ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 4 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 4

ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 4

- - Post a Comment

 ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 4


Sy. Ya rufe boot din motar ya shiga Mazaunin shi zai ja motar. 


Ummi ta ce, “Ya Fa’iz, Fa’iza fa ba ka ganta bane?” 


Wata muguwar harara ya yi mata, ya ce, “In na ganta sai me? Sai me zan yi? Ita ba ta ganin mutane? Ba ta san ta gaishe su ba ko don UWARTA! Ta koya mata rashin tarbiyya irin tasu ta kabilu”. 


Sai kawai ya ja motar ya badeni da kura. Ummi kira take “Fa’iza! Fa’iza!! Fa’iza!!!’? Amma ko sauraron ta bai yi ba. 


Na durkushe a nan na soma kuka, na yi kuka har muryata ta dashe. Na daga kai na dubi dai-daikun daliban da suka rage kwata-kwata babu ‘yan Kaduna, Zaria balle garinmu. Daga ‘yan Kano sai ‘yan Jigawa, sai ko dai-daiku daga jihar Gombe da Adamawa. 


Na dora hannuna aka na rafsa kuka. Duk dokina na son ganin Hajjah, Zanirah da Yaya Aliyu ya gushe, sai wani irin tukuki da zuciyata ke yi. 


Wannan wace irin kiyayya ce Ya Fa’1z ke 

min? Wace irin kiyayya yake yiwa mahaifiyata da ta shafe ni? Wannan ma ai rashin imani ne ba kiyayya ba. Duk irin kin da nake wa Fa’iz babu yadda za ayi in baro shi a jejin da na san ba shi da kowa, a gari mai nisa da babu kowa nashi. 


Na rasa inda zan sa kaina don bakin ciki, kawai sai na samu gefen bishiyar darbejiya na share na kwanta a wurin ina kuka. Ina addu’ar Allah ya kashe Fa’iz in huta. 


“Ke me kike a nan a kwance a kasa? Ko ba a zo daukar ki bane?” 


Muryar wata malama ta doki dodon kunnena. Na dube ta idona jage-jage da hawaye na ce, “Eh”. 


“Yar wane State ce ke?” 


“Na zo ne daga Giwa”. 


“Giwa? Giwa ta jihar Kaduna? Oh! Ke Bamalliya ce ko?” 


“Eh”. Na amsa a gajarce. 


“Amma kin yi nisa sosai, yanzu ya za ayi kenan?” 


Na ce, “Zan kara jira a nan zuwa yamma na san za a ZO min”. 

Ta ce, “Ba zai yiwu ki yi ta zama ke kadai a nan ba, ki tashi ki shiga daga Library tare da yaran can ‘yan Niger State, kinga za ki fi hango duk mai shigowa ki fidda naki”’. 


A sanyaye na ce, “To”. Na mike na kade jikina na dauki jakar littattafaina na rataya, da yake duk sauran kayan sawarmu suna cikin kayan da Ummi ta tafi dasu. 


Ban dade da zama ba barci ya dauke ni a kan daya daga cikin kujerun labiraren, na farka ne karfe biyar na yamma sakamakon tashin da wata yarinya ta yi min wai in tashi in yi sallar la’asar. 


Sai kawai na fashe da kuka ganin yadda duhun yamma ya lullube sararin samaniyar subhana. Na bita toilet din dake jikin labiraren muka dauro alwala muka yi sallah, ni azahar ma sai a lokacin na yi ta. Har na idar da sallah kuka nake. 


Ta ce, “Ki daina kuka, ai tabbas za a zo daukar mu ne, kema da baki da nisa kamarmu? Ai iyayenki babu yadda za ayi su manta dake”. 


Cikin kuka na ce, “An zo an dauki Ummi, 

ni tafiya ya yi ya barni, in Allah ya yarda ba zan dawo makarantar nan ba....” 


Shigowar daya daga cikin masu gadin makaranta yasa muka yi shiru muka zuba mishi mayunwatan idanuwanmu da yunwa da damuwa suka hadu suka jeme su, ya kira yarinyar nan wadda da alama ta girmeni cewar ta zo an zo daukar ta daga Adamawa. Ta fita tana daga min hannu har ta kule. 


Na kifa kaina cikin cinyoyina na ci gaba da kuka a hankali, ban san sanda sarkin barayin ya Zo ya Sake sace ni ba. 


Karfe bakwai na magariba na farka sakamakon azababbiyar yunwar da ta sake murda min ‘ya’yan hanjina, don saboda dokin zuwa gida ko karyawa(break fast) bamu tsaya mun yi ba saboda tunanin tuni Hajjah ta gama _ shirin karbarmu da hadadden girkinta. 


Na dafa cikina da hannuna daya na runtse idona da karfi, ganin yadda duhun dare ya mamaye Sararin sama, hawaye suka ci gaba da yi min lugude a fuska. 


Hannun mutum na ji ya cira ni tsaye, na 

bude ido firgigit na mike a razane cikin fadin “Wayyo Allah..... wayyo Hajjah....” Abinki da cikin da ba komai, sai hajijiya ta kwashe ni yuuuu! Gaba daya na fada ga mutumin da ke tsugune a gabana, na daddage na kara sakin ihu.... 


“Wayyo Hajjah na shiga uku na lalace.... na mutu!” 


Ya rungumeni sosai a jikinsa yana fadi cikin tattausar murya irin ta marasa koshin lafiya, “Relax, relax Fa’iza, relax”. 


Na dauki lokaci ina tunanin mai muryar, kwakwalwata ta shiga tariyo min inda na san mai murya mai taushi da rashin amo. In ban yi kuskure ba zan iya cewa ta YAYA ALIYU CE.... YA YA ALIYU HAIDAR NA’IBI A.B GIWA. 


Na lumshe idona na dan lokaci, bugun zuciyata na saisaita da zazzafan jikin Aliyu, zuciyata da ta yi zafi na yi min sanyi kadan-kadan. 


Tsayin minti biyar Yaya Aliyu na rike dani, ya ce cikin kankanuwar murya, “Fa’izah are you ok?” 


Na gyada kai, ya sake ni muka mike a 

tare yana rike da hannuna. Ya dauki jakar litattafaina da daya hannun nasa na hagu muka fita daga dakin karatun, ya bude gidan baya na shiga, ya fiddo cooler din abinci ya bude, kamshin girkin Hajjah ne ya doki hancina, ba girkin cikin gida ba, wannan girki ne da take yi lokaci zuwa lokaci da hannunta, da na dade da sani ya baibaye ni, ya tado min tsohuwar yunwar da na wuni da ita. 


Yawun bakina ya wani irin tsinke tun kamin in kai lomar farko sanda Yaya Aliyu ke zuba min a farantin cin abinci (plate), dafadukar shinkafa ce da aka yi rabinta da zallar tsokar kaza da ganyen alayyahu da kabeji. 


Ya bude wata foil paper din ya fiddo gasasshen naman nan na kan hanyar Gusau da ya saya mana a hanya a zuwanmu, duk ya ajiye min ya rufe kofar ya shiga mazauninshi ya ta da motar muka soma tafiya. 


Bayan ya miko min robar ruwan swan mai sanyi ya ce, “Kina iya kwanciya idan kina jin barci in kin gama”. Da gudu ya fizgi motar bayan ya daga ma masu gadi 

hannu ya kuma yi signing shaidar cewa an dauke ni. 


Amma fa ya sha fada daga malamin da ke kula da shige da ficen dalibai, har ya bawa uku lada. Magana daya yake fadi masu su yi hakuri ba laifinsa bane. 


A yayin da wata danja ta tsai damu kusa da wata fitila mai hasken gaske, garin kalle-kallena mai nuna ciki ya dauka na fara dawowa hayyacina, na dubi hannun Yaya Aliyu wanda ke bisa giyar motar, allurar karin ruwa na gani soke jikin jijiyar hannunsa jini na diga amma bai kula ba, tukin shi kawai yake. 


Da na kura ido sai na ga hanyar karin jini da wata siririyar allurar ita ma soke duka a hannunsa ya bi fatar jikinsa ya kwanta. Na dube shi a razane domin tun zuwan shi ban ga fuskarshi ba, ya rame sosai ya yi duhu ainun. 


Na daga murya da karfi cikin tashin hankali na ce, “Yaya Aliyu ka tsaya’. Ba tare da ya juyo ba, haka nan ban ga annuri a kyakkyawar fuskarshi ba ya ce, “A kan 

me zan tsaya? Bakya ganin tafiyar dare zamu yi?” 


Na ce, “Ni dai na ce ka tsaya ko? Baka ganin hannunka yana jini ne?” 


Ya ce, “Babu komi wannan, kina so mu yi kwanan hanya ne?” 


Na ce, “Eh, mu yi ba komai”. 


Maimakon ya tsaya sai ma ya kara ware speed zuwa (200), kada ki ga yadda ‘yan idanuwana suka yo waje, suka yi kwalakwala. Cikin kuka na ce, “Yaya Aliyu baka da lafiya.... you are bleeding....” 


Ya ce, “Don Allah don Annabi Fa’iza ki saurara min, da me zan ji ne? Insha Allahu lafiya zamu je gida babu abin da zai faru sai wanda Ubangiji ya riga ya kaddara”’. 


“To ka tsaya in cire maka allurar...” 


“Na ce ki barshi ko dole ne?” 


Yadda ya yi min maganar cikin tsawar da bai taba yi min ba ya sanya hantar cikina kadawa, ban kara tankawa ba don na lura yana cikin wani irin yanayi (tension) mai wuyar fassaruwa. Bai tsaya ba sai a Giwa, harabar adana motocin A.B Bamalli Estate. 

Tsakar dare muka iso gida, yadda na ga mazan Estate din duka a tsaye cirko-cirko manyansu da samarinsu a kofar gidan hajjah ya tabbatar min babu lafiya. 


Baba Barau ya hau shi da fada, cewa yake, “Baka da hankali ne iye Aliyu? Halaka kanka kake so ka yi? Wannan wace irin wauta ce ka cizge karin jini da na ruwa ka bar gadon asibiti, ce maka aka yi duk cikinmu an rasa mai zuwa dauko Fa’iza daga makaranta?” 


Aliyu zai wuce su kwayar idonshi na neman rufewa, ya yi kokarin yin magana amma ya kasa. Ganin yana neman shan kasa Baban Giwa ya kama shi, shi da Baba Salisu suka mai da shi cikin motar da ya fito bai samu ya rufe ta ba. Baba Salisu ya ja motar aguje suka fice da shi asibiti. 


Ni dai na shige cikin gida sai kuka nake saboda halin da na ga Yaya Aliyu a cikia dalilina. Hajjah ta taso ta rungumeni ta ce, “Baki kyauta ba Fa’iza, don me za ki tafi yawo a neme ki a rasa? Ga shi kin ta da hankalin dan’uwanki yana kwance asibiti amma daga jin labarin nan ya tsinke karin 

ruwan da ake masa ya dauki mota kamin kowa ya farga ya fice ya biki’”. 


Na dubi Ummi dake zaune da mamakin sabon sharrin Ya Fa’iz, ta sunkuyar da kanta. Na ce, “Ni Fa’izar ce na tafi yawo Hajjah?” Muryata kamar na aro, kamar ba tawa ba. 


“Kyale ta kawai Hajjah, babu inda ni da malaminsu bamu duba ba cikin makarantar nan amma yarinyar nan kamar aljana sama ko kasa an rasa ta’. 


Hajjah ta ce, “To ai shi kenan zancen ya wuce tunda dai an zo lafiya alhamdulillahi, Sai a kiyaye gaba. Ke Fa’iza jeki ki watsa ruwa ki ci abinci kafin asubahi ta karasa’”’. 


Na juyo da idanuna a hankali na dubi Fa’eez dake tsaye jikin bangon falon sai murmushi yake yi mai taushi, da idanuna da suka jawur na ce, “Kwarai, baka ganni ba Yaya Fa’iz, amma rabbil samawati wal’arshi shi yana ganinmu, kuma shi ya san abin da ke boye da wanda yake a sarari. Wata rana na zuwa da zai bayyana shi fili kowa ya gani”. 

Na wuce toilet abina yana fadin “Me kike nufi? Karya nake miki kenan?” Ko juyowa ban yi ba na shige toilet na rufo kofar da karfi. 


A zuciyata tausaya mashi nake kan halin da ya jefa kanshi a ciki, shin meye amfanin wannan kiyayya da yake nuna mini? Ya san girman ZUMUNCI a cikin addinin Islma kuwa? Me kiyayyar da yake yi min da hakan da yake yi min za su amfane shi da shi? A ce mutum sam-sam baya tsoron Allah a al’amarinsa sai Hajjah mutum ‘yar adam? 


Ni kam gani nake in an boye ma Hajjah da sauran mutane abu ko gaskiyar abu ba za a boyewa Allah ba, Allah ka shirye shi, ka ganar da shi illar karya da cin zarafin dan’uwa musulmi ba ma dan’uwa na jini ba. 


Na kwanta barci a wannan daren amma sam na kasa, tunanin shin wane halin Yaya Aliyu ke ciki a asibiti shi ya addabe ni? Me ya same shi? Me yasa ya boye min cewar ba shi da lafiya? Me ya tunzura shi ya yi fushi haka irin wanda ban taba gani 

daga gare shi ba? 


Na san dai ba zai wuce abin da Fa’iz ya yi mani a yau ba. A zahirin gaskiya ina tausayawa Fa’iz idan Yaya Aliyu ya fahimci cewa da gangan ya gudo ya barni. 


A wasu lokutan Yaya Aliyu na (acting according to) sunansa (mafadaci ne kamar kowanne mai suna Aliyu zakin Manzo). A duk lokacin da ya shiga irin wannan tension din babu mai iya tausasa shi sai Baban ABU wato (mahaifina). 


Tsorona Allah tsorona kada na zama silar wargaza zumuncin dake tsakanin Yaya Aliyu da Yaya Fa’iz (Mai sona da mai ki na). Don haka ya zama dole in kare Fa’iz albarkacin ZUMUNCI. In boye abin da ya yin wanda ba Aliyu kadai zai batawa rai ba har Hajjah dake matukar girmama shi da lyayenmu maza. 


Dan’uwa kowanne iri dan’uwa ne wanda na sani na kuma tabbata cikin familydinmu babu irin wannan hatsaniyar, ba zan so kuma in zamo silar ta ba. 


Na juya ga Zanirah dake gefena tana barci, sai na ga ashe ba barcin take ba 

sharar hawaye take yi. Na ce, “Ba kj yi barci ba Zanirah?” Ta ce, “Eh”. Na leka fuskarta sosai na ce, “To shin Zanirah me kike wa kuka?” 


Cikin dasasshiyar murya ta ce, “Yaya Aliyu? Shin ko a wane hali yake yanzun?’” 


Na ce, “Wai me ke damun shi ne Zanirah? Wane irin ciwo ne ya cucemu haka ya kwantar mana da Yayanmu Aliyu?” 


Ta share hawaye da bayan hannunta ta ce, “Yana da (ulcer) ne ba tun yanzu ba, ba ta tashi kada shi ba sai a ‘yan kwanakin nan muna makaranta, nima da Hajjah ta je mun (visit) take gaya mani. Ya dade a kwance, domin ta ci karfinshi sosai. Ana 1 gobe zamu dawo Hajjah ta ce numfashi ma sama-sama yake yinsa da taimakon oxygen a asibiti. 


Sun samu sun fara shawo kan matsalar aka daura mishi ruwa da jinin da kika gani, lokacin ni Yaya Sani ya dawo dani gida kowa da kowa yana asibitin, wurin azahar Fa’iz da Ummi suka shigo, mu duka muna waje suka shige ciki wurin Hajjah. Babu 

abin da Yaya Aliyu ya soma tambaya sai ina ka baro Fa’iza? Ya ce, “Wai bai ganki 


Wallahi sai ya tsinke jinin da ruwan ya dauki flask din abincin da Hajjah ta kawo mishi a lokacin ya fizgi mukullin motarshi hannun Ya Fa’iz, bai hana shi ba, shima sai ya yi ficewarsa. Abinki da taron mata babu wadda ta yi tunanin hana shi (tsai da shi), musamman a cikin yanayin fusatar da yake. 


Ya yi waje, Hajjah na kira da su Inna Kaltume amma bai ko waiwaye su ba, kuma babu mai ilimin kiran likita ko nurses a cikinsu balle kiran security na bakin gate. Ya tashi motar suka bude mai ya fita ya tafi dauko ki, shima Ya Fa’iz tafiyar sa ya yi......” Ta ci gaba da kuka, nima haka. 


Cikin kuka na ce, “Yanzu Zanirah a ganinki abin da yayanki ke yi a kaina, ko in ce nau’in zumuncinsa gareni yana kyautawa? Zan rantse miki da _ sarkin sarakuna Fa’iz da niyya ya taho ya barni a 

Gusau”’. 


Zanirah ta zaro ido, ta ce, “Shi Yaya Fa’iz din?’ 


Na yi mata alamar ta yi a hankali kada Hajjah ta ji. Na ce, “Kin san Allah ina tsaye gabansa ya ja motar suka tafi, wannan meye in ba kiyayya ba? Me na yiwa Yaya Fa’iz ya tsane ni a dangi Zanirah? Fa’iz ya nuna bai damu da rayuwata ba, ko da na bi wasu can sun sace ni ba asarar shi ba ce, ko da na fito daga cikin makaranta na bata bai dame shi ba, ko da yunwa za ta kashe ni ba ruwansa bane. 


Amma don Allah don Annabi Zanirah kada ki fadawa kowa tunda na kudurta zan rufa masa asiri wurin Hajjah da Yaya Aliyu to zan yi, bana so a samu kuskure daga gare ni kan kiyayyar da Yaya Fa’iz ke mani, na tabbata wata rana Allah zai bayyanawa duk dangi cewa, Ya Fa’iz bai dauke ni ‘ya a cikin gidan nan ba a kan dalilin da ban sani ba”. 


Sai na ga Zanirah na hawaye, muka yi ta 


Post a Comment for "ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 4"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...