ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

 ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 5  by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir

- - Post a Comment

 ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 5

by Sumayyah Abdul-kadir


kukan tare. Daga bisani da muka ga kukan ba zai amfanemu da komai ba, Zanirah ta ce, “Mu tashi mu yi sallar nafila mu rokawa Yaya Aliyu sauki”. 


Washe gari su Hajjah za su tafi asibiti da safe na marairaice na ce, “Hajja don Allah?” Ta ce, “Mene ne?” 


“Don Allah zan biku’. 


“Ki bimu ina?” 


“Asibiti wurin Yaya Aliyu”. 


“Ki yi me? Kai Fa’iza da rigima kike, to shige mu je”. 


Ba abin da na dauka illa hijabi da reportsheet dina muka tafi. 


Mun samu Yaya Aliyu yana shan tea da kaninshi mai binshi Mus’ab, ya hada mishi yana mika mishi bired da yankakken dafaffen kwai da (mayonnaise) yana Ci. 


Hajjah ta washe baki ta ce, “A’a, Aliyu lallai jiki ya yi kyau lafiya ta samu. Mus’abu an iya jinya, sai a dage da cin abinci a kan lokaci kuma yadda ya kamata yanzu ko? Tunda an ji kamshin kofar lahira’”’. 


Shi da Mus’ab suka yi dariya, ya sauko 

daga gadon da yake an cire mishi karin ruwan, ya gai da Hajjah. Abin da na fahimta duka hankalinshi kaina yake, na tsuguna na ce, “Yaya Aliyu ina wuni?” 


Ya ce, “Ko dai ina kwana Fa’izah?” 


Hajja ta ce, “Jiya ai Fa’iza da Zanirah basu yi barci ba ina jiyo shesshekar kukansu. Kai, tsakanin Fa’izah da Zanirah ban san wa ya fi son Yaya Aliyun nan ba, ko mi.... Hajja Yaya Aliyu, Hajja Yaya Aliyu ne ya bamu, Hajja Yaya Aliyu ya ce yana gaishe ki.....” 


Na rufe fuska da tafukana cikin jin kunya na ce, “Hajjah ai shima yana son mu ne, yana mana kirki, kuma ya damu damu shi yasa muke son shi”. 


Hajjah ta ce, “To Allah ya bar zumunci, yasa a daidaita da Hafizina tamkar hakan’”. 


A zuciyata na ce, “HAR ABADA Hajjah!” Amma a fili murmushi kawai na yi, zuciyata kamar ta fito ta bakin don haushin kalaman Hajjah. 


Yaya Aliyu ya ce, “Fa’iza_ ina alkawarinmu?” 

Na zaro(report card) dina cikin hijabina na mika mishi, ya duba ya yi murmushi. Hajjah ta ce, “Ai kamar an san za ka tambaya har an fito aka zura da gudu aka koma aka dauko shi, in ce ko dai an yi abin kirki ba irin na baya ba?” 


Ya dago kai yana dariya ya ce, “Anyi da kyau Hajjah, na tara cikin dalibai sittin kinga ko an ka da hamsin da daya”. 


Hajjah ta ce, “Lallat Asma’u za ta yi tsalle (Maman su Zanirah) har ta gode Allah, ita ce mai damuwa da sakamakon Fa’izah a kullum baya kai wa rabin na ‘yan’ uwanta. To takwara fa (tana nufin Ummi)”. 


Na kyalkyale da dariya na ce, “Ta yi na ashirin da daya cikin mutum sittin, ai ta yi kokari domin a primary ana yin magana ko koyarwa da Hausa, a can ko baa yi kuma an kaita ajin kasuwanci, ni kuma ajin Arabiyya ne tuntuni na iya Larabci tun a gida Zaria, shi yasa nake fahimta sosai cikin ajinmu. Amma ka ga sauran subjects din ai duk ban ci da yawa ba”. 


Hajjah ta ce, “Koh? Allah ya taimaka, 

gata nan ta kara habewa ta suntuma kamar yis, sai fada da karfi kamar diyar zaki amma babu karatun a zo a gani”’. 


Na ce, “A’a, Hajjah tana kokari”. 


Duka suka yi dariya ganin yadda na bata rai, don cikin mu ukun nan babu mai son a soki ‘yar’uwarta ko a gabanta balle a bayan idonta. 


Yaya Aliyu ya bar dariya ya ce, “Gaya min Fa’izah ya aka yi suka taho suka barki?” 


Na ce, “Wallahi Yaya Aliyu ba yawo na je ba, na shiga teachers area ne gidan su wata ‘yar ajinmu in kai mata littafinta da na ara, shine da basu ganni ba suka taho suka barni”’. 


Ya ce, “Next time kada ki kara yin irin haka, kin ji na gaya miki, kina wasa da ranki ne da lafiyarki masu muhimmanci ga wadanda ke da bukatar su. Shi kuma da yake babban sakarai ne ba zai iya jiranki ba? Allah Hajjah Fa’iz zai gamu dani da kyar ma in.....” 


“Na kashe zancen nan tun jiya Aliyu, kada wanda ya sake tado shi”. 

Yace, “An barshi Hajjah”’. 


Har yamma muna wajen Yaya Aliyu, wannan ya shiga wannan ya fita. Sai biyar da rabi Aunty Zainabu Maman su Aliyu da Baba Na’ibi mahaifinsu suka zo, sannan muka bisu muka tafi. 


Aunty Zainabu ke tsokana ta, “Fa’izah hutu bai zo da dadi ba, Babban Yaya babu lafiya ina kwanciyar hankali?” 


Baba Na’ibi ya ce, “Ai laifin su ne tunda basa matsawa Yayan yana cin abincin cikin gida sai dai ya basu kwai da Indomie su soya masa, kowa ya gaya musu wannan taliyar abinci ce oho!” 


Na ce, “Wallahi Baba daga yau ba zamu kuma dafawa Yaya Aliyu Indomie ba, durar tuwo kawai zamu dinga yi masa, ko kuwa Hajjah?” 


Hajjah ta ce, “Ni ina ruwana ne?” 


Satin Yaya Aliyu guda a asibiti aka sallame shi. Hutunmu ya ci gaba da tafiya cikin dadi tare da Yayanmu mai son mu Aliyu, wanda shiga goma fita goma in zai yi cikin gida sai ya neme ni, ko ya riko 

min wani abu. Na ci ne ko na amfani, ko wanda zai amfane ni wajen karatu. 


Babban farin cikinmu Fa’iz ané_ jyi balaguro zuwa Kaduna. Duk = gidan ‘yan’uwa mun zaga ba inda bamu je ba sai Kaduna da Zaria. 


Hutunmu ya rage saura sati daya mu koma makaranta Baban ABU ya zo suna hira da Hajjah a falonta muka shigo daga Islamiyya ni da su Zanirah, baki daya muka tsugunna muka gaishe shi, muka wuce dakinmu. 


Ya daga murya yana fadin “Lallai Fa’iza baki da kirki, kika yi tafiyarki Gusau ba sallama, kika dawo shima kina _ shirin komawa ba tare da an waiwaye mu ba ko? Ga su Walida kullum basu da zance sai na yaushe za ki dawo, kin kyauta kenan?”’ 


Na ce, “To Baba ai matarka ce ba ta nemana shi ya sa”. 


Ya ce, (cikin dariya) “Tana neman ki mana, jiya ma ta ce ka ga Fa’izah yau saura sati daya a koma makaranta amma shiru”. 

Na buga tsalle na makalkale shi ina cewa, “Zan bika, zan bika to Baba’. 


Zanirah ma ta ce, “Nima zan biku Baba ka sauke ni gidan Maman Ya Fa’iz (mahaifiyarta)’. 


Ya ce, “Ke fa tsohuwa (Ummi)?” 


Ta ce, “Ni area one za ni”. 


Ya dubi Hajjah ya ce, “Wai me yasa uwata ba ta son gidansu ne?” 


Haka dai muka debi ‘yan kayanmu muka bi Baba. Sai da aka fara kai Zanirah Kaduna (Jabi Road), ko shiga gidan ban yi ba don sanin cewa Fa’iz na nan. Amma Baba na karya kan mota zai fita a get din gidan sai ga shi ya shigo da litattafai a hannu, Baba ya dan rage gudu suka gaisa. 


Wai don ganin idon Babana Fa’iz ko kunya babu ya ce, “A’a, Fa’iza ba za a shigo a gai da Mama ba?” 


Ban ba shi amsa ba na dauke kai. Ummi ta ce, “Ka dai ce muna gaida ta”. 


Baban ABU ya ce, “Kun ci gidanku’. Ya auno mana umbola. “Ku zo har kofar gidan nan ba za ku shiga ku gai da Asma’u ba 

balle kannenku in Yaya Muntari baya nan?” 


Kafin ya rufe baki muka bubbude kofa muka fita, ni kuwa muna dan yin nisa da motar na zura da gudu na je na gai da Maman, sanda suka shigo falon shi da Ummi na sake kwasa da gudu na yi cikin mota kada wata kalma ta hadamu ko ya yi min zalincin nasa. 


Baba bai tsaya shawartar Ummi ba ya ja mota sai unguwarsu gidan Yaya Hauwa, wato gidansu. Ta ce, “Baba me zamu yi a gidan Maman Maryam?” 


Ya ce, “Haba Ummi, kowa na marmarin ganin uwarshi wata da watanni bai ganta ba, in ke bakya marmarin ganinta to ita tana bukatar ganin ki ko?” 


Ta zumbura baki irin na ‘yar fari, “Baba ‘ya’yanta fa fitsarin kwance suke yi, su bi duk su jike ni in na yi zarni a ce nice”. 


Ya ce, “To ai ba sai kin kwana ba, ku je zan jiraku ku gaida su ku fito mu tafi (Area One) din (gidanmu)”. Nan muka kama murna muka fice. 

Aunty Hauwa na tsaye jikin famfo tana wanke (under wears) din yaranta muka yi sallama da babbar murya. Ta saki wankin ta bude hannuwa ta rungumemu duka, fadi take, “Ka ga ‘yan Gusau an cakare har an cake! Irin wannan gayu haka kamar ba goyon tsohuwa ba”. 


Muka kyalkyale da dariya. Na dubi jikinmu ni da Ummi, ni kaina na san mun yi kyau. Wani riga da wando ne da mayafi ‘yan (Lahore-Pakistan a jikinmu, na jikina yellow na Ummi_green, — gashin kowaccenmu babu kitso kalmashe cikin tafkeken ribbon kalar kayan kowacce, wanda dama mahadin kayan ne tare ake sai dasu. 


Ashe Baba wayo ya yiwa Ummi, sai ga Yusuf da kayanmu ya shigo dasu wai Baba ya ce sai gobe zai zo ko ya turo direban makaranta ya tafi damu. 


Da daddare bayan cin abincin dare muka shiga bai wa Yaya Hauwa labarin rayuwar bording school daga A-Z, sam ban yi zancen Fa’iz ko halayen da yake nuna min da wani jininmu ba, ko da wasa ban taba yi 

ba. Haka abin da ya yi min ranar hutu, balle wanda yake yi min a Giwa. 


Haka Ummi ba ta tada zancen ba, ko da Yaya Hauwa ta sako sunan Ya Fa’iz cikin hirarmu bana tankawa (wannan_ shine babban kuskuren da na yi at the first place), ko kuma na kare shi idan Ummi ta so fadin rashin kirki da rashin alherinsa. 


Sai lokacin Baban Ummi Alh. Sabi’u ya shigo gidan, Sabi’u Kwangila shi ke rike da (Bamalli Farm) gidan gonar A.B Family dake cikin garin Kaduna, inda ake kiwon poultry da noman kayan marmari. Shi din kuma babban dan kwangila ne na karan kansa. 


Daidai gwargwado suna cikin rufinasirin Allah, ba abin da suka nema suka rasa, don ita ma Yaya Hauwa babbar ma’aikaciya ce, principal ce a makarantar Sarauniya Amina. 


Mahaifin Alh. Sabi’u shine babban aminin marigayi Abubakar Giwa, idan da wanda za a ce ya yi auren bare, ko ko auren da ba na jini ba to Aunty Hauwa ce, sai dai zumuncin dake tsakani irin tun na kuruciyar nan ne wanda aka zama tamkar 

jini daya. Ba shi kuma da niyyar yi mata wani abu wai shi KISHIYA, kamar yadda ya fahimci ba a yi sam a zuri’ar A.B Giwa, one-man-one-wife-one-life! 


Baba Sabi’u ya zauna gefen Aunty Hauwa ya ce, “Ummi ai mun yi fushi, tafiya ba sallama, dawowar ma sai da muka ci arzikin Zanirah, na tabbata da ba ta zo Kaduna ba ke da Fa’iza ba za mu ganku ba”. 


Ummi ta ce, “Don Allah Baba ka yi hakuri, wallahi ziyarce-ziyarcen ne ya yi mana yawa”’. 


Ya ce, “Ai dole duk inda hakuri take in je in sayo ta in hadiya. Ya ya jarrabawa? Ta nawa-nawa aka yi?” 


Ummi cikin doki tace, “Wallahi Baba ta ashirin da daya na yi’. 


Ya yi salati ya ce, “Allah ya yaye miki wautar da ke kanki Ummi, wallahi ki kama kanki, ki nutsu ki shiga cikin taitayinki, lokacin abu ayi shi in ya wuce ya wuce kenan”’. 


Ummi ta bata rai ta ce, “Baba na fa yi kokari na dauka za ka yaba min ne, a 

primary 40 fa nake yi”. 


Ya ce, “To da dan dama-dama sai a kara dagewa”. 


Washe gari da yamma Baban ABU bayan ya taho office gidan ya biyo har da kanwata Walida da Abdallah a _ bayan motar. 


Baba Sabi’u ya yi mana provision sosai, har da Zanirah da ba ta nan bai ware ta ba. Sayayyar da ya yi mana ko da Yaya Aliyu zai kara sai dai ya kara kadan. 


Muka nufi Zaria cike da farin ciki. Ita kanta Ummi sai na ga tana wani nishadi da annashuwa na musamman, na ce, “Yar banza ashe kina son su Yaya Hauwan?’ 


Ta ce, “To Fa’izah akwai wanda bai son mahaifan shi ne?” 


Na ce, “Ba gaki nan ba, sai an miki dabara za ki gun iyayenki’”’. 


Ta ce, “To ke kuma fa?” 


Na ce, “Ai ni dole ce tasa na barsu kema kin sani”. 


A gidanmu Momi na kicin tana girki muka yi mata sallama, ta washe baki tana yiwa Ummi sannu da zuwa ban da ni. Na ruga na rungume kugunta na ce, “Momi ni bakya nemana ko?” Muryata kamar zan yi kuka 


Ta yi ‘yar dariya dauke da wata irin matsananciyar kauna_ cikin kwayar idanunta, ta ce, “In neme ki in miki me? Su Walida basu ishe ni ba kenan?” 


Sal a lokacin na ga cikin Momi ya zama kato ya turo zani har baya kulluwa, na ce, ‘““Momi haihuwa za ki yi?” 


Ta ce, “Me kika gan?” 


Na ce, “Cikinki na gani ya kumbura suntum”’. 


Ta yi tsaki ta fice ta bar min kitchen din tana cewa da Ummi ta kashe mata heater din ruwan zafi mu fito mu rufo kofar kicin din. 


Walida ta zo kunnena ta rada min cewa, “Baba ya ce kanwa ko kani Momi za ta haifowa Kausar’”. 


Muka kyalkyale da dariya. Dariyarmu ce ta sata juyowa ta dube mu, ta girgiza kai tana murmushi, na san sha’awa muka ba ta. A kullum ni da Walida kamar ‘yan biyu 

muke, domin Walida akwai manyan barage, sai dai ita fara ce tas ni kuma ina da duhu. 


Da ganin Walida ka san za ayi babbar mace mai babban jiki nan da ‘yan shekaru, ba mai cewa Abdallah ya girme mata da shekaru dai-dai har uku, don ni kaina ta dara ni jiki da tsaho. Haka yadda muke kaunar junanmu duka abin sha’awa ne wurin Mominmu da ta haife mu ma balle ga sauran al’umma. 


Duk kawaici irin na Momi a wannan hutun na fuskanci ta ji dadin zuwana, domin ban taba kai wa irin tsahon wannan lokaci ban je ba. Kwananmu biyar muka juyo Giwa da tarin tsarabarmu na tafiya makarantar kwana. 


A can muka tarar da Zanirah ta riga mu dawowa tuntuni. Washe gari Yaya Aliyu ya mai damu makaranta, amma duk da kayan da muka samo bai rage komai ba a sayayyar da ya saba yi mana, bai fasa komi ba. 


To haka rayuwa ta ci mana gaba tsakanin 

gida da makaranta. Duk burin iyayenmu ya ta’allaka ne a kanmu mu ukun nan da burin gina mana =ingantacciyar rayuwa, kasancewar mu ‘yammata matasa kadai dake gabansu. 


Kauna ce muke gani daga kowanne bangare na iyayenmu, gata na duniya babu irin wanda bana gani daga iyayenmu, da kakarmu Hajjah da babban Yayanmu Aliyu Haidar. 


Wannan ne dalilin da yasa muka kara zage damtse don mu fita kunyarsu mu ba mara da kunya, mu nuna musu ba a banza suke wahalar da suke yi damu ba, we will insha Allah make them to be proud of it ta hanyar kara zafafawa kawunanmu da karatu. 


Sai dai gatan da ake nuna mana baya shafar tarbiyyar da muka taso a ciki, muka gada iyaye da kakanni, muka kuma tashi muka ga ana yi cikin gidanmu tuntuni. 


Ta fannin Yaya Aliyu, ya kara zage damtse da kokarin ganin na kara hazaka sosai da hikima da basira irin nasa. Ba zan manta ba a second term (zango na biyu) da 

na kai masa sakamakona na yi na shida, ya nuna min bacin rai sosai, ya daina kula ni, ya daina shiga sabgata, ko kallon inda nake ya daina. Ya daina sayo min gasasshen naman da ya zame min kamar taba. 


Maimakon hakan duk ya koma yiwa Zanirah wadannan abubuwan a madadina, ita da ta kawo (second position), duk na bi na damu, na shiga cikin kunci da takura na babu gaira babu dalili. 


Wannan ne ya zaburar dani na takurawa kaina da karatu a zango na gaba, iyakar ilyawata na kawowa Yaya Aliyu (3'4position out of 60). Yaya Aliyu ya daga ni ya yi sama yana juyi dani a falon Hajjah, kayan dadi da nama kuwa sai da Hajjah ta yi ta fada tana zai sangarta ni, in na auri wanda ba shi da halin ciyar dani nama kullum fa? In shiga raina abin da ya kawo mani?” 


A zangon farkonmu na sabon aji JSS 2, su Momin ABU, Maman Kaduna da Yaya Hauwa, Aunty Zainabu da matar Baba Barau Aunty Marwa, da matan su Baba Sadi duk suka yo Bus guda suka kawo Post a Comment for " ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...