BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 3 by sumayyah Abdulkadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 3 by sumayyah Abdulkadir

BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 3 by sumayyah Abdulkadir

- - 1 comment

 BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 3 by sumayyah Abdulkadirkudi masu yawa, ta karba ta yi godiya ta fito. 


Safah na tuki a kan titin da zai kaita Zaria daga Kaduna, cikin kankanuwar motarnan kia-optima, wadda Zahradden ne ya zabar musu ita. Ba yadda Mami bata yi da Daddy a kan direba ya kaita, amma ya ce shi ya daina sangarta ‘ya’ ya, motar ma daya barta ta dauka zai tura a dawo masa da ita. Ta shiga Adaidaita sahu ya daidaita mata sahu. 


Yanzu zata san yaya dalibai suke neman ilmi a jami’a, a tsaye ba’a kwance ba irin wanda suka samu, ta shiga cikin hostel ta zauna tayi rayuwa daidai da dan kowa, a kyale ta ta fara koyon darasin rayuwa. Domin batasan Annabi ya faku ba”. 


Gudu take sosai hawaye na sauka a kan kuncinta. Ta kan kalli gefenta mazaunin Marwah ne. Da tana cikin motar da yanzu ta kunna c.d na wakar India kabhi khushi kabhie gham, tana bin wakar tana rawa da daga inda take zaune. Allah sarki! Tuna Baya Shine Roko. 


Wai yanzu ita da Marwah suna duniya daya, amma muhalli daban-daban saidai a ga juna da shauki lokaci-zuwa lokaci. Wani irin nutsatstsen al’amari game da IMAM na sauka a zuciyarta, wani irin ni’imtaccen feeling ne da ba za ta iya fassarawa ba. 


Allah ne kadai ya kawo ta Zaria lafiya, cikin kiyayewarsa da alfarmarsa, amma fa ta sha zagi daga motocin gabanta da bayan ta. 


Ba ta sha wahalar samun daki a hostel ba da 

taimakon wata ‘yar ajinsu Jamila Sarki. Su biyu ne a dakin ita da Jamila. 


Ita Jamila ‘yar Kano ce, tana da aure amma ba ta haihu ba. Mijinta Mus’abu ma’aikacin M.T.N ne yana reshen Bauchi, ita kuma take karatu a nan Zaria. 


Duk gayun Jamila sai ta ke raina kanta a duk lokacin da ta daga ido ta dubi Safah Dan-Kasa, ita ba ‘yar gayun bace (ba mai sa kyale-kyale ba), non-transparent (ba mai daukar ido ba), asali ma sai ka kura ido sosai sannan zakaga kyawun bakar fatar data mallaka da nata salon gayun na halitta, komai nata natural babu kari da na kanti ko daya, daga fata, gashi, kyawun sura duka Safah ta mallake su amma in an extraordinary manner. 


Haka kawai Safah take burge Jamila, gata yarinya danya sharaf, don Jamila ta girme ta da wajen shekaru biyar. Sannan gata kwaruwa a fannin karatu, sam ba ta wasa oberall ce, abinda ya kawota kawai ta sanya a gaba. 


Sai dai a dan zaman da suka yi na tsayin lokaci Jamila ta fahimci Safah Dan Kasa na cikin matsananciyar damuwa da ba ta san ko ta mece ce ba. 


Tana so ta tambayi Safah abinda ke damun ta take yawan zama shiru silent sannan isolated, wato ta kebance kanta daga son shiga jama’a. 


Ta rufe wayoyinta gaba daya ba ta amsa wayar kowa. Tun fil azal kuma dama bata cikin kowanne ‘social network’. Wayar ma data dan rike na dan lokaci soyayyace ta rinjayeta, ita 

kuma tayi biyayya a gareta. To tunda ta zama tarihi suma wayoyin su zama tarihi kawai. Sai dai kuma Jamila ba ta so ta zamo mai shisshigi cikin abinda bai shafe ta ba. 


Don haka ta kawo ido ta zuba mata, cikin zuciyarta tana taya ta da addu’ar Allah Ya yaye mata duk irin matsalar da take ciki, sabida ita tsakanin ta da Allah take kaunar Safahn, ga Safahn kuma bata damu da kowa ba sai abinda ya kaita. 


Saidai duk wani hakkin Jamilah dake kanta na makwabci mafi kusanci tana saukeshi. Lokacin a zauna ayi hira ne ko jin tarihin juna da ire-iren hakan bata dashi. 


A zahiri damuwar itace, Safah ta fada wani hali na soyayya wanda ita kanta ba ta san cewa soyayyar ce ke dawainiya da zuciyarta ba, soyayyar tsohon mijinta dan uwanta Imam, wanda a halin yanzu ba ta san a halin da yake ciki ba, ba ta san inda yake ba. Yana raye ko baya raye? Wani zubin kwana take tana kukan nadama ba tare da sanin Jamila ba. Tana ganin ta gama kashewa kanta rayuwa tunda ta rasa shi. Soyayyarshi a zuciyarta a kullum kara karuwa take, kamar ana iza wuta. Kamar azal. A lokacin da ya riga ya zama haramiyar ta. Tunda daman babu iddarshi a kanta, kuma tuni lokaci ya mika. Kuka take sosai a duk ranar da ta tuno rabuwarsu ta karshe...... “Na tabbata dan halak, ba shege bane ko....?” 


Sautin da ke ta yi mata kuwwa a kunne kenan, a duk lokacin da ta zauna ita kadai, wanda ke kara 

ruruta wutar nadamar ta. Ita da bakinta tace da Imam idan shi dan halak ne cikin UWA da UBA ....to0 ya saketa....gashi ya sake tan kamar yadda ta bukata, to amma sakin ya zamar mata jafa’i....da dai wannan halin da ta tsinci zuciyarta da ruhinta a ciki na bege.... da so da kaunar ma gabadaya...... Harshe? 


Ya Allah ka bamu linzamin shi a hannun mu, yana kaimu wuta, yana kaimu sa’ira, yana kuma kai mu Aljannah. Again, yana lalata mana rayuwa, mu dinga rikeshi ta hanyar tauna Magana kafin mu fade ta. Idan ya furta baya taba mayarda ita komai dadinta ko dacinta. 


Harshe (da Hausa), tongue (da turanci), Lisan (da larabci). Wata tsoka ce mai amfani daban-daban da Allah Ya halitta a cikin bakinmu, wadda in muka iya controlling dinta, zamu iya controlling dukkannin al’amuran rayuwar mu.Ta kan ce, 


“Ina ma ana maida hannun agogo baya?” 


Me za ta yi ta yi repenting kuskuren da ta tafka a baya? Babu! Imam, foreber and eber (har Abadan) ya zama haramiyar ta. Ko da ace watarana ya dawo daga inda ya shiga. Domin dai ita kyakkyawan zaton yana lafiya take masa ba kamar Mami ba, kawai dai yayi hijira ne don ya raba duniyarsa da tata. Ta tabbatar ba za ta kara samun soyayyar sa ba. Bazata kara samun damar da ta samu har tsayin shekaru ashirin ba. Kenan ya zama dole ta yi hakuri, ta fuskanci rayuwarta ta gaba, ta baiwa mazan dake rububin ta damar fitowa, mafi yawa 

daga ciki farfesoshinsu da manyan Dactocinsu, wadanda yawanci hazakarta ce take sayo mata soyayyar, kamewa da kamalarta, ba kamar sauran dalibai ‘yan uwanta ba, da yake a dan tsukin aka tura su TH, wato ‘teaching hospital’ suna koyar ayyuka a aikace, gara tayi maneji da dayansu duk da dukkannin su masu iyali ne. 


To amma wa zata zaba wanda zai maye gurbin Imam a zuciyarta? Wa za ta samu ya so ta kamar yadda Imam ya so ta? Yaya za ta yi da dimbin soyayyar shi da a yanzu take dawainiya da zuciyarta??? 


2k ana kicin tana gashin pizzawarma da french bread da take so za ta yi kalaci da shi, ta jiyo sallamar Rabi’a a bakin kofar shigowa sassanta. 


Ta yi tsaki tsuww! Tana kunkuni, “Yaushe wadannan mutanen za su daina shiga sabgata ne? In abinci ne na ce bana cin jagwalgwalo a kyale ni mana?”. 


A fusace ta fito ta bude kofar, Rabi’a ce dauke da 

daga ciki farfesoshinsu da manyan Dactocinsu, wadanda yawanci hazakarta ce take sayo mata soyayyar, kamewa da kamalarta, ba kamar sauran dalibai ‘yan uwanta ba, da yake a dan tsukin aka tura su TH, wato ‘teaching hospital’ suna koyar ayyuka a aikace, gara tayi maneji da dayansu duk da dukkannin su masu iyali ne. 


To amma wa zata zaba wanda zai maye gurbin Imam a zuciyarta? Wa za ta samu ya so ta kamar yadda Imam ya so ta? Yaya za ta yi da dimbin soyayyar shi da a yanzu take dawainiya da zuciyarta??? 


2k ana kicin tana gashin pizzawarma da french bread da take so za ta yi kalaci da shi, ta jiyo sallamar Rabi’a a bakin kofar shigowa sassanta. 


Ta yi tsaki tsuww! Tana kunkuni, “Yaushe wadannan mutanen za su daina shiga sabgata ne? In abinci ne na ce bana cin jagwalgwalo a kyale ni mana?”. 


A fusace ta fito ta bude kofar, Rabi’a ce dauke da 

daga ciki farfesoshinsu da manyan Dactocinsu, wadanda yawanci hazakarta ce take sayo mata soyayyar, kamewa da kamalarta, ba kamar sauran dalibai ‘yan uwanta ba, da yake a dan tsukin aka tura su TH, wato ‘teaching hospital’ suna koyar ayyuka a aikace, gara tayi maneji da dayansu duk da dukkannin su masu iyali ne. 


To amma wa zata zaba wanda zai maye gurbin Imam a zuciyarta? Wa za ta samu ya so ta kamar yadda Imam ya so ta? Yaya za ta yi da dimbin soyayyar shi da a yanzu take dawainiya da zuciyarta??? 


2k ana kicin tana gashin pizzawarma da french bread da take so za ta yi kalaci da shi, ta jiyo sallamar Rabi’a a bakin kofar shigowa sassanta. 


Ta yi tsaki tsuww! Tana kunkuni, “Yaushe wadannan mutanen za su daina shiga sabgata ne? In abinci ne na ce bana cin jagwalgwalo a kyale ni mana?”. 


A fusace ta fito ta bude kofar, Rabi’a ce dauke da 

daga ciki farfesoshinsu da manyan Dactocinsu, wadanda yawanci hazakarta ce take sayo mata soyayyar, kamewa da kamalarta, ba kamar sauran dalibai ‘yan uwanta ba, da yake a dan tsukin aka tura su TH, wato ‘teaching hospital’ suna koyar ayyuka a aikace, gara tayi maneji da dayansu duk da dukkannin su masu iyali ne. 


To amma wa zata zaba wanda zai maye gurbin Imam a zuciyarta? Wa za ta samu ya so ta kamar yadda Imam ya so ta? Yaya za ta yi da dimbin soyayyar shi da a yanzu take dawainiya da zuciyarta??? 


2k ana kicin tana gashin pizzawarma da french bread da take so za ta yi kalaci da shi, ta jiyo sallamar Rabi’a a bakin kofar shigowa sassanta. 


Ta yi tsaki tsuww! Tana kunkuni, “Yaushe wadannan mutanen za su daina shiga sabgata ne? In abinci ne na ce bana cin jagwalgwalo a kyale ni mana?”. 


A fusace ta fito ta bude kofar, Rabi’a ce dauke da 

dawo dasu ta tura masa, yana cin funkason alkama da miyar alayyahun data ji kaji zukuzuku suna hira. 


Cikin hirar yake tambayar Inna 


“Wai Inna ina wannan Yayar taki ta rugar Ardo Lamido?’ 


Ta ce, “Yaya Badijo? Tana nan lafiya, sai dai fushi take dani don na kwan biyu ban je ba. Amma insha Allahu karshen watan nan zan yi kokari na je. Nura nake jira ya samu hutu don shikadai zai iya shiga wannan jejin mai kayoyi da kwazazzabo da mota ba tareda yayimin korafi ba. Bikin ka ma ban samu na aika mata ba saboda yadda abin ya zo a kurace, laifi kan laifi kam na yiwa Yaya Badijo, sai dai ta dubi Allah ta dubi zumunci ta yafe mini. 


To abu ne irin na jeji ko irin wayar zamanin nan basu da ita balle a samu saukin sadarwa. Sannan babu yadda ban yi da ita ba kan ta dawo nan mu zauna tare bayan rasuwar maigidanta ta ki. Ita ba da ba sai ‘yar jikallen ta Anisa wadda danta Iro ya mutu ya bar mata”. 


Ya ce, “Ita ce wadda kike gaya min kin sa ta makarantar su Rabi’a?” 


Inna ta ce, “Ita ce, yanzu ajinta uku kenan a karamar sakandire, tare suke da Rabi’an, abinda yasa baka ganinta nan in sunyi hutu can ruga take komawa ta yi hutun ta. Ko tazo min nan ana I gobe zata koma ne, yawanci kuma baka nan kana Kaduna. 


Amma gashi tun ba’a je ko’ina ba Yaya Badijo ta fara fadan karatun ya isa haka aure take so ayi 

mata, wai ta samu miji a can rugar su. 


Ita kuma yarinyar bata so tafi son ta yi karatu, sai dai kwakwalwarta bata ja, gashi tana son karatun kamar me, amma Allah bai bata kwakwalwa ba. Rabi’a ta ce ita ke daukar na karshe a ajinsu, sai dai hakan baya damuna don tun farko ba a dora ta akan turbar karatun ba, banda ma n adage na kafe aid a ko firamare bazata bar tat a je ba, sai kiwo da tatsar nono”. 


Zahraddeen ya yi dariya ya ce, “Duk sanda za ki Inna ki yi min magana zan kai ki nima in sada zumunci, bazan taba mancewa da kaunar da Badijo ta nuna min ina yaro ba, ita ta yaye ni, a wajenta nayi jinyar shayi (kaciya)”. Inna tayi dariya tace “ashe baka manta ba’”’. 


Ya mike ya zuba hannun shi cikin aljihu ya zaro mukullin motarshi ya nufi hanyar fita yana cewa, “Ni na yi nan Inna, Kaduna za ni hutun da Alhaji ya diba min ya cika, yau zan koma ofis ayi mana addu’a”. 


Inna ta ce, “Addu’a kullum ina yi maka Dini, Allah Ya ji kan mahaifinka, ya baka ‘ya’yan da za su share ma hawaye kamar yadda kake share min. Ya kare min kai daga sharrin makiya da mahassada, ya kai ka lafiya ya dawo min da kai lafiya”. Har ranshi ya ji dadin addu’ar Inna, ta wanke bacin ran da ya kwana da shi. Cikin sukuni yake tukinsa a kan titin da zai sada shi da garin Kaduna. 


Isarsa ofis ya tadda jibgin ayyuka na jiransa, don haka ya zamo busy a satin gaba daya. Sai da ya gama dukkan ayyukan shi sannan ya rubuta (res

ignation letter) wato takardar ajiye aiki da “Dan Kasa Holdings’ da hujjar tafiya karo karatu, ya tura ofishin Daddy. 


Alh. Aliko ya dade yana juya takardar Zahraddeen a hannunsa, wadda sakatariyarshi ta shigo mai da ita. Wadda ta ciro yanzunnan a kwamfuta. Kafin ya ce wani abu Zahraddeen ya yi sallama a ofishin cikin sallama, daga mishi kai kawai Daddy ya yi, amma ya kasa amsa sallamar shi. Binsa kawai yake da kallo kamar yau ya fara ganinsa. Zahraddeen ya zauna ya sunkuyar da kai shima ranshi babu dadi. 


Shiru ta ratsa a ofishin na tsayin mintuna biyu, sannan Zahraddeen ya yi ta maza ya gaida Daddy ya amsa, sannan ya sassauta mamakin sa ya ce. “Da gaske kai ka aiko da wannan takardar?” Cikin matsanancin ladabi ya ce, “Na’am Daddy ni na aiko da ita’. 


Ya ce, “Kuma don za ka je karo karatu sai ka ajiye aikin gaba daya?” 


Idanuwanshi na son zubo da hawaye yana kokarin maida su da karfin gaske, ba kuma na komai bane na ‘sabo’ ne da kaunar da yake yi ma Alh. Aliko, Uba mai cin tudu biyu a yanzu; siriki/ ubangida. 


Ya ce, “Hakan na ga zai fiye min kwanciyar hankali Daddy, ka yi hakuri kada ka kullace ni, ko ka yi min wata fahimta sabanin kyakkyawan kudirin dake zuciyata. 


Daddy ban yi haka don raini ko don na bata maka rai ba, ko don ka yi min wani laifi ba, ina da sha’awar zurfafa karatuna ne kawai”. 

Alh. Aliko sai ya yi murmushi don shi babba ne, tuni ya hasko abinda yasa Zahraddeen yin wannan zuciya. 


Ba shakka ya fahimci rainashin da Marwah ta yi shine dalilinsa na yin hakan. Sai ya ji yaron ya kara burge shi, ya kara shiga ransa. 


Ya ce, “Ina bayanka Zahraddeen, Allah Ya shige mana gaba. But Ill miss u so much.....(zan yi kewarka da yawa). Ina za ka je karatun?” 


Ya ce, “Ba wani waje bane, a nan ABU ne zan yi PhD dina tsayin shekaru uku, zan yi karatu ne full time shine dalilina na ajiye aikindon bana son in bata shekaru masu yawa wurin kammalawa’”. Daddy ya girgiza kai ya ce, “Ina yi maka fatan ALHERI, amma ba zan iya soke sunanka daga cikin ma’aikata na ba. 


Duk ranar da ka gama karatun, ka ga kuma kana sha’awar ci gaba da aiki tare dani, to kofa a bude take. Yanzun dai zan baka (leabe without pay), hakan ya yi maka?” 


Bashi da zabi banda ya daga mishi kai. Duk da ba haka yake so ba, so yake ya yi sallama kwatakwata da aikin ‘Dan Kasa Holdings’ ya bude sabuwar rayuwa wadda babu raini a cikin ta. 


Ya manta cewa babu wani aiki a gwamnatin ma da babu bin na gaba a duniya. Kafin mu hau sama, dole mu taka matattakala. 


Daddy ya bude jakarshi ya fiddo chekue ya yi rubutu na minti guda ya tura mishi. Ya kuma kara da cewa. 


“Duk sanda kake neman wata shawara kan wani al’amarinka ka neme ni, haka duk wata matsala 

da ta shafi karatun ma. 


Game da iyalinka kuwa Zahraddeen sai in ce ka kara hakuri, watarana sai labari. Sannan komai na duniya mai canjawa ne, musamman al’amarin yara mata, wanda kuruciya ta yi yawa a cikinsa. Kana da ra’ayin Marwah ta koma makaranta ko baka ra’ayi?” 


Ya dago ya dubi Daddy hawaye taf a idanun shi, hawaye ne na kauna, sabo da kewa. Domin ji yake kamar zai kara rabuwa da mahaifinshi ne a karo na biyu. 


Kaunar dake tsakaninshi da Alh. Aliko kauna ce tabbatacciya daga Allah!. 


Shima Daddy kokarin mai da nashi hawayen yake yi cikin dabara, don baya son Zahraddeen ya ga karyewar zuciyarshi. 


Ya soma kalubalantar kanshi da auren diyarshi da ya lakabawa Zahraddeen ba da son ranshi ba. Sai don nashi amfanin. 


A yanzu kam yana nadamar hada wannan auren, wanda babu so da kauna ko yaya daga kowanne bangare, duk shi ya jawo wannan, shi ya jawo a yau Zahraddeen ya zabi ya barshi don ya tsira da martabar sa a idon diyarsa da ‘society in gen


“Yaya zan aure ta tana karatun ta sannan in hana ta Daddy?” Muryar Zahraddeen dake sassarfa da karkarwa ta katse shi daga tunaninsa. 


Daddy ya ce, “Shi kenan Zahraddeen Allah Ya yi jagora”. 


Hannu biyu yasa ya karbi chekue din ya yi godiya ya mike ya doshi kofar fita. 

“Zahraddeen”. Daddy ya kara kiransa. 


Ya juyo ya dawo, sai kuma tari ya sarke shi, ya yi ta tari ba kakkautawa. 


Da sauri Zahraddeen ya bude dan karamin firjin dake gefe ya dauko gorar ruwan Ragolis ya cika tambulan ya mika masa, amma ya kasa karba, tari yake ba kakkautawa kamar mai ‘tuberclosis’. Gaba daya Zahraddeen ya rude ya rasa irin taimakon da zai bawa Daddyn, sai ya tsuguna a gabansa yana ta faman jera mishi sannu. 


Da kyar tarin ya lafa, ya karbi ruwan ya sha, ya koma ya kwanta a kujerar shi. Har zuwa lokacin Zahraddeen bai daina yi mishi sannu ba. 


Ya dafa mishi hannu sannan ya rufe takardun dake gabanshi ya tura su gefe ya mike. 


Ya ce, “Muje ka sauke ni a gida, ba zan iya aikin ba, bana jin dadin jikina”. 


Jikin Zahradden ya yi sanyi sosai, ya soma zargin kansa da rashin yiwa Alh. Aliko adalci. Mene laifinsa don yana kaunar ka? Ya dauki ‘yarshi da yake so ya baka ba don kwandalar ka ba, sai don kaunar da yake yi maka. 


Amma a kan shirmen diya mace ka ce ka rabu da shi duk da yakinin da kake da shi na cewa ba shi da mai taimakonsa tamkar ka. 


Ya soma girgiza kai da sauri ya ce, “Ka yi hakuri Daddy, na janye, wallahi na fasa_tafiya karatun....baka yi min laifin komai ba Daddy...” Hawaye suka balle a idanunsa. Daddy ya rungume shi ya ce, “A’a, Zahraddeen ina bayanka, ka koma karatun ka, ka kuma zabi duk yarinyar da kake so ka aura don Marwah ta shiga 

hankalinta. Yaran yanzu ne ka haife su amma halinsu a duniya suke daukar abinsu. Itama dayar abinda tayi min bazaka so ka ji ba, har gara ita wannan din inada kyakkyawan zato akanta tunda har ta yarda ta zauna zuwa wannan lokacin. Ko yau ta fito nasan na taba yi mata aure da miji nagari bani da wannan tambayar wajen Ubangiji. Tana bukatar lokaci kafin tasan menene rayuwa. Nayi kuskure babba wajen nunawa yarannan soyayya mai yawa” 


“babu kuskure acikin tarbiyyar daka yi musu Daddy. Ka basu tarbiyyah wadda ta dace baka barsu kara zube ba. Ka sa ido akan addini da tarbiyyarsu ni shaida ne akan hakan. A ko’ina kuma suna nuna su jakadu ne na mahaifinsu. Lamarin bai kai yadda ka zace shi ba”. Zahraddeen ya fada cikin kokarinsa na Daddy ya kwantar da haankalinsa. 


“Za ka yi min wannan alfamar dana nema din Zahraddeen ko ba za ka yi ba?” 


Da sauri ya ce, “Zan yi maka Daddy, wallahi zan yi maka”. 


Ya ce, “To na gode Zahraddeen muje gida, bana jin dadin jikina ko kadan”. 


Mami na kicin a lokacin da suka shigo. Zahraddeen rike da Daddy, ya taimaka mishi ya kwanta cikin doguwar kujera. 


Daidai lokacin da Mami ke fitowa ita da Shahida wadda ta sakko daga matattakalar bene. 


Mami ta ce, “Subhanallahi, lafiya? Me ya samu Daddy Zahraddeen?’ 


Zahraddeen wanda ya fisu shiga tashin hankali ya 

ce, ‘““Cewa ya yi baya jin dadin in kawo shi gida”’. Mami duk ta rikice, Alh. Aliko ya maida idanunshi ya rufe. 


Mami ta soma kokarin kiran wayar Dr. Mathew da wayar hannunta, ta yi sa’a bugu daya ya dauka. Ta gaya mishi ya zo cikin gaggawa Daddy ba shi da lafiya. 


Zahraddeen bai bar gidan ba sai bayan tafiyar Dr. Mathew, wanda ya yiwa Alhajin gwaje-gwaje, ya kuma yi mishi allurar barci. 


Ya ce da Mami da Hajiya kada su damu, in ya farka barcin shi da safe insha Allahu zai warware, 


hawan jinin shi ne ya motsa. 


Ya roke su su daina gayawa Alhajin duk abin da 


zai tayar mishi da hankali. 


Zahraddeen ya dauki laifin duk ya dora a kansa, 


da ya san abin da zai faru kenan da ko kusa bai zo 


ya ce da shi zai barshi ba. 


Don haka barcinshi a wannan daren kalilan ne. 


Da safe shine mutum na farko da ya danna musu 


kararrawa karfe takwas na safe. 


Shahida ta bude suka gaisa, sannan ta bashi 


hanya ya wuce cikin falon. 


A lokacin Daddyn ko farkawa bai yi ba. Mami na 


gefe ta zuba mishi ido ta rasa abin da ke mata 


dadi. Bai farka ba sai karfe tara na safe. Mami ta 


taimaka mishi ya yi wanka ya yi alwala ya 


gabatar da sallar asubahi da ta kubuce mishi, tare 


da jero istigfari. 


Bayan ya yi sallama abin da ya fara ce da Mami shine, “Ina Zahraddeen? Ta kara gwada layin Imam ko za ta same shi”. 

Cikin hanzari Mami take latsa wayar hannunta, kamar ko yaushe kwamfuta ta sanar da ita an daina amfani da wannan layin. 


Ta kira ta Zahraddeen nan ya ce da ita ai yana cikin gidan. Ta ce to ya karaso Daddy na kiransa. Hajiya Mama da Shahida duk tare suka shigo da Zahraddeen. Ya durkusa ya gurfana gaban Alhajin, shi kuma ya kama hannun shi ya rike tamau ya ce. 


“Zahraddeen na san ban kyauta maka ba da na baka auren diyata alhalin dukkanku bakwa so...” “Ka daina cewa haka Daddy, har abada jininka ya fi karfin rashin so a gare ni. Marwah kanwa ta ce ko da bata sona, ban taba tunanin akwai wata rana da za ta zo in ji bana kaunar ta ba, ko da kuwa ita bata son nawa. 


Aure da jininka Daddy yanzu na fara har ranar da na daina numfashi’. (Har abada hoton wannan ranar ba zai gushe daga zuciyoyin su ba). 


Daddy ya yi murmushi ya ce, “To na gode Zahraddeen, ina kuma shi wancan alkawarin da ka yi min?” 


A nutse ya ce, “Wane alkawari ne Daddy? Wallahi na manta”. 


Ya ce, “Alkawarin da ka yi min jiya na alfarmar da na nema cewa ka yi aure na soyayya da duk yarinyar da kake so?” 


Ya ce, “Na tuno Daddy, amma ka yi mana afuwa ba yanzu ba, sai lokacin da Allah Ya nufa, wato lokacin da na samu wadda zuciyar tawa ta kwanta da ita, in ka janye zancen ma Daddy zan fi yin farin ciki, Marwah zata so ni, jiki na na bani 


1 comment for "BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 3 by sumayyah Abdulkadir"

Unknown 27 August 2021 at 03:36 Delete Comment
This is interesting
Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...