Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

ZABIN MAHAIFINA COMPLETE

ZABIN MAHAIFINA COMPLETE

- - Post a Comment

 ZABIN MAHAIFINA COMPLETE


A fusace ya shig0 gidan yana faman kwalla mata kira kamar gidan zai tarwatse saboda tsabar ihun da yake yi, ke saude! Ke saude! Cikin hanzari ta fito daga daki tana amsa kiran da yake mata. Gani mallam ta fada tana karasowa  ya kalleta cikin daure fuska sannan yace se yanxu kikaga damar amsawa? Cike da ladabi tace kayi hakuri mallam wallahi sallah nakeyi shiyasa. Dan ta6e baki yayi sannan yace ina salma take? Ki gaya mata zatayi bako anjuma kuma saura yazo taki fita wallahi ranta seya baci dan nagaji da ganinta a gabana ba miji.

Inna saude ta kalleshi sannan tace haba mallam aure ai lokaci ne idan lokacinta yayi ko tana s0 ko bata so xatayi ai... Cikin jin haushi ya katse ta ke saude na dade da sanin ke kike zugata to bari na fada miki a wannan karon na tsaida magana. Na riga nayima salma miji ke baki isa na canja maganata ba  kuma ki ja mata kunne k0 tana s0 k0 bata s0 se anyi aurennan. Inna saude tayi kasa da muryanta tace dan Allah mallam kayi hakuri ni ban isa na zuga salma akan ta bijire ma umurninka ba sbd ni da ita duk a karkashin ik0nka muke, kuma insha Allahu salma bazata watsa maka kasa a ido ba kayi hakuri. Jin abinda saude tace ne yasa mallam amadi sassautawa sannan yace ai kene saude da wata irin magana ya zango ina miki maganar nayi mata miji amma kina cewa aure lokaci ne, ai lokacin yayi kenan tunda har na zabo mata mijin daya dace da ita. Gidan da zata je ta huta k0mai se anyi mata ba tare da tasha wuya va. Inna saude ta matso tana cewa  mallam irin wannan k0dawa se kace wanda zata auri govenor
DOWNLOAD HERE👈

Post a Comment for "ZABIN MAHAIFINA COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...