NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

- - Post a Comment

 NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELIWww.bankinhausanovels.com.ng 

A JIYA MUN TSAYA 

To babu laifi, Allah ya zaba mafi alkhari. Idan an samo sana’ar sai a sanar damu mu taya Murna. Tashi kaje” 

ZAMU TASHI

******

Garin Kano garin kasuwanci, unguwar kurawa unguwar sarakai. kuma unguwar maķotaka da kasuwar rimi bakin asibiti. - An ce duk mai makotaka da kasuwa baya tsiya, amma da alama wannan Kaulin ya tsame Adamu ciki, domin a Kurawa aka haife shi, ya girma a cikinta amma yau ya laluba sana’ar yi ya kasa ganowa ko kuma ita ta kasa ganinsa, - saboda haka kamar makotaka da kasuwar ta kasa yi masa rana. ° Bayan alhinin awa daya kacal~ wanda yayi bayan turin je-ka-ka-mutun da Alh. Yayi masa, ya dawo gida ya dinga cakuda rayuwa da mutuwa a hakuri da son Husna da kuma sauran rayuwarsa, da kyar ya wafto jarumtar tashi ya “nemo sana’a don kar ya mutu a matsayin ragon soyayya da rayuwa, tunda aikin malam ba lallai nan take zai ci ba.

Www.bankinhausanovels.com.ng Amma kaico! Kwana da yini kenan ya kulla lissafin sana’o’I sun fi a Kirga amma har yanzu ya kasa fitar da amsar ko guda, ba don rashin iyawa ko rashin sanin makamarta ba face don wadanda suke da saukin samu shi sam! Basu dace das hi ba kamar dai yadda me markade bai dace da zama mijin Husna ba. - Ya yarda tun daga yammacin jiya bayan sallamar da yayansa yayi masa’ kawo yammacin yau, Kwakwalwarsa ta fara karatun nemo mafita, hartayi digirgir amma ta fito fanko! » Kwance yake rashe-rashe kan ‘doguwar kujerar dakinsa da yammacin ranar cikin tunani a halin yanzu, sai gashi a halin zahiri an - wangale kofar dakinsa an shigo “Ho! Gayun gidan nan suna kusa?” Wani shegen takaici ya Kume shi, amma ya shanye shi ya dago kai ya dubi mai  shigowar lokaci daya kuma zuciyarsa ta rubuta ~ wata addu’a tana biyawa, “Ya Allah ka tsari gatari da saran shuka, Ubangiji ka tsare ni ko hada hanya da gajeriyar mace bare ta kai ga gina mata gida in ajiyeta Www.bankinhausanovels.com.ng  matsayin matar aurena, Allah ka san ni baki ne, amma bana son macen da ta fiye baki Allah ka. tsare ni da ita. Idan na ga-‘ya’ya masu idanuwa _ dakwa-dakwa Allah ka sani har jaje nake wa iyayensu to Allah ka tsare ni da macen da zata haifa min irinsu. Duk mace mai saurin murya * bana Kaunarta, Allah ka san wannan in ka jarrabe ni da irinta zuciyata zata iya fashewa.... Gaba daya Allah ka san doguwar mace nake so wankan tarwada mai, kyakkyawar fuska da kyakkyawan murmushi bana son mai yake, ina son mai kyawawan idanu mai dogon gashi, mai fara’a in so samu kuma mai suna Husna.... ita nake so, Allah ka mallaka min kayi min tsari da wannan da take tsaye a gabana yanzu’”’. . Salma ta Karasa shigowa dakin sosai tana nazarinsa tamkar wani baKonta. Dakin ya wadata da duk wani kayan more rayuwa daidai - matashi mai matsakaicin rufin asiri irin Adamu, Dakin na shimfide da shudin kafet, akwai dindimemiyar katifar sauko mu gaisa daga can_ Kuryar dakin wadda ta cika da shirgi kama da bargo kayan sawa wankakku da masu dauda Www.bankinhausanovels.com.ng litattafai har da wasu allunan rubutun sha guda biyu kamar yadda suke watse ciki da gefen akwatunan dake jere a nasu gefen ba. Daga wani gefen kuma ga fakej din kayan kallo masu dirma-dirman sifiku da kuma . Karamin firji a gefe. komai dai a dakin baya cikin hayyacinsa duk kyau kuwa da tsadarsa, can kwalbar turare nan filasan abinci, can bel nan kwalaben lemo. Abu bako a idanun Salma .*cikin dakin shi ne, wata shimfidaddiyar sallaya daga can bangaren gabas a karshen dakin “sannan ga wani jibgegen carbi zaune kan sallayar yana shan nasa sharafi. Kodayake iyakar sanin da tayi wa Adamu ma’abocin son ibada ne wato sallah akan lokaci da kuma yawan nema a wajen Allah, idan duk halayensa na kushewa ne to tabbas a nan bangaren ya sami na yabo. Ta dade da sanin Adamu tun suna yara, in dai yana jarabar son abu, to ya dinga kafa' goshi yana fadawa Allah kenan ba dare ba rana.  Lokacin da yake neman tsarin Allah da ita cikin zuci, ita kuma daidai lokacin take nazarin dakinsa sai akayi sa’a suka gama kusan lokaci daya guda, kuma kamar masu tseren Magana suka dago suka fuskanci juna, —_ “Ke matsalarki fadowa dakin mutane babu . Sallama” Ya riga ta Magana cikin matukar daure | fuska. | Duk da kusan a tare suka yi maganar ita ma ce masa tayl,“Lafiya kai da dakin naka na ganku duk a hargitse?  Dayake kafin ta dire taji nasa furucin sai ta zarce da amsa masa, “Au yanzu ban yi sallama ba na shigo? Kawai dai ka ce baka ji ba ka lula cikin tunani’.na |Haba ya ji kamar zai tura mata ashar, amma ya matse ya kawar da kai, “kin manta ne, ai ba daki kika shigo ba, Turu kika shigo... : Ta wuce ta zauna kujerar dake kusa da kafarsa tana dariya, : Allah ya baka haKuri Akaramakallahu... Ya tare ta a Kufule, don bai gama fanshe maganar data sosa masa gyambo a kirji ba Www.bankinhausanovels.com.ng “Tunanainki? To Kila ma ni gabadaya baa  halicce ni da zuciya ba bare a bata lokacin da zata bata wajen tunaninki” Salma ta katse shi cikin dariya da mayar da komai ba komai ba, “Kar ka damu, tawa zuciyar ta ishe mu tunana komai da ya shafe mu, yadda nake bata lokaci wajen tuna ka haka nake. Bata lokaci wajen tuna maka kaina......” -“Ba na son iskanci da wulakanci Salma... Ya sake tare ta.a zafafe saboda tsakani da Alla hadiyar bakin cikinta ya fara gagararsa. Salma ta shafe sama da minti biyar tana dariya cikin kallonsa kafin ta shanye dariyar cikin goge hawayen da dariyar ta samar mata. Ta jima tana kallonsa a nutse sannan ta tanka, “Komai ya ji a kai Adamu, gaye har gaye matsalarka daya baka san wasa ba. Wai kai a zatonka ko daura min kai a Kafa aka yi zan ja? Ai gara na yanke kafar ko ta katako ce na aro na yafa” Ya tashi zaune cikin rage damuwar fuskarsa | yana sauke numfashi, Www.bankinhausanovels.com.ng Ai kece kike neman zunguro wa mutane sama da kara, ‘yar wannan rahar da kike kin janyo manya sun sa mana ido, suna zaton son juna muke. Abin ma sam babu tsari, ko ina zan dauki gundumemiyar mace irinki in kai a matsayin mata?”’. - Duk kawaici da kai zuciya nesa irin na Salma sai da wannan maganar ta Adamu ta  Bata mata rai, don haka ta jima kafin ta gama hadiye ta. Cikin murmusbin yaKe ta ce, “Kar ka damu, kai zaka samo wanda zai iya daukar irina a matsayin mace ka aura masa, na san Kila kai ne waliyyin don haka in ka tashi tallatani sai ka dinga  cewa, Baka ce kuma gundumemiya™ Adamu ya dan yi saroro da jin wannan bakar maganar tata, amma dai ya takura fuskarsa kar ta bada maza, sai ma ya kada kafada nuna halin ko-in-kula, | “Ba ba’a ce ta kar uwar gizo ba Karar kwana ce, ni ba kushe ki nayi ba, ainihin halittarki na fada menene na jin haushi na? in ni-baki yi min a matsayin matar aure ba wani ai yana nan yana cin layar in ba ke ba sai rijiya”Www.bankinhausanovels.com.ng Salma ta so ta hasala, amma sai ta binne da Siyasa, “Haushinka na ji Adamu?” “Ni bana son janjanin magana don Allah” To an bar maganar’ Ta fada cikin saduda sannan ta koma bin dakin da kallo’ kusurwa bayan kusurwa musamman shimfidar sallayarsa mai jibgegen carbinsa a kai. Adamu na biye da ita da nasa idon tamkar yana gadinta ne, zuciyarsa a Kuntace domin yaĶinin wannan kallon Allah tsine uwar mai Karyar da take wa dakinsa sai ta jangwalo abinda sam bata da ruwa a cikinsa. Don haka ya katse mata hanzari, “Kin ga malama duk maganar da zata fito daga bakinki ya zamana ni da ke duk muna da hakki a cikinta, idan ba ruwanki ko ba ruwana to kar ki kawo mana ita, ato!”  Ta sauke ido a kansa cikin murmushi tana jin ciwon hanzarinta da ya katsewa  Idan ba idonta ke gizo ba a can kusa da jibgegen carbin nan ta hangi kwalbar turaren wurudi, cike take da fargaba amma dokokin Adamu na mata Www.bankinhausanovels.com.ng  burkin tambayoyin da zata fanshe, dole ta tattare ta hadiye da cin alwashin jiran wata haduwar kafin ya kafa dokar. Ta ciro Jakarta da ke rataye a kafadarta ta zaro wasu kyallaye guda biyu na les da na atamfa ta mika masa, Amina Kawar nan tawa! To bikinta ne ya taso saura sati biyu, wannan anko ne na kawo ka sai min, kunyar Alh. nake ji wallahi kullum na dinga damunsa da dawainiya”’ Da Adamu ya kalle ta sai ya. fahimci tsakaninta da Allah take Magana, don haka ya yayyafawa ashar din da ke turereniyar -fitowa daga makogwaronsa ruwan salama ya hadiye su. Yana bin hannunta da kalllon gefen ido ya ce,“To ajiye su nan, dama jiya-jiyan nan na siyo sabuwar Gariyo tare da AK 47, dare kawai nake jira ya tsala na fita” Duk da ta gane baKar maganar-da ya cinna mata sai tayi fuska, .“Ban gane nufinka ba” Kafin ta rufe baki ya mayar mata,Www.bankinhausanovels.com.ng dama kin zo ne ki gane nufina ko kuma dan na sai miki anko?” - “Anko ya kawo ni_ Ta fada a sanyaye. Ya nuna mata Kofa, “To ki ajiye ki je za a siyo’ Ta bi umarninsa ta hanyar miKewa tare da yi masa sallama, amma maimakon ta nufi Kofa kai tsaye sai ta zarce kan sallayar nan ta sunkuya ta dauki turaren wurudin nan ta hau sunsuna. | Adamu ya Kara cin magani ya kawar da kai daga kallonta, can ta juyo ta dube shi, tana -kallon fuskarsa ta tabbatar ashar dinsa a kan harshe take Karamin motsi bakinsa yake jira ya antayo ta waje. Ta so su hada ido ko dan ta gasgata zatonta, ' daya Ki-sai ta haKura tare da ajiye turaren ta juyo a sanyaye kai tsaye kuma ta nufi Kofa ta. fita ba tare da ta sake tankawa ba. A soro ta tsaya domin bawa Kwallar da ta cika cikinta dammar fitowa  Wani iri mugun ciwo ne ya kama Kirjinta? Ta tambayi kanta ba tare da sa ran samun amsa ba Www.bankinhausanovels.com.ng don ta sha kai wa kirjin nata duk wani lissafi a akan Adamu. Adamu ban da son’ sallarsa kulliyarsa bai cancanci a so ba, ashe ma bayan wannan ita kanta bai dauke ta a matsayin mace _ ba, Baka gundumemiya, wannan ce inkiyarta a — wajen Adamu wanda ta kwashe shekaru da saninsa saboda haka ta ga ko wane irin aibu nasa daga halittar jiki zuwa hallitar hali amma dukda haka ko kadan Kirjinta bai ji rauni a sonsa ba. | Ta ci kuka mai hadiye shassheKa a ciki sannan ta goge hawayenta daidai lokacin da zuciyarta ta cilla lissafin Adamu da zabgegen carbi hadi da turaren -wuridi, nan da nan kwanyarta ta rushe da canki-cankin Allah ya sa ba zargin da zuciyarta tayi ya tabbata da Adamu ba.  Tana cikin share hawaye Adamu ya fito daga dakinsa da nufin shiga cikin gida. Ya kula hawaye take tana sharewa, amma sai ya basar, “Au ashe ke ce baki tafi ba, haba tun dazu  nake jin kwashar-kwashar”’.Www.bankinhausanovels.com.ng Ta fara girgiza kai cikin rudewa da kokarin kwato furuci daga kwanyarta, amma ya gagara  Kawai sai ta sa masa ido da kallon Kurilla. Suka yi kallon-kallo tamkar kowa na hango cikin zuciyar kowa, amma shi sai ya basar ta hanyar kawar da kai yayi fuska, * “Ina abincina, kin taho min da shi?” Ta amsa da kyar cikin numfarfashi tana nuna masa cikin gida, ~“Tun dazu Sajida ta kawo maka ina tsammanin ba ta san kana ciki ba ta kai wa Hajiya” Ya kada kai ya wuce cikin gidan ba tare. da ya tanka mata ba, ita kuma ta bishi da kallo zuciyarta na kade-kade iri-iri wanda ko daya gangar jikinta ta kasa zabar daya ta taka masa -rawa, sai daga Karshe ita ma ta zabi kada kai ta fice tana Kara goge hawaye. 

******* 

Yana ta faman wurga loma tamkar mai shiri hadawa da harshensa ya hadiye, idan ya ajiye cokali kuma kafin ya cinye na bakinsa sai ya Www.bankinhausanovels.com.ng  cafko carbinsa ya hau ja hannunsa na  hagu kuma mafici ne yana ta faman fifita. Ga kwanon abincinsa ga kyallayen ankon Salma a gefensu, shaida ce taya kuduro batu a akansu ya kawo wa Hajiyarsa wadda Ke ta “yan hidimominta daga tsakar gida zuwa daki Da alama ita ma Hajiya hankalinta a kansa yake, tun bayan da babban danta ya je mata da batun ya sallama Adamu da maganar karatu sai duk hankalinta ya bi ya dugnuazume, tasan Adamu da kyau! Bai iya zaben komai ba bare ya zabi makoma tagari a rayuwarsa wadda babu hannun yayansa a ciki, sannan ta san kafiyarsa kan abinda-ya zabowa kan: nasa komai muni shi baya gani. Kari kan damuwarta bayan wannan shi ne yadda ya zaune mata yanzu yana cin abinci bakinsa a dinke, ta dade da sanin shirun Adamu sai da dalili don haka tuni ta fara neman tsarin Allah da jin dalili wanda zai shafi farin cikinta ko wanda zai sanyata zance da karkata kai. . Ta cigaba da shige da ficenta tana saKar abinda zai bugar mata cikinsa ta ji meya hadiya batayi aune ba kawai sai taji ya Www.bankinhausanovels.com.ng  kwarma ihu tare da furzar da shinkafar bakinsa . kana ya furta, “Na shiga uku!” Ta girgije tsoron da taji karon farkon ihunsa a hasale ta yi kansa da _ tsintsiyar hannunta, “Menene haka, kai wane irin mahaukaci ne?” Ya nuna mata shinkafa “daya furzar daga“Wata. shegiyar tsakuwa na gurza, in Sa’adatu ta iya girki Allah ya tsine min” Hajiya ta dinga motsa baki alamar takaici na neman hana ta Magana, amma dai ta daure ta warto, _ “Wato Adamu bakinka ba zai zama mai yawan ambaton alkhairi ba ko? Ka kwarma ihu _ ka biyo shi da na shiga uku anbi ba’asi kuma _ ka nemi Allah ya tsine maka. Adamu fata nagari fa lamiri ne., Alamar nasihar tata ta bayan kunnensa take shiga, kawai sai ya hau kakari tamkar mai  shirin finciko ‘ya’yan cikinsa a matsayin amai “sun ki fincikuwa. Www.bankinhausanovels.com.ng Da haushi ya ishi Hajiya kawai sai ta bi bango ta yi zaman dabaro tana kallon Adamu har ya gaji da kakarinsa ya dago ya dube ta ido jawur, “Wai Ibtila’I ya afkowa mutum amma sai ki ce saiya ce ya shiga aljanna a madadin ya shiga uku, aljanna ba dadi ba ce? Wata masifar kuwa in ana shiga dubu mutum ma ba sai ya ce dubu ya shiga ba.. Cikin sikewa Hajiya ta katse shi, “Ka’idar daidai ce sai ka ji dadi. zaka godewa Allah Adamu...?” Shi ma ya tare ta cikin nuna mata carbin hannunsa, “Mu da muke neman kusaci da Allah har a fada mana godiyar Ubangiji Hajiya? Ai kar ki damu kawai, Allah na kowa ne kowa ma azurtawa yake. Aljanna kuma ta mai rabo ce”. Furucinsa da carbin hannunsa ya sanya shakku ya dabaibabye zuciyar Hajiya ta ji numfashinta ya fara gudu a guje! Nan da nan Shazali dan gidan Hajiya Dudu da Malam mai almajirai suka fado zuciyarta. Www.bankinhausanovels.com.ng Wani malami ne a Warure da. labarinsa tsakaninsa da matasa ya fara karade bakunan _ Jama’a, ana zarginsa da neman matasa maza, _ wadanda yake yaudara da basu wurudin neman kudi, an ce wasu na tsallakewa su yi kudin wasu kuma su zama bayinsa da sai yadda yayi dasu yayin da wasu idan sun kuskure wurudin suke haukacewa kamar yadda Shazalin ya haukace kuma kwararo-kwararo yake bawa mutane labarin abinda ya faru da shi a daren wurudin tare da bayyana matasan da suka yi kudi ta hanyar wurudin, kowa a Kurawa da zagayenta ya san da wannan batun ciki kuwa har da Adamu wanda bai dauki hakan abin Kyama ba don lokacin da labarin ya zo musu suna tare da Hajiya da yayansa da Sa’adatu har ma da Salma. Suna ta jinjina labarin amma budar bakin Adamu sai cewa yayi, _ Ni ban ga abin jinjina lamarin nan ba wallahi, ai wurudi ka nemi kudi ba laifi ba ne in dai ba shirka zaka yi ba, shi ma Shazali akasi aka samu’” salma taceHmmm labari nata tafiya fa shin koya zata kaya? Kudai kuci gaba da kasancewa damu Www.bankinhausanovels.com.ng 

Post a Comment for "NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 3 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...