BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 6 by sumayyah Abdulkadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 6 by sumayyah Abdulkadir

BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 6 by sumayyah Abdulkadir

- - Post a Comment

 BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 6 by sumayyah Abdulkadir


Yana tsaka da daukar lacca ya ji shigowar sako ta hanyar blackberry messenger cikin wayarsa, ya duba sai ya ga image ne ya shigo. 


Ya bude yana kallon photocopy dinsa cikin mamaki, wani kosashshe kuma lafiyayyen jariri kamar yayi kaki ya tofar, ya tabbatar ‘Aliko’ ya zo. Ya lumshe ido ya yi murmushi ya sumbaci hoton jaririn. Karfe shidda na asubahin washegari shine mutum na farko da ya doka musu kofa. 


Inna da ke lazimi bisa sallaya ta mike ta nufo kofar cike da mamakin wane ne zai zo musu a daidai wannan lokacin. Sai ta ga Zahraddeen rataye da falmaran din bakaken ‘suit’ da yake sanye dasu, a daya hannun kuma karamar jaka ce ta matafiya da jibgegiyar rigar sanyi wadda daga ganinta kasan daga cikin kankara ya fito. Kai kace wani haifaffen Afro-American ne. Wato irin bakaken fatar nan haifaffun Amurka wadanda iyayensu haifaffun can ne tun lokacin cinikin bayi. 


Wadannan bakaken sun fi turawa kyau, sun fisu daukar hankalin mata, ga tsayi ga zati, ga koshin lafiya ta ko’ina. Sannan ga hutu a jikinsu kamar basa taka burbushin kasa. 


Ta kama baki tana murmushi domin ba ta zace shi ba, don ko jiya da dare sunyi waya da shi bai ce da kowa zai zo ba. 


Ta bashi hanya ya wuce ciki ta rufe kofar, ta dube shi suka yi dariya irin ta Uwa da danta. Ya zube yana gaishe ta, ta wuce daki ta barshi tana cewa. “Kai! Yaran zamani da son ‘ya’ya sai a barku’”. Shi kam murmushi yake ya matsu ya ga kyautar 

da Allah Ya bashi. 


Tana shayar da Babyn ya murda kofar ya shiga, idanuwa shi fes a kansu. Abinda ya fara ce da ita shine; BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE...... takawarki lafiya matar Zahradjina ta girmamawa. 


Zumbura mishi baki tayi 


“ka ga Allah ka bari bana so!” 


Sai ya tafi da sassarfa yana dariya ya hada su ita da bebin ya rungume su. Tsayin minti goma Zahraddeen ya kasa sakin iyalinsa, idon sa kawai ya rufe yana sakin ajiyar zuciya akai-kai, yana yiwa Alhaji Aliko addu’a ne batareda ita din ta sani ba. Saida babyn ya soma motsin matsar da akai masa sannan ya sake su. 


Ya ce, 


“na bari, bazan kuma TUNA BAYA ba. To amma Takori tace TUNA BAYA SHINE ROKO. Shiyasa na tuna din. Anyway kin biya ni Marwahhh..... (rana ta farko daya kirayi sunanta deeeeeeply a tsayin rayuwarsu) irin wannan ‘bouncing baby’ haka? (Ya fadi hakan cikin kokarin shigar da kwayar idanunshi cikin nata). Har ban san da wace kalma zan nuna godiya ta ba”. Ya sake fada, yana kokarin su hada idanun amma ta ki. Ta mike zata fita, don ita kadai ta san me ta gano cikin kwayan idanunnan nashi, wadanda daga cikin su yake fara sauya tasha a salon soyayyarsa, amma sai ya riko hannunta don ya gane tafiyar zata yi, ba tareda ta juyo ba ya 

cigaba da Magana “Marwanatouh Allah Ya barmu tare cikin ALHERInsa, har zuwa ranar da muka daina numfashi”’. 


Ta daga mishi kai, yace “ban ji kin ce amin ba” Murmushi ta yi, ta juyo ahankali ta kwantar da kanta a kafafunsa. Jaririn na bisa cinyoyinsa. Ya zuba mishi ido kamar zai hadiye shi. Still hannunta cikin nashi bai cika ba. 


“Guduwa zaki yi ki barni ko Marwanatuh? Alhalin tsallake komai nayi, nazo don muyi celebrating farin cikin mu mu ukku? Dubi nan...” ya nuna mata babyn, “me ya fishi dadi a rayuwa? He’s a life-time companion 2 his Dad (Zahraddeeni), his pet, his friend and a Dad’s pride. In ban kare yinin yau da darensa da Uwarsa a gefe na ba, cikin sanyata farin-ciki, na wahalar dana bata wajen daukar cikinsa, rainon cikin sa da nakudar haifeshi...., celebration din will be incomplete, .....yet meaningless........ !!! 


Ya fadi cikin murmushi, cikin wata irin murya mai taushi dake nuna yana yin maganar ne tun daga karkashin zuciyarsa. 


‘“Wata ukku, ban gan ki ba, ban ji dumin jikin ki ba ‘apple of my eyes....(the one I lobe most) ” ya fadi yana kokaerin dago habarta dake sunkuye, “ga Da na yau a hannu na jikan Alh. Aliko, wanda zan dora a kujerar Aliko....., in gaya masa kowanene Aliko....., in sa masa suna Aliko...., inyi ta addu’a ya debo halayen Aliko.... If u did not join me in my celebration you might not run away from me....... Banda Allah wa zai maka wannan kyauta? Farin cikin dana ke ciki a yau 

Marwanatoubhh, ban taba tsintar kaina acikin irinsa a tarihin rayuwata ba..... so plz join me.....!!!’. Ya fada kasa-kasa, tareda aje Dan a gefe, ya mikar da ita tsaye ya rungume sosai, kamar ya maida ita cikin jikinsa su zama mutum daya, ya soma ‘kissing deeply’ irin yadda bai taba yi ba. 


Cike take da kunyar iya shegen da ta rinka yi masa a baya, shine abinda ya sa ta kasa kallon idanun sa, yau ga dan sa ya fito daga jikinta tana shayarwa daga jikinta, domin cikin fadin duniyar nan a halin yanzu ba abinda take so sama da mijinta, da rabon da Allah Ya basu. 


Shiyasa aka ce in zaka yi kiyayya ka yi ta saisasaisa, haka in zakayi soyayya itama kayi ta tsakatsaki, don baka san me gobe zata haifar ba. 


Ta tabbata Daddy gata ya yi mata, ta yarda ta amince da hakan yanzu, hakan da Aunty Shahidah tayi ta gayamata, amma ta ki sauraronta da gangan, da ina za ta samo miji irin Zahraddeen a wannan zamanin? 


Babu shaye-shaye, babu neman mata, mai amana da gaskiya, wanda ke motsi cikin biliyoyin kudi, amma babu kobo da ya taba bata cikin lissafinsu, har ya samu ya maida ‘Dan Kasa Holdings’ abinda ta zama a yau. 


Ya koma gefe matsayin babban director mai bada shawara cikin hikima da baiwar da Allah Ya bashi wajen iya juya kobo ta koma dari. Bayan ya cika kamfanonin Dan-Kasa da hazikan ma’aikata 

ma’ abota zuzzurfan ilmi da suka san abinda suke yi. Jarumi kuma haziki a fannin komai, sadauki a fannin soyayyah. 


Hakan bai hana shi daukar nauyin ci da shansu da sutura da Allah Ya dora masa ba, kuma miji mafi kusanci wanda baya la’akari da abinda take dashi wajen sauke hakkokin ta da ke kansa, sai tunanin abinda shi zai bata. A kullum tunaninsa ya kare ne a abinda zai mata ya sata farin ciki ya kara inganta rayuwarsu, tunda itama bata rageshi da komai ba, kokarinta kullum a inganta aurenta ne da kokarin ganin ta dauke hankalin Zahraddeen daga sauran matan da ke farautarsa kamar su fyade shi, duk da dan-adam tara yake bai cika goma ba. Wanda baya waiwaye cikin abinda ta mallaka cikin rayuwar aurensu. Bata da abin da za ta ce da mahaifinta day a zaba mata Zahraddeen a matsayin miji sai fatan Allah Ya haskaka kabarin sa, ya yi masa rahma da gafara. 


2K KK 


Aliyu, da suke kira Daddy yana da shekara biyu Zahraddeen ya kammala PhD dinsa, ya dawo gida Najeriya cike da dimbin nasara, ya koma ofis aka cigaba da gudanar da komai cikin nasara da karin ilmi mai tafiya da zamani. . 


Don haka duk suka tattara suka koma birnin Tarayyah inda ‘main-branch’ na DAN-KASA HOLDINGS’ ya koma. Sai Dr. Safah ce ke kula da asibitinsu, kullum she is busy... don asibitin ya samu karbuwa yadda ba a zato, har daga sauran jihohi ana kawo patient masu fama da matsalolin 

hakori, dadashi da makogwaro daban-daban. Cikin dan lokaci kankani DAN KASA DENTAL HOSPITAL ya soma gogawa da sauran manyan Pribate asibitocin hakori na garin na Gwamna. Musamman da aka ji cewa na ‘ya’yan Dan Kasa ne. 


Don haka Dr. Safah ta zamo ba ta da lokacin kanta, wannan ya kawar da hankalinta daga halin damuwar da take ciki na rashin yin aure, wanda daga ita sai Ubangijinta suka sani. 


Tun Mami da Hajiya Maama na fada da kumfar baki a kan ta fito da miji ta yi aure, don sun gaji da wannan gantalin asibitin har sun gaji sun zuba mata ido, don a duk lokacin da suka ta da zancen aure kuka kawai take sanya musu. 


Almustapha Zubair Dan Kasa kadai zuciyarta ke yimawa kwakwa, take nema ruwa a jallo. Duk da tasan ko Allah Ya nufa ta kara ganinsa ko ya dawo don kansa, babu maganar aure a tsakanin su sai ta ‘yan uwantaka kamar yadda zuciyar ta mai kimsa mata komai ta zaba. Kaico da aikin zuciya musamman idan ka bata linzami da ragamar kanta. Ya tafi da duk wata soyayyar da Allah Ya halitta a zuciyarta, bai bar ko sako daya da take jin za ta iya jogana soyayyar wani da namiji a duniya a zuciyarta ba. Tun daga lokacin da zuciyartata da kuruciyarta suka hadu suka janyo mata asarar wannan BABBAN GORON da Allah Ya bata, in ba shi ba kowanne GORO karami ne a 


idonta, daci da bauri yake a bakinta. ok RK 

Yau litinin babbar rana. Dr. Safah ce ke kokarin daura lab-coat cikin hanzari a kan shudiyar atamfa (super) mai hasken sararin samaniya dake jikinta, dinkin riga da babban sikit wanda ya bude sosai daga gwiwarta zuwa kasa, dinkin rigar kuma dan karami ne daidai jikinta ya bi surar jikin ta ya kwanta, , ta kawo farin gilashinta ta dora ta nade kanta da siririn shudin mayafi (pashmina). 


Ta bude bed-side fridge dinta ta dauko gorar fresh milk mara sanyi ta bincire hancin ta kafa kai tana sha, sai da ta koshi sannan ta jawo kofar dakinta ta rufe rungume da jakarta, da alama cikin sauri take. 


Ta leka dakin Mami ba ta ciki, ta nufo kicin inda take jin motsin kwanuka, nan ta cimma Mami tana suyar chips da plantain (agada). 


Daga bakin kofa ta dakata, “Mami ni zan wuce....” 


Mami ta juyo ta kalle ta, sai ‘yar tata ta bata sha’awa, ta zama cikakkiyar matashiya ‘yar kimanin shekaru (27) da haihuwa, amma sai ka rantse da Allah shekarun ta goma sha bakwai. 


Ta yi mata murmushi ta ce, “Haka za ki fita baki ci komai ba Safah? Kin fi kowa sanin illar rashin cin abinci a kan lokaci, amma kin fi kowa sakaci da cin abincin. 


Shi yasa gaki nan kullum kamar a hureki ki fadi. Ungo wannan maza cinye ki bani farantin”. 


Ta narke fuska kamar karamar yarinya, “Allah Mami na yi break fast da fresh milk, in ba so kike na yi amai ba, to ki barni”’. 

Mami ta maida plate gefe ta ajiye, “Na barki, cikin ki ko nawa?” 


Ta yi murmushi, tana karanto damuwar Mamin akan rashin cin abincin nata cikin kwayar idon Mamin, amma kawaici da fulatanci ya danne komai, ta ce “To na tafi asibiti Mami, baki yi min addu’a ba”. 


“Allah Ya bada sa’a, a dinga aikin da kula. Zancen da bakya so kuma dole in yi miki, duk wannan gantalin da kike duk da cewa aikin lada ne, to ladan aure YA FISHI’. 


Ta zumbura baki ba tare da ta ce komai ba, ta juya ta fice, a ranta tana cewa, “Wa zan aura ne Mami? Duk masu so na masu iyali ne. Tukunna ma Mami har yau ban fidda rai da cewa WATARANA zai dawo ya maida ni ba, zai yi min uzri cikin kowanne hali’”’. 


Shigarta ‘office’ ke da wuya aka shigo mata da ‘file-file’ na marasa lafiya da za ta duba a safiyar yau. Haka nan ta samu kanta da kallon sunan mutum na biyu da za ta duba, domin suna ne ba boyayye ba. 


“NASEER ABDULKARIM (LAMIDO)’. Ta maimaita ta sake maimaitawa cikin zuciyarta. 


In bata yi kuskure ba, Nasir Abdulkarim shi ke rike da matsayin kujerar shugaban EFCC a halin yanzu, wanda ko baka san shi a rediyo ba, to za ka san kyakkyawar bafulatanar fuskarshi a talabijin, jaridu da mujallu, saboda matukar kwarewarsa wajen tsamo masu handame mana dukiyoyi da albarkatun kasarmu mai dimbin albarka. Idan har kana duba manyan journals da news-pa

pers na gida Nigeria, akan duk wani abu da ya shafi tagomashin tattalin § arziki, ayyukan ECOWAS, International Monetary Fund (IMF), Bureau of Public Enterprises (BPE) FMBN, NCP, NEPZA (Nigeria Edport Processing Zones), CAC (Corporate Affairs Commission), NEPC, NEDIM BANK, (Federal Mortgage Bank), dole kasan waye Naseer Lamido? 


Ta duba patient ta farko mai fama da ciwon dadashi, ta sallame ta da takardar magunguna da za ta Saya. 


A lokacin da ya sawo kai cikin ofishin, sai ta samu kanta da faduwar gaba mai tsanani, ta yi hanzarin canza gilashin idonta da PRADA mai duhu, ta cire mai hasken. 


Gaba daya ofishin ya karbi wani sassanyan kamshi, ashe tare yake da iyalinsa, mace da karamin yaro da bai fi shekaru hudu ba. Kyakkyawar mace karshen gaye rike da hannunsa, shi kuma yana dauke da yaron a kafadun shi. Juyawar nan da zai yi daga rufe kofar da ya yi, idanunshi farare kal suka karbi wani chemistry mai tsirgawa har cikin kwakwalwa. 


Ga ita likitan, ji ta yi ilahirin jikinta ya mutu, yana rawa cikin daburcewa, ba kyawun shi ne ya razanata ba, sai tsabar kamala, kwarjini da cikar zati. Rana ta farko da za ta iya kwatanta ALMUSTAPHA ZUBAIR DAN KASA da wani da namiji cikin zuciyarta a duniya. 


Har suka zauna a kujerun dake fuskantar ta bata koma cikin nutsuwar ta ba, inda ta gode Allah da 

dabararta na sanya ‘dark spaces’, da watakila sun fahimci dimaucewar ta da bayyanar Naseer Abdulkarim yau a gabanta, tare da wani boyayyen sirri da ya ratsa kowacce jijiya da kowacce gaba ta jikinta. 


Ta kirayi sunan Allah AL-LADIF domin neman nutsuwa cikin zuciya da gangar jikinta dake rawa. Cikin ikon Allah nutsuwa ta zo mata. 


Ta gyara gilashin idonta, a yayin da shi kuma ya zare na shi gaba daya yadda zai ji dadin kallon duk wani motion dinta sosai, yarinya kamar aljana, gaki baka amma tamkar ba’indiya, irin bakaken Indiyoyin Punjabi, ‘yar mitsila dake, amma cikakkiyar likitar hakori, ko su waye iyayenki sun kyauta, I’m edteremely impressed! Abinda yake fadi kenan cikin ransa, wannan kallon da yake ma likitar, kallo ne na sosai, nan da nan hakan yasa matarshi ta tsargu. 


Ga alama irin masu azababben kishin nan ce. Domin fizge danta ta yi daga hannunsa ganin yana neman kwala shi da kasa, ta wuce fuuu.... kamar guguwa ta bugo kofar da karfi. 


Da hanzari suka bita da kallo daga shi mara lafiyan, da malamar kiwon lafiyan. 


A tare kuma suka janye idanunsu daga kofar. Dr. Safah ta koma cikin nutsuwarta, ta kara gyara zaman gilashin idonta, ta bude ‘file’ din dake gabanta, cikin harshen Turanci ta ke tambayarsa abinda yake damun sa. 


Da nashi hardadden harshen wanda fulatanci da Ingilishi ya sarke yake mata bayani cewa, “Hakoranshi biyu na karshe basa barin shi ya yi barci 

saboda azaba”’. 


Ta mike daga mazauninta ta dawo gabanshi, ta dauki ‘yar cocilan ta sa shi ya bude bakin ta kama habarsa ta haska, ta lelleka ta koma kujerarta ta zauna. 


Sannan ta daga bakin gilashin zuwa goshinta, ta ce, “Za a cire daya, za a yiwa daya ciko, sannan za a yi flushing, da alama kana shan zaki da yawa....” 


Yadda ta yi maganar, cikin jarumta ne, da nuna halin ko’in kula, amma ilahirin jikinta rawa yake yi. Shi kuma kirjinshi ne yake bugawa babu sassauci. Saidai nutsuwar da yake da ita ta danne komi. 


Idanuwan nan farare kal na ‘patient’ din nata sun juye sun rikide zuwa lub colour, ta kan ga irin wannan kallon cikin kwayar idon Imam, ya kasa dauke idonshi a kanta, wanda hakan ya kara kidimata. 


Bata taba yarda da abinda ake kira lub at first sight ba sai yau. Wato da ya faru akanta. Ta yi maza ta maida bakin gilashinta ta ce, “Ina magana...” 


Ya yi wani irin murmushi, ya nitsa yatsunshi cikin sumar kanshi “Ina jin ki ai”. 


“To ya za’ayi?” 


“Ki yi duk abinda ya kamata”. 


“Ka shirya?” 


Bai amsa ba, daga mata kai ya yi. 


Ta mike ta dawo gaban shi, dole ta zare bakin gilashin, har zuwa wannan lokacin kallon ta kawai yake makale da murmushi a tattausar fatar bakin 

sa, ta cigaba da bayani 


“Za a cire na cirewar yanzu, na cikon da flushing sai a dawo gobe, because you could not endure the two injections concurrently (saboda ba za ka iya jure allurar dadashi guda biyu a lokaci daya ba)” 


Ya langabar da kai idanunshi a lumshe, “ni na gaya miki? Doctor, ki yi duk abinda ya dace, ina da uzri ba zan iya dawowa gobe ba, yanzu haka a kan hanya nake, Abuja zamu, ciwo ya ishe ni na ci karo da asibitin ku, nikadai nasan azabar da nake sha da hakoran nan, bazan iya isa Abuja dasu basu sumar da ni ba, shine na yanke hanya na shigo”. 


Ta gyada kai, “Babu laifi, in yi allurar za ka jure?” 


Murmushi ya yi, “Me ake da ‘yan mazan?” 


Itama ta murmusa. Ta mika hannu a hankali ta kama habarsa inda wani lallausan gashi mai santsi na fulanin usli ya kwanta tubus a kan fuskarsa. 


Ta jawo kayan aiki, idanunshi ya rufe, ta tsira mishi allurar dadashi ko motsi bai yi ba. Duk da azabar allurar. Nan da nan ta ballo hakorin, ta danne jinin dake fita da auduga, amma kamar ba jikinsa ake bantara ba, hakan ya faru ne a dalilin cewa, ya fada cikin wata rindimemiyar soyayya marar misali. 


Har ta kara yin wata allurar, ta yi ciko ta fara flushing bai bude idon shi ba. Sai da ta gama tsaf ta ce da shi, “Na gama”. 


Sannu a hankali ya bude idanunshi a kanta, ya kai 

hannu daman shi ya dafe kansa. Ya ce, “Akwai wani ciwon Doctor...” 


Ta dago da hanzari ta dubeshi, , “Name kuma?” Ya yi kasa da murya “Ciwon L ne!” 


Dariya ta kama ta, saboda yadda ya yi maganar kamar karamin yaro. Ba ta yi aune ba sai ji ta yi ya cire gilashinta, 


“Dubi kwayar idona Doctor, wallahi ciwon ‘L’ ne”. 


Murmushi ta yi, 


“To Allah Ya yi maka magani, don dai mu nan, bamu da maganin wata cuta mai wannan sunan, baya ga hakori, throaght da dadashi, watakila sai 


dai ko a kasashen da suka ci gaba, in kai sa’a sai 


Ya girgiza kai cikin dariya “Alright! Shawararki abar dubawa ce”. Ya dauki kan wayarta dake nan kan tebirinta, kan ta ce komai ya zuba lambobinshi a ciki ya kira, sannan ya yi sabing ya mike, ya rankwafa daidai kanta har suna iya jin hucin numfashin juna. 


Cikin sassanyar murya ya ce, “NASIR is in lub.....pld Doctor sabe a soul...”. Ya juya cikin kuzari da sassarfarshi ya fice daga ofishin. 


Binsa ta yi da kallo tana murmushi har ya fice daga ofishin, wannan shine Da namiji na uku da ta ji shi har cikin zuciyarta. A yau kuma take addu’ar Allah Ya sa kada shima ya kubuce mata, kamar yadda ta rasa Imam da Zahraddeeni. Bayan ta dandani wahalalliyar soyayyarsu mai wuyar fita daga inda tayiwa kanta muhalli cikin 

zuciyar da ke cikin kirjin ta. 


Har zuwa lokacin kamshin sa bai bar ofishinta ba, ta sauke idonta a hankali a kan tulin ‘files’ din dake gabanta wanda take tantamar anya za ta iya ci gaba da duba su? Ba ta da wannan kuzarin. 


Sai ta tattarasu ta ture gefe, ta dau wayarta ta kira Dr. Garba Bilal ta ce ya zo don Allah ya taimaka mata za ta wuce gida ba ta jin dadi. 


Ta tattara ‘yan komatsanta ta jefa a jaka, ta fice ko gabanta ba ta gani sosai. 


Mami sai ganinta ta yi ta dawo da wuri, ta ce, “Yana ganki yanzu?” 


Ta yamutsa fuska “Bana jin dadi ne sosai Mami”. Ta ce, “To ki sha magani ki kwanta ki huta, duk ke kika ga za ki iya ai, wannan aikin wahalar da har cikin dare baka tsira ba”. 


Ta murmusa ta wuce dakinta ba ta ce komai ba. A ranta ta ce, “Allah na tuba in ban yi aiki ba me zan yi? Imam ya tafi ya barni, bai yi min uzri da kuruciyata ba, bai kara waiwayoni ba, wanda ke nufin ya daina so na...!”” 


Ta yi juyi a lallausan gadonta, kwalla ta cika idanunta. Tabbas duk wanda bai yi biyayya ga iyayensa ba, yana tare da nadama...... yau shekarunta ashirin da bakwai babu aure...... ko sai yaushe? Ko Imam zai dawo? Ko zata samu ya yafe mata? Ko zata samu ya maida ita ta goge kuskuren ta na baya? Ko wani auren zata yi? Ta ma manta cewa Imam, ya haramta gareta kwatakwata. A yanzu kam ta tabbatar Soyayya aikin banzace, domin abuce mai gushewa, zata iya gushewa a kowanne lokaci kamar ba’a yi ta ba, 

ba kamar KAUNA ba. 


Musamman idan zuciyar da gangar jikin suka samu abinda sukeso, amma banda albarkar iyaye. Ga dai Marwah can da ta yi biyayyar mukus da ita a dakin mijinta, da ba soyayyar ce ta hadasu ba, har sun fara tara zurri’a, ina soyayyar da Zahraddeen ke mata? Da ya kunshe matarshi a daki ya manta da ita? Yake bata ‘ya’ ya daga jikin sa da yayi mata alkawarin nata ne ita kadai? Meye ribarta cikin soyayyah da jayayya da iyaye akan soyayya? 


Wata zuciyar tace da ita “Baki ga komai ba, yanzu zaki fara rayuwa Safah! Rayuwar aure ba??? Ga diya mace ba abu ce mai sauki ba, ba abinda ya kaita samun kalubale, musamman wadda ba’a ginata tun farko da albarka da biyayyar mahaifi ba. Don shi Allah Ya baiwa damar zabarwa diyarsa budurwa mijin aure. 


Mu sauke numfashi, mu bi Dr Safah Dan kasa cikin rayuwar auren ta, musamman da muka leka muka hango kamar ta samo wani BABBAN GORON, ko zata tauna? Ta ji shikuma yaya yake? Ko kuma tsohon GORON ata cigaba da yiwa jiran tsammanin warabbuka? Mu bi ta a hankali. ok oe OK Ta bude dakinta ta shiga ta kwanta a gadonta na alfarma. Daga kwancen da take ta mika hannu ta dauki remote din A.C a kan side drower ta karo karfin iyakwandishin din, sannan ta lumshe ido ta 

fada duniyar tunani kala-kala. 


Wayarta dake gefe ta yi kabbara, cikin melody mai dadi, wannan shine tune din wayarta. 


Ta mika hannu ta dauka ta duba, bakuwar lamba ce ta kamfanin Glo, ba ta san lambar ba, kuma a ka’idarta ba ta daukar wayar da ba ta san ko ta waye ba. 


Sai da wayar ta ci kukanta ta koshi Safah ba ta ko kara bin ta kanta ba. Ta yi zurfi a tunanin abin da ya kamata ta yi wa rayuwarta tunda sauran kuruciyarta. 


Duniya gaba take kara yi kullum ba baya take yi ba, duk wani burin rayuwa da dan Adam ke nema babu wanda Allah bai bata ba. 


Me ya rage mata a rayuwar duniyar nan banda AURE? Da Imam zai dawo tsayin wadannan shekarun ya isa ace ya dawo kowanne irin fushi ya yi da ita kuwa. 


Idan ita ta yi masa laifi me Mami da Daddy suka yi masa da zai nisancesu har tsayin wannan lokacin? 


Gara ta yiwa kanta fada ta hakura da Imam ta kama daya cikin dimbin masoyanta ta yi aure, ta ginawa kanta rayuwa irin ta kowacce diya mace, wato rayuwar iyali mai albarka. 


Hakan ba yana nufin cewa ta daina son Imam bane, amma gara ta wankewa Mami da Hajiya Maama zuciya haka ta yi aure, ko ba dan komai ba sai don cikar mutunci da kimarta, da kuma farin cikin mahaifiyarta da kakarta. 


Zuwa wannan lokacin wayarta ta yi ruri har ba adadi, sai kuma ta jiyo alamar shigowar sako Post a Comment for "BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 6 by sumayyah Abdulkadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...