RAUDHA CHAPTER 11 KARSHE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RAUDHA CHAPTER 11 KARSHE

RAUDHA CHAPTER 11 KARSHE

- - Post a Comment

 RAUDHA CHAPTER 11 KARSHE
📖 Murmushi ne ya suɓuce a kan kyakykyawar farar fuskar sa, sai dai be iya cewa komi ba illa kallon ta da yake yi+


While itama ta kasa ɗauke idanun ta kansa, sai dai a wannan lokacin sosai fuskarta ta kumbura da ɓacin rai, cike da fushin da bata san na mene ne ba tace, "ba'a gaya maka nan ɗin inda zan ajiye baƙo na bane da zaka zo ka zauna?"


Sai kuma ta juya tana kwaɗa wa Saude kira, taku ɗaya biyu tayi ta tsinkayi muryan sa yana faɗin


"Pretty ki bar wahalar da kanki mana, Ni ne Ƙalby ɗin ki".


Cakk ta tsaya tana juyo wa gare sa, ido cikin ido take kallon sa but ta kasa magana, sai kai komo da zuciyar ta ke yi wajen bugawa da ƙarfi


Murmushi ya sake yi yace, "nasan zaki yi mamaki da jin kalamai na, but ba abun mamaki bane, na shirya tsab don bayyana miki Ni ne wanda kike soyayya dashi batare da kin san ko waye ba, Pretty Ni ne Ƙalby ɗin ki, wanda kike matuƙar ƙauna da.."


Tsayar dashi tayi ta hanyar ɗaga masa hannu da faɗin, "ya ishe ka da Allah Malam".


Sake ware idanun ta da suke ɗigar hawaye tayi a kansa, wanda tun soma maganar nasa suka soma kwaranya. Sosai laɓɓan ta suke rawa but ta kasa furta abinda ke ranta, illa wani irin ƙunci da ya tokare mata maƙogwaro, juya wa tayi da sauri tayi hanyar fice wa parlour'n da gudun ta


Da sauri Ray ya tashi tsaye yana faman kwaɗa mata kira, amma ina tuni ta fice.


A tsakankanin farandan benen ta zube ƙasa ta hau rusa kuka, domin ko kaɗan baza ta iya kai kanta inda take son zuwa ba, saboda rawan da ƙafafun ta suke yi, gaba ɗaya jikin ta ma rawa yake yi tamkar an jona ta da shocking, ko gaban ta ma ba ta iya gani sabida hawayen da suke kwaranya cikin idanun ta, har wani jiri-jiri take ji Coz tuna maganganun sa dake dawo mata cikin dodon kunne, wani irin yawu take haɗiya tana jan numfashi tamkar zata shiɗe, daƙyar ta iya buɗe bakin ta daga laɓɓan ta ta furta "Noo! Ƙarya yake yi! Ƙarya ne! Bazai.. ba..zai taɓa za..ma shi.. shiii.." Lokaci ɗaya numfashin ta ya ɗauke sabida wani irin mahaukacin ja da tayi masa.


Dai-dai lokacin da ta ƙarisa sulale wa ƙasa, a lokacin ne kuma Daddy ya buɗo Lifter ya hange ta, Sunan ta ya kira da ƙarfi ya nufo ta cikin tashin hankali


A lokacin shima Ray ya fito a firgice ya tarar da abinda ke faruwa


Daddy na kallon sa yace, "taimaka Captain, taimaka min, Baby ba ta numfashi".


Cakk Ray ya ɗauke ta suka yi Lifter da sauri, suna sauka ƙasa suka fita waje, Daddy na kwaɗa wa Drever'n sa kira, nan da nan ya ƙariso, dama ba nisa yayi ba tunda yanzu ya sauke sa


motan aka shigar da ita, Ray ya shiga mazaunin Drever, Daddy kuma na zaune da ita a baya suka yi Hospital.


Suna zuwa babu ɓata lokaci aka amshe ta, aka yi da ita emergency word, inda anan likitoci suka soma ba ta taimakon gaggawa


Daga Daddy har Rayyan an kasa samun wanda sai zauna, sai kai komo suke yi ko wanne zuciyar sa da tunanin da yake yi, shi shaf Daddy tunanin sa be kawo masa ya tambayi zuwan Ray ɗin ba, ta ɗiyar sa yake yi hankalin sa duk a tashe.


Fitowar likitan da yayi jagora Wajen duba RAUDHAN, yasa gaba ɗaya suka dawo dogon tunanin da suka afka, suka nufe sa da sauri suna tambayan sa "shin ta farka?"


Likitan kwantar musu da hankali ya soma yi, kafin yayi musu bayanin "babu abinda ke damun ta, sun yi nasaran dai-dai ta numfashin ta sabida suman da tayi, dama abinda ya kawo hakan, sakamakon shiga ruɗu ne da tayi".


Daga Daddy har Ray nannauyan numfashi suka sauke sabida jin abinda likitan ya faɗa, ko wanne cikin su na faɗin "alhmadulillah"


"Za ku iya shiga ku duba ta, in yaso daga baya sai muyi magana". Cewar likitan yana murmushi


"Ok thanks doctor".


Ɗakin suka nufa, Daddy ne a gaba Ray na biye dashi a baya, har bakin gadon suka ƙarisa, inda Ray ya tsaya daga jikin gadon, Daddy kuma ya zauna akan farar kujeran Robber dake jikin gadon, ya riƙe hannun RAUDHA da idanun ta ke rufe ya kira sunan ta, "Daughter kina jina? Ya ya jikin naki?"


Shiru RAUDHA tayi duk da kuwa tana jin shi ɗin


Cike da damuwa Daddy ya sake cewa, "wai me ya faru ne lokaci ɗaya kika sume Baby? Me ke damun ki Baby na kiyi magana kinji? Meyasaka ki ruɗu?" Sai kuma ya sauya akalan tambayan ga Rayyan da cewa, "kai ne kake gidan, shin kasan abinda ya faru ne? Ni dai nasan na bar ta lafiya but sai na dawo na tarar da wannan tashin hankalin".


Sake runtse idanu RAUDHA tayi jin saukar muryan Ray a kunnen ta, hakan ya tabbatar mata da cewa ba mafarki ne take yi ba, gaske ne Ray shi ne Ƙalbyn ta, shi ne wanda ya zo gidan su a matsayin Ƙalbyn ta, sai kawai ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi


Sosai Daddy ya sake shiga tashin hankali, nan da nan ya ruɗe yana tambayan ta abinda ke faruwa


Shi kuwa Ray runtse idanun sa yayi yana jin babu daɗi a ransa, shi kaɗai yasan me yake ji a ransa, tashin hankalin da yake ciki baki ma bazai iya fasaltuwa ba, dauriya kawai yake yi da abinda yake shirin faruwa dashi


Daƙyar Daddy ya iya rarrashin ta, duk da ba shiru tayi ba, amma yanzu ta buɗe idanun ta, ko kallon inda Ray yake bata yi ba, tace wa Daddy "ita a sallame su, ba ta son zaman Hospital"

Yanda tace ɗin haka Daddy ya aiwatar, ya saka Ray Kiran Doctor ɗin ya basu sallama.


Ana sallaman su suka fito, Ray shi yaja motan su kuma suna baya, RAUDHA ta kwanta a jikin Daddy sai ƙananun kuka take yi, duk rarrashin da Daddy yayi mata taƙi haƙura, sosai ranta yake tsananin suya, baƙin ciki da ƙunci duk ya cika mata zuciya, har yanzu a ranta tana jin kamar mafarki ne take yi, idan ta farka zata tashi taga babu Ray a tare da ita, but da ta ɗaga idanu take sauke su a kanshi, sai ta sake jin wani baƙin ciki ya kanainaye ta, hakan ke sawa lokaci ɗaya sai ta sake fashe wa da wani sabon kukan


Sosai wannan abun da take yi ya so ba wa Ray dariya, duk da yana cikin damuwar me zai faru a soyayyar sa, but hakan be hana sa murmusa wa ba.


Suna isa gida, ta buɗe murfin motan tariga kowa yin gaba, Daddy na kiran ta but sam taƙi tsaya wa


Koda suka shiga parlour'n babu ita, hakan yasa suka zauna inda Daddy Ke tambayar Rayyan "zuwan nasa na bazata"


But shi dai Ray murmushi kawai yayi, don be san me zai ce mishi ba


Ɗaya daga cikin ƴar aikin su, da ta kawo musu Drinks ne, Daddy ya tambaye ta da cewa, "ko da suka fita baƙon RAUDHA ya zo ne?" Tunda a tunanin sa dai be rigada ya ƙariso ba, Maybe fitan su ya zo, su kuma ba sa nan


Cikin girmamawa take sanar masa da "Ray ne baƙon nata, kuma sun sauke sa tun ɗazu"


Da mamaki Daddy ya kalli Ray yace, "Captain maganar ta gaskiya ne?"


Cike da kunya Ray ya duƙar da kansa tare da amsa mishi


Farin ciki ne ya mamaye Daddy yace, "You mean Kai ne Ƙalbyn Baby, but taƙi sanar mana? Kaima haka? A cikin ku babu wanda ya sanar mana kuke ta ɓoyan soyayyar taku? Kai abu yayi kyau Masha Allah. To Ina muku fatan alkhairi, Allah ya tabbatar mana da mafi alkhairin sa".


"Ameen Daddy". Ray ya amsa cike da farin ciki shima a zuciyar sa, sabida ganin Daddy kansa yayi farin ciki da zamowan sa Saurayin Ɗiyar sa


"Amma to ta tafi ta bar ka anan? Ai sai ta zo taji da kai ko? Ko dayake gidan ba baƙon ka bane". Daddy yafaɗa yana dariya


Shima Ray dariyan yayi, but ya kasa cewa komi


"Tashi mu je saman, sai in Kira ta".


Tashi Ray yayi, suka haura sama, a parlour'n da ta shirya don tarban shi suka shiga, Daddy ya saka me aiki ta zuba masa abinci, sannan ya saka ɗaya daga ciki ta je ta kira RAUDHA. Har ta tafi kuma, sai ya ce "ta bar shi" shi ya tashi ya je kiran ta


Ray dai na zaune ya tasa abinci gaba, sai dai ko cokali ɗaya ya kasa kai wa bakin sa, hankalin sa kacokan yana ga RAUDHA.


🔵🔵🔵


Da farin ciki a fuskar sa Daddy ya ƙarisa ɗakin RAUDHA, but sai dai a yanda ya ganta ne hankalin sa yayi ƙololuwar tashi


Tana zaune a ƙasa, ta ɗaura kanta saman kujera tana ta riskan kuka, har da majinu


Da sauri ya ƙarisa wajen ta cikin tsananin tashin hankali yake tambayar ta abinda ke faruwa, duk ya ruɗe yana ta faman taɓa jikin ta yaji ko wani abun ne ke damun ta


Cikin kuka ta ɗago kanta tana kallon sa da jajayen idanuwan ta, tace, "Daddy RAYYAN ya zo gidan nan ne yau?"


Cike da mamakin tambayar ta yace da ita, "Ya zo mana Baby, ba ke kika gayyace sa ba? Kuma ya zo, yana nan a Parlour. Lafiya me ke faruwa ne?"


Kuka ta fashe da shi, idanun ta akan Daddyn tace, "Daddy kenan yana nufin shi ne Muhammad ɗina, shi ne wanda nake soyayya da shi?"


Sai kawai Daddy ya saki baki yana kallon ta, sai kuma yace, "baki san haka bane Daughter kike tambaya na? Ina ce ke kika gayyace shi ai?".


Girgiza kanta tayi, kafin tace, "no Daddy ba Ni ba CE, Sam ba shi ne wanda nake so ba, ya yaudare Ni ne, Ni ba shi nake so ba, wlh bazai taɓa zama Ƙalby na ba".


Sai kuma ta saka hannu ta riƙe masa nasa


"Daddy please ka farkar da Ni wannan mummunan mafarkin da nake yi, mutumin da na tsana shi ne zai zame min Mijin da na ke fatan aure? No impossible".


Daddy fa duk ya kasa gane abinda take nufi, dole ya saka hannu ya ɗago ta, yana jinginar da ita jikin sa ya hau rarrashin ta


"No Daddy bazan dena kuka ba, har sai na tabbatar da cewa ƙarya ne zancen nan, Daddy zuciya ta zafi take min". Ta ƙare maganar da saka hannun ta tana dafe ƙirjin ta, yayinda idanuwan ta suke kwararar da hawaye sosai


Sosai Daddy ya ruɗe, ya rasa yanda zai yi da ita, dole ya miƙe ya fita ɗakin, sai ga shi ya dawo tare da Rayyan, cikin tsantsan damuwa yake kallon Rayyan ɗin yake tambayar sa da faɗin, "Captain wani abun ne ya faru da kai da ita, na kasa fahimtar me take cewa, ka faɗa min tsakanin ku?".


Cike da sanyin murya Ray ya soma sanar masa da komi, idanun sa kan RAUDHA da ta kifa kai take ta rusa kuka, tamkar ana yankan naman jikin ta, duk da muryan ta ba ya fita amma sosai ta dage take kukan


Shi kansa Daddy sai da jikin sa yayi sanyi da abinda Ray ya sanar masa, sosai ya tausaya wa Ray ɗin, to abun tausayi mana, tunda ga shi yana soyayya but ashe ita wacce yake yi dan ita, ta kasa amsar shi a zahiri, sam ba shi ne take so ba


Zama Daddy yayi ya soma rarrashin ta, amma taƙi shiru


Ray dai tsaye yayi yana kallon su


"Baby tunda kin ce ba kya son shi meye to ya rage? Kiyi shiru mana kar ki saka wa kan ki ciwon kai". Daddy ya sake faɗan haka yana saka hannu ya soma share mata hawayen


Cikin dishewar muryan ta da ya ƙara shige wa, don daƙyar ma yake fita, har katse wa maganar nata yake yi tace, "I Hate him so much Daddy, na tsane shi sosai fiye da kowa Daddy, ko da zan zauna babu aure ne Daddy bazan taɓa auren sa ba, ba na son sa Daddy". Ta ƙare maganar tana dage wa tare da fashe wa da kuka


Daga Ray har Daddy babu wanda yaji daɗin kalaman ta, musamman ma Ray da har hawaye sai da suka zubo masa, ahankali ya tako zuwa wajen kujeran da suke, ya zuƙuna gaban ta, cikin hawaye yace, "Please RAUDHA ki taɓa zuciya ta ki ji yanda take harba wa da ƙaunar ki, duk socond ɗaya kullum ƙaunar ki sake wanzuwa take yi a raina, na jima ina dakon soyayyar ki a raina, na jima RAUDHA, don Allah gani a gaban ki, ki amince da soyayya ta RAUDHA, ina matuƙar ƙaunar ki, kuma ba na tunanin akwai wanda zai so ki fiye da yanda nake son ki, Ina matuƙar matuƙar ƙaunar ki RAUDHA, ke ce kika yi min alƙawarin baza ki taɓa bari na ba,".


Hannu Daddy yasa ya riƙe mata hannu, gaba ɗaya zuciyar sa ta gama karaya da tausayin Ray ɗin, yace, "Baby kin ga ya ba ki haƙuri, ko menene yayi miki ki yafe masa kinji? Babu kyau riƙo, bare shi da ya durƙusa gaban ki ya nemi yafiyan ki, na tabbata babu wanda zai fi shi son ki".

_______📖 Hannun ta ta zame daga na Daddy, ta tashi da gudu tabar ɗakin tana sake rushe wa da wani sabon kukan+


Daga Daddy har Ray dake hawaye bin ta suka yi da idanu har ta fice


Daddy sosai jikin sa ya sake sanyi matuƙa, har ya kasa ma yin magana, illa shiru da yayi yana afka wa duniyar tunani


While Ray, shima ya kasa koda jirga wa ne, illa lumshe idanuwan sa da yayi yana sauraron bugun zuciyar sa da ya sauya, ba ya jin zai iya jure rashin RAUDHA a tare dashi, yana matuƙar ƙaunar ta, ya rigada ya saka ta can cikin zuciyar sa, kuma fitan ta zai yi wuya a gare sa, tabbas yana ji a jikin sa muddin ya rasa ta zai iya shiga wani hali, shi kansa be san iya adadin ƙaunar da yake mata ba, kuma be san meyasaka soyayya tayi masa muguwar kamun nan ba..


    Muryan Daddy shi ya katse masa tunanin sa, yace mishi "ya je insha Allahu idan RAUDHA rabon sa ne, zai same ta, shi kansa yana goyan bayan ya kasance miji a gare ta".


Sosai Daddy ya ƙara masa ƙwarin gwiwa, kuma ya ce mishi ya dage wajen bata haƙuri, insha Allahu shi ke da nasara, shima zai taya sa roƙon ta

    Rayyan yaji daɗin kalaman Daddy, haka yayi masa sallama ya wuce Kaduna, sai dai a ƙasan zuciyar sa tunanin RAUDHA ne maƙil, amma babu yanda zai iya tunda yasan hakan sai ya faru.


              🔵🔵🔵


    Fannin RAUDHA kuwa abu yayi tsamari, gaba ɗaya ta hana kanta sukuni, ko kaɗan taƙi sauraren Daddy da maganar, da ya faro zancen zata soma mishi kuka akan "ba ta son sake jin maganar Rayyan". A cikin kwana biyu sai gata ta zabge sosai sabida damuwar da ta saka wa kanta, sosai take wahaltuwa da rashin Ƙalby ɗin ta, ita kanta ta san zai yi wuya ta jure rashin sa, tana mishi mahaukacin son da baki ma bazai iya fasalta shi ba, soyayyar sa ya rigada yabi jinin jikin ta, duk yanda ta so ta manta shi a ranta, ta cire sa ta goge sa gaba ɗaya a babin rayuwan ta, tayi rayuwa tamkar ma bata taɓa sanin sa ba ta kasa, dole ciwo ya kwantar da ita


Daddy gaba ɗaya hankalin sa ya tashi sosai, tausayin ɗiyar sa ya cika masa zuciya, sai dai taurin kanta yasa tana wahalar da kanta bayan tana da maganin matsalan ta, Doctor ya samo mace tana kula da ita a gida, da abun yayi tsamari dole aka wuce da ita asibiti, abu kamar wasa sai ga RAUDHA magashiyan tana jinya me tsanani har da su ƙarin ruwa, damuwar da ta saka a ranta ya haifar mata da ciwo me tsanani


Dole Daddy ya kira Suhaib ya sanar masa da komi, a ranan sai ga shi ya iso, sosai hankalin sa ya tashi ganin ƙanwar sa ta rame matuƙa, tausayin ta sosai ya kama shi, ba ma ita kaɗai ba har Rayyan, domin yasan cewa shima yana cikin wani hali koda be sani ba, tun farko ya gane Rayyan na ƙaunar ta, amma be taɓa tunanin shi ke bibiyan ta har suke wannan soyayyan ba, Allah Sarki Rayyan, ya so kiran sa ya sanar masa abinda ke faruwa da RAUDHAN, sai kuma yaga wani sabon tashin hankalin ne zai ɗaura masa, dole ya zauna rarrashin ƙanwar tasa, yana faɗa mata "ta amince da Rayyan, ta yafe masa domin samun kwanciyar hankalin su gaba ɗaya, domin yasan cewa shima yana nan cikin tashin hankali fiye da yanda take ciki".


Kuka ta fashe dashi tana kallon sa tace, "Yaya Ni bazan iya rayuwan aure da shi ba, infact ma ban taɓa saka wa a raina zai iya zamo min abokin rayuwa ba, Yaya kasan yanda na tsane mutumin nan duk a sabida abinda yayi min a baya? shi ne ya koya min tsanar sa, kuma ba na jin tsanar nasa zai iya goge wa a raina, domin wlh ji nake yi tamkar in kashe sa abaya saboda tsanar da nake mishi, but yanzu ba na jin haka saboda ya ragu sosai a raina, amma hakan ba wai yana nufin zan iya rayuwan aure da shi bane".


Riƙe hannun ta yayi yace, "meyasaka Baby baza ki bar komi ya wuce ba? Kar ki manta Dude ya zuƙuna ya baki haƙuri, duk ƙimar sa da mutuncin sa ya ajiye gefe, a matsayin ki na ƙanwar sa ya duƙa a gaban ki ya baki haƙuri, meyasaka baza ki yafe masa ba uhm? Idan kin ce kin tsane sa ai kuma kina son sa tunda kin Yi soyayya dashi".


"Yaya ai ban san shi ɗin waye ba shiyasa na so shi a rashin sani, amma yanzu ba zan iya auren sa ba, zan iya rayuwa da kowa ban dashi".


Yace, "Baby idan har zan samu ki yafe ma Dude ɗina ki aure sa, to wlh nima zan duƙa a gaban ki domin nema masa alfarma, don Allah Baby ki yafe masa".


Da sauri ta riƙo hannayen sa da yake shirin tashi ya duƙa mata, kuka sosai ta fashe da shi tana faɗin, "me ye haka Yaya? Me zaka yi don Allah?"


"Duƙa miki zan yi domin ki yafe ma Aboki na, Baby Yana matuƙar ƙaunar ki, domin nasan haka tun ba yanzu ba".


Kuka taci gaba da yi batare da ta furta komi ba, dole ya zauna rarrashin ta tunda yasan matsalan ta yanzu, doctors ma sun CE a dena saka mata damuwa


Daƙyar ya samu tayi shiru, be sake mata maganar ba har Daddy ya dawo


Ganin yanda ta ɗan saki jikin ta sosai sai hankalin su ya kwanta.


     Washe gari sai ga Rayyan, ba su san waye ya sanar masa ba, sai ganin shi suka yi a Hospital ɗin, lokacin ma RAUDHA tana barci ne


Daddy yace, "Captain wa ne ne ya sanar maka muna asibiti ka zo?" Sai kuma ya juya akalan tambayan sa ga Suhaib yana cewa, "ko kai ne?"


"No Daddy ba Ni bane, ban ma yi tunanin sanar masa ba".


Murmushi Ray Yayi yace, "Daddy duk abinda zai samu RAUDHA, wlh ina ji a jiki na! kuma duk halin da take ciki ina sane da komi, Daddy ƙaunar da nake mata bazai bar Ni kwanciyar hankali ba in har ba na bibiyan rayuwar ta".


Daga Daddy har Suhaib sosai yai matuƙar ba su tausayi, barin ma ganin yanda ya sauya duk ya faɗa, ga tarin ƙasumba da ya bari a fuskar sa ko gyara ba ya samu, kamar dai ba shi ne ɗan gayen nan ba


        Ita kanta RAUDHA sai da zuciyar ta ta karye da kalaman sa, hawaye suka soma sintiri a fuskar ta, sabida tunda ya shigo muryan sa ya doki kunnen ta ta farka, ta rasa meyasa zuciyar ta ta kasa yafe masa, duk idan ta tuna abubuwan da yayi mata sai taji babu daɗi a ranta, duk da tana son ya fe masa amma kuma kasancewar akwai maganar soyayya a tsakanin su, sai ta ji sam ba ta ƙaunar ta yafe masa, da ace haka kawai ne dole zata yafe masa..


    Maganar Suhaib ne ya dawo da ita duniyar tunanin ta, inda yake tambayar ta "meyasaka take hawaye?"


Ita bata san tana hawayen ba ma, sai kawai ta fashe da kuka


"Mene ne kuma na kuka Daughter? Me aka yi miki? Ke kenan kullum ba kya gajiya da kuka? Kin san abinda doctor yace miki ki dena saka damuwa a ranki, gaba ɗaya kin tsangwami kanki, kin ƙi kiyi abinda ya kamata, kuma kin san duk abinda ya same ki tamkar mu ya sama, damuwar da kike ciki mu ma muna cikin sa gaba ɗaya".


Sosai a wannan karon take kuka sabida kalaman Daddyn sosai ya shige ta, ta faɗa jikin sa cikin kukan take cewa, "Daddy ku yi haƙuri don Allah". Abinda take faɗa kenan tana ci gaba da kukan


Hannu Suhaib yasa ya ɗago kanta yana cewa, "haƙurin na meye ne Baby? Allah idan baki dena kukan nan ba zan yi fushi dake, kuma kin san abinda ban taɓa yi ba kenan".


Hannu ta saka da sauri ta soma share hawayen ta, Daddy na taya ta


Ray dai na zaune yana kallon su, zuciyar sa cike fam da soyayyar ta, tabbas da zai iya haƙura da RAUDHA, da tuni ya bar ta har ABADA


Daddy ya soma tashi ya fice bayan ya ce musu "zai je wajen doctor ne".


Shima sai Suhaib ya miƙe ya ɗauki waya ya fice batare da ya ce uffan ba, don ya gane manufar Daddy ɗin, shiyasa shima ya miƙe ya ba su wuri


RAUDHA da kallo tabi Suhaib dashi har ya fice, don bata yi tunanin wai fita zai yi ba, sai dai ganin ya fice kawai sai ta bi shi da ido ta kasa cewa komi..


Sunan ta da Ray ya Kira ne, yasa ta dawo da kallon ta gare shi, sai a lokacin ma ta kalli inda yake, shiyasa tayi saurin ɗauke kai da suka haɗa ido, sosai ta ga ya sauya mata saboda raman da yayi. Bata amsa mishi ba illa ɗaure fuska da tayi tana cin magani


Sarai ya lura da sauyawan ta amma hakan be dame sa ba, sai ya tashi daga kujeran da yake ya dawo na kusa da gadon, yana kallon ta yace, "Ya jikin naki Pretty?"


Shiru tayi masa tana sake jujjuya kanta don ko kaɗan ba ta ƙaunar kallon da yake mata, har cikin jikin ta take ji


Shiru ne ya ratsa na ɗan wani lokaci, kafin kuma ya sake buɗe baki yace, "Pretty idan har ban manta ba, ke ce da kanki kika yi min alƙawarin zaki kasance dani a duk halin da kika ganni, don me baza ki yafe min ba? Wlh duk abinda nayi miki a baya, nayi sa ne saboda ƙaunar da nake Miki, ki yarda dani, ina son ki sosai shiyasa ba na son wani abu ya same ki, duk abinda nayi miki a baya nayi hakan ne don ki kintsu ki dawo kan hanya madaidaiciya, amma duk idan na musguna miki, ina koma wa ne abun ya dame Ni matuƙa a rai, sai kuma naga babu hanyar da ya dace illa hanyan da nabi ɗin, duk kalaman da nake faɗa miki, na rantse da Allah, ba ke kaɗai suke ɓata wa rai ba, ina kwana ne da ƙuncin zuciya a duk sanda nayi miki irin furucin nan, sam ina ji ba na kyauta wa, sosai nake azabtuwa, amma kuma Ni duk a gani na hakan shi ne dai-dai, hanyar kawai da zan bi don ganin kin gane gaskiya, Pretty duk da nasan halin ki, na san ke wacece amma wlh ban hana zuciya ta ƙaunar ki ba, ina son ki da gaskiya Pretty! wlh ko da Zaki koma rayuwan ki na baya ne, zan kasance dake Pretty, sabida ƙaunar da nake Miki bazai bari na iya rayuwa cikin daɗin rai ba, ban taɓa son wata ba sai ke, a kanki zuciya ta ta fara soyayya".


Shiru yayi yana jan numfashi, sai kuma ya ci gaba da faɗin, "RAUDHA ina son ki, a gaban kowa zan fito in sanar cewa ina son ki, kuma ina me alfahri da hakan, ina roƙon ki ki bar komi ya wuce, ki amshe Ni a matsayin masoyin ki a yanzu, zan miki duk abinda kike so in dai zaki yafe min ki amshi tayi na, idan kuma kin ce ba kya so na, wlh zan bar rayuwan ki har ABADA kamar yanda kike so".


Tunda ya soma maganar nasa, ta haɗa kai da gwiwa a saman gadon tana faman rera kuka a hankali, sosai zuciyar ta ta karye da maganganun sa, "shin meyasa baza ta yafe masa ba?" Shi ne tambayar da zuciyar ta ke ta faman tambayan ta, tabbas tana ƙaunar sa itama, amma kuma bata san meyasa ba, sosai yake ba ta haushi, duk da kaso mafi yawa yanzu maganar sa yasa ta fahimci gaskiya, tabbas so ne, idan ba son ta yake Yi ba, da be mata abinda yayi mata ba, kuma da shi macuci ne a gare ta, tabbas tasan da tuni ya daɗe da cutan ta, saboda ya samu hanyoyi da dama amma be yi hakan ba..


Tashin da yayi ya saka ta dawo duniyar tunanin ta, ahankali ta ɗago kai tabi shi da kallo, har ya kai bakin ƙofa ta tsayar da shi da faɗin, "dakata Malam".


Cak Ray ya tsaya daga buɗe ƙofan da yake shirin yi, sai dai be jiyo ba yana jiran abinda zata ce


Sauko wa tayi daga kan gadon, ta saka hannu ta share hawayen fuskarta, duk da kuwa ba dena zubo wa suka yi ba, ta taka ta nufi wajen sa, tana ƙarisawa ta saka hannu tayi...Hannun ta ta saka ta kamo nashi, hakan yasa ya juyo yana kallon ta, ido cikin ido suke wa junan su kallo, batare da ko wannen su yana ƙyafta wa ba+


Sun ɗau tsawon soconni a haka kafin ita ta soma ɗauke kanta tana jan numfashi, sai tace, "I love you".


Tsaban maganar ta zo masa a bazata be san sanda ya fiddo idanuwan sa waje ba yana kallon ta da tsananin farin cikin da ya fito tun daga zuciyar sa, sai dai ya kasa magana illa kallon ta da yake yi


Jin yayi shiru sai ta mayar da idanun ta kansa, ganin kallon da yake mata sai ta taɓe baki tace, "Ina son ka ba yana nufin na amince zan aure ka bane". Tana gama faɗar haka ta saki hannun sa ta juya zata koma


Yayi saurin riƙe mata hannun, dole taja ta tsaya, but ta kasa juyo wa illa lumshe idanuwan ta da tayi tana sauraren bugun zuciyar ta


Tako wa yayi ya dawo gaban ta, idanun sa a kan ta da tsananin murna yace, "idan har kina so na, na tabbata zaki iya aure na, kenan kina nufin kin amince dani a matsayin masoyin ki?"


Huro hanci tayi sai dai ta kasa kallon sa, illa shiru da tayi tana haɗiyar yawu


Shi kansa ya lura akwai Magana a bakin ta, sabida yanda take ta motsa bakin tamkar zata buɗe tayi magana. Murmushi yayi yace, "I love You so Much RAUDHA! Ina son ki da yawa wanda baki ma bazai iya furta wa ba, kiyi haƙuri da duk abinda nayi miki kinji?"


Sai a lokacin ta ɗago manyan idanuwan ta ta sake kallon sa, sai tayi saurin ɗauke kai tare da janye hannun ta, ta gifta shi tana faɗin, "Ni fa ba ina nufin zan iya auren ka bane, duk da na faɗa maka wannan kalman, zuciya ta ce ta aiko Ni, but a zahiri baka yi min ba".


Sosai maganar nata ta ba shi dariya memakon haushi, sai da ya murmusa yana shirin magana, sai ji suka yi an buɗo ƙofan, daga shi har ita juya wa suka yi su ga wanene


Suhaib ne tsaye yana bin su da kallon tuhuma, ganin su cirko-cirko da yayi a tsaye kusa da juna, sai kawai ya saki fara'a a fuskar sa yana faɗin, "Baby kin.."


Saurin katse sa tayi da faɗin, "Yaya Ni dama Toilet zan je shi ne na sauko". Sai ta juya kuma tayi Toilet ɗin da sauri har tana kanannaɗe skert ɗin ta tun kafin ta isa don ya tabbatar Toilet ɗin take son zuwa


Daga shi har Ray da kallo suka bi ta, ko wanne na sakin murmushin da be shirya ba, sai kuma suka jiyo da kallon su ga juna suna ci gaba da murmushin


Suhaib yace, "Allah ya shirye ki Baby, har yanzu kin ƙi ki girma, Aboki na zaka yi aiki duk sanda ka auri Baby a matsayin mata, shawaran da zan baka kawai idan har ta kasance matar ka, to ka haɗa su biyu ka aura ka je dasu gidan a lokaci ɗaya, idan kuma ba haka ba, wlh zaka sha..."


Burum RAUDHA ta fito daga Toilet ɗin, fuskar ta gaba ɗaya a haɗe yake tace, "Yaya To dama wa yace maka zan aure sa? Wlh bazan taɓa zama da kishiya ba, be isa ya haɗa Ni da wata ba, idan ma yasan yana da mata yanzu tun wuri yaje ya sake ta.."


Wani irin dariya ne ya kufce musu su duka biyun


Dole yasa RAUDHA tayi shiru tana faman zare idanu, sai yanzu ta gane katoɓaran da tayi, sai tayi saurin kwaɓe fuska kamar zata yi musu kuka tace, "Ni fa ba ina nufin wani abu bane, misali nake yi idan zan kasance matar sa".


Suhaib na dariya yace, "to Baby dama wa yace miki muna nufin wani abu? Dariyan ne ya zo mana atare sabida tuna wani abu da muka yi, ko ba haka ba Dude?" Ya ƙare maganar da ɗage wa Ray gira ɗaya


Ray dai tsaban farin cikin da yake ji a ransa, sabida ganin cewa RAUDHA har yanzu tana ƙaunar sa, be iya magana ba illa gyaɗa masa kai da yayi yana ci gaba da darawa


Haɗa idanu suka yi dashi, sai ta banka mishi harara tana yin gaba, ta hau kan gadon tana koma wa ta kwanta, har da juya musu baya


Matso wa Suhaib yayi kusa da shi, ya zungure shi ganin yana ta kallon ta, murmushi yayi masa ya raɗa masa magana a kunne, sannan ya kalli RAUDHAN yace, "Baby bari mu je mu dawo, idan Daddy ya dawo ki ce masa mun shiga cikin anguwa zamu je wajen wani friend ɗina".


Shiru RAUDHA tayi bata ce komi ba har suka fice, suna fita ta tashi zaune tana tanƙwashe ƙafafun ta, tare da haɗa hannayen ta waje ɗaya ta tallabo haɓar ta, tsira wa waje ɗaya ido tayi tana me afka wa tunani.

🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵


       Washe gari dole RAUDHA ta matsa aka sallame ta, su ma su Daddy sun ji daɗi ganin yanda ta samu lafiya, shiyasa Daddy shima yace "a sallame su" tunda dama damuwar duk akan Rayyan ne, kuma sun ga ta sauko sosai akan sa.


    Suna komawa gida, Daddy ya Kira Uncle ya sanar da shi abinda ke faruwa, kar ku so ku ga murnan da ya nuna da shi da Ammee, kai gaba ɗaya ma ahalin, har Faruk da yake ƙaunar ta, tunda tuni ya ajiye makaman sa tun sanda ya gane cewa Yayan nasa yana ƙaunar ta, sosai kowa yake farin ciki da wannan haɗi.


     Ita kuwa RAUDHA ko kusa nuna wa take yi har yanzu baza ta iya auren sa ba, kuma sun ci gaba da soyayyar su a waya, domin yana kiran ta tana ɗauka, sai dai ta dinga gaya masa maganganu kenan don dai ta ɓata masa rai, amma kuma be hana gobe idan ya kira ta taƙi amsa wa ba


Shi dai Ray dariya ma abun nata yake ba shi, tamkar dai har yanzu akwai aljanu a kanta, domin wani abun idan tayi, baza ka ɗauka ƴar shekara 24 bane, RAUDHA akwai shirme a kanta sosai.


     Da weekend sai ga shi yayi mata bazata ya zo gidan, sosai a ranta tayi murna amma a fili ta nuna ko kaɗan hakan be burge ta ba, illa taɓe baki da take ta faman yi taƙi masa magana


Daddy na tashi a wajen yace da ita, "wai Pretty ko baki yi murna da gani na bane? Har yanzu kin ƙi ki yafe min gaba ɗaya ko?"


Kallon sa tayi, sai ta ɗaure fuska tace, "ai bazan taɓa yafe maka ba Ƙalby".


"Why?" Yace da ita cikin sanyin murya


"Sabida nima har yanzu kallon ƴar iska kake min, in har baka dena ba, Nima kuma bazan taɓa amince wa da kai ba, bare har in yafe maka".


Yace, "wlh nayi alƙwari daga yau bazan ƙara miki kallon haka ba, idan magana makamancin haka ya sake fito wa a baki na, na baki dama kiyi min duk hukuncin da ya dace dani, koda kuwa rabuwa dani ne, wlh Pretty soyayyar da nake miki ya wuce tunanin ki, ko da yanzu zaki koma rayuwan ki na Da ne, to Ni kuma nayi miki alƙawarin kasancewa da ke, bazan taɓa rabuwa dake ba, zan aure ki a haka, tabbas na yarda *SO ƘADDARAR ZUCIYA* ne! ( My new book), soyayyar ki shi ne ƙaddarar tawa zuciyar".


Kallon sa kawai take yi, amma a zuciya murmushi take yi tana me faɗin, "uhmmm Rayyan kenan! Tabbas zan fi kowa murnan ranan da zaka yi nadama da kira na da kalman ɓatanci da kake yi, zaka sha mamaki wlh".  A fili kuwa cewa tayi, "Fine". Tana ɗage kafaɗa tare da karkaɗa ƙafafu


Murmushi ya sakar mata, itama ta mayar masa tana faɗin, "sai yaushe zaka tafi?"


"Kin ƙosa in tafi ne?"


Ɗan zaro ido tayi tana kama haɓa tace, "laa haza haramun".


Dariya yayi sosai, saboda ba ƙaramin dariya ta bashi ba, itama tana taya shi, gaba ɗaya a nishaɗi suke jin su, tamkar dai an sauya musu wani abu a jikin su, ko kuma sun sauke wani nauyi


Tashi tayi don tayi masa tsiya tace, "to Ni bari in Kira maka Daddyn, tunda dama wajen shi ka zo".


Langaɓe kan sa yayi yana sakar mata wani shu'umin kallo, cike da sanyin murya yace, "haba Pretty Kar ki yi min haka mana, kin san fa domin ki na zo".


Murmushi tayi tana cije leɓen ƙasa, itama ɗin ta sakar masa wani kallo da ya kusa zauta shi, har da wulla idanun tamkar zata rufe su ta sake buɗe su a kansa, taku tayi ɗaya zuwa biyu a gaban sa, kafin ta juya tana tafiya cikin yanga, tamkar dai da gayya take masa


Sosai Ray ya rasa nutsuwar sa, yana bin ta da kallo ko motsin kirki ya kasa, har sai da ta ɓace wa ganin sa kafin ya saki wani Gwauron numfashi yana lumshe idanu, babu abinda yake gani sai kyakykyawar surar jikin ta dake masa gizau, "Oh Allah! My beby Zaki kashe Ni!" Yayi maganar a maƙoshi yana jingina kansa sosai jikin kujeran.


      Har Ray ya bar gidan be sake haɗuwa da RAUDHA ba, ƙiri-ƙiri ta maƙale a ɗaki taƙi fito wa, kuma ya kira ta duk taƙi ɗauka, duk da ga wayan a hannun ta tana yin Game, iyakan tayi murmushi ta katse kiran


Hakan ya tabbatar masa da tana ganin kiran nasa, murmushi yayi shima a zuciya yana faɗin, "Dani kike zancen Pretty, zan rama ne ai".

🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵🔵


      A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah, har ana shirye-shiryen saka ranan auren RAUDHA da RAYYAN, soyayyar su yanzu abun sha'awa ne, kullum suna nane a waya tamkar za su cinye juna, duk weekend kuma sai ya zo mata, ta saki jiki sosai dashi suna gurzan soyayyar su kamar za su haɗiye juna, soyayyar da suka yi a baya ma ba komai bane kan yanda suke yi


An saka ranan auren nan da wata ɗaya, sabida kowa a shirye yake kuma kuɗi ke aiki, shiyasa aka ce baza a saka da yawa ba


Tun sanda aka tsayar da ranan auren nasu, ta kira Zulain ta sanar masa


Sosai ya shiga tashin hankali da alhinin rasa ta da yayi, amma babu yanda zai iya dole sai haƙuri, duk da a lokacin ma tamkar ƙara wutar son ta ake masa a zuciya, dole ya haɗa kayan sa yace musu "zai tafi" tun da dai ya san idan ya tsaya a nan damuwa ce zai illata shi, haka yabi jirgi ya koma ƙasar su tare da ɗumbin soyayyar RAUDHA a zuciyar sa


Shi kuma ya bar Sharifa tare da nasa a zuciyar ta, sosai tayi kuka ranan da ya tafi, ta so ta sanar masa amma ta kasa, sai da ya tafi tayi dana-sani ba kaɗan ba, haka tasha kuka ta gode wa Allah, ga shi kowa ta ƙi ta sanar amsa son da take yi wa Zulain ɗin.


     _To Allah ya kyauta, inda rabon ayi dake ne to, in kuma babu shikenan, mu dai ƴan shan biki ne. 🤷_


              🔵🔵🔵


     Biki na ta ƙara to wa, inda ake ta shirye-shiryen bikin daga bangare biyun gaba ɗaya, su kuma masoyan suna ta shan soyayyar su.

Dama akace duk abinda aka saka mishi rana dole zai zo, to ga shi bikin su RAUDHA ya rage saura kwanaki ne, sosai Daddy ya ga jama'a a bikin nan, waɗanda suka zo masa daga cikin ƴan uwa, bare shi mutum ne na ƙwarai me kirki da hannun kyauta, shiyasa dangi duk suka taho masa, sabida sun san ba su za su ragu ba, sai dai ma su ƙaru, wasu tun ana kwana huɗu, uku duk suka zo da kayan kwanan su, sai bayan biki su koma, su suke yin komai tare da ƴan aikin gidan, Masha Allah gida ya cika maƙil+


Itama Farida tun ana saura sati ɗaya suka zo, daga ita har Suhaib da ya ajiye aikin sa kacokan, don zuwa bikin shalele kuma mafi soyuwa a birnin zuciyar sa


Zuwa lokacin duk shi yake kai ta duk inda take buƙata, duk da dama duk wani gyara da ake mata, har gida ake zuwa ayi mata, Farida ita ta ɗau nauyin komi ake gyara ta ba ni da gyara ba, domin tun sanda aka soma mata gyaran amarcin RAUDHA ta sauya, gaba ɗaya baza ka taɓa kallon ta kace ita ce ba, ta koma hurun aini🤫😜, kamar ka latsa ta jini ya zuba sabida haske da sulɓi da take yi, ga wani ɗaukan idanu da take yi, dayake hasken ta yayi yawa har wani jajja take yi kamar dai zabiya, amma kuma ko ƙuraje bata dashi. Hasken ta me kyau ne, me fizgar mutane zuwa gare ta.


Bata da ƙawaye ita take yin komi nata, sai ana jibi biki ne Ramcy ta iso, a ranan kuma ƙawayen Ramcy ɗin duk suka zo, dayake sun ce idan bikin ta ya zo a gayyace su duk za su zo, to shi ne fa RAUDHA ta samu ƙawaye da ɗan yawa, ga shi wasu ma da suke chart a cikin Friends ɗin sun ce za su zo mata.


Ranan juma'a 8 ga watan April, dubu biyu da ashirin da ɗaya 2021. Dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren *CAPTAIN RAYYAN HASSAN* da Amaryan sa *RAUDHA MUSTAPHA MAKAMASHI*


Da dare akayi shirin Dinner, inda me kwalliya ta tsantsara wa RAUDHA kwalliyan da ya ɗauki fuskar ta ainun, ya ƙara fito da tsantsan kyawun ta, ba wani karikitai aka cika mata ba, saboda tace ba ta so, shiyasa akayi mata light make-up, aka shirya ta cikin ash colour ɗin gown doguwar riga, rigan fitet ne, domin dai-dai jikin ta ne, amma daga ƙasan gwiwan ta ya buɗe sosai har yana jan ƙasa, me siraran hannu ne, sai wani ƙaton flower da aka saka mata daga hannun damar ta, da net akayi shi, sai kwalliya a gaban rigan da kalan jan zare, sai akayi mata amfani da jan net aka rufe mata gashin ta da ya sha gyara har kafaɗun ta, duk da an tufke mata shi a tsakiyar kanta, takalmin ƙafan ta me tsananin tsini ne sosai, kalan ja tare da pourse ɗin hannun ta


Sosai ta tafi da imanin duk wanda yayi tozali da ita sanda me make-up ta fito da ita, sai haska ta suke yi a photo ana sauri ayi status da ita😜. Kuma na san duk aikin WhatsApp fan's ɗin ta ne.🤭🤣


A lokacin motoci duk sun zo ɗaukar mutane zuwa Shagalin ku restaurant, inda a nan ne za'a yi dinner ɗin. Sai da kowa suka shiga mota suka tafi kafin Farida tare da Ramcy suka rako ta zuwa motan da za su tafi tare da Ray, galleliyar mota ce fara tasha kwalliyan balo-balo


Su suka buɗe mata motan ta shiga ciki ta zauna, sannan suka rufe suka nufi motan Suhaib da zai kai su


Numfashi kawai taja lokacin da ta shaƙa daddaɗan ƙamshin su da ya haɗe ya gauraye waje ɗaya ya ƙara wani sinadarin daɗi, juyowar da zata yi suka haɗa ido dashi dake zaune ƙyam ya kafe ta da ido ko motsin kirki ya gaza yi, saboda ba ƙaramin zauta shi tayi ba, ta ɗauke masa gaba ɗaya nutsuwar sa da numfashin sa, ya tafi wani duniyar da ya kasa tantance a raye yake ko kuwa a mace 🙈😜, hege Ray! Zaka dawo ma duniyar mu ne yanzu. 🤣, Bari dai ta falla maka mari🤭


Murmushi tayi ta matso da fuskar ta kusa da nasa, ta hura masa iska


Hakan yasa ya dawo cikin hayyacin sa, har da ajiyan zuciya


Ita kuma sai ta taɓe baki tana matsar da fuskar ta kusa da nashi, tare da gyara zaman ta


"Kin yi kyau Baby na". Yayi maganar tamkar ana masa dole, nan kuwa tsaban shiga tention ne 🤣 ya rasa kuzarin sa


Sake kallon sa tayi, suka ƙura wa junan su idanu, sai kuma ta sakar masa murmushi ahankali tace, "kaima kayi kyau Ƙalby, I Love You so Much".


Lumshe idanuwan sa yayi yana buɗe wa a kanta cike da wani irin farin ciki dake gudana a zuciyar sa, sabida kasancewar yau ɗin na musamman ne a rayuwan sa, Mallakar Abokiyar rayuwar sa. Hannun sa ya saka ya kamo nata wanda suka sha lalle suka yi mata matuƙar kyau, hannun kawai yake kallo


While itama tana taya sa


"Yayi kyau". Ya sake faɗa ahankali


Murmushi kawai tayi ta kawar da kanta, sai kuma ta lumshe idanuwan ta saboda jin ya haɗe hannayen su waje ɗaya yana faman matsa mata


"Baby kin Yi kyau".


"I know". Tafaɗa tana ci gaba da murmusawan ta


"Ina kishin ki". Ya sake faɗa yana kisses ɗin hannun nata da ya ɗago zuwa bakin sa


Shiru tayi masa wannan karon, tana me sake runtse idanun ta, sosai take jin wani iri a tattare da abinda yake mata, amma kuma baza ta iya hana sa ba, inda so samu ne ma, taji ta a jikin sa, sabida ba ƙaramin son kasancewar hakan take yi ba, duk a sabida ƙamshin turaren sa da ya cika mata hanci, tamkar ta shige jikin sa tayi ta shaƙa..


"Tunanin me kike yi?" Yayi maganar yana shafa fuskar ta


Buɗe idon tayi a kansa, sai kawai suka sake ƙure junan su da kallo, ko wanne na jin son ɗan uwan sa a zuciya..


Tsayuwar motan shi ya dawo dasu hayyacin su, dole suka nutsu suna me mayar da hankalin su kan Suhaib da ya buɗe murfin ƙofan side ɗin Ray, yace masa "ya fito"


Sai da ya sake yi wa hannun nata kiss, kafin ya sakar mata, sannan ya fito, kafin ya zagayo ta side ɗin ta, itama har an fito da ita


A tare suka jera zuwa hole ɗin, masu sauraro bazan iya fasalta muku yanda couple ɗin nan suka haɗu ba, da kuma Shagalin da akayi, amma kuyi tunanin abinda zai faru, 🤣 kun san halin RAUDHA dai, a bikin nata ma bata ji kunyan yin rawa ba, koda aka ce su fito fili, ita zaƙe wa tayi ta tiƙa rawan ta ba ko kunya, har da riƙe masa hannu, shima da ya ga dai abun ba na yi bane, dole ya ajiye kunya suka bar tarihi a wajen


Yawancin abokan sa na wajen aiki duk sun hallara, har wasan su na soji sai da akayi, a hotel ɗin aka kai su suka sauya kaya zuwa kayan sojoji daga shi har ita, sun yi matuƙar kyau sosai, sai wanda ya gani _(🤣 nasan ku ma kun gani ai? Tunda babu wacce bata zo Dinnern nan ba, kuma duk na ga inda kuka ɓoye kuna afa shinkafa da nama😲🤭)_ ita rigan da ta saka t.shirt ne blue Black, sai wandon sojoji da ƙaton Combat ɗin su, sannan ta ɗaura hulan kayan a saman kanta, shi kuma yayi shigan kayan nasu ne gaba ɗaya, sun yi mugun kyau gaskiya babu ƙarya, ko kaɗan RAUDHA bata nuna tsoro a wajen wasan nasu ba, duk abinda aka saka ta tana yi, duk da sosai take tsoron bindiga bare Harbin shi, amma wayewan ta ya saka ta ɓoye haka, sannan tana jin cewa ita Matar Soja ne a yanzu, _(🤣zata yi muku gori ne walle, ku auri soja akwai daɗi auren su 😜)_ don haka tsoro be kamace ta ba


Ray ɗin da kansa ya koya mata yanda zata yi Harbin, Yana tsaye a bayan ta, ya riƙe mata hannaye suka saita mutum-mutumin da aka ajiye musu, ta har ba


Sai shewa ake yi sabida yanda komi ya ba da kala, ya burge kowa na wajen.


A gurguje Please.. Haka dai taron ya tashi cikin ƙayatarwa. gida aka mayar da RAUDHA tunda ba yau za'a kai ta ba, sai zuwa gobe za'a wuce da ita Bayelsa, daga can kuma sai su dawo ita da Ray Kaduna wajen aikin sa, a can aka shirya mata gidan ta uban-uban su, duk da a cikin barikin sojojin ne inda yake zaune, amma kayan da aka zuba mata wayyo Allana, sai mun haɗu acan dai fans, ku waso Ido amma. 😊


Washe gari ƙarfe 09:00am jirgin su ya ɗaga zuwa Bayelsa, tare da Farida da Ramcy suka tafi, sai wasu mata biyu daga cikin dangin Daddy da yace aje dasu


Ray kuma zai taho ne zuwa anjima, don tare za su dawo da RAUDHA.


Koda suka isa, an yi musu tarba na girma, su kansu sun san cewa sun zo dangi masu karama da waye wa, ko a fuska ka kalle su ka san haka, ko kaɗan ba su da ƙyashi ko hassada a zuciyar su, gaba ɗaya kansu a haɗe yake, bare yanda suke girmama Ammee, komi suna iya mata don ganin farin cikin ta


A family house ɗin su aka soma sauke su, inda aka ware musu ɗaki guda tare da Toilet, aka zube musu abinci da duk abinda za su buƙata, tunda suka sauka Suhaima ta zo ta maƙale wa RAUDHA, sosai tayi farin ciki da kasancewar RAUDHA cikin dangin su, har ta kasa ɓoye murnan ta, sai washe baki take yi tana nan nan da RAUDHA, duk gaba ɗaya ta maƙale mata, ba ma ita kaɗai ba, har sauran ƴan matan gidan, tunda sun kai su uku ne ƴan matan.


Bayan sallan Asar su Farida suka soma haraman tafiya, shiyasa aka ɗauke su gaba ɗaya aka mayar da su gidan su Ray ɗin, inda Ammee da ƴan uwan ta suka yi musu tarba me kyau, suka mutunta su sosai


Ba su wani daɗe ba, Faruk ya kai su Airport, sai ga RAUDHA tana hawaye sanda za su tafi, gaba ɗaya sai taji ba ta ƙaunar tafiyar nasu, duk da sosai ta ba wa Ramcy tausayi, amma sai Ramcy ta dage tana ta mata dariya, don baza ta manta ba itama haka tayi mata, sai tsokanar ta take yi tana taɓa mata kumatu tana ci gaba da mata dariya


Sai da Farida tace, "Kin ga ƙyale ta dan Allah kar ki ɓaro mana abinda baza mu iya ba, kin san halin RAUDHA da taɓara, yanzu wlh sai ta birkice mana".


Langaɓe kai Ramcy tayi tana sake kallon fuskar RAUDHAN da yayi caɓe-caɓe da hawaye, ta cika fam ko motsi ba ta yi


"Allah Sarki my Besty, ki kwantar da hankalin ki yau ɗin nan za ku dawo ai, zuwa da dare zan saka Dear ya kawo Ni, kin ga sai mu sha hira".


Kallon ta tayi, da ƙyar tace, "da gaske kike yi?"


Gyaɗa mata kai tayi tana sake ba ta tabbaci


Da haka dai suka bar gidan RAUDHA bata sake wani maganar ba, illa kwanciya da tayi tana hawaye, sai da Ammee ta shigo ɗakin ta rarrashe ta, sannan tayi shiru, inda ta saka ta ta sake yin wanka ta kawo mata wasu tsadaddun kaya na musamman, baƙin less ne, ta saka, riga da zani ne kayan, duk gaba ɗaya daga zanin har ɗan kwalin ɗaura mata akayi, babu wanda ta iya da kanta, sosai kayan suka yi mata kyau, kasancewar ta fara shiyasa baƙin less ɗin ya yi mata matuƙar kyau, gyale aka yafa mata me ruwan Powder, daga saman kanta har zuwa gwiwowin ta ya kai mata, sannan ta saka Hill shoes, Ammee ta fito da ita zuwa parlour'n Uncle, inda yake zaune daga shi har ƴan uwan sa


Sosai suka yaba da tarbiyyan ta, suka saka mata albarka ko wanne fuskar sa cike da farin ciki, haƙiƙa sosai ta shiga zuciyar su, ko dan kyawun ta dole ne ka so ta.


Wajen magriba Ray ya shigo gidan, har zuwa bayan isha'i ba su haɗu da RAUDHA ba, tunda ita tana ɗaki a kwance, sai da Suhaima ce ta zo shi ne ta tashi suke taɓa hira, a tare suka yi sallan isha'i a ɗakin, inda Ammee ta shigo tace "mata ta kintsa za su tafi da Mijin ta" ta sha mamaki sosai, sabida ganin dare yayi, ai ya kamata ace sai da safe za su tafi, amma kuma bata ce komi ba, ta saka Shadda maroon Colour da aka sake kawo mata, sai dai ɗinkin doguwar riga ne da ya ji aiki sosai daga saman ƙirjin ta kawai, Suhaima tayi mata light make-up sannan ta ɗaura mata ɗan kwalin, irin me Steps ɗin nan, sai ta yafa mata farin gyale a kafaɗan ta, sannan ta ciro mata takalmin ta me tudu me haɗe da jakan sa, kalan Baby maroon Colour, sai ɗan ratsin fari a jiki, ƙasan takalmin kuma baƙi ne.


Tare suka fito Parlour inda suke murmushi dukan su, kasancewar Suhaima tana faɗa mata yanda tayi kyau ne, wai "Yaya Ray zai zauce idan ya ganta". Shi ne take murmushi itama tana taya ta


Tunda suka fito Parlour'n ya sauke idon sa kanta, kallon ta kawai yake yi tamkar idanun sa za su faɗo, shima sanye yake da kalan shaddar ta, yayi mugun kyau sosai


Ita ma bata hange sa ba, tunda gaba ɗayan su ne suke zaune a parlour'n, shiyasa tunda tayi musu kallo ɗaya ta ɗauke kanta


Ammee tace mata, "ta ƙariso wajen ta".


Inda ta zauna a gefen ta, Ammee na riƙe da hannun ta


Su Zannurain sai faman tsokanar ta suke yi suna ce mata "Matar Yayan mu".


Ita dai sai murmushi take yi


Sai da Uncle ya dakatar da su sannan suka yi shiru, ya soma musu nasiha daga ita har shi ɗin, sannan suka saka musu albarka har Ammee, suka yi musu addu'an zama lafiya har ƙarshen rayuwan su, tare da samun zuri'a ɗayyiba


Gaba ɗaya wajen suke amsa wa, ban da su da suke amsa wa a zuciyar su.


Har waje suka rako su inda za su shiga mota, RAUDHA da Suhaima suka rungume juna har da hawaye


Faruk ya ja motan, su kuma suna zaune a baya, tunda suka shiga ko motsi ba ta yi bare ta ɗago kai ta kalli Ray ɗin, duk da kuwa tana jin sanda ya lalubo hannun ta ya riƙe gam


Tafiya suka yi kamar na mintuna sha biyar, sai suka tsaya, horn akayi suka shiga wani gida, ashe a nan ɗin za su kwana zuwa gobe su wuce Kaduna, Gidan Ray ne da Uncle ɗin sa ya ba shi, ko da wataran sun zo a nan za su riƙa sauka.


Sai da suka fito sannan RAUDHA ta ware idanun ta tana kallon gidan, a ranta tana mamakin kenan ba Kaduna za su koma ba? Sosai gidan yayi mata kyau duk da babu wani yalwataccen haske, haraban gidan ba wani faɗi bane, amma zai iya cin motoci kamar biyu haka, sai kuma yanda aka yalwata ko ina da flowers masu ban sha'awa da abubuwan more rayuwa


Sanda suka shiga parlour'n ne, ai sai kallo ya koma sama, domin babu ƙarya, ba ƙaramin kuɗi Daddy ya kashe wajen tsara mata gidan nata ba, ƴar gatan Daddy kenan, gida biyu duk ita kaɗai, kuma an kashe kuɗi ba Ni da kuɗi ba, ɗakuna uku ne da Toilet a cikin su, sai Parlour da kichen tare da store, ko ina yayi kyau matuƙa tunda duk an cika su da kaya masu ban sha'awa, gaba ɗaya babu kayan Nigeria a gidan, shiyasa komi zai ba ka sha'awa da zaran ka kalla.

Tun a waje suka yi sallama da Faruk ya koma, su biyun suka shigo. Suna shiga ya sake riƙe mata hannu, hakan yasa ta juyo tana kallon sa tunda ita ce a gaba, murmushi suka sakar wa juna, inda ya matso kusa da ita yana faɗin, "alhmadulillah! Yau dai ga Pretty a gidan Captain Rayyan, sai godiyar Allah".


Murmushi kawai tayi masa, batare da ta ce komi ba idanun ta a kansa


Janyo ta yayi ya jingina ta a jikin sa, sannan suka taka har zuwa cikin parlour'n, ya zaunar da ita yana me zama gefen ta, hannun ta still ya riƙe yana me jan yatsun hannun, ita kuma tana bin hannun da kallo kamar yanda yake yi

"Ina son ki pretty, ban San ya zan kwatanta miki ƙaunar da nake miki ba a zuciya ta, amma kuma zan so ki bani dama domin nuna miki tsatsan sa a fili, ina fata Allah ya bar mu tare har ƙarshen numfashin mu".

"Amin Ƙalby". Tafaɗa tana kallon sa

Murmushi suka sakar wa juna kafin tace, "I love You more than you Ƙalby". Ta ƙare maganar da jingina a jikin sa


Hannayen sa ya saka gaba ɗaya ya rungume ta yana me sumbatar goshin ta, sun ɗau kamar mintuna biyar a haka, kafin yace, "Pretty ko kina jin barci?"

Ɗago kanta tayi tana kallon sa, kafin ta girgiza masa kai tana cewa, "na yi tunanin yau za mu koma Kaduna?"

Fuskar ta ya shafa yana bata amsa da faɗin, "a'a, Uncle ya ce mu zauna a nan sai zuwa gobe, sabida ba ya son tafiyan dare".

Gyaɗa kanta tayi tana me mayar da kanta ta sake ɗaura wa a kafaɗan sa

Ahankali ya matso da bakin sa setting kunnen ta ya raɗa mata magana, sai ta ɗago tana kallon sa, suka sakar wa junan su murmushi. Tashi yayi yana tayar da ita, sannan ya ƙarisa bakin ƙofa ya rufe, ya dawo ya riƙe mata hannu suka yi cikin ɗaya daga cikin ɗakunan


Koda suka shiga alwala suka ɗauro gaba ɗayan su, inda ya sauya kayan sa zuwa jallabiya, itama ta sauya zuwa riga da wando na barci, ta saka Hijab suka soma jero salloli, kawai don godiya ga Allah, kamar yanda Ray ya alƙawarun ta, duk randa ya mallake ta a matsayin matar sa, to fa a ranan zai kwana godiya ga Allah ne, duk da sosai yake jure buƙatar sa a gare ta, amma kuma soyayyar da yake mata ya fi rinjaye a zuciyar sa a bisa sha'awar ta, don dai kwana ɗaya kacal zai iya jure wa, ya cije don ganin be mata komi ba. 😆 Kaji masoyan asali 😍😴Tun suna yi har barci ya soma fizgar RAUDHA, dole ta kwanta a kan daddumar ta soma barcin

Shi kuma ya ci gaba da yi har sai da ukun dare yayi, sannan ya ɗauke ta ya mayar da ita kan gado, yana me zame mata Hijab ɗin, a gefen ta ya kwanta yana ta faman kallon ta yana lazimi, tare da tsarkake Allah da yayi wannan kyakykyawar halittan, RAUDHA tana da kyau matuƙa.


har sanda aka kira sallah, sannan ya tashi yayi nafila, ya tashe ta suka yi sallan asuba, a tare suka koma barcin har zuwa safe.Sai da Abubakar ya kawo musu breakfast sannan suka tashi a lokacin, shima be tsaya ba ya koma tunda ya gaishe su, saboda aiki zai tafiƘarfe 09:00am jirgin su zai ɗaga, shiyasa suka yi saurin shirya wa suka karya suka baro gidan, suna hawa jirgi sai Kaduna garin gwamna Nasiru El. Rufa'i. Me aiki domin ci gaban al'umman sa. Ba ya bari a ci sai dai a gani a ƙas..


_______📖 Zan iya cewa komi na gidan nan ɗaya yake da wancan, sai dai banbancin colour da kuma haɗuwa, amma tsadan su ɗaya, wannan dai ya fi haɗuwa sosai, akasarin komi fari aka saka mata shiyasa yafi ɗaukar ido da burge wa.+


      A gajiye suka shigo gidan, don haka sallah suka soma gabatar wa na azahar da asar, sannan Ray ya aiki Drever'n sa don ya yo musu take-away, kafin ma ya dawo har RAUDHA ta soma barci, sabida ba ƙaramin barci take ji ba


Tashin ta yayi yace, "ta zo su ci abinci".


Daƙyar ta tashi tana ɓata fuska, gaba ɗaya tayi yaushi sabida barcin ya rufe mata ido, zama tayi gefen gadon, ta dafe gadon da hannayen ta tana me lumshe idanun ta


Ahaka Ray ya fito daga Toilet ya sake tarar da ita har barci ya soma ɗaukar ta, ruwan hannun sa ya yarfa mata yana me faɗin, "Baby wake-up mana".


Buɗe ido tayi ta ɗan kalle sa kaɗan da idanun ta da suka sauya kala, sai ta ɓata fuska tace, "Ka bar Ni inyi barcin don Allah, ba na jin yunwa".


"Ban yarda ba, ke dai kawai ki ce barci kike ji, amma ba wai ki ce ba kya jin yunwa ba. miƙe kin ga idan kin ci sai ki koma ko?" Yayi maganar yana me lallaɓa ta


Turo baki tayi tana sosa kanta, sai kuma ta miƙe tana nufan ƙofan zata fice


Riƙe ta yayi suka fita Parlour, ya zaunar da ita saman kujera, sannan ya wuce kichen don ɗauko Plate


Jingina tayi da jikin kujeran tana me lumshe idanun ta, har ya dawo ya sake abincin bata motsa ba, shi da kansa ya bata abincin tunda ta ƙi ci, yana ta faman lallaɓa ta, sai daga baya ne ta Ware sosai taci tunda tana jin yunwa


Sai da suka gama yace mata "ta koma ta kwanta, shima fita zai yi".


Bedroom ta koma ta kwanta akan gado, babu jima wa barci ya ɗauke ta


Shi kuma sai da yayi wanka ya shirya cikin manyan kaya, gezna ne me ruwan kore, amma Light ne, ta sha aiki sosai har da babban rigan ta, sai dai be saka babban rigan ba, ya murza hulan sa mu haɗu a banki, sannan ya feshe ko ina nasa da turaruka, sak ya fito a Angon sa sai ƙyalli yake yi, fuskar sa na fid da annuri, keey ɗin mota ya ɗauka tare da wayan sa, ya matso gadon yayi mata kiss a leɓen ta, sannan ya shafa kanta yana murmushi a ransa yana aiyana abubuwa da dama. Fita yayi ya hau motan sa ya nufi gidan su RAUDHA


A can ya wuni wajen Daddy, har magriba be dawo ba, sai da RAUDHA ta kira sa tana masa shagwaɓan "ya bar ta ita kaɗai" sannan ne yayi haraman taho wa, da zai dawo sai da ya biya ya siya kazan amarcin sa, don yau so yake yi ya zama cikakken Angon sa


Da fara'an sa ya shigo gidan, inda ta tarbe sa tana me rungume sa tana faɗa masa "how much she missed him" kafin ta amsa kayan hannun sa tana me ƙara masa sannu da zuwa har da duƙawa alamun girmamawa


Sosai Ray yaji daɗin tarban nan da tayi masa, har ya kasa ɓoye wa ya janyo ta jikin sa yana cewa, "Baby ashe kin iya tarban miji haka? Gaskiya zan sha mamaki ashe, gaba ɗaya ina miki kallon wacce dole sai na koya mata irin waɗannan abubuwan na kula da miji".


Kallon sa tayi ta ɓata fuska kafin tace, "kenan kana nufin ban iya ba?"


"No Ina nufin dai abubuwan nan na Hausa wa nake son koya miki".


Taɓe baki tayi tace, "Ok na gano ka, wai don na amshi kayan hannun ka?"


"Yes ashe kin gane". Yayi maganar yana murmushi


Turo baki tayi, kafin ta kamo hannun sa tace, "to amshi kayan ka, bazan sake ba".


Dariya yayi sosai yana son ƙwace hannun sa da take tura masa ledan sai ya amsa, cikin dariyan yace, "sorry Baby, bazan sake ba, wlh suɓutan baki ne, ai na san duk wanda ya koyi ilmi dole zai san wannan, amma kuma.."


"Amma kuma me?.." tayi maganar tana tsare sa da ido


"Bar shi kawai ya wuce, bari in je inyi sallah ana kiran Isha'i, ki je ki ajiye ledan please".


Bata ce mishi komi ba ta juya da ledan a hannun ta


Shi kuma ya fice zuwa Masallaci.


          🔵🔵🔵


        A wannan dare ne Ray ya tabbatar wa kansa, RAUDHA cikakkiyar mace ce, ba kamar yanda yake mata kallo ba, be taɓa tunani ko a mafarki zai iya samun ta a yanda ya same ta yau ba, sai ga shi ya sha matuƙar mamaki, har kuka yayi sabida nadaman abinda yayi mata, tabbas yau yayi dana-sani, dana-sanin abubuwan da yayi mata, da kuma sanya zargin ta a zuciya, ba don soyayyar ta tayi masa kamu ba, da tuni ya daɗe da rabuwa da ita, duk a sabida yana mata kallon mazinaciya


Wannan ranan ta zo masa a matuƙar farin cikin da bazai taɓa manta ta a kundin rayuwan sa ba, ya kuma sake neman yafiyan ta sosai, tare da nuna mata nadaman sa


Dama wannan ranan take jira, kuma ga shi ya zo mata yanda take so, yau Mijin ta zai dena mata kallon ballagaza har a cikin zuciyar sa, ko da be nuna ba, tayi imani da Allah duk da yayi mata alƙawari, da ace ba haka ya same ta ba, dole sai ya riƙa kallon ta da abun, kuma hakan zai iya kawo saɓani a auren su, abinda yasa ta sake amince wa da auren sa, saboda ta nuna masa kuskuren sa, ta san cewa da ta aikata Zina kafin auren su, to, baza ta taɓa amince masa da auren su ba, domin kuwa ta san zargi shi zai riƙa yawo cikin auren su.


Alhmadulillah zaman auren su suna gina ta ne ta santsan kulawa da nuna tattali da soyayya, Ray ya dage yana ta gurzan Angon cin sa yanda yake so, hutun sati biyu aka ba shi a wajen aiki, kullum yana gida be fita ko ina, yana liƙe da Matar sa har sai da ya cinye kwanakin nan, sannan ne ya soma fita, kuma kullum duniya aika wa yake yi ayi musu take-away, sai daga baya ne aka turo Saude don ta riƙa mata aiyukan gidan, shiyasa RAUDHA babu abinda take yi yanzu sai zaman hutu da kuma tattalin mijin ta, duk hanyar da tasan zata faranta masa tana yi sosai matuƙa, duk da a yanzu tana buƙatar koyan girki itama don ta riƙa mishi, sabida ta san ladan da ake samu, shiyasa take kwaɗayin komi na gidan ta ace ta iya, a sannu- a sannu Saude take koya mata wasu abubuwan, irin su gyara gado da kunna Kuka gas, da dafa ruwan zafi, coz tunda take bata taɓa shiga kichen da sunan girki ba, bata ma san yanda ake kunna Kuka gas ɗin ba, sai yanzu da ta soma koya. Alhmadulillah tana ɗan gane wa kaɗan, duk da kasancewar ta me saurin gane abu, amma kuma sosai take shan wahala, domin sanda aka soma koya mata gyaran gado, sai da aka shafe wajen sati biyu ana abu ɗaya, daƙyar ta samu ta iya, idan kuma tayi dole sai ka gane ba gwana tayi ba.


     Shi Ray dariya yake yi duk sanda ya zo ya tarar ana koya mata irin waɗannan abubuwan, wai kamar ta har shara sai an koya mata, to riƙe tsintsiyan ma ba yanda ake yi take yi ba, to ana haka ne ta soma ciwo gadan-gadan, faraɗ ɗaya ciwo ya kamata me tsananin gaske, wanda har sai da aka dangana da asibiti, duk a tunanin su ciki ne, amma kuma abun mamakin ba shi ne ba, kawai ciwo ne dai take fama dashi, daga tace ciwon kai, sai ta ce cikin ta na mata ciwo, to duk dai ba'a yi tunanin wani abun bane, haka ake kula da ita, tsawon sati ta ɗan samu sauƙi kafin suka koma gida

      A ranan da suka koma kuma, sai ga shi cikin ta ya murɗe mata da ciwo me tsananin gaske, lokaci ɗaya jini yayi ta zuban mata


Hankalin Ray ya tashi tsantsa, haka ya sumgume ta sai asibiti, abun mamaki da al'ajabi, wai ɓari tayi, su kan su likitocin sun sha mamaki, domin kuwa basu gano tana ɗauke da ciki ba, amma kuma sai ga shi ciki suke gani tayi ɓari


Hakan da Daddy yaji, sai kawai tunanin sa ya basa tabbas akwai matsala, dole su dangana dana Islamic, ko za'a iya gano abinda ke faruwa. Malamin da suka nema mata magani a baya shi suka koma masa, kuma shi ya basu magani a wannan karon, domin ce musu yayi, "tabbas har yanzu akwai aljanun nan suna bibiyan ta, kuma sun yi alƙwarin sai sun cutar da ita, kuma su ne suka ɓoye cikin, daga ƙarshe suka zubar mata, domin su ne suke saka ta ciwon nan, dole sai sun tashi tsaye da yin addu'a da neman magani, ta hakan ne kaɗai za a iya tsira daga kaidin su".


             To tun daga ranan, ba su zauna ba, an ci gaba da nema wa RAUDHA magani, sannan itama tana yi sosai, tana kiyaye duk abinda zai jawo su gare ta, sallan dare kuwa tun bata saba ba, idan Ray ya tashe ta su yi, har yanzu ta saba, tare suke raba dare suna ibadan Allah, sai ga shi har azumin Litinin da Alhamis idan ta samu iko tana yi


Alhmadulillah sun ga sauyi sosai, domin lafiya yanzu babu abinda ke damun RAUDHA tunda ta samu wannan cikin, bata ƙara yin ciwo ba, har sanda ya soma girma suka soma zuwa awo


A lokacin ne kuma Ramcy ta haihu ɗiya mace, zo ku ga murna wajen RAUDHA tamkar ita ce ta haihu, musamman yanda ranan suna suka bata bazata, yarinyan taci sunan ta RAUDHA, tayi farin ciki tsantsa har da kukan ta, tabbas ta san cewa Ramcy na matuƙar ƙaunar ta, baza ta taɓa yin ƙawa kamar ta ba, duk da a yanzu ta zame mata ƴar uwa rabin jiki.


       Abubuwan da akayi a sunan RAUDHA, da suke kiran ta, Little RAUDHA, ba ya faɗuwa, Daddy, Suhaib da kuma Ray, sun Yi bajinta sosai a sunan nan, babu abinda basu yi ba, duk abinda ake wa ƴar gata Ramcy da ɗiyar ta sun samu, ita kanta RAUDHA abun da tayi ba a magana.


      Wata huɗu da haihuwar Ramcy, itama RAUDHA ta haihu ɗiya mace, yarinyan sak Mahaifiyar ta, tamkar dai tayi kaki ta tofar, sai dai ita bata da irin hasken nan jawur tamkar zabiya irin na RAUDHA, hasken ta irin na Ray ne. Ranan suna taci sunan Maman RAUDHA, wato Ruƙayya suna kiran ta Iman.


      Rayuwa kenan, sai ga RAUDHA da ɗiya, tamkar dai ba ita ba idan kuka duba rayuwan ta na baya, sai ga shi itama ta samu wacce zata riƙa wa faɗa, domin dai yarinyan tunda ta soma wayau halin ta ya bayyana tamkar RAUDHA, ko kaɗan ba ta ji yarinyan, ga taɓara kuma baka isa ka hana ta ba, tana da taurin kai irin uwar ta, don har ta ƙere ta tunda akwai ta da zuciya, yanzu da za su yi mata faɗa, ta dinga kuka kenan har sai ta kwana tana naci, kuma baza ta ci abinci ba saboda ita a ganin ta sun ɓata mata rai, gaskiya Rayyan da RAUDHA suna fama da Iman, sai dai nema mata shiriya suke wajen Allah, tare da dage wa wajen sun ga sun bata tarbiyya me kyau.


       Shekarun ta huɗu cif, RAUDHA ta sake haihuwa, wannan karon namiji ne, inda ya ci sunan Uncle, wato Hassan, suna kiran sa da Aslam. Watan shi bakwai sai ga RAUDHA da wani cikin, nan RAUDHA ta haukace "wai baza ta ƙara yarda ta haihu yanzu ba". Tun Ray na lallaɓa ta har dai ya gaji ya kai maganar wajen Daddy, shima Daddy duk rarrashin duniya yayi mata akan ta bar cikin, amma ina ta ƙi, wai bata san zancen ba, tunda a lokacin so take yi ta koma school, sannan tana son soma aiki a Companin Daddy da ya buɗe domin ta, ƙaramin Company ne irin kayayyakin mata na kwalliya, da suturu, har da na ƙananan yara duk akwai, kuma nan ba da daɗe wa ba ake son kawo injina waɗanda za su iya haɗa kayayyakin a Companin, ba sai an je ƙasashen waje an siyo ba, tunda dama daga can ake kawo komi, kyauta Daddy ya danƙa mata, inda aka saka wa Companin sunan Ta, *RAUDHA M.M Company.*


Ƙarshe dai sai da suka yi faɗa sosai akan wannan maganar, RAUDHA fa sosai ta tubure sai ta  zubar, har tayi yaji ta koma gida


Ran Daddy be taɓa ɓaci ba akanta, sai wannan karon, amma kuma sai ya danne yayi mata nasiha tare da nuna mata illan yin hakan, amma tamkar zuga ta ake yi, har Suhaib sai da ya zo musamman ya bata haƙuri ta koma gidan ta, ta haifi cikin ta, ganin dai rarrashin bazai mata ba, dole suka nuna mata ɓacin ransu, kuma Daddy yace, "muddin ta bari cikin nan ya zube, ko ba da sanin ta bane, wlh sai yayi mummunan saɓa mata, daga ranan zai cire hannun sa a komi nata".


Ba ita kaɗai ba, har ta Suhaib yayi mamakin furucin Daddy, amma kuma babu damar magana tunda tuni ya bar wurin da ɓacin rai.


     A ranan RAUDHA ta haɗa komi nata ta koma gidan Ray, dama acan ta bar Iman, sai ta taho da Aslam. A ranan kuwa kowa sai da ya ga fushin ta, daga yaran har uban nasu, domin gaba ɗaya ta ɗauke wa Ray, ko magana ba ta masa, Iman kuwa duk ɓarnan da zata yi, kamata take yi ta duka kamar jaka, haka ma Aslam, sai ya gama jiga ta da kukan yunwa kafin take kama shi ta bashi nono ya sha, a ranan ma ta sami Ray yana zaune a ɗaki, tace masa, "gwara ya nemo masa abinci, don daga yau baza ta sake shayar dashi ba" haka dai ta ƙarishe haukan ta ta tafi, duk dai neman hanyar da za su yi faɗa tsiya-tsiya take so


Shi Ray idanu kawai ya zuba mata yana kallon ikon Allah, domin wlh tausayi take ba shi tsantsa, har yanzu gani yake yi aljanu ke juya mata ƙwaƙwalwa wani lokacin, domin abubuwan da take yi me hankali kamar ta bazai yi ba, shiyasa ya zira mata idanu, duk hanyoyin da ta ɓullo na tsiyan ta, ba ya biye mata.


      A haka rayuwa taci gaba, inda har ta samu ta haihu ɗiya mace, har kuma lokacin ba su shirya ba, domin har yanzu RAUDHA gani take yi duk abinda Mahaifin ta yayi mata a wancan ranan laifin Ray ne, inda be kai ta ƙara ba, babu ta yanda mahaifin ta zai mata abinda be taɓa mata ba


Yarinya taci sunan mahaifiyar Ray, Hansa'u, za su kira ta da Islam.


        A taƙaice dai daƙyar Ray ya samu suka shirya da RAUDHA, inda suka koma kamar da, amma da sharaɗin dole za su yi family planning, sai nan gaba za su sake haihuwa, babu yanda zai yi haka ya amince mata, tunda dai yana ƙaunar ta.


      Alhmadulillah yanzu komi ya wuce, inda RAUDHA ta soma zuwa makaranta, kuma tana zuwa Company, kasuwanci sosai take yi, a gida da kuma wajen aiki, lokaci ɗaya Allah yasa mata albarka, sai ga shi ta zama wata Hajiya, tuni ta jawo Ramcy cikin Companin, tare suke yin komi, kuma tare suke saka hannun jarin su, itama yanzu Ƴaƴan ta uku ne, duka mata.


       Fannin Farida ma yanzu ta koma aikin ta, tare suke zuwa da Suhaib, yanzu yaran su haɗu ne su ma, ban da Haneep da Abdul, yanzu sun ƙara haihuwar me sunan Maman Suhaib, suna ce mata Ummee, sai Meenal Auta, wannan sunan sun saka mata ne kawai saboda suna so, amma ba sunan kowa ba ne.


      *TAMMAT BILLAH. ALHMADULILLAH! ALHMADULILLAH!! ALHMADULILLAH!!!*


_Duka-duka anan na kawo ƙarshen littafi na me suna RAUDHA, abubuwan da na faɗa dai-dai Allah ya bani ladan su, abubuwan da na faɗa ba dai-dai ba kuma, Allah na roƙe ka, ka yafe min, albarkacin wannan wata me falala. 🙏🙏_


Post a Comment for "RAUDHA CHAPTER 11 KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...