BAZAN BARSHI BA COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BAZAN BARSHI BA COMPLETE

BAZAN BARSHI BA COMPLETE

- - Post a Comment

 BAZAN BARSHI BA COMPLETE
Rayyanat! Rayyanat!! Rayyanat!!!
  Er 16 yrs ce ta fito da gudu tana fad'in "Na'am Baffanah"
  Shiru baffan nata yayi yana mai kallon Rayyanat wacce ta kasance chocolate ba qiba ba rama tana da kyau daidai gwargwado tana sanye da riga da zane bara da bana sae dankwalin kanta da shima ba kalarkayan jikin ta bane ga zanen jikinta duk gabad'ayan sa dashi ne ba masoka tsintsinya gashi ta riqe wani gurin da ya yage bata son aga jikin ta yace"Rayyanat baki sami allura da zare bane wannan karon? Abba ban samu ba naje suka ce baza su ara min ba sun gaji da siya ina qare musu zaren"cikin muryar kuka ta qarasa maganar ,Baffan ta yace"kar kiyi kuka Rayyant inshaAllah yau idan mai gari ya biyani kud'in noman da nake masa zan saya miki allura da zare domin ki huta da aro maqota kinji"to Baffanah na gode  Allah yasa ayi nasara fiye da kullum"
yace "Amin Rayyant, zan tafi ki kula da kanki banda yawon maqota"inshaAllah amma Abba yau baka so na raka ne?Rayyanat ta yaya zaki fita bayan zanin ki ya yage ga samarin da ke dandali a tsakiyar gari"Haka ne Baffa Allah kiyaye hanya"Amin Amin.
   Daga haka ya fita  rataye da fartanya kan kafad'ar shi inda Rayyant tabi mahaifin nata da kallo wanda shima tufafin jikin sa  duk sun tsufa sun tamure.
   sae da ta daina hango shi sannan ta koma d'aki tayi zaune
tana qarewa d'an akurkin d'akin ta kallo   wanda ba wasu kayan kirki a ciki face d'an kunshin tufafin ta da baza su wuce kala biyu zuwa uku ba sae tsofuwar tabamar da take kwanciya da wani  pillow akai mai kama latsatstsen biredi sae gidan sauro da aka dunqule shi aka soka jikin taga sae wasu kwallaye guda biyu da ke cikin d'akin da bansan meye a cikin su ba. 
  Tana cikin qarewa d'akin kallo cikin ta ya shiga qugi sbd yunwar da ke addabar ta wacce tun safiyar jiya da suka ci abinci  ita da Baffan ta   har yau washe gari basu sake samun abinda suka ci ba.

 Kwanciya tayi ko zata samu bacci ya d'auke ta kafin Baffan ta ya dawo amma yunwa ta hana ta bacci kamar yanda tayi fama a daren jiya wanda sae da ta cika cikin ta da ruwa ta samu tayi bacci haka ko yanxu tashi tayi taje waje gurin randar ruwa ta cika cikin ta tap ta koma ta kwanta .
   Har bacci ya soma d'aukar ta ne taji sallamar wata qawar ta mai suna "Sarat" 

Sae da Rayyanat ta amsa mata sallama sannan ta shigo .
  Yarinya ce doguwa er sililiya baka wacce ita ma tana da kyaun ta dai dai gwargwado zama tayi tace"Rayyanat kiyi haquri fa tun jiya naso ace nazo amma shiryen shiryen tafiyar da muke yi na komawa Birni bai barni ba "
  D'an guntun murmushi Rayyanat tayi taji kamar ita ce zasu je Birni ita da Baffan ta sbd ta kasance tana mugun son zuwa Birni amma ko sau d'aya bata ta6a samun zuwa ba.

Sarat ta miqa mata wata er baqar leda wacce ake kira cefanen mutum d'aya tace"dan Allah kar ki ce baza ki kar6a ba  sbd nasan halin ki kuma ban saya miki don wata manufa ba sae don nasan kina bala'in son rogo inda har ka kasuwa naje na saya miki  amma kiyi haquri nasan ba kya son haka "
  ba komai Sarat a yau zan kar6i kyautar ki sbd zaki tafi ki barni ban kuma san yaushe zamu sake had'uwa ba nagode amma yaushe ne zakuyi tafiyar ?a yau d'in nan kuma a yanzu shiyasa na baki haquri kan rashin zuwa na tun jiya nima ban so haka ba wlh...kar ki damu domin nafi kowa sanin yanda kika damu dani shiyasa a kullum bani da wata qawar da ta fiki...Uhm na gode Rayyanat ni zan tafi su Abba na a bakin qofar gida da mota suna jiran fitowa ta .
  Nan Rayyanat ta tashi suka fito inda Rayyanat ta russuna  cikin ladabi ta gaida iyayen Sarat kafin wani  d'an matashin saurayi ya fito a cikin motar wanda sak Sarat ce da alama yayanta ne.
  Da sauri Rayyanat ta duqar da kanta qasa cikin jin kunya tana d'an kame kame gayen yayi murmushi yace"ako yaushe ina sonki Rayyanat ba kuma zan daina ba duk rintsi duk wuya ina tare da sonki a cikin zuciya ta koda kuwa bana raye.
DOWNLOAD HERE👈

Post a Comment for "BAZAN BARSHI BA COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...