CIKI DA GASKIA COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

CIKI DA GASKIA COMPLETE

CIKI DA GASKIA COMPLETE

- - Post a Comment

 CIKI DA GASKIA COMPLETE          *Sautin* kukane ketashi acikin gidan, wasuma harda kururuwa da ambaton sun shiga uku, wasu nafad'uwa k'asa ana kamosu, duk Wanda kagani acikin gidan kasan yana cikin matuk'ar tashin hankalin rasa wani abu muhimmi.

     

Nikaina dai kukan nasu yatada hankalina.


Nakoma dagacan gefen wata matashiyar budurwa dabazata wuce shekaru 13 ba aduniya, dukda k'arancin shekarunta sainaga Nisan hankalinta, domin kuwa ita kukan NATA yana fita cikin salamane, babu kururuwa balle  fad'uwa k'asa, kamar yanda sauran 'yan uwanta keyi.

      

Kafin na samu damar tanbayarta dalilin kukan nasu? naji ta furta *ALLAH sarki babanmu, ALLAH ya gafarta maka*, yau katafi kabarmu, ALLAH daya bamukai babu shawararmu, yau yakar6eka babu shawararmu, (ALLAH kenan, buwayi gagara misali), jiya iyanzu yana taredamu, yaukuma mun wayi gari and'aukesa.

   Takuma fashewa da kukanta mai tsuma rai, Wanda inba kusada ita kakeba, bazaka ta6ajin sautinsaba.


(Humm wannan rasuwa ta tadamin mikin nawa tabon Na rasa mahaifina, a ranar 1 ga watan Rajab, wata uku kenan😭, ALLAH yagafarta musu baki d'aya, ameen).


Wani dattijone datun d'azu suke shigi da fici daga wani d'aki zuwa tsakar gidan yace, "ya salam! Habadai Dan ALLAH, wannan kuka bashine zaidawo mana da Malam Abubakar duniyaba, amatsayinku Na musulmai wannan kururuwar da ihun bai kamacekuba, addu'a Malam yake buk'ata agareku amatsayinku Na iyalansa, kukanmu bazai dawo mana dashiba, amma hak'urinmu da nutsuwarmu zaisa murok'a masa gafarar UBANGIJIN Al'arshi.

  Dan ALLAH muyi hak'uri hakanan, ALLAH ya gafarta masa, yabamu hak'urin rashinsa.

     Tunda dattijo yafara magana gidan yay tsit, wannan nasiha tashi tayi tasirin saka kowa yin shiru, saidai shashshekar kukan wasu da ajiyar zuciya.

       Cikin 2hours aka gama had'a gawar marigayi Malam Abubakar, nagartaccen malami, masani akan ilimin addini, mai kishin musulinci da musulmai, mafad'in gsky komai d'acinta, mai hak'uri da kawaici, mai uzuri ga komai Na rayuwa da halayen bil-adam.

  ALLAH ya gafarta masa, Dan bak'aramin rashi akayiba kam yau, ALLAH yad'auki Malam Abubakar bayan gajeriyar jinyar dayasha ta kwana 18 kacal, wadda tazama sanadin ajalinsa, yabar duniya bayan sallar asubahi, mintuna 3 da idar da sallar da ALLAH yabashi ikon sallata, wadda tazama ibadarsa tak'arshe adoron k'asa.

   Yarasu akan abin sallarsa, dan ko gusawa baiyiba saida aka zare ransane d'ansa da k'anwarsa dake d'akin sukaga ya tuntsure kasa yaraf.

    To saimuce ALLAH ya gafarta masa, da dukkan 'yan uwa musulmai dasuka rigamu gidan gsky.


*_marayu inayinku wlhy🙋🏻‍♀, ALLAH yak'ara mana hak'uri😭_*


Bayan kammala had'ashi, aka kira matansa biyu Barirah & Fad'ima  domin yin bankwana, sunmasa addu'a da Neman gafararsa, sannan suka fito cikin kuka.

    Daga nan aka buk'aci ganin 'ya'yansa, wad'anda suka kasance adadin su 9. d'akin barirah uwar gida nada 6,  sai amarya Fad'ima nada 3.

    Suma sunma mahaifinsu addu'a da fatan alkairi, duk suka fito cikin kuka.

    Mintuna kamar 17 da haka aka fito da gawar Malam Abubakar zuwa gidansa na gsky, sosai sautin kuka yafara tashi, haka akafitadashi sunaji suna gani, basuda damar hanawa.😭*_mutuwa kenan, maimaida mata zawarawa, mai mayar da yaro maraya, mai yanke jin dad'in duniya, mai yanke abota da 'yan uwantaka._*😭

   Yakai bawa ka aikata alkairi kodan tsoron wannan ranar👈🏻, yau babana yarasu, gobe abokina, jibi matata, gata d'ana, wlhy watarana Kaine zaka tafi👈🏻😫.


An sallaci gawar Malam Abubakar a k'ofar gidansa, sannan yasamu rakkiyar d'umbin mutane zuwa makwancinsa.

        Zuwa yanzun kam gidan yagama cika da mutane, anata gaisuwa ga wad'anda abin ashafa.

     To dama akance idan kaje gidan mutuwa kakan shaida Wanda akaimawa, wannan maganar haka take, dankuwa zuwa k'arfe 2na rana wasu harsun fara sakewa, harma suna lodama cikinsu abinci, saidai ga 'ya'yansa bahaka bane, Dan kallo d'aya zaka musu ka tabbatar har sannan suna tartare da damuwa sosai.


Wannan kenan👌🏼.*7days ago*


Ayau akayi addu'ar bakwai d'in Malam Abubakar, bayan lafawar komai kuma shak'ik'ansa suka had'a taro Na family.

      Ba'a samu nutsuwar kowaba sai 1:43pm zuwa sannan mutane duksun baje, 'yan uwa Na nesa Dana kusa kowa Yakama gabansa, sai shak'ik'ai, irinsu k'annensa da yayunsa.

 

Dattijo m. Bilyamin shiya fara gabatar da sallama agaresu, yayi doguwar addu'a ga mamaci Malam Abubakar, harmada sauran al'ummar musulmi dasuka rigamu.

    Daga nan yaja dogon bayani akan gado da kuma biyama mamaci bashi da kar6o abinda yakebi, yaymusu nasiha da nusar dasu muhimmancin rik'e zuminci, da kuma addu'oi ga mahaifinsu, yanda zasu rik'e maraicinsu harya amfanesu.

     Ya tausasa murya tareda binsu da kallo d'aya bayan d'aya, ya ce, "kuyi hak'uri da abinda zan fad'a, musammanma iyayenku mata, nasan duk uwa tana buk'atar tarayune da 'ya'yanta, saidai k'addara tarabasu, badan ansoba, kamar dai yanda nake gani kuma yau zata nisantaku da naku, Dan hakan shine babban gata dazamuyi gareku, kuma shine abinda zamuyi mu kwatanta k'yaunarmu ga d'an uwanmu, bayan k'asa tarufe idonsa mukula da zuriar daya bari.

      Sosai naga tashin hankali a fuskar iyayensu dasu Kansu 'ya'yan.

     M Bilyamin yacigaba da fad'in, bazamu kwashe mukusu dukaba, amma ZAMU d'auke k'ananun cikinsu, saboda sunfi buk'atar kulawarmu.

     Kamar yanda kuka sani, Jafar da Murtala sun mallaki hankalinsu, kuma yakamata abarsu domin kula daku iyayensu mata, basukai k'arfin daza'a bar musu nauyin k'annensuba tukunna, dukda kuwa sunada shekaru 24&26 aduniya.

      Saikuma Fadeela &  Hafsat suma zasu k'arasa zamansu da iyayensu mata tunda aurensu saura wata 1 da sati 1.

       To amma Sadiya da Rufaida da Aysha zasu dawo hannuna,  Sadiq(Abba) zai koma wajen Asma'u,  Ummulkhairi zata koma wajen Ahmad, ALLAH yasa hakan danayi yayi daidai kuma zaku goyamin baya.

     Gaba d'aya suka amsa da gamsuwa.

   M bilyamin yaji dad'in hakan dasukai masa.


Kukan Gwaggo bintu ne yakatsesu, cikin kuka mai tsanani tace, "yaya bilya ni mizaisa awareni ak'i bani d'a ko d'aya acikin tsatson Yaya babba, shin har yanzu baku yarda da tubanaba kenan? Kuna k'yamata kamar kamar baya?, aganina nafi kowa buk'atar yarannan, kodan rashin haihuwa daban samuba, amma babu komai namuku uzuri. Tamik'e tana sharar kwallah dafad'in zan koma, ALLAH ya gafartama yaya babba...

    Harta fara tafiya Malam bilyamin ya tsayar da ita dafad'in bintu!.

   Cak tatsaya, tana cigaba da matse kwallah.

   Yace, " dawo ki zauna".

  Babu musu tadawo wajen zamanta.

     Cikin tausasa harshe yace, "kiyi hak'uri bintu, banhanaki d'aukar yaro kod'ayaba, saidai ina dubi da cewar bakina zaune bane a gidan mijinki, kema 

DOWNLOAD BOOK 1 HERE👈 

DOWNLOAD BOOK 2 HERE👈

Post a Comment for "CIKI DA GASKIA COMPLETE "

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...