GUGUWAR HAMADA COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GUGUWAR HAMADA COMPLETE

GUGUWAR HAMADA COMPLETE

- - Post a Comment

 GUGUWAR HAMADA COMPLETE Lab'e take a jikin d'aya daga cikin tagogin d'akin wanda ba marufi gareshi ba sai d'an ubansun kwalliyan da ke jikin shi kasantuwar cikin dare ne kuma wasu fitilu ne a kunne a gefe da gefen tagan ba kuma wannan tagar ne kad'ai ba har sauran ma haka suke, ginin gurin kuwa na k'asa ne amma me uban tsayi domin hawa hud'u ne da shi daga inda take ma kuma sannan shi kanshi wannan gini a cikin wani ginin yake abun dai ya k'ayatar da ka gani kasan masarauta ce babba ,domin ko ina zagaye yake da gagga - gaggan Fadawa masu ji da k'arfi a jika, gasu bak'ak'e ne na asali.......


"Ya zama dole mu raba Raheena da abunda ta Haifa dole!!! Domin kuwa muddin suka taso cikin wannan gida na alfarma toh lallai ba mu ba rawar gaban hantsi!!" Cewar d'aya daga cikin matan da ke zaune a d'akin kenan wanda kasancewar ta bak'a baka kallon komai na fuskarta se hak'oran ta domin ko Hasken ido bata da shi .

D'ayar kuma tace " eh wannan haka yake kin yi gaskiya Ubaidah!! Ai dole mu rabata da yaran da ta Haifa domin kuwa babu yadda za'a yi muda muka zo bamu zuba kwayaye ba sai wadda aka kawo ta a bayan mu! In muka yi wasa sarki duk zai tattara hankalin shi da tunanin shi ya bata mu kuma Mun zama gumaka !!"

Ubaidah tayi karaf tace " yo banda abunki Zulaikha ai aikin gama ya riga ya gama ! Mutumin da ya zama kamar tinkiya sai da tunanin ta fa yake tunani toh ai kuwa kinga bamu ga ta zama ba , dole ne mu d'au mataki! Ke nifa na ma kasa yin tunanin abu d'aya , shin bakya mamaki yadda ta haifo yaran nan duk farare sol kyawawa anya kuwa wannan harka mai martaba ba'a cuceshi da wani k'atulan mak'atulan d'in ba kuwa:oops:? " Zulaikha tace" yo toh wa ya sani ne abu a duhu? Ko da yake ita ai tsatson Indiyawa ce wata'kila kyaun ta suka biyo ko na iyayen ta!" Ubaidah ta murtuk'e fuska ga muni tace " kaji min Zulaikha da wata sabuwa ! Yo in ma hakan ne bakya tunanin wani daga dangin su Kedai kawai a bar kaza cikin gashin ta !!"+


Duk maganganun nan da suke yi yana kunnen Shalini a yanda take a lab'en ta fara ja da baya a hankali hannayen ta biyu duk ta rufe bakinta da shi tana hawaye da gudu ta juya ta fita daga wannan 'bangaren ta nufi wani b'angare wanda shima duk irin wannan ginin ne ta banke wata k'ofa ta shige d'akin da gudu ta durk'usa gaban wani kyakkyawan gado wanda akayi shi da zinare da kuma azurfa sai zufa take yi jikinta na b'ari ,ta sa hannu tana shafa kan yaran da ke Kwance a kan gadon wanda basu wuce sati biyu da haihuwa ba ,kamannin su d'aya ne,babu abunda ya raba su. "Y'ay'a na !! Na yi alk'awari bazan barku ku wulak'anta ba ni zan kula da ku in Allah ya yarda babu abunda zai same ku na cutarwa! Ta d'auke su duk ta rungume cikin sand'a ta fice daga wannan 'bangaren sai juye juye take yi har ta kai inda ake ajiye dawakai ta kunce guda daya ingarma fari da ruwan 'kasa jikin shi ,ta ajiye Yaron guda d'aya a 'kasa saida ta sab'a guda a baya sannan ta d'auki d'ayan ta haye dokin ta yi hanyar fita ba tare da ta bari mai gadi ko d'aya yaga fuskar ta ba...........


Gudu take tsakani da Allah har gari ya fara wayewa ta yi nisa sosai daga gari gashi kuma cikin HAMADA (DESERT) Suke tafiya bata ankara ba ta jiyo Hayaniyar dawakai daga chan bayanta sun cimmata ,tayi mamaki sosai yadda aka gano fitar ta har aka biyota kuma da ta lura da wad'anda suke zuwa sai taga ashe na hannun daman su Ubaidah ne:oops:............Daga nan ta san cewa kashin ta ya bushe domin tasan tabbas sunga fitar ta ne . juyawa tayi gaba da baya,gabas da yamma ,kudu da arewa, sama da k’asa duk babu wani mafita da ya wuce ta saddaqar ta zubawa sarautar Allah ido. Suna k’arasowa duk suka sauk’a k’asa daga dawakan su kusan su biyar ne guda biyun Mahir da Nasir suna daga cikin manyan sojin yak’i na masarautar ,Mahir mugu ne na gaske shi yasa tafiyar su tazo d’aya da su Ubaidah da Zulaikha. Nasir kuwa mutum ne me sauk’in kai ga tausayi shi yasa Mahir yake cin karenshi ba babbaka a kan Nasir.

  

       Sauk’a itama tayi daga saman dokin ta rungume Yaron  da ke hannun ta ,yayinda d’ayan yana baccin shi a bayanta , gadan -gadan Mahir ya nufo inda take hannun shi da zabgegiyar takobi ko da ya k’araso itama ta zaro y’ar k’aramar wuk’ar ta ,yana isowa ya sa hannu zai wafce Yaron da ke hannun ta amma kafin ya kai ga hakan ta tsaga mishi fuska da wuk’ar tuni ya ja da baya ya zube k’asa sauran guda biyun suka rik’e shi suna duba lafiyar shi ,ganin haka yasa Nasir ya jata suka hau doki a guje dokin nan ya bar gurin , Mahir da ke Kwance ya nuna su da ‘kyar yace ” Ku .ku bi su!!! ” da gudu suka haye dawakan su suka bi bayan su Shalini yayinda shi kuma suka barshi nan cikin zafin rana ga yanka a fuska.+


        Mayak’an biyu sun bi bayansu amma ko kyallin su basu gani ba balle kuma har su kai ga kamasu, haka suka juya suka koma don sun san ko da sun ‘kara gaba ba samun su za’a yi ba. Suna dawowa inda yake suka tarar da Mahir tsaye jikin dokin shi ,ya dubesu da ido d’aya domin dayan shine gefen da aka ji mar ciwon , yace ” ya na ganku haka?!! Cikin rikicewa suka ce “ranka shi dade bamu same su ba ,Nasir ya riga ya tseratar da ita Mun rasa hanyar da suka bi ,shi yasa kawai muka dawo” cikin zafin nama Mahir ya zare takobin shi ya fille musu kai ,ya maida takobin yace ” aikin banza aikin wofi!! Har zaku kasa kama wannan yar ficikar abun wanda batafi na murd’e mata wuya ba!!”

( kar fa ku manta masu karatu shima kasawa yayi saboda rashin dabara amma Sam baya ganin gazawar shi sai nasu !)..


      ”  Bazai yiwu ba!! Bazan tab’a yarda cewa Matata Shalini zata aikata abin da kuka ce ba!! Ta gudu da yaran fa kuka ce!!! ” Sarki Abdallah kenan yayi wannan maganar yayinda su kuma iyayen sharrin da munafurci suna zaune murna fal ransu! Zulaikha tayi karaf tace ” dama Mun fad’a maka cewa wannan matar fa ba matar mutunci bane! In ba haka ba kanta farau? Ai ba kanta farau ba! Mu shekara nawa muka lashe bamu Haifa ba ,ko b’atan wata bamuyi ba sai ita zata zo da wani sabon salo Wai har ta haihu a gidan nan ,ni na tabbata ba y’ay’an jinin mu  bane chan dai da su gada” tsulum Mahir ya tsoma baki ” Ai ranka shi dad’e ni ina tunanin wannan Nasir d’in mai jar fuska kamar an gutsuri gauta  ba zai wuce shine uban yaran nan ba domin kuwa shi ne yayi silar tserewar da tayi har in tak’aice maka ma Allah ya baka nasara tare ya gudu da ita ” Ubaidah da ke zaune sai yanzu tace ” toh ai kuna wani abunku duk wannan maganganun da kuke fad’a sarki ba yadda zai yi ba sai Mun gabatar mishi da shaida ” sarki Abdallah ya juyo cikin rud’ani yace ” wanne irin shaida kuma ?” Ubaidah tayi wani munafukin murmushi tace ” kai Mahir ! Shigo da magatakarda !” Basu wani d’au lokaci ba suka shigo tare da magatakarda. Cikin salo irin na munafukai ya shigo ya tsaya hannun shi rik’e da wasu takardu ya bud’e ya fara karantawa , abubuwan da ya karanta kuwa sun yi kama da irin maganganun da su Ubaidah suka yi don nuna cewa y’ay’an ba na sarki bane ,rubutun kuma Sak irin na Sarauniya Shalini hakan ya sake dumar da sarki Abdallah.(Allah sarki bawan Allah bai san cewa zagaye yake da munafukai da kuma azzalumai ba ! K’ira ga y’an uwa mata ! Duk inda ka kai ga Kishi da kyashi da kuma ganin kai toh lallai a karshe zaka zama k’ask’anta ce Marar kima, babu kuma ribar da zaka ci in ka cutar da wanin ka ,Allah yasa mu dace Ameen).” Eheee!!! Ai dama na gaya miki duk da ta gudu zamu iya dumar da Sarki! Kin ga idanuwan shi kuwa !! Wollah ni wannan wasan ya burge ni” Zulaikha kenan ke magana. Ta ci gaba da cewa ” Yawwa! Nikam y’ar uwa yaya akayi kika iya shawo kan wannan d’an taurin kan ? Ina nufin magatakarda ” Ubaidah ta mik’e tsaye tace Hmmmm kina wasa da ni ! Ai wannan duk aikin me sauk’i ne ,kin san yanzu sai ki siye mutum da sulalla ” suka yi shewa harda tafa hannu sannan suka ci gaba da hira…..


          “Nasir ga GUGUWA can yana tahowa kuma gashi mu bamu da gurin fakewa  yanzu yaya zamuyi kenan? ” Nasir yayi shiru yana kallon yadda iskar ta ke zuwa ga shi da k’arfin ta take zuwa ga su kuma a tsakiyar HAMADA kafin suyi wani tunani har GUGUWAR ta iso inda suke ta ‘kank’ame Yaron da ke hannunta ta durk’usa gami da rufe idanuwan ta ,GUGUWAR tayi ta kokawa da goyon da ke bayanta har yayi nasarar fincike wa ,iskar yayi wani irin kururuwa mai tsoratarwa yayi sama da jaririn kafin kace me a take gurin ya washe kamar ba’a yi ba.

          Da gudu ta bi hanyar da GUGUWAR ta nufa tana kiran d’an nata NAWAZ!! NAWAZ!!! Wayyo Allah d’ana Nasir ya nufo inda take yana bata hak’uri yayin da ta rungume NAWAF a jikinta tana ta kuka ” Nasir yanzu yaya zan yi!!? Ka duba yadda GUGUWAR HAMADA ta raba ni da d’ana ! Ina zata kai shi ne!!? Nasir wa zai kula da NAWAZ!! Ki taimaka ki dawo da shi don Allah !! Kar ki raba ni da shi!  A fusace kuma ta tashi tace ” Me yasa ni bazaki d’auke ni ba !! Kika tafi min da d’ana kika rabashi da d’an uwanshi  ganin tana neman sulale wa k’asa yasa Nasir yayi sauri ya rik’e ta gami da d’aura ta a kan doki sannan ya koma ya d’auki NAWAF ya hau dokin shima da hannu biyu kachal yake tuk’in basu wani ‘kara gaba sosai ba ya hango su Mahir da wata k’atuwar runduna :oops:. Shalini ta sauk’o daga kan dokin a gala baice ta rik’e hannun d’an nata tace ” Nasir ku gudu kawai ! Ku tafi kar su zo su kama ku ,kar su maida min d’ana inda zai shiga halin k’angin bauta ! Ka tafi kawai nace maka!” Nasir cikin hawaye yace ” A’a Allah ya baki nasara bazan tab’a barinki a nan ba zasu kama ki kuma na tabbatar cutar da ke za’a yi!” “A’a Nasir!! In kana yiwa Allah ka tafi ,nidai abu d’aya nake buk’ata daga gareka ,shine ka sanar da d’ana mahaifiyar shi tana k’aunar shi,kuma zata kasance mai k’aunar shi har tsawon k’arshen rayuwar ta!” Ta ciro wani sark’a a wuyan ta ta aza a hannun Nawaf tace ga wannan shine kad’ai kyautar da zan iya bashi. Ta ciro d’ayar sarkan tace ” wannan kuma duk sanda kuka yi ido hudu da Nawaz don Allah ka bashi.” Ta ciro wasu warwaraye na gwal ta mik’a wa Nasir tace ka sayar da wannan domin ka kula da kanka da kuma abincin d’ana!”  Cikin kuka Nasir ya kad’a dokin a guje suka yi gabas ba tare da yasan inda suka dosa ba , su Mahir kuwa da sukaga basu iske yaran ba sai suka kamata suka koma da ita chan masarautar SHIMLA………….+GUGUWAR HAMADA da ta tafi da Nawaz bata zame ko ina ba sai bakin wani tafkeken kogi ,Nawaz na kuka kamar ranshi zai fita ga matsananciyar yunwa gashi kuma jariri ne d’anye, kamar kifta ido guguwar ta rikid’e ta dawo siffar zaki mai girman gaske ga uban gashi ,ya nannand’e Nawaz cikin zanen da yake sannan ya d’aura a saman ruwan ,abun mamaki Yaron bai lume cikin ruwan ba sai ma yabi hanyar da ruwan yake bi………..+


            Sarki Abdallah na zaune kan katafariyar kujerar shi na mulki shi kad’ai a fada sai tuno maganganun da suka faru yake yi duk ya birkice zuciyar shi na tafarfasa ,kofin azurfa ne a gaban shi ya yi firo da shi ya fad’i k’asa. Ubaidah da Zulaikha ne ke tahowa ,suna jin wannan ‘karar suka rugo cikin sigar munafukai suna lallashin shi “Haba ranka shi dad’e! Har yanzu kana so ka cemin ka saka ranka a tunanin wancan figaggiyar munafukar?” Ubaidah kenan wanda ta fi kowa sanin salo salo irin na munafurci!!  Kafin sarki ya bata amsa ji sukayi an hankad’o k’ofa kawai ganin mutum sukayi zube a tsakiyar fada duk a galabaice jiki babu kwari Raheena wato (Shalini kenan domin a fada Raheena suke kiranta da shi Shalini sunan yare ne ) ta d’ago kai tana duban su d’aya bayan d’aya ta sani cewa yanzu kam sun riga da sun kwashe duk wani martaba da take da shi a idon sarki Abdallah ,ba tare da ya dubi inda take ba ya ce ” ku jefa matsoraciyar a kurkuku ita da ganin Hasken rana kuma sun yi bankwana!!:oops: kar in ji ance wani ya je ganin ta domin kuwa a yanzu bana mata kallon wani abu face dodanniya, Ashe ke macijiya ce ban sani ba kina ta Sara ta !! Shalini ashe kyaun d’an maciji ne da ke!! Yadda kika tozarta ni kema haka zaki gama rayuwar ki cikin tozarta Raheena!!” Cikin tsananin kuka mai rikitar wa Raheena tace “A’a ranka shi dad’e ya kamata ka saurare ni ! Ka yarda ni bazan tab’a cutar ka ba !! Ni masoyiyar ka ce ta hak’ik’a kum……….kafin ta k’arasa ya dakawa fadawan shi tsawa yace ” Wai me kuke jira ne!!! Ku fitamin da wannan k’azantacciyar abun daga gabana kuma kamar yadda na fad’a muku ! Ba ita babu kallon Hasken rana har abada!! ”


          Kafin ka ce me har sun fice da ita daga fada inda aka kaita wani k’ask’antaccen kurkuku mai duhun gaske wanda ko abinci in an turo mata sai tayi lalume tukunna take samu ,ruwa kuwa sau d’aya ake samu a rana tafin hannu ma baya ganuwa a cikin wannan d’akin.


          Kukan yaro da ta jiyo daga wani ‘bangaren lambun yasa ta mik’e cikin hanzari baiwar da ke b’are mata ayaba ma ta mik’e tana cewa “Allah ya baki nasara anya kuwa kunnen ki ya jiye miki Abunda nake ji yanzu haka?” Matar da ta mik’e d’in wanda da ka ganta kaga jinin sarauta ta ce ” kamar kukan jariri nake ji ” su biyun suka d’unguma suka nufi hanyar da suke jin k’arar……….Da gudunta matar ta k’arasa inda yake wasu ciyawi sun tokare shi hakan ya hana ruwan ci gaba da tafiya da shi, cikin fuska irin na tausayi da kuma nuna tsananin k’auna ga wannan jariri ta saka hannu ta d’auke shi ta rungume bata tsaya wata wata ba ta nufi hanyar fita daga lambun yayinda rigarta na alfarma yake share hanya daga baya. Tana isowa fada ta nufi gurin sarki shima da ya ganta ya mik’e tsaye fuskar shi da fara’a sannan kuma da alamar tambaya, ” ran ka shi dad’e mai martaba adalin sarki!” Kirarin da tayi masa kenan yayinda shima ya k’araso inda take yace ” Mu dad’e tare Sarauniya kyakkyawa ,mai adalci! Yau me kika samo mana ne haka naga kina ta murmushi mara adadi? ” mik’a masa jaririn tayi sannan tace ” a bakin ruwan lambu na sameshi , daga gani tafiyar da yayi mai nisa ce Allah ya baka nasara tunda na samu Wannan Yaron nake ji a jikina kamar adduar mu ce aka amsa mana ,Allah ya bamu d’a bayan wasu lokuta masu tsawo da muka d’auka na hak’uri da juna akan Wannan jarrabawan da Allah ya d’aura mu a kai! Ni ina matuk’ar k’aunar Wannan Yaron har cikin raina ,kana ganin zamu iya ajiyeshi a matsayin d’an mu ?” Sarkin yayi murmushi ya shafa fuskar ta da duk hannayen shi ” me zai hana ne? Nima kaina da ko mintina masu tsayi bai yi a hannu na ba na kamu da k’aunar shi ballantana kuma ke!! Kar ki damu Yaron nan zai iya zama tare da mu!” Wani murmushin jin dad’i tayi karaf d’aya idon ta ya kai ga tafin hannun jaririn taga an yi rubutu kamar tsagun aska an rubuta NAWAZ hakan ya tabbatar musu cewa wannan shine sunan Yaron , NAWAZ ! Sarauniya Ruqaiyah ta sake maimaita sunan fuskarta cike da murmushi yayinda sarki Anwar ya sumbaci Yaron a kumatu. A yini d’aya kachal sun zama kamar wasu mahaukata yadda suke nuna wa Yaron soyayya a take aka masa wanka aka bashi madara kafin kace wani abu har yayi bacci har dare sun kasa fita daga wannan d’akin…….+


(K’ira a gareku mata marasa ganin darajar y’ay’a !!kar fa ku manta wani nema yake yi ko ta wanne irin hali bai samu ba , sai gashi Allah (S.W. T ) ya zab’e ku ya baku ,aikin ku ne ku kula da wannan Amanar da Allah ya baku , ko da kuwa ba naki na cikin ki bane Allah ya tsare mu daga aikata abunda bazai kaimu ga kyakkyawan k’arshe ba! Ameen.)………


            Wani k’aramin k’auye ya iso ga uban rana gashi babu wanda ya sani ,k’auyen ba wani nisa tsakanin shi da masarautar SHIMLA amma Nasir ya tabbatar a wannan k’auyen ma kad’ai zai iya rainon Nawaf kuma ya kula da shi ya kuma d’aura shi a kan tafarki madaidaiciya! Tafiya yake yana k’are ma ko ina kallo, da ‘kyar ya samu ya sayar da wannan gwala-gwalan yayi sa’a kuwa aka siya a kan farashi mai kyau wanda ya tabbatar in kana da wannan babu abunda zai hanaka siyan gida da kuma kama wata Sana’a. Hakan yayi mishi dad’i a rai ya sake rungume Nawaf wanda da ya gaji ko kukan baya iya yi ma sai baccin dole da ya kwashe shi. Wannan k’auyen da ya sauk’a a ciki ba wani bane illa k’auyen DUSHA k’auye ne wanda ba wani girma gareshi ba sai dai kuma mutanen garin akwai su da zuciyar nema ,duk wata Sana’a babu wanda basu yi , kama daga k’ira ,sassak’a ,noma dadai sauran su babu ruwan wani da wani ,su dai abunda suka sani shine su tanadi abun kai wa baka da kuma na sutura ko wanne sati kuwa sukan shiga birnin Shimla domin sayar da kayayyakin su a kasuwannin garin………Masarautar SHIMLA ta kasance masarauta a jerin masarautu ta farko da za’a a saka a jerin manyan masarautu masu  yawa tana da arzik’i maras adadi ga kuma kima da daraja da kuma d’aukaka! Hakan ya samo asali ne tun sarakunan baya da sukayi mulki ,mulki irin na adalci bisa tafarki na addini. A lokacin da aka nad’a sarki Abdallah sarautar wannan masarauta sarkin ya k’udiri niyyar yin abunda magabatan sa suka yi ,amma sai dai kash!! Ya had’u da mata marasa imani wad’anda duk yadda ya kai ga aikata alkhairi to sai sun yi kichin kichin sun hana ko ta wanne hali ne ,cewar su ” ai mu aka bawa sarauta ba’a ce mu zama almabazzarai ba kowa ya kawo kukan shi kace kai dole zaka nuna bajinta gaka kai adali ko?” Wani ikon Allah in suka yi makircin su ba wuya suke shanye masa zuciya. Hmm Ubaidah da Zulaikha kenan!!!+


         Masarautar  SULTANPUR kuwa masarauta ce wanda tsakanin ta da masarautar SHIMLA Nisan tafiya ne na tsawon sati biyu cir a doki kenan in kuwa a rak’umi ne toh tabbas tafiyar ta wata guda ne ,sarki Abdoul-Rahman shine ke mulkin wannan masarautar matar shi guda d’aya ce mai suna Sarauniya Ruqaiyah Kyakkyawar gaske ce ga tausayi , matsalarta d’aya rashin haihuwa ,hakan ya jawo mata zagi iri iri daga gurin y’an uwan mijin wanda hakan yayi sanadiyyar rabuwar kawuna tsakanin sarki Abdoul-Rahman da d’an uwanshi wanda suke uwa d’aya uba d’aya mai suna Muhammad Ja’afar hakan ya saka Muhammad din ya tattara nashi ya bar wannan masarauta ya koma cikin gari da zama a cikin d’aya daga cikin manya manyan gidajen da suke da shi  wanda shima babu abunda ya rabashi da masarautar illa girma da fad’i, nan ya keb’e shi da matar shi  Sadiyyah da d’an su guda d’aya mai suna farouq.


      Wannan kenan……..


Bayan shekaru Ashirin

         Zaune yake a mak’erar sai faman dukan k’arfe yake da guduma rigar jikin shi wanda ruwan Zuma ne duk ya koma bak’i haka ma farar fuskar shi duk ya goga mata bak’in yana zaune ya mik’e k’afa guda dayan kima ya nad’e ta. Ji yayi ana k’iran sa daga nesa ” Nawaf! Nawaf!!! Nawaaaaf!!! Da hanzarin shi ya fito yana gyara zaman sauk’ar wuyan shi ma’ana yana cusata cikin riga sannan ya amsa , wasu maza su uku suna tsaye wad’anda basu wuce Shekarun sa ba suka k’araso inda yake suma de duk kayan nasu Sam ma kal!! “Ya naga baka shirya ba? Kana so mu makara ne? Kasan fa shiga SHIMLA cikin dare babu dad’i me zai hana mu kama hanya yanzu ?” Daya daga cikin su  (Jabeer) ne yayi Wannan maganar murmushi kawai Nawaf yayi yace “toh ku jira ni bari na yi sallama da baba tukunna ,don na riga na kammala shiri na” babu musu suka ja gefe don su jira shi.


      Yana shiga d’akin da suke k’irar ya hango baban nashi yana ta faman narka k’arfe  ya sa hannu ya d’auki wani tsinke zai soka mishi, kamar mai ido ta baya Nasir yayi wuf ya chafke hannun Nawaf suka fara wasa kamar kokawa saida sukayi mai Isarsu kowa yana haki ,sannan Nasir yace “na fad’a maka ai har yanzu baka isa ka kayar da ni ba ” shima Nawaf cikin dariya yace Hahaha!! Ka dai dena cika baki na bar ka ne don naga ka wani tsofe kawai! Amma ba don haka ba da sai na kada ka har k’asa !!” Yana yi yana duban damtsen shi. Baba Nasir yayi murmushi yace ” D’ana !! Sau nawa zan gaya maka cewa shi k’arfi ba a damtse yake ba? A zuciya yake da kuma kwakwalwa ” Nawaf ya d’an Sosa ‘keya yace ” toh baba mu Mun shirya zamu tafi Shimla sai Mun juyo ” Baba Nasir ya dubeshi yace ” d’ana nasan ka da rigima ,ka kula da kanka kada Kaje inda ba’a kaika ba!” Murmushi kawai Nawaf yayi domin in da sabo ya saba kullum sai an masa wannan kashedin. Ya fice ba tare da ya ce ‘kala ba cikin zuciyar shi kuwa cewa yayi ” Baba kana ina zan shiga gari ai babbar masarauta ce sai na zagaya !”Wajen la’asar suka isa Birnin Shimla tun safe da suka taso hakan ma don suna yin gudu ne, kowa yana gudanar da ayyukan gaban shi cikin sauk’i suka zo wucewa Mahir na dukan wani bawan Allah Wai ya shiga hanyar da Sarauniya Ubaidah zata wuce Yaron yayi matuk’ar bawa Nawaf tausayi don daga gani ma bashi da wani galihu hakan yasa Nawaf ya sauk’o daga dokin shi ya nufi inda Mahir yake dukan Yaron yana zuwa ya fizge shi cikin salo na dabara yace “kai idonka yana ina ne zaka bi hanyar wanda ko zaka k’arasa rayuwar ka baza ka kai matsayi irin nata ba?!! Cikin wayo ya wurgar da Yaron gefe yace ” Haba jama’a!!! Ashe baza ku girmama wanda ya girme ku ba?” Ya nuna Mahir ya ci gaba da cewa ” ai wannan da kuke gani Isar sa ta kai ! Da har zaku zo kuna sashi gumi a tsakiyar rana ,ranka shi dad’e ina ganin Sarauniya fa zafin rana zai dameta ,me zai hana ne ta bar wajen nan saboda bai dace da ita ba!” Hakan da Nawaf yayi ya burge Sarauniya Ubaidah da shi kanshi Mahir hakan yasa Mahir ya mai da dorinar da yake dukan Yaron yace ” kai kuma waye?” Nawaf yayi wata y’ar dariya yace ” ni ba kowa bane kasuwanci ke kawo ni nan ina yin K’ira ne na ko wanne irin k’arfe, daga saman dokin da take Sarauniya Ubaidah tace ” daga yau kai da abokan ka duk wani kayan yak’i da masarautar mu ke buk’ata ku zaku dinga k’era ta!” Suka yi mata godiya ba tare da tace komai ba ta cigaba da tafiyar ta yayinda Mahir ya bi bayanta a nashi dokin,har saida suka k’ure sannan ya je ya d’aga Yaron ya bashi ruwa , yana dawo hayyacin sa ya masa godiya akan ceton shi da yayi domin yasan da yanzu wata’kila an fille masa kai ma! Kwanan su uku a cikin garin suka gama sayar da kayayyakin su sannan sukayi haramar komawa……..+


         ” Nawaz!! Ohhhhh Haba d’ana har yanzu kana so kace baka tashi bane? Ta fad’a idonta a kan shi yayinda yake Kwance a kan tangamemen gadon shi na alfarma. Tabbas ta san idon shi biyu kawai yayi likimau ne don bai son fitowa. Bata kuma cewa komai ba ta juya ta fice a d’aki fuskar ta d’auke da murmushi ,ya tashi ya saka rigar shi cikin sauri ya bud’e tagar d’akin shi ya gama lek’a wa babu kowa a chan k’asa sanadiyyar d’akin nashi yana hawa na uku , bai ga kowa ba cikin rashin tsoro da k’warewa a gun rigima ya fita yana daddafa wa a hankali har ya iso jikin wani taga a hankali ya bud’e ya dira ciki yana dariya.


       Kallon kallo suka tsaya yi ma juna daga shi har ita domin kuwa ba wanda yayi tsammanin gani cikin d’akin ya gani ba, wannan budurwa ce wanda bazata wuce shekaru goma sha takwas ba a duniya sanye da doguwar riga wanda daga wuya duk ta cinye haka ma hannayen rigar hannunta guda d’auke da tsintsiya d’ayan kuma d’auke da tasa (bowl) babba cike da kayan marmari duk ta had’a gumi ,rigar ma duk tayi daud’a ,bai daina murmushin da yake yi ba kuma bai ce mata komai ba ya wuce ta gefenta gami da zaro dami (bunch) guda na innibi ya bar d’akin kanta a k’asa kamar munafuka. Kai tsaye ya wuce d’akin cin abinci nan ya tarar da sarki Abdoul-Rahman da Sarauniya Ruqaiyah zaune suna shirin yin Karin kumallo duk ya gaida su cikin girmama wa sannan ya ja kujera ya zauna suka shiga aikin ci.


         AFREEN na zaune cikin akurkin d’akinta duk tunanin Yerima Nawaz ya hanata sakat, duk da shi bai ma san me take yi ba ita kam ta zama duk inda yake tana lab’e domin kuwa babu abunda take sha’awa kamar taga yana magana ,Muryar shi ,yanayin da yake tafiyar da motsin bakin shi , tafiyar shi bugu da k’ari yadda tunanin shi ya hanata sakat duk da ma tasan cewa sama tayiwa yaro nisa saidai yasa ido yayi kallo! Dad’in da take ji yau kuwa shine don yadda taga a karo na farko sun yi ido hud’u sannan har ya d’auki abin ci daga tasan hannun ta sai wani dad’i ya lullub’e ta. Ruwan da taji an kwara mata ne yasa ta mik’e cikin sauri jiki na b’ari tana goge ruwan fuskar nata da hannayenta gashin kanta duk ya jik’e ya mammanne mata a fuska. ” Sannun uwata! Ni ne zan je miki kasuwar ai ko ? Kin zo nan kin wani zauna ,ai ke baki gaji Hutu ba ! Yadda uwarki ta gama rayuwar ta a wahale haka kema zaki gama naki munafuka kawai in an yi magana ki fara hawayen iskanci , ga kud’i can gefen fitila je ki d’auka ki tafi kasuwa ,kinsan anjima kad’an zaki wuce aiki a fada amma don tsabar bak’in ciki don ba ke kike cin kud’in ba bari ki mana bak’in ciki ko?” Afreen ta zaro ido waje tace “kiyi hak’uri !! Don Allah ba haka bane wallahy dama jira nake ki fito sai inji me zan siyo a kasuwar ,matar ta mangare ta da bayan hannu tace fita ki d’auki kud’in!! Kuma saura ki siyo min abunda raina bai so ba kiga abunda zan miki a gidan nan!!”


        Tafiya take jiki duk babu kwari gashi duk a jik’e sai sauri take dokawa tana kuka ,cikin sauri ta wuce su ,shi da abokan shi Ammar da Hassan Nawaz ya gane ta sosai ya kuma ga halin da take ciki duk da bai san yarinyar ba bai kuma san sunan ta ba ,sunan da ya sa mata shine JAMEELAH (KYAKKYAWA) Ammar ya kalleshi yace ” yarima yau kuma me ya samu jameelah ?” Shima mak’e kafad’a yayi yace Allahu ya’alamu!”.   Chan bayan wani dutse ta samu mai ta zauna ta had’a kai da guwiwa tana kuka kamar ranta zai fita,………….


       Kamshin turaren da ta ji ne yasa ta d’ago kanta a hankali domin ta gane wa idonta wanda ya ke wannan uban kamshin wanda tayi imani babu inda ta tab’a jin irin sa face a jikin Yerima Nawaz………

Cikin sauri ta mik’e tsaye kamar yadda suka yi jiya bata tanka masa ba shima haka sai kallon juna da suka tsaya yi ,ya zaro abun share fuska ya mik’a mata ,babu musu ta karb’a ta share hawayen fuskan ta kafin ta bud’e ido ya juya ya tafi, wani dad’i ne ya ziyarci zuciyarta a take ta jingina a jikin wani bishiya da ke kusa da ita,ta kai mintina a haka ba tare da ta bud’e idanuwan ta da ta lumshe ba sai da ta gaji don kanta ta d’auki kwandon da zata yi siyayyar ta wuce hanyar kasuwan ,ta gama kwasan abunda zata kwasa ta wuce gida abunta ranta fal farin ciki……………


        “Baba don Allah muje mana ,bikin sarakuna fa za’ayi a k’asar Ramali kasan ina so inje ko dan naga wannan gimbiyar da maza suke rubibi a kanta ina nufin Gimbiya Saleena yar gidan Sarauniya Jaseena mai mulkin Ramali” dariya kawai baba Nasir yayi ya mik’a masa takobin da ya k’era don ya kaifa shi ,shima da yaga yayi bai sake tanka masa ba akan zancen.+


    Bayan sati biyu…….


        Nawaf na Kwance kan gadon shi na karare yayi rigingine tun safe bai kula baban Nashi ba. Baban ya shigo fuskar shi da fara’a yace ” ka shirya Muma zamu je kallon bikin da za’a yi a Birnin Ramali na sarakuna kaga kuma tafiya ce ta kwana uku cir don haka sai mu tafi tun yau” tsalle Nawaf yayi ya sauk’o daga gadon nashi ya rungume baba Nasir ” bari in sanar da su Ja’afar suma zasu je kaga Mun hadu mu da yawa kenan ko?” Baba Nasir yayi murmushi yace “toh yi maza kace su shirya” hakan kuwa akayi Ja’afar ne kad’ai zai je sauran biyun sun ce basa zuwa saboda haka suka kama hanya su uku  zuwa Ramali……….


       “Nawaz ya kamata ka fito kasan fa tafiyar da d’an rata zai d’auke mu kwana biyu kafin mu isa ,komai an had’a amma ka kasa shiryawa ka fito” tana k’arasawa ya fito yana murmushi duk kowa ya hau dokin shi aka fara tafiya amma shi yana chan baya ,sai hira yake da ASAD (Asad shine zakin nan wanda ya rikid’e daga guguwar hamada) babu wanda yake kallon Asad se Nawaz shi kad’ai ma in yana d’aki wataran ka jishi yana ta dariya ,ko kuma maganganu, tun abun yana damun iyayen nashi har ya zama musu jiki don sunga bazai daina ba ,wataran ma in sun ji shiru sai su tambaye shi ” yau Asad bai zo bane?”. Wannan kenan…………..


Birnin Ramali!!


       Sarakuna da iyalan su ne daban daban suka iso k’asar Ramali daga cikin su kuwa sun had’a da ,Sarki Abdallah da matan sa Ubaidah da Zulaikha, sarki Abdoul-Rahman da Sarauniya Ruqaiyah ,sarkin Kalahari Rizwan d’an sarki Jalalud-deen (daga littafin JASEENA) da matarsa Sarauniya Meenah, da dai sauran sarakuna da attajirai na wannan lokacin. Dukanin su sun samu karb’uwa an basu masauk’i ,cikin attajiran kuwa sun had’a da Muhammad Ja’afar wato k’anin shi sarki Abdoul-Rahman!


       Isowar su k’asar Ramali suka sauk’a a wata rumfa dake cikin kasuwar birnin nan suka yada zango domin dare yayi ,bikin kuwa za’a fara shi ne da hantsi, wanda ya had’a da wasanni irin na motsa jiki ma’ana (Olympic games a turance) wanda dama tun zamanin kaka da kakanni ya samo asali a k’asar Roma!!  ” baba k’asar Ramali na da girma amma naji ance bata kai chan k’asar Kalahari girma ba domin kuwa Kalahari ance ta kai kwatankwacin masarautar Shimla ” murmushi Baba Nasir yayi yace ” wannan haka yake ,amma ai yanzu sarakunan biranen biyu wato Kalahari da Ramali sun d’auki riga da sun zamar da masarautun nasu kamar guda ko baka da tarihin GIMBIYA JASEENA y’ar sarki Hameed na Kalahari?” Ai tarihin wad’annan masarautu biyu suna k’unshe a cikin wannan littafi” murmushi kawai Nawaf yayi hannayen shi duka biyu a kuncin shi ,domin shi a rayuwar shi yana son duk wani abu da ya shafi sarauta kama daga tarihi har rayuwar su…….Gari ya waye, duk da ma sanyi akeyi hakan bai hana rana b’ullo wa ba,sanyin da ake yi a garin ya saka Nawaf d’aukan wani d’an bargo maras nauyi ya rufe kansa da shi hakan yasa baka iya ganin fuskar shi me kyau suna tafe shida abokin shi Jabeer domin tsabar zumud’i ma basu jira baban nasu ba suka kama hanya…


      Tafe suke Jabeer yana ta mishi tad’i amma shi kuwa yana ta faman kallon k’auye a haka har suka k’araso kusa da masarautar ,ginin ya tsaru sosai ga uban tsayi ,yana ta kalle kallen shi ya hango ta tsaye sanye da kaya na alfarma shigarta Sak na Sarauniya Jaseena lokacin da take kogo sai shafa kan wani doki take yi fari sol da shi ,ai anan Nawaf ya ja birki turus !! Baki a bud’e ya zaro ido waje yace ” Allah mai halitta!!” Jabeer da ke neman inda abokin nashi yake kallo yace ” nifa ban ga komai ba Kazo mu tafih kar mu rasa zaman gaba ” Nawaf ya fizge hannun shi da Jabeer ya rik’e yace cikin hasala ” Kai barni mana!!” Ya ruga cikin sand’a ya wuce babu wanda ya ganshi. Tafiya take cikin nutsuwa ,takunta d’ai_d’ai tana wasa da bakin mayafin ta ,shi kuwa sai sand’a yake a bayan ta har ta shige wani d’aki ba tare da ta turo k’ofar ba ta tsaya taje gashin kanta a gaban madubi ai kuwa sai suka yi ido hud’u, a take ta saki wani irin ‘kara wanda yasa duk masu gadin kusa da gurin suka shigo ,kad’an ya rage su chafke shi kuwa da kyar ya sha ai kuwa da Jabeer ya ganshi da gudu shima ya ranci ta kare suka bar gurin ,ganin haka yasa masu gadin suka koma.+


     Ita kuwa Gimbiya Saleena kujera ta ja ta zauna se dariya take yi , ita ba tsoro ya bata ba ,bak’in tukunyan da ta gani a fuskar shi duk yayi dabbare dabbare a fuskar shi ne ya bata tsoro , amma yadda taga suna guje guje da masu gadin ya mugun bata dariya…….

     Nawaf kuwa ko da ya samu ya nutsu a filin wasan babu abunda yake tunani irin kyaun da wannan yarinyar take da ,shi ihun ma dariya ya bashi, Shi kad’ai ya bushe da dariya wanda hakan yasa duk mutanen gurin suka juyo suna kallon shi ,wasu ma dariyar fuskar tashi suke yi shi bai sani ba, Nawaf kenan sarkin shirme


Filin ya cika mak’il baka ganin komai se kawunan mutane kamar tururuwa, manyan masu matsayin kuma sune a saman benen ,sarki Abdoul-Rahman da Sarauniya Ruqaiyah suma suna ciki gefen da Nawaz ke zaune ,daga shi sai sarki Abdallah tun da suka zauna sai kallon kallo suke yi musamman sarki Abdallah ya fi kallon shi hakan ya sa ya tashi domin barin gurin .Sarki Abdallah ya gane saboda me ya tashi shikam ya ji matuk’ar son Yaron a zuciyar shi, kawai murmushi yayi ya juya yaci gaba da kallon wasannin da ake gudanar wa.


         Tafiya yake cikin nutsuwa cikin garin shiru duk an tafi gurin kallon bukukkuna sai mutane d’ad’d’aya suke wuce shi a hanya , takun shi kad’ai zai nuna maka ya dama ya shanye a sanin d’abiun gidan sarauta da kuma yanayin gudanar da rayuwar su, idonshi a kan wasu dawakai da suka tunkaro hanyar da yake kawai suka gwabzu cikin girmama wa ya d’aga wannan tsohon gami da gyara masa zaman mayafin shi ,kafin baba Nasir ya d’ago shi kuma ya juya zai tafi bayan yayi masa Sannu ,Muryar da yaji irin ta Nawaf ne Amma abunda yasa bai damu ba ,yasan Nawaf shi da saka irin wad’annan kayayyakin sai lokacin da gaskiya tayi halin ta ,mahaifin su ya karbeshi a matsayin d’a! Jikin shi ya yi sanyi a Wannan lokaci ya bi Nawaf da kallo har ya b’ace daga gurin ,Yana tafe Asad na biye da shi ko shima bai sani ba!!.


          Washegari da sassafe Nawaf ya fito gari ko karyawa bai yi ba yana tafe yana y’ar wak’ar sa yaji ance ” bawan Allah ka jefar da sark’ar ka!!!” Kafin Nawaf ya juyo Nawaz ya mik’a masa sark’ar ,abunda ya bashi mamaki shine zanen da idonsa ya gane masa ,na suna a tafin hannun Nawaz  yana had’a ido da Nawaz duk suka ja da baya ba tare da sunce komai ba suka juya kowa yaci gaba da harkar shi ,amma zukatan su cike suke fal da tambaya ,ganin yadda kamar tasu ta baci………Da gudu Nawaf ya koma masauk’in su, zubewa yayi a gaban Baba Nasir yana Haki ,cike da mamakin yanayin da yaga d’an nasa a ciki wanda bai tab’a gani ba yasa ya yi saurin mik’e wa zaune yace” me ya faru ne d’ana?? Me ya sameka?ko kayo tsokanan naka da ka saba?” Duk a tare yayi wannan tambayoyin , Nawaf bai iya cewa komai ma sai girgiza kai da yayi alamar A’a, sai da ya samu nutsuwa sannan yace ” Baba ashe de da gaske ne mutum na da mai kama da shi a duniya ? Yau naga wani ,baba kamar mu har ta b’aci sosai ,kuma har wannan rubutun yana da shi a hannun shi ,kasan me baba? Nikam tsoro naji domin kuwa nayi zaton gamo nayi da wani shed’anin aljanni yayi siffata”. Baba Nasir na jin wannan zancen ya mik’e a firgice yace ” Nawaf a ina ka ganshi!! Tashi muje inda yake!!!!!”. Bai ma jira me Nawaf zai ce ba ya fice da wuri ,ganin haka yasa Nawaf ya bi bayanshi babu abunda yake yi Illah tambayar kansa ko meyasa baban nashi ya rikice haka?. Nasir yayi duban duniya bai ga wanda d’an nasa ya k’ira da mai kama da shi ba tuni ya nemi guri ya zube a k’asa ya ciro d’ayan b’arin sark’ar da zai bawa Nawaz yana kallonta yace ” Sarauniya Raheena (Shalini) na miki alk’awari in de naga Nawaz zan had’a shi da d’an uwanshi Nawaz ko ta wanne hali ne in Allah ya yarda !!!” Yana kai wannan ya goge hawayen fuskar shi ,a d’ayan ‘bangaren kuwa zuciyar Nawaf cike take da tambayoyi marasa adadi …………+


        ” Umma gaskiya nake fad’a miki ,kamar mu d’aya ya kamata mu nemeshi kafin mu tafi amma kin k’i  kulani ,umma na rok’eki don Allah ” wani kallo Sarauniya Ruqaiyah ta watsa mishi ,irin wannan kallon idan ya gani yasan ranta ya b’aci don haka ya fice daga d’akin ba tare da ya furta komai ba ,itama bata so hakan ba don bata son ko dai dai da rana d’aya ta b’ata mishi rai ta kasa dena mamakin yadda yazo mata da magana ta share shi domin babu abunda zai nema bata yi mishi ba indai bai fi k’arfin ta ba! Duk Wannan abun a gaban Sarki Abdoul-Rahman aka yi ,shima kasa furta kalma d’aya yayi domin a tunanin shi hakan zai iya jawo rabuwar su da d’an nasu k’waya d’aya tak!!


            B’angaren Nawaf ma de haka ne domin Nasir ya ‘boye masa komai game da wannan Nawaz d’in da yake magana a kai kuma ya umarce shi da su shirya su kama hanya , b’angaren Nawaz kuwa kasancewar shi mai sauk’in kai bai nuna damuwa a fuskar shi ba ,a cewar shi in ma da akwai b’oyayyen alamari zai fito da kanshi .

Tafe take rik’e da tulu da gani neman ruwa zata, sai faman tattare yagaggen rigar ta take yi gashi ana iska da alama ruwan sama za’a yi.” Afreen!! ” daga nesa taji an k’irata ta tsaya chak domin ganin wanda ke kwala mata wannan k’iran haka ,kan dokin shi yake yana kallon ta suna had’a ido ya fad’ad’a murmushin sa ya cigaba da k’arasawa inda take tsaye , tuni ta kau da kai gefe cikin ranta tace ” wannan Wai me yake nema da ni ne? Mutum ba’a sonshi amma kamar maye ya mak’ale min!” Kafin ya iso ta juya taci gaba da tafiya ganin haka sai ya k’ara saurin dokin nashi itama da taga haka ai kuwa ta sake tulun nata ta ruga a guje yana binta a baya duk da haka bata gaza ba!


        Nawaz da iyayen shi suna isowa birnin Sultanpur ya sauk’a daga kan dokin nashi ya mik’a wa wani bafade domin ya shiga ciki da shi , bai bi ta kan iyayen nashi ba ya fice domin yaga gari ,yana tafe sai kalle kalle yake yi shi kwata kwata bikin ma da suka je bai wani burge shi ba, a cikin wannan halin ne Yaji ya ci karo da wata,ga dukkan alamu a tsorace ma take ,yana d’aga kai kuwa suka had’a ido da Afreen wanda tun da ta gane shine ta ‘boye a bayan shi gami da ‘kank’ame rigar shi ,shi kuwa se faman dube dube yake yi wa take wa wannan uban gudun. Wani murtuk’e fuska Nawaz yayi gami da damk’e hannun shi da ya ga ashe Wannan d’an iskan ne farouq yake bin ta yasan dama bazai wuce irin su ba! Farouq ya matso inda suke yana k’are musu kallo yayi wata mahaukaciyar dariya yana zagaya su ,ko girgiza Nawaz bai yiba yayinda farouq ya juya yana fad’in ” hey d’an lambu ! Ka juri zuwa rafi da tulu domin wataran sunan tulun nan fashashshe!! Ya wuce yana dariyar k’eta.+


    Duk da maganar d’an uwan nashi ya Sosa masa rai duk Kalmar d’an lambu tafi ci masa tuwo a kwarya….

” me ya had’a ki da wannan mahaukacin kuma?” Nan Afreen ta fad’a masa abunda ya faru ,sannan ta nuna masa fargabar da take ji in ta koma babu ruwa gashi an fasa mata tulun, Nawaz ya shaida mata cewa babu komai zai taimaka mata


       ” Baba Mun shirya zamu tafi Shimla ” cewar Nawaf kenan yana zaune gefen baba Nasir, ” Toh d’an nan! Ka kula da kanka  Allah ya bada sa’a! ” Ameen baba ” ya amsa gamida juyawa ya fice daga d’akin , nan suka kama hanya su da ayarin su suka nufi birnin SHIMLA!…..


          ” wad’annan makamai gaskiya sun k’eru ga su da haske fiye da na farkon,ga kuma kaifi gaskiya wad’annan sun yi ,yanzu ka biyoni muje inda za’a kai wad’annan makaman ” duk wannan maganar da Mahir ke yi idon Nawaf na kansa har ya k’arasa, ba tare da yace ‘kala ba ya d’aura jakar kayayyakin a saman keken dokin sa ya bi bayan su Mahir ,tafiya kawai yake yi amma babu wani sukuni a tare da shi ,ji yake a take jikinshi ya zama babu kwari wani tafkeken k’ofa suka shiga wanda aka yi ta da wani irin k’arfe sojojin da ke iya bud’e ko wanne b’ari na k’ofar guda ashirin ashirin ne ,idan aka had’a guri d’aya su arba’in kenan, cikin wannan k’ofar wanda wanda yake wajenta yana kallon cikinta kuwa makeken filine ba k’arami ba kuma zagayayye duk wannan filin kuwa shima zagaye yake da wasu mayak’an suna tsaye rik’e da mashi a hannayen su ,tsakiyar filin a lailaye da Gashi kai kace simintin yashi akayi a gurin. Suna tafe saida suka iso tsakiya sai Mahir ya dakawa Nawaz tsawa ,cikin jarumta ya ja dokin ya tsaya, kallon Mahir yayi cike da tuhuma me zaisa yai masa wannan tsawa haka? ” wannan gurin da ka gani kana taka shi sunan ka matacce domin kuwa babban tarko ne a gurin wannan an Gina shi tun zamanin sarki  Affan d’an Abdallah sarakuna biyar kenan kafin sarki Abdallah na yanzu kaga kuwa tarko ne mai cike da hikima mu kanmu bamusan me yake faruwa da mutum ba yayin da ya afka ciki ko aka jefa shi domin na tabbatar ko ma menene da wanda ya shiga in zai samu dama zai so ya dawo don bada labari” Mahir na kai wannan ya bushe da dariya yace ” ina matuk’ar k’aunar wannan tarkon ni da kaina na jefa masu laifuka sun fi a k’irga wasun umarnin Sarauniya Ubaidah ne wasu kuwa na y’ar uwarta Zulaikha! ” shidai Nawaf kai kawai ya jinjina yana mamakin rashin tausayi da bushewar zuciya irin ta Mahir nan ya chanja hanya ya bi gefe gefe suka shige wani sukufin lungu wanda tsabar duhun shi sai da fitilu masu gadin wurin ke tsaye ,k’ofofin wurin da ke Jere basu da tsayi kuma da k’akk’arfan ‘karfen nan aka yi shi mai ubansun nauyi ,suna isa wata kofa yaji wata irin murya wanda daga ji me shi a jigace yake ,nan k’irjin shi ya fara dukan uku uku jin abunda wannan Muryar ke  cewa!!………….

Cikin murya me rawa take cewa ” Nawaz da Nawaf sunanan tafe!! K’ararrawar mutuwar ku ce take kad’awa!! Y’ay’a na na nan zuwa sai sun d’auka min fansa bi-iznillah!! Ku tsoraci dawowar GUGUWAR HAMADA!!! ” abunda take ta fad’a kenan kamar wanda aka ba wa hadda ,Jim yayi a gurin k’irjin shi na dukan goma sha, ya rasa me hakan yake nufi a ranshi yaji yana son ganin wannan tsohuwar. Wani shu’umin murmushi Mahir ya saka sannan ya fara magana cikin Muryar nuna isa ” in dai wannan tsohuwar banzar CE zaka gaji da jin kalaman nata irin na mahaukata, ai yau kimanin shekaru ashirin da wasu watanni kenan tana sarkafe cikin wannan kurkukun ,babu wanda zai ci amanar sarki Abdallah ya kwana lafiya !!” Ko da Mahir ya kai k’arshen maganganun da yake furtawa Nawaf bai dena kallon wannan k’ofar ba ,yana cikin wannan halin ne wasu ma’aikatan gurin suka shigo da tukunyaye a hannu kowanne d’auke da abinci cikin salon wulak’anci suke wurga musu gayan tuwon cikin d’akin sannan su tura musu kwanon miyar ma a wulak’ance ,da kyar na ciki suke lalumar abincin domin wani ma ya shekara arba’in babu haske balle hira da mutum d’an uwansa, haka Nawaf ya bisu da kallo har suka b’ace bai d’auke idanuwan sa da suka ciko da kwalla ba tare da sun gangaro ba! Maganar matar ne ya sake janyo hankalin shi ya maida duban shi ga k’ofar ” Shin ban fad’a muku ba ? Cewa d’ana yana nan zuwa?!! Toh gashinan lallai lokaci kad’an ya rage muku azzalumai!! ” duk kalaman ta sun dagula masa tunani, ji yayi an ja hannun shi sun nufi wata y’ar siriryar hanya wanda k’arshen ta wata k’atuwar k’ofa ce itama ,kafin su k’arasa gurin kuwa har an bud’e k’ofar tun daga gurin Nawaf ya fara hango kayan yak’i iri iri masu ban al’ajabi domin wasun ma bai tab’a ganin irin su ba, wata Kyakkyawar takobi ne a soke cikin ‘kasa a tsakiyar d’akin sai d’auke ido take yi  ita kad’ai, ajiye kayan yak’in da suka shigo da shi yayi sannan ya dubi Mahir yace ” wannan fa?” Mahir yace wannan tun zamanin sarki na biyu a wannan masarautar mai suna SARKI NAWAZ DAN JAMAL aka k’era ta shi kad’ai ne ya iya d’aga wannan takobin tun bayan rasuwar sa kuma babu wanda ya iya d’aga ta yanda ya ajiye ta haka take ko girgiza bata tab’a yi ba. Zaro ido Nawaf yayi yace lallai Wannan takobin yana tattare da tarihi.+


          Shafa takobin yake yi a hankali Mahir kuwa ya tsaya kallon shi, ko da yayi yunkurin d’aga takobin kuwa sai karaf ya jita a hannun shi ,ga mamakin shi ko nauyi bai ji ba ,cike da mamakin hakan Mahir ya ce “yaya akayi haka! Yafi sau d’ari ina jarraba d’aga wannan takobin na kasa kamar yadda yau kusan shekaru d’ari da hamsin babu wanda ya ko girgiza wannan takobin ,babu shakka zan sanar da me martaba

Zaro idanuwa Nawaf yayi kafin yayi magana har Mahir ya fice daga gurin gami da yin umarni a sojojin gurin da cewar kar su bari Nawaf ya fito. Nawaf na yunkurin bin shi kenan yaji an rufe k’ofar ya koma ya tsaya juye juye yana neman gurin fita Allah da ikon shi ya hango wata yar taga chan sama da kyar ya tattaka ya dira ta wajen ya kuma manta bai jefar da wannan takobin ba yabi wata y’ar hanya ta kaishi kasuwa nan suka tattare kayayyakin su shida Jabeer suka nufi hanyar komawa DUSHA kafin kace wani abu har sun b’ace………


          Gudu kawai suke yi ba k’akk’autawa basu ankara ba sukaji k’arar kibiyoyi suna ta sauk’o wa ,k’ara gudun dokin nasu sukayi ba tare da sun juya ba ba kuma tareda sun san inda suka nufa ba ,sojojin SHIMLA har sun gaji sun juya su basu ma sani ba ,saida suka tabbata babu masu bin su sannan suka rage gudu. Wani daji suka hango daga chan nesa daga gani guri ne mai Ni’ima dama sun gaji ga k’ishirwa haka a daddafe suka k’arasa dajin nan suka yada zango domin gurin a wadace yake da ruwa mai gudana da kuma kayan itatuwa……….


       ” Wannan umarni na ne!! Ku je ku nemi duk inda wannan yaran suka fito a kawo min su da ransu, in ba haka ba duk sai kun raina kanku!! ” sarki Abdallah kenan yayi wannan maganar cikin hasala ba tare da ya juyo daga basu bayan da yayi ba ,kafin ya juyo har sun fice daga fada.

      Ubaidah da ke zaune ta mik’e fuska a murtuk’e tace ” Allah ya baka nasara! Yaya za’ayi ace Wai yaro da bai wuce shekaru ashirin ba ya d’aga wannan takobin wanda yau kimanin shekaru dubu d’ari da hamsin babu wani jinin sarauta ko mai mulki na wannan masarautar da ya iya d’agawa bayan sai wani wanda ba ma a nan birnin yake da zama ba zai d’aga ?? ” sarki Abdallah ya daka mata tsawa har saida ta tsorata, ya umarce ta da ta fice ta bashi guri babu musu ta fice simi simi da rawar jiki. Ko da ta tafi d’aki kasa zama tayi se sak’e sak’e take yi tana gudun kar abunda take tunani ya zamo gaskiya ,kar Nawaf ma’keri ya zama Nawaf d’an sarki! Da wuri kuma ta kawad da kanta gefe gami da gusar da wannan tunanin amma Sam hankalin ta bai kwanta ba. Nan ta yanke shawarar kashe magatakarda domin gudun kar wataran gaskiya ta fito ya fallasa ta ………….+


        Su Mahir kuwa kasuwa suka nufa suka samu ayarin da su Jabeer suka biyo nan suka sanar dasu daga inda su Nawaf suke ,ba tare da b’ata lokaci ba Mahir yaja ragamar tafiyar tare da mayak’an Shimla kusan arba’in zuwa k’auyen DUSHA.

Kowa yana harkokin gabanshi babu wani tashin hankali kawai su Mahir suka fara cinna ma bukkokin su wuta hakan yasa mazan da matan kowa ya fito wasu sun rasa hanyar Fitowan ma wasu y’ay’an su na ciki ga wuta yana ci ,gari ya rud’e kowa sai gudu ,su kuwa su Mahir duk wanda suka gani sai su fille masa kai ko kuma su soke shi da wuk’a ,wad’anda suka rage d’in kuma suka tarasu guri d’aya ciki harda baba Nasir wanda tun zuwan su ya gane fuskar Mahir wanda bazai tab’a mantawa ba,saidai shi Mahir bai gane shi ba sanadiyyar sumar da ta lullub’e masa fuska.

       ” ko ku fito da Yaron ku guda d’aya tak! Nawaf ko kuma mu hallaka ku baki daya kuma babu wanda zai rayu !! Ina yake nace??!!” Duk mutanen jiki na rawa suka amsa da” bamu sani ba ” wani mugun dariya ya bushe da shi ya ratsa cikin mutanen yana nazarin fuskokin su. Nasir bai ankara ba yaji an chafko shi anyi wurgi da shi ” abokina nasan zakayi zaton bazan gane ka ba ko?” Ya sake k’afa da Nasir yace ” ina wannan matsiyacin Yaron!!! ?” Nasir bai yi magana ba illa miyau da ya tofa wa Mahir a fuska abun ya bawa Mahir haushi ya sake mangare shi har saida bakin shi ya fashe haka suka d’aure shi kamar wani kaya suka haye dawakan su suna ta janshi cikin zafin rana ga k’ishi har suka koma SHIMLA.+


         A birkice Nawaf da Nawaz suka shigo k’auyen nasu ,babu komai sai k’onannun bukkokin da kuma matattun mutane wad’anda suka rage basu wuce su ashirin ba Galibi ma yara ne wad’anda aka kashe iyayen su, jaririya guda d’aya ce dake ta faman zabga kuka hakan yasa Nawaf ya nufi inda take domin kula da ita ,gaba d’aya ya kasa tunanin komai yaran ma da sauran mutanen suka nufoshi gami da rungume shi domin dama chan sun d’auke shi kamar wani jigo ne a rayuwar su tabbas yau ya fahimci hakan. Nan suka kwashe labarin abunda ya faru daga farko har karshe suka sanar da shi ,Jabeer kam tuni ya sare ma ganin yadda komai ya ruguje cikin rana d’aya tak! Nawaf kuwa ya d’auki laifin a kansa “saboda ni ne haka ta faru!” Abunda ya fad’a kenan har ya kai gwiwar sa ‘kasa, Jabeer ne ya dafa kafad’ar sa yace ” kar kace haka abokina ,duk abunda ya faru kaddara ce an riga an rubuta shi dole sai ya faru saboda haka yanzu tunanin abin yi ,ma’ana mafita zamuyi tun kafin dare yay mana in ba haka ba zasu iya cutar da sauran mu domin na tabbata zasu dawo saboda haka mu tattara abunda ya rage mana mu bar wannan gurin ,wata’kila ma samu taimako daga guri Sarauniya mai adalci ina nufin Sarauniya JASEENA y’ar sarki Hameed!! ”

   


         Nawaf ya dubeshi yace “toh in Mun tafi kuma baba na fa? Na tabbatar zai yi tsammanin zuwana domin kuwa bai haifi lalataccen namiji ba ,kudai ku tafi birnin Ramali ni zan koma SHIMLA” Jabeer yayi Jim yace ” kar fa ka manta sarkin yawa ya fi sarkin k’arfi dole ka biyo mu Ramali nasan Sarauniya Jaseena zata karb’a mana y’anci ! ” ba musu ya tashi suka fara had’a abubuwan da zasu iya suka saka yaran a keken doki me rumfa da kayayyakin abinci da zasu buk’ata sauran manyan kuma suka hau dawakai suka yi haramar Ramali…………


        “Nawaz na fad’a maka kai d’an mu ne ko baka sane da cewa akwai rashin jituwa tsakanin iyayen farouq da mu ne ? Ai shi yasa zai dinga yi maka wad’annan kalaman don de kawai ranka yayi bak’i ne!” Maganar da Sarauniya Ruqaiyah ta fad’a kenan wanda hakan yayi daidai da shigowar sarki Abdoul-Rahman.” Kar ki b’ata wa kanki lokaci ya Ruqaiyah! Gaskiya ne tayi lokacin ta kar fa ki manta magana ko a rami ka yi ka binne wataran sai an ji ,yanzu babu wani batun ‘boye ‘boye domin kuwa in Mun yi mishi haka kamar bamu masa adalci bane ,a misali in duk Mun fad’i matattu a nan ina zai sa kansa ,gashi Mun ‘boye masa gaskiya ko shi wanene Ruqaiyah ina so ki fahimce ni sosai ‘boye masa gaskiya bata da wani amfani a garemu domin kuwa ko an sanar dashi ko ba’a sanar da shi ba akwai kundin tarihi na wannan masarauta wanda babu abunda aka ‘boye a ciki

Nawaz gaba d’aya tunanin shi ya dagule ” ashe dama zancen farouq gaskiya ne? Toh idan ni ba d’an ku bane waye ni ,daga ina nake kuma su waye asalin iyaye na??” Duk lokaci guda ya runtumo wad’annan tambayoyi. Murmushi Sarauniya Ruqaiyah tayi mai cike da takaici yau zata fad’i abunda ta dad’e tana b’oyewa domin wannan Yaron da ya riga ya zama tamkar jinin ta ya zauna tare dasu har abada, ” Tabbas babu d’aya daga cikin tambayoyin da kayi min da zan iya baka amsar su ,Nawaz ban san ko d’aya daga tambayoyin da kayi ba kuma ban yi tunanin zan san su ba ,abunda na sani guda d’aya ne tak wannan bai wuce samunka da mukayi cikin lambu ba a bakin ruwa sai rabza kuka kake yi ,tun kana jariri da bai wuce sati biyu ba da haihuwa, k’aunar ka ne da kuma tsananin Tausayin ka yasa ni d’aukan ka a matsayin d’an da muka Haifa ,kasantuwar bamu tab’a samun haihuwa ba nida mijina,haka zalika Mun yi iyakar bakin k’ok’arin mu don ganin baka tozarta ba kuma hakan ne ya faru ,sai daga b’angare d’aya tak! Aka samu matsala wanda wannan b’angare sun kasance sune manyan mak’iyan mijina da duk abunda ya mallaka. D’ana bazan hanaka yanke duk wani hukunci da kayi niyyar yankewa ba ,amma inason ka sani har in koma ga Allah babu wani mahalukin da zai ce kai ba d’ana bane in barshi lafiya ,kai d’an mu ne Nawaz kuma duk abunda ke cikin wannan masarauta taka ce! Amma ina rok’on ka abu guda d’aya tak! Ko da ka samu asalin iyayen ka don Allah ka ci gaba da kirana da mahaifiyar ka wannan kad’ai zaka min na samu nutsuwa.” Umma kar ki damu ,bazan tab’a daina k’aunar ki ba kuma in Allah ya yarda zan ci gaba da kallonku a matsayin mahaifa na na asali domin kun yi min abunda nawa iyayen suka gaza duk da ma ban san dalili ba” rungume shi sukayi dukan su kowa na hawaye cikin zuciyar su kuwa kowa da abunda yake sak’a wa…..+


         Kwanan su uku cir suka iso birnin Ramali ,nan suka nemi ganawa da Sarauniya Jaseena, ba tare da b’ata lokaci ba Sarauniya mai adalci ta bada daman ayi musu iso fada su kuma yaran da sauran wad’anda suka jikkata aka basu masauk’i, kayan sawa da kuma abinci.

        Zaune take kan wata kujera gefen ta Sarauniya jaseena ce wanda tayi shiru wajen kimanin mintina hud’u kenan bata ce komai ba bayan ta saurari jawabin su Nawaf, Gimbiya Saleena kenan sanye da jar doguwar riga mai ratsin zinare ta yi kyau sosai ,Nawaf kawai take kallo tabbas ta gane shi sosai suna had’a ido ta kau da kai tana murmushi itadai wannan bak’in daud’a da ke fuskar shi ita ke bata dariya ba kad’an ba.


      ” Babu wani matsala koda ban d’auki wani mataki domin musguna muku da aka yi ba zan d’auka don rayukan da aka hallaka, wannan yana d’aya daga cikin d’abiun azzaluman sarakuna ,amma zan yi mamaki ,koko ince nayi mamaki yadda sarki Abdallah zai bari haka ta faru domin mutum ne Marar matsala gashi kuma kamili mai adalci ,ban san me ya faru ba”. Nawaf ya yi wa Sarauniya Jaseena godiya da irin tarbar da tayi musu. Murmushi tayi ta dubi Saleena da ke ta faman murmushi ta k’ura wa Nawaf ido kawai ta girgiza kai ta fice tana dariya, jin motsin ta ne yasa Saleena ma ta mik’e har ta kusa tuntube  duk wannan kallo fa a bak’in fuskar Nawaf take yi wa ,shi kuwa gogan naka ya zata ya burge ne sai dad’a fad’ad’a murmushin sa yake yi…………….

Abincin gaban shi har yayi sanyi bai ma ko kalli inda yake ba yayi shiru kamar me d’aukar darasi,hakan yayi daidai da isowar Afreen cikin d’akin cin abinci domin a tunanin ta har ya gama ci ya bar wajen, turus tayi tana duban shi cikin nutsuwa har na tsawon dak’ik’ai sannan ta k’arasa inda yake ta tabbatar koma me yake tunawa yayi nisa ,tayi ta dariya sannan ta saka hannu cikin wani kwanon ruwa ta yarfa masa a fuska bai san lokacin da ya mik’e tsaye ba ba shiri nan ta kwashe da dariya tace ” idan kaga zaki yayi shiru duk da ga namun dawa kewaye da shi bai kuma lura da su ba balle har ya kai musu farmak’i toh lallai akwai abu a k’asa ” murmushi yayi murya k’asa k’asa yace ” toh sarkin iya surutu me kika zo yi a nan?”  Aiki mana yanzu ma zuwa nayi in duba ko ka gama na tattare ” Haba jameelah ban hanaki kiyi aiki a nan ba? Ni na baki wannan y’ancin saboda kin chanchanta” murmushi tayi ta sake yarfa masa ruwa a fuska nan ya d’auki ruwan ya bita da shi sai zagaya d’akin cin abincin suke yi gyaran Muryar da Sarauniya Ruqaiyah tayi ne yasa duk suka daskare cikin k’arfin hali Afreen ta fara tattare kwanukan abincin ta fice simi simi kai a k’asa yayinda shi kuma ya nemi guri ya zauna , a hankali take takun ta cikin k’asaita ta k’araso inda yake itama ta zauna ,tabbas taji dad’in ganin walwalar shi kuma bai dameta ba Wai don da waye d’an nata yake soyayya in dai har hankalin shi zai kwanta, ” Tashi yayi shima zai fita ,cikin sauri tace ” ina zaka je haka?” Babu ! Umm dama zamu d’an fita wajen gari ne nida Afreen ,tace bata tab’a ganin hamada ba a rayuwar ta ,shine zan kaita gurin” murmushi Sarauniya tayi sannan tace ” Amma fa kar kuje da nisa sosai * kai kawai ya gyad’a mata yace toh”.+


               Tafe suke kowanne a saman doki sai hirarsu suke tayi ,suna isa wajen gari kawai Nawaz ya dubi Afreen yace ” Jameelah rufe idonki babu musu ta rufe ,ko da ya umarceta ta bud’e gurin da take ya matuk’ar bata mamaki ,(Kar fa ku manta masu karatu Nawaz yana tare da Asad) Zunzurutun hamada ne a gurin iska na tashi a hankali ,nan ta durk’usa tana shafa yashin gurin sai dariya take kamar sintacciya. Haka suka ci gaba da tafiya  cikin hamadar sai wasannin su suke in ka gansu gwanin sha’awa Kwatsam k’afar Afreen ta sark’e da wani igiya take inda take tsaye ya Burma tayi ciki gami da sa wani uban qara a take shima Nawaz ya bi bayanta ya afka cikin wannan makeken ramin wanda ya ta waje ya rufe kansa tamkar babu abunda ya tab’a Burma shi balle ya afka ciki:

Tsintar kansu sukayi cikin wani tafkeken d’aki cike da wasu murtuqa murtuqan macizai Afreen da ke Zaune a gurin kasa motsawa tayi jiki na b’ari a take ta sulale a wurin sumammiya ,yayinda macizan suka fara nannand’e ta ,cikin dabara Nawaz ya fara kwallo da macizan hakan ya bashi damar samun hanyar da zai k’arasa inda Afreen take a sume ,ya sunkuceta a kafad’a sannan ya nufi hanyar wata k’ofa da ya hango ,bai damu da farmak’i da macizan suke kawowa ba har ya k’ure daga wannan d’akin ko me ya taka a bakin k’ofar oho ! Kawai se k’ofar me macizai ta rufe da kanta ganin haka yasa ya bi hanyar da yaga itace kad’ai hanyar da ya gani a gurin..+


           Wasu k’ofofi ya iso duk a rufe suke ,ga kuma masu gadin ko wanne k’ofa a tsaye kamar gumaka, a gaban shi aka shigo da wani dattijo sai faman kokawa suke yi da wad’anda suka rik’e shi ,har wannan lokacin Afreen na kafad’ar shi ,suna had’a ido da Dattijon kawai se yace ”  Nawaz!! Nawaz !! Kai ne ?? Amma dukan da mutanen ke masa ya mugun nak’asa shi suka wurga shi cikin wani d’aki wanda da kyar ma k’ofar ta bud’e don da gani an dad’e sosai wannan k’ofar ba’a waiwaye ta ba har gindin ta ya zama mafakar k’ananan kwari. Hankalin masu gadin yayi kan Nasir basu san lokacin da Nawaz ya shige ba ya fita daga gurin yana tuna irin Muryar da yaji Nasir yayi amfani da shi ,kamar ya tab’a ji a wani waje, sai da ya fice ya tuna cewa shine tsohon da ya buge a birnin Ramali kuma sark’ar dake lilo a wuyan tsohon itace irin wanda ya gani ta fad’i daga jikin wannan me kama da shi d’in nan ,gashi kuma tsohon harya san sunan shi ,abun ya matuk’ar kulle mar kai sosai ba kad’an ba amma a yanzu ta lafiyar masoyiyarshi yake yi ba wannan ba shi yasa ya bi wata y’ar k’ofa ya fice cikin kwanciyar hankali yana k’arewa garin kallo ruwa ya hango a wata rijiya wanda ta cika taf har bakinta ,cikin hanzari ya nufi gurin ya shimfide Afreen a k’asa yasa abun d’iban ruwan ya kamfato sannan ya yarfa mata, a firgice ta tashi ta zauna tana maida numfashi gamida nuna razanarta a fili ta rungume shi jikinta na rawa, murmushi kawai yayi yace ” matsoraciya babu komai yanzu tashi mu tafi ” babu musu ta mik’e suka fara zagaya gari da dai sukaga sun rasa hanya sai suka yanke shawarar tambaya ko zasu samu sunan garin da suke ,ai kuwa suna had’a ido da bafaden da zai tambaya d’in bud’ar bakin shi yace ” kai !! Gashi can !! Ku bisu!!! ” koda Nawaz yaji haka sai ya fisgi hannun Afreen da gudu su kuma sojojin suka bi bayan su a guje ,su tsallake chan su haura nan har cikin kasuwar garin ,duk Afreen ta galabaita da kyar take numfashi se haki take ganin haka ya wafce wata butar ruwa daga hannun wani yana shirin shan ruwa ya damk’a mata tana gudu tana sha rabi na zubewa, da kyar suka samu wata y’ar k’ofa suka rufta ciki se haki suke yi ,Nawaz yana lek’en su har suka wuce yayinda Afreen ta yi lakwaf a jikin Nawaz sai sauk’ar da numfashi take yi…………….


             “Waye nan?” Tambayar da aka mishi kenan bayan y’an mintina da aka wurga shi a wannan kurkuku mai duhun. Ba tare da ya sake magana ba taci gaba da maganganun ta irin na kullum kamar yadda ta saba. “NAWAZ DA NAWAF SUNA NAN TAFE!! K’ARARRAWAR MUTUWAR KU CE TAKE KAD’AWA!! Y’AY’ANA NA NAN TAFE SAI SUN D’AUKAR MIN FANSA!!!!……..KU TSORACI DAWOWAR GUGUWAR HAMADA!!!!!………..


     Maganar da ta doki kunnen Nasir kenan kuma mai ambaton wannan maganganun bata daina fad’a ba se maimaita wa take yi kamar me karatu. Cikin murya me rawa da kuma hawaye Nasir yace ” Sarauniya Shalini!! Rrrrr….. AH I…NNA!!!!!………….

Da rarrafe ta k’araso kusa da inda taji Muryar Nasir na tashi ta zauna duk gab’ob’in jikin ta na karkarwa a hankali tace ” kai ne? Kaine ko mafarki nake yi ? Shekaru sama da ashirin ba wasa bane ! Nasir Kaine ko murya ce ,na shiga rud’ani ,na yi hauka mara adadi ,na zauce ,naci datti iri iri haske rabona da ganin shi tun daga bakin wannan ginin k’arfen da ka gani ban sake saka d’an Adam ko dabba a idona ba, Nasir nayi kuka mara adadi da naji abunda wanda yafi soyuwa a zuciyata yace a kaina, na kwana cikin wahala na tashi a wahale ,Nasir ban yi tsammanin zan iya kallo da wad’annan idanuwan nawa ba domin na saba da duhu ,ni ba a mace ba ni ba a raye ba,Nasir na rabu da y’an uwana dad’in dad’awa y’ay’a da na tsugunna na haife su ,ina ma ni na shayar da kayana! Da sunga gata iya gata !! Ka gaya min Nasir ina Nawaf yake ne! Nasir baka had’u da Nawaz d’ina ba? Nasir ka amsamin in ji sanyi a raina ! Wannan shine karo na farko da naji motsin d’an Adam a cikin wannan akurkin…

      “Naga Nawaz !! Raheena naga Nawaz yanzun anan kuma Nawaf yana nan zuwa ,na tabbatar zasu had’u!! Ina da yak’inin komai ya kusa zuwa k’arshe! Gaskiya zatayi halinta a karo na farko!”………+


            “Gimbiya Saleena dole in tafi neman babana ,shi kad’ai ya rage min ,bani da kowa in har na bari sukayi masa illa bazan tab’a iya yafewa kaina ba domin kuwa duk abunda ya faru dalili na ne ! Ni da tab’a musu abun su ni na d’auko wannan takobin mai cike da d’umbin tarihi a k’asar Shimla kinga kuwa ni ya kamata in d’auki duk wani horo da zasu zartar a kan baba ba shi ba!” Toh amma fa Nawaf akwai had’ari a abunda zaka aikata ,bai kamata ka tafi kai d’aya ba ,kayi hak’uri nasan Sarauniya tana iya k’ok’arin ta na neman hanya mafi sauk’i ” murmushi kawai Nawaf yayi jefi jefi yana jefa duwatsu cikin ruwan da ke tsakiyar masarautar a zagaye da gini sannan kuma yana da hanya wanda ruwan ke gudana. Mik’ewa yayi ya tsaya a saman ginin wanda tsakanin shi da ruwan ko da igiya aka zira zai kai mintina hud’u kafin ya isa ga ruwan amma haka ya sa kai ya afka cikin ruwan ,ganin hakan ya burgeta itama ta cire abayar ta da ta d’aura a saman kayan ta afka cikin ruwan nan suka fara watsawa junan su ruwa suna ta dariya ,lokaci guda wani farin ciki ya ziyarci Nawaf…….


       Duk abunda suke yi Sarauniya Jaseena tana tsaye saman benen d’akin ta tana k’are musu kallo ,bata tab’a ganin irin wannan nishad’i k’arara a fuskar Saleena ba ,hakan ya burgeta sosai, ba kad’an ba don tuni ita har ta kammala binciken da zatayi a kan ko waye Nawaf ! Duk wasu abubuwan da take buk’atar sani ta ji su daga bakin magatakarda na k’asar SHIMLA da su Mahir suka kusa hallaka wa , ya tsinci kanshi da nadamar abunda ya aikata yayinda wasu y’an kasuwa daga nan suka tsince shi a hanyar su ta dawowa ,ya kuma buk’aci ya ga Sarauniya wannan shine yadda akayi. Kuma duk shaidun da ya kamata ya gabatar suna chan k’asar SHIMLA wannan shine kad’ai abubuwan da take buk’ata!……..


       Juyawa tayi ta koma fadarta yayinda tana isa ta iske mijinta sarki Hydar ya dawo daga wata dad’ad’d’iyar tafiyar da yayi na kusan watanni shida, nan sabuwar babi ya bud’e suka shiga hirar yaushe gamo cikin soyayya da kewar juna……..Cikin wannan k’ofa da suka shiga gida ne madaidaici babu komai a ciki sai wata shimfid’a irin ta fatar dabba da ke shimfide a gefe ,wani gefen kuma akwai wata k’ofar ita kuma a rufe take, a hankali ya tura k’ofar yana ta nazarin d’akin Afreen kuwa na faman share yanar gizo da ya kama hannun ta a garin karkad’e wa tana ja da baya ta bugi wata y’ar karfe ai kuwa sai k’asan d’akin ya bud’e Nawaz da ke tsakiyar gurin ya afka ciki a firgice ta juya taga ashe abu ta dannan a wani b’angare ta hango matakala ai kuwa da gudu ta isa gurin tana k’iran sunan shi “Nawaf !!” Cike da firgici. Tsaye ta ganshi yana karkad’e jikin shi da yasha k’ura abubuwa ne iri iri a cikin d’akin wanda ya had’a da kundin tarihin birnin SHIMLA Afreen ta karkad’e takardan da niyyar d’aga wa amma ta kasa ta juya tana kallon Nawaz da yake ta fama da wata y’ar jaka wanda wasu takardu ne a jiki jakar tayi masa kyau hakan yasa shi ya rataya jakar ,Afreen tace ” Kazo kaga wannan babban takardan “!! Da saurin shi ya k’arasa inda take tsaye suka bud’e ya sauk’e k’asa suka fara karantawa abin mamaki Nawaz ya fara ganin abubuwa irin wad’anda suka faru a baya ,tuni ya rik’e kanshi yana rufe idanuwan shi a hankali ,gani yake kamar a mafarki kafin kace me har ya zube a gurin ,Anan Afreen ta shiga matuk’ar firgici hankalin ta yakai k’ololuwa wajen tashi gashi ko ta fita za’a iya ganeta saboda haka ta kifa kai a cikin shi tana ta zubar da kwalla har bacci b’arawo yayi awon gaba da ita a haka……………+


     ” Nifa abun nan ya fara bani tsoro! Kace zai dawo amma har yanzu shiru, nasan cewa Nawaz ba yaro bane amma kuma komai zai iya faruwa, su wad’anda suke tare da shi kuma sunce kawai suma neman shi sukayi suka rasa ,ba shi ba Afreen! Ba dole in saka a raina ba don Allah? Shi kad’ai nake da ,shekaru ashirin da y’an kai ba wasa bane mai martaba!!” Sarauniya Ruqaiyah kenan tayi wad’annan kalamai tana me ture kwanon abincin da aka aza mata a gabanta, hankalin sarki Abdoul-Rahman yakai k’ololuwa wajen tashi ,nan yasa aka baza soji aka shiga neman su shida Afreen ,duk da Afreen y’ar aikin fada ne amma Sarauniya Ruqaiyah tana jinta sosai har cikin ranta saboda yanda taga d’an ta cikin farin ciki yayinda yake tare da Afreen hakan yayi matuk’ar tada mata hankali ,har dare yayi babu labarin su ,rannan kam in ance Ruqaiyah tayi bacci toh an yi karya domin kuwa komawa tayi yadda kasan jaririya haka ma a B’angaren Abdoul-Rahman shima de haka ta kasance……….


     guguwar hamada.


    Hasken rana ne ya hasko inda suke Kwance a hankali Nawaz ke bud’e idanuwan shi yana kare Hasken da ya ke d’auke masa iso da hannayen shi jin motsin numfashi yayi yawa ya sa ta farka daga nannauyan baccin da ya d’ebe ta ,tana tashi shima ya tashi zaune yana ta k’ok’arin tuno irin mafarke mafarken da yayi, wannan jakar da ya rataya ya fara laluma a firgice, Afreen dai nata ido.

       Cikin sassanyar murya yace ” Ramali..Ramali… Afreen wannan jakar Ramali zamu kai ta dole mu kai ta zuwa chan!!” Toh ta yaya zamu fita daga nan bayan kasan cewa neman mu ake RUWA A JALLO!! Kuma na tabbatar suna nan zagaye da mu ,sannan zai d’auke mu kwana hud’u kafin mu isa Ramali ” Nawaz yayi shiru yana kallon ta har ta idar da maganganun da zata yi sai yace ” ASAD!! Asad zai kaimu Ramali” yana fad’in haka Asad ya bayyana bayan wata y’ar k’aramar k’ura da ta baibaye d’akin wannan shine karo na farko da Afreen ta ga Asad d’in Nawaz ido da ido, a hankali kuma yake sake rikid’e wa zuwa wani kyakkyawan saurayi yace ” Yerima Nawaz nayi kewarku sosai” yana maganar ne fuskar shi mai kyalli d’auke da murmushi ,Nawaz ya nufi inda yake ya rungume shi yace ” baka tab’a barin inda nake ba don na sha wahala ,muna cikin yanayin jin dad’i muka afka wani rami ,ni kaina bazan iya k’iyasce adadin lokacin da muka d’auka kafin mu iso ‘kasa ba ,muka fad’a d’aki mai maciz …….. ” Asad yayi saurin katse shi da ” duk nasan komai  Yerima yanzu kar mu b’ata lokaci ya kamata mu tafi chan Ramali koma menene zakaji…………


            A firgice ya farka yana ta faman dube dube duk gumi ya jik’a shi jagaf kamar Marar gaskiya sai murje ido yake yi ,a cikin wannan yanayin ne Gimbiya Saleena ta bud’e k’ofa ta shigo ,ganin yanayin da yake ciki duk ta rikice ta nemo Sarauniya Jaseena suka shigo tare ,har lokacin bai wani dawo hankalin shi ba Jaseena tayi saurin durk’usa wa a gaban shi ta gama nazarin shi sannan ta umarci wata daga cikin ma’aikatan da a kawo mishi ruwa ya sha ,haka kuwa akayi ,yana farfado wa yace” suna zuwa !! Suna zuwa !! Ban san shi ba amma ina ganin wani mai kama da ni a wasu mafarkai na ,kamar yadda na ganshi a zahiri ranar da na fara zuwa wannan birnin ” murmushi Jaseena tayi tace ” Allah ya kawo su lafiya” duk suka amsa da Ameen…………


          Kafin kace wani abu sai ganin su sukayi a Ramali ba b’ata lokaci masarautar suka nufa inda sukayi mamakin irin tarbar da aka yi musu kamar an san da zuwan su.

       Sarauniya jaseena ce ke sauk’owa daga matakala da mijin ta sarki Hydar bayansu kuwa Gimbiya Saleena ne  da Nawaf. Tun daga nesa suka had’a ido da Nawaz a take ya mik’e tsaye har suka k’araso ,Sarauniya ta umarci Nawaz da ya zauna nan fa tasa aka k’ira magatakarda ta sa hannun ta tayi nuni zuwa inda suke zaune tace ” ga chan Nawaz da kuma Nawaf ! Kuma ga jakar da ake buk’ata nan ta iso ba tare da an nemota da wuya ba , abunda ya rage shine ka sanar da su ko su Wanene su a yanzun nan”


        “Da farko de ina me neman gafarar ku bisa ga abun da na aikata muku na makirci wanda ba a son raina na aikata hakan ba ,sannan kuma nabi son zuciya ta na zab’i rayuwata akan tab’arb’arewar taku rayuwar har ga Allah ban yi don raina ya soba sai don kare mutunci na da na iyali na duk dan kishiyoyin mahaifiyar ku (Raheena) ta tozarta………… Nan ya kwashe labarin abubuwan da suka faru ya labarta musu. Cikin kuka yaci gaba da cewa ,bayan wayannan shekaru masu yawa kuma se suka nemi su hallaka ni domin sun ga gaskiya ta kusa yin halinta ,yanzu haka nasan hankalin su Kwance yake cikin ruwan sanyi basu san abunda suke gudu ne zai faru ba………..


          Nawaz da Nawaf a tare suka mik’e idanuwan su cike da k’walla ya juya gefen shi na hagu yace ” Asad ka kaini SHIMLA!! Ka kai ni Shimla yanzun nan !! Nawaf da ke gefe yana neman da waye ake magana sai lokacin Asad ya bayyana a gaban idon shi cike da mamaki ya dubi d’an uwan nasa yace ” ka kaimu Shimla ” Gimbiya Saleena da ke zaune a gefe ta mik’e tace ” A ina za’a bar Masoyiyar Nawaf!!!? Duk suka bushe da dariya yayinda Afreen ke zaune tana bin kowa da ido bata ce komai ba ,se Saleena tace ” k’awata yaya de? Tayi murmushi tace ” ai in banda wani ikon Allah babu abunda zai hana jameelah zuwa! Ta mik’e tana murmushi wanda ya burge su duk suka rufe idanuwan su daga nan bud’e idanun da zasu yi sai gasu a Masarautar SHIMLA babu b’ata lokaci Nawaz da Nawaf suka rufe fuskokin su da mayafi sai iya idanuwan su kake gani kai tsaye kurkukun suka nufa  ganin babu masu gadin ya basu mamaki ga kuma makullan ko wanne d’aki a rataye ,basuyi wata wata ba suka bud’e wannan k’ofar da suka tab’a jin maganganun Shalini ………..


             Su Saleena suna shiga fadar mai martaba sarki Abdallah yayi musu tarba mai kyau cike da mamakin abunda ya kawo su a wannan lokacin ,bayan sun huta ne Sarki Haidar ya umarci magatakarda da ya maimaita abubuwan da ya fad’a wanda ya sani ,su Ubaidah da Zulaikha kam basa nan sun fita yawon bud’e ido ,hakan ya sake bashi kwarin gwiwar zayyano wa sarki Abdallah duk abunda ya faru. Jikin sa na b’ari tun a zaunen da yake kafin kace me gumi ya karyo masa ,ya karb’i jakar ya duba ,asalin rubutun Sarauniya Shalini da ke ciki yaga abunda ta rubuta daban ne da wanda aka cika masa kunne da shi a chan baya, idanuwan sa cike da hawaye yace ” Kaicho na!! Na aikata babban kuskure a rayuwata da na yarda za zance marasa kan gado da suka d’aura ni a kai ,tsawon shekaru ashirin da wani abu Y’AY’ANA basuji d’umin jiki na ba,basu san dad’in rayuwa da iyaye ba ,basu kuma ji irin soyayya ta mahaifa ba tun bayan sun yi sati biyu kachal da zuwa duniya  Nayi nadaman zama da wad’anda basa son ci gaba na a rayuwar su ,kuma nagode wa Allah da yasa Raheena na nan da ranta nasan zata yafe min amma bana tsammanin Ubaidah da Zulaikha zasu sake samun jin dad’in rayuwa har abada!!!” Yana kai wannan ya umarci wasu manya manyan masu gadin gurin da cewar “a je a taho da su Ubaidah tare da Mahir!” ………


        Hannu tasa tana kare fuskar ta idanuwan ta ta kasa budewa wad’anda suka cika da hawaye domin irin rad’ad’in Hasken rana da take ji a idon ,kayan jikinta duk sun zama tsumma mayafin da Nawaz ya rufe fuskar shi ,shi yasa ya rufe mata jiki fatar ta duk ta yank’wane sai uban suma da ya sake tsayi har gadon bayan ta wanda don wahala babu irin bunu da yayi da babu a wannan kan ,babu abunda take yi sai gafi ,tunda cikin fitsari da ba bahaya take kullum nan ne kwanciyar ta ,cinta, Shanta, har ta manta a duniya me wanka yake nufi duk gab’ob’in ta rawa suke yi babu kwari gashi tayi bak’i sitik kai kace ba Shalini tsatson indiya ba, baba Nasir ne biye da ita shima Nawaf ya rik’e shi domin babu k’arfi jikin sa, suna tafe a hankali mutanen gari suna bin su da kallo har suka isa fada, a nan ne idonta ya d’an fara daidaitawa ta fara ganin Abdallah dishi dishi ,gaba d’aya hankalin shi ya tashi ganin wanda aka ajiye gaban sa a matsayin Raheenar sa jiki na b’ari ya sa hannu duk biyu ya tallafo fuskar ta da hannayen shi duka biyu sai faman rok’on ta yafiya yake yi ,kuka suke yi mai tsuma zuciya ,ita Raheena ta san bashida laifi ,shanyeshi kawai akayi amma na don haka ba da haka bata faru ba, itama wautar da ta tafka shine na yanke hukunci da tayi da kanta ta bar gidan ,haka ya sake dulmiyar da ita cikin laifi da akace ta aikata ,domin da ta samu sarki da haka bata faru har ya kai ga zartar da wannan hukuncinDomin da ta samu sarki da haka bata faru har ya kai ga zartar da wannan hukuncin ba ,don haka ta k’addara a ranta ta yafe mishi har Abadan ,a tare suka maida duban su ga Y’AY’AN nasu cikin nuna so da k’auna Abdallah ya bud’e musu hannayen shi ,basuyi wata wata ba suka rungume mahaifin nasu yayinda ya umarci kowa yaje ya huta shi kuwa ya keb’e da Shalini ,ranar nan shi yataimaka mata gurin gyara jikin ta ,ta fito fes da ita saidai wannan jiki nata se a hankali zai murmure tayi shiru tana kallon shi ,gaba d’aya ta manta rabonta da shak’ar iska mai Ni’ima irin ta yau…….


         Da rana ,yunwa taci Afreen gashi babu abunda take tunawa sai wannan muguwar uwargijiyar tata ,a ganinta in ta koma bata san yadda zata yi ta mata bayanin abunda yake faruwa ta bar gida ba ,ta dad’e a haka bata ankara ba taji an ja karan hancin ta ,tana d’aga kai suka yi ido hud’u da Gimbiya Saleena, tace ” yaya dai kin natsu haka kinata tunani ? Ai a ganina mace kamarki me kima da aji ga kyau babu abunda zai sata tunani irin haka ,ko de baku daidaita da Yerima Nawaz bane?” Murmushi Afreen ta sakar mata tayi Ajiyar zuciya tace ” tunanin da nake ba tunani ne akan komai ba Illah lokacin da naga wannan zuria ta sake had’uwa a k’ark’ashin inuwa d’aya sai naji dama ace nima zan ga nawa a lokacin ,ak’alla yau  da na cika shekaru goma sha takwas chif chif ,ban san yaya fuskar tawa mahaifiyar take ba ,sai muguwar kishiyar uwa ,haka mahaifina ma ya fad’i ya mutu ba tare da ya sanar da ni komai game da uwata ba ,ya barni cikin k’uncin rayuwa da wahala ,sai lokacin da Allah ya kawomin wani jigo cikin rayuwa da sunan Yerima Nawaz ,da nayi zaton nice nake d’auke da mugun ciwon son shi amma sai naga ba haka bane duk k’anin mu muna begen juna….” Lokacin da take maganar duk sun shigo d’akin, Sarauniya Raheena da ta d’an ji k’arfin jikinta tun da suka shigo kowa ya lura da kallon mamakin da take yiwa Afreen ,ko da ta dasa aya Raheena ta matsa kusa da ita tace wannan fuskar itace fuska da ko a cikin mafarki na ganta bazan manta ta ba balle kuma a zahirance!!” Duk suka maida duban su ga Sarauniya Raheena yayinda taci gaba da cewa ” ke y’ar gidan Lakshmi ce jikar Lakshmi rani ma! Duk wani d’a da ya fito daga gidan ku kuwa fuskar shi bata tab’a b’uya wannan yasa na gane ki sarai ,mahaifiyar ki y’ar babban gida ne gidan mutunci ,Mun taso tare tun ina y’ar shekara biyu Mun shaqu sosai ba kad’an ba ,lokacin muna y’an shekaru goma sha takwas aka aurar da mu ,wanda ya aureta babban me kud’i ne kuma auren soyayya suka yi ,ko ba mahaifin ki bane Othman Omar? ” eh shine ranki shi dad’e ” murmushi Sarauniya Raheena tayi tace ” lokacin da aka haifeki bana nan domin ni kaina ban shayar da y’ay’a na ishashen nono ba balle kuma in san halin da y’ar uwata take ciki ,tunda nake a rayuwa ban tab’a samun sab’ani da Lakshmi ba” kusa da ita Afreen ta matsa tace ” naji dad’in jin wannan labarin ,kuma ko ba komai abokiyar zamanta ta ciyar da ni kuma har na girma ,abun da tayi min na yafe mata amma bazan sake zama da ita ba ,gurin iyaye na inda zan samu gata nan ya fiye min komai” cikin kuka Raheena ta rungume ta tace ” kina gida Y’ata nan ma gidan ku ne domin kuwa babu wani abu na Lakshmi da zan kasa rikewa komi lalacin sa!!!+


       Nan suka d’unguma zuwa cin abinci ,ranar dai sun ci abincin ne cikin kwanciyar hankali ,k’auna kuwa tana nan k’arara a idon kowanne daga cikin su ,Nawaf bashi da aiki se tsokana tun Nawaz na murmushi har ya fara maida martani ,abunda ita kanta Raheena ta lura da shi shine ,sarauta tana jinin Nawaz fiye da Nawaf ,komai nashi daban ne ,cin abincin shi ,maganganun shi da yanayin da yake kallon mutane wanda yasha banban da Nawaf wanda babu ruwanshi bai ma san ya sarautar take ba saidai burgeshi kawai da take yi tun yana k’arami…………….     Alhamdulillah!

Post a Comment for "GUGUWAR HAMADA COMPLETE "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...