RAUDHA CHAPTER 2 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RAUDHA CHAPTER 2

RAUDHA CHAPTER 2

- - Post a Comment

 RAUDHA CHAPTER 2_______📖Su Saude dake zaune suna kallo a wayan Larai suka ɗago kai dasauri suna kallon RAUDHA, ko waccen su nan da nan tashiga hankalin ta coz sun san bata shigowa cikin ɗakin su idan har ba wani laifi sukayi mata ba, shanyayyun manyan idanuwan ta tasauke akan su tana bin su da kallo, sai da tagama ƙare musu kallo cike da isa tace+


"Uban me kuke yi da har zan kira ku ku kasa amsa min?"


Zuru-zuru sukayi da ido suna kallon ta, sai Larai ne tayi ƙarfin cewa


"Kiyi haƙuri Hajiya wlh bamu ji bane".


Dogon tsaki taja tace "ki shirya kizo in aike ki supper market".


Idanunta dake kan Saude shiyasa tagane da ita take yi


"To ranki yadaɗe". Cewar Saude tana miƙewa dasauri


Ita kuwa juyawa tayi tafice tanufi ɗakin ta, bata daɗe da zama ba Saude tashigo, kuɗi tamiƙa mata tafaɗa mata abinda zata siyo mata tafice, wayan ta taɗauka takira Ramcy, ringing ɗaya taɗauka


"Ramcy kibar aikin nan kawai".


Cike da mamaki Ramcy tace "meyasa?"


RAUDHA tace "na sauya shawara ne, zan kira ki anjima yanzu zan fita bye".


Ƙitt takashe wayan ta'ajiye, tashi tayi taɗauko Socks baƙi tasaka, dogo ne da yatsaya mata har gwiwa tasanya Hill shoes black me igiya, wayan ta tasake ɗauka takira Mahaifin ta yana ɗauka tace


"Daddy Ina buƙatar kuɗi".


"My dear me zakiyi da kuɗi haka?"


"Dad Kai dai kabani akwai abinda zan yi dashi ne". Tafaɗa a shagwaɓe


"Ok to bari in tura miki".


Tana katse kiran babu daɗewa taji Alarm ya shigo, HangBag ɗin ta taɗauka tafice, dasauri-sauri take taka Steps har tasauka tabar Parlour'n, a compound tatsaya tana gyara ɗan silin gashin ta da yasauko mata wajen ido, jakan ta tabuɗe taciro wani faskeken Eyeglasess baƙi tasaka, ko kaɗan bataji ɗar ɗin fita da kayan jikin ta ba don tarigada tasaba, sai dai ta zuge zeey ɗin Jarket ɗin  ta rufe iya cikin ta dake waje,  mota tashiga tabar gidan.


      Bank 🏦 tafara zuwa taciri kuɗi sannan tanufi police station👮, tana yin parcking tafito takulle motan, gaba ɗaya duk mutanen dake haraban Station ɗin babu wanda idon sa be kai kanta ba kuma duk kallon da ake mata ba wanda yake mata kallon musulma sai dai waɗanda suka san ita ɗin wacece, kallon ta kawai ake yi ita kuwa ko ajikin ta tanufi ciki cike da tafiyan ta me burgewa


Tana shiga duk ma'aikatan dake zaune wajen suka yi mata caa da idanu, daga masu haɗiyan yamu sai masu sakin baki kamar zasu cinye ta, bata kalli kowa ba tanufi Office ɗin DPO kanta tsaye kuma duk acikin su babu wanda yayi yunƙurin yahana ta

Nocking tayi aka bata damar shiga tatura ƙofan tashige, DPO dake duba wasu files a gaban sa yaɗago kai, dasauri kuma yatashi tsaye yana faɗaɗa fuskarsa da fara'a yace


"A ah Ranki yadaɗe kece yau a office ɗin mu? Barka da zuwa zauna mana".

Babu musu tazauna tana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya taɗaura HangBag ɗin ta a jikinta, shima komawa yayi yazauna yana sake mata Barka da zuwa, sannan yaƙara dacewa

"Ranki yadaɗe da kanki yau Alhaji ya aiko?"


Yana nufin mahaifin ta sabida mutumin sa ne kuma shine yasama masa aiki lokacin da yake ganiyan Siyasan shi, shiyasa duk abinda Daddy yanema awajen sa yana masa da gaggawa sabida albarkacin muƙamin da yaɗaura sa akai

Zare Eyeglasess ɗin ta tayi sai ga kyawawan lumsassun idanuwan ta sun bayyana, cikin muryan ta me daɗi ga kowa tace "No DPO wannan aikina ne".

DPO dake haɗiyar yawu kamar wanda zai cinye ta sabida kafe ta da idanu da yayi, yasake washe baki yace "to ranki yadaɗe wani aiki kenan za'a yi miki?"

Murmushi tayi me zautar da mutum kafin tace "Wani yaro nake so ku kama min shi, ina son ku hukunta shi bisa laifin Fyaɗe da yai ninyan min, sannan bana son ku bada belin shi har sai anzo an bani haƙuri".

"Ai baki da damuwa ranki yadaɗe duk abinda kikace shi za'ayi, aina yaron yake?"


Kamar yanda Ramcy tasanar da ita bayani akan sa haka itama tafaɗa masa, sannan taƙara dacewa "wannan maganan Ni da kai ne DPO, ko Daddyna bana son kasanar masa".

Sai kuma tabuɗe Jakan ta taciro maƙudan kuɗi ta'ajiye masa batare da ta furta komi ba, shi kuwa cikin tsananin murna yaɗau kuɗin yana kallo, sai kuma yamaida idanun sa kan ta yana lanɗe baki, Allah ya sani yafi buƙatar ta akan kuɗin nan, duk da yawan kuɗin da ace zata riƙe tabashi kanta da yaji daɗi fiye da bashi kuɗin da tayi, sai dai bazai taɓa iya nuna mata maitan sa ba gudun samun matsala, don yasan aikin sa ma da yake taƙama dashi zai iya rasa shi, yasan cewa rijiya ba wajen wasan makaho bane, yanzu sai yajawo ma kansa gobarar da bazai taɓa iya kashe sa ba

Muryan RAUDHA yakatse masa tunanin sa, yayi firgigit yana kallon ta da har ta rigada ta tashi, shima dasauri yatashi yana cewa

"Ai ranki yadaɗe yanzu ma zamuje har dani don mu soma miki aikin ki da wuri".


Murmushi tayi tace "nima ina son in bi ku".


"Ok babu matsala muje". Cewar DPO yana yin gaba dasauri kamar ana hankaɗa shi yabuɗe mata ƙofa

Sai da tafice sannan yabi bayan ta, tare da wasu ma'aikatan su biyar suka tafi, motan su ne agaba nata abaya suka nufi anguwan su Jawad

Suna zuwa da tambaya aka nuna musu shagon sa, huɗu daga cikin ƴan sandan ne suka shiga shagon, babu zato babu tsammani Jawad dake aikin zanen sa yaji anyi ram dashi, dasauri yajuyo yana kallon kwalawan dake tsaye kan sa biyu sun riƙe sa, miƙewa yayi jiki na rawa yasoma tambayan su abinda yayi


Ɗaya daga ciki yabuge masa baki yace "idan mukaje zakaji wuce muje".


Turjiya yasoma nuna musu suka hangaɗa shi sukayo waje dashi, lokacin ne Deeni abokin sa yaƙariso wajen don har an kai masa rahoton ga ƴan sanda can a shagon Jawad, dayake shima Shagon sa yana layin anguwan ne, ganin za'ayi wajen mota dashi Deeni yayi saurin zuwa yana cewa

"Dan Allah ranku yadaɗe me yayi zaku tafi dashi?"

Wani kallo ɗan sandan cikin su yayi masa yace "idan kuka biyo mu Office zakuji".

Jama'a sun taru ana ta tambayan ba'asi amma firr ƴan sandan nan sun ƙi magana sai son tura Jawad suke acikin mota, shi kuma ya dage akan lallai bazai shiga ba tunda yasan be yi komi ba duk da akwai tsoro a tattare dashi

Lokacin DPO yafito a mota yana cewa "wai ya gagare ku ne?"

RAUDHA dake cikin mota zaune tana kallon duk abinda ake yi sai faman cije laɓɓa take yi tana sakin murmushi, sai da taga an saka sa cikin mota sannan tafito tana gyara zaman Eyeglasess ɗin ta, nufan wajen tayi cikin tafiyan ta me ɗaukan hankali, nan kuwa sauran mutane suka maida kallon su gare ta har sun manta me ma ake yi

Deeni tunda yahango ta yasha jinin jikin sa, dama ya rina aransa dole ne abokin sa yafuskanci hukunci duk ranan da tajuyo kansa, shi yarigada yasanta yasan waye ita sabida ya daɗe yana zuwa Club ɗin


Tana zuwa wajen ƴan sandan suka matsa mata hanya ta'isa jikin motan tana kallon Jawad da shima yake kallon ta, sai dai nashi kallon na rashin sani ne don ba wani sanin ta yayi ba, bare cikin club ɗin akwai duhu sosai, cire Eyeglasess ɗin ta tayi tana sake ƙare masa kallo tana murmusawa, batace komi ba  kuma takalli DPO tace

"Daga nan zan wuce gida DPO, ku gana masa azaba sosai bana son ko kaɗan ku raga masa".

Daga haka tajuya batare da tasake bi takan su ba tanufi motan ta tashige taja tabar musu ƙura nan, ƴan sandan har suka shige su ma suka ja tasu motan Jawad kallon motan ta yake yi, har alokacin ƙwaƙwalwan sa be kawo masa inda yasanta ba duk da kuwa yaso yagane muryan, shi dai mamaki da yarufe sa ne yasa yamanta ahalin da yake ciki har suka tafi dashi

Jama'an wajen kuwa sai mayar da zance suke yi sun kasa sanin meke faruwa, wasu kuwa har sun rigada sun bata laifi sai zagin ta suke yi suna cewa "dama haka ƴaƴan masu kuɗi suke, don sunga sunfi ƙarfin mutum sai su nemi su takasa koda laifi kayi musu a rashin sani" wasu kuma wajen Deeni suka nufa suna tambayan ba'asi, amma shi hankalin sa duk atashe yake be saurare su ba yayi hanyan gidan su Jawad ɗin, wasu daga ciki suka rufa masa baya don jin ƙwaƙwaf.

      Har ta kai anguwan su sai kuma tajuya kan Motan tanufi gidan su Ramcy, a bakin ƙofar gidan tayi parcking tafito tarufe motan tashige cikin gidan kanta tsaye

Gidan madaidaici ne me ɗakuna biyar dasu Toilet da kichen, gidan yana da kyau irin dai na masu rufin asiri, Mahaifiyar Ramcy ta daɗe da rasuwa sai Amaryan Baban su take riƙe ta, su huɗu ne wajen mahaifiyar tasu, biyu maza sai ɗaya mace da tayi aure sannan ita Auta, Mahaifin su Dattijo ne sosai kuma itama Amaryan da ya'auro dattijuwa ne don bata taɓa haihuwa ba

Kasancewar Baban su na tafiye tafiye yana sana'ar Gwari wannan yasaka Ramcy take yin duk abinda taga dama, don bata jin tsoron yayyin nata bare Amaryan Baban su


RAUDHA na shiga tanufi ɗakin Ramcy ɗin tabuɗe labule tashige, ɗakin yayi kyau sosai dai-dai na budurwa me ji da kanta, kuma duk RAUDHA ce tasiyan mata duk abinda ke cikin ɗakin, har ta dana Amaryan Baban nasu sai da tasauya mata kayan ɗaki, shiyasa babu wanda be san ta ba agidan, kuma hakan yasaka wani lokacin basa matsa ma Ramcy idan sukaga ta fita don sun san can wajen RAUDHA take zuwa

Babu kowa cikin ɗakin sai tatsaya tana ƙare wa ɗakin kallo na tsawon daƙiƙu sannan tanufi kan katifa tafaɗa har da takalmin ta da bata cire ba, numfashi taja me ƙarfi tana lumshe kyawawan idanuwan ta.

Ramcy ce tashigo cikin ɗakin, ganin RAUDHA abun ya bata mamaki, dasauri taƙarisa kusa da ita cike da farin ciki tace

"Besty yaushe kikazo?"

Lokacin ne RAUDHA tabuɗe shanyayyun idanuwan ta tasauke kan Ramcy ɗin, memakon ta'amsa mata tambayan ta sai cewa tayi "ina kika shiga nashigo bakya nan?"

Ramcy tace "na shiga bayi ne wlh".

"Ok". Tafaɗa tana ɗauke kanta daga kallon Ramcy ɗin

"Besty me zakici in kawo miki?"

"Babu". Tafaɗa ataƙaice tana tashi zaune

Ramcy tace "yanzu dama nake tunanin kiran ki ashe zakizo, zan kira ki in sanar miki bikin da nace miki zani a Kaduna ya matso".

Kallon ta RAUDHA tayi kamar baza tace komi ba sai kuma tace "yaushe ne kenan?"

"Wannan satin amma sai ana gobe zan tafi".

Gyaɗa kai kawai RAUDHA tayi tana ɗaukan wayan ta tana latsawa, hira Ramcy tafara mata tana jinta bata amsa ba har sanda tagama abinda take yi a wayan taɗago kai tana kallon ta, cikin yatsina tace "zan biki mu tafi tare".

"Dagaske kike yi don Allah?" Ramcy tafaɗa cike da zumuɗi".

Murmushi RAUDHA tayi tana gyaɗa mata kai

"Wow besty naji daɗi wlh, dama Ni kaɗai ne zani don Aunty Nafeesa tace min bata jindaɗi baza ta je ba tunda tare zamuje da ita".

"Me yasame ta?" RAUDHA tafaɗa cike da kulawa tana kallon ta

"Wlh tunda tasami cikin nan abun dai babu daɗi, gashi har ya shiga wata shida bata dena ciwo ba".

"Ok Muje ki rakani in gaishe ta". RAUDHA tafaɗa tana miƙewa tsaye

Tashi itama Ramcy tayi taɗau gyalen ta suka fito waje


Da Amaryan Baban Ramcy sukaci karo tana fitowa daga ɗaki

"A'a babbar baƙuwa mukayi ne?" Cewar Amaryan Baba tana faɗaɗa fuskarta da fara'a

Murmushi RAUDHA tayi cike da rashin tarbiyyar da be ishe ta ba tace "Yakike?"

Murmushi Amarya tayi tace "lafiya lau RAUDHA, ya gidan naku?".

"Lafiya". Ta'amsa ataƙaice

Ramcy tace "Zamuje gidan Aunty Nafeesa ne?"

"To adawo lafiya".

Daga haka suka fice tabi bayan su da kallo tana murmushi, aranta tana tunanin yanda yarinyan take shigan banza babu me kwaɓa mata, tana da kirki sai dai babu tarbiyya ko a ido aka ganta an san haka, wuce wa kichen tayi aranta tana nema musu shiriya gaba ɗayan su

Duk da gidan babu nisa amma a mota suka je, bayan sun kai lungun gidan su Aunty Nafeesa inda mota bata shiga sai suka fito suka soma takawa a ƙasa, wani babban kwata suka zo tsallaka wa RAUDHA sai toshe hanci take yi tana yatsina fuska, abinda yake sawa bata zuwa anguwan kenan saboda wannan mummunan kwatan dake bata tsoro

Daƙyar tatsallaka shima sai da taimakon Ramcy, mutanen dake wajen kuwa sun kafo musu idanu sun saki baki suna kallon abun mamaki

Sun ɗan yi tafiya da suka shiga lungun sannan suka isa gidan Aunty Nafeesa, ita kaɗai ce agidan kuma ba wani babban gida bane, gida ne me ɗakuna biyu da Ban-ɗaki da kichen.Suna shiga ciki Ramcy tarangaɗa sallama

+

Aunty Nafeesa dake kwance saman kujera ta'amsa musu tana tashi zaune daƙyar

Su kuma lokacin ne suka shigo cikin ɗakin

Aunty Nafeesa tana ƙyalla idanu taga RAUDHA dake bayan Ramcy tafaɗaɗa fuskarta da fara'a tana cewa "kai kai kai yau RAUDHA ce a gidana?"

RAUDHA kuwa murmushi tayi tasami kujera taɗan ɗofana akai kamar wacce take jin tsoro

Ramcy itama zama tayi tana cewa "Aunty cewa tayi in kawo ta tagaishe ki".

"Allah Sarki ai kuwa na gode sosai".

Sai lokacin ne RAUDHA tabuɗi baki ahankali da muryan ta adishe tace "ya jiki?"

Cike da fara'a Aunty Nafeesa tace "Alhmadulillah RAUDHA, kina lafiya?"

Gyaɗa kanta tayi tana wasa da igiyoyin wandon ta (bazar)

"Rahma ɗauko mata ruwa mana".

Miƙewa Ramcy tayi tabuɗe ɗan ƙaramin Fridge ɗin dake ɗakin taciro fure water guda biyu taɗaura akan Fridge ɗin, sai da tarufe sannan taje taɗauko plate tajera ruwan takawo gaban RAUDHA ta'ajiye, ita dai kallon ruwan kawai take yi batare da ta motsa ba

"Besty kisha ruwa". Cewar Ramcy tana kallon ta da murmushi

Ɗan kwaɓe fuskarta tayi kawai tana girgiza mata kai alamun baza ta sha ba

Ƴarinyan Aunty Nafeesan ce tashigo ɗakin aguje, sai tatsaya kawai tana kallon su Ramcy, sai kuma tamaida idanun ta kan RAUDHA da itama takafe ta da idanu, ga duk kan alamu yarinyan bata gane ta ba don tasan Ramcy sosai, sai tanufi wajen ta tana ɗaura ƴan ƙananun hannayen ta saman cinyan RAUDHA, dai-dai wajen tsakankanin inda wandon ta da Socks ɗin da tasa basu rufe ba, sai kuma takoma tana wasa da bazar ɗin wandon

Ramcy tace "ke uwar ki tashi awajen nan".

Yarinyan kamar bataji ba sai tasake matsawa sosai wajen RAUDHA tana tattaɓa ta, ita kuma RAUDHA sai janye jikin ta take yi kamar taga abun tsoro, duk da yara suna burge ta amma bata son ko kaɗan su zo kusa da ita sabida suna bata tsoro wani lokacin idan suka cika ƙanƙanta, bare kuma wannan itama ƴar ƙanƙanuwa ce don baza tafi 2yrs ba

Ganin dai baza ta dena taɓa ta ba sai tazare mata manyan idanuwan ta tana hararan ta tare da matse jikin ta waje ɗaya, ko kunyan akwai Maman ta awajen bata ji ba

Aunty Nafeesa kuwa murmushi kawai tayi tamiƙe tana janyo hannun yarinyan tace "zo nan Khadeeja, bakiga baƙuwa bace?"

Ɓata fuska Khadeejan tayi tasoma gwarancin ta, sai kuma taƙwace hannun ta tana ficewa da gudu

Ajiyan zuciya RAUDHA tasaki wanda hakan yasaka duk suka kalle ta, ita kuma bata ma san suna yi ba

"Kin ƙi shan ruwan RAUDHA, gashi kuma babu abinci"

Yaƙe tayi tana sake girgiza kanta, sai kuma tace "a'a anty na ƙoshi ne".

Ramcy tace "Aunty tare da besty zamuje bikin Shatu fa"

"Haba dai don Allah dagaske?"

"Wlh kuwa tace zataje".

Murmushi Aunty Nafeesa tayi tace "Allah Sarki mun gode kuwa, idan kinje sai kigaishe ta dakyau ki faɗama Mama bani da lafiya ne, nima dai zan kira ta awaya in sanar musu".

RAUDHA miƙe wa tayi tana kallon su, hakan yasa itama Ramcy tamiƙe tana cewa

"Aunty mu zamu tafi, zan faɗa mata insha Allah".


Itama tashi tayi daƙyar tana cewa "to muje in taka muku".

RAUDHA da taciro kuɗi cikin jaka tamiƙa wa Aunty Nafeesa tana cewa "gashi anty".

Kallon kuɗin me uban yawa tayi tana cewa "ah RAUDHA har da ɗawainiya?".

Murmushi RAUDHA tayi

Kuɗin ta'amsa tana ta mata godiya cike da farin ciki, fitowa sukayi gaba ɗayan su Aunty Nafeesa sai sake mata godiya take yi aranta tana yaba halin kyauta irin na RAUDHA


Wani matashin saurayi ne yashigo gidan yana taje kansa da kumb, tsayawa yayi akan hanya yana kallon su gaba ɗaya kamar yanda suka tsaya su ma suna kallon sa, sai yarausayar da kai yana sauke idanun sa kan RAUDHA

"Aunty Nafeesa wannan kuma fa? aina kuka samo mana inyamura har cikin gida?"

Sai kawai tasaki baki ita da Ramcy suna kallon sa a yanayin tsoro

Ita kuwa RAUDHA naɗe hannayen ta a ƙirji tayi tana zuba masa lumsassun idanun ta da bata iya buɗe su sosai

Zai sake magana Ramcy tayi saurin katse sa da faɗin "haba don Allah Yaya Abba, tare fa mukazo da ita ina ruwan ka da ita?" Taƙarike maganar ta tana hararan sa

Washe baki yayi yace "eyya ai bansani ba my dear, shiyasa wlh nake ƙara son ki sabida wannan farin da kike min da ido🤒😅, wai yaushe ne zaki bani dama ne nariƙa zuwa gidan ku? kinsan son da nake miki Rahma bazan iya rabuwa dake ba, ki daure kiduba maganata"

Ramcy turo ɗankwali gaba tayi cike da jin haushin sa, tasan halin sa sarai zai iya tsokano RAUDHA yanzu abu yacaɓe musu idan har basu rabu lafiya ba, don haka tace "kabar wannan maganan idan muka sake haɗuwa zamuyi magana yanzu ina da baƙuwa".

Cike da jindaɗi  Abba yamatsa musu a hanya yace "yauwa masoyiya to shikenan sai mun haɗu ɗin, zan Bama Aunty Nafeesa saƙo sai ki amsa a wajen ta".

Yatsina fuska tayi kawai tawuce don tuni RAUDHA tafice abinta tunda yamatsa musu a hanya

Sai da Aunty Nafeesa tabi su har ƙofar gida tasake ɗaga musu hannu kafin tashige gida

Suna zuwa wajen motan suka shige RAUDHA taja suka tafi, a ƙofar gidan su Ramcy tatsaya taɗau jakan ta tabuɗe taciro kuɗi tamiƙa mata

Gashi ki Bama Amarya Ni zan tafi bazan shiga ba, gobe sai kizo ke ki amsa naki sai ki siya duk abinda kike buƙata a bikin, ban da ishashshen kuɗi anan".

Murmushi Ramcy tayi ta'amsa tace "thanks Babe Allah yabar mana ke".

RAUDHA riƙe sitiyarin motan tayi tana kaɗa yatsunta akai batare da tace uffan ba, ita kuma Ramcy ganin haka yasa tabuɗe motan tayi mata sallama tafice sannan taja motar tatafi.

Itama Ramcy halayyan su ɗaya da RAUDHA na rashin kula maza ko kaɗan babu ruwan su da shiga shirgin namiji, wannan dalilin ne yasaka RAUDHA tasake yarda da Ramcy tazama ƙawarta tunda halin su ɗaya, kuma shiyasa take mata duk wani abu ba sai ta buƙata wajen samari ba, duk da iya ƙoƙari dai mahaifin ta yana mata duk abinda tatambaye shi in dai yana da halin yi zai yi mata.


Cikin ƙanƙanin lokaci RAUDHA ta'isa gida, tana yin parcking tafito tarufe ƙofan tanufi cikin gidan, Direct ɗakinta tanufa, tana shiga taci karo da Babban baƙin leda ajiye saman Centre table dake kusa da kujera, siyayyar da Saude tayi mata ne

Kan gado tafaɗa tana sauke ajiyan zuciya, gaba ɗaya duk ta tara ma kanta gajiya a ɗan wannan fitan da tayi, sai faman yamutsa fuska take yi duk tana jinta babu daɗi sakamakon mummunan ƙaton kwatan nan na anguwan su Aunty Nafeesa da tagani, miƙe wa tayi a yanayin gajiya tafara cire kayanta tashige Toilet, wanka tayi sosai wanda yaɗauke ta tsawon lokaci kafin tafito, shiryawa tayi cikin Shuɗin Vest da baƙin Leggings takoma Kan kujera tazauna, buɗe ledan tayi tana duba duk abinda ke ciki, kayan zaƙi ne kala da iri su Chaculates, Biscuits, sweets da sauran su, ɗaukan Sweet tayi tabuɗe tasoma sha tatashi tanufi wajen gadonta taciro wayan ta cikin jaka, komawa kan kujeran tayi tasoma latsa wayan takira Daddyn ta, yana peacking tace

"Daddy Good Evening".

"My daughter kina lafiya?"

"Lafiya Daddy ya aikin ka?" Tace hakan tana lanɗe baki

"Me kike ci haka ki tsanmin my dear?" Daddy yafaɗa cike da ƙaunar yarinyan tasa

RAUDHA dariya tayi har fararen haƙoran ta suna bayyana tace "Daddy sweet ne".

"Oh Daughter ba na hanaki Shan kayan zaƙi ba?"

Cikin shagwaɓa tace "Daddy ai bana sha, wannan yanzu ne nasiya nasha".

"Ok to ki kula bana so, kinsan nafison lafiyan ki".

RAUDHA tace "ok.. Daddy zan bi Ramcy Kaduna ana bikin Cousin ɗin ta".

"Kaduna kuma Daughter?"

"Eh Daddy". Tafaɗa tana marairaice murya

Daddy yace "ok to shikenan but Sweetheart ki kula da kanki uhmm?"

"To Daddy Kai fa yaushe zaka dawo?"

"Zuwa nan da One Month insha Allahu ina tare dake my sweetheart".

Kuka tasaki cikin taɓara, nan da nan hankalin Daddy yatashi yasoma tambayan ta

"My daughter lafiya menene faɗa min mana kiyi shiru kinji?"

Cikin kukan take cewa "Daddy har sai One Month zaka dawo? Gaskiya Ni bazan yarda ba sai na biyo ka".

Cikin rarrashi Daddy yace "sorry My Baby umm? Kinga inada aiki sosai ne kuma zan wuce Chaina wani Business Ni da abokan aikina, zan yi two weeks acan kinga zan iya kai wata ɗaya kafin in dawo".

Tsalle tabuga akan kujeran tana cewa "Daddy Chaina?"

"Yes my dear".

Cike da tsananin murna tace "Daddy please kaje dani ina son zuwa".

Murmushi yayi don yasan babu ƙasar da tafi so sama da Chaina, Allah ya ɗaura mata son ƙasar kamar ranta, tana son duk wani abu da yadanganci can ɗin kuma sau ɗaya tataɓa zuwa, sai da tayi wata ɗaya acan ita da Daddyn ta har yaren sai da tasoma koya a lokacin, daga wancan zuwan bata sake komawa ba

"Kar ki damu Babyna kibari idan kin soma zuwa school kuna samun hutu acan zakiyi Holiday ɗin ki".

"Yeeeee Daddy I Love you so much".

Tabuga masa Kiss 😘 ta wayan cike da tsananin murna

Dariya Daddy yayi yace "I love you too my dear Daughter, ki huta kinji sai anjima zamuyi waya".

"To Daddy Byeee".

Daga nan katse wayan tayi tana ajiyewa cike da farin ciki.


.


🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐


     Yau kwana uku kenan da kama Jawad, idan kuka ganshi baza ku iya shaida shi ba sabida dukan da yake sha duk sun sauya masa kamanni, kuma an ƙi barin kowa yaganshi

A ranan na huɗun ne daƙyar DPO yayarda yagansu, Mahaifiyar Jawad ɗin ne tare da Deeni suka zo, duk iya magiyan da sukai masa sam ya hanasu ganin Jawad kuma yaƙi bada belin sa, daga ƙarshe sai ce musu yayi su je can su nemi RAUDHA su bata haƙuri sannan idan ta yafe sai asake shi

Babu yanda suka iya suka fito suka nufi gidan su RAUDHA, babban katafaren gidan mahaifin ta sukaje don nan Deeni yasani, sunyi bugun duniya amma an ƙi buɗe musu ƙofa, sun fi awa ɗaya a wajen ko zasuga wani yafito amma babu kowa dole suka tafi gida da niyyar gobe su bugo sammako su dawo.Ƙarfe 11:30am. Suka bugo sammakon komawa ƙofar gidan, yau ma sunyi bugun duniya amma shiru anƙi buɗe musu ƙofa, wasa-wasa sai da suka share fiye da awanni biyu a wajen suna jiran tsammanin marabbuka

+

Can daga ƙarshe da sukayi ta bugun ƙofan sai gashi an buɗo ƙaramin Door ɗin wani shirgegen mutum ya fito fuska a ɗaure, Me gadi ne kuma tun sanda suka soma buga ƙofan duk yana ji amma yaƙi fitowa a tunanin sa masu maula ne tunda sun saba zuwa, koron duniya idan yayi musu sai gobe ma sun sake dawowa kasancewar Alh. Mustapha mutum ne me kyauta sosai, abun hannun sa baya rufe masa idanu kuma a wajen shi RAUDHA takoya, don tacire maƙudan kuɗi ta kyautar hakan ba komi bane

"Wai uwar me za'ayi muku kuke ta bugun ƙofa? An ce muku Alhajin baya nan amma tunda ku mahaukata ne baza ku dena zuwa ba". Me gadi yafaɗa hakan yana bin su da uwar harara kamar yamaƙure su yake ji sabida tsaban takaici

"Bawan Allah ba abinda kake tunani bane yakawo mu, mun zo ganin Hajiya ne". Cewar Mahaifiyar Jawad cike da muryan tausayi

Me gadi sake bin su da kallon ƙasƙanci yake yi kamar ma be ji me suka ce ba yace "Hajiya..? Kuke neman Hajiya wata Hajiyar kenan?"

Tace "Yarinyan Alhaji".

Dogon tsaki yaja don takaici be tsaya sake jin me zasu ce ba bare yabasu amsa yajuya da ninyan komawa

Deeni yayi saurin matsawa kusa dashi yace "don Allah kataimaka mana kayi mana magana da ita, itace tace har sai munzo mun bata haƙuri kafin tasaka asaki Abokina da ƴan sanda suka kama".

Sai alokacin me gadi yaɗan dakata daga rufe ƙofan da yasoma yi, fuska babu walwala yace "to babu ita anan, ku neme ta acan gidan ta".

Sai da suka sake roƙon sa gaba ɗayan su don yafaɗa musu inda gidan ta yake, daƙyar yasanar dasu shima ɗin sai da yagama musu wulaƙanci da faɗa musu baƙaƙen maganganu

Daga haka dai basu iya cewa komi ba suka juya suka tafi, Napep suka hau yakai su har Zaria Locost inda gidan RAUDHA yake

Bayan sun sauka suka nufi bakin Gate ɗin gidan suka ƙwanƙwasa, babu jimawa Gate Man yabuɗe musu

"Bayin Allah lafiya?' cewar Gate man yana bin su da kallo

Deeni ne yayi masa bayanin RAUDHA suka zo nema, don haka yace "su jira sa anan yaje ya'isar mata da saƙon zuwan su"

Yanda yafaɗa musu haka sukayi suka jingina a garun gidan suna jiran dawowarsa

Shi kuma yanufi cikin gidan yayi Nocking a bakin ƙofan parlour'n

RAUDHA na kwance cikin one Sitter, sai lilo take yi da ƙafafuwan ta da basu samu zama kan kujeran ba, wayan ta take latsawa kuma tana bin music ɗin da yakaraɗe parlour'n da ƙara wanda tasaka shi a t.v


Har Larai dake Moping wajen Fridge sai da tajuyo Nocking ɗin ƙofa amma RAUDHA bataji ba, hakan yasa ta'ajiye sandan Moping ɗin tanufi ƙofan tabuɗe

Ganin Me gadi yasaka ta faɗaɗa fara'arta tana faɗin "Baba Ashe Kai ne?"

"Eh wlh tun ɗazu ina ta buga ƙofa shiru, dama Hajiya ce tayi baƙi awaje nazo in sanar mata".

"To Baba bari in faɗa mata". Larai tafaɗa maganar tana juyawa ciki dasauri

Gaban RAUDHA taje tarisina tasanar mata saƙon me gadi

Yamutsa fuska tayi tana kallon ta kamar baza tayi magana ba, can kuma tace "aje a tambayi su waye?"

"To ranki yadaɗe". Larai tafaɗa tana miƙewa tsaye takoma tasanar da Me gadi

Sai da yasake komawa yatambaye su kafin yadawo yafaɗa mata

Larai takoma wajen RAUDHA tace "Hajiya wai Mahaifiyar Jawad ne".

Shiru RAUDHA tayi tana tunanin me irin sunan, sake maimaita sunan tayi cikin ranta amma takasa tuno inda tasan me sunan, kuma bata tunanin tasan me sunan don haka takalli Larai tana jan gajeren tsaki tace

"Ke koma kice idan baza suyi bayani yanda zan gane ba su koma inda suka fito".

Babu musu kuwa Larai tasake komawa tashaida wa me gadi, shima yasake komawa yafaɗa musu yanda tace

Deeni ne yayi musu bayani yanda zata fahimta sannan akazo aka sanar mata

Umarni taba da a shigo dasu.

Lokacin da suka shigo cikin parlour'n sanyi da ƙamshin daɗi ne kawai ke ratsa ƙofofin hancin su, haka suka koma ƴan ƙauye suna kallon haɗaɗɗen tsararren parlour'n da aka kashe masa maƙudan kuɗi kamar baza'a mutu ba

"Gaskiya kuɗi na inda suke waii". Cewar Deeni da yayi maganar a maƙoshi yana sake ƙare ma parlour'n kallo alokacin da suka gurfana gaban RAUDHA

Bata yi musu magana ba don kallo ɗaya tayi musu tunda suka shigo

Mahaifiyar Jawad ɗin ne cikin girmamawa tace "dama munzo ne maganar yarona da kika sa aka kama, kuma ance sai munzo mun baki haƙuri kafin asake sa, don Allah kiyi haƙuri da duk abinda yafaru munsan yayi laifi hakan bazai sake faruwa ba, ki taimaka ki saka baki a sakar min ɗa shi kaɗai Allah yabani". Taƙarike maganar nata tana sharan hawaye da gefen Hijabin ta

RAUDHA kuwa sai faman yamutsa fuska take yi maganar matan duk ya cika mata kunne, sai da tadire aya kafin taɗago lumsassun idanuwanta taƙare musu kallo daga matar har Deeni dashi yakasa furta komi sai kallon RAUDHA yake yi, a ransa yana tunanin rashin mutunci da rashin imani na masu kuɗi

"zan saka a sakar miki yaro amma ki ja masa kunne, duk ranan da yasake muka sake haɗa hanya dashi wlh billahi sai na wulaƙanta rayuwansa, sai nayi masa abinda har ke uwarsa sai kinyi dana sanin zuwan ki duniya". RAUDHA tafaɗa maganar cike da wani irin fushi da rashin tarbiyya

Sosai ranta yasake ɓaci akan abinda yayi mata kamar yanzu ne abun yafaru, duk idan tatuna cewa shi kaɗai ne mutumin da yataɓa ɗaukan hannu yasaka ajikin ta da sunan duka sai ranta yayi mata ɗaci tare da tsananin tsanar sa me girma, har tana jin kamar hukuncin da taɗauka akan sa yayi kaɗan akan abinda yayi mata

Su kuwa tsananin mamakin maganar ta ne yake ɗawainiya dasu, sai dai sun kasa furta komi sai sake bata haƙuri da Maman Jawad tasake yi

Hannu kawai tanuna musu alamun su bar mata gida, haka suka tashi suka fice suna me sake mamakin yarinyan da babu ko ɗigon tarbiyya atare da ita

Larai dake tsaye tana ganin abinda ke faruwa taɓe baki kawai tayi taci gaba da aikin ta, aranta tana mamakin abinda waɗannan mutanen sukayi da har suka fusata Hajiyar tasu haka don tasan ba abu bane ƙanƙani

Ƙaran gudun RAUDHAN ne yasa tasake ɗaga kanta tana bin RAUDHA da kallo da har ta haye sama, gashi dama takalmi ne me tsini a ƙafafun ta da tafita dashi bata cire ba kasancewar a parlour tayaɗa zango dawowarta inda taje

Jinjina kanta Larai tayi tana al'ajabin wannan kasada na RAUDHA, ko tsoron tagurɗe tafaɗo bata yi

Ita kuwa tana shiga ɗakin Fridge tanufa tasaka keey tabuɗe taciro Wine 🍷 takoma Kan kujera tazube tana sha, yanda fuskarta yayi jazur zaka gane ba cikin Mood ɗinta take ba, sai faman kurɓan wine ɗin take yi babu ko sassautawa

Ringing ɗin wayan ta yadawo da ita cikin hayyacin ta, taɗau wayan taduba screan ɗin, DPO ne yakira ta sai tayi peacking batare da tajira yayi magana ba cikin muryan maye tace

"D..P..O kasakeee shiii kawai".

Tsinke wayan tayi batare da taji me zai faɗa ba, ta'ajiye taci gaba da kwankwaɗan Wine ɗin ta, sai da tasha tayi tatul sannan tahaƙura, daga nan barci ne yaɗauke ta a zaune akan kujeran kan ta na jingine jikin sofan.


       🌐🌐🌐

     Sai bayan magriba tafarka, idanunta tasoma buɗe wa tana rufewa, daƙyar ta'iya buɗe su gaba ɗaya tana faman yamutsa fuska, hannunta ɗaya taɗago taɗaura kan wuyan ta da yasanƙare sakamakon yanda takwanta ɗin, sake yamutsa fuskarta tayi jin azaban zafi ya ziyarce ta kasancewar wuyan yayi tsami sosai, daƙyar ta'iya ɗago kanta tana faman runtse idanu, a wannan karon duka hannunta taɗaura saman wuyan ta tana faman matsawa tare da juya kanta, ta jima ahaka kafin tasoma jin dai-dai

Wayan ta da tasoma tsiwa tana neman agaji takai dubanta ga wayan, sai kuma tasauke hannayen nata tana sake jujjuya kanta kafin taɗau wayan tana kallon screan ɗin

MY BLOOD yafito ɓaro-ɓaro a gaban wayan, peacking tayi takara a kunne cike da muryan maye da yahaɗe dana barci tace

"Ya..yah.."

Suhaib da yaji muryan ƙanwar tasa ta ratsa masa kunne sai yalumshe idanun sa cike da ƙaunar ta yace. "my Sweetheart Ina kika shiga ne na kira wayan ki but baki ɗauka ba?"

"Uhmm.. uhm ina.. barci ne Ya..yaah.."

Shiru yayi Suhaib yana sauraron yanda take masa magana, babu shakka yasan da cewa har yanzu ƙanwar sa bata bar halin ta na shaye-shaye ba, a duniya babu abinda yatsana sama da wannan ɗibi'an da ƙanwar tasa ta koya, but ƙaunar da yake mata yafi rinjayar komi hakan yasaka baya iya ɗaukan mataki wajen ganin ya hanata banzan ɗabi'an nan..

"Ya..ya kana jiiinaaa kuwa..?" Takatse masa ɗan guntun tunanin sa

Ajiyan zuciya yasauke cikin taushin murya yace "Baby Wai yaushe ne zaki dena shaye-shayen nan da kike yi? Babu shakka naji ajikina sai da kika sha kafin kiyi barci, ina ƙaunar ki My sister bazan taɓa iya juran abinda zai same ki ba nan gaba, kinsan da cewa duk wanda yake shaye-shaye ƙarshen sa baya kyau? Bana son kina cutar da kanki ƙanwata don Allah ki dena kinji?"

Shiru kawai tayi tana sauraron sa ba wai don taji maganar nasa ba, sai tamatse baki kawai tana cije leɓen ta batare da ta kula sa ba

Shi kuma shirun ta ya san cewa baza ta amsa bane, kuma yasan idan yaci gaba da mata magana zata iya yin fushi yanzu takashe wayan wanda baya fatan hakan tafaru

Murmushi kawai yayi yace "Baby ki kula da kanki kinji I Love You".

Kamar baza ta amsa mishi ba sai kuma tace "me too".

Still Murmushi yayi kawai yatsinke wayan yana sauke ajiyan zuciya, fatan sa ɗaya kawai kar ƙanwar tasa tayi fushi dashi don yasan fushin ta babu kyau, tana da matuƙar kafiya da taurin kan tsiya, wanda hakan yake sa duk abinda tabar shi ta barshi kenan har abada, idan kuwa tayi fushi dasu tana ɗaukan lokaci kafin takula su, sai tayanke duk wani alaƙa dasu gaba ɗaya.*WASHE GARI*+


Ranan da zasu tafi Kaduna bikin ƴar ƙanwar Maman Ramcy

12:30pm. Me keke napep yasauke Ramcy a ƙofar gidan RAUDHA


Tayi shiga cikin wata koriyar atamfa me ratsin ruwan hanta ajiki, ɗinkin babu ƙarya yayi kyau sai dai anci ma atamfan mutunci sosai, riga da skert ne akayi mata kuma yayi mata kyau duk da kasancewar ta baƙa amma kyakykyawa ce Ramcy sosai, ta yafa gyale a kafaɗun ta sai jakan da tazuba kayan ta ciki

A haka tashige gidan tana taku ɗai-ɗai

Koda tashiga cikin parlour'n da Saude suka ci karo ta fito daga kichen, gaisawa sukayi tatambaye ta RAUDHA

Saude tafaɗa mata tana ɗakin ta har yanzu bata sauko ba

Bata sake cewa komi ba tanufi upstairs ɗin, tana zuwa tatura ƙofan tashiga tana kallon RAUDHA dake kwance tayi baja-baja saman tafkeken gadon ta dake iya cin mutum biyar, sai sharan barcin ta take yi hankali kwance bata da alaman farkawa

Shigowa ciki Ramcy tayi tanufi bakin gadon tazauna, shiru tayi naɗan wani lokaci tana tunanin yanda za'a yi tatashe ta, daga ƙarshe dai tayanke shawara takai hannun ta tana taɓa ta tare da kiran sunan ta a hankali

Ta jima tana faman tashin ta kafin tabuɗe shanyayyun kumburarrun idanuwan ta da suka sauya kala sosai sabida tsaban barci, sake lumshe idanun tayi tana sake buɗe su akan Ramcy dake faman kallon ta

Cikin tausasa murya tace "Besty har yanzu baki tashi ba? gashi har 12:00pm. Ɗin ta wuce".

Shiru RAUDHA tayi bata iya ce mata komi ba, sai faman kokuwa take yi da lumsassun idanun ta da suka ƙi buɗe wa

Sai da tayi wajen mintuna 5 kafin tasoma yunƙurin tashi zaune tana faman riƙe kanta

Ramcy kuma tashi tayi takoma kan kujera tana faman kallon ta sai dai bata furta komi ba, don tasan ko ta sake magana ba kula ta zatayi ba

Sai da tagama nawan ta kafin tatashi tasoma cire kayan ta batare da taji kunyan Ramcy ɗin ba tunda ta saba

Ita ma kuma Ramcy ko ajikin ta sai kawar da kai tayi tana latsa wayan ta

Mintuna 20 RAUDHA taɗauka kafin tafito cikin Toilet ɗin, lokacin duk abinda tasha a daren jiya ya sake ta ta koma normal, idanun ta ma sun washe sosai sun koma fari tarrr ɗin su sai dai kumburan da sukayi ne be washe ba, wanda hakan yasaka suka sake lumshewa

A gaban dressing mirror tazauna tasoma busar da yalwataccen gashin kanta da yakasance baƙi siɗik me yawan gaske, bayan ta gama tashafa Expensive Lotions ɗin ta masu tsananin ƙamshi, batayi kwalliya ba illa powder da tashafa tasaka gazal a fararen idanuwanta, hakan yasaka suka ƙara kyau tare da ɗaukan hankali ga duk wanda yakalla, Lipstick tashafa a ƙananun laɓɓan ta tamiƙe tanufi Sif ɗin kayan ta

Kaya tasoma zaƙulowa tana ajiye wa asaman gado

Lokacin ne Ramcy tataso tazo bakin gadon tazauna tana kallon ta tace "dasu zaki tafi?"

Gyaɗa mata kanta kawai tayi taci gaba da ciro kayan

Ramcy tace "ok Aina zan shirya miki?".

Tsayar da abinda take yi tayi tanuna mata jerin Trolly ɗin ta tace "ki ɗau na saman".

Tashi Ramcy tayi taɗauko ɗan ƙaramin Trollyn kamar yanda tace mata tasoma shirya mata kayan ta ciki

Ita kuma alokacin taciro waɗanda zata saka tamatsa wajen kujera tasoma saka wa

Riga ce Robber me gajeren hannu baƙa da tatsaya mata iya ƙasan gwiwan ta, gaban rigan me tattara ne kuma anyi masa ado da stone masu tsananin ƙyalƙyali, sannan yana da igiya da taɗaure ta bayan ta, sai tasaka gajeren Socks red colour da Hill shoes ɗin ta me igiya shima Red colour, sai yazamana Ƙwaurin ƙafafun ta a waje suke

Gaban Looking mirror tanufa tasoma gyaran gashin ta sannan taɗaure da jan Ribom a tsakiyar kanta, shi kuma jelan taninke shi tayi kamar Dhounot, sai taɗaura Facing Cap baƙi da akayi harafin *R* agaban da jan zare, Parfomers ɗin ta taɗauka tafeshe jikin ta dashi sai faman zuba ƙamshi take yi, sosai tayi kyau kamar wata baby doll

Duk abubuwan da zata ɗauka sai da tazuba su cikin HangBag ɗin ta sannan suka fito Ramcy na jaye da Trolly ɗin

Su Saude da suke parlour nan sukayi musu adawo lafiya duk da kuwa basusan inda zasu je ba, amma ganin su da Trolly sun san tafiya ne yakama su

Ramcy ce kawai ta'amsa musu har suka fice

Suna fita compound ɗin gidan suka shige cikin farar motan da RAUDHA tace a wanke mata, horn tadanna tanufi bakin Gate a guje

Kafin ta'iso tuni me gadi ya hangame mata Gate ɗin tacilla motan waje sai saman kwalta

Kallon Ramcy tayi kafin takau da kanta zuwa titi tace "Besty ciro min tables ɗin nan cikin HangBag".

"Ok". Cewar Ramcy tana ɗaukan HangBag ɗin tabuɗe taciro mata

Nuni tayi mata da yatsu biyu hakan yasa taɓallo mata guda biyu tamiƙa mata, ta'amsa tasaka abaki tasoma tsotsa

Itama Ramcy ɗin cire ɗaya tayi tasaka a bakin ta sannan tamayar da sauran cikin jaka

Gudun da RAUDHA take tsulawa a saman kwalta ɗin baza ka taɓa tunanin zasu iya kai wa lafiya ba, over taking kawai take yi cike da ƙwarewa batare da ko tsoro ba

Sun ɗau hanyan Kaduna ɗoɗar lokacin ƙwayoyin da ta'afa sun soma aiki, gudun yanzu da take yi ma yafi na da

Gab da sun kusa shiga Kaduna tun daga nesa suka hango Sojoji sun tare hanya, but hakan be sa ta rage Speed ɗin motan ba

Wannan dalilin ne yasaka wasu daga cikin sojojin suka tsaya a tsakiyar hanyan riƙe da bindigogi suna jiran isowar motan

Sai da ta'iso gab dasu kamar zatayi ciki dasu kafin taja wani wawan burki da har yatsorata su tatsayar da motan cakk

Tashin hankali, gaba ɗaya Ramcy ta tsure don batasan me zai biyo baya ba da ganin yanda sojojin suka fusata sosai sukayo wajen motan

Ita kuwa RAUDHA ko a jikin ta sai faman ware lumsassun idanun ta dake faman rufewa take yi

Suna isowa biyu daga ciki suka bugi motan da ƙaton takalmin su cikin tsawa suka basu umarnin fitowa

Waɗanda suka hangi su Ramcy cikin motan sai abun yayi matuƙar basu mamaki ganin macece me wannan aika-aikan batare da taji tsoron abinda zai biyo baya ba, sakin baki kawai sukayi suna kallon RAUDHA da tasauke hulan ta ta'ajiye saman cinyan ta tazuba musu narkakkun manyan idanuwanta bata da alamun fitowa

Biyun da suka bugi motan waɗanda suka fi kowa fusata su ma leƙa motan sukayi da ninyan su ci mutuncin na ciki sai suka hangi mata , haɗiyar yawu duk kansu suke yi suna kallon su cike da sha'awa, kun san yawancin sojoji mayun mata ne 😅🤫, bare waɗannan masu ido a tsakar ka kallo ɗaya kayi musu zaka hango zalaman su, yawancin su ma duk Christian ne

Ɗaya daga ciki ne yabuɗe baki cike da murmushi a face ɗin sa yace "ah Madam Ina zuwa haka?"

Ramcy da har yanzu jikin ta ke faman rawa takalle sa kamar zatayi magana sai kuma taga RAUDHA yake kallo tayi gum da bakin ta

Cikin dashashshiyar muryan ta tabashi amsa a taƙaice tana kawar da kanta

Washe baki yasake yi yana kallon sauran ƴan uwan nasa da suka tsira wa RAUDHA idanu kamar sun sami t.v yace "ku wuce kawai zan ji dasu".

"Ok". Suka faɗa atare suka juya suka tafi batare da sun so ba, sai dan shi ɗin shine babban su dole subi umarnin sa

"Baby bakya jin tsoro kike yin irin wannan tuƙin?"

Shiru tayi bata tanka sa ba

Sai yasake sakin murmushi yakalli Ramcy yana kashe mata ido ɗaya sannan yanuna mata RAUDHA da hannu
*_________________________*


Daga can nesa wani matashin saurayi ne da yake tsaye yana waya amma idanun sa na kan motan su RAUDHA, tun sanda suka taho yake kallon motan yana mamakin ƙarfin hali da rashin hankalin matuƙin

Sanye yake cikin kakinsa da sukayi masa bala'in kyau tare da fito da ƙaƙƙarfan ƙirar jikin sa, wanda kallo ɗaya idan kayi masa zaka san Jarumin Namiji ne na bugawa a jarida, sannan a kallo ɗaya idan kayi masa baza ka iya tantance shi ɗin wani irin yare bane coz ko kusa be yi kama da ɗan Nigeria ba

Wayan yakashe sannan yatura cikin aljihu yanufi wajen motan cikin takunsa na mazantaka da nuna shi ɗin Jarumi ne


Isowar sa wajen maganar Sojan da yake wajen su Ramcy yasauka a kunnen sa, yana tambayan su Numban waya

Ɗaure kyakykyawar fuskar sa tamau yayi don yarigada ya gane mata ne aciki

Jikin motan yaƙarisa yanda zai hangi mutanen ciki, nan kuwa yasauke idanun sa kan Ramcy da itama tazuba masa idanun cike da tsananin firgita da ganin murɗaɗɗen mutumin dake tsaye a gaban ta babu ɗigon annuri

Saurin Solute ɗin sa Sojan yayi

Be kalle sa ba sai sake tamke fuska yayi yakai duban sa side ɗin RAUDHA da takawar da kanta har alokacin kuma bata sauke hannayen ta kan sitiyarin motan ba, sai faman karkaɗa yatsunta take yi

Tsira mata idanu kawai yayi yana kallon kyakykyawar fuskarta

Lokacin ita kuma tajuyo da face ɗin ta sosai yanda zai iya ganin ta sai dai idanun ta suna lumshe ne batare da ta kalle sa ba takwantar da kanta jikin kujeran

Gashin giranta dake haɗe masu yawan gaske yabi da kallo kafin yasoma bin jikin ta da idanunsa kamar wanda ke neman wani abu, sosai yarinyan tatafi da imanin sa sai dai shigan da tayi ya san cewa ita ɗin ba kalan su bane don batayi masa kama da me kallon gabas ba

Ajiyan zuciya yasaki a ɓoye, sannan yakalli sojan dake tsaye yana kallon sa tare da Ramcy sai yaji kunya, amma sai yawayance yakau da kansa yana sake haɗe rai yace

"Jone Aikin da kazo yi kenan tambayan numban su?"


Jin muryan sa cikin kunnen ta yasaka ta buɗe idanun ta tana kallon sa

Shi kuma alokacin kallon Jone ɗin yake yi


"No Sir". Cewar Jone ɗin yana sake Solute ɗin sa


Gajeren tsaki yaja yana maida idanun sa cikin motan, nan kuwa idanun sa yafaɗa cikin nata da tazuba mishi tana kallon sa batare da kunyan sa ba

Gaban sa ne yafaɗi sai yayi saurin ɗauke nashi idanun murya a kausashe yace "kuna mata kuke irin wannan tuƙin gangancin kuna da hankali kuwa?"

Duƙar da kanta Ramcy tayi duk jikin ta sai mazari yake yi, sosai muryan sa yatsorata ta, tasan da cewa wannan mutumin ba barin su zai yi ba, shikenan yau RAUDHA taja musu ta kawo su inda za'a kashe su

Ita kuwa RAUDHA har yanzu kallon sa take yi batare da  tsoro ba, sai ma lumshe idanun ta tayi bata da ninyan bashi amsa, ko kaɗan a yanzu bata son yin magana sabida ƙwayoyin da tasha

Sosai yaji haushin shirun da tayi, cikin fusata yace "ba da ku nake magana ba?"

A karo na biyu tasake kallon sa shima ɗin tsatstsare ta da idanun sa yayi batare da ya kawar ba

Cikin rawan murya Ramcy tace "yallaɓai kayi haƙuri don Allah".

Shima Jone cikin girmamawa yace "Oga sorry sun faɗa min abinda yasa..."

Ɗaga masa hannu yayi dole yayi shiru yahaɗiye ƙaryan da yake son shirgawa.._To fa yau RAUDHA da alamun ta taɓo dai-dai ita, bari mu jira me zai faru

Post a Comment for "RAUDHA CHAPTER 2"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...