan sofa, inda itama RAUDHA ta koma ta zauna


"My daughter ko wajen ki suka zo ne?" Daddy ya tambaye ta yana murmusa wa


"Na'am Daddy". Ta amsa mishi tana murmushi


"Ok Masha Allah, bari in Baku waje to?" Yayi maganar da fara'a yana shirin tashi


Sai ta langaɓe kai tana cewa, "Daddy da ma kayi zaman ka".


"No daughter, KU dai gama maganar ku, in ya so sai ki kira Ni daga baya mu gaisa sosai".


Gyaɗa masa kai kawai tayi, shi kuma ya wuce ciki.


     Kallon su tayi tace, "ku daure ku ci wani abun mana, ga shi baku taɓa komi ba?"


Murmushi Zulain yayi yace, "no ba ma buƙatar komi ɗin ne a yanzu, illa amsar ki, ki daure ki sanar da Ni abinda ke zuciyar ki ko da nima tawa zuciyar zata samu sukuni daga zugin da ta daɗe tana min".


Sharif Ya amshe zancen da faɗin, "Please RAUDHA, ɗan uwana na matuƙar ƙaunar ki fiye da yanda kike zato, tun haɗuwar da kuka yi a airport ya kamu da soyayyar ki. A taƙaice dai ya kasa samun sukuni tun zuwan sa ƙasan nan, sai kuma Allah yasa bazai sha wahala ba, ya haɗu dake cikin sauƙi anan gidan, ina ga Allah ya ƙulla wani alaƙa a tsakanin ku ne shiyasa har ya sake haɗa ku batare da ya sha wahala haka ba, ki duba magana ta RAUDHA, Zulain na ƙaunar ki matuƙa".


Murmusa wa tayi sabida maganar Sharif ɗin, idanun ta a kansu tace, "eyya gaskiya ban san me zan ce muku ba yanzu, amma dai zan iya sanar muku da cewa na rigada na ba wa wani.."


Katse ta Sharif yayi da faɗin, "ba sai kin faɗa ba RAUDHA, don Allah ki dai ba wa Ɗan uwana dama ko sau ɗaya ne, ta hakan ne kaɗai zaki fahimci wanene shi, kuma zaki so shi wlh, domin shi ɗin na daban ne, ba ko wace mace take samun Sa'a wajen mallakar irin su ba".


Wannan karon dariya RAUDHA tayi tace, "uhmmm Sharif kenan! Na ga alamu kana son ɗan uwanka da yawa ko?"


Murmushi duka suka yi


Jinjina kanta tayi tace, "amma Ni ba na so mu ja zancen da tsawo haka, ina da Masoyi na, ina son shi yana so na, so babu amfanin mu ɓata lokaci akan abinda bazai yiwu ba".


Lumshe ido Zulain yayi, sai kuma ya buɗe akanta, cikin ido suke kallon juna ya ce, "I love You RAUDHA, bazan iya haƙura da ke ba har sanda na ga kin zama mallakin wani, ma'ana an ɗaura miki aure. Yanzu ma na soma son ki, idan har baki kore Ni ba, Ni kuma zan ci gaba da gwagwarmayan samun ki har sanda Allah zai yi ikon sa".


Kau da kanta tayi, sai dai bata iya cewa komi ba, sai ta tashi tana faɗin, "bari in Kira muku Daddy".


Ta juya ta tafi abun ta.


      Koda ta kira musu Daddy, ɗakin ta ta wuce bata sake bi ta kansu ba, don bata san ma sanda suka tafi ba. Sai da Daddy ya kira ta sannan ta fito, anan yake tambayar ta "me suka zo yi wajen ta?" Ta sanar mishi da komi tunda babu ƴar kunyan haka a tsakanin su


Murmushi Daddy yayi yace, "Baby in baki shawara?"


Gyaɗa masa kai tayi tana cewa, "Yes Dad".


"Ok gaskiya yaron nan yayi matuƙar dacewa da ke, ki daure ki duba son da yake miki kar ki yi watsi da shi akan wani".


Murmushi tayi idanun ta akan sa tace, "Daddy kai ma kasan ina da saurayi na, ban ga abinda zai saka na ɓata lokaci na kan wanda bazan taɓa son shi ba idan har Ƙalby na tare dani. So Daddy Kar ma su biyo ta hannun ka su ba ka cin hanci ka ce shi zan aura".


Waro ido yayi yana dariya yace, "Baby?"


"Yes Daddy." Tafaɗa tana dariya itama


Shafa kanta yayi yace, "ki dena maganar haka kin ji Baby na? Domin wanda kike so shi nima nake so, duk wanda kika kawo a matsayin Mijin ki, shi ne zai kasance Mijin ki, ba zan taɓa baki wanda ba ke ne kika kawo ba".


Dariya tayi tana ɗaura kanta saman kafaɗan sa tace, "Daddy Nima Wasa nake maka fa".


Hancin ta ya ja yace, "i know Baby, but yaushe ne zaki kawo min suruki na in ganshi, yakamata kema ki zo kiyi auren nan ko da nima zan soma ganin Jikoki na ta wajen ki".


Ƙyalƙyale wa tayi da dariya tana cusa kanta a hannun sa tace, "Daddy".


"Umm Babyn Daddy, ai gaskiya na faɗa".


Murmushi kawai tayi bata yi magana ba


Shima sai be sake cewa komi ba ya sauya maganar suka ci gaba da hira.Daddy ya saka ana ta shirye-shiryen tarban iyayen Rayyan da za su zo, an gyara musu ɗakunan ƙasa da ba a amfani da su, duk wani abubuwan jin daɗi ya saka an zuba musu+


Alh. Hassan da suke kiran sa da Uncle Hassan, shine Abokin Daddy. Asalin Abotan su ya fara ne sanda Daddy yayi zaman Bayelsa yin wani course, to anan suka haɗu da Uncle Hassan Wanda gaba ɗaya ahalin su sunan da suke kiran sa da shi kenan, tun yana ƙarami, kasancewar sunan Kawun sa shima ya ci, to lokacin da aka haife sa a lokacin ne Kawun nasu ya rasu, shiyasa da aka mayar da sunan Kawun shi ne suke kiran sa da Uncle Hassan kamar yanda suke kiran Kawun, har Allah yasa ya girma da sunan ake kiran sa, yanzu haka har iyalan sa duk Uncle suke kiran sa, su Rayyan ba sa kiran sa da Baba sai dai Uncle.


      Kasancewar Daddy yana yawan zuwa gidan su Uncle Hassan, anan kusa da gidan su ya haɗu da mahaifiyar su RAUDHA, suna maƙotaka ne da gidan su Uncle Hassan, inda babu ɓata lokaci soyayya me ƙarfi ya shiga tsakanin su, koda ya tashi aure sai Allah yasa ita ɗin rabon sa ne, a time ɗin iyayen sa suna raye, har can suka je nema masa auren Ruƙayyah, inda aka ba shi babu wani ja'inja


    Anan Zaria suka soma zama, cikin ƙofan doka, Allah da ikon sa rayuwa taci gaba da gudana, inda a gefe ɗaya suna Abotan su sosai da Uncle Hassan, shima be daɗe ba yayi aure a can Bayelsa


Babu jima wa Matan nasu suka haihu a tare, inda yaran suka ci sunan Rayyan da Suhaib. Haka rayuwa taci gaba da gudana, Ruƙayya dai bata sake haihuwa ba, sai matar Uncle Hassan Hansa'u da ta haifi Umar Faruk, suna kiran sa da Faruk tunda sunan mahaifin ta ne, wani lokacin kuma su kira sa da Abba, daga shi kuma sai Usman da suke kiran sa da Zannurain, sai kuma  Abubakar autan su, shi ne sa'an RAUDHA, an haife shi babu daɗe wa aka haifi RAUDHA, shekarun ta biyar a duniya Ruƙayya ta rasu a wajen haihuwar ƙanwar ta, lokacin tana cikin naƙuda, domin har ta kusa haihuwa, da ita da abun da ke cikin ta gaba ɗaya suka koma ga Allah saboda ta sha wahala a lokacin. Wannan dalilin ne Daddy da Suhaib suka ɗauki son duniya suka aza wa RAUDHA, ga tsaban tausayin ta da suke ji.


          🌐🌐🌐


      Drever yaje ya ɗauko su a airport sanda suka sauka, suna iso wa Uncle da Daddy suka rungume juna, ko wannen su cike da farin cikin ganin Abokin sa, domin sun jima rabon da su haɗu sai yanzu, shiyasa Uncle Hassan ya shirya zuwa gaba ɗaya har iyalan sa


Sai da suka daɗe suna gaisa wa cike da barkwanci kafin suka samu wuri suka zauna, inda su Faruk ɗaya bayan ɗaya suka hau gaishe shi. Ya amsa musu cike da fara'a yana tambayan su school da aikin su. Sannan suka gaisa da Ammee cikin mutunci


Uncle ne ya soma tambayan RAUDHA, kasancewar shi kaɗai ya san ta, ita kanta Ammee tun tana yarinya rabon da ta sake ganin ta


Daddy na murmushi yace, "yanzun nan zata dawo, ta je gidan ƙawar ta ne (Ramcy)".


"To Masha Allah, Allah ya dawo da ita lafiya".


"Ameen ameen". Daddy yafaɗa still yana murmusa wa. sai kuma ya kalli su Faruk ya ce, "Abba sai kuma ga ku a Nigeria ko?"


Dariya suka yi gaba ɗaya, inda Abubakar yayi tsalan ɗin cewa, "wlh kuwa Daddy, wannan shi ne zuwa ta na farko ƙasar ku, ashe dai yana da daɗi".


Daddy dariya yayi yace, "sosai ma Habu, ai zan sa a zaga da ku zaku fi jin daɗin garin sosai".

Duka suka yi dariya


"Ya kamata Ku yi wanka ku huta, bari in saka a nuna muku masaukin ku". Daddy ya faɗa yana kallon su da murmushi


Gyaɗa masa kai suka yi, don su ma sun fi buƙatar hakan


Daddy da kansa ya nuna musu, be ma bari an nuna musu ba, har Ammee itama ɗaki ta wuce, inda Daddy ya dawo suka ci gaba da hira da Uncle suna ta dariya, babu abinda suke yi sai tuna baya, idan sun tuno abinda yayi musu daɗi da ba su dariya har kashe hannu suke yi.


     A lokacin ne RAUDHA ta shigo gidan


Daddy na ganin ta yace, "yauwa Baby kin ga har su Uncle ɗin ki sun ƙariso baki dawo ba, sai tambayan ki yake yi".


"My daughter ƙariso mana". Uncle yafaɗa yana nuna mata kusa da shi


Da murmushi a fuskar ta ta ƙariso wajen sa ta zauna, sannan ta gaishe sa cikin mutunci sosai


Hakan sai ya faranta ran sa, ya saka hannu a kanta yana shafa wa ya ce, "Allah ya miki albarka my daughter".


"Ameen Uncle".


Murmushi yayi yace, "kin girma sosai my daughter, rabo na da ke tun kina ƙarama, amma kuma kina nan a yanda kike, domin ko aina na ganki sai na shaida wannan ɗiya ta ce".


Dariya suka yi daga ita har su ɗin


Anan ne itama Ammee ta fito, ta ƙariso ta zauna idanun ta akan RAUDHA da itama take kallon ta


Kafin ma tayi magana RAUDHA tayi ƙoƙarin gaishe ta, sabida ba ƙaramin kamannin Rayyan ta gani a tare da ita ba, kamar an tsaga kara, wannan dalilin ne yasa ta gane mahaifiyar shi ce


Cikin fara'a Ammee ta amsa ta tana cewa, "taho nan kusa dani mana ɗiya ta in ji ɗumin ki".


Taso wa tayi tana murmushi ta dawo kusa da ita, sosai taji farin ciki da wannan ƙauna da iyayen Rayyan suka nuna mata, har sai da ta tuno sa, a ranta tana cewa, "shi kuwa be da kirki kamar su, ko wa ya biyo oho masa".


Anan ne su ma su Faruk duk suka fito, inda Daddy duk ya gabatar mata da sunayen su


Farin ciki duk ya cika RAUDHA, musamman da tagan su har su uku, sai ta washe baki ta soma ba ma Abubakar hannu wai su gaisa


Sai hakan gaba ɗaya ya burge su har su Ammee, duka suka saki murmushi


Abubakar kuwa hannun ya miƙa mata yana dariya yace, "Abubakar Sadiq your friend".


Gyaɗa kanta tayi tana sake washe baki tace, "ana RAUDHA"


Duk dariya suka sake yi


Sai shima Zannurain ya miƙo mata hannu yana dariya yace, "Ni dai ba friend ɗin ki bane, Yayan ki ne, Ki kira Ni Bro Zannu".


Kasancewar yayi maganar ne cikin barkwanci, duk sai suka yi dariya gaba ɗaya


"Bro Zannu". Itama ta faɗa cikin dishewar muryan ta me daɗi tana murmushi, sannan sai kuma ta kalli Faruk dake tsaye ya harɗe hannayen sa yana kallon ta yana murmushi. Sosai gaban ta ya faɗi sabida ganin kamannin su ɗaya da Ray, har ta Yi tunanin ko shi ne, sai taga kuma wannan be kai shi haske ba, sannan be da jiki kamar shi, Faruk siriri ne sosai


Hannu ta miƙa masa tana murmushi


Sai ya saka nashi shima yana murmushin yace, "kina lafiya?".


"Ana bikhair.. ant?" Tayi maganar idanun ta a kansa tana ci gaba da murmushin ta me kyau


"Ana jayyidan".
      Dainning suka wuce gaba ɗaya suka ci abinci, ita dai RAUDHA ba ci take yi ba tana zaune gefen Abubakar suna zuba surutu, sai dariya take yi


Cike da nishaɗi haka suka kasance a ranan har yamma, anan ne RAUDHA taja hannun Abubakar suka nufi bayan gidan, inda anan ne aka saka basketball, da kuma abubuwan Game dai kala-kala


Tare suka soma ƙwallon suna ta dariya, fara wa da iya wa har ya ci ta biyu, nan ta saka mishi rigima wai bata yarda ba


Sai kawai ya faɗi ƙasa yana ta mata dariya, shi kawai dariya ta bashi sabida yanda take shagwaɓan ta tamkar yarinya, baza ka taɓa tunanin ƴar shekara 24 bane


Kaɗa kai tayi, ta zuƙuna ta soma kanannaɗe farar wandon ta, sai ta kama gashin ta ta sake ɗaure shi da kyau, ta tashi tana tsalle tace, "to taso mu ci gaba, yanzu sai na sa ka kayi kuka".


Dariya ya sake kwashe wa dashi.        Daga nesa Faruk na tsaye yana kallon ta yana murmushi, gaba ɗaya RAUDHA ta gama tafiya da imanin sa, salon ta da komi nata burge sa yake yi, yana nan yana kallon yanda suke ƙwallon, duk RAUDHA bata iya ba amma ta dage sai ta ci Abubakar, shi kuma sai saka mata ƙwallo yake yi ta kasa cin ko guda ɗaya, duk ta gama gajiya sai nishi take yi, don daƙyar take gudu ma


Kamar ance ta kalli inda yake tsaye, ta hange shi kuwa ya kafa mata idanu, da gudu ta nufe sa ta ƙariso wajen sa tana nishi, idanun ta a kansa tace, "Plz Brother taimaka min in ci shi, wlh wayau yake ta min duk ya gajiyar dani".

Dariya maganar nata ya ba shi, wai wayau yake mata, bayan bata iya bane


"Kaji?". Tayi maganar tana riƙe masa hannu


Murmushi yayi yace, "wa yace miki na iya? Nima irin ki ne ai".


Langaɓe kai tayi kamar zata yi kuka

Zannurain ne ya ƙariso wajen yana tambayan me ke faruwa


"Yauwa Dear Zannu, zo mu je ka taya Ni cin Friend, ka ga sai cinye ni yake yi".


"Ok mu je". Zannurain yafaɗa yana yin gaba tare da kanannaɗe hannun rigan sa


Faruk dai yana tsaye yana kallon su har sanda suka tashi wasan, sannan ya juya ya bar wajen.
         🌐🌐🌐


      Washe gari wajen ƙarfe 10:30am sai ga Suhaib ya zo shi kaɗai, lokacin RAUDHA da Abubakar da Zannurain sun fita zaga gari, sai Faruk ne da be bi su ba, time ɗin ma barci yake yi


Uncle rungume Suhaib yayi kafin suka gaisa, ya soma tambayan sa iyalan sa


Yace, "suna gida, sun ce in gaishe ku sosai". Sannan ya gaishe da Ammee


Ta'amsa cike da fara'a itama tana tambayan sa iyalan, sannan tace, "meyasaka baka zo da su ba?"


Shafa kansa yayi yace, "babu komi wlh, nima na zo ganin ku ne ai".


"Ka kyauta ai, amma su ma da kazo da su mun ga juna, tunda ba daɗe wa za mu yi ba, kuma idan mun tafi ba kawo mana su zaka yi har Bayelsa ba". Ammee tafaɗa hakan da fara'a


"Haka ne Ammee, ban yi tunanin hakan ba wlh".


Daga nan hira suka ɗan taɓa, inda Suhaib yake tambayan "ina su Faruk?"


Kafin ma su ba shi amsa, Faruk ya fito daga ɗaki

Ammee tace, "ga Faruk ɗin nan ya fito, su kuma sauran sun fita da RAUDHA".


Faruk gaishe shi yayi, inda ya amsa mishi yana tsokanar sa da faɗin, "har da kai ƙaton kawai aka zo da kai?"


Dariya Faruk yayi yana shafa kansa yace, "ai ban wuce zuwa anguwa ba Yaya Suhaib".


"Eh naga alama, amma ai ka isa ajiye mata, har yanzu shiru da kai da Dude".


Uncle yace, "bar su Suhaib, ai na san maganin su, ina gajiya nima auren zan yi musu, ka ga wannan ƙiri-ƙiri ga matar sa a gida, amma har yanzu sai kwana-kwana yake mana, kuma shi ya amsa yana son ta, amma yanzu kuma yana son Wai ya koma karatu ne, abun dai da yaga ɗan uwansa nayi shine shima yake son yayi. Ko sha'awar ka ɗan uwan (yana nufin Rayyan) ba ya ji, ga ka har ka tara iyalan ka gunin sha'awa".

Daddy na murmushi yace, "ai komi nufin Allah ne, wata rana sai labari, idan lokaci yayi za su yi".

Uncle sauya maganar yayi suka ci gaba da hiran su, inda Ammee ta tashi ta koma ciki, dama gaisa wa da Suhaib ya fito da ita. Su kuma Suhaib da Faruk suka fita waje suna zanta wa.


    A lokacin ne su RAUDHA suka dawo, duk suka nufi wajen su


RAUDHA rungume sa tayi tana murnan ganin sa, tace, "Yaya ina su Daddy na?"


"Suna gida ban zo da su ba".


Buga ƙafa ta soma yi tana mishi rigima


Abubakar ya dunguri kanta yace, "ke dai kin cika rigima wlh, ki bari mu gama gaisa wa mana, kin wani ƙwaƙwime sa kin hana shi ya san damu a wajen".


Dariya suka yi gaba ɗaya


Inda ita kuma tabi sa zata bige sa, ya gudu. Nan suka soma zagaye wajen suna dariya


Zannurain yace, "mu dai ku dena zagaye mu haka".

Bata ƙyale shi ba kuwa, sai da ta kama shi ta naushe shi a kafaɗa


"Aushh! Wlh Yaya Suhaib wannan yarinyan muguwa ce, ta iya mugun ta".


Sosai Suhaib yake dariya, musamman yanda ya ga ƙanwar tasa ta saki jikin ta, fara'an ta ma daban ne, shi kansa yasan ƙanwar tasa tana cikin nishaɗi sosai. Family wani abu ne me girma da daraja, me saka nishaɗi a zuciya.

     Anan suka shantake, sai daga baya suka shige gidan.

      Da rana sai ga Rayyan ya zo.Lokacin da Rayyan ya shigo gidan, time ɗin su Daddy gaba ɗaya suna masallaci, sai Ammee dake zaune a Parlour, RAUDHA ta ɗaura kanta a saman cinyoyin ta suna ta hira suna dariya, sosai RAUDHA ta saki jiki da Ammee, sai tana kallon ta tamkar Mahaifiyar ta, bata taɓa kewar Mahaifiyar ta ba tunda take, sabida Daddy da Suhaib sun ɗauke mata komi, duk abinda uwa zata yi mata suna mata, ba su taɓa barin gurbin da zata ji kewar Maman ta ba, shiyasa ta taso ko kaɗan bata taɓa tuna wa da ita ba, ko a hoto ba ta ganin ta, duk da suna da hoton nata, amma ita ba ta ɓata time ɗin ta wajen ganin ta a hoto. shiyasa yanzu da Ammee take nuna mata ƙauna da kulawa, sai taji sosai take kewar Maman ta, sai taji tana matuƙar ƙaunar ta, har tana jin da ma tana raye ta so ta itama kamar yanda Ammee take mata fa. a jiya da take tunanin nan har sai da tayi kuka sosai, shiyasa a ranta yanzu ta ɗauki Ammee tamkar tana tare da maman ta ne, komi da zata iya faɗa mata zata iya sanar wa Ammee+


Yanda RAUDHA ta saki jiki sosai, hakan sai ya faranta ran Ammee matuƙa, sosai take jin soyayyar ta a ranta, kasancewar ta me ƙaunar ɗiya mace, tunda Allah be bata ba.


     Sallaman Ray, shi ya dakatar da su daga hiran da suke yi suna dariya, a tare suka amsa mishi har RAUDHA da tayi tunanin ko Faruk ne, tunda muryan su ba shi da banbanci, sai dai yanda taji ƙamshin turaren sa ya daki hancin ta, sai tayi saurin lumshe idanu tana sake zuƙo turaren sosai, but duk a tunanin ta ba shi bane.


      Allah ya sani turaren sa yana matuƙar mata daɗi, bata san meyasa ba. tana jin sanda suke gaisa wa da Ammee, sai hakan ya bata mamaki tayi saurin ɗago kanta tana sauke idanun ta akan shi, yanda idanun ta suka faɗa cikin nasa sai tayi saurin ɗauke kai tana koma wa ta kwanta


Murmushi shi kuwa yayi, ya kalli Ammee dake shafa kanta a yanzu ɗin yace, "Ammee su Uncle fa?"


"Sun je masallaci".


"Ok Nima bari inje dama ban yi sallan ba". Har ya miƙe kuma sai ya kalli RAUDHA da idanun ta ke rufe yace, "pretty babu gaisuwa?"


Wani irin sara wa gaban ta yayi, dasauri ta buɗe idanun ta tana sakin numfashi me ƙarfi, sake mayar da idanun ta tayi, ahankali ta furta, "naharan sa'idan".


Murmushi yayi ya kalli Ammee da itama take murmushin, don sosai zuciyan ta ta ɗarsa mata wani abu yanzu-yanzu da Rayyan ɗin ya kira RAUDHA da Pretty, sai ta ga sosai suka dace da juna, har tana ji a ranta da ma su kasance mata da miji


Shi kuwa Ray, har ga Allah manta wa yake yi yake kiran ta da suna Pretty a ko ina, sabida bakin sa ya saba. Sallama yayi wa Ammee ya fice


Sai a time ɗin RAUDHA ta buɗe idanun ta, sosai ranta yake kawo mata tunani kala-kala "meyasa yake kiran ta da sunan da Ƙalby ɗin ta ke kiran ta? Shin ba shi da wani sunan da zai iya kiran ta da shi ne sai wannan? Meyasa take jin muryan sa na shige da na Kalby? Ko dai shi ne?" Take ƙirjin ta yayi wani irin buga wa, tayi saurin tashi zaune tana riƙe wajen


"Lafiya Daughter? Me ya faru ne?" Ammee tafaɗa tana riƙe mata ɗaya hannun cikin kulawa


Kallon ta tayi, sai kuma ta saki murmushi tana faɗin, "babu komi Ammee na tuna wani abu ne, bari inje ɗaki ina dawo wa".


"Kin tabbatar?" Ammee ta sake tambayar ta


Gyaɗa mata kai tayi tana miƙe wa tsaye


"Ok ki kula".


     Kai tsaye ɗakin ta ta wuce, ta soma neman layin Ƙalby, sai dai akashe ake ce mata, ta gwada ya kai fiye da biyar, but the same answer. Runtse idanu tayi tana buɗe wa da sauri, sai kuma ta tashi ta soma zagaye wajen tana tunani kala-kala


Wani Gwauron numfashi taja tana dukan cikin tafin hannun ta da ɗaya hannun, afili ta furta "Nooo impossible!". Hannun ta ta saka a baki tana cizon yatsan ta, taci gaba da Safa da marwa, sai kuma taja burki da sauri tana riƙe goshin ta


"A'a tunani na ne wannan, amma wlh Ƙalby bazai taɓa zama shi ba! Me zai saka ma yayi min irin wannan wasan? Meye haɗi na dashi? Na tsane shi fa! I hate him so much". Taƙarike maganar kamar zata yi kuka


Zama tayi daɓas akan gadon ta, ta sake ɗaukan wayan ta ta kira Numban nasa, a time ɗin yana shiga sai dai ba'a ɗauka ba, sai da tayi two missed calls kafin a ɗaga. Tana kara wa a kunne abinda ta soma tambayan sa, "ina ka shiga Ƙalby?"


Murmushi Ray ya saki, yana gyara muryan sa yace, "Pretty Ina aiki ne".


"Aiki kuma? Wani aiki kenan bayan yau ba ranan aiki bane?" Ta sake tambayar sa da sauri, ita kanta a ruɗe take, so kawai take yi ya bata ƙwaƙƙwaran amsar da zuciyar ta zata iya yarda dashi


Stiil Murmushi yayi yace, "kin manta nace miki muna zuwa Gona Ni da Abba na?".


Shiru tayi


Ya sake cewa, "lafiya dai Pretty? Me ke damun ki? Ina ji a jiki na akwai abinda ke damun ki?"


"Yeah akwai Ƙalby, Ni na gaji da ɓoye min kanka da kake yi, ina so mu haɗu". Tayi maganar da tsananin sanyin murya


"Kar ki damu Pretty nayi miki alƙawari Very soon zamu ga juna, amma don Allah ki faɗa min meyasa kike son mu haɗu da wuri?".


Shagwaɓe murya tayi tace, "Ni ina son ganin ka ne fa, kuma ka ga su Daddy suna ta tambaya na kai, sannan Ni fa ina so mu yi aure nan kusa ne, kai nake jira".


"Ohhh Pretty Ni kike jira? Ashe kin ƙosa kamar Ni anan?" Yayi maganar cikin dariya


Itama dariyan tayi tana kwanciya kan gadon, ta sake matse wayan a kunnen ta, cikin ƙasa-ƙasa da murya tace, "to dama kai kaɗai ka ƙosa, nima ai har da Ni".


"Me kika ce Pretty?"


Saurin faɗin, "no ba da kai nake yi ba?"


Dariya ya kece dashi, itama tana taya sa, yace, "ok kenan dama akwai wanda kike magana da shi bayan Ni?"


Turo baki tayi kamar tana ganin shi tace, "a'a babu kowa fa".


"To nace da Ni kike yi kika ce ba dani ba?"


"Au da kaina nake yi".


Dariya yayi yace, "kin ganki ko? Zaki sake maimaita abinda kika faɗa duk sanda muka haɗu".


Dariya tayi kawai tana rufe idanun ta


"Baby in tambaye ki mana?"


"Ina ji Ƙalby". Tayi maganar tana tashi zaune


"Wai dama kina da kunya haka?"


Turo baki tayi sabida bata yi tunanin tambayan kenan ba, sai da ta harari wayan kafin tace, "ban sani ba".


"Oh Allah ya baki haƙuri my Pretty, kin san me? Wlh kina saka Ni nishaɗi duk sanda zan kasance ina waya dake".


Murmushi tayi tace, "buri na da fata na kenan, a koda yaushe ka kasance cikin farin ciki, ina matuƙar matuƙar ƙaunar ka Ƙalby".


Lumshe idanun sa yayi cike da jin sanyi a ransa yace, "nima haka My Baby, Ina matuƙar ƙaunar ki, fata na ki kasance mata a gare Ni, kuma uwar ƴaƴa na, Allah ya nuna min ranan da zan mallake ki, ina ga ranan ko uhmmm farin ciki na bazai misaltu ba".


Murmusawa tayi idanun ta akan hannayen ta da take wasa da su, ta amsa masa da "ameen" cikin muryan ta me daɗi.

     Da haka suka ci gaba da wayan cike da nishaɗi, ko wanne na bayyana ma ɗan uwansa irin farin cikin da yake ji idan suna tare da juna.


      Ƙarfe biyar Ray yabar gidan, Suhaib kuma sai zuwa dare ya bi jirgi ya koma Abuja.

      A ɗan kwanakin da su Ammee suka yi kafin su tafi, sosai RAUDHA ta shaƙu da su gaba ɗaya, har Faruk da be da yawan magana, shima yanzu sun saba sosai. sati ɗaya suka yi suka soma haraman tafiya, RAUDHA ta so bin su, amma dayake akwai bikin Ramcy sai ta fasa, amma Daddy sai ya ce mata "ta je tunda bikin saura Two weeks ne, sai tayi sati ɗaya ta dawo".


Murna sosai RAUDHA take yi, nan da nan ta haɗa kayan ta a Trolly tabi su suka tafi.Post a Comment for "RAUDHA CHAPTER 9"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...