MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 11 Na Samira Harouna - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 11  Na Samira Harouna

MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 11 Na Samira Harouna

- - Post a Comment

 MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 11

Na Samira HarounaπŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *41*
Numfashi ya sauke yana ci gaba da kallon fuskarta, hannu yasa ya fara shafa gaban goshinta zuwa gashinta yana hura mata iskan bakinshi, kallonshi take kam ba ko k'yabtawa cike da jin haushi, tana ji ina ma zata iya magana da k'arfi tace ya daina bari gemunshin nan yana tab'a mata fuska, muryarshi ce ta katse mata hassalarta cikin rad'a yace "Ryam kiyi hak'uri kinji ki yafe min, ni mai zunubi ne kuma babban mai laifi a gareki, ki yafe min kinji, duk yanda na kai ga son rashin tab'a lafiyarki ya zama dole na d'aukeki na kaiki mataki babba, ina so na kaiki muk'amin da kowace mace ke alfahari tana rik'e da kambunshi a gidanta, kiyi hak'uri kinji yan matana, ki juri wannan rad'ad'in iya na yau ne kawai."


Yana fad'a ya had'a goshinsu wuri d'aya ya sake lalubo bakinta, kakkaucewa take dan bata so amma saida ya had'a bakinsu, yana fara hak'arta ta sake zabura ta fashe da kuka tana babbuga damtsenshi, k'in cire bakinshi yayi sai ma ya shiga neman harshenta ido rufe dan yasan in ya barta tsaf zata tashi har yaranshi daga bacci barre kuma Hafsat.


Kuka na hawaye da majina babu wanda ba tayi ba, ta yageshi ta cijeshi ta mintsene shi duk da ya k'yaleta, duk yanda yake tausaya mata ba laifi dai sha'aninshi yasha sosai, shi kan shi ya tabbata data matsu, saida ya zo gab da zai kawo ya wani damk'eta ya shiga jijjigata, yana saki ya fad'a kanta inda ita kuma ta shiga sauke numfashi kamar tayi gudu had'e da shashek'ar kuka.


Kallonta yake sai gumin kanshi zuwa fuskarshi dake d'iga a jikinta na wahalar da yasha sanda ya shiga yanayin kawo da curarren ruwan dake mararshi, yatsanshi yasa yana zagaya labb'anta a hankali kuma yana cire jikinshi daga na ta jikin, rintse ido take kamar za'a d'auki ranta tana k'amk'ameshi gam, yana cirewa gaba d'aya a tare suka saki wani irin numfashi, ita na wani sabon rad'ad'in da ta ji ya ratsata kamar wacce aka watsawa barkono, shi kuma jin wani iska daya bugeshi sakamakon fitowa daga duniyar d'umi.


Yunk'urawa tayi zata tashi zaune ya mayar da ita, d'aukar towel d'inshi yayi ya d'aura kafin ya tsuguna gabanta, hannunta ya rik'o yana kallon fuskarta, kawar da kanta tayi tana shashek'ar kuka, cikin muryar rarrashi yace "Haba yan matan tsohonta, ki kalleni mana."


Da k'arfi ta juyo dan ta d'an jujjuya masa baki, sai kuma ta kasa kawai ta shiga sauke numfashi kamar mai cutar asma, cikin rarrashi yace "Shikenan kinji, ya isa haka yi hak'uri."


Fashewa tayi da kuka da sauri ya rufe mata baki hankali tashe yana "Shiiiiii! Ryam kar kiyi kuka mana, girma ne fa Allah ya baki da ba kowace mace yake ba wa ba, kada kiyi wa Allah butulci mana ta hanyar zubar da hawayenki, kamata yayi kiyi godiya da Allah ya nuna miki ranar nan, Ryam karki manta fa mata dayawa basa samun gatan da zasu ga ranar nan da idonsu, wasu kuma ba mazajensu dake halilinsu bane suke karb'ar wannan abun mai daraja, kinga ke kuma..."


Bai k'arasa fad'a ba ta kalleshi da wani yanayi daya sa gabanshi fad'uwa yaji yarinyar ta bashi tsoro.


Dafe gaban goshinshi yayi yana d'an murmushi cikin k'arfin hali yace "Ki yarda dani Ryam gaskiya nake fad'a miki."


Cikin shashek'ar kuka ta sake d'auke kanta daga kallonshi tana yatqina fuskarta.


Mik'ewa yayi yana tallabarta yace "Muje na taimaka miki to kinji."


Kumburo baki tayi amma ba tace k'ala ba har suka shiga ban d'akin, komai dama ya tanada dan haka yana zuwa hannunshi ya d'an fara sakawa a ruwan dake cikin baho, jin zafin ba zai cutar da ita ba yasa shi sakata a nutse, zunbur tayi tana rik'o hannunshi zata tashi a matuk'ar gigice, da sauri ya rik'e ya mayar da ita ta zauna mutsu mutsu ta shiga yi tana girgiza kai alamar rad'ad'i amma ta kasa magana.


Durk'usawa yayi yace "Kinga yi hak'uri, idan ba haka ba fa jikinki zaiyi ta ciwo ne."


Rintse ido tayi wasu k'walla suka d'aso mata tana cije baki sosai, sake rik'e hannunshi tayi gam ta k'i saki, kallonta yake yana jin k'aunarta na sake shiga zuciyarshi, wani basaraken murmushi ya saki a ranshi yace " *Hak'ik'a tawakallin da nayi ne Allah ya musanya min da alkairi akan abinda nake zargi, tabbas wannan shi ne sakamakon da ubangiji yai min*."


Sakin murmushi ya sake yi yana kallonta ido rufe cikin sanyayyar murya yace " *Ina sonki Maryam*."


Bud'a ido tayi a hankali ta sauke a kan shi, saida ta ja majina ta d'auke idonta a tsaurare tana kawar da kai, cike da rashin jin dad'in yanayin da yake kallonta ya raunana murya yace "Dan Allah mana ki min magana Ryam."


Kallonshi tayi a zuciyarta tace "Kai ne mutum na farko da nake shakkar cizgawa, amma yanzu kai ma lokaci yayi da zaka d'and'ani *sarautar Mimi* ka ji idan da dad'i."


Kamar zaiyi kuka ya sake fad'in " *Mahmi*, kada ki yanke min wannan hukuncin yanzu, ki gafarceni kinji."


Sunkuyar da kai tayi tana cije baki dan sosai take jin zafi a k'asanta, kallonta yayi ya kalli ruwan da take zaune ciki, zunbur ya mik'e yana fad'in "Oh subhanallah!"


Bud'a idonta tayi ta kalli kanta a cikin bahon sai taga yanda zuwan suka canza, a rud'e ta kalleshi ta fashe da kuka amma ta k'i magana, sunkuyawa yayi ya rufe mata baki da yatsarshi yace "Shiru."


Tsaf ta had'iye kukanta sai kallonshi da take tana shashek'a, tana kallo ya bud'e wurin magudanar ruwan suka tafi kafin ya zuba mata wasu masu zafi amma ba sosai ba, kyab'e fuska tayi tana kallonshi da ta je tayi kuka saiyaharareta, ganin su ma ruwan sun canza kala ya sakΓ© gasgata lallai fa tayi k'ari, amma sai bai fad'a mata ba kawai ya taimaka mata ta fito ya aje mata buta yace tayi wanka, har zai fita a ban d'akin sai kuma ya tsaya ya kalli kan ta.


Cike da tuhuma yace "Ban tab'a ganinki da kitso ba, yanzu da kan haka zakiyi wankan tsarki? Taya ruwa zai samu kowane silin gashinki?"


Wani irin turo baki tayi gaba ta rufe ido irin fa ba ruwankan nan, cike da gargad'i yace "Dani kike?"


Bud'e idon tayi ta girgiza kai alamar a'a, k'wafa yayi ya juya ya fita ita kuma ta fara wankan tana mitar "Ba dai ni ka ma haka ba? Gobe kaf a gidajen jarida sai na buga labarinka, malam ba tausayi bare imani."


Tana gama wankan ta fito tana tafiya kamar wacce ta haihu, kayanta ta d'auka ta mayar ta nufi k'ofar fita dan bata ganshi a d'akin ba, had'ewa sukayi a bakin kofar ya kamo hannunta ya dawo da ita, zai zaunar da ita bakin gado tayi tsaye k'erere ta nuna mishi k'ofa da idonta alamar fa fita take so tayi.


Ba tare daya kalli fuskarta ba yace "Kin dawo gidanki kenan."


Da sauri ta juya ta kalleshi yana tattare zanin gadon, kawar da kai tayi ganin yanda zanin ya b'aci tana cije leb'e.


Har ya gama abinda ya ke ya shiga ban d'aki, kuka ta shiga rerawa kmaar wata marainiya tana jin abun duniya duk ya dameta, yana fitowa tsaye ya sameta kamar ta had'iyi tab'arya, yanda take ta share hawaye yasa shi kallonta da kyau yace "Wai ke ba kya gajiya da kuka ne?"


Ko kallonshi ba tayi ba bare ta kulashi, ban d'aki ya sake shiga da kayan baccin daya cire mata ita kuma ta zauna bakin gadon dan k'arfin halin ne take, dafe k'ugu tayi tana girgiza kai ta rintse ido, da sauri ta mik'e sakamakon tunawa da yanda abun ya ratsata da farkon nan, gaba d'aya tsigar jikinta ta ji tana tashi saboda tuna wannan abun al'ajabi, Anya kuwa sheikh ne mai shekarun nan? Ita ai ta d'auka zuwa yanzu irin sojan tayi la'asar d'in nan kad'an take iya zungura.


Zafin daya k'ara tsikararta yasa ta kuma cije fuska tana matsa k'ugunta, yana fitowa tayi saurin sakin fuskarta kamar babu abinda ke damunta.


Daga nan zaune take jin jikinta na wani gab-gab-gab yana rawa, d'an tab'a wuyanta tayi taji masifaffen zafi zazzab'i ya sauko mata, d'ora kanta tayi a cinyarta tayi lak'was abinta, gaba d'aya yanayin jikinta bata jin dad'inshi, abubuwa take ji kawai sabi da bata saba da su ba, fitowarshi daga ban d'akin yasa ta d'ago kanta a hankali amma bata kalleshi ba, gabanta ya durk'usa yana rik'o hannayenta yana kallon fuskarta, cikin rarrashi da tausayi yace "Ryam, ki yi magana kinji, ki ce wani abu dan Allah."


Wani huk-huk-huk ta fara yi tana tuk'ak'o amai,  da sauri ta mik'e zata nufi hanyar ban d'aki kawai rawar da jikinta keyi da rashin kuzari suka zubar da ita a k'asa warwas tare da dannowar amai, da sauri ya mik'e ya matsa kanta yana furta "Subhanallah! Ryam sannu kinji."


A galabaice ta kalleshi duk da bata son yi mishi magana da k'yar ta iya bud'a baki tace "Ka cire min abinda ka saka min a ciki."


Da mamaki ya kalleta sai kuma ya saki murmushi yana durk'usawa yace "Ba abinda na saka miki Ryam, watak'ila dan ina tsoho ne shiyasa na k'arar da k'arfi na a yau d'in nan."


Kamata yayi zasu shiga ban d'aki amma ya kula k'afafunta sai hard'ewa suke, d'aukarta yayi suka shiga ta kurkure bakinta suka fito, tana kallo ya tsaftace wurin data b'ata kafin ya d'auki wayarshi, saida ya fita a d'akin kafin ya amsa.


Kafin Rakiya ta zo gidan mintunan da aka d'auka sai Mimi ta k'arasa gigicewa ta fita hayyacinta, abu ga farar fata lokaci d'aya ta zube tayi fiyat da ita, zazzab'i sosai take ji yana taunar k'asusuwan jikinta ga kuma rad'ad'in da k'asanta keyi har yanzu, ko da Rakiya ta zo Mimi bata san tana kan ta ba tsabar raki da kuma wahala, banda muryar sheikh dake kayar mata da gaba ba abinda kunnuwanta ke ji.


Mimi dai da ba allura take so ba, tunda aka kira Rakiya daga asibiti shi da Rakiya dake gaggawa ko ta tafi gidanta ita ma haka sukayi ta rarrashi amma ina, kuma ta k'i magana saidai ta girgiza kai kawai tana share hawaye dan tayi niyya daga yau har gobe sheikh ba zaiji muryarta ba, k'arshe dai Rakiya ce ta kalli sheikh cikin rad'a tace "Sheikh kawai ka rik'e mana ita a mata allurar bacci, dan ba zata tsaya a mata d'inkin nan ba."


Saida ya je inda take zaune akan gadon ya zauna shi ma, jawota yayi a jikinshi ya rumgume, tana ganin Rakiya tana gyara tsinin allura ta nemi zillewa a jikinshi, tsam ya matseta a jikinshi hakan ya hanata damar motsawa sai yan k'afafunta kawai saΓ― kuma gunjin kuka, bata d'ago daga jikinshi ba bacci yayi awan gaba da ita, gyara mata kwanciya yayi kafin ya fita ya d'akin ya zauna falo kan kujera, kan shi sadde k'asa yana tunanin yanda yar mitsitsiyar yarinyar nan ta shayar da shi ruwan mamaki, murmushi kawai yake saki tare da cin burika na kyautata mata da kuma fanshe mata ranar ta.


Fitowar Rakiya daga d'akin ta sashi mik'ewa ya tarbeta, da kulawa ya tambayeta "Ya take?"


Fara'a ta masa tace "Da sauk'i, na mata d'inki sannan na k'ara mata ruwa."


Ajiyar zuciya ya sauke yace "Nagode Rakiya, kiyi hak'uri na saki latin zuwa ga iyalinki kema."


Murmushi tayi tace "Ba komai sheikh aikinmu Kenan."


Kallon d'akin yayi yace "Ba komai dai yanzu ko?"


A ladabce tace "E sheikh, zuwa safe zan sake zuwa da kaina na dubata."

  

Tana tafiya shi ma fita yayi ya siyo kaji ya dawo, alwala ya d'auro ya shinfid'a sallaya ya kabbara sallah, raka'a hud'u yayi masu tsayin gaske a jowace sujada yana godiya ga Allah daya masa wannan kyauta tare da neman gafara akan zargin yarinya da yayi, abun ne shi ma yafi k'arfinshi, so ne ya rufe mishi ido sai kishi yayi tasiri a zuciyarshi, abinda ya faru a ranar dole ya firgita nutsuwarshi ya jefa zuciyarshi a hali na wasi-wasi, bai san gaibu ba bare yasan gaskiya, dan haka kishi ya dinga d'awainiya da shi ya dinga jin kamar wani ya rigashi.


*04:00* k'arar agogo tasa ta motsawa dan baccin ya saki idonta, da k'yar ta bud'a idonta da suka mata nauyi ta kalli rufin d'akin, dake harda allurar kashe jiki ta mata sai lokacin ta ji wani azababben ciwo ya taso mata na zafin d'inki da kuma musababbin d'inkin, yunk'urawa tayi ta tashi zaune tana sakin hawayen da ita kanta bata so suka taho mata ba, sauke idonta tayi akan sheikh dake gefenta zaune akan sallaya.


Da sauri ya taso ya durk'usa yana fad'in "Ryam kin farka? Sannu kinji."


K'asa tayi da idonta ta kasa kallonshi kuma ba tace komai ba, rik'o hannunta yayi tare da kai d'aya hannun a wiyanta, jikinta da zafi har yanzu sosai tab'a goshinta yayi shi ma dai da zafi alamar ciwon kai, wani huci yayi na rashin jin dad'in halin daya sa yar mutane a ciki, sai ya tuna sanda ta shigo d'in nan tana bashi labarin daya tabbatar k'irk'irarshi tayi.


Mik'ewa yayi yana fad'in "Bari na taimaka miki ki shiga ban d'aki kiyi alwala, lokacin sallah subah tayi."


Hannayenshi ya kai zai kamo na ta ta mak'ale kafad'a alamar um um, turo baki tayi gaba kan ta sadde, cikin rarrashi yace "Haba mana Ryam, muje ko?"


Sake mak'ale kafad'a tayi alamar dai um um, tsaye yayi yana kallonta yana sauke numfashi, nufa hanyar fita yayi yace "Bari to na kawo miki abu ki ci saΓ― ki sha magani."


Tana kallo har ya fita a d'akin, jim kad'an ya dawo d'auke da faranti k'arami, ajewa yayi kusanta ya zauna yana d'an yago naman kazar yace "Yawwa to bud'a bakin."


Sake mak'ale kafad'a tayi har da fad'in "Um um."


Waro ido yayi yace "Shi ma ba zaki ci ba?"


Zuba mishi ido tayi tana kallo, cikin rarrashi yace "Kinga Ryam kiyi sauri ki ci, idan kika gama akwai abinda zan baki kinji."


Kallon da take masa sai ya fara jin ya tsargu dan kamar macijiyar daka kashewa miji ce a gaban idonta, sunkuyar da kan shi yayi yace "Fad'a min me kike so? Ya kike so nayi Ryam? Har yanzu ban ji muryarki ba, kina tunanin hakan abu mai sauk'i ne a gareni?"


Shiru ta masa hakan yasa shi d'ago kai ya kalleta, da sauri ta sauke na ta idon k'asa tana kallon farantin kazar (uwata ba'a wulakanta kazi fa😟) kofin madar daya zubo ya d'auka zai kai bakinta shi ma ta kawar da kai, kamar zai fashe da kuka ya kalleta yace "A'a, wai ya kike so dani ne? Ryam kin k'i ci kin k'i sha kuma kin k'i magana."


Bud'e baki tayi da iya k'arfinta ta fashe da kuka, hankali tashe ya aje kofin hannunshi ya tallabo fuskarta yana fad'in "...
*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *42*
Bud'e bakinta tayi da iya k'arfinta ta fashe da kuka, hankali tashe ya aje kofin hannunshi ya tallabo fuskarta yana fad'in "" A'a Mimi, me na miki kuma daga magana? Kinga idan ba zaki sha ba to shikenan, amma daina kukan kinji."


Hannaye duka biyu ta rattab'a a fuska tana murzar ido tana ci gaba da kukanta, zaune yayi da kyau kusanta ya jawota ya d'ora kanta a k'irjinshi yana shafa kanta yana fad'in "Shikenan to, haba yan matan tsohonta, so kike ace raguwa ce ke a miki dariya?"


Wata irin shashek'a ta shiga yi da gangan kamar zata had'e zuciya, sake tallabo fuskarta yayi ya marairaice yace "Haba Ryam, so kike sai kin nunawa duniya yau sheikh Abdul Waheed ya zo gareki? Ki daina mana kinji, ya isa haka kar kanki yayi ciwo fa."


A tak'aice dai yanda sheikh yaga wannan dare haka ya wayi gari, rarrashin duniya ba wanda bai mata ba amma ina ta k'i ji, kuma gashu ba lokacin jawo aya ko hadisi bane bare ya tab'osu ko ta saurara, a daddafe yayi sallah ya dawo kan ta ya zauna yana kallonta, idonta sun kumbura sunyi ja har fuskarta ta canza. 


Wani dogon numfashi ya sauke yana jin tausayinta na k'ara tsumashi, kukan da take sam bai d'aukeshi na tab'ara ba saina hak'ik'anin gaskiya, kukan shagwab'ar ya mishi yanda yake buk'ata, ya so a ce iya su kad'ai ne a gidan nan da sai ya nuna mata k'arshen zalamarta, zai biye mata ya riritata ya goyata a bayanshi ya mata dokin wuya yanda dole tayi shiru, da zai aje komai na shi ne ya shiga faranta mata rai har sai yaga hak'orinta sun bayyana da sunan dariya.


Tsaf take k'are masa kallo daga rufe fuskarta daa tayi da hannaye tana murzawa wai ita me kuka, sai yanzu ne ta kula ashe fa ustazun nan d'an gaye ne, askin fa kad'an ne ya banbantashi da irin na yan zamani, kawai dai shi ya aske duguzar ne sosai yanda ba'a barta a doron kan ba, amma har wani gyaran fuska yanda gemun ya masa sai ta ga ya birgeta yau kam, ga jallabiyar data fito da surarshi sosai.


Hannayen na ta daya kamo yasa ta rintse ido tana shashek'a, cikin sanyin murya yace "Ryam, zaki sha chocolat?"


Girgiza kai tayi alamar a'a, d'an jim yayi yana kallon gefe alamar tunani sai kuma yace "Zaki sha madara?"


Sake girgiza kai tayi alamar a'a, da sauri yace "Zaki sha ice cream?"


Girgiza kai ta sake yi alamar a'a, d'orawa yayi da "To fad'a min me kike so?"


K'ura masa ido tayi da k'yar ta bud'i bakinta murya can k'asa tace "Gidanmu nake so."


Tsura mata ido shi ma yayi, a take a shiga tunanin ta ya zai kaita gidansu a halin da take cikin nan? Kowa yasan ya zo wa wannan yar yarinyar? A gaskiya yana jin kunya kula ba zai iya ba, shi fa Hafsat ma baya so ta samesu a halin nan, gashi kuma ba zai iya kaita wajen Hajia ba dan kamar akwai cin fuska ma, duk da uwa take gareshi amma ai 'yarta yake aure, haihuwa kuma ba wasa bace, tun suna kawaici suna kawar da kai wata rana shaid'an da zai fara zugasu da saka musu tunani marar kyau.


Rik'o hannayenta yayi da kyau yana kallon fuskarta yace "Ryam, ba zamu je gidanku ba gaskiya, amma idan kina so zamu je wani wuri, na tabbata zai k'ayatar dake, kina so?"


Zuba mishi ido tayi kamar bata gane yarenshi, lumshe ido yayi alamar rok'o yace "Dan Allah Ryam."


Rufe idonta tayi alamar ba ma zata kula shi ba kenan, mik'ewa yayi tsaye ya daddage ya daka mata tsawar data saka ta zabura ta bud'a ido sanda yake fad'in "Dake nake magana malama kina min shiru."


Kyab'e baki tayi zata fashe da kuka ya nunota da yatsa ya sunkuyo daf da ita yace "Kika min kukan nan saina kuma zazzabga miki bulalar da zata fahimtar dake me nake nufi."


Tsaf ta had'e kuka tayi k'asa da kanta, nuna mata k'ofar ban d'aki yayi yace "Maza je kiyi wanka kiyi alwala kiyi sallah."


Jiki na kakkarwa ta shiga saukowa daga kan gadon, saidai allurar da har yanzu bata gama sakin jikinta yasa k'afafunta kasa d'aukarta, shirin fad'uwar da tayi yasa shi azamar tallabota jikinshi, cak ya d'auketa ya nufi ban d'akin da ita yana kallon fuskarta fuskarshi a had'e yace "Yarinya sai taurin kai, bakya gane magana cikin sauk'i."


Tsayar da ita yayi ya shiga cire mata kayan jikinta, nok'ewa ta shiga yi ita ma hakan yasa shi d'aga kai ya kalleta yace "Miye na kunyar kuma? Ba mun zama d'aya ba?"


D'auke kanta tayi tana kumburo baki, murmushi yayi yace "Shikenan bari ki gani, aidai zakiyi  k'orafin na kalleki babu kayana ne ko? To bari muyi wankan a tare."


Kar-kar-kar! Jikinta ya fara ta shiga taka k'afafunta zata fita a ban d'akin, rik'ota yayi ya had'ata da k'irjinshi yana kallon fuskarta yace "To miye a ciki? Ni ba naki bane?"


Ko kallonshi ba tayi ba ta shiga sinne kan ta k'asa, b'alle botir d'in rigar yayi tare da tattarota daga k'asa yayi sama da ita, yanda ta ganta kwance a k'irjinshi da babu riga sai kwantaccen bak'in gashin daya kusa mamaye knirjin mai sulb'in gaske kamar na kan shi yasa ta saurin juya baya, hakan ya bashi damar k'arasa cire...😎 ya jawota ya had'a da jikinshi, yanda yaji jikinta ya fara d'aukar zafi da gaske ga rawar da yake mata yasa shi sakin murmushi ya d'ora hab'arshi a kafad'arta cikin kunne ya rad'a mata "Ryam ga ki da tsoro amma kuma ke ma kina bada tsoro."


Kakkaucewa ta shiga yi saboda kayan jikinta daya fara shirin cire mata, bai bata damar matsawa nesa da shi ba saida ya rabata da kayanta, yanda jikinsu ke gugar na juna tana jin duk wata hallita ta bawan Allahn nan a fatar jikinta sai ta nemi numfashi ta rasa, gaba d'aya ta sarewa lamarin mutumin ko ta ce lamarin maza.


Duk girmanshi, duk shekarunshi, duk matsayinshi yanzu nan ya aje su gefe har ya tsaya gabanta babu kaya zasuyi wanka? Tunda taja numfashinta sama bata maido shi ba ita dai ta k'ame wuri d'aya ta rintse idonta dan bΓ’ zata iya kallonshi ba. Sheikh ko a jikinshi, wanka yake musu sosai cikin nutsuwa tare da wasa da ita, Mimi dai abun jin shi take wani iri, ita dake burin d'an k'aramin mijinta suyi wanka tare sai gashi yau old man ne ke mata wanka kamar baby.


Tana jin sanda ya kashe panpon ruwan suka tsaya, jim kad'an taji yana saka mata rigar wanka, kamo hannunta yayi suka fara takawa tana jin k'asanta na d'an mata zuzar zaren d'inkin nan hakan kuma na k'ara mata rad'ad'i.


Kan kujera ya zzunar da ita gaban madubi, mai ya d'auka ya durk'usa ya fara shafa mata man, kallonshi take yanda har yanzu towel ne a k'ugunshi, sam sai yake mata  kamar ba tsoho ba, yanda yake d'aukarta da yanda yake sarrafa jikinshi ba alamar manyanta irin ta tsofaffin da zaka ga suna fama da ciwon baya k'afafu da sauransu. Yanda take kallonshi idonta bud'e yasa shi sakin murmushi yace "Inna Issa har yanzu ba zaki min magana ba."


K'in d'auke idonta tayi a kan shi, d'an murmushi kawai ya sake saki ya ci gaba da murza mata mai, yana gamawa doguwar riga abaya ya d'auko a cikin kayan daya k'ara zuba mata na ban mamaki, pant ya d'auko da bras ya sake durk'usawa ya zura mata k'afafun, kamata yayi ta mik'e zai k'arasa saka mata sai kuma ya kalleta, d'an sosa kai yayi da irin alamar jin kunya yace "Yan matan tsohonta, anya kuwa wannan zai isheki? Ni fa kallon baby nake miki."


D'auke idonta tayi daga kan shi ta k'arasa saka wandon, tam ya mata alamun dai ya matseta sosai, d'aukar bras d'in tayi ta saka ita ma haka ta mata kip, d'aukar rigar tayi ta saka da sauri ya zaunar da ita kan kujerar, macaji ya d'auka ya fara caje mata gashinta, tsaf ya d'aure mata shi da mad'auri sannan ya d'auki kallabin rigar ya fara yane mata kan cike da k'warewa, yana gama mata ya tallabo fuskarta ya sumbaci goshinta sannan ya nuna mata sallaya yace "Kiyi sallah, zan je na saka kaya nima."


Takawa tayi ta k'arasa gaban sallayar, tana ganin fitarshi a d'akin tayi saurin cire pant d'in nan dan yana tab'ata a jikinta sosai tana jin zafi saboda d'inkin da aka mata, sallah ta kabbara shi kuma ya shiga d'akinshi dake nan b'angarenta dan shiryawa.
                 *Asa-Ma'u*Tunda Asma'u ta zauna jiran Mimi ta ga ba alamarta sai kawai ta ma Hafsat sallama suka taf tare da Kabiru, ita ma suna zuwa gidan suka had'e da Asas, ita kanta sai ta ji kunya da suka had'u da shi ba'a gida ba, a d'arare ta bishi suka nufi na su gidan suma.


A daren kam tasha abubuwa da dama, kunya, fad'uwar gaba, farin ciki da kuma bak'ar wahala, dan kuwa Asas ya nuna mata ya samu lafiya, sun sha amarci sosai da kuma soyayya har garin Allah ya waye, daga wajen Hajia kawai yasa aka kawo musu abinci suna ci ya dunk'ule matarshi a bargo suka shiga ramuwar bacci.


Sake matseta yayi a jikinshi yace "Husna."


A hankali ta amsa da "Na'am."


Cikin taushin murya yace "Kina so na?"


Sinne kanta tayi a k'irjinshi tana d'an shafa cikinshi da hannunta ke kai tana murmushi, cikin shafa bayanta yace "Ina jinki mana, ko ba kya so na?"


Girgiza kai tayi a hankali tace "Ni ban ce ba."


"To me kika ce kenan?" Ya fad'a kai tsaye, cike da jin kunya tana b'oye fuskarta a jikinshi tace "Taya zan ce bana son mijina wanda a yanzu ya zama sirrina, a yanzu fa babu wani abu daya mana shamaki ni da kai, ko na so ka ko na k'i ka ka riga daka zama wani b'angare na jikina."


Matseta yayi sosai ya sumbaci kanta cikin dadad'an murya yace "Ina sonki *Asmy* na, ina sonki sosai, Allah barmu tare."


Cike da jin ya k'arawa kanta girma da farin ciki ta matseshi ita ma cike da jin kunya murya k'asa k'asa tace "Ni ma haka."D'an tsakulkuli ya mata yana dariya yace "Ke ma me? Sai kin fad'a fa malama ko nima na dawo da kayata na rik'e."


Cikin bille bille ta shiga k'yalk'yala dariya tana fad'in "Nima haka, na fad'a to na fad'a."


Dakatawa yayi yace "Me kika fad'a to? Fad'i ko kuma na sake juyewa a kan ki yanzun nan, dama ba isata kikayi ba dan naji kin k'ara wani irin dad'i."


Dukanshi tayi a k'irji cike da kunya tace "Kai wallahi, haba dai."


Cikin dariya yace "Gaskiya na fad'a ai, na tabbata shirya min kanki kikayi kafin dawowata."


Girgiza kai tayi tace "Ni ba abinda nayi."


"Kin tabbata?" Ya tambaya yana lek'an fuskarta, jinjina kai tayi alamar eh, murmushi yayi yace "To yanzu fad'a min na ji, ke ma kina so na?"


Turo baki tayi tace "To wai me yasa ka damu da sai na fad'a maka nima? Ka yarda da abinda na fad'a maka mana."


Mak'ale kafad'a yayi yace "Um um! Kawai ki fad'a min Husna ko nayi kuka."


Waro ido tayi ta kalleshi da mamaki yanda kam duk ya kyab'e fuska shi shagwab'abb'e, kunya tasa ta rufe fuska tace "To ni ma ina sonka."


Sake k'amk'ameta yayi yana murmushi yace "Ko ke fa, har na ji dad'i."


Cikin farin ciki suka samu baccinsu a nutse suna k'amk'ame da juna kamar dama can asali masoya ne.
 

             *Mim-Sheikh*Cikin wata dakakkiyar shadda ya shigo d'akin wacce ta sa shi bayyana sak a angonshi, fara ce shaddar ga rigar daya d'ora irin ta malamai ga hula da takalmi k'afa ciki, shagala tayi da kallonshi dan gaskiya da zata iya bud'a baki a wannan lokacin tayi magana to zata ce "Kayi kyau." Ne, amma data ga yana mata murmushi saita d'aure fuska har saida ya tsaya gabanta yace "Zamu iya tafiya?"


Mik'ewa kawai tayi ta nufi hanyar fita, rik'e hannunta yayi suka kalli juna, ba alamar sakin fuska yace "Bana son jin shirun nan idan muka fita, zan d'auki wannan shirun ne kawai saboda ni na ja, amma iyalina ki girmama min su ta hanyar bud'a baki kiyi magana idan sun miki, Hafsat a gaba take da ke, karki jira sai ta gaisheki kafin ki gaisheta."


Shafa kumatunta yayi yace "Kin gane?"


Sunkuyar da idonta tayi saboda k'wallar da taji sun cika mata ido, tallabo fuskarta ya sake yi cikin sanyin murya yace "Kiyi hak'uri kinji, nayi alk'awari na yau kawai zan baki lokaci na gaba d'aya, zan sa ki fara tunanin tsohonki a zuciyarki, sannan nayi alk'awarin saka murmushi a fuskarki yau d'in nan."


Kama hannunta yayi suka shiga takawa a nutse, ta k'ofar waje suka fita kafin ya zagaya ta k'ofar shiga falon Hafsat, saida ya d'an k'wank'wasa sau uku kafin ya shiga da sallama a bakinshi yana sakin hannun Mimi, yaran dake zaune dukansu falo suna karatu ne suka juya suna kallonshi da amsa sallamarshi, da k'yar da lahaula ta cira labb'anta ta furta "Assalama alaikum."


Ido suka fara zuba mata da d'an mamakin nan ta kwana ko me? Sai kuma suka amsa mata sallamar suna gaishe da mahaifinsu a ladabce, cikin k'arfin hali Mimi ta kallesu da fara'a tace "Karatu ake."


Kallonta suka sake yi dukansu sai Munzeer dake k'arami daya washe mata baki yace "E aunty."


Sheikh ne ya kalleshi yace "Ina mamanku?"


Nuna d'akinta yayi yace "Tana ciki."


Hanyar nufa d'akin Hafsat yayi sai kuma ya kula da wani kallo da Aisha da Heezam suka rakashi kallo ne mai tattare da "Abienmu me kake nufi? Yarinyar nan anan ta kwana? D'aki guda kai da ita?"


Sai kawai ya ji ya tsargi kansa, saidai baiji kunya ba dan ita ma matarsa ce, halalinsa ce ba kuma haramun ya aikata da ita ba. Tsaye yayi dan sai yake ganin kamar zasu iya dakuwa da ita idan ya matsa, Mimi kuma da tsayuwar ta gundureta zaune tayi a kan kujera tana kallonsu ita ma.


Zai sake nufa d'akin Hafsat sai gata ta fito da hijab d'inta a jikinta, duk zuba mata ido sukayi har ta k'araso da sakin fuska tana kawar da komai daga ranta tana fad'in "Mimi da safe haka aka taso ki? Amma dai sheikh ka shiga lokacinta."


Duk murmushi sukayi sai Mimi data sunkuyar da kai tace "Ina kwana aunty."


Da fara'a tace "Lafiya lau Mimi, antashi lafiya?"


Da kunya ta amsa da "Lafiya lau."


D'orawa tayi da "Ya kwanan bak'unta kuma?"


D'an murmushin yak'e kawai tayi sai muryar Munzeer da suka ji yace "Amie gidanmu aunty ta kwana?"


Da fara'a Hafsat ta kalkeshi tace "E."


Aswan kam kamar da gangan kamar sub'utar baki sai cewa yayi "A b'angaren Abie ta kwana?"


Kallonshi duk sukayi sai Mimi da taji kamar ta k'urma ihu, a tsawace Hafsat ta kalleshi tace "Aswan wace maganar banza ce wannan? Ina ruwanka to?"


A tsorace ya kalli Hafsat yace "Amie kiyi hak'uri dan Allah, ba zan sake ba."


D'auke kanta tayi ta kalli sheikh daya tsurawa Aswan ido yana tunanin dole yayi wani abu gaskiya, Aisha dake mace zai matsar da ita dan za'a fi samun matsala da ita saboda mace ce, mazan kuma dama dai lokacin karatunsu yafi yawa akan lokacinsu na zama gida, dan haka zaiyi k'ok'ari yaga raini bai shiga tsakaninsu da matarshi ba.


Kallonta sheikh yayi yana k'ak'aro murmushi yace "Manga kin tashi lafiya?"


Da fara'a tace "Lafiya lau, antashi lafiya?"


Da fara'a shi ma ya amsa da "Lafiya lau."


A ladabce tace "Ya gajiya kuma?"


Kashe mata ido yayi yana murmushi amma bai ce komai ba, girgiza kai tayi tana murmushi ita ma ta d'auke idonta daga kanshi, d'orawa yayi da fad'in "Manga zamu fita da yarinyar nan mu dawo, ba wara matsala?"


Murmushi ta fad'ad'a tace "Ba matsalar komai sheikh, Allah ya tsare hanya, sai kun dawo."


Mik'ewa Mimi tayi tana d'an cije baki, kallonta Hafsat tayi tana sakin murmishi tace "A dawo lafiya?"


Da murmushi ita ma ta amsa da "Allah yasa, mun gode."


Gaba Mimi tayi sheikh ya ma yaran addu'a kamar yanda ya saba kafin ya bi bayanta yana duba agogon hannunshi ta azurfa data nuna k'arfe *06:20* na safe, da kanshi ya bud'e mata gaban motar ta zauna ya rufe kafin ya zagaya ya shiga suka bar gidan.
*Sorry mutane na, wlh gaba d'aya ne aka d'auke mana network.*

*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *43*
Wani k'ayataccen gida ya sauketa da gaba d'ayanshi bai wuce zaman mace d'aya, tun wajen gidan take kallo kamar wata bak'auya, komai na gidan sai taji ya birgeta daga tsarin gidan zuwa kayan cikinshi, a matsakaicin falonta zaunatana kallo ya shiga ciki, ta d'an jima zaune kafin ta ji bud'e k'ofa alamar zai fito.


Sunkuyar da kanta tayi saida ta ji shi tsaye a kan ta yana fad'in "Ryam me zaki ci na dafa miki?"


Da sauri ta d'aga kanta ta kalleshi jin wai yace ya dafa mata, k'walalo ido tayi da matsanancin mamakin ganin shi da k'ananan kaya, riga da wando masu kamar na sport kamar kuma na bacci, amma irin kayan da yan zamani har fita suke dasu idan suka saka, wani irin kyau daya mata da kayan yasa ta saurin had'e mamakinta ta mayar da kanta k'asa a ranta tana fad'in "Oh Allah, wai me ye haka? Shi ma dai d'an duniya ne ashe."


Gaban tv ya k'arasa ya kunna mata wani caset naa wa'azin Hafsat wanda tayi shi ne lokacin auren wata daga cikin d'alibanta, dake magana ce tsantsa akan zamantakewar aure shiyasa ya kunna mata shi, dawowa yayi gabanta ya sunkuya ya rik'o hannayenta yace "Ryam, ni ne ba zaki ma magana ba?"


Lumshe ido tayi alamar eh, marairaicewa yayi yace "Saboda me? Dan na kaiki mataki babba?"


Jinjina kai tayi alamar e, numfashi ya sauke yana murmushi yace "To na ji kiyi hak'uri, yanzu fad'a min me zaki ci na kawo miki, idan kin gama kinga ke ma saiki rama ko? Haka ya miki?"


Girgiza kai tayi tana kawar da kan ta, wata ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mik'e zai shiga k'aramar madafar, hannunshi da har yanzu bai k'arasa sakin na ta ba tayi saurin rik'ewa gam, juyowa yayi yana kallonta, cikin had'e fuska ta kawar da kai tace "Ni gida nake so ka kaini."


Sake sunkuyawa yayi yana kallon fuskarta yace "Me zakiyi a gida idan na kaiki Ryam? Ba kya jin kunyar Mama ne ke?"


Turo baki tayi gaba cikin shagwab'a tace "To ai ba zan fad'a mata komai ba."


Murmushi yayi ya girgiza kai yace "Ryam, ko ni dake namiji idan na kalli mace ina iya fahimtar halin da take ciki, bare kuma uwa mace, dole mama na kallonki zata fahimci me ya faru da ke? Ko kina so ki ce min Mama bata tab'a saka miki ido bane?"


Jim tayi kamar mai tunani hakan yasa shi fad'in "Idan kina so zan kira miki Abbanki sai na baki shi ku gaisa."


Had'e yawu tayi sai kuma ta jinjina kai alamar to, murmushi yayi na jin dad'i ya shafi kuncinta yana fad'in "Yarinyar kirki kenan."


Mik'ewa yayi yana zame hannunshi a nata yace "Ina zuwa."


D'akin daya shiga ya koma jim kad'an ya dawo da waya a hannu, yana zuwa ya mik'a mata yace "Gashi sai ki kira."


Karb'a tayi shi kuma har ya juya sai kuma ya tsaya yace "Fad'a mine zaki ci to?"


Sake turo baki tayi gaba ta nok'e kai tace "Ni bana cin girkin maza, mazan ma wanda basu da k'warewa."


Fad'owa yayi kan kujerar ya mata rumfa kamar zai tausheta yana mata wani shu'umin kallo, had'ewa tayi a jikin kujerar tana sinne kan ta, cikin wani irin salo yace "Ni ne ban da k'warewar? Fad'i abinda kike so na girka miki idan ba tsoro ba."


Cikin sissine kai tace "Indomie."


Wani murmishin gefen labb'a yayi yace "Taliyar yara zaki ce, to kazarki kuma fa?"


D'an d'aga idonta tayi ta kalleshi da alamar tambaya, d'aga mata gira yayi yace "E, kazar amarcinki fa? Na kawo miki ne ki ci?"


Shiru tayi sai turo baki da take yi gaba, caraf ya damk'i leb'enta na k'asa yasa a bakinshi ya tsotsa kamar wata alawa, saida ya ja leb'en kamar zai cirashi ya sakar mata baki yana fad'in "Bani minti biyar yan matan tsohonta."


Yana fad'a ya shige madafar, da kallo ta rakashi tana jin kanta na neman fashewa saboda abubuwan da tsohon ke zuwa mata da su, a gaskiya sai ta ga ya koma mata wani sharaf da shi a cikin k'ananan kayan, sai ta rantse kamar bai tab'a kyau irin na yanzu ba, ko kuma dai bata saba ganinshi da irin kayan bane?


Wayar dake hannunta ta shiga saka lambar Abba, tsaf lambar ta fito da sunan *vieux* (tsoho), bata san lokacin data mik'e tsaye ba ta dafe k'ugu tace "Lallai ma!"


Ai da sauri tsabar jaraba ta nufi madafar, tana isa k'ofar a bud'e take yana tsaye yanaa aiki kam tuk'uru, cike da yarinta ta nuna wayar tace "Yanzu Abban na wa ne tsoho?"


Juyowa yayi yana kallonta da mamaki sai kuma ya d'aga kafad'a yace "Gare ni na ji."


Cikin turo baki tace "Kamar ya gareni? Ni fa Abba nake cewa."


Juyowa yayi da kyau yace "Ranar aurenmu na ji kince tsoho ne, shiyasa ni ma na rik'e a kai na."


Shiru tayi alamar tunani, sai yanzu ne ta tuna sanda tace ta so nemawa Abbanta auren Asma'u saboda nagartarta, tab'e baki tayi ta murgud'ashi tace "Ai dai Allah bai ce hakanan ba, ina laifin ma ka saka mishi abokina tunda dai ai na ga ka girmeshi."


Yanda take maganar ita fa iya gaskiyarta take fad'a, takowa ya fara yi tare da aje ledar indomie hannunshi, jawo k'ugunta yayi ya had'a da na shi yana kallon fuskarta yace "Ya kike so ayi yanzu *sarauniyata*?"


Cike da sangarta tace "Kawai ka saka mishi aboki."


Karb'ar wayar yayi yana fad'in "Angama yan matan tsohonta."


Tana kallo ya shiga daddana wayar na yan dak'ik'u kafin ya nuna mata yace "Haka yayi?"


Dubawa tayi ta ga ya saka aboki, murmushi tayi ba tare da saninta ba tace "Ko kai fa."


Mik'a mata wayar yayi ta juya zata fita yana binta da kallo, wato indai ka auri yarinya dole ka zama yaro wani lokaacin kuma ka zama mai raino. Tana daf da fita kuma ta tsaya ta juyo irin da mamakin nan tace "Amma kuma ai sirikinka ne, ya zaka sakawa lambarshi sunan aboki?"


Numfashi ya ja yace "Bai yi ba shi ma?"


Marairaicewa tayi tace "Haka nake tunani."


Murmushi yayi yace "Yanzu ki fara kiranshi ku gaisa, kafin ki gama wayar zan tayaki tunanin sunan da zamu saka, hakan yayi?"


Jinjina kai tayi alamar e, fita tayi shi ma ya juya ya ci gaba da aikinshi yana tunanin sunan da zai saka ma lambar nan ya huta, dan alamu na nuna zai sha matsi akan sunan lamba kawai.


Zaune tayi akan kujera ta d'ora kafafunta sama ta cire kallabin rigar abaya ta aje gefe, tana jin tana ringin da sauri aka d'aga Abba na fad'in "Assalama alaikum akaramakallah."


Dariya tayi cikin ladabi tace "Wa'alaikum salam, Abba ni ce fa, Mimi."


Kamar a d'an tsorace yace "Mimi? Ke me kike da wayar sheikh yanzu da sassafen nan?"


Turo baki tayi tace "Abba ina kwana?"


A dak'ile yace "Lafiya lau."


Jin bai k'ara da komai ba yasa tace "Abba ina Mama? Ku bani ita."


Muryarshi ta ji yana fad'in "Rabi'a karb'i nan, uwata ce yanzu ta kira da lambar sheikh?"


Jim kad'an ta ji Mama a dak'ile ita ma tace "Ina jin ki?"


Numfashi ta sauke tace "Mama ina kwana?"


"Lafiya lau." Ta fad'a a tak'aice, cikin sanyin murya tace "Mama ina so na je gida wajenki, dan Allah Mama ki ce na zo kinji, bana da lafiya Mama ina son ganinki."


Shiru Mama tayi tana nazarin duka maganganunta, can daga bisani ta nisa tace "Mimi, yanzu ke fa ba yarinya bace, ina so na ga kin aje wannan shirmen kin rungumi sabuwar rayuwarki, ba k'aramin mutum kike aure ba fa, Mimi a yanzu idon jama'a dayawa zai sake hawa kan ki ne da son ganin kalar damun da zaki wa ta ki rayuwar ta yanzu, ki nutsu ki kwantar da hankalinki, ajin nan dana sanki dashi da kuma tsafta, iya kwalliya da iya girki, Mimi na sanki da iya zama da mutane, na tabbata indai a b'angaren ladabi ne da girmama babba ba zaki samu ta biyu ba, ya kamata kiyi anfani da damarki kinji, sannan da kike maganar baki da lafiya, ya kamata kisan wacece ke, baki da k'anwa ko aunty da zasu iya taimaka miki a wasu abubuwan, tun yanzu ki fara koyon yanda zaki taimakawa kanki idan buk'atar hakan ta tashi, dan akwai gurin da ko giyar wake na sha ba zan iya tunkara ba da sunan taimaka miki, kin fahimta?"


Mimi da jikinta ya gama sanyi wata ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi kafin tace "Na fahimta Mama, nagode."


A takaice tace "Ba komai, ki kula da kanki."


Saida ta had'e wasu hawaye da suka taho mata kafin tace "To Mama."


A hankali ta kashe wayar tana sako da hawayen na jin zafin rashin mataimaki a rayuwarta, lallai zatayi kamar yanda Mama ta fad'a, zata koyi kula da kanta sannan ta fara koyon yaanda zata shanye damuwarta ita kad'ai, bugu da k'ari zata koyi yanda zata iya farantawa mijinta rai ita ma. Dan maganganun Mama ba iya wannan k'arfin gwiwar kawai suka k'ara mata ba, har da na d'amarar zama da sheikh ma, zata zauna da shi ta masa biyayya ta masa ladabi, saidai bΓ’ hakan na nufi ta zama sakara bane a gidan miji, kasancewarshi tsohon daya haifeta ba shi zai sa ta kwanta ya jata a k'asa ba, haka ma matarshi kasancesarta wacce ta haifi kamarta ba zata d'auki wani abun daga gareta ba, saidai ta yarda zata mata ladabi ta kuma bita sau da k'afa, kuma ta yarda ko a wayo ne zata iya wanketa ta shanye, dan haka tasan ba zata kara da ita ba ta kowane fanni, amma ita ma zatayi iya bakin k'ok'arinta.


Aje wayar tayi gefe ta gyara zamanta sosai tana kallon tvn, ta jima zaunen kafin ya fito hannunshi d'auke da wani k'aramin tangaren mai kama da kwano, akan table d'in tsakiyar ya aje tare da d'auko table d'in gaba d'aya ya dire a gabanta yana fad'in "Oya Hajia, ga indomienki."


Kallonshi tayi da girmamawa tace "Sannu da aiki."


Gefenta ya zauna yana murmushi, cokali mai yatsu ya d'auka ya saka a ciki ya tallabe kwanon a tafin hannunshi, d'ibowa yayi ya nufi bakinta yana fad'in "Bismillah."


Cike da kunya ta bud'a bakinta ta karb'a, jim tayi tana d'an taunawa a hankali tana son tantance abinda take ji, k'ura mata ido yayi yana murmushi yace "To ya kika ji?"


D'aga gira tayi ta kashe masa ido d'aya tace "Ba laifi, dama ka iya girki ne haka?"


Dariya yayi yace "Hakan na nufin na birgeki ta wannan fannin?"


Sunkuyar da kai tayi alamar kunya, sake d'ibowa yayi ya ci gaba da bata a nutse tana karb'a, tas ta cinye dan yunwa take ji dama kuma shi ma bai barta ba saida ta cinye, kakkaurar madara ya bata ta sha sannan ya b'allo maganin da Rakiya ta bayar yace "Yawwa yan matan tsohonta, yanzu wannan zaki sha sai ki samu bacci ko?"


Marairaicewa tayi tace "Abdul bana son magani wallahi, kaga dai wannan abubuwan biyu bana son su ko kad'an."


Kallon tuhuma ya mata yace "Menene su?"


Cikin turo baki tace "Allura da magani."


Wata yar harara ya mata yace "Da duka kuma? Kin manta kin ce ba kya son duka."


Da sauri tace "E hakane, da duka."


Girgiza kai yayi yace "To yanzu fad'a min, idan na jik'a miki maganin zaki sha?"


Kyab'e fuska tayi irin kamar zatayi amai tace "Tirrrrr! Amai zanyi."


Matsawa yayi daf da ita yace "To kinga bari kiga dubarar da zamuyi."


Gyara maganin yayi a yatsunshi biyu yace "Bud'e bakinki ki d'aga kan ki saiki rufe idonki sosai."


Had'e yawu tayi sannan ta rintse ido ta bud'e bakin kamar yanda yace, bata ankara ba taji maganin can k'asan mak'oshinta, kafin tayi wani yunk'uri kuma ya kora mata ruwa tare da saka yatsu biyu ya rufe k'ofofin hancinta, hakan ya tilasta mata had'e maganin da ruwan tana sauko da kanta k'asa, kallonshi tayi tana zazzaro ido shi kuma yana murmushi yace "Gashi har kin shanye."


Waro ido ta sake yi tace "Da gaske?"


Jinjina mata kai yayi, cike da mamaki tace "Duka biyun?"


Sake jinjina mata kai yayi alamar e, dafe k'irji tayi tana dariya tace "Yau ni na sha magani haka, kai Allah nagode maka."


Dariya yayi ya jawota jikinshi ya kwantar yana shafata yace "Kinga yanzu haka zamu dinga shan maganin kenan."


Sunkuyar da kanta tayi k'asa ba tace komai ba, gyara zamanshi yayi ya kwanta akan kujerar tana jikinshi ita ma, cikin sanyin murya yace "Ryam, kin yarda ina sonki?"


Shiru tayi kamar ba zata amsa ba sai kuma ta numfasa tace "Ban yarda ba."


Da sauri ya d'agota a jikinshi yana kallon fuskarta da mamaki da kuma tsoro yace "Baki yarda ba Ryam? Kina ganin zan miki k'arya ne."


Tab'e baki tayi ta d'auke kanta daga kan shi, cikin tashin hankali da jin zuciyarshi na bugawa ba daidai ba ya cabko wuyanta ya juyo da kallonta kan shi yana fad'in "Dake nake magana kin wani shareni, fad'a min na ji mana, k'arya na fad'a miki kenan?"


Fizge kanta tayi ta mik'e tsaye tana fad'in "Kawai ni na ce ban yarda ba."


Shi ma tsaaye ya mik'e ya jawota gaba d'aya jikinshi yana kallon fuskarta yace "Me yasa Ryam? Dan kin tabbatar ina son ki ne kike min haka?"


Mutsu mutsu ta fara na son k'wacewa tana fad'in "Ba so na kake tsakani da Allah ba, jikina kake so Abdul."


Da wani matsiyacin mamaki ya kalleta yana sakinta gaba d'aya ya girgiza kai, yanda bakinshi yayi nauyi yasa shi d'agawa da k'yar yace "Ryam...soyayyar tawa...ce abar wannan..wulak'antawar? Me yasa Ryam?"Kawar da kanshi yayi kamar mai son b'oye hawayen idonshi, girgiza kai tayi ita ma cikin sanyin jiki tace "Ni ba k'aryatawa nayi ba, amma dai nasan jikina kafi so, sheikh na tabbata kana d'aya daga cikin mutanen da suke zargina da aikata zina, yanda kake min wani kallo, da yanda kake fad'in wasu maganganu akai na, da yanda ka zo min jiya, ni yarinya ce mai k'ananan shekaru, amma ba mahaukaciya ba."


Gyara tsayuwarta tayi tana kallonshi tace "Ka d'auka ni ballagaza ce shiyasa ka zo min a yanda babu wata budurwa da aka tab'awa haka, kawai ni yanzu so nake ka kaini gidanmu dan ina so nima a rakoni kamar yanda ake rako kowace mace."


Juyawa tayi zata fita a falon da niyyar ta zauna bakin k'ofar ya rik'o hannunta, hankalinshi tashe zuciyarshi ta makance ya jawota sosai, marairaicewa yayi cikin rawar murya yace "A'a Ryam, ba haka bane kinji, karki zargeni akan haka dan Allah, kuma maganar tariyarki na fad'awa Hajia kuma ta fad'awa Abbanki kin tare d'akinki, karki damu da wannan kinji."


Da mamaki ta kalleshi tace "Ban gane na tare ba? A hakan?"


Kamar zaiyi kuka yace "To miye a ciki? Dama ai ni ko mahaifinki ne ya kalata mu rakaki d'akinki, duk wannan shirmen da ake yi bidi'a ce Ryam, dan Allah ki kwantar da hankalinki kinji."


Kallonshi tayi tana had'e hawayenta, tuna maganar Mama da kuma tabbatarwa bata da wata madafa, sai kawai ta fizge jikinta gareshi ta koma kan kujerar ta zauna, zaunawa yayi shi ma yana kallonta ya buga tagumi, cikin raunin murya yace "Ryam ke ce jarabawata, dan Allah ki taimaka min ko na samu cinye jarabawar nan a sauk'ak'e."


Jan majina tayi saboda bata son yin kuka, ganin bata kulashi ba yasa shi jingina a kujerar ya jawota a hankali ya kwantar a jikinshi, hakan ne yasa ta fashewa da kuka tana cukuikuiye rigarshi tana fad'in "Abdul bana jin dad'i, jikina da zuciyata ciwo suke min, gashi kai kuma bansan me yasa ba bana iya maka tsayayya, dolena ne na girmama wanda iyayena ma suke girmamawa."Shafata ya ci gaba da yi yana sumbatar kanta yana fad'in "Shiiiii! Ya isa haka Ryam, kiyi hak'uri kinji, bari na miki addu'a to."


Kwantar da ita yayi kan kujerar ya zura hannunshi ta saman rigar, a hankali cike da kissa da k'warewa ya shiga shafa nonowanta da suka k'ara kumbura, shiru tayi da mamakin wace irin addu'a ce haka? Tana ji tana saurarenshi yake ta shafawa yana lailayawa har saida ta ji sak'on ya fara isar mata, gaba d'aya ta ji tana wani bank'arewa tana neman shigewa jikinshi, jin abun zai fi k'arfinta sai kawai ta fashe da kuka ta matseshi tsam.


A hankali ya laluba ya kamo bakin kuka ya had'a da na shi ya shiga tsutsa hakan ne ya tirsasa mata yin shiru tana saurarenshi.

*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *44*
Hannun da taji yana zurawa ta k'asan rigarta alamun akwai gab'ar da yake son kaiwa yasa ta saurin hautsinawa ta mik'e tsaye, kallon juna suka shiga yi kamar masu tuhuma ko zargin juna, sai kuma ta dafe gaban goshinta tana yatsina fuska tace "Aouch!"


Da sauri ya mik'e yana rik'o hannunta yace "Menene? Kina lafiya?"


Cikin yatsina fuska tace "Bana jin dad'in jikina ne, bacci nake so nayi."


Murmushi yayi ya jawota suka shiga takawa a hankali, d'akin daya shiga da ita yasa ta d'ago kanta tana k'arewa d'akin kallo, kwantar da ita yayi kan lafiyayyen gadon tare da shafa kanta yace "To kiyi bacci."


Lumshe ido tayi alamar to, mik'ewa yayi daga sunkuyawar zai fita sai kuma ya tsaya, a nutse ya haura kan gadon ya d'aga kanta ya d'ora kan k'irjinshi, shafata ya ci gaba da yi yana fad'in "Bacci...bacci...bacci...bacci."


Samun kanta tayi da d'oa hannunta na dama akan k'irjinshi ta rufe ido, sannu sannu sai kuwa bacci yayi gaba dasu dukansu.


Awa d'aya ya samu a baccin nan ya tashi saboda rashin sabo, falo ya dawo ya zauna yana gudanar da wasu harkokinshi, a k'alla awa biyu ya d'auka anan zaune kafin ya shiga madafar nan, kazar daya sa mai gadi ya kawo masa ya saka a cikin na'urar d'umama abu, kafin tayi zafi kuma kokombre ya saka a blender tare da na'a na'a da citta d'anya ya markad'a, da k'aramar rariyar roba ya tace ya saka zuma ya kai fridge, yana kammalawa ya ciro kazar tare da sakata a plate ya yankata yanda zatayi daidai da cin mutum a sauk'ak'e kafin ya d'ora plate d'in a babbar faranti, lemun nan ya d'auko ya d'ora akan farantin sannan ya d'auko fresh milk  ya d'ora ya nufi d'akin baccin.


Baccinta ya samu take yi har yanzu, aje farantin yayi ya nufi ban d'aki ya had'a mata ruwan wanka masu d'umi, fitowa yayi ya zauna gefenta ya rik'o hannunta yana kallon fuskarta, a nutse ya shafa kumatunta tare da furta "Innar Issa."


A hankali ta shiga bud'a idonta tana mitsikasu, saida ta bud'e duka ta saukesu fes a kan shi, tashi tayi zaune tana murza idon ta juya dan neman agogo ta ga awa nawa ta d'auka, murmushi ya mata yace "Awa hud'u babu minti goma kika d'auka kina baccin nan."


D'an matse bakinta tayi tana k'ok'arin sauko da k'afafunta k'asa, taimaka mata yayi har ta mik'e tsaye tana jin bata jin k'warin jikinta, saidai ciwon jikinta ya ragu sosai, saida suka isa bakin k'ofar d'akin ya tsaya yace "Ki shiga kiyi wanka na gama had'a miki ruwa, kiyi alwala daga nan dan 12:30 tayi."


Jinjina kai tayi ta shige ban d'akin ya rufo mata k'ofar, falo ya koma shi ma ya shiga ban d'akin dake nan yayi alwala, dawowa yayi d'akin ya zauna bakin gado jiranta, ta d'an d'auki lokaci kafin ta fito d'aure da towel babba a jikinta, kanshi na k'asa a lokacin yana ganinta ya d'aga gaba d'aya, santala santalan cinyoyinta masu kauri da haske ya fara kallo, da k'yar ya had'i wasu yawu tare da kawar da kanshi saboda alwalar dake jikinshi.


Cikin shak'akk'iyar murya yace "Ryam gaggauta muyi sallah kafin k'arfe 01:00."


Jinjina kai tayi da sauri ta nufi rigarta zata d'auka yace "Ki duba cikin drower nan akwai kaya."


Da sauri ta nufi drower ta bud'a, duka abaya ne sai kuma kaya masu taushi na bacci da hijabai, d'auka tayi ta saka wata abayar ta d'auki hijab ta saka, gabanshi ta tsaya tace "Na gama."


Mik'ewa yayi yana tsaya sosai akan sallaya yana fad'in "Na manta rabon da nayi sallah jam'i a gida, yau dalilinki zanyi hakan."


Zaro ido tayi tace "Saboda ni? To ka je masallaci mana ni sai nayi a gida."


Murmushi yayi yace "Ai anan kusa ne babu masallaci, kuma na miki alk'awarin zama tare dake na tsawon wunin nan."


Kallonshi tayi ba tace komai ba ita dai har suka kabbara sallah tana daga gefenshi, a minti ashirin da d'aya suka gama sallah har Mimi ta fara tunanin ko k'iyamu-lail zai sa su yi, suna idawa ta mik'e ta cire hijabin ta aje kan gado, mik'ewa yayi shi ma yace "Zauna ga abinci."


Zaune tayi kamar yanda yace ya aje mata farantin gabanta, hannunshi ya sa ya fara bata a bakinta shi ma kuma yana ci. Har suka gama ya bata madarar tasha shi kuma ya d'auki lemun nan ya shanye.*Wuni* ne na ban mamaki a wurin Mimi, wuni ne da zata iya cewa ya shiga tarihin rayuwarta, yanda ya mu'amulance ta ya tafi da ita sai abun ya tsaya mata cak a zuciya da tunani, yanda ya kula da ita ya riritata ya k'ara shagwab'ata, ko kare bai yarda ta d'auka daga nan zuwa can ba, komai shi ya yake mata saidai ta ci ta zauna suyita hira, duk da mamakinshi ya sa ko sakin jikin ta kasa yi da shi, amma dai ba laifi wunin nan yasa ya tsaya mata a rai har ta fara jin tsohon a k'asan zuciyarta. Saidai abu d'aya da bata sani ba shi ne dama ba tun yau take jin shi ba, can ma rashin bawa abun mahimmanci ne da shiririta yasa bata iya fahimta ba.


20:30 tana zaune kan cinyoyinshi biyu ya d'ora hab'arshi kan k'irjinta yana danna wayarshi ita kuma tana kallon tv, lumshe ido tayi ta sauke numfashi a hankali tace "Ab..yallab'ai."


Kallon fuskarta yayi yace "Um um! Ki kirani da Abdul."


Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um! Ni tsoro nake ji."


Girgiza kai yayi yace "Tsoron me kuma? Allah Ryam kin d'aukeni kamar kakanki."


Murmushi tayi tace "Ba haka bane, kaga idan na saba da fad'in Abdul idan a gaban mutane ne fa? Kaga su suna giramamaka idan na kira sunanka za'a kalleni marar tarbiya ne."


Murmushi yayi yace "Hakane kam, to ki canza min wani sunan mana mai dad'i."


Jim tayi ta d'aga kanta sama alamar tunani, sai kuma tayi saurin kallonshi tace "To idan na ce bawan Allah fa."


Wani sanyayyan murmushi yayi yace "Haka ma yayi, babu abinda zai sani k'ara k'ank'ar da kaΓ―na kamar na tuna ni d'in bawan Allah ne ba wata tsiya ba."


Murmushi tayi ita ma sannan tace "Abdul nan zan kwana?"


Kallonta yayi yace "Kina son hakane?"


D'aga kai tayi alamar e, sake matsata yayi jikinshi yana shinshina jikinta yace "Um um! Gida zamu koma, ba zan iya barinki a nan ba."


Turo baki tayi gaba tace "Ni dai kawai ka barni nayi bacci na a nan."


Girgiza kai ya sake yi alamar a'a, kyab'e fuska tayi ta turo baki ba tace komai ba, kallon fuskarta yayi ganin yanda ta kyab'e a dole tayi hushi yasa shi aje wayar hannunshi ya mata cakulkuli yana dariya da fad'in "Haba dai gimbiya, kinga fuskarki kuwa yanda tayi? Sai kika zama kamar wata mage na jin bacci."


K'yalk'yalewa tayi da dariya bata sani ba tana bille-bille har ta fad'i kan carpet d'in tana zillewa, bin ta yayi ya mata rumfa yana fad'in "To yi min dariya sannan."


Cikin k'yalk'yalawa take fad'in "Na yi to, nayi ya isa haka, Abdul cikina zan mutu."


Dakatawa yayi yana dariya shi ma da kallon fuskarta, ba taee daya d'aga daga jikinta ba y'a kalli fuskarta yace "Ryam ina sonki sosai, ki yarda da haka kinji."


Mak'ale kafad'a tayi tace "Um um! Ban yarda ba."


Kallon mamaki ya mata yace "Ya kike so nayi dan na tabbatar miki?"


Cikin murmushi tace "Da kaina zan tabbatar da haka."


Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ta ya ya?"


Kashe masa ido tayi ta d'an k'yata bakinta, sumbatar bakinta yayi sosai kafin ya d'agata yace "Tashi ki shirya mu tafi gida kafin dare yayi."


Kamata yayi ta mik'e tsaye ta suka shiga d'akin, a tsanake suka shirya suna raharsu har suka gama suka fito bayan ya rufe kowace k'ofa suka d'auki hanyar komawa gida.


Suna shiga cikin gari ta kalleshi a marairaice tace "Abdallah ice cream."


Ta gefen ido ya kalleta yace "Me ice cream yayi?"


Turo baki tayi tace "Zan sha."


Girgiza kai yayi yana murmushi yace "Hummm! Amma dai kinsan ba zan lamunci shan kayan sanyin nan ba ko?"


Dafa hannunshi tayi da yake tuk'i tace "Dan Allah fa, daga wannan ba zan k'ara ba."


Jinjina kai yayi yace "Shikenan, watak'ila fa yarona ko yarinyata ce a cikinki."


Da k'arfi tace "Me? Da wuri haka? Tabb'!"


Kallonta yayi yace "Kina mamaki ne da yin ubangiji?"


Girgiza kai tayi tace "A'a, amma dai ai yayi wuri."


Murmushin gefen labb'a yayi mata har suka tsaya daidai shiga wani alimentation, fita yayi zai rufo k'ofar ta d'aga masa hannun tace "A dawo lafiya."


Murmushi yayi yace "Wato ba zaki zo muje ba saboda ba kya son ki jera da tsoho."


Dariya tayi tace "Ba haka bane, ai na d'auka ba zaka so na shiga gurin nan ba."


Girgiza kai yayi ya rufe k'ofar ya juya ya shiga wurin, a hankali ta bud'e motar ta fito da k'afafunta kafin ta fita gaba d'aya, rufe k'ofar tayi ta tunkari shiga ita ma tana murmushin mugunta.


Ta b'angaren kayan mak'ulashe ta nufa tana hangenshi tana b'oyewa, kwando ta d'auka ta dinga loda kayan k'walam biscuit chacolat da saurensu, saida ta cika basket d'in ta nufo inda yake tsaye yana laluban aljihu, tana zuwa ta aje basket d'in tana murmushi ganin ya tsaya sororo yana kallonta da mamaki.


Murmushi ta masa ta kalleshi tace "Ga wanda na d'auko ta can."


Galala ya kalli matashin sai kuma ya kalleta ya matsa kusanta yace "Ryam lafiyarki k'alau? Wa ya ce ki fito?"


Murmushi ta saki tana takowa ta tsaya daf da shi tace "Kayan dad'i na siyo."


Iska ya furzo da tunanin ya zaiyi da ita, yana kallo ta shiga ciro kayan tana d'orawa kan kantar da za'a dubasu a musu kud'insu, yana kallon ikon Allah shi dai aka fad'a mishi kud'in ya biya aka saka musu a leda, zai d'auka tayi saurin d'auka tana fad'in "Lahhhh! Haba Abdallah ya zan bari ka d'auka?"


D'auka tayi suka fita yana kallonta shi dai, saida suka shiga mota ya fara tafiya ya kalleta yace "Ryam kinsan ina da kishi?"


Ba alamar damuwa a tare da ita tace "Na sani."


"Kuma kinsan zan iya yin komai a kanki?"


Kai tsaye ta sake fad'in "Na sani."


Kallonta yayi yace "To me yasa kikayi abinda kikayi?"


Marairaicewa tayi tace "Sorry."


Murmushi yayi tare da lak'ato hancinta yace "Nayi sorry yan matana, amma kar a sake daga yau."


Jinjina kai tayi tace "Insha'Allah."


Da hirarsu ta farin ciki suka isa gidan, ta falon Hafsat suka sake shiga kuma sunyi sa'ar samunta zaune tare da Aisha suna karatu, abun haushi shi ne kallon da Aisha ke musu shi da Mimi, gashi bai ji ta gaishe da ita ba sai ma Mimi ce tayi k'ok'arin fad'in "Aisha karatu ake?"


Amma sai ya ga ta mik'e ranta a b'ace tana fad'in "Amie saida safe."


Da kallo ya bi Aishar har ta shige, Mimi ma d'akinta ta nufa tana fad'in "Saida safenku."


Shigewa tayi ta barshi tare da Hafsat, shi ma yau babu fara'ar nan ya kalleta yace "Zan shiga ciki nayi wanka, kafin na fito ina buk'atar ganin duka yaran nan a falona."


Da fara'a ta amsa mishi da "Angama sheikh nawa."


Shigewa yayi ta bishi da kallo sai kuma tayi saurin mik'ewa ta je had'o mishi kan yaran da tunanin ko lafiya? Bai d'auki lokaci ba ya fito daga wanka ya shirya cikin jallabiya fara tas da ita, yana fitowa falon kam ya samesu dukansu har da Munzeer, mutmushi yayi na jin dad'in girmama maganarshi da Hafsat tayi, duk da abinda zai fad'a yanzun bai shafi Munzeer ba, amma da yace yaran duka saita tasoshi daga bacci shi ma, dan gashi nan kanshi a cinyarta tana daddab'ashi ya tashi saboda ganin sheikh ya fito.


Zaune yayi akan sofar yana kallonsu dukansu, had'e fuska yayi sosai cikin fad'a da muryar tashin hankali yace "Auren da nayi ne yasa nake gani raini k'arara a idonku ko kuma dama can akwai rainin tsakaninmu yanzu ne ya fito? Shin haramun ne na aikata da girmansa ya gawurta har zai iya janyo min rainin 'ya'yan cikina dana haifa? Me na yi? Akan me?"


Ya k'arashe yana kallonsu musamman ma Aisha da Heezam, duk sanda kawunansu sukayi hakan yasa shi d'orawa da fad'in "Auren da nayi? Ko kuma yarinyar ce bata muku ba? Bana son tashin hankali kun sani, amma daga auren yarinya har zaku fara min kallon hadarin kaji har wasunku ma zasu iya bud'a baki su min tambayar da duk ta zo bakinsu bayan na tabbata kuna da hankalin tauna magana kafin ku furtata, to akan me?"


Jinjina kai yayi tare da k'wafa yace "Da ba'a aure ai da ban haifeku ta hanyar aure ba, k'addarata ce ta kawo Mimi a Wanda k'arfina ya fara k'arewa, idan zamuyi adalci yarinyar ce abar dubawa anan, amma ku mahaifiyarku kawai kuka sani, ita kuke taya wa kishi kenan? Shin ita kunga tayi makamancin abinda kuka min ne a yau d'in nan? Haka kawai na tsaya gabanku kuna k'are min kallo cike da raini da son tantance me na aikata da matata a d'akinta."


Kallon Hafsat yayi a sanyaye yace "Qawwama bana da matsala da ke, na tabbata kina iya k'ok'arinki akan tarbiyar yaran nan, amma ki sani zanyi wani abu da ban san ko zai miki dad'i ba, kasancewata uba namiji dole na d'auki matakin gyara kan iyali tun yanzu, dan a yanda na fahimta idan lamarin nan ya gawurta wata rana zan iya shigowa gidan nan na samu d'aya a cikin yaran nan suna dakuwa da Mimi, musamman ma da suke ganin shekarunsu d'aya kumaa tsayinsu d'aya da ita."


Kallon Aisha yayi yace "Ki shirya ma aurenki ranar juma'a mai zuwa insha'Allah."


Kallon Heezam yayi yace "Zan gama kammala maka shirin tafiyarka Madina a satin nan, da zaran kaga d'aurin auren yar uwarka zaka bar k'asar nan."


Kallon Aswan yayi yace "Daga sallah magriba zuwa isha'i zaka fara darasi tare damu a majalisin su Anas, daga isha'i zuwa lokacin da zaka kwanta bacci zaka kasance a d'akin karatu na kana bitar karatunka."


Duka yaran kallonshi suke kowa kamar zaiyi kuka musamman Aisha data fara hawaye, amma sai suka sadda kawunansu k'asa Heezam na fad'in "Ka gafarcemu Abie, mun tuba ba zamu k'ara ba insha'Allah."


Aisha ma da sauri tace "E Abie, ka yafe mana dan Allah, ba zamu sake ba wallahi, zamu d'auki aunty Mimi kamar mahaifiyarmu."


Da mamaki ya kallesu yace "A ganinku saboda ita ne na yanke hukuncin nan? Kar ku min gurguwar fahimta mana, hak'ik'a Aisha sai bayan aurena ne da naji wasu kalaman a bakinki na yanke hukuncin aurenki, amma sauran ai dama na jima da fad'a muku ina da wannan tsarin, yanzu ne lokacin zartarwa yayi."


Cikin shahsek'ar kuka Aisha tace "Abie ka yafe min ba zan k'ara ba, ina so na kammala karatu Abie ba yanzu na ke son aure ba."


Harara ya dalla mata yace "A lokacin da kike buk'atarshi kuma saiki kirashi ya zo?"


Kallon Hafsat yayi da ita dai tayi shiru take kallon yaran, amma fa a zuciyarta kamar zata kama da wuta haka take ji, a gaskiya hukuncin yanzu bai mata ba, dan ita ma kawai ta ta'allak'a haka da aurenshi da Mimi ne, akan me zai yanke ma yaranta wannan hukuncin? Saboda sun kalleshi kawai? Ajiyar zuciya ta sauke sanda yace "Hafsat me kika ce akan haka?"


Girgiza kai tayi a sanyaye tace "Ba komai sheikh, Allah yasa haka shi yafi zama alkairi, Allah ya mana jagora a lamuranmu."


Wani tattausan murmushi ya saki yana kallonta, a gaskiya da zai bud'a zuciyarshi ya nuna mata irin girma da k'aunar da yake mata musamman halayen nan nata na karamci, tabbas da sai ta ji babu mace mai sa'a a duk duniya kamar ta, da zatayi rawa tayi tsalle ta buga k'irjinta a gaban dubbanin mata kan cewa babu kamarta. Kallon yaran yayi yace "Ku tashi ku je ku kwanta."


Mik'ewa sukayi jiki duk a sanyaye sai Munzeer daya shiga baccinshi a k'afar Hafsat, saida suka fita dukansu ya taso ya d'auki Munzeer d'in sannan ya kama hannunta ta mik'e, a hankali suka fita har suka k'arasa d'aki ya shinfid'eshi ya tofa mishi addu'a, d'aki ya rakata ita ma ta kwanta kafin ya mata saida safe ya fito.
*Alhamdulillah*

Post a Comment for "MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 11 Na Samira Harouna"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...