MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 14 Na Samira Harouna - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 14  Na Samira Harouna

MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 14 Na Samira Harouna

- - Post a Comment

 MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 14

Na Samira Harouna
πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *53*
Sak'o ta tura masa gahere kamar haka _"Me za'a dafa?"_


Sanda sak'on ya riskeshi dubawa yayi da kyau dan baya tunanin ta tambayeshi, a gajarce shi ma ya maida mata da _"Idan zan samu had'in salade ma ya wadatar."_


A gajarce ta sake maidawa da _"An gama."_


Shi ma a gajarce ya maido da _"Nagode."_


Fitowa tayi ta samu Iya zaune a cikin rumfar da take girki, zaune tayi Iya ta kalleta sama da k'asa ta girgiza kai tace "Mimi Allah ya shiryaki, kuma tun jiya ciwon bai sake dawowa ba."


Dariya tayi irin ta 'yan zamani tace "Haba Iya share zancen nan, kin san wani abu ma?"


Tab'e baki tayi tace "SaΓ― kin fad'a."


Cikin nutsuwa tace "Kinga sheikh ne yace na had'a masa salade, kinga kuma yanzu ba yara ke akwai ba da zan aika, shi ne na ce na aikeki mana."


Dak'uwa Iya ta mata tace "Uwarki! Wato ni da aurena ba aure bane ko?"


Dariya Mimi tayi tace "Ba haka bane Iya, to idan kinyi niyya ki barni na je da kaina mana na siyo."


Wata dak'uwar ta kuma yi mata tace "Uwaki, an k'i a barkin."


Turo baki tayi ta tura k'afafunta kamar zata hamb'are Iya tace "To ni wanga tsohuwar na rasa gane miki, yanzu kuma so kike na sab'a umarnin mijin na wa ko me? Na ce ki je kin ce a'a, na ce zan tafi kin ce a'a."


Cikin fad'a Iya tace "Tashi d'auko kud'in ni zan je na siyo miki, amma ba zan bari ki fita ba kinji na fad'a miki."


Galala ta kalleta tace "Taya zan baki siyayyar nan mai yawa haka? Wallahi na san ba zaki iya fad'in sunan kokombre ba bare kuma su karas da mayonnaise."


Jim Iya tayi tana kallonta sai kuma tace "Ai shegun abubuwan nan naku ne na yan zamani da wuyar fad'a."


Dariya tayi tace "Yawwa to na je ko?"


A hankali ta kalleta tace "Gaskiya Mimi ina tsoron fitarki, ba wai dan ban yarda dake ba saidai kinga yanzu kamar amana ce ke a wurina, in wani abu ya faru ni za'a ce da sanina."


Marairaicewa tayi tace "Iya na miki alk'awarin babu abinda zai faru, kuma ba zan jima ba zan dawo tunda kinga ba k'asa zan tafi ba."


Sallama suka ji a farfajiyar gidan suka amsa yaron ya shigo, cikin girmamawa ya kalli Iya yace "Ina kwana Iya?"


Da kulawa ta amsa da "Lafiya lau Sadam."


Mik'o mata k'ullin goro yayi yace "Gashi wai in ji mamanmu ta ce goron Nuseiba ne aka raba."


Da fara'a ta karb'a tace "A'a masha'Allah, har an raba kenan?"


"E." Ya fad'a yana juyawa zai fita, da sauri tace "Sadam zo nan d'an albarka."


Dawowa yayi yana kallonta ita ma ta kalli Mimi tace "D'auko kud'in ki bashi ya siyo miki."


Cikin kumburo baki ta mik'e ta nufi d'akin ta d'auko kud'in, kawo tayi ta zauna ta lissafa mishi komai sannan ta ce ya shiga taxi zuwa kasuwa, cike da dattako yaron yace "A'a ki bar kud'in taxin, akan moton yaya Bello na ke."


Da jin dad'in dattakon daya mata tace "To nagode sosai Sadam, ka kula da titi kaji."


Fita yayi ita kuma ta d'auki wayarta ta kira Jamila dake kusa da gidan Iya, tana d'agawa daga b'angarenta ta fara fad'in "Shegiya Mimi amarya, sai yau kika tuna damu?"


Tsaki Mimi tayi cike da jin sarauta akan ta ta yatsina baki tace "Ke bana son iskanci, wai ku baku san inda mutum yake bane?"


Cikin dariyar mugunta Jamila tace "Ke tafi can marar mutumci, waye zai je gidanki kina kwasar amarci ke da sugar Dady d'inki."


Wani irin b'acin rai ne ta ji ya taso mata da bata tab'a jin shi ba, haka kawai ta ji ta bata masifaffen haushi, da k'unar zuci ta katseta da fad'in "E d'in, sai me? Na ci amarcin da shi da matsala ne?"


Tsagaitawa tayi da dariyarta tace "Ke ni ba masifa nake ji ba yau, fad'a min me ke labari? Zaki zo ranar k'umshina ne?"


Cikin dak'ilewa tace "K'umshin me?"


Da mamaki tace "Baki san ni zanyi k'umshin Salma ba na farko?"


Ba tare da wani kulawa ba tace "Ko? Ya akayi ta baki k'umshinta kamar ta rasa dangi?"


Cikin jin haushi Jamila tace "Ban gane ba Mimi? Wannan ai wulak'anci ne ma, yau a makaranta mun d'auka zaki zo ai shiru."


Cike da iskanci tace "Ke ni fa ba lafiya ma gareni ba, laulayi nake, ciki ne da ni."


Cike da zumud'i Jamila tace "Da gaske? Kai amma na ji dad'i, ashe dai shehinmu da saurenshi, da wuri haka?"


Wani lalataccen murmushi Mimi tayi a ranta tace "Can da yawonki, wai ciki, mtsss?"


A fili kuma d'orawa tayi da "Ke farantai nake so manya masu, idan akwai ki aiko a kawo min ina nan gidan Iya."


Da sauri tace "Da gaske? Yaushe kika zo?"


Tsaki tayi tace "Ban sani ba, idan zaki aiko min to, in kuma babu ki fad'a min."


Dariya Jamila tayi tace "Zan kawo miki da kaina ma, zan zo gidan yanzu dawowata kenan daga makaranta."


Tab'e baki tayi tace "Wato kuna zuwa kuyi shik'a ou dawo ko? Ai kunsan yanzu ba'a fara komai ba."


Dariya Jamila tayi tace "Ai ki bari kawai, in fad'a miki PC (Physique Chimie) ma wallahi saida ya tambayeki, Lariya ma tana ganinmu ke ta fara tambaya, ga su Sadiq da su Omar, ke kowa fa bakinshi a Mimi."


Wata shak'iyiyar dariya tayi kafin tace "Allah sarki Mimi mai masoya dayawa."


Cike da izgili Jamila tace "Kamar aljanna ba."


D'auke wayar tayi a kunne tace "Sai kin zo." K'it ta kashe kiran tana dariyar saboda tuna rayuwarta ta makaranta, a gaskiya zata sake lallab'ashi dan ta koma makaranta, tana son rayuwar nan sosai saboda rayuwa ce mai cike da 'yanci da nishad'i.
     *Bayan kwana biyu*
Dke yammacin alhamis ne aiki take tuburan wajen had'awa sheikh abun bud'a bakin da ita ta saka kan ta ba tare da saninshi ba, 04:30 ta gama da komai ta saka a basket d'in da Jamila ta kawo mata ta ajiye jug d'in lemu gefe ta shiga wanka, wanka ta tsala ta fito ta shirya cikin doguwar rigar leshe wacce ta mata masifar kyau, kwalliya tayi sassauk'an mai ban mammaki ta kashe d'aurin d'an kwali, turare ta shafe jikinta da shi kafin ta d'auki mayafinta mai d'an girma ta rufe duka jikinta da shi ta saka saka da takalmi ta fito.


Kallo Iya ta k'are mata cike da jimami tace "Mimi kina ganin shirin nan baiyi yawa ba kuwa?"


Kallon kanta tayi tace "Iya wane yawa kuma? So kike na je a hargitse ne to ina wari."


Jinjina kai tayi tace "Ba haka nake nufi ba, Allah ya kiyaye hanya."


Dariya tayi tace "Yawwa Iya ta, sai na dawo."


Cikin zolaya tace "Kuma ki tabbatar kin karb'o min na wa abun bud'a bakin a wurinshi."


"To." Ta fad'a tana kallon Jamila dake shirin d'aukar basket d'in kwanukan da sauri tace "To uban wa zai d'aukar miki jug d'in?"


Hararanta Jamila tayi tace "Ban sani ba, ke uban me zaki d'auka bayan jakarki?"


Juyawa tayi ta kalli Iya tace "Iya dan Allah ba gabanki likita aka ce na daina d'aukar abu mai nauyi ba?"


Da mamaki Iya tace "Yaushe? Akan wane dalili kuma?"


Dariya Jamila tayi tace "Iya rabu da ita raina min hankali ne zaatayi."


Matsowa tayi daf da ita tace "Nima dai na kusa auren nan na samu ciki."


Hararanta tayi tace "Kafin kiyi dai ai har cikina yayi k'wari."


Iya dai na jinsu har suka fita suna wannan cacar bakin bayan Mimi ta karb'i basket d'in ta bΓ’ wa Jamila jug d'in lemu, suna fita kam basu sha wahalar samun taxi ba suka d'auki hanya, wayarta ta ciro a jakarta ta dannawa lambarshi kira.


Yana tsakiyar masallacin dake ma'aikatarsu duk yan ma'aikatar sun zagayeshi suna d'aukar darasin daya zamar musu saurare dole, ba komai kullum yake fad'a musu ba sai rik'o da amana da kuma yin aikin domin Allah, sannan nuna musu mahimmancin aikinsu da tuna musu al'umma suke ma. Wayarshi na fara vibration ya laluba aljihu ya cirota dan ya kashe kiran, sai dai? Wacce take kira tafi k'arfin ya katse kiranta, hasalima mamakin ganin kiran na ta ya shiga yi sanda sunan daya saka mata a lambar ya bayyana da *yan matana*.


Kamar wani marar gaskiya ya saci kallon mutanen dake gabanshi sannan ya d'aga wayar ya d'ora a kunne, cikin rad'a yace "Salam, ina darasi ne, zan sake kiranki."


Da sauri jin zai kashe wayar tace "Abdul."


Sam ba da son ranshi ba ya dakata saboda sunan Abdul data kira, cikin shagwab'abb'iya kuma siririyar muryarta tace "Gani nan fa tafe wajenka, zamu had'u a gidan nan ne ko kuma na zo ma'aikatar?"


Zabura yayi yana nufin tashi tsaye sai kuma ya kalli mutanen gabanshi ya dakata, ture hularshi yayi ta gaba ta koma baya yana tsatsare mutanen da ido da suma dayawa shi suke kallo, gyara zamanshi ya sake yi da kyau ya rufe bakinshi da tafin hannu cikin rad'a yace "Ryam ban gane gaki nan tafe ba? Munyi dake zaki fita ne?"


Cike da shagwab'a tace "To ba kai ne ka fad'a min kana azumi ba, shiyasa na maka abun bud'a baki, ni kawai ka fad'a min inda zan zo na sameka kaga fa ina cikin taxi ne."


A hankali ya lumshe ido ya furta "Hasbunallahu wani'imal wakil."


Bud'ewa yayi fes a kan mutanen dake gabanshi yana jin kamar ya fashe da kuka, ba wai fitowar babu izininshi bane matsalar, tunanin yanda ta fito daga gidan shi ne yake masa yawo a kai, shin ta rufe jikinta da hijab ne? Ta saka nik'ab da safar k'afa? Ko kuma dai yanda ya santa a haka ta fito kowa da komai ya gama kalle masa halalinsa?


Zunbur ya mik'e tsaye yana fad'in "Ku gafarceni, kira ne na gaggawa."


Da sauri ya juya inda jami'anshi suka rufa masa baya da sauri su ma, suna shiga mota yace "Gaggauta dan Allah, Tallague zamu je."


Yana maganar ne yana kiranta a waya, tana d'auka hankali tashe kamar wanda aka shaidawa iyalinsa na d'akin nak'uda yace "Ryam kina ina yanzu?"


Cike da rashin damuwa a tare da ita tace "Yanzu muka baro gida."


Da sauri yace "Hakan na nufin bakuyi nisa da gida ba?"


"E." Ta fad'a kan ta tsaye, wata ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfi yace "Ryam ku dakata, ku dakata dan Allah gani nan tafe sai mu tafi tare."


Kallon Jamila tayi dake gefenta tace "Amma fa ba ni kad'ai bace, tare da k'awata muke."


A sanyaye yace "E, har da ita d'in."


D'aga kafad'a tayi alamar shikenan sannan tace "Ok."


Yanke kiran yayi ya mayar da wayar aljihu, maida kan shi yayi ga kallon gabanshi sai sukayi ido hud'u da dreba dake tuk'i fuskarshi d'auke da mamaki, matse bakinshi yayi ya feso wani sanyayyen iska yana tsare dreban da ido yace "Yarinya ce, wahala take bani, amma dai nasan na d'an lokaci da ta k'ara girma zata bari."


Murmushi dreban yayi yace "Hakane." Ci gaba yayi da aikinshi sai sheikh daya sake fad'in "Kana ga na ci gaba da lallab'ata a haka? Wani lokacin kamar mahaukaci nake zama wallahi, ban san ya zanyi ba."


Satar kallonshi dreban ya sake yi a ran shi yana fad'in "Allah ya sauk'ak'a maka sheikh, abun ya ta'azzara kam."


*Bakin* titi aka aje su suka gyara tsayuwarsu dan jiran tsammani, duk da suna cikin unguwar ne amma sun d'an yi nisa, suna tsaye sun aje kayan hannunsu a k'asa motar ta tsaya a gabansu.


Mugun bugawar da k'irjinta yayi yasa ta dafe k'irjin dan tsaf ta san motar waye, bata gama tsurewa ba saida Muttak'a ya fito a gadarance har ya tsaya gabanta k'ik'am yana k'are mata kallo daga sama har k'asa.


Bata tab'a jin haka ba sai gashi tana kallonshi a mugun tsorace bakinta bud'e tana had'a yawu da sauri sauri, hannu ta d'ora a kan cinyarta tana ta cumimiye rigarta, wani sakaran murmushi ya saki yace "Mimi kenan, ashe kina nan?"


Ba tare data d'auke idonta a kan shi ba ko ta rusuna su ta ci gaba da kallonshi, wani mayen kallo ya mata yace "Mimi na fad'a miki idan ban sameki ba babu wanda zai sameki, na yarda wannan karan an fi k'arfina, Sheikh ko aljanun kaina suna kunyarshi bare kuma ni kaina."


Daf da ita ya sake matsowa yana kallon fuskarta yace "Kinyi kyau fa, amma ki sani baki dace da zama matar tsoho ba, babu abinda zai iya yi miki."


Baya ya ja ya bud'e murfin motarshi yace "Ki kula da kanki, hakan ba yana nufin na hak'ura bane."


Shigewa yayi ya tashi motar yayi baya baya sai kuma ya tsaya, Mimi da har wata zufa ta keto mata sauke numfashi tayi da k'yar ta kalli Jamila dake kallon Muttak'a da bai gusa a wurin ba, dafata tayi cikin b'arin murya tace "Mu tafi kinji, mu matsa gaba dan Allah."


Sunkuyawa Jamila tayi tana d'aukar kayan tace "Waye shi kuma waccen mahaukacin?"


Yatsina baki tayi tace "Rabu dashi kawai, d'an k'waya ne."


Sun fara takawa kenan ta hangi motar sheikh tsaye ga dukkan alama kuma tsaye suke a nan watak'ila sun jima, takawa ta shiga yi a hankali sai Jamila data tsaya tana kallonta dan ta tabbatar su d'in ne, Muttak'a na ganin haka shi sam bai ga motar su sheikh ba sai ya sake murd'awa motar giya ya taka da k'arfi ya nufi Mimi gadan gadan wanda hakan yasa Jamila kaucewa da sauri har tana sakin jug d'in hannunta.


Sheikh da ke hangen komai a cikin mota zufa ta jik'eshi sharkaf sakamakon ganin Muttak'a na wani shigewa jikin matarshi kamar zai tab'ata, ga mugun wankan da ya ga ta d'auka, yanzu kuma da yake ganin motar da wani matsiyacin gudu tana nufi kan Mimi yasa shi bud'e motar da sababin sauri ya fito takalminshi d'aya irin babush d'in nan k'irar Rusia mai sunan MisTsar ya baroshi a motar sai d'aya a k'afarshi ya tako da mugun sauri har da gudu gudu ya fizgi hannunta hakan yasa shi ya tsaya ta inda motar ke tahowa ita kuma ta koma baya.


Kallon juna sukayi saidai kafin wani cikinsu yayi wani yunk'uri Muttak'a ya taka birki da iya k'arfinshi saboda gaba d'aya ya razana saboda ganin sheikh, duk da haka saida motar ta daki gwiwan sheikh daya bada baya yana kallon fuskar Mimi. Sanda motar ta dakeshi lumshe ido yayi amma sam bai motsa ba, da sauri yayi baya-baya ya ja motar ya d'auki titi da gudu ya bar wurin a tunaninshi sheikh bai ganshi ba.


Numfashi ta shiga saukewa gaba d'aya fuskarta ta nuna yanayin tsoro, ba tare daya saki hannunta ba ya juyar da ita ya shiga takawa da ita da k'arfi suka nufi mota, saida ya fara takawa yana jin lallausan k'afarshi na taka tsakuwa ya fahimci babu takalme a k'afarshi, turata yayi cikin mota ta shiga sannan shi ma ya shiga ya zauna, tayar da motar sukayi suka bar Jamila nan tsaye ta rasa me zatayi? Ina zata nufa? Ya zatayi da d'an sauran abinda ya rage musu? Tunda jug d'in ya fashe kasancewarshi na kwalba sanda ta sakeshi abun ciki ya zube.


Gidan daya kaita ranar suka je kai tsaye ya bud'e da makulli suka shiga, a falon ya zauna kan shi a k'asa hannayenshi a jimk'e, ita ma jiki a sanyaye ta zauna kan kujera tana kallonshi, shiru d'akin babu wanda yace wani abu a k'alla minti talatin, gajiya tayi da zaman shirun kawai ta muskuta tana ci gaba da kallonshi tace "Abd..."


Jajayen idonshi da jar fuskarshi da k'arara ta nuna b'acin rai ya d'ago ya kalleta kafin ta k'arasa, da sauri ya mik'e kamar an mintseneshi ya cire hularshi ya aje kan kujerar, tattara babbar rigarshi yayi ta malamai ya aje gefe ya nufo kan ta, yana tsayawa gabanta ya rik'o hannunta tayi tsaye ba tare data shirya ba, hab'arta ya tallabo ya zuba idonshi cikin na ta cikin muryar b'acin rai yace "Waye shi?"


Muryarta na rawa tace "Tsohon...saurayi..."


Bata gama fad'a ba ya saki hab'arta yace "Shi ne kuka had'u dan ku gaisa?"


Da mamaki ta kalleshi tace "Kamar ya? Kasan me kake fad'a kuwa? Kai fa ka tsayar damu a hanya ka ce kana zuwa."


A mugun tsawace yace "Amma na ce ki kula wani d'an iska ne? Ba ma wannan ba ni na fad'a miki ina buk'atar abun bud'a baki ne? Da izini na kika fito daga gida? Me kika d'aukeni ne Ryam? Nema kike ki mayar dani wani sakarai mahaukaci, akan wane dalili?"


Yanda ya rufe ido yake mata masifa a cewarta yasa ta yin zaune kan kujerar tana had'e hannayenta, da mamaki ya kalleta sai kuma ya d'auke kallabin kan ta hakan ya bayyanar da yalwataccen gashinta yana fad'in "Wannan shirin fa? Wai ke baki da hankali ne?"


Da sauri ta kalleshi idonta taf da hawaye ta mik'e tsaye, cikin zubo da hawayen idonta tace "Ni ce ma marar hankalin? Saboda ina ganin nayi abinda zan birgeka."


Juyawa tayi kan kujerar ta d'auki jakarta da kallabinta ta juya a fusace zata fita ita a la dole ita ce yanzu aka b'atawa rai, rik'e k'ugu yayi shi ma yana kallonta har ta fita yana jin shi ma fa shi aka b'atawa dole ma a bashi hak'uri.


Tana fita taxi ta shiga aka nufi gida da ita shi kuma zaune yayi a falon ran shi a b'ace kamar zai ciji wani, banda tsaki da dukan iska babu abinda yake yi yana ta tunanin lamarin yrinyar nan, ya yarda akwai k'uruciya saidai a lamarin Mimi har da wauta da hauka ma._(Dan Allah ku fahimce ni, ba labari ne da nake rubutawa dan daidai da son ran kowa ba, abunda nake da tabbacin zai iya faruwa ga duk wanda hakan ya faru dashi nake rubutawa, ma'ana zahirinmu ba wai abinda ba zai yiwu ba, idan mukayi duba da shekarun Mimi da bud'ewar idonta, da kuma shekarun Sheikh dole hakan ya b'ata masa rai, sannan ita ma dole ta ji kamar tsuntsuwa ce da ake neman cirewa pika-pikinta dan hanata tashi sama.)_
*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *54*

*Kwana biyu* kenan da faruwar abun nan amma babu wanda ya kula wani ko a waya, Sheikh ya zuba ido ne ya ga tana da wayon da zata tuntub'eshi har tayi k'ok'arin bashi hak'uri, amma shiru kake ji kamar malam ya ci shirwa yasha ruwa, hakan ya d'ugunzuma hankalinshi wajen tashi sosai, dan shi fa ba haka Hafsat ta koya mishi ba, ba haka ta raineshi ba, shiyasa rainon na Mimi yanzu yake neman dagula masa lissafi gaba d'aya.


Gashi a daren ranar kuma shi da uku daga cikin wasu malamai suka tafi k'asar Abuja dan gabatar da wani babban taro na malaman k'ungiyar ahlul-sunna wal-jama'a, duk da yana wurin amma kuma hankalinshi yana kan wayarshi yana saka ran ganin ko da flashing d'inta ne, gashi muguwar kewarta na damunshi, har yau idan ya tuna darensu na farko da sauren dareren da yake wasa da ita sai ya ji yana buk'atarta a kusa da shi, wasu lokutan yana d'aukar wayar dan ya kirata amma kuma saiya dakata da niyyar ya d'an hukuntata ta gane ta mishi ba daidai ba.                   *Mimi*Sabo aka ce tirken wawa, rashin ganin kiranshi a wayarta, rashin jin muryarta uwa uba a kwana biyun nan da ta zama mai masifar son jin k'amshin turarenshi had'e da son taji tattausan hannayenshi a na ta hannayen, sai suka taru suka mata yawa kamar zatayi hauka, tsabar d'orawa kai damuwa daren jiya mafarki tayi da ita dai ba zata kirashi da mummuna ba tunda da mijinta ne ta ga suna wata kalar azababbiyar soyayyar data saka ta tashi a wani mugun kasalance jikinta yayi mugun nauyi ga kuma fitowar ruwan da suka sa dole wanka ya kamata.


*Kwana* na uku kenan yau ta tashi da wannan muguwar kasalar, haka ta zauna tana kallon Iya na kad'a miya zatayi d'umame, yar yaloluwar rigar jikinta mai k'ananan hannuwa duk sai ta ji ta mata nauyi, tagumi ta buga tana ci gaba da kallon Iya tana jujjuya wayarta.


Kallonta Iya tayi tace "Tunda kin tashi me zaki ci na samu yaro ya siyo miki? Nasan dai bΓ’ mtuwo kike ci ba ai."


Ba tare data d'auke tagumin ba a kasalance tace "Ki barshi kawai Iya, idan na tashi ci zan nema."


Da kulawa ta sake kallonta tace "Kunyi waya da mijinki kuwa? Tun shekaran jiya da Hajiar ta zo nan ta ce yayi tafiya."


Cikin turo baki tace "Ina kira ba'a samu, amma zan sake kira."


Daga haka Iya bata sake cewa komai ba ta ci gaba da aikinta, Mimi kuma wayarta take kallo tana d'an kai hannunta kamar zata danna lambarshi kuma sai ta dakata, ajiyar zuciya kawai take saukewa lokaci lokaci tana d'an tuna shawarwarin Rayya wanda ko jiya sun jima suna hira a waya, tunawa da wata shawarar ta saka ta mik'ewa da sauri ta shiga d'aki, kwance ribom d'inta tayi take gashinta ya zuba a kafad'unta, gyara zamanta tayi sosai ta d'an duk'o yanda gwiwan hannayenta ke kan cinyoyinta, hakan kuma yasa rigar matsewa sosai nonuwanta suka d'an turo gaba.


Saita wayarta tayi ta d'auki kan ta selfie tare da shiga lambar sheikh, turawa tayi bayan ta tabbatar ta kyab'e fuskarta irin zatayi kuka sannan ta rubuta daga k'asa _"Na fad'a maka baka so na, dubi yanda na rame saboda kewarka?"_


*Abuja*, a babban d'akin taro suke kowanensu da babbar riga da ruwa da lemu a gaban teburen suna ta ci gaba da tattaunawa musamman a game da harkar sabon tsarin kula da marayu, wayar dake kan teburi ne tayi zuuuuu! Alamar shigowar sak'o kasancewar idan yayi nesa da gida yana barin connexion a bud'e, ganin sunan wacce ya kwana uku yana marari da d'okin son ganin sunanta ya fito ne yasa shi d'an jan Γ©cran d'in sama ya bud'e tsaron wayar, ko da ya shiga lambar da sauri ya d'aga kai dan ya tabbatar babu mai kallonshi.


Gyara zama yayi a kujerar ya tallabe hab'a yana k'arewa k'irjinta kallo da ya ga ya mishi wani kyau yayi mulmul da shi, wani k'asaitaccen murmushi ya saki yana girgiza kai ya furta "Ryam."


D'aga kan shi yayi ya mik'e daga kujerar yana kallon shugaban ahlul-sunna ya d'an mishi alama da kai da hannu, da ido shi ma ya amsa mishi dan ya fahimci zai yi waya ne mai mahimmanci.


Yana fita ya kirata hoto mai motsi (vidΓ©o call, appel vidΓ©o). Tunawa da maganar Rayya cewa _"Ke macece kuma kin riga da kin shiga gidanshi, wani sauran aji ya rage miki da zaki ja a gidan miji? Akwai lokacin da kina jan shi ma tsinkewa zai yi dan an riga da an gama da ke, ladabi da biyayya da kuma hak'uri sune zasu zama miki jigo a rayuwar zaman aurenki, akwai lokacin da zaki ja ajinki amma kuma akwai lokacin da dole ki sauke girman kai dan ke ce a k'asa da ke, musamman ma ke Mimi da kike auren shahararren mutum wanda a iya majigi kawai 'yan mata da zawarawa ke kallon fuskarshi suna jin ina ma zai zama na su, ki iya takunki Ryam ta yanda zaki san lokacin da zaki gasawa mijinki aya a hannu da kuma lokacin da zaki fi k'ank'ara sanyi a gareshi. Kamar yanda kike da abokiyar zama zai fi kyau duk tsanani sirrinki tsakaninki da mijinki ya dinga tsayawa iya falonki ko na sa, karki bari ko da wasa ta san bakwa shiri bare har ta kaiki ga daka yajin barkono, na haneki da haka Mimi ba dan na isa ba saidan jin dad'in zaman aurenki."_


Tuna wannan kalamai yasa Mimi d'aga kiran tana sake narkewa tana wani karairaiyewa, fahimtar yau bebyn rigima take ji kuma ta gama faranta masa rai da tayi abinda bai d'auka zatayi ba sai kawai ya shagwab'e shi ma kamar yaro yace _"Ni fushi nake yi ma, shi ne sai yanzu za'a tuna da ni?"_


Kamar wata jaririya haka tayi da fuskarta cikin murya mai d'auke da shauk'i da son yin kuka tace _"Ni ce ma na manta da kai? Abdul kai ne fa baka so na, me yasa kayi hushi dani?"_


Gyara tsayuwarshi yayi ya girgiza mata kai yace _"Ryam ina sonki, na fad'a miki haka har na kusa gajiya, ki yarda ina sonki mana."_


K'wallan da take rik'ewa ne suka taho tace _"Yaushe zaka dawo? Ina so na gan ka Abdul."_


Lumshe ido yayi ya k'urawa k'irjinta ido yace _"Ry..ammm!"_


A hankali ta amsa da _"Na'am."_


Bud'e idonshi yayi fes cikin na ta yace _"Ki rufe abubuwan nan...indai ba so kike...na miki."_


Zuba mishi ido tayi tace _"Me zaka min?"_


Cikin murmushi yace _"Na miki ciki mana."_


Rufe fuska tayi da tafin hannu cike da kunya, cikin murmushi yace _"Bud'e fuskar mana, ai babu kunya a tsakaninmu, ko kin manta ke d'in matata ce sirrina."_


D'an bud'e fuskar tayi amma ba duka ba ta kalleshi tace _"Ni dai ka fad'a min yaushe zaka dawo?"_


Sauke numfashi yayi yace _"Ryam yanzu haka muna zaman k'arshe, insha'Allah yau komai dare zan koma gida, dan na bar aikin al'umma a can hutu ne na nema."_


Da saurinta tace _"Tom, sai ka zo."_ Kashe kiran tayi irin kunya take ji fa, wata dariya ya saki yana girgiza kai yace "Watak'ila fa shirin tarbata zatayi."


Juyawa yayi zai koma d'akin taron yana fad'in "Ashe dai tana d'an hankali wani zubin."


K'arasa shiga yayi yana ta dariyarshi shi bai ma san yanayi ba, haka ya zauna da wannan yanayin har suka gama taron nan misalin 12:30 na rana, daga nan ma tare da sakataran (secrΓ©taire) k'ungiyar suka halarci wani wa'azi, haka dai suka kasance har sanda dare yayi suka rakashi filin jirgi suka d'aga.*Tuni* Mimi bacci ya jima da d'aukarta a gadon Iya dan ba wani abun take yi ba, Iya ma dai har ta kwanta bacci ya fara d'aukarta taju gadon na zuuuu! Bud'e ido tayi ta daddab'a Mimi tana fad'in "Ke tashi, hala shegiyar wayar nan ce ta ki mai kukan raguna."


Da k'yar ta bud'a ido ta lalubo wayar tana fad'in "Wai ke Iya a dare ma masifa kike?"


K'ulli ta shirga mata a baya tana fad'in "Zan ci uabnki yanzu."


Mimi kam ganin lambar sheikh ce nutsuwa tayi ba tare da sanin tayi ba ma ta d'ora a kunne, shiru kamar babu wanda zai yi magana sai kuma yace _"Fatan kina cikin aminci?"_


 Numfashi ta sauke sannan tace _"Um! Ba kayi bacci ba?"_


Murmushi yayi mai sauti kafin yace _"Um! Gani a k'ofar gidansu Iya na zo d'aukarki."_


Da k'arfi ta zabura tace _"Me?"_


A dak'ile ya sake fad'in _"E, ina jiranki yanzu."_


Da mamaki tace _"Amm..."_


Bai bari ta fad'a yace _"Ryam ina jiranki yanzu ki shirya ki fito, ba buk'atar sai wani ya rakaki, ni da ke ma mun isa."_


K'it! Ya datse kiran alamar ya gama magana kenan, da sauri ta sauka a gadon tana fad'in "Iya tashi, tashi tashi Iya."


Mik'ewa tayi zaune tana fad'in "Lafiya wai? Ke wannan akwai jaraba."


Tsaye tayi ta kalleta tace "Wai shi ne a k'ofar gida ya zo mu koma."


Da sauri ta sauko tana fad'in "Alhamdulillah, ka ga malamai magada Annabawa, haka ai shi ne daidai dama wallahi, maza maza to a tafi a bar min gidana."


Tale baki tayi tace "Eyeee! Wallahi Iyar nan ma dai, ba komai."


Zage doguwar rigarta tayi gaban Iyar ta shiga neman abaya a cikin kayanta, kawar da kai Iya tayi tana fad'in "Kai Allah ya shiryaki, bawan Allahn nan haka yake shan tab'arar nan iri iri a wurinki."


Ba tare data juyo ba tace "To me na yi kuma?"


Tab'e baki Iya tayi tace "Bakiyi komai ba." Murya k'asa k'asa kuma tace "Allah yasa ki je gabansa kina cire kayan ya tsala miki bulala a baya."


Kad'awa Iya d'uwawu tayi tace "Ba bakin ki ba Iyale."


Tsaki Iya tayi tace "Yar banza kinga yanda kika k'ara zama dumemiya kuwa?"


Saka doguwar rigar tayi ta saka kallabinta ta yane kan ta, turare ta d'auka ta shafe jikinta sannan ta tusa duk kayanta data barbaza ta rufe jakar, d'aukar k'aramar jakarta tayi da wayarta ta kalli Iya tace "To su Iya, a yafi juna kuma dan Allah, ni na koma inda na fito, idan Abba ya zo ki fad'a masa na koma."


Girgiza kai Iya tayi tace "Allah raka taki gona."


Waro ido tayi tace "Yanzu Iya ina ce wa na zo gidanki shan kunu amma kike min irin haka, shikenan zan je gidan Aunty Shafi'a kawai."


K'yaci Iya ta mata tace "Allah ya sawak'e min wahalar zan d'orawa kai na, ai can kuje ku k'arata."


Jan jakar tayi tana fad'in "Iya har da madara fa zan dinga sha a madadin kunu, baki so mu sha tare?"


Hararanta tayi sai kuma tayi murmushi ta girgiza kai irin ba magana kawai, dariya tayi tana k'arasa fita a d'akin tana fad'in "Iya dai baki yasan dad'i, to ki kula min da mai gidana idan ya dawo."


Da kallo ta bita har ta fita sannan tace "Allah ya tsare, Allah ya baku zaman lafiya, Allah k'ara miki farin ciki a rayuwarki."


Tana fitowa ta tsaya turus saboda ganinshi jingijine a jikin motar, cikin tak'on k'asaita ya shiga takowa gabanta, jakarta ya karb'a a hannunta ya jata zuwa bayan motar ya bud'e ya saka, juyowa yayi ya kalleta tana tsaye har yanzu.


Tunani take daga tsayen tare da hango yanda zata kwanta a k'irjinshi, wallahi har ranta take son taji ta shiga jikinshi tayi luf shi kuma ya sake rufeta da hannayenshi dake d'auke da babbar rigarshi, tan so ta lumshe ido ta ja numfashi sosai ta sake k'amk'ameshi. Amma wani abu d'aya shi ne daga ganinshi yanzu da yanda turarenshi ya daki hancinta sai taji tsigar jikinta ta tashi, wata kasala ta ji a take har saida ta lumshe ido saboda sanyayyen fad'uwar gaban da ta ji, haka kawai ta ji har wani abu yana tsikara mata a gabanta tare da jin wani mutsu mutsu kamar ruwa na zubo mata.


Gyara tsayuwarta ta sake yi ta matse k'afafunta wuri d'aya sai kuma ta ji tattausan hannunshi data kwana biyu tana mararin ya tab'a na ta hannun, janta yayi a hankali ya bud'e mata k'ofar ta shiga ta zauna, shiga yayi shi ma ya zauna sai lokacin ta tatbbatar tare suke da dreba ashe. Har suka d'auki titi babu wanda ya ce wani abu, saidai hannunshi dake cikin na ta har yanzu yana ta murzawa yasa gaba d'aya ya kashe mata jikinta, banda zubar abu a k'asanta babu abinda take ji, k'aik'ayi take ji jikinta na d'uka musamman ma k'asan dz kuma nonuwanta, lumshe ido take tana lashe leb'enta da take jin yana bushewa.


Sheikh da a hankali yake satar kallonta shi ma lumshe idon yake yana jin dad'in yanda yake tattausa hannun na ta mai tuwon gaske, saida suka yi nisa a hanya kafin ya d'an sunkuya kusan kunnenta yace "Kinyi kewata ne?"


K'ara rintse ido tayi sai taji kamar zata ce "Wayyo Allah na."


Sunkuyar da kai tayi dan ita kam wannan abu da take ji kuka ma yake neman sakata, murmushi ya saki na jin dad'i tare da kuma rusunawa yace "Ina kewarki."


Rawa bakinta ya d'auka hakan yasa ta d'agowa ta kalleshi da idonta da suka canza kala dan jaraba bakinta na hard'ewa tace "...
_Karku saka ran ganin rubutu gobe dan ina da abubuwa dayawa gaskiya._πŸ₯°


*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *55*

Rawa bakinta ya d'auka hakan yasa ta d'agowa ta kalleshi da idonta da suka canza kala dan jaraba bakinta na hard'ewa tace "Ab..du...l."


Murmushi ya saki yana kallonta bai ce komai ba har suka isa gida, da kanshi ya bud'e mata k'ofar ta fito ya zagaya ya d'auki jakarta, tunkarar shiga falon sukayi yana fad'in "Da fatan ba zaki sake yi min yaji ba ko?"


Cike da kunya ta sunkuyar da kai sai kuma ta kalleshi tace "Indai Aisha ba zata daina min rashin kunya ba gaskiya..."


Kallonta yayi yace "Da matsala kenan? To indai Aisha ce kwantar da hankalinki, tana d'akin mijinta ita ma."


Da sauri ta kalleshi tana zaro ido tace "Aishar? Har..."


Sai kuma tayi shiru, jinjina kai yayi yana tura k'ofar falon a sanyaye yace "E, kwananta biyu d'akin mijinta."


Cak ta tsaya tana kallonshi da yanayin rashin jin dad'i tace "Amma kuma baka fad'a min ba, ban sani ba wallahi da na..."


Ajiyar zuciya ta sauke da rashin jin dad'i, murmushi yayi yana kallonta yace "Ba biki akayi ba, nasan kuma fushinki ba zai wuce ki ce baki zo biki ba, aure kawai aka d'aura a masallaci, ni ma bana nan akayi d'aurin auren."


Sallama yayi a falon a tausashe yana shiga gaba d'ayanshi, gaba d'aya k'ofar suka zubawa ido suna amsa sallamar da fara'a a fuskarsu, duk mik'ewa sukayi da sauri sukayi kan shi, Munzeer ya fara d'auka kafin Aswan ya rumgume shi haka ma Heezam, Hafsat ma a hankali ta k'araso tana kallon Mimi dake bayanshi tana amsa gaisuwar su Heezam da fara'a.


Tafukan hannayenta ta saka ta rufe fuskarta cike da raha tace "Har na ji kunya k'anwata, na ji kunyar ganinki ba tare da ni na je na taho dake ba."


Sai kuma ta bud'e fuskarta ta matsa kusan Mimi suna kallon juna tace "Amma kiyi hak'uri dan Allah, wallahi sabgar auren Aisha ne ta d'auke min hankali na."


Cike da dauriya da jin kunya ita ma ta d'an turo baki tace "Ni ai hushi nake daku aunty."


D'an waro ido tayi tace "Lahhhh! Me mukayi kuma? Ko da yake nasan muna da laifi, amma ki gafarcemu."


Takwaf takwaf tayi da fuskarta tace "Aunty auren Aisha fa akayi ban sani ba."


Sai kuma ta sunkuyar da kanta tace "Ko da yake laifi na ne, inda ina nan da anyi komai da ni ai."


Da farin ciki Hafsat ta rumgumeta a jikinta tana fad'in "Kiyi hak'uri Mimi, ranar ma sharrin shaid'an ne abinda ya faru, insha'Allah ba zai sake faruwa ba."


Cikin d'ari d'ari ita ma ta d'an shafa bayanta tace "Ni ma ki yafe min aunty wallahi nayi nadama."


"Ba komai." Ta fad'a tana d'agowa daga jikinta, Sheikh dake kallonsu cike da jin dad'i ne yace "Wato ni an wareni ko? Ko ganina ma ba'a yi."


Wani farrrr Hafsat ta masa da ido tace "To ina ta yar uwata ina zan dubeka sheikh."


Jinjina kai yayi yace "Uhum! Ni kuma da ba d'an uwanki ba ko?"


Murmushi tayi tace "Ranka shi dad'e barka da zuwa, an zo lafiya?"


Da murmushi shi ma yace "Lafiya lau Sawwama, ya gida da yara? Na bar miki ragamar komai a hannunki ko? Allah ya miki albarka ya ci gaba da baki ikon kula da gidan nan ko bayan raina."


Wani dammm! Mimi ta ji tayi saurin kallonshi, murmushi Hafsat tayi tace "Ameen ya Allah."


Murmushi ya mata ya kalli Mimi yace "Ki wuce ciki."


Jinjina kai tayi ta ja jakarta ta nufi na ta falon, d'an kallonta Hafsat tayi sai kuma ta dawo da kallonta kan Sheikh dake fad'in "Hajia muje a had'a min ruwan wanka ko."


Kallon yaran yayi yace "Zan shiga na fito sai mΓ» zauna da ku muyi hira."


Da ladabi Heezam yace "A fito lafiya Abie."


Saida suka nufi hanyar d'akinta cikin rad'a Hafsat tace "Yallab'ai, ina ga me zai hana ka je wajen k'anwata, kaga yau ta dawo ya dace ka zauna da ita."


Da mamaki ya kalleta yace "Ban gane ba? Kin manta kwananki ne? Ai ita tayi yaji ta bar gidan, hakan ba zai sa dan ta dawo ba na d'auki kwananki na kai mata ba."


Murmushi tayi tace "Ba haka nake nufi ba nima, nufi na na bar mata kwanan na wa, duba da yajin ma ai ni da 'yata ne silarshi."


Girgiza kai yayi yana wucewa da alamar bai fa gamsu ba, rik'o hannunshi tayi a marairaice tace "Dan Allah sheikh, wallahi na bar mata ne har cikin zuciyata."


Harara ya galla mata yace "To na fad'a miki ina da buk'atar wani abu ne a gurin wata? Bacci zanyi na huta gajiya malama, idan kwa'a dani ne ba zaki iya ba sai ki je d'akina."


Wucewa yayi ya barta hakan yasa ta binshi da kallo, girgiza kai tayi ita ma kafin ta bi bayanshi gabanta na fad'uwa tana tunanin ta yanda zata fara fad'a mishi bata sallah yanzu, a k'aida dama tana ganin jini take fad'a masa ko da baya gidan, wannan kuma an yi katarin baya gari kuma yau data kira dan ta fad'a masa sai layin ya k'i shiga har sai yanzu da ya zo, da a ce bata riga ta masa tayin kwana d'akin Mimin ba, yanzu idan ta fad'a masa sai ya ce dan tana so a dole y'a kwana a can ne.


Cikin kissa da salo take tayashi cire kayan tana ta langab'ewa tana son fara d'aukar hankalinshi zuwa kan ta kafin ta fad'a masa, tsura mata ido yayi yana kallo sai kuma ya saki murmushi yace "Menene?"


Cikin shagwab'a kamar wata yarinya tace "To ni ai..ai jiya ne..."


Sai kuma ta turo baki ta k'i cewa komai, ba tare daya daina kallonta ba yace "Ke ai me? Ina jinki."


K'asa tayi da kanta sannan tace "Ai bak'ona ne ya zo jiya, kuma ina ta k'ok'arin fad'a maka amma..."


Tallabo hab'arta yayi yana kallon cikin idonta yace "Manga? Ya kike neman zo min da wata sabuwar tsirfa kuma? Ni d'in ne baki buk'ata yau a shinfid'arki?"


Da sauri ta kalleshi ita ma tace "A'a a'a! Ba haka bane wallahi, da gaske nake fad'a maka."


Da zolaya ya bita da wani kallo yace "In gani to."


Zaro ido tayi sai kuma ta ja baya tana dariya tace "Haba dai."


Hararanta yayi yace "Baki da gaskiya kenan?"


Sake marairaicewa tayi tace "Na rantse gaskiya na fad'a maka."


Jawota yayi ta fad'a jikinshi da k'arfi cikin rad'a yace "Ko gaskiya ne ai kin fi kowa sanin hanyar da kike bi kina saukeni idan na hau."


Cikin jin kunya ta sunkuyar da kai tace "Da zaka daure ka je wajen yar uwata da na ji dad'i sheikh, wallahi tausayi take bani yarinyar bata da matsala."


K'arasa cire kayan yayi kawai ya shige ban d'aki ya barta nan, girgiza kai tayi ba tace komai ba sai ma fita dan ta shirya masa wajen cin abinci, bata jima ba ta dawo haka shi ma bai jima ba ya fito, zaune yayi ya ci abincin sosai ya k'oshi kafin ya kalli agogon dake d'akin inda ya nuna masa k'arfe 10:58 na dare, nauyayyen numfashi ya sauke tare da fad'in "Bari na duba k'anwarki na ga ko tayi bacci."


Da sauri ta mik'e tana murmushi tace "To, saida safe."


Da mamaki sosai a fuskarshi yace "Wai da gaske kike?"


Jinjina kai tayi ta matse d'an k'aramin bakinta alamar e, a sanyaye ya jawota jikinshi ya rumgume yana lumshe ido, sumbatar wuyanta yayi tare da saka harshenshi ya d'an lashi wuyan na ta, tsam! Ta sake rik'e bayanshi tana mai sake lumshe idon ta, cikin kasalalliyar murya yace "Allah ya miki albarka Qawwama, zanyi kewarki."


Kamar zatayi kuka tace "Ni ma haka." A hankali ya d'agota daga jikinshi yana kallon fuskarta yace "Allah ya baki ladar abinda kikayi na alkairi."


"Ameen." Ta fad'a tana sauke numfashi, kuncinta ya sake sumbata sannan ya fita a d'akin, saida ya samu su Heezam suka d'an tattauna a tsatsaye kafin suyi sallama kowa ya nufi d'akin baccinshi shi ma ya wuce d'akin Mimi.


Da sallama ya shiga amma shiru babu amsa, saida ya k'arasa shiga cikin d'akin bacci ya fahimci har ta kwanta, saidai bai da tabbacin bacci take ko kuma idonta biyu, dawowa yayi ya kashe wutacen ya koma d'akin, cire doguwar rogarshi yayi ya aje sannan ya haura gadon ya kwanta daf da ita, zanin data dunk'ule cikinshi ya ja ya shiga shi ma yana lek'a fuskarta yace "Ryam."


Cikin magagin baccin daya fara d'ibarta ta amsa da "Uummm!"


A sanyaye yace "Bacci wai?"


D'an muskutawa tayi ta gyara kwanciyarta hakan ya bashi damar jawota gam a jikinshi, shiru tayi ba tace komai ba tana tunanin me ya tsaida shi bai shigo ba har tayi wanka ta shafa mai da turare ta saka rigar bacci ta kwanta, jin hannunshi cikin rigarta yana shafa mararta yasa ta saurin zabura ta kalleshi, shi ma kallonta yayi saboda yanda ta zabura yace "Ya dai? Yunwa kike ji ne?"


Da sauri ta girgiza kai alamar a'a, ci gaba yayi da shafa marar har ya fara haurawa zuwa sama yana shafa k'irjinta cikin lumshe ido yace "Waye shi Ryam? Me yake fad'a miki a ranar?"


Shiru tayi tana jin gaba d'aya hankalinta na neman gushewa ya barta saboda al'amarin da take ji yana ratsata, kasa magana tayi dan har ga Allah idan tana jin yanayin nan sai taji kuka ke son taho mata, cikin kunne ya sake rad'a mata "Uhum! Ina jin ki?"


Zubo da hawayen tayi cikin shashek'a tace "Abdul jaki ne wannan mutumin, ban tab'a jin ko da sha'awar kallon fusskarshi ba na minti d'aya bare har na ji k'aunarshi, na tsaneshi, na tsaneshi saboda baya da hankali."


D'ago hab'arta yayi ya kalli fuskarta a hankali ya had'a bakinshi da na ta ya shiga tsutsa, duk k'ok'arinta na son rik'e kan ta saida ta samu kan ta da matse k'afafunta tana bank'arewa tana kuma shafa kan shi da hannayenta biyu, alamar dai abun na mata dad'i kuma a shirye take data karb'eshi. 


Inda a wajen Sheikh kuma ya ke sake gasgata lallai fa yarinyar na da wadatar lafiya, hakan ya saka mishi tsoron kar fa a zo ita d'in irin hallitar nan ce mai maysananciyar sha'awa, idan hakane kam dole yayi gaggawar canza sabon tsarin tafiyar da gidanshi, dan kam ba zai yarda yayi sanadiyar shiga yarinya halaka ba, haka kuma zai dage wajen k'ra inganta lafiyarshi dan ganin bai cutar da ita ba.


Cikin nutsuwa ya sab'ule mata rigarta ya shiga lailaya k'irjinta, a hankali ya kai hannunshi k'asanta ya soka a cikin pant d'inta, da sauri ya d'ago kan shi ya kalleta a d'an tsorace yace "Ryam, me kika sha? Wani abu kika sha ne?"


Mimi da idonta ke rufe ta cije leb'enta girgiza masa kai kawai tayi, da sauri ya hau ruwan cikinta ya k'arasa yin k'asa da pant d'in ya d'an wara k'afafunta, shi ma sab'ule...😎 ya kalli fuskarta yana mai saita kan shi izuwa duniyarta yana rad'a mata "Inna...kin, kin shirya? In shiga? Kin tabbata ba za..."


Shiru yayi yana sauke tagwayen numfashi tare da fara danna kan shi izuwa matancinta, rintse ido yayi ya cije leb'e yana addu'ar saduwa tare da addu'ar Allah sauk'ak'a mishi shi dai ya shiga hanyar nan ba tare da an ji kan su ba, cikin ikon Allah kam dake wurin a jik'e yake kuma ya tafi a hankali a hankali har ya samu hanya ya wuce.


Yana shiga ta waro idonta tana sakin k'ara da fad'in "Wayyo Allah!!! Washhhhhhh! Abdul zafi."


Lumshe ido tayi hawaye suka gangaro mata a gefen idonta, shi kan shi sauke wani numfashi yayi ya kwantar da kan shi a tsakiyar mamanta, sannu sannu ya ci gaba da gyarawa kansa zama a jikinta saida ya ji komai daidai, a hankali ya fara aikatar da ita cikin nutsuwa da fitar hayyaci da zaucewa, tun yana daurewa yana rufe bakinshi yana fito da sautin gurnaninshi har saida al'amarin yar babyn yafi k'arfin tunaninshi ya fara bud'a muryarshi yana fad'in "Wayyo Allah! Wayyo Ryam, Ryam, wayyo Allah...."


Dad'in da yake jin yana ratsashi ga ambaliyar ruwan da ke sauka mai damk'o da kauri yasa shi dagewa iya iyawarshi yayi ta caccakar yarinyarshi yana yi yana sambatu mai d'auke da muryar kuka da dariya. Mimi kuma na jin azabar ta fara mata yawa ta fara rera kuka tsakaninta da Allah tana fad'in ita fa wallahi ta gaji zai kasheta, wani k'arfi yaji kukan na ta na k'ara masa tare da ji a ran shi ashe shi ma ya cika namijin da ke wahalarwa akan gado, hakan yasa shi sake nuk'urk'usarta yana fad'a mata sannu ya kusa zuwa. Saida tayi laushin da hannu kawai take iya d'aga tana daddab'a damtsenshi tana fad'in "Ya isa, ya isa Abdul na gaji, ka daina hakanan ka ji."


Saida ya kammala k'ark'af kafin ya cire jikinshi a nata a hankali, wata rumguma ya mata kamar za'a rabashi da ita yana manna mata sumbata a baki da hanci da kumatu da goshi yana fad'in Allah ya mata albarka Allah ya faranta mata kamar yanda ta faranta masa. Sai gashi yau sheikh ko da sukayi wanka tare ya canza musu zanin gado rumgumeta yayi tsam suka shiga bacci hankali kwance a nutse ba tare da jin yau zai tashi cikin dare ba, ita ma k'am tayi a jikinshi ta lafe tana sauke ajiyar zuciya tana fad'awa kan ta "Ashe haka yake? Dama haka tsofaffin suke? Wai ya akayi ne take neman kwafsawa ta kayar da kan ta? Garin ya ya lamarin tsohon nan ke neman gagararta ne? Gaba d'aya al'amarin shi neman fin k'arfin tunaninta yake, gashi a gado ma tun tana jin dad'in abun da farko har ta fara jin rad'ad'i tana kuka da hawaye tana nuna tayi saranda, gashi wani abu da da take ji daban a game dashi abun ya fi k'arfin wasa, abu ne da zata iya kwatantashi da har ranta zata iya fansar raina dana sheikh."


Da wannan tunanin bacci ya fara yin gaba da ita kafin ya fahimci haka ya tofeta da addu'a shi ma ya rufe ido yana neman bacci ido rufe.             *Asuba ta gari*Soyayya mai tsafta da mutumta juna ke guda a gidan na sheikh Abdul Waheed, matanshi na zaune lafiya suna girmama junansu kowace tana ba wa yar uwarta da darajarta, gashi yanzu gidan na su ya sake yin shiru babu yara, Heezam Allah yayi tafiyarsa Madina, Aswan kuma wasu lokutan sai daf da magriba yake dawowa gidan ya sake shiryawa ya tafi masallaci wani sa'in sai shiga kwana yake dawowa, daga su sai Munzeer kawai dan Khadija ma har yau tana asibiti saidai su je su ganta su dawo. Hakan yasa lokuta da dama sheikh ke titseyesu yana fad'in dan Allah su haifo masa yara mana da zasu dinga masa oyoyo, Mimi dai murmushi take yi bata magana, dan ita fa indai a gaban Hafsat ne nunawa take ita d'in wata manja-gara ce da bata san me ye aure ba, amma fa idan suka shiga daga ciki sheikh har yi yake kamar zai suma dan lamarin Mimi kam abun sai addu'a.


Duk da wata nutsuwa ta fara zuwa mata tare da wani irin sanyi kamar ba ita ba, amma kuma ranar da take jin k'arfin jikinta yana shan mamaki, dan kad'an ne a aikinta ta tsaya gabanshi ta dinga kwasar shoki tana jefa masa ita a fuska ko tana masa rawar mazaunai, tun abun na masa wani banbarak'wai har ta d'an fara bashi kunya, yanzu kuma kawai sai take birgeshi tunda dai ai shi ne ake ma ba komai bane. Tabbas akwai k'uruciya a tare da ita mai d'auke da wautar kasancewarta 'yar fari kamar yanda aka canfa, saidai a haka yake tafiya da abarsa kuma babban abun farin cikin a yanzu shi ne yanda take d'aukar kowane na shi tana sawa a kan ta, hatta makaranta daya umarceta ta dinga fita tare da Hafsat bata masa musu ba, watak'ila abubuwan da ake koyarwa suna tasiri a gareta shiyasa yanzu take sake girmama shi da kambamashi har take tutiya da ita ma matarsa ce, dan idan kwananta ya k'are a kwana biyun Hafsat babu abinda take yi ban da kula da kan ta, idan kuma kwana biyun ta ya cika haka zatayi ta masa billi tana botsarewa tana kukan shagwab'a a dole zai tafi ya barta har kwana biyu.          *Bayan wata uku*Da sauri ya shigo d'akin dan duba me ya tsaida ita Hafsat har ta shiga islamiyya ban da ita, zaune ya sameta bakin gado ta buga tagumi, shigowarshi yasa ta d'aga kanta ta bishi da kallo, d'auke tagumin tayi ta mik'e a kasalance ta nufeshi ita ma. Sheikh daya bi gaba d'aya jikinta da kallo ganin kayan dake jikinta alamar ko shiryawa ba tayi ba, gashi kayan nan masifan birgeshi suke idan ta saka, duk wata tsohuwa da sabuwar sha'awarshi tayar masa suke yi, kasancewarta fara sai kayan kalar bak'ak'e suke karb'an fatarta, rigar hannayenta kamar na singlet suke ta kamata sosai, sai wandon da tsayinshi iya cinyarta ne kawai sai rubutun Gucci da aka zagayesu da shi, suna mata kyau sosai, suna had'ewa kawai ta fad'a jikinta ta kwanta luf cikin shagwab'a tana fad'in "Abdul bana jin dad'in jikina, dan Allah ka min addu'a ka ji."


Tallabo kan ta yayi suka kalli juna cike da kulawa yace "Me yake damunki yan matana? Shiyasa baki yi shirin islamiyya ba kenan?"


Cikin turo baki tace "Um."


Da kulawa yace "To fad'a min me kike ji?"


D'an d'aga girarta tayi sama tace "Kai! Abun fa dayawa ne."


Shi ma d'aga Girard yayi yace "Allah? To zo zauna ki fad'a min na ji."


Jan ta yayi suka zauna bakin gado yana kallonta yace "To ina jinki."


Cike da shirme da sakarci ta shiga nuna masa da hannu tana fad'in "Ka ga nan marata sai ta dinga ciwo idan na tab'a, sannan ina jin ana motsi wani lokacin kamar ana harbina."


Ta fad'a duk tana d'ora hannunshi a marar ta ta, tas ya zuba idonshi kan marar ta ta yana fad'ad'a murmushi a ran shi yana godewa Allah dan shi kam har ya harbo jirgin, d'orawa tayi da "Kuma ka ga sai kaina ya dinga min ciwo dan danan, sannan ga ciwo a tafukan k'afafuna kamar ana kunna min wuta, sannan bayana sai ya dinga min ciwo..."


D'ora kan ta tayi a cinyarshi tace "Ni wallahi ma kamar na mutu nake ji..."


Duk da ta kai k'arshen kalmar amma saida ta dakata ba tare da shiri ba, fizgota yayi da k'arfi suka kalli juna a wani yanayi na daban, yanayin rauni ne ya bayyana a tattare da shi tare da sassauta muryarshi yace "A'a Ryam! Ba yanzu ba kinji? Mutuwa dole ce ga mai rai, amma ba yanzu ba Ryam, ina sonki, ina son ki ci gaba da rayuwa har ki ga jikokinki."


Murmushi tayi ta rumgumeshi tsamtsam tana sako da hawayen da take jin su daga zuciyarta ne tana fad'in "Abdul wani abu nake ji a kan ka, a can cikin zuciyata nake jin wani muhimmin abun da bayan iyayena babu wanda nake jin kwatankwacin haka a kan shi sai kai."


D'agota yayi a jikinshi ya kalli fuskarta yace "To ki fad'a mana ki huta Ryam, ki fad'a min ki ce Abdul ina sonka."


Mak'ale kafad'a tayi tace "Ni ai ba so bane, kawai dai dan mun shak'u ne."


Dungure mata kai yayi yace "To tashi canza kaya muje asibiti a duba min ke, kafin mu dawo na wa su Hajia albishir kina da ciki."


Da k'arfi ta kalleshi ta dafe k'irjinta da taji ya buga tana zazzaro ido tace "Me? Ciki?"


Sai kuma ta mik'e a tsoraxe tana shafa mararta ta kalleshi tace "Tsohon yan matanshi ka daina min irin wannan wasan, kaga dai babu kyau tsorata musulmi ko? Ka daina dan Allah bana so."


Juyawa tayi zata nufi falo tana fad'in "Haba dan Allah, na samu ciki na kalli mutane da wane ido kuma? Shikenan sai na yi tsaye na kallesu su kalleni su kalleka su ce ni da kai dama lalatattu ne?"


Mik'ewa yayi da sauri ya rik'o yana fad'in "Mu ne lalatattun? Ko kuma dai ni da nayi cikin?"


Da sauri ta rufe ido tace "To ai haka mutane zasu fad'a, haba dan Allah ni fa yar yarinya ce, kai kuma ka ga babba ne ko?"


Da zolaya yace "Sa'an Abba ko?"


Dariya tayi ta fad'a jikinshi tana sauke numfashi tace "Abdul tsoro nake ji, bana so na samu ciki yanzu dan Allah kayi wani abu a kai."


K'am k'am ya matseta a jikinshi yace "Tsoron me kuma bayan ina tare da ke?"


Sake lafewa tayi jikinshi tana jin wata k'aunarshi na ratsata, dan gaskiya soyayyar da yake nuna mata bata tunanin da Asas ta aura zata samu kwatankwacinta, kai ita ta ga aya k'arara, tsohon nan ya bud'e mata kwanyarta ta d'auki darasin rayuwa, ita kam da za'a maida rayuwarta baya da zata sake fatan auren *babban mutum* mai addini kamar sheikh d'in ta.


Duk yanda ya so su je asibiti nunawa tayi ai babu abinda ke mata ciwo kawai ba zata je ba, k'yaleta yayi bai takura ba saidai yasan dole zata buk'aci ganin likita.
                  *Aish-Nas*
Duk da ba wata soyayya bace a tsakaninsu, amma dai akwai girmama juna da mutumtawa, yau ma shiryawa sukayi zuwa gidansu Anas d'in dan gaishe da mahaifiyarshi da bata da lafiya, a tartsetsiyar motar da sheikh ya bashi a matsayin kyauta ta kyautatawa tsakanin d'alibi da malami suka isa k'ofar gidan, suna zuwa tare suka fita yana rik'e da kwanukan abincin, suna kaiwa daf da k'ofar ya mik'a mata yace "Shiga zan jiraki a nan."


Da mamaki ta kalleshi duba da sau uku haka na faruwa, idan ya kawota gidan saiya tsaya ita kad'ai ke shiga, ba tare data daina mamakin ta sunkuyar da kan ta cike da ladabin da uwarta ta d'orata a kai tace "Ka gafarceni idan ka ji haushin tambayata, amma dan Allah me yasa kai baka shiga kullum sai dai ka tsaya a nan?"


Murmushi yayi ya d'an kalli gefenshi kafin ya kalleta yace "Aisha ba zan shiga gidan nan ba a yanzu, amma zan shiga wata rana."


Sake d'agowa tayi da mamaki tace "Me yasa to?"


Numfashi ya sauke ya gyara tsayuwa da kyau yace "Kin gane? Abbanmu ne ya mana iyaka da shiga gidansa, ba ni kad'ai ba duka 'ya'yanshi maza masu hankali, ke har da ma mata masu aure ya gindaya mana tsinuwa idan muka shigar masa gida ba tare da izininshi ba."


A firgice ta kalleshi tace "Subhanallah! Yaya Anas me kuka masa da zafi haka? Babu kyau irin wannan fa ko kad'an, ka fad'a min dan Allah sai na tayaku bashi hak'uri ya yafe muku."


Ba tare daya daina murmushin fuskarshi ba yace "Humaira, ba wani babban laifi bane muka aikata, k'anina dake bi min ne wata rana ya samu mahaifiyarmu da matar Abbanmu amaryar da yayi suna fad'a, shi ne ya siye fad'an har yayi gangancin dukanta, akan wannan ne ya had'amu gaba d'aya ya nesantamu da shi."


Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta yace "Tunda yayi auren nan komai ya canza, mahaifiyarmu ma bata da lafiya ne saboda shi, amma bamu da bakin magana, kullum cikin fatattakarmu yake da hantararmu, akan amaryar nan nunawa yake babu mai mahimmanci sama da ita."


Murmushi ya mata ya nuna mata k'ofar yace "Shiga ciki zan jiraki a nan."


Jiki a mace Aisha ke kallonshi tana jin wani abu a zuciyarta, sai take tuna sanda na su uban yayi aure da kalar iskancin da tayi amma sau d'aya kawai mahaifinta ya iya marinta, kai a dalilinta ma har yaji matar uban na ta tayi kuma a haka bai d'auki tsatsauran mataki a kan ta ba, hasalima har gaisheshi take ya amsa saidai sake mata fuska kamar baya ne ya daina. Kuma har yau idan ta je gidan bata wani sakin fuska da jikinta ga Mimin, hasalima daga gaisuwa bata k'ara ce mata komai ba, amma yanzu da ta ji abinda Anas ya fad'a mata sai kawai ta ji wata kunya ma ta kamata, sai taji tana buk'atar bΓ’ wa Mimi hak'uri sannan su koma kamar yanda suke a baya kafin ta tare gidan uabnsu.


*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *56*
Rayuwa kenan, yau Mimi da kan ta ce tasa a tuk'a mata tuwo dan ta ci, tunda ta kira Aunty Shapi'a ta fad'a mata haka sheikh ya tsura mata ido yana kallo da mamaki, tunda ta fahimci kallon me yake mata ta d'auke kai tana basarwa, murmushi yayi ya mik'e tsaye yana fad'in "Allah ya raba lafiya."


Kallonshi tayi cikin turo baki tace "Ni fa babu abinda nake da, a fa daina alak'antani da ciki."


Bai juyo ba sai ma wucewa da ya ci gaba da yi zai fita yana fad'in "Yo mutum idan masifa yake ji ya fita waje yayi mana, ni a wani tsatsareni nan dan an ga ba ruwana bana duka."


Fashewa tayi da kukan shagwab'a tace "Sheikh ni ko? Ni kake fad'a ma magana? Ba komai ka ci gaba da yi cizgani, kuma ai ko dan cikin jikinka ga dinga lallab'ani kana lelena."


Juyowa yayi yana gimtse dariyarshi yace "Toh! Dama ciki ne da ke?"


Da sauri ta girgiza kai hakan yasa shi sakin mirmushi ya juya ya fita a d'akin yana fad'in "Na tafi tafsir sai na dawo."


D'aga masa hannu tayi alamar bye bye tace "A dawo lafiya tsohon yan matanshi."


Shi ma hannun ya d'ago mata sanda yake fita a d'akin zuwa falonta kafin yake ficewa, saida ta tabbatar ya isa falon ta mik'e da gudu tana hangen bayanshi tayi tsalle ta hayeshi wanda hakan ya zo mishi a bazata saida yayi gaba da k'arfi yana tangal tangal sai kuma ya tsaya da k'afafunshi yana juyo da kan shi yana son kallonta yace "Oh Allah! Oh Allah ka ga baiwar nan taka ka shirya min ita."


Dariya ta kyalkyale da ita tare da saukowa a bayanshi tana fad'in "Ni ma na rama abinda ka min a ranar."


Da fara'a ya kalleta yace "Amma Ryam ke ai yanzu ba ke kad'ai bace, ciki ne da ke fa, ko kina ki zubar mana da shi ne? Kinsan dai ina son ku aje min yara ko?"


Bubbuga k'afafun ta shiga yi a k'asa tana fad'in "Um um fa! Idan fa kana kirana mai ciki zai daina yi maka shokin ma, kasan dai kai ka ce tana birgeka idan ina yi ko?"


Cikin fad'ad'a dariya yace "Idan kika daina sai ki koya min ni na dinga yi miki."


Da sauri ta zaro ido tace "Lahhh! Astagfirullah, Allah ya tsareni da koyawa shehi na rawa, ai sai mala'iku su tsine min."


K'yalk'yalewa yayi da dariya yana fad'in "Wato dai so ake na makara a tafsir ne ko?"


Matsowa tayi daf da shi ta shiga gyara masa zaman hularsa da rigarsa tana fad'in "Kaga dai yau babban tafsir zakayi kuma haskawa kai tsaye ne, ka kula sannan ka nutsu ka aje hankalinka wuri d'aya ko Allah ya sa ka dace da fad'arsa."


Sumbatar kuncinta yayi yace "Nagode Ryam, ina k'aunarki sosai, ina alfahari dake."


Murmushi tayi tace "Baka buk'atar komai?"


Girgiza kai yayi alamar a'a yace "Babu, sai abu biyu kawai, bansan ko zan samu ba?"


Da kulawa ta kalleshi tace "Me fa? Yallab'ai ka d'auka ma angama."


Suna kallon cikin idon juna yace "Na farko ina so ki bani damar sumbatar k'aramin Abdul Waheed d'in dake kwance cikin mararki, hakan zai k'aramin karkashi. Na biyu kuma ina so na ji kin fad'a min kina so na."


Murmushi ta saki tare da d'aga rigarta tace "Na baka izini tsohona, idan ma kana buk'ata zan iya ara maka shi ku tafi tare ai."


Tintserewa yayi da dariya yace "Taya zan tsinana wata tsiya a tafsir ina da k'aramin cikin nan, ai zan zauna nayi ta shafarshi ne."


Dariya ita ma ta dinga yi har saida yace "To na biyun fa."


Wulwula idonta tayi sai kuma ta d'aga k'afafunta ta cimma tsayinta ta manna masa sumbata a kuncinshi da ke zagaye da yalwataccen gemu, da gudu ta nufi shiga d'aki inda ya bita da kallo yana dariya, girgiza kai yayi ya sa kai ya fita zuciyarshi wasai yana jin wani nishad'i.


Babban masallacin Gaddafi suka sauka inda yake d'auke da manyan mutane, masallacin cike yake da dubbanin jama'a sun kasa kunne suna sauraren nutsatsen wa'azin, inda yake nusar dasu da raha yanda zasu fahimta tare da kafa musu misalai, gabanshi cike yake da wayoyi ga kuma kamarori dake d'auka da babban gidan telebejin tΓ©lΓ© sahel dake d'auka su ma suna haskawa kai tsaye.


K'aramar wayarshi daya bari kunne ne mai d'auke da lambobi masu mahimmanci tayi haske alamar sak'o ya shigo, sanin ko ma waye yasan yana tsaka da mahimmin abu yasa sheikh d'aukar wayar dake gabanshi, duk da haka kuma bai daina fad'an abinda yake fad'a ba a bakinshi, saidai yana sauke idonshi a kan gajeren sak'on da Mimi ta turo masa mai d'auke da tsirarun kalmomi kamar haka _"Ina sonka."_


Sai ya samu kanshi da yin shiru na 'yan tsirarun sakanni, aje wayar yayi a ranshi ya fad'i "Nagode Ryam." A zahiri kuma d'an saita nutsuwarshi yayi ya kalli gabanshi yana d'an gyaran muryar da zummar ci gaba sai kawai suka had'a ido da Abba dake zaune sahun gaba kuma a kullum ya ga sheikh d'in shi dai fatanshi bai wuce "Allah ka tsayar da hankalin yarinyar nan wuri d'aya, Allah ka cire mata duk wasu tsutsotsi dake kan ta kar ta tarwatsawa bawan Allah nutsuwarshi." Ba yasa yanzu ma tar yake kallonshi, dan shi a kowane lokaci gani yake za'a ce ga abinda Mimi tayi marar kyau.        *Washe gari* Ana addu'ar kaffaratul majalis aka fara mik'ewa, da sauri ita ma ta mik'e tana kallon Hafsat d'in data kasance malamarta a aji ta nufi wurin, tana zuwa sunkuyawa tayi tana d'an mamatse k'afafu tace "Aunty Hafsat ba zan jiraki mu tafi tare ba yau, da gudu zan tafi wallahi saboda..."


Sai kuma tayi shiru suna kallon juna, da fara'a Hafsat tace "Saboda me?"


Matse k'afafu tayi gam har tana d'ora hannunta a mararta tace "Aunty fitsari, fitsari nake ji sosai..."


Da sauri ta juya ta nufi k'ofar fita inda Hafsat ta bushe da dariya tana fad'in "Kar dai ki b'ata mana aji malama."


Ko juyowa ba tayi ba ta d'auki takalminta a hannu da gudu tayi b'angarensu, sauren yan ajin da suke d'aukar hadda da basu fita bane suka dinga dariyar Mimin da kuma k'iyasta yanda zamansu da Hafsat ke birgesu, kawai rayuwa ce suke irin ta yaya da k'anwarta, ko da suna kishin juna to saidai sun b'oye a zuk'atansu, amma a zahirinsu kam babu wannan alamar.


Tana shiga falon da gudu d'akinta tayi hari dan tunda ta tare bata tab'a shiga ban d'akin Hafsat ba dake falon, tana cikin gudunta zata shiga d'akinta ta ji muryar Aisha tace "Aunty Mimi."


Cak ta tsaya tare da juyawa ta b'angaren k'ofar d'akin Hafsat d'in da mamaki, ganin tabbas Aisha ce yasa ta sake fad'ad'a mamakinta dan tun kafin ta tare gidan nan rabon da taji ta kirata da aunty, a zahiri kuma sai ta d'an d'aure fuska dan kar ta kawo mata wargi tace "Umm."


Da fara'a a fuskarta ba kamar da ba tace "Auntyna gudun me kike haka?"


Ba yabo ba fallasa tace "Zan shiga ciki ne."


K'arasowa Aisha tayi wacce ta d'an jima da zuwa bata samesu ba hannunta rik'e da plate da biscuits a ciki tana ci, gaban Mimi ta tsaya tace "Auntyna kuma shi ne sai ki dinga gudu cikin gida, idan fa kika wahalar mana da k'ane."


Bud'e baki Mimi tayi ta zaro ido bata san sanda tace "Ke kuma wa ya fad'a miki?"


Murmushi Aisha tayi tana sunkuyar da kai tace "Ai kwanan baya da mukayi waya da Hajia ta fad'a min baki ji dad'i ba, sai kuma akayi sa'a ciwo iri d'aya mukayi da ke, shiyasa na gane."


Sunkuyar da kai Mimi tayi ta bushe da dariya haka ita ma Aisha, suna cikin k'yalk'yala dariyarsu Aisha tace "Aunty Mimi wajenki na zo dama."


Da kulawa ta kalleta tace "To, ina jinki, lafiya dai ko?"


Jinjina kai tayi tana wasa da biscuit d'in cikin plate d'in tana fad'in "Lafiya lau Aunty, dama hak'uri na zo baki akan abubuwan da suka faru a baya, dan Allah ki yafe min insha'Allahu ba zan k'ara ba."


Da murmushi a fuskarta tace "Aisha na yafe miki da jimawa, taya kike tunanin na rik'e a zuciyata har haka, wallahi ba komai na yafe miki, nima ki yafe min kinji?"


Da sauri Aisha ta fad'a jikinta ta rumgumeta tana fad'in "Nagode auntyna, Allah ya saka da alkairi."


D'an shafa bayanta tayi tace "Ba komai Aisha, ya wuce har abada."


Da wata fara'ar tace "Nagode."


D'an sake shafa bayanta tayi tace "Aisha."


A sanyaye ta amsa da "Na'am."


A hankali ita ma tace "Fitsari nake ji, kar ya fara b'ata min jikina."


Da sauri ta janye daga jikinta tana dariya tace "Haba Aunty, ashe shiyasa kika shigo a guje."


Ai bata tsaya cewa komai ba ta kwasa da gudu tayi falonta, a ban d'akin nan ta shiga tayi fitsari har wani rufe ido take saboda yanda yake fita tana jin mararta na yin wani sakai, tana fitowa Aisha ta samu ta zauna kan kujerar dake kusa da fridge ta bud'a alamar zata d'auki wani abu, cire k'aton hijabinta tayi ta aje tana fad'in "Wai kin jima a nan ne?"


Kallonta tayi tace "E aunty ba sosai ba, dama nasan kuna aji shiyasa na zauna jiranku."


Ita ma fridge d'inta nufa ta d'auki ruwa ta bud'e zata sha ta zauna kan kujera, ganin Aisha ta d'auko bud'on had'in dabinonta da madara mao had'e da kankana yasa ta saurin fad'in "Karki sha wannan, magani ne."


Kallonta Aisha tayi ta kuma kalli bidon, ita dai tana ganin alamun madara a ciki, cikin yatsina fuska tace "Aunty maganin me?"


Ita ma yatsina fuskar tayi tace "Mama ta aiko min da shi jiya, na kasa sha ne ma da naji babu dad'i."


Da sauri Aisha tace "Halan na ciki ne? Haka ni ma Hajia ta ce zata kai min magani na dinga sha wai yana wanke dattin yaro, amma ba yanzu ba sai cikin ya girma."


Cike da dagiya da son b'atar da ita Mimi tace "E su ne, amma wannan d'in Mama ta ce na sha ne."


Mayarwa Aisha tayi ta d'auki maltina ta bud'e tana sha tana korawa da biscuit d'inta, Mimi ma tana shan ruwan ta cire safar k'afarta ta mik'e da kayan da jakarta mai d'auke da kayan makaranta ta nufi ciki, tana shiga siket d'in yadin na uniforme ta cire ta cire riga ta d'aura towel ta shiga wanka.Sanda Hafsat ta dawo gidan ta samesu ta ji dad'in ganinsu a tare, ko ba komai alamu ya nuna sun manta da komai kenan zasu rumgumi junansu, hakan yasa ita kan ta a nan falon Mimin suka dinga hirarsu ta rayuwa tunda akwai 'yarsu ba zasu yarda su saki layi ba, sai sallah azahar ce ta tashesu Mimi tayi a nan d'akinta Hafsat da Aisha suka fita, a can ne kad'ai suka samu damar tattaunawa na 'ya da uwa tare da k'ara mata da shawarwari na zaman aure.


Mimi na idar da sallah Aisha ta shigo tace "Aunty Mimi inji Amie ki zo mu ci abinci."


Mik'ewa tayi akan sallayar tace "To."


Cire hijab tayi ta nad'e sallayar ta wuce tana fad'in "Muje."


Da kallo Aisha ta bi bayanta, a gaskiya ita ma dake mace kuma tsararta wannan sura da halitta ta Mimi abar kallo ce, musamman yanzu ma da kwanciyar hankali da jin dad'i suka tilasta mata k'ara zama rusheshiya tubarkallah, tayi k'iba ta cika mulmul ko ina mazaunanta sun sake fitowa, kuma sa'ar ta d'aya tana da tsayi amma fa a haka ma ta fara gajarcewa, saidai duk k'ibarta bata da wawan tumbin nan, gashi dai tana da ciki amma kuma dake k'arami zaka rantse bata da shi har yanzu mararta ce kawai ta taso.*Zaune* suke yana tsakiyarsu yana kallon kowace duk sun zubawa takardun gabansu ido suna kallo, Mimi a ranta addu'a take "Allah kasa Hafsat ce zata ci zab'en nan, ba zan iya tafiya na bar k'asata a wannan halin ba."


Inda ita ma Hafsat addu'arta ita ce "Allah kasa Mimi ce zata d'auka, ni na tafi so ba adadi ya kamata ita ma na bata 'yar damarta, Allah ka sani nayi iya k'ok'arina wajen ganin ba sai ya bi ta hanyar nan ba, amma ya nuna min hakan ne adalcin da zai iya yi."


Sheikh dake ta kallonsu ganin kowace sai mi-mi take da bakinta yasa shi fad'in "Ku fa nake jira, kowace ta d'auki d'aya."


Kallonshi Hafsat tayi ta marairaice tace "Sheikh na fad'..."


Bai bari ta fad'a ba ya d'aga mata hannu alamar tayi shiru, shiru tayi cikin sand'a ta kai hannunta ta d'auki d'aya a cikin takardun, Mimi ma a hankali ta kai hannu ta d'auka, jikinsu duk a mace suka shiga warwarewa, Hafsat na ganin babu komai a ta ta takardar ta daka tsalle kamar yarinya tana fashewa da dariya da fad'in "Woooo! Mimi tafiyarki ce, dan haka a tashi a shirye, ni dai a taho min da tsaraba."


Juyawa tayi ta nufi d'akinta tana fad'in "Allah ya kiyaye hanya oga, a dawo lafiya."


Da kallo suka bita saida suka ga shigewarta Mimi ta kalleshi tana matsar k'walla tace "Sheikh bana son tafiyar nan, a tsorace nake sosai wallahi, ji nake kamar ajalina ne ke kirana."


D'ora yatsarshi yayi a labb'anta yace "Shiiiii! Babu abinda zai faru dake Mimi, ki had'a kayanki kinji, muna tare insha'Allah."


Marairaicewa tayi tace "Amma kuma fa ciki ne da ni."


Jinjina mata kai yayi yace "Ba wani abu bane wannan, na gama da matsalar nan tun tuni."


Shiru tayi tana kallonshi sai kuma ta saki murmushi tace "Wow! Yau ni ce burina zai cika ta hanyar keta hazo."


Rik'o hannunshi tayi tace "Kuma ka ga fa zan samu damar rainon cikina ba tare da kowa ya ganni ba, dan ni dama kunya nake ji wallahi."


Dungure mata kai yayi yace "Kina jin kunyar a kalleki a ce cikin tsoho ne jikinki ko?"


Dariya tayi ta kwanta a k'irjinshi tana fad'in "Tsoho, humm! Ni kad'ai nasan waye wannan tsohon, tsohona jarumi ne, ingarman doki ne ko kuma na ce matashin doki ne."


K'amk'ameta yayi yana dariya yace "Ki ce dai na ciri tuta?"


Ita ma cikin dariya tace "Tun a waccen ranar."


D'ago hab'arta yayi yace "Wace rana?"


Kallon idonshi tayi tace "Waccen ranar mana, ranar daka kusa sumar dani."


Tintserewa sukayi da dariya ya mik'e da ita a jikinshi yana fad'in "Mu shiga daga ciki sai ki rama to."


D'an shak'o wuyan rigarshi tayi tace "Da gaske? Zaka bani dama na rama?"


"Um." Ya fad'a yana d'aga mata kai, jinjina kai tayi tace "Kuma karka rama, ka barni ni kad'ai nayi komai na."


Cak ya d'auketa suka nufi d'akin yana fad'in "Na yarda yan matana, zan baki dama ki more ke ma."


Cike da kunya ta rufe idonta har suka shiga ciki ya direta, cike da farin ciki da k'aunar juna suka shiga farantawa junansu rai musamman Mimi ma data zage damtse ta nemi susuta shi da yammacin da har saida jam'in sallah la'asar ya sub'uce musu dukansu.

*Alhamdulillah*

Post a Comment for "MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 14 Na Samira Harouna"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...