MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 7 Na Samira Harouna - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 7  Na Samira Harouna

MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 7 Na Samira Harouna

- - Post a Comment

 MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 7

Na Samira HarounaπŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *25*ko da isar su asbiti da gudu asas ya bude murfin mota din ya dauketa sai cikin dakin marasa lafiya hafsa da su Asmau na beye da shi inda su Asma'u da sauran kawayensu  suke kuka


tancikbacci bata riga ta farka ba Mamar Asma'u data shigo gidan yanzu ta shafa mata lalle a kan ta da hannaye da tafin k'afa, zunbur ta tashi zaune tana kallonta tana mata dariya, ganin ta fita a d'akin sai kawai ta cire lallen na hannayenta ta shafawa fuskar Zeinaba dake baccinta, a firgice ta tashi tana fad'in "Waye? Mimi."


Dariya ta kwashe da ita tare da mik'ewa ta fita a d'akin ta shiga ban d'aki da d'an kwalinta a kai.


Safiya na yi Mama ta dinga aikinsu Yaseen suna raba alawa ta wankan amarya da yamma, Mimi kam banda fad'uwa da gabanta keyi duk jikinta ma yayi sanyi sosai, sai taji tana rasa karsashinta da zumud'inta da ma farin cikinta, misalin 08:00 Mimi dasu Rauda suka shirya suka shiga gidan Maimuna, anan k'awayenta suka dinga zuwa suna shan hirarsu da haka har aka samu wuni, dan kuwa saida la'asar tayi kad'ai aka kirasu suka shigo gidan, lokacin gidansu kuma ya cika da mutane yan uwa da yan unguwa an zo wankan amarya. Daga gurin angaye aka turo da motoci guda takwas dan kai su inda za'ayi wanka, kusan mutanen babu wanda bai je ba saboda wadatar motoci da aka samu, gidan yar uwar su mama dan waankan farko ana yin shi ne a dangin uwa.


Gaba d'aya basu d'auki minti arba'in ba tafiyarsu da dawowarsu, Mimi kam ta jik'a tayi laushi sosai dan tasha wankan ruwan lalle masu d'auke da itatuwan da kakaninmu suka yarda cewa yin wanka dasu yana zubar da duk wata shiririta da shirme, yana k'ara maka hankali da nutsuwa, tun a mota take hawaye har suka zo gida bata daina ba, tunda ta shiga d'aki kuma k'awayenta duk suka watse zuwa nasu gidajen aka barta da su Zeinaba kad'ai.


Alhamdulillah kam aure rahama ne kuma alkairi ne, a dalilin auren Mimi Abba da Mama sun samu gudumuwa sosai daga dangi da kuma abokan arziki, hatta da Alhaji Saminu ya aiko da gudummuwar buhun shinkafa da kuma kud'i har jaka hamsin, duk da dai baya bayar bane cikin dad'in rai, kawai yayi ne dan kar ace bai yi ba amma sosai ya ji zafin yanda Mimi ta banzatar da shi ko wayarshi bata tab'a d'agawa ba. Wasa wasa sai gashi lokaci na ta tahowa kamar almara.              *Ranar kamu*Ko da k'arfe 08:00 ta buga suna salon ana ma su Asma'u kitso da k'unshi Mimi kuma saida aka fara mata gyaran jiki, ana idawa aka shiga zana mata k'unshi da jan lalle, mai salon d'in ce ta tsaya kan ta zata fara mata kitso k'anana, da sauri ta janye kanta tace "A'a, a'a bana so."


Da mamaki tace "Ban gane ba kya so ba? Kina amarya?"


Kamar zatayi kuka tace "Bana so ni dai, zafi ke akwai wallahi, bana son kitso."


Kamar da wasa Mimi ta ko dage ba za'a mata kitso ba ita kuka zatayi, dole k'arshe ta k'yaleta amma suna ta mata nasiha ta gyara a matsayinta na mace, ita dai saurarensu take bata kula kowa ba. Da azahar su Salma suka zo suma sunyi lalle da kitson su tsaf, dan haka ko da 03:00 tayi na rana suka fara shiri dan dukansu da kayansu suka zo, mimi ma ana ida lallen aka mata siraci ta shiga wanka, tana fito a sauk'ak'e kuma a nutse aka fara mata gyaran kakkauran gashin girarta, kad'an aka rage mata shi hakan yasa yayi kyau sosai tuni fuskarta ta fito shar da ita dake gashin nata bak'i ne wulik, kayan da Hafsat ta kawo mata ranar ta fara sakawa.


Doguwar riga ce abaya kalar ja mai duwatsu da kwalliya, tun ranar da aka kawo kayan Mimi bata duba su ba har Asma'u ta so bud'ewa ta hana, yanzu kam data saka sai suka saki baki suna kallonta, yanda rigarta ta zauna mata d'as a jiki ta mata kyau, ga tsarin rigar na ban mamaki wanda ya birgesu, wato idan sun fahimta komai a mutumce ne ya mata shi dan kar a sab'a k'aida, rigar zubin babbar riga aka mata na maza saidai a rufe take kirip har k'asa tana jan k'asa, gashi hula ce a bayanta irin na rigar sarauta alkyabba, sannan tana da kallabi ware daban wanda ake fara d'aurawa.


Kwalliya aka mata mai kyau da sauk'i wacce zaka rantse abonda aka shafa mata a fuska dama a fuskar ta ta yake, ana gama salllah la'asar dukansu yan matan sun fito sun haska a cikin rigunansu kalar pink na kakkauran yadi mai taushi, inda dukansu aka d'aura musu d'an kwali kala d'aya wanda suka siya.


Dogayen takalma k'afa ciki aka saka mata da jakarsu k'arama mai kyau da walk'iya, ga agogo data kama tsintsiyar hannunta dam ta zauna, kallabin abayar yanda aka d'aurashi daga ciki da kuma hular da aka d'ora mata sai ta fito sak gimbiyarta yar sarki jikar sarki.


Yamma sosai motoci guda uku dukansu k'irar benz suka paka a k'ofar salon d'in, a hankalce kuma a tsare yan matan duka suka kewayeta suka shiga takawa har waje, suna fita Asas ya hangesu daga cikin motar, wani murmushi ya sub'uce masa tare da jin yana sha'awar ya tsokaneta kamar ita d'in *matar yayanshi ce*, a sanyaye ya bud'e motar ya fito tare da bud'e mazaunin da zata shiga ta zauna, duk tsaye sukayi a bayanta saida ta shiga ta zauna ya rufe ya kallesu yace "Nagode k'awaye da gyara min amaryata."


Murmushi sukayi Salma tace "Mu ba k'awayenka bane, ga k'awarmu nan kana shirin rabamu da ita."


Murmushi yayi yana tsaye yana kalli duk suka shiga motar, sai Asma'u data zagaya d'aya b'angaren da Mimi take ta shiga, a hankali suka bar wurin suka d'auki hanyar gidan saukar bak'i na sheikh Abdul Waheed Salman Aliyu Sharif.


Kecup! Suka ji k'arar waya tare da hasken daya d'auke idonsu, da sauri suka kalleshi sai kuma kunya ta kamata ta sunkuyar da kai, murmushi yayi yace "Maah kin ga yanda kika had'u? Har saida na ji gabana ya fad'i tsabar razana."


A hankali ta d'ago matsakaitan idonta da suka sha eyeshadow a tausashe kamar mai rad'a tace "Me yasa gabanka ya fad'i?"


Ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Sadeeq yace "Saboda ganin kamar *matar manya* na d'auka, bana so na zama tururuwa uwar jaye-jaye."


A sauk'ak'e ta kalleshi tace "Wannan maganar kamar dani kake, kar kasa na ji ba dad'i mana."


Sunkuyar da kanta ta sake yi shi kuma ya kalli Sadeeq dake fad'in "Ba wannan ba ma abokina, na ga amaryar ta mu kamar jinin sarauta, dan Allah daga wace masauratar take?"


Yar dariya tayi cikin sanyayyar murya tace "Ni ba yar masarauta bace, hasalima ko gidan sarauta ban tab'a shiga ba daidai da gaisuwa, idonku ne kawai suke yaudararku."


Dariya sukayi sai Asma'u data rik'o hannunta tace "Mimi gaskiya ya fad'a, jininki da zubi na tsarin yanayinki kamar na wacce aka haifa a cikin masarauta ne."


Murmushi Asas yayi yace "Kin gani, k'awarki ma haka take gani, amma ba komai karki damu, gaba kad'an zan mayar dake kamar sarauniya."


Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta sosai, Asma'u ma dariya tayi tace "Allah yasa."


"Ameen." Ya fad'a yana gyara zamanshi, Sadeeq ne ya saci kallonta ta madubi yace "Ke ma da zaki bada dama ai gaban kad'an sai a mayar dake sarauniyar."


Dariya Mimi tayi tana sinne kanta wani dad'i na ratsata Asma'unta zata samu babban yaro, Asma'u kuma cike da zolaya tace "Wa zai mayar dani sarauniya bayan bana da suffar ko gimbiya?"


Dariya yayi yace "Gani, Allah da gaske nake Asma'u."


Kallon Asas yayi yace "Abokina fad'a mata mana."


Hararanshi yayi yace "Rainin hankali, ban tabbatar dana rik'e tawa a hannu ba zan zauna tayaka jefa k'uri'a? Kowa ya ji da kansa."


Da mamaki ya kalleshi yace "Au! Hakane kenan?"


"Eh d'in." Ya fad'a yana d'auke kai, jinjina kai yayi yace "Ba komai zan rama."


Sake kallon Asma'u yayi ta madubi yace "Asma'u kinji ko? Dan Allah ki bashi kunya mana ta hanyar amince min."


Kunya ce tasa ta sadda kanta k'asa tana wasa da yar wayarta a hannu, jin shiru yasa shi sake marairaicewa yace "Dan Allah *Asma'ul Husna* ki amince min kar na zauce."


D'aga kai tayi ta kalleshi da mamaki, ita ina zata kai babban yaro haka kamar Sadeeq? Bata tab'a saurayin daya taka ko da matakala ta farko na a b'angaren aji bare hawa na uku, ita kam ya zata ce mishu ne yanzu? Tabbas tunda suka san juna yake nuna mata kulawarshi da abubuwa masu wuyar fassara, ta d'auka mutumci ne kawai ashe abinda ke ransa kenan?


Mimi ce ta d'an tsamiketa a cinya hakan yasa ta fad'in "Washhhh!" Da sauri ta kama bakinta tana kallonta, da ido Mimi ta mata alamar ki amince mana, ita kuma ta mata alamar ni a wa? D'an tsaki tayi tare da yin kamar zata daketa, hakan yasa Asma'u jinjina kai tace "To zanyi tunani ko?"


Cikin murmushi Sadeeq yace "Ba matsala, zan jiraki har kiyi tunanin."


Bud'e baki sukayi da mamakin ashe ya ji me ta ce, da hirar raha da nishad'i har suka isa katafaren gidan daya had'u sosai aka k'watashi saboda hidimar da za'ayi.


Tabbas gidan ya cika mak'il da mata manya da yara ga kuma yan mata, saidai maganar gaskiya sun zo ne ganin zahiri da idonsu, tabbas su d'in ahali ne masu ilimi da sani sosai, amma fa suna da wani abu da saika rantse gidan jahilai ne, maganar talaucin gidansu Mimi a yanzu ba shine gabansu ba kamar da aka fad'a musu su waye iyayenta, sai suka zo tabbatarwa da tambayar kansu dame yarinyar tafi na su yaran da dayawa daga ciki aka so had'a Asas dasu amma ya k'i. Yan matan kansu suna so suga yarinyar ne dan su mata kallon hadarin kaji idan da hali ma har su yaga mata rigar mutumcinta.


Ai kuwa yamma na k'ara yin sanyi sai ga motocin angaye sun aje dangin Mimi, yanda suka fara shigowa harabar d'aya bayan d'aya yasa duk akaa kafesu da ido, su Shapi'a ne a gaba suka fara shigowa, hakan yasa wani gungu na 'yan mata kecewa da dariya ganinsu dunk'ul dunk'ul kamar yara amma kuma da fuskar dattijai, ajiyar zuciya Sahura ta sauke tace "Allah gamu gareka, nagode Allah da Mimi bata wurin nan da anyi b'atacciya."


Shapi'a ce tace "Ni kam fatana yanzu ta zo dan naga yanda zata ci uwar yarinya idan aka nemi wulak'anta mu."


Ido Sahura ta zaro tace "Rufa mana aisri Shapi'a, kai tsaye fa zata ce ta fasa auren d'an uwan nasu."


Cike da rashin dana sani Shapi'a tace "Idan tayi haka ma ai sai ta birgemu, wannan ai rashin sanin darajar d'an adam ne kamar ba gadon ilimi Sharif ya bar musu ba."


Murmushi Sahura tayi tace "Ya bar musu gadon ilimi, amma yayanshi kuma sun bar musu gadon dukiya, hakan ya jawo dayawa daga ciki dukiyar ce tafi aiki a tunaninsu."


Tab'e baki tayi tace "Allah ya kyauta musu."


Dogaye da gajeru ne suma haka duk suka samu wuri suka zauna ana d'an gaggaisawa sama sama, hakan ya jawo kowa ware nashi ya koma gefe ana k'us-k'us-k'us, tubarkallah farfajiyar ta cika har kujeru na neman yin k'aranci duk yawansu, dan kuwa kafatanin ahalin Sharif duk sun hallara, kama daga iyalin Aliyu Sharif, Usman Sharif, Salmanu Sharif da sauran abokan arzik'i, sosai Hafsat ke k'ok'arin ganin an samu sanayya da kuma fahimtar juna tsakanin danginsu da dangin Mimi, hakan yasa take ta nunawa iyayensu su Shapi'a a matsayin iyayen Mimi, wasu suna sakin jiki su karb'esu a gaisa, wasu kuma gaba da gaba suke yatsina fuska suna musu yak'e, hakan bai ma Hafsat dad'i ba amma ya ta iya, sharesu tayi ita ma tana fama da cikinta da wunin yau ta ji bai motsa mata ba ga wata muguwar kasala, jefi-jefi kuma sai taji gabanta ya fad'i kawai ba dalili, saidai bata bar ambaton ubangiji ba a bakinta da haka take jin sanyi sanyi a ranta.Sanda motocinsu suka tsaya angayen ne suka fara fitowa suna shigowa filin, sai k'awayen Mimi da suka jera gwanin sha'awa suka sakata tsakiya tare da Asas dake ta doka murmushi, Mimi kan kanta na k'asa tana fama da rik'e jakar hannunta rigarta kuma na jan k'asa.


Kowa sake waro idanu yayi dan tabbatarwa kanshi abinda yake gani, dangin Mimi da dama sun san kayansu ba daga nan ba indai wajen d'aukar wanka ne da iya gayu, saidai yanda ta zama tamkar wata balarabiya ya k'ara birgesu da kashesu a game da ita.


Inda yan matan nan kuma suka shiga tamtama wai dama haka yarinyar take, sam babu wata makusa a tare da ita da zasu kushe, duk da kwalliya tana canza hallitar mace ta gyarata amma dai sun tabbatar zata yi kyau, na farko tana da dogon hanci ga ta jar fata, su kam idan aka barsu sai su ce wata baralabiya ce, duk sai suka kasa motsawa a wurin dan kwarjini ma suka ji tayi musu yarinyar, sai yan matan amaryar ne da angaye da suka dage suna ta d'aukarsu hotuna, da haka aka isar da Mimi kan kujerarta sai su Asas da suka bar wurin dan dama fa anyi ba dasu za'a yi hidimar ba.


A cikin taron yan matan nan akwai guda d'aya wacce ita ba fa abinda ya kawo kowa ya kawota ba, na ta k'udirin babba ne daya girmi na kowa dan kuwa sak'on Muttak'a ta zo isarwa, tasan kasada zatayi amma kud'in daya bata tare da yi mata alk'awarin aure yasa ta ji zata iya yin koma menene, tun shigowarsu Mimi ta mik'e ta shige zak'ewa akan komai tana kamkamba kamar wata yar uwa. Dangin Mimi kallonta suke yanda rawar kanta yayi yawa suna tunanin wata yar uwace makusanciya ta Asas. Inda suma dangin Asas suke kallonta wata marar hankali daga b'angaren Mimi take, da wannan kallon da duka kusurwoyin ke mata aka kasa samun wanda zaiyi mata maganar shishigewa da take musamman ta b'aangaren abinci.


Magriba na gabatowa Hafsat ta gabatar da masu ruwa da tsaki ayi kamun amaryar, ana idawa Hafsat tasa Aisha da su Fanna suka kawo cake dan ta yanka tunda ba wani abun ci aka ware mata ba ita, da taimakon Asma'u ta yanka Asma'u ta d'an saka mata a baki aka musu tapi ana dariya, *Feena* ita tayi babakere ta d'auki lemu ta tsiyaya a cup na glas, a hannunta dama akwai k'aramar k'waya babu wanda ya kula da tsiyarta bare ya lura har ta saka, mik'awa Asma'u tayi ita kuma ta mik'awa Mimi, amsa tayi ta d'an kurb'a zata aje Feena ta sake fad'in "Ki k'ara mana, ko ruwa baki sha ba fa."


Dayawa kallonta sukayi sai Mimi da take kallonta a matsayin dangin wanda zata aura, wannan kunyar tasa ta d'an k'ara kurb'awa kafin ta aje, Feena kam murmushi tayi duk da bata ji dad'i ba da bata sha sosai ba, amma dai tunda Muttak'a ya bata tabbacin guba ce mai had'ari sauta share kawai, a hankali ba tare da lurar kowa ba tayi kamar tana amsa waya ta fita a wurin.


Ana kwad'a kiran sallah magriba su Asas na dawowa d'aukar amarya, Hafsat ce ta rik'e hannunta saΓ― Asma'u a gefenta sauran yan mata a gaba wasu a baya suka nufi hanyar fita, Mimi dake jin matsanancin murd'awar ciki da jin kamar an rik'e mata numfashi ba tare da ankarewar kowa ba ta tafi baya luuuu! Ta fad'i a wurin, da sauri Hafsat ta kalleta tare da sakin hannunta tana furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Mimi."


Asma'u ma da sauri ta durk'ushe tana kiran "Mimi, Mimi lafiya."


Take aka rufe wurin ana tambayar lafiya, cikin tashin hankali Hafsat ta d'ago kanta ta kalli Aisha tace "Eesha kira Asas a waje."


Mayar da kallonta tayi kan Mimi, a hankali ta lura da jinin daya fara b'ullowa ta hancinta, cikin tsananin tashin hankalin da take jin bata tab'a riska ba ta daure ta d'ora hannu a kai tace "Na shiga uku, me ya sameta?"


Da gudu Asas ya shigo tare da rakiyar zaratan mazan a bayanshi, suna zuwa suka bud'a musu hanya, da sauri ya durk'usa yana fad'in "Me ya sameta? Me aka mata?"


Shapi'a ce tace "Ba abinda aka mata, ni fa ina ganin ko mayya ce ta kamata a wurin nan?"


Dayawa daga cikin mutanen suka kalleta sai wata mace mai aji sosai da tace "Nan ciki akwai wanda ya miki kama da maye ne?"


Hafsat ce tace "Bana tunanin haka, mu kaita asibiti jini ne yake fita a hancinta fa."


Wata dattijuwa ce tace "To ko tana da iska ne?"


A sukwane Asas ya mik'e tsaye tare da tattara k'arfinshi ya d'auki Mimi cak ya fita da ita da gudu, duk rufa masa baya akayi hankali tashe da tunanin miye zai faru, yana sakata mota yaja da gudun tsiya zuwa asibitin sheikh data fi kusa dasu har da ma gidanshi duk yana kusa da masaukin bak'in na shi, duk tarin tilin motocin dake wurin kad'an ne suka bi su zuwa asibiti dan su san halin da take ciki.

*Gobe d'aurin aure fa*😁
*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *26*Ana gama d'aurin auren ya lumshe idonshi yana jimk'e hannunshi kamar zai naushi wani, kabbara aka d'auka a masallacin dan shi ne aure na k'arshe da aka d'aura tsakanin *Maryam Adam Shehu* da kuma *Abdul Waheed Salman Aliyu Sharif*, duk mik'ewa mutane sukayi ana fita da magana a baki, wasu hakan ya musu daidai da son zuciyarsu, wasu kuma hakan bai musu ba ko kad'an, sheikh kam bai motsa a wurin ba haka aka dinga bashi hannu ana mishi addu'ar fatan alkairi, su Abba ma fita sukayi yana kiran gida ba'a samu, dan haka mijin Sahura da suke tare ya jaraba kiranta kuma aka samu, shi ne fa suka sanar musu dan karsu ji abun daga sama kafin su isa gida. Saida yaji masallacin yayi shiru alamar ba mutane kafin ya d'aga kan shi, ai kamar wanda aka kora da gudun tsiya sai kuwa yayi wuf ya mik'e yana sab'a babbar rigarshi ya fita shi ma su Alhaji Ibrahim da Saleh suka rufa mishi baya tare da jami'anshi.


Duk motocinsu suka shiga inda sheikh ya kalli dreba yace "Dan Allah kayi sauri, gidan Hajia zamu je."


"To sheikh." Ya fad'a yana sake murza sitiyarin da kyau, ji yake an k'i kawowa gidan, gaba d'aya gani yake ba'a sauri kamar ya fita yaje da gudu a k'afarshi, tambayar "Anya kuwa Hajia tasan wa ta bani?" Yake yi, numfashi kawai yake saukewa lokaci zuwa lokaci, da wannan tashin hankali suka isa gidan daya k'ara kaurewa da mutane maza da mata, a k'ofar gidan motar ta tsaya sheikh ya fita, duk da hankalinshi a tashe yake kuma sauri yake sosai, amma tafiyar a nutse yake yin ta cikin hankali, gaisheshi ake da girmamawa kamar wani sarki shi kuma yana amsawa da murmushin yak'e a fuskarshi, har suka shiga cikin gidan ya fara hango Hajia a b'angaren Asas zaune a k'ofar shiga falon, mutane duk anyi cirko cirko wasu zaune wasu kuma tsaye babu mai magana.


Da sauri ya isa garesu saida ya kai daf dasu ya fahimci matar Alhaji Ibrahim ma tana tare dasu Kubra da matar Saleh sai Hafsat zaune kan ta a k'asa, kallonta yake yana karantar yanayinta, sosai ta bashi tausayi dan alamu sun nuna tasan abinda Hajia ta aikata musu.


Kallon juna sukayi da Hajia cikin rikitacciyar murya yace "Hajia ya haka? Ina Asas?"


Sake rumgume hannayenta tayi tace "Yana ciki likita na dubashi."


Sake kallon Hafsat yayi, matsawa yayi kusanta ya durk'usawa ya kamo hannayenta cikin na shi, da k'yar ta d'aga idonta ta kalleshi tana mai danne abinda ke zuciyarta tare da dakatawa da karatun suratul nisa'i data shiga tunda abun ya faru dan ta tunawa kanta cewa hukuncin Allah ne fa, shi ne ya hukunta musu suyi,  da k'yar ta k'ak'aro murmushi da shi yana gani yasan bai kai ciki ba tace "Barka, ina tayamu murnar k'ara girma, ina tayaka murnar k'ara samun wanda zaka ciyar fisabilillah, Allah tayaka rik'o sheikh."


Yanda muryarta ke rawa yasa ta dakatawa dole dan bata so tayi kuka, girgiza kan shi yayi tare da d'ora hannunshi a cikinta shi ma kamar zaiyi kukan yace "Kin tabbatar kuna cikin k'oshin lafiya?"


Saida ta d'ora hannunta akan na shi ta jinjina kai tace "Eh, ba komai."


Girgiza kai ya sake yi yace "Da komai Hafsat, zamuyi magana a gaba kinji."


Mik'ewa yayi tare da sakin hannunta ya kalli likitan daya fito, yanda suka zuba mishi ido yasa shi girgiza kai yace "Saidai kuyi hak'uri, Allah ya gafarta masa."


Da sauri ya rab'ashi ya wuce d'akin haka Alhaju Ibrahim da Saleh ma da kuma Sadeeq da suka samu a nan, tabbas dai abinda kowa ke gani shi suma suka gani, a hankali ya zauna bakin gadon yana k'arewa fuskar Asas kallo, lallai duniya *budurwar wawa*, jiya suna tare da bawan nan har safe ma haka, kai har k'arfe 10:45 suna tare dashi yana mishi mitar ya bashi jaka d'ari biyu shi babu kud'i a hannunshi, kuma banki a lokacin yasan ba zai samu ba dan juma'a ce, shi ne yanzu kwance haka a gabanshi baya motsi.


A sanyaye ya sauke wani numfashi kanshi k'asa yace "Zamuyi mishi sutura yanzu, bayan sallah la'asar insha'Allah saimu kaishi gidanshi na gaskiya."


Jinjina kai Saleh yayi tare da kallon Sadeeq da idonshi zasu tabbatar maka kuka yayi yace "A samo mana abinda ya dace a mishi wanka."


Jiki a sanyaye ya fita yana sako da wasu hawaye, a kullum Asas fad'i yake "Aure na shine silar warakata." Ashe wannan warakar yake nufi? Duk tunaninsu zai warke ne daga ciwon ashe warkewa ta har abada yake nufi, bayan wani lokaci ya dawo gidan a lokacin kowa yayi zugum anyi zaune kan tabarmi an shirya zaman makoki, yana kawo musu abubuwan buk'ata sheikh ya mik'e yana aje hularsa akan gadon, cire babbar rigar yayi tare cire machette na wuyan hannun rigar ya aje ya tattare hannayen, cire agogo yayi da takalminshi haka ma safar k'afarshi fara tas, sunkuyawa yayi ba tare da jin nauyin gawa ba ya tallabi Asas kamar yaro ya shiga dashi ban d'aki, akan tabarmar da Saleh ya shinfid'a ya aje shi a hankali kamar k'wai.


Farin towel babban ya rufa mishi daga k'ugu zuwa gwiwanshi kafin yayi dubara ya cire mishi singlet d'in daya saka da wandon shaddar da kuma na ciki k'arami, fararen ruwan masu kyau da aka jik'a da ganyen magarya ya d'iba ya fara da bismillah zai mishi tsarki. *Kamar* jira ake dama a zuba mishi ruwan sai kuwa Asas yayi *zunbur* kamar dukanshi ne aka yi, abun ka ga namiji mai zuciya sam sheikh bai girgiza ba bare ya tsorata saidai idonshi kawai daya zaro yana kallon Asas daya mik'e haka kamar wanda aka maidowa rai da k'arfin tsiya.


Kallon juna suke sosai Asas yana so yayi magana bakinshi ne yayi nauyi, hannu sheikh ya kai ya tab'a goshinshi yaji babu wani sanyi k'alau, a hankali ya kamashi ya mik'ar dashi tare da d'aura mishi towel d'in a k'ugu, d'aukar kayanshi yayi ya bashi yace "Saka wannan."


Karb'a yayi hannayenshi sunyi mugun nauyi, lura da haka yasa sheikh kamo hannunsa hakanan suka fito zuwa falon, da k'arfi Saleh ya mik'e yana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."


Su ma mik'ewa sukayi har saida ya zaunar dashi bakin gado, kallon kallo suka shiga yi babu wanda yayi magna, sun jima haka kafin Asas ya d'aga kai ya kalli sheikh, kamar mai koyon magana yace "She..ikh...Au...rena,,,an d...aura?"


Ruf sheikh ya rufe ido da kunyar kallon Asas yace ai kanshi aka maida auren, a hankali ya rab'a Asas ya zauna gefenshi tare da dafe gaban goshin shi, Alhaji Ibrahim ne ya kalli Sadeeq yace "Kira mahaifiyarsa."


Da sauri ya fita inda Saleh kuma ya karb'i kayan dake jimk'e hannun Asas har yanzu ya saka mishi rigar, aje k'amarin wandon yayi ya durk'usa ya zura mishi dogon, yana cikin d'aure mishi zariya Hajia da Hafsat suka shigo tare, da farin ciki Hajia ta fad'a jikin Asas tana fad'in "Allah nagode maka, Allah ka yaye mishi wannan ciwo dake rabashi da rayuwa idan ya taso."


Kamar baya fahimtar me ke faruwa haka ya kalli Hajia data d'ago yace "Hajia, Mimi...aure...an d.aura?"


Tarrr! Hajia ta sauke ido a kan shi, saidai dake ita d'in ba masu kwalo kwalo bace sai tace "Ai tunda muka ganka kwance kamar gawa muka d'auka shikenan, har za'a fasa d'aura auren sai kuma na ce kar ayi haka ko dan ita yarinyar, shiyasa na ce a d'aura auren da d'an uwanka sheikh."


Shi ma dai wani kallo ya bita dashi duk da ya gane hausar da tayi, amma sai yaji yana neman k'arin bayani a sauk'ak'e, ya jima haka kafin ya iya cewa "Hajia matata sheikh ya aura?"


Girgiza kai tayi ta kamo hannunshi tace "A'a autana ba matarka ya aura ba, da matarka ce ai da bai aureta ba."


A sanyaye murya na shak'ewa yace "Hajia matata ya aura, ni ne fa zan auri Mimi."


Had'e fuska tayi tace "Ashraf Mimi dama *ba matarka* bace, baka ga gaba d'aya numfashinka saida ya bar gangar jikinka ba kafin ya auri *abar sa*? Ko kana so ka ce min baka yarda da hukuncin Allah bane? *Maryam matar sheikh* ce shiyasa ka lek'a lahira kafin ka dawo aka d'aura aurensu."


Kamar zai fashe da kuka yace "Hajia hakan ba daidai bane, wannan hukuncin bai yi ba sam, ina son matata, ina son ta Hajia dan Allah a bani matata tunda dai ban mutu ba."


Wata tsawa ta daka masa tana fad'in "Kai kanka d'aya kuwa? Ya auri matar ne zaka ce a mayar maka da matarka? Ita d'in yar tsanace ko wata abar wasa? Ko kumaa auren kake so kayi wasa dashi?"


Alhaji Ibrahim ne yace "Maryama ba haka za'ayi ba." Kallon Asas yayi yace "Kai Ashraf zauna kaji."


Cikin sako hawaye ya juya ya kalli sheikh da kanshi ke k'asa yana ta matse tafukan hannayenshi, shi kanshi fatanshi shine su amince ya sauke wannan nauyin dake kan shi, dan ba zai iya d'auka ba, ba zai yarda ya fara zaman aure da yarinyar da har ga Allah yake jin k'yamarta da kuma zarginta a ranshi ba. Zaune yayi k'asa kusan k'afafun sheikh yana kallon Alhaji Ibrahim daya gyara tsayuwarsa yace "Ashraf, kasan da cewa a duniya *wani* baya *auren* matar *wani*?"


Cikin kuka yace "Eh Abba."


Jinjina kai yayi yace "Sannan kaji ana cewa *matar mutum k'abarinsa*?"


Jinjina kai ya sakeyi yace "Na ji Abba."


Jinjina kai yayi yace "To ka yarda da wannan maganganun na hikima sannaan ka d'aura abinda ya faru akaan mizani sai ka bawa kanka amsa cewa *Mimi matar waye a cikinku*?"


Alhaji Saleh ne yace "Gaskiya ne, haka Allah ya so shiyasa abinda ya faru har ya faru, duba da ita kanta yarinyar jiya guba tasha mai had'arin gaske, amma a k'arshe Allah ya tashi kafad'unta, sannan kai ma gashi ka d'auki awanni a doguwar suma, amma kuma aka sake ara maka numfashi Asas, wannan ya isa ya nuna maka dama can Mimi sheikh ne mijinta."


Hafsat da Asas kallonshi suke kamar basa gane me yake fad'a, cikin magiya Asas yace "Yanzu kuna nufin na hak'ura kenan bayan ni ne zata aura? Shi fa ba son ta yake ba ita ma haka? Kenan auren dole kuka musu?"


Hajia ce tace "Wane irin auren dole kuma? A duniya ina ga bayan matarshi akwai wani mahaluki da zai nuna maka sanin sheikh ne? Ai kasan bΓ’ zai k'untata rayuwarta ba."


Cike da k'arfin hali da dakiya da kuma jarumta da son yin abinda Allah zai yarda da ita tayi k'ok'arin kawar da komai a tausashe tace "Gaskiya ake fad'a maka Asas, na tabbata da Mimi matarka ce da ka aureta ko da kuwa minti d'aya ne da d'aurawa kai kuma kabar duniyar, zaka fahimci ba matarka bace tunda har Allah yasa bata da rabon yi maka takaba, kuma da matarka ce da igiyar aure bata had'ata da *mijina* ba."


Cike da tausayawa Hajia tace "To kaji yar albarka ma."


Alhaji Ibrahim ne ya kalli sheikh yace "Sheikh ana ta magana ba ka ce komai ba."


Wani wawan numfashi ya sauke ya d'aga kan shi ya kallesu, sake sunkuyar da kai yayi yace "Da zaku min lamuni a gaskiya dana sawak'e mata, bana son shiga hakk'in d'an uwana, bugu da k'ari ni ko ita babu maganar fahimtar juna a tsakaninmu."


Hajia ce tace "Ka sawak'e mata? Ka mayar musu da yarinya bazawara kake nufi daga d'aura auren?"


Da sauri ya kalleta yace "A'a Hajia, dana saketa sai a d'aura musu aure tunda babu iddata a kanta."


Saleh ne yace "A gani na fa da Allah bai hukunta wani abu a tsakaninka da ita ba da haka bata faru ba."


Alhaji Ibrahim ne yace "Ni ma abinda nake so suyi duba dashi kenan, amma suna rufe idonsu."


Caraf Asas ya rik'e k'afar  sheikh yana fad'in "Dan Allah sheikh ka saketa tunda kai ma baka son ta, sheikh na ci buri sosai wajen tsara rayuwata da Mimi, ka taimaka min dan Allah sheikh."


K'ura masa ido yayi yana kallo yana sauraren magiyarshi tare da yanda shi ma zuciyarsa ke wani tsalle tana duka, da sauri ya mik'e tsaye tare kallon Asas yace "Ka shirya zamu tafi gidansu *yarinyar*."


Jiki na b'ari Asas ya fara kakkarwa saka rigar kayanshi da Allah bai nufeshi da sakawa ba, sheikh ma takalminshi ya saka ya d'auki babbar rigar ya saka ya d'auki agogo ya zuba aljihu, hula ya d'auka ya d'ora a kai zasu fita Alhaji Ibrahim yace "Sheikh karka manta wani abu, kai babban mutum ne bai kamata kayi abinda zai tab'a kimarka ba."


Saleh kam cewa yayi "Ba ma zasu tafi su kad'ai ba, muje tare dasu kawai Alhaji."


Hajia ma cewa tayi "Ku jira muje na ga me zakuyi, wallahi ba zaka saki yarinyar nan ba."


Zasu fita Hafsat ta rik'o hannunshi hakan yasa suka kalli juna ido cikin ido, marairaicewa tayi ta girgiza masa kai tace "Na yarda da kai, nasan ba zakayi abinda bai dace ba, kayi tunani mai kyau kafin ka yanke hukunci, sannan kayi tunanin makomar yarinya da iyayenta, sannan ka duba girman wanda ya umarceka da aurenta."


Tana fad'a ta saki hannunshi tare da kaucewa a hanyar, jiki a sanyaye ta kashe mishi gabb'an jikinshi suka k'arasa fita, Asas dad'i yake ji za'a je a sakar masa matarshi ya aura, inda iyayen suke ciki zulumi da tunanin hukuncin da zai yanke. Saleh ne ya tuk'asu a mota d'aya suka tafi inda Hajia ke gaba sai su sheikh baya tare da Asas da Ibrahim.


    

          *Mu ci gaba*Da sauri Mimi ta d'ago ta sauke ido akan Iya Delu data fashe da kuka, sallalamin da gidan ya d'auka yasa Mimi ta shiga bin kowa da kallo, yanda ta bud'e baki tana lumshe ido alamar jiri na d'ibarta ne yasa Sahura saurin rik'eta ta shiga d'aki da ita, zauna da ita tayi akan gado tana yaye mata darar dake kanta, k'ura ma Sahura ido tayi tana kallonta, d'an girgiza kan ta Sahura tayi tana fad'in "Yi magana ina jinki."


Kamar wata doluwa saikuwa tace "Aunty, Asas ya mutu? Da gaske ya rasu? Yau ne fa aurenmu, shi ne ya rasu ya barni."


Fashewa tayi da wani kukan tare da k'amk'ame Sahura da suka kawo kai d'aya sanda take zaune ita kuma aa tsaye, daddab'ata ta shiga yi tana fad'in "Dangai dangai, dangai yar Abbanta, shiru karki masa kuka kinji."


A sanyaye suka ji sallamar su Iya da yayar Malam sun shigo d'akin, amsawa su Asma'u sukayi hakan yasa Iya kallonsu tace "Yan mata, dan Allah ku d'an bamu wuri zamuyi magana da ita."


Mik'ewa sukayi jiki a sanyaye cike da tausayi Asma'u har ta fara zubar da k'walla, Sahura ce ta rik'e hannun Asma'u ta mata alamar ta zauna kusa da Mimi, zaunawa tayi sai su Zeinaba da Salma da suka fita k'ofar gida, Sahura ma zaune tayi tana kallonsu Iya su ma suna kallon Mimi, cikin nutsuwa Iya tace "Mimi, *wani hanin ga Allah baiwa ne* ki yarda ubangijin daya halliceki shi yafi sanin abinda ya dace a game dake, Asas ba alkairi bane a gareki ko nace ba mijinki bane, shiyasa Allah ya d'aukeshi a sanda lokaci k'alilan ne ya rage ku zama d'aya a baki wanda ya fi shi cancantarki."


Yayar malam ce tace "Gaskiya ne, kuma dama ai *matar mutum* k'abarinsa, ya mutu ne saboda babu rabon aure a tsakaninku."


Dafe kan ta tayi da hannu tana sako hawaye tace "Kai na juyawa yake Iya, waye ya daceni? Waye ya fi Asas alkairi a gareni? Jiya ni na kusa mutuwa yau kuma shi ya mutu."A hankali Iya tace "D'an uwansa ne, sheikh."


"Me!!!" Ta fad'a a razane tana mik'ewa tsaye kamar zata had'esu da ido, girgiza kai tayi cikin d'aga murya tace "Abdul? Ba zai yiwu ba bana son shi, ban shirya aurenshi, akan me za'a d'aura min aure dashi? Shi ne ya buk'ata saboda hukuntani akan k'aryar dana masa?"


Kama hannunta Sahura tayi tace "Yi hak'uri Mimi ki zauna kinji, babban mutum ne fa mai ilimi, na tabbata ba zai wulak'antaki ba."


Kallonta tayi tace "Kawai ni ma bana son shi ne aunty, bai min ba ko kad'an, *tsohon*?"


Yayar malam ce tace "Ke kin ci uwaki! Waye tsohon? An fad'a miki namiji na kad'an ne ko yayi yawa?"


Cire darar tayi ta jefa akan gado tace "To ni bai min ba, bana son shi ko kad'an, kawai a warware wannan auren."


Zata fito Sahura ta rik'e hannunta tare da Asma'u, rarrashi suka shiga yi da nuna mata tayi hak'uri, Mama na waje tana saurarensu, saida ta ji abun ya bata haushi ne ta lek'o d'akin, kallonsu tayi tace "Iya dan Allah ku k'yaleta, idan mahaifin na ta ya dawo saita fad'a mishi a warware auren tunda haka take so."


Sakin labulen tayi zata fito Abba da malam suka shigo tare da Abban Asma'u, gaisawa sukayi da mutanen dake nan suna taya juna murna da kuma jimami, d'akin suka wuce da sallama inda matan suka gyara musu suka zauna a kujerun da Asma'u ta d'auko ta aje musu.


Kallon Mimi Abba yayi yace "Uwata, kin ga abinda ya faru ko?"


Cikin kuka tace "Abba ni kawai a warware auren nan, Abba bana son shi wallahi."


Da mamaki Abba yace "Subhanallah! Ba kya son shi? Me yasa?"


A take tace "Saboda bai min ba, Abba sa'anka ne fa, ya zan auri sa'an Babana."


Salallami suka d'auka a d'akin inda malam yayi dariya ya zura hannunshi yana fad'in "Zo nan amarsu."


Mik'o mishi hannun tayi t taso ta zauna a k'asa kusa da k'afafunshi, cikin dattako yace "Amarsu wani ne ya fad'a miki tsoho ne shi? Dama ba'a auren tsoho ne? Miji irin wanda kika aura ba'a kiransa da tsoho saidai dattijo, dan dattijon arziki ne daga gidan dattijai, Mimina, ni dai banga abun a had'in nan ba ko kad'an, kiyi wa iyayenki biyayya ke ma sai Allah ya baki masu yi miki biyayya, kinji ko?"


Fashewa tayi da kuka tace "Kakana baya so na, na tabbata ya karb'i aurena ne dan ya hukuntani."


Abba ne yace "Hukuntaki kuma? Kar dai wata tsiyar kika tabkawa babban malamin nan."


Turo baki tayi ba tace komai ba, Abban Asma'u ne yace "Mimi 'yata kiyi hak'uri kinji, tabbas can dama Allah ya tsara shi ne mijinki, karki damu kanki bare kiyi k'ok'arin cutar da kan ki, nasan kina da ilimi kuma kinsan cewa zab'in Allah shi ne daidai."


Suna kan tattaunawar nan Rauda ta shigo da sallama d'akin, amsa mata sukayi inda tace "Abban Mimi kunyi bak'i a waje."


"Su waye?" Ya fad'a yana kallonta, da kamar tsoro a fuskarta tace "To har da dai Asas, da kuma sheikh sai wasu guda b..."


Bata gama fad'a ba Mimi tayi tsaye tace "Asas kika ce?"


D'aga mata kai tayi ai da gudu tayi niyyar fita a d'akin tana fad'in "Asas kuma?"

 Rik'ota Abba yayi yana fad'in "Zubar mana da mutumci zakiyi? Maza zauna acan."


Komawa tayi ta zauna kusa da Asma'u inda Abba ya kalli Rauda yace "Ki ce su shigo ciki."


Sahura kuma darar Mimi ta d'auka ta shiga gyara mata ita a jikinta, an d'an d'auki minti biyu zuwa uku kafin suji sallama da gaisawarsu da mutane, har suna jin mama na tambayar Asas Hajia na fad'in "Haka Allah ya nufa, suma yayi saidai gaskiya bai tab'a mana irin haka ba."


Muryar Mama suka ji tace "Ku wuce ciki suna nan."


Da sallama a bukansu suka shigo inda Abba' Asma'u ya kalleta suka mik'e yana fad'in "Malam Adamu na ga magana ce ta cikin gida, zan jiraka a waje."


Da girmamawa yace "Haba malam *Bashir* ni da kai ai mun zama d'aya, dan Allah ka zauna zaka iya wakilta ta ai."


Komawa yayi ya zauna inda Hajia ma ta zauna bakin gado, mazan kuma duk kujera aka basu suka zauna, a hankali ta d'aga dararta dan so take ta kalli fuskar Asas d'inta, tana d'aga darar tare da idonta sai kuma idonsu suka had'e da nashi.


Da sauri ta ja darar ta koma gabanta na fad'uwa tana turo baki tace "Bana son ka dai, ba zaka bar nan ba saika sakeni."


Alhaji Ibrahim ne ya shiga fad'a musu duk abonda abinda ya faru daga farfad'owarshi har zuwanshi gidan, malam ne ya kalli sheikh yace "Yanzu kenan ya zo ya bata takardar saki a gabanmu ne?"


Da sauri sheikh ya kalleshi sai kuma yayi k'asa da kai cike da kunya, murya a raunane Asas yace "Ku taimaka min dan Allah, ina da buri sosai akan matar da zan aura, ina ji a jikina samun lafiyata zai ta'allak'a ne da matata, ku taimaka min dan Allah iyayena."


Ajiyar zuciya Saleh ya sauke yace "Idan hakane Asas kayi hak'uri da Mimi, a dangi akwai yara birjik sai ka zab'i wata a ciki."


Saida ya share hawaye yace "Tarbiyar Mimi ta min a rayuwa, halayenta na fad'in gaskiya tana birgeni, Mimi tana da *wayewa* daidai gwargwado, saidai ba kowa ke fahimtar kalar wayewarta ba sai wanda ya zauna da ita."


Kallonshi Asma'u tayi haka ma sheikh da yaji kamar ya gaura masa tapi a kunci, d'an satar kallonta ya sakΓ© yi amma bai iya ganin komai ba a jikina sai jar darar kawai.


Abba ne ya gyara zama yace "Indai wannan ne yasa kake so Mimi, ni nasan wacce tafi ta komai, me zai hana ka amince sai a d'aura muku aure?"


Duk kallon Abba sukayi inda Asas yace "Wacece zata fi Mimi a wajena?"


Kallon Asma'u yayi yace "Gata nan, k'awarta Asma'u."


Da sauri ta yaye darar fuskarta idonta tas akan fuskar Abba, sai kuma ta kalli Asas sannan ta juya ta kalli Asma'u data mik'e tsaye dafe da k'irjinta, wani murmushi ta saki tare da sunkuyar da kan ta k'asa. Asas ma kallon Asma'u yake data mik'e tsaye, ba ta da wata makusa namiji zai iya cewa bata mi shi ba saidai in baka son kyakyawa kuma fara, d'an kallon sheikh yayi da shi ma yake kallonshi, a tausashe cikin ladabi yace "Sheikh kai ne babba, ka zab'a min abinda ya fi dacewa dani, idan ta maka na amince ka min wakilci."


Yana fad'a ya done kanshi k'asa cike da Alhini, d'an murmushi sheikh yayi ya kalli Abba yace "Wannan karamci ne, mun gode sosai."


Kallon Asma'u yayi yace "Kin amince a had'in nan? Ki fad'i abinda yake zuciyarki."


Mimi da ta ji kamar da ita ake kai tsaye tace "Bai min ba, bana so."


"Uwata." Yanda Abba ya kira sunan yasa ta saurin d'aga kai ta kalleshi, sai kuma ya fashe da kukan shagwab'a tace "Abba na fad'..."


Mik'ewa yayi cikin fad'uwar gaba kar ta fad'i abinda take fad'a a bayan idonsu kamar zai mareta, cukuikuye Sahura tayi tana kwamtsa k'ara da fad'in "Abba zai kasheni."


Hannunta ya kalla dake kan k'irjin Sahura wanda yayi masifar yi mishi kyau a cikin k'unshin nan gwanin birgewa, d'auke idonshi yayi yana d'an girgiza kai a hankali, Abban Asma'u ne ya kalleta yace "Asma'u."


A sanyaye tace "Na'am Abba." Zubewa tayi k'asa gabanshi cire da taradaddin wannan abun, cikin nutsuwa yace "Me kika ce akan zab'in nan?"


Satar kallon Mimi tayi ita ma a lokacin lek'en fuskar Asma'u take, sunkuyar da kanta tayi tace "Abba ku iyayena, kun fi ni sanin daidai da ba daidai ba, duk abinda kuka yanke a kai na daidai zanyi biyayya insha'Allah, amma..."


Shirun da tayi yasa Abbanta yace "Amma me? Yi magana kinji."


Kamar zatayi kuka tace "Ina so k'awata Mimi ta amince da zab'in nan, bana so ta kalli hakan a matsayin cin amana."


Duk kallon Mimi akayi har da sheikh daya bita da kallon banza yana so yaji me zata ce, tabbas indai ta hanata aurenshi to zai sa yarinyar nan a bak'in jadawakinshi, dan shi kam Hafsat rainon gata ta masa bai saba da wahala ba, yakiceta zaiyi a jikinshi ba tare da shakkun komai ba.


A hankali Mimi ta kamo hannun Asma'u ta zaunar da ita kusa da ita, kallon Asas tayi tace "Indai uwa ta gari ka ke nemawa yaranka to Asma'u ta kai ta zama uwar kowa, gareni ta zama aminiyar da babu kamarta, gareka miji nasan zata zamar maka b'aren jiki, bata da k'yashi a zuciyarta bare ta ji tana hassada da kai, tana so ne dan Allah kuma tana k'i ne dan Allah, duk wani mugun abu dana aikata a baya ita ce mai nusasheni, mun yi fad'a da ita bila-adadin akan na daina ba kyau, *Ashraf da ina da yaya namiji dana nema mishi auren Asma'u*, ko mahaifina bai mishi tayin aurenta bane saboda a gaskiya ba zan so ta auri *tsoho* ba."


Dak'uwa Abba ya mata yace "Uwaki ce tsohuwar, mutuniyar banza."


Dariya Iya da Sahura sukayi har da Hajia ma sai Asma'u data sinne kai, Mimi kam gimtse fuska tayi tace "Ko sanda nake cika baki ina nuna nafi k'arfin na auri tsoho, ita ce ke dakatar dani tana nuna min kamar fariya nake, ashe gaskiya take fad'a tunda gashi na auri *sa'an babana*."


Da sauri sheikh ya kalleta yace "Allah ka yafe min akan ashar d'in nan da zanyi."


Jinjina kai yayi yace "Jar uba! Wai dama haka rashin kunya da fitsarar yarinyar nan ta kai? Lallai ashe dai *kallon kitse* nayi ma rogo ban sani ba."


Numfashi Hajia ta sauke ta kalli Mimi tace "Kiyi hak'uri kinji takwarata, shi ma ba tsoho bane zaki gane haka gaba kad'an."


Cikin k'arfin hali Asas ya d'aga kai ya kalli sheikh yace "Hajia tsoho ne mana kar ki sa ya ji dad'i a ransa."


Kallon Mimi yayi saidai ba da waccen idon ya kalleta ba, a yanzu yanzun nan da idon ke *matar yayana* ce ya kalleta yace "Matar yaya karki yarda kin ji, idan kuma ana da ja ba tsoho bane ya cire hularshi mana."


Dariya suka saka a d'akin bai da Mimi da Asma'u da kuma sheikh, Ibrahim ne yace "To yanzu ya zamuyi kenan? Za'a sake saka wata ranar ne kafin a d'aura musu aure?"


Da sauri Asas yace "A'a dan Allah Abba, ni dai kawai a d'aura mana aure yanzu idan sun amince, bana so a k'ara jan lokaci wani abu ya biyo baya."


Jinjina kai Saleh yayi ya kalli Bashir yace "Abban Asma'u ya kace?"


Nuna Abban Mimi yayi yace "Ga uban yarinyar ai, duk yanda yayi wallahi d'aya ne."


Abba ne ya gyara zama yace "A gani na kamar yanda ya buk'ata, indai akwai shedu da sadaki kawai a d'aura."


Alhaji Ibrahim ne yace "To ina ga ai kamar maganar maza ce, muje waje sai mu tattauna."


Mik'ewar da sukayi yasa Mimi kallon sheikh da tambayar kanta "Wai ba zai sakeni ba yake nufi?"


Da sauri tace "Abba shi f..."


Kallon da Abba ya mata yasa tayi shiru, cikin fad'a yace "Wai ke kina lafiya kuwa? Me yake damunki ne Mimi?"


Fashewa tayi da kuka ta fad'a jikin Iya tana fad'in "Abba na fad'a maka ni bana so wallahi, kawai a sawak'e min."


Wani uban rank'washi ya zuba mata a kai daya sata d'agowa dafe da gurin tana lumshe ido da suke rufe mata k'arfi da yaji, hannu ya kai kamar zai mareta yana fad'in "Ke dan ubanki har kinyi tsaurin idon da a gabana zaki dinga fad'in a sakeki? Yaushe aka d'aura auren Mimi, ina wasa dake ne da z..."


Malam ne yace "Dan Allah wuce mΓ» je zaka tsaya kana biye mata."


Hajia ce tace "Wai kuna nufin yanda zaku mata kenan idan mun barta a hannunku? A halin da take ciki kuma har ta cancanci duka da fad'a irin haka? Gaskiya ba zai yiwu ba jama'a."


Kallon Iya tayi tace "Mama dan Allah ki mana alfarma yau kam 'yata ta tare a gidana kafin mijinta ya sama mata gurin da zata zauna."


Cike da dattako iya tace "Wannan ai ba matsala bane Hajia, tunda dama ai a yau d'in ake da shirin tarewarta."


Da fara'a Hajia tace "To a shirya mana ita zamu d'auki abarmu, dan nan kam naga matsi zata sha."


D'an dungure ma Mimi kai Iya tayi tace "Gwara ta tafi ai ko na huta da jarabar taurin kan ta, dan in nan zata zauna saina fasa mata jikinta da duka."


Da raha Hajia tace "Ai na ga alama ne Iya."


Malam ma cewa yayi "Hajia kin kyauta min da zaki d'aukemin amaryata daga gurin sak'agunan nan, abinda suka iya kenan su sakata gaba suyita narka."


Duk wannan rahar da suke su sheikh na tsaye na saurarensu gaba d'aya jikinshi ya mutu jin hukuncin da Hajia ke ta yankewa a kan shi, haka suka fita Mimi kuma ta sake b'allewa da kuka, Asma'u ma duk da halin da take ciki saida ta taya su Iya rarrashinta, a k'arshe dai wajen kukan nan baccin wahala ya d'auketa dan wajen kukan har jan numfashi take sama sama.


Ai kuwa suna fita a masallacin unguwar sukayi sallah la'asar, ana sallamewa mutanen dake nan aka tattarasu aka d'aura auren Asma'u Bashir da Ashraf Sabi'u Aliyu Sharif, tuni unguwa aka d'auka kowa ya shiga fadin abinda ya ji ya kuma k'ara da abinda ya fahimta a kai, haka dai gidansu Asma'u ma sai suka fara wani shirin daban suma, inda kishiyoyin mamanta suka shiga bak'in cikin wannan had'i musamman da aka ce sheikh ne yace zai mata lefe bayan ta shiga d'akinta, tunda shi ma Asas ne yayi wa matarshi😁, abun bai musu dad'i ba ko kad'an sai ma da aka ce yau ita ma zata tare tunda dai da lallenta da kitsonta, ango kuma ya gyara d'akinshi to babu abinda za'a fasa.

*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *27*Sosai dangi suka ci gaba da bikinsu saidai kusan duka angaye da amaren zuciyoyinsu babu dad'i, Sadeeq kan shi yayi wani iri a zuciyarshi da ya ji an d'aura auren Asas da wacce yake da burin aura, amma sai bai nuna ma kowa ba kawai suka ci gaba da shagalinsu, Asas ma sosai yake k'ok'arin nuna dauriya amma abun ya gagara, yayi kuka sosai na rashin Mimi, yana tunanin yanda zai fara rayuwa da wacce sam ba ita ce a tsarinshi ba, sannan ya rayu a kusa da sheikh da matar daya ci burin aura, a wuni d'ayan nan duk sai ya zabge ya fita hayyacinshi, kana kallonshi zaka san yana da damuwa. Haka ta b'angaren Mimi ma ta kafe ta k'i cin duk abinda aka bata ta k'i shan komai ta fad'a ta nanata ita fa asa sheikh ya saketa, tun ana bata maganar har akayi banza da ita aka ci gaba da sabga, labari kuma ya karad'e gari da kewayenshi, sheikh Abdul Waheed yayi aure amarya shakaf, wasu na fad'in dalilin auren wasu kuma a iya auren suke tsayawa. Amma a wajen k'awayen Mimi abun ba haka bane, sosai suke Alhini da kuma son ganin yanda Mimi zata rayu a gidan sheikh, wacce take wanda suka auri tsoho iskanci, ita me fad'in Allah ya rabata da auren sa'an babanta, yau gashi ta samu a b'agas ba fahimtar juna ba soyayya? Abun kam ya jijjigasu inda kowace jiki yayi sanyi tare da komawa gefe dan suga me zai faru.           *D'aukar amarya*Ta wajen Asma'u kam motoci ne manya da k'anana guda goma sha hid'u suka d'auki dangi da abokan arziki aka nufi da ita gidanta cikin yada magana, kayan jikinta kawai aka d'aukar mata dan dama Asas yace baya buk'atar komai. A wajen uwata Mimi kam saida Abba ya nunata da bakin muciya kafin ta fito a gidan, mota uku Hajia ta turo a d'auketa a had'a da wanda zasu rakata gidanta kafin ranar tarewarta, a mota saida ta cika kunnen shi kan shi dreba dan kuwa kuka take sosai tana kiran "Mama, mama ke, mama, wayyo mama."


Har suka isa gidan Hajia dangi suka tarbeta aka sauketa a d'akin da Hajia ta ware mata wanda aka saka mishi komai na buk'ata, k'arshe dai kowa ya tafi ya barsu ana addu'ar fatan zaman lafiya da zuri'a ta gari. Kusan ba kowa a gidan kafin Hafsat ta zo dan su tarben matar Asas suka tafi, sanda ta samu Mimi aa d'aki kuka take sosai kamar ranta zai bar gangar jikinta, cike da tausaya mata ta zauna gefenta da k'yar tana cije fuska dan sosai ta gaji ga cikinta da take jin bak'in abubuwa da bata saba ba, saida ta dafa kafad'arta cikin taushin murya tace "Mimi."


D'an tsagaitawa tayi amma dai bata yi shiru ba, d'orawa tayi da "Mimi kuka kike dan an aura miki sheikh?"


Shashek'a ta shiga saukewa da sauri sauri, jin batayi magana ba yasa ta sake fad'in "Mimi ki kwantar da hankalinki kin ji ko, nasan waye mijina ba zai tab'a cutar dake ba, ki bani had'in kai mu zauna lafiya dake kinji Mimi?"


D'aga kanta tayi ta kalleta ido sun mata jajir sun kumbura tace "Dan Allah ki sa mijinki ya sakeni, ba zan iya zaman aure da shi ba, bana son shi kuma ba zan so shi ba."


Wani murmushi tayi mai ciwo tace "Mimi zaki so shi, ni ma da fari haka na d'auka, Mimi ko kinsan ni da sheikh *auren je ka ga d'akin ka* aka mana, ban sani ba shi ma bai sani ba dan a lokacin ma yana madina wajen karatu, mahaifina ya kwanta rashin lafiya kawai aka kira sheikh ya dawo gida, yana zuwa suka taramu suka fad'a mana ai sun d'aura mana aure, gidanmu kawai suka turamu muka fara zama."


Numfashi ta sauke tace "Mimi ke ma idan kika nutsu kika wa iyayenki biyayya zaki ga ribar hakan, ki daina wannan tashin hankalin hakan zai tab'a zuciyoyi da dama wanda ba zasu tab'a mantawa ba har abada, musamman iyayenki da suke ganin sun isa dake, amma a zahiri sai nunawa kike kamar kinfi k'arfinsu ko kuma dai basu isa su umarceki ba, ya kike so mutane su kalleki? A matsayin 'ya wace ta raina iyayenta bata jin maganarsu?"


Jikinta kam yayi sanyi dan haka ta dakata da kukan ta sake kallonta tace "Ban raina iyayena ba, hasalima ina fad'a da duk wanda ya raina min su, indai har abinda nake yi a yanzu yana nuna rashin girmamawa ne ga iyayena, to na daina, zan musu biyayya iya iyawata da yardar Allah."


Murmushi Hafsat tayi tace "Yawwa *yer uwa*, ko ke fa, ki share hawayenki kinji ko."


Jinjina kai tayi tasa hannu tana share hawayen, yunk'urawa Hafsat tayi da k'yar ta tashi tsaye tana fad'in "Wallahi ga gajiya ta baibayeni ga kuma nauyin da cikin nan ya min."


Da kallo kawai Mimi ta bita har tace "Saida safe Mimi, kiyi alk'awarin kin daina kuka."


D'an murmushin yak'e tayi tace "Na daina."


Da kallo ta bita har ta fita tana jin anya kuwa zata iya abinda matar nan tayi? Tab'e baki tayi a ranta tace "Indai kuka na alamu ne na raina iyayena ai na daina har abada, amma wallahi sai mijinki ya shiga *uku* dan zai ga tab'ara."


Cikin shashek'ar kukanta ta d'aga kai ta shiga kallon d'akin, ajiyar zuciya ta sauke da tunanin yau ita ce zata kwana a nan? Wacce take shinfid'a bargo ta kwanta, ba panka sai iskan Allah dake kad'awa,  yau gata a d'aki mai ac lak'e ga kuma panka, gyara dararta tayi ta kwanta ta dunk'ule sosai tana ci gaba da sauke ajiyar zuciya. *Asas*! Shi ne sunan daya diro mata a lokacin, da yanzu fa tana d'akinshi a matsayin matarshi, amma shi ne yanzu take zaman matar sheikh k'awarta kuma tana gidan Asas a matsayin mata, lallai inba hukuncin Allah ba me zai juya wannan al'amari haka, ai ko cewa akayi ka tsara dole zaka buk'aci dogon nazarin ta yanda abun zai kasance, amma gashi dake yin Allah komai ya canza kuma da wanda ya so da wanda bai so ba dole an hak'ura da yanda Allah ya tsara.               *Asa-Ma'u*


Tunda ya shigo gidan dare ya tsala sosai ya buga tagumi yana kallon Asma'u dake dunk'ule cikin k'aton hijabi ta had'a kai da gwiwa, baisan ta ina zai fara ba ko kad'an, a yanda ya tsara da Mimi shi ne zai mugun riritata. Ganin zaman shirun ba zai masa ba sai kawai ya sake k'ureta da ido yace "Asma'u."


A hankali ta d'an d'ago kanta tana jan majina da share hawayenta, a sanyaye ya sake fad'in "Muje muyi sallah ko?"


Jinjina kai tayi tare da k'ok'arin sauka a kan gadon, ita ta fara shiga tayi alwala ta fito shi ma ya shiga, sallah sukayi inda ya dafa kanta yayi addu'ar neman alkairin dake tare da ita da kuma neman tsarin dake tare da ita, mik'ewa yayi ya fita hakan yasa ta mik'ewa ita ma ta koma bakin gadon ta zauna tayi tagumi, "Allah sarki Mimi." Shi ne abinda ta fad'a, wa yayi tunanin canzawar abubuwa haka? Sosai take taisaya ma k'awarta musamman data tabbatar ba zatayi saurin duk'awa k'asa ta yarda da zab'in nan ba...Shigowar Asas ta sata saurin juyawa ta kalleshi, d'auke yake da tire da k'aramin faranti a sama, gefenta ya aje tare da fad'in "Bismillah."


Girgiza kai tayi cikin dakusashiyar murya tace "Na k'oshi."


Wani kallo ya mata cike da kawar da komai yace "Kina son d'ure ne?"


Girgiza kai tayi alamar a'a, fuska a had'e yace "To ci."


Jiki a sanyaye ta kai hannu ta d'an tsakuri naman ta kai bakinta tana rarraba ido saboda yanda ya tsaya yana kallonta, murmushi yayi tare da zaunawa kusanta ya saka hannu shi ma ya shiga d'auka yana ci yana saka mata a baki ita ma.


Suna idawa ta koma ban d'akin ta wanke hannaye ta kurkure baki ta fito, ganin baya nan sai kawai ta kwanta a kan gadon da zunbulelen hijabinta, ya d'an jima bai shigo ba har bacci ya d'an fara d'aukarta, kamar daga sama ta ji an bud'e d'akin da sauri ta bud'a ido amma bata juya ba, shi kuma yana ganin haka saiya kwanta gefenta yana karanta addu'a bacci.
                 *Shei-Haf*Hannu ya kai zai bud'e k'ofar d'akin amma saiya tsaya cak saboda muryar Aisha da ya ji tana fad'in "Amie wai me yasa Hajia tayi mana haka? Kuna zaman lafiyanku ke da Abie zata had'ashi da wata, me yasa bata hak'ura ba ta sake samun wani saurayin ta aura, Abien mu ba son ta yake ba ita ma haka, idan fa a dalilin auren nan matsololi suka fara faruwa? Ni gaskiya Amie ba zan juri wata yarinya ta raina min uwata ba, kawai ki fad'a ma Abie ya saketa can ta samu wani ta aura."


Bud'e k'ofar yayi sanda Hafsat ke k'ok'arin yi mata tsawa, kallon daya jefi Aisha da shi yasa sunkuyar da kai tana fad'in "Sannu da zuwa Abie."


Cikin yanayi mai rikita bil-adam yace "Sannu da zuwa Kike min Aisha? Ke!"


Yanda ya fad'i ke d'in yasa ta d'aga kai sai kuma ta sake sunkuyar dashi tana d'an wasa da maganin cowon k'afafun data gama shafawa Hafsat, cikin b'acin rai yace "Eesha ke ce da fad'ar wad'annan maganganun a bakinki? Yaushe kikayi girman da har magana mai girma irin wannan zata fita a bakinki? Kina so ki ce min taya uwarki kishi kike kenan?"


Da sauri Hafsat ta kalleshi da mamakin abinda ya fad'a, sai kuma tayi k'asa da kan ta ita ma ba tace komai ba, a tsawace yace "Tashi ki bani wuri, kuma na sake jin bakinki na magana kan abinda bai shafeki ba ki kuka da kanki."


Mik'ewa tayi jiki na b'ari tayi hanyar waje, tana daf da fita yace "Ke!"


Tsayawa tayi ta juyo tana d'an sunkuyawa, cikin murd'add'iyar murya yace "Zan d'aura aurenki da Anas ki fara shiri akan haka dan kowane lokaci zan iya d'aura muku aure."


Da sauri ta kalleshi ido waje baki bud'e, cikin rud'ewa tace "Abie Anas kuma?"


Sama da k'asa ya harereta tare da zaunawa bakin gadon kusa da k'afafun Hafsat da ita dai take jin su da kallonsu, ganin bai kulata ba sauta mik'e tana maimaita Anas a ranta, ta sani bai da wata makusa yaro ne mai k'ok'arin neman ilimi a duk inda yake, d'aya ne a cikin almajiran mahaifinta, yana da ladabi da biyayya sosai suna kallonshi kamar yaya saboda sheikh na d'an sakewa da shi, wasu lokuta ma har karatu yake d'ora mata, to amma ai babu wani tsari na soyayya a gabanta a yanzu, to me ma ya jawo maganar aurenta? Dan kawai ta yi wannan maganar? Ko dai mahaifinta na tsoron kar zamanta a gidan yasa a samu matsala idan amaryarshi ta zo gidan? Babban fargaban shi ne yanda bai saka lokacin ba kawai yace a kowane lokaci, hakan na nufin rana tsaka zata iya jin an d'aura mata aure kenan?


Kallon Hafsat yayi bayan fitar Aisha ya kai hannu kan cikinta yace "Ya kuke?"


D'an murmushin yak'e tayi tace "Lafiya lau, ya hidima?"


Numfashi ya sauke ya gyara zamanshi sosai yace "Manga, kin ga me ya faru a yau ko? Hakan ya sake tabbatar mana ba mu ke da ikon juya rayuwarmu a yanda muke so ba, k'arin aure Allah ne ya halatta mana shi, sai dai a yanda na wa k'arin ya zo a birkice sai naji hankali ya kasa d'auka, tabbas Hajia uwa ce a gaareni data isa zartar da kowane irin hukunci a kaina, saidai a wannan karan qta yanke min hukunci mai tsaurin gaske."


Numfashi ya sauke ya kalleta yana rik'o hannunta yace "Sawwama, na so a ce idan lokacin nan yayi na shawarce, na rarrasheki kamar kowace mace, sannan na miki bajinta kamar yanda ake yi a al'adance ta hanyar kyautatawa, amma duk da haka *Qawwama* ina mai baki hak'uri da yanda abun nan ya zo mana, nasan ke mai hak'uri ce da kawar da kai ga kuma juriya, kiyi hak'uri da hukuncin mahaifiyarmu mu yi mata biyayya, ni dama ke ce k'ashin bayana kuma martabata, dan Allah ki yafe min kinji."


Wani sanyayyen murmushi tayi tace "Hak'uri wai akan me kake bani sheikh nawa? Ni babu abinda ka min wallahi, sheikh karka manta fa na tab'a maka k'orafin k'ara aure amma sai ka ce lokaci ne baiyi ba, to yanzu lokacin ya zo ni kam zai saka ka tsaya kana bani hak'uri?"


Da k'yar ta gyara zama tana fad'in "Idan dai a yanda abun ya zo ne karka damu kan ka, ni Hafsat ina bayanka ba zan tab'a bari a rasa zaman lafiya a gidanka ba insha'Allah."


Murmushi yayi yace "Nagode Hafsy, yanzu fad'a min me kike so?"


Dariyar tsokana tayi tace "Dokin wuya."


Dariya yayi tare da mik'ewa ya durk'usa gabanta yace "Hau muje kinji ta wa."


Dariya tayi sosai tace "Na yafe, wace ni dan zan haye wuyan babban malami a daren nan?"


Wani shu'umin kallo ya mata yace "Ke a mai d'akin shehi mana."


Gyara zama tayi tana yatsina fuska tace "Hakane, amma ai mala'iku ma zasu iya yin hushi dani."


Cike da kulawa ya dafa cikinta yace "Ba kya jin dad'i ne?"


D'an k'aramin tsaki tayi tace "Gaba d'aya cikin nan ya daina min dad'i yanzu, bansan me yasa ba."


Cike da alhini yace "To kinga ki shirya gobe sai muje asibiti ko?"


Jinjina kai tayi dan dama ba musu take mishi ba, ko tana so ko bata so indai yace ayi to yi kawai zatayi.
                   *Asabar*Tun asuba da Hajia ta tashi Mimi a bacci ta ji zazzab'in dake jikinta, saida tayi sallah ta kawo mata magani tasha, kallon Hajia tayi da tunanin anya kuwa? Ta ya zata fara shan magani a gabanta? Bata son magani a kai saboda d'aci, karb'a tayi tace "To."


Fita Hajia tayi hakan yasa Mimi d'aukar maganin ta jefa ta windown dake jikin gadon, d'an kurb'a ruwan tayi tare da komawa ta kwanta tana dunk'ulewa, ta d'auka bacci zai d'auke ta saidai sam zafin jikinta da kakkarwar da take ga ciwon kai sai suka hanata samun baccin.


*08:00* Hajia ta turo Salamatu data zo tace ta kira Mimi ta zo tayi kari, tana shigowa d'akin da yatsina fuska ta tunkareta, yanda ta ganta a kwance ta d'auka bacci take har take fad'in "Hmmm! Yar matsiyata kenan an samu wuri, ga lafiyayyen gado ga ac na hura miki iska mai tafe da sanyi, kinga har da wani baccin safe take alhalin iyayenta na can na fama da rana a tsakiyar kansu."


Duk bala'in ciwon da take ji saida ta yaye hijab d'in ta tashi zaune, wani kallon tsana da k'yama ta shiga jefawa Salamatu, ba wai ita mai aiki ba ko Hajia ce ta fad'i haka wallahi saita narka mata magana kafin ta tattara ta bar gidan, kamar yanda ta ji ita ce tasa aka aureta to saidai ta sa a bita da takardarta gida.


Gyara zama tayi sosai cikin muryar wahala da jigatuwa ta kalli idon Salamatu tace "...
_Wannan page gaba d'aya sadaukarwa ce gareki *Bilkissu Kanar*, Allah ya saka miki da alkairi._
*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *28*Gyara zama tayi sosai cikin muryar wahala da jigatuwa ta kalli idon Salamatu tace "Gaskiya ne, saidai na ga dasu iyayen nawa da ke ma d'in duk a kanku ranar ta fito ai, tunda babu wanda ya tara dukanku nema kuma, kuma gwara iyayena tunda neman nasu yana wadata zuciyarsu, ke kuma fa? Dubeki kamar ba'a gidan masu kud'i kike aiki ba tsabar bak'ar zuciya, amma dubeni..."


Ta fad'a tana nuna mata fatar jikinta tace "Duk da a cikin talauci muka taso sannan babu kyakyawan rayuwa, amma hakan bai hana fitowar hutu a jikinmu ba saboda wadatar zuci, kinga Baaba bansan ki ba, amma ya zama na k'arshe da zaki dinga huce haushina akan iyayena, bana d'auka wallahi."


Murgud'a mata baki tayi tare da gyara kwanciyarta ta sake rufewa a cikin hijabi, da mamaki Salamatu data nemi daskarewa ga wani shakkun yarinyar ta zabura tayi waje, saida ta kai falon kawai ta fashe da kuka ta d'ora hannaye saman kai, hankali tashe cikin fad'uwar gaba Hajia ta tarbeta tana fad'in "Salamatu lafiya? Me ya faru da Mimin? Me akayi?"


Cikin kuka kamar zata tsaga gidan tace "Hajia tunda na ke ban tab'a ganin fitsararriya kuma marar kunyar yarinya irin wannan ba, da girma na da mutumcina a gidan nan, duk zaman mutumci da amanar da muke daku ace yarinyar can daga zuwanta gidan nan jiya zata tsaya tana zagina tana min iskanci."


Cikin jin haushin dogon sharhin Hajia tace "Wai me ya faru ne? Me ta miki da kike mana wannan kukan?"


Ba tare data tsagaita kukan ba tace "Hajia daga shiga na tasheta kawai ta kama fad'a min magana wai bansan darajar mutum ba, hada fad'a min ina aiki gidan masu kud'i amma talauci ya k'i barina saboda abun a zuciyata yake, ni? Ni? Salamatu shi ne har da nuna min jikinta take wai ita yar talakawa ma ta fini kalar hutu."


Me Hajia zatayi banda kecewa da dariya, girgiza kai tayi tana dariya kawai ta wuce d'akin Mimi ta bar Salamatu tsaye, da kallo ta bita na mamaki tace "Me ye abun dariya kuma?"


Saida ta ga shigewarta d'akin sai kuma ta zaro ido tace "Kar dai ta fad'a mata abinda na ce?"


Da sauri ta nufi madafa hannu a kai tana fad'in "Na shiga uku na lalace."


Hajia na shiga da sallama Mimi bata iya amsawa ba, da sauri ta k'arasa ganin sai kakkarwa take, tallabota tayi cikin tsananin tashin hankali tana fad'in "Subhanallah Mimi! Dama zazzab'in nan bai rabu da ke ba har yanzu?"


Saida ta gyarata ta zauna kafin ta kalleta da tausayawa tace "Wallahi na d'auka tunda kika sha maganin bacci kike, ashe zazzab'i ne yayi k'amari."


Jiki na rawa ita ma ta shiga lalubar poshet d'inta da take yawo da ita ko a cikin gida, waya ta ciro tana fad'in "Bari na kira sai muje asibiti ko?"


Lambar sheikh ta dannawa kira wanda a lokacin yake d'akin karatunshi da na'urarshi a gaba yana kurb'a shayin da Hafsat ta kawo masa, d'aukar wayar yayi a sauk'ake ya furta "Salam."


Da sauri Hajia tace "Wa'alaika, sheikh kana ina ne?"


Jim ya d'anyi kafin yace "Hajiarmu lafiya dai ko? Ina gida ban fita ba."


Da sauri tace "Yawwa dan Allah ka zo yanzu, kaga Mimi ce wallahi zazzab'i tun asuba kuma tasha magani amma bai sauka ba, shi ne na ce gwara aje asibiti."


Shiru yayi kamar bai ji ba ko kuma ba da shi take ba, wani numfashi ya sauke dan yana tashi da asuba ya tuna kan shi fa nauyin mace biyu ne yanzu, a hankali kuma a gadarance yace "Gani nan zuwa."


Jiki na rawa Hajia tace "To sai ka zo." Kashe wayar tayi ta kalli Mimi data koma ta kwanta, sunkuyawa tayi ta shafi kuncinta tace "Sannu kinji takwara, kiyi hak'uri yanzu *mijinki* zai zo sai muje asibiti."


Da k'yar ta d'aga idonta ta kalleta har sun canza mata launi, cikin son dole sai tayi magana ta rik'e hannun Hajia tace "A'a, a'a Hajia, bana so, bana son zuwa asibiti, ki ce yayi zamansa dan Allah na rok'eki."


Zaune tayi gefenta tace "To banda abun ki Mimi an tab'a zama da ciwo haka? Zazzab'i bala'i ne takwarata, tsaf yanzu zai rabaki da jininki sai an koma tarbata ana k'ara miki."


Sake jimk'e hannun Hajia tayi tace "Ni dai idan kika zuba min ruwa a jikina ma zanji sauk'i, bana son zuwa asibiti wallahi, kana zuwa allura suke maka."


Komai Hajia ba tace ba sai mamatsa hannun Mimi data dinga yi, a k'alla minti ashirin ya kawoshi gidan, kai tsaye d'akin ya shigo da sallama a bakinshi, da sauri Hajia ta amsa sai Mimi da tayi ram da k'ugun Hajia cikin muryar galabaita tana fad'in "Karki bari ya kaini asibiti kin ji uwata, bana so wallahi na tsani allura, idan kika bari ya tafi da ni ba zan zauna gidanki ba."


Yanda take cumimiye k'ugun Hajia yake kallo ita kuma tana ta murmushi, kujerar gaban madubi yaja ya zauna yana kallon Hajia, ita ma kallonshi tayi tace "Ya zamuyi yanzu? Tace bata son zuwa asibiti."


Wani kallo ya wurga mata duk da ba fuskarta yake gani ba yace "Dama ba dan tana so zamu kai ta ba."


Kallon Hajia yayi yace "Ku shirya sai mu tafi."


Dariya Hajia tayi tace "Ba dani zaku tafi ba, dan har yanzu akwai bak'in da basu tafi ba."


Kallon Mimi tayi data dunk'ule tace "Tashi ki gyara hijabinki sai ku tafi."


Girgiza kai tayi alamar a'a, wani kallo kawai ya shiga bin ta da shi, cikin muryar da babu wasa a ciki yace "Jiranki fa nake, ina da abun yi."


Gabanta ne ya shiga fad'uwa da k'yar ta yunk'ura ta d'ago, a kan shi ta sauke idonta wanda shi ma a kan ta na shi idon suke, da sauri ta sinne kan ta saboda wata irin kunya data kamata, ko a tv bata tab'a ganinshi da kaya irin na yau ba, zallar d'inki ne kawai riga da wando tazarce sai hula a kan shi.


Ganin kallon da yake mata yasa Hajia mik'ewa tace "Bari na sama mata ko madara da zata saka a cikinta."


Fita tayi ba tare da ta ji me zai ce ba, rawar da jikinta ke yi ne ta k'aru sai ta rasa yanda zata yi ta sauka a kan gadon, murya a dak'ile yace "Jiranki nake malama."


Hijabi tasa tana murza ido cikin kukan shagwab'a tace "Ni bana son zuwa asibiti, na warke fa babu abinda yake damuna."


Mik'ewa yayi tsaye yace "Ke." Da sauri ta kalleshi dan indai y'a ce ke dole ka kalleshi, da sauri kuma tayi k'asa da kan ta sanda yake fad'in "Sauko a gadon nan kafin na tsula miki tsumagiya, kinsan haushinki ne dani ko?"


Da sauri cikin rashin k'arfin jiki ta shiga saukowa a kan gadon, saida tayi tsaye k'afafunta na mata rawa sosai ta kalleshi tace "Abdu..." Gumtse bakinta tayi sai kuma tace "Yallab'ai, dan Allah idan munje karka bari su min allura."


Wani firgitacen kallo ya mata daya razanata yace "Har a baki sai na ce a miki ko zaki daina yin k'arya."


Da sauri ta shiga nuna mishi da hannayenta tace "Na daina ai tun ranar, wallah..."


Sake zaro mata ido yayi shi yasa tayi shiru saai kuma tace "Tun waccen ranar na daina, ba zan sake ba Allah ko."


Yatsina fuska yayi yace "Wuce muje."


Silipas d'inta dake gaban gadon ta zura k'fafunta tayi gaba jikinta na rawa gab-gab-gab kamar ba zata iya tafiyar ba, saida ta kusa kaiwa k'ofar fita yace "Miye wannan kuma malama?"


Juyowa tayi sai taga ashe yana tsaye inda yake, dudduba jikinta ta shiga yi ganin bata ga komai ba saita kalleshi da alamar tambaya, cikin murtuke fuska yace "Wannan hijabi ne a jikinki?"


Duk'ar da kanta tayi tana kallon hijabin daya saukar mata har wuce gwiwoyinta, d'agowa tayi da mamaki tace "Hijabi ne mana."


A take cike da gatsali yace "Bai min ba, canza shi."


Galala tayi da baki ta kalleshi, ganin bata da niyyar yin abinda yace yasa shi cewa "Na ce ki canza shi ko?"


Turo baki tayi cikin sangarta tace "Ai duk sauran ma haka suke, kuma ba duka kayana bane aka d'auko."


Tab'e baki yayi yace "To nik'ab fa?"


Baki bud'e ta kalleshi tace "Nik'ab kuma? Ni da ba lafiya gareni ba?"


Cikin wurga mata harara yace "Dan baki lafiya sai aka ce jikinki abun talla ne?"


Gumtse bakinta tayi ta sinne kan ta, sama da k'asa ya harareta yace "Shi waccen sharb'eb'en da kike sakawa sai kina son nuna ta Allah ce ke ko?"


Takowa yayi da sauri yana fad'in "Muje, amma ki sani dole ki canza tsarin shigarki, dan wannan bata min ba."


Kaucewa tayi da sauri ya bud'e k'ofar ya fita sannan ta bi bayanshi, tana fitowa haka tayi ta jan hijabinta tana rufe fuskarta saboda bak'in dake nan wasu na ta haramar komawa inda suka fito, gaishesu tayi a ladabce suka amsa tare da fatan sauk'i a gareta. Tana fitowa daga falon ya shiga hangenta daga zaune da yake a motar, kamar wai ba ita ce yake jira ba take wata tafiya kamar wahainiya, yo shi ko Hajia ma ta tab'a sashi jiranta kamar haka kuwa? D'auke kai yayi daga kallonta yanaa d'an jan guntun tsaki.


Baya ta kama zata bud'e ya juyo ya kalleta, saki tayi ta koma gaba ta bud'e ta shiga, kakkauran hannunshi ta kama wanda agogon hannun ta cikashi dam, d'auke idonta tayi a ranta tace "Hummm!"


Saidai yanda ta fad'i humm! D'in yasa shi kallonta dan ta fito, saida ya juyar da kan motar zasu fita ya kalleta yace "Miye?"


Kallonshi tayi tace "Ba komai."


BΓ’ tare daya kalleta ba yace "Ban son k'arya, ki tabbatar kinsan me zaki dinga fad'a min kinji ko."


K'wafar da yayi yasa ta saurin cewa "To." A ranta kuma tana sake k'iyasta yanda ta wani shiga mota d'aya da mijin aurenta, mijin ma kuma tsoho sa'an babanta, yanzu nan a ganta da k'uruciyarta sai kawai ta ce shi ne mijinta, wasu k'walla ne ta ji sun taho mata tare da saka yatsarta ta share kawai tana kallon titi ba mai ma kowa magana.


Yana paka mota kamar jira take tayi saurin fita ta tunkari asibitin, cikin dak'ilalliyar murya yace "Ke!"


Lumshe ido tayi a ranta tace "Ohhh! Wai wani ke! Miye haka dan Allah."


Juyowa tayi a hankali tana kallonshi a ladabce, da ido ya mata alamar "Tsaya a gefena."


Take fuskarta ta nuna alamar rashin jin dad'i, juyawa tayi ta d'an shiga kallon mutanen dake kai kawo, tana cikin yatsina fuska kamar yasan me take tunani yace "Kunya kike ji a ga kin jera da *tsoho a matsayin mijinki*?"


Kumbura fuska tayi da baki tare da jan hijabinta ta rufe daga bakinta har zuwa hanci, k'wafa yayi tare da wucewa gaba yana fad'in "Bansan rashin kunyarki ta kai haka ba Ryam."


Ita dai biyarshi take yi a baya yana shiga lungu da sak'o na asibiti, ganinshi a asibitin yasa duk ma'aikatan da suka ganshi suke gaisheshi da girmamawa, wani matashin ma'aikaci ya tambaya Dr. Rakiya? Dan haka da kan shi ya musu iso zuwa ofishinta dan tana tsaka da duba mata da suka kama layi, sanda zai shiga ofishin ne ya kula bata bayanshi, juyawa yayi saiya hangeta nesa dashi sai wani rufe fuska take, jinjina kai yayi a zuciyarshi yana fad'in "Ba dai ni kike jin kunyar jerawa dani ba? Zaki gane baki da wayo."


Shigewa yayi ofishin ya zauna yana karb'an gaisuwar Dr. Rakiya, saida suka gama gaisawa kafin Mimi ta shigo da sallama k'asan mak'oshi, Rakiya ce kawai ta amsa tana sakar mata murmushi, sosai take kallon yarinyar wacce jiya labari ya karad'e gari sheikh ya aura ko kuma an aura ma sheikh ita, dan har hotonta ta gani wanda aka had'a ita da Asas amma Allah bai nufa ba. Tsaye tayi tana kallon kujerar da zata zauna wacce ke fuskantar sheikh dake zaune, hannu ta kai zata ja kujerar baya taa zauna sheikh yace "To ke da zaki fad'a mata abinda ke damunki, ya kuma zakija baya *Mari*?"


Kallonshi tayi kamar ta gaura masa mari domin ta fahimci so yake ya cizgata a gaban mutane, kaikaitawa tayi ta d'an tsoma mazaunanta tana kallon likitar, murmushi ta sakar mata tare da d'aukar katin marasa lafiya tace "Madame sunanki?"


Saida ta ja hijabinta sosai kafin tace "Mimi...au! Maryam."


K'ura mata ido yayi kamar mai burin rikitata yana sakin murmushin mugunta, Mimi kam data fahimta ko kallonshi ba tayi ba har likitar tace "Sunan mahaifi?"


A sanyaye tace "Uban kowa."


Da sauri ta d'aga kai ta kalleta haka ma sheikh daya sake kafeta da ido, sai kuma yayi murmushi ya d'an d'ago daga jinginar da yayi tare da kai hannunshi ya lalubo hannun Mimi a cikin hijabi ya rik'o, a razane ta kalleshi tare da k'ok'arin k'wacewa, sai kuma ya jimk'e hannun gam yana mata murmushi, ba tare daya daina wannan murmushin ba yace " *Innar Issa*, sunan Babanmu zaki fad'a mata kinji, ki daure ki fad'a mata."


Kyab'e fuska Mimi tayi ta fashe da kuka dan ta lura kawai ci mata mutumci ne ma zaiyi, wai babansu? Sa'an Abba ne fa amma yake cewa babansu, d'auke kanshi yayi daga kallonta ya kalli likitar yace "Dr. Ki saka Maryam Adam Shehu, shekaru 18."


Da sauri ta fizge hannunta tace "Abdul ban kai 18 ba fa, 17 ne wallahi."


Da sauri sheikh ya cije leb'enshi na k'asa sakamakon dariyar data nemi kubce mishi, hannu ya kai akan hab'arshi yana d'an saita kanshi tare da rik'e dariyar. Rakiya kam zaro ido tayi a ranta tace "Tofa! *auren yarinya* kenan."


Duk'ar da kanta tayi tana rubuta abinda ta tambaya, d'agowa tayi ta mik'owa Mimi abun d'aukar zafi, karb'a tayi tare da marairaicewa tace "Dan Allah ba zaki min allura ba ko?"


Murmushi ta mata tace "Ba zan miki ba indai zazzab'inki bai kai matakin ba."


Sheikh dai na kallonta sai k'ok'arin saka abun awon zafin take, saidai dake tun kayan jiya ne jikinta da suka matseta sai hannunta ya k'i shiga bare ta saka abun ya zauna mata a hammata.


Lura da haka yasa Rakiya fad'in "Ko ki zage zip d'in rigar? Dan naga kamar ta kamaki sosai."


A hankali ta aje abun d'aukar zafin ta zura hannayenta baya ta fara kiciniyar cirewa, sheikh kam takaici ne ya kamashi da tunanin haka take saka kayan kenan ita ma kamar dai 'yan zamani. Kamar da wasa sai ko yasa hannu biyu ya jawo gaba d'aya kujerar da take zaune wanda hakan ya haddasa bayar da k'ara akan tiles d'in 'kiiiiiiii! Zaro ido Mimi tayi ganin yanda ya jawota kamar wata beby duk da girmanta, bata gama sarewa da lamarinshi ba saida ya zura hannayenshi a cikin hijabinta ya kaisu a bayanta ya shiga lalubawa inda zai ji zip d'in. Tuni Mimi ta fara kakkaucewa tana babbank'arewa, zafin da yaji a jikinta yasa shi jin kamar ya cire mata rigar gaba d'aya ya rumgumeta a jikinshi ko ya samu damar d'auke mata zafin, saida ya ji ya rik'e zip d'in ya ja shi a hankali tare da sake matsawa daf da ita a kunne ya rad'a mata "Tsofaffi ba ruwansu tunda ba sha'awa garemu ba, miye na d'aga hankali daga cire zip na riga."


D'aukar abun awan zafin yayi tare da d'aga hannunta ya soka mata ya had'e mata hannun sannan ya ciro hannayenshi daga hijabin, Mimi kam addu'a take kar Allah ya d'auki ranta da mamakin tsohon nan, wata tambaya ta jefawa kan ta "To wai me yake nufi ne?"


Gemunshi kawai ta k'urawa ido mai d'auke da farin gashi d'ai-d'ai, saida taji tinnnn! D'in abun awon zafin ta d'an zabura ta kalli likitar data tara mata hannu, cirowa tayi ta mik'a mata ta duba, mik'ewa tayi tana fad'in "Bari mu gwada jininki mu gani."


K'ura mata ido Mimi tayi ganin ta d'auki d'an shud'i abu k'arami ta cire a gidanshi sai kuwa tsinin allura ya bayyana, zabura tayi ta mik'e tsaye tana saka kukan shagwab'a da fad'in "Bana so ni dai na fad'a miki tun farko, Abbana, Abba ma ya san bana son allura wallahi."


Ganin tana shirin zabgawa da gudu yasa shi mik'ewa ya tura kejarar baya, hijabinta ya rik'e yana kallon fuskarta duk ta rud'e yace "Innar Issa ya haka? D'an tsikara miki ne fa za'ayi ba zafi, haba mana *'yan matan tsohonta*, so kike a mana dariya ne."


Dariya Rakiya keyi inda Mimi ta shiga tsatsare k'aramin bakinshi da ido wanda bak'in gashi ma yake hanashi fitowa da kyau,wasu hawaye masu zafi ne suka taho mata akan kumatu, ba tare data d'auke idonta a cikin nashi ba murya a raunane tace " *Bawan Allah*, amma dai ai saida na fad'a maka bana so ko?"


Wani daban yake ji shi wallahi a lokacin a wani sake sakayau, ga isashen lokaci ga kuma wata k'uruciyarshi da yake jin ana neman dawo masa da ita baya, babu masu fad'in gafarta malam, babu ranka shi dad'e, babu sheikh ko malam, babu kurantawa da girmamawa mai cike da kambamawa, babu amsa umarninshi cikin d'aukakawa. Hasalima a nan shi ne ke k'ak'arin rarrashi, kai tsaye ake kallonshi ana fad'a masa abinda akayi niyyar fad'a, yau gashi har yake iya bada umarni sau biyu, bugu da k'ari ma har yayi magana kai tsaye aka ce a'a ba haka bane, wanda ko cikin wa'azi da dubannin mutane ke kallonshi da saurare aka samu akasi da ajizanci na d'an adam ya fad'i ba daidai ba kai tsaye ba'a katseshi, wani saidai bayan an tashi ya fad'a ko kuma a kirashi a waya ko kuma dai a rubuta mishi wasik'a.


Wani k'ayataccen murmushi ya sakar mata tare da jawota gaba d'aya ta kusa fad'awa jikinshi, d'an kashe mata ido d'aya yayi yace "...

_Sadaukarwa ga duk 'yan *duk nisan jifa* da kuma *matar mutum*_
*Alhamdulillah*

Post a Comment for "MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 7 Na Samira Harouna"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...