BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 9 by sumayyah Abdulkadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 9 by sumayyah Abdulkadir

BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 9 by sumayyah Abdulkadir

- - 1 comment

 BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 9 by sumayyah Abdulkadirbude taron, da addu’a. 


Bayan an shafa ya dubi ‘ya’yan nashi baki daya tsayin mintuna goma bai ce komi ba, yana son kowannensu ya Samu nutsuwa. 


Sannan ya ce, “To ‘yan biyu wannan taron kusan nace naku ne, Safah ke ce babba zan fara dake. Ba sai na tsaya ina yi miki bayanin wane ne mijin auren ki ba kin san shi, tun baki san kanki ba. 


Amma kika ture kika kawo maganar Zahraddeen, kuma mun yi alkawari kin bar wannan magana har abada. 


A kokarina na rashin son Zahraddeen ya kubucewa zuri’a ta, na yanke shawarar bashi MARWAH.....” 


A razane suka cira kai dukkaninsu banda Mami da Safah wadanda tuntuni sun san da zancen. Ba tare da ya damu da razanar su ba ya ce. ‘“Hajiya Maama ki zama shaida, Baffa Sufyan kai ma ka zama shaida, ko bayan raina wani a nan ya tada wannan auren da zan daura a gobe 

'>? 


Allah Ya isa ban yafe masa ba........-: Marwah ta rushe da kuka ta ce, “Ni Daddy ya ya za ai min haka? A rasa wanda za a hada ni da shi sai yaron babana...... bana so.....wallahi bana son shi.....na wuce da ajinshi!” Kalaman da _ suka _ shiga kunnen Zahraddeen kenan, a lokacin da ya sawo kai zai shigo falon, domin amsa kiran Daddy, wanda bai samu ya zo a kan lokaci ba, sakamakon ayyuka masu yawa da suka tsare shi a ofis. 


Sal ya ja ya tsaya ya kasa shiga cik1, nan ya jiyo Daddy na zabgawa Marwah mari tare da fizgo wayar t.b ya shiga tsula mata yana cewa. 


“Yaron nawa za ki aura, in yaso ki kashe kanki saboda_ bakin ciki. Shashasha wadda bata san Annabi ya faku ba. Ban san inda kika debo bakin hali ba, na girman kai da son duniya, ba haka ‘yar’ uwarki take ba. 


Ko mutuwa na yi na fada na kara ban amince a daura miki aure da kowa ba sai Zahraddeen. Ke ko mutuwa ki kai 

kafin gobe sai na fara kai gawarki gidan Zahraddeen kafin in kai ki kushewa.....” 


Safah ce ta mike da gudu ta kifu a kan ‘yaruwarta ganin irin dukan da Daddy ke mata, tana kuka ta ce. “Daddy doke ni a madadinta, fatar jikina ta fi tata kwari.....” Imam baisan sanda yayi dariya ba, 


Daddy ya ce “Ko ki kauce ko in hada da ke....” 


Ba ta kauce ba ya hadasu ya dinga tsula musu wayar Imam na rikewa yana bashi hakuri. Da sauri Mami ta mike ta ce, “Za ka kashe min ‘ya’ya ne saboda Zahraddeen?”’ 


Ta sha gabansa ta rike wayar da Imam ya kasa kwacewa. Hajiya Maama ta ce cikin mamaki, “Zainabu? Yau gaya mana kike ke kika haifi “‘ya’yan? Ai mun kwana da sanin wannan, ba sai kin maimaita ba’. 


Daddy kuwa wanke ta ya yi da mari abinda bai taba yi ba a tsayin shekarunsu talatin da biyar da aure. 

Ta kama kuncinta ta rike ta ce, “Ka mare ni, duk akan Zahraddeen?”’ 


Ya ce, “Na mare ki, don Allah ki Ba ta rama din ba ta juya ta fice daga falon, ya daga murya yana cewa, “Ki zo ki sa ‘yar taki a gaba ku tafi duk inda za ku in har ba za ta zauna da mijin da na zaba mata ba, to nima ba za ku zauna min a gida ba”. Zahraddeen dake bakin kofa idanunshi suka yi jajir, jikinshi na rawa ya juya zai fita. Daidai lokacin Mami ta fito cikin sauri-sauri gudu-gudu, ta yi mishi wani irin kallo wanda har abada ba zai goge daga zuciyar shi ba. Sannan ta karasa da gudu ta bi matattakalar bene. 


Haka taron ya tashi, jikin ‘ya’ yan hutu Safah da Marwah ya yi rudu-rudu, har dai Marwah da take fara sol! 


Shi kam Imam kamar mutum-mutumi ya koma. Sai dai fa jin bulalar Daddy dake sauka a bayan Safah yake kamar a jikinsa, amma kawaici, kunya da kau 

da kai ya danne komi. 


Dakin nasu ya biyo su, a lokacin Safah ta cikawa Marwah ruwan dumi a baf ta zuba dettol, ta dawo ta ce, “Je ki gasa jikin ko kya ji dadi”’. 


Marwah wadda har zuwa lokacin kuka take yi, ta mike ta nufi bandakin. Kafin ta fito Safah ta fiddo mata doguwar rigar barci mara nauyi. 


Ta dade a kwamin dumin ruwan na ratsa jikinta, yana rage zogi da radadin da jikinta ke yi. Sannan ta bude ruwan ya tafi, ta sake tara wani ta yi wanka da sabulu sannan ta fito, ta sanya rigar da Safah ta ajiye mata. 


Safah na murza mata manthaleta a kafafunta da gadon bayanta inda bulalar Daddy ta kwanta rada-rada. 


Ya daga labulen yana kallon su, sai suka ba shi dariya. Abu kadan yana amusing din Imam, a bery jobial and lobing personality. Ya saki labulen ya yi mai isarsa tukunna, ya shigo hannayenshi biyu sarke a baya, ya tsaya jikin kofar yana kallon su 

kowacce idonnan kamar an zuba dakakken barkono. 


Ya ce a tausashe, “Haka kawai kin sa Daddy ya zabgar min ke???” 


Hararar shi ta yi, ta ci gaba da shafawa ‘yar'uwarta manthaletan a dogayen yatsunta na kafa, inda wajen ya tashi sosai ya nuna shatin kwanciyar tsabga, ya toshe baki kada dariyar da yake yi ta fito ya ce, 


“biyu kyautar Allah....!!! 


Hadin kanku kan birge ni, but not all the time, (ba ko yaushe ba). 


Kamar dai yau din nan da babu ruwanki amma kin kai kanki kin sha bulala adalilin mai bakin = rashin kunya, ita mai cewa ba ta _ son Zahraddeen din me za ta nuna mishi? Da wani hacinta kamar tumatiri. Banda Allah Ya kashe Ya baki ai Zahraddeen Sal BABBAR YARINYA....” 


Haka ya yi ta tsokanar su uffan basu ce masa ba. Kulawa ma yabawa ce in ji ‘yan magana. Cikin zuciyar Safah 

Cewa take yi sai an kula kashi yake yin doyi. Ni din da banyi bakin rashin kunyar ba son naka nakeyi? Bai yi aune ba ya ji saukar carbi a gadon bayanshi, ya juya Hajiya Maama ce, carbin ya shige shi sosai. 


Ya ce, “Kai-kai! Kin taba jin mata ta doki miyinta?”’ 


Ta ce, “Idan mijin ya zamo babban kwabo wani lokacin sai matar ta doke shi, ina ruwanka dasu? Tunda ka kasa kwatarsu sai bayan an gama tafkarsu zaka zo ka dame su? Kuma ba ka ce ka sake ni ba yaushe ka kara mai dani matar taka?” 


Ta sa shi a gaba suka fita suna ta yi tana yankarshi yana ramawa. 


A tsayin daren baki daya Zahraddeen bai runtsa ba. Maimakon daren ya zamo jajibiren ranar farin cikinsa, sai ya zamo Jjajibiren ranar bakin cikinsa. Kalaman Marwah yake tunawa..... “A rasa wanda za a bani sai YARON BABANA....bana so, wallahi bana son shi....na wuce da ajin shi”. 

Shikadai kamar zautacce, bai san sanda yace da karfi 


“’vyammata nima ba son ki nake yi bal”. 


Da kuma kallon da Mami ta yi mishi, wato kallon raini tsagwaro. Ya tambayi kanshi me ya yi zafi ne? Ko dai ya kira Daddy ya ce mishi ya hakura? Tunda shi ma ba son yarinyar nan yake yi ba? 


Wata zuciyar ta kwabe shi da cewa “Daddy ya fi Karfin haka!!!’. 


Shin yaya zai ji idan ya ce ya fasa 


auren diyarshi, a wannan lokacin da ya riga ya gayyato duniya? Yake ta narkar da aljihunsa domin_shiryeshirye? Hatta katin daurin auren a Leceister aka bugo shi. Ya shiga tausar kanshi da kanshi har ya amincewa zuciyarshi auren diyar Aliko Dan Kasa da zuciya daya, amma fa sai ya daidaita mata sahu. 

Asabar din karshen watan Maris, dubban jama’a cikin garin Kaduna da wajenta suka shaida daurin auren Engr. Imam Zubair Dan Kasa da Safah Aliko Dan Kasa, sannan na Engr. Zahraddeen Aminu Maitama da Marwah Aliko Dan Kasa, a Kaduna State Central Moskue, a kan sadak1 mafi kankanta. 


Daga nan angwayen suka zarce da walima a gidan saukar bakin Alh. Aliko dake unguwar Jabi Road. 


Mami na fama da jama’a, kawayenta, ‘yan’uwanta, ‘yan’uwan Hajiya Mama da ‘yan cin arziki, makota da abokan arziki, don haka ko tana cikin bacin ran abinda ya faru jiya ba za ka gane ba. 


Hidima ta sha kanta, gidanta a cike yake taf ba masaka tsinke, musamman lokacin da ‘yan uwanta suka iso daga Yola, Bus biyu suka ciko. 


A cikin akwai ‘ya’yan wanta Rahima da Badriyyah da ake kira Badar, tsaran Safah da Marwah ne. 

Sannan akwai kawayen Marwah ‘ya’yan kawayenta su Fadila, Fatee, Maimuna da Yasmin duk sun zo, duk da ba Marwan ce ta gayyato su ba. Mami ta yi musu waya sun biyo lyayensu sun zo, su suka takurawa ‘yan biyun suka yi wanka amma juyin duniya sun ce ba za su yi kwalliya ba. Marwah ta ce, “Saboda boyi-boyin Baban nawa zan yi kwalliya? Sai ku sa ni inyi kwalliyar in gani.” 


Safah ta juyo ta kalle ta da idanuwa masu kaifi..., (sharp-eyes). Jikinta ya yi sanyi da ta tuno da alakar Safah da Zahraddeen. Ta yi shiru ta yi lakwas. Tun daga lokacin bakin ta ya mutu. (abincin wani gubar wani) 


Badar da yake abokan wasa suke wato ‘yar mace da ‘yar namiji, ta ce, ‘“Wallahi ko ki tashi ko mu danne ki mu tube ki mu sa miki”. 


Ta ga dukkaninsu sun mike suna shirin danne tan, ga Badar masha Allah da ita (lukuta ce) ta ce, “Ku dakata, mai yasa kuka damu sai ni? Ita 

Safah ba za ku danne ta ba?” 


Suka ce, “Ai ke kin fita baki ne, bakin tsiwa da rashin kunya. Ita ba za ta bamu matsala ba kamar yadda kike bamu, Allah Ya sa dan kanzo ne angon mu bai dame mu ba, muna bisa umarnin Mami ne”. 


Ta ga dai da gaske tube ta zasu yi, kuma an ce sarkin yawa..... ba girma ba arziki ta karbi kayan ta saka tana kunkuni tana cewa, 


“Yo ba gara dan kanzon ba da wannan sumumu-kasau din? Yana tafe yana zukar iska da kyar kamar dole ake yi mishi sai ya shaketa, bayan da ganin shi ka ga dan talakawa, yaushe ya shigo garin da shaddar shi za ta burge ni?’ 


Suka sa dariyar data kara kular da ita suka ce, “Eh, hakan dai zamu wanke ki mu kai mishi Zaria. Arziki kuma na Allah ne, babu wanda aka haifa da shi kowa a nan duniya ya samu”. 


Da wannan suka kashe bakinta. Badar ta fiddo robar kayan lalle ta ce, “Ni 

bani kafa ki gani in rangadawa bawan Allah lalle’”’. 


Ita kuma Rahima kan Safah ta koma ta zame mata dankwali ta ce, “Wannan tufkar za a kwance, relader zan shafa miki’. 


Haka suka rufe su, mai yin kunshi na yi, mai dilka na yi, mai gyaran gashi na yi. Kamin ka ce meye wannana sai ga ‘ya’yan Mami sun fito ragas. 


Karfe takwas motocin diban jama’a zuwa wajen Dinner sun iso. Nan ma sai da aka tafka rigima da Safah da Marwah, domin sun ce ba inda za su. Imam da Zahraddeen suna waje tare da zugar abokansu. Badar ta fito ta shaida musu cewa sunyi iya yinsu, amaren sun ce baza su je ba. 


Hutu na musamman Alh. Aliko ya bai ma dukkanin ma’aikatan DAN KASA HOLDINGS, don haka kwansu da kwarkwatarsu. suna_ cikin tawagar Engineer Zahraddeen Maitama. 


Ga Peter da Ahmad Kutama manyan manajojin Daddy a hagu da daman 

shi. Peter ya sha shadda kai ka ce Bahaushe ne, har da hular zannabukar. 


Yayin da angon ke sanye cikin wani lallausan yadi mai shara-shara fari sol har kana iya hango best dinshi da manyan damatsanshi masu nuni da alamun karfi da cikakkiyar lafiya da mazantaka ta ko’ ina. 


Kallon yadin kadai ya ishe ka kimanta tsadarshi, domin a kalla ya ba naira dubu tamanin baya. Anko ne suka yi ko in ce Daddy ya yi musu shi da Imam, wanda haske da kwarjininsa ya dushe hasken duk wani matashi mai ji da kansa dake harabar gidan. 


Idan aka ce ka bambance wanda ya fi dan’uwansa tsakanin Zahraddeen da Imam Almustapha, an sanya ka cikin rudu. 


Dukkanninsu bakake ne amma ba can ba, sannan ba za ka hada wanda ya rayu cikin arzikin tun haihuwarshi da wanda a rana daya ne Allah ya yi mishi arzikin ba, wannan shine kawai 

bambancinsu, shima cikin kwayar ido da yanayin fatar jiki yake ba a halittar su ba. Shi Zahraddeen din ya zarta Imam a kyawun fuska shikuma ya zartashi a kyawun fata da wayewar cikin kwayar ido. Wato ya _fishi edposure. 


Duk rabin jama’ar Imam jar fata ne daga garuruwa daban-daban na yankunan Birtaniya, inda ya zauna ko yayl wani aiki ko karatu ko yake da abokai. 


Ya dubi Badar ya ce, “Suna ina?” Hausarshi kanta bata fita sosai. 


Ta ce, “Suna dakin su’. 


Ya ce, “Mami fa?’ 


Ta ce, “Mami hidima ta yi mata yawa, baka ganta ba abin tausayi, tun safe ko ruwan shayi ba ta kurba ba shi ya sa bamu gaya mata ba, don ranta ne za ya baci’. 


Ya ce, “Kun yi hankali Badariyya, wuce muje cikin gidan’’. 


Ya janyo hannun Zahraddeen wanda ke amsa wayar Rabi’a ta ce, “Yaya ku 

kadai ake jira, jama’a sun cika kowa ya kosa ku iso”. 


Ya ce, “Ku yi hakuri gamu nan”. 


Da sassarfa suka taka matattakalar da za ta kaisu dakin “yan biyun. 


Suna zaune a bakin gado ana ta tafka rigima tsakaninsu da su Rahima, angwayen suka bankado dakin suka shigo babu ko sallama. Basu kadai ba, hatta kawayen sun razana da bayyanar wadannan ZARATAN MAZA, ma’abota haiba da kamala. 


Imam ya cire links din hannunshi ya soma nade hannun riga ya ce da Zahraddeen, 


“Nade hannun rigarka ka daukar min waccan mai kama da gwandar, ni zan dauki mai kama da kwakwar’”’. 


Ya sunkuya ya sunkuci Safah kanta ko dankwali babu. Kuma ba tareda ya duba cewa tayi wani shiri ko bata yi ba. Zahraddeen na dariya ya kwashi Marwah kamar ya dauki tsintsiya sabida rashin nauyl. 


Kawayen in banda dariya ba abinda 

bani kafa ki gani in rangadawa bawan Allah lalle’”’. 


Ita kuma Rahima kan Safah ta koma ta zame mata dankwali ta ce, “Wannan tufkar za a kwance, relader zan shafa miki’. 


Haka suka rufe su, mai yin kunshi na yi, mai dilka na yi, mai gyaran gashi na yi. Kamin ka ce meye wannana sai ga ‘ya’yan Mami sun fito ragas. 


Karfe takwas motocin diban jama’a zuwa wajen Dinner sun iso. Nan ma sai da aka tafka rigima da Safah da Marwah, domin sun ce ba inda za su. Imam da Zahraddeen suna waje tare da zugar abokansu. Badar ta fito ta shaida musu cewa sunyi iya yinsu, amaren sun ce baza su je ba. 


Hutu na musamman Alh. Aliko ya bai ma dukkanin ma’aikatan DAN KASA HOLDINGS, don haka kwansu da kwarkwatarsu. suna_ cikin tawagar Engineer Zahraddeen Maitama. 


Ga Peter da Ahmad Kutama manyan manajojin Daddy a hagu da daman 

Suke,Saima suka fiddo waya da ipag Suka hau snapping dinsu a hakan, kowaccensu cike da mamakin waj Wannan ne mijin da Marwah ke kushewa? Lallai kowa ya samu rana Sai ya yi shanya. 


Maimuna ta ce, “Gwaggaron fa da takalmansu?” 


Imam ya ce, “Ku biyo su da shi mota”’. 


Haka suka wuce Mami da kawayenta a falon kasa, ta ce, 


“Yau ni Zainabu na ga ta kaina, ku sauke su, ku saukesu nace, su taka da kafafunsu, wadda ta ki takawa na yarje muku ku dauke ta....” 


Suka dire su a gabanta. Rahima ta karaso da Gwaggwaron da takalaman suka kikkifa musu. Safah da Marwah, don takaici sai suka barke da kuka. Mami ta ce, “Kuka ko? Sai ku yi ta yi tunda kun ga shi zai fissheku, ku wuce ku je sai kun dawo”’. 


Za suyi musu suka ga Imam ya fara tattare hannun riga, suka daga kafa da 

Sauri suka yi gaba har suna tuntube. Kowa ya ce me zai yi ba dariya ba? Kawayen suka rufa musu baya zuciyar kowaccensu cike da alhinin ina ma ita ce... Safah ko Marwah, domin ga dukkan alamu basu san baiwar da Allah Yai musu ba. Na_ basu wadannan mazaje na kwatance, na likawa a goshi. Suka fada a zuciyar su. Mota daya suka shiga. Imam ke jan motar Safah tana gefen shi fuskarta cikin cinyoyinta sai kuka take. Na wannan kunya da aka bata cikin taron dangi da ’yan uwa. Zahraddeen da Marwah suna baya wadda ta murje ido take gaya mishi magana son ranta. “Idan ma kai ka zo ka ce da Daddy kana sona, haka za ka koma ka gaya mishi baka so na. Don wallahi ka zabi zama dani ka sayowa kanka bakin ciki da rashin kwanciyar hankali. Don bazan taba zama da kai cikin dadin rai ba”. 


Jin bai tanka ba, ta kara fusata 


“Ka dube ni da Allah na yi kama da 


1 comment for "BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 9 by sumayyah Abdulkadir"

Unknown 9 August 2021 at 01:22 Delete Comment
Ho can i get the complete book
Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...