MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 15 KARSHE Na Samira Harouna - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 15 KARSHE  Na Samira Harouna

MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 15 KARSHE Na Samira Harouna

- - Post a Comment

 MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 15 KARSHE

Na Samira Harouna
πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *57*

Sun jima wajen Hajia suna ta hira tunda suka zo mata ban kwana, Mimi na gefensu tana saurarensu tana sinne kai tana ta b'oye cikinta a cikin hijabi duk da ba fitowa yayi ba sosai, saida suka tashi zasu tafi duk suka mik'e tare Hajia na sake jaddada "Allah ya kiyaye hanya, Allah ya tsare, ku kula dan Allah."


Da fara'a suka amsa da "Ameen." Dafa kafaf'ar Mimi tayi tace "Ki kula da kanki kinji ko, duk abinda kika ji a jikinki kar kiyi k'auron baki ki fad'a masa."


Sunkuyar da kai ta sake yi tana jinjina kai alamar to, takawa sukayi zata rakasu saidai daf da fita k'ofar Asas ya turo k'ofar da dama a bud'e take yana fad'in "Assalama alaikum."


A tare suka amsa da "Wa'alaika salam." Ban da Mimi da ta amsa k'asa k'asa tana kakkawar da kan ta, dan ita fa yanzu kunyar Asas take ji, shiyasa duk lokacin nan da aka d'auka sau biyu kawai taje gidan Asma'u.


Da fara'a kamar yanda suka saba sukayi musabaha Asas na fad'in "Hajia bak'i kikayi ashe?"


Dak'uwa ta masa tace "Su waye bak'in a gidan nan?"


Sheikh ne ya tab'e baki yace "Watak'ila shi Hajiarmu, ya manta mu 'yan gidan nan ne."


Dariya Hajjia tayi tace "Da alama kam."


Kallon sheikh yayi yana turo baki gaba yace "Ni fa ba bak'o bane, ni da gidan Hajiata d'in."


Harara sheikh ya dalla masa yace "Kai bana da lokacinka, tafiya zanyi sai na dawo."


Murmushi yayi ya d'an saci kallon Mimi dake bayan Hajia kad'an yace "Matar yaya ina wuni?"Rintse ido tayi tana d'an yatsina fuska ta amsa k'asan mak'oshi da "Barka."


Da murmushin shi a fuska ya d'ora da "Ya su Hafsy? Kwana biyu baki lek'a k'awarki ba?"


Bud'e ido tayi a hankali ba tare data kalleshi ba tace "Lafiya lau."


Mayar da kallonshi yayi kan sheikh dan ya fahimci bata cika son kulashi ba yace "Sheikh sai ina? Ko shak'atawa aka fito?"


"Um." Ya fad'a yana wucewa inda Mimi ta bi bayanshi yana fad'in "Zan sameka gida ne?"


Juyawa Asas yayi ya kalleshi yace "Yaushe?"


"Yanzu." Ya fad'a kai tsaye, da mamaki yace "Da gaske wai? To indai hakane saidai na tafi yanzu dan ku sameni."


Juyowa yayi ya kalleshi yace "Ba abun ujila bane, daga nan gidansu zan kaita, daga nan ne zan wuce da ita can." Da kallo ya bisu suka k'arasa fita kafin ya maayar da hankalinshi kan Hajia.*Tsaye* suke k'ofar gidan cirko cirko kamar masu jiran fitowar wani, a karo na ba adadi kenan da sheikh ya kalleta yace "Ryam, yanzu a nan zamu tabbata a tsaye kamar wasu masu zance?"


Sake marairaicewa tayi tana d'an kukan shagwab'a tace "Ustaz ba haka bane, ni wallahi kunyar Mama nake ji, data ganni fa zata shiga k'are min kallo har sai ta gane ina da wannan."


Ta fad'a tana dafa cikinta, girgiza kai yayi yace "Ryam abun farin ciki ne fa, Mama zatayi murna da haka fiye da tunaninki, ita a wajenta hakan ya tabbatar mata lallai 'yarta ta girma, hakan yana mata nuni da cewa 'yarta ta zama babba, hakan na alamta mata ashe 'yarta tauraruwa ce ita ma a gidanta, hakan na nuna mata ke ma mijinki na kulaki, ba wai kara zube kike a gidan shi ba, Ryam Mama zatayi farin ciki zata samu jika daga gareki, ke 'yarta ta farko, duk soyayyar da take miki da wannan alkunyar kasancewarki 'yar data fara haifa, yanzu zata koma kan d'an dake cikinki ne, a da idan Mama bata kulawa da ke, a yanzu sanadin cikin nan zata zamo tana kulawa da ke fiye da yanda kike jaririya, dan Allah Ryam ki shiga mu gaishesu sannan ki nemi afuwarsu abisa komai kafin mu bar k'asar nan."


Jikinta a mace ta jinjina kai tana kallonshi tace "To muje."


Gaba tayi yana d'an binta a baya yana fad'in "Ki fara shiga sai ki fad'a musu tare muke."


"To." Ta fad'a tana saka k'afarta d'aya a cikin gidan, kamar an tsayar da ita kuma sai ta tsaya ta juyo tasa yatsarta babba a baki tana d'an cizawa tana kallonshi tace "Sheikh kasan wani abu? Kuma fa Mama ma..."


Sai ta nuna mishi ciki ta nuna cikin gidan alamar Mama ma ciki ne da ita, sai kuma tayi kamar zata fashe da kuka tace "Ni wallahi kunya nake ji."


Da k'arfi sheikh ya rik'e dariyarshi a zuciyarshi yana fad'in "Oh Allah." A zahiri kuma saiya gimtse ya kalleta yace "Ryam zan shiga masallacin nan na shelantawa mutane kina d'auke da ciki, kinsan dai zan iya ko?"


Zaro ido tayi da sauri ta shige cikin gidan tana fad'in "Sheikh."


Da sallama ta shiga Abba dake wanke hannaye ya gama cin tuwo ya amsa yana zuba mata ido, bai bari ta k'araso ba yace "To uwata shirmatu, yau kuma da wace aka zo mana?"


Murmushi tayi ta k'arasa kusa da shi ta durk'usa da ladabi tace "Abba na daina komai fa, ina wuni?"


Girgiza kai yayi yace "Za dai ki daina uwata, ni tunda na ga ruwan lalle basu sa kinyi hankali ba ai na sare da lamarinki."


Mama data fito daga d'aki ne ta kalleta tace "Ke kuma fa daga ina warhaka?"


Da girmamawa tace "Ina wuni Mama?"


Zaune mama tayi tana d'an shanye cikinta daya fito sosai a k'alla wata shida tace "Lafiya lau."


Mik'ewa Mimi tayi ta k'arasa kan tabarmar kusa da Mama ta zauna tana satar kallonta, kunya take ji sosai tana rufeta ita da ciki mamanta ma haka, sai kawai ta sunkuyar da kan ta tana d'an cije leb'e, Abba ne yace "Wai ke da wa kika zo a daren nan?"


Turo baki tayi ta kalleshi tace "Abba tare da shi ne fa." Kallon Mama tayi tace "Mama wai ina su Yaseen?"


A dak'ile Mama tace "Sun tafi gidan Iya na aikesu."


Mik'ewa Abba yayi yace "Kinga irinta ko? Kin gani, yanzu shigowa tayi ta baro waje ko a jikinta."


Ficewa yayi yana gyara zaman hularsa, jim kad'an ya dawo da sauri yana d'auko kujerar roba ya aje ya cewa Mama "Shigowa zaiyi ya gaisheki, kinji wai yana mahaukaciyar zai d'auka su tafi k'asar waje."


Kyab'e fuska Mimi tayi ta kalli Mama da ita ma ta kalleta, mik'ewa mama tayi ta d'auko d'an k'aramin hijabinta ta saka ta zauna tana takura kanta yanda ba za'a gane cikin jikinta ba, cikin nutsuwa da dattako ya shigo d'ai bayan d'ai cikin shigarshi ta kamala, a nutse ya zauna kan kujerar bayan yayi sallama Mama ta amsa, kanshi sadde k'asa yana kallon hannayenshi suka shiga gaisawa da Mama sosai, kafin daga bisani ita ma ya fad'a mata zasuyi tafiya ne su ka zo yi musu ban kwana.


Cike da dattijantaka Mama tace "Allah ya kiyaye hanya, a je lafiya a dawo lafiya."


Kallon Mimi tayi tace "Sai a kula kuma, ban da shiririta dan Allah."


Murmushi yayi a ranshi a furta "Akwai ta kam."


Mimi kuma turo baki tayi tana mamakin yanda duka iyayen na ta har yanzu suke ganinta da shirme bayan ita tasan ta daina yanzu.


Sun jima zaune kafin ya mik'e yace "Zamu wuce, sai anjimanku."


Mik'ewa Abba ma yayi yana fad'in "To shikenan, sai anjima, Allah kiyaye hanya Allah tsare."


"Ameen Ameen." Ya fad'a yana d'an satar kallon Mimi duk da ba hasken wuta ke akwai ba, Mama ce ta d'an zunguri Mimi hakan yasa ta mik'ewa a kasalance ta saka takalminta cikin shagwab'a tana fad'in "Abba, Mama ni dai ku yafe min duk abinda na muku, kunga dai jirgi zan hau ko? Ban son ko na sauko a raye ba."


Bata jiran amsarsu ba ta yi gaba sai sheikh ne ma ya bita a baya,a k'ofar gidan suka ci karo da su Yaseen sun dawo, tsayawa tayi da k'annanta suka gaisa tana fad'a musu zasuyi tafiya, ai da sauri Amir yace "Mimi ni dai ki kawo min irin moton nan na wasa."


Yaseen kam cewa yayi "Ni dai duk abinda kika kawo min ina so."


Dariya tayi tace "To shikenan zan kawo muku, amma ku kawo kud'i?"


Zazzaro mata ido sukayi suna kallo sai kuma suka saki murmushi Yaseen na fad'in "Idan kika siyo zamu biyaki."


Sheikh dake saurarensu ne ya kamo hannun Amir yana sunkuyawa sosai yace "Rabu da ita kaji, idan ma bata siyo ba ni zan siyo."


Hannunshi yasa aljihun babban rigarshi ya ciro sababbin kud'i a mik'e zar ya damk'a mishi yace "Wannan na kashewa ne idan zaka tafi makaranta."


Godiya yayi cike da jin kunya yana rik'e kud'in da hannu biyu, shigewa sukayi ciki su ma suka shiga mota suka nufi gidansu Iya, nan ma sun d'auki lokaci suna ta raha da tsokanar juna malam na fad'in ya yarda ya ara mishi amaryarshi su je su dawo, hakan yasa sheikh farin ciki sosai da jin wani sabon nishad'i, nan ma d zasu tafi kud'i a aje musu suka fito zasu tafi.


Iya ce ta rik'o hannunta cikin rad'a tace "Ke! Wai yanzu wata na nawa koke ciki ne? Bana son sai kinje can zaki fara awon farko."


Da mamaki Mimi ta kalleta tace "Iya watan me? Wane irin awo kuma? Na masu tamowa?"


Dak'uwa Iya ta mata tace "Na masu shan Inna dai, ina maganar k'warai zaki saka min shirme."


Turo baki tayi tace "To Iya ban gane me kike nufi ba ko?"


D'auke kai Iya tayi daga gareta tace "To na ji, cikinki na ce watanshi na nawa ne yanzu?"


Bud'e baki tayi tace "Lahhh! Iya kuma haka kika koma? To ni gaskiya ban sani ba."


Dungure mata kai tayi tace "Ke wai ba zaki cire shirme a rayuwarki ba, to karki sani bari na tambayi wanda ya sani."


Zaro ido tayi tace "Wa wai?" Nuna mata sheikh tayi dake tsaye bakin mota shi da malam suna d'an hira, ganin ta nufesu yasa ta rik'o hannun Iya tana fad'in "Kinga Iya ki daina bana so, a kan me zaki tambayeshi wai cikina, na fad'a miki ina da shi ne to?"


D'an gajeran hannunta ta kwad'a mata a kan ta tana fad'in "Sakeni ja'ira kawai, kin rainani dan kinga tsawona bai wuce k'ugunki ba ko?"


Ai kuwa fitowa Iya tayi ta tsaya daga bakin soron tana kallonsu da kunya tace "Yarinyar can wai nake tambaya watanta nawa ne yanzu? Ina so ta fara awo a nan gaskiya ba k'asar masu jajayen kunnuwan nan ba."


Kallonta sheikh yayi sai kuma ya kalli makullayen hannayenshi yana fad'in "E to, ina jin dai watanta na hud'u ne wannan."


Murmushi Iya tayi tace "Yawwa to ina ga tunda tafiyar ta ku jibi ne me zai hana gobe na rakata ta je awon fari, kenan idan kun dawo ta ci gaba da zuwa."


Da fara'a sheikh yace "Hakan ma yayi Iya, Allah ya nuna mana goben da rai da lafiya."


"Ameen." Ta fad'a ta juya zata koma ciki Mimi kuma ta k'arasa fitowa, hararan juna sukayi ita da Iya tana murgud'a baki tace "Gaskiya ni a daina min haka, ina ce dai yanzu na bar miki tsohon mijinki tunda ni ma na samu nawa, to me ye na son cizgani a cikin mutane kuma?"


Kallon malam tayi dake ta k'yalk'yala dariya yace "Malam na tab'a fad'a maka wani abu ne tunda muke?"


Girgiza kai yayi yana ci gaba da dariyarshi, Iya kuma shigewa tayi tana fad'in "Idan jin ta kike dani ki bari gobe da safe na sameki gidan naki sai muyi."


Juyowa tayi tana kallonta tace "Iya kika je gidana da sassafe da angulu zan had'aki."


Dak'uwa ta mata tana dariya tace "Ta jima bata kasheni ba angulun, yar banza b'ulelliyar wofi."


Gwalo ta mata tace "Yo Iya kuma yaushe aka fara hassada da k'ibata? Yar mulmujewar dana fara yi har an fara saka mata ido."


Zagayawa tayi ta mota zata shiga ganin yanda malam da sheikh kamar zararri suke ta k'yak'yata dariya, Iya ma dariyar tayi a yanzu tace "Wannan k'ibar ce 'yar mulmujewa? Ai ina ga da kin haihu sai an ganki a d'auka ma ke ce uwar gida, dan jikinki bud'ewa kawai yake."


Saida ta bud'e murfin motar zata shiga tace "Na ji dai, ki ci kanki Iya."


Shiga tayi ta zauna tana ci gaba da kallonshi yana ta dariya, haka ya tayar da motar suka d'auki hanyar komawa, ba tare daya tsagaita da dariyar ba yace "Wasar Kaka da jika akwai dad'i, ina ma na wa kakan ko kakata suna raye, dana kwatanta irin haka da su nima."


Murmushi tayi tace "Hakan ya birgeka ne?"


Jinjina kai yayi yace "Sosai, kun birgeni matuk'a, kamar na zauna nayi ta kallonku."


Cikin zuba mishi ido tace "Idan zaka dinga biyanmu ai sai ka dinga kawoni kullum muna dramar a gabanka kana dariya."


Wata dariyar ya sake bushewa da ita yace "Ke mai wayo ko?"


Turo baki tayi tace "To miye a ciki, ai kowa yan...tsaya tsaya tsaya sheikh, dan Allah." Ta k'arashe tana kallonshi, da sauri ya taka birki bai shirya ba dan yanda tana tsaka da magana ta shiga fad'in ya tsaya ta sa gabanshi fad'uwa, kallonta yayi yana sake dudduba jikinta yace "Lafiya? Me ya faru Ryam?"


Nuna mishi mai baron da suka baro baya kad'an tayi tace "Bredi nake so, gashi nan baya."


Wata k'akk'arfar ajiyar zuciya ya sauke ya had'a kanshi da sitiyari yace "Hasbunallahu wani'imal wakil."


D'an dafa kafad'arshi tayi a sanyaye tace "Akaramako, kan ka ne ke maka ciwo?"


D'agowa yayi ya zuba idonshi cikin na ta da mamakin jin wai akaramako, girgizz kai kawai yayi ya juya ya kalli mai bredin dake tafiyarshi ya soma musu nisa, bud'e murfin motar yayi ya fita zai rufo sai kuma ya kalleta ya nunota da yatsa cikin muryar gargad'i yace "Ki jirani na dawo, idan kika fito a motar nan ranki zai b'ace."


Jinjina kai tayi alamar to, da kallo ta bi shi har ya siyo bredin aka saka mishi a leda ya dawo motar, mik'a mata yayi tana karb'a ta fara sincewa, tayar da motar yayi yace "Da fatan dai ba ciye-ciye zaki min a mota ba?"


Kallonshi tayi tana kwance ledar tace "Yawuna har tsinkewa suke, idan ka hanani wallahi hukumar kula da hakk'in yara zan kai k'ararka."


Murmusawa yayi yace "Ki ce na tauye hakk'in abinda yake cikinki?"


Nuna kanta tayi tana fizgar bredin mai laushin gaske ta kai bakinta tana taunawa tace "Ni dai, ni nake nufi."


Zaro ido yayi yace "Oh! Wai ke ce yarinyar dama?"


D'aga kai tayi alamar e, shi ma jinjina kai yayi yace "Lallai, Ryam zanyi addu'ar Allah yasa mace zaki haifa."


Da sauri ta kalleshi tace "Me yasa? Ni ma ai ita nake so na haifa."


Kallonta yayi yace "Me yasa kike son haifar mace?"


Cike da rashin damuwa tace "Na dinga mata kitso na saka mata ribom na mata kwalliya na saka mata riga da siket na kanti ko kula riga da wando sannan na tafi biki da ita."


Galala kawai yayi yana kallonta yana jin ba dan tuk'i yake ba da sai yayi tagumi ya k'are mata kallo, sai kawai ya girgizz kai a zuciyarshi yace "Allah ya miki albarka Sawwama, duk da shekarun k'uruciya aka had'amu, amma ban ga irin haka daga gareki ba."


Sake kallon Mimi yayi yace "Ni kuma saboda ta zama silar zamarki uwa ta gari nake son ki fara da mace."


Kallonshi tayi irin kallon na na fahimta na basira, sai ta d'auke kan ta a hankali tace "Zan zama, zan zama insha'Allah, da kuma taimakonka."


Murmushi yayi yace "Da taimako na, amma kuma da taimakon Qawwama, dan ta fini kula da yara yanda Allah da manzon sa suka fad'a."


Da fara'a ta kalleshi ita ma tace "Na ji dad'in kasancewata a cikinku."


Murmushi kawai ya sake mata da haka har suka isa gidansu Asas kamar yanda dama suka shirya zasu je suyi ban kwana da su, Asma'u ta ji dad'in ganin Mimi haka ta sako hijab bayan Asas ya shigo da sheikh ta cika gabansu da kayan ci, saidai babu abinda suka tab'a sai ruwa musamman ma Mimi data ci bredi ta k'oshi a mota, basu jima ba suka mik'e dan 10:00 na dare har ta wuce sosai, sallama suka musu tare da addu'ar Allah ya kiyaye hanya. Daga nan kuma gida suka wuce, dake dama kwana Hafsat ne kai tsaye d'akinta ya wuce yayi shirin bacci.


Tana kwance kan k'irjinshi hannayensu a had'e suna wasa da su, d'aya hannunta kuma k'irjinshi take shafawa tana fad'in "Sheikh nawa, ka ga dai zanyi kewarka na wata d'aya ko? Dan Allah kamar yanda ka min alk'awari ka dawo nan da wata d'aya, ina buk'atarka a kusa dani."


Sumbatar yalwataccen gashinta yayi dake ta tashin k'amshi yace "Na miki alk'awarin nan Mangata, insha'Allah zan dawo a kan lokaci."


Hannunshi dake sakale cikin na ta ta sumbata tace "Nagode mijina, duniyata, aljannata."


Da fara'a yana d'an lumshe ido yace "Madalla da mata ta gari."


Ita ma a sanyaye tace "Madalla da miji na gari."


A tare suka fad'i "A bisa koyarwar addinin islama."


Tallabo hab'arta yayi suka kalli juna yace "Ina sonki sosai Hafsat, ina sonki uwar ya'yana, Allah ya sani ke ce ni kamar yanda ni ma ni ne ke, ke ce farin cikin gidana kuma salama a cikin rayuwata, wani lokacin har tuna irin gararin da zan shiga nake yi idan aka ce yau babu ke a tare da ni, sai na tambayi kai na an ya kuwa zan iya ci gaba da rayuwa? Sai na tambayi kai na anya zan sake murmushi a fuskarta? Anya kuwa idan na rasaki daga ni har 'ya'yana ba zamu tagayyara ba?"


Da sauri ta d'ora yatsanta a labb'anshi tace "Shiiiii! Haka ba zata faru ba mijina, Allah yana tare da ku, insha'Allah muna tare ka ji." Ta fad'a tana k'amk'ameshi k'am a jikinta, numfashi a dinga saukewa a kan ta mai fito da zafi ya sake fad'in "Ina k'aunarki sosai."


A sanyaye ta furta "Ni ma haka." A hankali ya rad'a lata a kunne "Muje na miki wanka, kar ki yi bacci da najasa a jikinki."


Dariya tayi tace "To a d'aukeni mana."


Yunk'urawa yayi ya sauka a gadon ya d'auki towel ya d'aura ya kimkimeta tsaf suka nufi ban d'akin.

                  *Washe gari*Sosai Iya ta ji dad'in yanda tunda safe ya tura mota sukutum aka je d'aukarta, saidai ga ta zaune falo tana jiran ja'irar ta bakinta ta fito bata gama shiryawa ba.


Sheikh ma dake kwance kan gadon tun shigowar Iya ya shigo tashinta, kallonta yake tana shiryawa a tsanake, da yaga dai shirin ba mai k'arewa bane yasa shi fad'in "Ryam Iya fa jiranki take, a k'alla ta d'auki minti ashirin zaune a falon nan ita kad'ai."


Yatsina baki tayi tace "Ai na fad'a mata tun jiya kar ta min sammako a gida, kuma ma awon sai ta wani rakani, salon muje tayi ta tona min asiri."


Dariya yayi yace "Ke da zaki jira layi a b'angaren masu ciki, ai kallon kallo zaku yi wa juna ke da su, da dukanku abu d'aya ya takaru, ta inda kika bi kika sameshi haka suma."


Juyowa tayi ta dakata daga shirin shafa jan bakin da take tace "Da gaske? Tabb'! Lallai zan sha kallo, wallahi sai na k'arewa kowace kallo, kuma idan kika min kallon da ban so bΓ’ na ce ni da ke duk kanwar ja ce."


Ban da k'yalknyala dariya babu abinda yake kafin yace "Amma dai kiyi a hankali kar ki ja fad'an da zaki daku fa a asibitin nan."


Murmushi ta masa tace "Karka damu ba zan yi ba."


Da son gasgatawa yace "Kin tabbata?"


"Na tabbata." Ta fad'a tana juyawa zata shafa jan bakin, mik'ewa yayi da sauri ya rik'e hannunta ya karb'e jan bakin yan fad'in "Kina da sani akan mutanen da Allah ya yarje ma ganin kwalliyarki kawai, amma me yasa kike son take saninki ne Innar Issa?"


Shagwab'e fuska tayi tace "Kayi hak'uri to, ka yafe min?"


D'aga kai yayi alamar ya yafe, mak'ale mishi tayi a wuya tana sumbatarshi, warware hannayenta yayi yana fad'in "Maza dan Allah, hanzarta Iya na jiranki."


Turo baki tayi tace "Ni fa na ga Iyar nan sai wani ji da ita kake, zan fara zargin ko son ta kake fa?"


Da mamaki ya kalleta yace "Yanzu ne ma zaki fara zargin? Ke a ganinki dan bana son ta ne na auroku? Ai da tsohuwar zuma ake magani."


Da sauri ta kalleshi tace "Lahhh! To sabuwar fa?"


Kyab'e fuska yayi yace "Tafi haukatamutum."


Tintserewa tayi da dariya ta d'auki jakarta ta rataya kafin suka fito a tare, Iya na had'a ido da ita ta wurga mata harara tana d'auke kai, Mimi ma d'auke kai tayi tace "A zo gidana kuma a harareni."


Kallon sheikh tayi tace "Yallab'ai ina angulayen nan suke wai?"


B'oye dariyarshi yayi yana kallon Iya yace "Iya kiyi hak'uri ta tsaidake."


Kallon Mimi yayi yace "Ku je dreba na jiranku."


Mik'ewa Iya tayi tana fad'in "Nagode Allah daya zamana ana allura a awon fari."


Zaro ido Mimi tayi tana kallonta sai kuma ta kalli sheikh, girgiza masa kai tayi tace "Um um! Wai da gaske ana allura?"


Lura da Iya zata b'allo musu aiki yasa d'an saisaita murya yace "Ina jin fa wasa take miki."


Ajiyar zuciya ta sauke tace "Haba, tunda ai ka ga bana jin ciwon komai ko?"


D'aga kai yayi alamar e, juyowa Iya tayi ta kalleta da kyau sai kuma ta gyara tsayuwa tace "Ke! Doguwar riga ce kika saka?"


"E." Ta fad'a tana kallon kan ta, cikin fad'a Iya tace "Ke bana son k'ananan iskanci, awon cikin ne zakiyi  mje da doguwar riga, to ya zakiyi  idan za'a miki awon kwance? So kike ni ma d'in a ce mahaukaciya ce kamar ke?"


Cikin jin haushi Mimi tace "Kamar 'ya? To me rigata tayi kuma? Haihuwar ce zan je yi?"


Matsowa tayi irin a zafaffen nan tayo kanta tana fad'in "Ke ki kiyayeni wallahi."


Baya ta ja sai sheikh daya kalleta da alamar gargad'i yace "Je canza kayan ki fito."


Juyawa tayi ta shige d'aki inda suka bita da kallo, a sanyaye Iya ta kalli sheikh dan sai taji ma ya fara bata tausayi, a ladabce tace "A yi ta hak'uri dan Allah, yarinyar ce kamar mai shafar aljanu wani zubin, ka d'an dinga tofa mata ayatul kursiy wasu lokuta."


Murmushi sheikh yayi yace "Insha'Allah."


Suna nan tsaye ta fito sanye da riga da zane mai kamar siket ya fito mata da tsarin zubin k'ugunta sosai, tuni sheikh ya bita da kallo "Lahaula walaquwatta illa billahil-aliyul azim!"


Sai kuma ya had'e yawu ya ci gaba da kallonta tana saka hijabinta da d'aura nik'ab, kallon Iya tayi tace "Sai mu tafi ko?"


Harara Iya ta banka mata tayi k'wafa, ita ma hararen gefenta tayi tace "Wannan awon ni sai na ce ma na fasa."


Cikin sub'atar baki Iya dake daf da fita tace "Yo fasa mana, ni na ce kiyi cikin ko a jikina yake?"


Da sauri Mimi ta juya ta kalli sheikh daya d'an zaro ido sai kuma ya kalleta ya saki murmushi, cikin fashewa da kukan sangarta ta nuna Iya data fita tace masa "Ka ji ko? Wai ita ce tace nayi cikin?"


Matsawa yayi kusanta yana share mata hawayen da ko alamarsu babu yana fad'in "Yi shiru haba rabu da Iya, kinga fa so take ta tsufar min dake, shiyasa take yawan sakaki jin haushi da surutu, daina kukan kinji ko tawajena."


Turo baki tayi tace "To na yi, amma ka min alk'awarin kafin na dawo zaka siya min tsire.?"Jinjina kai yayi yace "Zan siya, kuje Allah ya tsare."


Juyawa tayi ta nufi hanyar fita tana fad'in "Kuma ka kira Rakiya ka fad'a mata wallahi ban da allura."


"To." Ya fad'a yana kallonta har ta fita, yana hangensu daga nan ma yana kallon bakunansu na ta motsawa alamar dai sun d'ora a inda suka tsaya, girgiza kai yayi ya k'arasa ya rufe mata d'akin ya kulle kafin ya nufi d'akin Hafsat, dan nutsuwa yake son samu yayi bacci cikin sallama tunda an bashi hutu a wurin aikin. A gidan nan kuma indai nutsuwa mai sunan nutsuwa yake so da hutu to fa dole sai wajen uwar 'ya'yansa, mahutarsa kuma annashuwar gidansa wato Hafsat.


Amma Ryam! Ryam! Ryam! Zuciya ce kawai da abunda take so, bΓ’ dan haka ba irin gwaramar da yarinyar ke had'a masa da babu soyayya to tabbas tuni ya yanka mata ticket, idan ba zuwan Ryam ba wa ya tab'a gigin taka rawa a gidanshi, sai gashi a gaban idonsa ake yi tun yana kakkawar da kai har ya fara kallo wani lokacin ma yaji ta birgesa har ya juye da ita a cikin kogi su shiga iyo.

*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *58*
*A gurguje*
Yau Mimi ce ta bud'e idonta k'afarta akan babbar birnin k'asar DubaΓ― wato Abu Dhabi, lokaci lokaci saΓ― mta kalli sheikh ta tintsire da dariya, shi kuma sai dai ya girgiza kai yana kallonta kawai, da haka suka isa babban masaukinsu suka shiga wanka kafin su zauna cin abinci, buga kai tayi a k'asa wallahi ba zata ci wannan kalan abinci ba, da k'yar ya lallab'ata ta ci gasassar kazar da ita ma tace babu d'and'ano ba yaji ita kawai ba dad'i.


Da fari dukansu sun d'auka ko rashin sabo ne da tafiya ya jawo mata zazzab'i da kuma ciwon k'afafun, amma data kwana uku babu sauki sai ya nemi su tafi asibiti, data nuna a'a k'yaleta kawai yayi dan ba zai manta da suka tafi awo da Iya ba, iya d'ibar jinin da ake na kan yatsa ma bata yarda an mata ba, haka aka zo allura bata tsaya ba kafatanin asibitin saida aka san Mimi ta halarta, mutane dayawa sun sa baki kan ta tsaya a mata dan lafiyarta da ta abonda ke cikinta, amma bata saurari kowa ba ta ce gida zata koma, haka wasu suka dinga fad'in ai tayi raguwar dubara tunda ta yarda ta d'auki cikin, zasu su suka ga yanda zata haihu d'in. _(Ina nak'udar Khalid na ga mai cikin da bata son allura,🀣 haka na manta da nak'uda nake na shiga kallonta ana neman tausheta a mata allura, wallahi a k'arshe sai likitocin ransu ya b'ace suka ce mijinta ya d'auki tsiyarshi🀣 su basu wuri)_


Haka sheikh ma sukayi saida rana da suka dawo gida aka kira Hajia tare da Rakiya ta mata abinda ya dace shi ma saida sheikh ya had'e fuska ya nuna sam bai san ta zai ma kikkifa mata mari kad'ai ta tsaya.


Magani dai yake mata dubara a sauk'ak'e tana sha, saida ta d'auki sati a haka kafin jikinta ya warware da kyau, daga ranar fa ta ce k'afa mai na ci ban baki ba? SaΓ― ta bud'e shafin yawo ita da sheikh, soyayya suke bugawa mai rai da lafiya mai cike da yarinta da wauta a ciki, tunda suka zo sheikh zanzarewa yake da k'ananan kaya irin wanda suka dace da shi dattijon arzik'i.


Yanzu kam ya fara zarmewa shi ma, dan ranar farko da suka fara fita Mimi b'oye fuskarta take wai kar a ganta a d'auka ko kakanta ne? Da fari maganar cakarsa tayi sosai a zuciya, amma daya d'auki hak'uri ya d'ora bai san sanda ya sureta ba ya labta a bayanshi, wutsil wutsil ta fara yi sai ya sauketa shi kuma ya k'i saida suka yi nisa, har saida ta kai ta gyara kwanciyarta a bayanshi tayi shiru dan ta fahimci babu ma wanda ya kula da su, tun daga ranar ne ya zama ko fita sukayi bata shakkar tab'a shi a wani sassa na jikinshi shi ma baya jin d'ar d'in tab'ata ko sumbatar goshinta ko kunci.


Wasa wasa sai ga Mimi ta sake wata k'iba masha'Allah wacce ita kan ta ta fara jin ta fara mata nauyi yanda take ganin idan ta k'ara fiye da haka zata takura mata, shi kan shi sheikh da wasa wasu lokutan yake fad'a mata "Ryam ki dakata da k'ibar nan haka dan Allah, bana so ki kai matakin da ba zan iya d'aukarki ba, kinga dai tsufa nake k'arawa ke kuma kina k'ara k'iba."


Marairaicewa kawai take tace "To ya zanyi? K'ibar ce lokacinta ya zo ni kuma ban tara ko sisi ba, zan zubawa sarautar Allah ido kawai."


A haka suka kwashe wata d'aya cir a k'asar Abu Dhabi wanda a wannan lokacin har Paris saida suka lek'a kwanansu hud'u, zuwa lokacin kuma shirye shirye ya kam-kama sosai saboda gabatowar watan azumi, hakan yasa suka juyo zuwa dawowa k'asarsu dan duk yanda abubuwa zasu taso ma sheikh da zasu iya sa shi barin k'asa ban da wannan watan, ko ma menene ya kan hak'ura d shi dan ya samu damar azumtar watanshi a cikin iyalenshi da kuma jama'arshi.                 *Ramadan*Kaf ya gama da duk wata buk'ata ta gidanshi, kama daga kayan sallahnsu zuwa kayan abinci da yasan ya kan tanada na bud'a baki da suhur. Dan haka suka zauna duka a falonshi bayan ya kalli kowace yace "Muna saka ran tashi da azumi gobe, mu d'ora niyyar azumtarshi, idan Allah yasa mun riskeshi mu tsawwala aiyukanmu na alkairi, kada mu raina aikin lada komai k'ank'antarshi, mun fahimta?"


Jinjina kai duka sukayi inda ya kalli Hafsat yace "Kinsan komaai Hafsat a game da watan nan, Mimi ce bak'uwata a yanzu."


Ya fad'a yana kallon Mimi dake ta jijjiga k'afafunta dake mata masifar ciwo, d'orawa yayi da "Sai kinyi hak'uri Mimi da yanda zaki sameni a yanzu, duk watan azumi abubuwan sukan taru su sakΓ© min yawa, hakan na jawowa iyalina rasa kaso mai yawa a cikin lokacina, amma idan kikayi hak'uri kamar yanda 'yar uwarki tayi, zaki zo ki saba ke ma har ma wata rana ki k'arfafa min gwiwata."


Saida ta cije leb'enta na k'asa sosai kafin ta sauke numfashi, nauyi sosai take ji a jikinta wallahi gaba d'aya bata jin dad'in jikinta, a sanyaye tace "Ba komai Abban Humaira, Allah ya mana jagora, Allah ya taimakeka a dukan lamuranka ya bada sa'a."


"Ameen." Ya fad'a da farin ciki tare da kallon Hafsat yace "Ba wani abu dana manta ban yi ba? Ko kuma kuke da buk'atarsa?"


Girgiza kai tayi da fara'a tace "Ba komai yallab'ai, ban sani ba dai ko uwar yan hud'u."


Tare suka kalli Mimi da ita ma ta kalli Hafsat d'in suna mata dariya, turo baki tayi cikin shagwab'a tace "Ka gani ko? Wai saita dinga kirana uwar hud'u?"


Dariya ya sake fashewa da ita yace "Haka ta gani ai."


Sake turo baki tayi ba tace komai ba ta kawar da kai, cikin dariya yace "To Hajia ba abinda kike buk'ata?"


Girgiza kai tayi tace "Babu, idan ma akwai ba zai wuce yakuwa da nake son ci ba, kuma zan sa su Yaseen su kawo min."


Murmushi yayi yana girgiza kai yace "Nagode Allah da ba'a ce na je na tsinko da kai na ba."


Hafsat ce ta kalleta ta k'yabta mata ido tace "Tab'! Da ni ce kam sai ya cirota da kan shi."


Wani kallo Mimi ta mata ta murmusa tace "Bar shi auntyna, akwai abinda zai min ne na musamman shi."


Zaro ido yayi yace "Ba dai ni zan kwad'a miki ba ko?"


Fari ta masa da ido tace "Wannan ai mai sauk'i ne."


A hankali ya kanne mata ido ya d'auke kan shi tare da mik'ewa tsaye, har zai fita ta marairaice tace "Dan Allah taimaka min na koma d'aki na kwanta yallab'ai."


Cike da kulawa da tausayi Hafsat tace "Har yanzu k'afafun basu daina ba?"


Cike d jimami tace "Aunty idan na sha maganin ma kamar k'arawa yake."


Mik'ewa tayi ita ma tsaye tace "Allah ya sauk'ak'a miki, ya baki ladar."


"Ameen." Suka fad'a tare da sheikh daya kama hannayenta ta mik'e tsaye, a hankali suka shiga takawa tana jin kamar tana takawa akan garwashin wuta, haka suka k'arasa d'akinta zai zaunar da ita tayi tsaye tace "Um um!"


Kallon tuhuma ya mata yace "Me?"


Cikin shagwab'a tace "Ni d'akina nake so nayi bacci."


Kama hannunta yayi yace "Muje to."


Mak'ale kafad'a tayi tace "Sai dai ka d'auke ni."


Girgiza kai yayi yace "Nawa zaki biya?"


Kashe masa ido tayi tace "Ka yarda na shayar da kai?"


Da sauri ya matso da ita kusa da shi yana mata wani mayen kallo yace "Zan fi son haka fiye da komai, d'an bani naji."


Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um, sai mun shiga d'aki ko."


A hankali yasa hannunshi cikin rigarta daga sama ya fito da nononta, sannu sannu ya kai harshenshi kan nononta yana zagayawa da harshenshi daga haka har...
        *Bayan wata hud'u*Wahala iya wahala Mama ta yi ta a wannan ciki har kawo yau da take nak'uda, dama ita ke haihuwa da kan ta yanzu ma haka likitocin suka tabbatar zata haihu, saidai yau kwana biyu kenan tana ta nak'uda a asibiti shiru, Abba hankalinsa ya tashi ya fita hayyacinsa, dan kamar dai yanda tayi nak'udar cikinta na farko ne na Mimi.


Suna zaune dukansu a tabarmar da suka shinfid'a wayar Abba tayi k'ara, yana dubawa ya ga lambar sheikh ce, da sauri ya kalli malam dake gefenshi yace "Kunga malam sheikh ne ke kira, bana so yarinyar nan ta ji halin da mahaifiyarta ke ciki, shiyasa tun shekaran jiya ina ganin kiranta bana d'agawa."


Malam yace "Gaskiya ne, ga Mimi da saka abu a rai ga kuma ita ma halin da take ciki."


Iya ce tace "To ka d'auka mana tunda ba ita bace."


Da sauri ya danna ok ya d'ora a kunne yana rangad'a sallama, fashewa tayi da kuka cikin tashin hankali tace "Abba me nai maka baka d'aga kirana? Abba kwana na uku ban da lafiya shi ne nake ta kiranka dan na nemi gafararku, amma baka d'aga kirana."


K'urawa su Iya ido yayi sai kuma ya sunkuyar da kai a sanyaye yace "Uwata me yake damunki?"


Cikin shashek'ar kuka tana sunkuyar da kan ta ita ma tace "Abba jikina ne gaba d'aya babu dad'i, k'afafu na sun kumbura sosai, jiya da muka je asibiti sun ce ban da jini ne."


Sai kuma ta sake fashewa da kukan da yasa sheikh sake rumgumata a jikinshi yana jin kamar zaiyi kukan shi ma, dan sosai yake tausaya mata halin da take ciki. Da k'yar Abba ya b'oye damuwarshi yace "Kiyi hak'uri uwata, zan zo na dubaki da kaina to."


A raunane tace "To Abba, yaushe zaka zo?"


A hankali yace "Gobe." Sai kuma yace "Ina sheikh?"


Mik'awa sheikh wayar tayi tana fad'in "Gashi."


Karb'a yayi cikin nutsuwa yayi sallama, sama sama suka gaisa dan kowa da abinda ke damunsu na larurar matan na su, daga b'angaren Abba ne yace "Kwanan biyu yau a asibiti mahaifiyarta na kan gwiwa ne, bana so ta ji dan bansan wane hali zata shiga ba, gashi ita ma tace bata da lafiya."


A hankali sheikh ya zameta a jikinshi ya mik'e tsaye ya shiga uwar d'akinshi yana fad'in "Subhanallah, Allah ya bata lafiya, Ubangiji Allah ya sauketa lafiya, amma ai da ko ni an sanarma, amma ba komai insha'Allah zan zo asibitin yanzu."


Godiya Abba ya masa kafin sukayi sallama ya fito, kusanta ya zauna ya d'auki madarar daya kad'a mata yace "To karb'i ki shanye, kin min alk'awarin zaki sha idan na kira miki Abba da ma."


Yatsina fuska tayi tana sako da hawaye ta rik'o hannunshi gam gam tana kallon fuskarshi tace "Sheikh tsoro nake ji, tsoro ya kamani sosai akan cikin nan, ji nake kamar ba zan rayu ba wallahi, sheikh ka yafe min ka ji, na san nayi maka abubuwa da dama..."


Da k'arfi ya fizgo kan ta ya d'ora a k'irjinshi ya k'amk'ameta, numfashi mai zafi ya shiga saukewa a saman kan ta daya dunk'ule sosai ya cukurkud'e saboda rashin gyara dan halin da take ciki ya fi k'arfin wasa, yanda zuciyarshi ke suka tana k'onewa, tausayinta na ratsa duk wata gab'a ta jikinshi sai ya ji idonshi sun cika taf da k'walla, a hankali ya lumshe idonshi sai kuwa hawayen suka sauko a kumatunshi, hakan yasa shi k'ara rintse ido ya furta "Ya isa haka Ryam, baki min komai ba kinji, na yafe, na yafe miki, ni ma ki yafe min dan Allah, duk ni ne silar shigarki wannan halin, ki yafe min dan Allah."


D'ago kan ta tayi suka kalli juna tana zaro ido tayi saurin saka hannunta ta share mishi hawayen tana fad'in "Lahhhhh! Sheikh? Kuka kuma? Haba dai, sai ka karya min zuciyata ai."


Sake kwantawa tayi a k'irjinshi tayi luf tana fad'in "Ni ma baka min komai ba, kawai ka tayani da addu'a na sauka lafiya."


Yana k'ara k'amk'ameta shi ma yace "Ina ta miki addu'a Ryam d'ina, tunda kika samu cikin nan nake miki addu'ar sauka lafiya, insha'Allah zaki haihu lafiya."


Shiru sukayi babu wanda ya sake magana saida ya ji tana sauke numfashi a hankali a hankali alamar bacci, cikin nutsuwa ya zameta daga jikinshi ya gyara mata kwanciyarta, d'aukar k'afafunta yayi da suka zama sumtuma sumtuma ya d'ora a kujerar, tsaye yayi yana k'are mata kallo yanda ta sauya kamar ba ita ba, tayi fuyau da ita alamar babu jini a jikinta, babbar damuwarshi da tashin hankalinshi da suka jawo masa rage walwala da cin abinci bai wuce yanda Rakiya ta fad'a masa wai jinin Mimi ya hau a awon ta na satin daya wuce, jinin Mimi ya hau kamar ya? Me ya kawo mata hawan jini? Ga matsalar rashin jini ga ta rashin cin abinci ga kuma kumbura da kullum k'afafunta ke k'arawa, ga nauyi da take jajen jikinta na dad'a yi mata kullum, hatta da alwala fa yanzu indai yana gidan sai ya taimaka mata, akwai ranar da taimama ya ce tayi dan shi baya gida kuma ta kasa ta shi a inda take ga lokacin sallah n wuce kawai yace tayi taimama a waya.


Madarar ya d'auke ya kai fridge kafin ya rufo mata k'ofar da makulli saboda ko Munzeer ba zai so ya tasheta ba, dan baccin kan shi ba samu take yi da dare ba, sauk'inta d'aya da Hafsat ta d'auke mata aikin gidan.


 

                   *09:20*Sai wannan lokacin kad'ai Allah ya sauke mama lafiya ta samu 'yarta mace, sanda sheikh ya samu labari saida yaje asibitin, kuma bayan ya je gida ya fad'a ma su Hafsat suka ce zasu tafi, haka ya kaisu duk da dare yayi kuma har da Mimi dake fama da ciwon k'afafu.


Da suka je Iya na ganinta ta shiga bin ta da addu'ar sauka lafiya, dan tana ganinta tasan ita ma lokaci ya kusa, sun jima asibitin suna ta hira ana dariya kafin suka bar asibitin.Kwana biyu da haihuwar Mama sheikh ya bawa Mimi kud'i yace ta yi wa iyayenta bajintar da zata birgesu, saida ta shawarci Hafsat ta bata shawara kafin ta raba kud'in uku kamar yanda ta ce, kaso d'aya a cikin uku ta ba wa aunty Sahura tace su yi siyayyar kayan cefanai na ranar suna, kaso biyu kuma ta bawa Abba tace yayi hidimar gabanshi, sai ga Abba na neman yin kuka da hawaye dan a lokacin ba wai sheikh ba daya masa kyauta data zautar d shi, Asas kan shi saida ya d'auke masa nauyin ragon suna da wasu abubuwan dayawa, gashi kuma 'yar Mimin sa ita ma ta kai lokacin da zata iya tallafawa rayuwarsa, sai kawai ya nemi fshewa da kuka, da k'yar Mimi ta dakatar da shi daga barin hakan.
*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *59*
A nauyaye ta tashi zaune tana furta "Hasbunallahu wani'mal wakil, hasbunallahu wani'imal wakil."


Gefenta ta zura hannu ta kunna siririn haske ta shiga rarumar wayarta dan kiran sheikh dake d'akin Hafsat yau, saidai wata zungura da aka mata a ciki tasa ta dafe mararta ta rintse ido tana fad'in "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Sheikh, Abdul, aouch!"


Zuro k'afafunta tayi da k'yar ta sauko a gadon tana sake kai hannu zata d'auki wayarta, wani irin ciwo ne marar misaltuwa bayanta ke yi da ba zata iya kwatantashi da komai ba, tana mik'ewa tsaye tayi saurin durk'ushewa tana sakin k'ara da fad'in "Wayyo bayanaaaaa! Wayyo Allahna."


Durk'ushewa tayi sosai k'asan gadon ta shiga cakumar darar dake kan gadon tana girgiza kan ta, wata zufa ce ta shiga tsatsafo mata tana ta sauke numfashi tana cika bakinta da iska.


Tun k'ararta ta farko ta sauka kan Hafsat dake zaune kan gado tana karatun Qura'ani, da sauri ta zabura tana kallonshi ta sauko daga kan gadon tana waiwaya wa inda zata ga hijabinta, tana d'aukar hijabin zata fita sheikh ma dake tsaye yana sallah ya kalleta yace "Ina zaki je?"


A rikice tace "Mimi, ihun Mimi ne, ina ga fa nak'uda take."


Juyawa tayi shi ma da sauri har doguwar rigarshi na nad'e mishi k'afa kamar zai kifa ya fad'i, saidai bud'a k'ofar da Hafsat tayi ya farkar da Khadija da yanzun ta saba kwana da ita kuma bata rabuwa da mahaifiyarta, fashewa tayi da kuka hakan yasa Sheikh saurin dawowa gareta ya d'auketa cak ya fita da ita hankali tashe.


Suna shiga suka sameta durk'ushe kan gadon ta fita hayyacinta ta canza kala, a rikice Hafsat tace mi shi "Nak'uda take, muyi gaggawar kai ta asibiti gaskiya."


Aje Khadija yayi kan gadon Mimi yace "Taimaka mata ta canza kayan jikinta to."


Da sauri Hafsar ta nufi inda kayan Mimi suke ta bud'a ta shiga duba mata riga da zane simple, sheikh daya durk'usa kusanta gashinta ya shiga gyara mata cike da tausayi yana fad'in "Sannun kinji Ryam, zamu tafi asibiti yanzu, komai zaiyi...haaaa"


Wani yunk'uri yayi ba tare daya ankara ba sanda ta shak'o wuyan rigarshi ta had'a goshinsu wuri d'aya, huci ta shiga saukewa tana fad'in "Zan mutu, zan mutu, sheikh mutuwa zan yi, Abdul bayana, bayana ciwo yake..."


Cikin dubara ya zura hannunshi ya b'amb'are na ta hannun a wuyanshi yace "Ba zaki mutu ba, insha'Allah zai bari kinji ko, kiyi ta addu'a."


Da sauri Hafsat ta dawo kusansu ta shiga k'ok'arin kamata ta mik'e tsaye, sheikh ma kamata yayi suka mik'ar da ita tsaye, kayan Hafsat ta mik'a mi shi tace "Ka taimaka mata ta canza wnnan, bari na dubo kayanta da aka siyo."


Karb'a yayi yana jinjina kai, juyawa Hafsat tayi ta fita a d'akin zuwan d'akin da aka ware na zuba mata kayan haihuwa har abinda yaro zai buk'ata, zare mata rigar baccin yayi ya saka mata wanda Hafsat d'in ta bashi, a hankali ya shiga jan ta zuwa fita a d'akin yana fad'in "Muje to."


Shigowa Hafsat tayi ta kalleshi da mamaki tace "A'a, hijabinta fa."


Sakin hannun Mimi yayi ya juya dan d'auko mata hijabin Mimi ta matse hannunshi gam gam ta durk'ushe tana fashewa da kuka da fad'in "La'ilaha illalahu Muhammad rasulillahi sallalahu alaihi wasallam! Wayyo Allah na bayana, bayana wallahi zai tsage."


Da sauri ya tallabota ya kalli Hafsat yace "D'auko mata hijabin dan Allah."


Da sauri ta nufi kayan na ta ta d'auko mata suka saka mata kafin suka fita, sai gashi yau sheikh da indai yana tare da matanshi bai cika barin ana tuk'ashi ba amma yau duka matan dole ya bari dreba ya jasu, dan kuwa Mimi ta rik'e rigarshi gam ta k'i saki, a haka har suka isa asibitin yana godiya ga Allah da yasa ba shadda ce jikinshi ba da tayi biji-biji a jikinshi, dan ba laifi fa yasha matsa daga gida zuwa asibitin nan, dan har akaifu take luma mi shi a cinyoyinshi ko kuma ta dinga bubbuga cinyarshi tana sallalami da salati.


A gaggauce aka shiga da ita d'akin haihuwa inda Rakiya ce ta jagoranci tsayuwa a kan ta, saidai tabbatarwa da tayi Mimi ba zata iya ba yasa ta fitowa ta shiga ofishinta ta cike takardar daya kamata sannan ta fito wurin sheikh dan bΓ’ shi ya saka hannu, suna zaune shi da Hafsat dake goye da Khadija sun buga tagumi, dan Hafsat d'in ce tace kar suyi gaggawar sanar ma gida tukuna su ji me ake ciki, zunbur ya mik'e yana kallonta yace "Ya ake ciki Rakiya? Ta haihu ne?"


A sanyaye ta sauke numfashi ta girgiza kai tace "A gaskiya sheikh Mimi ba zata iya haihuwa da kan ta ba, kwal d'inta k'arami sosai kuma gaskiya abinda ke cikinta ba k'arami bane, yana da girmama sosai shiyasa ba zata iya ba."


Wani iska ya furzo ya sunkuyar da kai yana tasbihi, ya d'an jima kafin ya d'ago jin Hafsat na fad'in "Yanzu miye abun yi Rakiya?"


Kallonta tayi tace "Zamu mata aiki ne a cire shi indai ana son ceto rayuwarta dana abinda ke cikinta."


Da sauri sheikh ya kalleta yace "A yi mata, a mata Rakiya indai zata rayu, dan Allah ki k'ok'arta ki ceci rayuwarta."


Da mamaki Hafsat ta kalleshi tace "Rakiya tayi iya k'ok'ari, muyi fatan Allah ya bata damar ceto rayuwarta."


Baya baya ya ja ya zauna inda Rakiya ta mik'a masa takardar hannunta da alk'alami, karb'a yayi ya saka hannu tare da mik'a mata, da sauri ta nufi d'akin nak'udar suka shiga kimtsa duk abun buk'ata ita kuma Rakiya ta kira babban docteur d'in dake wannan aikin.


Lokacin da aka fito da ita zasu shiga d'akin tiyata lokacin sheikh na waya da Abban Mimi suna sanar musu halin da ake ciki, Abba sai da yayi hawaye tare da koro musu addu'a, da kallo ya bita sanda suke wucewa tayi lak'was kamar bata motsi, saida ta b'ace ma ganinshi kad'ai ya lumshe idonshi, sannu ya shiga taro 'yar gajeruwar rayuwarshi da ita, k'iriniyarta da rashin jin ta, kwalliyarta da shan k'amshinta, a hankali ya d'an murmusa yace "Allah ka bata lafiya."


"Ameen." Hafsat ta fad'a tana kallonshi, da sauri ya bud'e ido ya kalleta dan ya d'auka a zuciyarshi ne yayi addu'ar.


*02:00* aka fito musu da santaleliyar yarinyar aka mik'awa Hafsat data rigashi tara hannunta, k'urawa yarinyar ido tayi mai d'auke da gashi luf luf a gaban goshinta kamar zai rufe mata ido, ba tayi mamakin ganinta mai gashin nan ba dan Mimi ba laifi tana da yalwarshi uwa uba kuma sheikh dake bafulace. Saidai wani abun mamaki a tare da yarinyar shi ne irin girmanta, tubarkalla gata jaririyar amma wata b'ulleliya ga kuma kan ta masha'Allah mai fad'i, haka kuma daga yanda halittar hannayenta da k'fafunta suke zaka san tabbas yarinyar nan irin hallitar iyayen Mimi ce da ita indai ba wani nufi na Allah ba kuma.


D'agowa yarinyar tayi sosai ta sumbaci goshin yarinyar tare da sakin murmushi tana kallon sheikh ta mik'a masa ita, karb'a yayi hannayenshi na rawa shi ma ya k'ura mata ido, murmushi ya saki ya kalli Hafsat yace "Kinga kamar uwarta, ja'ira Allah yasa kada tayi k'iriniya irinta uwarta, dan ta wahalar dani ba kad'an ba."


Hafsat da Rakiya a tare suka k'yalk'yale da dariya sai kuma ya kallesu yana had'e fuska yace "Ya mahaifiyarta take? Tana lafiya?"


Murmushi Rakiya tayi tace "Tana lafiya, insha'Allah za'a fito da ita nan da awa biyu a kai ta d'akin hutu."


Ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhamdulillah."


Kallon yarinyar ya sake yi yana jin k'aunarta ita ma kamar sauran yaranshi a sanda ya d'ora idonshi a kan su, duk da wannan d'in yafi wahaltuwa wajen rainon cikinta, amma ganinta na yanzu ya zama sanyin idaniyarshi tare da jin ya manta kowace azaba har da ta murzar daya sha yau sanda uwarta ke fama. Iya ce ta zo tare da Abba saidai shi ya koma ya barta nan ta kwana tare da Mimi. 


Kwanansu hud'u aka sallamesu bayan an tabbatar da ingancin lafiyarta data abinda ta haifa wacce ta ci sunan *Halimatu-Sadiya*, sunan mahaifiyar sheikh kenan wanda sanda ya rad'a sunan Mimi ta kalleshi tace "To yanzu ya zan kirata kenan? Mimi ko Maama?"


Murmushi yayi yace "Ya rage na ki."


Iya ma tab'e baki tayi tace "Gaskiya kam, idan tana so ma ta ce Uwani."


Turo baki tayi tace "To Iya na k'i na ce Uwanin, ba zan ce ba."


Hafsat dake ta musu dariya ne tace "Gaskiya Iya sunan gayu zamu dinga kiranta da shi."


Kallon Mimi tayi tace "Kinga k'anwata mu dinga kiranta da *Amatullah*."


Dariya Mimi tayi tace "Shiyasa nake son aunty na, ba kamar yan cikin bak'in ba."


Dariya sukyi dan sun fahimci da Iya take. Sun isa gida kuma Mimi ta fara gurza kalar na ta jegon mai cike da wuyar sha'ani, a zahiri ita ake ganin wautarta na k'in wasu abubuwan da take yi, bata shan kunu saita gaurayashi da madara yayi fari fat tasha sugar sannan ta kifa kai ta shanye, shan maganinta kam wannan k'a'ida ne sai sheikh ya zo yake bata shi ta sha, inba shi bΓ’ kam kowa aikin banza ne, duk wani abu da za'a ce tasha dan ruwan nono su zo ko 'yar ta mulmuje ta k'i, kuma a bad'ini sheikh ne ke zugata yana nuna mata ba addini bane, ta ci ta k'oshi kawai indai abun mai anfani ne a jiki zata samu ruwan nono ba sai tasha komai ba.

_🀣Dole fa mu k'are yan uwa, komai yayi farko da ma yana da k'arshe ai, wasu ma😁 a account d'in aure yak'in mata suke ta tura kud'i wai na matar mutum, ai da kun fad'a min tun farko dana siyar da littafin tunda na ga ya kawo wuta😎😜 amma zan muku *Mim-Sheikh* returns._         *Bayan wata biyu*Da k'arfi ta fizge zata yi waje tana fad'in "Wallahi ban yarda."


Sake rik'ota yayi ya had'a da jikinshi yana kallon cikin idonta yace "Da gaske Ryam, ba an miki allura ba ranar da kika kai Amatullah wajen tsaga ba? To ai a ranar kema na sa aka miki, ba zaki d'auki ciki yanzu ba."


Marairaicewa tayi muryar na b'arin tsoro tace "Abdul kaga dai cikin Ama ai na kusa mutuwa ko? To dama baka so na ne shiyasa yanzu ma ka lallab'o kake son sake min wani cikin?"


Sinne kan shi yayi yana ta k'ok'arin lalabo bakinta, d'ago da kan shi tayi tace "Fad'a min gaskiya sheikh na sani."


Kallonta yayi da idonshi da sukayi jajir suka rine yace "Ryam ina sonki mana, ke yanzu fad'a lin zaki ji dad'i idan na shareki bana kulaki?"


Da sauri tace "E, ni babu abinda zan ji, kawai ka tafi wajen Aunty Hafsat ta maka abinda kake so."


Had'e fuskarshi yayi yana kallonta yace "Korata kike ne?"


K'wacewa tayi daga rik'on daya mata ta ja baya tace "Ni ba korarka nake yi ba, amma dai ka je wajenta na yafe mata har zuciyata."


Da irin kallon nan mai nuna ran shi ya b'ace kuma zai iya yin komai ya kalleta yace "Kin tabbata na je?"


Ba abinda ya dameta tace "E, ka je."


Jinjina kai yayi ya juya inda Amatullah ke kwance cikin d'an gadonta, sumbatarta yayi a goshi d'aga hannayenshi ya tofa addu'a ya shafa mata sannan ya juya ya fice a d'akin bai kulata ba.Tun daga ranar Sheikh yayi wuri ya aje ta, dan yana so ya nuna mata akwai abinda dole ko yana cikin ran ta ta b'oyeshi indai akan shi ne, dan shi ba banza bane mijinta ne? Ko d'akinta ya shiga Ama ce ke kai shi ya d'auketa ya fito yasha wasarshi da ita sannan ya mayar d ita ya aje, yanzu dake tana zuwa d'akinshi gaishe shi ko taje gaisuwart yake amsawa ya shiga sabgar gabanshi.


Wasa wasa sai hakan ya fara damunta, musamman kayan marmarin data dinga had'awa tana ta kambama tana sha sai abun ya fara zam matsala, dan kuwa dan sha'awa ke neman haukatata inda k'amshin turarenshi kawai take ji ta dinga jin tsigar jikinta na amsawa. 


Gashi kuma ya k'i kulata bare ta bada kai bori ya hau, sai hakan yasa ta zama kullum a b'acin rai take, dan danan ta hau ta tunzura, gudun kar a samu matsala tsakaninta d Hafsat sai t zab'i zaman d'akinta kawai indai t gama abinda take.


*Yau* ma kamar kullum da sassafe ta shiga d'akin na shi sanye d hijab d'inta tayi sallama, amsawa yayi tare da aje Qur'anin hannunshi ya mik'e, dan ba komai yasa shi kakkauce mata ba saΓ― gudun kwafsawa, dan shi ma turarenta na rikitashi ga uwar k'ibar da tayi jikinta yayi wani irin luwai luwai, fatarta ka rantse zallar madara yanda ta kwanta da kyau abu ga fara dama, shiyasa baya son dogon zance ko mu'amula a tsakaninsu. 


Zai shige ban d'aki tayi saurin fad'in "Ina kwana."


Ba tare daya juyo ko ya tsaya yace "Ban ganshi ba."


Ba tayi mamaki ba dan tasan baya amsawa dama, saidai ganin ya shige ya barta tsaye yas ta sakin baki tana kallon k'ofar, sai kuma wata zuciyar ta izata kawai ta sa kai a ban d'akin.


Yana tsaka da cire rigarshi t shigo amma bai kulata ba, k'arasa cire rigar yayi dan dai ta fita ta bashi wuri yayi shirin zame wandonshi, ganin bata kula da haka ba sai ma gyara tsayuwa da tayi ta fara zazzga masifa tana fad'in "...
*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                  *K'arshe*

                                  *60*

Ganin bata kula da haka ba sai ma gyara tsayuwa da tayi ta fara zazzaga masifa tana fad'in "Wai ni kam Abdul me na maka ne kake wulak'antani a gidan nan? Dama da ake cewa da ka fara haihuwa sai namiji ya canza maka gaskiya ne? Duka haihuwa d'aya sai ka wani fara d'auke min kai? Me na maka dan Allah? Idan ka fara gajiya da ni ne ka fad'a min mana dan nasan inda dare zai min."


Dakatawa yayi daga shirin cire wandon ya k'ura mata ido, tsakaninta da Allah take maganar kuma babu alamar wasa, saidai abu d'aya daya fahimta duk da cikin fad'a take maganar, amma kuma muryarta a sanyaye sosai kamar wacce ke neman wani abu.


D'auke kai yayi yana sake had'e fuska ya kalleta da kyau yace "Kina buk'atar wani abu ne?"


K'yabta masa ido tayi idonta na cika tap da hawaye sai kuma tace "A'a."


Nuna mata k'ofa yayi yace "Fita to ki bani wuri, wanka zanyi kuma dai kinsan ba zan yi tsirara a gabanki ba ko?"


Galala tayi tana kallonshi sai kuma ta ji gabanta ma na fad'uwa dan yanda ya mata maganar ba da wasa bane, a hankali ta juya zata fita jiki a mace sai kuma ta juyo da sauri ta kuma kallonshi, marairaicewa tayi sosai ta sake kashe muryarta tace "Abdul kana hushi dani ne akan abinda ya faru ranar? Kayi hak'uri to kaji na tuba, wallahi ba zan sake ba, Abdul idan kana min irin wannan hushin a gidan nan ya kake so nayi to? Gidan nan dai ai saboda kai nake zaune, kai ne abokin hirata kuma farin cikina, idan ka yi hushi dani ya zanyi kenan?"


Kafeta yayi da ido yana kallon fuskar tausayinta kamar ya jawota ya rumgume, saidai a yanda yasan Mimi kai shi yasan da walakin goro a miya, tabbas akwai abinda take da buk'ata, amma sau nawa suke samun sab'ani saidai shi ya d'auki da dangana da girma ya nemi sulhu, amma ita ta dinga botsarewa kenan tana fusata tana hawa da sauka.


Ita ma kallonshi take ganin yana ta kallonta sai kawai ta fad'a jikinshi ta fashe da kukan shagwab'a tana fad'in "Kayi hak'uri yallab'ai ka yafe min ka ji."


Wani munafikin murmushi ya saki a ran shi yace "Na-san a rina dama, mata da kurb'e kurb'e musamman idan sun haihu."


Dariyar mugunta ya dinga saki ya shiga shafa jikinta yana zura hannayenshi cikin rigarta, tsam tsigar jikinta ta fara tashi tana rage sautin kukanta sai kuma ta d'ora hannunta na dama kan nonon shi tana shafawa tana rufe ido.


Biye mata yayi shi ma sosai saida yaji suna buk'atar kwanciya kawai ya janyeta a jikinshi ya sake nuna mata k'ofa da idonshi da shi ma ya kamu da jarabar yace "Fi...ta a nan."


Da mamaki ta kalleshi sai kuma ta sake langab'ewa ta matso zata rik'e hannunshi ya sake nuna mata k'ofar alamar ta fita, duk k'ok'arinta saida hawaye suka fito mata dan sosai take jin yanayi marar dad'i a jikinta, juyawa tayi a fusace ta bar d'akin zuwa d'akinta ta cire hijabinta ta kwanta gefen 'yarta dake baccinta ta k'ura mata ido.


Tun tana d'an lumshe ido tana matse k'afafunta har bacci ya d'auketa ita ma marar dad'i. A hankali ya shigo d'akin ya zuba mata ido, murmushi ya saki yana godewa Allah daya nuna mishi lagon yarinyar nan, kamar kowa'e d'an adam yana da rauninshi, haka shi ma yanzun ya hango na ta raunin, ba zai cutar da ita ta haka ba dan cituwar zata iya shafarshi, saidai shi ya d'an samu sauk'in wani abun daga gareta, abu d'aya da zaiyi shi ne ya sake dagewa wajen inganta lafiyarshi dan samun sauke mata hakk'inta, ya sani har ga Allah wasu lokutan idan ya zurfafa tunani ya kan ji kamar ya tauyeta, dan a lokacin da tsufa zai riskeshi ya kai k'adamin da baya buk'atar mace, ita kuma a lokacin ne zata kai ganiyar shekarunta da dole wutar sha'awa ke ruruwa a jikinta, tambayar anan ita ce shin ya zaiyi idan lokacin nan ya zo? Shin zai saketa dan kar ta fad'a halaka? Ko kuma idan ya rik'eta zata fad'a wata mummunar hanya ce?


Nauyayyen numfashi ya sauke yace "Hasbunallahu wani'imal wakil."


A hankali ya k'arasa kusanta tare da sunkuyawa yasa hannayenshi cak ya d'agata gaba d'aya, bud'a ido tayi da sauri tace "Waye?"


Sai kuma suka had'a ido, rufe idonta tayi jin yace "Waye kuwa ban da na ki."


Turo baki tayi tana wuntsila k'afafu tace "Sauke ni k'asa malam, bayan yanzu ka koroni a d'akinka."


Dariya yayi yace "Na gane ban kyauta ba ai, shiyasa na zo bada hak'uri."


"Ni kawai ka saukeni ba zan hak'ura ba." Ta fad'a tana kumbura, cikin fara'a yace "Muje kan gado tukuna na bada hak'urin, sannan ne zan tantance an hak'ura ko ba'a hak'uran ba."


D'akinshi ya shiga da ita ya rufe ya kaita kan gadon ya sauke, rumfa ya mata ya nemi had'a bakinsu sai kuma tayi zurum ta had'a bakinshi da na ta, waro idon da yayi ya kalleta yasa ta jin kunya ta cire bakinta a na shi ta sunkuyar da kai, tallabo hab'arta yayi yana kallonta da tausayi yace "Ryam, ni ne ko? Ni ake da buk'ata a wannan lokacin ko?"


A hankali ta jinjina kan ta sai kuma ta sunkuyar da kai cikin muryar kuka tace "Abdul k'aik'ayi nake ji a jikina, sai na dinga ji kai kawai nake so na ji kana tab'ani, ko k'amshin turarenka kad'ai na ji saina ji wani irin abu da bana gane ko miye, Abdul tsoro hakan yake bani, wasu lokuta ma idan kana d'akin Aunty Hafsat haka nake jin zuciyata na bugawa da sauri, sai na dinga jin haushin komai sai nayi ta kuka ni kad'ai a d'akina, amma ban tab'a fad'a maka ba dan bana so ka d'auka zan raina Aunty Hafsat ne."


Wuf yayi da bakinta a na shi ya shiga tsutsa dan kad'an ya rage ta saka shi kuka wallahi, ta bashi tausayi sosai yarinyar, hakan na nufin tana jin kishin shi kenan, amma bata nunawa ko kad'an ko da daga ita saΓ― shi ne saboda kar tayi laifi.
                 *Asa-Ma'u*
Sagala yaron yayi a gabanshi irin goyon nan na zamani hannunshi rik'e da bulunbotin yaron yana d'an jijjiga madarar da ake bashi wasu lokutan. Da sauri ta fito a d'akin tana fad'in "Yasha ne?"


Kallonta yayi yace "Yanzu dai zan bashi, kin shirya ne?"


K'arasowa tayi tana gyara hijab d'inta tace "Na shirya Baby, to wai me ya tsayar da kai da har yanzu bai sha ba?"


Turo baki yayi yace "To ni na iya ne, dan Allah ki bashi da kan ki."


Dariya tayi tace "Nima ban iya ba, yanzu dai muje Baby, kaga fa an kusa sallah la'asar yanzu."


Nufa hanyar fita yayi tayi saurin fad'in "Kawo shi to, so kake ka fita a haka a ce kai ke goyonshi?"


A hankali ya shiga since yaron daga jikinshi, saida ya kalli fuskarshi yana ta baccin shi ya mik'a mata ta karb'eshi, fita sukayi a gidan yana rufe k'ofar take fad'in "Yau nasan sai na ci d'an banzan duka a wurin Salma, bikin sunanta a ce sai yanzu nake fita a gida."


Juyowa yayi ya kalleta yace "A'a fa Hajia ba dole, idan ana ganin kinyi rana a warhaka ma wallahi sai mu koma ciki, ai kinsan duka kwananki uku yau da yin arba'in, babban jarumta fa na yi ta barinki fitar nan."


Dariya tayi tana kallonshi tace "Nagode to jarumi na, amma idan ka hanani ai kuka zanyi."


D'ora yatsarshi yayi a baki yace "Dan haka to a min shiru, kuma a je a dawo mu d'ora inda muka tsaya."


Bud'e mata k'ofar mota yayi zata shiga ta kalleshi ta ja kunnenshi tace "Wai kai abun nan baya isarka ne?"


Girgizz kai yayi ya rintse ido cikin shagwab'a yace "Wayyo Hajia zata cire miki kunnen yaro."


Sakinshi tayi tana dariya ta shiga ta zauna, saida ya shiga shi ma yayi oda mai gadi ya bud'e musu k'ofar sannan ya kalleta yace "Ko kad'an ba kya isata Ma'u na, ni kaina ina mamakin yanda bana gajiya dake kamar wani maye."


Dariy ta fashe da ita tace "Mayen Ma'u kenan?"


Jinjina kai yayi yana dariya ya bata hannu suka buge yana fad'in "Ashe kin gane, mayen Ma'u ne ni."


Isowar motarsu tayi daidai da isowar jibgegiyar motar sheikh, Asma'u na ganin motar tayi dariya tace "Shegiyar k'awa kenan, na d'auka ni kad'ai nayi maraice, ashe harda kayan gidan sheikh."


Dariya Asas yayi shi dai bai ce komai ba dan kan abinda ya shafi Mimi bai cika zak'ewa ba yanzu, karbar *Mujaheed* yayi ta fita sannan ta zagayo ta karb'eshi, k'aramar sumba ya aika mata tare da fad'in "Ki kula da kan ki Ma'u na, sannan ki kula min da zakina, ina sonku."


Murmushi tayi tace "Kai ma ka kula da kan ka, sai ka dawo."


Shiga gidan Salma ta nufa inda Mimi ma ta fito d'auke da Ama ta mata wani irin shiri na ban mamaki ga hijab d'un da aka saka mata yarinyar mai d'aukar hankali ta ci uwar kwalliya a fuskarta, murmushi Asma'u tayi ta nufesu a ran ta tana fad'in "Da alama shirin Ama kad'ai zai d'auketa awa uku."


Tana k'arasowa da ladabi ta d'an lek'a ta gaishe da sheikh Mimi na k'ok'arin karb'ar Mujaheed tana masa wasa, ita ma Asma'u karb'ar Ama tayi sukayi musaye. A mutumce sheikh ya amsa mata tare da mik'awa Mimi hannayenshi ta bashi yaron, sumbatarshi yayi kafin ya mik'o musu shi, zasu wuce ya sake kallonta yace "Ryam."


"Na'am." Ta fad'a tana juyowa, cike da gargad'i yace "Kin dai san aikina na baro na zo dan na kawoki nan, ki koma gida a kan lokaci kinji?"


"To tsohon yan matanshi." Ta fad'a tana wucewa ta bi bayan Asma'u data wuce da Ama, cike da zolaya Asma'u ke fad'in "Mimi irin wannan shiga haka kamar wata 'yar mafiya, wallahi babu mai ganeki saΓ― wanda ya sanki."


Banza ta mata har suka shige ciki suna ta ratsa taron matan suna shiga inda d'akin Salma yake, suna shiga da sallama Asma'u dai da ba nik'ab gareta ba an ganeta, amma dayawa basu gane Mimi ba, dan ruf take k'afafunta da safar k'afa d'auke da takalmi mai tsini, hijabinta dogo har k'asa ga kuma nik'ab, saida ta d'aga nik'ab d'in suka gane wacece, ai tuni suka kwashe da shewa ba ma kamar Jamila da ita ma ba'a jima da aurenta ba tace "Iyee! Ashe kayan gidan sheikh ne."


Salma kuma dak'uwa ta ma Mimi tace "Shegiyar matar malam, Mimi ke ce."


A hankali ta mik'awa Jamila Mujaheed ita kuma ta cire nik'ab d'in tasa a jakarta ta tattaro hijabin shi ma ta jefawa Jamila data fashe da ihu tana fad'in "Wai wai wai! Ke Mimi me kika ci haka a gidan sheikh wai? Kin ganki kuwa?"


A sanyaye kamar ba Mimi ba ta haura kan gadon ta samu wuri ta zauna tana gaisawa da sauren k'awayensu wanda ta sani da ma wanda bata sani ba, suna had'a ido da Asma'u dake kallonta da mamakin yanda ta ga bata kula da tsiyar da su Jamila ke mata ba, a sanin data ma k'awarta ta d'auka zata juya musu manyan d'uwawun nan na ta ne data k'ara masha'Allah sannan tayi fari da ido ta kwankwatsa musu magana, amma sai bata ga hakan ba ta ma fita a harkarsu.


Mimi ma murmushi ta sakar mata tace "Asma'u nayi hankali fa yanzu, ta y'a zan tsaya ina shiririta a gaban 'yata."


Dariya su Jamila suka fashe da ita inda Mimi ta kalleta taja tsaki, hararanta Jamila tayi tace "Mimi an matan tsohonta, wai dan Allah me kike sha ne."


Cikin jin haushi tace "Ke madarar mijina nake sha, ina dalilin wannan jaraba haka, na ji tsohon ne amma ai dan ubanki ke gaki nan har yanzu baki da ciki, ni kuma zuwa d'aya tak ya min na d'aukeshi."


Sauke numfashi tayi ta nunata da yatsa tace "Kinga ki rabu dani ko na ji da abinda ke damuna."


Salma dake ta k'yalk'yala dariya ce tace "To fa! Me ke damunki ne?"


Jamila ce tace "Watak'ila wani cikin ya mata."


"To sai me?" Cewar Asma'u, a raunane Mimi ta kalli Salma tace "Wallahi jiya kusan kwana mukayi a asibiti Mamar malam ba lafiya."


Da sauri Asma'u tace "Mamar malam kuma? Wane malam d'in?"


Nuna Ama tayi tace "Ama nake nufi dan Allah."


Cike da tausayawa Salma tace "Me ya sameta?"


Cike da jimami tace "Wallahi asma (athim)."


"Take da?" Cewar Jamila a tausashe, jinjina mata kai tayi tace "E, kamar da wasa fa yanzu gashi abun sai girma yake."


Addu'a sukayi ta jera mata kafin su ci gaba da hirarsu irin ta k'awayen zamani.Sanda aka fara shigo da abinci ne Mimi ta hangi Aisha na shigowa d'auke da *Ahmad* yaronta ita ma, da sauri ta kalli Salma tace "Ke dan ubanki ba dai k'awance kike da d'iyata ba?"


Kallonta Salma tayi ta kalli inda ta nuna sai kuma tace "To miye a ciki? Ke 'yarki ce ni kuma k'awata."


Duka ta kai mata tana fad'in "Ke tsir!"


Dariya Salma tayi tace "Ke wallahi ba wani k'awance bane muke, kawai irin gaisawar nan ce ta yanar gizo."


Shigowar Aisha yasa Mimi d'auke wuta ta kama jikinta irin ba wasan nan, da farin ciki Aisha ta k'arasa kusanta tana mik'a mata Ahmad ita kuma ta d'auki Ama tana mata dariya da fad'in "Aman Abie, kina lafiya?"


Mimi ma wasa take ma Ahmad dan ko gida Aisha ta tafi da shi Hafsat ce ke mishi tsiya, amma ita Mimi tace tana son abun ta, hakan yasa wata rana ma sheikh yace ta daina kawo masa shi gida tun kafin ya hanashi kwanciyar hankali a gida.                 *10:30*Fitowarshi kenan daga d'akin Hafsat ya mata saida safe ya shigo d'akin, ganin wuta kashe yasa shi lalubawa ya kunna, dau! Idanshi suka sauka a kan ta tana tsaya bakin gado ta dafe k'ugu da hannayenta duka biyu, daga k'asa ya fara kallon irin guma guman takalmin data saka, takalmi ne fa irin na 'yan matan zamani k'afa ciki wanda har maza na sakawa, wando dogo na mata wanda ya matse daga k'asa sama kuma a bud'e a wajen gwiwan da cinyoyi duk a yage irin dai na 'yan gayu, sai rigar mai botira a gaba amma duk ta b'allesu saita d'aure daga k'asa sosai, sai bras d'inta fara tas data d'an bayyana kad'an ita ma. Hula ta d'ora da ake kira hana sallah ga wani uban gilashi tartsetse a fuskarta da ta ci uwar kwalliya, sai bakinta dake d'auke da lolipop tana tsutsa.


D'an k'asa tayi da gilashin ta kalleshi da idonta da suka sha eyeshadow ta kashe mishi ido d'aya, a saukake ya had'a yawu murya can k'asan mak'oshi yace "A'uzu billahi mina shaid'anin rajim."


A hankali ta shiga takowa cikin takon birgewa har ta tsaya gabanshi hannunta dafe da k'ugu, sauke gilashin ta sake yi ta d'ora hannunta a kafad'arshi tace "Sheikh ni ce shaid'aniyar kuma?"


D'an zabura yayi dan wallahi sai yaji kamar mafarki ne yake, tar ya sauke idonshi a kan ta yana mata wani kallo kamar wacce ta gaura masa mari yace "Ryam yau kuma wane fitsararren ne a jikinki haka? Na ga kayan bacci kala kala a jikinki har da wad'anda kamar babu, amma wannan fa? Baturen wace k'asar ce?"Bushewa tayi da dariya kamar zararra sai kuma ta had'e rai tana kallonshi tace "Abdul, ni ce mai iskokai a kai? Haka kake nufi ko? Nagode."


Sake d'ora hannunta tayi a kafad'arshi cikin rad'a tace "Abdul ka manta ne, yau muka shekara cif da aure, shiyasa na maka wannan shigar, kuma kai na ji ka fad'a a wa'azinka cewa babu laifi mace ta wa mijinta gayu na d'aukar bakin duniya indai daga ita saΓ― shi ne, to shi ne nawa sai ya zama abun fad'a har an tofe ni da a'uziyya."


Kallon k'wayar idonta yayi shi ma yace "Da gaske? Yau ne aka d'aura aurenmu."


D'aukarta yayi cak ya shiga lalubar k'irjinta yana fad'in "Lallai yau zan baki mamaki, wannan gayu ai sai na biya ma zuwa safiyar gobe, amma kafin goben mu fara ban ruwa wa gonarmu ko yan matan tsohonta."


Cire hular kan ta tayi ta jefar haka ma alewar bakinta tana fad'in "Hakane tsohon yan matanshi."


Fad'awa sukayi kan gadon inda suka shiga tallafawa junansu cike da so da k'auna da kuma...🀣
_Allah nagode maka daka nuna min ranar nan, yau gani a k'arshen *matar mutum*, Allah ka bani ladar fad'akarwa kasa a anfana da hakan, kuskuren da nayi Allah ka yafe min tare da makaranta na._


*Kamar yanda na fad'a muku ina son yin dogon hutu insha'Allah a k'alla na tsawon watanni, a wannan lokacin zan samu damar nazari da bincike akan labarin da nake son tab'owa insha'Allah wanda ni ce zan k'irk'iri k'asata da kuma sunayen mutane na dan kaucewa cin zarafin kowa, watak'ila kafin nan mu had'u daku a labaren dake riskata na gaskiya, akwai yiyuwar hakan akwai kuma yiyuwar barin hakan, fatana dai Allah ya sake sadamu da alkirinsa.*

*Alhamdulillah*

Post a Comment for "MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 15 KARSHE Na Samira Harouna"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...