ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 6  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

 ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 6

by Sumayyah Abdul-kadir


mana ziyara. 


Momin ABU rungume da sabon baby dinta kyakkyawa kamar Baban ABU, na rungume shi na rasa inda zan sa kaina don farin ciki. Bakina kamar ya yage don fara’a ina rungume da babyn, na ce, “Wai ya ya sunansa Momi?” 


Ta ce, “Ban sani ba, ni fa ba wurinki na zo ba Aku sarkin magana’”’. 


Na yi narai-narai da ido kamar zan yi kuka. Yaya Hauwa ta ce, “Rabu da ita Fa’iza, sunan shi Baban Kaduna (Mukhtar) shi kenan?” Na ce, “To, Ya Hauwa ya zamu ke kiran shi?’ Ta ce, “Kowa a gida yana ce mishi ‘WALID’. Dadi ya rufe ni, na ce, “Yeh! Mun samu Waleed da Waleeda”’. 


Ta fannin Fa’iz karatun Diploma a Kaduna Poly ya sha masa kai, a kokarinsa na hattama (ND) wato National Diploma. Fa’iz wani irin mutum ne da baya son karatun boko sam. Diplomar ma sai da suka takura masa su Baban ABU suka 


bude mishi wuta, don bayan kammala sakandire dinshi a Madina kin ci gaba ya 

yi, kai dai barshi da tukin mota. 


Duk wanda ke son zuwa unguwa Fa’iz ne direbansa, ba sai ka roka ba shi zai roke ka ka ba shi key din mota ya kai ka. Babu yadda bai yi ba Baba Muntari ya ba shi mota ya ki, don ya ce tukin mota ne yake hana shi karatu don haka duka bus-bus din A.B Estate mukullan su yana hannun Fa’ iz. 


Kowa da (nature) dinsa, kowa da 


kaddararsa, to “tukin mota shine kaddarar Fa’eez Mukhtar Abubakar Giwa’’. 


Yana kwanan makaranta ne a Kad Poly don haka yawancin hutun da muke zuwa muna samun sa’ida. Week end kawai yake zuwa Giwa ya koma lahadi, don haka marorinmu sun sarara cikin shekarun nan. 


Wannan hutun da muke zangonmu na karshe na aji uku na karamar sakandire (JSS.) mun dukufa karatun jarrabawar (placement). A wani dare a hostel na dubi Ummi wada ke nazarin wani_littafin Islamic Studies na B. Aisha Lemu (For Juniors) na ce, “Ummi kin san tunanin da ya Zo min kuwa?” 

Ta ce, “A’a, sai kin fada”. Tare da rufe littafin da ke hannunta. 


Na ce, “Wallahi tunani na yi, gara mu hada baki mu ki makarantar nan _haka. Babu mai tunawa damu, babu mai zuwa mana a kan kari ko akai-akai, komai mune karshe. In ba don ma Yaya Aliyu da ke zuwa duk wata ba, ai da mun kade. 


Kina da masaniyar cewa Zanirah duk sati sai an je mata an kai mata girkin Hajjah da dambun nama, gaskiya ni ba zan dawo ba”. 


Ummi ta ce, “Ni babu ma abin da ya fi ban haushi irin ranar hutu, kullum mune karshen dauka bayan yunwa ta gama kwakwale mu”. 


Na ce, “Abin da nake so ki gane kenan, kawai mu bude wuta mu ce mu sai Sarauniya Amina(Queen Amina College Kaduna) inda Yaya Hauwa ke. aiki. Makaranta ce ta hazikai kwarai, Aunty Hauwa ta taba gaya min dan JSS 2 a Queen Amina zai iya rubuta Formal Letter ba tare da kuskure ba, duk da ba ta federal govt. ba ce”. 

Ummi ta ja numfashi ta ce, “To shi kenan, sai mu bi ta kan Yaya Aliyu shi kadai zai yi mana wannan kokarin, kuma shi kadai ne zai mara mana baya, amma cewa za’a yi don muna son kusa da gida ne kawai”’. 


Na ce, “Ai Allah ya ga zuciyata, ni dai abin tarihi da alfahari ne a gare ni ace na zamo daya daga cikin daliban makarantar nan mai tsohon tarihv’. 


Ranar hutu muka shiga sallama da kowa kamar har mun tabbatar ba zamu dawo din ba. Bamu bar ko tsinkenmu ba, mune har da amsar address din wasu daga cikin ‘yan dakinmu da “yan ajinmu wadanda aka saba da juna tsayin shekaru uku. 


Yaya Aliyu ya ga kaya cancarakas! Har da su loka da katifu da filallika, ya ce, “Ku lafiya? Ina za ku da wannan kayan?’ 


Muka kyalkyale da dariya ganin yadda ya razana, muka shiga danna kaya a but muna fadin “Mun yi graduation ne Yaya Aliyu’”. 


Ya ce, “Aure za ku yi?” 


Muka hada baki wajen cewa, “Eh! Yaya makaranta ta ishemu aure muke sooooo!” 

Ya zuba hannaye a bannet din motarsa yana fadin, “La’ilaha illallahu......” 


Na ce, “Muhammadur rasulillahi..... 


Ummi ta _ ce, “Sallallahu alayhi wasallam”’. 


A kan hanya muke yi masa bayanin shawarar da muka yanke. Ya ce, “Ke dai Fa’iza ko dai don ki dinga cin abincin Aunty Hauwa ne?” 


Na ce, “Wallahi a’a Yaya Aliyu, kawai ina so na zamo daya daga shahararrun daliban Sarauniya Amina wadanda tarihin Najeriya ba ya mancewa dasu (Old Student of Queen Amina _ College Kaduna)’. 


Yace, “I trust you my dear sissy”. 


A falon Hajjah Yaya Aliyu ya ta da zancen,ranar da muka kwana uku da komawa. Bashir da ya zo daga Kaduna ya ce, “Gaskiyar Fa’izah, don ko wannan jelen daga Giwa zuwa Gusau-Gusau zuwa Giwa ba karamin wahala bane”. 


Fa’iz ya ce, “Wane irin wahala Yaya Bash? Tunda Allah ya hore abin da za a 


sayi man fetir din da lafiyar da za a tuka 

motar ba shi kenan ba? Kawai dai Fa’izah jakar yarinyar nan ka san ba son karatu take ba shine ta zuge Ummi don ita ma ta maida ta jaka kamar ta, amma ta ya ya zaa ce wai Govt. School ta fi ta federal Govt. Na san don su dinga ganin Aunty Hauwa ne kurum..” 


Aliyu ya yi saurin katse shi da cewa, “Ban tari hanzarinka ba Fa’eez, ban kuma ce Fa’eezah mutum ce ba jaka ba ce tunda uwarta ba A.B ba ce, don haka Fa’eezah ba mutum ba ce. Amma da ka ce wai don su dinga ganin Aunty Hauwa ne a kan me? Shin watanni nawa suke sharewa ma a nan garin ba tare da sun ziyarce ta ba ma sun taba damuwa? Ko ka taba jin tsakanin Ummi da Fa’iza wata ta taba tambayata yaushe zamu je wajen yaya Hauwa? In da ka ce Maman Kaduna to wannan sai in yarda” 


Fa’iz ya kyabe baki ya ce, “Kai ai Yaya Aliyu ai dama kullum kana bayan Fa’izah, ba ta taba yin ba dai-dai ba ka kwabe ta, 


komi ta yi, duk hukuncin da ta yi dai-dai ne a_wurinka, alhali she’s (empty

mindend)”’. 


Ya ce, “Yes! Fadi da babbar murya ina bayan Fa’ia a kullum, domin da ka ki da ka so FA’IZAH yarinya ce mai tunanin kanta, hikima da kaifin basira, da wuya tunanin ta in an auna shi za a ga rashin hikima a cikinsa. Kuma da kake cewa wani wai Allah ya hore kudin man fetir, to don Allah in tambaye ka, shin ka taba kashe kwandala ka sayi man ka zuba a mota ka kai ko ka dauko Fa’iza daga Gusau ko da sau daya ne? Ka taba kashe lokacinka ko da minti talatin ne ka je ka gano Fa’iza da Ummi a Gusau? 


Amma Zanirah! Ka gaya mani don Allah, sau nawa kake zuwa mata visit per-term? Ko ko ka taba kawo kwandala ka basu ka ce su sayi sabulun wanka a makaranta? Amma Zanirah sau nawa kake sayen kaya ka kai mata Fa’iz! A wane dalili don Sun nemi sauyin makaranta za ka sanya baki, don haka ba damuwar ka ba ce bai shafe ka ba ina fatan ka gane?’ 


Fuskar Fa’eez ta yi jawur da wannan wankin babban bargo da Yaya Aliyu yal 

masa, ya ce, “Amma ka san ni ba wani aiki nake ba baya ga karatu, ina zan nemo kudin da zan ke musu provision har su uku, kuma su suna da nisa?”’ 


Yaya Bashir ya ce, “Line perfect, wannan karatun naka ne kake kiran shi karatu? Wai National Diploma, amma a hakan ina kake nemo wanda kake yiwa Zanirah? Ina kake nemo wanda kake dinka sabuwar shadda duk sati? Tukunna ma, ina kake kai rabonka da ake baka na A.B family duk wata? Ban ga amfanin mutum ya tsaya yana faman cacar baki da mutumin da bai san ciwon kansa ba irin Fa’iz Bamalli....” 


Hajjah ta zaburo ta ce, “Ku kun san Allah ku kiyaye ni, haka kawai kun sa min miji a gaba kuna tsiga kuna tsattsaga kamar ku kuka haifi Fa’izar da Ummin? Sai ku bari in ya zo ya ce muku yana son daya daga cikinsu sannan ku yi masa wannan goregoren naku”. 


Yaya Aliyu ya ce, “Ai shima baya fara ba, baya soma ba Hajjah, Ina! Ai alamar karfi yana ga mai kiba, kuma abin da ka yi shi za a yi maka. Makaranta ce ni Ali zan 

canza musu, zan ci gaba da kula da hidimarsu duka ba zan bambanta ba, ba zan fasa ba, don ni irin nawa ZUMUNCIN KENAN duka daya ake, A.B abu guda ne bana jikin-jikina kawai ba, in har ina da iko sai in ko bana numfashi Hajjah’’. 


Ta ce, “To Allah ya ba da sa’a, ga fili nan ga mai doki”. 


Fa’iz ya ce, “Sai sukuwa Hajjah”’. 


Yaya Aliyu ya danna mai harara ya yi ficewarsa yana murmushin tura haushi. 


2K 2 Ag ok 


Ina toilet ina wanka na ji landline din Hajjah na ta faman (ringing) babu wanda ya dauka ta yi ta ruri har ta katse, ta sake kama wani sabon kukan har tana neman ta sake katsewa. Cikin hanzari na ja tawul na daura duk jikina kumfa na fito falon aguje na dauki wayar na amsa da sallama. 


Sai ga Ya Fa’iz ya sanyo kai falon, cikin captan na makubar shadda Hilton, ya yi shar kamar ango sabon aure. Shigowar tashi da tunanin yanayin sutturar da nake ciki ya sanya ni rawar kafafu tare da 

sarkewar harshe wajen amsa sallamar. 


Muryar Maman Kaduna ce ta ce, “Fa’izah ga direba nan na turo yanzu ku biyo shi dukkanku tafiya zamu yi Kano gidan Rabi”. 


Na yi tsalle na dire na saki ihun murna, na ce, “To Mama’. Na ajiye wayar amma saboda rawar da hannuna ke yi na ajiye shi ba dai-dai ba. 


Dagowar nan da zan yi muka yi ido hudu da Fa’iz yana yi min wani irin asirtaccen kallo da shi kadai ya san ma’anarsa, sai dai na nemi kibiyar kiyayyar dake cikin idanun na rasa. Kallo ne na kurulla wanda ya wuce gejin kallon addini. Na tuna a yanayin da nake na saki wani dogon tsaki na juya na shige dakinmu, na shige toilet na rufe na ci gaba da wankana. 


Bayan na kammala na fito ina muttsika mai a fatar jikina (Norwegian Formula). Su Ummi suka shigo suna ta hira da kwasar dariya, na ce, “Ku don Allah mu shirya ga direba nan Mama ta turo zai debe mu zuwa Kaduna, daga nan mu tafi Kano wajen Ya Rabin Yaya Muftahu”. 


Nan su Ummi har da tsalle aka fada 

wanka, Zanirah na hada mana kaya cikin (luggage). 


Hajjah ta shigo daki ta ce, “Ku kuma shirin me kuke haka kamar za ku tashi sama?” 


Na ce, “Hajja Kano zamu”. 


Ta ce, “Kano? Wajen autata amma shine baku gaya min da wuri na tanadi tsaraba ba?” 


Na ce, “Hajjah muma yanzu-yanzun nan Mama ta yo waya ta gaya min na gaya musu, amma na san ita Maman za ta yi tsaraba ai’. 


Muka sha doguwar riga mai rubi biyu ‘yar Oman (tsarabar Baba Sadi ne ta Hajjin Bara), nawa baki da ratsin maroon, na Ummi baki da bula-bula mai_hasken sararin samaniya, na Zaneerah ja da baki, muka debi ‘yan kayan da zamu butaka cikin travelling bag. 


Kamar jira yake mu kammala, malam Garba direban Maman kaduna sai ga shi ya aiko su Abba ya zo mu fito. 


Mun shiga mota Hajjah na daga mana hannu, nice a gaba su Ummi a baya, sai ga 

Yaya Aliyu ya fito daga gidansu ya ce, “Sai ina kuma ‘yammatan Hajjah?’ 


Na ce, “Sai Kano”. 


Ya ce, “Kano? Gaskiya Fa’iza ban yarda ba, na ji an ce samarin Kano kwarraru ne wajen fashin mata”. 


Cikin mamaki na ce, “Matar wa to za su kwace?” 


Ya yi hanzarin gyara zancensa da cewa, “Ke dai kada ki kula maza a Kanon, Idan Baban ABU ya ji kin yi saurayi zai gayawa Hajjah ne ayi gaggawar yi miki aure ke da su Ummi, ba zai bari ki yi Sarauniya Amina ba”. 


Su Ummi suka kyalkyale da dariya (ban da Zanirah). Na ce, “To na ji ba zan yi ba, amma su Ummi su yi?” 


Ya kada kafada ya ce, “Eh, ba komai su suyi, ai kinga su sun girme ki. Baki ga Ummi ta yi biyunki ba’. 


Malam Garba ya ja mota muka wuce muna mishi dariya ban da Zanirah da ta yi fuskar shanu tana ta sakin tsaki, to wa take yiwa? Allah masani. 


Da muka isa Kaduna already Mama ta 

shirya ita da Junior, bamu bata lokaci ba sauran yara suka yo mana rakiya bakin mota da kayan Mama Kano ta diba. 


Kusan karfe biyar na yamma muka iso Kano, unguwar da su Anti Rabi suke wai ita Gadon Kaya. Unguwa ce da ta tara duka masu karfi, masu karamin karfi, ‘yan kasuwa kawo ‘yan boko babu irin rukunin mutanen da ba za ka taras a unguwar ba. 


Duk da babu inda ban sani ba a Kaduna, ban ga kyakkyawan gari mai albarkar al’umma irin Kano ba. Gidan su Aunty Rabi yana ‘Yarda Avanue.’ Mama ke yiwa Malam Garba kwatance har kofar gidan. 


Abdul-Rahim dan Aunty Rabi muka fara gani suna wasan kwallo shi da wani yaro dan makotansu, duk da bamu san shi ba, amma tsagin mallancinmu da karan hancin sun tona shi, muka kama shi muka rungume. 


Aunty Rabi ta fito da gudu ta makalkale Mama kamar wata karamar yarinya, tana lale Maman Kaduna, lale da ‘yan Giwa, lale da ‘yammatan Hajjah. 


Ta yi mana jagora zuwa falonta, Yaya 

Muftahu ya fito daga nashi dakin shima yana mana marhaban, nan muka ga yadda ake karrama bako, ko da jini ne ba bako 


ba. 


Kwananmu daya washe gari suka kwashe mu don nuna mana Kano ciki da bai dinta, duka kofofin nan, Kansakali, da Kabuga, Gadon Kaya, Kofar Ruwa, Duka Wuya, Dan Agundi, Kofar Famfo da Na’isa babu wadda bamu ratsa ta cikinta ba mun daga kai mun karanta sunan ta ba. Kofar Nassarawa, Kofar Mata. 


Manyan wuraren tarihin Kanon Dabo irin su Gidan Makama (Museum), gidan Dan Hausa, Dutsen Dala da Gwauron Dutse, Gidan Zoo, Gidan Sarkin Kano da Fadar Masarautar Kano, har gidan Tsumburbura dake kan Dutsen Goron Dutse. 


Haka manyan shopping malls din Kano babu wanda Yaya Muftahu da Aunty Rabi basu kai mu mun ciko ledoji ba, tun daga Sahad, Country Mall, Well Care, Grand Square, Jifatu da Ado Bayero Mall. 


Lallai na yarda Kano ta amsa sunanta ta Dabo-ci-gari, yaro ko da me ka zo an fika. 


Mune har gidan Zoo da gidan Makama 

Museum. Sannan ranar juma’a mika ya da zango a fadar Sarkin Kano Alh. Ado Bayero muka yi gaisuwa ga Dabon Kano, duk da bai sanmu ba, ranar juma’a ya ware ta yana amsar gaisuwar talakawansa Allah ya yi masa rahma (amin). 


Gaskiya mun ji dadin ziyararmu Kano fiye da duk wani gari da muka taba zuwa. Ko da yake mu dama duk yawon namu iyakacinshi Kaduna da Zariya, don haka zuwan mu Kano da kwanaki uku kacal da muka yi tare da Aunty Rabi da iyalinta ba karamin dadinsa muka ji ba. 


Bayan mun dawo Yaya Aliyu ne ya tsaya ya sama mana gurbi a Queen Amina, duk da Yaya Hauwa ta so hanawa Hajjah ta ce ta kyale mu. Muka tattara muka koma muka fara karatu babu kama hannun yaro. 


A hutun karshen zangon karatu na karshe na aji hudu da muka zo, Fa’iz yana makaranta ya kama daki a cikin makaranta. Don haka na saki jiki nake rayuwata cikin walwala da nishadi. 


Ranar wata asabar Baban Kaduna ya zo 


Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...