KAREENATEEY COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KAREENATEEY COMPLETE

KAREENATEEY COMPLETE

- - Post a Comment

 KAREENATEEY COMPLETE 
Sauri nake domin na karasa gida dan yau garin da rana gashi azumi nake,jikin na 


kuwa har diga yake da zufa. 


Get na kwankwasa aka bude mata,cikin girmamawa na gaishe da mai gadin 


sannan na wuce ciki. 


Gidane mai part part da yawa,kusan guda hudu,biyu dake gefe Wanda daya yana 


kallon daya,daga gaban gidan kuwa,wani hadadden part ne Dan madaidaici. 


Wannan karamin part din na kalla,jtakalma na gani a kofar part din wanda hakan yana nuni da babana yana gari kenan,part din nan guda hudu na biyu na kwankwasa. 


Kanwata hafeeza ita tazo ta bude mini,cikin natsuwa na shiga da sallama,,ummi dake kitchen ta amsa mini,da sauri na karasa kitchen din,ganin ummi tana 


girki,raina ya bace. 


Daki naje na ajiye jaka ta sannan na dawo kitchen din har ta gama dafa doyar,amsa nayi na daka mata sakwarar,ina gamawa ana kiran sallar magrib,don 


haka na fara hada kunun aya. 


Dabino naci sannan na wuce dakin mu domin yin sallah,babu kowa sai dai dakin tsaf yake ko'ina a gyare,bathroom na shiga nayo alwala na fito,Ina idar da sallah 


nayi azkar sannan na fito. 


A falo na sami ummi tayi wanka ta canza kaya nasan saboda yau ita take da girki ne kuma abban mu na gari,cikin natsuwa nace mata"ummi zanje in gaishe da Abba nayi mishi sannu da zuwa",amsawa tayi da “a dawo lafiya,amma kiyi sauri 


domin kinga baki ci komai ba" ina tafiya na amsa da to. 

Cikin natsuwa na isa part din mahaifina,har lokacin akwai takalma a kofar falon 


shi,sallama nayi sai da ya amsa sannan na nemi izni na shiga. 


Yana zaune a kan abin sallah,littattafai ne gasu nan da yawa a gaban shi,sai 


mutane guda biyu wanda duka daliban shi ne,kusa dashi naje na zauna. 


Matso dani jikin shi yayi yace"mama na ya azumi,ance Dani kinyi azumi",daga kai 


nayi alamar eh kafin nace"nayi Abba kasan na saba da hakan’,girgiza kai kawai 


yayi. 


Na dade a wajen shi sannan na fito domin na tafi,a bakin get na hadu da rufaida tana ta faman sauri,dafa ta nayi cikin sauri ta juyo,a hankali tace"Abba ance ya dawo",cikeda takaici nace"haba rufaida meya sa kike hakane tun safe da kika fita sai yanzu kika dawo fa’,harara ta galla mini tace"dalla rufe mini baki,ina ruwan ki 


dani matsa ni ki bani waje",bangaje ni tayi ta wuce. 


Da idanu na bita ina mamakin hali irin na wasu daga cikin yan gidan mu. 


Koda na koma na samu ummi tana kallon aljazeera,zama nayi sannan nace"ummi sannu da hutawa’,cikin farin ciki tace"yauwa sannu yar albarka,jeki ki dauko abinci kizo kici kada ki zauna da yunwa',cikin natsuwa na mike naje kitchen na 


dauko abincin. 


Sai da naci na koshi sannan na tashi,wanka kawai nayi na daura alwala sannan nayi sallah,doguwar riga nasa banyi wata kwalliya a fuska ta ba amma duk da haka rigar tayi mini kyau,hijab har kasa na zumbula sannan na fito,nasan yau aji 


zai cika domin Abba yana gari. 


Kamar yadda na zata haka kuwa ya faru domin bangaren,hajiya a cike yake,waje 

DOWNLOAD HERE 👈

Post a Comment for "KAREENATEEY COMPLETE "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...