GUDU A JEJE COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

GUDU A JEJE COMPLETE

GUDU A JEJE COMPLETE

- - Post a Comment

 GUDU A JEJE COMPLETE 🌳🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️
Alhamdulillah! dukkan yabo da godiya su kara tabbata ga Allah Subhanahu wata'ala, salati da daukaka da tsira da aminci su kara tabbata ga Shugabanmu Annabi Muhammad(S,A,W) da Iyalan gidansa da Sahabbansa.
Na dawo a karo na biyu fans fatan za ku karbi wannan book da hannu bibbiyu fiye da yan da kuka karb'a *Halitta Daga Allah Ne.*
+
Ummu nasmah'ta ina mugun yinki ngd sosai da kulawa Allah ya raya mana zuria, Allah ya ba ki ikon kammala shahararren book dinki mai dinbun fad'akarwa, wato *Nasmah ko Nasirah* ameeen.
Short story✍🏻


☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️☘️

بسم ا لله لر حمن لر حيم
🅿_1⃣➡2⃣
Gudu su ke yi ba ji ba gani,
a wani tangareran jeji wani saurayi da budurwa, da ka gansu ka san gudun ceton rai suke, duk da sun galabaita matuka,
Barin ma budurwan janta kawai saurayin ke yi domin ya riƙe hannunta,
Su na cikin gudun ne yarinyar  tayi tuntube da wani dutse nan ta fadi kasa kanta ya bugu, tsantsan wahala kasa kuka tayi sai numfashinta da ke fita sama-sama, bakinta fari sol alamun wahala.
Da sauri cikin tashin hankali marar misaltuwa  ya hau jijjigata yana kiran sunanta
"SAFREENA ! SAFREENA !SAFREENA!."
Da kyar ta iya bude ido da baki tana magana numfashinta kamar zai dauke ta ce.
"YAYA KHALIFA, ba zamu tsira ba a wannan jeji, wannan gudun har yaushe zai kare yau kwanan'mu 14 muna gudu amma basu dai na bin'mu ba mu tsaya kawai ka basu takardun nan Mu huta da azaban wannan jeji, idan kuma ba haka ba za muyi mutuwar da babu gata acikin jejin nan"  ta saki wata wahalalliyar kuka mai ban tausayi, cikin kuka ta ke cewa.
"Ba zan tab'a yafe maka ba *BABA DAUDA* Allah ya isa! Allah ya isa! jinin Abbana da Momyna ba ka kashe a banza ba,  sannan wannan wahalar gudu a jejin da ka sa ka ni, shi kadai ya isheka azaba! Wallahi ko da na mutu a jejin nan za ka ga inda karshen ka zai yi muni wai Dan U....kasa karasawa ta yi, saboda kukan da ya ci karfinta.
Tausayinta ne sosai ya ci ka zuciyar Khalifa ya ce.
"ya isa haka Safreena ki tashi Mu bar wajan nan, Sannan ke a tunanin ki idan na basu wannan takardun zasu bar mu haka ne? wallahi kashemu za su yi, domin Dauda ba zai bari mu rayu ba kodan kar mu tona masa asiri gwanda Mu ci gaba da gudun ceton ran'mu, idan Allah yasa zamu rayu to ba Dauda ba ko namomin jejin babu abun da suka isa su yi mana."

         "Yaya Khalifa, zan sha ruwa, ba zan iya tafiya ba"
Shuru ya yi, yana nazari, juyawa ya yi ya kalli gabas, kudu, arewa, yamma, babu abin da ya kewaye su  ban da wasu bishiyoyi, wasu masu duhun gaske ya ce.
"Safreena babu ruwa anan, mu kara gaba ko zamu samu" 
Shuru ta masa kuma bata tashi ba.
"Ba za ki iya tafiyan ba da gaske?"
Ta gya ɗa masa kai alamun eh,
Durƙusawa ya yi ya ce "hau mu tafi"  ba musu ta hau bayansa ya ci gaba da gudu ya nayi yana juya baya.
***********
Bari Mu waiwaye tushen labarin.

Wacece SAFREENA.?
Wanene KHALIFA.?
_____

STORY CONTINUES BELOW
Safreena y'ar gidan wani shahararren  attajirin mai kudi ne, mahaifinta *Alhaji Muhammad Bello Badamasi*  ya shahara, mutum ne mai kudin gaskiya ya mallaki abubuwa da dama a rayuwa, asalinsa Dan jalingo ne, su biyar ne wajan mahaifinsu, amma a cikin biyar din nan shi ka dai ya rage.

Mahaifinsa mutum ne mai rufin asiri kasancewar Muhammad ne kawai ya rage masa ya yi matukar kokari akan karatunsa kama daga abin da ya yi primary skull secondary skull har ya kai matakin university mahaifinsa bai taba gajiya da shi ba.
Mahaifinsa yana da Ƙani wanda uwarsu ba daya ba, yana da yaro daya shi ma mai suna Dauda,   tun su na yara ya tsani Muhammad saboda ko a makaranta ya fi shi ilmi, sannan ya fi shi jama'a sannan ko wani abun alkhairin ne sai dai Muhammad ya samu amma ban da shi sabofa muguyan halayyarsa, kwata-kwata baya abota da mutanan kirki, tun yana primary skull ya ce shi ba zai sake zuwa makaranta ba, shi kudi ya ke so yana so ya zama shahararren mai kudi , yanabso ya zama mai iko da karfin mulki sannan kuma mai faɗa aji.
        Lokacin da Muhammad ya tafi yin digree dinsa a Kaduna ya hadu da wani mutum Wanda taimakon mutumin ya yi daga hannun y'an fashi,
Mutumin ya ji dadi haka ne yasa ya kira Muhammad ya tambayesa waye shi.
Muhammad ya bansa labarinsa a takaice da abin da ya kawosa Kaduna, mutumin da shike Babban mutum ne Alhaji Murtala Bala  lokaci daya yabji ya aminta da Muhammad.

Dan haka ya biya masa kudi zai koma America yayi degree dinsa a can har ma da masters.

Ko da Muhammad ya gayawa mahaifansa fatan alkhairi suka yi masa Dauda, tsantsan baƙin ciki mutuwa ne kawai bai yi ba.

Shekaran Muhammad 10
a America, kafin ya dawo ya mallaki kudi kasancewar Alhaji Murtala Bala yana da jama'a, kuma shi duk da yana da kudi amma ba ya da d'a ko y'a, kuma an ce matsalan daga wajansa yake shi ya sa ya hakura ya falwalawa Allah, ga shi dai ba ya da d'a sai azababben kudi,
Allah ke nan, idan ya hanaka wannan ni'imar sai ya baka wata.
Ko lokacin da  Muhammad zai dawo yana da manya-manyan shops na gwala-gwalai har 4 a America Wanda yake mallakinsa ne halak malak.
Ya dawo ya tadda mummunar labari na mutuwar iyayensa Wanda aka rasa mai ya kashesu.
Dauda kuwa yanzu ya zama tantirin mai safaran miyagun kwayoyi,
Ko da ya ga Muhammad yanda yabdawo har kuka ya yi.
Muhammad ya yi kukan mutuwar iyayensa a lokacin daya zama mutum zai taimakesu lokacin suka barsa.

Takardan wasiyya ya ci karo da shi Wanda mahaifinsa wai yabar masa in ji Dauda.
"Assalamu alaykum ya kai ɗana lokacin da wannan sako ya iso gareka ni kuma na koma ga mahaliccina, ka dauki Dauda Dan uwanka ka riƙesa kayi masa duk wani abin da za ka min,
Sako daga mahaifinka Bello Badamasi."

Abun da ya ɗaurewa Muhammad kai shi ne, ya aka yi mahaifinsa ya san zai mutu? tun da babu Wanda ya san ranar mutuwarsa kuma harda Innansa! da ya ga bai da wannan amshoshin ne ya sanyawa Zuciyarsa salama ya tattara kayansa ya dauki Dauda suka bar garin jalingo ya koma Kaduna gidan Alhaji Murtala Bala.

Lokacin ne ya fara wani dangareran gidansa a garin ABUJA a GWARIMPA, gida ne daya amsa sunanshi gida, unguwa ne sai wane da wane amma gidan Muhammad karshe ne, part  2 ya gida na shi daya  na Dauda daya, domin a lokacin ya fara maganar aure da wata yarinyan da suka hadu mai suna Khadeejah, kyakkyawa ce ajin karshe, ko da ya kai Dauda domin su gaisa, ji ya yi a duniya Muhammad ya tare masa iskar numfashi domin Khadija bata dace da Muhammad ba da shi ta dace domin irin matan da ya ke so ke nan.

Ana saura wata 1 bikin Muhammad da khadija tsakar dare Muhammad na kwance ya ji wayarsa na ringing yana dubawa ya ga Babana Murtala, da sauri ya dauka nishi
kawai ya ke ji na tashi, cikin tashin hankali ya tashi amma bai ga Dauda ba.
Part din Alhaji Murtala ya shiga ya gan shi kwance cikin jini ko INA na jikinsa yagan wuka ne kawai, an farfarke cikinsa hanji duk ya yi waje, da sauri ya karasa yana jijjigasa yana kuka sosai.

Sai ga police sun iso Alhaji Murtala yana so ya yi magana amma ya kasa,
Kawai ya dauki wasu takardu ya damƙawa Muhammad a hannu, da kyar maganarsa ke fitowa ya ce.
"ban da yara ban da mata,
Kai ne ɗana, wannan takardun dukiyar da na mallakane duk na mallaka maka su, halak malak ka taimaki addini Muhammad"
Ban da kuka babu abin da Muhammad
ke yi, ya ce.
"Baba waye ya maka haka!?" yana so ya fadi amma inaa jini kawai yake zuba a bakinsa, daga nan ya fara kalman shahada a hannun Muhammad ya cika.

Muhammad rabin hauka ne kawai bai yi ba.

Sannan tun da aka yi mutuwar bai ga idon Dauda ba har aka yi adduar uku.

Ga shi duk wani binkice anyi amma an kasa samun  wani information
Haka aka hakura tun da dai Wanda ya mutu ya mutu.

Bai kara ganin Dauda ba sai ranar da aka yi adduar 7 tukunna ya shigo gidan, Muhammad na tashi ya wankesa da mari,nan yasa kuka ya shirgiɗa masa karyan  abin da  ba ayi ba.
Ko da Muhammad ya basa labarin Baba ya mallaka masa dukiyarsa bindiga ne kawai zuciyar Dauda  bai yi ba, nan ya fara tunanin kawar da Muhammad a doran kasa.
More comments more typing✍🏻 ku biyoni domin jin yanda zata kasance.
Comments
And
Share

Alqalamin✍🏻✍momyn ahlan ne

🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Fan's naji dadin comments amma Ku kara ngd Allah yabar qauna  💔💔
بسم ا لله لر حمن حيم
🅿_3⃣➡4⃣
Da haka dai har aka yi bikin Muhammad da Khadija suka tare akatafaren gidansu dake abuja a gwarimpa.

Babu yanda Muhammad bai yi da Dauda akan ya yi aure ba, amma ya ki ya ce shi bai ga matar da yake so ya aura ba.+

Abin da Muhammad bai sani ba shi ne aure kwata-kwata baya gaban Dauda idan kuma wata bukatarsa ce to ya gwammaci ya je gidan karuwai ya dauki karuwa ya biyata ya biya bukatansa.
Babu kalar harin da Dauda baya kai wa Khadija da ta gano shi ta fadawa Muhammad, fada ya mata akan cewa
karta shiga tsakaninsa da Dan uwansa, hakuri ta basa daga nan ta shiga kulle kanta idan Muhammad baya nan.

Har ta fara laulayin ciki murna a wajan Muhammad baya misaltuwa ya yin da Dauda ya ji wannan lbrn, ji ya yi duniyar ta yi masa baqiqirim , yanzu idan Khadija ta Haifi namiji shi kenn duk wannan uban dukiyar zai zama mallakin dan'sa shi kuma miye makomarsa.

Babu kalar tuggu da munafurcin da Dauda bai shirya ba wajan ganin ya kawar da Muhammad da Khadija amma INA abun ya ci tura.

Har Allah ya sauketa lpy ta samu santaleliyar yarinyarta mace kyakkyawar gske mai kama da ita fara sol wato SAFREENA.

Lkcn da Dauda ya ga mace aka haifa ya danji sukuni kadan a cikin zuciyarsa.

Haka Khadija da Muhammad suka ci gaba rainon yar'su Safreena cikin kulawa da gata.
Har Safreena ta gama secondary skll dinta a wani skll mai suna
A,C,I,C academy abuja.
Safreena yarinya ce mai ji da kai kasancewar tana da kyau  ubanta kuma mai kudi sannan wulakancin a wajanta ba komai bane.

A wannan lkcn kuma Dauda babu abin da yake sha'awa kamar Safreena SBD dirin da  Allah ya mata,
Ta bukaci mahaifinta daya kai ta London domin ta yi university dinta a can, ba tare da bata lkc ba ya aminci SBD ita ke nan y'ar Dan Mommy bata sake haihuwa ba.
KHALIFA.

Driver ne a wajan Alhaji Muhammad Bello Badamasi
Khalifa Dan garin katsina ne wani karamin local government mai suna dutsen Ma
Ya tashi a wajan Matar Babansa Wanda kwata-kwata, baya jin dadin zama dasu,
Tun yana karami yake sha'awar aikin   engineering.

Da buga-buga  yake yin kwadago yake biyan kudin makarantansa.

Har Allah yasa ya kammala degree dinsa anan dutsen ma.
Ya karanci abin da yake sha'awa wato engineer ya ta yawon neman aiki amma bai samu ba ga takuran da matar babansa take masa,
hakanne yasa ya kwashe kayansa yabar garin katsina
Ya koma abuja
A wata karaman unguwa farkon shigowa abuja wato maraba.

Nan ya samu wata garage da kyar ya roqa aka daukesa aiki  a wajan.
A cikin 2weeks ya yi wa ma'aikatan da ake ji dasu zarra,
Daga nan suka fara jin haushinsa su na masa baqin ciki.
STORY CONTINUES BELOW
Har suka kulla masa sharrin ya saci motar da darajan kudinta ya kai 67m Wanda shi ya gyara motan
Hakanne yasa aka koresa a garejin.
Ya shiga kunci sosai daga baya ya roqi Allah abin da yafi alkhairi a gareshi pure water ya koma siyarwa Wanda shine silar haduwarsa da Alh Muhammad Bello Badamasi.
Motarsa ce ta tsaya
Lkcn kuma Khalifa yana tsaye a wajan da pure waternsa a hannu , ganin yanayin mutumin ya yi kamar yana cikin damuwa yasa Khalifa zuwa wajansa  ya ce.
"Alhaji, mai ya sami motar taka?" ya ce.
"wlh ka ga haka kawai motar ta tsaya"
Duba masa ya yi daga nan ya bude gaban motan ya juye mata ruwan pure waternsa guda biyar.
Ya ce.
"Alhaji kunna ka ji  ya yi?"
Yana kunnawa mota ta tashi gdy sosai Alh Muhammad ya hau yi wa Khalifa ya Ciro kudi Wanda bai san iyakarsu ba ya ba shi, murmushi Khalifa ya yi ya ce.
"Na san za ka iya biyana da abin da yafi haka, amma ni kam Dan Allah na maka ka bar kudinka" nan take ya ji kaunar Khalifa ya kamasa.
Card dinsa ya basa yace anjima yasamesa agida ko a office murmushi khalifa yayi kafin ya karba card din har alh yashiga mota ya leko da kansa ta window yace plss kazo fa ya sunanka
Sunana khalifa zanzo alhaji
o shikenn
Da khalifa baiyi niyyar zuwa ba amma kuma yanayin alh ya nuna masa mutumin kirki ne hakanne yasa yace zaije
Haka kuwa akayi da yamma bayan ya siyar da pure water dinsa ne ya shirya yatafi gidan alh Muhammad bello badamasi dayaga gidan saida ya tsorata domin bai taba ganin irin wa innan gidan afili ba saidai film
Yana zuwa akayi masa iso har Babban parlour'n
Da alh yake ganawa da baki alkcn yana waya da safreena tana cemasa abbana ka turomin da kudi na hannuna sun kare yace to ba damuwa my baby yanzu inada bako zan kira ki ya katse kiran
Sannan ya kalli khalifa yace kaban lbrnka
Atakaice kawai yace masa shi Dan katsina ne yazo Neman aikine a abuja amma bai fada masa yayi karatu ba
Alh Muhammad yace ka iya driving da sauri khalifa yace eh alh na iya yace to zaka dinga driving dina zan biyaka 100k ya maka khalifa baisan lkcn daya miqe tsaye ba yace alh 100k fa kace
Eh haka nace idan kuma yamaka kadan 300k
Kuka khalifa yasa yana gdy wa Allah da kuma alh batare da bata lkc ba ya yarda dari bisa dari
Haka khalifa yaci gaba da aiki agidan alh Muhammad yayinda basu shiri ko kadan da dauda  SBD yasha ganin
dauda da karuwai da wasu tantirai
Har yayi 3yearh agidan sosae alh Muhammad ya yarda dashi SBD gskynsa
Khalifa yaje gida yayi dankareriyan gidansa agarinsu yayinda matar babansa tadinga yawo a unguwa tana cewa khalifa yazama Dan yankan kai

Waya take da momynta tana cewa itakam zata dawo gobe domin tunda tatafi London ba tadawo
Nigeria ba saidai su Abba su kai mata ziyara
Abba ne ya kira khalifa ya fada masa akan cewa gobe da yamma zaije airport ya dauko safreena cikin girmamawa ya amsa da to Abba domin yanzu yahanasa kiransa da alhaji
Har yanzu kuma dauda yana hada kunguya mai karfi Wanda zai kawar da Muhammad kullum saiya karba kudi ahannunsa masu yawan gske Muhammad bai taba hanasa ba kuma bai taba tmbyarsa mai zaiyi da kudi ba tunda mutum kamar dauda aiyasan ciwon kansa

Washe gari
Da yamma misalin 4:00 yaje airport dauko safreena
Tun daga nesa ya hangota tayi shigan riga da wando kanta ko Dan kwali babu balle gyale
Magana ya mata akan cewa shine driven da mahaifinta ya aikosa kallon sama da kasa tayi masa taga baiyi wani kama da driver ba amma dukda haka
wani wulakantaccan kallo ta masa tunda ganan yasan cewa albasa batayi halin ruwa ba
STORY CONTINUES BELOW
Tsayawa tayi agaban mota tanajira yabude mata khalifa dayaga haka kuma ya fahimci abinda take nufi yace tab lallai bazamuyi shiri da wannan yarinyan ba mota yabude yashiga yayi zamansa yabarta nan tsaye ranta ne yabaci ta bude motan tashiga Sai yamutsa fuska takeyi tana tsaki
Sun iso gida gateman ya bude musu tun motar bai tsaya ba tafice
Tunda daga ranar da safreena ta dawo basu shiri ko kadan da khalifa
Alh Muhammad dayaga yanayin dabiun yar'sa ya canza yace bazata koma ba tayi kuka harta hakura

Ranar tana ta Neman Wanda zai amata assignment amma ta rasa tafito garden din gidansu lkcn khalifa na zaune awajan tagansa tsaki tayi ta zaune can gefe dashi  ta kira wata friend dinta tace ke nifa wlh bangane ba nakasayi kawar tace nima wlh bangane ba ai bai kamata su bamu assignment akan wannan ba cox sai Wanda sukayi karatu ta fanni engineering su zasu sani tsaki tayi ta kashe wayar tana sake duban book din
Duk abinda takeyi khalifa yana kallonta kuma yanajinta tashi yayi yaje inda take batare da yayi mata mgn ba ya karba book da pen din ya koma ya zauna kasa mgn tayi azcyarta take cewa ji wannan shashashan ko meya sani oho harda karbamin book dina bari daina naga iyakan sakarcinsa yana batamin book
nasa Abba ya  koresa

5mnts ya dawo mata da book dinta ba ko gdy dubawa tayi taga rubutansa gwalalo ido tayi tace kai nice writing
Ko washe gari da taje skll ita taci
Kunya taji yakamata ta tuno ranar da fada yahadasu ta zagesa da turanci kenn yaji abunda nace kyaleni kawai yayi wayyo ni safreebaby
Zuwa tayi tabawa abbanta lbr yaji dadi sosae kiran khalifa yayi ya tmbyesa akan cewa dama yayi karatu ne yace masa eh degree ne dashi fada sosae yayiwa khalifa akan cewa bai kyauta masa ba gobe yakawo masa takardunsa zai sama masa aiki yace to tare da gdy

Da daddare Abba yata kiran wayan khalifa bai dauka ba yafito ya kira mai gadi yace kiramin khalifa ya amsa da to cikin girmamawa

Ba ajima ba yafito yace ina ka ajiye wayarka ne
Abba ga ta a aljihuna
Shine na kiraka baka dauka ba ? Abba tana silent ne
OK amma gsky ka cireta SBD sha,anin rayuwa yace to !Abba gani
Aa khalifa jeka kawai abunka dare yayi haka kawai baisan dalilin dayasa ya kira khalifa ba
Tsakar dare misalin 2:00
Abba da momy na kwance adaki suna bacci ji suke ana tashinsu bude ido da Abba zaiyi wazai gani dauda da wuka
ahannunsa yana zaune a daya daga cikin kujerun
Dake  dakin agefe kuwa wasu samudawan qarti ne fuskansu amurtuke
Abba zaiyi mgn yaji ihun safreena kallon dauda yayi yace wai meke faruwa ne dauda
Dry dauda ya hauyi yace Muhammad bello badamasi au yi hkr Yaya yaka mata kasan wani shirri shigowa da safreena akayi dauda ya karbeta yana shinshina wuyanta kuka takeyi tana kiran sunan abbanta da momynta khadija itama kukan take
Abba yace wai dauda kayi hauka ne sakemin ya'ta dry dauda ya sheke dashi yace yimin shuru
Na tsaneka kafini komai duk abinda yakamata ace Nina mallaka amma
Kaine mallakinsu bari na fada maka wani sirrin danace zan gaya maka

Nine nan na kashe mahaifinka da mahaifiyarka
Suman zaune Abba yayi domin mgnr dauda ji yayi kamar anbuga masa guduma akunne
Ganin haka yasa dauda kara sakin wata dryn yaransa suna tayasa
Yace wai Yaya ka tsorata ne to harta alh murtala nine nan na farfarkesa da wuka kuka Abba yafara yace dauda meyasa cikin daga murya yace SBD na tsaneka dole yau ka mallakamin duk wani kadara daka mallaka
Abba ya dauki wayarsa babu Wanda yagansa ta kasa kasa ya rubutawa khalifa message Sannan yayi dealing din numbern
Bugu uku khalifa ya dauka Abba yakashe bude idonsa yayi yaga  message din Abba da sauri yatashi  yayi cikin gidan da gudu
Yana shiga abakin kofar parlor aka kamasa akayi dakin Abba dashi
Alkcn Abba ya dauki takardu ya miqawa dauda yakarba yana dryn mugunta
Agaban Abba dauda yafara shafa safreena yana cewa dama najima INA sha,awarki mamanki nafara sha,awa ashema zata haifamin Wanda tafi kanta akyau Abba ne yasa hannu zai kwace safreena garada biyu suka shaqe Abba momyn tana kuka ta durkusa agaban dauda ta hada hannunta biyu tana roqonsa dry yakeyi ya damqo kashen momy yacaka mata wuka aciki ihu safreena tasaki tayi baya baya kamar
zata fadi lkcn aka shigo da khalifa da sauri yatare safreena Abba na ganin khalifa yace khalifa ka dauki safreena Ku gudu ka kulamin da ita
Dauda kallon khalifa yayi yace dama kai ne last target dina
Yace kalli yanda zan kashe Dan uwana akan dukiya haka kaima zan kasheka matsiyaci
Daukan takardun yayi ya nunawa khalifa yace kagansu nan lkc yayi da za afara kiran sunan alh dauda yahya
Khalifa yana tsaye yakasa mgn domin jiyake kamar mafarki yake ta bayan Abba dauda  yazagaya yasa wukan ya yanke masa wuya da sauri khalifa ya rufe ido gamida rungume safreena
Addua yakeyi yana Neman  mafita
agefen drawer yaga Mobil insecticide daukawa yayi ya feshesu dauda dashi  sannan ya kwace takardun dake hannun dauda yaja hannun safreena Wanda ta koma kamar gawa suka fice da gudu yana fizgan safreena Wanda bata iya tabuka komai
Ko da suka fito gate mai gadi kwance acikin jini
Dan haka sukasa kai suka fice sanadiyar shigansu jeji kenn dauda yasa aka bisu akashesu sannan akawo masa takardun dukiyarsa.
Gudu sukeyi ajeji har garin Allah ya waye kafin safreena tasamu bakin kuka
Kasa lallashinta khalifa yayi domin shima kuka yake har yamma basu ankara ba sukaji karan bindiga sbd
dauda yahada kungiya da yan bindiga dadi
Cikin tashin hankali khalifa yaja hannun safreena su gudu amma taki cikin kuka da muryanta da baya fita tace nagaji ka kyaleni su kasheni Allah ya Isa baba dauda ka kashemin abbana ka kashemin momyna nima kawai akasheni babu amfanin rayuwata tashi tayi da gudu tayi hanyar da ake harba bindiga cikin zafin nama khalifa yariqota tana zillewa yayi2 ta tsaya taqi da iya karfinsa ya wanketa da mari lkc daya ta tsaya cak kafadunta ya riqo yana mgn jikinsa har rawa yake

Kin yarda ki mutu bakiga karshen wannan azzalumin ba ?kin yarda ki mutu bakiga karshen wannan butulun ba ? kin yarda ki mutu bakiga mummunar karshen Wanda yasa wuka  agaban idonki ya soki mahaifiyarki da wuka sannan yasa wuka ya datsawa mahaifinki wuya kin yarda ki mutu bakiga karshensa ba ?sannan kin yarda kema ki koma ya kasheki?
Tunda khalifa yafara mgn take kallonsa tana wasu zafafan hawaye mai cike da qunan Zcy
Mahaifinki mutumin kirki ne  yace na kula dake kuma nayi alkawari wa kaina zan kula dake harna bar numfashi
Hannun ya miqa mata yace idan kin amince gudu ajeji yanzu muka fara miqa masa hannnu tayi
Awannan gudun ne suka kwashi 14days kuma ba adaina binsu ba domin kullum dauda sabbin mutane yake aikowa

Amma sunkasa kama khalifa da safreena
Idan sukayi gudun suka gaji ko sukaji yunwa khalifa ne yakemusu dabara saisu nemi ruwa koda a rafi ne  su sha
Wasa farin girki
CIGABAN LABARI

______________________

Sai mun hadu a next page🤪
More comments more typing....✍🏻
Alqalamin✍🏻✍🏻momyn ahlan ne
Comments

And

Share

🌳🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Wow gsky fan's😍bani da bakin gode muku amma inayinki over 😍kuci gaba da sambadomin comments
Ni kuma bazan gaji wajan sambado muku typing ba Allah yabar kauna much luv to urs fans💔

Dedicated to feedyn bash marubuciyar ARNAN DAJI
Heart u sister💓
بسم ا لله لر حمن لر حيم
🅿_5⃣➡6⃣

Yayi gudu mai nisa da ita  kafin ya sauketa akasa yana haki alamun yagaji
Kallonsa tayi ta sun kuyar da kai kasa tace sannu yaya khalifa
Murmushi yayi yace waima yaushe kika fara kirana da yaya ne ?
Itama murmushin tayi tace tun ranar da muka fara gudu ajeji
Yaya khalifa kayi hkr ka yafemin abinda namaka hakika na yarda Dan Adam ba abin wulakantawa bane domin baka San Wanda zai taimake ka ba
Ka yafemin wlh harda sharrin kawaye da suke zugani wai inada kyau abbana yanada kudi
Kuka tafara mai taba zcy ta cigaba da mgn
Tun alkcn da baba dauda yasa wuka ya kashe iyayena tun alkcn na sallamawa duniya sannan rayuwa awannan ajeji ita kadaima darasi ce agareni wlh har kunyarka nakeji Yaya khalifa kai garkuwa ne agareni ka yafeni Dan Allah ta kuma sakin wata kuka mai ban tausayi gamida durqusawa agabansa tacigaba da basa hkr
+
Khalifa har kasan zuciyarsa yakejin kukanta
Durqusawa yayi shima agabanta yace naji nifa na yafe miki tuntuni Dan Allah kibar wannan kukan  karya ja miki ciwo kinga dai ajeji muke balle nayi tunanin kaiki asibity
Kukan tadan tsagaita tana kallonsa tace Yaya khalifa wai wannan jejin yasunansa?
Kallonta shima yayi ya miqe tsaye kafin  yace taya zan sani kedai tashi mutafi kawai kafin azzaluman nan suzo nan su samemu tashi tayi suka fara tafiya
Dauda yana zaune ya hakimce akan kujeran da Abba ke zama akatafaren parlourn sa
Ya daura daya kan daya
Babban rigan Abba ne ajikinsa fara sol
Cike da masifa ya kalli samudawan dake zagaye dashi yace mutum biyu !mutum biyu!mutum biyu
Ace duk yawanku duk katancinku amma kun kasa kamasu mutum biyu kacal
Dukkan Ku baku da amfani yanda na turaku haka kuke dawowa wasu ma kam babu su babu labarinsu
To idan bazaku iyaba na namemo wasu Wanda suka fiku iya mugunta Dan wlh idan takarduna suka bata gabaki dayanku saina kasheku
Ku wuce Ku fita Ku ban waje qartin banza marasa amfani daya daga cikinsu ne yayi mgn yace boss wlh namijin ne wayo garesa gashi jejin akwai namomi masu cinye mutane
Harara dauda yafara aika masa fuskansa amurtuke  kafin ya miqe tsaye jikake Tass!Tass!Tass! Maruka   uku ya sauke masa yace zancan banza zancan wofi to ni INA ruwana idan yaga dama ya cinyesu harda Ku dinma ni burina kawai akawomin takardun nan
Ku fita yanzun nan kafin raina yakara baci
Fita sukayi gabaki dayansu
Dauda ya koma ya zauna
Khalifaaaaa safreenaaa
Saina kasheku
Dana san zaki girma ki kawomin cikas a plan dina dana kasheki tun kina yarinya kai kuma khalifa na raina ka ashe kai zaka zamemin qashin kifi to wlh bazan barku ba duk gudunku ajeji saina sa ankamo min Ku
Suna cikin tafiya safreena ta hango wani bangare mai haske tace laahh Yaya khalifa kalli can wajan daga idonsa yayi ya kalla yace muje mugani
Suna zuwa sukaga ashe wata babbar fili ne awajan ga ruwa kwance abin sha,awa tsalle safreena tayi gamida jin dadi da gudu taje tafara shan ruwan tasha sosae SBD tanajin qishi juyawa tayi ta kalli khalifa tace kai bazaka sha bane?
Murmushi yayi kuma baiyi motsi daga wajan da yake tsaye ba wani Dan karamin fashashshen kwarya tagani ba'ri daya ta dauka ta wanke duk yana tsaye yana kallonta ruwa ta dibo ta kawo masa ya karba yana murmushi yasha kafin yace ngd Anty safreena hade rai tayi ta turo baki ta zauna kusa da bakin rafin
Shima zama yayi yace menene ? tace to ba kai bane kawani kirani da suna Anty safreena dry yayi karo na farko da safreena tafara ganin dryn khalifa domin shi bai cika dry ba idan wani abunne yafiyin murmushi
Abinda yabasa dry kuma yanzu yanda tayi mgn cike da shagwaba tana turo baki kawai yaga tayi masa kyau shiyasa ya dara
Kallonsa kawai safreena keyi yace mata yadai wannan kallon fa ? Murmushi tayi tace dryn ne naga yayi maka kyau
Sassauta dryn yayi yace kema mgnr da kikayi yanzu tayi miki kyau murmushi ta kuma yi kafin shuru ya biyo baya
Duk kansu tunani suka shiga yi khalifa tunani yakeyi wannan gudun da sukeyi ajeji yaushe zai kare gashi kullum kara shigewa sukeyi
Taya zasu fita ajeji sannan bayan sunfita taya zai fara fuskantar sharia da dauda akan kisan kai din daya dingayi SBD wani burinsa na banza
Ita kuma tunani takeyi ko ya akayi da gawan mahaifanta shin anyi musu suturan daya dace kuwa ko an wulakanta mata gawan iyaye Allah yasa dauda ba jefar mata da gawan iyaye yayi ba kamar Wanda suka aikata mummunar laifi bata San lkcn da kuka ya kufce mata ba
Kukanta ne yadawo da khalifa daga duniyar tunanin da yakeyi kallonta yayi kafin ya fuskanceta yafara mgn cikin sanyin murya
Haba safreena meyasa bazaki daina wannan kukan ba kullum sai kinyita ahalin yanzu babu abinda su Abba da momy sukeso banda adduah nasan abun ba sauki da ciwo tunda agaban idanunki akayi amma yakamata ki daure kiyi yaki da zuciyarki ki fuskanci gaba
Cikin kuka tace. Wlh Yaya khalifa ko nayi yunkurin daurewa bana sanin lkcn danake kuka babbar tashin hankalina bansan ya akayi da gawan Abba da momy ba duk mutumin da ya mutu burinsa bazai wuce ayi masa sutura akaisa gidansa na gsky ba amma baba dauda babu digon imani azuciyarsa idan har akace ya jefar da gawan iyayena ne to hakika zan dauwama cikin baqin ciki taci gaba da kuka
Lallashinta khalifa ya hauyi yana bata baki tareda nasiha harta Dan sassauta kukan
Yace lkcn magriba yayi kitashi muyi sallah tunda ga  ruwa tashi tayi batare data basa amsa ba  gawani masifaffen yunwan datakeji yana addabanta kallon tausayi khalifa yabita dashi ji yake kamar  yayita kuka
Bayan sun  idar da  sallan ne gari yayi  duhu tsoro ne Yakama safreena tamatso kusa da khalifa ta zauna sai ba'rin sanyi takeyi
Yace sanyi kikeji ne?
Ta gyada masa kai alamun eh rigarsa daya yacire na saman dashike biyu ne yasamata suna nan zaune har lkcn sallan isha yace safreena lkcn sallah yayi tashi tayi sukayi sallah gamida adduah Allah ya kubutar dasu awannan jejin Allah kuma yabasu sa,a akan dauda
Zama sukayi shuru banda kukan  namomin jeji babu abinda kakeji ga tsoro ga yunwa
Khalifa ya kira sunanta  ahankali safreena kinajin yunwa ko ? Shuru tayi batabasa amsa ba Sai ga hawaye tace ai kaima kanaji ta kuma cewa
Kafata kemin ciwo kafan ya kalla duk sun kumbura yace na matse miki batace mishi komai ba ya hau matse mata kafan tausayi itama yabata batasan lkcn da tasaki kuka ta kwanta ajikinsa ba tace Ina tausaya mana Yaya khalifa muna mutane amma mun koma rayuwar jeji da gudu ajeji
Ya bude baki zaiyi mgn kenan saiga hasken touchlight mai hasken gske ji sukayi ance  gasu can
Tashi yayi ya kama hannun safreena
Suka cigaba da gudu ajeji cikin duhun dare

Suna gudu ana binsu
Ana harbi amma inaa basu kamasu ba balle bullet yashiga jikin dayansu
Jan safreena kawai khalifa keyi ayayinda shima da kyar yake gudun har garin Allah ya waye

Tsayawa sukayi ya juya ya kalli safreena amma mai layi tafarayi kafin ya riqeta ta zube kasa.....
_____to  suma  tayi mutuwa tayi nima dai bansani ba
Idan muka hadu a next page maji
Taku momyn ahlan✍🏻
Comments

And

Share

  M ahlan

🌳🌳🌳🌳🌳

       🌳🌳

     GUDU AJEJI

🌳🌳🌳🌳🌳

      🌳🌳

       Na

     Zahra Abdul


     (Momyn ahlan)

🌈kainuwa writers association✍🏻

Dashen Allah


Assalamu alaykum fans kuyi hakuri phone dina yasamu problem amma ga kadan kuyi manage

Bismillahi rahmanirrahim

🅿_7⃣➡8⃣

Dagota yayi ya hau jijjigata yana kiran sunanta safreena Dan Allah kitashi karki karaya a kwana 15 safreena kuka yasaka yana neman taimako amma babu mai taimako rungumeta yayi ya cigaba da mgn yana jijjigata amma ko motsi safreena batayi babu alamun sauran numfashi atare da ita

Gabaki daya ya rasa yadda zaiyi duk ya rude kallonta yasakeyi yana kuka safreena Dan Allah ki bude idonki karki mutu Dan Allah ki tashi kece karfin gwiwata na gudu ajejin nan Dan Allah kitashi+

Ya kai kusan awa biyu awajan yana rungume da ita can kamar daga sama ya hango wasu halittun mutane maza su biyu jikinsu kayan fata ne daka gansu kaga qabilun jeji

Ihu ya hauyi yana kiransu bayin Allah taimako

Su kuma da sukaji ihu sun dauka wani naman jejin ne suka hau waige2

Can suka hango su khalifa wajansu suka karaso

Sai kallonsu suke SBD basu taba ganin halitta mai kyau kamarsu ba dayan cikinsu ne yasa hannu ya shafi fuskan khalifa yana murmushi khalifa kallon ikon Allah kawai yakeyi

Dayan ne shima ya miqa hannu zai shafi fuskan safreena da sauri khalifa ya buge hannunsa ya hade rai ya girgiza masa kai alamun aa ja da baya yayi

Mgn yake musu amma sun tsaya kallonsa SBD basu gane yaren da yakeyi shima kuma baya gane nasu da hannu ya musu alama da suna neman taimako

Mgn suka hauyi da Dan uwansa kamar fada fada

Bayan sun gama ne suka kalli khalifa suka masa alama da hannu sutafi


Tashi khalifa yayi ya dauki safreena kamar baby ahannu Wanda har yanzu bata motsi tafiya suka hauyi Wanda da kyar khalifa keyi SBD shima agajiye yake ga yunwa ga qishin ruwa

Sunyi tafiya kusan awa daya kafin su iso wani dan karamin kauye Wanda duka duka mutanen kauyen bazasu wuce 25 ba da yan bukkokinsu kanana

Sai kallonsu khalifa sukeyi da safreena wani Dan karamin bukka suka nuna masa ya kai safreena wajan

Bukkan yashiga yaga wata tsohuwa fuskanta duk ya yamutse murmushi ta masa

Sannan tayi masa nuni da gadon kara alamun ya kwantar da safreena akai ba musu ya kwantar da ita domin matar kamar mai magani ce

Fitowa yayi yana neman ruwa can ya hango wasu manya manyan tuluna da ruwa acike fal da wata gwangwani aciki dauka yayi ya hau shan ruwan nan kamar ba gobe  yan' kauyen sai kallonsa suke yana gamawa yafadi kasa asume da sauri suka daukesa suka kaisa wani bukka

Magani suka fara yi musu SBD gabaki daya kafarsu ta kumbura sannan wani waje ma harda yankan qaya

Dauda agaban wani mutum daka gansa gaka cikakken mugu marar imani da tausayi fuskarsa baqiqirim amurtuke ga tubi  babu alamun rahma shi karan kansa dauda rissinawa yayi agaban mutumin mai suna black snake

Dauda yafara mgn cikin rawar murya black snake taimako nazo kamin da mutanen ka wani dan iskan yarone ya gudu min da dukiyata shida wata yar'iskan yarinya na tura mutane sunfi aqirga amma sun kasa kamasu SBD gudu ajeji sukeyi wasu mutanen ma basu dawowa wai naman jeji ya cinyesu shine Nazo ka taimaka min wani abokina ne yabani lbrnka akan cewa idan kasa yaranka aiki mutum yasa aransa aikinsa yayi angana shiyasa nayi tattaki nazo tundaga abuja har lagos Dan Allah ka taimakeni black snake

Wanda aka kira da black snake ya kalli daya daga cikin yaransa yayi mgn yace idan harka yarda zaka raba dukiyar taka kashi uku mu dauki kashi biyu ka dauki daya zaro ido dauda yayi kafin yace haba dai ina ma laifi kuce arabata kashi biyu na dauki daya Ku dauki daya


STORY CONTINUES BELOW

Wannan karon black snake dinne yayi mgn yace idan ka amince to idan kuma baka amince ba tashi katafi

Tunani dauda ya hauyi idan fa bai amince ba to hakika babu Wanda zai iya kamo mishi su khalifa Dan ya fahimci yaro ne mai matukar wayo sannan ko a kashi dayan nan ne tofa dole sunansa ya fito aduniya wato alhaji dauda yahya wani murmushin mugunta yayi kafin yace ya amince

Black snake yace jeka kawai kasa aranka takardunka sunzo hannunka murmushin nasara dauda yayi yace akashesu duka yaro da yarinyar takardun kawai nake bukata


Black snake yace amma sainan da sati daya tukunna zan tura mutane na sbd a helicopter zan turasu

Jejin da kake mgn bazaiyu ace antura mota ko aje da kafa ba amma parat daya zamu musu

Dauda ya miqe tsaye yana cewa babu damuwa black snake ngd ayi musu kisan wukalanci kafin yasakai yafice

Khalifa bai farfado ba sai dare yana farkawa yaga hasken wuta awaje tashi yayi yafito yaga ashe wuta suka kunna sbd dare wato karare yana fitowa hanyar bukkan daya kwantar da safreena yayi wani tsoho ya riqesa amma ya kwace hannunsa bukkan yashiga yaganta kwance har zuwa yanzu bata motsi wasu zafafan hawaye ne suka wanke masa fuska na tausayin safreena lallai saiya koyawa dauda hankali saiyasa dauda duk second na rayuwarsa mutuwa ce tunda yasasu gudu ajeji

Wannan tsohuwar ce ta kamasa ta zaunar dashi kusa da safreena wasu kwanuka ne ta dauko  masa Wanda akayisu da kwallon kwakwa abinci ne aciki tana murmushi ta tura masa gabansa budewa khalifa yayi yaga wani bakin tuwo da bakin miya wanda ko kashesa za ayi ace yafadi tuwon miye ne bai sani ba

Tunani ya hauyi dole zaici wannan abincin domin ya rayu SBD mutanen kauyen shi sukeci suke rayuwa Dan haka shima  da safreena zasuci domin su rayu

Su tozarta dauda a idon duniya

Tuwon ya hau ci baji ba gani saida yaji karfi sosae ajikinsa  kafin yabari ruwa tsohuwar tabasa ya karba yasha sannan ya tashi ya fito waje ya hau alwala duk suka koma kallonsa har yagama ya gyara guri yatada sallah duk suna kallonsa harya idar tukunna ya koma inda safreena take ya zauna yasa kansa agefen gadon karan datake kwance nan  wata bacci mai nauyin gske tayi awun gaba da shi

Bai farka ba saida rana tayi zafi sosae tukunna yatashi agurguje yayi alwala yayi sallah nan ma saida suka tsaya kallonsa

Wasa wasa saida safreena ta kwashi kwana uku bata farfado yashiga tashin hankali marar misaltuwa Dan shi gani yake kawai ta mutu amma suna kwantar masa da hankali akan cewa tana raye duk da ba yaren juna sukeji  ba

A kwana ukun nan sosae khalifa yasaba dasu  wani lkc har rafi yake binsu kamun kifi

A daren kwana ukun ne 

Safreena ta farka kamar kullum  khalifa yana zaune kusa da ita yaga hannunta yafara motsi

Da sauri yatashi yafara kiran sunanta ahankali ruwa tsohuwan tabasa yabata dagota yayi yamata masauki akatafaren qirjinsa sannan ya hau bata ruwan tana sha tana gamawa ta hau tari yana bubbuga bayanta ahankali da kyar take iya hada harafin sunan  yaya  khalifa

Hannunta yakara kamawa yace safreena gani akusa dake zakici abinci? Daga masa kai tayi alamun eh da kansa yadinga bata abincin tana ci harsai da ya tabbatar taci dayawa kuma ta koshi tukunna yabarta

Da washe gari ta warware dama gajiyar gudu ajeji ce da yunwa da rashin bacci ga kuma tashin hankali

Sosae suka saba da yan kauyen duk da basu iya mgn da juna saidai mgnr kurame

Yau sati daya tacika dauda sai murna yakeyi yau za akashesu khalifa da safreena sannan akawo masa takardun dukiyarsa

Su khalifa da safreena da yan kauyen suna rafi gabaki dayansu sunata wasa da ruwa safreena sai tsokanar khalifa take da gangan zata dibo ruwa ta watsa masa

Yayi kamar bai San tanayi ba

Hade rai tayi tazo gabansa cikin shagwaba tace shine kayi banza dani zaro ido yayi yace na isa nayi banza dake ai sai Allah ya tmbyeni kawai zanso ki natsu ne SBD naga alama kamar kin manta kalubalan dake gabanmu sannan kum.....bai karasa ba yaji karan bindiga daga sama

Da sauri safreena ta rungumesa SBD tsoro


Jan hannunta  yayi cikin tashin hankali amma inaa an kewayesu ko ina harbin bindiga ne

Saiga mutane sunfara  zubewa kasa sakamakon bullet din dake huda cikinsu

Duk a mutanen kauyen nan babu wani kwaro da yayi saura araye

Idon safreena a kulle gam tana jira taji bullet ajikinta amma can anjima taji shuru tana bude ido tayi arba da gawanwaki ihu tasaka da karfi tafara kiran sunayen yan kauye amma ina babu mai sauran motsi khalifa mutuwar tsaye yayi domin a idonsa mutane sukadinga zubewa kuma da gangan su aka ki harbinsu aljihunsa ya shafa yaji takardun suna nan Dan baitaba rabuwa dasu ba 

Karasowa gabansu

Sukayi wani yasa hannu zai kama safreena da zafin nama khalifa ya fizgota bayansa

Amma ance sarkin yawa yafi sarkin karfi

Yanje safreena sukayi da karfin tsiya suka rufe khalifa da duka baji ba gani

Gabaki daya sunyi mai jina jina safreena ihu kawai take tana kuka


Wayyo kuyi manage da wannan sai mun hadu a next page

Wlh wnn ma da kyar nayi insha Allah gobe zan sake typing


Comments

An


Share

By mommyn Ahlan

🌳🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Gsky Ku tayani jaje phone dina taki gyaruwa
Baxaku dinga samun typing akai akai ba amma idan nasamu aron waya zaku dinga gani😭

بسم ا لله لر حمن لر حيم
🅿_9⃣➡🔟

Dukansa suke suna tmbyarsa ina takardun suke
Da sukaga bazaiyi mgn bane sai daya daga cikinsu yace  wannan yaron taurin kai ne  dashi
Bazaiyi mgn ba amma idan muka Jibge yarinyar zaiyi jawabin inda takardun nan suke
Ganin anfara wanke safreena da zafafan mari ne yasa khalifa cewa Ku dakata zan Baku takardun dry suka sheke dashi kafin suce to kawo takardun
Khalifa murmushi yayi yace ai hannun kuturu da makaho za ayi Ku bani safreena nabaku takardu
Sukace basu yarda ba bazai raina musu hankali ba
Dry khalifa yafarayi da kyar yake iya mgn yace ai bazaku iya kashemu ba har sai munbaku takardun idan kuma kuka kashemu wazai Baku tunda babu Wanda yasan inda na boye takardun dole idan Ku barmu araye harsai nabaku
Shuru sukayi domin sunsan mgnr khalifa gsky ne idan suka kashesa basu karba takardun ba black snake zai kashesu Dan haka suka tura safreena
Tana zuwa ta rungumesa tana kuka kallonta yayi kumatunta yayi jajur bakinta yafashe SBD marin datasha hawayena ya zubo a fuskan khalifa hannunta yariqe gam ya kashe mata ido sannan ya kallesu yace musu muje
Ba musu suka bi bayansu tafiya ahankali khalifa da safreena sukeyi yayinda suka riqe da hannun juna
Saida sukazo saitin rafi khalifa ya kalli safreena yace bani rigan saman jikin kin nan ba musu ta cire tabasa dama nashi ne Wanda yabata ranan
Kallonsa sukayi sukace to me kake nufi da abaka riga murmushi khalifa yayi jini na fita abakinsa yace yanzu zaku gani kudai burinku ina na Baku takardu ko? Sukace eh yace to Ku kwantar da hankalinku yanzun zan Baku
Daure kugunsa yayi da rigan da safreena tabasa
Ya rige hannun safreena ya kallesu yace kunyi kadan nabaku takardun nan ko da kuwa zan mutu domin sai burina yacika
ga sako Ku fadawa dauda ko da na mutu safreena zata dawo ta wargaza rayuwarsa kamar yanda ya wargaza tata
Sannan kuma ni idan ban mutu ba inanan dawowa na tarwatsa rayuwarsa aduk second na rayuwarsa mutuwa ce
Zamu fita ajejin nan bayan mungama gudu acikinta
Zamu dawo yana gama fadin haka yaja hannun safreena suka fada ruwa
Harbi suka dingayi aruwan amma inaaa su khalifa sun tsere
Dauda tsaye a parlounrn Abba sai safah da marwa yakeyi yana jira yaji gud news ankashe khalifa da safreena
Sannan ankawo masa takardun dukiyarsa har lissafi yakeyi nanka kasashen da zaije da kalar matar da zai nema
Su mutanen black snake babu kalar neman da basuyiwa su khalifa ba amma basu gansu ba gashi sunajin tsoro su koma suce su khalifa sun tsere ai abun kunya ne agaresu
Nandai sukadinga shawara daga karshe suka yanke kawai su koma sunje sunshiga helicopter dinsu suka kunnata  taki tashi nan hankalinsu yatashi gashi wayoyi babu network
Nan fa idanuwansu suka raina fata can zuwa anjima sukaji kukan kura nan suka fara gudu ajeji suma
Su khalifa sunyi tafiya sosae acikin ruwa saukinta ma sun iya swimming Dan haka basu sha wahala sosae ba
Wani jeji suka kara riska agabansu kuka safreena tasaka tana cewa gudu ajeji bazai kare ba
Muna fita awani ga wani sai yanzu mutuwar wa incan qabilun yafado mata kuka sosae ta hauyi Wanda ko amafarki bata taba tunanin zata riska irin wannan rayuwar ba
Juyawa tayi ta kalli khalifa taga hannunsa jini na zuba alamun bullet yashiga baya baya yayi ya jingina da wata katuwar bishiya mai cike da duhun gske
Da sauri safreena tazo garesa ta riqesa tanaganin bullet yashiga jikinsa takara sautin kukanta tarasa yazatayi sunansa ta hau kira tana kuka
Khalifa ya dago kai zai mata mgn yaga wata katuwar maciji tawajan wuyanta yasa hannu ya kamo macijin yasaresa a hannu
Wurgi yayi da ita sannan ya kunce rigan kugunsa ya daure hannun yasa baki ya zuqo dafin
Ya tofar sannan yafadi kasa asume
Kansa safreena tayi tana jijjigasa amma gabaki daya jikinsa yayi sanyi
Tarasa ihu zatayi ko kuka zatayi
Rungumesa tayi jikinta na ba'ri

Kuyi hakuri da wannan

😭😭😭ba waya yanzu
Comments
And.  Share

🌳🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Short story✍🏻

بسم ا لله لر حمن لر حيم
😂😂gsky shiyasa nake sonki my cwty surayyah duk masoya book din🌳gudu ajeji🌳Ku hado kudi Ku saimin waya domin abban ahlan yace baxai siya yanzu ba 😂

My dear khadija journalist miss u
Wannan page din Ku ne my fans ina sonku ina kaunar Ku ina ganin comments kuma inajin dadi kucigaba da comments ni kuma zan cigaba da karban aron phone😂domin muku typing ko kadan ne
Kuyi manager da wannan

🅿_1⃣1⃣➡1⃣2⃣

Ta kai kusan awa uku rungume da khalifa amma har zuwa yanzu baya motsi waige2 ta hauyi ko zataga wani halitta amma shuru
Tashi tayi taimama ta tada sallah adduah sosae tayi sannan ta koma ta daura khalifa bisa cinyarta ta rufe ido can zuwa anjima taji ana taba khalifa da sauri ta bude ido wani mutum tagani da kayan maharba murmushi yamata
Tambyarsa tafarayi waye kai? Amma ko amsa bai bataba kan khalifa yayi yafara kokarin cire masa bullet din dake jikinsa
Bayan ya cire masa ne
Ya dauko wata garin magani acikin jakarsa ta fata ya barbadawa khalifa awajen Harbin da kuma inda maciji ya saresa
Yana gamawa yatashi yadauki jakarsa ya hau tafiya gdy safreena ta hau masa gamida tmbyarsa wayeshi amma ko uhumm bai cemata ba saida yadanyi nisa kafin ya juyo yamata murmushi gamida jefo mata wata kullin magani zuwa tayi ta durqusa ta dauka kafin ta taso bata gansa ba yabace bat
Duk yawan mutanen black snake babu Wanda ya koma gida araye
Dauda
Hankalinsa ba karamin tashi yayi ba babu mutanen black snake babu labarinsu gashi jejin ba network gabaki daya ransa abace yake
Har dare khalifa bai farka ba tsoro ne Yakama safreena sai adduah take domin wannan sabon jeji cike yake da duhu gashi babu motsin wani bil adam
Adduah take idan sun mutu Allah yasa karshen wahalarsu kenn ajejin nan har zuwa yanzu khalifa yana kwance akan cinyarta rungumesa tayi ta kwanta akan qirjinsa
Wani ikon Allah Bacci ne mai nauyin gske ya kwashe safreena bata farka ba saida taji wata zabebbiyar zafin rana tukunna ta bude ido
Mamaki ta hauyi lallai Allah shike kare bawansa daga dukkan sharri idan Allah yakare bawansa babu wani mahalukin daya isa ya cutar dashi
Hamdalah tayiwa ubangiji sannan tafara kokarin daga khalifa daga jikinta motsi yafarayi gamida bude idonsa ahankali ahankali yana ambaton sunan ubangiji yana miqewa zaune
Wani dadi ne ya rufe safreena ta hau kiransa da wata sabuwar sunan da batasan lkcn da yafito daga bakinta ba wato (MY HERO) kiransa take tana dry hadi da kukan farinciki harda sujjadar shukur tayiwa ubangijin talikai
Khalifa kallonta yayi gamida sakar mata murmushi Wanda saida
Taji tsikar jikinta yatashi tayi saurin kauda fuskanta gefe tana masa sannu
Jinginuwa yayi da bishiyar dake kusa dashi
Sun kuyar da kanta kasa tayi wani tausayin khalifa ne yakamata duk halin da khalifa yashiga a yanzu duk adalilinta ne batasan lkcn da wasu zafafan hawaye suka zubo mata ba data tuna irin kalar rashin kunyar da tayi masa
Lallai kam rayuwa kenan Wanda kake kallo ba kowa bane ko kuma kake masa kallon banza hakika wata rana shi zai maka rana hakika khalifa yacika jarumin uban maza gagara kasa hakika khalifa namijin duniya ne idan har Allah ya ara musu rayuwa mai dadi nan gaba bayan sun gama gudu ajeji tofa saita....

Bata karasa ba taji muryansa nace mata kukan me kikeyi kuma bana CE miki banaso nakara ganin ko da digon hawayenki ba yayi mgnr yana mai hade giran sama Dana kasa
Kukan sosae tasaki tace yaya khalifa inason nazama mutumiyar kirki inason inzama yarinya kamila mai natsu
Shuru yayi yana kallonta kafin yace duk abinda kika lissafa kina dashi
Mace tagari CE ke
Murmushi tayi tace da gske ya jinjina mata kai
Kuyi manager da wannan plss

Luv u oll
Comments
An
Share

🌳🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Ina tayaki murnan kammala shahararren book din ki  (ummu nashma ) wato nasmah ko nasirah Allah yasa kinfara sabo asaa❤

Short story✍🏻

بسم ا لله لر حمن لر حيم
🅿_1⃣3⃣➡1⃣4⃣

Zata karayin wata mgn yace kitashi muyi sallah mubar nan wajan Dan zama anan akwai hatsari
Ba musu ta tashi taimama sukayi sakamakon rashin ruwa awajan
Bayan sun idar da sallan ne khalifa yatashi yafara tafiya tana binsa abaya
Tunowa tayi da maganin da maharbin nan yabata ta juya ta koma da gudu khalifa yana tmbyarta ina  kuma zataje batako kulasa ba saida ta dauko maganin tadawo tace maharbin nan dana fada maka jiya shiya bani wannan maganin tafada tana nuna masa karba yayi ya kalla kafin yasake miqa mata
+
Suka hau tafiya  har yamma khalifa daurewa kawai yakeyi amma shi kadai yasan abinda yake damunsa gabaki daya sunji jiki ga bakinsu yayi fari fat alamun yunwa da qishin ruwa
Suna cikin tafiya safreena ta hango wata yar karaman bukka tsalle tayi tace yaya khalifa kalli wata bukka acan da kyar khalifa ya iya daga kai ya kalla murmushi yayi yace to mu kuma mai zamuyi da bukka tace zama mana
Wata yar' karaman hanya tagani tace laah yaya khalifa kalli wata yar' karaman hanya a can wajan muje mugani gudu tasa da niyyar bin hanya da sauri khalifa ya cafko hannunta yace ki natsu
Domin wannan jeji naga kamar akwai hatsiri dole mubi asannu bayansa ta koma shi yayi gaba
Suna fita sukaga wata yar karaman rafi ihu safreena tayi Wanda saida khalifa ya tsorata harara ya galla mata Wanda saida taji gabanta yafadi nan ta natsu gamida sun kuyar da kanta kasa
Rafin suka leka Wanda cike yake da albarkatun kifaye murna sosae khalifa ya hauyi yayinda fuskansa dauke da kyakkyawar murmushi
Ruwa suka hau sha kamar ba gobe
Bayan sunsha sukayi alwala suka gabatar da sallar azhar da la'asar
Da hannu khalifa ya hau kama kifi saida yakama manya2 guda 6 safreena bude baki tayi tana kallonsa tace to yanzu yaya khalifa taya zamu ci
Murmushi yamata batare da yayi magana ba ya gyara kifin ya wanke duk tana zaune tana kallonsa
Harya gama
Tashi yayi ya hau tafiya tana binsa abaya wajan wannan bukkan sukaje
Khalifa ya hado kirare ya dauki dutse yan daidai guda 2 duk abinda yakeyi safreena ta zuba masa ido tana kallonsa
Qyatta dutsen yayi saiga wuta yakama da sauri safreena ta tashi zata gudu dry khalifa ya hauyi yana cewa ina kuma zakije ?

Ido take zarewa tace dama yaya khalifa ka iya magic ne ? Magic kuma safreena meyasa kikace haka ?

Turo baki tayi cikeda shagwaba tace to ba gashi ka kunna dutse yakama da wuta ba
Kallonta yayi yace shagwaba yana miki kyau idan kikayi har burgeni kikeyi
Sannan wannan ba magic bane dabara CE ta yan'kauye Dan baki taso a kauye bane kuma baki taba zuwa ba shiyasa
STORY CONTINUES BELOW
Zaunawa ta koma tayi tace yanzu kam ma  ba kauye ba jeji ma nake dry khalifa ya hau mata SBD yanda ta karashe mgnr ne yabasa dry
Kallonsa safreena takeyi tace nidai idan kana dry kyau kake karawa yaya khalifa
Kallonta yayi batare da yayi magana ba itama tashi tayi tashiga bukkan nan ta hau karkadewa ganye ta yanko ta hau share bukkan shi kuma khalifa yana aikin gasa kifi
************
Ba karamin tashin hankali black snake yashiga ba sakamakon rashin dawowar mutanensa SBD Wanda yake jidasu ya tura
Waya yadaga ya kira dauda yace wai bangane ba na tura mutane na amma  basu ba labarinsu ko lafiya ?

Dauda cikin tunxuran zuciya yace nima ai shurun naji
Black snake yace wlh idan wani Abu yasami yarana saina kasheka dauda kai da Dan iskan yaron nan
Yana gama fadin haka ya kashe wayar
Dauda shawara ya yanke shida kansa zaije jejin nan domin ya koyawa khalifa hankali lallai khalifa yayi wasa dashi baisan hatsabibancin sa bane amma yanzu zai gane yaja da Wanda suka fisa ma balle shi yaro karamin alhaki

********

Cin kifin nan sukayi sosae suka koshi suka kora da ruwa
Duk da ba gishiri balle ayi tunanin maggi ko oil burinsu kawai su koshi
Har dare bayan sun idar da sallah isha suna zaune awajan bukka ga wuta naci Wanda khalifa ya kunna musu da kirare
Shuru sukayi kafin safreena ta katse Shurun da cewa yaya khalifa kataba soyayya ?

Tambayarta ta yajita daga sama Dan haka yace meyasa kika min wannan tmbyar ?

Sosa keya tayi tana jujjuya idanuwanta Wanda suka kara mata kyau tace kawai tmbyarce tazomin kabani amsa
Yace eh na taba lkcn ina....bai karasa ba yaji safreena ta buga wata uban tsaki Wanda hakan ba karamin mamaki yabawa khalifa ba yace safreena lpy kuwa wannan tsaki haka?
Cikin fushi tace to ni ina ruwana
Yace ina ruwanki dame  safreena?
Tace da tmbyarka danayi ko ka taba soyayya ta karashe mgnr tana murguda masa baki murmushi yayi yace to ai baki tsaya kin karasa jin lbrn ba kika katseni itafa yarinyan ma tayi aurenta babanta ne yace bazai aureta ba shine yabayar da ita ma wani dan Dan' uwansa
Dry tayi tace lallai fa ya kyauta kam dama zatayi karanbanin auren mijin da banata ba
Tashi tayi tashige bukkan khalifa ya bita da kallo yakasa fahimtar mgnr ta
Can ta leko taga ya kwanta awaje tace yaya khalifa kashigo mana tashi yayi yana mata kallon amma bakida hankali
Yace inadin zan shigo safreena?

Hankalinta kwance batare da tunanin komai ba tace ciki mana
Murmushi yayi yace lallai safreena har yanzu akwai yarinta na yawo asaman kanki
Mu kwanta adaki daya ke bakisan duk inda mace da namiji suka hadu waje daya su biyu cikon na ukunsu shaidan ne
Yakamata muguji sharrin shaidan da sharrin zuciya
Ke amana CE agareni inaso na sauke wannan amanar kullum adduata Allah ya fitar damu cikin wannan jejin sannan na maka dauda a kotu ayi masa hukunci daidai da abinda ya aikata
Tunda khalifa yafara mgna ta natsu tana sauraronsa yana dasa aya tace haka amma kuma ai Allah yaga zuciyarmu bamu da wata mummunar nufi
Murmushi ya kumayi yace har yanzu dai baki ganewa safreena ita zuciya batada qashi sai tsoka
Kitashi ki shiga ki kwanta
Kin tashi tayi tace nikam bazan iya bacci na barka anan kai daya ba saidai mu kwana anan
Khalifa bai kara mata magana ba tashi tayi tashiga ta dauko maganin da maharbin nan yabata tazo ta zauna kusa dashi hannunsa ta kama ta hau barbada masa maganin sai binta da ido yakeyi tana gamawa yayi murmushi yace ngd
Hade rai tayi ta tashi ta ajiye maganin tadawo
Dry yayi yace to shi kuma wannan fushin na miyene da yazo yanzu kefa kincika rigima
Nan ma bata kulasa ba shima kyaleta yayi ya cigaba da hidimarsa
Da

Washe gari dauda
Ya shirya helicopter da wasu majiya karfi da garada zasuje jeji

Sai mun hadu a next page

Comments
And
Share
By momyn ahlan✍🏻✍🏻

🌳🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Kuyi hakuri fans 🤦🏻‍♀har yanzu babu labarin waya
Wannan page din Ku ne 💘Allah bar kauna💘

Sannan ina barar adduar Ku mahaifiyata bata da lpy Ku tayamu da adduah Allah yabata lpy🤲🏻
Kuyi manager✍🏻da wannan
Short story✍🏻

بسم ا لله لر حمن لر حيم
🅿_1⃣5⃣➡1⃣6⃣

Har yashiga helicopter aka kunnata taki tashi
Akayi akayi amma taki
Tsaki dauda yashiga jerawa ba qaqqautawa cike da qunan zuciya ya kalli mutanansa yace to uban me kuma yasamu jirgin yanzu?+

Daya daga cikin mutanan nasa ne  yace oga wlh lpyr jirgin nan qlu bansan mai kuma yasameta yanzu ba
Idon dauda ne ya canza kala zuwa jajur da karfi ya kwala kiran sunan khalifa
Yana huci saina kashe ka khalifa ni dauda nine ajalinka saina kashe ka saina nuna maka cewa ni  hatsabibi ne saina gwada maka dauda bayada imani ko kadan nayi da wa inda suka fika jida taurin kai kuma duk na shafesu
Kallonsu yayi yana huci yace agyara jirgin nan domin jejin nan dole naje dole na koyawa Dan iskan yaron nan hanabakayana kaiwa nan ya koma cikin gida rai bace
Yana shiga wayarsa ya hau ringing yana dubawa yaga sunan black snake tsaki yaja kafin yadauka cikin isa da gadara yace miye ne kam black snake kafa ta kuramin dame zanji ?
Cikin fushi black snake yace kai dauda kai karamin Dan iska ne ni zaka gayawa zancan banza to wlh nabaka nan da 1wk mutane na su dawo

Dry dauda ya sheke dashi yace dauda shima gagare ne ba kanwan lasa bane mu zuba mugani black snake shege ka fasa yana gama fadi ya kashe wayar
******

Yau safreena ta tashi da wata matsanacin ciwon ciki da ciwon Mara sai juyi take a bukka takasa fitowa khalifa yana waje duk a tunaninsa bacci takeyi domin tunda tafito tayi alwalan asuba ta koma bukkan ta kwanta bata kara fitowa ba har wajan karfe 1 jin shurun yayi yawa yasa khalifa ya lekata idan ma bacci take ta tashi tazo taci abinci ga mamakinsa yana lekawa ya ganta kwance fuskanta shabe shabe da hawaye da kyar numfashinta ke fita sama sama tana rike da cikinta da maranta
Cikin tashin hankali marar misaltuwa yakarasa wajanta ya dago da kanta ya daurata abisa cinyarsa jikinta duk ya jike da zufa alamu tanajin jiki
Murya na rawa ya hau jera mata tmbyoyi
Safreena! Safreena! Safreena
Meya sameki ? Meke damunki ? Me yake miki ciwo ? Sannu Dan Allah ki fadamin menene ke damunki
Cikin wahalalliyar murya tafara hada kalmomin mgn
Tace yaya khalifa cikina marana ciwo
Khalifa yama rasa yanda zaiyi da ita
ajiyeta   yayi yafita ya dibo ruwa yazo yayi tofi ya dagota yabata ta karba tasha
Shuru tayi ahankali taji ciwon namata sauki
Ga kasanta yafara jiqa
Wani hawaye ne mai zafin gsk ya zubo mata gashi bakon watanta yazo kuma baya mata da sauki yanzu yazatayi ga khalifa wani kunya ne taji yakamata ta fara tsinewa dauda acikin zuciyanta
STORY CONTINUES BELOW
Bacci ne mai nauyi yayi gaba da ita ajikin khalifa
Bata farka ba sai wajan karfe 4 tana farkawa da khalifa tafarayin tozali murmushi ta sakar masa
Ya maida mata shima tashi tayi taji batajin ciwon sosae ba kamar dazu ba
Tana tashi zaune taga jini ya gangara har bakin kofar bukkan da suke zaune wata kukan bakin ciki tasaki tasa tafin hannuwanta ta rufe fuskanta
Sai a lkcn khalifa ya kula Dan shi tunda tafara bacci yatafi duniyar tunani Dan haka bai San halin da take ciki ba sai yanzu
Da yagane me takeyiwa kuka yatashi yafita
Ba da jimawa ba yadawo amma bai shigo ba lekowa yayi yace safreena ki daina wannan kukan kinga bakida lpy karya kara miki ciwo kitashi kije rafi ki gyara jikinki
Cikin kukan bakin ciki tace to wani kaya canza ?

Shuru yayi zcyrsa na masa zafi ga tausayin safreena
Yace bari na cire nawa nabaki ido waje take kallonsa kafin tace kai kuma fa
Murmushi yayi yafita ya dibo kasa ya zuba sannan ya jire rigansa na saman yarage vest ajikinsa tace to barshi haka zanyi manager na daura Dan kwalina
Murmushi yayi
Ta hade rai tace to rufe idonka na wuce
Ba musu ya rufe gamida juya bayansa tafita
Taje rafi ta wanke jikinta da kayan bata koma inda khalifa yakeba har gefen magriba saida kayanta sukasha iska tukunna tasa ta yanka Dan kwalinta kadan tayi ciko dashi agabanta
Tadawo tasa mesa zaune ya kunna wuta murmushi tayi tamiqa masa rigansa
Yace kixo kici abinci yamutsa fuska tayi alamun batajin dadi bazata ciba

Girgiza mata kai yayi alamu bayason gardama
Haka kawai ta tsinci kanta da kasa yimasa musu akan bazata Ciba duk da batajin zata iya ci
Khalifa da kansa yadinga bata kifin daya gasa Wanda shine abincinsu
Awannan sabon jejin da suka shiga
Agurguje
Kwanan safreena biyar ta warke tayi wankan tsarki khalifa yace safreena tunda kinji sauki yakamata mubar wajan nan
Tace to amma yaya khalifa anya zamu fit...bata karasa ba yace mata shiii batason jin komai kawai muyita adduah dama Allah yace zai jarrabe bawansa ta inda baya tunani ki kaddara wannan  itace jarrabawan mu kuma allah yana gwadamu yaga ya karfin imaninmu yake Dan haka karki karaya mucigaba da gudu a jejin nan har Allah ya fitar damu
Murmushi tayi hawaye na zuba a idonta tace muje yaya khalifa na yarda da kai million%
Shima murmushi yayi suka tashi
Suka fara tafiya

Dauda

Angama shirya helicopter
Dan haka sai jeji
Sunyi tafiya kusan kwana  biyu  kafin wata camera mai nuni Wanda su dauda suka taho dashi yafara nuna danger alamun akwai mutum mgn yayi Wanda yake kula da camera din yace oga akwai mutane anan wajen cikin qaguwa yace asauka anan
Su khalifa da safreena suna cikin tafiya sukaji karan helicopter gabaki dayansu saida hanjin cikinsu ya tsinke afili khalifa yace !daudaa!

Ido waje safreena ta dafe qirji tace baba dauda dai kuka tafara tana cewa mun shiga uku da wannan bakin mugun azzalumi butulu baciyi ama.....bata karasa ba taji bindiga
Hannunta khalifa yakama suka fara gudu amma inaa mutanan dauda sun kewayesu khalifa baiyi auni ba yaji saukan kotan bindiga akai yasaki hannun safreena ya fadi kasa rufesa da duka sukayi baji ba gani
Yayinda wasu ke riqe da safreena
Jina jina sukayiwa khalifa kafin dauda yafito khalifa yana ganinsa ya hau dryn karfin hali naushi dauda ya kaiwa khalifa Wanda hakan yasa takardun dake jikinsa ya fado kasa yasa hannu zai dauka dauda ya harbesa ahannu
Amma yaki yasaki ihu safreena CE tayi kara gamida cewa yaya khalifa
Daukan takardun dauda yayi yace dama na gaya maka yaro rijiya bawajen wasan makaho bane yanzu wayayi winning din game din ?

Murmushi khalifa yayi yace dauda wasa bai kare ba yanzu aka fara ai dama jarumi baya nasara lkc 1 kasa aranka zan dawo domin na nuna maka  banbancin jahili da mai ilma
Dryn mugunta dauda yayi yace idan ka rayu kenn yana fadin haka yakarawa khalifa harbi har biyu safreena CE ta kwace taxo gaban dauda ta wankesa da maruka har biyu

Da iya karfinsa ya mareta ta gangara wata tsiririyar rami mai kamar hanya
Takardun ya kalla yayi wata murmushi yace lkc yayi dauda
Yace Ku cillar da Dan iskan yaron nan kuzo mutafi
Cilla khalifa sukayi
Suka shiga helicopter dinsu
Su tashi sai gida

Tofa anayinta kudai kubiyo ni muji su khalifa sun mutu ko suna raye

Comments
And
Share
By momyn ahlan✍🏻

🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Gsky nayi missing dinku my fans momyn ahlan tadawo
domin cigaba da nishadantu daku kudai ku dage da gobarar🔥cmmnts so much qauna 💔fans

Luv u sis amatullah 😘 thix ix ur page inajin ddin cmmts dinki
Short story✍🏻

بسم ا لله لر حمن لر حيم
🅿-1⃣7⃣➡1⃣8⃣
Kwanan khalifa biyu kwance ajeji kamar gawa
Wani jarumin maharbi
Mai suna zakin dawa ne ya tsinci khalifa sbd yakasance yakan shiga jeji yayi har wata uku kafin ya koma wata karamar kauyensu dake cikin gafen jeji mai suna kauyen babban bishiya
Ko da zakin dawa yaga khalifa saida ya tsorata domin shi tunda yake shiga jeji bai taba ganin wata halitta kamar wannan ba domin yanzu ace zai koma kauyensu na babban bishiya saiya kai kusan rabin wata kafin ya isa duk da yanada doki+
Durkusawa yayi gamida yin addua kafin yataba khalifa ya tabbatar tabbas mutum ne hannunsa ya kai saitin hancin khalifa baiji komai ba yasake kai hannunsa saitin qirjin khalifa nanma shuru yaji gabansa yafadi kunnansa yakara aqirjin khalifa yakai kusan 30scnd kafin yaji kamar zcyrsa tana harbawa da sauri yadagosa dama yaga jikinsa da kamar  an harbesa dan yaga shatin alburushi agefen kafadarsa da kuma gafen wajan dantsansa tunani ya hauyi shi kuma wnn daga ina kuma ko meya samesa

Wuka ya ciro gamida kunna wuta sannan ya hau cire masa bullet din yasa masa magani ya daukesa ya daurasa adokinsa
Da yazo da niyyar kaiwa wata uku a jeji amma sakamakon yanda yaga wannan bawan allahn nan yana bukatar taimako hakanne yasa yafasa ya dauki hanyar babbar bishiya

Gudu zakin dawa yakeyi baji ba gani kwanansu sha uku kafin  suka isa kauyen saidai yadan tsaya yasa masa magani ya du'ra masa ruwa
Kauyen cike yake da albarkatun shukuki na ya"yan itatuwa
Ga albarkatun gona  kauyen dai gashinan kore shar dashi masha allah abin sha,awa
Amma daka ga mutanan kasan basa fita cikin gari amma mutane ne masu karamci da gani

KO da zakin dawa yadawo duk wanda yagansa saiyayi mamakin ganinsa domin wa'adin dayakeyi ajeji bai cika ba yadawo amma sakamakon ganin mutum atare dashi yasasu gane cewa lallai to akwai matsala
Gidansa ya wuce kai tsaye ya kirawo masu magani aka duqufa yiwa khalifa magani
Wasa wasa saida khalifa ya share sati 2 amma duk da haka bai farfado ba amma ba laifi jikin nasa yayi kyau dan sosae zakin dawa ke basa kulawa haka kawai yaji khalifa ya kwanta masa arai
******
SAFREENA

kwananta daya kwance ajeji sakamakon marin da dauda yamata ta gangara ta bugu da wata dutse tana farkawa kasa gane kanta tayi dan gabaki daya ji tayi kanta yasara mata  batasan wacece itaba hanya tagani tasa kai tafara gudu ajeji baji ba gani
KO tsayawa hutawa batayi sannan idan dare yamata bata tsoro ko tunanin abinda zai sameta dan kuwa hankalinta yagama fita
A wannan gudun da safreena takeyi ne saida ta dibi kwanaki sha hudu masu lafiya tukunna akwana na shabiyar ta tsinci kanta akan titi da yamma tafito titin kenn tana shirin burmawa wata jejin
Saiga wata mota nan take tayi sama da ita nan take numfashinta ya tsaya cak
Cikin tashin hnkl yafito amotan  wani saurayi ne  kallonta yayi cike da tsoro bakinta fari sol abushe harya tattare da fatan bakinta rigan jikinta duk ya yage yayi kace2  kafafunta kuwa bazasu misaltu ba yanda suka koma
Nan da nan yaji tausayinta yakamashi yaduba yaga jejin da tafito tsoro yakamasa taya mutum bil adam yafito awannan gungumiyar jejin da rai agogon hannunsa ya duba yaga karfe biyar na yamma da sauri ya sureta ganin bata motsi yasata amota yana adduar allah yasa dai ba mutuwa tayi ba da mugun gudu yaja motan suka bar wajan
******

DAUDA

adan wannan lkcn duniya tamasa dadi ba karamin facaka yakeyi da kudi ba
Asati biyu kadai yaje kasan turawa sunkai goma neman mata kuwa sai abinda yakaru domin yanzu dauda baya neman mata a nigeria saidai baturiya yar kasar waje yayi abokai tantirai ga qattin da yajerasu agidan duk da yanzu baya kai kwana 2 a nigeria zai barta

More comments more typing
Share
By mmn ahlan✍🏻

🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Short story✍🏻
Gsky ina ganin comments daga wasu group din kuma inajin ddi ngd
Yan group din gudu ajeji karku yarda afiku comments awasu groups din dannaga ana shirin afiku🙄gsky ku kara dagewa

بسم ا لله لر حمن لر حيم
🅿-1⃣9⃣➡2⃣0⃣
Wannan kuwa itace sanadiyyar rabuwar khalifa da safreena
Shin zasu sake haduwa kuwa ? +
Ku dai kuci gaba da bin mmn ahlan dan jin yadda zata kaya

------------------------------

Dauda hankanlinsa kwance babu wanda zai takura masa duniya tasamu amma kullum saiyayi mafarkin maganganun khalifa
Amma daya farka zai bawa kansa kwarin gwiwan cewa to ai sun mutu ya shafe labarinsu
Khalifa idan ma harbin daya masa bai mutu ba wannan jejin kam akwai abunda zai karasasu
(Saidai dauda kamanta allah shike kashewa kuma shike rayawa ba mutum ba )

DA wannan tunanin yake kwantarwa da kansa hankali
******

Sai karfe 8:30
Ya shiga birnin ADAMAWA hospital kai tsaye yawuce wata prvt hospital ne mai suna amana clinic hospital
Cikin tashin hankli yashiga yayiwasu nurses bayani yana tare ne da marar lpy kuma tana bukatar taimakon gaggawa
Cikin hanzari suka fita da gadon daukan marasa lpy suka dauko safreena aka wuce da ita emergency allah yaso a tym din akwai doctors biyu nan suka duqufa bawa safreena taimako da iya basiran da allah yabasu
Magana yayiwa nurses din akan cewa bari yaje gida zai dawo da kanwarsa amma sukace yadan tsaya sbd dole abukaci wani abun yace to ba damuwa
Wasa wasa saida aka kwashe awa biyu da rabi ana aikin akan safreena oxygen aka samata sbd numfashinta ya tsaya
Dayan dr ne yace anya yarinyar nan zata tashi kuwa inagafa ta mutu idan kuma bata mutu ba to gsky bazatayi rai ba murmushi dayan dr yayi gamida cewa haba dr sokoto bai kamata amatsayinka na mai  kare lpyr dan adam kadinga wnn mgnr ba
Sannan da kake cewa bazata tashi ba ai rayuwarta ba ahannunka yakeba
Allah yabaka hkr dr bakura ni bawai na fada da wata manufa bane
Murmushi dr bakura yayi yace kaima kayi hkr
Jin Shurun ne yasashi tashi domin yaje yasake yiwa su nurses mgn saiga dr bakura yafito yana sharbe gumi
Da sauri yataresa dr yadai? Allah yasa dai bata mutu ba murmushi yayi yace bata mutu ba kuma kokarin muke numfashinta yadawo kafin ayiwa jikinta treatment sbd tasamu rauni sosae muje office dina dr yayi gaba yabisa abaya
Zama yayi sannan yayi rubuce2  ya miqa masa
asiyo wa innan yanzu zamuyi amfani dashi
Amma menene din ka ita yarinyar sbd zamu bude mata file gabanshi ne yafadi yanaso yace kanwarsa ce to idan akace mai yasameta haka mai zaice? Kai bari yafada masa gsky kawai
STORY CONTINUES BELOW
Sauya fuska yayi yace dr wlh bansanta va kawai tsintarta nayi ahanya acikin wnn halin
DA mmki dr bakura yake kallonsa yace baka santa bafa kace ? Ko sunanta ma baka sani ba kenn ?

Eh Dr bansanta ba dan allah dr kamin wata alfarma ga card dina ga kuma kudi ayi mata duk abinda yakamata zanje gida wayata ta mutu kuma nasan zasu nemeni hnklnsu zai tashi zanje nataho da kanwata
Ga shi yanxu har 11:30

Murmushi dr bakura  yayi domin ya fahimci gskyr abinda yake fada masa yace to ba damuwa card din da kudin yakarba
Gdy yamasa yatashi ta sauri yafita gashi NABEEL ya dauke masa chaja amota  balle yasa chaji mtssw
Handlam quarters

Awata katafaren gate madaidaici yayi horn gateman ya bude masa yashiga da sauri ko tsaya parking baiyiba yafice amotar
Kai tsaye parlon yashiga ya hau kwala kiran sunan
MADEENA!MADEENA!MADEENA!

da sauri wata yar budurwar yarinya da baxata wuce kimanin 19yeas ba ta fito idanunta da alama kuka tayi rungumesa tayi takara sakin kuka
Sannan tace haba YAYA SAMEER  meya sameka nida mami hnklnmu yatashi munata kiran wayarka switch up duka biyu
Dagota yayi yace oh kash yadafa kansa kuyi hakuri ku
gafarceni wlh matsala aka samu kanwata ina hanyar dawowa na tsinci wata yarinya.....nan yabata lbrn abinda yafaru
Cike da al'ajabi madina tace innalillahi wato dai yaya idan mutum bai mutu ba yanada sauran kallo
Yace kedai bari wlh karkiga jejin datafito  saikin tsorata
Kuma phones dina duk sun mutu ba chaji
Chazar motata kuma nabeel ne yadauka sbd rashin M irin tasa
Murmushi ta hauyi jin yakira sunan nabeel ta juya zata shiga daki saiga kiran mami wanda duk hnklnta baya jikinta
Dauka madina tayi tace mami ga yayan yadawo miqa masa wayar tayi tashiga domin ta shirya su koma hospital din tunda bawani nisa ne dasu sosai ba
Hakuri yabawa mami tareda bata lbrn abinda yafaru nan itama ta tofa albarkacin bakinta
Sannan tace ai angama bikin gobe ma zandawo
To allah dawo mana dake lpy maminmu ta amsa da ameen sukayi sallama

Sameer ruwa kawai yawatsa yasaka jallabiya yafito yasamu madina tana jiranshi da basket din abinci domin yace bazai iya tsayawa yaci ba saiya je hospital din
Kafin su isa dare ya tsala domin kuwa sai karfe 1 suka isa har lkcn doctors suna kan safreena
Basu samu daman samun numfashinta ba kuwa sai gefen asuba
Duk suka fito agajiye ba yadda suke sbd sun sha matukar wahala akan safreena sannu kawai ake jera musu
Gamida yimusu fifita duk da ac dayake tashi awajan
Suma su sameer da madeena basu rintsa ba yanda sukaga rana haka sukaga dare
Saida misalin karfe 11 tukunna aka farayiwa safreena treatment
Su sameer sunje gida dan dr bakura yace akawo mata riga marar nauyi
Sameer kafin suje gida wata yar madaidaiciyar shop mall ya tsaya ya saiwa safreena dogayen riguna kala shidda domin kayan madina bazai mata ba dan madina batada auki ko kadan
Haka dai sameer da madina suka dinga sintirin asibityn har mami ta dawo aka daura da ita
Kulawa sosae safreena tana samun shi masha allah
------------------
Bayan wata uku
Abubuwa dayawa sun faru awannan lkcn
Wanda sai awannan lkcn khalifa yasamu daman farfadowa daga azabebbiyar ciwon dayasha idan ka kallesa saika tsorata sbd wata uwar raman da yayi
KO da khalifa ya farka sunan safreena kawai yake ambata  yana kokarin fita da kyar zakin dawa ya lallabashi ya zaunar dashi aka kawo masa abinci yaci yasa aka kaimasa ruwan wanka yayi wanka tukunna zakin dawa ke tmbyarsa wanene shi bai boye masa komai ba yabasa lbrn
al'ajabi zakin dawa yashigayi shida matarsa yana jinjina kai
Tab lallai wannan dauda anya akwai digon imani atare dashi kuwa gsky allah yana sonku kuma insha allah dauda bazaiyi karshe mai kyau ba
To yanzu ita safreena ina za aganta cikin muryan kuka khalifa yafara roqon zakin dawa dasu koma jejin yadubo safreena
Ido waje zakin dawa ke kallon khalifa yace halifa kasan me kake fada kuwa ?
Kodana tsintoka kafin muzo nan mun debi kwanaki13 kafin kuma ka farfado saida ka kwashi wata uku yanzu watan ka uku kafin ka farka cikeda tsoro da mamaki yake kallon zakin dawa kafin yasa kuka kamar karamin yaro

Zakin dawa yace ai kawai tunda kai ka rayu kana iya zuwa ka dauki fansa akan wannan azzalumin
Amma ita wannan yarinya saidai mubita da addua allah ya jiqanta da rahma
Cikin kakkausar murya khalifa yace aaa aa baba safreena bata mutu ba inaji ajikina safreena tana raye baba kamin alfarma 1 tak
Zakin daya yace fadi naji idan baifi karfina ba
Baba sonake nafita ajejin nan inaso nashiga gari domin bazan taba yafewa dauda ba safreena kuma zan koma na cigaba da mata  addua allah yasa da rabon fuskokinmu su sake haduwa
Wasu hawaye masu zafin gske suka wanke masa fuska
Zakin dawa yace ba damuwa amma kabari jikin ka yakarayin kyau kafin katafi
Khalifa bazai iya musu dashi ba dan haka yace to yadinga kwararo masa addua da ftn samun lada mai yawa awajan ubangiji na taimakonsa da yayi dan yace babu abinda zai iya biyansa saidai allah ya biyasa tunda baya zaman gida amma sbd lpyrsa gashi bai shiga jeji ba

Safreena kuwa watan ta biyu a asibity ta farka amma saidai kash kasa gane mutane tayi jitake kamar yaune aka haifeta su mami da madina sunyi tmbyr duniya ta fadi sunanta amma tace bata sani ba dan haka sameer yasa mata sunan (NAJMA) dashi aka bude mata file
Koda sameer yayiwa dr mgn dr bakura yace a gsky sakamakon buguwan da kanta yayi jini yashiga kwakwalwarta zata iya tunowa da abinda yasameta amma fa saidai atuna mata wajajen da ta taba rayuwa ko kuma ta hadu da wani wanda tasani kuma gsky tana bukatar kulawa sosae dan kar adingayin abinda zai daga mata hnkl
Gdy sameer yayiwa dr bakura sbd ba karamin kulawa yabawa safreena ba
Wanda suke kira da najma yanzu
Mami ce da kanta tayiwa safreena wanka ta gyara mata gashin kanta ta wanke mata shi tass ta shiryata ta shafa mata body lotion nanda nan safreena ta dawo gal da ita amma har yanzu kafafunta a kumbure suke tana dingisawa mami tashafa mata turare kala2 sai wani kamshi safreena take fitarwa mami ta zauna ta baje mata gashin kanta wanda har gadon bayanta tana busar mata dashi da handdryer tanayi tana shafa mata man gashi mai kamshin gske da laushi

Sameer ne da madina sukayi sallama suka shigo dakin cak ya tsaya yana kallon safreena ji yayi duk jijiyoyin jikinsa yadaina aiki ya kura mata ido ko kiftawa ba yayi
Wani bakon yanayi ya ziyarci zuciyarsa
To fa
More comments more typing

Comments
And
Share
By Mmn ahlan✍🏻

🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Short story✍🏻

yaυ wannan page dιn ѕadaυĸarwa ce gareĸυ
gaĸυ nan ĸaмar нaĸa
ιlнaм
мy dear ĸнadιja joυnalιѕт (мarυвυcιyar raѕнιn υwa -rayυwar gιdan ĸawυna and rayυwaтace нearт υ тawan )
мaн ѕιѕтo nerpнerѕerт
doтer ѕυrayya dan ango
dr нerpѕerт
мaмan ғadeelerт ιnajιran wayarĸι ĸι ĸawoмιn na ĸara da nawa 😂)
aмeenaтυ
aѕмa'υ alιero
тeeмaн ғaѕнιon
мd aмιr
мυвaraĸa
ا حلام فاطمة
υммυ aвdυllaнι
мoм aвdallaн
υвeenaн
мaмan ĸυѕar
υммυғaтι
jaммυl
aιѕнa
мoмyn elнaмa
ғaтιмa nυнυ aвdυѕѕalaм+
Λ∩Ð t∏ξ ®ξ§t

Wa ïndä żän ïÿä lïssäfäwä kënän ġä wäċċë bätäjï sünäntä bä hänkälï ïdän näġä ċömmënt dïntä żätä ġänï
nġd
dä säürän ġröüps mämÿn ählän tänä ġdÿ 💔💔

بسم ا لله لر حمن لر حيم
🅿-2⃣1⃣➡2⃣2⃣➡2⃣3⃣
Mami ce ta kallesa ganin gabaki daya yatafi wata duniyar idonsa ƙyam akan safreena
Kai kuma fa? Kawani tsaya abakin ƙofa idan zaka shigo ka shigo idan kuma bazaka shigo ba to ka koma
Sannan wannan kallon da ka ƙura mata ido haka saika ce zaka cinyeta
Madina ganin mami nata zuba mita kuma ko motsi sameer baiyiba yasata tashi dan ita kam harta zauna
Gabansa taje ta tafa hannunta biyu afuskarsa
Firgigit
Yace iye na,am madina me kikace ?
Dry ne ya subuce wa madina har tana cike ciki hararan ta yayi yace wato ina wasa dake ĸo? girgiza kai tayi tana kan dryn bata bari ba tace yi hkr ya sameer ina kaje ne kam mami tana ta yimaka mgn amma baka jita ba
dan sosa keya yayi yace afuwa mamina wlh ban jiba
Girgiza kai kawai mami tayi tace to allah ya kyauta
Kallon safreena yayi yace najma wannan kyau haka mami ta gyaraki sosae
Kasa tayi da kai batare da tayi mgn ba dan mgnr ma bata wahala yakeyi
Bayan kwana biyu aka sallamesu suka koma gida nan suka cigaba da kula da safreena daki daya suke kwana da madina kullum madina tana yimata hira masu dadi amma takasa sakin jiki dasu

Saida khalifa yabawa sati biyu baya kafin yakara warwarewa zakin dawa da kansa ya dauki khalifa yafitar dashi bakin titi na tsawon kwanaki 14
Ko da zakin dawa ya ajiyesa yace kana ganin zaka iya gane komai murmushi khalifa yayi yace eh baba zan gane ngd allah yamaka ma saukin agidan aljanna na taimako na da kayi insha allah idan nayi rai nan gaba zanyi kokari na shigo kauyen jejin babbar  bishiya domin kawo maka ziyara rungumesa
Yayi yace ina maka fatan samun nasara arayuwarka khalifa allah kuma ya daura ka akan dauda murmushi yayi yace ameen baba ngd saduwar alkhairi ya hau dokinsa ya koma
Tsayawa khalifa yayi yana ƙarewa inda yake tsaye kallo to nan din ma inane oho guntun tsaki yaja ya kalli guzurin da yake hannunsa wanda matar zakin dawa ta hada masa murmushi yayi domin yaga ƙauna awajansu
STORY CONTINUES BELOW
Har gefen yamma khalifa yana zaune yana jiran tsammanin inda zaiga mota har gefen magriba sadaƙarwa yayi yatashi zai fara tafiya da ƙafa kamar daga sama yaji karan mota da sauri yayi kan titi yana sa hannu alamun atsaya taimako
Ba zato ba tsammani motar ta bugesa wata burki mai motar yaja gamida fitowa da sauri yayi kan khalifa daya riqe kafafunsa
Wasu samari ne su biyu suka hau masa sannu amsasu yayi yace dan allah ku taimaka kufitar dani gari daya daga cikin samarin yace yanzu dai muna gaf da shiga cikin garin daura ne idan kuma nan zamu ajiyeka to muje kallonsa dayan yayi yace baka da hnkl ko sa'eed baka san mutum ba wata kilama dan fashi ne sun boye nan wajan yayi maka kama da wani bil adam zai tsaya neman taimako
Sa'eed yace haba nabeel kai meyasa kaci ka zargi kaddara ma eh hakanne ai duk wanda yayi nagari dan  kansa kuma bakaga na bugesa da mota bane
Khalifa dake jinsu kalaman wanda aka kira da sunan nabeel ba ƙaramin zafi sukayi masa ba dan dai kawai babu yadda zaiyi ne ga magriba da wallahi bazai shiga ba
Tsaki nabeel yayi ya koma mota sa'eed kuwa kama khalifa yayi yana basa hakuri murmushin karfin hali khalifa yayi yace kayi hkr kaima na hadaka fada da dan uwanka ko
dry sa'eed yayi yace wlh ko daya karkayi tunanin wani abu yanada saukin kai amma saidai matsoraci ne
Gidan baya sa'eed ya budewa khalifa ya zauna yatada motar suka bar wajan amota sa'eed sai jan khalifa yakeyi da hira
Tun khalifa yana amsawa sama sama harya koma yana amsashi sosae yana murmushi
Amma shi nabeel ko uhum baice ba dan shi gsky taimako yana basa tsoro azamanin yanzun nan
Cikin hiran da khalifa da sa'eed sukeyi ne ke tmbyarsa me yakawosa wannan wajan ya zauna kodai tafiya sukeyi yazaga motar tatafi tabarsa
Tmbyar tadan bawa khalifa dry amma saiya dake yace lbr ne mai tsayin gske da kuma al'ajabi dan shi harga allah sa'eed ya burgesa ƙosawa nabeel yayi da hiran nasu ya kalle sa'eed yayi masa magana cikin harshen turanci
Wai dan kar khalifa yaji yace masa sakarai baka san mutum ba kasaki baki kanata zuba masa surutu mtsww
Sa'eed hararansa yayi shima da turancin yace to ina ruwanka nikam ya kwanta min arai
Tsaki nabeel ya kumayi batare da ya kumayin mgn ba

Khalifa kuwa wata uwar murmushi yasaki yana kallon nabeel da gefen ido kafin acikin ransa yace ikon allah duniya kenn wato kowa da irin halinsa to allah ya kyauta yaganar damu akan hanya madaidaiciya
Yana kan tunanin zuci yaji muryan saeed na cewa my new friend yanaji kayi shuru murmushi khalifa yayi daidai lkcn da suka shigo garin daura.
Saeed ya kuma cewa ina zamu ajiye ka ko kuma kafada mana gidanku saimu ajiye ka
Tsaki nabeel yayi gamida yiwa saeed mugun kallo yace allah dan shiga uku? Dan naga alama ɗima kanka yayi yawa murmushi khalifa yayi yace ko ta inama ka ajiye ni ba damuwa niba dan daura bane dan katsina ne
Dry saeed yayi yace lahh ai kuwa gobe zamuje katsina ɗaurin auren abokinmu matar yar katsina ce shi kuma abokin namu dan daura ne dan haka kabari muje tare ko kazo yin wani abun ne dan naga da alama kamar bakasan kowa ba
Da har khalifa zaice aa ya tuno fa bayada ko sisi aljihunsa idan suka barshi daura ai ya kaɗe gsky saeed yanada mugun kirki duk azuciyarsa yake wannan tunanin dan haka ya amince afili

Nabeel kuwa fita yayi amotar aransa yana cewa wlh saeed bazaka jawo akashe dani ba gwanda kai kanada ƙanwa ni kuma ni daya ne awajan iyayena saidai ku tafi tare
Mamaki ne yakama khalifa bama shi kadai ba harda saeed to ina zaije yafita da sauri suka bisa ganin yana shirin hawa mashin
Riƙo sa saeed yayi yace haba abokina miye haka dan allah ?
STORY CONTINUES BELOW
Yace dallah sakeni malam dan kaga munzo a motar ka shine kakemin wulaƙancin to idan har zaka cigaba da biyema wannan mutumin saidai mu raba hanya kai harma da wajen kwana yau dan bazan yarda ahadamu daki daya da kai ba tsakar dare naji saukar harbi inaa samm bazai yu ba haka kawai baka san mutum ba wato kai gaka uban masu shishshigin duniya sarkin azargwaɗi mai baƙin rawani ko to wlh nikam baza ayi haka dani ba

Ran khalifa ne yabaci dan shi fa wani abun shuru yakeyi sbd saeed amma yanzu nabeel yayi mgnr da dole nema yabasa amsa nabeel yana shirin hawa mashin khalifa ya damƙo hannunsa idanunsa harsun canza kala
Nabeel yadan tsorata amma yadake yace ayyo wato ni kaga babu nasara akaina shine zaka aiwatar tun yanzu
Hannu khalifa yadaga masa gamida cewa   enough i said enough karka sake aibata ni nabeel kake ko wane da suna?
Arayuwa kadinga yiwa dan uwanka musulmi kyakkyawar zato
Ko ka manta da cewa manzon allah sallallahu alayhi wa sallam yace
(المسلم ا خوالمسلم لايظلمه )
To wannan bai isheka ba saika cutar dani da baƙaƙen maganganu tun ina shuru bai kamata ba yakamata kamin zato mai kyau duk da banga laifin ka ba sbd yanzu bazaka iya shaidar mutum ba
Amma kai kam banga ta inda zan cutar da kai ba idan ma akwai hakan arai na da tun alkcn da kuka bugeni kuka tsaya dana aiwatar to banyi hakan a inda ba mutane ba sai yanzu da muka shigo jama,a danni nafi kowa rashin kunya baka san ni waye ba haka nima bansan ku ba juyawa yayi ya kalli saeed wanda jikinsa yayi sanyi da kalaman khalifa yace kuyi hakuri ba burina ba kenn na wargaza kanku ngd sosae saeed da taimakon ka agareni kuma bazan manta da kai ba domin ni bana manta alkhairi duk girman sharri nabeel kayi hkr khalifa baya fada ko tashin hnkl sannan idan ranka yabaci acikin kalaman dana fada maka kayi hkr dan ba lallai bane mu sake haduwa dan adam ajizi ne sannan baifi karfin kuskure afada masa gsky ba duk da gsky ɗaci gareta dan haka nake baka hkr ba ƙaramin sanyi jikin nabeel yayi ba gabaki daya gwiwoyinsa sunyi sanyi khalifa ya juya yafara tafiya da sauri nabeel ya riqosa yace dan uwa kayi hkr ka gafarceni wlh bansan abinda yashiga kaina ba amma kayi hkr kazo muje na amince wlh
murmushi khalifa yayi yace aa ba damuwa wlh kuje saeed yace kai dallah kuzo mutafi
Kai nabeel kasan fa ahmad ba hakuri ne dashi ba yanz...bai karasa ba kuwa saiga kiran Ahmad na shigowa wayar saeed yace kun gani ba gashi yana kira dallah guys kuzo mutafi yafada yana mai daukar wayar ya kara a kunne yashiga mota

Ahmad yace wai saeed kuna inane kam ?
Yi hkr aboki gamu nan zuwa
To mu kam mun wuce ku samemu acan katsina road
OK kawai saeed yace kafin ya katse kiran

Saida suka fara wucewa masaukin su sukayi wanka khalifa ya jima yana wanke jikinsa da sabulu kafin yafito nabeel da saeed sun ajiye masa shadda da yadi wanda acikin kayansu wanda suka ɗinka na biki kala uku shine suka cire masa kala ɗaɗɗaya
Miƙa masa nabeel yayi yana dry yace kayi sauri kai kawai muke jira kasame mu a parlor idan ka gama
Murmushi khalifa yayi yace ngd nabeel
Fita yayi yabasa guri
Khalifa ya shafa mai sannan yaɗaga kayan yana kallonsu dabadin ya rame ba ai kayansu nabeel bazaimin ba sbd nafisu faɗin ƙirji
Yana saka kayan ya dauki hula yasaka wow masha allah lallai yau khalifa yafito a khalifansa na da turare ya feshe jikinsa dashi sai wani kamshi yake bazawa kamar shine ango daga fuska yayi fayau abunsa amma cikin zcyrsa tunani yakeyi ta yadda zai billowa babbar lamarin da yake gabansa wayyo safreena kina ina kece karfin gwiwata
agogo yagani akan dressmirror ya dauka ya ɗaura ahannunsa yayinda yake fitowa parlor yace kuyi hkr na bata muku lkc ko
Gabaki dayansu suka zuba masa ido saeed ya riqe baki gamida cewa kutmelesyyy khalifa wlh kar muje ayi tunanin kaima angonne kai kaganka kuwa murmushi khalifa yayi domin yanda ya fuskanci saeed akwai barkwanci
Nabeel yace aini wlh ma nakasa mgn
My man wannan kyau haka
STORY CONTINUES BELOW
Khalifa ma dry suka bashi yace muje fa kafin ango yasake kiranku nikam ba ruwana kun tsaya sai surutu kukeyi nan suka fito suna dry idan kagansu saika rantse sun jima da sanin juna
Har inda ake taron sukaje ahmad sai mita yakeyi ya kalli khalifa suka gaisa daga nan aka cigaba da gudanar da dinner wanda familyn ango suka shiryawa dan uwansu shida abokansa kafin a ɗaura aure akawo amarya asakeyin wata dinner din duk abinda su saeed zasuyi tare da khalifa akayi sosae ahmad yasake da khalifa harma idan wasu friends dinsa suka tmbyesa sai yace amininsa ne haka har akayi taro aka watse ko da suka dawo masauki agajiye suke su hudu suka kwana waje daya da washe gari suka baro daura suka kama hanyar katsina khalifa kallon hanya kawai yakeyi yatafi duniyar tunani
Rabonsa da katsina ya jima gsky ko har yanzu gidansa yana nan daya gina oho to ma ina gidan zaije wani dadi yaji daya tuna takardun gidan suna cikin gidan kuma yasa mai gadi to amma wannan dan tsawon lkcn allah yasa mai gadin yana nan
Karfe 10 suka isa katsina
Karfe 2 kuma aka ɗaura aure sbd ta kama ranar jumma,a ne dan haka ana gama daurin aure suka wuce  reception
Karfe uku suka tashi da niyyar komawa amma dangin amarya suka roqi alfarma su bari sai gobe awuce gabaki daya yanzu zasuyi dinner anjima babu yanda suka iya haka suka hkr suka zauna khalifa yace to nikam bari na samu na wuce gida tuntuni nake
son tafiya amma kun hanani saeed yace kayi hkr mn khalifa idan ka tafi ahmad bazaiji ddi  ba tunda kaga lkc daya aka saba duk da bamu gabatarwa juna kanmu ba dan yanzu babu lkcn hakan sai hnklnmu yasamu angama bikin nan kabari sai dare
to kawai khalifa yace dan bayason yawan magana
Mgn suka farayi akan cewa sukama hotel nabeel yace nifa wlh ban cika son zuwa hotel ba saeed yace to atiti zamu shirya ko kuma mu kwanta idan dare yayi ?

Ahmad yace  kaidai badai magana ba wlh saeed
nabeel yau ne kawai muje hotel din kayi hkr
Khalifa yace idan bazaku damu ba kuzo muje gidana amma fa bansan yana nn ko baya nan ba
Sakeke suke kallonsa
Saeed yace kamar ya ? Kaida gidanka kace baka san yana nan ko baya nan ba murmushi khalifa yayi batare da yayi mgn ba yace lkc yana tafiya yanzu kusan karfe biyar saura muje mugani sannan musan abunyi
Mota suka shiga ahmad yace khalifa kaima dan local government din dutsenma dinne ?

Eh ahmad
Ok wace unguwa kenn?
Unguwar sarki bayan kofar fada
Laahh to ashe kace ba nisa khalifa yyi murmushi yace eh ba nisa Ahmad

Kwatance yayiwa nabeel dan shike driving din motar
Har suka iso gate din gidan fitowa sukayi atare nabeel da saeed da ahmad suna aiyana gidan tun awaje
Kwankwasawa khalifa yayi sun jima suna buga gate din amma shuru dan haka suka yanke shawarar su balla kofar Sai sukaji motsi ana budewa
Baba mai gadi yafito yana fadin suwaye ne kam kum....bai karasa ba yaga khalifa murje idonsa yayi kodai mafarki yakeyi ko kuma gizo ne yace yallabai khalifa kaine ?

Murmushi yayi yace eh baba nine
Amma kuma duk garinnan cewa aka dingayi ka mutu matar babanka ce tace wai kungiyar shan jinin da kashiga ne suka kasheka kuma wai ita bazata taba zuwa nan ba haka tai ta bataka agarin nan shine ni kuma na    ɗauko iyalaina muka cigaba da zama can gidan bayan nan (bosquater) dan kar gidan yabaci
Sbd ban yarda da kalamanta ba shiyasa kullum nake zaman jiranka sbd alkhairin da kamin bazan taba mantawa ba
Murmushi khalifa yayi yace to ai ba komai ban mutu ba da raina
To amma yallabai khalifa ina kashiga haka duk da nasan kana watanni sosae baka zo ba amma wannan yayi yawa
Khalifa  ƙosawa yayi da mgnr yace yanzu de baka ganni da abokaina bane kuma lbr ne mai tsayi abinda yafaru a ƙaƙƙabe mana ƙuran gidan mu shigo mu shirya zamuje dinner ne na abokinmu gashinan ya nuna ahmad
Yace to yallabai khalifa cikin gidan yayi yana kiran matarsa da yaransa

Juyawa yayi yana kallonsu saeed nabeel da Ahmad wanda da kaga fuskokinsu tambayace kwance akai amma khalifa yayi fuska kamar bai kula ba ya dauki hanyar gidan matar babansa duk suka bisa abaya tana tsaye tana shanya yayi sallama juyowa tayi tana kallonsa baki sake
Da karfi tace KHALIFFAAAA dama baka mutu ba
****kai bari mu waiwaye dauda muga wace wainar yake toyawa da dukiyar marainiya
Safreena
---------------------
Kwance yake a ƙasar england awata katafaren hotel mai suna  DOLLAR HOTEL ENGLAND
Wanda hotel ne ko a mutanen england din sai wane da wane
Wata katafaren daki wanda zata iya cin girman parlor daya da wata gado wanda mutane kusan goma zasu iya kwanciya ta ishesu babu takura
A   ƙofa kuwa bodyguards dinsa ne sunkai mutum 20
Dauda kwance atsakiyar gado ga wasu turawan ladys agefensa su uku dukkansu tsirara haihuwar iyayensu
Dauda ma haka sai aikata aikin alfasha sukeyi a bedside drawer kuwa kwalaben giya ne maqil
(Eh lallai kam dauda duniya taqara dadi humm)
Shafasu yakeyi yana jagwalgwalasu iya son ransa
Yayinda su kuma saiyin abunda zai burgesa sukeyi sbd ba ƙaramin kudi ya ajiye musu ba
Duk sun gama fita hayyacinsu sai saukar numfashi dake tashi kawai kakeji a bedroom din

Safreena zaune adaki ta rafka uban tagumi daga waje kuwa kira madina ke kwala mata
Sis najma !sis najma!sis najma!
Harta shigo parlor bata nan dan haka ta shige daki azaune taganta ga hannunta biyu a kumatunta
Girgizata madina tayi tace sis najma tunanin me kikeyi tun daga waje fa nake kiran ki
Firgita safreena tai
Dafe kai tayi tace yi hkr sis ban jiba bane shiyasa
Harga allah taji kiran amma samm sunan bai shigeta ba dan haka batasa arai ita bace dukda tasan ita suke kira da najma din
'''''""""""
Mah Fans adage akara yawan  comments da
Sharhi
m̷u̷ t̷a̷r̷o̷ a̷ n̷e̷x̷t̷ p̷̷a̷̷g̷e̷
Share it

🌳🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
A gsky GUDU A JEJI FANS BANI DA BAKIN DA ZAN NUNA FARIN CIKINA SBD GOBARAR🔥🔥 COMMENTS DIN DA KUKAMIN KUMA YA KARAMIN KARFIN GUIWA Yau ma ABU DAYA KAWAI ZAN IYA CEWA SHINE WANNAN PAGE DIN MA NA MALLAKA MUKU 💃🏻
Am busy that's why bazan iya lissafuku ba luv urs oll mah ppls🥰

Short story✍🏻

بسم ا لله لر حمن لر حيم

🅿-2⃣4⃣➡2⃣5⃣
Murmushi khalifa yayi yace inna ba haka kika so ba ko kinso ace na mutu tunda haka kika dinga fadi na mutu inna ban mutu ba da rai na yanzu ma kuma nazo na gaisheki ne sannan na duba lafiyar ki kuma Alhamdulillah nagani kina lpy ina miki addua Allah yaƙara miki lpy da nisan kwana kici gaba da aibata ni yana kaiwa nan ya juya  ya fice abunsa su saeed suka rufa masa baya suna son yimasa mgna but yanda sukaga fuskarsa babu walwala dan haka suka ƙyalesa+

Kafin su koma an gyara gidan tass mai gadi da matarsa da yaransa
gdy khalifa ya musu
Ya kalli su Ahmad yace zamuyi sallar magriba ne ko kuma mu fara wanka shap shap?
Nabeel yace aa gsky mu fara watsa ruwa tukunna idan yaso sai muyi sallah mu wuce tunda lkc ya ƙarato
Ok mu  shiga
Suka rufa masa baya

Babbar parlour ne kam wanda yaji ɗima ɗiman kujeru na alfarma daidai wadaida sannan akwai toilet a parlor din daga hannun dama akwai wata qaraman parlor da toilet itama acikinta
Sai manya manyan bedroom ko wanne dauke da toilet 
kallon gidan su Ahmad keyi suna jinjina kai afili suka hada baki gamida cewa kai Masha Allah khalifa gidan ka kam tubarkallah yayi mugun kyau
Murmushi yayi yace ango ga bedroom dina can kashiga kayi wanka aciki
Saeed nabeel ga rooms ku shiga kuyi wanka
Ni zan shiga nayi a bathroom din ƙaramin parlour
OK sukace kafin
Ahmad yayi hanyar dakin da khalifa yamasa nuni dashi su kuma su nabeel suka shiga ɗaɗɗaya
Har zai shiga kenn Ahmad yafito yace kayanmu suna both din mota fa yace ok bari nasa ashigo mn dashi kasamu kashiga wanka gashi ana kiran sallah
Ok kawai Ahmad ya fada ya juya ya shiga daki
Khalifa kuma yayi waje yana kwala kiran haruna ɗan baba mai gadi yace ya shigo musu da kayansu dan Allah
Daga nan shima ya wuce ya shiga wanka
Shap shap suka shirya khalifa ya fito yashiga dakinsa yasame su dukkansu sun gama shiryawa ango yana ɗaura agogo yasha kyau sai ƙamshin angonci yakeyi khalifa yace ango kasha ƙamshi fa
Murmushi Ahmad yayi yace ngd aboki ai wani shagalin sai Allah ya kaimu gobe
Nabeel yace kuji dan iska to dawa kakeyi
Oho muku da wanda ya tsargu nakeyi
Saeed yace Allah yaso ban tsargu ba
Khalifa dry kawai yake musu batare da yayi magana ba ya bude  wata ƙaramar akwatynsa wanda yasan kayansa ne aciki ya ɗauka ya shirya shap2 shima saida suka yi sallarh magriba tukunna suka fito
Sai kamshi ke dashi
Baba mai gadi ya kira yace zasu dawo anjima amma baisan karfe nawa zasu dawo ba domin dinner ne

To yallabai khalifa adawo lpy suka shiga mota
Suka kama hanya
Tsaki khalifa yaja daya tuna ATM dinsa yana abuja kuma yanada kuɗi a  account dinsa akalla zaikai 10m to ko wannan dan iskan daudan zai bar mishi to ma dauda mai zaiyi da wa innan kudin nawa  ƙalilan bayan gashi ya ƙwamushe masu dinbin yawa wanda bazasu lissafu ba
Dauda ko kana inane yanzu oho
kai koma ina kake wlh ina nan zuwa gareka domin bazan maka ta dadi ba yanda ka wargaza rayuwar safreena kasamu GUDU A JEJI nayi maka alkawari saika ɗanɗana baƙar azaba a hannu na ni khalifa daka kira da sunan yaro duk wannan maganganun khalifa ya ɗauka acikin zuciyarsa yakeyi baisan afili yakeyi ba gabaki dayansu kallonsa sukeyi harda saeed da yake driving yana kallonsa ta  mirror
STORY CONTINUES BELOW
Lumshe ido khalifa yayi gamida cewa SAFREENA !SAFREENA!SAFREENA !
Allah ya nuna min ke nan kusa  domin dole saida ke zan iya ɗaukar miki fansan abinda dauda ya miki
Nasan bazaki mutu ba batare da kinga karshen dauda ba bazaki mutu ba my safreena inaji ajikina kina raye sannan jikina yana bani kema kinfita awannan wahalalliyar JEJIN
Allah yasa kina hannu nagari safreena jiyayi hawaye yana shirin wanke masa fuska yayi saurin mayarwa shi kam kwata kwata ya manta ma a ina yake balle yayi tunanin dasuwa yake tare bai ankara ba yaji karan ta fi rap rap da sauri ya bude ido yaga fa ashe ba shi kadai bane rufe baki yayi a zuciyarsa yace badai sunji abunda nace bane muryan nabeel yaji yana cewa gsky zan so nasan wannan luv story din dan wlh daga ji zai bata onga
Ahmad zaiyi magana wayarsa ta dauki ringing ya dauka yace mufa gamu a kofar hotel din mun iso
OK kawai yace kafin ya ajiye wayar
Khalifa yace au wai dama mun iso ne saeed yasa dry yace ah lallai kam kayi nisa tun yaushe muka iso amarya yanzu muke jira dan mun rigasu isowa kasan shirin mata ashafa wannan amulka wannan agoge wancan dry suka saka dukkansu
basu wani jima ba amarya ta iso da kawayenta tasha kyau
Fitowa su khalifa sukayi da ango suka rakasa har wajan kofar motan amarya kawayen amarya sai wani kallon abokan angon sukeyi barin ma khalifa kamar zasu haɗiyesa
Ango ya kama hannun amaryarsa
A yayinda akayi layi domin rakasu
Anshiga an zauna anyi shagali ansha rawa anyi addua tare da fatan alkhairi dan kuwa basu tashi awajan ba sai sha biyu saura ahakan ma dan ango yace agajiye yake sannan gashi gobe zasuyi asubanci
aje daura din ma akwai wata dinner din dan haka suka tattara badin sunso ba kawayen amarya sai hari suke kawowa khalifa amma ko kallon inda suke baiyi ba hakan nan kuma wasu suka dinga cewa yana da girman kai dan ya gansa yana da kyau
Ko da suka koma gida sun gaji dan sai sha biyu da rabi suka isa gidan
Wanka sukayi suka zauna a parlor suna dan taba hira sama sama saeed yace nifa wlh yunwa nakeji
Ido khalifa ya ware waje yace ai kuwa gidan nan babu kayan abinci ko ƙyalli dan tunda aka gama gininta baifi sati acikinta ba nafita sannan rabona da gidan nan wlh saeed bazai ce maka gashi ba
Yace to kenn yanzu ko tea bazan samu ba
Wlh babu saeed
Nabeel yace ai da kayi mana magana mun biya mun saya kafin mu dawo inba haka ba zamu zauna da yunwa ne
Gwanda shi wannan ango ne bazaiji yunwa ba tunda aurensa akeyi mu kuma fa ?

Khalifa yace to ko zamu fita nema ne !
Nabeel yace Mee Nee Afita neman Mee karfe 1 yanzu wlh babu inda zanje azamanin yanzun nan tab inaa badani ba wai gaɗa a maƙabarta samm dry gabaki dayansu suka saka khalifa yace haba jarumina wlh bai kamata kadinga bada maza ba
Nabeel ya galla musu harara yace au haba
To wlh kuma ina baku shawara karku fita mu hakura da safe ido naganin ido muje
To shikenn nabeel mun hakura
Shuru wajen ya ɗauka nadan lkc kafin saeed yace khalifa ya kamata muyiwa juna introducing sbd kaine kawai baka sanmu ba
Muna kuma haka

Nidae sunana shine
SA'EED BASHIR AWWAL kuma ni haifaffen garin zaria ne mahaifina dan kasuwa ne nima kuma  ina business ta hanyar arkallan motoci
Ata ƙaice kenn sannan biyu ne kacal nida kanwata ihsan
Murmushi khalifa yayi gamida jinjina
Kai
Ni kuma sunana NABEEL ABDULSALAM GAMBO
nima dai dan zarian ne domin kuwa da mahaifin saeed danawa abokaine kuma sana'arsu daya wato kasuwanci ni kadaine awajan iyayena ni kuma arkallan gidaje shine business dina
Nan ma khalifa murmushi yayi batare da yayi magana ba

Ni SUNANA AHMAD GARBA ATULE MAGAJI ni dan daura ne kuma nan iyayena suke mukam munada yawa dan matan babana biyu ne kuma abotanmu a university muka hadu
a) a.b.u zaria daga nan shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninmu
STORY CONTINUES BELOW
Amma ni aikina yasha banban danasu domin kuwa ni CBI ne wato jami'in bincike
Kai fa khalifa ?

Shuru khalifa yayi yana nazarin shi kam ta ina zai fara karanto musu wannan lbr nasa
Kamar sunsan me yake tunani nabeel ne ya dafa kafadarsa yace khalifa ka yarda damu karka damu karka boye mana komai agame dakai domin mun fuskaci kana cikin damuwa ka dauke mu amatsayin aminai na haqiqa
Ajiyar zuciya khalifa ya sauke kafin fara da cewa
Zakuji lbrn da baku taba jinsa ba kuwa
Nidai sunana KHALIFA ABDULLAHI TASI'U
Haifaffen garin katsinan nan kuma wnn local government din ta dutsenma
Ni kadaine awajan mahaifiyata matan babana biyu zan iya cewa ma bansan mamata
ba domin tana maifata Allah yamata rasuwa mahaifina kawai nasani shima inada shekara goma cif  Allah yamasa rasuwa na koma zaman awajan matar babana babu kalar wahalar daban fuskanta ba
Amma na kasance tun ina qarami niba rago bane ko malalaci kamar wasu yaran mazan
Ga shi inason karatu kuma ina sha'awar aikin engineering sbd abu idan karfe ne ina iya sarrafata ta ko wace siga sannan ina gyarawa dan haka nashiga kasuwa duk aikin dana samu indai bai sabawa addini ba inayi da haka nasa kaina a mkrnt
Makarantar
Muhammadiyya kuwa tun ina dan shekara tara nayi sauka kafin rasuwar mahaifina
DA haka har Allah ya taimake ni harna shiga university kai na kare muku zance harnayi digree dina
Amma sani agaban da inna tayi gashi na gama karatu Sai
Yawon neman aiki nakeyi bansamu ba yasani kwashe  kayana na koma abuja........daga nan yacigaba da basu lbrn aikin da yasamu agareji da sharrin da aka masa aka koresa da saida purewater din da yafara har Allah ya hadasu da abban safreena wato ALHAJI MUHAMMAD BELLO BADIMASI
DA dan uwansa dauda kalar cin amana da kisan wulakancin da dauda yayiwa mahaifin safreena agabansa shi da safreena din
Babu abinda yarage musu
Har akazo lbrn GUDU A JEJI da kalar baqar wahalan da suka sha shida safreena har izuwa rabuwarsu
da haduwarsu dasu saeed da taimakon su daya nema
Banda kuka babu abinda su saeed nabeel ahmad sukeyi
Cikin kuka saeed yace ko a film da gidan tv da mujallu ban tabajin wnn lbrn ba gsky dauda ya cika azzalumi butulu maciyi amana marar tausayi marar imani
Gsky ya kamata dauda yagane kurensa ace ka kashe dan uwanka akan dukiya wayyo duniya ina zaki damu ne
Cikin kuka nabeel yace haqiqa da ban bar saeed ya taimake ka ba
to da ban yafewa kaina ba kayi hkr khalifa insha Allah zaga sakayyar ubangiji na wannan jahadin da kayi domin kuwa jahadi ne tsakanin rayuwa ko mutuwa bakaci amana ba ka kula da safreena gsky kai mutum ne khalifa

Karka damu zamu taimaka maka idan har kana bukatar taimako daga garemu muma a shirye muke damu tayaka daukar fansa akan dauda ko ya kuka ce? ya fada yana kallon su ahmad da saeed
Ahmad wanda tun dazu yakasa magana sbd kuka muryansa harta soma dashewa yace nabeel aiba saika tmbye mu ba
Khalifa muna tare dakai duk rintsi duk wuya sannan akwai abokin mu lauya ne bai samu damar zuwa bikina bane da kun hadu sunansa barrister S,M,J
Yana da kirki nasan idan yaji lbrn nan shima zai shigo cikin wnn aikin ladan ayi dashi
Saeed yace shima abokinmu ne kuma iyayenmu ma abokaine mgnr da nake maka ma dadyna da dadyn nabeel dashi dadyn S,MJ din tare sukayi tafiya dan sunkai 6months basu gari
Sanadiyyar abotan kuwa ya nuna nabeel yace kanwar S,M,J din budurwarsa ce dasu dady ma sun dawo inaji za afara mgnr aurensu

Wani dadi ne yakama khalifa cikin hawaye yace nagode muku my guys
Kunsan wani abu kuwa ?
Atare suka ce aa saika fada yace wlh ban taba abokanai ba kwata kwata nikam bani da aboki amma dashike Allah yanaso na a lkc daya nayi abokai uku cikon na hudu sai mun hadu dashi tukunna kuma dukkansu nagari gsky Alhamdulillah
STORY CONTINUES BELOW
Ahmad yace yanzu dai ku dakata duk ba wannan ba babbar tashin hnkln shine safreena ina zamu ganta?
Domin kuwa wani abun dole sai tana nan barinma zaman kotu
Khalifa yace wlh nasan da haka
Kullum ina mafarkinta inaji ajikina safreena tana raye
Saeed yace kodai jejin zamu koma ne
Nabeel yace to tawani hanya zamu fara bi kaji ka fa da wata magana
Khalifa yace inaji ajikina safreena tabar jeji amma bansan ta inda zan fara nemanta ba fatana daya Allah yasa idan tafito ta fada ahannu nagari domin su kulamin da ita
Ahmad yace insha Allah zamu nemeta amma tayaya ?
Kana DA pic dinta ne khalifa ?

Eh inada shi
Yawwa gud khalifa ina pic din yake ?
Khalifa yace yana bangon zuciyata
Mtsww  ana serious matter amma ka kawo wasa
Saeed yace aa nabeel gskyrsa ne tana bangon zuciyarsa dry suka kwashe dashi
Ahmad yace to Allah yabamu sa'a
Suka amsa da ameen
Suna tashi sukaji ashe har antada sallar asuba
Ido suka ware dukkan su gamida asuba
Alwala sukayi da sauri suka fita izuwa masallaci
Suna dawowa suka kwanta karfe 11 suka tashi sukayi wanka
Suka fara biyawa restaurant sukaci abinci tukunna kafin su dauki hanyar daura karfe 4 suka isa

Haka aka cigaba da hidimar bikin ahmad da amaryarsa khairat
Anyi shagalin lpy angama lpy Sai fatan Allah yabada zaman lpy
KO da khalifa zai koma katsina su nabeel da saeed sukace samm saidai yabisu su koma zaria idan ya koma katsina aikin mezaiyi haka ya tattara suka koma zaria
******

Safreena zaune abun duniya ya taru yamata yawa wani lkcn ba takan rasa tunanin me takeyi amma ta warke tayi tass abunta
Da sauri madina ta shigo dakin ta ajiye mata kaya ajiki
Sis najma gashi nan naki ne yaya sameer yace in kawo miki murmushi tayi ganin kullum saiya siya mata abu ko gajiya ba yayi ne
ki tashi muje Kitchen cewan madina wajen mami mu tayata girki yau dad zai dawo daga tafiya
Shuru safreena tayi to ita tama iya girkin ne
Au to ashe babansu nada rai yo duk zamana agidan nan ban taba ganin saba
Tace yww sis madina dama inaso in tmbye ki ina dad yake da zama murmushi madina tayi tace dad dan kasuwa ne Sai ya kai miki wata biyar wata shida wata bakwai ka wani lkcn ma har shekara baya gida yanzu ne ma mami ta daina binsa
Jinjina kai safreena tayi madina tace amma yaji lbrnki sosae awajan ya sameer da mami da kuma ni
Dan tabe baki safreena tayi ta miqe tsaye ta dauki gyelenta ta yafa tace muje
Mami suka samu a kitchen suka mata sannu tace yawwa sannunku yan matana maza maza madina zo ki dauki fruits din nan kiyi juice keda najma to mami
Domin su ukune wai zasu dawo
Mami su uku kuma eh madina

DA dadynku bashir da dady sirkin ki
Murmushi madina tayi tana rufe fuska
Mami tace yar'ne ma yau kuma ni kikejin kunya
Safreena dai ido kawai take binsu dashi suna burgeta
Hawaye ne taji ya cika mata ido tayi saurin mayarwa
Ta kalli madina sai murmushi takeyi
Sallaman sameer sukaji amsawa sukayi ya gaishe da mami ta amsa safreena ta gaishesa batare da taɗago ba ya amsa ya kalli madina yace kema fa naga alama kina shirin zaucewa kitafi zariya ko da yake ma ashe can zamu kaiki
Dry ne ya subucewa safreena sbd mgnr da sameer yayi karo na farko kenn
Da ta taba dry suka gani wanda haƙoranta farare tass suka bayyana
Wannan dry ma ƙaramin kashe sameer yayi ba dan saida yaji shock acan ƙasar zuciyarsa
Madina ce kawai ta lura da yanayinsa azuciyarta kuwa cewa tayi duk yanda akayi yaya sameer ka fada tarkon so
Amma idan kuwa haka akwai matsala sbd basusan najma ko wacece itaba tana da aure bata dashi
Tab yaya karka sa kanka awahala
Amma zanyi jarabawa domin na tabbatar wa kaina cewa ko kana SON NAJMA ne ko aa

Tashi ta ta dibo ruwa a cup tazo gabansa tace yaya ga ruwan firgigit yace no madina ba ruwa ba najma ki hadamin coffee din da kike hadamin ki
kawomin part dina
Kai aƙasa tace to yaya yafice mami tabisa da kallo ta girgiza kai tace sameer kenn
Idon madina ƙyam akan coffe din da safreena ke hadawa ta gama tafice
-------

Afuwa my fans am so busy wlh kuyi
Hkr
Yadda naga comments dinku naso ace nayi muku typing yafi haka
Amma ku cigaba da comments ni kuma zan cigaba da anbaliyar typing

Share it
by mmn Ahlan

🌳
🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Short story✍🏻
(Doter surayyah dan ango ALLAH yabawa mom dinmu lpy fans asa mom a adduah)

بسم ا لله لر حمن لر حيم
🅿-2⃣6⃣➡2⃣7⃣➡2⃣8⃣
Bayan ta kai masa ta dawo suka cigaba da aiki a kitchen suna taya mami girki har akayi sallarh magriba kafin suka gama gabaki daya safreena tagaji anya ita ta taba aikin girki kuwa ta tambayi kanta ?
To ma banda abina wazai bani amsa mtsww

Haka dai suka wuce bedroom itada madina suna shiga madina ta zube a bed gamida cewa wash Allah na nagaji wlh sis+
Murmushi safreena tayi tace ahh ahakan kuma zamu kaiki gidan yaya nabeel din ɗan wannan aikin shine kike cewa kin gaji ?

Murmushin farin ciki madina tayi dan tanajin nishadi idan aka kira sunan abincin ruhinta wato nabeel
Sis najma kinsan wani abu kuwa ?

Aa saikin fadamin

Wlh ina mugun qaunar nabeel har jinake kamar bazan iya rayuwa batare dashi ba
Riqe baki safreena tayi tana kallon madina tace tab lallai kam kinyi nisa wannan so haka gashi nikam bansan shi ba ko pic dinsa baki taba nunamin ba
Hararan wasa madina tayiwa safreena tace kajiki fa sai kace kina zama muyi wata hiran arziƙi bayan wani lkcn ma nizan tamiki magana amma kimin banza ta fada tana murguda baki
Dry safreena tayi ta zauna kusa da ita
Ta rungumo kafadarta tace haba madinatuna wlh ba haka bane a condition din DA nake ciki na rashin sanin wacece ni na tabbata idan kece haka zaki zama kamarni
Karki manta bansan sunana ba bansan daga ina nake ba bansan wani nawa ba kullum inaso na tuno ko da abu daya ne tak agame  da rayuwata amma dana fara hakan sainaji kaina yanamin barazanar tarwatsewa dole nake hakura
Kuma a yanda kuka riqeni da kunya nace wa mami inaso atayani neman ahalina to barin ma kuma yaya sameer da kullum yake dawainiya dani hakan sainaga kamar nayi muku butulci ne
Amma insha Allah daga yau nayi miki alkawari zan sake  daku zan zauna daku amma zan cigaba da addua Allah ya bayyana min wacece ni
Ta karashe mgnr da kuka mai ban tausayi wanda baya fitar da sauti sosae

Sosae madina taji tausayin safreena tanason tayata kukan amma bataso taƙara karya mata zuciya dan haka ta daure ta hau bata baki har tasamu  tadanyi shuru kafin ta miqe tace bari na watsa ruwa kafin nayi sallah dan wlh jikina  kamshin abinci yakeyi
Madina tace nima haka kiyi ki fito sai nima na shiga na watsa ko kuma bari naje nayi a dayan dakin ta fada tana miqewa  ta fice
Safreena kuma tashiga bathroom din dakin domin tayi fresh up
Su dad basu iso ba sai bayan sallar isha kafin suka iso  sallama sukayi acikin babbar parlorn dad da sauri sameer dake tsaye yakaraso gabansu gamida durqusawa yana gaida iyayensa
Dagosa dady bashir yayi ya rungumesa cikin wasa da dry yace ah my son kafa qara girma kodai idona ne
Shima dryn yakeyi batare da yayi magana ba dady abdulsalam yace ai wlh aure zamuyi musu karsu tsufa batare da sun ajjiye mana jikoki ba wata kilama aciki jikokin ma samu wanda zamuyi  ƙari dasu
STORY CONTINUES BELOW
Dry dad yayi wato mahaifin sameer (ALHAJI MUKHTARH JAFAR)
yace ah to baku kuke sangartasu ba gashi dai ɗana nabeel kwanan nan zan auran dashi
kai Alh bashir nace kabani ihsan na hadasu kace ba haka ba ai saiku ta zuba masa ido
Gaban sameer ne ya fadi dan babu abinda yafado masa illa najma da yaji dad dinsa ya kira sunan wata da  sauri yace my dad's kuyi hakuri kun iso amma na tsayar daku dry sukayi kafin suka wuce cikin parlor din suka zazzauna dad kuma ya wuce part din mami domin kuwa ba ƙaramin missing dinta yayi ba so yake yaje yayi tozali da beautiful face dinta b4 yashiga wanka lolx

Su madina suna daki suna hira wayar madina yana hannun safreena tana kallon pics din da madina ke nuna mata na nabeel
Safreena tace amma fa sis madina nabeel dinki fa kun dace dashi
Wani fari da ido madina tayi na jin ddi tace da gske sisna?

Ehmana to amma wanene wannan nagansu atare yawancin pic din ?

Mugani cewar madina
Kalla tayi tace yaya saeed ne abokin yaya sameer da kuma nabeel din wanda tare dadynsu  zasu dawo daga tafiya yau tare da  dad kuma.....bata karasa ba wayarta yahau ringing tace lahh kinga ihsan ce ke kira kanwar yaya saeed ce takanzo tayi hutun ta anan but yanzu ta jima batazo ba shiyasa bakusan juna ba amma tanajin lbrnki awajena kuma yaya sameer ma yana bata lbrnki murmushi safreena tayi batare da tayi magana ba

Ɗaukar wayar tayi suka fara gaisawa sannan tace ya sis najma
Lpyrta kalau waike yaushe zakizo ne ?

Ihsan tace to ni nadinga zuwa kenn ke bazaki zo ba ?

Dry madina tayi kafin ta sassauta murya tace sis saurin me kikeyi ne nida zan dawo zama na dindindin gabaki daya

Dry itama ihsan din tayi tace lallai fa naga alama kin ƙosa ya kamata su dad suyi harzarin saka bikin nan ayisa mu huta
Yanzu dai bani sis najma mu gaisa
OK gata
Ta fada tana miqawa safreena wayar wanda tunda suka fara mgn da ihsan ta  zuba musu ido tana kallon madina tanajin muryan ihsan

Karba tayi ta mata sallama ihsan ta amsa cike da fara'a sannan suka gaisa
Ihsan tace sis yaushe zakizo mana zaria ?
Murmushi safreena tayi tace idankinaso ai gobe ma saina zo. Dry ihsan tayi tace inaso mana inason muga juna sannan mu saba sosae afili amma nasan ke bazaki zo zaria yanzu ba dan na kira yaya sameer nake tmbyarsa yaushe zakuzo yacemin ko da zakuzo ba yanzu ba amma ni insha Allah ina gama peper na a wannan satin zanzo
Ayya to Allah ya kawoki lpy sis
Ameen sis najma tnx
Ke baki da waya ne ?
Shuru safreena tayi kafin tace eh bani dashi tukunna amma zamu dinga gaisawa da wayar mrs nabeel
Dry ihsan tayi tace ok shikenn sis najma bye
OK bye
Ta miqawa madina wayar  ta karba tasa akunne
Ihsan tace su dady basu iso bane inata kiran wayarsa bata shiga harda wayar dady abdulsalam lpy dae ko ?
DA Sauri madina ta miqe zaune tace wlh sis namanta akan cewa su dad zasu dawo yau maybe ma sun ISO bari muje mu duba dan banji motsin motoci ba gsky dan wlh gabaki daya hankalina yana kan wata littafi da kuma wayata dake hannun sis najma ina nuna mata pics dinsu yaya nabeel da yaya saeed amma bari muje mu duba

OK Idan sun iso lpy saiki kirani ki fadamin
OK ba damuwa bye
Kashe wayar tayi ta kalli safreena tace sis najma tashi muje
Mu duba mugani ko sun iso kinsan Allah gabaki daya na shafa'a kuma zaman hiran da mukayi ne yasani namanta
Safreena tana dry ta dauki dogon hijab dinta har ƙasa tasa kafin tace yoo dama ana hiran nabeel kam ba dole ki manta dad zai dawo yauba
Itama madina dryn take ayayinda ta dauki nata hijab din tana sakawa domin kayan bacci ne ajikinsu tace wai nikam rufamin asiri kar dad yaji yaƙisa bikin nan kusa tana fadi tayi waje tana dry
STORY CONTINUES BELOW
Murmushi safreena tayi tabi bayanta tace Allah ya shiryaki madina
Atare suka taho hanyar da zata sadasu da babbar  parlorn dad sukayi safreena bata taba bin hanyar ba dan itakam daga dakinsu dakin mami  sai kitchen sai kuma part din sameer dan ita tafi zama acikin daki ma abunta dan haka duk zamanta agidan ba ko ina ta taba shigaba kuma dama bason shigan take ba

Har sunsa hannu zasu bude kofar parlor din sameer shima yadanno kai zai fita karo sukayi da safreena da sauri ta matsa baya tace yi hkr yaya bansan kataho ba murmushi yayi yace is ok najma ina zakuje haka da wasu manya manyan hijabai sai kace masu shirin tashi sama ko kuma wanda zasuje tafsiri ?

Dry suka sa kafin madina tace yaya su dad sun iso ne ya bude baki zaiyi magana sukaji muryan dad na cewa eh auta mun iso yanzu nake tmbyar maminku akan cewa ina yarana suke
DA gudu madina taje ta rungumi mahaifinta cikeda jin dadi da farinciki
Kafin ta sakesa ta duqa har ƙasa tana gaidasa wanda hakan ya zamo tarbiyyar gidan ALHAJI MUKHTARH JAFAR dole idan yara zasu gaishe da iyayensu tofa ya zama dole su duqa sbd girmamawa
(Akasin wasu gidajen da tarbiyya tayi ƙaranci yaro zaiga mahaifinsa amma bazai duqa  ya gaishesa ba saidai atsaye zangangan ko kuma yana gaishesu amma hankalinsa yana kan waya yana dannawa wani gidan ma kam yaro zaiga  iyayensa amma saidai ya wuce ya shige kansa asama dan  Allah ya kamata agyara kuma wannan gyaran bana kowa bane face ke UWA domin rabi da kwatan tarbiyya ahannunki yake domin shi UBA idan yafita yabarku watakilama ba lallai bane yaƙara dawowa gidan  ba sai dare dan haka mu daure gyara Allah yasa mudace)

Safreena gefe ta koma ta rakube banda kwalla babu abinda ke fita a idonta sai gogewa takeyi da sauri Ko itama tana da iyaye oho sannan suna mata irin wannan son oho azcyrta tace Ya Allah kafitar dani daga wannan halin ka turomin haske acikin rayuwata domin na tuna wacece ni
Duk halin da take ciki sameer yana kula da ita ya kafeta da ido har ƙasan zuciyarsa yaji babu dadi
Dago kanta tayi suka hada ido dashi ya girgiza mata kai
Mami ce tace doter najma ya naga kina murza ido kuka kikeyi tazo gabanta ya ɗago fuskarta
Aa mami ba kuka nakeyi ba abu ne ya faɗamin a idon yanamin zafi
Ayya sannu ko najma murmushin karfin hali tayi tace yama dai min zafin yanzu mami
To jeki ga dad dinku
Gabansa taje ta duqa har ƙasa itama cike da girmamawa ta gaishesa amsawa yayi gamida riqo kafadarta ya ɗagota  yace masha Allah ƴata kisaki jikinki kinji ko murmushi tayi tace to dad
Suka shiga parlorn atare
Gaishe dasu dady bashir su madina da safreena sukayi daga nan mami ta hau. .serving dinsu abinci
Bayan sun gama ne dady bashir ya tashi yace to masha Allah alh Mukhtarh mungode sosae bari mu wuce masaukin kafin gobe kuma mu qara ɗaura wata tafiyar
Dad yace to ba damuwa
Saida safe kenn ko
Zamuyi waya kawai mu katasa mgnr ba damuwa
To Allah yabamu Alkhairi
Suka fita gabaki dayansu dady Abdulsalam sai tsokanar madina yakeyi wai sirkata sai ankawo ki zaria
Sai rufe fuska takeyi ajikin safreena
*************

Khalifa zaune adakin nabeel suna hira wanda khalifa sama sama yake amsawa
Izuwa yanzu khalifa yaɗan saba dasu iyayen nabeel da saeed sannan sun yaba da hnklnsa da natsuwarsa
Nabeel yace gobe fa dadyna zai dawo kuma kullum ina basa lbrnka hajia ma tana basa lbrnka
Murmushi khalifa yayi yace Allah yakawo dady lpy nabeel ya amsa da ameen
Sallaman saeed sukaji da mamaki suka daga ido suna kallonsa dan a lkcn shaɗaya saura
nabeel yace dawowa kuma kayi
Yace eh wlh dadyna ne wai nazo nan na kwana idan sun iso gobe saina muce dashi gida
Ok kawai nabeel yace
Khalifa yace to miye wannan a hannunka saeed?

Guntun tsaki yaja yace ihsan ce ta hadani dashi wlh
Dazu ma wai sun sha waya da kanwar  barrister S.M.J wai sunyi wata sabuwar kawa mema sunanta am um wai NAJMA
Gaban khalifa ne yaji yafadi amma ya dake batare da yayi magana ba ya kata maimaita sunan aransa yace NAJMA
To miye hadina dake ana kiran sunanki naji zcyta ta amsa mtsaw to ma miye ruwana
Nabeel yace ai kullum sainaji lbrn najma awajan madina saidai ban kirata ba
Khalifa yace wai dan Allah menene Asalin sunan barrister S.M.J dinnan?

Saeed ne yayi dry yace inkiyarsa ce S.M.J awajan aiki
But full name dinsa
Shine
BARRISTER SAMEER MUKHTARH JAFAR

🥺🥺
Wayyo sai mun hadu a next page

Comments

And
Share

🌳🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

dєdícαtєd tσ
fírdαuѕч huѕѕαín nαncч nαjí ddín cσmmєntѕ dínkí
ummín íhѕαn
nαfєєѕαt
ummu вílαl
nαjlqt
mєєrєrh
dєѕtínч wíll nєvєr chαngє
mmn ѕαjjαd
αíѕhα
αíѕhα.
---------------------------
wlh чαu tчpíng nαkє чαnα gσgєwα dαn hαkα nαgαjí wlh😩
Short story✍🏻

بسم ا لله لر حمن لر حيم
🅿-2⃣9⃣➡3⃣0⃣
Ko da washe gari dasu dady bashir suka iso saeed ya dauki mahaifinsa suka wuce gida
Sosae dadyn nabeel ya yaba da khalifa
DA kuma hnklnsa da nutsuwarsa

*******

Dad ne ya tara su mami akan mgnr auren nabeel da madina yace sun yanke nanda wata hudu masu zuwa sosae mami taji dadi kuma tayi musu fatan Alkhairi tare da sa musu Albarka
Dad yayi gyara murya yace wani hanzari ba gudu ba sameer shekarun ka sun kai ace yanzu kana da  ƴaƴa ba  mata ba inaso zan hadaka aure da ihsan ƴar gidan alh bashir idan yaso ayi lkc daya kawai na huta
Cikin faduwar gaba sameer yace kayimin afuwa dad tunda kake bani umarni ban taba musa maka ba amma dan Allah dad kayi hkr NAJMA nake so ba IHSAN ba
Wani kallo dad yayiwa sameer yace me kace ?

Mami tace zancan banza kenn NAJMA kuma ?

Dad ya dagawa mami hannu alamun ta dakata yace sameer najma fa kace ?
Saida ya saci kallon safreena wanda tayi mutuwar zaune tun lkcn daya furta cewa ita yakeso harda madina itama da take kallonsa cike da mamaki ko da yake ma itakam ta juma da gano hakan
Eh dad ita nakeso dan Allah dad ka aure min ita plss wlh ina mugun ƙaunarta
Shuru dad yayi domin tunda suke da sameer
mgn makamarciyar haka bata taba shiga tsakaninsu ba kuma bai taba yi masa musu ba shiyasa yayi ma ɗan nasa uzuri yau
Mami ce cikin kiɗima tace alh kayi mgn mn kayi shuru naga alama.sameer yana neman zaucewa
Dad yace ya isa haka ya kamata aduba lamarin gsky
Mami tace tayaya za aduba bayan ba musan wacece najma ba kaddara yanzu mu aure mata sameer idan akazo tunaninta yadawo kuma fa sannan ma duk ba wannan ba idan tunaninta yadawo tana da aure sai yayi yaya kenn ?
Yanda yake cewa yana sonta
Dan Allah alh ka duba zance na
Kasan dai haramun ne AURE AKAN AURE
Sameer ne yayi mgn da muryan sa adashe sbd tashin hankali yace mamina inaji ajiki na najma bata da aure
Dan Allah mami ki taimaki rayuwar ɗanki Allah inasonta tun ranar dana ganta naji sonta ya ɗarsu a zuciyata
Jikin mami ne yayi sanyi ganin lkc daya yanda ɗan nata ya canza jijiyoyin wuyarsa harsun tashi
Tace to naji amma dai abi haqqin yarinya a tambye ta tukunna
Dad ya kalli safreena yace my daughter kina son SAMEER ?
wani wawan faduwar gaba taji gabaki daya jitake kamar babu rai atare da ita
DA mugun gudu ta tashi tayi hanyar dakinsu tana kuka da sauri sameer shima yatashi yabi bayanta madina ma tashi tayi jiki asanyaye
STORY CONTINUES BELOW
Har zata shiga dakin ya damƙo hannunta jikinsa na rawa plss NAJMA don't say no accept me as ur husband to be insha Allah plss
Kukan ta ne ya ƙaru ta fizge hannunta
Tace ..I A'M SORRY YAYA SAMEER ta shige daki
Fita sameer yayi daga gidan gabaki daya
Madina ce tadinga lallashin safreena
Ranar dai haka aka wuni agidan kamar ana makoki
Sameer kuma bai dawo gidan ba har dare
Safreena hankalinta ne taji yaqi kwanciya kar tazamo butulu fa nan da nan taji zuciyarta ta karaya gashi duk gidan babu wanda yaci abincin kirki
Sai safa da marwa takeyi acikin daki madina tayi sallama tashigo
KO amsa sallamar madina bata tsaya yi ba tace yaya sameer ya dawo ?

Girgiza kai madina tayi alamun aa
Sabon kuka safreena ta saki gamida durqushewa awajan tanayi iya karfinta
Har qasar zuciyarta takejin zafi haqiqanin gsky batajin son sameer ko kadan sannan batajin qinsa ga wani mummunar bugawan da zuciyarta ke mata
Kamar zai tsaga qirjinta yafito waje

Madina ce ta ɗagota tana lallashinta
Cikin kuka tace kuyi hakuri na wargaza muku farin cikin ku ko wlh gabana ne ke faduwa yanzu ina yaya sameer ya shiga ta kuma sakin kukan itama dai madina kukan takeyi na tausayin dan uwanta
Domin jiya da daddare ta kai masa
Coffe irin wanda najma ke hada masa tace najma ce tace na kawo maka nan take taga fuskarsa ya dauki annuri
Sannan take tmbyarsa shin yana son najma ne ?
Bai boye mata ba yace yana sonta
To yau kuma ga abinda ya faru
Suna cikin haka mami tashigo dakin nan tashiga lallashin najma tace ki kwantar da hankalin ki kinji najma yau idan kikace baki son sameer ko daya bazamu ga laifinki ba
Cikin kuka tace mami kiyi hkr bawai bana son yaya sameer bane aa rashin sanin wacece ni shine abinda yafi damuna
Mami tace na fahimci komai najma Allah ya muku Albarka madina kema kukan ya isa haka zo ki dauka muku abinci kuci ku kwanta
Mami ta miqe zata fita safreena tace mami yaya sameer fa bai dawo ba murmushi mami tayi tace karki damu sameer ɗanane nina haifesa nasan halinsa bazai taba kwana awaje ba dole zai dawo ki kwantar da hnkln ki kinji ko
Ta gyada kai mami kuma ta fice madina tabi bayanta domin dauko musu abinci
Bata jima ba ta dawo da tray tace mami tace mu cinye duka
Saukowa tayi daga gadon ta zauna akan carpet
Madina tayi serving nasu amma safreena takasa ci jitakeyi duk itace silan komai gashi ɗan masu gida yabar gida sbd ita
Madina ganin bata cin abincin ne yasata cewa najma shin kema kina son yaya sameer ne ko kuma tausayinsa kikeyi ?

Tmbyar madina taji yamata wani iri
Madina nima bansani ba bansan me yake azuciyata ba
Murmushi madina tayi tace to kidaina wannan damuwar kice abinci ko kuma naje na kira mami tazo ta zauna kici agabanta
Tuttura abincin kawai takeyi da haka har suka cinye
Suka canza kaya suka kwanta kowa da abinda yake tunani
Dare ya tsala amma safreena takasa bacci sai juyi takeyi
Da kyar bacci barawo yasaceta acikin baccin ne tafara wata mafarki
Suna gudu itada wani saurayi yana riqe da hannunta awani jeji amma takasa ganin fuskan wannan saurayin sbd duhun jejin da suke gudu aciki
Suna cikin gudun ne aka harbi saurayin yafaɗa wata babbar teku
Ihu tasaka ta miqe da sauri tana salati madina dake alwala a toilet tafito da mugun gudu ko gama alwalan. Batayi ba sakamakon jin ihun najma
STORY CONTINUES BELOW
Zaune ta sameta abakin gado jikinta ya jiqe da zufa sai ba'ri takeyi

Tambayoyi madina tashiga jera mata
Sis meya sameki?
Meya faru ?lpy kuwa?
Kuka tasaka ta kwanta ajikin madina
Da kyar madina ta lallasheta tayi shuru kafin tace mafarki nayi wani saurayi yana jana muna GUDU A JEJI banga fuskarsa ba sbd duhu kawai naga an harbesa ya fada ruwa ta kuma sa wata kukan
Madina tace haba najma kuma saiki hau kuka addua zakiyi ba kuka ba yanzu dai tashi kiyi alwala dan asuba tayi
Bari na ƙarasa nawa saiki shiga kiyi

Bayan sun idarne safreena tace madina anya wannan mafarki baya da nasaba da rayuwata kuwa inaji ajikina
Jinjina kai madina tayi tace kedai kawai ki dage da addua Allah takawo mana da sauki ta amsa da ameen

Wasa wasa safreena ta rabu da ganin sameer har na tsawon sati daya
Kuma ba wai baya gidan bane aa ita din ne yake guduwa mata
Yau gabaki daya suna zaune a parlorn mami harda mamin suna kallo amma safreena ta lula duniyar tunani
Sallama sukaji da gudu madina ta miqe gamida cewa oyooyooooo my ihsan
Ihsan fuskarta cike da fara'a tashigo suka rungume juna itada madina
Duk da safreena bata cikin yanayi na nishadi amma saita daure itama ta miqe tana cewa oyoyo manya manya dry ihsan tayi suka rungume juna tace woww gsky kinfi kyau ma axahiri gsky nice to meet u
Safreena fuskanta dauke da murmushi tace me too
Nan suka  karasa parlorn mami tace oyoyo ihsan dina har kasa ihsan ta duqa ta gaida mami
Mami tace yasu mama ?
Suna lpy gabaki dayan sunce na gaidaku
Safreena ta dauki akwatyn ihsan tayi daki dashi
Mami tace masha Allah muna amsawa ina saeed da nabeel da khalifa
Ihsan tace duk lpyrsu kalau mami yaya handsome ma yace na gaisheki sosae kafin yazo ayya ina amsawa ɗan kirki
Madina tace kai nikam inason ganin khalifan nan kullum sai yaya nabeel yaban lbrnsa
Ihsan tayi dry tace wlh ya handsome ya hadu in gaya miki babu ruwansa karkiga yanda kawaye na ke zuwa gidanmu idan yazo wai dan Allah na musu hanya
Madina tasa dry daidai nan safreena ta dawo ta zauna
Ana cikin hira sameer yayi sallama da sauri safreena ta ɗago ido tana kallonsa har yadan rame wani tausayinsa taji ya kamata
Ihsan tace oyoyo my yaya murmushin yake yayi yace ah my ihsan ashe da gsk kikeyi
Ehmana ka dauka wasa ko to ykake ?
Da sauki dai zance dan kwana biyun nan ina fama da zazzabi
Ayya sannu my yaya shiyasa gabaki daya naga ka canza kuma ka rame murmushi yayi
Ya kalli safreena da gefen ido itama shi din take kallo da kyar tace yaya sameer dama baka da lpy ne?

Kallonta yayi yace uhum
Tace ya jikin ban sani ba ai
Ko amsa bai bata ba yafice abunsa zcyrsa na masa quna
Ihsan ce ta kalli madina tace lpy meke faru shuru madina tayi dan tasan ihsan tana son yaya sameer duk da bata taba fada mata hakan ba safreena tashi tayi ta koma daki ta zauna ta rafka tagumi
Haka dai har aka kwashe sati biyu
Ranar suna kitchen dukkansu safreena madina ihsan
Wayar ihsan ce tayi ringing ta duba screen din sunan YAYA HANDSOME ne ya bayyana dauka tayi gamida sallama suka gaisa tunda ihsan tafara waya safreena taji natsuwarta tafita ajikinta duk da batajin me suke cewa
Fita ihsan tayi tace ok yaya handsome bari na duba maka shi kashe saika sake kira
STORY CONTINUES BELOW
Fita tayi part din sameer yana kwance a 3seter
Ya lumshe ido kamar mai bacci yaji sallamar ihsan
Amsa sallamar yayi tace my yaya kodai bacci kakeyi ne na tasheka no my ihsan idona biyu menene?

Dama yaya handsome ne keson mgn da kai
OK barshi kawai zan kirasa ok
Zata fita ya kira sunanta IHSAN
Juyowa tayi tace naam
Kwalin waya ya dauko yace gashi ki kaiwa najma saida tayi tsalle kafin ta rungumo sa tahau zuba masa gdy sai kace ma ita aka siyawa wayar da gudu tafice
Shi kuma ya dauki waya domin ya kira khalifa
Da gudu tashiga dan harta basu tsoro ma madina tace ai saiki sa mu mutu lkcnmu baiyiba miye hakan ?

Tace dallah malama bake ba sis najma gashi waya tagani sabuwa tace na waye ihsan tace yaya sameer ne yace in kawo miki
Asanyaye ta karba tafita a kitchen din daki tashiga tasha kuka kafin tasa wayar a chaji da daddare bayan angama cin abinci
Dukkansu suna parlorn dad harda dad
Yace balaraba ya kamata ace an fara shirye shiryen bikin nan fa asan abunyi
Lkcn sai qaratowa yakeyi

Safreena cikin sanyin murya tace dad inada mgn
Kowa da mamaki yake kallonta barinma sameer to yanzu kuma me zata ce ?

Dad yace feel free my daughter menene?

Amm ehh ahh oh dama...dama..dam..am
Mami tace najma fadi mana kidaina wannan kame kamen fadi kawai me kikeso ?

Sun kuyar da kai kasa tayi tace amm dama so nake nace na amince da auren yaya sameer
Agigice duk suke kallonta sameer cikin tsananin farinciki  yace najmata da gske kike kin amince zaki aure ni gyada kai tayi asanyaye
Dad yace to shikenn Allah yasa hakan yazamo Alkhairi suka amsa da ameen
Mami tace to yanzu za ahada bikin kenn ko
Madina tace dadyna inada mgn
Dad yace inajinki mamana
Tace inaso afara bikin yaya sameer idan yaso koda da wata daya ne sai ayi nawa da yaya nabeel din

Dad yace to ba matsala kutashi kuje Allah ya muku albarka suka amsa da ameen

Dad yace nanda wata biyu za ayi  bikin ko ya kika gani hajiya
Mami tace hakan ma yayi Allah ya nuna mn

Sameer bakinsa yaqi rufuwa sbd jin ddi
KO da suka koma daki safreena tashiga toilet ta kunna ruwa tasha kuka kamar ranta zai fita
Madina ta lura da yanayin ihsan ya canza dafata tayi tace sis meke damunki
Murmushin boye damuwa tayi tace babu komai me kike gani sis

Nan dai suka dauki shuru batare da kowa ya kula dan uwansa ba
Aban garen sameer kuwa ya kira su khalifa saeed nabeel ahmad yabasu lbr najma ta amince da aurensa nan da wata biyu za ayi biki murna suka tayasa
Khalifa kuwa cewa yayi kowa da damuwarsa ni tawa tasha banban dana saura
KO DA khalifa yayiwa sameer mgn akan case dinsa yace da angama bikinsa zasu duqufa akai tunda bikin ya kusa nanda 2months ne
Shirye shirye ya kankama
Abun ba wuya awajan Allah yau bikin SAFREENA(NAJMA) DA SAMEER saura sati biyu cif shirye shirye akeyi sosae
Khalifa yana kwance gabaki daya kwanan nan ji yake gabansa na faduwa kamar ma baida lpy
Nabeel da saeed suna zaune kowa da wayarsa ahannunsa yana chatting

Nabeel yace ah ah ah lallai saeed kalli najman s.m.j
Karban wayar saeed yayi yace woww kai kai kai gsky masha Allah shegen sama shiyasa ya dage mana ashe ya tsinci dami akala ne
Khalifa tsaki yayi ya juya baya azuciyarsa yace ni anya zanga yarinyar data kai safreena ta kyau kuwa muryan nabeel yaji yana cewa khalifa kalleta
Tsaki khalifa yaja gamida cewa naga alama bakusan halin danake ciki bane shiyasa
Saeed yadawo kusa dashi ya zauna yace kayi hkr aboki insha Allah kwanan nan zamu wargawa daulan dauda kabari agaba bikin sameer sai mu faɗaɗa bincike
Batare da yabasa amsa ba ya lumshe ido
Nabeel yace KHALIFA HAQIQA SON SAFREENA YA MAMAYE MAKA ZUCIYA
Zaune yatashi yana kallon nabeel yace bana tunanin hakan
Saeed yace kaji karyan banza kaida ranar kace tana bangon zcyrka murmushi yayi ya kwanta ya lumshe ido yana hango beautiful face dinta
*******

Ihsan zaune awajan ata bayan window tayi tagumi jitayi andafata da sauri ta ɗago taga madina
Zama madina tayi akusa da ihsan tace sis wannan boye boyen ya isa haka kina son yaya sameer ?
Murmushi ihsan tayi tace ehmn inason sa amatsayinsa na yayana
Mtsww rainin wayonki ya isheni haka ihsan ki fadamin gsky
Dryn karfin hali tayi tace bana baqin ciki ko jin haushi dan yaya sameer zai auri najma ina murna dan haka kibar wnn shirmen
Madina  Tace wlh bawai ganin idonki ba naso ace yaya ya aureki
Murmushi ihsan tayi tace haka Allah yaso yanzu dai kitashi muje gdn gyaran jikin nan
Aguduje
""""""
Biki saura kwana 3
Madina ihsan
Sun shirya dinner kafin daurin aure ranar alhamis kenn
Sameer yace subari adaura aure amma sunce aa
Saeed nabeel sai shiri sukeyi khalifa na kwance bayajin ddi
Saeed yace gsky madinan ka yar bidi'a ce
Harara ya aika masa yace naga dai harda ihsan aciki
Kallon khalifa yayi yace katashi ka shirya mana
Murya ciki2 yace wlh bazan iya zuwa ba kubawa sameer hkr
Lallashinsa suka shigayi akan yadaure saikace va namiji va ai sameer bazaiji dadi ba idan baijeba
DA haka harya tashi ya shirya amma jikinsa amace

Suka kama hanyar adamawa
Sai gefen magriba suka isa direct part din sameer sukayi gidan acike da jamaa yan biki
Sai da sukayi ishe'i kafin suka shirya
Safreena da kyar aka shiryata sbd batajin dadi zazzabi ya rufeta sakamakon mafarkin datayi
Na wannan saurayin yana ce mata karta bari ayi auren nan shine masoyinta na haqiqa
Masha Allah amaryan najma ansha makeup itada   su madina da ihsan da sauran wasu friends dinsu
Khalifa saeed nabeel ahmad ango da saura wasu abokai
Suna tsaye ana jiran fitowar amarya
Zuwa can saiga su sunfito tana tsakiya madina da ihsan suna gefenta
Khalifa ya juya baya har suka iso jikin motar ana kokarin ta shiga
Sameer yana gefenta da karfi ya kira sunan khalifa
Yace khalifa kazo muje anan
Afirgice safreena tadago sbd sunan yadaki dodon kunnanta juyowar da khalifa zaiyi
Sukayi 4 eye's da safreenan shi wani ihu safreena ta saki gamida sulalewa kasa asume
Sai mun hadu a next page
qurí'α wαчα kíkєѕσ

1 khαlífα
2 ѕαmєєr

kσwα чα fαdí gwαnínѕα αkαn ѕαfrєєnα

C̸͟͞o̸͟͞m̸͟͞m̸͟͞e̸͟͞n̸͟͞t̸͟͞s̸͟͞

A̸͟͞n̸͟͞d̸͟͞

S̸͟͞h̸͟͞a̸͟͞r̸͟͞e̸͟͞

B̸͟͞y̸͟͞

M̸͟͞m̸͟͞n̸͟͞ a̸͟͞h̸͟͞l̸͟͞a̸͟͞n̸͟͞✍🏻✍🏻✍🏻

🌳🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

qυrι'ar мυ na jιya

😂😂
wanda ѕυĸa laѕнe
ѕυne.... yan тeaм dιn.........
💖K̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞L̸͟͞I̸͟͞F̸͟͞A̸͟͞  💖

  ѕorry......    S̸͟͞A̸͟͞M̸͟͞E̸͟͞E̸͟͞R̸͟͞. qυrι'a вιyυ ĸawaι ĸaѕaмυ

мy ғareeda мrѕ υмar (ммn мυѕтy)
😂😂 ѕorry ĸυnѕнa ĸaѕa
Short story✍🏻

بسم ا لله لر حمن لر حيم
🅿-3⃣1⃣➡3⃣2⃣
Da gudu khalifa ya ɗago safreena kafin sameer ya ɗagota cikin tashin hankali marar misaltuwa yahau jijjigata yana kiran sunanta
SAFREENA
SAFREENA
SAFREENA
kira yakeyi ba ƙaƙƙautawa
Kowa kallonsu kawai yakeyi cike da mamaki+

Saeed Ahmad nabeel afili suka furta safreena dai cike da mamaki da al'ajabi tab lallai akwai matsala
Ganin haka yasa ihsan ta juya da mugun gudu ta koma cikin gida tana kuka ƙotsa kai kawai takeyi acikin jama'a har ɗaurin ɗan kwalin da aka mata ya kunce na zuwa wajan dinner

Can ta hango su mami  mama  mom cikin cikin jama'a ana raha
Da kuka ta isa mami ce ta riqota cikin tashin hnkl tace ihsan meya faru awajan dinnern naku lpy waya mutu
Takasa magana sai nuni takeyi da hanyar waje mama ce tayi mata tsawa
Dallah ke miye ne kam ana tmbyarki kina kuka kina nuna mana hanyar waje duk kin tayar mana da hnkl meya faru ?
Waya mutu bakuje dinnern bane ko menene mama (mahaifiyar ihsan da saeed )

Da kyar ihsan tace mama ....na.naj...najma...ce...

Dafe qirji mami tayi tace meya samu najma din saida nace muku ku kyale yarinyar nan batada lpy amma kuka min kunnan uwar shegu itama ta biye muku sbd tana son farin cikin ku akan wani dan banzan dinner  yanzu meya sameta?
Har yanzu ihsan bata bar kuka ba kuma takasa mgn domin yanda taga najma tayi ihu ta fadi ko motsi batayi ya daga mata hnkln matuƙa
Zata kumayin mgn saiga madina da kuka
Mom (mahaifiya nabeel) tace kawai kuzo muje muga menene ke faruwa amma wannan yazo da kuka wannan ma yazo ai abu baiyiba

Gaba su mom mami mama sukayi ihsan madina suna binsu abaya dawasu sauran kawaye suna kan kukan basu bariba
Suna fita waje sukayi turusss innalillahi wainna ilayhirrajiun shine kawai abinda mami mom mama ke  iya nanatawa
Mami tace ku shigo da ita cikin parlorn ko kuma akaita asibity
Daukarta khalifa yayi yashiga ciki da ita sameer kasa motsin kirki yayi sbd tashin hnkln sai maimaitawa yakeyi safreena dai ?

Lallai kuwa akwai yaƙin duniya na uku dan wlh za ayi BADAR matar da nake son din ashe itace wacce khalifa ke nema tab ya Allah kasa karta tuna komai domin bazan iya hakura ba
Duk kowa yayi jingum jingum ruwa ihsan takawo khalifa ya karba ya hau yayyafawa safreena can zuwa anjima tayi ajiyar zuciya mai nauyin gaske
Khalifa yana rungume da ita gam yaki sakinta sameer yana gefe riqe da hannunta shima gam
kowa ya zuba mata ido ana jira tabude ido
STORY CONTINUES BELOW
Zuwa can anjima tafara tashi daga jikin khalifa yayinda ta kwace hannunta daga hannun sameer idonta arufe
Salati tafara tana kiran sunan ALLAH kanta ne taji yana jujjuya mata da sauri tariqe kan hannun bibbiyu
Memorynta ne yafara dawowa ahnkl tafara tuno rayuwarta na baya da kashe mata iyaye da baba dauda yayi da gudunsu ajeji ita da yaya khalifa da rayuwar da sukayi ajejin har izuwa rabuwarsu
DA rayuwarta tare dasu sameer na mantawa da komai datayi har izuwa yau dataji sunan khalifa da 4eyes's din da sukayi
Da sauri ta bude ido tana waige waige tagansa kusa da ita  kuka mai tsuma zuciya ta saki gamida daga hannayenta biyu wanda suke rawa kamar mazari tana shafan fuskarsa. Domin ta tabbatar shidin ne ko kuma gizo ne

Shima hawaye yakeyi
Cikin muryan kuka tana shafa fuskarsa tace ya..yay...yaya...kha...khali.....khalif....khalifa...

Daga mata kai yayi alamun eh my safreena nine ya riqo hannunta
DA sauri ta rungume sa tana kuka tana mgn dan Allah yaya khalifa karka sake tafiya kabarni zuciyata bazata ɗauka ba
Hannu  biyu yasa shima ya rungumeta yana hawayen farin cikin sake ganin safreena arayuwarsa
Haqiqa adduar bawa bata fadi ƙasa banza saidai jinkiri gashi Allah ya amsa du'a'insa yasake hadasa da safreena
Duk gabaki daya sun Zama abin kallo
Jama'ar dake wajan kansu ya ɗaure sun kasa fahimtar komai
Amma banda mutum uku
Ahmad
Nabeel
Saeed

Mami ce tace waini balaraba meke faruwa ne kam kun samu aduhu fa kuyi mana bayani mana yanda zamu fahimta kufitar damu a ruɗani

Nabeel ya bude baki zai magana bai ankara ba sameer ya fizgi safreena daga jikin khalifa ya rufesa da duka kamar Allah ya aikosa

Kokarin shiga tsakani akayi amma ina sameer idonsa ya rufe da kishi. ganin tabbas fa zai iya rasa najma idan baiyi da gske ba Duka kawai yake kaiwa ta ko ina wa khalifa

Safreena tashiga tsakaninsu tana hana sameer wanda idonsa ke rufe bisa tsautsayi ya kai mata duka tasaki ƙara zata fadi ihsan da madina suka tarota
Ahmad nabeel saeed kokarin riqe sameer sukeyi amma yana zillewa
Sameer baiyi auni ba yaji sauƙan maruka hudu a fuskarsa da sauri yadafe kuncinsa sbd marin ya shigesa nan da nan ya samu natsuwarsa sakamakon tozali da idon mahaifinsa da yayi  ranshi abace
Ganin fadan nasu bana ƙare bane  yasa mami ta kira dad tace mishi kazo gidan biki ya zama gidan fada ga sameer na dambe shine ran dad yabaci suka taho dukkansu shida dadyn nabeel da dadyn saeed
Dad yana huci cikin muryan tsawa yace sameer kalan tarbiyyan dana baka kenn ? Irin ilmin dana baka kenn? Ina hnklnka yake ? Ina natsuwar taka take ? Wannan shine abinda zaka sakamin dashi kenn?

Dadyn saeed ne ya dafasa yace alh ya isa haka yanxu dai ba asi yakamata muji dalilin wannan fadan
Caraf madina tace dadyna wlh duk ya khalifa ne yajawo domin da baizo ba da yanzu muna can muna gudanar da shagalinmu cikin kwanciyar hankali

Kwace yakeso yayiwa yaya sameer najma wai yake kira da safreena
Nabeel yace madina ki rufawa mutane baki bakisan komai ba

Cikin tsiwa tace au yaya nabeel kaima bayansa kake bi kenn lallai kam ansamu waje sosae
To kai din waye khalifa ?

Tsawa nabeel yamata yace banace ki rufe bakinki ba

Lallai khalifa kasamu waje dama kam ance duk wanda yasamu waje saiyayi shanyarsa kuma wlh.....

Hannu safreena ta dagawa madina gamida cewa
Ya isheki haka madina
Shin kinsan waye YAYA KHALIFA kinsan wacece ni
STORY CONTINUES BELOW
Kallon dad da mami tayi tace haqiqa na yarda da cewa NA ANNABI basu ƙarewa aduniya duk lalacewar mutanen duniya akwai na kirki dad mami ku abin alfahari ne
Kun riqeni bana cikin hayyacina kun kula dani babu abinda zan ce muku illa Allah ya muku masauki agidan ALJANNA
Yau kuma zakuji tarihin wacce kuka riqe da matsayin wannan bawan Allah ta tuna khalifa dake tsaye kansa aƙasa
Kallon madina tayi tace madina mema kikace waye khalifa ko murmushi tayi hawaye na zuba a idonta tace
Shidin garkuwa ne agareni shidin haske ne agareni NA takaice miki zance shidin RAYUWA NE agareni
Sbd lkcn da ya fita arayuwata namanta komai amma yau gashi daga dawowarsa wannan hasken yadawo gareni
SAFREENA saida KHALIFA zata rayu
sunana SAFREENA MUHAMMAD BELLO BADIMASI

dad yace tsaya alh Muhammad bello badimasi dae wanda nasani shaharerran mai kudin nan wanda yake zama a garin abuja
Gyada kai safreena tayi tace eh shine mahaifina kowa a parlorn kallonta yakeyi dady bashir yace haba ai alh Muhammad babban mutum ne waye bai sanshi ba munji lbrn mutuwarsa kwanakin baya can
Cikin kuka safreena
Ta hau basu lbrn yanda iyayenta suka mutu kisan wulaƙancin da ƙanin abbanta dauda ya musu
da namijin kokarin da khalifa yayi akanta wahalar da  suka sha ajeji
Kallon madina tayi wacce take kuka harda sheshsheƙa tace madina yaya khalifa ya sadaukar da rayuwarsa akaina munyi rayuwa ajeji tare da shi yasha ƙalubale
Yaya khalifa yasha bullets wajan ma'aikatan dauda ranar da zamu rabu dashi ajeji harbi uku baba dauda yamasa
Madina babu wanda yadace da rayuwar safreena bayan khalifa
Sbd ya taimake ya kareni tun ni ba komansa bane yakike tunani idan nazama matarsa wace irin kalar kulawa zan samu
Na tabbata duk yan matan da suke nan zasu so su samu mijin jarumi tsayayye mai gsky da riqon amana da alkawari kamar YAYA KHALIFA
wajan ya dauki shuru sbd Al'ajabin halin dauda
Sameer kansa aƙasa shima dan kwata kwata baiji full story dinba tunda baije zaria sun zauna sunyi mgnr ba
Madina ce tazo gaban khalifa tana kuka tace haqiqa na jahilci lamarin kayi hkr yaya khalifa tabbas babu wanda yafi dacewa da najma..au .ina nufin safreena sai jarumi khalifa murmushi khalifa yayi batare da yayi mgn ba
Yaje gaban sameer ya dafasa yace dan uwa ko da zaka ɗauko wuka ka cakamin bazan taba daga maka murya ba sbd ina ganin girmanka balle kuma ace duka
Wlh sameer ko zaka kasheni da duka hannuna bazaiyi motsi da sunan ramawa ba sbd duk wanda ya taimaki safreena yazama babba awajena
Sameer bai ɗago ya kalli khalifa ba illama fita da yayi yana hawaye
Dad yace aure dai babu fashi tunda jama'a sun taro kuma na fasa jibin nan gobe goben nan za aɗaura auren kuma dukka za ayi
Ina nufin
Zan ɗaurawa KHALIFA aure da SAFREENA
sannan a ɗaura na NABEEL & MADINA
shima kuma SAMEER din zan aura masa IHSAN
Duk agobe jumma'@ INSHA ALLAH bana bukatar shawaran ku plss
hajiya aje acigaba da hidimar biki
Mami tace to alh
Ihsan ne taji kanta yamata nauyi tanaso tayi mgn amma kuma dad yace baya bukatar shawaran su dady balle kuma ita innalillahi wainna ilayhirrajiun
Mami tace duk su koma daki
Suna shiga daki kawaye suka dasa hira suna dry madina kuwa hnklnta ne yatashi da suka hada ido da nabeel ya galla mata harara tunowa da rashin kunyar datayine yasata kuka
STORY CONTINUES BELOW
Ihsan ma kuka ta hauyi na tausayin kanta ita burinta ta aure mijin dake sonta so na haqiqa ko da kuwa bata sonsa tasan wata rana idan haryana kyautata mata zata soshi amma ta auri wanda baya sonta ita take sonshi ai tashiga 39
Safreena kuwa kukan rayuwa takeyi domin kuwa sunga jarabawa awajan ubangiji
Nan kawaye suka dinga tsokanarsu
Barinma su ihsan da madina
Suna ce musu biki babu shiri
Dad ne ya kalli su nabeel yace kuje ku kwanta gobe amasallacin jumma'a ana idar da sallah za aɗaura aure to suka amsa dashi
Sannan dad yace khalifa kayi hkr da abinda sameer ya maka fa murmushi khalifa yayi yace ba komai dad ai ko harshe da hakori ana samun sabani balle kuma dan adam ajizi
Dad yayi murmushi yace Allah ya muku albarka suka amsa da ameen suka fice
Part din sameer suka koma amma basu gansa ba khalifa yace ina sameer yaje
Mtsw dallah kyalesa waya san inda yaje ai dai sameer ba yaro bane cewan nabeel
Khalifa yace aa nabeel dan Allah kuzo muje nemansa
Nabeel yace wlh nikam babu inda zanje
Saeed yace zai dawo karka damu khalifa
Sameer kuwa bai dawo ba sai sha biyu saura ya shigo a parlorn ya samesu dukkansu
Sallama yayi suka amsa batare da ya kula kowa ba yashige bedroom dinsa khalifa ya tashi yabi bayansa
SAMEER khalifa ya kirasa asanyaye
Juyowa sameer yayi wanda idonsa jajur ya ɗagawa khalifa hannu yace kayi hkr khalifa amma banason jin komai pls leave me alone

Fita khalifa yayi batare da yasake mgn ba
Sannan sameer bai san da zancan aurensa da ihsan ba
WASHE GARI RANAR JUMMA'ATU BABBAR RANA

gidan yasake cika tam da jama'a gabaki daya amare sun tashi da zazzabi barinma ihsan gabaki daya ta zabge tun safe take kuka babu kalan rarrasshin da kawaye basuyi mata ba amma taqi shuru karshe ma
Harda su madina da safreena aka koma rarrashin ihsan amma taƙi shuru
Mama ce tashigo dakin taja hannun ƴar ta ta suka fice adakin
Dakin mami sukaje sbd lkcn ba mutane adakin zaunar da ita tayi taga idonta sunyi luhu luhu sbd kuka
Mama tace ihsan kiyi hkr nasan bazakiji dadi ba ace lkc daya za amiki aure sannan kuma mijin hnklnsa baya kanki amma kisani ihsan hakuri wata bishiyar maɗaciya ce ayayin da kike taunarta zakiji ɗaci amma idan kika cinye zata miki magani ajiki ina nufin zakiga ribarta keda kanki
Dan haka nina san tarbiyyan dana bawa ƴata ihsan kiyiwa sameer biyayya domin kuwa kinsan auren nan babu fashi tunda dad Mukhtarh ya fada kidaina wnn kukan kinji ko ƴata
Kuka ihsan ta kuma sawa ta kwanta ajikin mama rarrashinta mama tayi kafin ta ɗagata ajikinta tace su madina sunyi wanka amma ke bakiyi ba dan haka na haɗa miki ruwan wanka tashi ki shiga kafin mai makeup ta gama yiwa su safreena da madina tazo nan ta miki kinji
To mama ta fada asanyaye tashiga toilet din mama kuma ta fice adakin
Su khalifa sun shirya cikin kaya iri daya wanda dad ya aiko musu dashi da safe su uku su saka  bugeggiyar shadda ce fara sol mai baƙin aiki da baƙin takalmi sai baƙin hula
Saeed yace tab wlh bazan iyaba nima kwanan nan zanyi aure lkc daya  gashi jiragenku zai tashi yabar nawa gsky nima anemamin mata
Dry Ahmad yayi yace gwauronmu
Hade rai saeed yayi yace wlh banso fa wlh
Kayan sameer khalifa ya ɗauka ya shiga dakin yasa mesa akwance
Ajiye masa kayan yayi yace dad yace ka shirya yanzu mu samesa a parlornsa yana kaiwa nan yafice abunsa
Tashi sameer yayi ya shirya amma zcyrsa cike da mmki gashi kayan nasu iri daya su uku
Atare suka fito
Awaje suka samu su dad's
Dad yace ku shiga mota mutafi haka kuwa akayi
Masallaci sukaje ga mutane tam bayan an idar da sallah ne
Aka fara sanarwan daurin aure
Rumtse ido sameer yayi dayaji ance an ɗaura auren KHALIFA ABDULLAHI TASI'U tare da amaryarsa SAFREENA MUHAMMAD BELLO BADIMASI
Bai kai ga bude ido ba yaji ance anɗaura auren SAMEER MUKHTARH JAFAR tare da amaryarsa IHSAN BASHIR AWWAL
wani zufa ne ya ketowa sameer
Sannan akace anɗaura auren NABEEL ABDULSALAM GAMBO tare da amaryansa MADINA MUKHTARH JAFAR
Akan sadakin dubu dari dari
ALLAH YABADA ZAMAN LPY AMEEN
Sameer bai jira ganin kowa ba yashiga mota ya koma gida

####

Wayyo kuyi hkr naso ace nayi typing yafi haka amma abubuwa sunsha gabana
Sai mun hadu a next page
Sharhi nakeso sosae idan ba haka ba kuma na ajjiye ALQALAMI NA
COMMENTS
AND
.SHARE
BY MMN AHLAN✍🏻

🌳🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*fílín gαíѕhє gαíѕhє zαn gαíѕhє dα mαѕσчαnα gudu α jєjí dαmα ѕαurαn grσup'ѕ kαmαr hαkα*............
*ѕαí α nєхt pαgє zαn fαdí ѕunαчєn ku kunα rαínα αlwαчѕ*❣
Short story✍🏻
*بسم ا لله لر حمن لر حيم*
🅿-3⃣2⃣➡3⃣3⃣

Dad babu kalan neman sameer da baiyi ba amma bai gansa ba har aka koma gida
Su amare zaune adaki bayan  su dad sun dawo ne ake shaidawa mutanen gida an. Ɗaura aure lpy  wasu ƙawayen da suke waje  sukaji da gudu suka koma daki domin su shaidawa amare an ɗaura aure
+
Da gudu suka shiga dakin suna murna cike da zolaya sukace masha Allah aure ya ɗauru gam ba rabuwa insha Allah
Wani faduwan gaba ne ya zuyarci zuciyoyinsu nan suka shiga kuka
Ƙawaye suka hau basu baki haba dan Allah kudai na wannan kuke kuken saika ce gidan mutuwa ba gidan biki ba
A yau fa kun taka matsayin da duk wata mace mai hnkln da tunani takeson takawa gdy ya kamata ace kunyiwa ubangiji ba kuka ba

Wata tace saidai idan kukan farin ciki kukeyi dry suka saka amma banda amare dake kuka basu bari ba

Ihsan a zuciyarta tace uhum ba gwanda ma su safreena da madina ba auren soyayya ne dama akwai shiri ni mai lkc daya kuma nace mene ai na boni wlh addua tashiga yi a zuciyarta Allah yasa auren ya zamto Alkhairi agareta ita da mijinta Allah kuma yasa yasota koda kaɗan ne

Dad ne ya turawa sameer text message *KA SAMENI A BEDROOM DINA*

Sameer dake kwance adaki yana jin zafi a zuciyarsa roqon Allah yakeyi Allah ya sassauta masa son matar wani domin yanzu ita haramiyarsa ce
Astagfirullah shine kawai abinda yake iya nanatawa a zuciyarsa saqon dad yagani saida ya gyara fuskarsa ya saita natsuwarsa kafin yafito baiga su khalifa ba azuciyarsa yace to ina sukaje ko dai an haɗa reception ne
Yanata tunane tunane harya fita jama'a ne yagani fal aciki da wajen gidan ga maroƙa suna wa'sa dad ya auren da yara maza uku a lkc daya sai fatan Allah ya ƙara girma suke masa
Yama rasa tayaya zai fara bin ta cikin wannan  jama'ar
Yace yauwa bari nabi kofar baya
Nan ma yaga ashe akwai mutane nan suka shiga yimasa fatan alkhairi suna tayasa murna
Murmushi ya kwaƙulo yanayi yana daga musu hannu harya samu yashiga part din dad
A bedroom din ya samesa yana zaune yayi sallama dad ya amsa ba yabo ba fallasa
Zama yayi a ƙasan carpet ya duƙar da kansa ƙasa yace dad gani
Dad yace ina kaje bayan an ɗaura aure ban ganka ba cikin sanyin murya yace kayi hkr dad zazzabi ne ya rufeni shine nadawo gida nasha magani
Dad yace sameer na isa da kai ko ban isa da kai ba? tmbya ce kabani amsa

Gaban sameer ne ya fadi yace
dad ka isa dani
STORY CONTINUES BELOW
Dad ya kuma cewa kuma inada sauran ƙima a idonka ?

A firgice sameer ya ɗago yana duban mahaifinsa kafin yasa kuka ya kamo hannun dad yace
Dadna yau idan ka umarceni na fada ruwa dad nayi maka alkawarin zan fada amma dan Allah dan Annabi dad kadaina irin wannan maganganun idan akan abinda na aikatawa khalifa ne dad kayi hkr zan bawa khalifa hkr kuma bazan sake mgn akan matar khalifa ba ya ƙarashe mgnr yana share hawaye
Dad ya rungumo sa yace sameer ina matuƙar son ka amma bana goyon bayan rashin gsky agidana ko kuma lalacewar tarbiyya bazanso ace ga ahalina ana aiba tasu awaje ba
Sameer a yanda kake cewa na isa da kai hakan ne yasa na ɗaura maka aure da IHSAN duk da ka taba cemin baka sonta sameer kaji tsoron Allah ina maka gargadine amatsayina na mahaifinka mai qaunarka wanda bazan so ka halaka ba sameer kaji tsoron Allah kaji tsoron Allah ka riqe ihsan da amana amatsayinta na matarka ta sunna wanda yau dibban jama'a suka shaida hakan sameer kasan wacece ihsan kasan tarbiyyarta kasan asalinta
Sameer karka manta da alkhairin mahaifin ihsan atare dakai wato alh bashir karka manta irin so da ƙaunar da ya nuna maka yanzu gashi ya ƙara maka da ƴar cikinsa
Sameer aikin da kakeyi mahaifin ihsan shi ya nema maka aikin tun banso kazama barrister ba shiya sanyani harna amince kuma ya nema maka aikin karka manta da wannan alkhairin sameer
Sameer ka riqe ihsan karkaga dan bamu gani kace zaka cutar da ita Allah bazai barka ba kayi hkr ka ɗauki kaddara safreena dai MATAR KHALIFA ce kayi kokari kayi yaqi da zuciyarka ka cire safreena sbd ina jiye maka fushin Allah
Sosae maganganun dad yashiga jikin sameer kuma insha Allah zaiyi kokarin hakan duk da bayin kansa bane
Yace dad insha Allah zanyi yanda kace dad ka tayani da addua plss
Murmushi dad yayi ya shafo kansa yace kullum adduata tana tasiri akanka Allah ya maka Albarka Allah yabaku zaman lpy ameen sameer yace

Dad yace tashi kaje kuyi pics watakila su khalifa sun dawo sunje neman inda zakuyi dinner ne
Idan angama tunda dama gidan ka yana nan su iyayenku mata da gwaggwanni sunje yi muku share share ita kuma madina gobe zasu wuce zaria tunda nabeel acan gidansa yake
Shima khalifa nayi masa mgnr akan gida amma dadyn nabeel yace akwai gidansa kusa da na nabeel khalifan ya fara zama acan kafin suje abuja wajan wancan dan iska tsinannan
Sameer yace to dad ba damuwa nine lawyer din da zan karbi shari'ar insha Allah
Dad yayi murmushi yace yanzu nasan ina magana da ɗana sameer shima murmushi sameer yayi
mahaifinsa yana da sauki yana da zafi
Tashi yayi ya fita yasamu su khalifa sun shigo khalifa yace sameer ina kashiga ne inata neman ka kuma har wayarka na kira baka ɗauka ba murmushi yayi wanda ba khalifa ba harta su saeed saida sukaji mamaki

Yace zazzabi ne ya rufeni shine nadawo gida nasha magani
Ayya sannu kaji kodai muje asibity ne ?

No khalifa nasha magani fa yanzu da sauki
Khalifa kayi hkr da abinda ya faru jiya
Murmushi khalifa yayi yace kai haba dan Allah kamanta babu abinda ya faru Allah yasa mufi karfin zcyrmu Allah kuma ya mana katangan karfe tsakaninmu da shaidan suka amsa da ameen
Cikin parlor suka shiga sai guɗa ke tashi ana ga angwaye ga angwaye tsofaffi sai zoyalarsu sukeyi
Amare sun saka less dinsu masu matuƙar kyau sunsha makeup
Sunyi kyau kamar kasace su ka gudu dasu

Kawaye suka rakosu nanma aga dinga zolayarsu ga amare ga amare
Nan aka shiga pics safreena sai satan kallon khalifa takeyi shima haka domin ba ƙaramin kyau tayi ba gashi tasha gyaran jiki sosae tunda ita anjima ana gyarata

STORY CONTINUES BELOW
Madina sai kallon nabeel takeyi amma ya kauda kai
Sameer ma ba laifi yana kokarin boye damuwarsa ihsan duk ta kasa sakewa abun ma kamar amafarki takeji har akayi pics aka gama Ahmad yace wa ihsan ina khairat
Cikin sanyin murya tace tana kwance zazzabi ne ya kamata mami ta bata magani ta samu bacci nan da nan hnklnsa yatashi yace kodai na kaita asibity ne
Safreena tace tana dakin mami ne fa sbd kar adameta
Ok kawai yace amma fuskarsa alamun damuwa
Da daddare haka akaci kwalliya
Amare sunyi matuƙar kyau kayan su iri daya net ne mai tsadan gske mom ce ta ɗinka musu red&yellow sai dauke ido sukeyi
Nan sukaje babbar wata hotel da suka kama mai suna INTISAR LALIMERH HOTEL  wajen  ya tsaru fadin yanda wajen yake bata lkc ne
Wajan zaman amarya da ango uku
Aka jera waje daya amma anɗansa rata atsakani kadan
Nan aka shiga aka dinga gudanar da event
Gsky jama'a sun cika sosae
Nan na hango ƴan *gudu ajeji fans  da anko dinsu suma sunyi matuƙar kyau dama abu nasu da yan *rayuwatace fans*  sai rawa sukeyi suna kwasowa harda shoki lox
Nan akaci aka sha tare da fatan alkhairi amma ko awajan dinner nabeel bai kula madina ba tanason masa mgn amma taga ba fuska shi kuma yana sane da ita amma ya fuske abunsa
Ihsan ma haka duk takasa sakewa sameer yana kula da ita bata sake ba tun shigarsu mota har suka iso kanta aƙasa yake yanzu haka
Masha Allah haka akayi lpy aka gama lpy
Ko da suka koma gida agajiye suke wanka sukayi suka canza kaya sai bacci
Domin da ance tunda ihsan gidanta anan ne sai amiqata kawai amma tana sa kuka mami tace abarta cikin yan uwanta kar arabasu yanzu abari kawai goben kafin yan zaria su wuce sai akaita da safe
WASHE GARI
Yan zaria sun shirya zasu tafi amma za akai ihsan tukunna

Nasiha sosae yan uwa suka musu akan haqqin miji akan matarsa

mami tace mama bari akawo miki ihsan  kiyi mata nasiha  mama tace aa tunda kun mata ai shikenn mami tace aa kam uwace ke ya kamata ki mata naki nasihan
Hnkln safreena ne yatashi data tuno momynta
ta tabbata da ace tana raye ba ƙaramin dadi zataji ba tunowa tayi ranar da tayi mata laifi take ce mata my safree ke kam wlh sai addua Allah ya shiryamin ke ranar aurenki da kaina zan kaiki ɗakin miji na fada masa saifa yayi hkr dake murmushi tayi gamida kwantawa ajikin momynta tace ameen momyna ranar aurena mai zakimin ?
Momy tace ai bazai faɗu abaki ba safreena kedai Allah ya nuna mana

Kuka safreena takeyi sosae gamida yiwa iyayenta addua tunowa da abbanta tayi ranar yana lissafin gina gida tace abbana nawaye ne yace naki ne my doter ranar aurenki zan mallaka miki shi amatsayin babbar kyauta ya fada yana shafa kanta

Kuka takeyi sosae kamar ranta zai fita tace
Dauda Allah ya isa bazan taba yafe maka ba ka cuceni yau ni safreena anyi aurena ba uwa ba uba kawaye sai rarrashinta sukeyi suma suna tayata kukan
dan ita kadaice ta rage adakin madina itama tana wajen mami bayan angama musu fadan ne su duka wasu yan uwa sukace mami da mama su kebe su kara yiwa madina da ihsan fada amatsayinsu na uwa
( Allah sarki *UWA*)

Allah ya wulaƙanta rayuwarka dauda innalillahi momyna yau anyi auren safreenan ki abbana anyi auren safreenan ka
Amma duk baku nan yanzu ba wanda zai zaunar dani ko mu kebe ya fadamin ga abinda zanyi ga wanda bazanyi ba
Mom ce tashigo dakin tuntuni tanajin abinda safreena ke fada kuka ne yakeson yaci karfinta na tausayin safreena daurewa tayi tace waya gaya miki babu wanda zai zaunar dake ya fada miki gsky ga wata mom din nan idan kinaso ta fada tana kallon safreena
STORY CONTINUES BELOW
Mom tace ku fita zamu kebe da doterna .
Fita sukayi mom ta zauna kusa da safreena nn tashiga yimata nasiha lallashinta

Masha Allah
Angama komai
Ihsan kuka takeyi tana riqe mama daga zuwa hutu shikenn za atafi abarta amatsayin matar aure
Da haka aka kaita gidan BARRISTER SAMEER dinta
Haka aka tafi aka  barta sai kuka take  daga ita sai halinta
*AURE KENAN YAƘIN MATA*
To haka suma yan zaria suka wuce madina itama tayi kuka har aka shiga mota aka tafi
Dama shi Ahmad tun safe ya wuce daura da matarsa da bata da lpy
Mota daya khalifa safreena nabeel madina
saisu mom da mama dawasu sauran yan uwa suma motarsu daban
Ko amota nabeel yaqi kula madina tashiga damuwa sosae wanda daka ganta kasan tana cikin damuwa
Nabeel ke driving sai madina agefensa

Khalifa yana zaune abaya shi da habibtynsa
Ganin ta takure ne yasan yashi janyota jikinsa jin jikintan yayi rauu yasashi kai bakinsa saitin kunnanta yace my safree baki da lpy ne ?

A madadin ta basa amsa saita ƙara lafewa ajikinsa
Shafa bayanta ya shigayi  a hnkln da haka bacci ya sureta
Itama madinan baccin ne ya kwasheta agefe tunda dama ba baccin kirki sukayi ba ganin rana a fuskanta yasa nabeel gyara mata kanta yadawo saitin fuskarsa inda babu rana

Sai karfe 4 suka isa gidan mom aka fara wucewa kafin aka wuce aka kai amarya safreena da madina gidan babu nisa dan zaka iya zuwa ma da ƙafa
Ga gidajen masha Allah sunyi kyau sosae duka kuma plat ne amma na
Sameer upstairs ne
####

Sai dare tukunna khalifa ya shigo gidan direct bedroom din safreena yawuce tana kwance sbd batajin ddi kukan da tayi yasa mata zazzabi mai zafi
Ɗagota yayi yace sorry habibtyna jikin ne ? Kodae muje asibity?

A hnkl ta bude ido tana kallonsa sai kuma tafara hawaye
Yaya khalifa Allah shine gatana sai kuma kai ba uwa ba uba ba yan uwa ba dangi duk wannan abinda na lissafa kaine su yanzu agareni

yaya khalifa ka fadamin abu daya
Yace mai zan fada miki komai kikeso fadamin
Kana sona?

Murmushi mai tsada ya mata kafin yace so na haqiqa nake miki my wife
Kefa kina son wannan bawan Allah ya fada cikin muryan yara haɗi da shagwaba
Duk da batajin ddi saida tayi dry tace tun ranar da kafara riqe hannuna muka shiga jeji nafara son mijina ta fada tana rufe fuskarta a qirjinsa dry yayi yace kitashi muyi sallah mu godewa Allah da ya nuna mana wannan ranan
Sallah sukayi sannan sukayi addua sosae
Ledar kazan daya shigo dashi  yabata da kyar taci tasha fresh'yo  ya dauko
Magani yabata tasha tana ya mutsa fuska daga nan yayi mata masaukin aqirjinsa gami da rungumeta sosae
Haka sukayi bacci cike da nishadi da soyayya
#######
Madina har wajan sha ɗaya tana zaune tana jiran nabeel yadawo tabasa hkr amma shuru babu shi babu lbrnsa har tayi wanka ta canza kaya tasha magani sbd batajin ddi bai dawo ba bacci ne ya ɗauketa sbd maganin datasha akwai maisa bacci
Nabeel sai shabiyu yashigo gidan da ledar kaza ahannunsa ahnkln ya tura kofan dakin yashiga ya ganta kwance amma duk atakure take har bakin gadon ya ƙarasa ya duqa yana kallon fuskanta shafo fuskan yayi
Aransa yace i love u my madina bawai inajin ddin abinda nake miki bane but nn gaba idan nayi mgn daya zaki dinga ji
Ya ajiye mata ledan yafice

STORY CONTINUES BELOW
#########
Ihsan bata tsaya jiran sameer ba tanayin sallar isha ta kwanta abunta sai  karfe10 harta fara bacci taji ya turo kofa yashigo zaune ta miqe tana kallonsa
Ajiye mata laden kaza yayi yace gashi nan ki tabbatar kinci kafin kiyi bacci
To kawai tace ya juya yafice abunsa
******

Da washe gari gidajen iyaye sunyi girki sun aikowa da amare
Safreena ko da ta tashi bataga khalifa adakin ba  dan haka tashiga tayi wanka tafito ta shirya cikin doguwar abaya ta feshe jikinta da turarukan da mom mama mami suka bata sai baza kamshi takeyi
Bedroom dinsa taje
Sallama tayi yana tsaye ajikin dressmirror yafito wanka ta mirror ya hangota ya mata murmushi gamida amsa sallaman yace shigo mana kodai tsoron dakin mijin naki kikeyi?

Tun kafin ta iso turarenta suka dingayi masa guɗa asaman kai take yaji hnklnsa yatashi

Har tazo gabansa ƙura mata ido yayi ganin haka yasata hura masa iska a idon yayi saurin lumshewa janyota jikinsa yayi ya fara aika mata da shu'umin kallon
Bakinsa ya hada danata
To daga nan fa labari ya canza

#######

Madina zaune a parlor tana jiran fitowar nabeel zuwa can anjima ya fito suna hada ido ya ɗauke kai zai fita da gudu ta rungumosa ta baya  tana kuka tana basa hkr akan bazata ƙaraba
Wani irin shock yaji amma ya cije yace naji sakeni tukunna qi tayi tace saikace ka hkr ka yafemin
Eh naji zan fada sakeni
Sakesa tayi ya kamo hannunta suka koma suka zauna yace madina abinda ya wuce ya wuce saidai atari gaba amma karki sake kinji ko ta gyada masa kai tana hawaye ya rungumeta yace to kukan ya isa haka tashi muje muyi sallan da bamuyi ba jiya yaja hannunta suka shiga bedroom dinsa
Amma ta bangaren ihsan babu abinda ya canza tsakaninta. Da sameer kuma babu abinda yashiga tsakaninsu sannan ko mgn wnn bata shiga saidai gaisuwa
balle hidiman auratayya kwata kwata ihsan batajin ddin yanayin zamansu ita da sameer
Adaddafe har akayi sati biyu ranar tana tsaye tana goge tv yayi sallama yashigo dan harya koma bakin aikinsa
Amsawa tayi ta karba jakarsa tare da masa sannu da dawowa yace yawwa ruwa ta kawo masa yasha kafin tace inason zamuyi mgn idan ba damuwa

Inajinki

Dan Allah ya sameer banajin ddin zaman da mukeyi da kai nasan baka sona amma ni inasonka tunda kai mijina ne ko da bazaka daukeni amatsayin matarka ba dan Allah mu cigaba da mu'amala
Kamar da ta ƙarasa da goge hawaye tausayinta yaji har kasan zcyrsa to miye aibun ihsan da baxai so ta ba

Share mata hawayen yayi sannan yace kiyi hkr sannan ki yafemin my ihsan insha Allah daga yau zan daukeki amatsayin matata ba ƙanwa ba ya kwantar da ita ajikinsa daga nan komai ya canza
Masha Allah haka suke shan soyayya kamar baza amutu ba
Khalifa nan nan yakeyi da safreenan shi ita kuma ga shagwaba tadinga narke masa kenn shi kuma yana biye mata wani lkcn ma idan ta tashi saita ce bazata iya wanka da kanta ba saidai ya mata

*********

Bayan wata biyu
Dukkan wani bincike khalifa yasa anyi masa akan dauda shiri sukeyi gobe zasuje abuja su dad's sun basu goyan baya dari bisa dari tare da yimusu addua

Sameer ma yazo  harda ihsan dinsa dan yanzu yafara son abunsa yana kula da ita sosae

Duk suna zaune a parlorn khalifa
STORY CONTINUES BELOW
Ahmad yace a binciken danayi dauda bai siya komai ba
ta yanda plan din mu bazai bamu wahala ba kenn
Sameer yace ai kasan mugu tunanin mugunta kawai yakeyi banda wani abun kirki haka dai suka dinga shawara yanda zasu gudanar da aikinsu
Da washe gari su hudu suka dauki hanyar abuja suka baro matansu a zaria
Sun isa da wuri domin dauda jiya yazo nigeria yaso ya koma ƙasar waje sai zazzabi  ya rufesa
Su khalifa hotel suka kama
Da daddare bayan sallar isha'i  sukayi shigarsu na tsofaffi ga wasu manya gashin kai da suka saka sukayi rawani ga gamu nan harna tabo qirjinsu
Bayan sun shirya dasu kaga kansu a mirror dry suka hauyi saeed yace tam lallai dauda yau maza bisa kanka
Ahmad yace to yanzu khalifa wannan shigar da kasamu mukayi fa taya zamu fara gudunar da aikin ?

Murmushi khalifa yayi yace kawai duk abinda nace shi zakuyi kun fahimta ?

Nabeel yace amma dai baka da hnkl khalifa daudan ne zai ɗauki takardun yabamu da hannunsa ai ko giyan wake yasha na tabbata bazai baka takardun nan ba
Khalifa yace ni kuma shida kansa zai bani kudae muje lkc yana tafiya fita sukayi suka shiga mota khalifa ke driving har gwarimpa yanata kallon hanyan yana tuno abubuwa dayawa har sukayi parking a katafaren gate din

Nabeel Ahmad saeed sai yaba gate din gidan sukeyi
Hanasu shiga akayi khalifa ya karkace murya ya kalli qartin da suka hanasu shiga yace kaje kacewa boss din naku yayi baƙi daga ƙasar nijar sannan munzo masa da lbrn KHALIFA da SAFREENA ne
Juyawa yayi yashiga bai juma ba yafito yace boss yace ashigo daku
Baki khalifa ya karkace yayi murmushin nasara sannan ya kalli su sameer yace mujenku
Fitowa sukayi saida aka caji jikinsu babu koda tsinken ashana ne kafin wasu qatti sunkai 15 suka sakasu tsakiya har parlorn abba khalifa hawaye ne ya cika idonsa gani yakeyi duk abinda yafaru kamar a film

Dauda zaune ya bararraje a kujeran abba
Sunayin 4eyes's gaban dauda ya fadi yace kai tsoho ya  ina ganinka na tsorata jikin khalifa har tsuma yakeyi sameer ya riqe hannunsa ganin yanda jikinsa ke ba'ri

Da kyar khalifa ya saita na nutsuwarsa dan ji yake kamar yaje ya sheqe dauda
Yau gashi ga dauda
Khalifa yafara mgn kamar tsohon gske
Yaro dole gabanka ya fadi daka haɗa ido dani sbd ni ba kamar kowa bane sannan nidin na musamman ne
Yaro baka ce mu zauna ba ?

Dauda yayi tsaki kafin yace to ai saiku zaune
Zama sukayi dauda yace ance kazo min da jawabin akan khalifa da safreena
Bayan a iya sanina sun mutum kuma abinda yasa nace ashigo daku bansan a inda kuka sansu ba ya mgnr take ?

Yaro gsky kai jaki ne waya gaya maka sun mutu.
Dauda ya zabura ni kake kira da jaki ?
Saeed yace yaro ba a budewa  shugba ido ka kiyaye danmu badaga duniyarku muke ba a duniyar aljanun nijar muke dan haka mun fasa taimaka maka din shugaba tashi mutafi
Dauda jin haka yasan yashi cewa kayi hakuri shugaba Ahmad ma ya karkace murya yace
Kaiiiii ba abawa shugaba hakuri daga tsaye zuwa zakayi ka duqa ka riqe ƙafafunsa kabasa hkr
Jiki na rawa dauda yazo ya riqe kafar khalifa yi hakuri  shugaba
Wani murmushi khalifa ya saki sameer kuwa dry ce ke cinsa shida nabeel duk sun kasa mgn
Khalifa yace to yaro na hakura
Nasan duk yanda kukayi da wannan yaron khalifa kuma yace maka zai dawo ko...dauda yace eh sannan...
Maidawa dauda yanda sukayi ajeji da khalifa  yayi dauda tuni jikinsa yafara rawa yace eh wlh tsoho haka mukayi dashi
Khalifa ya kuma murmushi yace to kasan wani abu kuwa ?
Cikin zaƙuwa dauda yace aa
Khalifa yace to dai
khalifa da safreena

Suna raye kuma suna gaf da zuwa inda kake domin karban takardun dukiyar dake hannunka ni kuma bazanso hakan ba domin ajikin takardun duk kadarorin nan sunan safreena ne akai sannan nasan wani abun bazaka iyaba sbd babu sa hannun safreena
Dauda yace eh hakane  tsoho
Khalifa yace to yanzu dai ba tare da bata lkc ba ka ɗauko takardun nn kabani zanje nasa yaron aljani yasamaka hannu sannan ka cigaba da sheke ayarka
Shuru dauda yayi yana nazari kafin ya miqe da sauri yayi daki
Minti kadan yafito da takardun ya kawo ya miqawa khalifa
Mamaki ne ya kamasu sameer nabeel Ahmad saeed ganin dauda ya miqawa khalifa takardun

Dubawa khalifa yayi sannan yayi dry mai sauti yace da kyau yaro dauda lkc yayi da zaka zama abin kwatance
Dauda yace kamar ya ?

Murmushi khalifa yayi yace ta yadda duk inda ka shiga za adinga nuna ka

Dauda ya hau dry  dan bai fahimce inda mgnr ta dosa ba
Miqewa khalifa yyi ya kalli dauda yace karkayi motsi daga nan ina zuwa zan duba dakin yaron nan khalifa
Dauda yace to ai tun fitarsa babu wanda yaje wajan
Khalifa yace akwai ajiyar da yayi ne zaije daukowa dauda nan ma to yace
Khalifa yafice su saeed sukabi bayansa har izuwa dakinsa na da ya kwashe abubuwansa masu amfani dan babu abinda aka taba adakin su nabeel suka tayasa dauka yafito yasa amota
Suma suka shiga mota sannan khalifa ya kira daya daga cikin samudawan dauda yace masa kiran min boss dinku
Yana shiga yafito khalifa yace yaro mun gama zamu dawo gobe amma ba lallai bane dawowar tayi maka kyau sannan nasan ko a yanzu zaka iya banbance tsakanin jahili da mai ilmi yana gama fadin haka yaja mota suka bar dauda atsaye baki sake yana maimaita kalaman khalifa


*بسم ا لله لر حمن لر جيم*

🌳🌳🌳🌳🌳🌳
        🌳🌳
*GྂUྂDྂUྂ Aྂ JྂEྂJྂIྂ*
🌳🌳🌳🌳🌳🌳
           🌳🌳
*₴тояу щяїттёи Ьу*

*ᏃᎯᏂᖇᎯ ᎯᏰᎴᏌl{mᏫm ᎯᏂlᎯᏁ}*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassoc

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

*filin gaishe gaishe*
*jinjina da gdy gareku masoya na* *wanda nasani da wanda bansani ba yanda kuka bibiyi lifftafina ina gdy sosae kuma ina matuqar qaunar ku naso na lissafu ku amma ina busy Allah yabar qauna*

🅿-3⃣4⃣➡3⃣5⃣➡🔚

Anya kuwa ba khalifa bane wannan ?
Domin muryan sa naji a ƙarshen maganarsa
Na shiga uku ni dauda gashi na basa takardun nan
Amma duk iya makircinka zaka haɗu da dauda ne ya koma cikin parlorn jikinsa na masa zafi ga tashin hankali ga zazzabi+
Doctor yasa aka kira masa ya duba sa domin jikin na  ƙara masa zafi sosae ga ƙaiƙayi wani lkc har kwakwalwarsa yakejin ƙaiƙayin
Khalifa kallon takardun yayi sannan yayi murmushi a mota babu mai mgn har suka isa hotel din da suka kama sukayi othern abinci
Suka watsa ruwa kafin suka zauna domin suci abincin

Saeed ne yafara kyalkyala dry ba ƙaƙƙautawa nabeel Ahmad  ma  suka hau tayasa domin sun gano dryn da yakeyi

Sameer da khalifa suka sake baki suna kallonsu
Sameer yace lpyr ku kodai kafin mu baro gidan dauda yabaku abu kunsha ne ?

Cikin dry saeed yace wlh ban taba tunanin dauda asalin zindiƙin jahili bane kamar haka ace baka san mutane ba amma ka ɗauki takardun dukiya mai tsaban yawa kamar haka kabasu lallai dauda asalin maloho ne
Sameer ma dry yasa yace ai irin su dauda mugunta ne aransu kwata kwata basu sa komai agaban su ba
banda mugunta anya irin su dauda suna tunanin mutuwa kuwa?

Ahmad ya ɗan sassauta dryn sa yace ina kuwa mutane masu halin dauda zasuyi tunanin mutuwa bayan su bazasu mutu ba ai shi makashi gani yake kamar baxai mutu ba
Saeed yace wlh kuwa inaji dauda shine a gate din farko ya ƙarashe mgnr da sakin wata dryn
Khalifa yace gate din farko kamar ya?
Saeed yace na gadin duniya mana khalifa yayi murmushi domin mgnr su tabashi dry
Ahmad yace yanzu gobe zamuje da jami'an tsaro aka masa ko dan gsky mutane ire iren dauda barinsu cikin al'umma babbar hatsari ne
Khalifa ya girgiza kai yace ko daya ba gobe za akama dauda ba
Duk gabaki daya suka tsaya suna masa kallon tuhuma mai kake nufi khalifa?

Murmushi takaici yayi idonsa suka ƙaɗa sukayi jaa yace inaso sai dauda ya rasa ma tsuguni domin harta takardun gidan abba wanda daudan yake zaune yana nan acikin wa innan  takardun kuma dauda bai siya wata kadara ba balle ya tsira dashi

Nabeel yace ai shi duk a tunaninsa kun mutu ya kashe ku shiyasa yake cin karan sa ba babbaka

Sameer gobe zamuje da kai zaka siye gidan abba na gwarimpa wanda dauda ke ciki amma kafin nan zanyi mgn da my wife domin tasan halin da ake ciki
STORY CONTINUES BELOW
Sameer ya dafa qirji yace me kace khalifa na siya gidan abba da wani kudin? Ai ko gidana na adamawa na siyar sannan na siyar da gidan dad na haɗa kudin bazasu kai na siya wannan gidan gwarimpan ba gsky ka canza shawara
Murmushi khalifa yayi yace ai duk acikin plan dinmu ne ku saurareni da kyau abinda zan fada muku

Yanda za ayi shine........
Jawabi yake musu suna jinjina kai alamun fahimta
Sannan sameer yace ayyo yanzu nagane khalifa yace yauwa yanzu dole gobe matata tazo abuja domin tasa hannu idan yaso tayi asubanci driver ya kaita kaduna saita hau jirgi tazo dan zatafi saurin isowa
Nabeel yace pls azo da madina dan nima gsky nayi missing din matata
Sameer yace wato ni kuma sai abarmin my ihsan ina sam wlh saidae su taho duka
Ahmad yace karku raina min hnkl ai duk nafiku bukatar matata akusa dani ita da take bukatar kulawa na da babyna kunsan fa kwanan nan zan zama daddy nima ya fada yana kashe ido

Nabeel yace to fada ma wanda baya da mata
Saeeed yace ni kenan nima kwanan nan zanyi auren mata nake nema na huta da gorin ku

Khalifa yayi dry yace kufa baku gajiya da drama to ai shikenan dukkansu suzo
Wayarsa ya ɗauka yaga miss calls din habibtynsa murmushi yayi sannan yashige daki yabarsu a parlor
Kiran ta yayi ringing biyu ta ɗauka amma sallaman da kuka yaji
Sosae hnklnsa ya tashi ya hau tmbyarta my safree menene

Bata basa amsa ba sannan ba tabar kukan ba rumtse ido yayi sbd kukanta har kwakwalwarsa yakeji
Cikin sanyin murya yace my safree me namiki ? Kike azabtar dani da kukan ki ? Baki kusa dani dana sa kin taba saitin zuciyata kiji yanda take bugawa da karfi hawayenki tamƙar ruwan narkenken dalma nakeji my wife ki taimaki mijinki kidaina kuka sannan ki fadawa mijinki meya saki kuka idan ma shi yasaki kuka yabaki hkr ya lallasheki
Jin haka yasata sassauta murya cikin muryan shagwaba da kuka ta fara mgn to ba kai bane kaje wajan wancan marar imanin kuma tun dazu nake kiran ka baka ɗauka ba shine naji hnklna yatashi kuma nayi missing dinka dayawa gashi nakasa bacci
gadon yamin girma nakasa saka kaina akan pillow sbd qirjin mijina dana saba kwanciya akai
Murmushin jin ddi yayi haba my safree nifa dama kiran ki nayi na fada miki gobe kizo
Cikin murna tace d gsky my lyf ?

Yace ehma
Labarin yanda plan dinsu yayi yabata sannan da hannun zatasa acire kudi abawa sameer ya siyan. Gidan
Tace tsinanne mugu 
Khalifa yace su sameer sunce aka masa gobe amma ni kuma bana so dauda yayi mutuwar sauƙi yanda muka sha wahalan *GUDU A JEJI* haka shima zan ɗanɗana masa azaba kafin nasa aka mashi alƙali ya masa hukunci daidai da abinda ya aikata

Wani sabon son mijinta taji yana yawo akanta tace  *I LOVE YOU MY HUSBAND*  haqiqa ni nayi dacen miji jarumin maza gagara gasa tsayayye saidai nayi ma wasu fatan samun miji kamar nawa

Murmushi yayi sannan yace nine wanda nayi dacen mata *ANA UHIBBUKI MATATA*
nan dae suka cigaba da hiran soyayya yayinda suke fallasawa junansu sirrin zuciyoyinsu
Washe gari

Dauda kwance a parlorn doctor yadawo da result din text din da yamasa jiya da daddare
Doctor ya fara jawabi kamar haka alh a gsky binciken mu da mukayi mun gano kana ɗauke da cutar HIV
Zunbur dauda ya miqe zaune
Kaiii wlh karya kakeyi likita kace ina ɗauke da cutan ƙanjamau
Likita yace kayi hkr alh amma mu abinda muka gani kenn dan ba ni kadai bane nayi bincike kuma ya maka mummunar kamu domin akalla zai kai wata 7 jikin ka yanzu kuma harya fara maka illa domin kuwa duk jinin jikin ka ya gauraye ƙaiƙayin da kakeji kuma alamun fitar ƙuraje ne
STORY CONTINUES BELOW
Wani zufa ne ke ketowa dauda ta ko ina domin gabansa ma ai ya jima da fara ƙurajen tashin hankali HIV wayyo Allah na ni dauda nashiga uku
Likita yace to nidai alh saidae nace maka Allah yakara sauki sai inkazo karban magani idan ba haka ba
Hatta shiga mutane zai gagare ka sannan ko a yanzu  idan rana yataba ka zakaji ƙaiƙayi kana sosawa kuma kuraje ne zai fito maka  dan haka alh shawara gareka kayi hanzari zuwa karban magani doctor ya fice abunsa yabar dauda da zufa kwata kwata ma yanzu babu kudi ahannunsa wayyo Allah ni dauda
*********

Karfe 2 suka sauka a airport khalifa ne yaje ɗaukan su
Tana hangosa ta faɗaɗa murmushinta da gudu ta rugo domin tayi hugging dinsa amma me kafin ta iso jiri ya kwasheta ta zube kasa asume
Cikin tashin hnkl madina da ihsan suka hau jijjigata khalifa da gudu yazo ya ɗagota yana kiran sunanta kallonsu ihsan yayi yace dama yau ta tashi da zazzabi ne? girgiza kai sukayi alamun aa
Ɗaukarta yayi cak yasata amota sai CITY HOSPITAL
Binciken farko aka gano tana ɗauke da jaririn ciki na wata daya da sati biyu
Khalifa tsantsan murna da farin ciki zubewa yayi awajan yana hawaye tare da gdy wa Ubangijin talikai
Sai gasu sameer da hanzari dan ihsan ta kira sa tace masa safreena ta suma suna asibity dan haka sukazo cikin tashin hnkl da gudu ihsan ta rungume sameer tace mun samu ƙaruwa safreena tana ɗauke da baby tukunna hnklnsu ya kwanta nan su sameer nabeel saeed Ahmad suka hau tayasa murna
Ahmad cikin zoyala yace ah mukam kwanan nan za afara binmu da gudu ana cewa daddy daddy khalifa yasa dry
Nabeel yayi tsaki yace nima ai kwanan nan za afara cemin dadyn ai wannan kuma saidae kayi da saeed dan shine gwauro
Tsaki saeed yayi yace keee ihsan
Sameer yace ah haba mana malam karka tsorata min mata irin wannan kira haka
Aiho kai matar kace ni kuma ƙanwata ce
Sameer. Yayi dry yace aidai nafi iko da ita dan haka yimata mgn ahnkl

Khalifa dae dakin safreenan shi ya wuce domin ance zai iya shiga yaganta dan yanzu ma za ayi discharge dinta
Kwance ya sameta tana hawaye da sauri ya  ƙarasa wajanta kwantawa yayi ajikinta yana shafa cikinta
My safree kin gama min komai arayuwata Allah ya miki albarka Allah yafito da babynmu lpy ina sonki
Shafa kansa tayi yaya khalifa nikam nagama samun dukiyata
Share mata hawayen yayi sannan ya bata hot kiss a lips dinta
Knocking doctor yayi khalifa ya ɗago yabasa takardan sallamansu
Safreena ta sauƙo da niyyar tafiya amma me khalifa ɗaukarta yayi cak yafita da ita kowa sai kallonsu yakeyi domin sun burge
Bayan sun koma hotel din ne khalifa yace yanzu kam dole mu ƙara kama wasu rooms din ni kubarmin nan nabeel sameer kuma ku kama wani daban idan yaso Ahmad da saeed ku kama daya
Sameer yace eh hakan ma yayi
Fita sukayi khalifa ya koma ɗaki wajan safreena takardun yabata yace my safreena kisa hannu sbd yau bana so dauda yaƙara koda rabin dare ne agidan
Karba tayi duk gabaki daya takardun tasa hannu sannan ta miqawa mijinta
Karba khalifa yayi ya duba da sauri ya miqe tsaye gami da cewa safreena miye haka wannan wani irin rashin hnkl ne nifa ba irin wannan sign din nace kiyi ba maza karba ki canza ya faɗa ranshi bace
Miqewa tsaye itama tayi ta rungumesa tabaya hawaye yafara zuba a idonta  mijina idan abunda nayi yabata maka rai kayi hakuri amma ni bana bukatar wata dukiyan duniya wanda baya ɗorewa abbana daya tara su yanzu yana ina ?  Yaya khalifa safreena tagama samun dukiyarta
Kaine dukiyata kai da ɗan da yake cikina nagama nikam kune dukiyata kune rayuwata

STORY CONTINUES BELOW
Dan haka dukiyar nan na mallaka maka shi halak malak
Hannu yasa ya janyota tadawo gabansa yana kallonta
share hawayen fuskanta yayi sannan yace safreena kar muyi haka dake umurni nake baki da riqe dukiyarki domin kuwa naki ne
Kuka tasa masa dama ashe baka sona yaya khalifa ni atunani na dani da abinda na mallaka duk mallakin ka ne kuma kana da iko damu ashe kuskure nayi
Parlor ta fita tana kuka da sauri ya bita ya riqo hannunta tana kwacewa da kyar ta tsaya yace naji na karba amma ki riqe rabi da kwata ahannun ki idan yaso saina cigaba da gudanar da business din abba hakan ya miki ?

Turo Baki tayi tace to amma inaso agina gidan marayu da makarantu  sannan agina rijiyoyi da bohul a shuka bishiyoyi ya zama sadakatul jariya ga iyayenmu ina nufin agina su da sunan iyayena da naka ladar Allah ya kai musu ƙabarinsu
Rungumeta yayi yace Allah ya miki Albarka matata
Ameen ta amsa sannan ta manna masa kiss a kumatu

Yace bari naje nadawo ya fita su sameer ya tarar suna jiransa yashiga mota suka tafi tare da wasu ma'aikatan Ahmad da kuma abokan aikinsa
#####

Dauda kwance a parlor yana juyi lkc daya abubuwa sun cakuɗe masa
Wani yaron sa ne ya shigo da sauri yace boss wasu mutane sunzo wai suna son ganin ka zasuyi magana da kai
Dauda yace kace su shigo fita yayi ba ajima ba sameer Ahmad saeed
Da wasu mutane suka shigo
Gaishe da dauda sukayi da kyar ya amsa sannan sameer yace wannan gidan nawane nabaka nan da 10hours ka fita domin na siye sa

Afirgice dauda ya miqe yana musu wani banzan kallo
Yace me kace ? Gidan ka dae to nan gidan dan uwana ne
Ahmad yace au gidan dan uwanka ai ba gidn ka bane sannan ya siya gidan ne ahannun yar mai gidan wanda take da alhaki da iko da gidan ƴa daya tilo SAFREENA ALH MUHAMMAD BELLO BADIMASI
zufa kawai dauda keyi yace ina safreenan take sameer yace wannan ba damuwar ka  bace nidae kafita min a gidana idan ba haka ba wlh hukuma ce zata fitar da kai
Nan dauda yafara sanbatu kamar wanda yasamu tabin hnkl
Ganin haka yasa saeed yace ai kuwa mun fasa baka nan da 10hours din nan yanzu zaka fita kuma bari kaga wanda zai fitar da kai
Juyawa yayi yana kallon kofa sannan yace
*KHALIFAA*
Dauda kallon kofar yakeyi yaga tayaya khalifa zai shigo ahnkl khalifa ya danno kai a.parlon yana taku cike da isa irin na jaruman maza marasa tsoro har yazo gaban dauda yana masa wani shu'umin murmushi alamu kaine yau aƙasa dauda
Khalifa yace dauda nadawo
Acikin tsoro yace ba kai bane nasan ka mutu nida hannu na na kashe ka a jeji
Khalifa yayi dry yace kayi kuskure dauda amma baka kashe mu ba domin ran mu ba ahannun ka yake ba Allah shiya karemu sannan ya fiddo mu lpy daga jeji saidai kawai wahalan da mukashe
Wuya bata kisa saidai ta ladabtar da mutum mun sha wuya kam amma kasani dauda karshen ka yazo
Dauda zaiyi magana khalifa ya ware hannunsa jikake tass!tass!tass!tass!
Mari hudu saida dauda ya zube kasa domin marin ya gigitasa
Fuskan khalifa ya canza kala yace marin dana maka fansan marin matata da kayi ne naci alwashi saina rama mata zunbur dauda ya miqe tsaye hannunsa a kumatunsa sbd har yanzu bai dawo nml ba yace matarka wacece matar ka ?

Safreena
Khalifa yabasa amsa ya taƙaice sannan ya fizgi rigan dauda ya hau jansa da iya karfinsa ya fitar dashi wajan gate ya wullar dashi
Ya nuna shi da yatsa yace naso ace yau kayi kwanan cell amma yanda kabamu wahalar GUDU A JEJI kaima saika ɗanɗani azabar yawo akan titi sannan aka maka ayi maka hukunci abinda ka aikata

STORY CONTINUES BELOW
Yana gama fadin haka ya juya ya koma cikin gidan ya umurta qattin dauda dasu bar gidan yanzun nan ba shiri sukayi takansu domin a idonsu aka ja boss dinsu kamar jaki
Akayi waje dashi balle su
Dauda sanbatu kawai yakeyi batare da yasan me yake cewa ba lokaci daya duniya tayi masa attishawan tsaki
Kulle gidan khalifa yayi sannan yasa adinga bibiyar dauda
Ya koma ya cigaba da kula da matarsa gini yasa akafara yi asabuwar wata unguwa mai suna *katampe* sosae ya tayar da gini
Dauda yaga masifa gashi duk inda yaje koransa akeyi (dama abinda ka shuka shi zaka girba)

Dare ya tsala gashi ba wajan kwana duk inda ya kwanta za akoresa ga yunwa ga ƙishin ruwa ga ciwo
Karshe dae a lambatu ya kwanta dan ji yake kamar zai mutu
Da washe
Idan kaga dauda saika tsorata fuskarsa duk ƙuraje sunfito akwana daya tak
(KADAN KENAN DAGA CIKIN SARAUTAN ALLAH  ZAI ARA MAKA LKC KAYI DUK ABINDA KAKESO AMMA LKC DAYA IDAN. UBANGIJI YATASHI IKONSA ZAI SHEFE KA KA ZAMTO KAMAR BA AYIKA BA A DORAN ƘASA ALLAH YASA MUFI KARFIN ZUCIYARMU AMMA A GSKY YANZU SON KUƊI DA BURIN DUNIYA YANA SA MUNA MANTA LAHIRANMU YA ALLAH MASU HALI IRIN NA DAUDA ALLAH KA SHIRYAR DASU DAMU BAKI DAYA ALLAH YAƘARA SHIRYAMU AMEEN)

yana kwance yaga an miqo masa bottle'water baiga fuskan wanda ya miqa masa ba da sauri ya karba ya hau kwankwaɗar ruwan yana gama sha ya hau amai saida ya amayar duka
sannan ya koma yana jan numfashi awahale ɗogo ido da zaiyi yaga su police akansa
Tari ya farayi wani abu yauƙi yauƙi yana fita abakinsa police din ƙyaman tabasa sukeyi kiran khalifa sukayi suka fada masa halin da dauda yake ciki gashi nan zuwa kawai yace musu
Bayan kamar 40mnts sai gasu su duka sameer ihsan madina nabeel saeed Ahmad khalifa safreena
Safreena tana ganin
Dauda ta hau salati gami da kuka har wani irin wari yakeyi toshe hanci tayi tace kadan kenn dauda Allah ba azzalumin bawansa bane saidai shi bawa ya zalunce kansa kafin ka mutu ka fadamin yakamin da gawan iyayena kuka tafara sosae khalifa ya rungumota
Yaya khalifa ku tmbyesa ya yamin da gawan iyayena anyi musu sutura ko kuma jefarmin dasu yayi ta cigaba da kuka
khalifa yace ko  a yanzu dauda kazama abin kwatance Allah ya mana tsari da irin halayenka wanda zaka kashe dan uwanka domin kudi
Khalifa ya kalli yan sandan Yace kubarsa Allah ya nuna masa ishara ahakan ya ja hannun safreena suka shige mota
Yan sandan ma suka tafi akabar dauda awajan
Kwanan dauda uku bai mutu ba amma jikinsa harya fara tsutsa
Sati daya cif da safe jama'a suna wucewa sukaji ɗoyi natashi toshe hancinsu sukayi duk da tunaninsu kare ne ya mutu agefen bola
Ko da mutane sukaje suka ga dauda salati suka hauyi nan yadinga karanto musu abubuwan da ya aikata wasu harda yimasa video suna Allah wadai da masu halin irin naka bayan yagama faɗi ne yafara tarin jini yana ta murƙushe murƙushe sai juyi yakeyi zuwa can anjima ya tsaya ɗif yadaina motsi
Jama'a sai tsine masa sukeyi kowa gudunsa yakeyi ga jikinsa duk yabaci da kuraje tsutsotsi nata fita kowa yace bazai tabasa ba
Da kyar wasu da warin ya ishesu suka tattarasa suka tona rami suka binne sa haka ba wanka balle ayi tunanin yimasa SALLAH
( Innalillahi wainnan ilayhirrajiun ya Allah ka rabamu da mummunar karshe Allah ka ɗauki ranmu acikin salihan bayi bijahi Annabi sallallahu alayhi wasallam Allah ameen )
******  ZARIA
su khalifa zaune a parlon dadyn saeed su duka har dasu dad da dadyn nabeel mama mami mom
Dad yace Alhamdulillah yanzu komai yayi daidai Allah ya muku Albarka suka amsa da ameen
STORY CONTINUES BELOW
Khalifa yace dad dady dady haqiqa babu abinda zan ce muku saidai Allah ya muku masauki agidan Aljanna aka amsa da ameen
Sannan yace sameer saeed nabeel Ahmad kun zama jinin jikina Allah yabarmu tare suka amsa da amen
Khalifa yace dad dama na gina mana gida mu hudu inaso su sameer saeed da nabeel mu koma abuja da matanmu mu cigaba da business dinmu dama shi Ahmad kwana biyu da suka wuce akayi masa transfer ya koma abuja shine yanzu yaje ya taho da matarsa
Dan Allah dad's mom's Ku sa mana Albarka
Sosae sukaji ddi sukayi musu fatan Alkhairi
Khalifa yace  a satin nan zamu koma
Saeed yace wlh sai anyi aure na tukunna dad yace son ka samu matar ne yace eh dad yar gidan fa baba hashim ne fa dadynsa yace wacce acikinsu yaran uku ne ai
Saeed yace  ƙaramar su hayrat
Dady yace to ba damuwa tazo da sauƙi ai gobe zamuje idan yaso ayi bikin cikin satin nan saiku tafi tunda me za a tsaya jira
Agurguje
Dad sunje anyi mgn kuma anbasu nan aka ɗaura auren saeed bakinsa yaqi rufuwa shima yau gashi ga matarsa
Ya huta da gori haka khalifa ya kashe kudi akayi shagali kamar ba gobe
Haka suka tare a babban gidan su mai part biyar amma ko wanne akwai gate dinsa upstairs ne yayi kyau sosae masha Allah
A katampe

Soyayya sosae khalifa da safreena sukesha yayinda suke tattalin junansu basu son bacin ran junansu
Kafin dan   ƙaramin lkc khalifa ya zama babban mutum sunansa ya zagaye duniya shida matarsa safreena sbd taimakon al'uma da sukeyi
Kuma sunje katsina khalifa yabawa baba mai gadi gidansa na katsinan sannan ya siyawa inna gida ya ajiyeta ya mata komai amma duk da haka bakin inna bai mutu ba
Har jejin babbar bishiya saida khalifa ya kaiwa zakin dawa ziyara da farko ma bai gane khalifa ba saida ga baya sosae khalifa yamasa sha tara ra arziki masha Allah wannan kenan

Cikin safreena yashiga watan haihuwa yanzu kullum khalifa yana gida
Khairat matar Ahmad ma ta haifi ƴarta mai suna zaitun
Ihsan da madina da hayrat suma sunada ƙananun ciki
Zaune suke a parlor tana kwance akan cinyarsa yana mata susan kai riqe mara tafarayi wayyo Allah yaya khalifa marana bayana
Da sauri khalifa ya ɗauketa sai asibity bayan tasha wahalan awanni ta haifo ƴaƴanta biyu mace da namiji
Masu kama da iyayensu
Murna awajan khalifa abin ba a tonawa har mamakin kansa yakeyi wai yau shine khalifa ya zama babban mutum haka ga yara biyu alkc daya ranar dai sadaka yadinga yi kamar ba gobe

Har aka sallamesu ranar suna namijin yaci sunan abba wato Muhammad zasu dinga kiransa da (Al'ameen ) mace kuwa sunan mahaifiyar khalifa aka samata wato safiyyah (sabeerah)

Masha Allah haka suka cigaba da kula da yaransu masu farin jini
Bayan wata uku da haihuwar safreena ihsan itama ta haifi ɗanta mai suna khalid
Bayan wata biyu madina itama ta ajiye ɗanta namiji mai suna suhail
Bayan madina ta haihu da wata biyu  again hayrat ta haifi  ƴarta mace mai suna falak
Haka suke zaman su cike da soyayya da amana da  annushuwa
*after 3years*

Zaune suke a garden yara nagani sai wasan su sukeyi amma banda yarinya daya wacce zata kai 4years
Momynta tace sabeerah ke bazakiyi wasan bane ?
Ya mutsa fuska tayi batare da tayi magana ba abbanta yace wlh sabeerah halinki ta ɗauko kin batamin yarinya dry safreena tayi tace lallai fa abban al'ameen nikam ba haka halina yake ba saidae halin abbanta tafaɗa tana miqewa tsaye
Falak tace anty sabeerah ya al'ameen kuzo muyi basketball zaitun
Tazo da gudu tace ƙanne na kuzo dadyna ya siya mana ice cream da gudu dukkansu suka bi zaitun khalifa yaja hannun safreena yace momyn twice zo muje kema na siya miki ice cream

Murmushi tayi tace bazan iya tafiya ba
Shima murmushin yayi ya duqa yace hau muje tana hawa tace wlh harna tuna *GUDU A JEJI*  dry yayi yace ke ba kyau tuno abinda ba alkhairi ba
a bedroom dinsa ya ajiye ta bisa gado yace haba su sabeerah suna bukatar ƙanne haka  hutun ya isa dry takeyi da haka ya haɗe bakin su waje daya
*****
Da haka nima maman ahlan nace bari na ajiye alqalamina anan
Acikin wannan littafi nawa *GUDU A JEJI* kuskuren danayi Allah ya yafemin abinda kuma na fada daidai Allah yabamu ikon amfani da ita
(Tammat bi hamdulillah )

Sai mun ana gaba


Post a Comment for "GUDU A JEJE COMPLETE "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...