RAUDHA CHAPTER 6 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RAUDHA CHAPTER 6

RAUDHA CHAPTER 6

- - Post a Comment

 RAUDHA CHAPTER 6

Baby kin ga me sunan Daddy? Yana kama dake ko?"

+

RAUDHA da ta ƙura wa jaririn idanu ko ƙifta wa ba ta yi, ko taɓa sa ta kasa yi illa gyaɗa wa Yayan nata kai da tayi

Murmushi yayi don ya san halin ta akwai tsoron ƙananan yara, don ya tsokane ta yace, "ki ɗauke sa mana kar yayi fushi dake".

Maƙe kafaɗa tayi

"Baby Daddy ne fa, ko ba kya son sa?"

Har yanzu idanun nata akan jaririn yake taƙi dena kallon sa, cikin muryan ta da baya fita ko kaɗan tace, "yaya ka bari sai ya sake girma zan na riƙa ɗaukan sa".

Dariya kawai Suhaib yayi, yana sake rungume yaron nasa tare da sumbatar sa.

     Lokacin ne Inna Haule tashigo ɗakin tana faɗin "a'ahh Mijina ashe kana nan ne?"

"Eh Inna, na rako RAUDHA ganin Baby ne".

"To madalla, ai ga ta nan kuwa ta kafa masa idanu amma taƙi ta ɗauke sa". cewar Inna cike da fara'an ta

Suhaib dariya yayi yana kallon RAUDHAN, kafin yace, "Baby baki gaishe da Inna ba".

Sai alokacin ma RAUDHA ta kalle ta tun shigowar ta, gaishe ta tayi kamar yanda Suhaib yace mata

Inna Haule kuma ta amsa mata cikin fara'a, itama tana tambayan ta "Ya jikin ta?"

Wannan karon ma Suhaib ne ya amsa mata, don yasan RAUDHA ba sake magana zata yi ba

Inna Haule zama tayi suka hau hira da Suhaib ɗin, don dama sun saba sosai, har aka kira sallan isha'i suna tare kafin ya tashi yafice, itama RAUDHA bin bayan sa tayi takoma ɗakin ta.

      Inna Haule miƙe wa tayi taje ta sako ruwan wankan, kafin tazo ta tashi Farida don tayi mata wankan.

     Bayan tayi mata wankan jegon sannan tayi wa jaririn, sai ta ɗauro alwala tafito, lokacin har Suhaib ya sake shigowa ɗakin ya fice

Babu jimawa Kuku yashigo musu da abinci da kunun me jego.

       RAUDHA kuwa tunda tashige ɗaki kwanciyar ta tayi bayan ta saka ƙwayoyin ta cikin baki tana tsotso, bata jima ba barci ya ɗauke ta

Koda Suhaib yashigo duba ta yaga tayi barci, be tashe ta ba ya gyara mata Bargon da tarufa tare da kashe mata fitilan ɗakin yafice.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

       Ranan suna jaririn ya ci sunan Daddy Mustapha, zasu riƙa kiran sa da Haneep kamar yanda RAUDHA ta saka masa

Ƴan uwa na nesa da na kusa duk sun hallara bikin sunan, gidan Suhaib ya cika maƙil don shi kansa yayi mamaki da mutanen da suka zo taya sa murnan sunan, har da wasu daga cikin dangin mahaifiyar su da ke Bayelsa sai da suka zo, dayake ita ɗin ƴar can ce, su ma wasu daga cikin dangin Daddy dake aure a gari maban-banta duk sun samu zuwa, duk da su ɗin ba dangin sa na kusa bane, but Daddy mutum ne me kyautatawa ko kaɗan ba ya manta wa dasu wajen taimako shiyasa har yanzu suke zumunci, duk da ƴaƴan sa ba zuwa suke yi ba, amma shi yana zuwa wajen su sosai don jin matsalolin su. Itama Farida ƴar dangi ce, don haka dangin ta masu yawa sun hallara ranan sunan, ga matan abokan Suhaib ɗin duk sun zo, hakan yasa jama'a suka yi yawa, an yi taron girma da arziƙi kowa ya tafi yana yaba wa.

      Ita kanta RAUDHA da ba son mutane tacika yi ba, sai da tashiga cikin su aka yi suna da ita, daga ƙarshe ne ma da kanta ya soma mata ciwo tashige ɗaki ta'afa ƙwayoyin ta sai barci, bata sake sanin me ake yi ba sai dare da ta tashi, lokacin duk an gama watse wa, sai wasu tsirarun mutane ƴan uwan Farida da ƴan Bayelsa suka rage.

      Washe gari su ma duk suka watse aka bar Inna Haule kaɗai dake mata wankan jego. Ita taci gaba da kula da ita har sanda suka yi arba'in, kafin ta tattara ta tafi cike da alhrerai kala-kala da Suhaib ya haɗa ta dasu.

      Zuwa lokacin itama RAUDHA tuni ta koma school ɗin ta, sun sake ɗinke wa da su Rash sai abun da yayi gaba yanzu, sai dai yanzu babu Zen yayi tafiya na sati biyu zuwa asalin tushen su Kwara state, an yi musu mutuwa shine suka tafi gaba ɗaya ahalin su.

        Yanzu RAUDHA, Rash da kuma Man suna tare ko ina tare suke zuwa, babu abinda suka fasa na game da rayuwan su, sai ma sake taɓarɓare wa da suke yi, ta kai ta kawo yanzu RAUDHA wani lokacin ba ta kwana agida, duk inda suka ce zasu tafi bin su take yi.

     Suhaib ya tashi hankalin sa matuƙa da irin wannan sabbin halayen da RAUDHA ta tsiro da su, yana gudun abinda zai faru kamar yanda ya rasa ta kwanakin baya, sosai ya zaunar da ita yayi mata faɗa, but ko sauraron sa bata yi ba, a ranan ma sai da ta kwana biyu bata dawo gidan ba, dole sai shi Suhaib ɗin ya neme ta ya bata haƙuri, gaba ɗaya yanzu ya gama rame wa a tsaye sabida zullumi da tashin hankalin da yake ciki, ga kuma abun tashin hankalin da ya sake riskan su, ciwon Haneep kullum gaba yake yi, yanzu wani tsira ne ya fito masa a ciki, koda yaushe ƙara girma tsiran yake yi, wai ma don suna zuwa asibiti ana magani, dole ya yanke shawaran fita kasar waje don aduba lafiyan sa, daga nan sai yaje inda Daddy yake don sanin halin da yake ciki, tunda har yanzu be sake kiran su ba, duk wasu abokan sa da suke hulɗa sai da Suhaib yabi ya tambaye su ko sun san wani abu agame da Daddyn nasu, but babu wani bayani.

          🌐🌐🌐

       Yau dayake Saturday ne RAUDHA basu da school, shiyasa take ta sharan barcin ta, jiya a club suka kwana sai da asuba ta dawo, that's why tunda ta shimfiɗe akan gadon ta take barci tamkar kasa, har zuwa ƙarfe biyu taƙi tashi

Wayan ta dake faman tsiwa tana neman agaji, ita ta tashe ta daga nannauyan barcin da take faman yi, ƙiri-ƙiri ta kasa buɗe idanun ta sabida kumburan da suka yi tsaban barci, haka tayi ta kokawa wajen buɗe idanun suna lumshe wa, daƙyar ta iya buɗe su da suka gama ƙanƙance wa suka yi jazur

Wayan dake kan drower ta jawo, lokacin Three missed Call aka yi mata, but me kiran be gaji ba ya sake kiran na huɗun, tsaki taja wanda ko kaɗan be fita ba, ta sake ware idanu kan wayan don ganin nataccen dake kiran ta

Ai tuni ta wartsake sabida ganin sunan Daddyn ta na yawo a screan ɗin wayan, wani ƙara ta ƙwalla da dusashshiyar muryan ta, jikin ta na rawa ta amsa kiran tana kiran sunan Daddy cikin ihu

Lokacin Suhaib ya turo ƙofan ya shigo, jin RAUDHA na ihu tana faman kiran sunan Daddy, ai tuni ya iso wajen ta shima ya zauna yana son ƙwace wayan da faɗin

"Da gaske kike yi Baby? Daddy ne ya Kira ki?"

Cikin tsagwaron murna ta ciro wayan daga kunnen ta tana nuna masa tana faɗin "eh shine Yaya, ka gani ko wlh shine Daddy ne.."

"To saka a hans free Baby".

"To". Ta amsa mishi da sauri tana saka wa

A lokacin ne muryan Daddyn ya bugi kunnen su yana faɗin "Hello kuna ji na?"

"Daddyyyy.." RAUDHA ta sake faɗa tana me fashe wa da kukan jin muryan Daddyn ta

Shima Suhaib ɗin sunan Daddyn yakira ahankali

Daga can Daddy ya amsa musu cikin tsananin kewar yaran nasa, kana yaci gaba da faɗin "Auta na menene kuma na kuka? Ko kin fi son na kashe wayan ne ba kya son jin muryana?".

Cikin kukan take girgiza kanta tana faɗin "A'a Daddy na dena kukan, ina so Daddy.. Ina so.. nayi kewar ka ne sosai da sosai Daddy, yaushe zaka dawo I miss You so Much".

Sai tasake fashe wa da kuka tana faɗa wa jikin Suhaib, shine ya amshi wayan daga hannun ta ya riƙe

Daga can Daddy yace, "Very soon zan dawo gare ku Baby, ki dena kuka kin ji?"

Sai kuma yakira sunan Suhaib ɗin yana tambayan sa lafiyan sa da matar sa

"Daddy lafiya lau kowa lafiya, har Wifey ta sauka an yi maka takwara".

Daga cikin wayan sosai zaka gane Daddy yayi murna da maganar da yaji, nan yayi ta nuna farin cikin shi yana saka musu albarka gaba ɗaya

RAUDHA da take faman share hawaye tace, "to Daddy yaushe zaka dawo?"

Numfashi Daddy yaja kafin yace, "Baby bansan ranan dawowa na ba".

"Why Daddy?". Tafaɗa kamar zata yi kuka

"Ƙaddara Sweetheart, ƙaddara ce ta faɗa min, na faɗa muku kaya na sun sami matsala, bansan ya aka yi ba aka samu Cocaine cikin kayan mu, to har yanzu ana kan bincike ne, dole zamu zauna har sanda za'a gama, idan kuma basu gano waɗanda suka saka ba, zasu riƙe mu ne na shekara ɗaya a Jeil, wannan shine dokan su".

Tun be ƙarisa zancen ba RAUDHA take kuka sosai

Shi kansa Suhaib tuni idanuwan sa sun kaɗa sun yi jazur sun tara hawaye, rungume RAUDHA yayi cike da tsananin tausayin kansu

Daddy shima daga can hawayen yake ta faman share wa, taya zai iya rayuwa na tsawon shekara batare da ya ga Iyalan sa da suka fi soyuwa a ransa ba? Babu wanda yake tausayi sama da RAUDHA, yasan zata shiga wani mawuyacin hali sabida rashin sa, daɗin sa ma da akwai Suhaib, da be san ya zai yi da rayuwan sa ba

Shanye hawayen sa yayi, cikin jarumtan muryan sa yahau rarrashin su gaba ɗaya, yana faɗa musu kalamai masu daɗi

RAUDHA dai taƙi yin shiru sai kuka take yi tana kiran sunan Daddy

Ganin lokacin da aka ɗiba masa na yin waya dasu ya kusa ƙare wa, hakan yasa yakira sunan Suhaib ɗin

Murya na rawa Suhaib ya amsa yana share ƙwallan shi da suka zubo saman kuncin sa

"Suhaib ga amana nan na bar maka, kai kaɗai RAUDHA take dashi a yanzu, kai ne kaɗai gatan ta, a yanzu kai kaɗai ne zaka zame mata Uwa, uba, yaya da kowa ma, Ni yanzu addu'ar ku nake buƙata, idan har da rabon gaskiya zai fito zan dawo gare ku nan kusa, idan kuma Allah be nufa ba, ya ƙaddara dole sai nayi zaman Jeil na shekara ɗaya zan ɗau ƙaddara ta, Ni dai fatana a yanzu Suhaib ka kula da ƙanwar ka, ina so in dawo in yi alfahri da ita, ka kula da ita da kyau, kayi haƙuri da duk wani halayen ta, ina son ka kula da tarbiyyan ta".

Cikin raunin murya Suhaib yace, "insha Allahu Daddy nayi maka alƙawarin kula da Baby, zaka dawo kasha mamaki saboda sauyawan ta, babu abinda zai faru da ita, zan kula da ita sosai".

Murmushi me sauti Daddy ya saki, kafin yace, "yauwa Allah yayi muku albarka gaba ɗaya, kaci gaba da kula da komi nawa, nasan yanzu ba lallai ku sake ji na ba, domin wannan shine daman da aka bamu na ƙarshe da zamu iya yin waya, yanzu zan kashe wayan".

Suhaib addu'a ya soma ma mahaifin nasa akan Allah ya bayyana gaskiya, shi kuma yana amsa wa cike da ƙaunar ɗan nasa

Da zasu yi sallama Daddy yana ta kiran sunan RAUDHA, but ƙiri-ƙiri taƙi amsa wa sai kuka take yi, sai da taji ya kashe wayan kafin tayi saurin wawuran wayan tana me sake fashe wa da kuka, tana kiran sunan Daddy kamar wacce zata shiɗe

Sosai Suhaib ya rungume ta ganin yanda take kukan kamar ranta zai fita, sai faman sambatu take yi tana faman kwaɗa wa Daddyn ta kira

Abu kamar wasa Suhaib ya rasa gane kan RAUDHA, yayi rarrashin duniya taƙi yin shiru, daga baya ma dukan sa tasoma yi sai ya sake ta, kasancewar ya riƙe ta gamm ganin tana bige-bige, lokaci ɗaya kuma numfashin ta ya ɗauke a jikin ta.Farida ce tashigo ɗakin a rikice, sabida ihun RAUDHAN ne ya tashe ta daga barci shine ta hayo saman taga me ke faruwa

+

Dai-dai lokacin da Suhaib yake ƙoƙarin zuba mata ruwa a fuska, shima ɗin duk a rikece yake hankalin sa duk ya tashi

Da sauri taƙariso wajen gadon tana tambayan sa abinda ke faruwa

Be iya ce mata komi ba saboda hankalin sa na kan RAUDHA da ta kawo numfashi, sai dai bata buɗe idanu ba illa wani irin nannauyan barci da ya kwashe ta

Girgiza ta Suhaib ya soma yi yana kiran sunan ta, sai daga baya shima ya fahimci barci ne ya ɗauke ta, mamaki sosai ya cika sa da barcin nata, da sauri ya sake zuba mata ruwa ko wai zata farka, amma ko motsin kirki taƙi yi, ga dai shi numfashin ta na fita normal irin na masu barci amma taƙi farka wa

Farida dake tsaye kan su itama tana kallon RAUDHAN, duk hankalin ta ya gama tashi, sake tambayan sa tayi

Anan ne ya faɗa mata abinda ke faruwa, har zuwa suman da RAUDHA tayi, kafin yaja numfashi yana saka hannun sa a aljihu don ɗauko wayan sa ya kira doctor, domin dai hankalin sa ya gaza kwanciya da wannan barcin da RAUDHA ta kama a lokaci ƙanƙani

Shaf ya manta ma, yau be yi amfani da wayan sa ba, kuma a kashe ya barta tun jiya, wannan dalilin ne ma Daddy da ya kira sa be same sa ba, sai ya kira RAUDHA

Kallon Farida yayi yace, "Wifey ɗauko min wayana in kira Doctor, sabida hankalina ya gaza kwanciya da wannan barcin da Baby ta hau yi, anya ma barcin take yi?"Umarnin sa Farida tabi, tafice da sauri taje ta ɗauko masa wayan

Kiran doctor yayi ya sanar masa da halin da ake ciki

Nan yayi masa alƙawarin zuwa nan ba da jima wa ba, tunda yau weekend ne yana gida.

Babu jima wa kuwa sai gashi yazo, duba RAUDHA ya hau yi, sai dai shima be gano komi dake damun ta ba illa barcin

Nan ya yi wa Suhaib bayani kafin yayi masa sallama ya fita

Sai alokacin ne hankalin Suhaib ɗin ya ɗan kwanta, rufe ta yayi da bargo sannan suka fito shi da Farida, a Parlour suka zauna zugum duk rai babu daɗi, musamman Suhaib da damuwar suka haɗu sukai mishi yawa, ga matsalan Daddy da be san ma ta ina zai soma ɓullo wa al'amarin ba, ga kuma halin da RAUDHA take ciki.

          A haka ranan suka wuni sukuku, har dare RAUDHA bata farka ba, hakan yasa hankalin Suhaib ya sake tashi, dole ya sake kiran wani doctor ɗin ya duba ta, shima ɗin be gano komi ba, barcin dai ya sake faɗa musu shi take yi

Abun da zai basu mamaki shine duk yanda Suhaib yayi ƙoƙarin tashin ta amma ko motsi taƙi yi, ya zuba mata ruwa yayi duk wani dabara taƙi tashi, sai sharɓan barci take yi, dole ya haƙura ya bar wa gobe, idan ma bata farka zuwa goben ba ya yanke shawaran Hospital zai kai ta.      Washe gari ƙarfe 07:39am RAUDHA ta farka

Farin ciki duk ya cika Suhaib sai tambayan ta yake yi "ko akwai abinda ke damun ta?" sai dai kuma taƙi yin magana, juyin duniya Suhaib yayi mata magana but taƙi tanka sa, ga dai shi tana kallon sa amma taƙi ta kula sa, kuma taƙi cin abinci, ga idanuwan ta da suka sauya kala, su ba kore ba su ba ja ba

Sabon tashin hankali Suhaib ya sake shiga, shi da Farida gaba ɗaya sun tsorata da yanayin da RAUDHAN ta tashi

Koda yayi yinƙurin kai ta asibiti, ita RAUDHAN taƙi yarda, sai ma kwanciya da tayi ta juya masa baya taƙi koda kallon sa

A taƙaice dai a ɗakin Suhaib ya wuni yaƙi jirga wa ko nan da can, duk yanda ya kai da lallaɓa ta akan ta tashi koda abinci ne taci, taƙi kula sa, dole ya haƙura ya ƙyale ta ba don ya so ba.

       Bayan sallan Asar da yadawo ɗakin ne ya ganta tana ƙoƙarin sauko wa daga gadon, da sauri ya ƙarisa wajen ta jikin sa na rawa yakira sunan ta

Ɗago kai tayi ta kalle sa da idanuwan ta da suka koma fari fatt a yanzu ɗin, ɗan kwaɓe fuska tayi cikin shagwaɓa tace dashi, "Yunwa.."

Hannun ta ya riƙe cikin farin cikin jin tayi magana, dasauri ya maida ita ta zauna, yana faɗin "yunwa ko Baby? To bari in kawo miki abinci, ki zauna kar ki tashi ina zuwa".

Ya saki hannun ta ya juya da sauri.

      Yana fita itama ta tashi tabiyo bayan sa, be san tana bin sa ba har sanda ya dangana ga kichen ɗin, dasauri ya juyo yana kallon ta

"Baby biyo NI kika yi kuma?"

Gyaɗa masa kai kawai tayi tana ƙarisowa kusa dashi.

     Abincin ya ɗiba mata cikin coolar sannan ya riƙo hannun ta suka fito daga kichen ɗin, a Parlour suka zauna yana bata a baki, ita kuma tana amsa batare da tace mishi uffan ba duk da kuwa maganan da yake mata.

      Itama Farida fitowan ta kenan daga ɗaki ta gan su a parlour'n, tana riƙe da Haneep a hannun ta ta iso wajen su fuskar ta cike da annuri, zama tayi kan two sittern dake Kallon wanda suka zauna, idanun ta akan su tace, "Ƙanwata duk kin ɗaga mana hankali da rashin cin abincin ki, don Allah idan fushi kike yi damu ki dena wasa da cikin ki irin haka kinji? Baki ga yanda muka tashi hankalin mu ba akan rashin mana magana da kika yi".

Ɗago kai kawai RAUDHA tayi tazuba ma Faridan idanu, batare da tace komi ba dai take amsar abincin da Suhaib ke faman ba ta, yana yi yana shafa kanta tamkar wata ƙwai, ji yake yi kamar ya ɗauke ta ya maida ta ciki sabida ƙaunar ta

Farida dai bata damu da rashin mata magana ba, tunda ta saba da halin ta, girgiza Haneep take faman yi sabida kar ya tashi daga barcin da yake yi.

      Be dena bata abincin ba har sai da ta ture hannun sa, hakan yasa ya janye yana ɗaukan ruwa a Cup ya miƙa mata

Amsa tayi tasha sannan ta ba shi ya'ajiye

Kallon ta kawai yake yi yana zuba mata murmushi, sai kuma ya saka hannu yana gyara mata gashin ta dake zube a gadon bayan ta babu Ribom, tattare mata ya hau yi yana ƙoƙarin ɗaure mata shi

Ita dai tana jin sa batace komi ba, ba wai don ba ta da abun cewa ba, a'a, sai don rashin daɗin da jikin ta ke mata, kamar an zare mata laka haka take ji, ga kanta da be gajiya da mata ciwo ko yaushe.

      Tashi  Suhaib yayi ya riƙo mata hannu yana faɗin "tashi muje ki raka Ni Baby".

Tashi tayi babu musu

Farida ta kalle sa tana cewa, "Husband sai ina kuma?"

Keey ɗin motan sa dake ajiye akan Centre table ya ɗauka yana bata amsa da faɗin "super market zan kai Baby".

Adawo lafiya tayi musu

Fice wa suka yi ita kuma ta raka su da ido, ajiyan zuciya ta sauke aranta tana tunani daban-daban.              🌐🌐🌐

     Babu inda suka zarce sai super market, kayan ciye-ciye duk ya jido mata cikin leda, daga nan suka yo gida

Suna shigowa RAUDHA tanufi sama da kayan ta

Shi kuma Suhaib zama yayi akan sofa yana zaro wayan sa dake faman Ring, idanun sa ya kai saman wayan, sai kawai ya saki murmushi idanun sa a waje

Be ɓata time ba ya amsa kiran yana kara wa a kunne

"Wlh Ni nayi fushi ℝ𝔸𝕐, baka san da tuna wa dani ba sai yanzu". Suhaib ya faɗa hakan har yanzu da kyakkyawar murmushin sa shimfiɗe a face ɗin sa

Daga can wata dakakkiyar murya me tsananin daɗi da sanyi tasoma magana, shima daga ji mamallakin muryan yana a cikin nishaɗi ne

"Afwan ranka ya daɗe tuba nake, kaina bisa wuya Dude".

Suhaib yace, "Ni dai nayi fushi da kai, kuma ban san wa zai shirya mu ba, nayi ta neman Numban ka but a kashe koda yaushe".

Murmushi me sauti wanda aka kira da Ray ya saki, kana kuma yace, "Plz Dude I'm so sorry, wlh bansan da bakin da zan yi maka bayani ba, laifi na shine aiki ya mantar dani na bar waya ta a can Bayelsa, kuma na taho nan Nigeria da ninyan in zo har gida but aiki ya riƙe Ni, sai da na sauya waya kuma na tuna ban riƙe sabon Numban ka ba, har ta na Daddy ma ba na samu wlh, yanzu haka na koma gida ne na samu na kira ka".

Suhaib dariya yayi cike da farin cikin jin Abokin nasa, tare da tsantsan ƙaunar junan su yace, "babu komi Dude na amsa tuban ka, and sai dai ka kiyaye gaba don idan ka sake irin wannan babban laifin tabbas zamu samu matsala".

Gaba ɗayan su suka yi dariya wannan karon, sai Suhaib yayi saurin cewa, "wai ma tsaya, kar inyi saurin yafe maka, I tot kana Kaduna ne, Right?"

"Yeah Ina Kaduna wlh, wajen Six months kenan yanzu nayi".

"But I know baka taɓa nema na ba acan?"

"Sorry Dude aiki ne.."

"Eh na sani aiki ne zaka ce dama". Suhaib ya katse sa da faɗan hakan

Sai kuma suka yi dariya gaba ɗaya kafin su soma gaisa wa cike da kewan junan su, duk kan su farin ciki yalwace a fuskokin su, kai da gani kasan akwai soyayya da shaƙuwa sosai a tsakanin su

Suhaib ya tambayi iyalan gida gaba ɗaya

Ya ba shi amsa da "Alhamadulillah kowa lafiya" sannan shima ya tambayi lafiyan matar shi da ƙanwar shi RAUDHA

Murmushi Suhaib ya saki yace, "I know yanzu Baby ta manta da kai, ko kai ma nasan baza ka gane ta ba yanzu ai".

Murmushi shima yayi yace, "gaskiya ne, to shekaru sun ja, ina tunanin ma rabo na da ita 14years Ago fa, sa'ilin tana 5years, uhmm yanzu nasan ta girma sosai, ta zama ƴammata".

Suhaib yace, "really! gashi yanzu har ka zama Daddy yanzu ma".

"Dude da gaske?"

Murmushi Suhaib ya saki yana ƙara bashi tabbaci, kafin ya faɗa masa abun da aka samu

Sosai ya nuna farin cikin sa, cike da ɗoki yace, "kace zan zo a Sa'a kenan, domin zuwa gobe insha Allahu uwar haka ina nan Abuja, an dawo damu nan zamu yi 3years, so har na ba da cigiyan gida anan, domin ba zan zauna a Barrack ba".

Shima Suhaib murna ya hau yi, cike da tsantsan farin ciki yace, "ai gidana kawai zaka zo, taya ma zaka zauna a wani waje bayan kana dani, No No hakan ma bazai taɓa yiwu wa ba, ai kawai anan zaka zauna".

Dariya shi dai yayi, don daman ya san halin abokin nasa, shiyasa be wani ja zancen ba suka ci gaba da hiran su, daga ƙarshe suka yi sallama cike da farin cikin gobe zasu ga juna, tsawon shekaru uku kenan rabon da su ga juna ido da ido, sai a waya, a wayan ma yanzu kusan 7months

Koda aka yi auren Suhaib be halarci bikin ba, lokacin an tura su Jejin sambisa don kawo ƙarshen ƴan boko haram, a time ɗin kusan shekaru biyu suka yi acan suna karan batta, daga ƙarshe ma an yi tunanin sun mutu don tuni an rasa inda suke, an duba su ko ina ba'a same su ba saboda a lokacin an rigada an kashe mutanen su gaba ɗaya, sai su iya goma da suka sha, a wani ƙauye suka zauna tsawon shekara ɗaya da watanni suna a mawuyacin hali, domin duk kan su sun sha harbe-harbe babu kyan gani, sai da aka yi jinyan su har suka gama warke wa, kafin su samu su dawo gida daƙyar, don a hanya ma sai da suka sake cin karo da ƴan boko haram, gashi time ɗin basu da makamen aiki, daƙyar suka sha aka kashe musu mutum uku.

Sai dai sun san juna sosai a waya shi da Farida, don suna yawan gaisa wa akai-akai, har a hoto ma ta san shi tunda tana gani a wayan Suhaib.

      Suhaib ɗin na sauke wayan a kunnen sa, Farida tafito daga ɗakin ta, zama tayi tana tambayan sa "shi da wa yake waya yake ta faman fara'a?"

Lokacin itama RAUDHA ta sauko daga sama, ta ƙariso wajen ta zauna gefen Yayan nata, tana jin duk amsan da Suhaib yake ba wa Farida but bata saka musu baki ba, tunda ita be shafe ta sai tasan ko wanene ba a ganin ta.

       Sosai Farida tayi farin ciki itama da zuwan Ray ɗin, nan suka soma shawaran ɗakin da za'a gyara masa zuwa goben, Suhaib yace, "a gyara masa sama kusa dana RAUDHA, nan zai fi".

Ɓata fuska RAUDHA tayi kawai batare da ta tanka su ba

Suhaib ya janyo ta jikin sa yana cewa, "Baby baki ce komi ba, kina jin zamu yi baƙo?"

Baki ta taɓe tace, "to Ni ina ruwana dashi".

Murmushi Suhaib yayi yace, "ai kuwa ke kike da ruwan ki Baby, Yaron Uncle Hassan ne fa, wanda ada yake siyo miki chaculate time ɗin kina ƴar ƙararrama, sai ki maƙale masa idan yazo gidan mu kice sai kin bi shi, har kin manta sa ko?" Yayi maganar cike da tsokana

Turo baki tayi tace, "Ni Yaya na manta shi, kuma bazan iya tuna shi ba".

Hancin ta yaja yace, "dama wasa nake miki Babyna, time ɗin ai kinyi ƙarama da yawa, but ina so in faɗa miki zamu je Ƙasar India wajen likita, saboda Haneep, zaki bi Ni Ko zaki zauna ki kula da karatun ki?"

Kallon sa tayi, sai kuma ta kawar da kanta cike da sanyin murya tace, "bazan je ba".

Murmushi Suhaib yayi domin shima yafi son hakan, gwara ta zauna tayi karatun ta har sanda zasu dawo, tunda a ganin sa yanzu yana da wanda zai ba ma amanar ta, hankalin sa kwance zai bar ta yaje ya dawo. 𝗧𝗼𝗺𝗼𝗿𝗿𝗼𝘄 𝗠𝗼𝗻𝗱𝗮𝘆

Ƙarfe 10:00am. Yau RAUDHA suke da Lectures, zuwa ƙarfe 09:20am. Har ta gama shirin ta, ta saka riga da wando, dack blue Jeans pencil crazy, sai ta saka ƙaramar riga t. Shirt me gajeren hannu baby blue colour, sannan ta ɗaura baƙar Kimono akai, yau har da Facing cap ta saka a kanta sannan ta saka hill shoes, taɗau jakar ta tafito

+

Sai da tashiga har ɗakin Farida ta yiwa Haneep kisses kafin tafito tafice, mota tahau tabar gidan da gudun da ta saba.🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

     Zuwa ƙarfe 02:30pm. Suhaib ya nufi airport ɗauko abokin sa, time ɗin yazo babu daɗe wa sai ga jirgin su ya sauka, don haka yafito yanufi haraban airport ɗin.

     A cikin waɗanda suke sauko wa na farko-farko, Suhaib ya hangi babban Amininsa wanda tuni yanzu ya zame masa ɗan uwa, *Captain Rayyan Hassan* kenan

Shima tuni ya hange sa, don haka tun sanda ya sauko a matattaƙalan benen jaye da Trolly ɗin sa yanufo sa fuskar sa cike da fara'a

Yayinda shima Suhaib ɗin ya tako zuwa gare sa dasauri, yana zuwa suka rungume juna ko wannen su yana me nuna farin cikin ganin ɗan uwan sa, sai kuma suka saki juna suna me cafe hannaye bakin su a washe

Sai da suka gama gaisawa kafin Suhaib ya amshi Trolly ɗin yaja, suka nufi inda yayi parcking motan sa riƙe da hannun juna.

       Ko a motan ma hira ne ta ɓarke a tsakanin su har suka isa gida.

     Farida na jin su tafito daga ɗaki cikin fara'an ta ta tarbe shi, dama tuni ita da kukun ta sun shirya masa girkin tarba, don haka koda suka gaisa sai Suhaib yaja sa zuwa sama, ya nuna masa ɗakin sa don yayi wanka kafin yazo yaci abincin.

     Bayan yayi wankan ya sauya kaya, sannan ya sauko ƙasa suka zauna da Suhaib a saman dainning

Farida tayi saving ɗin su kafin ta wuce ɗaki tabar su don su sake.

    Bayan sun gama cin abincin Parlour suka dawo suka dasa wani hiran

Lokacin Farida tafito ta kawo masa Haneep don ya ganshi

Miƙa masa tayi tana faɗin, "wannan ɗan dai ya taki Sa'a, yazo duniya da ƙafan Nasara tunda ya haɗu da Mahaifin shi batare da ya sha wahala ba, ko in ce ba sai ya girma ba ya soma tambayan mu Daddyn sa".

Dariya suka yi gaba ɗaya

Rayyan yace, "kar ki saka in ji kunya mana Momyn Dady, kin san fa an ce yara kunne ne dasu, kar kuma ace yana jin k.."

Maganar tasa ne ta ƙaƙare sabida kukan da Haneep ya tsandara, dasauri yasake riƙe yaron sosai sabida ganin zai kubce masa, hakan yasa ya sake ɗaura hannun sa a ciwon sa, sai ya sake tsandara masa ihu

Taso wa Farida tayi ta amshe shi tana cewa, "kayi haƙuri Captain na manta ban sanar maka yana da tsira a cikin sa ba, idan aka taɓa masa shine yake kuka". Taƙarishe maganar tana girgiza yaron bayan ta buɗe wajen ta gani

Sosai Rayyan yaji tausayin yaron ganin girman ƙulun dake cikin sa, sai ya kalli Suhaib yace, "Dude menene wannan ɗin? Ya akayi baku nema masa magani ba?"

       Farida juyawa tayi ta wuce ɗaki don ta rarrashe shi.

     Nan Suhaib ya sanar masa da halin da ake ciki, kafin ya ƙara da faɗa masa "sun samu DOCTOR a India zasu je can ya duba sa".

Numfashi Ray yasaki a hankali yana jinjina kansa, sai kuma yayi masa addu'an samun lafiya yana sake nuna tausayin sa.

     Daga nan sun ɗan taɓa hira kafin shi Rayyan ɗin ya tashi, yace masa "zai je Barrack ɗin su"

Tare suka tashi suka fita bayan sun ɗaura alwala a Toilet ɗin parlour'n, sai da suka yi sallah suka komo gidan kafin drever ya ɗauki Rayyan zuwa Barrack, Kasancewar daga can zai taho da motar sa that's why drever zai kai shi.

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

      Ƙarfe 05:00pm. RAUDHA tashigo gida agajiye, yau Lecture ɗaya suka yi a school ɗin, sai suka fantsama yawo da su Rash, bata dawo ba sai yanzu, tana shiga wanka tasoma yi, ta saka Biri da wando mara hannu kalan sararin samaniya, sai ta ɗaure gashin ta da Ribom baƙi ta saka room Slippers me kamar Socks, ta sauko ƙasa

Abinci ta ɗibo ta zauna gefen yayan ta dake aiki cikin Lapton, tana ci suna taɓa hira duk da shine ke maganar, ita iyakan sauraron sa take yi tana saka loma.

      Bayan ta gama ajiye Plate ɗin tayi saman Centre table, ta ɗauki Remote tare da gyara zaman ta ta ɗaura ƙafafu saman kujeran, sannan tasoma sanja channels, idan tasaka wannan be mata ba, sai ta sauya da wannan, ahaka har ta samo tashan da ake yin wrestling, tunda yau Monday ne sai dare MBC Action zasu yi.

"Yaya wai ina baƙon da kace zamu yi?" Tayi maganar idanun ta na kan t.v

Shima batare da ya ɗago kansa ba ya bata amsan "ya fita zuwa Barrack ɗin su".

Be fi kamar minti goma da maganar nasu ba, Rayyan yadawo shima.

      Yana shigowa parlour'n, RAUDHA tayi zumbur ta tashi tamkar ta ga abun tsoro

Hakan yasa Suhaib ya kalle ta da mamaki, sai kuma ya maida idanun sa kan Rayyan ɗin da take kallo

Yana takowa cikin parlour'n ne shima idanun sa kan ta, zuciyar sa cike fall da mamakin ganin ta anan ɗin, domin dai bazai taɓa manta ta ba a rayuwan sa, yanda ya santa a baya haka take har yanzu, sai dai raman da yake kallo a kyakkyawar fuskar ta

Bakin ta na rawa tace, "You..". Sai kuma ta datse bakin tana ƙara ware idanun ta kan shi

"Ikon Allah! Baby kin san shi ne?" Cewar Suhaib yana kallon ta fuskar sa cike da fara'a

"Yaya kar dai ace shi ne abokin ka da zai zauna tare damu?"

Suhaib yace, "shine Baby".

Taɓe baki Rayyan yayi yana isowa wajen, ya sami waje ya zauna batare da ya nuna shi ya gane ta ba, duk kuwa da cewa sosai yake mamaki a ransa da ganin ta, "kar dai ace wannan sheɗaniyar yarinyan ita ce RAUDHA ƙanwar abokin sa?"..

Be kai ga lalubo amsar ba, Suhaib ya tabbatar masa da maganar sa

"Dude wannan ita ce ƙanwata RAUDHA, Baby ga Yayan ki Captain Rayyan". Suhaib yayi maganar cikin fara'a

Sake haɗa idanu suka yi, yayinda Rayyan ya sake haɗe fuska don ma kar ta kawo mishi raini, ganin kallon da take mishi, sai ma ya ɗauke kai yana sake taɓe bakin sa

Hakan ya tunzura RAUDHA, kamar an tsikare ta ta kalli yayan nata, cikin tsiwa tace, "yaya Ni wannan mutumin sam be min ba, mugu ne azzalumi.."

Dasauri Suhaib ya katse ta da faɗin, "baby kina da hankali kuwa, Dude ne fa Abokina? Me yayi miki kike kiran sa azzalumi?"

Cikin fushi tace, "shi ne wanda muka taɓa karo dashi a hotel ɗin Kaduna, har ya buga Ni ajikin bango ya zazzage Ni, wlh yaya bazan zauna dashi a gidan nan ba, sai ya bar mana gida domin na matuƙar tsanar sa". Taƙarishe maganar ta idanun ta akan Ray batare da tsoro ko shakkan sa ba

Tasowa Suhaib yayi ya riƙe ta yana faɗin, "haba Baby me yayi zafi haka? Nasan dai Dude bazai zage ki a sanin sa ba, kiyi haƙuri tunda be san ke ce ba".

       Rayyan kuwa sosai ransa ya ɓaci da maganganun RAUDHA, sai kuma abun ya koma ba shi mamaki ganin yanda Suhaib yake rarrashin ta, tsamm ya miƙe yayi hanyan steps cikin tafiyan sa na ƙasaita

Itama RAUDHA Steps ɗin tayi da gudu ta wuce ɗakin ta

Suhaib ma biyo bayan ta yayi, sai dai be shiga ɗakin ta ba ya wuce ɗakin Rayyan.

     Yana tsaye ransa duk a ɓace, shigowar Suhaib ya ɗago jajayen idanun sa da suka sauya kala lokaci ƙanƙani ya kai duban sa gare shi

Zuwa Suhaib ɗin yayi ya riƙo hannun sa yana ba shi haƙuri, tare da faɗa masa "wai kuskure ne RAUDHA tayi amma baza ta sake ba"

Ɗan guntun murmushi Ray yayi a ransa, ya dubi abokin nasa yace, "Suhaib kana nufin wai yarinyan nan ita ce RAUDHA? Ita ce ta koma haka? Wannan tarbiyyan dama kuka ba ta, kana ganin hakan me ɓulle wa ne? Shin wani irin gata ne wannan da kuka nuna mata har ta zama haka?"

Fuskar Suhaib cike fal da damuwa yace, "Dude zauna muyi magana".

Babu musu Ray ya zauna, kasancewar ya ga damuwa ƙarara a fuskar abokin nasa, shiyasa be masa musu ba yayi yanda yake so

Shima kuma Suhaib ɗin zama yayi a gefen sa.

     Tattaunawa suka soma yi, sun daɗe kafin su gama, sannan Suhaib ɗin ya fito, ɗakin RAUDHA dake kallon na Rayyan ya nufa, sai dai a rufe yake, be yi yunƙurin ƙwanƙwasa wa ba don ya san baza ta saurare shi ba

Ya daɗe anan tsaye a corridor ɗin saman, yana jingine jikin ƙarfen wajen, har sai da ya gaji don kansa kafin ya sauko ƙasa ya wuce ɗakin su.
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

      Tun daga ranan kuma RAUDHA ta hau fushi da kowa da ke gidan, da zaran ta fita ba ta sake dawowa sai dare

Ko Suhaib ya tunkare ta yana ba ta haƙuri, tare da lallaɓa ta, ko kallo be ishe ta ba, da zaran ma ya same ta a waje tashi take yi ta bar shi

Shi kuwa Rayyan ma basu sake haɗuwa ba, tunda ba ya zama shima agidan sosai, sai dare yake dawowa, kuma idan ya dawo time ɗin ko RAUDHA na wajen yawon ta, ko kuma tana ɗaki.

       Yanzu gaba ɗaya ta maida kanta kullum a buge take, karatun ma ba kullum take zuwa ba, sai ta ga dama.

     Ahaka har aka shafe sati guda, gashi su Suhaib har sun gama shirye-shiryen tafiyan su ƙasan India, sai da ta ga da gaske zai tafi kafin ta dena fushi dashi, don tana ƙaunar yayan ta matuƙa, ba ta son ya tafi tana fushi dashi, zata yi missing ɗin sa sosai.

     A ranan ma da zasu tafi ƙin zuwa school tayi, ita da kanta ta ɗauke su zuwa airport, time ɗin Captain Rayyan yana wajen aiki, sun rigada sun yi sallama tun kafin ya fita da safe.

       Tana dawowa gida wanka tayi ta sauya shigan ta na doguwar riga 👗iya gwiwa purple colour, sai ta saka flet shoes 🥿 baƙi, ta sake fice wa agidan

Direct gidan su Rash ta nufa, acan ta zauna har dare taƙi dawowa gidan, saboda rashin yayan ta, wuni tayi a buge tana ta sharan barci, da daren kuma bata dawo ba suka wuce club

Wajen sha ɗayan dare amma yanda kuka ga rana haka wajen yake, mutane ne birjik maza da mata kowa sai raƙashe wa yake yi, dayake akwai partyn da ake yi ne, that's why mutanen suka cika, wasu na rawa wasu na zaune suna shaye-shayen su, wasu kuma na harkan gaban su, kowa da abinda yake yi

Ita dai RAUDHA tana cikin ƴan rawa ne sai raƙashe wa take yi, daga ƙarshe ma ita kaɗai aka bar wa filin tana ta rawa, ana mata tafi da ihu, suna sake koɗata tare da mata kirarin dake fasa mata kai, hakan ke sa wa tana sake zaƙe wa abun ta

Gaba ɗaya mazan wajen burin su kawai su je gare ta, domin kuwa ba ƙaramin tafiya da imanin su tayi ba, sai dai Zen da Man tare da sauran abokan su; sun baƙe-baƙe sun hana kowa.

      RAUDHA dake ta faman ihu tana rawan ta bata ma san me ake yi ba, jin ta take yi cikin nishaɗi da walwala, domin babu abinda rawa ke saka ta illa farin ciki, tana ƙaunar rawa fiye da ranta, ko wani irin ƙunci take ciki idan har zata ji kiɗa na tashi sai taji zuciyar ta tayi mata sanyi, wani nishaɗi ya tabaibaye ta.

        Jin an damƙe mata hannu, babu shiri ta tsai da rawan da take yi tana juyo da kanta ga wanda ya riƙe ta ɗin

Idanun su ne suka haɗe waje ɗaya, a take gaban ta yayi wani irin bugawar da yasa ta waro lumsassun idanun ta gaba ɗaya waje, mamaki da tsoro ne ya cika ta ganin Rayyan tsaye a gaban ta tamkar wani zaki, gaba ɗaya ya haɗe fuskar sa kamar be taɓa sanin wani rahma ba, fararen idanuwan sa kuwa sun yi wani luhu-luhu sun yi jazur har wani ƙyalli suke yi

Sosai RAUDHA ta tsorata da ganin sa, domin dai bata taɓa tunanin ko a mafarki zata iya ganin wannan halittan a inda take ba..

Jin ya soma jan ta zai bar wajen da ita, nan ta aro jarumta, cikin tsananin fushin da bata san dalilin yin sa ba ta buɗe baki cikin dashashshiyar muryan ta tace, "How dare you! Da zaka taɓa min jiki da wannan banzan hannun naka? Zaka cika Ni Ko sai na baka kashi?"

Juyowa yayi ya tsaya yana kallon ta, ransa idan yayi dubu to a ɓace yake, sai dai ya san idan har ya biye mata, to, tabbas zai iya kakkarya ta anan wajen.

     Su Zen da basu san lokacin da Rayyan ya iso wajen RAUDHA ɗin ba, tsaya wa kawai suka yi suna mamakin ganin mutumin da sam babu alamun sauƙi a tare da shi, musamman ma yanayin jikin sa ka san ya kai a kira sa cikin zaratan maza, waɗanda ko kallon su kayi sai ƙirar jikin su ya baka tsoron tunkaran inda suke.

Ganin ya ja RAUDHA kiiiiii.. yayi hanyan fita da ita, sai gaba ɗayan su suka yi kansa

Sai dai basu kai ga yin taku uku ba, ya nuna musu bindiga, cikin kakkausar muryan sa me firgitar wa yace, "wlh duk wanda ya sake yin taku ɗaya acikin ku, sai dai uwar sa ta haifi wani".

Tuni ya juya ya fice ko sake bi ta kansu be yi ba, bare ma ya saurari RAUDHA dake faman yakushin hannun sa tana son ƙwace wa, sai ƙunduma masa zagi take yi.

     Sai da ya fice gaba ɗaya a wajen kafin su Zen sukai waje da gudu, don a tunanin su sace ta yake son yi, amma abun mamaki suna fita suka gansa ya jefa RAUDHA cikin motan sojoji, hakan ya sake firgita su, ai kowa sai ya nufi hanyan tsira ganin hukuma ne da kan su, suna ganin ya ja motan ya bar wajen, su ma sai suka nufa motocin su kowa na ta kansa, don a tunanin su sojojin zasu dawo su da yawa su farmake su ne. 𝗧𝗼𝗺𝗼𝗿𝗿𝗼𝘄 𝗠𝗼𝗻𝗱𝗮𝘆

     Sai da ya fice gaba ɗaya a wajen kafin su Zen sukai waje da gudu, don a tunanin su sace ta yake son yi, amma abun mamaki suna fita suka gansa ya jefa RAUDHA cikin motan sojoji, hakan ya sake firgita su, ai kowa sai ya nufi hanyan tsira ganin hukuma ne da kan su, suna ganin ya ja motan ya bar wajen, su ma sai suka nufa motocin su kowa na ta kansa, don a tunanin su sojojin zasu dawo su da yawa su farmake su ne._______📖 Sanda ya jefa ta cikin motan sai da kanta ya bugu sosai da jikin kujera, hakan yasa ta dafe kanta tana me fashe wa da kuka, yunƙura wa tayi don ta tashi amma ta kasa, dole ta dakata domin kuzarin ta yadawo, tana runtse idanun ta tana ci gaba da kukan ta

+

Shi kuwa tuƙin sa kawai yake yi be damu da kukan nata ba

Daƙyar ta samu ta ɗago daga kwancen da take ƙasan kujera, a fusace tasoma ƙoƙarin buɗe ƙofan don ta fice, amma kuma ya rigada ya saka luck, dole ta dakata tana sake fashe wa da kuka cike da hasala, idanun ta ta sauke akansa da suka cika da ruwan hawaye, cikin kuka da ɗaga muryan ta da ba ya fita tace, "kaii ɗan tasha ka sauke Ni in fita, wai meye haɗina da kai ne? Me na tare maka? Uban wa ya aiko ka ka ɗauke Ni?"

Rayyan be da alamun kulata sai ma ƙara Speed da yake yi, danne ɓacin ransa kawai yake yi don ba ya so ya nuna masa ainihin wanene shi a yanzu

Ita kuma shirun da yayi mata yasa ta sake fusata, ta miƙe a ƙufule ta hantsala gaban motan, babu wata-wata tasoma ƙoƙarin murɗa sitiyarin motan, nan da nan motan ta fara tambal-tambal akan titi, Allah yaso dare ne sosai babu ababen hawa, da tuni sun yi hatsari

Duk yanda ya so ya tsayar da ita wajen riƙe mata hannayen ta, but ya kasa, dole ya ja wawan burki a tsakiyar titin, wanda yaja RAUDHA tafaɗo jikin sa suka gwara kai

Gaba ɗayan su sun ji zafi, musamman RAUDHA da sai da numfashin ta ya ɗauke na wucin gadi, sabida azaban da taji sai da tariƙa ganin taurari suna gifta mata, kasancewar ta bata saba shiga wahala ba, bata ma san shi ba a rayuwan ta

Shi kuwa Rayyan duk da zafin da ya ziyarce shi, sai yaji gaba ɗaya ya ɗauke sakamakon runguman da RAUDHA tayi masa, sai kawai tunanin sa ya tsaya cak yana sauraron wani irin baƙon yanayin da ya ziyarce shi, ga shi tarigada ta kanainaye shi, ta tusa kanta cikin ƙirjin shi ko motsin kirki bazai iya ba

Wani irin numfashi yaja wanda ya dawo da RAUDHA duniyar mutane

Dasauri ta ɗago kanta tana kallon shi, wanda hakan yasa idanun su suka faɗa cikin na juna, zaro idanu tayi ganin fuskarta kusa da nashi, sai tayi saurin duba inda take ɗin da har ta samu kusanci dashi haka, ganin ta akan jikin sa ai babu shiri tayi wani irin zame wa takoma kujeran me zaman banza, tana mayar da hannun ta saman kanta da har yanzu yake mata zugi, take ta runtse idanun ta tana me sake fashe wa da kuka

Da kallo yabi ta dashi tamkar wani soko, ko kaɗan ya kasa kataɓus bare wani muhimmin tunani

Idanunta ta ɗago da suka yi jazur ta sauke kansa, wani irin kallon tsana take aika mishi dashi wanda bata taɓa yi wa wani mahaluki ba, zuciyarta sai ta farfasa take yi, haka ma jinin jikin ta, ji take yi tamkar ta shaƙe shi ta kashe shi ko zata dena jin raɗaɗin da ke baƙuntan ta.

Juyawa tayi ta buga ƙofan don ta buɗe, sai dai har yanzu akwai luck, jijjiga ƙofan ta hau yi tamkar zata ɓalla, sai buga wa take yi amma ko alamun motsi ba ya yi

"Wlh idan har baka buɗe ƙofan nan ba, sai na kashe ka! Sai na maka kisan gilla". Tayi maganar a tsananin fusace jajayen idanun ta akan sa

Kallon ta kawai yake yi yana nazartan ta, so yake yi ya gano ainihin abinda ke ranta domin dai yarinyan abun mamaki ne da ita, shi gani yake yi ko tasha ƙwayan nata ne ta bugu, don haka be sake bi ta kanta ba yayi wa motan keey yaci gaba da tafiya

RAUDHA kuka ta fashe dashi ganin be kula ta ba, itama sai bata sake yunƙurin yin wani abu ba, ta lafe a jikin kujeran tana ci gaba da kukan ta, jira kawai take yi taga inda zai kai ta, da abinda yake shirin yi, idanun ta a rufe suke, bata sake buɗe su ba sai da taji tsayuwar mota, ɗago kanta tayi tana kallon inda suke, a mamakin ta sai taga sun dawo gida ne, juyawa tayi wajen sa, amma kuma shi tuni ya fice a cikin motan

Jin an buɗe inda take ne, tayi saurin juyowa tana kallon sa

Shine tsaye ya haɗe giran sama da ta ƙasa, fuskar nan babu walwala yace, "fito".

Ko motsi taƙi yi, sai ma ɗauke kai da tayi tana sake matso hawaye

Hannun sa ya saka ya finciko ta waje, jan ta yasoma yi zuwa ciki, amma ita kuma tana tokare wa baza ta je ba, tare da bugun hannun sa akan ya sake ta

Dole ya saka mata ƙarfi ya ja ta ciki, suna shiga ya jefar da ita kan kujera, ya koma ya rufe ƙofan da keey, dawowa yayi be ce mata komi ba ya haura sama.

    Dasauri ta tashi ta biyo bayan sa tana zagin sa da gaggaya masa maganganu, amma ko ta kanta be yi ba ya rufe ƙofan shi

Ajikin ƙofan ta zube tana dukan ƙofan tana kuka tana faɗa masa "yazo ya buɗe ta takoma inda ta fito". Tamkar mahaukaciya haka takoma sai bugun ƙofan take yi taƙi ta haƙura, kuma bakin ta yaƙi yin shiru.

Sai da takai har gabanin asuba a zaune a wajen sabida jaraba, ita bata dena kukan ba kuma bata dena surutun ta ba

Shi Rayyan ma har yayi barcin sa, don be san ma tana yi ba.

Rarrafa wa tayi tashige ɗakin ta, akan kujera ta kwanta tana sauke ajiyan zuciya, nan da nan barci ya ɗauke ta kasancewar shi ne fal a idanun nata, amma taurin kai da naci ya hana ta sararawa kanta, da takalmin a ƙafan ta tayi barcin ta.

      Bata farka ba kuwa har ƙarfe biyun rana, a lokacin da ta tashi sosai kanta yake mata ciwo sabida kukan da tasha jiya, idanun ta ma daƙyar take iya buɗe su, fuskarta gaba ɗaya ya yi jazur tamkar tattasai, musamman wajen idanun ta, kasancewar sun kumbura sunyi luhu-luhu

Miƙe wa tayi daƙyar tasoma cire kayan jikin ta, wanka tashige ta hau zuba ma kanta ruwa tun daga saman kanta, ta jima a tsaye ruwan na dukan ta idanuwan ta arufe ruf, sai da ta soma jin dama-dama sannan ta hau yin wankan, bayan ta gama tafito ɗaure da towel ajikin ta, gaban dressing mirror tazaun bayan ta jona socket ɗin handrayer, ta hau busar da baƙin gashin ta da ya kwanta a bayan ta, tana yi tana kallon kanta a mirror, fuskar ta ko alaman walwala babu, kumburin da yayi har yanzu be ragu ba, har ta gama zuciyarta a cinkushe take, miƙe wa tayi ta isa gaban Sip ɗin kayan ta tabuɗe ta soma ciro kayan da zata saka, cikin sauri take shirin ta sabida yunwan dake azalzalan ta

Biri da wando me siraran hannu ta saka, kalan sa tamkar kayan sojoji haka yake, sai dai wannan ya cika duhu sosai, amma kuma suna amfani dashi sojojin, dayake me haɗe da Socks ne shiyasa bata tsaya saka takalmi ba tafita da gudu, Direct ƙasa tanufa tayi wajen dainning

An jera abinci da alamu yanzu ma kukun ya gama, domin da ta buɗe coolarn abincin sai faman tururi yake yi

Zuba wa ta hau yi cikin Plate, ta saka spoon ta soma ci kanta a ƙasa, ko ɗago kai ba ta yi, abincin kawai take aika wa bakin ta, wanda idan ta kai ɗaya sai ta ɗau sokonni kafin ta sake kai wani.

Ray ne ya sauko daga saman da kakin sojojin sa ajikin sa, sosai suka yi masa kyau suka sake haska farar skin ɗin sa, tare da ƙawata ƙaƙƙarfan ƙirar jikin sa, wanda kallo ɗaya idan kayi masa zaka san Jarumin namiji ne na bugawa a jarida.

     Takun takalmin sa yasa RAUDHA ta ɗago kai, kallo ɗaya tayi masa ta mayar da kanta ƙasa, sai dai ta kasa ci gaba da cin abincin illa juya cokolin da take faman yi aciki

Shima sai da ya sauko kafin ya kula da ita, dama ya rigada ya fita dawowa yayi, shine yanzu zai koma

Zuwa yayi kan kujerun parlour'n ya zauna, idanun sa akanta amma fuskar sa a matuƙar murtuke yace, "kee?"

Har cikin kanta taji muryan nasa ya tsirga mata, sai dai ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta da alaman yi, idanun ta kafe akan abincin ko ƙyafta wa ba ta yi

Numfashi yaja yana ɗan kawar da kansa daga kallon ta, yaci gaba da maganar sa batare da ya damu da ta'amsa ko kar ta amsa ba

"Kina jina daga yau babu ke babu sake fita a gidan nan, school ɗin ki zaki dakatar dashi har sanda yayan ki zai dawo, sabida ya bani amanar ki, Ni kuma bazan bari kina fita kina yawon ta zubar alhanin an bani amanar ki ba, ya rage na ki, ki bi umarni na ko ki saɓa.." sai ya ja numfashi yana cije leɓe tare da mayar da idanun sa kan ta

Tun sanda ya soma magana tuni ta ɗago kanta ta kafa masa rikitattun idanun ta, a take a lokacin suka sake sauya kala suka rikiɗe zuwa jazur, har wani ƙyalli suke yi

Shi kansa Rayyan ya kasa jure kallon da take masa, don bazai iya tantance wani irin kallo bane, amma kuma sosai kallon ya shige sa, har tsigan jikin sa tashi yake yi.

     Ƙunci da baƙin cikin dake nuƙurƙusan RAUDHA shi ya hana ta yin magana, ga dai shi bakin ta na motsi but ta kasa furta komi, sai kawai gani yayi ta miƙe zumbur ta nufo wajen sa, a tsakiyar parlour'n ta tsaya ta hau cire kayan ta...😳

Zaro idanu Rayyan yayi da tsananin mamakin ta, da sauri ya runtse idanuwan sa ganin ta saki rigan yayi ƙasa, daga ita sai gajeren wando fari ƙal da bra ɗin sa

+

Shaf ta manta da cewa shi soja ne sai yanzu da ta kalli kayan jikin ta taga irin nasu ne, saboda tsantsan tsanar da take masa hakan yasa baza ta iya juran ganin rigan a jikin ta ba, wannan dalilin ne yasa ta soma kwaɓe wa.

      Ɗaukan rigan tayi ta wurgo masa ajiki, ta ruga aguje tayi hanyan kichen

Rigan ya cire daga fuskar sa yana bin wajen da take da kallo, but a mamakin sa babu ita a wajen, ajiyan zuciya ya sauke da ƙarfi yana damƙe rigan a hannun sa, sai kuma ya saki a ƙasa yana miƙe wa tsaye, yayi hanyan dainning, dama abinda ya zaunar dashi kenan yaci abinci ya bar gidan, sai gashi ya haɗu da abun mamaki wajen birkitacciyar ƴar ƙwayan yarinyan nan, har yanzu mamakin meyasaka ta cire rigan yake yi

Tabbas yanzu ya tabbatar ita ɗin ba ƙaramar sheɗaniyar ƴar duniya ba ce, tunda har ta iya cire riga a gaban sa batare da ta ji kunyan sa ba.

      Yana jan kujeran ya zauna ya hange ta ta fito daga kichen, riƙe da kalanzir cikin galan da ashana a hannun ta, sakin baki yayi kawai yana kallon ta

Rigan tanufa ta ɗauka tayi waje da gudu

Shima sai ya tashi da sauri yabi bayan ta, time ɗin da ya fita tuni ta diddila wa rigan kalanzir ɗin, ta saka ashana ta ƙyasta wa rigan nan da nan ya soma ci

Tsayawa yayi kawai yana kallon ta, Allah ya sa a farandan gidan ta tsaya, kuma daga nan masu aikin gidan ko sun fito baza su iya hango ta ba, in ba sun yo wajajen ba

Hannayen sa ya saka a aljihu kawai yana bin ta da kallo.

        Sai da rigan ta kusa ƙonewa kafin ta ɗago rikitattun idanun ta ta sauke akansa, cikin dashashshiyar muryan ta da tasake shigewa sosai tasoma magana

"Yanda na ƙona rigan nan haka kaima zan yi maka sabida tsananin tsanar da nayi maka, babu wanda ya taɓa shiga rayuwata ya ƙuntata min sai kai, bazan taɓa yafe maka ba sai na kashe ka idan baka fitar min cikin rayuwa ba, na tsane ka kana ji ko, na matuƙar tsanar ka fiye da mutuwa ta, i hate youuuuuuuu! Ta ƙarishe da ƙarfi tana rugawa cikin gidan tare da fashe wa da kuka

Ko motsi ya kasa yi a wajen, idanun sa kan rigan da ya ƙurmushe ƙurmus, sosai yake cikin ɓacin rai da kalaman ta

"Wai yarinyan nan me take ji dashi ne da har take iya kallon idanun sa tana gaya masa magana irin hakan? Ko dan ya ƙyale ta? Tabbas yau zai koya mata hankali, zai saita ta ya dawo da ita hayyacin ta, idan ma ƙwayan ta ke faɗa mata ƙarya zata san wanene aihinin Captain Rayyan".

Takawa yayi yawuce wajen motan sa, ya shiga yaja yabar gidan.

      A cikin kujera ta shige tasoma rera kuka, sosai take yin kukan har muryan ta ba ya iya fita, sai da kanta yasoma sara mata tana ganin dishi-dishi kafin ta saurara wa kanta, miƙe wa tayi ninyan yi, sai ta hangi HangBag ɗin ta kan kujera, wanda bata san ma ya akayi yazo wajen ta, don jiya bata san inda ta wulla sa ba tun da Rayyan ya ɗauko ta

Jakan ta ɗauka ta zazzage, wayan ta kaɗai ta faɗo, babu komi aciki duk da kuwa ta zuba ƙwayoyi a jakan, but kuma babu a ciki, bata damu da tabi ba'asi ba tasoma neman layin yayan ta, sai dai switch off, ƙin dena Kira tayi har sai da ta gaji don kanta kafin ta saki wayan tana sake fashe wa da kuka

Sai ta miƙe ta saka hannu tasoma share hawayen ta, har da saka bayan hannun ta, gaba ɗaya idanuwan ta da fuskarta sun haɗe sun yi jazur, musamman saman hancin ta, abun ku ga farar mace kamar zabiya

Sai da ta ɗauki wayan ta kafin tanufi

Sama da gudu tashige ɗakin ta, Direct toilet ta faɗa ta sake sheƙa wankan ta, ta fito tayi shirin ta cikin ƙananan kaya, wando ta saka ɗan guntu iya cinyan ta Brown colour, sai ta saka farar riga me shara-shara da zanen layi-layi a jiki, ko cibiyan ta be kai ba, ta ɗaure gashinta a tsakiyar kai da Ribom baƙi, sannan ta zira Hill shoes black

Inda take ajiye kayan zaƙin ta tanufa, ta ciri Chwingum ta ɓare tare da jefa wa a bakin ta, feshe jikin ta tayi da turaruka ko ta ina, sannan ta ɗau HangBag ɗin ta ta fito, yanda take takawan ne tamkar ba ita ba, gaba ɗaya ta saki jikin ta ta koma normal sai taunan Chwingum ɗin ta take yi

So take yi ta nuna wa Rayyan be isa da ita ba, shiyasa ta yanke shawaran barin gidan, kuma baza ta dawo ba sai sanda taga dama.

      Waje ta nufa tashige motan ta taja zuwa bakin Gate, horn ta soma buga ma me gadi, but ko ƙeyan sa bata gani ba, kuma taƙi ta dena sai faman danna horn ɗin take yi tamkar zata ta da gidan

A fusace tafito a cikin motan tanufi bakin Gate ɗin, ganin ƙofan ɗakin me gadin a rufe yake sai taja tsaki, ta nufi Gate ɗin ta saka hannu zata buɗe, sai dai kuma an rigada an garƙame Gate ɗin da kwaɗo, buga ƙofan tayi da hannun ta tajuyo a fusace tana kwaɗa wa me gadin kira, jin shiru kuma tana ɓata wa kanta time sai ta buɗe small Gate zata fice

Sojoji ne su wajen goma a bakin ƙofan taci karo da su, sai taja da baya tana cire ƙafanta da ta taka ƙofan zata fice, da idanu ta dinga bin su tana sake tamke fuska, don a tunanin ta har da Rayyan a wajen ne, duk da zuciyarta sosai ta cika da tsoro

Su kuma shigowa suka yi ciki ko wannen su da bindiga a hannu

Ɗaya daga cikin su ne yace, "Ma'am ki koma ciki sabida an ce kar mu bari ki fita".

Bata saurare su ba, tayi hanyan fita tana son raɓa su ta fice

Wanda yayi maganar yace, "Ma'am ko ba kya ji ne? Ki koma ciki tun kafin mu ɗau mataki akan ki, domin Oga ya ba mu dama idan kika yi mana taurin kai mu harbe ki".

Ko kallo basu ishe ta ba, duk da kuwa ranta idan yayi dubu to ya ɓaci, har fuskarta da ya so ma dawowa normal ya canza kala

Kare ƙofan suka yi, har da rufe wa

Dole taja ta tsaya tana bin su da kallo tamkar idanuwan ta zasu faɗo ƙasa, sai dai kuma yanda zuciyarta gaba ɗaya ta cinkushe ta kasa musu magana, duk da kuwa aranta akwai tsoron su but ta danne

Ganin tana neman musu taurin kai, sai ogan cikin su ya saita bindiga akanta ya harba gefen ta

Ai tuni ta tsure ta kurma mahaukacin ihu, duk da kuwa muryan ta ba ya fita, jikin ta na rawa tayi hanyan gidan a guje

Hakan sai ya ba su dariya, suka hau yi suna bin ta da kallon sha'awa, sai dai gargaɗin Rayyan a gare su yafi komi illa a gare su idan suka saɓa masa

Ogan na su ma har da sake harba bindigan sabida shaƙiyanci

Daga inda take tana jiyo dariyan da suke mata, hakan sai ya sake tunzura ta ta ɓarke da kuka, bata tsayar da gudun nata ba sai da tashige ɗakin ta ta faɗa kan gado ta sake fashe wa da kuka, kuka sosai take yi tana hargitsa gadon tare da banga wa Rayyan zagi ta uwa ta uba, sai kuma ta miƙe zumbur tanufi drowern da take ajiye ƙwayoyin ta ta buɗe, babu komai aciki gaba ɗaya an kwashe. Fridge ta nufa da sauri shima ta buɗe don ta ɗauki wine, amma nan ma babu komi sai drinks da aka zuba mata

Nan ta haukace ta soma ihu tana bige-bige tana kiran sunan Rayyan, tamkar mahaukaciya haka ta koma gaba ɗaya sai da ta hargitsa ɗakin, hannayen ta sai zubar da jini suke yi sabida har Centre table sai da ta fasa, kuka take yi kashirɓan har da majinu, sai da ta gaji don kanta tazube a ƙasa ta kifa Cikin ta da kanta a ƙasa sai ajiyan zuciya take yi, gaba ɗaya ta gama hargitsa gashin kanta.

Bata san iya awannin da ta ɗauka ahaka ba, ko motsin kirki taƙi yi, tunda ta kafa kanta bata sake ko motsawa ba, illa numfashi da take sauke wa akai-akai.

      Zumbur ta tashi sabida jiyo kamar an buɗe Gate, bakin window ta nufa ta yaye labulen, hango Rayyan da tayi cikin mota ya fito sai tayi saurin nufan ƙofa tafice da gudu

Time ɗin da ta kai cikin parlour'n, shima ya sawo kai ciki, da kallo ya bi ta sabida ganin ta a hargitse, ga hannun ta dake bushe da jini

Duk da yayi mata kwarjini tare da cika mata ido but hakan be sa ta dakata daga abinda tayi ninya ba, da gudu ta sheƙa gun sa, babu tsammani yaji ta shaƙo wuyan rigan sa ta kai ma fuskar sa nushi

Ba don Allah ya sa ya kau da fuskar ba, sai ta same shi, da tsantsan mamakin tsageranci irin nata ya cafke hannun ta gam, haka ma ɗaya hannun da ta kawo zata buga masa

A zuciye tasoma zagin sa tana ƙoƙarin ƙwace hannun ta, idanun ta sai zubar da ruwan hawaye suke yi

Ko motsi ya gaza yi illa riƙe tan da yayi gam, danne zuciyar sa kawai yake ƙoƙarin yi sabida yanda yake jin ɓacin rai da irin zagin da take masa, tunda yake a rayuwa babu wanda ya taɓa masa cin mutunci, but wannan tsagerar yarinyan ƴar tatsitsiya tana gaban sa tana zagin sa, sai kawai ya lumshe idanun sa jin hawaye na son zubo masa, yawu kawai yake haɗiye wa sabida tsantsan ɓacin rai da baƙin ciki

Lokaci ɗaya ya buɗe jajayen idanuwan sa ya aza kanta, da hannu ɗaya ya matse hannayen ta gam tamkar zai karya mata su

Azaban da ya ratsa RAUDHA tuni ta dena buzge-buzgen da take yi da zagin na sa, kuka ta fashe dashi tana ƙoƙarin zame wa ƙasa da son ƙwace hannun ta, but ya ƙi saki

Jan ta yayi zuwa cikin parlour'n ya jefar da ita, sai da kanta ya bugu da kujera

Ƙara ta saki tana dafe tsakiyan kanta

Ya daka mata tsawan da sai da ta ɗago rinannun idanuwan ta ta aza kansa

Tamkar zaki me farautar namomin dawa haka ya koma mata, idanunsa gaba ɗaya sun juye, sai jijiyoyin kansa da suka fito raɗo-raɗo, cikin kakkausar amon murya yace, "keee! har kin isa kin kai matsayin da zaki ci kwalan riga na? Kina da hankali kuwa?"

Sai kuma ya matse bakin sa yana nuna ta da yatsa, at the same time ya ɗauke hannun sa tare da dunƙule wa ya kai wa iska naushi

"koda yake ƙwayan ki ne ke faɗa miki ƙarya har kike tunanin yi min rashin kunya ko? Shashashan yarinya ƴar ƙwaya sauran maza ballagaza! Idan kina taƙaman ke ƴar iska ce me bin ko wani banzan na miji, Ni Ni Rayyan Hassan!"

Ya nuna kansa yana sake ware idanuwan sa akanta, cikin fushi da ɗaga murya yace, *"NA FI ƘARFIN KI HAR ABADA,* na wuce da sanin ki, ba na harka da sauran maza, baki da abinda zaki iya burge ni, idan kina so ki haɗa gwanji dani ki je ki soma samun tsarkin Musulunci, sannan ki tsarkake ƙazantacciyar jikin ki sai ki dawo ki sake taɓa ni, jahila mara ilmi mahaukaciya, tirrrr dake!"

Ya tsit ta miyau gefe ya nufi sama da sauri

Cusa kanta tayi tsakiyar cinyoyin ta tana wani irin kuka tamkar ana fid da ranta, kalaman sa kawai suke mata yawo a cikin ƙwaƙwalwa, take ta ƙwalla ƙara ta ɗauki flowern dake saman Centre table ta rotsa shi akan table ɗin, nan da nan suka tarwatse har flowern, zafi da ƙuncin da take ji cikin zuciyarta yasa ta ɗauki kwalban ɗaya ta soma yanka hannun ta don samun rage raɗaɗi, but babu abinda yayi mata illa baƙin ciki da ƙunci dake nuƙurƙusan ta, ji take yi tamkar ta haɗiye zuciya ta mutu, har wani ɗaci-ɗaci take ji a maƙogwaron ta, idanunta gaba ɗaya sun kaɗa sun yi jazur har wani kore-kore suke yi sun daɗa ƙanƙance wa, kuka kawai take yi tana faɗin "ta tsane shi", ko kaɗan ba ta jin zafin yanda take yanka jikin ta kamar yanda take jin raɗaɗi a zuciyar ta, wani irin tsantsan tsanan Rayyan ke ƙara wanzuwa a cikin zuciyarta a ko wani socond, yana bi ta magudanan jinin ta yana aika mata ta jijiyoyin jikin ta

Ko ta ina sai da ta yayyanka hannayen ta, sai zubar da jini suke yi, tamkar mahaukaciya haka ta miƙe tana jefar da glass ɗin tayi upstairs tana layi, ɗakin ta ta shige tanufi bakin gadon ta ɗauki wayan ta, ko kaɗan bata damu da yanda jinin ta ke yawo yana zuba tamkar an kunna famfo ba, burin ta kawai ta dace da kiran yayan ta

Numban sa na ƙasan waje ta lalubo ta kira, but be ɗaga ba har sai da tayi masa two missed call sannan ya ɗaga, jin muryan yayan ta a dodon kunnen ta sai ta saki wani marayan kuka tana kiran sunan sa

Wlh bazan iya fasalta muku tashin hankalin da ya shigi Suhaib ba, gaba ɗaya ya rikice ya kiɗime da jin kukan ƙanwar ta sa, musamman yanda ya fahimci tabbas tana cikin wani mawuyacin hali

Numfashi kawai take ja kafin ta samu jarumtar haɗo kalmomin bakin ta

"Ya..ya, ya.. yA! Na tsane shi na matuƙar tsa..nar sa fiye.. da mutuwa na, yaya bazan taɓa barin.. sa ba, sai na kashe sa wlh.. da hannu na zan kashe sa, me yake taƙama dashi meye yafi Ni dashi? Y..a..ya..ya I want to be a SOJA.. becouse.. becouse..."

Sai ta fashe da wani irin kuka me tsuma rai, cikin rawan baki tace, "zannn nuuna masa be fi.. ƙarfi na.. ba... Dai-dai nake daa..shi, INA SON ZAMA SOJA YAAYA".

Post a Comment for "RAUDHA CHAPTER 6"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...