ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 8 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 8  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 8 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

 ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 8

by Sumayyah Abdul-kadirkadai ba, ko baki son wata rana in zamo Farfesa kamar Baban A.B.U? In yi gida nawa na kaina a duk inda nake so a outside ba a A.B Bamalli Estate ba cikin kauyen Giwa? In yi family mai tsari irin na Baban A.B.U? In yi rayuwa mai tsari irin ta Baban A.B.U? Ba irin ta su Baba Barau ba Fa’izah”. 


Ban san sanda na tuntsire da dariya ba. Na ce, “Ai ni na yi zaton don ka gaji da kai mu makaranta da dauko mu ne da zuwa mana visiting shi ya sa ka koma karatun don ka gaji da saya min nama, Zanirah (Bounty) Ummi (Kit-kat), ka gaji da kai mu shopping da koya mana karatu, shine ka tafi’”’. 


Dariya mai suna dariya kam Yaya Aliyu ya yi ta har ya gaji, ya ce, “Fa’iza yaushe za ki daina wauta ne don Allah? Shin in tambaye ki, da can waye ya sani yi muku hidimar makaranta? Waye ya sani sai muku balangun da alawa? Waye yake sani in kula daku in ba don ina son ku ba? 


Na rantse da sarkin sarakuna ba zan taba gajiyawa da hidimta miki ba muddin 


rayuwata! Ko da bani da shi, zan yi aikin 

karfi da lafiyata in nemo in yi miki in har za ki yi farin’ ciki. Balle kuma alhamdulillahi Allah ya hore mana arziki na duniya dai-dai gwargwado, ta yadda har nake raina ‘yar hidimar da nake muku wanda har ke kike kallon ta kike kiranta hidima. 


Ko da duk abin da na mallaka zai kare wurin sai miki nama ba zan damu ba, saboda dalilin da har yanzu kika kasa ganewa. Kada ki kara saka wannan a ranki (wai ina yi muku hidima), kada ki kara tunanin hakan, sa a ranki wannan Dutyn Aliyu ne”. 


Ina wani irin murmushi mai fitowa tun daga karkashin zuciyar dan adam na ce, “Ba zan kara ba Yaya Aliyu”’. 


2K KK KK 


Washe gari muna gidan Baba Na’ibi (gidan su Yaya Aliyu) muna kallon wani wasan kwaikwayo na ANTAR-BNSHADDAD da ABLAH, domin mu zuri’armu kaf daga shekara kasa da sha 

takwas, ba a kallon finafinan Turawa, na Hausa ko na India, ko na ‘yan kudu (Nigerian Film), sai hikayoyi na Larabci da Risalah, ko tarihin Sahabbai da ake yi a matsayin film kamar na _ Khulafa’urRashidun. 


Domin wannan finafinai da na zayyano a sama a ganin Hajjah duk nau’! ne na illata tarbiyyar yara da hana su mai da hankali ga karatu. Daga na yake-yaken Larabci (Adventure) sai zaluncin da Isra’el ke yiwa ‘yan’uwa musulmi na yankin Gaza, sai Islamic Channel wadanda suke nuna halin da kasashe marasa karfi ke ciki, irin su Somalia da irin tallafin da NGO’s suke yi musu, irin su ‘Human _ Appeal Organization’ masu daukar nauyin irin wadannan kasashe ta hanyar abinci, ilimi, asibiti da tufafi. 


Wadannan al’umma masu ban tausayi abubuwa ne dake karawa yara imani da wadatar zuci. Sai ko labaran Larabci na Al-jazeera, CNN, BBC. Saboda yawan kallon al’amuran Larabawa da nake, da sauran labaran Larabci da_ kallon 

rayuwarsu a talabijin, dadin-dadawa ana 


yin Larabci as (Subject) a ajinmu, sai ya kasance na iya Larabci sosai, kuma shine harshe mafi soyuwa a gare ni tun ina (Area One). Tun ina karama Allah ya dora min kaunar Alifun-Ba’un, Alifun-Arnabun, Ba’un-Bagaratun. 


Maryam ta dube ni muna cikin kallon ta ce, “Wai me Antaru ya ce kenan Fa’ izah?’ Na fassara mata, ban ida rufe bakina ba Yaya Aliyu ya shigo. 


Ya samu gefen mahaifiyarshi ya zauna, ta ce, “Ya ya dai Yayansu? Na ganka rather moody? In ce ko ka dauki abincinka ka c1?” 


Ya dan yi tsaki ya ce, “Mama na sha kunun alkama fa a wurin Hajjah yanzun nan”. 


Ta dube shi tsaf, cikin babbar murya ta ce, “Aliyu!” Da hanzari ya dago ya dube ta. 


“Na gaji kullum magana daya ta ki ci ta ki cinyewa. Yanzu kamar kai Aliyu sai an 


rarrasheka ka ci abinci za ka ci, sai ka ce 


wani karamin yaro, da gangan kake wasa 

da lafiyarka, to na daina, sai dai ka kashe kanka kai kadai, wallahi ka kwanta ciwo ko hanyar asibiti ba za ka ganni ba. Ko da yake in ka kashe kanka ai kai ka jiyo, wa ka yiwa asara?” 


Na juyo daga kallon T.V na ce, “Mama mu mana? Mu aka yiwa asara”. 


Zanirah ma ta ce, “Tabbas mu ya yiwa asara, we cannot, never found a caring brother like him, Yaya Aliyo don Allah daure ka dinga cin abinci in ka mutu mun shiga uku”’. 


Na ce, “Mun shiga uku ko mun shiga tara?” 


Ummi ta ce, “Har mun lalace’”’. 


Zanirah ce ta mike ta yi kitchen da zafin namanta, ta shako plate da dankali soyayye da murtukekn kwai, ta zo ta zauna tsakanin Mama da Yaya Aliyu kasancewar suna zaune kujera daya ne mai cin mutum uku. 


Cike da kulawa ta mika mishi, kana cikin muryar lallashi da kulawa ga karamin yaro in ya ki cin abinci ta ce, “Yaya Aliyu don Allah ka ci”. 


Gaba daya aka kwashe da dariya har 

Maman dake bambamin fada, babu shakka yadda muke kula da Yaya Aliyu da hidimarsa, da yadda shima yake kula damu da al’amuranmu, yana yi mata dadi, don ko Maryam da suke ciki daya ba ta kulawa da al’amarinsa kamar yadda muke masa, haka shima. 


Ga shi tana masifar son Yaya Aliyu kamar ba dan fari ba. Ita cikakkiyar lauya ce mai zaman kanta, sam ba ta irin kawaicin Momina, mu’amalarta da Yaya Aliyu kamar ta Yaya da kaninta mai binta da suka fito ciki daya. Hakan ba karamin bani sha’awa yake ba, in yi ta dakacen inama ace nice. 


Na taso tsam daga inda nake zaune zuwa garesu na ce, “Mama tashi ki bamu fili in bai ci ba dura zamu yi masa”. 


Ita da Yaya Aliyu suka sa dariya, ta ce, “Lallai kam “yammatan Hajjah kadan daga aikin ku, kuma aikinku yana kyau, Allah ka bani tsawon ran da zan ga da wacce za ayi tsakanin ke, Ummi da Zanirah.....” 


A hargitse Yaya Aliyu ya yi ma Mama gyaran murya ga alama bai ji dadin abin da 

ta fada a gabanmu ba. Ta mike ta bar mana falon tana dariya tana fadin “Sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade ba a je ba”. Sai da muka tilastawa Yaya Aliyu ya cinye abincin nan tas, sannan muka kyale shi. 


Ya ce, “Ummi ban ji yadda aka riski Queen Amina ba?” Ta ce, “Tambayi gimbiyar taka mana ni ai baka yi dani Yaya Aliyu, ka kawo mata nama, Zanirah pack din Bounty, amma ni ko sannu don ni lukuta ce tun ranar da ka fada Zanirah ke tsokanata ba a yayin lokutayen mata”’. 


Ya murmusa a hankali, ya fiddo pack din kit-kat a aljihunsa ya cillawa Ummi. Ta dauke tana dariya tana godiya, ya ce, ‘“Saboda Allah Zanira ina ruwan ki cikin wannan maganar har da kike tada ta bana nan?” 


Ta ce, “Rabu da ita Yaya Aliyu, ita ta fara ce min mai wuya uwa marikin lema, an fada din, ba a yayin lukataye sai ‘slim’ din ki yi duk abin da za ki yi”. 


Ya fiddo mata ido ya ce, “Kada na kara jin irin wannan maganar, babu kyau gorin halitta Zanirah, kada na kara ji”. 

Ummi ta ce, “Rabu da ita Yaya Aliyi, so take jikinta ya gaya mata ta ga ranar lukutin jiki, sai shegen cika bakin tsiya babu kwanji, don ta ji Hajjah na cewa ta girmemu to ba shekaru biyu ba ko goma kika bani in kika kara ce min lukuta lallasaki zan yi’. 


Yaya Aliyu ya rasa inda zai sa kansa don dariya, ya ce, “Ana girma ana cin kasa Ummi da Zanirah! Inda Fa’izah ke burgeni kenan, tunda kuka shiga aji hudu ta watsar da shirme ta bar muku”’. 


Ummi ta ce, “Eh, ai daman a wajenka Yaya Aliyu Fa’iza ba ta laifi, ita ce ta iya komai, bayan ita din a bayan idonka tantiriyar kanta ce”. 


Yana dariya ya ce, “Bakya son a fadi gaskiya, amma Fa’izah ta fiku hankali, nutsuwa da kamewa. Ko zaman wuni guda mutum ya yi daku zai fuskanci haka”’. 


Ummi ta sake kuluwa, ta tashi faramfaram ta fice. Yana kiranta yana ba ta hakuri amma ba ta juyo ba. Zanirah ko a jikinta, daman ita yarinya ce mai matukar sanyi cikin al’amuranta ba ta da fushi, ba 

ta da daukar zafi ko kadan a kan duk abin da za ka yi mata, da wuya ka ga bacin ranta. Kullum fuskarta cikin annuri take, ita dai barta a cika baki da kokarin karatu kamar Alhuda-Huda. 


Ya maido duban shi gare ni ya ce, “Fa’izah ba a bani labarin Sarauniya Amina ba’. Na ce, “To Yaya Aliyu me zan ce maka ga yara duk sun zubo min ido?” 


Maryam ta ce, “Lallai ma, su waye yaran naki?” Na ce, “Gaku nan mana juniors ‘yan JSS”. Ta ce, “Mts! Ke har yaushe kika fara SS din da za ki raina mutane?” 


Yaya Aliyu ya ce, “Ke rufe mana baki ko na hambareki, wa ya sako ki cikin zancen nan? Ko sa’arki ce?” Na faki idonsa na yi mata gwalo, ta dalla min harara. 


‘Maza dauko biro da takarda ta rubuta min labarin Queen Amina”. 


Zanirah ta ce, “Ba za ta iya ba Yaya Aliyu, ba ta iya Turanci sosai ba”. 


Ya ce, “Da kowacce luggah Fa’izah rubuta min labarin Queen Amina, be it Hausa, Arabic, English, Fulfulde, Kanuri, Yoruba or Igbo, in har kika rubuta am sure 

zan iya karantawa in fahimta”. 


Da karsashi na karbi takardar da biro, na matsa nesa dasu na soma yarfawa Yaya Aliyu kyawawan rubutu da_harshen Larabci tsaftatacce. Na mika masa ya shiga karanta musu a fili, ga fassarar abin da na rubuta. 


“Yaya Aliyu mun je Queen Amina lafiya, makarantar Sarauniya Amina _babbar makaranta ce mai kyawun tsari, tsohuwa mai tsohon tarihi. Malamansu da dalibai duka masu kwazo ne. Bamu da kawaye, amma muna gaisuwar musulunci da duk wanda wata mu’amala ta hadamu da shi. An kai ni ajin Arabic, an kai Ummi ajin zane-zane (Art) saboda shi ta fi tyawa. 


Akwai club-club a Queen Amina, irin su Maths Club, English Club, Jet Club, Arabic Club, Hausa Club, Science da sauran su. Na raba kafa na shiga Clubs har guda biyu, wato Arabiyya da English Clubs, Ummi ta shiga Jet don Allah bai halicce ta da kwakwalwar rike karatu ba, 

Jet kuma ana koyar da sana’o’in gida ga dalibai ne. 


Aunty Hauwa ba ta kulamu ba ta neman mu, ta ce don ita muka dawo Queen Amina, don haka ba ruwanta damu mu manta mun santa, ba abin da take kawo mana daga gidanta ta ce mu karata”’. 


Nice Kanwarka. Fa’izah A.A Giwa. 


Yaya Aliyu ya ajiye takardar ya ce, “Good, very good, a tafawa Fa’iza, na ce a tafa mata!” Raf! Raf!! Raf!!! Suka hau tafi. Ya yin da Yaya Aliyu ya shiga manna min 


sababbin wa-zo-bia a goshina har guda shida. 


2K KK 


To haka rayuwarmu ta ci gaba da 


mikawa, tafiya ta yi tafiya. Shigarmu ajin karshe a sakandire na dauke da wasu muhimman al’amura da ba zan taba mantawa dasu ba cikin tarihin rayuwata. Don haka ya zama dole in farka shekarar baki dayanta. 

Alal hakika a lokacin na fara wadatuwa 


da abin da ake kira “Hankali” wanda yawan shekaru ke samar da shi. A lokacin ne kuma na fahimci mu’amalata da Yayana Aliyu ba komi ba ce _ illa SOYAYYAH! Soyayya ce muraran yake nuna min cikin ‘yan’uwana baki daya ba tare da shi kansa ya sani ba, a gaban kowa baya iya boye kulawarsa gare ni. Duk dangi babu wanda bai kwana da sanin matsanancin son da Yaya Aliyu yake min ba ko ba a furta ba. 


Sai dai da bakinsa bai taba ko da kuskuren gaya min da fatar bakinsa ba, sai dai actions and emotions dinsa su nuna. Ko da cikin hira ya yi subul da baka sai ya yi kokarin gyarawa ya mai da zancen ko subutar bakin sa (otherwise). 


Shekaru na goma sha takwas kenan, duk wani budurci ya tabbata gare ni. Hankali da nutsuwa sun wadace ni. A zahiri, tunda na soma hankalin nima nake so da kaunar Yaya Aliyu, so ba na wasa ba. Cikin kannena da tsararrakina da danginmu duka zancena daya ne (Yaya Aliyu). Shin don 

mene ne ba zan so Aliyu ba. 


Mutumin da ya kwashe shekaru goma sha daya yana kula dani, kulawar da iyayen da suka tsuguna suka haifeni basu yi min ita ba. Yana bauta mini, yana dadada mini, yana faranta mini. In har ban so Aliyu Na’ibi ba, wallahi ni butulu ce cikin butullun ababen halitta wanda zuciya ba ta aiki a jikinsu. 


Tun daga aji biyar na sakandire na dauki wasa na aje gefe, na bude file na sanya shi na adana a cikin akwatun karfe. Na yi “facing” karatuna yadda duk wani dalibi na kwarai ke yi da taimako da shawarwari da kulawa tattare da kwarin gwiwa irin na Yaya Aliyu. 


Allah ya hore min baiwar kirkira (fiction) na labarai masu ma’ana da fadakarwa ko kuma articles, ina ba da wa ana sanyawa a 


magazine din makaranta, fili guda aka ware min a mujallar makaranta mai suna “KNOWLEDGE IS LIGHT’ tare da Fa’izah Ahmad Abubakar (English Club). Nice kan gaba a fita muhawara (Quizz and Debate) din duk da za ayi da harsunan nan 

uku, Hausa, Turanci da Larabci. 


Da farko in na yi rubutun ‘yan ajinmu nake bai wa su karanta in ajiye, daga bawa shugaban clud dinmu ya karba ya duba sai ya mika shi ga hukumar makaranta. A lokacin an canza Yaya Hauwa daga principal an kawo Haj. Amina Atiku. Ita ta fara dubawa ta ce “Akwai ‘sense’ da ‘exceptional talent’ a ciki”. Rubutuna ya burge principal dinmu sosai, ya kuma bawa malamanmu da yawa mamaki da sha’awa. 


Wani novel ne na rubuta labarin wata Bafillatanar yarinya da wani_ dan makarantarsu da yake taimaka mata a fannin karatu, kasancewarta dakikiya har ta zamo zakakura sahun gaba a masu kokarin makarantar. 


Jin dadin hakan ne ya sa ta yi masa alkawarin za ta aure shi da zarar sun gama karatun sun samu aikin yi. Tsawon shekaru takwas tana dakon alkawarin. Bayan nan suka rabu kowanne ya koma wata duniya daban.Ga shi ta yi alkawarin ne a shekarun odolscence (goma sha uku ba ta gama mallakar hankalin kanta ba, ba ta san mene 

ne alkawari ba da muhimmancinsa balle SO, kauna da auren kansa). 


Rayuwa ta mika, bayan rabuwarsu ta Ci gaba da jiransa. Katsam Barister Haseen Danbatta ya fado cikin rayuwarta, wanda ya fassara mata hakikanin mene ne so, ya karantar da ita fannoninsa from every angle, dadinsa, dacinsa, zakinsa da rashin dadinsa, bambancin so, kauna, kusanci, shakuwa da halacci. 


A zahiri wannan shine mutumin da zuciya da ruhinta ke so, suka kuma aminta da shi. Gangar jikinta da tsokar zuciyarta baki daya ke buri tun kafin bayyanarsa. Ga shi iyayenta sun takura mata da ta fidda mijin aure haka nan, shekaru takwas tana jiran wanda ta yiwa alkawari ya kuma yi mata halaccin da ba ta taba jin an yiwa diya mace ba. 


Abin da mai karanta labarin zai tambayi kansa shine, shin za ta ci gaba da jiran wanda ta yiwa alkawarin ko kuwa za ta watsar da halarcin da alkawarin ta auri wanda zuciyarta da rayuwarta ke so? 


Labari ne tsakanin soyayya da alkawari da na sanyawa suna ARE VOWS MEANT 

TO BE BROKEN? 


Ga shi na yi shine cikin sassaukan Turanci dai-dai karantawar dan sakandire, kuma dai-dai iyawata. Gyare-gyaren da malamar English Language dinmu ta yi min a ciki ba mai yawa bane, grammertical correction ne ta yi. Sai ka rantse da Allah Abubakar Gimba ne ya rubuta. 


Principal dinmu ta kirani ta ce za a kaddamar da littafin ranar da zamu gama makarantar, kuma za a buga shi a dinga saidawa a makarantun da ake _ yin Literature da kasuwanni don_ sauran al’'umma masu_ karatun Novels don nishadi. In yaso sai makaranta ta rike ribar, amma duk abin da aka samu_ wajen kaddamarwar nawa ne. 


Da wannan daddadan labarin na tarbi Yaya Aliyu a wani visiting da ya zo mana. Na zaci zai yi farin ciki, amma sabani ga tunanina ya yi shiru bai ce komai ba. Na ce, “Baka ji dadi bane Yaya Aliyu? Na dauka abin kirki na yi? Na yi zaton wannan abin farin cikin mu ne duka?” 


Ya ce, “Ba wai ban ji dadi bane da hikimarki ba Fa’izah, amma ina son ki san 


Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 8 by Sumayyah Abdul-kadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...