MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 5 Na Samira Harouna - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 5  Na Samira Harouna

MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 5 Na Samira Harouna

- - Post a Comment

 MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 5

Na Samira HarounaπŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *17*Idonta taf hawaye ta kalleshi tace "Tsoro nake ji ni dai."


Murmushi yayi yace "Tsoron me? Ba mugu bane ba fa." Ya fad'a yana satar kallon sheikh da a lokacin yake kallon fuskarta, shi wallahi maamaki ma yarinyar ke bashi, ta ya ya k'aramar yarinya kamar wannan tayi abinda tayi? Me yasa ta aikata mishi haka? Me ye burinta a duniya ko a rayuwa? 


Da takon k'arfi ya juya da hanzari ya fita daga falon dan har ga Allah zuciyarshi tafasa take, musamman idan ya tuna shi ne aka wa wannan shak'iyancin, da sauri Asas ya kalleta yace "Muje." 


Bin bayanshi yayi da sauri inda Mimi ta shiga takawa da k'yar tana sab'a rigarta a hannu da take jin ta mata nauyi, Hafsat da yaran kam daga baya suke binta suna mata addu'ar Allah ya tsare, duk da dai Hafsat tana jin wani abu a zuciyarta, da fari yanayin mai gidanta kawai ta kalla a lokacin da yake kallon Mimi ta fahimci akwai wani abu, uwa uba daya ce zai mayar da ita gida, saidai dake tasan waye mijinta kuma ta yarda dashi, sam bata kawo komai a ranta ba musamman mummunan zargi, daga bakin k'ofar suka tsaya ita ta wuce wajensu, tsaye suke sheikh na shirin shiga mota ta kalli Asas tana sako hawaye tace "Ka mayar dani gida da kanka, na fad'a maka tsoro nake ji."


Tsayawa yayi dan sarai yaji me ta fad'a, kallonta yayi irin kallon naan na ban tsoro duk da idonshi a cikin glas suke, cikin muryar da bata saba ji ba ko a tv yace "Me kike ji ma tsoro? Kina da laifi ne da ba kya son tafiya tare da ni?"


Kallonshi tayi tana girgiza kai hawaye na zubowa a idonta, a sanyaye Asas yace "Wuce ku je maah."


Hannu tasa a idonta ta shiga murzawa sosai tana fashewa da kuka cikin siririyar muryarta harda bubbuga k'afafu tana fad'in "Ni wallahi bana so, kawai ka san yanda zakayi da ni."


Baki bud'e Asas ya shiga kallonta da matsanancin mamakin shagwab'ar da take bugawa. Inda a wajen sheikh kuma yayi saurin d'auke kanshi yana furta "Hasbunallahu wani'imal wakil."


Cije leb'enshi yayi na k'asa tare da lumshe ido, ya d'auki minti d'aya haka kafin ya juyo ya kalli Asas yace "Ba sauri kake ba?"


Jinjina kai yayi yace "Wallahi ina so naje naga halin da bawan Allahn nan yake."


Da ido ya fara masa alama kafin yace "Je kawai."


Jinjina kai yayi tare da kallon mimi, k'yabta mata ido yayi ya wuce bai ce komai ba, saida ya saka ledar da Eesha ta bashi kafin ya ja motar ya bar gidan. Tunda ya ba Asas umarnin tafiya ta kama bakinta ta rab'e wuri d'aya. Juyowa yayi ya kalleta a mugun dak'ile ya mata alama da hannu ta shiga, jiki na rawa ta matso daf da shi ta rab'ashi ta d'aga k'afarta ta wuntsila cikin motar, rufe k'ofar yayi tare da kallon dreban ya tara hannu alamar ya bashi makulli, mik'a mishi yayi ya karb'a tare da fad'in "Zan dawo yanzu, ku jirani a nan."


Bud'a mazaunin dreban yayi ya shiga, a tsanake kuma a hankalce ya tayar da motar ya shiga janta har suka fita a gidan, shiru motar ta d'auka babu ko sautin numfashi bare redio, a sanyaye yake tuk'i sai d'an sautin ac kawai da sanyayyen k'amshin dake fita.


Daga bayan nan da take hangenshi kawai take tana k'are masa kallo, hak'ik'a yanayinsa kalar fuskarsa, saidai a zahiri da bad'ini yana da b'oyayyen k'wanji, ga kuma iya d'aukar ado da k'wallisa da kuma kyau. Had'e hannayenta take a tsakanin cinyoyinta saboda fitsari take ji sosai, kayan cikinta yamutsawa kawai suke yi ga kuma fad'uwar gaba.


Daidai babban hanyar dake d'auke da titi biyu a hannun da suke ya ratse gefe yaja birki ya tsaya, dum dum dudum! Gabanta ya shiga dokawa da mugun k'arfi, sake k'amk'amewa tayi sosai tana rintse ido hawaye na silalowa, a ranta take fad'in "Tabbas da tare nake da Asma'u, da haka bai faru ba, wayyo Allaana k'awata."


Da sauri ta bud'e ido jin k'arar bud'e motar, tana kallo ya fito a nutse ya rufe k'ofar ya bud'e inda take, ganin ya bud'e k'ofar da take zaune yasa ta ja baya da k'arfin bala'i tare da kama d'aya k'ofar zata bud'e, wani kallo ya watsa mata duk da akwai duhu yace "Kina fita a nan zan had'ani da karnuka."


Dakatawa tayi tare da fashewa da wani sabon kuka irin na tab'ara saidai kuma da gaske take yin shi, hannayenta biyu ta d'ora a kai tana fadin "Na mutu na lalace ni Mimi? Dan Allah dan annabi ka yafe min sheikh, na tuba wallahi bΓ’ zan sake maka k'arya ba."


Ba tare daya daina kallonta ba ya shiga ya zauna yaja murfin ya rufe, shi kanshi sai yaji abun wani iri saboda rashin sabo, idan ba Hafsat ba babu macen da ya tab'a zama da ita haka a mota, gyara zama yayi sosai yanzu suke fuskantar juna, muryar a dak'ile ya shiga wurga mata wani kallo yace "Me yasa kika min k'arya? Akan me kika maidani shashasha? Akwai gaba a tsakanina da wani naki ne?" 


Girgiza kai tayi cikin matsanancin kuka tace "Wallahi babu, ni ma ba'a son raina bane haka ta faru, wallahi a lokacin..."


"Shiru." Ya fad'a a matuk'ar tsawace, a harzuk'e ya kalleta yace "Taya kuka had'u da Asas? Wane irin so kike masa?"


Cikin kukan tausayin kanta baki na rawa sosai tace "Ni wallahi ina son shi da zuciya d'aya, amma idan ka ce na daina kulashi zan daina daga yau, kuma ni na manta inda muka had'u."


"Kin manta?" Ya tambaya yana mata tuhumammen kallo, cikin in'ina tace "Eh to...ina ga..kamar dai a hanya..., ni wallahi na manta ina ne, a rikice nake Abdul..."


Duk da ta kai k'arshe saΓ― kuma tasa hannaye biyu ta rufe bakinta tana k'walalo ido, ita kanta bata san me yasa take son kiranshi da sunan ba musamman idan suna tare. Duk da wani mugun dad'i ne ke kasheshi ganin rud'ewarta da duburburcewarta had'e da kukan nan, ga kuma sunan data kira daya kwana biyu yana mararin sakΓ© ji daga bakinta, daurewa yayi sosai ya had'e fuska yace "To me yasa kika amince na je gidanku yau?"


Cike da makirci ta dafe cikinta tana fad'in "Cikina ciwo yake, ka ajiye tambayoyin zan amsa maka su a gaba idan mun sake had'uwa, yanzu ka kaini gida nasha magani."


Wani k'ayataccen  murmushi ya saki yana mamakin Mimi da ya ga sam bata d'aukeshi da girman da kowa ya d'aukeshi ba, jinjina kai yayi ya sake kafeta da ido yace "Fad'a min gaskiya, zaki iya zama da Asas domin Allah?"


Da sauri ta kalleshi tace "Wallahi zan..."


Nunata yayi da yatsa yace "Kika sake min rantsuwa a wurin nan kafin magana saina tsinka miki mari Ryam, tabbacin k'arya zaki fad'a shiyasa kika min rantsuwa akan k'arya."


Girgiza kai tayi tana dafe kumatunta da hannu biyu, wata harara ya kuma wurga mata yace "Yi magana ina jinki?"


Gyad'a kai ta shiga yi kamar k'adangaruwa tace "Ina son shi, zan zauna da shi."


Lumshe ido yayi tare da jingina bayanshi a kujerar yasa hannun dama ya cire glas d'in fuskarshi, "Hasbunallah wani'inal wakil, La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntun minna zalumin."


Abinda ya dinga maimaitawa kenan kafin ya bud'e idonshi tar a kan titi, cikin d'aga sauti yace "Astagfirullah, Allah na tuba ka yafe min zunubaina, Allah ka gafarta min laifukana, nasan ni d'an adam ne kuma ajizi, bansan yaushe kuma a ina ba, amma ina neman gafararka ubangiji."


A hankali ya girgiza kai ya juyo ya kalleta, kanta a k'asa tana share hawaye ga wani mugun tausayin mutumin da taji ya dirar mata, fuskarta sam ba tayi kama da wacce zata iya aikata abinda ta aikata ba, sam *kamaninta bata da suffar cutar da kowa*, saidai shi ta cutar da shi sosai, ta raunata zuciyarshi yanda har takai matakin babbakewa k'urmus. A hankali cikin amon murya mai d'auke da alhini da jimami yace "Ban tab'a tsammanin haka zai iya faruwa dani ba."


A hankali ta d'ago ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kai, d'orawa yayi da "Ryam idan kinsan ban miki ba me yasa kika b'ata min lokaci? Ko kinsan cewa da zuciya d'aya na so samunki a matsayin matar aurena? Ni ba yaro ba ne tunda har ina da 'ya kamarki, ni ba zauna gari banza ba tunda ina da aiki, daidai gwargwado zance ni ba mutumin banza bane, ana girmamani ana ganin darajata a k'asashe da dama bare kuma k'asata."


Da k'arfi ya sake juyowa kanta a hassale sosai cikin daka tsawa yace "To a kan me zaki maidani wawa da bai san me yake ba?"


Wani matsanancin kuka ta fashe dashi ta sake yin k'asa da kanta tana fad'in "Kayi hak'uri ka gafarta min, har zuciyata ban yi haka da niyyar cutar da kai ba saidan ganin kai d'in babban mutum ne, har zuciyata nake jin rashin dad'i idan ina son fad'a maka gaskiya, dan Allah kayi hak'uri karka cutar dani."


Wani iska ya shiga furzowa mai zafin gaske na tsananin b'acin rai, bai sake magana ba sai kallonta kawai da yake, d'an tsaki yaja k'arami ya fita daga motar ya rufo mata k'ofar da k'arfi ya zauna mazaunin dreba, da k'arfin tsiya ya figi motar har saida ta gwara kanta a k'ofar da take zaune, kuka take kamar zata mutu ba k'akk'autawa, sosai take jin zafi a zuciyarta na jefa babban mutumin nan cikin wani hali marar dad'i. Shi kuma ko juyowa bai sakeyi ba har saida ya ja pakin a k'ofar gidansu ya tsaya, tashin hankalin da take ciki ya mantar da ita Asma'u da sukayi mahad'a da ita, tashin hankalinta yasa ta manta wayarta a jakarta kuma a kunne take saidai a vibrations.


Shiru tayi bata bud'e motar ba bare ta fita ta k'ura mishi ido ta baya tana kallo yanda ya had'e fuska kamar hadarin gabas, saida ta sake share k'walla tayi k'arfin hali ta bud'a baki cikin dakusashiyar muryar kuka tace "Dan Allah ka gafarceni, karka rik'eni a zuciyarka, wallahi bana jin dad'i a zuciyata."


A sanyaye kuma a ladabce kamar ba shi yayi maganar ba yace "Shiru! Mak'aryaciya kawai."


Da sauri tace "Wallahi gaskiya nake fad'a maka."


Girgiza kai yayi ba tare daya juyo ba yace "Alamar k'arya kika fad'a kenan, wannan rantsuwar da kikayi.".


Saida ta gyara zamanta sosai cikin magiya tace " Abdul gaskiya nake fad'a maka, maganar nan daga zuciyata take fitowa, bana jin..."


Wani kallo ya watso mata ta madubi na mamaki, suna had'a ido ta sunkuyar da kanta saboda kwarjininshi, a hankali ta jinjina kai cikin sanyin murya tace "Ni ma haka kawai nake jin bakina yace Abdul, kayi hak'uri dan Allah."


Yanda fuskarta tayi gwanin tausayi tasha kuka gashi ta sunkuyar da kai, hakan ya bashi damar sakin murmushin gefen labb'a tare da d'auke idonshi a kanta, a dak'ile sosai yace "Na yafe, amma ki kula ki daina k'arya, ba kyau Ryam."


Jinjina kai tayi da sauri tace "Insha'Allah."


Matsawa tayi jikin k'ofar ta bud'e murfin a hankali ta sauka tare da rufo mishi murfin, ta glas d'in motar ta k'ura mishi ido tana takawa zuwa cikin gidan, ta gabanshi ta wuce hakan yasa shi saurin rufe idonshi, abayar ta fito da k'irar jikinta sosai kuma da yake ita d'in yar duma duma ce hakan ya wanzar da wani tasiri a zuciyarshi, ga kallabin rigar dake shirin fad'uwa a kan ta wanda yake nuna mishi lallai zatayi gashi a kan ta ko ba sosai ba, saidai yana so yasan su d'in wace k'abila ce? Mahaifinta bak'i ne sosai kuma gajere dake manne da k'asa, saidai kakanta daya haifi mamanta dogo ne sosai, amma kuma ita bata d'auko mahaifinta ba ta ko ina. Yana cikin tunanin ya sake bud'e idonshi a k'ofar gidan, a lokacin tana daf da shigewa ciki ta sake juyowa, a hankali ta d'ago hannunta ta mishi bye bye tana sakar masa murmushi.


Da sauri ya kuma lik'e idonshi yana dafe gaban goshinshi ya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un."


Yanda shed'an ke ta k'awata mishi ita a zuciya ne yake son yakicewa, so yake ya manta da komai ya rik'eta surukarshi matar k'annanshi, saidai shed'an sai hura mishi wuta yake a kan yarinyar komai tayi sai yaji zuciyarshi na fad'a mishi " *Komai na ta yanda kake so*."


Cak a daidai bakin k'ofar ta tsaya sakamakon komai nata daya daina aiki, Abba zaune dangalgal akan k'asa ba takalmi a k'afafunshi, ga kuma Mama zaune a gefe kan kujera sai Asma'u ita ma durk'ushe gefen Abba tana share hawaye, tunda ta ga haka ta san yau wannan rana bak'a ce k'irin a gareta, yau ranar kam babu sa'a a gareta, me ya faru? Me kuma zai faru?


*Tun* bayan tafiyarsu ba jimawa Abba ya dawo daga masallaci ya samu Muttak'a a k'ofar gidan, ba yabo ba fallasa suka gaisa inda Muttak'a ke fad'in "Abba dama na zo wajen Mimi ne, saboda ina ta kiranta bana samu shi ne na zo naji ko lafiya."


Da matsanancin mamaki Abba ya d'aga kai sosai ya kalleshi dan shi ma a tsaye yake ba ko rusunawa yace "Kiranta kuma? Dame kake kiran nata?"


Da mamakin tambayaar yace "Da wayarta mana, ina ta kirane shiru ba'a samu, ko ita wannan wayar ta samu matsala ne? Idan ta lalace sai na sake mata wata ai ba damuwa bane."


Jim Abba yayi yana kallonshi yana jin mamakin kalamanshi, ba tare da yabi ta kanshi ba kawai ya juya a fusace ya shiga cikin gidan, Mama data idar da sallah ya tsaya bayanta akan tabarma yace "Ke kinsan *Maryama* tana da waya ne?"


Da sauri ta juyo da mamakin jin yau sunan mahaifiyar ma tashi ya kama haka, tabbas yana kiranta Maryam wasu lokuta, amma dai jin sunan Maryama ba dai a bakinshi ba, cikin rashin sani tace "Waya kuma? Wace irin waya malam?"


Wani dogon tsaki yaja tare da kutsawa d'aki ya shige, akwatinta guda biyu duka ya jawo a k'ark'ashin gado, bud'esu yayi ya shiga ciro kayanta d'aya bayan d'aya yana zazzagewa yana dubawa, har k'ananan kayanta daya ci karo dasu pant da bras da cotton saida yayi cilli dasu a tsakiyar d'akin, jikinshi har rawa yake kamar mazari. Ganin bai samu komai a nan ba yasa shi jawo jakunkunanta na hannu sama da guda goma duk k'anana na yan zamani, a tsanake ya shiga dubasu yana bud'a kowane gida a cikinsu, babu waya babu alamarta, saidai ya samu layiyyika (sim) a k'alla guda bakwai, ga poshet na waya wanda take cirewa ta sake wasu suma har guda biyar, ga kuma tsabar kud'i daya samu a wata k'aramar jakarta har jaka ashirin da uku, wata irin juwa ta d'ebeshi ta kayar akan kujerar robar dake d'akin, wannan k'arar ce tasa Mama tashi da gudu gudu ta shiga hankali a tashe, tana k'arasawa ta shiga kiran sunan "Malam, malam lafiya? Wai me yake faruwa ne?"


Bud'a ido yayi a matuk'ar wahalce ya kalleta, zunbur ya tashi tsaye yana sake kallon hannayenshi, nuna mata yayi amma bai ce komai ba saboda nauyin da bakinshi yayi, rab'a Mama yayi ya fito da sauri ya saka takalminshi ya fita a gidan.


Yanda yake saurin zaka rantse dungurawa zaiyi ya fad'i saboda yanayin hallitar, amma kuma haka yake tafiyar yana sauri dan isa gidan Iya Delu, yau kam yasan sai yayi abun kunya gidan surukai, amma fa babu mai hanashi karya Mimi idan sukayi ido takwas takwas.


Suna barin k'ofar gidan Abba na kawowa hakan yasa ya had'e da Asma'u da zata tafi gidansu Jamila, a tsawace sosai yace "Ke tana ina?"


Duburburcewa tayi ta shiga rarraba ido, matsowa yayi zai kamo hannunta ya durk'usar da ita sai tayi saurin ja baya tace "Abba sun tafi."


"Ina?" Ya fad'a da jin haushi, cikin rashin gaskiya tace "Can, wallahi Abba ni babu laifina, saida na fad'a mata mu tafi tare tace wai..."


Shiru tayi saboda tausayin k'awarta tasan yau kam saita Allah Mimi, nuna mata hanya yayi yace "Wuce muje, zataa zo gidan ta sameni, zaku fad'a min abinda kuke shiryawa da bamu sani ba."


Da sauri ta wuce har tana had'awa da gudu Abba ma biyarta yake da saurin kamar zai had'a da gudu shi ma.Mimi dake tsaye ta rasa yanda zatayi, ta koma da baya ne ta nemo taimako a gidansu Iya? Ko kuma dai tayi k'undumbala ta shiga? A gaskiya bata son abinda zai tab'a mata lafiyar jikinta, bata son jin duk wani abu daya danganci rad'ad'i a jikinta, muciyar data gani gefen Abba kuma irin muciyar nan ce mai kama da ice irin na yan damagaram, ta tabbatar da ita yake shirin dukanta. Ajiyar zuciya ta sauke a b'oye tana ci gaba da rarraba ido, d'agowa yaayi ya kalleta idonshi jajir kamar wanda yayi kuka yace "Shigo."


Marairaicewa tayi ta durk'usa a wurin tace "Abba kayi hak'uri dan Allah karka dakeni, ka tambayeni da baki zan fad'a maka komai."


Wuntsi Abba ya wulk'ita ya tashi tsaye yana sake d'aukar muciyar a hannunshi ya nuna mata gabanshi yace "Maryama ki zo nan indai ni na haifeki, in kuma kina so ki nuna min ke babbar mace ce da kika isa da kan ki to ki bar gidan nan."


Fashewa tayi da kuka tana girgiza kai ta kalli Mama da kanta ma ke k'asa, cikin rikicewa tace "Abba karka dakeni dan Allah, zan maka bayanin komai wallahi da dalilina na yin haka, Abba karka dakeni ka ji, zan zo yanzu amma ban da duka."Sheikh da har yanzu bai guda daga wurin ba ne ya fara jin kamar hayaniya, sai zuciyarshi ta raya mishi ko dai jimawar da tayi ne ya sa tayi laifi haka, a hankali ya bud'e motar da tunanin ko sallama ne yayi ya fad'i dalilin jimawar, a hankali cikin kamala da dattako ya shiga takawa izuwa k'ofar gidan, a nan ya tsaya ganin Mimi durk'ushe tana magiya.

*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *18*

Abba saida ya k'ara tamke fuskarsa yace "Mimi idan baki k'araso inda nake ba na damk'e ki saina fasa maki baki da hannuna."


D'an mudil mudil d'in hannun sheikh ya bi da kallo kafin yake d'an k'ara k'arasawa yana son yin magana amma yanayin da mahaifin nata ke ciki saiya d'an dakata yana sauraronsa.


Abba ya rasa ina zai saka ransa, kwata kwata bai kula da cheikh ba hakan yasa yayi taku ya kai goma yana kai kawo a d'an wajen da ba girman kirki ne da shi ba ga mama kanta sadde jikinta har yanzu b'ari yake cike da alhinin wannan tashin hankali.


Su dukansu basu shirya ba suka ga Abba ya hau dutsin dake kusa da Mimi wanda ta durk'usa kad'an kusa da shi bata kai tsayinta kaf ba amma ta rage tsayin nata sosai ya d'aga wannan hannu nasa dugul ya wanka mata marin da ya sakata zabura daga d'an durk'ushen da tayi ta falla ihu ta shiga dira tana rik'e gefen kuncin nata tana kururuwar a taimaketa Abba zai kasheta.


Rai b'ace ya d'aga muciyar nan zai kuma doka mata ita da sauri sheikh ya rintse idonsa yana jin wani irin rad'ad'i a zuciyarsa tamkar shi aka doka ba ita ba.


A hassale Abba yace "Yanzu Mimi kece da wannan rayuwar? A gidan wa kike samu wayar dake hannunki da kud'in dake nanik'e cikin jakarki? Wato kin banzatar da kanki ko? Biye biyen maza kike da suke baki wannan d'in ko me?"


Gaba d'aya ya bud'e idonshi zuwa yanzu yana jin wata zufa na son karyo masa da girmansa da komai haka kawai kan rigimar budurwar yar da bai san haka cikinta yake ba.


Mimi kam tana dire diren nan ta tsaya da sauri jikinta na rawa ta had'e hannayenta tace "Abba na rantse da sarkin dake busa numfashi bana haka, sam ban san wannan hanyar ba, Abba ban tab'a aikata zina ba tunda mama ta haifeni, wallahi wallahi wallahi ban iya ba."


Abba ya kuma matsowa yanzun da take tsugune ya damk'i kunnenta na hagu yace "K'arya kike uwata, wannan zamani da ya zama na bala'i me kike tunanin kina iya fad'a min na yarda dake? Ba zai yiwu ba wuce mu tafi wajen Hajia Gambo, wuce!"


Zuwa yanzu mamanta kanta hawaye take sharewa a tsugunen da take kuma ita sarai ta ga sheikh wanda gaba d'aya ya jinginar da bayansa jikin garu yana jin juwa na d'ibansa na wannan abu dake faruwa.


Mama dake son dakatar da shi dan kar a yi wannan abin a gaban mutane idan har abinda yake zargin kenan su tonawa kansu asiri muryarta na rawa tace "Malam, ka ga sheikk ne a tsaye fa, na san sallama yake."


Malam ya kai dubansa inda take nuna masa, sai a lokacin ya ganshi, shi da kansa sai da gabansa ya k'ara fad'uwa cike da tsoron shikenan ta tabbata ta gama janyowa kanta tashon hankali mai yiwuwa maganar fasa auren ta kawo shi nan shima ya lumshe idanuwansa cike da tashin hankali muryarsa zuwa yanzun ta k'ara yin sanyi yace "Nasan abinda ka ji kenan ka zo wajena ko sheikh? Sai dai ka ganta nan ban san rashin jin nata ya kai cen ba, Innalillahi wa'inna ilaihi raju'une ban san cewa tana rik'e da wayar salula a hannunta ba har ta tara kud'i irin wannan a jakarta ba, ka ganni nan talaka ne mai wadatar zuci haka mahaifiyarta, sannan irin yadda muke taka tsantsan a kan shige da fitarta bamu san ta waye haka ba, idan ka ce kun fasa ba zan k'ullaceku ba domin ni kaina yanzu ban yarda da mimi ba. Zan kaita gidan Hajia Gambo cen layin likita ce ita ke duba mana mararsa lafiyar anguwa ni baba take ce min muna mutunci sosai da ita domin mai d'akina ke mata tuyar wainar juma'a, zan kaita ta duba min ita idan ta rigaya ta gama lalacewa shikennan sai a fasa ta dawo ta zauna..."


Irin yadda Abba ke maganar gaba d'aya hankalinsa a tashe ransa a b'ace, Mama kuwa kunya da tashin hankali ya sakata shigewa ciki da saurinta, Asma'u kuwa hawaye take wani na korar wani inda mimi gaba d'aya bakinta ya gama mutuwa tana tsugune ne gaba d'aya jikinta na mata rawa hankalinta ya gama tashi.


Sheikh yayi iya yinsa ya aro dukkan jarumtar da ta rage masa da k'arfin addu'a sannan ya gyara tsayuwarsa da shigarsa ta kamala ga k'amshin da yake ta fitinar hancin kowa da shi mai dad'in gaske ya tausasa muryarsa yace "Ba za'a yi haka ba malam, a yi hak'uri, na zata ko dan ta yi dare ne na zo na fad'i cewar shi wanda aka saka masu ranar ne ya je asibiti shi yasa na kawota, aman ina ga mai zai hana a shiga ciki a tattauna a nutse ta yadda komai zai shiga cikin haske ba tare da rayuka sun b'aci ba."


Cike da girmama shi Abba yace " Akaramakallah, ba zaka gane wacece mimi ba, idan bamu je ba ba zan tab'a samun nutsuwa ba , kuma idan kuka fasa aurenta ba zan tab'a jin haushinku ba domin tsatso mai kyau ake wawa ba sakarya ba!" Ya k'arashe yana harararta.


Zuwa yanzu ta gama gane cewar ashe duniya banza ce? Yar gajeruwar k'afarsa ya saka ya hanb'areta yana fad'in "Tashi muje, mutuniyar banza kawai."


Tana ji tana gani mahaifinta ne gaba da aminiyarta da mutumen da zata iya rantsewa cewar bata tab'a jin nauyi da kunya da darajar wani d'an adam mai saka wando da zariya bayan mahaifinta irin na wannan bawa ba, sai gashi a yau sanadiyar yan samari da take kulawa, da d'an karb'ar abin hannayensu ba tare da iyayenta sun sani ba ta b'allowa kanta ruwa, an tisota a gaba za'a kaita wajen likita a ware k'afafunta a dubata ita ba mai shirin haihuwa ba ita ba mai rashin lafiya ba.


Gaba d'aya ta nemi wani kukan ta rasa, haka kuma baki d'aya ta zama wata sukuku tana ganin ikon Allah har suka ja suka tsaya a k'ofar gidan wanda sheikh ne ya nemi a sirrinta shi kam in ba dan wani irin girman dattijon mahaifin Maryam ba da ba zai yarda a aikata wannan lamari da shi ba.


Suna fitowa suka ga motar Asas wanda ganin shigarsu mota yayi gaba d'ayansu ya saka shi fasa tsayar da tasa ya karkata ya bisu dan a yadda ya ga da k'yar Abbban sahibarsa ya cibcib'a ya wuntsila cikin motar da irin yadda da k'yar ya shiga baya ga sheikh da kansa ke tuk'in sai ya ga kamar ba lafiya ba.


Daga motar ta fito  wannan karon d'an kwalin abayarta a hannunta yalwatacen gashin kanta ya bayyana bak'i sid'ik da shi har wajen gaban goshinta.

Gabanta ne ya buga a lokacin da suka yi ido hud'u da Asas a hankali ta lumshe lumsasun idonta wasu hawaye suka zubo mata.


Cire dubanta ta yi tana ganin yaron daya fito yake shaidawa Abba cewar su shiga, kasancewarta likita tana samun bak'i maza da mata ta ko ina a kowane lokaci.


Cike da tausayawa take kallon Mimi bayan Abba ya gama kora bayanin abinda yake buk'ata, uwa uba sheikh dake zaune kansa sadde k'asa tunda ya shigo ta rasa ina zata saka kanta dan murna domin har k'asa ta duk'a ta gaishe shi dan kuwa a duniyarta wa'azi idan ba nasa bane bata jin dad'insa, nutsuwarsa, kamalarsa ya saka take son wa'azinsa domin a sanyaye yake isar da sak'on Allah.


Sai Ashraf da ya zabura jin bayanin Abba yana kallon Abban, da Mimi da du wanda yake wajen yana son k'arin bayani amma ba hali domin sheikh ya had'e fuskarsa.


A nutse Hajia Gambo tace "Ayya Abban Mimi, ai kam Mimi akwai nutsuwa duk da baka shaidar d'an yanzu amma bana tunanin idan har zata zubar da mutuncinta haka ba, ka san ba duka 'yan matan namu suka zama d'aya ba duda abin yanzu ya zama na tir sai addu'a, amma dayawa kuwa sun iya taka rawarsu daidai da kid'an ta yanda komai dubararka ba zaka iya gane takonsu ba. "


Abba ya kawar da kansa daga duban da Mimi ke masa yace "Ni kam ki duba min ita Hajia, kin ga bana son na mutu da hakk'in kowa gasu nan da yaron da magabatansa idan aka yi komai a gabansu shikenan!"


Mik'ewa Hajiar tayi tana mai yiwa Mimi maganar cewa ta tashi su shiga ciki.


Asma'u kam kuka take sosai gaba d'aya ta bi ta tsurewa wannan lamari, ta sani ba tare suke kwana da Mimi ba, amma tana iya k'ok'arin bugar k'irji da hallayen k'awar tata, a bar Mimi da caje aljihun gara amma sam wancen harka ba halinta bane.


Jiki a sanyaye ta mik'e tana kallon Abba, cikin tsawa yace "Zaki wuce ko saina ragargaza miki fuska, yar banza mai kama da aljanu."


Idonsa da sukayi ja ya d'ago a hankali haka kawai ya sauke a kanta a lokacin da ta bada baya tana tafiya dukkan wani lamari nata na motsawa daidai da takun tafiyarta.

Da sauri ya kuma sadda kansa yana mai jan "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'ne." Cike da fad'uwar gaba ya shiga korar shed'an a hankali ya sauke dubansa a kan Asas daya sauko k'asa ya had'e hannayensa yana hawaye harda shashek'a yace "Ya sheikh dan Allah koma mecece koma me tayi ni ina son aba ta, ni ba wai wannan nake so ba ni ita nake so, wannan zamani kuwa ba ita ce ta farko ba kuma ba zata zama ta k'arshe ba a fannin cin kud'in maza, wasu da haka suka gina gidaje da motoci da komai, ni kam ina sonta a haka dan Allah."


Muryar Abba ne cike da tausayawa yana kallonsa yace "Yaro, halayan fa? Idan yau aka shaida mana ta banzatar da kanta ya ya tarbiyar 'ya'yanka? Ban tab'a sanin uwata ta kai cen ba har ta iya b'oye min waya, ina bada misalai da tarbiyarta? Ina saka baki idan ana maganar 'ya'yan wasu da suke irin haka,  ashe tawa na kwance tamkar macijin kumba."


Cikin ladabi Asas ya kalleshi yace "Abba na tabbata ko da an sameta da laifi wallahi yanayin rayuwa ne, ni fa gaskiya zuciyata bata gamsu da abinda kuke tunanin ta aikata ba, ta yaya yarinyar da bata jin kunyar fad'an ko ita wacece a gaban kowa zata aikata haka? Mimi fa yarinya ce mai aji ba ballagaza ba."


A hankali ya kuma sadda kanshi k'asa maganganun nan suna hawa masa kai sosai, shi sai yanzu ne ma yake sake tantance yanda zuciyarshi ta wani d'aukaka yarinyar a matakin da baiyi tsammani ba.


Abba kam gyara tsayuwa yayi yana fad'in "Ban sani ba ko dan Allah yayi ta kyakyawa ne? Amma ta yaya na zama sakarai haka a gaban yarinyar Ddna haifa?"


Da sauri sheikh ya kalleshi da mamaki, sai yaji shi kanshi fa sunanshi kenan inda a gaban Mimi ne, domin kuwa ta mayar dashi wani sha-tara har ya kasa ganota.


*A ciki* kuwa suna shiga Hajia Gambo ta umarceta ta cire pant d'inta ta kwanta akan gadon, sarewar da tayi a lamarin yasa Mimi ba gardama tayi abinda ta ce, tana kallo ta saka shafa ta likitoci a hannunta ta matso kusanta, kaallon fuskar Mimi tayi tace "Mimi, garin yaya kika bari har irin wannan zargi ya shiga tsakaninki da mahaifinki?"


Hawaye ne suka sakΓ© sulalo mata ta rintse ido tace "Tsautsayi, k'addara, da kuma rashin jin maganata."


Girgiza kai tayi tace "Kenan da gaske kin zama babbar mace tun a waje Mimi?"


Wani sakaran murmushi tayi tace "Ke da zaki tabbatar yanzu, me yasa zaki tambayeni kuma?"


Murmushi ta mata tare da d'an gyara k'afarta tace "Hakane."


Yanda take jin hannunta na neman shiga gabanta yasa ta k'amk'ame jikinta tana sake lik'e ido gam, tana jin hannun na daf da shiga tayi saurin rik'e hannunta ta sauke k'afafunta ta kwantar dasu, bud'a idonta tayi suka kalli juna, Hajia Gambo ce tace "Mimi ki fad'a min gaskiya mana, idan kinsan baki san namiji ba kar ma a fara shigar da wani abun da zai kawowa budurcinta rauni."


Kawar da kan ta tayi hakan yasa Hajia Gambo ci gaba da aikinta, yatsanta biyu kawai ta saka amma saida ta nemi shid'ewa, ganin kawai zata wahala a banza ya cakata cire hannayenta tana murmushi tace "Ki ci gaba da tsare mutumcin kanki Mimi, a wannan duniya budurci ya zama kamar shine macen ma, kindai gani me ya faru, iyayenki ma sun kasa yarda dake, bare kuma mijin da kika aura ko zaki aura."


Saida ta cire safar ta saka a kwadon shara tace "Tashi ki saka pant d'inki."


A hankali ta tashi ta d'auki pant d'in zata saka Gambo tace "Nasan dai za'a sha dangwarma Mimi a daren farkonki, dan wannan kafin ki bada kai bori ya hau sai an nemi ji miki ciwo."


K'ala ba tace mata ba saida ta saka ta gyara rigarta, Gambo na juyawa zasu fita ta rik'o hannunta, tsayawa tayi tare da kallonta da mamaki, durk'usawa tayi cikin magiya da neman alfarma tace "Hajia dan Allah na rok'eki ki rufa min asiri, karki fad'awa mahaifina komai a gaban mutanen can, ina jin kunyarsu bana so na ci gaba da tozarta a gabansu."


Tsam ta kalleta sai kuma ta jinjina kai tace "Shikenan ba komai, muje."


A sanyaye suka fito hakan yasa dukansu suka saki ido suna kallonsu, saidai banda sheikh da hannayensa ke jimk'e yana ta karanta hasbunallah wa'ni'imal wakil! Da sauri Abba ya taresu yace "Ya ake ciki Hajia Gambo?"


D'an bud'a baki tayi sannan ta kalli Mimi, a hankali ta d'auke dubanta daga kanshi tace "Abban Mimi kayi hak'uri dan Allah, zuwa safe zan zo gidan na maka bayanin komai insha'Allah."


Abun ka ga marar tsayi d'an duk'ul, ba wanda ya lura sai zamanshi suka gani a k'asa b'ingil yana tapa hannaye yana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Oh Allah na Mimi kin kasheni, kin gama dani a duniyar nan."


Da sauri kuma ya wulk'ita ya mik'e tsaye ba zato ba tsammani kawai ya ja k'afar Mimi ta dama, yanda abun ya zo mata yasa ta fad'uwa irin fad'uwar nan ta yan bori tippp! Ta daki k'asa, "Ahhhhhhhhh!"


Wannan k'arar data saki ta saka sheikh da Asas zabura a tare suka mik'e tsaye saΓ― sheikh daya had'a da jimk'e hannunshi gam, da gudu Asas ya rik'e k'afar Abba dake shirin hawa jikin Mimi ya takata, cikin magiya ya kalleshi yace "Abba karka kasheta, wallahi zan aureta a haka na ji na gani Abba, karka ji mata ciwo dan Allah."


Cike da k'una Abba ya sake yin zaune ya fashe da kuka yana fad'in "Mimi ni kika tozarta haka? Ashe duk ladabin da kike mana da girmamamu duk na banza ne wawaye kika d'aukemu? Yau kinsa na ji ni tauyayye ni a cikin hallita, yanda nake d'an tsirit a cikin k'asa haka k'wak'walwata ma da tunani na, ke kad'ai mace amma na kasa kula da tarbiyyarki, uwata me na miki da kika min haka? Talaucinmu ne ya jawo?"


Da sauri Asma'u da jikinta ke rawa ta sunkuya ita ma tana kuka tace "Abba wallahi wallahi wallahi ni dai nasan Mimi bata bin maza, Abba karka yanke hukunci ka tsaya kayi bincik..."


Tsawa ya mata yana fad'in "Binciken uwaki zanyi, ke da ita ai duk kanwar ja ce, tunda kullum tare kuke manne da juna."


Nunawa Asas Asma'u yayi yace "Kaga yarinyar nan da zaku tafi gidanku cewa nayi su tafi tare, amma a k'arshe suka zagaye ita ta dawo ita kuma ta tafi ita kad'ai, to nasan niyyarta da tayi maka tallar kanta ne tunda taga kai aure ne a g..."


Cikin wani matsanancin kuka Mimi tace "Abba...abba ka daina ci min mutumci haka, wallahi ban aikata abinda kake zargina ba, ni ba 'yar iska bace Abba."


Cikin muryar data fara shak'ewa Abba yace "Wacece ba 'yar iskar ba? Ke fita..."


A tausashe cikin son danne abinda ke ranshi kamar an mak'ureshi yace "Dan Allah ko zaki iya barin maganar nan har kuje gida?"


Cike da girmamawa Abba yace "Me zai hana sheikh."


Wani rank'washi ya kai wa Mimi yace "Wuce muje."


Da k'yar ta yunk'ura ta mik'e ga zafin da take d'an jin a k'asanta sakamakon hannun da aka so turbud'a mata, yanzu ma d'an kwalinta a hannu yake dan duk a rikice take a gigice, suna fitar k'ofar gidan kusan shi ne a bayansu sai Mimi dake bayanshi.


Kamar daga sama sukaji muryarshi yace "Daure ki rufe kanki, hakan ba kyau."


Dukansu saida suka kalleshi har da ita data fara k'ok'arin gyara kallabin ta d'ora a kai, yanzu ma dai duk a motar sheikh suka koma gida sai Asas shi kad'ai a motarshi, amma zuciyarshi zallo take sosai yana jin sirikin na sa na neman b'ata mishi rai.*Idan na ga ruwan comment gobe zaku ga uku ma (peut Γͺtre)*😎*Alhamdulillah*

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *19*
Duk zaune suke akan tabarma guda sai Asas da sheikh dake kan kujerun roba farare duk da ba sababbi bane, mama kanta na sadde a k'asa dan bata so zama a nan ba saboda kunya da takaici, Mimi daf da k'ofar shiga d'aki take zaune ta had'a kai da gwiwa tana ta shashek'ar kuka, Asma'u na gefenta ta rik'e hannunta gam tana ta murzawa alamar rarrashi, cikin nutsuwa da dattako sheikh ya kalli Abba a nutse yace "Yaran da muka haifa wata rana sukan koya mana darasin rayuwa da bamu tab'a karanta ba, hakazalika wani lokacin sukan sa muji kamar su suka haifemu ba mΓ» muka haifesu ba, idan har Allah ya bawa mutum haihuwa dole wata rana sai ya zama tamkar jami'in binciki na k'asa da k'asa, wata rana kuma saiya koma kamar lauyan dake gaban wanda ake tuhuma, wani zagayen kuma rigar malunta zaka ara ka yafa dan yi musu nasiha a tsanake sannan su fahimci karatu, akwai lokacin da dole uba sai ya zama mai zafi da kausasawa ga yaranshi, kafin wata rana ka zama mai taushi kamar audiga sannan mai sakin jiki dasu dan suma su shiga jikinka. Amma fa duk wannan matakan tsaron zasu biyo bayan addu'ar nema musu shiriya ne, duk yanda zaka kai ga saka ido ko tattare al'amarin yaranka idan Allah bai nufesu da shiriya ba to fa zasu baud'e maka ne, dan haka malam kayi hak'uri ka bΓ’ wa zuciyarka hak'uri, idan har ta b'acin rai zaka bi tabbas zaka iya ganin bayan yarka, idan haka ta faru kuma wace akayi kenan?"


Numfasawa yayi yace "Kayi hak'uri, ga Asas nan yace har yanzu yana son ta da aure, ni nan zan tsaya masa har naga hakan ya tabbata, mu musu fatan alkairi da zaman lafiya mai d'orewa kawai."


Jinjina kai malam yayi ya sauke numfashi yace "Gaskiya ka fad'a sheikh, ni shaidane akan k'wak'waran darasin da uwata ta koyar dani, kuma kamar yanda ka rok'a mata alfarma na yafe mata duniya da lahira, Allah ya tabbatar da alkairi,Allah ya shirya mana zuri'a baki d'aya."


"Ameen ya Allah." Suka amsa malam da Asas, kallon Mimi yayi da niyyar ya mata nasiha mai ratsa zuciya ya ja mata ayoyi da haddisai, sannan ya umarceta ta nemi gafarar iyayenta da ta ubangiji, amma tuna abinda ya faru da abinda likitar nan ta fad'a, alamu ne kenan na eh ta zubar da mutumcinta, sai zuciyarshi ta sake maimaita mishi kalmar nan "Kamaninta bata da suffar cutar da kowa, yanayinta bai nuna hakan ba."


Da sauri ya d'auke kanshi kawai ya mik'e yana fad'in "Saida safenku."


Mik'ewa duk sukayi banda Asma'u da Mimi suka fita sai Mama data shiga d'aki, suna ganin haka Mimi ta d'ora kanta a kafad'ar Asma'u cikin shashek'ar kuka da raunin murya tace "Asma'u kin gani ko? Kinga rashin jin maganarki me ya ja min? Asma'u Abbana ne yake zargina fa."


Dafa kanta tayi tana shafa mata gashinta ita ma tana shashek'ar kukan tace "Kiyi hak'uri kinji Mimi, komai zai wuce insha'Allah."


Ajiyar zuciya duk suka shiga saukewa har Abba ya dawo cikin gidan, a k'ofar shigowarshi ya ci karo da jakarta data jefar a nan, da k'afa yayi cilli da ita hakan yasa yar jakar buguwa a bango ya bayar da k'ara mai d'an nauyi dake nuna bana jakar bane, da sauri ya taka tare d'aukar jakar ya bud'e, ciro wayar yayi yana kallonta yana jujjuyata, sake jifa yayi da wayar ya kalli su Mimi da duk suka sunkuyar da kawunansu, dogon tsaki yaja tare da sake fita y'a bar gidan.


A hankali Asma'u ta zame kan Mimi daga kafad'arta ta mik'e tace "Mimi zan tafi gida nima, saida safe kinji, kiyi hak'uri kuma kar kiyi kuka zai iya haddasa miki ciwon kai."


Jinjina kai tayi ta bita da kallo har ta fita, wata irin k'aunar k'awarta ta take ji a ranta, lallai ita yar halak ce kuma ta cancanci ta so ta, a hankali ta yunk'ura ta mik'e ta shiga d'akin, zaune ta samu mama zugum sai su Yaseen dake rik'e da littafin karatunsu amma da gani kasan suma suna cikin alhini, a hankali ta durk'usa gaban Mama ta d'an rik'o zaninta tana fad'in "Mama, dan Allah kar kiyi kuka a kai na ba kyau mama, kina so Allah yayi hushi dani ne? Mama kin gani wallahi ban tab'a issss..."


Kasheta tayi da mari tare da fizge k'afarta, hak'ik'a duk da basu da tsayi mutanen amma Allah ya basu wata baiwa, wannan baiwar kam ita ce ta k'arfi, k'ashi d'aya garesu da idan suka rik'eka zaka sha mamaki, hakan yasa Mimi k'arasa zaucewa taji wani zuuuuuu! A cikin kanta, da k'yar ta dafe kuncinta tana jin muryar Mama a cikin matsanancin kuka tana fad'in "Mimi a dalilinki fa aka mana wannan terere! Yanzu ke ko kunya baki ji ba domin Allah, yarinya kamar ki Mimi, ina miki kallon k'aramar yarinya ashe ke ma babbar macece ke tunda har kin iya d'aukar namiji, Mimi har ke ce wai za'a baki kud'i da abu dan ayi anfani dake?"


Wani kuka ta kuma fashewa dashi tana zama kan kujerar tana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un, Allahuma ajirni fi musibati, waklufli khairan minha."


A hankali Mimi ta muskuta ma su Yaseen da zasu fita daga d'aki saboda ganin har yanzu rigimar bata k'are ba, mik'ewa Mama ma tayi tare da yin k'wafa ta bar mata d'akin, hakan yasa Mimi fashewa da kuka marar sauti kamar zata shak'e kanta ta mutu.


A ranar dai kam bata sake jin motsin Abba bΓ’ dan a masallacin unguwar ya kwana, Mama kuma ko shinfid'a bata fitar waje ba a kan gadonta ta haye saidai ita ma ba bacci tayi ba kamar Mimi dake k'asa kwance.
                   *Sheikh*Cikin nutsuwa ya sake gyara zamanshi yana kallon Hajiar da alama kalamanshi sun fara ratsata ya ci gaba da fad'in "Hajiarmu, ai sun gama kyau da daraja tunda Allah ya hallicesu a 'yan adam, domin kuwa fad'ar Allah ne cewa *lallai an hallici mutum cikin mafi kyawun hallita*, ita kuma wannan hallitar Hajia ubangijin daya hallici ta wa hallitar shi yayi ta ki, haka kuma shi ne dai yayi tasu hallitar, hakan ba dan baya son su bane ko kuma sun mishi wani laifi, hakan ganin damarshi, haka ya so kuma babu wanda ya isa ya hana, dan ya fad'a mana a littafi mai tsarki a suratul buruj aya ta goma sha shiga cewa *yana yin abinda ya so ne*, Hajia karmu k'yamacesu dan hallutarsu, mu k'yamace dan munanan d'abi'unsu ko halayensu, kuma mun tabbatar babu su Hajia, hallitarsu hallita ce ta Allah wanda idan ya so yanzun nan zai iya mayar dani irinsu, ko kuma cikin dake jikin Hafsat ta haifo mai kama dasu, duk yin ubangiji ne wannan, Hajiarmu, *shin da wace ni'imace kuke k'aryatawa*? Ni dai ba'a da ja akan cewa Allah ba zai iya salwantar da hallitata ba, ban sani ba ko ke Hajiarmu?"


Da sauri ta girgiza kai tace "A'a sheikh ni a wa? Ni ma bana da ja, dama tun farko raina ya b'aci ne saboda babu wanda ya sanar dani kalar jinsinsu, sai kuma yarinyar da naga zubinta yafi k'arfin yanayin iyayenta a yanda aka fad'a min, bugu da k'ari Salamatu ta fad'a min ta gansu suna fad'a har ana kiranta da karuwa."


Girgiza kai yayi yana fad'in "Subhanallah, astagfurillah! Wannan shaci-fad'i ne na mutane, dama ai babu inda za'a fara maganar aure ba'a samu masu kushewa ba, Hajiarmu Asas yana son yarinyar nan tunda har kika ga ya sameni gida da sassafe haka ya ce na sameki, ki musu fatan alkairi a matsayinki na uwa hakan nada matuk'ar tasiri akan su fiye da yankan wuk'a."


Jinjina kai tayi cike da gamsuwa tace "Shikenan na amince, Allah ya tabbatar da alkairi."


Murmushi yayi yace "Ameen Hajia, nagode da wannan alfarmar da karamci, Allah k'ara girma da lafiya."


"Ameen." Ta fad'a cike da son suruki kuma d'an d'an uwan mijin nata, mik'ewa yayi yana mata sallama ya fita a falon inda ya samu Asas a bakin motarshi da alama shi yake jira.


Yana zuwa cike da zumud'i yace "Ya ake ciki sheikh? Dan Allah ka ce min ta amince?"


D'an zuba masa ido yayi da fari sai kuma ya jinjina kai ya lumshe ido yace "Ta amince, ka je ka ci gaba da shirye shirye."


Rumgumeshi yayi yana fad'in "Alhamdulillah, gaskiya na ji dad'i."


Murmushin yak'e kawai ya masa amma har zuciyarshi wani suka yake ji kamar ana soka mishi allura, ga wani irin mataccen yanayi daya taru ya baibayeshi saboda abinda ya zo mishi wanda bai tab'a tsammani ba, da kuma rashin baccin da bai samu ba a daren jiya ko na minti d'aya, saida ya raba jikinshi da nashi kafin ya d'an bubbuga bayanshi yace "Ni zan wuce, sai munyi waya."


Da kallo Asas ya bishi har ya rab'ashi zai shiga mota Asas yace "Sheikh."


Tsayawa yayi tare da juyowa ya kalleshi, kafeshi yayi da ido saboda yana son fahimtar yanayin da zai shiga idan ya ambaci sunanta sannan yace "Me ye tsakaninka da Mimi?"


Sake zaro idonshi yayi yana k'urawa Asas da mamakin tambayar, a hankali ya had'e fuskarshi yana binshi da kallon tuhumen tambayarshi, lura da haka yasa Asas fad'in "A'a cheikh! Ba wai ina zarginka bane da wani abu, kawai dai na fahimci kamar akwai sanayya a tsakaninku, shiyasa na tambaya."


D'an d'auke idonshi yayi daga kan Asas ya bud'e murfin motar yace "Ba komai tsakaninmu, karka k'ara min tambayar nan."


Wani murmushi Asas yayi ya kallonshi har ya shiga motar, zai ja murfin ya rik'e yayi saurin rik'eshi yace "To ya maganar Ryam d'inka?"


Ba tare daya kalleshi ba yace "Tana lafiya, zamuyi magana a gaba."


Yanda ya amsa mishi yasa Asas bai da wani zab'i daya wuce yar rufe mishi murfin dreba ya ja shi suka bar gidan, saida ya ga b'acewarsu kafin ya nufi b'angarenshi dan shiryawa, yana so idan ya fara zuwa asibiti daga nan saiya wuce ya ga yanda Mimi ta kwana.
                *Mim-Ma'u*Ita maganar duniya bata b'uya ko da k'ark'ashin k'asa aka yi ta, tashin hankalin daya faru a gidansu Mimi tsaf a kunnuwan mutan gidan su Asma'u, dan dama katangarsu d'aya ne, wannan ya jawo cece-kuce har abun ya so juyewa kan maman Asma'u, dan ita kanta Asma'u saida kishiyoyin uwar suka fara yada musu magana suna cewa abokin b'arawo ai b'arawo ne, hakan ya jawo fad'a sosai a gidan suma jiya, dalilin haka kuma mahaifin Asma'u ya fad'a da babbar murya cewa ya soke k'awance tsakanin Asma'u da Mimi har abada.


Ita kanta Mimi yau data tashi sai ta samu kanta kamar bak'uwa a gidan, suna fara had'a ido da Mama kamar yanda ta saba ta duk'a har k'asa tace "Mama ina kwana."


D'auke kai tayi kamar bata ji ba ta wuce aikin gabanta, mik'ewa tayi jiki a sanyaye ta d'ora hannu akan mad'aurin gidan sangensu Yaseen zata kwance, murya a dak'ile Mama tace "Barshi zan d'auke da kaina."


Kallonta tayi zuciyarta na harbawa tace "Amma Mama..."


Kujera ta data ta d'auka ta aza ta kuma tak'ark'are ta taka kujerar ta shiga kiciniyar kwance sangen, kasa katab'us tayi tana kallo har ta kwance duka, mik'awa Yaseen tayi tace "Kai d'aki."


Karb'a yayi ya wuce Mama kuma ta fara tattare shinfad'ar, muk'ut tayi ta had'e kukanta tare da k'arasawa gaban murhun da mama ta fara k'ok'arin hura wuta, shi ma dai cikin fad'a tace "Bana so, ban sakaki ba Mimi, idan baki da abinda zakiyi ki nemi waje ki zauna, dan makaranta ma kin gama zuwanta."


Da tsananin mamaki ta kalli Mama hawayen da take rik'ewa suka gangaro, cikin muryar kuka tace "Mama ku yafe min, nasan nayi laifi amma dan Allah karku hanani samun albarkarku."


Wani tsaki Mama taja tare da k'uk'utawa ta d'auki bargon zata shiga dashi d'aki, har ga Allah bargon yafi k'arfinta amma tsabar hushi haka ta wuce dan kai shi d'aki, a daidai k'ofar shiga tsautsayi yasa mama gurd'ewa ta fad'i ita da bargon, da gudu Mimi ta tunkareta haka ma su Yaseen da suka tsaya bakin k'ofar, kamata tayi ta mik'e cikin jin haushi tace "Sakeni, karki taimaka min."


Cikin matsanancin kuka Mimi tace "Mama me yasa ba zaki bari na taimaka miki ba? Wani ma bana jurar ya cutar daku bare kuma ku naga kuna k'ok'arin haka."


Duk'awa tayi zata d'auki bargon Mama ta fizge da k'arfi ta k'arasa dashi ciki ta aje ta fito, fitowa tayi ta samu Amir na nad'e tabarmar, Mama kuma na hura wuta zata d'ora d'umame, tsaye take saita rasa me zatayi ma sai hawaye kawai.


Bud'e gidan da suka ji yasa Mimi saurin juyawa, tana ganin Abba sukuku dashi idonshi jajir tayi saurin durk'usawa tana fad'in "Abba ina kwana? Abba ina ka tafi mun..."


Nunata yayi da yatsa hakan yasa ta yin shiru, ta gabanta ya bi zai shiga d'akin mama ta kalleshi tace "Ina kwana?"


A dak'ile ya amsa da "Lafiya lau." Su Yaseen ma gaisheshi sukayi ya amsa, nan ya barta tsugune saida ya shige sai kawai ta ja k'ugu ta jinjina a bango ta rakub'e tana hawaye, haka Abba ya fito zai shiga wanka mama ta d'auki bokiti ta zuba mishi ruwa, a yanda suka saba Mimi ke d'aukar bokitin, amma yau basu barta ba Abba ne ya lailayeshi ya kai ban d'akin, tana zaune har mama ta zubawa su Yaseen tuwon suka fara ci Abba kuma ya fito.


Gaba d'aya ta rasa ya zatayi ina zata saka kanta ta ji dad'i, a halin yanzu kam kunyar fita waje take kuma tana kunyar had'a ido da Asas, saidai gashi iyayenta ma na neman zama mata dodo su saka ta fara fatan mutuwa. Mik'ewar su Amir suka wanke hayyane suka d'auki jakunkunan makarantarsu yasa Mimi cikin shashek'ar kuka tace "Amir, lek'a gidansu Asma'u ka kira min ita kafin ta tafi makaranta."


Juyawa yayi zaai fita Mama tace "Kai." Juyowa yayi yace "Na'am."


A d'aure tace "Wuce ku tafi inda zaku je."


"To." Ya fad'a yana bin bayan Yaseen suka fita, tusa kanta tayi tsakanin gwiwoyinta ta sake fashewa da kuka, fitowa Abba yayi yana saka takalminshi ya kalleta yace "Kuka ko? Yanzu kika fara ai Mimi, ai duk wanda yasa iyayenshi kuka shi ma sai yayi marar iyaka."


D'agowa tayi cikin matsancin shid'ewa tace "Abba dan Allah dan girman Allah karku min baki, Abba ban aikata abinda kuke zargina da aikatawa ba, wallahi ban tab'a ko da d'aura niyyar fara bin wannan hanyar ba."


Tab'e baki yayi yace "Maganar banza, shi wanda ya baki wayar kenan d'an mahaukaciya da zai baki ita ba tare da shi ma ya moreki ba."


Rintse ido tayi tace "Abba ka tambayeshi kaji idan kana so, wallahi ko hannuna bai tab'a rik'ewa ba."


Zaune yayi akan kujerar katako ba tare da yace komai ba, ga abinci mama ta aje mishi amma saiya tsura mishi ido yana kallo, ganin kamar baya hayyacinshi yasa mama fad'in "Malam."


D'agowa yayi ya kalleta hakan yasa tace "Lafiya, ka ci abinci mana karka bari hawan jini ya kamaka a banza."


Girgiza kai yayi yace "Wallahi Allah ba dan girman sheikh da nake gani ba, da na mayarwa da yaron nan kayanshi ita kuma na bayar da sadakarta a masallaci."


Yanda Mimi ta k'ura mishi ido tana kallo yasa yace "E! To yaushe zamu d'aukeki gwalagwaje mu kai a wannan babban gida, bayan kasantuwar fak'irai kuma wadanni mun zama iyayen karuwar gida..."


Sake had'a kanta tayi da gwiwa ta fashe da kuka tace "Abba ka daina dan Allah, Abba ka daina babu kyau wallahi, Abba ni ba karuwa bace."


Sallamar Gambo tasa su dakatawa suka amsa, wuri mama ta bata ta zauna suka shiga gaisuwa cike da alhini, kallon Mimi tayi da ko d'agowa ba tayi ba tace "Abban Mimi ba dai har yanzu maganar nan bata wuce ba?"


Kallonta yayi yace "Wucewa? Haba dai yaushe?"


Girgiza kai tayi ta gyara zama tace "Abban Mimi, a gaskiya abinda kayi jiya baka kyauta ba ko kad'an, tabbas laifin Mimi ya isa ya hanaku nutsuwar zuci, amma kuma ai komai yana son sirri, yanda ka tozarta kimar yarinya a idon k'awarta da babban malami da kuma mijin da zata aura abin sam baiyi dad'i ba, ka fa sani duk lalacewar da Mimi zatayi wallahi ba zaka iya cireta a 'ya'yan daka haifa ba. Gashi yanzu kuna ta zargin yarinyarku a banza yarinyar da ko yatsa bai iya wucewa ta gabanta ba, kun d'auki alhakinta sosai gaskiya, dan zaku iya yin komai a tsanake."


Kallon Mimi tayi tace "Kamar yanda na fad'a miki jiya Mimi ki ci gaba da rik'e mutumcin kanki, wannan d'in shi ne darajarki a wannan k'arni, iyayenka ma suna wofantar da kai idan ka zubar dashi a waje."


Kallon Abba tayi tace "Idan baku yarda ba ku kaita wata asbitin, amma ka sani duk tozarcin da zaka jawo mata kanka ka jawo ma, dan kafin a nunata sai an nunaka da yatsa tunda kai ne namiji mai fita."


Mik'ewa tayi tare da fad'in "Sai anjimanku, ina sauri dama zan wuce asibiti nace bari na tsaya dan cika alk'awarina."


Babu wanda yace mata k'ala harta fita a gidan, jiniyar kukan Mimi kawai suke ji amma babu mai sauke ko da numfashi da k'arfi. Da k'yar Abba ya sauke numfashi ya kalli Mama yace "...

*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *20*

Da k'yar Abba ya sauke numfashi ya kalli mama yace "Kina ganin gaskiya ta fad'a?"


Zuru ta masa da manyan idonta tana kallonshi ba tace komai ba, kallon Mimi yayi tare da fad'in "Tashi shiga ciki."


Mik'ewa tayi tana kuka kamar ranta zai fita ta shiga d'aki, kallon Mama ya sakeyi yace "Ni fa sai naga kamar gaskiya ta fad'a."


Saida mama ta d'aure fusja tace "Ko da gaskiya ne bai kamata mu sake sakar mata fuska ba, ai ta yaudaremu ta munafurcemu, shi kuma wannan laifin fa?"


Jinjina kai yayi yace "Hakane, a gaskiya ban tab'a kawo faruwar haka a raina ba, uwata? Uwata ita ce ta aikata wannan babban kuskure."


Ajiyar zuciya kawai mama ta sauke ba tace komai ba, abincin ya ci gaba da ci yana idawa ya wanke hannu ya fita a gidan. Yana fita kuma malam ya sallamo gidan, jiki na rawa mama ta shiga amsawa tana k'ok'arin d'auko mishi kujera, ta tabbata abinda ya faru ne ya kawoshi gidan, dan ko haihuwa tayi malam ba gidan yake zuwa ba, ai kuwa ciki ya shigo fuskarshi a had'e tsabar b'acin rai, dan har gida Gambo ta biya yanzu ta sanar dashi abinda ya faru jiya, ita tausayin Mimi da ganin yanda ta sameta a gidan yasa ta zuwa ta fad'a mishi.


Kanta k'asa ta durk'usa tana fad'in "Malam ina kwana."


Cikin fad'a yace "Kwanan lafiya? Ina Mimi?"


D'aki ta kalla tace "Tana ciki."


Abinda bai tab'a yi ba a rayuwarshi, sai gashi yayi yau dan kuwa wucewa kawai yayi d'akin yana cire takalmi ya sake yin sallama, da mamaki mama ta bishi da kallo dan ita dai tasan baya haka. Mimi na jin sallamarshi ta sauko daga kan gado ta sake fashewa da kuka, a hankali ta d'ora kanta a k'irjinshi tana sake sako wani kukan, cike da tausayinta ya dafa kanta yace "Amaryata yi shiru kinji, ki rabu da mutanen gidan nan, yau ba zaki kwana a gidansu ba sai nawa, dan na basu amanarki har na gama k'era miki gidanki, shi ne za'a ci min amana haka."


K'wafa yayi a hankali Mimi ta fara jin sanyi a zuciyarta ta ji tana neman yin murmushi, d'aga kanta tayi saidai bata kalli fuskarshi ba saboda kunya tace "Angona ban aikata ba, ban aikata abinda suke zargina ba, kawai dai ina karb'an kud'i ne idan aka bani amma ban tab'a rok'a ba da kaina, ko waya ma dana rik'e bani nace a siya min ba, kawai anga rashin dacewar ace bana da waya ne yasa aka bani, ni kuma na sa hannu na karb'a, amma wallahi kakana ban tab'a zubar da mutumcina ba kafin a bani wani abu."


Kama hannunta yayi suka zauna kan kujerun robar yana kallonta yace "Na sani Mimi, ni ban tab'a ji a raina ba damaa zaki iya aikata wannan mummunan aiki ba, laifinki kawai karb'an abun hannun kowane gara da wawa, ta hakane wata rana wani zai zo miki da buk'atarshi, dan wani in ya baki dan Allah wani kuma wani abu ya hango a tare dake da yake son mora, dan haka saiya fara siye zuciyarki da kyaututtuka marasa anfani."


Numfashi ya sauke yace "Naji dad'i da yaron nan yace bai fasa aurenki ba, hakan ya tabbatar min shi namiji ne kuma d'an halak."


Cikin share hawaye tace "Kakana kunyar Asas nake ji, da wane ido zan kalleshi bayan abinda ya faru? A gabanshi komai ya wakana kakana."


Sake dafa kanta yayi da babu d'an kwalin sai tarin sumar mai yawan gaske da tsayi saidai bai wuce iya wuyanta ba yace "Karki damu kinji, idan ya zo shi ma ki nemi gafararsa, sannan ki fad'a mishi abinda kika fad'a min yanzu, zai k'ara fahimtarki har ma ya sake miki alk'awarin aure."


Jinjina kai tayi alamar to, cikin rarrashi yace "Zan tashi na tafi kasuwa yanzu, me kike so na taho miki da shi?"


Cike da kunya ta sunkuyar da kanta tana d'an murmushi, hancinta ya lak'ace yana fad'in "Kaga ja'ira ko? Yaushe aka fara tausayina haka har ake tsoron ragargaza min aljihuna?"


Fashewa tayi da dariya mai sauti har hak'oranta suka fito, sosai yaji dad'in ganin wannan annuri na ta, dan haka yace "To fad'a min me zaki ci?"


Girgiza kai tayi tace "Bana son komai, kuma ma ai wannan tsohuwar matar taka ta hanani cin kayan yaji yanzu."


Kumatunta ya shafa yace "Kenan da abu mai yaji zan siyo? To ai naji dad'in haka."


Mik'ewa yayi hakan yasa ita ma ta mik'e tsaye, kama hannunta yayi yace "Fad'a min yanzu zaki zauna anan? Ko kuma kina so idan na dawo daga kasuwa na biyo mu tafi tare dake? Dan naga a nan cutar min ke a ke yi."


Shiru ta d'anyi tana tunanin abun yi, ji tayi ya shafa kumcinta data sha mari jiya yana fad'in "Ga shaidar sawun hannu a fuskarki, wannan jar fata ai bayan sabulu da ruwa ban yarda komai ya tab'ata ba."


Dariya tayi tace "Kakana zan fara tambayar izinin Abbana, idan ya amince sai naje."


Jiijina kai yayi yace "Shikenan to, sai anjima."


Jinjina kai tayi ta bishi da kallo cike da k'aunar kakan nata har ya fita a d'akin, mama na ganinshi ta sake sunkuyawa tace "Allah ya tsare malam, a dawo lafiya."


A dake ya amsa mata da "Allah yasa." Ya fice a gidan, haka kawai ta samu kanta da sakin murmushi, wato duk abinda Mimi tayi ba tayi laifi ba d'an hukuncin da suke son yi mata shine su har sun aikata laifi, mik'ewa tayi ta ci gaba da kai da kawonta.


Da k'yar ya samu yaron daya turo ya shigo cikin gidan da sallama, mama ce ta amsa tana kallon yaron da alama almajiri ne, cikin girmamawa yace "Ina kwananku? Aka ce wai ana sallama a waje."


Da mamakin maganar yaron tace "Waye?"


A nutse yace "Yace wai Ashraf ne."


Numfashi ta sauke mai nauyi kafin tace "Ka ce ya shigo ciki."


Da sauri ya mik'e ya fita dan isar da sak'on, jim kad'an ya shiga doka sallama mama na amsawa har ya shigo ciki, har k'asa ya durk'usa suka gaisa kafin ya ajiye ledojin hannunshi yace "Mama dama wannan sak'on Mimi ne na jiya, Hajia da kuma aunty Hafsat ne suka bata, shi ne nace bari na kawo mata."


Cike da kunya da kuma rashin farin cikin ganin sak'on tace "Harda wahala haka? Wallahi da ma ka barshi ai, a halin yanzu bana jin mahaifinta zai yarda ta karb'i kayan nan."


Ba tare daya kalleta ba yace "A daure a karb'a mama, tun jiya kayan ke hannu na, idan na mayar musu yanzu ba zasu ji dad'i ma suma."


Jim tayi alamar tunani sai kuma tace "Shikenan angode, Allah ya biya."


"Ameen." Ya fad'a da fara'a, mik'ewa mama tayi ta nufi d'aki tana fad'in "Tana ciki ai."


Tana shiga zaune ta samu Mimi tana jin komai dake waknaa a wajen, cikin d'aure fuska tace "Kije ku gaisa, amma karki yarda ki wuce minti biyu."


Jiki a sab'ule ta mik'e tana d'aukar hijabinta na makaranta, yau kam Mimi bata bi ta kan duba madubi ko shafa turare ba haka ta fita, tunda ta fito kanta k'asa bata so su had'a ido, amma tana jin yanda idonshi ke yawo a jikinta, saida ta tsaya d'an nesa dashi a fargajiyar gidan kamar zata duk'a mishi tace "Ina kwana."


Da murmushi a fuska yace "Lafiya lau maah, antashi lafiya?"


Bakinta kawai ta iya motsawa ta amsa amma bata fito da sautin ba, wani murmushi ya saki ganin yanda take ta wasa da hannayenta a cikin hijabi, saidai ta bashi tausayi ssoai ganin yanda fuskarta ta wahala dan kuka da marin da ta sha, numfashi ya sauke yace "Maah ni zan wuce, dama kayanki na zo kawo miki."


Sake sinne kanta tayi, duk da kuwa bata so amma ba zata iya d'aga kanta ta kalleshi ba bare ta fad'a mishi, a sanyaye ya sake furta "Sai anjima, nan da jibi zan dawo insha'Allah."


Jin ya juya zai tafi yasa Mimi d'aga kanta ta bi bayanshi da kallo, kamar yasan ta d'ago kai sai kuma ya tsaya ya juyo hakan yasa idonsu sark'ewa a juna, hawayen dake mata ambaliya ne yasa shi saurin matsowa yana fad'in "Maah lafiya? Me ya faru kuma yanzu kike kuka?"


Cikin fashewa da kuka tace "Kayi hak'uri Asas na cuceka, ka yafe min dan Allah kaji."


D'an tsakin nan yayi irin haba ke ma tare da fad'in "Naanah, tun jiya na fad'a aurena da ke babu fashi insha'Allah, gaskiyarki tasa nake k'ara sonki, kuma wannan gaskiyar yanzu haka gata nan ina hangowa cikin idonki, dan haka ki kwantar da hankalinki kinji."


Jinjina kai tayi tana share hawaye tace "Nagode, amma ina jin kunyarka da ahalinka da iyayena da kowa da kowa, Asas ya zanyi da abun kunyar nan?"


D'an matsowa yayi kusanta kad'an yana murmushi yace "Maah le, na ce ki kwantar da hankalinki kinji, karki damu da komai dan Allah, kinji."


Jinjina kai tayi alamar to, wani murmushi ya saki yace "Yawwa ko ke fa, dan Allah karki bari damuwa ta samu muhalli a zuciyarki har tayi tasiri a shagulgulan bikinmu, ina so na ganki cikin walwala."


Nan ma sake jinjina kai tayi alamar to, jinjina kai yayi shi ma yace "Zan wuce, sai jibi insha'Allah."


Jinjina kai tayi tace "Allah ya kaimu."


"Ameen." Ya fad'a yana juyawa, ita ma juyawa tayi ba tare data d'auki kayan ba ta koma d'aki, dan ita da sake karb'an abu a hannun wani kam har abada indai ba aure tayi ba, tana shigowa d'akin mama ta mik'e tana binta da wani kallo, yanda take ta b'oye hannayenta a hijabin ya dasawa mama alamar tambaya a game da ita, dan haka ta fizgota da k'arfi taja hijabin ta cire mata ta jefar, kallon hannayenta tayi tace "Me kike b'oyewa yanzu kuma?"


Saida ta durk'usa k'asa tace "Wallahi mama ba komai."


K'in yarda tayi da tsiya sunkuya ta saka hannu a k'ugunta tsakiyar siket d'inta, lalabawa ta shiga yi Mimi kam d'an kakkarewa take tana kallon Mamar, buge hannunta tayi tana fad'in "In kina da gaskiya ki bari na duba mana."


Da sauri ta d'auke hannayenta da tunanin mama ta gani ko ta samu rangwame, a tsawace ta kalleta tace "Mik'e tsaye, mai ladabin kunama kawai, kin iya sinne kai kina wani durk'usa mana kamar gaske."


K'are mata kallo ta shiga yi kafin tace "Zazzaga min siket d'in nan."


Cikin marairaicewa tace "Wallahi mama babu komai, mama me zai bani yanzu daga zuwanshi?"


"Ni ina zan sani? Ai kin fini sanin komai Mimi, dan yanzu ni tsoro ma kike bani." Cewar Mama tana ta lalabeta har cikin riga, saida ta tabbatar babu komai kafin ta tab'e baki ta juya ta fita, kayan da suka bari a tsakar gida ta d'add'ako da k'yar ta kawo ta aje, nuna mimi tayi da yatsa tace "Kuma ban yarda ko kallon ledojin nan kiyi ba har sai mahaifinki ya dawo."


Jinjina kai tayi alamar to tare da d'auke idonta daga kan ledojin, fita mama tayi a d'akin ita kuma ta gyara zama ta kifa kanta a cinyoyinta ta saka wani kuka mai ban tausayi, cajewar da Mama ta mata yanzu ta tsaya mata a rai sosai, daga shigowar Asas yanzu har tayi tunanin ya bata wani abu data b'oye? To me zai bata dan Allah? Shi fa ba haka yake ba, aure ne kawai a gabanshi ba shashanci ba, hasalima har yanzu babu wanda ya tab'a jaraba yi mata wannan ko da cikin wasa ne. Da wannan Mimi ta ci kuka ta gode Allah a wannaan wuni kam, ba aikin fari dan ko tsintsiya ta d'auka mama zata ce bata so ta aje, sallah kawai take mik'ewa tayi amma hatta da abinci mama bata ce mata gashi ba, sai yamma ne da taji yunwa zata kasheta ta d'iba da kanta cike da zulumin kar mama ta hanata shi ma. Gashi tun tana zuba ido ganin Asma'u har ta cire rai, kuma babu damar aiken Yaseen ko Amir su kira mata ita ko taji sanyi a ranta.                  *Sheikh*A d'aki ya sameta tana sallah isha'i da ta kubce mata har aka idar, zaune yayi bakin gado ya buga tagumi yana kallon enveloppe d'in hannunshi, abinda ya wuni yana damunshi ne ya sake fad'o masa a rai a daidai lokacin, idan ya tuna abun nan har ji yake kamar yayi ihu ko yaji zuciyarsa ta rage nauyin nan, saidai ina ba zai iya hakan ba, sai ma kama istigfari da yayi a zuciyarshi, har ta mik'e ta nad'e sallayar ta cire hijabi ta zauna kusa da shi bai lura ba, saida ta dafa kafad'arshi tana lek'a fuskarshi tace "Sheikh da tunani hakka?"


Da sauri ya kalleta yana murmushi, numfashi ya sauke yace "Kin idar ashe?"


"Na idar amma sheikh nawa ya tafi duniyar tunani." Ta fad'a cikin shagwab'a, d'an murmushi yayi yace "Ba tunani nake ba, akwai abinda nake yi ne."


Da mamaki ta kalleshi tace "Karatu kake? Ko wani sabon zikiri ne aka samu mai falala ba'a fad'a mana ba."


Dariya yayi tare da jawota ya rumgume yanda ba zai cutar da abinda ke cikinta ba yace "Sabo ma kuwa, yanzun nan na bincikoshi a wani littafi."


Cikin dariya tace "To fad'a min a kunne naji, dan kar iska ta d'auka ta fitar a waje."


Shi ma cikin dariyar tare da son kawar da abinda ke ranshi ya tallabo fuskarta da hannu d'aya yace "Wannan ai ko ido bana bari ta gani ba bare kuma kunne ta ji."


Daidaita bakinta yayi akan na shi ya had'e labb'ensu, a sauk'ak'e ya shiga paputukar neman kamo harshenta, cikin samun nasara ya shiga tsutsar harshen yana sake k'amk'ameta a jikinshi yana son zura hannayenshi cikin rigarta, da k'yar ta jawo bakinta tana mayar da numfashi da k'yar kanta a k'asa, sake tallabo kanta yayi yana son had'a ido da ita yace "Ba kya ra'ayi na ne?"


Da sauri ta kalleshi tace "Ni d'in? Haka ya tab'a faruwa ne?"


Mik'ewa tayi tana gyara rigarta tace "Kai ma ai kasan duk sanda ka zo min ina maraba da kai, kawai dai baka tab'a kirana bane a wannan lokacin."


Dariya yayi ya sake yin tagumi yana kallonta yace "To yau na kiraki, wannan ai shi ne hadisin da kike son sani, an fad'a min akwai samun nasara sosai a fad'an bayan sallah isha'i da magauta."


Dariya tayi tana girgiza kai tace "Ba sai an min wani wayo ba, kawai mutum ya fito fili ya furta abinda ke zuciyarshi."


Wani shu'umin kallo ya mata da k'ananan idonshi yace " *Sawwama*."


Cike da karsashi tace "Na'am yah sheikh."


Mik'ewa yayi yana aje enveloppe d'in yace "To na kiraki da k'arfi yanzu, za'a iya bani had'in kai?"


Yanda ya jawota a hankali ya had'a jikinsu tare da zame mata hannun rigarta yasa ta yin murmushi tace "Dole na mana, idan na k'i amsa kira na kwana ina shan mita ana min wa'azi a gida."


Dungure mata kai yayi yace "Iyeeh! Ni ne ma sarkin mitar kenan? Yanzu fad'an Allahn da nake fad'a ma ya zama laifi, shikenan zan daina daga yau."


Hafsat dai dariya kawai take yi har ya rage musu hasken nan mai k'arfi, saida ya kwantar da ita a nutse ya mata runfa yace "Me zaki bani tukuncin ziyarar da zan kawo miki yanzu?"


Lumshe ido tayi cike da k'aunar mijin nata tace "Me kake da buk'ata *shugaba na*?"


Saida ya waina ido alamar tunani kafin yace "Ki amince zaki tafi dani hutu k'asar waje na sati d'aya."


Murmushi ta saki tace "Na amince."


Sumbatar bakinta yayi tare da jawo musu babban bargo suka rufe rabin jikonsu. 😎(Sheikh ka ci gaba da zazzaga tsiyarka a nan, Asas ma lokaci ya kusa)       *Bayan kwana biyu*Ba wani abunda ya zanca mata har yanzu, zaman shiru da kad'aici kawai take, ga makaranta da aka hanata zuwa bare kuma k'ofar gida, babban bak'in cikinta shiq ne yanda har yanzu Asma'u bata shigo gidan bΓ’ ita ma, sosai take buk'atarta take so suyi hira ko zata d'ebe kewa, amma ita ma shiru babu motsinta.


Tunda safe su aunty Sahura suka zo kamar yanda sukayi da ita, da k'yar Abba ya yarda su tafi tare dan cewa yayi saidai su tafi kawai, Shapi'a ce ta nuna masa basu son kalar da zasu d'auko mata ba, shiyasa yace su tafi tare amma fa karsu yarda ko daidai da shiga fitsari ban d'aki ta b'ace musu. Haka suka fito suna gaba tana baya dan kunya take ji ta jera dasu tunda ta fisu tsayi, su kuma akan tafiya suke bare ta durk'usa musu saboda girmamawa.


Haka suka je babbar kasuwa sukayi siyayya ta zab'i abinda take da buk'ata kafin suka juyo zuwa gidan har rana ta take sosai, taxi na aje su k'ofar gida ta sunkuya ta rik'e hannun Sahura cikin magiya tace "Aunty Sahura, dan Allah ku rakani na ga halin da Asma'u take ciki, kwana uku kenan ban ji motsinta ba kar a zo bata da lafiya."


Juyawa Sahura tayi ta kalli Shapi'a tace "Shiga da kayan ciki muna zuwa."


Jinjina kai tayi rumgumi kayan da k'yar ta shiga dasu ciki, su ma gidansu Asma'u suka shiga daidai da fitowar mahaifinta daga d'akin amaryarshi zai fita, saida Mimi ta duk'a tace "Ina kwana Abba."


Shiru yayi kamar bai ji ba sai ma gyara zaman hularsa da yake, mik'ewa tayi Sahura na gaba zasu k'arasa shiga ciki, cikin dakakkiyar murya yace "Dakata Mimi."


Tsayawa sukayi a tare suna kallonshi, sabo yasa saida Mimi ta k'ara durk'usawa saboda girmamawa tana saurarenshi, saida ya gyara tsayuwarshi da kyau ya shiga nuna mata da hannu yana fad'in "...
*Alhamdulillah*

Post a Comment for "MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 5 Na Samira Harouna"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...