YAWON SALLAR HAJIYA IYA COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YAWON SALLAR HAJIYA IYA COMPLETE

YAWON SALLAR HAJIYA IYA COMPLETE

- - Post a Comment

 YAWON SALLAR HAJIYA IYA COMPLETE


Gudu yakeyi iya karfinsa amma saboda yanayin girma ga tsufa lokaci guda suka cin masa.


A tsakiya suka saka shi suna kokarin rike hannuwan sa, dan tsoho yayi wani kukan kura cikin karaji irin yanda jariman india sukeyi idan suka fusata, yasa gwiwar hannuwan sa ya kai musu duka yana fadin, " wallahi bansan da makiya nake tafe ba sai yanxu idan kuka maidani cikin motar nan ban yafe muku ba.


Ku sake ni na karasa bichi a kafa, idan kuka kaini mota wallahi alhakin mutuwata a wuyanku yake, cikin hanzari suka kara matsowa zasu kama dan tsoho, aykuwa ya yi sauri ya matsa baya hadi da buga kafa daya, ya kara kwalla kara yana fadin, " yeeeeeeeee ku matsaaaaaaaa ko in ma ke kuuuuuuu, ya karasa fada yana dunkule hannuwa har huci yake.


      Daya daga cikinsu ya kallin dayen yace,  " wai kuwa Anya bazamu kyale tsohon nan ba yaje yayi ta tafiyarsa, tunda anasan ceton rayuwarsa yana san yayiwa mutane illa, kana ganin yanda ya kaimun duka a gefen fuska badan na kauce ba da ya gwabjeni yayi mun mahangurba,     " kai haba yanxu tsohon nan ne zai gagaremu, idan aka ce mun kasa kamo shi ba muji kunya ba dan Allah rabu dashi bari kaga muma karfi zamu nuna masa, muna zuwa ciccibarsa zamuyi farat daya  zamuyi masa.


     Aykuwa suka tunkari dan tsoho me buhu, yana ganin sunyo kansa gadan-gadan ya fara kai duka ta ko ina, yana yi yana ja baya sai kuma yayo gaba kamar zai doko wani daga cikin su, yan da kasan yana filin danbe.Basu bi ta kansa ba, sukub haka suka sun kuci dan tsoho suka mammakure hannusa a hammatarsu sai wutsul-wutsul yake da kafafuwa, yanayi yana wani karaji shi bai yarda ba dole kwacewa zaiyi daga hannunsu.


Bakin motar suka karaso suna kokarin saka dan tsoho sai fisgewa yake yana ciccijewa har suka samu suka tura shi ciki, wani daga gefe ya dan leko su yana fadin,  " to ita ma iya ku sata aciki man, kunga kun huta, idan fa kukayi sake tsohon nan ya kubce wallahi dawa zai shiga, dan na lura motar nan ta tsora tasu dayawa,  juyawa sukayi zasu dauko hjy iya.πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

      πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

      πŸ‘œ

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_)

_15/6/2020_

πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

         πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

     πŸ‘œ


*Written* by _Ameera_ _Adam_ { _Mom_ _Aslam_ }

    

    πŸ“š *HADAKA*πŸ“š

   πŸ“ *WRITER'S*πŸ“

πŸ–Š️ *ASSOCIATION* πŸ–Š️

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

@: *Facebook*

_HADAKA_ _WRITER'S_ _ASSOCIATION_


@: *wattpad*

_AmeeraAdam60_


*SADAUKARWA* *GA* *DUK* *MASOYA* *NA* 😊🀝🏻

_Wannan_ _labarin_ _kirkirarre_ _ne_ _banyi_ _shi_ _dan_ _wani/wata_ _ba._

       3&4

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


Subhanallahi nikam me nake gani ni jikar indo, yau ni ce da gudawa a zani, " aykuwa naga ta kaina, " hjy iya ke sallalallami lokacin da takai bakin kofar toilet, " jin cikinta ya kuma hautsinewa da sauri ta banka kofar toilet ta shige.

*BAYAN* *WANI* *LOKACI*

Hajiya iya ce kwance akan carpet magashiyan, jikinta duk ya mutu ba kwari, " cikinta ne yake yamutsawa amma karfin jikinta ya kusa karewa, a hankali ta tashi zaune da rarrafe ta karasa toilet din, "zuwa wani lokaci ta fito da kyar take tafiya tana dafa bango har ta fito babban falon ta, cikin kasalalliyar murya take kwalawa inna zainabu kira, " zainabu  πŸ—£️zainabu magana fa nakeyi hansai wai duk ba me ji na, "sai kace masu baccin mutuwa suwaiba suwaibaπŸ—£️ wai duk babu me ji na ne?


Audi me gadi ya fito daga bandaki sama sama yakejin muryar hjy iya tana magana da hanzari ya karasa falon ganin hjy iya daga ita sai riga da dan tofi yasa shi saurin juyawa, a hankali hjy iya ta kirashi,  "Audi jeka kiramun zainabu kace ta xo yanxu, to hjy amma ina fatan lafiya dai ko, dan na lura kamar akwai abunda yake damunki, " Audi nace ka kiramun zainabu, hjy iya ta fada a kufule, to ayi hakuri hajiya, yana gama maganar ya fita da sauri.+


*BA'A* *DAUKI* *LOKACI* *BA*

sai ga inna zainabu da Audi me gadi sun shigo da sauri, hajiya iya ance kina nema na Allah sa dai lfy, kafin hjy iya tayi magana audi ya karbe hjy iya zan iya tafiya ko akwai abunda zan taimaka muku dashi dan naga kamar kina bukatar taimako? Audi  ka kwana anan kaji, idan akwai abinda zakamun zance maka ka kiramun zainabu ne, dauko shinfida ka kwanta idan muka gama abunda zamuyi sai ka tafi sakaran banza sakaran wofi wuce ka bamu guri, "sum sum sum sum Audi ya wuce be kara magana ba.


Zainabu wlh cikina ne ya lalace tun dazu naketa bayan gida har saida na bata kaya na, matso indafa ki mu je ciki ki gyara gurin dan karfina duk yayi kasa, "zainabu cikin zuciyarta take fadin inbanda rigimarki hjy kinci alala ta sakar miki ciki  kuma kin matsa amiki lemon tsamiya ba dole ciki ya lalace ba idan anyi mgn kuma cibi ya zama kari..........


zainabu wuce muje cikina na motsamun kinyi kikam kamar gunki, hjy iya ta fada cikin fada, "to hjy kuma kinsha magani kuwa? Zainabu wannan jawabin sai na fito kyayimun shi, inna zainabu kama hannunta tayi suka wuce ciki.

Inna Zainabu ba ita ta gama gyara dakin hjy iya ba sai kimanin karfe 1:30am lokacin hjy iya har ta samu ta kwanta, gudawar tayi sauki sakamakon maganin da tasha.


Hjy iya nagama zan iya tafiya? Eh zainabu jeki Allah yayi albarka amma karki tasheni da asuba jikina duk ba dadi bazan iya azumi ba, to shikenan hjy iya Allah ya tashemu lfy, 'Aameen ki jamun kofa iya ta bata amsa.


*WASHEGARI*

Kimamin karfe tara na safe hjy iya na kishingide a falonta tana jin radio, karar bude get taji daga baya ta ji shigowar mota, "ba'a dauki lokaci ba taji sallamarsa cikin falon, "barka da safiya hjy iya da fatan kuntashi lfy? Cikin girmamawa habibu ya tsugunna yana gaida mahaifiyarsa.


Lafiya klau muka tashi habibu ni ce ma banji dadi ba jiya da daddare cikina ya dan baci amma da sauki dan yau ma ban iya daukan azumi ba, subhanallah hjy iya me kika ci hk me yaran nan suka girka jiya? A'a ba wani sabon abu suka dafa ba kasan larura idan Allah ya kawo basai kaci wani abun ba, " to ko zamu je asibiti kinsan gudawa cin karfin mutum take inyaso sai su dubaki su rubuta miki magunguna, " haba habibu gudawar ce sai munje asibiti nasha magani kuma ta tsaya.

To shikenan Allah kara afuwa amma zan wa su inna zainabu magana su dinga lura da abunda zasu dinga girkawa, "sallamar Audi me gadi ce ta katse su falon ya shigo hannunsa dauke da babbar leda, "agaban hjy iya ya ajiye ya juya ya fita, "yauwa hjy iya ga kayanku fa'iza da ciwon kai ta tashi amma tace agaya miki cikin satin nan zata zo, "to madalla ashe kaya sun iso, Allah sarki  yanxu nake shirin ma tambayarta ashe batajin dadi Allah ya sawake yasa kaffara.


Hjy iya ce keta fito da kaya cikin farin ciki kayanta ta fara ware wa agefe sannan ta ware nasu inna zainabu, ta gama ware kayan kenan Audi ya kara shigo da wata katuwar ledar, " ya ajiyeta gaban hjy iya, "Audi maza jeka kirawomun su zainbu kace dukkansu inasan ganinku Auwalu (Driver) ma kace yazo ku taho tare, Audi washe baki ya farayi  πŸ˜ƒ  cikin murna yace angama hjy iya ya juya da sauri ya fita.


*BA'ADAUKI* *LOKACI* *BA*

Gaba daya yan aikin gidan suka hallara afalon hjy iya, "kowannen su cikin farin ciki yake, murnanr su taki boyiwa.


Cikin dan lokaci hjy iya ta raba musu kowanne kayansa set biyu da takalmi su zainabu harda hijabai, " cikin farin ciki da girmamawa suka durkusa suna kwasar godiya harsai da Alh habibu ya dakatar dasu ya sallamesu kowa ya kama gabansa.


Habibu ina bukatar yan kudi, dan na hannuna bazasu isheni ba dan guraren da zani da yawa kuma kowanne naje zan musu hasafi. Hjy iya kudi ko nawa kike so zan baki amma dan Allah hjy iya ki hakura da wnn fitar na rokeki ba dan niba, idan  komai ya lafa na miki alkawari da kaina zan kaiki duk inda kike so. Kai habibu ka kiyayeni wai sa'arka na koma ko abokiyar wasanka, wai ma yaushe ka koyi ja'inja dani ne to ka fita ido na rufe inba haka ba ranka zai baci.


Hjy iya dan Allah kiyi hakuri ki fahimceni bada wata manufa na hanaki fita ba, wlh ko fita kukayi go slow ma kadai ya isheku, go slow yau na fara haduwa dashi kaga habibi idan zaka bani kudi kaban idan kuma bazaka bayar ba ka rike abunka zumuncin Allah dai bazaka hanani ba.


Ayi hakuri hajiya iya ga wannan, "ya karasa maganar yana zaro kudi a aljihu, " yan dubu-dubu ne na dubu dari da hamsin ya mika mata, "cikin farin ciki hjy iya ta karba tana murna. Nagode habibu Allah dada budi Allah shirya zuri'a, Allah yayi ma albarka, cikin jin dadin addu'ar mahaifiyarsa yake amsawa da Aameen.


*INA* *TARIHIN* *HJY* *IYA*?

Hadiza shi ne aynihin sunan hjy iya asalinsu yan kauyen kano ne cikin  wani kauye  me suna rigana dake cikin garin lambar kunci, "ita da mai gidanta marigayi mlm sani auren zumumci aka musu hjy iya su uku ne gurin iyayensu itace babba laraba take binta sai Auwalu "mlm sani ya rasu tun Alh habibu nada shekara biyar aduniya, shi kuma su biyar ne gun mahaifansu maza hudu sai mace daya itace autarsu


Mlm sani kasuwanci ne ya ke kawo shi kano ya koma daga baya ya dauko matarsa suka dawo kano inda suka zauna a unguwar bacirawa, sana'ar icce yakeyi a hakali Allah yasa mai albarka har ya fara janyo yan uwansa suma a hankali kowa ya nemi sa'ar da yakeyi    sannu a hankali suma suka dauko iyalansu.


Alh habibu shi kadaine dansu rayayye hjy iya ta haifi yara takwas duk mutuwa sukeyi sai akan habibu Allah ya bar mata kuma daga kansa bata kara haihuwa ba.


Hadiza (Hjy iya) mace ce me fadan gaske bata da daukan raini sai dai bata da riko, gata mace ce mai kyauta   ga san zumunci, hjy iya tasha wahala matuka bayan rasuwar mlm sani domin yan uwan mahaifinsa ba wanda yake taimaka mata, itace wankau sirfau dakau har sana'ar kosai da waina tayi dan ta samu habibu yayi karatu, ' ahaka har ya zama saurayi ya fara buga buga suna  rufawa kansu asiri dg nan hjy iya ta daina wahala sai dai ya fita ya nemo musu har Allah yasa ya kammala karatunsa ya sami aiki kuma yana hadawa da kasuwanci, " yayi aure, " yanada mata biyu da 'yaya goma sha uku, sai jikoki guda goma sha takwas.


Alh habibu yanaji da mahaifiyarsa matuka duk abunda zayi dan ya faranta mata yanayi iya kokarinsa, tunda dadewa ya bukaci hjy iya ta koma gidansa dake gyadi-gyadi fir taki wai batasan zama da sirikai ko unguwa daya bata bukatar su zauna, " shiyasa yasai mata katafaren gida a na'ibawa ya zuba mata yan aiki da me gadi da driver.


hjy iya tayi yan aiki sunfi a irga sbd fadanta kanayin abunda bai gamsheta ba zatasa

a sallameka inna zainabu ce suka shafe shekara da shekaru suna tare kasancewarta mace me hakurin gaske typin.....πŸ˜‰


_BACK_ _TO_ _LABARI_ ✍🏼


*Vote*

*Comments*

*Share* πŸ˜ŽπŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

      πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

      πŸ‘œ

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_)

_15/6/2020_

πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

         πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

     πŸ‘œ


*Written* by _Ameera_ _Adam_ { _Mom_ _Aslam_ }

    

    πŸ“š *HADAKA*πŸ“š

   πŸ“ *WRITER'S*πŸ“

πŸ–Š️ *ASSOCIATION* πŸ–Š️

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

@: *Facebook*

_HADAKA_ _WRITER'S_ _ASSOCIATION_


@: *wattpad*

_AmeeraAdam60_


*SADAUKARWA* *GA* *DUK* *MASOYA* *NA* 😊🀝🏻

_Wannan_ _labarin_ _kirkirarre_ _ne_ _banyi_ _shi_ _dan_ _wani/wata_ _ba._

        5&6

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


*JAJIBERI*

Hjy iya na hango a harabar gidan hakimce akan farar kujerar roba, "daga cen nesa su suwaiba ke gyaran kayan miya ita da hansai, "gefe guda inna zainabu ce ke wanke nama abakin famfo, "suwaiba dama haka kike gyara mana kayan miya munaci da tsutsa bakiga yanda hansai take gyarawa ba sai ta sa wuka ta bude cikinsa.+


Ashe mun dade muna cin kazanta gwara da Allah ya nunamin da ido na, 'hjy iya wlh ba hk bane wai bari nai ingama tarasu sai na gama cire hancin attaruhun da tattasan sai insa wuka inbude cikin zai fi sauki.


Ja'ira sarkin kyuya karya nayi kenan zaki cemun ba haka bane, "suwaiba ki kiyaye ni wlh,  kwanaki ma haka na kamaki kin dama mana kunu kinbarshi a bude har kuda ya fada ciki, "to kinyi na biyu ranar da kikayi na uku ranar zaki bar gidan nan dan bana shiri da kazami shashasha kazamar banza. Dan girman Allah hjy iya kiyi hakuri wlh bazan kara ba, "ki kara mana suwaiba kigani yarinya karama sai kyuya da san jiki.


ke kuma hansai tashi kije daki ki dauko mun radio na lokacin tafsir ya kusa.


   "to hjy iya, hansai ta fada tana kokarin wanke hannu, "hansai har taje bakin kofa hjy iya ta kwalla mata kira.


          "hansai barshi ma zo ki mikomun takalma na, " bari na shiga ciki kar kafata tayi tsami  wannan zaman kujerar da nayi.


Angama hjy iya, "yauwa hjy iya markadan yanxu za'a kai ko?   Eh "yanxu za'a kai miyar ma so nake agamata yau, inyaso tuwon koda asuba adora shi.


To shikenan hjy iya.


Hjy iya falonta ta koma ta bar su suwaiba da hansai suna aiki, " bayan shigarta daki ta kunna radio ta kamo tashar Dala Fm 88.5 kunnawarta yayi daidai ta fara tafseer din Mlm. Dr. Isa Ali pantami wanda suke sawa karfe biyar daidai na yamma.


Gidan hjy iya aiki sosai suke na shirye-shiryen sallah, sai soye soye ake gidan ya garwaye da kamshiπŸ˜‹πŸ˜‹πŸ˜‹

1

   *YAU* *AKE* *GOBE* *SAI* *LABARI* πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ


Garin kano gari ne me dumbun musulmai da yawa gari ne na masoya manzan Allah (S.A.W)  "ranar lahadi itace ta kasance ranar sallah bayan gabatar da azumin watan ramadan me girman daraja,    "fuskokin mutane na kunshe da farin ciki yara da manya maza da mata kowannen su sunsha ado da sababbun kaya.


Hannayen su dauke da daddumar sallah wasu na tafiya akasa wasu a motoci wasu a mashina yayinda wasu ke kan kekuna.


   Burin kowannen su ya samu gabatar da sallar idi. ( kwalelenku mutanen kaduna, Edin bana anyi ba kuπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺ)


Hjy iya na gani ta fito shar da ita cikin galleliyar atamfarta, " kafar nan tata jawur da jan lalle tasha dungulminta sai sheki take, fuskar dattijuwar wasai cikin sabon hijabinta sai murmushi take,   "daka kalleta kasan tana cikin farin ciki.

Fitowarta harabar gidan, da sauri Auwalu driver ya bude mata mota,   "ba'a dauki lokaci ba sai ga su hansai kowaccen su cikin sabon dikin baku nansu yasha jan jambaki ( _kanta_ _waye_ )


Shigar su keda wuya, Auwalu driver yaja mota sukayi masallacin sahaba dake kundila.

     *BAYAN* *SALLAR* *IDI*

Hjy iya ke zaune a falonta tanacin tuwon shinkafa miyar agusi, " tasha man shanu sai kamshi yake πŸ˜‹

Sallamar Alh habibu taji ya shigo cikin manyan kaya, har kasa ya tsungunna ya fara gaida mahaifiyarsa.

    " hjy iya barka da safiya dafatan kun tashi lfy? Lafiya mu klau habibu ya iyalan da fatan kunyi sallah lafiya? Wallahi lafiya klau hjy iya Allah ya maimaita mana,

"Aameen Aameen habibu.

Tashi ka leka ka kiramun yaran nan suxo su zubo ma tuwo,   "kai haba hjy iya ni naki ma zanci dan na kwana biyu bamuci abinci tare ba,

   " habibu har kaci jagwalgwalon tsohuwa.

Dan Allah hjy iya ki daina fadin haka, duk duniya nafijin dadin cin abinci dake fiye da kowa,

" Allah ya kara girma hjy iya.

Aameen ya rabbi habibu, hjy iya ta fada cikin jin dadi da kaunar danta d'a d'aya tilo agurunta, daya tamkar da dubu.

Gwanin birgewa suke cin abincin su bayan sun gama cikin hikima Alh habibu yake tambayar mahaifiyar sa.

                 "wai hjy iya nace ba, ina da ina zaki je ne tunda muna hutu kinga sai  na kaiki da kaina, " kinga nan da zuwa dare mun dawo.

Habibu tafiya ta ay bata wuni bace, dan rigana zanje kuma sati guda zanyi, kuma idan na dawo zan sauka bacirawa gidan laraba inyi kwana biyu, "sai gdn  Auwalu da zani nai kwana daya.

Haba inna me zakije rigana kiyi ko wata uku bakiyi da zuwa ba,  "habibu mahaifa ta ce fa dangin mahaifina dana mahaifiyata ay wasunsu suna nan wasu ne dai suka rigamu gidan gaskiya.

     Eh haka ne hjy iya amma ki hakura da zuwa sai wani lokaci dama kuma akwai wasu kaya na da zansa Auwalu driver shi da iro su dauko mun su kai gidan gona ta.

     Shikenan habibu naga dai baka san tafiyar nan tawa na hakura, " cikin farin ciki Alh habibu yake fadin,  " yauwa hjy iya Allah ya bar min ke,

      Aameen habibu ta fada tana murmushi, cikin zuciyarta tana fadin,     " idan ba motar gida ay akwai ta haya, idan ba haka na maka ba bazaka kyaleni ba,  " gwara na bullo ma ta haka,  haka kawai ahana mutum zumuncin Allah.

        To hjy iya ni zan wuce,  " har zaka tafi habibu, to agaida yaran ina jiran shakiyan nan tun cikin azumi da suka zo suka sha ruwa dama sunce mun sai sallah,  " eh naji kamilu na cewa gobe anan zasu wuni harda yaransu gaba daya.

    Lallai kace gobe da manyan baki agidan nan,  " to Allah kawo su lafiya,  Aameen au banda abinsu ma ay gobe ba hanya,  "sai laraba kuma inajin sai dai su xo laraba.

Au habibu har yanxu wannan dokar tana nan ta hana zumunci, to Allah yayi mana magani.

     "Aameen hjy iya ni na wuce,  "inajin sai zuwa juma'a zan bullo,  " Allah ya kaimu da rai da lfy habibu.

  *BAYAN* *FITAR* *ALH* *HABIBU*

Wato har yanxu wannan dokar tana nan aykuwa bazan bari sai laraba ba zani kauye, tunda dai yanxu safiya ce bari inhada kaya na intafi nasan nan da azahar na je, " hjy iya ke zance ita daya a falo, kamar anzabureta da sauri ta tashi tayi cikin daki.

Drower ta ta bude yar jaka ta dauko ta hannu madaidai ciya ta debo kayanta kala biyar da hijabai biyu ta zuba ajarkar ta rufe.

kudin da Alh habibu ya bata ne ta debo su dubu talatin ta irga ta sa ajaka ta irgi dubu hamsin ta zuba aciki kaja ( _wani_  _siket_ _ne_ _da_ _ake_ _wa_ _tsofaffi_ _aljihu_ _ajiki_)

Sai da ta kamalla komai sai gata ta fito falo fes da ita gwanin sha'awa, " mukulli tasa ta rufe sashenta, tana fitowa harabar gidan ta hadu da Audi me gadi, "yashe baki ya farayi da sauri ya karaso gurun hjy iya, "hjy iya unguwa zaki ne? Naganki da jaka gahi Auwalu sun tafi  hi da Alh dazu.

Kauye zani maza kaje ka kiramun su zainabu dukkansu, da sauri Audi ya tafi basu jima ba sai gasu sun dawo tare, "cikin russunawa kowannensu ya dan russuna, " gamu hjy iya ance kina neman mu!

Zainabu kece babba kisa ido acikin gidan nan domin kauye zani inyi sati guda, kar indawo inga ba daidai ba nasan store akwai duk kayan bukata, " nasan babu abinda za'a bukata.

Kai kuma Audi ba kaga bana nan ba ka shiga daki ka dinga bacci ba, dama  kamar kasa haka kake bacci, " kuma ka cewa Auwalu karya sake ya fita da mota indai ba habibu ne ya umarce shi ba.

To ni na tafi sai na dawo,  hjy iya ta fada lokacin da ta nufi hanyar get"to hjy naga zaki fita ke kadai Auwalu fa sun tafi da Alh.

Fita zanyi intari dan adaidaita ya kaini tasha na hau mota.

😳😳😳 cikin mamaki kowannensu ya kalle ta kamar hadin baki suka furta TASHA kuma hjy iya?

Eh tasha ko akwai me hanani fita?  A'a hjy iya amma abin ne da ban mamaki, inna zainabu ta fada fuskarta na kara bayyana mamaki πŸ€”

Ku ne abun ya baku mamaki amma ni ba abun mamaki bane aguri na, " amma gaskiya Alh besan zaki tasha Ki hau mota ba hjy iya, na tabbata daya sani vazai barki ba.

Audi ka buga masa waya mana ka gaya masa, "uban yan tsegumi da munafurci, Audi ka taka a hankali inba haka wlh zan sa a sallame ka, naga kanaso ka wuce makidi da rawa,  " kiyi hakuri hjy iya idan nayi ba daidai ba.

Kayi ta kanka karka shiga nutsuwarka idan na dawo baka kintsa kanka ba zaka yi asarar aikinka, " hjy iya na gama fad'anta ta bude kofa ta fice.

        Baki sake gaba daya haka suka bita da kallo har ta fice.

     *BAKIN* *TITI*🚦

Hjy iya tafi minti goma tsaye abakin Titin na'ibawa tanasan tsallakawa sai taje tsakiyar titi zata tsallaka sai ta dawo baya da gudu🀣 " tayi haka yakai sau uku sai da wani saurayi yazo ya rike hannunta sannan suka tsallaka tana ta shi masa albarka.

Da tsallaka titin hjy iya ta fi awa daya bata samu abun hawa ba, duk dan sahun da yaxo kowanne acike yake zuwa, ga rana ga tsayuwa hjy iya sai zabga gumi take wuyan hijabin ta duk ya jike🀣

Tana nan tsaye sai ga wata bus 🚌 din yan kura taxo ta tsaya kusa da ita ta sauke passenger, " cikin sa'a hjy iya ta samu ta hau suka tafi _typin_ ........πŸ€ͺ

*Don't* *forget* *to*

*Vote*

*Comments*

*Share*πŸ˜ŽπŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

      πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

      πŸ‘œ

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_)

_15/6/2020_

πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

         πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

     πŸ‘œ


*Written* by _Ameera_ _Adam_ { _Mom_ _Aslam_ }

    

    πŸ“š *HADAKA*πŸ“š

   πŸ“ *WRITER'S*πŸ“

πŸ–Š️ *ASSOCIATION* πŸ–Š️

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

@: *Facebook*

_HADAKA_ _WRITER'S_ _ASSOCIATION_


@: *wattpad*

_AmeeraAdam60_


*SADAUKARWA* *GA* *DUK* *MASOYA* *NA* 😊🀝🏻

_Wannan_ _labarin_ _kirkirarre_ _ne_ _banyi_ _shi_ _dan_ _wani/wata_ _ba._

       7&8

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*+


Hjy iya na zaune a kujerar farko ta kusa da maleji daga ita sai kofa, tana nan zaune da yar jakarta a cinya adogace take ko kadan bataji dadin zaman ba ga malejin ma cike yake da yara ga zafin inji na bugota, "basuyi tafiya me nisa ba wani saurayi ya kara tsaida mator ba musu kwandasta ya buga murfin motar da karfi yana fadin aje ta master ga wani kayan ansamu, cikin tsorata hjy iya ta kankame wata mata dake kusa da ita.


Cikin tsananin fada hjy iya ta fara magana, " kai yaron mota me kakeyi haka sai kace karamin yaro, ji yanda ka tsoratani yanzu daka sa aka tsaya a ina zaka sashi baka ganin motar cike take har maleji, " master sata ta nan, faka ta megida,  yaaah ina zakaje ne babban yaya? Duk fadan da hjy iya keyi kwandasta ko 'kurarta bai kalla ba bare yasan tana yi, magana ma yakewa fasinjan daya tsaidasu, aykuwa iya kuluwa hjy iya ta kule.


" Isyaka rabi'u zani, kudinka naira hamsin amma maleji ne ba kujera  kwandasta ya bashi amsa, " ba musu ya taka mota zai hau bisa tsautsayi ya taka kafar hjy iya aykuwa kmr ya watsa mata ruwan zafi da rufeshi da fada dama ga zafi ya addabeta.


Kai kam wane irin mara kunyan yaro ne dan nema zaka takani ko baka gani ne?  To iya idan naga kafarki zan takaki ne kawai daga andan bigeki zaki ishi mutane da sababi ya kara magana lokacin da ya zauna, " au dan bigeni ma kayi lallai yaran nan baka da mutumci fitsararre wanda baisan darajar manya ba amm............... Sorry iya nifa banasan mita kukuma dama tsofaffin nan kadan kuke jira ku jawa mutum jafa'i dan bakinku kaifi gareshi kamar takobi, "kai kwadasta hawo mu wuce na zauna matashin ya fada yana kokarin saka headphone akunne.


     Sakin baki hjy iya  tayi tana kallonsa kamar tamai magana kuma sai ta fasa, " rufe musu kofar kwandastan yayi ya zagaya ta baya ya shige booth,  " duk bidirin da sukeyi driver yana jinsu,yana jin kwandasta ya zauna ya fizgi mota ya cilla ta titi.


Cikin abinda baifi minti talatin da biyar ba suka karasa kano Gestin hjy iya ta sauko da kyar tana dan dingisa kafa, jakarta  ta rike sosai ta hango wasu mata zasu tsallaka titi ta karasa kusa dasu zuwanta keda wuya wani dan karota yazo ya tsallakar dasu.


motoci ne ajere taji ana kiran kofar ruwa, kurna, rijiyar lemo, bacirawa, multara dawanau ciko saura mutum hudu.

   wannan karan hjy iya jikin window ta samu tana nan zaune ba jimawa fasinja suka cike motar, wanda yawanci motar duk maza ne mata uku ne, " daga hjy sai wasu mata biyu abaya, motar su hjy iya na tashi wani driver ya dora tashi su hjy iya aka shilla titi🀣🀣


Suna cikin tafiya kwandasta ya fara hada kan kudin mota yana bawa mutane canji, tafiya ta fara nisa mutumin dake kusa da hjy iya ya fara gyangyadi idan yayi gaba sai kaji luuuu ya dawo jikin kujera, cen da bacci yayi dadi hjy iya batayi aune ba sai jin mutum tayi ya fado jikinta, ganin baccin da yk yi yasa bata damu ba ta sa hannunta tadan tureshi.


A dan tsorace ya bude ido cikin jin kunya yabata hakura.


Jingina kansa yayi jikin kujera ya cigaba da baccinsa, suna cikin tafiya mota ta taka birki firgigit ya tashi yana yan kalle-kalle amma da ganinsa ya tsorata da yanda yaji birkin motar, " can tafiya na kara mikawa luuuuu mutumin nan ya kara fadawa jikin hjy iya baccinsa yake lakadan dan sai sakar minsharinsa yake, wannan karan hjy iya dan karamin tsaki taja ta dan turesa da hannu.


Ko kadan baima san tanayi ba, minshari yake saki ji kake kaaaarrrrr huuuuu mummm kakkakakaka 🀣🀣 ( _kamar_ _minsharin_ _shamsiyya_ πŸ€ͺ )


Mutumin dake kusa dashi ne ya dan tasheshi, cikin kosawa yake fadin malam kana dan bige dattijuwan nan, " a kunyace ya hau murza fuska yana gyara zaman hularsa kamar gaske ya zauna yana kallan hanya .


Mutumin hjy iya be daddara ba haka bacci ya kara daukansa wannan karan bacci yake hardasu yawun bacci, luf yayi agefen kafadar hjy iya, sosai hjy iya ta kai bango cikin jin haushi ta hada karfinta guri daya ta hankade shi hadi da danna shi kan dayan mutumin dake cen gefen nasa🀣🀣🀣


Sosai ta bawa yan motar dariya ashe duk budurin da ake suna kallo, " dariya suke a fili yayin da mutumin nan ya kule sosai ya juya ya ballawa hjy iya harara hadi da tsaki yafara maganganu kasa-kasa, " zagina zakayi ne kaa saa uwar bacci naji kana gunguni me baccin larura, dan wannan baccin naka bana lafiya bane Allah ya yaye maka cutar nan da kake fama da ita, mutum sai baccin asara ta karasa maganar tana juya kanta wajen window.


A harzuke ya juyo gurinta yana fadin, " ni babu wata cuta da take damuna haka kawai ina zaman zamana zaki ja mun ciwo muji da  wannan annobar cutar ta corona mana, ba dama mutum ya kishingida sai afara jamai masifa, to ni lfy ta klau na ma kusa sauka na huta.


kai karan mota idan kaje Bacirawa kwanar madugu zan sauka, kwandastan da aka kira da karan mota ya dago da rinannun idanuwansa jawur cikin dakusashiyar murya yake fadin "kai master ka iya bakin ka fa, na rantse da buwayar Allah idan ka kuma cemun karan mota sai na maka aikin karnuka, ya karasa maganar yana cije baki gefe.


Tsit kake ji ba wanda ya kara magana har akaje inda mutumin nan zai sauka.


Motar su hjy iya ba ita ta kaisu multara ba sai karfe 3:10 pm  lokacin kowa ya fito hjy iya wani gida ta hango daga cen tsallaken titi, yanayin gidajen kanana ne wasun su ma ginin kasa ne.


kasancewar titin babu motoci sosai nan da nan hjy iya ta tsallaka da sallama ta shiga gidan, bayan sun gaisa ta koki alfarmar zatayi sallah, ba musu matar gidan tazuba mata ruwa a buta, hjy iya tayi sallah azahar tana nan zaune tana lazumi matar gidan ta zubo mata tuwo miyar taushe da kunun gyada ta ajiye mata agefenta.


Hjy iya na idar da lazumi ta dau kofun kunu ta fara sha ( _nikuwa_ _nace_ _su_ _hjy iya babu ma dan jan aji_) sai da ta kusa shanyewa ta ajiye jin kiraye kirayen sallah la'asar take yi , sallah  tayi ta fito tana yiwa matar gidan godiya,  dubu biyu ta zaro ta mikawa yaron matar wanda befi shekara hudu ba, aykuwa tasha godiya har kofar gida matar ta rako hjy iya tana mata Allah ya tsare hanya.


Tafiya ta danyi cen tsallaken titi cen ne ta hango yan gada-gada suna lodin motar bichi lamba dan zqbuwa, tana zuwa motar ta cika har driver ya janyeta.


Wata bus din aka matso da ita hjy iya itace farkon passinger wannan karan ma itace jikin window, a hankali mota take ta samun passingers har ta cika, hjy iya na nan zaune mutumin dake kusa da ita ya dan fara janta da hira tun hjiy iya na maze fuska harta saki jiki, cikin hikima yake tambayarta, baba yanzu karfe nawa ne wlh wayata ta mutu ba caji, gashi kuma inda zani  ana jirana, akan idonsa πŸ‘€ ta zuge jaka ta dauko wayarta " cikin mamaki take kallon agogo karfe 4:50 pm wato biyar saura, afili ta furta lokaci baya jira Allah dai yasa mu cika da imani Aameen.


Shi dinma da Aameen ya amsa mata, yana nan yana fakon hjy iya harta zuge Aljihun jakarta tasa ta rufe.


Shiru ne ya biyo baya bame cewa wani uffan, hannu ya fara mikawa sannu a hankali har Allah yabashi sa'a akan wayar hajiya iya.


   _Tabdijan anyi WUFF da wayar hjy iya akwai sabon rikici_

2

*Vote*

*comments*

*Share*πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

      πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

      πŸ‘œ

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_)

_21/6/2020_

πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

         πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

     πŸ‘œ


*Written* by _Ameera_ _Adam_ { _Mom_ _Aslam_ }

    

    πŸ“š *HADAKA*πŸ“š

   πŸ“ *WRITER'S*πŸ“

πŸ–Š️ *ASSOCIATION* πŸ–Š️

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

@: *Facebook*

_HADAKA_ _WRITER'S_ _ASSOCIATION_


@: *wattpad*

_AmeeraAdam60_+


*SADAUKARWA* *GA* *DUK* *MASOYA* *NA* 😊🀝🏻

_Wannan_ _labarin_ _kirkirarre_ _ne_ _banyi_ _shi_ _dan_ _wani/wata_ _ba._

       9&10

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


       Cikin hikima ya zagayo da hannunsa saitin aljihunsa, yana yi yana fakon idon mutane har ya samu ya zurata cikin aljihu, guntun murmushin gefen baki yayi ya kara adaidaita zamansa yana yi yana basarwa.


Passinger kusa dashi ne yake yiwa kwandasta magana,  " yauwa yaron mota nagaya ma idan kaje dawanau zan sauka, eh " aydama ku biyun nan ne kawai zaku sauka a dawanau kai da baba ta baya,  ya karasa fada yana kallan wata tsohuwa dake zaune a akujerar baya, "eh yaro kuma ni ce me farin buhun nan me ratsin ja da baki.


Ba matsala ay mun kusa karasawa ku saka takalman ku kar................ Karaf mutumin kusa da hjy iya yace kwadasta bani sauran canji na nima idan kun karasa dawanau zan sauka, "malam ba a badime kace zaka sauka ba ?  To na fasa akwai abunda zan tsaya na karba, to ba komai ungo ragowar kudinka, "kwandasta ya mikamai canjinsa.

Ana zuwa kasuwar dawanau kuwa su ukun suka sauka, mutumin kusa da kwandasta kuma ya koma gunda tsohuwa ta sauka a kujerar baya.


Har motar zata tashi wasu passinger su hudu suka tsaidasu daya tsoho uku samari amma kowannensu da inda zai sauka, tsohon shi bichi yayi su kuma matasan a kwa zasu sauka.


           Tsohon shi ya fara shiga ya zauna a maleji kasancewar kudin maleji gareshi sukuma matasan suka hau kujera mota ta d'ame taya suka shilla titi.


Dattijon nan Akallah zai girmi hjy iya sai dai dake jikin namiji da mace ba daya ba, "yana zaune kan maleji yana facing din hjy iya da dan buhunsa makale akan cinya, tunda ya shigo idonsa na kan hjy iya itakam titi take kallo ta window bata ma san yanayi ba.


Buhunsa ya bude ya zaro wata leda, gyada ce aciki marau marau, cikin kashe murya yake wa hjy iya tayin gyada 🀣


           Ranki ya dade ga gyada amaro ko zaki taba, " dan waige hjy iya tayi ko zata ga da wacce yake sai dai motar duk maza ne ita kadai ce mace, dan murmushi tayi tace Alhamdulillah nago................. Haba ke kuwa wa yace miki ana maida hannun kyauta baya, sai kace wata indo kinsan masu suna Aisha sune suke abu kamar ba wayayyu ba (πŸ™„πŸ™„πŸ™„πŸ™„πŸ™„ *lallai ma ka raina mana hankali😏* ) karbi dan kar muyi haka dake, ya karasa maganar yana mika mata gyada kamar zai ruko hannunta ya dan'ka mata.8


Hjy iya karba tayi amma badan ranta yaso ba, sai dai dan karta gwaleshi, " nagode Allah saka da alheri, hjy iya ta fada lokacin da ta karbi ledar gyadar ta dora acinyarta kusa da jakarta.


     Haba kekuwa me sunan tsofaffi wannan godiya haka, kamar wacce nayiwa wata babbar kyauta,  duk wannan maganar da yake wa hjy iya kasa-kasa yake yin ta.


Hmmmm nifa ba suna na indo ba, suna na hadiza, dama abinda tsohon nan yake son ji daga gareta, " kara kashe murya yayi cikin kwarkwasa yana fadin, Allah sarki kice sunan uwar gida gareki, Allah ya gafarta miki dije halinki na gari ya biki, "au ta rasu ne ? Allah ya jikanta ya kyauta makwanci,  cikin nuna halin jimami ya amsa da Aameen.

Ni baki tambayi suna na ba, ya kara kasa da murya kamar me rada, "da mamaki hjy iya take kallansa dan ta lura abun nasa babu hankali aciki,  "yi tayi kamar bata ji shi ba.


Kara dan sunkuyowa yayi da kansa, kamar wanda zai dauki wani abu, ya kara yiwa hjy iya magana,   " hadizatu nace baki tambayi suna na ba ? To sunan bame wuya bane dan lami ake kira na , na gaskiya kuma kabiru, ya karasa magana yana kashewa hjy iya ido daya hade da daga mata gira πŸ˜‰πŸ˜‰1


         sototo hjy iya tayi tana kallansa dan ranta tuni ya fara baci, dan ita abun har ya fara bata mamaki, tana kokarin yi masa magana sai ji tai ya rike hannunta dake jikin window, yana fadin dan bude mu musha iska mana ko bakyajin zafi ne ?

   Salati hjy iya ta rafka sai da hankalin kowa ya dawo gurunsu, cikin bacin rai take fadin, " kai tsohon banza tsohon najadu angirma ba'asan angirma ba, ni zaka gwadawa iskanci da kwartanci ido biyu,  wlh ka ci darajar Ba kusa nake da habibu ba, da tuni ya dau mataki akanka shasha mara kan gado da lissafi.


  Tsuru yayi yana tsilli-tsilli da ido, lokaci daya mutanen cikin motar suka zubo musu ido kamar dama jira suke, cikin fuffukar borin kunya ya fara magana.


   " lafiyarki baiwar Allah daga cewa ki dan bude mana kofa musha iska sai ki fara zagina, me yayi zafi da har kikemun wannan zagin na tsamar nama, bayin Allah ku tayani ji kuyi mama alkalanci, ya karasa maganar yana kallan mutanen cikin motar.


Au haka ma zakace, lallai kai kam ko kwalba ma nan ta ganka ta kyale ka.


   Wani passinger   dake baya ne cikin sigar lallami ya shiga bawa kowannen su hakuri,  " baba kuyiwa Allah kuyiwa Annabi kuyi hakuri wannan ba girma da mutumcinku bane, dan Allah kowannen ku yayi hakuri, dama zaman guri daya sai hakuri, yanxu da kowa yaje inda zai sauka shikenan wani har abada bazaka kara ganinsa ba.


wani matsahin saurayi da yake gidan gaba ya juyo yana magana, " to banda abunku ma tsofai tsofai daku dan Allah meye na wani hatsaniya, zaman mota har wani zaman jin dadi ne da har kuka samu damar yin wani fad................. Kai dakata mun rasa kunya waya kasa da kai ko so kake kaci mun mutumci, ka ga yaran zamani da rashin kunya.


    Banda ma kaddara me zai kawo ni cikin  wannan tsohuwar motar, me kama da gwangwani, tunda dana yana da wacce ta ninnika wannan kyau.


     A zafafe driver ya taka birki ya juyo gun hjy iya, Tsohuwa karfa ki ci mana mutumci da kinsan akwai ta dan naki ya barki kikaxo kika hau ta haya, ay da ya kaiki da kansa idan har ya damu dake kuma yana neman albarka,  kuma yanxu gwangwanin ay ta miki rana.


Kinsan Allah Daba dan ina duba tsufanki ba kuma nan dokar daji ne da sai kin sauka daga motar nan, aykuwa kamar ya watsawa hjy iya ruwan zafi ta rufe shi da fada.


Karya kace wallahi, wallahi habibu dan Albarka ne kuma zai gama da duniya lafiya, na tabbata har ka mutu baza kayiwa mahaifiyarka abunda habibu yake yi mun ba, kuma motar ka idan na sauka sai me? Tunda ba motar shiga Aljanna bace, ja'irin yaro mara mutumci wlh da habibu yana kusa zaka gane baka da wayo.


parking din mota driver yayi ya juyo yana fadin, wai waye shi wannan habibun da kike takama dashi, waye shi a garin nan, habibun banza da wofi.


    Kai yaro dubeni nan habibu na ya wuce ka kirashi banza da wofi.


Wani dattijo ne ya sauko daga motar ya zagaya gun driver ya jashi gefe ya lallameshi kuma ya bashi baki akan koba koma ya dubi girman hjy iya, kuma yayi mata uzuri domin wani abun harda tsufa.


      Hjy iya nacen sai faman banbamin fada take yi, da kyar suka lallasheta ta hakura,  driver ya shiga mota ya tasheta suka hau hanya.

       Basu fi minti goma da fara tafiya ba, hjy iya ta fara duba jaka damin dauko waya, dan ta duba agogo kasancewar yamma tayi likis, waya tace daukeni inda kika ganta.


Babban aljihu ta kara dubawa, itama babu, " gurin da kayanta suke tasa hannu ta duba nan ma wayam.


Aykuwa hjy iya ta rafka salati La'ilahaillallahu Muhammadur Rasulillahi Sallallahu alaihi Wasallam yau na gamu da gamo na, gaba daya hankalin passingers yayi kanta ,  suka zubawa sarautar Allah ido, suna san tambayar ta suna tsoron fadan ta.


    Daya daga cikinsu ne yayi karfin halin magana,  " iya me ya faru kuma? Yaro wayata aka sace mun, kuma kana gani tunda na shigo motarnan jaka ta na kan cinya ta, hjy iya ta bashi amsa.

Driver Dan Allah dan yi parking da mota, wayar baiwar Allah nan Aka dauke wa waya.


   Haba megida wannan tsohuwar ta cika rigima fa, ga hadari ya hadu agarin ko so kuke ruwa ya riskemu a hanya.


  Ay ba ruwa ba wallahi idan kankara ce dole ka tsaya inba haka ba ka biya ni waya ta, hjy iya ta fada lokacin da take kokarin sauke jakarta daga cinya.............✍🏼

*Karku manta yawan comments yawan typing*


_Masoya na ina yin ku irin sosai din nan_


*Vote*

*Comments*

*Share*πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

      πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

      πŸ‘œ

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_)

_21/6/2020_

πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

         πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

     πŸ‘œ


*Written* by _Ameera_ _Adam_ { _Mom_ _Aslam_ }

    

    πŸ“š *HADAKA*πŸ“š

   πŸ“ *WRITER'S*πŸ“

πŸ–Š️ *ASSOCIATION* πŸ–Š️

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

@: *Facebook*

_HADAKA_ _WRITER'S_ _ASSOCIATION_+


@: *wattpad*

_AmeeraAdam60_


*SADAUKARWA* *GA* *DUK* *MASOYA* *NA* 😊🀝🏻

_Wannan_ _labarin_ _kirkirarre_ _ne_ _banyi_ _shi_ _dan_ _wani/wata_ _ba._

       11&12


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


   Tabdijan ay wlh banci nanin ba nanin bazata ci ni ba, ya za'ay inbiya waya bayan ba ni naa dauka ba, ki binciki na kusa dake su fito miki da wayarki.


Kai driver me kake nufi ne? Mutumun kusa da hjy iya ya fada a harxuke.


To ka tsaya da motar nan ayi caje dan waya ta acikin motar nan aka sace ta, Saboda bayan na shiga motar nan har ogogo na duba, kuma inadubawa inga babu ay da sake wallahi.


     Iya nifa bazan tsaya ba kuyi cajen ku a haka kina gani hadari yake hadowa ga iska nan har ta fara tashi.


Mutumin kusa da hjy iya ne ya fara magana, " to wai iya me kike nufi kinga dai nine akusa dake shin ni kike san lakabawa sata ko yaya? Au kai tun kafin ma afara cajen har ka fara tsarguwa?


Ni babu wanda na nuna nace ya daukar mun waya, amma na tabbata aciki motar nan aka dauken waya ta, hayaniya ce ta fara tashi kowa da abinda yake fada, ba shiri driver ya gangara da mota yayi parking, saukowayayi daga motar ya zagayo ya bude murfin motar.


Me gida dan Allah ku sauko aduba mata wayarta yanxu haka ma kasan mota ta fada bata sani ba.


     Ba musu haka mutanen kujera su hjy iya duk suka sauko itace ta karshen fitowa da yar jakarta a hannu.


Kwandasta yasa ya shiga duba mata, sosai kwandasta ya duba kasan kujera lungu da sako amma babu waya, cikin kosawa ya fito yana wa driver magana.


Master wayar nan fa bata gurun cen dan na duba iya yina banganta ba, to iya wayarki bata nan dan Allah kiyi hakuri ki barmu mu karasa lafiya tunda muka shigo ke kadai kike mana hayaniya a mota, driver ya fada cikin gajiyawa, dan iya gajiya ya gaji da hjy iya Allah-Allah yake yaje inda zai sauke ta ya huta.


Yaro ba naki ta taka bane amma ni nafi zargin waya ta dauka akayi ba faduwa tayi ba tunda jakata nakan cinya ta, amma yanxu ka caje mun su kawai,  " dafe kai driver yayi, yanxu iya magidanta kamar wadannan za'a hau cajewa?


Cikin bacin rai wani passinger dake gefe dama ya cika fam ya fara fada, wallahi ban dauki waya ba babu zindikin katon da zai caje ni, iya tunda dai baki ga wayarki ba ki dau na Annabawa mana, Amma ni ko sama da kasa zata hade babu me caje ni.


To Aykuwa inada dan zargi akanka, idan kana da gaskiya ay baza ka ki acaje ka ba, "  driver dan Allah zo ka caje mu muyi mu tafi wallahi na dade banyi tafiyar data bata mun rai  kamar wannan ace nan da lamba kamar masu zuwa kaduna.


Driver caje su yayi daga aljihun riga har na wando, amma ba wayar hjy iya ba alamunta, mutumin da yace baza'a ace shi ba shi ya rage anxo caje shi amma fir yaki, har mutanen mota suka fara zargin anya ba kuwa shi ya dau wayar hjy iya ba.


Dan tsohon me buhu shima duk ancaje su amma wayam wayar hjy iya, " cikin zakalkalewa tsohon nan ya fara magana.


Amma yaro ka bamu kunya matashin saurayi da kai ka rasa me zaka dauka sai wayar tsohuwa kamar wannan kai amma Allah wadaran naka ya lalace, gaskiya kayi asara ancuci kuruciya wallahi, matashi dakai da halin bera.


Cikin zafin rai matshin nan ya bashi amsa, " kai tsoho ina ganin mutumcin ka wallahi ka kiyaye bakinka me zanyi da wayar tsohuwar nan kawai dai ni baza'a cajeni ba alhalin ban dauki waya ba, waya sani ma wayar ko rakani kashi ce.


Aykuwa lokaci daya mutanen mota suka mai caaa kowa da abinda yake fada, cikin hikima wani ya lallameshi har ya yarda aka caje shi, shima ba wayar hjy iya.


Sunkuyawa tayi tana kara duba jakarta duk suka zuba mata idanu cikin takaici kowa da abinda yake ayyanawa zuciyarsa.


Tana cikin duba jakarta wani mutumi da yake kujerar baya ya leko ta window yake mata magana,  " iya kuma kin tabbata kinsaka ta acikin jakarki kuwa? Yaro tunda na fito daga gida ban ciro  waya ta ba sai a motar nan da wannan yaron ya tambayeni agogo na gayamai, kuma ina fada masa na maidata jaka........................ Karaf kwandasta ya karbe wane ne acikin wadannan mutanen?


Dan jimmm kadan tayi ta dan dago da kanta tana kallon su sannan tace,  " a'a ay ya sauka tun a dawanau wanda yace ka bashi canjinsa ya fasa zuwa badime, to shi ne.


Wata wawuyar dariya kwandastan nan yayi yace ay iya yasha dake, sai dai kiyi hakuri aykuwa duk mutanen gurin suka dauka, amma gaskiya anwahalar damu haka kawai aka samu wahala ana ta wani caje mu kamar barayi, gashi duk an bata mana lokaci.


Ay iya sai dai kiyi hakuri kawai, yayi  miki guzurin cen, wani mutumi ya fada yana daga gefen hajiya iya.

Hjy Iya kamar zatayi kuka dan bakin ciki, cikin jin haushi tace, to ay yayiwa kansa Allah ya shirye shi yasa ya daina, dan Allah ku yafe ni dama nayi tunanin waninku ne ya dauka, dukkan su suka amsa da a'a babu komai iya komai ya wuce, sai dai ki kara kula da kayanki.


Daya bayan daya kowannen su suka fara shiga mota, kwandasta y shiga shima suka hau titi.


Shiru ne ya biyo baya, ba me cewa wani uffan, tafiya sukayi ba me yawa ba sukaxo gidan mai lokacin har anfara kiran sallah magariba.


Mai suka sha kowannensu yayi alwala, sallah suka gabatar daga cen tsallake wata me abinci suka hango wasu suka siya wadanda kuma suka kusa sauka kuma ko tsallakawa ma basuyi ba.


Su hjy iya sunci sunyi kat, basu suka bar gurun ba sai wajen karfe takwas da  minti goma, kowannensu sai da ya gabatar da sallah isha'i alokacin iska ta fara kadawa hadari ya fara hadowa, a gaggauce suka hau mota, driver ya take ta suka bar gurin.


Ganin hadari na kara hadowa yasa driver ya karawa motarsa wuta, gudu yake kamar zai tashi sama, " ganin gudun nashi yayi yawa yasa mutanen cikin motar suka mai magana, dan sassauta gudun yayi amma badan yaso ba.


Suna nan cikin tafiya aka fara yayyafi, ganin haka yasa driver su ya kara bawa motar sa wuta, cikin fada hjy iya take masa magana itada wasu passingers biyu.


Kai malam kashe mu zakayi ne, wannan gudun da kakeyi kamar zaka tashi sama, ka bi damu ahankali mana................... Idan ruwan sama kakewa gudu tunda har anfara yayyafi dole sai ya riske mu, da tuntuni bakayi gudun ba ido na ganin ido sai da dare yayi sannu sannu bata hana zuwa........... Hjy iya ce ke wannan maganar, ko ta kansu ma bai bi ba,  tukinsa yake yana yan wake-wakensa.

Aykuwa basuyi aune ba sai ji sukayi mota ta bada kiiiiiiiiiiΓ―iiiiiiiiiiii garaaaaaam.


Motar su hjy iya tayi taho mu gama da wata bus πŸ™†πŸΌ‍♀️


   _Don't forget to_ πŸ‘‡πŸΌ


*Vote*

*Comments*

*Share*

        _Mum Aslam Ce_πŸ˜ŠπŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

      πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

      πŸ‘œ

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_)

_23/6/2020_

πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

         πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

     πŸ‘œ


*Written* by _Ameera_ _Adam_ { _Mom_ _Aslam_ }

    

    πŸ“š *HADAKA*πŸ“š

   πŸ“ *WRITER'S*πŸ“

πŸ–Š️ *ASSOCIATION* πŸ–Š️

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

@: *Facebook*

_HADAKA_ _WRITER'S_ _ASSOCIATION_


@: *wattpad*

_AmeeraAdam60_


*SADAUKARWA* *GA* *DUK* *MASOYA* *NA* 😊🀝🏻

_Wannan_ _labarin_ _kirkirarre_ _ne_ _banyi_ _shi_ _dan_ _wani/wata_ _ba._+

       15&16

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


Gudu suma suka sa lokaci daya suka rufawa baba tsoho me buhu baya, gudu ya zage yakeyi iya karfinsa amma saboda yanayin girma ga tsufa lokaci guda suka cin masa.


A tsakiya suka saka shi suna kokarin rike hannuwan sa, dan tsoho yayi wani kukan kura cikin karaji irin yanda jariman india sukeyi idan suka fusata, yasa gwiwar hannuwan sa ya kai musu duka yana fadin, " wallahi bansan da makiya nake tafe ba sai yanxu idan kuka maidani cikin motar nan ban yafe muku ba.


Ku sake ni na karasa bichi a kafa, idan kuka kaini mota wallahi alhakin mutuwata a wuyanku yake, cikin hanzari suka kara matsowa zasu kama dan tsoho, aykuwa ya yi sauri ya matsa baya hadi da buga kafa daya, ya kara kwalla kara yana fadin, " yeeeeeeeee ku matsaaaaaaaa ko in ma ke kuuuuuuu, ya karasa fada yana dunkule hannuwa har huci yake.


      Daya daga cikinsu ya kallin dayen yace,  " wai kuwa Anya bazamu kyale tsohon nan ba yaje yayi ta tafiyarsa, tunda anasan ceton rayuwarsa yana san yayiwa mutane illa, kana ganin yanda ya kaimun duka a gefen fuska badan na kauce ba da ya gwabjeni yayi mun mahangurba,     " kai haba yanxu tsohon nan ne zai gagaremu, idan aka ce mun kasa kamo shi ba muji kunya ba dan Allah rabu dashi bari kaga muma karfi zamu nuna masa, muna zuwa ciccibarsa zamuyi farat daya  zamuyi masa.


     Aykuwa suka tunkari dan tsoho me buhu, yana ganin sunyo kansa gadan-gadan ya fara kai duka ta ko ina, yana yi yana ja baya sai kuma yayo gaba kamar zai doko wani daga cikin su, yan da kasan yana filin danbe.

Basu bi ta kansa ba, sukub haka suka sun kuci dan tsoho suka mammakure hannusa a hammatarsu sai wutsul-wutsul yake da kafafuwa, yanayi yana wani karaji shi bai yarda ba dole kwacewa zaiyi daga hannunsu.


Bakin motar suka karaso suna kokarin saka dan tsoho sai fisgewa yake yana ciccijewa har suka samu suka tura shi ciki, wani daga gefe ya dan leko su yana fadin,  " to ita ma iya ku sata aciki man, kunga kun huta, idan fa kukayi sake tsohon nan ya kubce wallahi dawa zai shiga, dan na lura motar nan ta tsora tasu dayawa,  juyawa sukayi zasu dauko hjy iya, bayan sun rufe kofar motar, Aykuwa dan tsoho ya Duba, ya waiga yaga duk basa kallansa, ya zura kafafuwan sa ta window.


Gurin hjy iya suka koma da zummar su dauko ta aykuwa ta rike kafar wani saurayi dake kusa da ita, duk tabi ta kadandane shi, masu daukan hjy iya sun yunkura zasu ciccibeta aykuwa suka taho da saurayin nan, saura kadan su zube kasa gaba dayansu, da hanzari suka maida hjy iya kowannensu ya cika ya kule dan takaici, " daya daga cikin ne yayi magana.


        " wai dan Allah tsofaffun nan ya suke so muyi dasu ne kowanne ana san taimaka masa amma baya gani, nifa na gaji wallahi yau ko su suka haifeni sai haka, nifa bari ingaya muku gaskiya wlh idan mota taxo ko a booth ne shiga zanyi ta wuce dani wannan wacce irin masifa ce haka, dame zamu ji da lalacewar mota koda hadarin da yake ta haduwa ko kuma da wadannan tsofaffun................. Wani daga gefe shima ya karbe, wlh ina bayanka abokina ko tafiya mukayi muka bar tsofaffunan Allah bazai tambaye mu ba tunda iya hakki mun fita hakkinsu, banda ma zuciyar musulci kana ganin dattijuwar nan yanda tasa aka caje mu wai mun daukar mata waya,  hmmm wallahi dandai taimako nada amfani kuma ina duba darajar tsufansu, da tuni ban sabi hanya ba inyaso idan naje cikin garin, wallahi ko a rumfar me shayi zan iya kwana , Allah na tuba dan yan awanni da zan karasa ko a tsaye bana tsaya gari ya waye ba.


Hjy iya dake gefe tana jin irin maganganun da suke yi, cikin nuna jin haushi ta maida musu martani,  " Kai yaro kalle ni nan, gaba daya suka zuba mata idanu kowa ya tattara hankalinsa dan jin me zata fada.


Gori kuke mun saboda kun taimakeni daga mota zuwa bakin bishiya? To idan kunawa Allah da manzan sa kar wanda ya kara taimako na, koda na sakan biyar ne marasa mutumci kawai............. Mu kike cewa marasa mutumci? Dayansu ya katse ta, eh kuna da mutumci ne idan kuna da shi za ku maidani cikin motar nan ne kuma gashi sai gori kuke mun, akaina, " wato burunku inmutu ko?


wallahi baba kina kara kaini bango yanxu da bamu fito dake daga cikin motar nan ba Allah na tuba ko kashin ki idan aka zo za'a samu ne?

A'uzubillahi minashshaidanirrajim bakin bakinka ya koma kanka, mugu me mugun hali, wayyoni wayyo Allah ashe so kake ka kashe ni shiyasa kukaxo ku maida ni na kone, hjy iya ta kara fashewa da kuka.


wani mutum da ke gefensu ya zabga tagumi, ya karaso yake musu magana, dan Allah meyasa kuke biyewa tsohuwar nan ne? bakwa gani rikici ne fal kanta, kuna ganin dai dazu fitsari tayi take cewa jini na bin jikinta, banda abinku sai ku kyaleta duk abunda take yi bata cikin hayyacin ta.


     Amma me gida................. Kayi hakuri abokina nasan da ciwo amma kuyi hakuri, idan akayi hakuri cikin yan awanni zaku ga kowa ya kama gabansa..............


              Wayyo Allah na jama'a ku kawo mun agaji nakai kaina ga hallaka, dan Allah ku xo ku cece ni ku kawo mun dauki, kaina da kafafuwa na sun makale, nikuma wannan itace kaddara ta.

Dan tsoho me buhu ne yake ihu daga cikin mota,  gaba daya suka juya gurinsa suna kallon ikon Allah, wani malolon bakin ciki ne ya zo wa kowannen su,  kamar hadin baki lokaci daya suka saki tsaki cikin takaici da bakin ciki.


kowannen su bashi da niyyar tunkarar motar domin, gaba dayensu kowa jikin sa yayi tsami da gajiya, " ihu ya kara saki wannan karan harda kukansa, yana fadin,  " ku zo ku kawon agaji wuyana da kafafuwa zaku karye.


A hankali suka fara takawa zuwa bakin kofar motar, dukkan su dan tsoho suka zuba ido ganin yanda ya 'kadandane kansa a kofar window.


kafafuwansa da kansa suna ta wajen mota, gangar jikinsa da hannuwan sa, suna ta cikin mota, sai nishi yake da kyar, daya daga cikin su ne ya fara magana,  " dan Allah yanxu ku kalli tsohon nan yanda yasa kanshi a masifa, mota bata kashe shi ba shi zai kashe kansa, a aikin banza da wofi.

Abokina ba tsayawa zamuyi muna surutu ba ay tunda Allah ya hadamu da wadannan tsofaffun kuma sai dai muyi hakuri, wasu su zagaya ni bari na shiga ta ciki ku fara turo kansa mu gani, tunda jikinsa yafi yawa ta cikin motar, da ace hannuwan sa suma sun fita ta window da sai mu tura jikinsa, ku zagaya mu gani.

Zagayawa suka yi aka shiga kiciniyar cire dan tsoho daga window, kuka yake ka shirban yana sharce maji na, da kyar suka samu suka maida kansa cikin motar sannan aka turo kafafuwan sa, lokacin da suka fito dashi daga motar gaba dayansu kowa ya wahala, sai da suka huta cen nesa dasu suka hango driver da kwandasta sun hada kai da gwiwa kamar masu shawara.


Yafuto su sukayi da hannu alamar suna san magana dasu, a gajiye suka taho, suna tafe kowanne fuska babu walwala, suna karasowa wani daga ciki ya jefa musu tambaya.


yauwa, nace ' wai ya ake ciki ne kunga fa dare kara yi yake muna cikin dokar daji nan, sannan gurin nan fa ba dakin iyayen mu bane da zamu saki jiki, bamusan yawan shedanun gurin nan ba, yanxu ba fa ta nake mana ba idan wata muguwar dabbar ta fito tayi mana illa fa?


Kwarai kuwa maganarka akan hanya take, gaskiya atsaida magana daya tunda motocin kowanne, a cike yake zuwa mu tura motar mukarasa cikin gari, idan muka je cikin mutane abun zai xo mana da sauki, wani daga cikin su ne ya kawo wannan shawarar.


    To wadannan tsofaffafun ya zamuyi da su, kuna ganin sunki shiga mota kuma su ba iya wannan doguwar tafiyar zasuyi ba, kai malam kai kake ta tasu su ware kafarsu man tunda ankawo musu mafita sunki, wani saurayi ya bada amsa.


hjy iya tashi tayi tana dan dingisa kafa a hankali, ta zura hannu ta dauki yar jakarta, dan tsoho kuwa yanda suka ajiyeshi yayi dai-dai hk yake bashi da alamar tashi.


Suna cikin haka hasken touchlight suka hango daga cen nesa, gurun suka zubawa kallo suna nan suna jira har suka ga mr tahowar.

wani mutum ne akan amalanken shanu tafe yake akai da shanunsa biyu, baya kuma ya xuba harawa da ciyayi, sallama yayi musu har zai gota hjy iya ta tsaidashi.

Dan Allah dan Annabi yaro ka taimaka ka rage mun hanya motar mu ce tayi hatsari ni ko lada ma sai inbiya ka.......................... Kaf saida hjy iya ta kwashe abunda ya faru ta gaya masa, cikin tausayawa yace ita da dan tsoho me buhu su shigo, da kyar kowannensu ya samu ya hau suka fara tafiya.


Amalanken su hjy iya na gaba motar bus dinsu na baya suna turi, sunyi tafiya befi ta minti goma ba, "aka fara yayyafi kafin wani lokaci ruwan sama ya sauka, lokaci daya suka rafka salati, cikin tashin hankali.


Dan tsoho me buhu ne ya dubi iya yace, oh kinga ikon Allah ko wai ruwan sama ya sauko ammafa zamu sha dukan ruwa, ummm eh, Allah dai ya kaimu lafiya, hjy iya ta bashi amsa atakaice fuska ba alamun wasa, " karasa maganar tayi tana kokarin xuge jaka.


zaninta guda daya ta dauko da hijabi ta hada ta rufe kanta dashi, ta dukunkune guri daya, ruwan sama sai kara karfi yake.


ummm nace ba, dan Allah ko zaki bani zanin ki guda daya, ko yaya dai ragi ay ragi ne, kinga naji saukin dukan ruwan, wallahi larurar mura gareni ko yaya ruwa ya tabani na dinga mura da tari kenan.


Banza hjy iya tayi dashi kamar bataji me yake fada ba.


wannan karan da karfi yake magana, tsammaninsa hjy iya bataji saboda karfin ruwa, yace'  idan bakya san bata wani zanin nace ko inshigo ki dan raba ni daga ciki..............✍🏼

*SISTER'S WAI INA LABARIN HABIBU DA YAN AIKIN HJY IYA NE* ???

*Vote*

*Comments*

*Share*πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

      πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

      πŸ‘œ

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_)

_22/6/2020_

πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

         πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

     πŸ‘œ


*Written* by _Ameera_ _Adam_ { _Mom_ _Aslam_ }

    

    πŸ“š *HADAKA*πŸ“š

   πŸ“ *WRITER'S*πŸ“

πŸ–Š️ *ASSOCIATION* πŸ–Š️

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

@: *Facebook*

_HADAKA_ _WRITER'S_ _ASSOCIATION_+


@: *wattpad*

_AmeeraAdam60_


*SADAUKARWA* *GA* *DUK* *MASOYA* *NA* 😊🀝🏻

_Wannan_ _labarin_ _kirkirarre_ _ne_ _banyi_ _shi_ _dan_ _wani/wata_ _ba._

       13&14

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


Hayaki ne ya fara tirnike motar daga gaba gurin mazaunin driver, gaba daya suka dau salati masu ihu nayi masu addua nayi, cikin hanzari kwandasta ya bude murfin kofa suka fara fita, hjy iya dai sai wasu mutum biyu ne suka dauko ta dan gaba daya ta rude ta gigice idan kaganta ma bazakayi tsammanin tana cikin hankalin ta ba.


Itama dayar motar mutanen cikinta fitowa suka farayi, kowanne zuciyarsa fal fargaba.


Gefen titi suka koma suka bar kwandastoci da drivers kowannen su ya kunna fitila yana duba irin matsalar da motar sa ta samu.


    *A BANGAREN SU HJY IYA*


Tanacen an shinfitar da ita jikin wata bishiya tana sauke numfashi da kyar, sai jero Addua take ba kakkautawa, tana sakin wannan zata kama wata Addua harta shiga bandaki ta maimata ta yafi a irga.


     Allah cikin ikonsa babu wanda yaji mumman ciwo yawancin su buguwa ce mutum biyu ne suka samu kurjewa daga driver sai na kusa da shi.


Hjy iya ma kafarta ce ta bugu amma ganin yanda motarsu ta yi lokacin da zasuyi accident yasa ta rudewa tana tunanin taji mugun ciwo.


Sannu suke ta jero mata wani matashi shi kuma yana ta mata fifita da gefen rigarsa, jitai abu na yawo  daga cinyarta har zuwa tafin kafarta, cikin rudewa ta kara fashewa da kuka tana fadin,   " wayyo ni Allah ashe ajali ne yake kirana, kaico duniya kaico abinda zai kare mu cikin duniyar nan, mutuwa karshen kowa ashe ajali na ne yaxo shiyasa habibu ya hanani tahowa naki yarda da maganarsa.1


Yanxu shikenan nida habibu sai a lahira 😭 Allahu akbar habibu na yafe maka duniya da lahira dama ni ba abinda kamun kullin cikin kyautata mun kake, Allah ya shirya ma zuriyarka habibu, nikam tawa yau ta kare, ganin irin surutun da hjy iya take bame karewa bane yasa wani daga cikinsu ya katse.............. Iya dan Allah ki kwantar da hankalinki duk cikin motar nan babu fa wanda yaji wani matsanancin ciwo ko akwai wani guri da yake miki ciwo ne?


      Cikin rudewa hjy iya ta fara magana yaro nifa tawa taxo karshe, dan Allah ku kira mun habibu a waya, muyi bankwana dashi damin ni nan cikin jiki nake tsamo-tsamo kunga da jinin mutum ya kare ay sai mutuwa 😭, hjy iya ta kara rushewa da kuka.


Aykuwa nan da nan hankalinsu ya kara tashin jin hjy iya tace cikin jini take, da sauri wani saurayi ya ciro wayarsa ya kunna touchlight dama wani dattijo ya kunna tashi fitilar amma batayi hasken wannan ba.


Cikin tashin hankali matashin nan ya cewa sauran mutanen,  " dan Allah yanxu meye abun yi nifa na tsoro ta tunda kunji tace jini ne yake zuba ajikinta gamu cikin dokar daji, eh to hasko mu dubata muga ina ne taji ciwon inyaso ko dankwalinta sai asa adaure ay bama zuba mata ido tana ta fama da ciwo a jiki ba.


Haskata saurayin yayi, mutum biyu daga cikin su suka fara dubata, duk wannan abun da akeyi hjy iya bata daina surutai da Addua ba, " kunga nifa banga wani jini ajikin baiwar Allah nan ba ko kurjewa ban gani va sai dai ko buguwa............ Aykuwa hjy iya tai karaf ta karbe


Wayyo Allah na  ga jinin nan ta wajen kwauri na, Dan Allah  ku biya mun kalmar shahada, ance duk wanda yaxo gangarar mutuwa adinga biya mai ita har sai ya daina numfashi. Sai kuwa ta fara fadin,  " la'ilahaillalahu muhammadurrasulillahi sallalahu alaihiwasallam, Allahumma innanasta'inuka, Rabbana latazuq'alaitana, Bismillahi tawakkaltu alallahi, Amanarrasulu, kulhuwallahu ahad, ihdinassiradal mustakim, ya rahamanu, Algaffaru.............. Aykuwa Hjy iya ta kara ruda musu ciki.


Daya daga cikinsu ne yayi ta maza ya zauna gefen hjy iya ya rungumota jikinsa yana kara duba wajen kafafuwanta tunda yaji tace kwaurinta jini na zuba.


         Yana sanya hannunsa yaji danshi dama daidai gun da hjy iya ta bugu ne, aykuwa ta kara fashewa da kuka wannan karan harda sharce majina tana shashshe'ka.


       Ku dan haskomun sosai kamar fa fitsari ne tayi, "Fitsari fa? Suka amsa gaba daya, " eh, fitsari ne inajin tsoratar da tayi ne, amma ba wani jini kawai dai ta rude ne.


Kuma daina cewa fitsari ne dan ku kwantar mun da hankalina ninasan jini ne, kun fadi haka ne dan ku boyemun, ya za'ay inyi fitsari ido biyu kuma ina cikin hankali na, hjy iya ta sharce kwallah da gefen rigarta, cikin kuka ta kara fadin,   "  nifa yanda nakejin kafar nan tawa nasan ta kakkarye nidai dan Allah ku kiramun habibu yaxo mu gana 😭 banasan inmutu bankara ganin fuskar habibu ba.


Ga dukkan alamu sun fara gajiya da sumbatun hjy iya , cikin kosawa suka ce, " To iya tayaya zamu kira miki wayar habibu bayan dazun nan aka nemi  wayar taki aka rasa.


Ba na ganku da wayoyi a hannu ba dan Allah ku kira mun shi akwai wasiyyar da zan bar masa.


To shi kenan ki kwantar da hankalinki zan kira miki shi amma sai kinyi shiru, ko kinasan akirashi yaji kina kuka hankalinsa ya tashi? Wani mutum ne daga cikin su ya tsugunna yana rarrashin hjy iya, dan ya lura ta tsorata sosai idan bada rarrashi ba sai su wuni su kwana agurin. Kamar karamar yarinya tai saurin girgiza kai, tana fadin,  " a'a nayi shiru wallahi na daina bazan kara kuka ba.


Suna nan tsaye sai ga driver da kwandastansa sun karaso, kowannen su fuskarsa ba wata walwala, kamar hadin baki suka fara tambayarsu, yaya driver da fatan dai babu wata matsala ko?  Eh, to wlh da yar matsala dan akwai abunda ya kone yanxu hk ma nayi-nayi ta tashi ta ki, sai dai akwai wani dan karamin kauye nan gabanmu idan muka dan tura ta zamu samu mu karasa matsalar dai dare yayi ne tunda na tabbata yanxu goma saura,  sai dai ko idan mun samu wata motar mu saka ku aciki, ko mu karasa mu gani ko zamu samu mu saya mu saka.

         Kamar wadanda ruwa ya cinye su babu wanda ya iya magana acikinsu, wadanda suka dauko hjy iya lokacin da wuta tashi yanxu ma su suka kara dauko ta, suna zuwa bakin mota zasu sata  hjy iya ta tokare da hannunta hadi da kara fasa kuka tana fadin............


      Wayyo Allah na jama'a zasu maidani cikin mota ta kone ni, jama'a ku taimakeni ku kawomun agaji, πŸ™†πŸΌ‍♀️ Habibu kazo ka kawo mun dauki.


Wannan karan ba wanda baiyiwa hjy iya dariya ba, dan sosai ta rikice iya rikicewa.


  Motar bus ce taxo wucewa driver su ya tsaidata amma ina, sai horn yayi musu domin motar cike tske da passingers, tsoho me buhu suka gani ya miki gefen titi yana tafiya da dan buhunsa makale a hammata. Da karfi suka kwalamai kira,   " Baba ina zaka kabi gefen titi? Juyowa yayi sai da ya kare musu kallo tsaf sannan yace.........


Yara duk duniya ba abinda nafi tsoro kamar hatsarin mota, yanxu kuma Allah ne ya auna azziki da kwanan mu gaba dan haka ni na yanke hukuncin na tafi da kafa inyaso idan Allah yayi na karasa to idan kuma ta Allah ta kasance shikenan.


Baba wannan fa ba mafita bace, kazo ka shiga mota kaida iya sai mu tura ku tunda driver yace akwa wani dan kauye anan gaba.


Kai yaro raba kanka kaji, idan ka ganni a lahira kaini akai...... zungwi-zungwi tsoho me buhu ya cigaba da tafiya da dan buhunsa a makale.

Yanxu haka zamusa ido wannan tsohon yabi wannan tsohon daren ya mika cikin daji? kunsan fa idan mutum ya tsufa tunaninsa dana yara duk daya yake zuwa, wani mutum ya fada yana daga gefen gunda aka kara zaunar da hjy iya.


Gaskiya kam ba zai yuwu ba domin alhakin tafiyarku duk ta rataya awuya na, tunda nine me motar kuma na karbi kudaden ku, driver ya fada cikin halin jimami da gajiyawa.


Kai me gida muje mu taho da tsohon nan ko yaki ko yaso dan baza mu biye ta tashi ba, wani saurayi ya fada yana maida wayarsa aljihu.


Ay tsoho najin ance za'a taho da shi ya watsar da buhun hannun sa, ya take kafarsa ya manna da gudu....read more

*AMINIYAR ARZIKI ( _Shamsiyya isah_ ) KWANA 2 DA BAKYA ONLINE NAYI MISSING NASAN NIMA INA RANKI AMMA KARKI DAMU WANNAN SHAFIN NAKI NE KE KADAI*🀝🏻


*Vote*

*Comments*

*Share*πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

      πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

      πŸ‘œ

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_)

_23/6/2020_

πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 

         πŸ‘ 

πŸ‘œπŸ‘œπŸ‘œ

     πŸ‘œ


*Written* by _Ameera_ _Adam_ { _Mom_ _Aslam_ }

    

    πŸ“š *HADAKA*πŸ“š

   πŸ“ *WRITER'S*πŸ“

πŸ–Š️ *ASSOCIATION* πŸ–Š️

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

@: *Facebook*

_HADAKA_ _WRITER'S_ _ASSOCIATION_


@: *wattpad*

_AmeeraAdam60_


*SADAUKARWA* *GA* *DUK* *MASOYA* *NA* 😊🀝🏻

_Wannan_ _labarin_ _kirkirarre_ _ne_ _banyi_ _shi_ _dan_ _wani/wata_ _ba._

       15&16

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


Gudu suma suka sa lokaci daya suka rufawa baba tsoho me buhu baya, gudu ya zage yakeyi iya karfinsa amma saboda yanayin girma ga tsufa lokaci guda suka cin masa.+


A tsakiya suka saka shi suna kokarin rike hannuwan sa, dan tsoho yayi wani kukan kura cikin karaji irin yanda jariman india sukeyi idan suka fusata, yasa gwiwar hannuwan sa ya kai musu duka yana fadin, " wallahi bansan da makiya nake tafe ba sai yanxu idan kuka maidani cikin motar nan ban yafe muku ba.1


Ku sake ni na karasa bichi a kafa, idan kuka kaini mota wallahi alhakin mutuwata a wuyanku yake, cikin hanzari suka kara matsowa zasu kama dan tsoho, aykuwa ya yi sauri ya matsa baya hadi da buga kafa daya, ya kara kwalla kara yana fadin, " yeeeeeeeee ku matsaaaaaaaa ko in ma ke kuuuuuuu, ya karasa fada yana dunkule hannuwa har huci yake.


      Daya daga cikinsu ya kallin dayen yace,  " wai kuwa Anya bazamu kyale tsohon nan ba yaje yayi ta tafiyarsa, tunda anasan ceton rayuwarsa yana san yayiwa mutane illa, kana ganin yanda ya kaimun duka a gefen fuska badan na kauce ba da ya gwabjeni yayi mun mahangurba,     " kai haba yanxu tsohon nan ne zai gagaremu, idan aka ce mun kasa kamo shi ba muji kunya ba dan Allah rabu dashi bari kaga muma karfi zamu nuna masa, muna zuwa ciccibarsa zamuyi farat daya  zamuyi masa.


     Aykuwa suka tunkari dan tsoho me buhu, yana ganin sunyo kansa gadan-gadan ya fara kai duka ta ko ina, yana yi yana ja baya sai kuma yayo gaba kamar zai doko wani daga cikin su, yan da kasan yana filin danbe.

Basu bi ta kansa ba, sukub haka suka sun kuci dan tsoho suka mammakure hannusa a hammatarsu sai wutsul-wutsul yake da kafafuwa, yanayi yana wani karaji shi bai yarda ba dole kwacewa zaiyi daga hannunsu.


Bakin motar suka karaso suna kokarin saka dan tsoho sai fisgewa yake yana ciccijewa har suka samu suka tura shi ciki, wani daga gefe ya dan leko su yana fadin,  " to ita ma iya ku sata aciki man, kunga kun huta, idan fa kukayi sake tsohon nan ya kubce wallahi dawa zai shiga, dan na lura motar nan ta tsora tasu dayawa,  juyawa sukayi zasu dauko hjy iya, bayan sun rufe kofar motar, Aykuwa dan tsoho ya Duba, ya waiga yaga duk basa kallansa, ya zura kafafuwan sa ta window.


Gurin hjy iya suka koma da zummar su dauko ta aykuwa ta rike kafar wani saurayi dake kusa da ita, duk tabi ta kadandane shi, masu daukan hjy iya sun yunkura zasu ciccibeta aykuwa suka taho da saurayin nan, saura kadan su zube kasa gaba dayansu, da hanzari suka maida hjy iya kowannensu ya cika ya kule dan takaici, " daya daga cikin ne yayi magana.


        " wai dan Allah tsofaffun nan ya suke so muyi dasu ne kowanne ana san taimaka masa amma baya gani, nifa na gaji wallahi yau ko su suka haifeni sai haka, nifa bari ingaya muku gaskiya wlh idan mota taxo ko a booth ne shiga zanyi ta wuce dani wannan wacce irin masifa ce haka, dame zamu ji da lalacewar mota koda hadarin da yake ta haduwa ko kuma da wadannan tsofaffun................. Wani daga gefe shima ya karbe, wlh ina bayanka abokina ko tafiya mukayi muka bar tsofaffunan Allah bazai tambaye mu ba tunda iya hakki mun fita hakkinsu, banda ma zuciyar musulci kana ganin dattijuwar nan yanda tasa aka caje mu wai mun daukar mata waya,  hmmm wallahi dandai taimako nada amfani kuma ina duba darajar tsufansu, da tuni ban sabi hanya ba inyaso idan naje cikin garin, wallahi ko a rumfar me shayi zan iya kwana , Allah na tuba dan yan awanni da zan karasa ko a tsaye bana tsaya gari ya waye ba.


Hjy iya dake gefe tana jin irin maganganun da suke yi, cikin nuna jin haushi ta maida musu martani,  " Kai yaro kalle ni nan, gaba daya suka zuba mata idanu kowa ya tattara hankalinsa dan jin me zata fada.


Gori kuke mun saboda kun taimakeni daga mota zuwa bakin bishiya? To idan kunawa Allah da manzan sa kar wanda ya kara taimako na, koda na sakan biyar ne marasa mutumci kawai............. Mu kike cewa marasa mutumci? Dayansu ya katse ta, eh kuna da mutumci ne idan kuna da shi za ku maidani cikin motar nan ne kuma gashi sai gori kuke mun, akaina, " wato burunku inmutu ko?


wallahi baba kina kara kaini bango yanxu da bamu fito dake daga cikin motar nan ba Allah na tuba ko kashin ki idan aka zo za'a samu ne?

A'uzubillahi minashshaidanirrajim bakin bakinka ya koma kanka, mugu me mugun hali, wayyoni wayyo Allah ashe so kake ka kashe ni shiyasa kukaxo ku maida ni na kone, hjy iya ta kara fashewa da kuka.


wani mutum da ke gefensu ya zabga tagumi, ya karaso yake musu magana, dan Allah meyasa kuke biyewa tsohuwar nan ne? bakwa gani rikici ne fal kanta, kuna ganin dai dazu fitsari tayi take cewa jini na bin jikinta, banda abinku sai ku kyaleta duk abunda take yi bata cikin hayyacin ta.


     Amma me gida................. Kayi hakuri abokina nasan da ciwo amma kuyi hakuri, idan akayi hakuri cikin yan awanni zaku ga kowa ya kama gabansa..............


              Wayyo Allah na jama'a ku kawo mun agaji nakai kaina ga hallaka, dan Allah ku xo ku cece ni ku kawo mun dauki, kaina da kafafuwa na sun makale, nikuma wannan itace kaddara ta.

Dan tsoho me buhu ne yake ihu daga cikin mota,  gaba daya suka juya gurinsa suna kallon ikon Allah, wani malolon bakin ciki ne ya zo wa kowannen su,  kamar hadin baki lokaci daya suka saki tsaki cikin takaici da bakin ciki.


kowannen su bashi da niyyar tunkarar motar domin, gaba dayensu kowa jikin sa yayi tsami da gajiya, " ihu ya kara saki wannan karan harda kukansa, yana fadin,  " ku zo ku kawon agaji wuyana da kafafuwa zaku karye.


A hankali suka fara takawa zuwa bakin kofar motar, dukkan su dan tsoho suka zuba ido ganin yanda ya 'kadandane kansa a kofar window.


kafafuwansa da kansa suna ta wajen mota, gangar jikinsa da hannuwan sa, suna ta cikin mota, sai nishi yake da kyar, daya daga cikin su ne ya fara magana,  " dan Allah yanxu ku kalli tsohon nan yanda yasa kanshi a masifa, mota bata kashe shi ba shi zai kashe kansa, a aikin banza da wofi.

Abokina ba tsayawa zamuyi muna surutu ba ay tunda Allah ya hadamu da wadannan tsofaffun kuma sai dai muyi hakuri, wasu su zagaya ni bari na shiga ta ciki ku fara turo kansa mu gani, tunda jikinsa yafi yawa ta cikin motar, da ace hannuwan sa suma sun fita ta window da sai mu tura jikinsa, ku zagaya mu gani.

Zagayawa suka yi aka shiga kiciniyar cire dan tsoho daga window, kuka yake ka shirban yana sharce maji na, da kyar suka samu suka maida kansa cikin motar sannan aka turo kafafuwan sa, lokacin da suka fito dashi daga motar gaba dayansu kowa ya wahala, sai da suka huta cen nesa dasu suka hango driver da kwandasta sun hada kai da gwiwa kamar masu shawara.


Yafuto su sukayi da hannu alamar suna san magana dasu, a gajiye suka taho, suna tafe kowanne fuska babu walwala, suna karasowa wani daga ciki ya jefa musu tambaya.


yauwa, nace ' wai ya ake ciki ne kunga fa dare kara yi yake muna cikin dokar daji nan, sannan gurin nan fa ba dakin iyayen mu bane da zamu saki jiki, bamusan yawan shedanun gurin nan ba, yanxu ba fa ta nake mana ba idan wata muguwar dabbar ta fito tayi mana illa fa?


Kwarai kuwa maganarka akan hanya take, gaskiya atsaida magana daya tunda motocin kowanne, a cike yake zuwa mu tura motar mukarasa cikin gari, idan muka je cikin mutane abun zai xo mana da sauki, wani daga cikin su ne ya kawo wannan shawarar.


    To wadannan tsofaffafun ya zamuyi da su, kuna ganin sunki shiga mota kuma su ba iya wannan doguwar tafiyar zasuyi ba, kai malam kai kake ta tasu su ware kafarsu man tunda ankawo musu mafita sunki, wani saurayi ya bada amsa.


hjy iya tashi tayi tana dan dingisa kafa a hankali, ta zura hannu ta dauki yar jakarta, dan tsoho kuwa yanda suka ajiyeshi yayi dai-dai hk yake bashi da alamar tashi.


Suna cikin haka hasken touchlight suka hango daga cen nesa, gurun suka zubawa kallo suna nan suna jira har suka ga mr tahowar.

wani mutum ne akan amalanken shanu tafe yake akai da shanunsa biyu, baya kuma ya xuba harawa da ciyayi, sallama yayi musu har zai gota hjy iya ta tsaidashi.

Dan Allah dan Annabi yaro ka taimaka ka rage mun hanya motar mu ce tayi hatsari ni ko lada ma sai inbiya ka.......................... Kaf saida hjy iya ta kwashe abunda ya faru ta gaya masa, cikin tausayawa yace ita da dan tsoho me buhu su shigo, da kyar kowannensu ya samu ya hau suka fara tafiya.


Amalanken su hjy iya na gaba motar bus dinsu na baya suna turi, sunyi tafiya befi ta minti goma ba, "aka fara yayyafi kafin wani lokaci ruwan sama ya sauka, lokaci daya suka rafka salati, cikin tashin hankali.


Dan tsoho me buhu ne ya dubi iya yace, oh kinga ikon Allah ko wai ruwan sama ya sauko ammafa zamu sha dukan ruwa, ummm eh, Allah dai ya kaimu lafiya, hjy iya ta bashi amsa atakaice fuska ba alamun wasa, " karasa maganar tayi tana kokarin xuge jaka.


zaninta guda daya ta dauko da hijabi ta hada ta rufe kanta dashi, ta dukunkune guri daya, ruwan sama sai kara karfi yake.


ummm nace ba, dan Allah ko zaki bani zanin ki guda daya, ko yaya dai ragi ay ragi ne, kinga naji saukin dukan ruwan, wallahi larurar mura gareni ko yaya ruwa ya tabani na dinga mura da tari kenan.


Banza hjy iya tayi dashi kamar bataji me yake fada ba.


wannan karan da karfi yake magana, tsammaninsa hjy iya bataji saboda karfin ruwa, yace'  idan bakya san bata wani zanin nace ko inshigo ki dan raba ni daga ciki..............✍🏼

*SISTER'S WAI INA LABARIN HABIBU DA YAN AIKIN HJY IYA NE* ???

*Vote*

*Comments*

*Share*πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

       _25/6/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

    _AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


                19&20

   Mungode kaji yaro Allah saka maka dagidan aljanna, Allah ya jikan mahaifa ya raya zuri'a, hjy iya ce ke ta zabga Addu'a tun yana amsawa daga karshe yace iya ku hawo man kunga fa dare karayi yake, nikaina yau rabon zan dauko ku ne ya tsaidani da tuni na manta da naje gida, ku hanzarta mu karsa kunsan tafiya da dare bata da dadi.+


Rufe bakin me amalanken shanu keda wuya, saurayin nan yayi wuf ya d'ane kai, hjy iya saida ta kara kokartawa da kyar sannan ta samu ta kara komawa kai.


Driver da kwandasta  yanke shawarar kwana sukayi amota, wasu sauran mutum hudu suma suka amince, sauran mutum biyar acikinsu akwai dan tsoho me buhu.


Suna nan tsaye sai ga wata motar tirela ta karaso kusa dasu,  wani mutum ne ya bude tempol din saman motar  ya sauko, da 'yar jakarsa a hannu, kafin kace me mutanen nan suka zagaya ta gefe suna neman alfarma gurin driver ya taimaka ya rage musu hanya, ba musu hanya,kuwa yace su bude tempol su shiga, ko sallama basu yiwa driver da su hjy iya ba suka yi tsalle suka kama karfen jikin mota suka haye, mota ta tafi dasu ko waiwaye basayi.


Driver su hjy iya shima cen kasan wani layi, ya gangara da motarsa jikin wani gidan kallo daga dan lungu, bazakayi zaton akwai wata mota agurin ba saboda duhu.


Mutuwar tsaye dan tsoho yayi, ganin duk anwatse anbarshi agurin, wata irin kara ya kwalla cikin karaji ya zuba da gudu gangaren da ya hango su hjy iya sunyi da me amalanke, hadizatu  hadizatu Andizo dan Allah ku tsayani, kun tafi kun barni a dokar daji, wayyo Allah kar kura ta fito ta cinye ni.


Me amalanke ne ya dan tsagaita da jan akalar yace, iya wancen ba mijinki bane yake kiranki ko baki nemi izninsa ba kika hawo amalanken nan? kai yaro ina ganin mutumci da kimarka, waye mijin nawa ? Wancen tsohon to ni nan da ka ganni ba dangin iya bare na baba, haduwar mota rabuwar mota ce.


       Hadizatu magana nake fa kinmun banza dan Allah karki mun haka, gudu yake dan  tsoho buhunsa na biye dashi, duk inda yasa kafa ji kake facal-facal da ruwa har ya kusa karasowa wajen amalanken shanun.


         Maganar gaskiya iya idan kinsan za'a samu matsala ki sauka daga amalanken nan, babu yanda za'ay muna tafiya mijinki na biyo mu har mu karasa gidan me gari, kince ba mijinki bane yanxu idan muka je gidan me gari yayi kara ta wa gari ya waya, kinsan horon da me gari zai  sa ayi mun ne?


Bakin ciki ne ya cunkushe hjy iya ta kasa magana, shi kuma  dan tsoho be daina binsu yana magiya ba, wannan karan y kusa karasowa gurunsu, da karfi yake kwalla musu kira,      " kai yaro me amalanke ka tsaya mana magana fa nake ta muku, cikin kosawa me amalanke ya juya yana tambayar saurayin da suka hau da hjy iya tare,   " Abokina wai wannan tsohuwar ba matar dan tsohon nan bace gwara in tambayeka tunda tare na ganku, kar insa kaina a matsala.


            A dakile matashin saurayin ya bashi amsa, ba matarsa bace kowa tafiyarsa daban.............. Cikin azama dan tsohi ya katse musu magana,  " yauwa to na karaso dan Allah ku gyara mun in haye ciki, da ido kowannen su ya bishi ba wanda yace mai uffan , tunda ya hau yake ta zabga surutu ba kakkautawa, cikin gajiyawa saurayin nan ya kalleshi afusace yace,

                   " wallahi ko ka rufe mana baki ko inwurga ka cikin kwatamin cen, ka damu mutane da surutu kamar ka kone aka, bakinka cakwai kamar wanda akayiwa gorin magana, nan-nan dazu haka ka kusa yimun jini da majina ashe kana sani iskanci ne, kasan kana jin tsoron kurar dazu ka bamu wuya, muna janka kana janmu.


Haba yaro yanxu dan Allah..... Kasan Allah ka kuma cewa tak sai na war'bo ka kasa, inyaso sai kayi me dalili.


Tsit kake ji bakin dan tsohi shiru,  dan  ya tsorota da kalaman matashi ganin yanda yaga fuskarsa ba annuri, shiru ne ya biyo baya ba wanda ya kara cewa ko uffan, dama zuciyar hjy iya fes domin itama suruntun nasa ya dameta, ga yanayin jikin ta kamar batajin dadin sa.

Tafiya sukayi me dan tazara har suka karaso kofar gidan me gari.


_A KOFAR GIDAN ME GARI_


    Me Amalanken shanu ya tsaida shanunsa, ku sauko mun karaso, ya fada lokacin da yake zarge igiyar shanun, saurayin ne ya duro ta saman amalanken sannan hjy iya da dan tsoho  suma suka sauko.


Gidan me gari arufe suka same shi, bugawa suka farayi, tun suna bugu da hannu har sai da suka sa dutse, zuwa cen wani lokaci, suka ji anzare sakata tura kofar me amalanken yayi aykuwa yaji andannota da karfi, da hanzari ya kara turawa yaji ta adatse da sakata.


  Kai wai waye ne da tsohon Daren nan? suka ji anfada daga cen bangaren, Allah ya taimakeka ni ne dama baki ne na taho dasu............. Kai wa? Kuma wadanna irin baki ne cikin wannan talatainin daren nan?


Allah ya baka yawan rai Dan Asabe ne na gidan mariya me waina, Dan Asabe fa? Dan Asabe dai na wajen halilu me shanu? Eh,  shi ne ranka ya dade, a hankali aka fara bude kofar gidan, haske su aka yi da fitilar touchlight irin me jikinta silver nan, sai da mai gari ya kare musu kallo, sannan ya zame jikinsa daga kofar ya fito.


A'a dan Asabe lafiya naganka cikin daren nan harda baki? Allah ya baka yawan rai wadannan mutanen daka gani...


Tas yabawa me gari labari da kuma taimakon da suke san ayi musu, cikin girmamawa ya sa aka shiga dasu hjy iya, wacce tuni ta fara rawar dari saboda dukan ruwan da suka sha.


Dan Asabe na ganin shigar su hjy iya, shima ya ja akalar amalanken shanun sa ya wuce gida.


    Matar sa yaje ya taso tana daki bacci take lakadan, sama-sama take jin megidan nata yana tashin ta, bayani yayi mata sannan ya bukaci da ta bawa hjy iya kaya ta sauya dan ya lura da rawar darin da takeyi tun zuwansu.


Kayansa ya debo ya kawowa  dan tsoho, dan ya sauya shima na jikinsa, dakin jikansa maahe ya leka ya tasoshi, ya umarce shi da ya debowa saurayin da suka xo tare da hjy iya kaya, dan tsoho shida saurayin nan a dakin maahe suka canja kaya, kafin kace me kowannensu y canja kayan jikinsa.

Tuwo aka zubo musu aykuwa kan kace kwabo sun  cinyeshi tas, wanke hannuwa sukayi kowa ya shiga dakin da aka nuna masa.


shigar dan tsoho dakin maahe keda wuya, tari ya turnike shi sai zabga attishawa yake, tari yake sosai saura kadan ya amayar da abincin dake cikin sa.


Hjy iya na kwance tana ta karkarwa sai da matar me gari ta fuskanci halin da take ciki, fita tayi taje turakar me gari ta yi masa baya ni, cikin jimami yake tambayrta ko tana da maganin zazzabi tunda dai yanxu babu sauran rushin wuta bare akai mata taji dumi, wlh mal babu aguri na amma ga wata dabara bari indebo manyan zannuwan gado arufa mata, kaga zataji dadin jikinta jin sanyin ma zai ragu.


Eh, hakan ma da kikayi yayi kyau, ga wancen bawan Allah nan sai tari yake, kai gaskiya ruwan nan ba karamin duka yayi musu ba, eh, wallahi ga kuma jikin girma.


  Idan Allah ya kaimu da safe kafin su wuce sai aje sabon gari a siyo musu magunguna, ko in aika akiramun dafta tanimu ya duba su, to hikenan Allah yakaimu ni bari na wuce naga ya jikin nata, mu kwana lafiya, " sabuwa matar me gari ta bashi amsa.


          Daki ta koma yanda ta bar hjy iya haka ta dawo ta sameta tana ta rawar dari ga zazzabi ruf jikinta, sannu take ta jera mata daga karshe ta debo zannuwan gado guda biyu ta rufa mata.


_WASHEGARI_

  Bayan sallah asuba gari ya fara haske, me gari ne ya shiga dakin jikan sa maahe dan su gaisa da dan tsoho, akudun dune ya sameshi cen kuryar daki kamar kayan wanki, da sallama ya shiga dakin , suka amsa masa, gaisawa  sukayi cikin mutumci da karramawa shi da matashin saurayin nan, cikin tausayawa me gari ya kalli gurun da dan tsoho yake, gaidashi ya farayi yana tambayarsa ya saukin jiki, amsawa yake amma ko kadan ba'ajin me yake fada sai dai aga yana bude baki, har me gari ya fita beji magana daya da dan tsoho ya fada ba.


Dakin da hjy iya take ya shiga ta na kwance kan gadon karfe me rumfa, tana cikin zannuwa a kudundune, gaisawa sukayi yayi mata ya jiki, da kyar take bashi amsa jikinta sai karkarwa yake bakin ta na rawa.


   Da Kansa me gari ya fita kofar gida yasa aka kira masa tanimu ba da jimawa ba tanimu ya karaso jin kiran na me gari ne gashi da farar safiya lokacin karfe, 07:07 am, cikin girmamawa tanimu ya sunkuya ya gaida me gari, " Barka da asuba ranka ya dade, da fatan duk jama'ar gari lafiya? Ina zaune maahe yaxo yace ana san gani na, eh, tanimu dama matsala ce ta harkar lafiya ta taso,  baki ne suka sauka jiya a gurunmu...


( *Tanimu kaf garin gangaren hayi shi kadai ne ma'aikacin jinya, shi kadai ya karancin fannin lafiya,shiyasa suka dauke shi amatsayin babban likita* )


Tas me gari ya gaya wa Dafta tanimu duk abunda yake damun su hjy iya da dan tsoho me buhu.


Gwalo 😳 idanu dafta tanimu ya fara yi yana ja da baya, cikin tsufe fuska me gari ya kalli tanimu  yace, kai dafta tanimu banasan sakarcin banza ya ina gaya maka halin da bayin Allah suke ciki me makon ka basu agajin gaggawa, zaka kafe ni da ido.


Tanimu kara ja baya yayi ya janyo kasan rigarsa ya hau rufe bakinsa da ita, mamaki ne ya kara cika me gari yace, " wato ma dafta tanimu rainin har ya kai ina magana ka toshe hanci, kaniyarka, me gari ya yiwa tanimu dakuwa πŸ–πŸ» ya cigaba da cewa, " wallahi idan bakaje ya taimakawa mutanen cen ba har wani abu mummuna ya faru dasu sai  na dau hukunci me tsauri akanka.


  Bawan Allah nan kwana yayi yana tari yanxu haka muryar sa bata fita.


Tanimu na gama jin zancen me gari ya juya da gudu yana ihu cikin firgici, yana fadin,  " wayyo Allah jama'a kowa yayi ta kansa corona ta shigo garin gangaren hayi........readmoreπŸ€ͺ


*MASOYA NA INA MATUKAR GODIYA GA NUNA SOYYARKU AGARENI, INAYINKU IRIN SOSAI DINNAN ALLAH YA  BAR ZAMAN TARE CIKIN SO DA KAUNA,  KU CIGABA DA SAMBA'DO COMMENT'S KUNA TAKU DAI-DAI INA BINKU DA TURARE, MUJE ZUWA KAWAYEN HJY IYA TA 'DAN TSOHO MAI BUHU IKON ALLAH* πŸ€ͺ


*Vote*

*Comments*

*Share*


       _MOM ASLAM Ce_πŸ˜‰πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

       _27/6/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

    _AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


                20&21


Galala me gari ya saki baki da hanci yana kallon dafta tanimu, cikin jin haushi ya kalli mutum daya daga cikin yan zaman fadarsa yace, " aje ataho da dafta tanimu cikin gaggawa, kirar mutumin ita zata tabbatar maka da kakkarfa ne, tun kafin me gari ya rufe baki haladu ya shuri takalmansa ya rufawa tanimu baya.+


Gudu tanimu yake sosai, yana tafe dafe da hannu aka yana kurma ihu, duk taran mutanen daya wuce da sunji ya ambaci corona zaka ga kowa ya take kafarsa ya manna da gudu, Haule me kosai da koko tana bakin kaskonta, cike yake da masu siya wasu na jira azuba musu su tafi, wasu kuma anzuba musu suna ci,  tanimu suka hango daga cen nesa ya taho da gudu ga mamaki suke kallansa, balele ne ya kasa rufe bakinsa cikin mamaki ya dubi abokan cin kosansa  yace,    " bukar wai kaga abunda nake gani kuwa? Eh, ka rigani afili na riga ka azuci, kamar dafta tanimu nake hangowa.......... Haba balele ba kama bace shi din ne, lawwalu ya katse balele.


To kuwa akwai babban al'amari tunda kaga mutum dan gayu me ji da boko ga taku dai-dai kamar dafta tanimu yana gudu wallahi akwai muhimmin abu......... Kudai kun cika tsoro kamar ba maza ba, kuluwa yar  haule me kosai ta katse su, to dan kunga tanimu na gudu sai me........... Ke raba kanki kuluwa kinsan duk fadin garin nan ansan waye dafta tanimu, mutumin da ko kasa baya san takawa inyana tafiya, balele ya katse kuluwa.


Kai ka biye ta ma walla............. Wayyo Allah jama kowa yayi ta kansan corona virus ta shigo gagaren hayi, wallahi kowa ya killace kansa karya sake yaje gidan me gari inba haka ba shima ya zama marigayi, tanimu ne yake zabga gudu yana wannan surutan daga dan nesa kadan haladu na biye dashi, har ya karaso gurun su balele.


Jin kalmar corona virus ita tafi tsoratar dasu aykuwa azabure gaba daya gurin aka fashe kowa yayi ta kansa, haula batasan lokacin da tayi gaba da kullin kosantaba, kowa takai-takai yake yi, kuma kowannen su idan yaje guri shima gaya musu yake corona ta shigo gangaren hayi, kafin kace me gari gaba daya ya hautsine da labari.


_A GIDAN ME GARI_


   Hjy iya jikin nata ya dan fara sauki, saboda garwashin wutar da aka kai mata najin dumi, matar megari taje kaiwa dan tsoho abincin karin safe daidai soro ta riski maganar tanimu lokacin da yake ambatar corona virus gabanta ne ya yanke ya fadi, cikin tsoro ta karaso gurin hjy iya take labarta mata,     " iya kinji me nake ji da farar safiyar nan, ay wallahi dama nasan za'a rina tunda dama yau sai da nai mafakin maahe yana fadar wasu maganganu yana nuna waje, tunda na tashi dama nake ta wasi-wasi azuciya ta.


To me yake faruwq agarin ne? Hjy iya ta tambaya,  " kinajin wai muguwar abar nan ce ta shigo.......... Wacce aba kuma, hjy iya ta katse ta, wannan cutar mana da ake ta fada mufa nan gaskiya bamu yarda da ita ba, amma tunda kika ji ta fito daga bakin dafta tanimu to ta shigo din.


Magana kike tamun kin ki kigaya mun wacce cuta ce, hjy iya ta fada, cutar nan mana ta korola baros.


😳😳😳 zare idanu hjy iya tayi, tana fadin, wai dama wannan ciwon gaske ne nima fa ban yarda dashi ba, wallahi gaske ne tun da tanimu dai babban likita ne munan duk garin nan idan harkar lafiya taxo mana shi yake magance ta, to kuwa kinga ay maganar wasu-wasi tq wuce.


A zabure hjy iya ta tashi ta janyo kayanta da suke makale ajikin karfen gado, ta fara kokarin sawa.


Tana yi tana salallami, cikin mamaki matar me gari take tambayarta iya me yake faruwa naga kina hada kaya ko karyawa baki gama ba......... Hjy iya ta katse ta,  tafiya zanyi dan wallahi bazan zauna ba tunda dama habibu yaban labari wai killace mutane ake aguri daban nikam gaba zanyi, dama fakewq mukayi saboda dare amma yanxu tunda gari y waye bari na kama gaba na.


Tanimu ka dakata daga nan karka bari inkama ka inba haka ba zaka yabawa aya za'kinta, kasan irin daukan da nayi wa musubahu rannann ko? Haladu ne yake wannan maganar ganin irin gudun da suke yi shida tanimu, dan waigowa tanimu yayi yana fadin naki na tsaya din kaima kayi ta kanka, kara gudunsa haladu yayi da kyar ya samu ya dango wuyan tanimu, sama yayi dashi ya sa'bashi a kafada mutane suka zuba musu idanu kowa na tofa albarkacin bakinsa.


Mutane ne dam'kam suka rufawa tanimu da haladu baya kowa na tafe yana tsegumi, wasu har tuntube suke dan suje gun megari suga wanne irin laifi tanimu yayi da har akasa haladu ya daukoshi.


Wasu ma da suka daurewa karya zani ta bayan layi suka biyo dan su riga su haladu karasawa, aykuwa kafin kace kwabo fada ta cika tayi makil da mutane ansa tanimu a tsakiyar tabarma kowa da abinda yake ayyanawa.


Tanimu na zaune ya janyo gefen rigarsa yana rufe hanci dashi, yana yi yana watsawa mutane harara, hayaniya ce take dan tashi kasa-kasa ana ta tsegungumi, gyaran murya me gari yayi nan da nan kowa yayi shiru.


Me gari ne ya kalli tanimu cikin daure fuska yace,       " Tanimu me ka dauki masarauta ne? Idan kana ganin kai kadai ka samu ilimin fannin lafiya, karka manta ni da kaina naje gidan Alh ya'u tsohon kansilan mu na koki alfarmar ya turaka ka karanci fannin ilimi abirni lokacin ko babbar sakandire baka gama idan baka manta ba sai da mukayi yarjejeniya akan zaka tallafi mutanen garin nan muddin ka dawo, bama wannan ba dazu nakira ka ina maka magana akan bakin da muka samu jiya,  har ka na toshe hanci saboda raini, me gari y kara sunkuyo da kansa ya kalli tanimu cikin daure fuska yace,  " ko ka gaya mana dalilinka ko kuma insa abaka horo me tsanani, domin bazamu  dauki wulakanci da raini acin garin gangaren hayi ba.


Dago da idanuwa tanimu yayi ya karewa mutane kallo, duk inda ya kalla idanunsu yana kansa yana waigawa gefensa ya hada ido da innarsa tana goge hawaye, cikin daga murya san kira ya yi wa tanimu magana,  " kai yaro tanimu kasan a inda kake me gari na saurarenka, dan muskutawa gaba kadan tanimu yayi ya fara magana, cikin toshe hanci,    "   Jama'a salamu alaikum me gari ya sameni yau ya sanar dani halin da bakinsa suke ciki, kuma a bincike da manyan likitocin duniya tayi ta tabbatar da duk mutumin da aka samu yana mura da tari da sarkewar numfashi hade da zazzabi to fa yana dauke da corona virus.

Kuma duk alamomin da na lissafa shine abunda me gari ya sameni yake gaya mun, tanimu kara gyara hannunsa yayi ya kara toshe hancinsa da kyau ya cigaba da jawabi, to atakaice dai abunda nake san gaya muku shine bakin me gari suna da corona virus kai harshi kanshi me gari da iyalan sa ina da tabbacin suma sun shaki wannan ciwon,  hayaniya ce ta kaure gurin kowa da abinda yake fada, cikin bacin rai me gari ya bugawa tanimu tsawa, dakata tanimu bamasan maganar banza da wofi mu zaka kawowa maganar shashanci?  Me kake shirin fada ne.............. Daya daga cikin fadawan me gari ne yadan rissana cikin girmamawa ya fara magana,  " Allah ya baka yawan rai me zai hana abar tanimu ya cigaba da jawabi saboda tunda muke da tanimu bai taba mana irin wannan wasan ba, sai nake ganin dafta tanimu maganarsa kamar da kamshin gaskiya acikinta.

Hayaniya ce ta kaure gurun cikin hadin baki mutanen gurin suka fara fadin,  " tabbas dafta nada kamshin gaskiya, tunda haka kawai bazai yiwa me gari karya ba.


Tanimu ne ya mike tsaye ya cigaba da magana, yanxu kowannen ku dole ya dauki matakin kare kansa, danni nan da kuke ganina babu wanda zan iya bawa wata kariya, kowa tashi ta fisheshe....................... Tarin dan tsoho me buhu ne ya katse shi, juyawa suka daga wajen kofar gidan me gari suka ga dan tsoho ya fito duku-duku, tari yake yi yana tofar da ka-ki gefe gurin taron mutanen daya hango yake niyyar zuwa.


       Aykuwa suka ce me gaba daya mutane suka fara gudu, wasu fadawan me gari malin-malin har tad'e kafarsu take suna faduwa.

_Sorry sister's jiya kun ji ni shiru chani ne babu, ina godiya da kulawar ku iya wuya muna tare_.


*Vote*

*Comments*

*Share*

         _MOM ASLAM Ce_πŸ˜‰πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

       _29/6/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

    _AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


                23&24Kafin kace me guri ya watse  babu kowa sai me gari shida maahe, sai kuma kurar da take tashi agurin,  da sauran takalman mutane harda masu barin huluna da rawani,  me gari kai ya hada da gwiwa bakin cikin duniya ya cika shi, zuciyarsa sai zafi take ransa yana kuna.

+

Maahe ne ya takarkare ya kurma wani ihu, ya fashe da wani marayen kuka me tsuma zuciya, kansa ya cusa cikin cinyoyin sa kuka yake kashirban kamar wanda yaji sakon mutuwa, idan yayi kukan yayi ihu sai ya dago kai ya kalli me gari suna hada ido sai ya takarkare ya kara barkewa da kuka.


*CIKIN GIDAN ME GARI*


   Yanzu iya tafiya zakiyi to ki jira a gayawa malam mana kinga ba dadi ya ganki kin fita yana waje bari inleka dakin maahe idan yana nan insashi ya yi masa magana, matar me Gari ce take rarrashin hjy iya wacce ta debo kayanta ta niyyar tafiya, karamcin ma da kuka nuna mun nagode amma gaskiya tafiya zanyi, ki bari kawai idan na fita mayi sallama dashi nagode ungo wannan, dubu uku hjy iya ta debo ta mikawa matar me gari, hannunta har rawa yake tasa hannu ta karba tana godiya.

To bari intaso miki abokan tafiyar taki ko,  Matar me gari ta fada tana leka dakin maahe, matashin saurayin nan ta samu ya koma bacci, sama-sama yaji ana tashinsa firgigit ya mike, sanar mai tayi da maganar tafiyar hjy iya.


Cikin yanayin bacci ya bata amsa, baabah ki kyaleta ta tafi dama wannan tsohuwar arikice take dama ba tafiyar mu daya ba, kuma kinsan dai yau ba hanya sai laraba ko da  tafiyar zamuyi da ita,  duk maganganun da saurayin nan yakeyi a kunnen hjy iya aykuwa tayi caraf ta karbe,    " yaro karka mun rashin kunya yau dai kowa zai kama gabansa ko na huta da cin mutumcin ku kuma hanya koda hanya ko babu ita ni tafiya ta zanyi ay su ma'aikatan sunsan darajar tsofaffi ba irin ku bane marasa mutumci.


*FADAR ME GARI*

     Kukan da maahe yake yi kamar karawa me gari takaici yake yi abubuwa sun hadu sun cinkushe masa, da me zai ji da ciwon da aka ce suna dashi ko da bijirewar da mutane suka yi masa, sannan shi kuma maahe yaxo ya sashi a gaba yana kuka da ihu, takaici goma da ashirin, aykuwa da zuciya ta debeshi cikin fushi ya d'akawa maahe duka a gadon baya.


( _kunsan dukan da mutum be sanda shi ba yafi zafi_ 🀣)


Aykuwa maahe ya tashi a zaburewa yana gantsarewa da gudu yayi cikin gida yana tafe yana sosa baya, dan tsoho me buhu ne ya karaso gurin me gari yana fadin, haba kai kuwa ya da girmanka da komai xaka dinga yiwa yaro duka irin wannan, ay sai kaje kayi masa illah, wai ma nace ba lafiya naga mutane sun zuba gadu kamar wadanda aka ce ga mutuwa................ Kai dallah rufemun baki duk baku kuka jawomun masifa ba, wallah da nasan zuwanku zai zame mun annoba da ban karbe ku ba da, tunda nake da mutane na ko musu ba wanda ya tabamun muddin ina magana, kai ni bantaba karbar baki masu bakar aniya ba irin su, mutane na suna vari daraja da kima, amma wai yau ni jama'ar garin gangare ni zasu bijirewa.


Kasake dan tsoho ya yi cikin mamaki yake tambayar me gari, laifiya dai kuwa naji kana aybantamu alhalun yau da safe ba haka muka gaisa da kai ba, to bari inyi maka gwar -gwari, me gari ya fada yana kallon dan tsoho, korona boris ita kuka kawo mana, kusan faduwa dan tsohu yayi saboda firgici da tashin hankali.


Me gari kake ko wa??? Saboda munxo gidan ka ka taimake mu shine zaka kulla mana sharri? Ni zaka kallah kace mun inada korola wallah inda cikin birni muke da ba abinda zai hanani inmaka ka akotu, dan tsoho me buhu na cikin masifa tari ya tirnike shi, da sauri me gari yaja baya ya fara rufe hancinsa da babbar rigarsa, daga karshe ma ya wuce cikin gida ya bar dan tsoho sake da baki yana mamakin sauyin da ya gani gurin me gari.


      Shigar me gari cikin gida keda wuya, ya tarar da hjy iya a tsakar gida da yar jakarta a hannu tana niyyar fitowa, cikin tsuke fuska me gari ya kalli hjy iya yana fadin ina zaki? Zan tafi gurin da na fito dominsa, naji ance korola ta shigo garinka gwara intattara kaya na inbar gidan nan tun bata xo ta same ni ba, IYA!  IYA!!  IYA!!! sau nawa na kirawo ki? Sau uku ka kira ni ubana hjy ya ta bashi amsa cikin jin haushi, to Kinsan Allah da girma yake wallahi babu inda zaki, baza ku shigo mana da cuta har cikin gida ba sannan ku tsallake mu ku tafi ku bar mana ita ba kuma ku barmu cikin tsangwama.


Kuna gani tun yanxu mutanen gari sun fara kyamar mu, suna gudunmu........... Hjy iya ta katse shi wai wacce cuta kake maganar mun zo mun kawo muku ita har gida, sai kace masu kanjamu?


Kallan kin raina mun hankali yayi wa hjy iya cikin kunar rai yace,  " au kina nufin duk budirin da akeyi baki ma san me ake ciki ba? To cutar konora boris da kuka kawo mana akanta muke magana,  kuma wallahi nayi rantsuwa harda Allah dukkanku ba me tafiya.

Suna cikin magana sukaji dan tsoho ya shigo yana fadin, " harni kake nufi  bazan tafi ba me gari, tabdi ashe akwai yakin badar na biyu a gidan nan.


Yanxu kai maahe dauko mun kuuba πŸ—️ ka rufe mun gidan nan, me gari ya umarci maahe, cikin sauri maahe ya wuce dan shima acike yake da su hjy iya tunda sune suka shigo musu da annoba gari.


Rufe kofar gidan maahe yaje yayi ya dawo yana kallonsu hjy iya dai-dai, sai muzurai yake aykuwa hjy iya ta cika tayi fam sabida bakin ciki, sai huci take lokaci-lokaci tana bussar da iska, yar da jakarta tayi gefe guda ta zauna, dan tsoho me buhu gaba daya ransa ya 'baci zuciyarsa ajagule, yana nan tsaye ya hada kai da jikin bango da ya waiga sun hada ido da me gari zai gasawa me gari harara shikuma  dan tsoho da sun hada ido da maahe shi kuma sai ya feshe shi da hararara, ya dunkule hannu ya nunawa dan tsoho alamun naushi, sum-sum-sum ya sunkuyar da kai kasa.


Suna nan zaune har zuwa wani lokaci kowa yayi jugun-jugun cikin zuciyarsu kowa da abinda yake ayyanawa, wata shawara ce ta fadowa baba dan tsoho saboda murna har sai da yadan murmusa afili, aykuwa adai-dai lokacin suka hada ido da hjy iya, cikin jin haushi  ta ga sa masa harara.


Bai bi ta kanta a zabure ya mike tsaye, ganin haka yasa maahe zuwa bakin kofar ya tsaya, d'an tsoho ko ajikinsa  waige-waige yake yi cen gefe kusa da matar me gari ya hango dan buhun sa, da sauri yaje ya wawuri abinsa ya ma'ke shi a hammata gam cen kuma sai ya fara muzurai, gaba dayan su kowa ya zuba masa ido suna jiran su ga me dan tsohon yake shirin yi.


Kwarara ihu yayi da karfi cikin karaji ya kai duban sa zuwa katangar gidan me gari, ya waiga ya kallo dakin matar me gari na kallon katangar, aykuwa ya kara kukan kura ya zura dakin matar me gari da gudun gaske.


   Ganin haka yasa matar me gari rafka uban salati tana tafa hannuwa, me gari beyi wata-wata ba ya rufawa d'an tsoho me buhu baya cikin dakin, yana shiga ya ganshi sunkuye yana nad'e kafar wandan sa, me gari na shirin yi masa magana aykuwa sai ji yayi dan tsoho ya kurma kalmar shahada kamar me shirin shiga filin yaki, yana ma'kale da dan buhunsa ya tunkari kofar dakin, da sauri me gari ya matsa gefe, yana ganin dan tsoho ya fita da gudu shima ta rufa mai baya dan a tunaninsa besan barnar da dan tsohon xai aykata ba.


    Gadan-gadan dan tsoho ya nufi katanga ya na gudu yana kalmar shahada yana hadawa da ihu, caraf dan tsoho ya rike katanga yana shirin dora kafarsa wani gefen daya tsage ajikin katangar ya yo baya aykuwa dan tsohon  ji kake luuuuuuuuuuu yayo baya, dai-dai lokacin me gari  yaxo wajen katangar aykuwa dan tsoho yayi kan me gari suka zubo kasa ragwabπŸ™†πŸΌ‍♀️


Kowannan su yaji jiki gaba daya ihu suka saki kowa yana wayyo Allah.


   *GIDAN ALH HABIBU*


Alh habibu suna zaune da safe kimanin goma da 'yan mintuna na safe shi da yalansa, hira suke gwanin ban sha'awa da birgewa sun hadu a babban falo kowa na cikin annushuwa da farin ciki, khaleed ne ya shigo cikin falon hannunsa rike da waya akunne dan karamin tsaki yaja lokacin da yake kokarin zama akan kujera, Eman ( _Me sunan hjy iya_) ta kalle shi ta dan sunkuyo da kanta gefensa tana kasa-kasa da murya, tana fadin.

                    " bro kai kuma lafiya ka shigo kana tsaki?  Shafa πŸ‘‚πŸΌmun ko wata ta 'bata maka rai neπŸ€ͺ ta karasa maganar cikin sigar tsokana.


Hararar wasa ya sakar mata yana fadin,  " kedai kin cika son jin gulma wallah, kallan mahaifiyarsa yayi yana mata magana,  " mami dan Allah bani aron wayarki inkira hjy iya wallahi tun jiya da daddare nake kira, idan na kira sai ace mun akashe, nidai nasan wayar hjy iya 24/7 akunne take ko tawa wayar ce take san ta bani matsala.


     Gaskiya kam sai dai in wayar ka ce dan jiya ana sauko daga Edi Eman ta kira mana ita dukkanmu mukai mata barka da sallah, kuma hjy iya wayarta da kullin ka nema kana samu kila dai harda matsalar network, matar Alh habibu ta biyu da suke kira da mama ita tayiwa khaleed wannan bayanin.


Kaje falo na ka dauko wayar tana kan kujera sai ka gwada kira ko zata shiga, mahaifiyarsa ta bashi amsa, tashi yayi ya wuce falon mami su kuma suka cigaba da hira Alh habibu yana danna laptop dinsa yana dan sa musu baki.


          Wayar Alh habibu ce ta fara ringing sa'adatu ne ya fito akan screen din ( _yar Alh habibu me aure da yarinya daya_ )


( _badan halinki ba na shafa da sunanki 😜 nasan kinsan kanki_)


Da sallama ya amsa bayan sun gaisa ta shiga yimasa bayani kamar haka,   " Daddy wai meyasa mu wayar hjy iya ne jiya Abban khairat ya kira zai mata barka da sallah yaji ta a hannun wani, da muka kara kira sai mukaji a kashe yanzu haka na kara kira sai naji ta shiga yana dauka sai cemun yayi wai kar inda me shi da kiran waya harda yi mun tsaki ya kashe..................... Whaaaaaat? Alh habibu ya katse ta cikin tashin hankali, what do u mean? wait bari na kira naji.


Gaba daya falon sunyi cirko-cirko ganin irin yanda yanayi mahaifin nasu ya sauya lokaci daya sun san ba lafiya.


Cikin hanzari ya fara kiran no hjy iya da farko da ya kira akace is not reachable daga baya ne wayar ta shiga, har tuntuben harshe yake yi cikin sauri ya fara magana,  "hjy iya, daga cen bangaren wanda ya dauka ya fara magana cikin maye,   " kai wai wane gara ne yake san takuramun cikin early money din nan ko warwarewa mutum bai gama yi ba? Yana gama maganar yaja tsaki ya kara kashe ta gaba daya.

Cikin tsananin fushi da tashin hankali Alh habibu ya furta *This is possible* da karfi ya fada har sai da yan daki gaba daya suka tsorata.......✍🏼


     _Wayyo Allah πŸ™†πŸΌ‍♀️su lauwalu kunga ta kanku hjy iya ta shafa muku kashin kaji_


*Ahayye sha madarar lilo πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ sister's nagode kwarai da yanda kuke kara bani kwarin gwiwa ku cigaba da gashi suya sai ranar sallah Iya wuya iya dadi ana tare*


*Vote*

*Comments*

*Share*

       _MOM ASLAM Ce_πŸ˜‰πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

       _1/7/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

    _AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

@: *Facebook*

_HADAKA WRITER'S_

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


                25&26


Tashin hankali wanda ba'a sa masa rana, huci kawai Alh habibu yake yi gaba daya ransa ya gama baci ga tsananin tashin hankalin da yake ciki, shin me yake faruwa da hjy iya ne? Wa ye ya dauki wayar hjy iya kuma ta yaya har aka shiga cikin gida aka dauki wayar hjy iya me yake faruwa a gidan ne? Amma da ace akwai wani abu daya faru ay zai ji labari ko agidan makotan su hjy iya tunda duk abokan arzikinsa ne wasu ma abokansa ne, Alh habibu shi kadai yake jerowa kansa wadannan tambayoyin, cikin tashin hankali yake ta furta innalillahi wa'inna ilahirraji'un, sa kaiwa yake yana dawowa, gaba dayan yan falon duk sunyi tsuru kowa hantar cikin sa ta kada.+


Duk sunyi carko-carko aka rasa me yiwa Alh habibu magana, su dai sunji ya ambaci hjy iya tunda suka ga ya canja yanayi suka san tabbas akwai gagarumar  matsala, mami ce tayi karfin halin tambayarsa kirjinta na bugun uku-uku,   "  Daddyn yara me yake faru da hjy iya ne naji ka ambace ta kuma ga yanayin ka duk ya sauya Allah yasa dai babu wata damuwa? Cikin hanzari ya bata amsa matsala kam akwai ta, wayar hjy iya ce a hannun wani yaro da alama ma irin yan shaye-shayen nan ne amma ina zuwa bari naje gidan yanxu.


Yana gama bata  amsa be jira cewar su ba da hanzari yayi get gurin motoci, cikin gaggawa ya shiga horn yake yi ba kakkautawa da gudu ma'awiya me gadi ya fito domin bai saba jin irin wannan horn din ba, har yana shirin yin masifa ganin motar Alh yasa shi saurin wangale get, tun ma'awiya bai karasa  bude get din ba Alh habibu ya danna kan motar sa ya fice da gudun gaske.


     Ma'awiya ya jima a tsaye yana jimamin halin da ya ga me gidansa aciki, tabbas ya san akwai wata gagarumar matsala data taso dan bai taba ganin sa acikin irin wannan halin ba, jiki a sanyaye yaja get din yana ta'ajibi.


Alh habibu driving yake kamar zai tashi sama duk get din da yaje na titi police da sun tsaida shi ji yake kamar karawa tafiyarsa tsawo suke yi, da sun tsaida shi sun tambaye shi ina zashi saidai yace musu mahaifiyarsa ce aka kirashi bata da lafiya ganin yanayin da yake ciki babu inda ya sami matsala.


Ikon Allah dai shi ya kai Alh habibu unguwar na'ibawa da wani kafirin gudu ya sha kawanar gidan su hjy iya, layin tas yake ba wani alamar damuwa ko tashin hankali yanda ya sa ba ganinsa idan yaje yau ma haka layin yake zuciyarsa ce ta dan fara lafawa.

Horn yake dannawa na tashin hankali ba kakkautawa, lauwali dake dakinsa yana bacci cikin bacci yake jin horn kamar zai fasa gidan afirgice ya mike yana mirza idanu ta dan karamin window din dakinsa ya leka, motar Alh habibu yayi tozali da ita wani irin yamutsawa cikin sa yayi nan da nan gumi ya shiga karyo masa jikinsa har karkarwa yakeyi.


Safa da marwa ya fara yi a dakin daga farkon bangon dakinsa zuwa karshe, ji yayi andakata da horn din ya sauke ajiyar zuciya yana dafe kirji, bai karasa ba yaji anshiga bugun kofar kamar za'a balle ta, da gudu lauwali ya fitar harabar gidan cen bayan dakin su inna zainabu ya shige jikin wani dan lungu ya rabe sai raba idanu yake.


Inna zainabu dasu suwaiba suma a daki kowannen su ya kasa zaune ya kasa tsaye, hansai ce ta kalli inna Zainabu tace,     " inna zainabu na tabbata Alh ne yaxo yake wannan horn din yanxu kuma kinji bugun kofa mukam yau mun shiga uku.............. Katse ta Suwaiba tayi tana  sharce gumin goshinta ta ce,  " to ina lauwali yake kinji shiru har yanxu bai bude ba ko baccin asarar yake yi,  ke suwaiba wannan wanne irin bacci ne hk sai dai in yana bandaki, inna zainabu ta basu amsa sannan ta kara da cewa,    " yanxu dai wani acikin ku ya je ya bude kofar kar laifin mu ya karu............... Cabdi, hansai ta katse inna zainabu, wallahi bazan je ba haka kawai duk abinda ma zai yi wato a fara ta kaina sai dai suwaiba taje, wallahi bazani ba sai dai a mutu har liman arasa me jan sallah, suwaiba taba hansai amsa, inna zainabu ce tai karfin hali ta tunkari get din kirjinta sai lugude yake tana tafe tana motsa baki ga dukkan alamu addu'a take karantowa 🀣

Kofar take san budewa Amma ilahirin jikin ta karkarwa yake yi har iya lokacin Alh habibu bai daina bugun gida ba, karfin ta tattaro da bismillah ta bude kofar, aykuwa da karfi ya hankado kofar saura kadan inna zainabu ta bugu da bango, jikinta na karkarwa har tuntuben harshe take yi tana yiwa Alh habibu magana,       " Alh iya sannu da zuwa ina kwana ya hanya, duk lokaci daya inna zainabu take jero masa gaisuwar nan, fuska ba walwala ya kalli inna zainabu, fuuuuu ya wuce ta ko ta kan gaisuwarta bai bi ba, direct sashen hjy iya nufa yana zuwa bakin kofa yaci karo da garnakeken key, daaammm kirjinsa ya buga jikinsa har rawa yake yi da sauri ya juyo sashen su inna zainabu.


Tun daga harabar waje yake kwallawa musu kira, Zainabu! Zainabu!! Zainabu!!! ( _yau ba innar ma_ πŸ€ͺ) ke suwaiba kuna ina?  Har gwaren kawuna suke yi suna bangazar juna, sum sum sum kowaccen su taxo ta tsugunna suka sunkuyar da kai, *INA HJY IYA*? Alh habibu ya tambaye su, ji sukayi kamar ya buga musu guduma, cikin inda-inda suka fara magana, eheeyyy na'aamm dama  eh dama jiya ne ta ce mana zata tafi kauye....... Kau me? A zafafe Alh habibu ya katse su.


    Tsilli-tsilli  sukayi kowa ya hau raba idanu, cikin kausashiyar murya yake tambayar su,    " Ina Auwalu driver yake? Shiru sukayi sai zuwa cen hansai tace ay tun jiya da yamma daya shigo ya ajiye mota ya fice bai kuma dawo wa ba.


    Kuna nufin ajiyan bayan yabar gidan gona ta ya dawo gida ya kai hjy iya har ya dawo gida, shiru ne ya biyo baya suka kara sunkuyar da kai kasa, cikin tsawa ya ke musu magana, " ba tambayar ku nake yi ba? Atare suka fara magana, iyeee na'am dama cewa tayi tasha zata je ta hau mota, suka karasa maganar suna satar kallan sa ta kasa, aykuwa a zabure yace, *TASHA*? *HJY IYAN CE TA TAFI TASHA HAWA MOTA*?

  *MU KOMA KAUYE*

Me gari shi da dan tsoho me buhu sun bugu iya buguwa me gari ma da yake shine ya bugu da kasa yafu dan tsoho jin jiki sosai, matar me gari ce ta taho da gudu tana sallallami , da kyar ta samu ta d'ago me gari ya dafa jikin bango ya mike tsaye, kafadarta ya dora hannun sa tafe suke yana dan dingisawa.


'Dan tsoho tunda suka fado ya baje a kasa dai-dai ya kasa motsi, sai salati da yake ta jerowa, ganin matar me gari ta janye me gari yasa dan tsoho karkace kai gefe yana fadin,   " Hadizatu ki taimaka nima kixo ki tafi da ni kina ganin yanda matar me gari itama taxo ta tafi dashi, ( _kuji tsoho da rikici_🀣).


Hjy iya yi tayi kamar bata san ma ke yake fada ba, maahe da ke gefe yana yiwa me gari sannu yace,  "  iya anya kinasan ki zarce cikin salama ki wuce Aljanna ba dauraya kuwa, kina gani mijinki yayi tamola daga katanga sannu ma ta gagara, gashi sai kwala miki kira yake ki taimake shi kin'ki ko amsa masa............ To ubana, hjy iya ta katse shi, shi din da kake balokoko akansa meye hadina da shi ubana ne ko miji na kai da shi idan aljannar taku ce innazo shiga sai ku tad'e mun kafafuwa, kai nikam yau naga ta kaina ina ganin rayuwa ni hadizatu, hjy iya ta karasa maganar idanunta na zubda hawaye.


Matashin saurayin da suka xo da su hjy iya yana daga d'aki duk abinda suke yi akan idon sa, kai tsaye fitowa yayi ya tunkari gun da dan tsoho yake, tsayawa yayi akan sa yana nazari cen ya hango wata kujera abakin murhu da sauri yaje ya dauko ta ya ajiye jikin katangar, da karfin gaske ya sunkuci dan tsoho, dan tsoho me buhu har yana kara kwantar da kai cikin jin dadi ya fara yiwa matashin godiya.


A kafadarsa ya dora dan tsoho ya taka kujera ya dora dan tsoho kan katanga, yayi saukowarsa ya koma gefe ya sawa dan tsoho ido, ihu dan tsoho ya saka yana neman dauki,   "  wayyo Allah na ku taimaka ku sauko dani zan kuma fad'owa, dan Allah kuxo ku kawon d'auki, wannan ciwon na corola bai kashe ni ba yaron nan zai kashe ni.


Wannan maganar da dan tsoho yake yi tayi dai-dai da zuwan wasu mutane da suka xo tsegumi saboda labarin da aka basu na zuwan bakin da suka xo da cutar corona virus.


Zaro idanu suka yi daga dan nesa da dan tsoho, shi kuma ganin suna kallonsa ya kara sakin marayan kuka yana fadin,     " jama'a ku taimaka mun wannan cutar bata kashe ni ba amma yaron nan yanasan kashe ni, su kuwa akunnen su sam ba haka sukaji ba, ji sukayi kamar yana cewa wannan cutar zata kashe ni.


Aykuwa suka ce kafa me naci banbaki ba, ta cikin kasuwa suka ratsa suna isa suka fara haki saboda gudun da suka sha majalisar idi me shayi suka tsaya, mutta'ka ne  ya kalle su yace,  " d'an lami meye haka kukeyi kamar kananan yara yanxu gudu kuka yo......... Eh gudu mukayo, sha'aibu ya katse, kai kaga dama haka wannan ciwon gidan me garin yake ? Cikin son jin gulma idi me shayi yace,  "me  yake yi ciwon, hummm bari ashe mutum har tashi sama yake yi ya dinga ihu idan ciwon ya motsa, kai ka bari dan Allah muttaka ya tambaya, wallah kuwa ganin ido na naga wani tsoho a sama yana ihu, cabdi kace nida me gari har abada kenan, idi ya fada yana mikawa muttaka biredinsa, kai ware wani Abokina da yake birni rannan mukayi waya yake gayamun sahihin maganin wannan ciwon nalami ne yake magana yana kurbar shayi, cikin hadin baki suke tambayar sa.


Mene ne maganin? Eh to, sha'anin ne kunsan kar kace ayi amfani da wani abu azo asamu matsala adinga maka dan biki, kai dai na lami ka gaya mana tunda karuwar mu ce gaba daya mutta'ka ya fada, A'a ba mayi abu da ka ba mu nemi dafta Tanimu muji ta bakinsa, idi me shayi ya fada, to shikenan bari mu karasa shan shayin nan sai muje gurinsa.


*GIDAN MEGARI*


Kai tsoho karka ishemu da ihun banza da wofi, ba kantagar zaka hau ba to ga fili ga me doki dama ka saba da kurarin karya ay, ka manta daren jiya ka ce mana zaka shiga daji ka karasa bichi a kafa? wannan karan dan tsoho harda hawayensa kuka yake wiwi,  sai da ya jima a haka sannan matashin saurayin ya sauko dashi.


Matar me gari ce ta dora musu ruwan zafi a tukunya bayan ya tafasa ta sauke musu ta fara gasawa me gari gurin buguwar da yayi, shi kuma dan tsoho ya fara gasawa da kansa.


Bayan kimanin awa buyu da rabi, wajen karfe goma sha daya suna, suna zaune kowa yayi jugum, bugun kofa suka ji da sauri maahe ya sa kuuba πŸ—️ ya bude kofar, Dafta tanimu ya gani cikin wata iriyar shiga hannunsa dauke d wani zabgegen tiyo ( _irin wanda yan bunburutu suke zuko petir da shi_) ........πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

       _5/7/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

    _AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


                27&28


Tun daga sama har kasa maahe ya tsaya yana karewa Dr tanimu kallon mamaki, wata shiga ya ganshi da ita da bai taba gani ba, riga me hade da wando ce ajikin sa na buhu ga wani kwabcecen takalmi akafarsa fuskarsa ya nade ta da wani farin kyalle hannuwan sa sanye da safa daga sama an kara buhu annade shi, hannunsa ne rike da zabgegen tiyo, nalami na rike da wani inji irin wanda ake yin ban ruwa dashi a gona, muta'kka da idi sun karaso da wata amalanke andora mata garwa manya-manya guda hudu kowacce cike take da wani irin ruwa me wani irin launin kala.+


        Dr tanimu lafiya naganku haka kamar masu shirin zuwa yaki anya lafiyarku kuwa, maahe ya fada yana karewa su muttaka kallo da suke ta hidima da amalanke, lafiya klau agajin gaggawa ne muka kawo muku nida su nalami, ina megarin yake................. Wai maahe su waye ne najika kuna magana dasu kuma maganar taki ta kare, matar me gari ce ta katse musu maganar da sukeyi lokacin da ta leko.


Washe baki ta shiga yi cikin farin ciki take fadin au Dafta tanimu ne barkanka da zuwa likita bokan turai, yauwa inna ayi mana sallama da me gari inasan magana dashi, tun kan dr tanimu ya rufe baki megari ya dingiso yana fadin waye yake nema na gani nazo ina fatan dai lafiya.


Au dan nema ka kara zuwa ka cimun mutumci ne har gida tunda yanxu naga harda mukarrabanka ka taho , shi ne duk kuka toshe hanci ko, to mungode basai kun kara dizgamu ba wanda ka mun daxu ma nagode kai maahe ke wuce muje ci............ Dr tanimu katse me gari yayi da, Allah ya baka yawan rai taimako ne mukaxo kawo muku game da ita wannan cuta da kuke da ita, nalami yaje ya same da maganar cewar abokinsa ya gaya masa wadansu abubuwa da ake hadawa a gargajiyance,  wanda kuma yace acen gurinsu angwada kuma cikin ikon Allah ansami nasara, da farko ban gasgata maganar ba sai da nayi waya da wadanda aka gwada musu kuma suka warke, kuma sai da na duba naga shin idan anyi amfani dasu babu wata illah da zatayi wa mutum, sannan a likitance nayi wani bincike na gano wadansu magunguna da idan na hada na baku za'a samu waraka, akarshe ina neman gafarar me gari bisa kuskuren da nayi ayafemun na tuba sharrin shaidan ne da kuma firgici domin lokacin ina cikin firgici da tashin hankali.

   Ajiyar zuciya megari ya sauke, sannan yace, duk naji bayanan ka kuma na gamsu sai dai baka yimana bayanin irin magungunan ba, da yanda za'a saraffa su, kuma su wadannan rigunan buhun da kuka sassaka maganin me sukeyi sannan ta kan wa za'a fara gwajin maganin?


Gwajin magani ay ba wani abun damuwa bane Allah ya baka yawan rai, ko da kai ay sai a fara gwadawa, su kuma rigunan nan daxu nasa yakubu ya dindinka mana su sune suke bada kariya ga wadanda basu da wannan cutar, su likitoci a birni ba irinta suke sawa ba amma nan tunda bamuda irinsu sai na yanke shawarar bari na sa a dinka ma buhunhuna (🀣 _chaiii tanimu wai kuwa dr gaske ne_πŸ™„).


     Sannan sukuma magungunan gasu zan maka bayaninsu.


Wancen katon buhun dake hannun idi ni'ka'kken rogo  ne wanda aka hadashi da tafarnuwa da kajiji sai dan kaninfari da aka kara dashi kadan.


Waccen amalanken shanun kuma garwoyin cen da kuke gani ruwan tafarnuwa wanda aka hada da ganyen rai dore ne, sai alimun da dan tsami da karin dan gishiri aciki, za'a dauki garwa daya a tafasa shi sai axuxubawa kowannen ku yayi sirace da shi, sauran garwa ukun da suka rage kunga wancen injin na hannun nalami za kunna shi ajonashi, sai nad'e muku idanunku da wani kyallen saboda kar afara yi muku feshi ya shiga ido.

Ita kuma wannan tafarnuwar zaku dinga bare ta kamar cikin murfin buta kuna hadiya ba'a tauna ta hadiya zakuyi da ruwa.


Ga matakan da ake bi domin fara wadannan magungunan, da farko feshi za'a fara muku sai wannan garin nikekken rogon zaku shafe jikinku dashi kuna gama shafawa zakuyi sirace sai ku dauko tafarnuwar nan da ruwa ku hadiya idan kuka gama zakuyi wanka da ruwa sannan anasan ku yawaita cin Albasa,  sai kunyi haka na tsawon mako guda.


Sai kuma na baturen shi wannan ko da na muku bayani bazaku gane ba kawai saidai intsara muku yanda zaku dinga sha, wannan bayanin da na muku shi zamu aywatar muku duk wanda ya bijire kuma, wallahi sai na kira hukumar *NCDC* inyaso suzo su tafi dashi dan karkuxo muma ku shafa mana ita, to kaji yanda abun yake ranka shi dade.

Dafta tanimu ni banki ta taka ba amma maganar gaskiya baza'a fara gwadawa ta kaina ko iyalina ba, su bakin da suka zo da ita ta kansu zaku fara idan muka ga yanda abun ya kaya shikenan.


Hjy iya fitowa tayi taci karo da maganar me gari cikin jin haushi tace,  " to mugu maketaci aniyarka ta bika mugu me bakar aniya wlh daga kai har yan garinka babu wanda ya isa yace zai shafa ko fesamun wani abu azzalumu.


Maahe ya kalleta cikin jin haushi yace,   " kakan nawa kike zagi kuma a gaba, kai dafta tanimu wai me kuke jira da bazaka yi hobbasa ka fara ta kan tsofin nan ba tunda kana ganin irin abubuwan da suke mana, d'azu haka tsohon nan yaso yaja mana masifa, yooo masifa mana idan ya karya me gari ayni ya cuta shi kuwa karkari indauke ahi inkai shi gefen hanya, Dan Allah dafta tanimu kayi da gaske ka fara yi musu maganin nan dan wallahi inba haka ba sai sun nemi su ja maka masifa, da hanzari dafta tanimu yasa su nalami  fara shiga da kayan aikin, ganin haka yasa hjy iya banka kofar ta shige da gudu d'akin matar  me gari tana rafka salati.


*GIDAN HJY IYA*

          Alh habibu dafe kansa yayi cikin tsananin tashin hankali, cikin firgici da bacin rai ya dubi su inna zainabu yace,   " wace tasha tace muku zata je lokacin da zata fita?    Alh wallahi bata ce mana ga tashar da zata ba munyi-munyi karta tafi amma............. Cikin bacin rai Alh habibu ya katse suwaiba da take ta jero masa jawabi, ina Audi ya tafi? Cikin kausashshiyar murya   Alh habibu yake tambayar su.


'Dazu dai dana fito wanke-wanke yana cen gurin a zaune amma bansani ba ko bacci yake hansai ta bashi amsa, ke suwaiba jeki duba mun dakinsa ki kirawo munshi Alh habibu y umarce ta, har tuntube suwaiba take jiki na 'bari taje kiran Audi tana shiga daki taga dakin wayam, da sauri ta fito taxo tana sanarwa Alh habibu cewar Audi baya nan, iya bacin rai aykuwa Alh habibu ransa ya kai kololuwa, cikin fada ya fara magana.


                 " wato dama haka yake tafiyarsa yabar gida abude ko to wallahi ................ Ringtone din da wayar sa take yi ne ya katse masa maganar da yakeyi.


Da sallama ya amsa, mami ce dai still ta kara kiransa dan taji meke faruwa a gidan hjy iya, cikin yanayin damuwa take magana,  " Alh munji shiru ne nace bari na kira dan muji yanda ake ciki, tas duk abinda yazo yasamu ya gaya mata aykuwa suka hau sallallami, basu jima suna waya ba ya katse kiran.


Number wani kawunsa ya kira wanda ke kauyen rigana, dama hjy iya duk zuwan da tayi ta gidansa take fara  sauka ta kwana daya daga nan sai taje duk inda tai niyya, cikin girmamawa suka gaisa karaf kawun nasa ya jefo masa tamabaya, " habibu ya hadizatu ne wallahi naso  zuwa inyi mata barka da sallah amma dan Allah idan ka je kace  mata sati na sama zan shigo danma wayar tawa jiya aka maidomin ita daga gurin gyara, Daaam kirjinsa ya buga nan da nan ya shiga wani tunani, kawun nasa shiru yaji na dan wani lokaci yana ta masa magana sai zuwa cen Alh habibu ya amsawa kawun nasa daga nan sukayi sallama.


      Gudun kar ya d'aga musu hankali yasa Alh habibu bai tambaye shi hjy iya bata karaso ba ne, number wata innarsa ya kira itama suka gaisa daga karshe ta bashi sa'kon gaisuwar ta gurin hjy iya, aykuwa cikinsa ba karamin ruwa ya dura ba hankalin sa ya kuma tashi, saboda tsananin bacin rai idanunsa sun kad'a sunyi jawur.


   cikin hanzari wata number ya nemo anyi saving din ta da *DPO  sharada* Dialing no yayi daga daya bangaren aka fara magana.

                   " Allah ya taimaki me gidana da kansa Abokina ka manta dani fa rabonda muyi waya fa tun kafin azumi........ Abokina akwai matsala Alh habibu ne ya katse shi cikin damuwa, meyake faru wace irin matsala? Ce duk lokaci daya Dpo ya jerowa Alh habibu tambayar, wallahi Abokina hjy iya ce------------------- tas Alh habibu ya kwashe ya gaya masa abinda yake faruwa.

Inalillahi wa'inna'ilahirraji'un Abinda DPO ya furta kenan, cikin damuwa yace, yanxu kana nufin hjy iya bata karasa rigana ba kenan tabbas dole kuwa zan tura yarana yanxu-yanxun nan, kuma Abokina ka kwantar da hankalinka hjy iya nima mahaifiya ta ce insha Allah cikin abunda befi awa biyu zuwa uku ba za'a gano bakin zaren, sannan zan turo wasu daga cikin yarana zasu xo nan gdn hjy iya su taho da yan aikin gidan saboda dole bincike ya biyo ta kansu, idan kuma suka xo ka basu kwalin wayar hjy iya za'a ayi tracking agano waye shi wannan wanda ya dauki wayar tata, amma ina fatan zaka kwantar da hankalinka insha Allah everthing will be successfully.


To shikenan nagode kwarai Allah saka da alheri Abokina, sai dai kwalin wayar hjy iya yana cen gidana tun lokacin dana sai mata Alh habibu ya bashi amsa, to  Allah ya bamu nasara Dpo ya fada, gaba daya suka amsa da Ameen, sallama sukayi kowa ya kashe wayar sa.


Alh habibu kallan su hansai yayi cikin damuwa yace, kowannen ku sai ya kintsa dan anjima kadan police officers zasu xo su tafi daku, saboda dole abincike ku kuma.


Gaban su ne yayi mummunar faduwa inna zainabu, tsugunnawa tayi tana bashi hakuri, ba shiri su suwaiba ma suka dur'kusa suna yiwa Alh habibu magiya musamman suwaiba domin Allah yayi ta da tsananin tsoron dan sanda, kai bama dan sanda ba duk wani ma'aikaci wanda zata ga ya rike bindiga to shikenan hankalinta idan yayi dubu ya tashi.

Ko kadan Alh habibu bai bi ta kansu ba, number Audi ya nemo ya fara kira, kararta suka jiyo a dakinsa jin haka yasa Alh habibu katse kiran.


Duk abinda yake faruwa Audi na labe a lungu yana kallan su, kalmar police ita ta daga mai hankali ji yay inama yayi tsuntsuwa ya fice batare da anganshi ba.


Suna nan cikin wannan yanayin, lauwali ya turo kofa ya shigo, ganin halin da su suwaiba suke ciki yasa shi jin zuciyarsa fes harda dan murmusawa a fakaice, cikin zuciyarsa yake fadin,   " ashe Allah ya kawo ni a daidai aykuwa sai na kara tunxira Alh habibu, hadin kan da kuke nuna mun yau sai yayi muku rana.


     Fuskar sa ba yabo ba fallasa ya karasa gurin Alh habibu yana fadin, " Barka da safiya Alh dafatan anxo lafiya, lafiya kalau kawai Alh habibu ya bashi amsa.

 

          Lauwali tsugunnawa yayi agefe ya sunkuyar da kai kasa, fuska cikin tsananin damuwa yake fadin,  " Allah ya kara girma da nisan kwana Alh Allah ya ja da ran hjy iya cikin kwanciyar hankali da koshin lafiya, Alh ina fatan ba wani laifi mukayi ba? Dan Allah Alh duk hukuncin da zakayi mun nidai ka taimaka karka rabani da gidan nan domin hjy iya ta zame mun uwa da uba na, Allah sarki hjy iya uwa ma bada mama baya goya marayu, Aykuwa lauwali ya karasa maganar yana zubda kwallar munafurci.


Su hansai sakin baki da hanci sukayi cikin mamaki suna kallon lauwali, aykuwa suna hada ido a fakaice yayi musu gwalo, ya kara sunkuyar da kai yana kamo kafar Alh habibu cikin magiya da zubda hawaye.

_Nagode muku kwarai da gaske bisa ga kulawar ku agareni tabbas yanxu nasan kun damu dani ina godiya bisa ga Addu'ar ku *ciwon kai* ya warka Allah ya kare mu da lafiya inayinku yanda kukayi na Allah ya bar zumunci da kaunar juna_


_Dungurungun na sadaukar da wannan page gareki *HASSANA* nagode da kulawarki sosai Allah ya bar zumunci_.

*Vote*

*Comments*

*Share*

    _MOM ASLAM Ce_πŸ˜‰πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

       _6/7/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

    _AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


                29&30

    Wani irin abu ne ya kara tasowa Alh habibu jin irin maganganun da lauwali yake fada akan hjy iya, zuciyarsa ce ta karye ya tuno bayan sallar idi daya zo gaisheta da lokacin da suke cin Abinci, nan da nan yaji kwallah na shirin zubo masa, cikin dakiya da jarumta ya kalli lauwali yana fadin,  " Karka damu lauwali insha Allah hjy iya aduk inda take muna sa ran tana cikin koshin lafiya, maganar laifi kuma ni ba wani laifi da kamun hasalima lokacin da hjy iya zata tafi ay muna tare da kai a gidan gona ta, nayiwa Dpo magana da yardar ubangiji za'a bincika inda hjy iya take.+


Zaro idanu gaba sukayi su hansai da lauwali kamar hadin baki suke tambayar sa, Alh bamu gane za'a binciko hjy iya ba 'bata tayi ne? Dan jim kadan yayi ya hadiyi yawu me d'aci sannan yace, " nayi waya rigana bata karasa ba kuma wayarta na hannun wani yaro, shi ne kiran da nayiwa Dpo dazu tafiyar da za'ayi da ku inna zainabu zaku amsa tambayoyi ne ba wani abu ba.


Wannan karan ba su inna zainabu ba hatta lauwali sai da yan hanjinsa suka kad'a saboda tsananin tsoro da tashin hankali, shi duk a tunaninsa ya zaci fada Alh yake wa su suwaiba akan tafiyar hjy iya, ashe babban lamari ne, gumi ne ya shiga karyowa dukkanninsu aka rasa me bakin magana.


Audi dake cen jikin katanga hankalin sa ya bi duk ya tashi, cikinsa  ne yake hautsina masa ga gumi yana karyo masa.


Lauwali na nan gefe a tsugunne kamar wanda aka tsunkula yace,  Alh ina  Audi ko shi babu shi acikin laifin? Baya gidan, Alh habibu ya bashi amsa atakaice,  suwaiba ce tace, " nifa Alh ina ganin kamar Audi yana cikin gidan nan saboda ban dade da barin gurin cen ba naga ya shiga d'aki.


Idan yana gidan zanzo inyita horn be bude ba? Hjy habibu ya tambaya fuska ba walwala, ganin yanayin da Alh habibu yake ciki yasa duk suka yi shiru.


Turo kofar suka ga anyi a tsammanin Alh habibu ko yan sanda ne suka iso, khaleeda, huzaifa, Ameer da Sulaiman ya gani, kowannen su daka kalli fuskarsa kasan yana cikin damuwa, cikin halin jimami suke tambayar mahaifinsu,  " Daddy  d'azu mami take sanar mana abunda yake faruwa wai hjy iya ta tafi Rigana kuma wayarta na hannun wani yaro"

Eh haka ne, kuma na kira cen riganan ma bata karasa ba, 😳 zaro idanu suka yi lokaci daya suna tambayarsa, " ba tun jiya akace ta tafi ba? To me yake faruwa"

Kofa aka banko da karfi gaba daya idanunsu yayi bakin kofar, police ne sun kai su bakawai sai human police daya, Alh habibu nuna musu su hansai yayi, aykuwa su inna zainabu suka fashe da ihu duk wanda yake gurin ya ga irin kukan da sukeyi sai sun bashi tausayi.


Lauwali ihu yake yana fadin wallahi ba hannuna asace hjy iya, ku tambayi Alh kuji muna gidan gonar sa, dan Allah ku min rai ko shaida bantaba zuwa bayarwa ba offishin yan sanda, babu wanda yabi ta kan Lauwali, incharge dinsu ne ya kalli Alh habibu yace,  "Alh suke nan ko? Eh su kenan Alh habibu ya bashi amsa, sallama yayi wa Alh habibu har ya yi hanyar get ya juyo da niyyar tambayarsa, Aykuwa ya hango d'an kai daga jikin bango ana lekowa, kallan gurun yayi da kyau Audi na ganin sun hada ido ya koma ya ma'ke yana maida ajiyar zuciya.

Alh wancen me lekowar kasan da shi ne,  waye yake lekowa? Alh habibu ya tambaya, tun kafin ya rufe baki, incharge din yabi lungun da gudu, Audi najin antaho gurin da yake yayi sufa ya kama jikin wata bishiya ya kankame, police din na zuwa ya d'aga kai sama ya hango kafafun Audi na rawa a sama.


Ka sauko ta cikin laluma ko na sauko da kai, police din ya fada cikin tsuke fuska yana gyara zaman bindigarsa, Audi da farko biris yayi har yake kokarin kara hayewa saman bishiyar, yana hango bindiga ya silalo ya sauko yana sinne kai kasa.


Suna fitowa daga lungun cikin mamaki Alh habibu ya kalli Audi, dan takaici ma kasa magana yayi, Audi ganin haka ya fara ba wa Alh habibu hakuri, Ku tafi dashi me gadin gidan nan ne, Abinda Alh habibu ya iya fada kenan.


    Bayan fitar su Audi Alh habibu ya bawa 'yayansa umarnin sukai sanarwa kafofin yada labarai da television sannan ya kara da cewar su hada da hoton Hjy iya.


Mukulli yasa Aka siyo aka rufe gidan hjy iya, gaba daya walwala ta kau a gidan Alh habibu, cikin lokaci kankani aka shiga sanarwa akan 'batan hjy iy.


*INA LABARIN HJY IYA*?


Hjy iya na shigewa dakin matar me gari ta turo kofar ta rufe, ta janyo sakatar dakin ta rufe.


Suna shigowa suka nemi hjy iya suka rasa, dafta tanimu yayi iya yin sa hjy iya ta bude ta ki, su nalami sai shigo da kayan aiki suke garwar farko da aka shigo da ita aka ajiye a gefe, wata katuwar tukunya suka hango kici-kici matar me gari ta fara hura wuta ruwan suka zuba aka dora tukunya awuta sai balbala mata karare akeyi, idan baka ka sani ba ka shigo a lokacin zaka rantse girkin biki akeyi.


Matashin saurayin da suka zo da dasu hjy iya me suna yusuf, tunda suka shigo be ce musu uffan ba shi abun nasu ma ya daina bashi haushi, mamakin irin jahilcin da suke yi yake, duk wani me ilimi idan ya kalli dr tanimu yasan banda jahilci da hauka ba abinda yake shukawa agarin gangaren hayi.


Dan tsoho na gefe yana fama da kansa shima kallon su yake dan shi har yanxu baisan abinda ake shirin aikata musu ba, maahe ne ya kalli yusuf yace wa dr tanimu, " Dafta tanimu tunda ita waccen tsohuwar ta kulle kofar to cikin su biyun nan dawa zaka fara? Dafta tanimu kallansu yayi sannan yace, " Bari mu fara da wannan dattijon dan naga kamar yana jin jiki, to ay ma tunda feshi za'a fara yi musu ko su biyun ma a hada ayi musu kawai, kai idi kaida mutta'ka ku dauko tsohon nan , Allah ya baka yawan rai  ko ahada daku gaba daya ko kuma dai agama dasu din? Me gari ko uffan be ce ba ya dallawa dafta tanimu harara.


Yusuf na tsaye yana jiran karasowar su idi aykuwa suna sunkuyawa zasu dauki dan tsoho me buhu, yasa kafarsa ya hankada su saura kadan su ci da baka, tsuke fuska yayi ya fara magana,  " ku wadanne irin jahilai ne mahaukatan banza da wofi kodan kai tanimu kai ne babban da'ki'ki kuma mahaukaci, waya ce maka wannan kayan haukan daka hada sune maganin cutar corona virus, kai kuwa ko secondary school ma ka kammala kuwa? Wallahi wannan idan na fita daga garin nan sai nayi karar ka ga hukuma.................. Katse shi me gari yayi da.


" kai yaro karka kawo mana maganar banza da wofi waya ce ma dafta tanimu ba likita bane? to mu nan tunda tanimu ya dawo daga birni shine likitanmu kuma komai ya hada mana mutanen gari na suna warkewa, kai dafta tanimu ku cigaba da aikinku.


Wallahi kana fesa mana wannan garin sai na kira muku yan sanda bari ma ku gani, yusuf ya karasa maganar yana zira hannu a aljihu ya ciro wayar sa, cikin tanimu ba karamin ruwa ya dura ba Amma gudun kar ayi saurin gano shi ya hau borin kunya yana fadin.

            " kai ka kira majalisar dinkin duniya kasan dawa kake magana kuwa, kasan makarantar da nayi har na samu shaidar wannan takardar ta likitanci kuwa? To idan baka sani ba ka sani makarantar *School of nosin and midwaifa Aminu kano* ita nayi kuma harda certificate.


(😨😨😨 _Kai tanimu wallahi idan su *Dr. Magashi* suka ji ka ba ruwa na_)


Kallon rainin hankali yusuf yayi masa yace, kai karka raina mun hankali ni nan cikakken bakano ne kanin babana babban likita ne a AKTH, babu wani alaye da zakayi mana ko ku bude mana kofa nida tsofaffun nan ko kuma inkira muku ASP kabeer musa, ay Dafta tanimu baiyi wata-wata ba ya ba su nalami umarnin su bude gida, hjy iya na jin ankawo musu mafita ta bude kofa ta fito, dan tsoho dan dingisawa yayi ya mike tsaye.

Me gari mamaki ne ya kamashi, ya kalli dafta tanimu cikin jin haushi yace.

                  " kai sakaran banza yanxu wannan kurarin da yaron nan yayi maka shine har kayi saurin mi'ka wuya bakasan irin fankamar su ta 'yan birni ba"


Tanimu afakaice yake yiwa megari nuni da yayi shiru, sukuwa su hjy iya dama masu jira nan da nan ita da dan tsoho da yusuf suka fice daga gidan megari, tafiya suke yi kowannen su zuciyar sa fes kamar anbasu babbar kyautar.

Har sun kusa karasawa titi dan tsoho ya ca ke a gefen hanya, kallonsa hjy iya tayi shekeke tace kai kuma meye haka, jin maganar hjy ne yasa yusuf waigowa shima tsayawa yayi dan yaji me dan tsoho zai ce.

Dan buhu na na manta a gidan me gari gaskiya mu koma na dauko dan tsoho ya fada yana kara gyara tsayuwar sa, wani uban ashar yusuf ya lailayo sannan yace,  " wallahi kai dai wannan tsohon da kai kakana ne wallahi sai na saita ka da wannan iskancin da kake yiwa mutane, kana gani da kyar muka sha daga cikin gidan kace wai ka manta dan buhunka , to bari kaji duk maganganun da na gayawa tanimu inayi kirjina na dukan uku-uku dan ban taba tunanin zan fito basu nada mun na jaki ba, wallahi ko ranka ne acikin buhun nan sai dai ka koma ka dauko inkuma iya zata raka ka sai ku tafi tare amma ni kam Allah ya kubuto dani ba abinda zai maidani"


hjy iya ta kalli dan tsoho cikin takaici ta ce, " wai dan Allah kai wanne irin mutum ne mara kan gado da tunani, kana ganin irin ukubar da mutanen cen suka so siyi mana, wai ma meye acikin buhun naka?

   Gyada ce amaro sai yalo dana taho dashi zan kaiwa yan jikokina.


Dogon tsaki yusuf yaja sannan yace, " yanxu baba saboda yar gyadar da batafi rabin kwano ba zaka koma, kaje Allah ya baka sa'a idan suka babbake ka suka turbid'aka cikin rogo zakayi bayani, nidai kunga tafiyata yusuf ya karasa magana yana mikar hanya.


Hjy iya ma rufawa yusuf baya tayi suka fara tafiya, dan tsoho ko me ya tuna sai gashi ya ya dingiso ya biyo su da sauri.


A haka suka karasa titi bame cewa wani uffan, suka tsaya jiran mota amma titi wayam sai tsararin motocin gida da suke wucewa.

_Kawaye na ina matukar jin dadi da irin comments din da kuke sam'bad'omun, har gaban gobe inayinku irin sosai din nan_.


_Wannan shafin naku ne 'Yan *Hadaka* Allah yabar zaman tare_.

*Vote*

*Comments*

*Share*


         _MOM ASLAM Ce_πŸ˜‰πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

       _11/7/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

    _AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


                31&32

Kai mene ne sunan ku kuma meye matsayinku a gidan hjy iya, wani dan sanda me suna samuel ya bugawa lauwali da Audi tsawa da suke cikin cell sai muzurai suke suna zare idanu, duk an tube musu kayansu daga su sai singlet da gajeren wando, kallan juna suka shiga yi basu da alamar magana kowanne kirjinsa sai bugawa yake, aykuwa samuel ya kara buga musu tsawa, " Kai you are very stupid, am talking to you and u  are looking each other kuna hauka ne kunsan a ina kuke kuwa" lokaci daya cikin su ya kara hautsine wa a zabure kowannen su ya amsa lauwali ne ya fara magana, " ni suna lauwali ni ne driver gidan hjy iya kuma wallahi lokacin da hjy iya ta fita................." katse shi samuel yayi da, "shutoff your mouth waya tambaye ka " ay kafin samuel ya karasa magana tuni lauwali ya tsuke bakin sa.+


Audi ne ya fara magana,  " ni suna na Audi ni ne me gadin gidan hjy iya" baki Audi yaja ya tsuke ganin yanda akayiwa lauwali yasa yaja baki yayi gum yana fargabar ta kanwa za'a kuma jeho tambayar, samuel ne ya tattara hankalin sa gun audi yace,  " good, like you said you are getman dat mean u are the security of the house,ok? " Audi kallan samuel ya shiga yi kamar me fahimtar wani abu amma sam be gane me samuel yace ba, tsawa samuel ya buga masa, " am asking u and u just looking at me, ko so kake sai na hada maka da duka ne? "


Audi ganin samuel ya fusata da jin kalmar duka yasa yafara magana, " me na me gadi hjy iya go and me nace karta fita, Alh zaiyi fada and hjy iya starting fada and tace everybody gayawa Alh zatasa akore mu, Audi ba karamin bawa samuel dariya yayi ba jin yanda ya takarkare yana zabgo turanci, amma gudin raini yasa shi ya tsuke fuska ya cigaba da tambayarsa da hausa.


Meyesa baku dakatar da hjy ba lokacin da zata fita tunda kunsan bata fita ita kadai? Audi labari ya bawa samuel duk abunda ya faru da hjy iya kafin fitarta, juyawa yayi gurin Lauwali da yake ta raba idanu tambaya ya watso masa,  " kai ne driver ko? Kana ina lokacin da hjy ta fita tunda kaine me kaita duk gurin da zata je ? Lauwali dama jira yake azo gurinsa dan lokacin da samuel yake jero masa tambayoyin ji yake inama ya fara bada amsa tunkafin ya gama, amma tsoro ya hanasa magana har sai da samuel ya bashi dama aykuwa cikin sauri lauwali ya fara  bawa samuel labarin duk abunda ya faru na fitarsa gidan gona da Alh habibu da dawowarsa da yanda yazo ya samu Audi.


Samuel ne ya kalle su sannan yace, " ok duk naji bayanan ku kuma idan wasu tambayoyin suka kara tasowa za'a bukaci ku bada amsa, ya karasa magana ya na kokarin fita, bayan fitarsa ya janyo kafa ya maida ya rufe.


Da sauri Lauwali ya karaso bakin kofar yana fadin, " yallabai dan Allah nidai ka taimaka ka fitar dani tunda na maka bayani kuma ni banida laifi aciki, samuel ko waiwayensa baiyi ba ya kara gaba, haka lauwali da Audi suka dinga magiya ta jikin kofar cell din, wani dan sanda ne ya taso ya zo baki kofar ya buga musu tsawa,  " kai kuyi mana shiru kar ranku ya b'aci sakarkarun banza, tsit suka yi ba wanda ya kara magana, juyawa yayi ya koma gurinsa ya zauna.


        Zuwa wani lokaci yunwa ce ta fara sasukar Audi da lauwali, sake lekowa sukayi suna magana,  " officer dan Allah ku taimaka mana da Abinci wallahi yunwa muke ji ga kishirwa na damun mu, shi kuma Lauwali fadi yake yallab'ai ataimaka afitar dani tunda banida laifi, wani police ne yaxo wucewa yaji sunata ihu cikin fada ya fara musu magana,  " kai wai ku kadai aka kawo nan da zaku cika mana guri da ihu wallah duk wanda na kuma jin maganar Allah idan nazo sai ya goya kansa ko yayiwa kansa makawuya, tsit kake ji kamar anyi ruwa andauke su Audi baki ya mutu ganin yanayin dan sandan ba karamin tsorasu yayi ba kato ne me kiba ga tumbi hannunsa dauke da wani katon kulki, kallansu yayi yace " da kunsan kuna san iskar wajen kuka aykata laifi sai kuyita zama har wanda yasa aka kawo ku nan in yazo ya bude ku, ya karasa maganar yana yin gaba abinsa.


Bayan wasu yan mintina kadan aka shigowa su Audi da wani dan shaye-shaye wai yaje satar TV shagon wani me gyaran tv aka kama shi, sai layi yake yana tangadi ga warin abar sai tashi take, su lauwali ido suka zuba mai suna ja da baya, ganin ana wurgoshi ciki yayi taga-taga zai fado kansu.


_A BANGAREN SU HANSAI_


Ana shigowa da su cikin station din aka ware su acikin wani cell wanda shi ne na mata, su kuma su Audi akayi gaba da su cikin dayan cell din na maza, inna Zainabu cikin rudewa ta ke tambayar su hansai kasa-kasa yanda na waje bazai ji ba,  " suwaiba inane nan aka kawo mu nifa tsoro ya fara kamani karfa Alh yasa a salwantar damu " ta karasa maganar kwallah na ziraro mata.


Suwaiba tagumin da tayi da hannuwa biyu ta cire cikin sanyin jiki tace, " inna zainabu wallahi nima bansan ina ne nan ba dan bantaba zuwa nan ba, wallahi duk shedanci na a baki ne bantaba zuwa ko makamancin gurin nan ba"  hansai kad'e sauran da suke ta cizonta tayi tana yan soshe-soshe sannan tace,  "  wallahi ni inna zainabu tunda muka shigo nan zuciya ta karye ni na fidda rai da cigaba da rayuwa ma" aykuwa sai hansai ta rushe da kuka me tsuma zuciya ta sanya kanta cikin cinyoyinta tana sharbar kuka san ranta.


( _Hjy iya kindau Alhakin mutane da yawa_🀣)


Hankalin su suwaiba ne ya kara tashi cikin karfin hali take tambayar hansai, " hansai me yasa zaki ce haka bayan Alh ce mana yayi tambayoyi kawai za'ay mana?" Duk suka zubawa hansai idanu suna jiran suji me zata ce, cikin muryar tausayi da karaya ta fara basu amsa,  "  suwaiba kenan, kin tuna wani kallo da muka tabayi a falon hjy iya, acikin kaset din ankama *Ali Nuhu* ankawo shi irin gurin nan kuma daga nan ba koti aka kaishi ba, suka ce kashe shi za'ayi kinga muma aytamu taxo karshe kashe mu zasuyi, Allah sarki bello na shikenan wata zai aura yanxu duk kudin kayan dakin da nake tarawa sun tashi a banza, inna ta sai dai taji shiru ba labari" wqnnan karan ba hansai ba gaba daya haka suka fashe da marayan kuka.


Kukan su haka ya fara cika wa police din gurin kunne, da sauri wata human police me suna Ramatu ta taso tana musu magana cikin gurbatacciyar hausarta,  " Haba mama ya degirmanci taza biyewa yara cuna kuka haka kaman wanda mamanci ta mutu, be patient mana inde kunbada hadin ke anmuku tambaya cikenan, kuyi ciru kuna cika mana kunne mana.


Dan tsagaita kukan sukayi hansai ce ta fyace majina gefe sannan tace,  " yallab'iya dan Allah kuyi hakuri karku kashe mu dan girman Allah"

     heeeee look at this mumu girl, waye yace zai kace ku ? See i don't have ur time ooo, ramatu ta fada lokacin da tabar bakin cell din.


Aykuwa sabon kuka suka dasa sai ga wannan katon police din yazo bakin kofar, ko uffan be ce musu ba wata uwar harara ya watsa musu kowa yaja baki ya tsuke suna ajiyar zuciya.


         Suna nan jugum-jugum kowa da wasik'ar da yake karantawa acikin zuciyar sa, ba me bakin magana sai dai kaji jan majina da shashshek'a sama-sama suna sharce hawaye.


Mukulli sukaji ansa ana bude kofar da sauri suka mike kowannen su yayi carko-carko, wata police ce ta shigo me suna Abigal, yanayinta ba yabo ba fallasa tambayar su ta shiga yi daya bayan daya tana daukan statemen, kowa iya abunda ya sani shi ya bata amsa bayan ta kammala ta fito ta ja kofa ta rufe, aykuwa nan wani takaici da bakin cikin ya turnike su ga sauraye sai cizon su suke.


*_MU KOMA KAUYE_*


     Su hjy iya na tsaye a bakin titi Akalla sun shafe sama da awa daya babu motar haya babu alamunta sai yan tsiraun motocin gida, suma idan daya ta wuce sai ashafe minti goma wata bata kara wucewa ba, tun suna tsaye har suka fara gajiya, dan tsoho ne ya fara zaman agefen wata yar itaciya da take gefen hanya, zuwa wani lokaci hjy iya itama ta nemi guri ta zauna dan kafafunta sun fara tsami, yusuf ne ya karaso gurin da su hjy iya suke zaune cikin gajiyawa da sarewa yace,  " Anya kuwa iya hanyar nan kuna ganin akwai yuwuwar samun mota, kuna gani tun d'azu muna tsaye shiru nifa inajin tsoron kar muxo mu rasa mota, kunsan fa lockdown din nan motaci sai ranar lahadi, laraba da juma'a suke fita yau kuma kunga litinin.


Kai haba yaro karka damu zamu samu mota ba wani lokrawun karka manta nan fa kauye ne, wannan iyayin sai birni dan tsoho ya fada yana kishingid'ar da kai gefen bishiya.

To inbanda Abinka ba daga birni zasu taho ba suxo kauyen, kai dai muyi Addua'a Allah sa mu samu mota, hjy iya ta fada tana jingina da bishiya.


Cabdijan yanxu kuwa muka rasa mota ya zamuyi? sai dai mu koma gidan megari, kai nidai wallahi bata ba kadararriyar tafiya kamar wannan ba, yusuf ya fada kamar zai fashe da kuka dan takaici, shima gefe ya nema ya zauna iska na kad'a su suna hira sama-sama. Wata motar gida ba'ka suka hango daga nesa ta danyi parking agefen hanya, mutumin cikinta ne ya fito ya bude gaban motar yadan Zubawa injin motar ruwa, hjy iya k'uri tayiwa motar kamar tasan me ita, cen kamar wacce aka tsikara ta gyara zama cikin murna take fadin, waccen da gani motar habibu ce wallahi itace ga gefen ta nan inda pantinta ya dan kurje, ayke kinji matsalar ki iya magana kadan kice habibu wai shi wannan habibun da kike ta magana Allah sa ma ya damu dake haka, kuma ba'a abu iri daya kawai daga ganin mota sai kice tashi ko shi kadai akayiwa irinta, idan ma gizo idanki yake miki ki mirjeshi wata kila ma yana cen yana sabgarsa ya manta dake........


Cikin bacin rai hjy iya ta katse shi, " kai yaro dakata kaji habibu daban yake acikin yara d'an Aljanna ne samun irinsa sai antona, kai dai ka bari motar ta karasoa, ba kai ba har iyayenka sai sunsan ka hadu da habibu na.


Motar yan sanda suka hango ta sharo da gudu har ta dan gota bakar motar da suka hango, da sauri saurayin nan yace, " iya ku tashi mu buya a bayan tukubar tsiren cen dan wallah wadannan yan sandan irin masu kamen nan ne, suna kama wadanda suka fito tunda kunga yau ba ranar fita bace, tunkafin ya kai karshe dan tsoho tuni ya mik'e yana dan dingisa kafa yayi gaba, kai yaro ba yan sanda ba ko sojoji ne ba inda zani ina gano motar habibu kace mun in wani buya ni nan ba inda zani, hjy iya ta fada lokacin data mike tsaye ta sabi yar jakarta a hannu.


Ganin motar na kara kusanto su yasa yusuf fizgar hannun hjy iya da karfi sukayi bayan tukubar tsiren, ya durgusar dasu shigar su ba wuya motar police din ta wuce sun mike tsaye kenan bakar motar itama ta rufawa ta police din baya. Hjy iya jikinta har rawa yake tabbas jikin na bata motar habibu ce, bayan fitowarsu titi hjy iya ta kurawa motar ido ceeeen nesa dasu hjy iya ta hango motar nan ta tsaya data police din.

Hjy iya har tuntube take tana kara lekawa, hango yanayin tsayuwarsa tayi yana magana da wasu makiyaya, basu jima ba taga ya sallami mutanen da yan kudi, juyowar da zai ya shiga mota ta hango fuskar habibu radau, iya karfinta ta bude murya tana fadin, haabiiiibbuuuuu  ta fadi haka yafi sau uku shi kuwa tuni ya shiga mota police din suma suka d'ane tasu suka shilla titi.


Yusuf sakin baki yayi yana kallon hjy iya bai yi aune ba yaji ta kurma ihu da kuka lokaci daya, tana surutai, ta fashe da kuka me tsuma zuciya duk wanda yake gurin sai ya tausayawa hjy iya,  " kaico ni hadizatu me yake faruwa dani ne yau ga habibu ina hangowa amma baisan inayiwa ba, dan Allah yaro ka taimaka ka kiramun habibu inbaka da kudi ga dubu daya ka sayi kati kasa na gaji da wannan bak'ar wuyar da nake sha tun jiya, gaskiya iya kina da damuwa yanxu ya'ay inkira miki habibu bayan ni bansanshi ba, banta ba samun number sa ba kiyi tunani gaskiya, Aykuwa hjy iya kamar dama jira yake ta kara rushewa da kuka.


Dan tsoho ne yayi magana, " inada shawara idan zaku dauka tunda kin tabbar shine habibu naki, ya karasa magana kasa-kasa kamar me rad'a a kunne.

_Allah ya barmu cikin Aminci da kaunar juna, wannan shafi naku ne yan uwana da Abokan arziki._

_Masoya A cigaba da gashi_❤️❤️❤️


*Vote*

*Comments*

*Share*


_Mom Aslam ce_πŸ˜‰πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

       _13/7/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

    _AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


                33&34


Tun bai rufe baki ba hjy iya ta katse shi cikin fada, " ka bude baki sosai kayi magana sai ka dinga mun rad'a kamar wasu munafukai mece ce shawarar taka? " Dan tsohi ko ajikinsa yace me zai hana muje gurin wancen makiyayan muji me habibun yace musu kinga kila mu samu mafita.

Kwairai kam gasky baba kazo da shawara mu gangara gurinsu naga suma nan suke tahowa sai mu tambaya su, yusuf ya fada yana gyara takalminsa.+


Hjy iya saboda takaici ko kadan idanunta ba hawaye sun bushe ashe kuka ma rahama ne, tafiya suke suma makiyayan nan suna kara kusanto su har suka cimmusu, da sallama suka isa garesu k'uri yayiwa hjy iya yana kallan ta, hjy iya ce ta fara magana.


" Bawan Allah sannu ya aiki, dan Allah wannan mutumin na d'azu da yaxo a mota me yace maka? " Iya cigiya ya kawo mun, zaro hoton hannunsa yayi yana kallo ya kara k'urawa hjy iya kallo sannan yace, " ni sai kike mun kama da wacce ya kawo mun hotonta ikon Allah ko kuma kama ce dan gaskiya ta jikin hoton nan ta fiki yarinta " wallahi ni ce bawan Allah ka taimakeni ka kaini gurin habibu wallahi d'ana ne matsalar mota muka samu jiya.


Dan jim kadan yayi kamar me nazari sannan yace eh to dama cigiya ce suka bani da hoto, yana cikin magana suka hada ido da haruna  ya kifta masa idanu ganin musa bai gane inda haruna ya dosa da maganar ba yasa shi saurin karbe maganar da, "  wannan maganar bai kamaci mu zauna a nan anayi ba mu karasa gida ko ruwa su sha mana"


A'a basai mun karasa gida ba nidai dan Allah ku hadani da habibu yazo ya dauke ni, hjy iya ta fada tana kara rikice musu, iya gsky dan uwana ya fada kuxo mu wuce gida nan tsallaken ne kunga awaki na sunyi gaba kar suyi wani guri musa ya fada yana yin gaba abinsa, badan sunso ba haka su hjy iya suka bi musa da haruna zugwi-zugwi abaya babu me cewa uffan.


_*BAYAN MAGRIBA*_


   Alh habibu na zaune a falonsa bayan ya fito daga wanka, yana zaune yana nazarin rayuwa hawaye yaji suna ziraro masa, tunanin hjy iya yake da halin da take ciki  yana nan yana tunani wata zuciyar tace masa.

Hjy iya ko dai saceta akayi yan garkuwa da mutane, kai da garkuwa akayi da ita ay da tuni ankirani kuma da kiran da akewa hjy iya tuni da sun bukaci kudi.

Dayar zuciyar kuma tace to ko hatsari sukayi acikin masu kawo agaji wani ya dauki wayar hjy iya, kai hasbunallahu wani'imalwakeel, Abunda Alh habibu ya furta kenan yana kara share kwallar data zubo masa. Tuno irin tafiyar da suka sha yau yake sumbi hanyar bichi da lamba har sau biyu amma ba alamar hatsarin mota duk garin da suka shiga sai sunyi tambaya sun kuma bada cigiya amma babu wanda yace ko me yanayin hjy iya ya gani, haka suka tarkato shi da police din da suka je suka dawo.


_Mahaifa ba wasa ba tabbas duk wanda yayin rashin mahaifa to kuwa yayi babban rashi me girma, duk girman mutum idan yana da mahaifa uwa ko uba to kuwa dangata ne kuma yaro ne, Allah ya ja da ran iyayen mu ya basu jinkiri me amfani dan matsayi da isar Annabi S.A.W_


Yana nan zaune cikin tunani wayar sa ce ta fara ringing ,  sunan *DPO* ne ya fito hannun Alh habibu har rawa yake yi kafin ya dauka, cikin sauri ya dauka da sallama daga cen bangaren aka fara magana.

      " Alh mun samu nasarar kamo yaron da wayar hjy iya take hannunsa shida wani abokinsa, mun tamabaye su ina hjy iya kowannen su yace mana basu san inda take ba........  Dpo bai gama magana ba Alh habibu ya katse shi,  " Abokina bari na karaso maganar nan bazata yuwu ta waya ba, inasan ganin yaran amma kar ataba jikinsu dan Allah kar adoki mutum daya daga cikin su bari nazo, bai jira abunda DPO zai ce ba ya katse kiran, agurguje ya tashi key kawai ya dauka har hardewa yake yi kafin ya fita get, iyalansa duk suna falo ganin yananyin da ya fita yasa mami kiran su khalid ta shaida musu, su dinma basu dade suna waya ba suka ce mata ta katse zasu kira mahaifin nasu suji halin da ake ciki.


Alh habibu yana fitowa mota ya dauka ya fita, gudu yake kamar zai tashi sama har ji yake kamar baya sauri yana ganin sharada ta kara nisa, ikon Allah shi yakai Alh habibu police station din sharada ko parking bai karasa ba ya fito daga motar da sauri ya shiga ciki, ko kallan gabansa baya yi.


Kai tsaye yana shiga da copral musa ya hadu,yana ganinsa suka gaisa cikin zumud'i Alh habibu yake tambayar copral musa,  " office inasan ganin DPO inafatan yana ciki ko? " tun musa bai bashi amsa ba sukaji maganar DPO yana tunkaro gurinsu da alama waya yake yi, karasowar sa gurunsu yayi dai-dai da gama wayarsa.


Hannu Alh habibu y mik'a masa suka gaisa, kai tsaye cell din da aka rufe su lauwali nan suka nufa.


Fitila aka kunna sannan aka sa key aka bude su, aykuwa Audi naarba da Alh habibu ya wani zabura zai fito, tsawa DPO ya buga masa ba shiri gaba daya yan cell din kowanne ya nutsu.


Sai soshe-soshe sukeyi suna kade sauro ga zafi da yake damunsu, saukinta ma da magriba ankawowa su lauwali Abinci, saboda Alh habibu yace kar ayi musu horon yunwa hakan ne yasa ya bada kudi yace asai musu abinci da ruwa su sha.


Lauwali da audi na gefe suna muzurai, sai dan shaye-shayen da aka kawo musu, gefe daya kuma wasu matasa ne suma kowannen yayi zuru-zuru daya daga ciki yafi kalan yan shaye-shaye, kafarsu na daure da Ankwa.


Umarni DPO ya musu da su fito ay kuwa jikinsu har rawa yake suka taso, Lauwali ganin anfitar da wadanda suka xo abayansu yasashi fashewa da wani marayan kuka.


Audi ne cikin bakin ciki da takaici yace, " Dan Allah Alh idan ma baza'a fitar damu ba ko maganin sauro ne a bamu wallahi gaba daya jikina ya nune da cizon sauro " Alh habibu ko takansu baibi ba suka nufi wani guri da aka ajiye kujeru masu dan dama agurin, suka zauna sukuka matasan suka zauna a kasa kowa da abinda yake sakawa azuciyarsa.


     Kai ya sunanka? Alh habibu ya kalli dan jageren ciki me yanayin yan shaye-shayen yana tambayarsa, idanu a lumshe ya d'ago kai yana magana, da alama bata gama sakinsa ba,  " sunana sarari.


Kallan sa Alh habibu ya karayi sannan yace, " Acikin ku waye wayar hjy iya take hannunsa? " ni ne, sarari ya bashi amsa, ina me wayar? Alh habibu ya tambayeshi.


     Eyee, Alh nifa waya kawai nasan na siya amma bansan labarin wata me waya ba wlh tunda nazo suke tambayata nace musu ni bansan wacece me wayar ba, sai dai ko a tambayi sarkin jagwal tunda shi ya kawo mun wayar na siya, ya kara maganar yana kallan wanda ya ambata da suna sarkin jagwal.


_IZNA gareku masu siyan wayar hannu ya kamata kusan agurin wanda zaku dinga siya, ku tabbatar da cewar ba wayar sata ko fashi bace, domin wasu daga cikin masu saida wayar hannu wayar sata ake kawo musu su saya su kuma su saidawa wani idan matsala ta biyo baya kunga kai da kake ciki kaima ka kwana aciki._

_Yanxu misali idan wayar fashi ce akayo ko aka kashe me wayar aka sayar kai kuma ka sayo to fa anayin tracking ka kwana aciki domin idan aka kama ka sai dai ka fito da wanda ya sayar maka shima anemo wanda ya saya agurinsa, Allah ya tsare mu ya kare daga mummunar Kaddara._


DPO kallan sarkin jagwal yayi yace, " kai ina kakai me wayar nan tunda yace agurinka ya saya" inda-inda ya shiga yi yana kame-kame, wani wawan mari DPO ya sakar masa yana fadin, " zakayi bayani ko bazakayi ba" kuka ya fashe dashi yana rokon DPO da yayi hakuri, Alh habibu magana ya kara masa, " ina ka ajiye me wayar kuma ya akayi wayarta taxo hannunka har ka saidawa wani?

Goge hawayen da ya zubo masa yayi sannan ya fara magana, " suna nan sarkin jagwal amma na ainihi sunan jamilu agarin badime nake, ranar lahadi muka hau mota da wata tsohowa na zauna akusa da ita tsautsayi yasa na dauki wayarta da take cikin jakarta, kuma wallahi yallab'ai ba halina bane tsautsayi ne ya kara maganar yana fashewa da kuka.


Cikin tsawa DPO yace wato bazakayi bayanin inda me wayar take ba kenan, kai Sergent bulus kuje dashi yayi muku bayani, tunkafin DPO ya kai karshe akaxo aka figi sarkin jagwal yana ihu yana magiya.


_Allah ka shirya mana zuriya da kullihin musulmai, Allah ka karemu da daukan abun da banamu ba, ubangiji masu yi Allah ya ganar dasu ya shiryar dasu su daina._πŸ‘πŸΌ


Wani police shima yaxo ya ja sarari aka maida su cikin cell, b'acin rai da bakin ciki ya cunkushe Alh habibu fargabarsa daya kar hjy iya ko tana cikin mummunan hali, idanunsa ne suka kada sukayi jajir, ganin yanayin da yake ciki yasa DPO ya fara kwantar masa da hankali, sannan yace yabasu zuwa nan da awa guda watakila inyaji wahala zaiyi bayani.


Alh habibu yaji dadin wannan bayanin yana nan zaune cikin zuciyarsa yana saka da warwara yaji sallamar su Ameer su wajen hudu, ( _Manyan 'yayansa_) da sauri suka karaso gurunsa suna tambayar ko akwai wani labari, abunda ya faru ya sanar dasu jikinsu duk ya mutu musamman da suka ga yanayin da mahaifinsu yake ciki.


Boye tasu damuwar sukayi suka dinga bashi baki suna gaya mai kalmai masu tausasa zuciya.


_Bangaren Hjy Iya_


A gajiye suka karasa gidan musa kasancewar da yar tafiya, ba bangaren gidan me gari bane daga dayan tsallaken titin ne, suna shiga gidan suka samu larai na sirfen gero da saurinta ta karaso ganin megidan ta da tayi tafe da bak'i tana fadin.

            " sannun ku da zuwa malam baki mukayi ne maraba lale ku shigo"

Larai baki ne abasu fura su sha bari na kewaya idan sun huta sai inshigo inmiki bayani, larai da karramawa ta karbesu awata rumfa ta shinfida musu babbar tabarma, ruwan cikin randar kasa me sanyi ta kawo musu da muhutai kafin kace me har ta dama fura takawo musu, ita dai hjy iya duk hankalinta baya jinkinta gama daya ji take kamar akan k'aya take duk da taji dadin irin tarbar da akayi musu, idan ka kalli fuskar ta inbanda yake ba abinda take yi.


  Bayan wani lokaci haruna ne ya shigo gurunsu, zama yayi acen gefe suka gaisa idanunsa kyam suna kan jakar hjy iya, bayan sun dan taba hira ya tashi yana fadin, " iya bari ashigar muku da kayan ciki mana kafin shi yaya ya dawo kunga kwa kara samun dama sosai, karaf hjy iya ta katse shi, " haba yaro wane sarari zamu kara samu muda ba zama muka xo yi ba jira muke dan uwanka ya dawo inji ko da lambar habibu agurinsa" kamar me jin haushi aykuwa cikin tsiwa yace ay shikenan sai kuyita jiran nasa har ya dawo" daga karshe har yana sakin guntun tsaki yayi gama yana yan gunguninsa.


Idanun suka bishi dashi suna mamakin abunda yayi musu, dan tsoho yasha fura yayi nak ga iska na fifitashi nan da nan bacci yayi awon gaba dashi.


Suna nan zaune hjy iya da yusuf sukaji sallamar musa, zama yayi daga gefe bayan sun kara gaisawa hjy iya ta fara magana, " bawan Allah mungode kwarai da yanda aka karrama mu Allah saka da alheri amma dan Allah ka taimaka idan da wani bayani da habibu yayi maka kayimun ko naji dadi" ehto, ya bani lambar wayar sa da kuma hotonki sai ihsani da yayi mun lambar waya yace idan anji labari ko kishin-kishin akan maganarki koda flashing ne yace inyi masa nima kuma ya karbi lambata"


Hjy iya dan murna kamar ta zuba ruwa a kasa tasha bakinta har kunne, har ta kasa boye farin cikinta, cikin zumud'i tace, " dan Allah yaro kiramin shi amma Allah saka maka da gidan Aljanna.


To takardar da ya bamu da hoton naki yana hannun haruna  dayake dazu ban fita da wayata ba, amma bari na tura yaro ya kira munshi, ke larai ina tsahare? ya kwalawa matarsa kira, malam tsahare taje debo mun ruwa amma nasan ta kusa dawowa.


Suna cikin maganar tsahare tayi sallama da ruwa aka.


Aykenta musa yayi yace taje bakin rumfar kasuwa ta kira haruna, dan nanne gurun zuwansa, da sauri tsahare taje ta kira haruna ba jimawa suka shigo tare.


Tambayarsa musa yayi takardar gurunsa da hoton hjy iya, dan jim kadan yayi sannan ya fara magana, " yaya wallahi tana cikin shago a aljihun wandona na manta da nayi wanka ban dauko ta ba gashi isiya ya rufe ya tafi hayin malam Audu mukullin na gurunsa.


( _cikin zuciyarsa kuwa fadi yake tabdi yaushe zanga samu inga rashi bayan wannan dankwaleliyar jakar da gani bazata rasa motsi ba wallahi sai kun kwana yanda zan samu inbi dare inyi gaba da ita_)


Dogon tsaki musa yi ya shiga yiwa dan uwan nasa fada yana bawa su hjy iya hakuri, hjy iya bakin ciki kara cikata yayi har ta kasa magana makogaronta har d'aci yake dan takaici, ganin ranta ya baci yasa musa ya fara mata magana, " iya karki damu zuwa nan da bayan magariba insha Allahu zai dawo baya wuce magariba, ni da kaina ma zanje inkarbo lambar inkira muku shi, to kawai hjy iya tace masa taja gefe ta kishingid'a.


_A POLICE STATION_


Ba karamar azaba aka dinga ganawa sarkin jagwal ba gaba daya ya fita hayyacinsa anyi masa walmukalifatu 🀣 da kyar yake takawa lokacin da aka kara fito dashi, jikinsa duk yayi tsami tambayarsa aka kari amsar dai daya ce irin wacce ya bayar da farko.


Su lauwali kowannen su yayi tsuru a lungu ganin irin azabar da akewa sarkin jagwal.


DPO ne ya kalli Alh habibu yace, Abokina karka damu ka bamu zuwa nan da gobe inajin bai ji jiki bane zai fadi inda hjy iya take cool your mind my friend, to shikenan Abokina nagode kwarai Inasan afito da su lauwali da inna zainbu tunda ansamu wanda yake da masaniyar inda hjy iya take, Alh habibu ya fada fuskarsa cikin damuwa.


Fito dasu hansai akayi su Audi murna ji suke kamar  ranar sallah sai godiya suke zabgawa Alh habibu , motar sa ya umarcesu da su shiga yayiwa DPO sallama ya figi mota suka wuce.


_Maman maleek ya karfin jikin Allah ya kara afuwa Aameen._


_Ina matukar godiya masoya Allah bar kauna._


*Vote*

*Comments*

*Share*


   _MOM ASLAM Ce_πŸ˜‰πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

       _16/7/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

    _AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


                35&36

Tunda magriba ta doso hjy iya ta kasa nutsuwa idanunta suna kan kofa, duk motsin wanda taji zai shigo sai ta waiwaya ta kalli gurin, dan tsoho dake gefen bishiya ya kalleta bakinsa da murmushi yace, " su hadizatu baki har kunne ana murna za'aje aga habibu" kallansa tayi bata bashi amsa ba ta cigaba da yan kalla-kallenta.+


Kamar wanda aka kara tsunkula ya kara kallanta yace, " hadizatu nifa Abinda yasa kikaga naki tafiya na biyo ku wata shawara na yanke" karaf yusuf ya tsomo musu baki, "wace shawara ce baba?"  ehto, nikam maganar gaskiya kafata kafar hadizatu dan akwai wani abu da yake tamun yawo araina kuma na tabbata zai zame mana alheri nida ita".


Dariya yusuf ya shiga yi yana kyakyatawa harda rike ciki, cikin zolaya ya kara zolayo dan tsoho da hjy iya, " nifa baba da farkon hawa mota ta na dauka matarka ce dan kunyi bala'in birgeni har ina fatan nima idan nayi aure nida mata ta mu kasance kamarku har tsufanmu"  zuciyar dan tsoho tas har wani murmushi ya kara saki sannan yace, " yaro kenan, ashe kaima ka hango abunda yake cikin raina, gashi tunda naga habibu naji ya kwanta mun azuciyata ji nake kamar ni na haifeshi, nasan idan nayi masa bayani shi zai fahimceni"


Hjy iya da kamar bazatayi magana ba amma ganin dan tsoho sai zance yake kamar ya kone aka yasata yi masa magana.

          " dan Allah mai yasa kai idan kana magana kamar karamin yaro kaifa kace gurin jikokinka zakaje, kawai daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki, kamar muna garin gab'a-gab'a sai kawai ka debi jiki zugwi-zugwi ka bini mu tafi, to ba habibu ba kowa zaka gayawa duk abunda yake cikin zuciyar taka sai dai kayi ta fada" hjy iya na gama maganar ta tashi ta dau buta kasancewar anata kiraye-kirayen sallah, da ido dukkansu suka bita dan tsoho wannan karan yaji haushi, shi ba haka yaso ba amma ya lura hjy iya akwaita da taurin kai.


( _yoooo kaine sai yanxu kasan taurin kan hjy iya, tunda habibu ya hanata tafiya ta kafe gashi nan ta d'aga hankalin bawan Allah._🀣)


Yusuf dariya har son subuce masa tayi ya maze yace wa dan tsoho, " yanxu baba Tsakani da Allah yaushe ka karewa habibu kallo da har kaji ya shiga zuciyarka, ko ni da na fika kwarin ido bana shaida kamanninsa ba, ko dai dankwaleliyar motarsa ce ka karewa kallo har kaji ya shiga zuciyarka?" mtsswwww, dan guntun tsaki dan tsoho yayi sannan yace, " kai kam wannan yaro anyi jarababbe da bin k'ok'k'ofi kai ko tusa mutum yayi sai ya kafeshi da tambayoyi, to idan ma motar tasa na gani meye aciki, nan da dan lokaci nima zaka ji labarin anfara tuka ni acikin irinta bayan Aurenmu da hadizatu na"4

😨😨 _kai kam dan tsoho wallahi anyi kwadayayye, ance ba'ayi amma kana kara tura kanka._


Wannan karan tusuf dariya yake harda rike ciki, ganin irin san abun duniyar dan tsoho karara afili, larai matar musa tana gefe tana jinsu itama har suka so bata dariya.


_BAYAN MAGRIBA_


Musa sallama yayi ya shigo bayan sun gaisa hjy iya cikin k'aguwata jehomai tambaya, " musa nace har yanxu dan uwan naka bai dawo bane kar dare yayi" wallahi iya yanxu haka daga shagon nake na samu yaron da suke kwana abakin titi ina tambayarsa haruna yacemun, yace masa unguwa zashi amma bai gaya masa takamaimai inda zashi ba, shi ne na dawo inxo in zauna a gidan dan nasan ,bazaiyi nisa ba tunda yasan ina jiran sakon da ke gurunsa, nasan dai idan ya dawo tanan zai biyo"  musa yake wa hjy iya bayani, ji tayi kamar ta dora hannu aka ta kurma ihu dan bakin ciki.


Wannan karan ba ita kadai ba gaba daya abokan tafiyar tata ransu ya b'aci, domin kowannensu ya kagu ya ganshi a gida, har musa ya kare maganarsa uffan ba wanda yace masa, yajima anan gurunsu amma ba wanda ya bashi ko da kalma daya ce, ganin haka yasa ya tashi ya koma tabarmar da larai ta shinfida masa.


_BANGAREN SU HANSAI._


Kai tsaye Alh habibu gidansa ya wuce dasu, kowa ba baka sai idanu da suke ta rabawa kamar shege a rabon gado, sunyi zatan gidan hjy iya za'a kaisu dan cikin zuciyar kowannen su da abinda yake ayyanawa.


Bayan shigar su cikin gidan babban falon gidan ya shiga, yana gaba suna biye dashi a baya, sai dan waige-waige suke yi, suna karewa gidan kallo.

Suna shiga duk mutanen dakin suka mik'e tsaye carko-carko, barka da zuwa suka yi masa sannan ya nemi guri ya zauna su kuma su hansai suka zauna saman carpet, Audi da lauwali tun shigowar sa ya basu umarnin zama a dakin su nura me wanki.


Tambayar sa su mami suka fara yin game da labarin hjy iya, dan su khaleed sun sanarwa mahaifiyar tasu inda mahaifinsu ya tafi bayan sun kirashi a waya.


Kafin ya basu amsar, umarni ya bayar da akai su inna zainabu bangaren su ladidi me aiki.


Bayan fitar su duk abunda y faru a police station din ya basu labari.


_A BANGAREN SU LADIDI_


Su suwaiba aka kai hannun ladidi kasancewar ta fi sauran yan aikin gidan shekaru, amma a shekaru bata kai inna zainabu ba dan shekarunta bazasu wuce talatin da biyar zuwa da bakwai ba, sauran ma'akatan kuwa ladifa, hazuma, da ta rasulu duk basufi shekara sha tara zuwa ashirin da biyu ba, ganin anbawa ladidi ragamar gurun yasa take mulka su ladifa, tana sarrafa su gurun yin aiki yanda ta ga dama, inbanda wanka, sallah da cin abinci ba abinda ladidi take yi.


Laifi kadan mutum zaiyi ta yi masa hukunci yanda ta ga dama ko ta shirya mai makircin da dasu mami zasu yiwa mutum fadan da ransa zai b'aci, shiyasa suke tsoron ladidi fiye da matan gidan, sunaji suna gani ladidi zatayi ta satar kaya tana boyewa inzata tafi garinsu tayi backo guda ta fice da ita, amma basu da halin magana.


Bayan shigar su inna zainabu, ladidi ce kansu a tsaye tana kafa musu dokoki kamar haka, " da alama naga sababbin yan aiki akayi dan haka inasan inji sunayen kowa daga cikin ku " ba musu su hansai daya bayan daya suka fara gaya mata sunan su, kowa da abinda yake ayyanawa azuciyarsa.


Ladidi magana ta cigaba da yi musu cikin isa da nuna iko, " doka ta farko da zan fara kafa muku ita ce, idan ina bacci ba'a tashi na indai ba su hjy bane suka turo ku ku kirani, ko kuma idan daukan wani abun amfanin zakuyi" a tare su suwaiba suka kalli junansu suna mamakin wannan mai maganar ita kuma wacece agidan.


Cigaba da jawabinta tayi,  " sannan daga sallah asuba ba wanda yake komawa bacci, dan zaku dinga taya su ta rasulu aiki dan kuga irin ayyukan da akeyi a gidan, nan da kwana uku nasan kun fahimci komai, kuma ba wanda ya ke fara yin wanka sai na yi inyaso daga baya sai kuyi kuma duk wacce ta kasance itace ta karshe zata kara wanke bandakin dan banasan kaxanta".


Iya ke na lura akwai dan girma tattare da ke, bazaki iya abinda zasuyi ba zuwa safiya zan nuna miki abubuwan da zakiyi, ina fatan kun fahimceni.


Gyada mata kai sukayi saboda yanayin su kadai zai tabbatar maka da agajiye suke, ga bacci da yake fusgarsu, sai sakin hamma suke ga yunwa ta fara taso musu.


Suwaiba ce ta kalli ladidi tace, " dan Allah yunwa muke ji ku bamu abinci"


Wata dariyar rainin hankali me hade da shewa ladidi ta saki, sannan tace, " tabdi lallai da gani mayunwata aka kawo mana gidan nan, daga zuwan ku har kun fara neman abinci ko dan anbaro kalgo da sabara anxo birni dole anemi me maiko, anbaro iya da baba anafama da arne da cot ta kara tintsirewa da dariya.


Sosai ransu ya baci har inna zainabu da bata da hatsaniya amma tabbas taji haushin abinda ladidi tayi musu, hansai ce ta kalleta cikin jin haushi tace, to abincin zaki bamu ko sai kin gama nuna mana wannan wabgegen bakin naki kamar kofar gari, su hazuma sakin baki sukayi cikin tsoro suna kallan hansai, cikin zuciyar su suna fadin " lallai hansai ta debo ruwan dafa kanta"


Tassss kake jin saukar mari a fuskar hansai, ladidi ta wanketa dashi ta hada da zaginta, " uwarki ce me wabgegen baki ni zakiyi wa rashin kunya, yar isk........"


Aykuwa bata karasa ba hansai ta kunduma wani uban ashar ta daga hannu ta buga tsalle ta wanke ladidi da mari.


Aykuwa ladidi ta janyo hansai ta fara duka ta ko'ina, suwaiba na ganin haka ta shigarwa hansai dama tun zuwan su jininta bai hadu da ladidi ba, ga karin wulakancin da tayi musu.


Inna zainabu ce ta mik'e tana basu hakuri, tana zuwa rabawa lokacin ladidi ta kawowa suwaiba duka aka mazge inna zainabu a kafada, cikin jin zafi taja gefe tana shafa gurun.


Su ta rasu ganin fadan yaki karewa yasa dan dole suka shiga rabo, suma zuciyarsu fes take ganin ana nadawa ladidi uban duka dan sarkin yawa yafi sarkin karfi.


Dakyar suka samu suka raba kowa sai haki yake yana maida numfashi, cikin fada ladidi ta fara magana, " yara kunjawa kanku wallahi dani kuke zancen bari inkarasa gurin su hjy zaku san wacece ladidi" fuuuu ta sa kafa fita tana gyara wuyan rigarta tayi bangaren su hjy mami.


_MU KOMA KAUYE_


       Su hjy iya tun suna nan zaune suna sa ido suga shigowar haruna har suka gaji, shi kansa musa yayi mamakin rashin ganin haruna shida be cika yin nisa da daddare ba, ga wayarsa idan ya kira ta akashe.


Har andoshi karfe karfe tara da rabi na dare, dan dole musa yasa aka yiwa su hjy iya shinfida.


Hjy iya ita da larai matar musa a daki daya shikuma shiga su baba dan tsoho a daki daya, suna tsakar gida suna shan iska musa ya shigo da ganda acikin samira, da ya siyo musu a bakin kasuwa.


Zubawa kowa akayi suka fara ci hjy iya kam har zuwa lokacin taki sakin jiki, dan haka da aka bata tace ta koshi, sai larai tayi ta yi mata magiya sannan ta dauki guda biyu taci, tace ta koshi.


Dan tsoho kuwa zagewa yayi ya dinga sharbar romo yana cin ganda, yusuf ma bai ci ta kirki ba ya tashi ya barwa dan tsoho kwanan, aykuwa yace dawa Allah ya hadani inba da ganda ba, sai da yaji cikinsa har ya fara yi masa k'abe-k'abe sannan ya janyeta gefe , ya yunkura da kyar ya tashi yaje ya wanke hannu.


_KIMANIN KARFE BIYU NA DARE_


      Haruna ne rabe a jikin katanga yana sand'a yana yan waige-waige, hannunsa da fitila yana son kunnata yana gudun kar aganeshi, bakin kofar dakin larai ya tsaya ya dan zura kansa yana san shiga, yaji magana kasa-kasa daga dakin musa, da sauri ya ruga bayan bishiya ya buya.


Adai-dai lokacin da yaji wannan motsin cikin dan tsoho ne ya rikice, gudawa ta matse shi yake tashin musa, touch light musa ya kunna masa ya fito ya rakoshi bakin katangar bandaki, shi kuma ya juya daki.


Ganin haka yasa haruna kara sandowa ya kara zuwa bakin kofar dakin larai, wannan karan baiyi wata-wata ba ya fada ciki, yana nan tsaye ya yaji komawar dan tsoho daki, touch light din hannunsa ya kunna ya danne ta da hannunsa ya fara yan haske-haske da gefen fitilar.


Cen saman karamin gado ya hango hjy iya kwance tana bacci jakarta na daga saman kanta jikin kusurwar bango, dan murmushi ya saki yana gyara tsayuwarsa, sand'a ya fara yi yana tafiya a hankali, tarin larai yaji da sauri ya tsuguna a bayan gadon hjy iya,  kirrrrrrr kwaaarrrrr yaji larai ta cigaba da sakin munshari.

Mik'ewa ya karayi cikin sand'a ya nufi jakar hjy iya, har ya mik'a hannu zai dauki jakar kafarsa ta zame ya wad'a kan hjy iya, cikin barci hjy iya taji mutum ya fad'o kanta, kafin tayi magana tuni haruna ya zura aguje ya koma daga bayan katanga.


Salati hjy iya ta saki tana sallallami, larai cikin bacci ta fara jin maganar hjy iya tana,  " la'ilaha'illallahu ni yau hadizatu me idanuna suka gane mun, me jikina ya jiyo mini da tsohon daren nan, oh innalillahi'wainnailahirraji'un wannan wacce irin masifa ce ta kwartayen zamani, ace ni tsohuwa ma basu kyale ba yau naga ta kaina wannan wacce irin jafa'i ce haka".


Larai murza idanu ta farayin cikin bacci, jin irin maganganun hjy iya yasa ta ware idanunta, fitila ta janyo ta kunna tana tambayar hjy iya me yake damunta.


Cikin tsananin mamaki hjy iya take  gayawa larai abunda taji kuma ta gani, dan jim kadan larai tayi tace, " iya kwarto kuma a gidan nan anya ba mafarki kikayi ba kuwa, gidan nan shekarata goma sha biyu kenan amma ko barawo bai taba shigo mana ba sai dai ko........


           Katse ta hjy iya tayi cikin jin haushi da ganin ta raina mata hankali ta fara fada, " ke yarinya dube ni nan karki nemi ki karyata ni, idan ba'a shigo dakin nan ba babu yanda za'ayi nace muku wani ya shigo amma tunda kin ce haka  shikenan, dakinki nazo duk abinda kika ce mun nina ja.


A'a dan Allah kiyi hakuri iya wallahi ba karyata ki nayi ba, abun ne ya bani mamaki amma kiyi hakuri bari naje na taso malam....., a'a basai kin taso shi ba, hjy iya ta katse ta, ki bari kawai Allah ya shiga tsaninmu da mugu.


Hjy iya da larai komawa sukayi suka kwanta, ba jimawa bacci ya kara kwashe larai, sai sakin munshari take hankali kwance, hjy iya bacci kaurace mata yayi tana nan kwance idanunta kyam akan kofa.


Duk maganganun da su larai sukeyi akan kunnen haruna suka yi, jinkirtawa yayi dan bacci ya kara daukansu.


Adakin su musa tunda dan tsoho ya koma yake dan murkususun ciwon ciki, yana daga kwance sai juye-juye yakeyi, musa ne ya waigo yace, " baba har yanxu cikin ne?" ehwlh, ji nake kamar bandaki zan kara komawa, to muje inraka ka mana bari indauko fitilar daga nan nima nayi fitsari musa y fada yana kokarin tashi.


Fitowa dan tsoho suka yi shida musa, fitowarsu tayi dai-dai da shigar haruna dakin su hjy iya, karaf idan musa ya kai gurin ganin inuwar namiji ya shige dakin larai, basarwa yayi kamar  bai gani ba saida ya raka dan tsoho bandaki ya dawo da sauri ya janyo kofar dakin larai ya tura da karfin gaske ya datse ta.


*_DAMINA 🌧️🌧️🌧️ TA KANKAMA ALLAH YA BAMU ALBARKAR CIKINTA SHARRINTA ALLAH YA KAREMU._*

_Masu yin comments ina godiya matuka, duk wadda banyiwa replay ba tayi hakuri na sake sabon whatsapp, waiting yake samun a rubutu ina matukar Alfahari daku._

*Vote*

*Comments*

*Share*


   _MUM ASLAM Ce_πŸ˜‰πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

       _17/7/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

    _AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


                37&38

Hjy iya na kwance ta ga shigowar mutum tana shirin kurma ihu batayi aune ba taji anbanko kofar da karfi ga duhu dakin, cikin tsananin tashin hankali da gigicewa ta rafka wani uban salati tana neman agaji.

            " Jama'a ku taimaka ku kawon agaji yau ni hadiza me nake gani agidan duniyar nan, abunda nake jinsa wai-wai shi ne yau ya iso gareni, tsofai-tsofai dani na hadu da shaidanun zamani"+


firgigit larai ta bude ido tana yan dube-dube cikin duhu, ta wawuri fitilarta haska dakin ta farayi bata ga komai ba cikin mamaki take tambayar hjy iya, " anya iya nikam ba mutanen boye bane suke san su fara tsorata ki, cikin dare sai ihu kike ko dai gamo kikayi?

        A'a hange nayi ba gamo ba, me kika dauke ni ne yarinya? To iya kina gani dai na haska babu komai adakin larai ta fada tana kara haska jikin bangwayen dakin.


Idan bakiga komai ba to ki sauka ki haska har karkashi gadajen nan, hjy iya ta bata amsa, da himmarta larai ta muskuta zata sauko daga gado tana hasko kasa ta hango inuwar mutum a jikin zanin gadon ta ya tsugunna, da alama wani ne ya lab'e a karkashin gado.


Wani razanannan ihu larai ta saki ta koma gado da baya tayi cen kuryar gado tana zunduma ihu.


_GIDAN ALH HABIBU_


Buguzum-buguzum haka ladidi ta tafi sashen su hjy mami, tana zuwa bakin falon ta canja tafiya tana dan dingisawa, tana shiga falon ta fashe da kukan karya na munafurci, matan gidan ne zaune da yara, lokacin Alh habibu ya shige sashen sa, dan tun lokacin da abun hjy iya ya faru ya ke kadaice kanshi daga cikin mutane.


Ido suka zuba mata har ta karaso cikin falon, tana zuwa tsakiyar falon kuwa ta kara rushewa da kuka sai da tayi mai isarta sannan, Auntyn yara ta fara tabayarta,  " lafiyarki ladidi ko wani abun ne ya faru?" girziga kai ta fara yi, mami itama ta jeho mata tambaya,  " to ladidi ko waya aka miki daga gida akace ba lafiya? Hjy ba daya daga ciki, yanxu hjy kamarni wai yaran nan zasuyiwa irin wannan cin mutumcin na tsamar nama, harda duka.


       duka yan falon zaro idanu sukayi cikin mamaki, Mami tace " duka ladidi ana zaune kalau to me yake damun su hazuma" , sharce hawaye tayi gefe sannan tace, " hjy ba su hazuma bane, sababbuun yan aikin da aka kawo ne" ladidi kina nufun  su inna zaunabu? To dududu mintinsu nawa a gidan ko awa guda basuyi ba shine har zasu nuna halinsu lallai da sake.


Ay ba tsohowar bace wannan yan matan ne akan ina gaya musu ayyukan gidan nan kuma nace musu bakwa san kazanta a gidan shine suka fara zagina dan nace zan gaya muku shine suka ce inje infada, dayar cikin su harda zagin uwata nikuma naji haushi na mareta shine suka rufeni da duka, ladidi na kaiwa karshe ta kara fashewa da kuka.

Sororo su hjy mami sukayi suna jin abunda ladidi taxo musu dashi.


Bayan fitar ladidi daga dakinsu, ta rasulu ce ta kalli su hansai tace,  " ku kuwa wane tsautsayi ne yaja ku yin fada da ladidi harda damb'e wallahi yau kunshiga uku da makircinta, da kun sani baku biye mata ba, muma nan da kuke gani wallahi hakuri mukeyi da ita, muna hakurin ma ya yakaya bare ku daga zuwanku har fada ya hada ku" ladifa ta karbe zancen da, " ni wallahi da suka fara fadan ma har kifta musu ido nake yi akan su kyaleta amma basu lura ba gaskiya suwaiba kun janyowa kanku, aikin da ladidi ma zata dinga saku kadai ya isheku"


Suwaiba ce tai musu kallan tsab sannan tace, " makirci kuka ce kome? To ay idan ladidi na tak'ama da  makirci gidan taxo, wallahi ba'ayi hegiyar da zata zagarmun uwa inkyaleta ba kawai daga munce abamu abinci sai abun ya zama cin mutumci, ta dade bataje ta kai karar mu ba, ninan warki ce daidai da k'ugun kowa"

Hansai ce ta cigaba da magana, " to wai ma intambayeku ita din wacece acikin gidan nan ko yar uwar Alh ce? Shiyasa take nuna muku isa da iko", a'a ba yar uwar kowa bace itama yar aiki ce kawai dai ta fimu dadewa agidan ne, kuma ta fimu shekaru.........., zancen banza, suwaiba ta katse su, au ashe ma ba kowan kowa bace ita ma matsayinmu daya da ita, har take neman ta ci zarafin mu lallai ta taro aradu da ka.


Sunan cikin tattaunawa fatima ( _Autar mami_) ta shigo dakin da sallama, tsit sukayi kamar ruwa ya cinye su, kiran suwaiba da hansai tayi basuyi mamaki ba dama sun san za'ayi haka, ba wata alamar damuwa atattare dasu suka amsawa fatima tashi sukayi su bi bayanta tana gaba.


Suna tafe a hanya suwaiba ta tab'o hansai kasa-kasa tace, " hansai idan muka je duk abinda kikaji nace idan antambaye ki kice eh, ko kuma ki kara da naki dan na lura wannan ladidi ta amu guri agidan nan da yawa, gyada mata kai hansai tayi suka karasa cikin falon.


     Suna shiga cikin falon suwaiba ta fara dingishi ta jan magina kamar wacce ta ci kuka ta more, zama sukayi a kasan carpet suwaiba harda cije baki alamar kafarta ciwo take.


Mami ce ta kallesu fuska a tsuke ta ce, " me ye dalilin daya sa kuka yiwa ladidi rashin kunya, daga zuwan ku har ta kaiku da dukanta.

Kuka suwaiba ta fashe dake sannan tace, hajiya na tabbata ladidi bazata fada muku aynihin abunda ya faru ba amma nasan da zakuji kuma da sai ranku ya b'aci, kuma banyi tunanin ladidi har zata iya zuwa kawo kara ba" da mamaki Auntyn yara ta kalli suwaiba tace, " me ladidin tace yi mana bayani mana kibar kukan"

Ladidi sakin baki tayi tanasan taji me suwaiba take shirin fada.


Jan magina suwaiba ta karayi, ta goge hawayen wanda dama kukan yafi hawan yawa, ta fara musu bayani, " D'azu bayan ankaimu gurunsu ladidi muna zaune sai ladidi tace mudin su waye? Sai mukace mata 'yan aikin gidan hjy iya ne, sai ta ja dogon tsaki tace, Au dama ku yan aikin wannan jarababbiyar tsohuwar ne? Kankanba da shegen iyayinta yasa ta tafi kauye ta b'ata, kawai za'a kwaso ku akawo mana ku nan, wato kunzo cin arziki ko?


Ni kuma na kalleta nace, " wallahi hjy iya ba jarababbiya bace kuma hjy iya ta fiye mana ke sau dubun dubu, dattijuwa me rikon addini ga tausayin nakasa da ita, suwaiba na zuwa nan ta kara rushewa da kuka cikin kukan karya take fadin, " oh Allahu akbar hjy iya Allah ya bayyana mana ke ko iya kwana biyun nan da bata nan munyi babban rashi.


Ba ladidi ba hatta hansai saida ta jinjinawa suwaiba, akan maganar da sukaji ta shirgo, cikin huci ladidi tace, ke dan ubanki ni zakiwa karya kaji yar iskar yarinya da sharri............. Mami ce ta katse ladidi cikin b'acin rai, " ladidi rufe mana baki kar insake jin kuma kin zagi daya daga cikinsu" ladidi haushi taji ta gallawa suwaiba harara, suna hada ido kuwa suwaiba ta fakaicin idon mutane tayiwa ladidi gwalo.


Ke suwaiba munjinki cigaba da bayani.


Suwaiba sunkwi da kai kasa tayi ta cigaba da magana, "  to dana gaya mata haka sai cewa tayi kilama hjy iya hatsari tayi a hanya ta mutu, dan haka karma muga munxo nan muyi zatan zamu mike kafa, ana gano gawar hjy iya zamu koma kauye mu cigaba da cin tuwo da bak'ar miya".


Laaaha'ilahailahaillahu muhammadurrasulillahi sallallahu,alaihi wasallam, gaba daya dakin aka dauki salati cikin al'ajabin abinda ladidi tayi, Auntyn yara rike baki tayi ta karewa ladidi kallan mamaki, cikin jin haushin ta tace, " gaskiya ladidi kin bamu kunya yanxu hjy iya kike gayawa haka jiya-jiya muka jajantawa dake akan batan ta ashe ke murna kike fal zuciyarki lallai mugu bashi kam.


Ganin maganganun suwaiba sunyi tasiri gurunsu mami, yasa suwaiba dan zunguro hansai da kafa tana kifta mata ido.


Jin falon ya tsagaita da hayaniyar yasa hansai karbe zancen tana dan murza idanu tace, "  ni wallahi abunda yafi bani mamaki ma da naji tace wai dama kadan take san samu ta shawo kan Alh ya amince da aurenta duk tayi maganinku, acewar ta wai taga yanda kuke wadak'a da dukiya kuda 'yayanku, shi ne muka fara cacar baki har dambe ya hada mu, da taji munce xamu xo mu gaya muku sai tace ita zata fara zuwa tai mana sharri agurunku.


Wannan karan ma salati suka kara sawa cikin mamaki suke kallan ladidi da bakin ciki yasata sunkuyar da kai kasa tana mamakin yara kanana sun iya makirci, bata taba tunanin haka daga garesu ba saboda taga su ta rasulu sam basu da wayo da dabara koda sharri ta kulla musu haka zasu kwana ciki sai dai suyi kuka su goge hawayen su.


( _Dama ay ba kullin ake kwana a gado ba, kuma hausawa sun ce rana dubu da barawo_ ............)


Fatima dake kusa da ladidi cikin tsiwa da jin haushi ta fara yiwa ladidi magana, " Wallahi ayau basai gobe ba zaki bar gidan nan munafuka algunguma wato zagwan kasa kika dade kina yi mana ko, kakarmu ta b'ata kina murna sannan kina ikirarin zaki auri ubanmu da ki zalincemu nida iyaye na, annamimiya dama tsintacciyar mage bata mage" ta karasa maganar tana kaiwa ladidi hauri da kafa.


Ke fatima bana san rashin kunya ko ba komai kinsan dai ashekaru ta haifeki ko, kar inkara jin bakin ki, mami ta fada cikin tsawatarwa, turo baki fatima tayi ta dauke kanta gefe.


Mami ranta ya gama b'aci ta dubi ladidi tace,  " ladidi iya zamanmu da ke mun nuna miki kauna da kyautatawa duk cikin yan aiki ba wacce muka janyo jiki kamar ke, duk abubun da kikeyi ina sane da wasu, ashe dama mugun kudurin da ke cikin zuciyarki kenan? Ba abinda zamu ce miki kije ke da Allah sannan ki tattara ya naki ya naki, bazan kore ki yanxu ba tunda yanxu dare ya farayi amma gobe gari na wayewa ki bar mana gida.


Auntyn yara ta kalli mami tace,  " mami ya zaki ce ta bari zuwa safiya idan ta fita yanxu ay bazata rasa mota ba.


A'a Auntyn yara abari zuwa safiyar dai kawai.


Ladidi zuwa tayi ta kama kafafuwan mami ta na bata hakuri tana karyata su suwaiba, duk cikinsu ba wanda ya kulata, ganin zata dame su da kuka yasa, Auntyn yara ta basu umarnin kowa ya fita ya bar musu falon.


Ladidi kin tafiya tayi tana basu hakuri, da suka ga abun nata ba na kare bane duk suka tashi suka bar mata falon, ba don taso ba ta fito jiki ba kwari ta kara jinjina makirci irin nasu suwaiba.


_INA LABARIN B'ARAWON JAKA_ 🀣


Haruna na karkashin gado sai kyarma yake yana rawar dari saboda tsoro da firgici, luf yayi kamar babu mutum agurin, gumi ta ko ina sai keto masa yake.


Musa na ce tsakar gida yana tunanin abinyi, cikin zuciyarsa kuma yana mamakin waye ya shigo masa gida har ya fada dakin matarsa, wata zuciyar tace, " ba kazo da baki jiya ba wata kila wani ya biyo jakarsu ko zai samu nasarar dauka.


Kamar wanda aka zabura yaje ya dauko katuwar gora, ya taso yusuf, lokacin dan tsoho ya fito daga bandaki ya fara jiyi ihun su hjy iya.


Ganin musa da gora yasa shi yin gum da baki yana kallan ikon Allah, fitilar hannunsa ya haska kofar dakin tura kofar sukayi da kafa suna haske-haske, ganin haka yasa larai buga uban tsalle daga gado ta fito, hjy iya yunkurawa tayi da kyar ta tashi itama da sauri tayo waje.


Motsi sukaji alamar za'a fito aykuwa da sauri suka ja kofar suka datse, carko-carko sukayi a tsakar gida daga baya suka tatattara suka yi dakin da su dan tsoho suke.


Suna shiga dan tsoho ya fara magana, " hadizatu wai me ya sameki da tsohon daren nan kike ta ihu, ni nayi zatan ma gamo kikayi, da har nace a miko mun buta inyi alwala inshigo.


πŸ™„πŸ™„πŸ™„πŸ™„ _kai dan tsoho kai kam akwai sakin layi._


Kallansa hjy iya tayi bata tanka masa ba dan abun na dan tsoho yanxu haushi yake bata ba mamaki ba, yusuf ne ya kalli dan tsoho yace, " baba yan yanxu ma bata baci ba baka ga mun rufo kofar ba, ay aljanin yana cikin d'akin indai rukiyya ce zaka iya fitar dashi"  dan tsoho yi yayi kamar be ji me yusuf yace ba ya fara yan waige-waige yana basarwa.


_DA ASUBA_


Ana kiran assalatu musa da yusuf suke shawarar yanda zasuyi da mutumin cikin dakin larai, daga karshe suka yanke shawarar su kira makota ayi masa atile.


       Bayan  fitar su, dan tsoho ne ya fito yaxo bakin kofar ya fara kukarin banza, " yooo Allah na tuba yaro ni da za'a barni da kai da baka ga yanda ake surfe da casa ba, ayni basu gayamun barawo bane, da banyi maka daurin huhun goro ba", ya karasa maganar yana tura kofar dakin.


       Haruna dama na labe jikin kofar yanajin fitar su musa yake ta ayyana yanda zaiyi ya fita, sai kuwa dama taxo masa dan tsoho ta turo kofar, da karfin gaske haruna ya banke dan tsoho ya sha kwana da gudu ko waiwaye baya ni.


su larai na daki sai ihun dan tsoho sukaji, suna fitowa yayi daidai da shigowar su musa da wasu makotan su  hudu, gaba daya kansa sukayi suna tambayarsa tsab ya basu labari, cikin takaici suka kinkimi dan tsoho suka kai daki suna bakin cikin guduwar barawon.


     Da safe bayan sun karya sunyi wanka, haruna ne ya shigo kamar ba shi ba gaida su yayi ya mikawa musa dan kati da hoton da Alh habibu ya basu ya juya ya fita, musa na kiransa ya waiwayo yace masa yana zuwa.


Hjy iya yanda take murna kamar habibu ta gani ba no sa ba, musa ne yasa no awayarsa ya dialing call, a speaker ya sata kowa naji ya kira har sau biyu no answer, hjy iya har ta fara sarewa musa ya kara kira a kashi na uku sannan Alh habibu ya dauka da sallama.

Tun kafin musa yayi magana hjy iya cikin d'oki da zumudi tace habibu naaaaaa.


Kamar amafarki Alh habibu yaji muryar hjy iya, shima cikin farin ciki ya furta Hjy iya.

  _Wash yasin nasha typing ku saurari shafi na gaba_✍🏻


            *Juma'at khareem* 😊


*Vote*

*Comments*

*Share*


    _MUM ASLAM Ce_πŸ˜‰πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

       _25/7/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

    _AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


                39&40


Hjy iya farat tayi ta karbe wayar daga hannun musa ta cigaba da yiwa habibu magana.


Alh habibu har rasa bakin magana yayi dan farin ciki da jin muryar hjy iya, cikin d'oki da murna yace, " hjy iya yanxu kina ina ne naxo na taho dake?" kwallar farin ciki hjy iya ta goge sannan tace, " muna wani dan kauye amma bari ga wanda muke gidan nasa ya gaya maka sunan garin da muke, habibu nayi kewarka dan Allah ka hanzarta kazo taho dani"+


cikin kewar mahaifiyarsa yace, " hjy iya karki damu kinmanta habibunki ne, magana bazata yuwu ta waya ba bashi wuyar muji sunan garin insha Allahu baza'a dau lokaci ba zaki ganni"


wayar ta mik'awa musa, sallama ya yiwa Alh habibu bayan sun gaisa ya gaya masa sunan kauyen, godiya ya yi masa yace abawa hjy iya wayar.


     Dan tsoho ne yayi karaf ya karbi wayar da murmushi a fuskarsa ya fara magana, " D'ana habibu barka da safe yau kuma sai kaji muryar hadizatu to muna nan muna jiran isowarka, kai ammafa munsha karakaina........


Fisge wayar hjy iya tayi tana mita, ba tare da dan tsoho ya gama wayar ba, " magana ta cigaba da yiwa Alh habibu cikin farin ciki har suka kammala wayar.


Hjy iya bakinta har kunne, kowa ya ganta yasan tana cikin farin ciki, dan tsoho ne ya kalleta cikin marairaicewa yace, " yanzu hadizatu habibun ma bakya san mu gaisa dashi? Wai ni meye aibuna da ko kadan bana birgeki? Bakisan Abinda Allah ya boye ba, ba'a ja da hukuncin Allah.......

        Cikin jin haushi hjy iya ta katse shi, dan Allah ina cikin farin ciki karka sa raina ya baci, kai ni narasa irinka sai magana kamar ka hadiyi radio, Allah ya sawake maka"


Aameen kawai dan tsoho yace saboda ya lura da gaske hjy iya batayi dashi din, gefen bishiya ya koma ya zauna yana kallan su kowa da Abinda yake yi.


Lokacin da musa ya kira Alh habibu yana toilet yana wanka, shiyasa suka kirashi har sau biyu bai dauka ba sai ana uku wanda yayi daidai da fitowarsa daga wanka ya dauka.


Bayan sun gama waya da su hjy iya agurguje yasa kaya ko mai be shafa ba, fitowa yayi babban falo iyalan gidan duk suna zaune breakfast sukeyi.


Kana kallan fuskar Alh habibu kasan yana cikin matsanancin farin ciki bakinsa har yaki rufuwa, ganin yanayin daya fito yasa Auntyn yara ta fara tambayarsa.

          " Daddyn yara lafiya meyake faruwa na lura kana cikin farin ciki, ko wani albishir din akayi maka.........


Katse ta yayi da, " kwarai kuwa ban dade da samun albishir ba"

Mene ne albishir din, mami ta tambaya.


Wallahi dazun nan wani bawan Allah ne ya kirani wai hjy iya na gidansa.


Gaba daya falon ya rude da ihu saboda murna da farin ciki.


Kairat da khaleed ne sukayi farat suka ce, " dady dan Allah muje tare wallahi munyi missing din hjy iya"

Banasan fa bata lokaci, dan munyi waya da DPO zamu hadu da yaransa a hanya, Alh habibu ya fada yana kokarin fita.


Da sauri khairat ta mike tana fadin, " daddy wallahi ba abinda zanyi hijab dina kawai xan dauko nasan kafin ka tada mota ma na fito" ta karasa maganar tanayin part dinsu da gudu.


Fatima ce ta rufa mata baya tana fadin, " wallahi nima daddy zani kowa dai a gidan nan yasan hjy iya ta hannun dama na ce"


Shigewar su fatima ba jimawa ladidi ta shigo tana sharbar hawaye, da mamaki Alh habibu ya kalleta yace, " lafiya ladidi meya sameki"


Durkushewa tayi a k'asa ta kara sautin kukanta,  cikin dakusashshiyar murya ta fara magana, "  Hajiya dan Allah kuyi mun rai karku koreni daga gidan nan, wallahi duk abinda suka fada sharri suke mun, Alhaji ku dubi girman Allah kumun rai ku kyaleni na cigaba da yi muku aiki, idan na bar nan bansan ya rayuwar mu zata kasance ba nida yan marayu na ba......"


" To bak'ar munafuka waye yace ki shigo cikin falon nan, wai ba an sallameki ba ko wani tiggun kika shigo ki kara kullawa" fatima ce ta katse ladidi cikin tsiwa.


Wata razananniyar tsawa Alh habibu ya dakawa fatima, ba shiri tayi gum da baki tana watsawa ladidi harara.


" Ke ladidi wuce kije bangarenku banida lokacin wannan sakarcin naku sai na dawo tukunna" Alh habibu ya fada yana sa kai waje.


Yana fita ladidi ta rufa mai baya zuciyarta fal farin ciki, su khairat ne suka bi bayan ladidi, harabar da motocin gidan suke nan suka nufa, mota Alh habibu ya dauka su fatima na shiga shima khaleed ya fito yana shiga motar, Alh habibu ya bata wuta suka fice daga cikin gidan.


Hanyar kauyen sabon garin malam suka nufa tafiya sukayi me dan nisa, wacce akallah sun shafe kusan awa daya da minti arba'in sannan suka je garin.


Gangarawa gefen hanya Alh habibu yayi, sannan ya kira wayar musu kiran farko da yayi is not reachable, sai da ya kara trying sannan ta fara shiga, sai da ta kusa tsinkewa sannan ya dauka da sallama.


      " Assalamu alaikum barka dai Alhaji ko ka iso ne"


Cikin d'oki Alh habibu yace, " na iso ay ina bakin hanya ma, ina zan shiga?"


"A'a bari nazo na taho da ku dan kwatancen ne sai kazo kasha wahala" musa ya fada.


" to shikenan ina jira sai kaxo malam musa" Alh habibu ya fada fuskarsa fal farin ciki.


Suna gama wayar, lambar copral sunusi ce ta shigo, da sauri Alh habibu ya dauka, " hello officer kuna wajen ina ne?" daga dayan bangaren aka amsa,  " mun kusa shigowa cikin kauyen idan mun shigo wacce hanya zamu bi?"


" Zaku ga wata Ash din mota tayi parking agefen hanya mota ta ce, nayi waya da mutumin da hjy iya take gidansa yanxu xaixo ya taho damu"  Alh habibu yayi musu bayani.


" ok, sai mun karaso" copral sunusi ya bashi amsa yana kashe wayar.


Ba'a dauki lokaci me tsayi ba motar su copral sunusi ta karaso gun da Alh habibu ya kwatanta musu.


Daga nesa suka hango wani mutum na tahowa gurinsu shida wani matashin saurayi, amma ganin motar yan sanda agefe yasa musa da yusuf dan dakatawa suna kallan juna.


yusuf ne ya fara magana, " malam musa kardai wancen mutum wanda naga suna hira da yan sandan cen shine Alh habibun?"


      " To nima ina na sani tare da kai fa muka taho, amma to meye na zuwa da yan sanda, gaskiya nikam na fara jin tsoro kar *DAGA TAIMAKO*( _Sadnaf_) nazo na shiga cikin matsala, waya sani ma idan mukaje ko kwashe mu zasuyi gaba daya" musa ya fada a dan rikice.


Dan jim yusuf yayi, sannan yace, "  kuma fa maganarka tana hanya wallahi nima na tsorata kai kaga dalleliyar mota kamar bata taka titi,  da alama fa mutumin nan me kudin gaske ne, wallahi Allah ne kadai yasan kudin da yabawa yan sandan cen dan su kame mu"

Alh habibu na tare da su cp sunusi suke hirar wahalar cigiyar hjy iya da suka sha, hango su musa sukayi suna dan tattaunawa, Basajin me suke fada amma Alh habibu ya so ya gane fuskar musa.


Kallan su cp sunusi yayi yace, " da alama wancen mutumin shine mukayi waya dashi dan naga suna kallo gurin nan, me zai hana mu karasa gurinsu inyaso sai mu daukesu a mota mu wuce"


" shikenan angama Alhaji" cp sunusi ya bashi amsa yana d'ane bayan mota.


Kowannen su mota ya shiga suka nufi wajen da su musa suke tsaye, ganin motocin sun tunkaro gurunsu, musa ya kalli yusuf yace.

            " wallahi da gaske zuwa yayi su kama mu, kai ni na arce kaima kayi ta kanka"


Kamar hadin baki musa da yusuf suka juya aguje, Alh habibu ne ya fara yi musu horn cikin mamaki, dan waigowa yusuf yayi yaga sun kusa cin musu, iya karfin sa ya zage yake zabga gudu.


Musa gudu yake kamar zai aro wata kafar ya kara, lokaci daya shida yusuf takalmansu ne suke tsalle, takalmin daya daga cikinsu har saman glass din motar Alh habibu.


Fatima da take  guntse dariya tace, " daddy wai mutanen nen gudun me suke yi haka kamar wadanda suka ga yan mafiya"


Shiru ne ya biyo baya bai bata amsa ba, khairat tace, kila dai ko motar police din da suka gani ce kinsan halin mutanen mu ko gani suke kamasu za,ayi" lokaci daya suka kwashe da dariya.


Da sauri motar su cp sunusi ta sha gabansu musa,  yan sanda biyu ne suka diro daga motar suna musu magana cikin limana, " Abokina dan Allah ku dakata haka da gudun nan sai wahalar da kanku kuke, muma kuna wahalar damu"


Cen gefe musa ya rakub'e yana raba idanu, yusuf ne ya dan saki jiki ya matsa kusa da su cp sunusi, amma har zuwa lokacin be gama sakin jikinsa ba.


Alh habibu ne ya fito daga mota, gurin musa ya tunkara da sakin fuska yana masa sallama, bayan sun gaisa Alh habibu yace, " mlm Ba kai bane musa wanda mukayi waya dashi d'azu?"

        "Eh, nine" musa ya bashi amsa.


" to naga kun zuba da gudu ne, shigo mota sai mu karasa gidan ko" Alh habibu ya bude masa kofar.


Bayan shigar musa da yusuf mota, musa ya kalli Alh habibu yace.

      " wallahi tsoro mukaji da muka ganku harda polisawa munzaci kama mu zasuyi"


Alh habibu yace, "Haba malam musa, banda abinka me kuka mun da zamu kama ku, kundai tsorata ne kawai"


Suna tafe motar su cp sunusi tana biye dasu, duk inda suka bi sai anbisu da idanu, kowa da abinda yake fada azuciyarsa wasu ma har tab'o yan uwansu suke suna nuna musu.


Yan kallan kwaf wadanda suka hango musa kuma, mamaki sukeyi, inusa me nik'a ne ya kalli dauda me walda yace, " Dauda wai kaga abinda ido na ya gani kuwa, musa mijin larai ne fa acikin waccen hadaddiyar motar, yau musa wane aiki yayi da har zai shiga irin wannan hadaddiyar motar"


" uhummmm inusa kenan kamar bakasan musa da neman suna ba, kasan shi wai shi me zuciyar tausayi naji labarin ance wai taimakon wasu mutane yayi jiya, lokacin da suka wuce ay baka nan, ina zaune na ganshi ya wuce da wasu yan birni, Allah sa ma ba masu laifi ya dauko ba, tunda kaga motar yan sanda na biye dashi" dauda ya karasa maganar yana mik'ewa tsaye.


Inusa yace, " to Allah ya kyauta, dauda ina zaka muna hira kuma?"


Dauda yace, " zan karasa wajen gidan musa mana inba ido abincinsa, da abaka labari gwara ka bayar, ninan sai nagano kwal uwar daka"


"To Allah ya shiryeka ni dad'i na dakai san jin gulma"  inusa ya fada, dauda yace " Aameen kai ka zauna idan na dawo na baka labari, ni nayi nan"  dauda ya karasa maganar yana nufar hanyar da motar su Alh habibu ta wuce.


Alh habibu suna tafe musa yana nuna masa hanya har suka karasa kofar gidan, parking din mota sukayi suna fitowa suka ga mutane sun musu caaa, mata sai lekowa suke ta katanga, mazansu duk sunyi carko-carko kowa yana jiran yaga me zai faru.


Hjy iya tun lokacin da taji Alh habibu ya karaso wa musa waya yace yana bakin titi, ta tada musu da rigima akan dole sai ta bi musa sunje tare, ba yanda beyi da ita ta bari yaje ya taho dashi, amma fir taki yarda harsai da yace zai fasa zuwa tukunna ta hakura, shi yana guje mata wahalar tafiyar da zasuyi.


Ji tayi kamar tayi tsuntsunwa, bayan fitar musa amma ta dake ta hakura, tana nan zaune ita da dan tsoho suka ji tsayuwar motar Alh habibu.


Da sauri hjy iya ta mik'e ko takalmi bata sa ba, tayi hanyar fita tana cikin tafiya wani itace ya tad'e mata kafa, gaba daya hjy iya ta tafi luuuu ta gaba zata fadi har ta saddak'ar zata kai kasa.


Cikin azama Alh habibu, ya tafi da sauri ya riko hjy iya, cikin murna ya fara magana, " hankali hjy iya zaki fadi"

Hjy iya rugume habibu tayi ta fashe da kukan farin ciki, cikin kuka tace, " Habibu na Ashe zamu kara ganawa, Allah yayi maka Albarka habibu, Ashe gata kayi mun daka hanani tahowa " hjy iya ta kara fashewa da kuka.


Alh habibu shi dinma kwallah ce ta xubo masa ta farin ciki yace, " hjy iya na shiga tashin hankali mara misaltuwa alokacin dana ji labarin baki karasa rigana ba, amma Alhamdulillah tunda kin fada hannu na gari"


   " Kafin mu fad'o hannu nagari amma ay mun fige kazar wahala ko hadixatu? " dan tsoho ya fada yana dariya.


"Mu kuwa da har mun fara dakan gumba muna sadaka, dan tuni mun fara zaman makoki " fatima ta fad'a cikin zolaya.


Khaleed yace, " hjy iya ina shirin fadawa rijiya dan inbiki, daddy yace mun anji labarin inda kike.


_Gaba daya shafin nan sadaukarwa ne  ga tsohon kwamishinan yan sanda na jihar kano  wato, *CP WAKILI (SINGAM)*_πŸ‘¨πŸΌ‍✈️ ( _Tunda naxo garin nan kun karaji anyi? Kash!!!  nace kun karaji anyi_)πŸ˜ƒ


  _*Kanawa kuna ina? AkaftaπŸ‘πŸ»*_


*Vote*

*Comment*

*Share*


     _MUM ASLAM Ce_πŸ˜‰πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

       _1/8/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

    _AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


                41&42

Hjy iya hararar wasa ta watsawa khaleed tace, " meyasa baka biyoni har nan neman nawa ba kabar ubanka yake ta zarya" ta cigaba da cewa, " ke kuma ja'ira ina nan har sai naga aurenki da 'yayanki ke ni nan sai na mammaka miki ganye idan kika haihu.+


Juya kai gefe fatima tayi cikin wasa tace, " cab lallai ma hjy iya da kanki zakiji ko da ruwan zafi? "


Musa ne ya katse musu hirar cikin girmamawa yace, " Alh ku shiga daga rumfa mana ga tabarma ku zauna"


Guri suka nema suka zauna larai matar musa ta kawo musu ruwa me sanyi na cikin randa, sha sukayi sosai suna santin sanyinsa.


Hira ce ta barke atsakaninsu anata hirar yausha gamo, hjy iya tana kusa da Alh habibu ta rik'e hannunsa gam kamar wanda zai gudu ko za'a kwace shi sun shafe kusan awa guda suna hira daga karshe Alh habibu ya nemi kebewa da mlm musa.


Dakinsa musa ya jashi suna shiga dakin Alh habibu yace, " mlm musa nagode kwarai da irin taimakon da abinda kamun duk fadin duniya banida sama da mahaifiya ta, ina kaunar hjy iya zan iya rabuwa da kowa da komai akanta, bani da wani abu da zan maka na godiya dan Allah kayi hakuri da wannan " kudi ne yan dubu-dubu bandir biyu, Alh habibu ya janyo hannu mlm musa ya sa masa aciki.


Kamar amafarki mlm musa ya zurawa kudin idanu, yana kallo dan murna fashewa yayi da kuka yana kamo kafar Alh habibu yana zabga masa godiya.


Alh habibu hannu yasa ya d'ago shi sannan yace, " haba mlm musa meye na tsugunnawa sam ni banasan irin haka, kuma abu na gaba banasan idan mun fita kacewa wani daga cikin su na baka wani abun"


Jan majina yayi ya sharce hawaye ya amsawa Alh habibu.


Bayan Alh habibu ya dawo gurin su hjy iya kallanta yayi yace,  " hjy iya kin gama komai zamu iya wuce wa ?"


Cikin murmushi hjy iya tace, " nagama komai habibu na yau sai gida, ke fatima tsallaka ga jakata cen jeki dauko"


Hjy iya kudi ta debo masu yawa ta bawa larai sai zabga godiya takeyi.


Fitowa sukayi kofar gida, duk makota sunyi carko-carko suna lekensu, Alh habibu ya kalli yusuf yace, " samari kaida baba ya sunan garin da kuke sai mu saukeku "


Yusuf ne ya fara magana, " nidai a kurna nake baba kuma bansan a ina yake ba"


Kallan sa Alh habibu yayi alamar yana san yaji ta bakinsa.


Dan tsoho  kallan hjy iya yayi ya saki wani malalacin murmushi sannan yace, " ummmm d'a habibu dama kai nake jira infayyace maka duk abinda yake faruwa, to kuma bansamu lokaci na maka maganar ba"


Da mamaki Alh habibu ya kalli dan tsoho yace, "To baba lafiya dai ko?"


Ehto dama tun ranar da muka hadu da hadizatu Allah ya dasamun wani abu a zuciya ta, nayi kokarin infahimtar da ita amma kamar tamun mummunar fahimta, so nake na aureta ne muyi zamanmu cikin lumana da kwanciyar hankali"


Khaleed, fatima, khairat da yusuf dariya suka fara harda rik'e ciki, khairat saboda dariya harda hawaye.


Alh habibu murmushi yayi dan dama tun zuwansa ya fahimci wannan batun daga gurin dan tsoho amma ya basar, tsohon ya bashi dariya sosai saboda da alama irin rigimammun tsofaffun nan ne, kuma shi dan tsoho zuciyarsa daya yayi maganar, Alh habibu tunowa yayi da bayan rasuwar mahaifinsa zawarawa sunyi ta kawowa hjy iya tayi tun ma da kuruciyarta amma babu wanda ta bawa fuska bare yanxu da tsufa yaxo, tunowa yayi akallah mahaifinsa zai samu shekara sama da hamsin da rasuwa, da irin gwagwarmayar da hjy iya tasha akansa, nan da nan kaunar mahaifiyar tasa ta kara ratsa jinin jikinsa........."

Dan tsoho ne ya katse masa shirun da Alh habibu yayi yace, "  d'ana habubu kayi shiru ko kaima bazaka ce komai akai ba?"


Wani murmushin Alh habibu ya karayi  Akaro na biyu ganin yanda dan tsoho ya hak'ik'ance, yace, " to baba magana ay ba aguri na take ba tana gurin hjy iya sai abinda tace" ya karasa maganar yana kallan hjy iya da ta cika tayi fam.


       Hjy iya na kallan habibu tayi ta fara fad'a, " kai habibu ka fita idona na rufe ka rabani da wannan maganar mara kan gado, idan ba haka ba ranka zai baci banasan shashanci, da kuruciya ta ma ban kara wani auren ba sai yanxu da giji tazo, idan ka kuma sako ni cikin wannan maganar zan b'ata maka rai"


      " Ay dama hjy iya nafiso ne yaji ta bakinki kafin na yanke hukunci" Alh habibu ya fada.


Karaf khairat tace, " gaskiya baba tsoho ina bayan ka hjy iya ko bataso sai anyi auren nan, wayasan abinda Allah ya b'oye kila dama rabone ya fito da hjy  iya tunda dama daddy ya hanata tak'i" ta karasa maganar tana yiwa hjy iya dariya.


  Dukan wasa hjy iya ta kai mata cikin wasa tace, " ja'ira yar nema sai dai ke ki aureshi, kinsan idan nasa ubanki ya aura miki shi anyi angama ko? "


  " Cab haba hjy iya kinsan bame yuwa bane "  khairat ta fada.


  Khaleed ne ya kalli dan tsoho yace, " au ashe da abokin takarata nake tsaye bansani ba, cab lallai kace na kara zage dantse dan kuma tsofaffun nan akwai zafafan kalamai"

Gaba daya gurin aka sa dariya.


Su hjy iya sallama suka yiwa mlm musa yana ta zabga godiya da fatan sauka lafiya, mota suka shiga suka tafi motar police tana bayansu.


   Alh habibu tambayar dan tsoho ya karayi garin da yake, ba musu ya gaya masa.


Sun danyi nisa da tafiya ya zaro kudi ya mik'awa dan tsoho ya mik'awa yusuf bandir din yan dari biyar ne na dubu hamsin-hamsin, godiya suka shiga yi masa yace musu baya bukatar godiyar su.


     Hjy iya taji dadi sosai har cikin ranta, shiyasa take takara alfahari da habibu mutum ne me kyauta da tausayin talakawa, bashi da kyashi ko kadan da girman kai kamar ba shi ne yake ta dukiya haka ba, sam dukiyarsa bata sashi tak'ama da jiji da kai ko ganin yafi wasu.


Cikin zolaya hjy iya tace wa dan tsoho, " to ka zura kudi a Aljihu kuma baka kawo na toshi ba"


Dariya dan tsoho yayi ganin sun maidashi abun tsokana.


Dan karamin katinsa Alh habibu ya dauko ya mik'awa yusuf yace, " ga wannan katin idan ka koma gida ka nutsu ka neme ni, kaima baba gashi wannan dan katin da ka gani number waya ta ce aciki, duk wacce ka samu anan kauyen naku indai kun daidaita to kamun magana, ka adana shi da kyau karya b'ata"


    Yusuf jiki na rawa yasa hannu ya karba, yana ta godiya da mamakin irin karamcin Alh habibu, cikin zuciyarsa yake fadin, " lallai dan Adam daraja gareshi idan kaga mutum karka wulakantashi, bakasan baiwar da take tattare dashi ba, tunowa yayi da irin jarabar da suka dinga yiwa hjy iya da yanda driver motarsu yake fadan maganganu marasa dadi akan Alh habibu, kunya ce ta kama shi yana ganin kamar kallansa suke da abun, tabbas Alh habibu d'a ne kamar yanda hjy iya take fada.


Cikin zuciyarsa yake fadin, " lallai tsofaffi akwai rigima yanxu wannan dankwaleliyar motar me AC ta dan hjy iya ce, amma ta biyo wata motar haya kai lallai duk wanda yake tare da tsoho sai yayi hakuri da halinsu"


        Sunyi tafiya me nisa sannan akaje garin da dan tsoho zai sauka, bayan ya fito daga motar sallama yake wa hjy iya itama duk sai taji ba dadi lallai sabo akewa kuka duk sai taji zuciyarta ba dadi, jaka ta karba ta zuge ta debo kudi ta karawa dan tsoho.


Cikin damuwa dan tsoho yace, " nagode kwarai hadizatu na tabbata alkairi ne hadamu dan Allah ki yafemun ko na miki laifi cikin dan zaman da mukayi dake, nikam ba abinda kika mun idan akwai ma na yafe miki duniya da lahira, Allah sada mu da alherinsa"


     Kwallah ce ta ciko idan hjy iya tace, " na yafe maka bare ma ni ba Abinda kayi mun, karka manta ka adana dan katin da habibu ya baka zai maka amfani, Allah ya jishshemu alheri ka gaida iyalanka gaba daya"


     Duk cikin motar sai da jikin su yayi sanyi, shi kansa yusuf duk sai yaji wani iri dan sabon da sukayi na kwana biyu, sun saba ko yaushe suna tare suyi fada su shirya.


Motar AlH habibu ce ta fara tafiya dan tsoho yana d'aga musu hannu har sai da yaga kulewar motar sannan ya goge yar kwallar data zubo masa, jiki a sanyaye yaja kafa ya gangara hanyar da zata sadashi da gida.


     Jugun sukayi cikin motar ba me cewa kowa uffan, sun lura hjy iya tayi kewar dan tsoho sosai, su kansu su fatima dan zuwan su sun lura tsohon nada barkwanci da abin dariya.


Tafiya suka yi me nisa sannan suka shigo cikin gari, adaidai kurna babban layi yusuf yace zai sauka, cikin kewa yake cewa hjy iya.

    "   Iya nima dai ki yafeni kinsan zaman tare sai ka b'atawa mutum ba baka sani ba, kiyi hakuri da abubuwan da suka gabata zamana dake na dauki darasi iri-iri, nagode kwarai Alh Allah saka da alheri"


Hjy iya duk jikinta yayi sanyi tace, " haba yaron nan ni ba abinda kayi mun kasan zama da tsoho sai hakuri Allah ya yafe mana gaba daya"


Ana zuwa bakin gadar babban layi Alh habibu yayi parking yusuf ya fito, godiya yake tayiwa Alh habibu har motarsu ta wuce, ido ya zurawa motar har ta b'ace sannan ya hau gadar babban layi ya wuce gida.


A cen police station duka izaya iri-iri ba wacce ba'ayi wa su sarari ba, sun sha wuya matuka sun galabaita, ayau da safe dama kafin Alh habibu ya kira DPO har ya yanke shawarar mik'a su bompai dan ganin anbincike su daga baya bayan yaji labarin ganin hjy iya ya fasa.


Ta sharada Alh habibu ya biyo, abakin titi yayi parking motarsa ya tsallaka, bayan sun gaisa da DPO Alh habibu yasa aka fito masa da su sarari, kallan tsab Alh habibu ya yi musu cikin takaici yace.


" dan Allah ku gaya mun ribar abinda kuka tsinta acikin wadannan halaye da kuka tarkarwa kanku, ina ribar shaye-shayen naku ina kuma ribar satar da kukeyi, kufa matasa ne kuna da sauran shekaru agaba, meyasa bazaku mori kuruciyarku ta hanyar neman ilimi da neman na halak dinku ba, kuna ganin wannan hanya ce me billewa, atunaninku al'umma zasu yi alfahari daku ko kuma a addinan ce musulumci zai yi alfahari daku, duk bama wannan ba kuna ganin iyayen da suka haifeku zasuyi alfahari daku amatsayin ku na yan shaye-shaye ko masu satar kayan wani, shin ku bakwa fatan kuyi aure ku ajiye taku zuri'ar, yanxu ku zaku so adinga cewa Ay uban wance barawo ne ko ace uban wane dan maye ne, ku gaya mun tsakaninku da Allah yanxu zaku so 'yayanku su taso suga kuna cikin wadannan munanan halin?? "


Su sarari shiru sukayi duk irin tambayoyin da Alh habibu yake yi musu, sai duk jikinsu yayi sanyi sunajin ba dai-dai ba, wata tambayar ya kara jefo musu yace.


    Yanxu kuna ganin kunyiwa iyayen ku adalci kenan, duk irin dawainiyar ku da suka sha kuna yara sakayyar bakin cikin da zaku musu kenan? "


Wannan karan asanyaye suka amsa da " a'a" suna sunkuyar da kai kasa.


Alh habibu zai cigaba da magana sarkin jagwal ya katse shi yace, " Alh dan Allah ka dubemu da idanun rahama tsakanina da Allah zan gaya maka wannan maganar, wallahi nayi nadamar duk abubuwan da na aikata a baya amma wallahi-wallahi bansan inda tsohuwar nan take ba, nasan dai na dauki wayar amma wallahi ko kur'ani zan iya dafawa akan bansan inda take ba"


Murmushin takaici Alh habibu yayi sannan yace,  " ay abinda yasa na taraku kenan nake muku wadannan maganganun, angano inda take yanxu haka ma tana cikin motata, na tara ku ne ina nuna muku illar halayen da kuke aikatawa, yanxu wannan dattijuwar misali da ba'a ganta ba kuna ganin hukuma zata kyaleku koda kuwa zaku dawwama kuna rantse musu akan bakusan inda take ba, kunga da abanxa za'aje a kashe ku ko kuma kuyi ta zama a gidan yari, ko ba'a kashe ku ba aka yi muku daurin rai da rai ay anyi muku mutuwar tsaye, meye mutuwar tsaye? Anraba ku da iyayenku da yan uwanku da kowa naku baku da 'yancin kanku, tun iyayenku da 'yan uwa na ziyararku akwana atashi zasu gaji su daina, zaku mutu ba aure bare ku hayayyafa, ina me baku shawara da idan bacci kuke ku farka, ku shiga cikin hankalinku kusan me kuke ciki, ku gina rayuwarku da tubali me kwari yanxu ina amfani wayar da bata taka kara ta karya ba ta ja muku duka da kaskanci da wulakanci, yanxu da baku dauka ba mezai kawo ku gurun nan, dan Allah yarana ku tashi ku nemi na kanku domin ku amfanar da al'umma baki daya"


       Gaba daya jikinsu yayi sanyi asanyaye, sarari ya kalli Alh habibu yaba zubda kwallah yace,  " Alh nagode da irin wannan nasihohin naka Allah ya yi maka jagora, amma Alh  shekarata biyu kenan rabona da gida mahaifina ya koreni saboda shaye-shaye na da harkar da ba, ashagon abokaina nake kwana wadanda tare duk muke yan zuk'e-zuk'en da muka saba, maganar gaskiya Alh nasihar da kayi mana tasa naji duk na tsani duk wanj kayan maye ina neman wata alfarma agurinka dan girman Allah Alh" sarari ya sa gwiwoyinsa akasa ya hada hannunsa alamun rok'o.


        Tausayin yaran ne ya kara ratsa Alh habibu, ya kalli sarari yace "fadi bukatarka ina jinka Allah sa ina da ikon yi"


Sarari goge kwallar idonsa ya yi sannan yace, " dan girman Allah Alh ka taimaka ka rakani gidanmu ka sasantani da mahaifina, natabbata idan ni kadai naje kara korata zaiyi bazai fuskance ni ba, wannan ita ce alfarmar tawa" ya karasa magana yana kallan Alh habibu.


      Ajiyar zuciya Alh habibu ya sauke sannan yace,  " wannan ba komai bane insha Allahu zanje har gidanku gurin mahaifinka kamar yanda ka bukata, kuma naji dadi matukar gaske inafata zakuyi tuba na din din din ba tuban muzuru ba"


     Sarkin jagwal ne ya fara amsawa sannan yace, " nima insha Allahu  na daina yan sace-sacen da nakeyi dama gidanmu basusan inayi ba kuma nima da yardar Allah na daina, ko tsinke nagani muddin bani na ajiyeshi ba bazan taba shi ba"


    sosai Alh habibu yaji dadi har cikin zuciyarsa, yana kuma kara godiya ga Allah bisa ga silar da ya kasance na gurb'atattun mutane, suka dawo nagari.


'yan rubuce-rubuce akayi ya sallami DPO suka fito shi da su sarari, su hjy iya harsun fara gajiya, karasowa sukayi wajen motar.


Alh habibu wani me adaidaita sahu ya tsaida musu, umarni ya bawa me adaidaitan akan ya dinga binsa abaya har zuwa gida.


_BARKANMU SALLAH INA JIRAN NAMAN SALLAH._ πŸ˜‰


_Vote_

_Comments_

_Share_


      _MUM ASLAM Ce_πŸ˜‰πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

       _4/8/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

    _AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


                43&44


Yana shiga motar hjy iya ta fara cewa, " habibu wai me kaje yi ofishin yan sanda ka shafe lokaci muna cikin mota azaune muna jiranka, wadanne mutane ne naga ka fito dasu laifun me sukayi ?  "+


Murmushi yayi wa hjy iya yace, " Allah ya taimaki hjy iya mu dan karasa gida mana sai inyi miki bayani"


" To shikenan Allah ya kaimu lafiya " hjy iya ta fada.


Tafiya suke yi me adaidaita sahun yana biye dasu har sukaje unguwar gyadi-gyadi, abakin gate Alh habibu ya tsaya ya fito ya sallami me dan sahu, horn yayi megadi ya bude bayan ya shiga cikin gidan su sarari suka rufa masa baya, me gadi ya bawa umarnin akai su sarari suyi wanka kuma su basu kaya su canja, su kuma aika abasu abinci.


Iyalan gidan Alh habibu gaba daya sun hallara agidan, wannan gayawa wannan shima ya gayawa wannan, gidan cike yake da yara da manya kowa jiran karasowar hjy iya yakeyi, suna zaune a babban falo sukaji alamun shigowar motar Alh habibu, hjy iya ce ta taka ta fito daga motar kafin kace kwabo gaba daya iyalan gidan suka fito cikin murna suna ambatar sunan hjy iya, zuwa sukayi gaba daya suka zagaye ta suna ihun murna.


   Alh habibu ne ya katse su yace,  " kai kuyi mata ahankali fa kar ku kadamun tsohuwa "


Dariya suka sa lokaci daya suka ciccibeta sukayi falo da ita, hjy iya murna ce ta kamata ganin irin farin cikin da iyalan gidan habibu suke ciki, bayan sunje falo suka zaunar da hjy iya a kujera falon ya cika makil, kallansu ta farayi daya bayan daya cikin zuciyarta tana fadin, " ikon Allah kenan Allah me yanda yaso asanda yaso, kai kadai ne d'ana habibu amma dubi yanda ubangiji ya cika ka da zuri'a yanxu wadannan duk iyalaina ne ni hadiza, Inama Allah ya raya mlm yaga irin zuriyar da Habibu yake da ita, Allah sarki mlm Allah ya gafarta maka, habibu ina alfahari da kai Allah ya albarkaci zuriya" hjy iya ta karasa mgnr tana fashewa da kuka.


Gaba daya ido suna zuba mata masu tsokana sukayi masu lallashinta nayi, mami ce tace, " hjy iya dan Allah ki daina kukan nan, yanxu meye zai dameki gamu ga daddyn yara gaki cikin iyalanki dan Allah kiyi shiru, kinga daddyn yara idan ya shigo ya ganki kina kuka bazai ji dadi ba "


Share hawayenta hjy iya tayi sannan tace, " kukan farin ciki ne nakeyi dajin dadi ganin duk wannan ahalin nawa wai habibu duk shi yake da wannan iyalin "


Karaf Alh habibu ya bawa hjy iya amsa lokacin da ya zauna kusa da ita yace, " Haba hjy iyata, ay ba kuka ya kamata kiyi ba murna da farin ciki zakiyi da Allah ya ja kwananki cikin iyalanki, kin tuna lokacin da nake zuwa secondary idan zan fita me kike ce mun "


Hararar wasa hjy iya ta yiwa Alh habibu alamar yayi shiru, aykuwa su sa'adatu suka ce, " a'a dan Allah daddy gaya mana muji "


Murmushi yayi sannan yace, " kullin zan fita waje sai hjy iya ta kirani ta rike hannun tace, habibu na kaga kai kadai ne baka da wa bare kani, dan Allah habibu karka dinga tsokana aje ana cin zalinka, kaga ni ina gida ba wanda zai rama maka Allah ya raya minkai habibuna " Alh habibu ya cigaba da cewa, " idan makarantar boko zani sai hjy iya ta rakani har titi na tsallaka, kai wani lokacin ma sai taga shiga ta mota take dawowa idan kuma ranar bazata rakani ba ta dinga cewa, habibu ka kula ka lura da hanya kodai inzo inrakaka, sai ince mata, " haba iya nifa na san hanya dan Allah ki daina rakoni kina bawa kanki wahala, dubeni kamarni wai za'a dinga rakawa zuwa makaranta"


Ranar kuwa hjy iya salati tayi tace, " Au habibu kai nan gani kake ka girma ka zama saurayi, yoooo shekarun naka nawa ne kaida ko sha takwas bakayi ba, inajin sai maulidi yaxo ma zaka shiga sha shida har shine kake cewa kamar kai za'a raka, Allah na tuba habibu yaushe na daina maimaita maka aike " sai nace mata,, " a'a iya nifa ba haka nake nufi ba kawai abokai na ne suke tsokana ta wai da girmana ana rakoni " sai hjy iya tace mun, " ay sai  kace musu kai dangata ne, kai bari kaji habibu Aure kawai zakayi na daina maka rakiya idan zaka guri, a'a kujimun ja'irin yaro dududu nawa kake habibu kodan kaga kayi tsawon kafa ka fini a tsaye "


     Alh habibu yayi murmushi yana kara kallan hjy iya da ta nutsa cikin tunani, gaba daya falon sunyi tsit suna sauraron sa sannan ya cigaba da cewa, " idan kuma zani makarantar allo hjy iya har rumfar mlm me laraba take kaini  idan zata dawo sai tace mun, " kai habibu kaga kar insake kar inji kana tsokanar wadancen kolawan suxo su yi ma duka abanza bame tare ma, kaga ni na girma adoke bazan iya taba wani daga cikinsu ba, Allah ya tsaremun kai habibu kayi karatu sosai kaji Allah ya rayamun kai inga auranka da 'yayanka, wai ranar dana 'yayanka ay sai nayi rawa na juya "


Alh habibu kallan hjy iya yayi yace, " to hjy iya kinga ay ba kuka ya kamata kiyi ba tunda yau Allah ya nuna miki 'yayan habibunki harda jikoki, Allah ya barmun ke hjy iya ta " ya karasa maganar cikin jindadi.


    Murmushi hjy iya tayi tace, " Habibu kenan Allah baxai barni ba kasan dai duk me rai mammaci ne bare kuma ni da shekaru suka ja, giji ay ta taho shekarun da nayi abaya nasan ko kwatansu bazan yi ba, lallai habibu na yarda da ake cewa da haihuwar yuyuyu gwara daya kwakwkwara, tabbas habibu na nuna maka so iya so kuma kaima duk wani hakki nawa daya rataya awuyanka ka sauke shi habibu na, habibu tunda ka mallaki hankalinka  baka taba mun komai ba aduniya wanda zai b'ata mun rai na, kai ko da kamun na yafe ma duniya da lahira, Allah ya raya maka zuri'ar ka  kaima kuma Allah ya ja da kwananka cikin iyalanka" gaba daya dakin suka amsa da Aameen.


   Gaba daya jikinsu yayi sanyi da kalaman hjy iya, ganin kamar ta sanyaya musu jiki yasa ta sako musu wata maganar tace.


          " Habibu idan ka huta inasan magana da kai " Alh habibu cikin kulawa ya amsawa mahaifiyar tashi.


Su khaleed ne suka ce,  "  hhy iya dan Allah ki bamu labarin cakwakiyar da kika sha a hanya mana ko masha dariya, wai ma me ya kaiki gidan mlm musa keda kikayi kauyen rigana, fatima tace gaskiya hjy iya kin tsurar mana da ciki muna zaman zamanmu kika samu cikin zullumi, gaskiya nan gaba kika kara fita sai dai mu biki da kullin kayanki "


" Auntyn yara ce ta katse su tace, " kai duk kunci gidanku kunxo kunsa ta a gaba kuna cikata da surutun banza da wofi, ku barta taji da gajiyar tafiya man, hjy iya muje ciki kiyi wanka ki huta  " hjy iya tace, " wallahi kuwa bari na shiga daga ciki kafin anjima habibu yazo ya kaini gida  "


Bayan tafiyar hjy da kadan-kadan falon ya watse kowa ya nufi ssshen mahaifiyar sa.


_A BANGAREN 'YAN AIKI_


       Rikici ne ya dinga barkewq tsakanin su suwaiba da ladidi duk yanda taso ta dasa musu tsoronta azuciyarsu sam taga idansu abude, ba kamar su ta rasulu ba da suke gidadawa wadanda ko kara ta ajiye basu isa su tsallake ba, ganin sun zame mata karfen kafa ba yanda ta iya dasu ga kuma korar da su mami suka mata, yasa ta fara sakkowa tana neman shawo kansu da kyar.


    Ladidi duk abun duniya ya dameta su hansai sun hade mata kai, su tarasu ma da take ganin ta isa dasu suma ganin irin abinda su hansai suke mata yasa suma suka yi mata bore, domin sun lura alkadarin ladidi duk ya karye, ayanda suka lura ma ladidi ta fara shakkar su hansai, agurin inna zainabu kawai take samun sassauci itace take zama su danyi hira ta kawo mata yan matsalolinta game da abunda su suwaiba suke mata, shi ma kuma sai ta ga su hansai duk sun fita, Abinda yake kara bata mamaki da safe tana zaune ta kalli haxuma tace ta debo mata ruwan sha budar bakin hazuma tace mata bazata debo ba idan ita bata da kafa shikenan kishirwar ta kasheta, shiru tayi bata tanka mata ba ganin su hansai zaune suna watsa mata harara, danma inna zainabu tana dan tausarsu ta basu baki shiyasa suke rangwanta mata.


         A daren ranar da su mami suka ce zata tafi garinsu kwana tayi ba bacci tana sak'a da warwara, lokacin da suka tashi daga falon su mami suna komawa sashen su ladidi ta cukumu wuyansu gaba daya ta hau danna musu ashar, fisgewa sukayi suka kara rufeta da duka da kyar ta kwace tana haki ta fada d'aki, sai da inna zainabu ta shawo kansu hansai da kyar sannan suka kyale ladidi, tun daga lokacin ladidi ta koma kamar mujiya acikinsu.


    Sauki daya taji da Alh habibu yace ta wuce ciki inya dawo zai nemeta, amma tana fargabar abinda zaije kunnensa na sharrin dasu suwaiba sukayi mata.


     Hansai ce tashigo dakinsu cikin zumud'i tacewa su suwaiba, " ku nifa wani abu naji dazun nan kamar murnar dawowar hjy iya naji mutanen gidan sukeyi " da sauri inna zainabu tace, " ke hansai da gaske kike ko zolayar mu kikeyi hjy iya fa kikace "  hansai tace, " wlh inna zainabu itace, kintabajin shewa da murna tunda mukazo gidan nan, kullin gidan ba tsit yake ba kamar gidan makoki " suwaiba tace, " to munanan indai hjy iya ce zamuji labari zuwa anjima, ko kuma bari na leka gurunsu Audi kinsan sune na bakin kofa kowa ya sauka akan idonsu yake zuwa" hansai tai dariya tace, Allah  sa ba yana baccin asarar tashi har suka wuce ba"


_BAYAN AZAHAR_


Hjy iya ce zaune cikin iyalanta take basu labarin irin gararanbar rayuwar da suka sha ahanyar su ta zuwa lamba, gaba daya dakin dariya suke shekawa harda masu hawaye, ita kanta sai yanxu take dariyar irin rigingimun da suka dinga yi da yan motar.


Alh habibu ne ya shigo cikin jindadin ganin yanayin da suke ciki yace, " lallai gidan nan kuna cikin nishadi me kuke tattaunawa haka ne naji kuna ta dariya"


    Labarin hjy iya suka fara bashi shima yayi dariya sosai amma ya tausayawa mahaifiyar tasa matuka duba da yanayin shekarunta da kuma hargitsin da suka sha a hanya.


    Har ya tashi zai fita hjy iya tace zatayi magana dashi, iyayen gidan ne suka fara tashi sannan yaran suma duk suka watse suka bawa Su Hjy iya guru.


Zama yayi kusa da ita yace, " hjy iya wace magana ce dake haka"


Gyara zama hjy iya tayi tace, " magana ta farko dama gaya maka zanyi bayan magariba zaka maidani gida dan bansan wainar dasu zainabu suke toyawa ba, kuma kasan ni banasan zaman gurin sirikai"


Alh habibu yace, " Hjy iya ay su Zainabu suna cikin gidan nan bari mu gama akira miki su, kuma hjy iya mezai hana ki dan kwana biyu anan koda sati daya ne inyaso sai amaidake daga baya "


     Hjy iya cikin jindadi tace, " naji dadi kwarai da ka kawo su zainabu nan saboda nan yafi cikin jama'a amma batun inyi sati ma be taso ba yau zamu koma nida su "


Alh habibu badan yaso ba yace, " To hjy iya ta angama yau zaki koma cen din sai kuma magana ta gaba"


Hjy iya murmushi tayi tace, " Allah yayi maka albarka habibu, magana ta gaba akan wani kauye ne me suna gangaren hayi inda muka sauka kafin muje gidan musa inda ka dauko mu "


Dan jim kadan yayi sannan yace, " to me yake faruwa akauyen hjy iya "


" wani mahaukacin likita suke dashi wannan yaron banyi tunanin ko sankadire yayi ba" hjy iya tas takwashe duk abunda dafta tanimu yayi ta gayawa Alh habibu sannan ta bashi umarnin da ya aika yan sanda su kamoshi su binciki inda ya samu takardar aikin likitanci.


Mamaki ne ya kama Alh habibu jin irin tabargazar da ake tafkawa akauyen cikin girmamawa yace wa mahaifiyarsa, " insha Allah hjy iya gobe zanje garin dama akwai yaran da zan maida su gidan iyayensu daga cen sai mu wuce"

_Barkanmu da sallah_


_Vote_

_Comments_

_Share_

   _MUM ASLAM Ce_πŸ˜‰πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

       _9/8/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

    _AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


                45&46

_Kuyi hakuri da yanda kuka sameshi wlh nayi kusan rabi ya goge_πŸ˜’


Murmushi jin dadi hjy iya tayi sannan tace, "  Allah yayi maka albarka habibu sharrin makiya da mahassada Allah ya kare "


" Allahumma Aameen hjy iya ta, idan kin gama anjima sai amun magana, bari nasa aturo miki su inna zainabu" Alh habibu ya fad'a.


Be jima da fita ba sai ga su suwaiba sun shigo falon, da murna sukayi gurin hjy iya cikin so da kauna suna mata murna da zuwa, ita dinma tayi kewarsu cikin sakin fuska take tambayarsu ya yanayin zaman da suke, sun dan tab'a hira sannan suka tashi sukayi sashen su suna murna zasu koma cen gidan hjy iya.+


Bayan magriba kuwa Alh habibu da kansa ya da kwashe su gaba daya iyalan gidan hjy iya, su Audi sai yashe baki suke dama gaba daya atakure suke, bayan ya kai hjy iya gida har zai tafi ya koma ya karbo address din garin da zashi washe gari, sallama yayi mata yasa kai ya fice yana kewar hjy iya.


Su suwaiba murna harda tsalle dama gaba daya zaman cen bai musu dadi ba, saboda aikin gidan yawa gareshi ba kamar na hjy iya ba, ita matsalar hjy iya mita da sa aiki amma duk da haka sunfi san gidan hjy iya.


_Washegari_


Alh habibu ne ya shirya tsab cikin wata dakakkiyar shadda ya fito harabar gidan, su sarari yasa aka kirawo masa mota yace su shiga ba musu suka shiga shima ya shiga ya take ta suka fice daga gidan.


Kai tsaye sharada ya wuce gurin DPO , bayan sun gaisa Alh habibu ya bawa DPO labarin duk abinda hjy iya ta gaya masa da kuma address din garin.


    Yarasan ya kira masu farin kaya guda biyu ya hadashi dasu kowannen su tsuke yake cikin riga da wando ba wanda zai ce yan sanda ne,, sannan aka hadasu da motar police daya duk irin plan din da zasuyiwa dafta tanimu sun shirya tsab sallama sukayiwa DPO suka dauki hanya.


Suna tafe sannu ahankali sarari yake kwatantawa Alh habibu layin su, motarsu ce ta kutsa kai cikin unguwar miltara, akofar gidan su sarari sukayi parking Alh habibu yasa akayi masa sallama da maifin sarari, bayan ya fito gaisawa sukayi da Alh habibu cikin mutumci, sarari ne ya sunkuya har kasa yana gaida mahaifinsa, da sakin fuska mahaifin nasa ya amsa duk atunaninsa yaron  Alh ne yake gaisheshi.


Sai da sarari ya d'ago da kansa mahaifinsa na ganinsa ya fara danna masa ashar,  sarari sam baiji dadin abunda mahaifinsa yayi masa ba duk da yasan shine musababbun duk abunda yayi masa, katse shi mahaifin nashi yayi cikin zagi yace, " kai bana koreka daga gidana ba ka dawo ne ka kasheni da bakin cikinka ka cuci sauran 'ya'yana da yan uwana, ka manta me nace maka ko, ba ce maka nayi idan ka dawo mun gida ba sai na tsine maka ba, shashashan banza mara kan gado, uwarka tana nan tana zaryar asibiti saboda hawan jinin daka saka mata, ko ka dawo ne karasa ta itama, wallahi-wallahi tun muna shaida juna ka tashi ka barmun kofar gida, tunda bansan dame kazo ba wa ya sani ma ko zuwa kai da sigar mutanen kirki ku farmakemu ku halaka mu, zaka  tashi ko sai na yimaka yekuwa anyi maka dukan tsiya " mlm muttaka ya karasa maganar yana niyyar kai wa sarari duka.


Da sauri sarari ya tashi yayi bayan Alh habibu ya 'buya yana zubda kwallah.


Alh habibu cikin laluma ya farayiwa mlm muttaka magana yace, " Dan Allah idan bazaka damu ba inasan mu shiga daga ciki, akwai maganar da nake san yi da kai, saboda nan naga mutane sun dan fara sa mana ido "


Mlm muttaka amsawa Alh habibu yayi ya bada umarnin a ayi musu shinfida ashagon gaban gidansa, yana kokarin shiga shagon yana watsawa sarari harara.


Zama sukayi Alh habibu ya fara yiwa mlm muttaka magana yace, " mlm muttaka da farko dai suna na habibu, ni mazaunin cikin garin kano ne unguwar gyadi-gyadi, nazo wucewa na gamu da yaronka , yazo gurina yana neman alfarma akan intaimaka insasantashi da mahaifinsa, da farko dai gaskiya banji dadin ganin da nayi masa ba saboda yanayi ne irin na yan maye, amma naji dadi kwarai bisa tunanin da yayi, mlm muttaka yanxu babu wani batun tone-tone ya kamata mu amanta duk abubuwan da suka faru abaya, saboda yaron nan ba abinda ya boye mun tsakaninsa da mahaifansa, sannan ya nuna mun nadamar sa mlm muttaka kai mahaifinsa ne, Allah na iya jarabtarmu ta hanyoyi da dama wata kila wannan yana cikin jarrabarka, idan ka koreshi baka tunanin ya fada cikin wata rayuwar wacce tafi wannan muni, hannunka baya rub'ewa ka yar tunda yaron nan yayi nadama ya kamata ka karbeshi hannu bibbiyu, kuma ka cigaba da janshi ajiki kana nuna masa kulawa kamar sauran yaranka, ka dinga sanya shi cikin addu'a kana kara nusar dashi akan abubuwan da ya kamata"


sarari yayi mamaki kwarai yanda yaji Alh habibu ya rufa mai asiri agurin mahaifinsa.


Nannauyar ajiyar zuciya mlm mutakka ya sauke sannan yace, " Alh naji duk bayaninka na kuma fahimceka, nagode kwarai Allah saka da alheri da wannan tunarwar, lallai kam da nayi kuskure amma insha Allahu baxa'a kara karo na biyu ba, lokacin ma da hakan ta faru b'acin rai ne Allah ya kara shirya mana zuriya Aameen "


    " naji dadin wannan kalam naka Allah ya tabbatar mana da Alheri, ya kara tsare mana yaranmu bissa tafarkin sunna" cewar Alh habibu.


Sarari tsugunnawa yayi gaban mahaifin nasa ya rokeshi gafara ba musu mahaifin nasa ya yafe masa.


     Cikin jin dadi Alh habibu yace,  " to Alhamdullah Allah yayi maka albarka, sannan abu na gaba inasan zan daukeshi aiki akarkashin sabon kamfanin robobina da zan bude nan da wata biyu masu zuwa, kasan sana'a ma tana rage musu wadansu yan halayen nasu, Allah yayi mana mawafak'a Aameen "


Godiya sosai mlm muttaka yakeyi Alh habibu daga haka sukayi sallama ya debo dan abun ihsani yayi wa mlm muttaka tare da bashi number wayarsa ya kara masa sallah akaro na biyu suka tafi.


Gidan su sarkin jagwal sukaje shima sun sami mahaifinsa, cikin mutumci suka gaisa  da yanayin mamaki ya kalli sarkin jagwal yace, " harisu ina ka tafi tun shekaran jiya waccen muna nemanka ka daga mana hankali ko wayarka bama samu ? "


Zaiyi magana Alh habibu ya yi farat karbe maganar da, " mlm dahiru dama magana ce naxo maka da ita ni uban gidan abokinsa ne, akamfanina wani yaro yake aiki to sai rannan sukaxo tare akan yanasan shima ya fara aiki akamfanina, to duk zuwan da sukeyi sabani mukeyi dasu  sai aka kwatanta musu gidana acen suka sameni, nikuma inadan uxuri bansamu ganinsu ba sai bayan kwana biyu, da naji bukatarsa sai nace na amince zan daukeshi, sai yace mun dan Allah intaimaka inbashi wata shaida dazai xo gida ya nuna dan kar ayimai fada ya kwana biyu baya gida, nikuma nan hanyar garinmu ce shiyasa nace ya bari idan zan wuce sai mu taho tare insamu mahaifinsa inyi maksa bayani " Alh hsbibu yafada yana kallon mlm dahiru.


  Dan jim kadan mlm dahiru yayi yace, " to idan haka ne Alh ay sai ya kirani a waya, kasan  tashin hankalin da na shiga kuwa nida mahaifiyarsa "


" To kayi hakuri mlm dahiru amma nima na tambayeshi ya cemun wai ansace wayar tashi " cewar Alh habibu.


Godiya sosai mlm dahiru yayi masa y dauko dan katinsa ya bawa mahaifin sarkin jagwal sannan yayi musu sallama, kai tsaye suka nufi kauyen gangaren hayi gurin dafta tanimu.


Hanya suka hau sosai, tafiya sukayi me nisan gaske sannan suka karaso kauyen gangaren hayi, abakin titi suka hadu da wani dattijo yana tafiya, tambayarsa sukayi gidan me gari, ita kuma motar police din tayi parking agefen hanya, tiryen-tiryen yayi musu kwatance basu sha wata wahala ba suka karasa gidan me gari.


Mutanen kauyen gangare duk inda motar su Alh habibu ta shiga sai sun bita da idanu, wasu har sun fara yan tsegume-tsegume masu bin kwakwaf har samun motar suke bi abaya dan suga inda motar zata shiga, wasu kuwa tuni suka yanke hukunci na cewar ko Alh kansila ne ya kawo musu ziyara, wasu kuma suce ko abokan karatun dafta tanimu ne suka zo gurinsa, kai garda masu cewar ko gwamnati ce tayi aike gidan megari.


Parking Alh habibu yayi suka fito sallama suka fara kwalawa a kofar gidan me gari, saboda tun lokacin da dafta tanimu yace megari da bakinsa suna da corona shikenan mutane suka daina zaman fadar megari, ko ta kusa da gidan sa sun daina raba suna tsoron karsu kamu suma da ciwon.


    Maafe ne ya lek'o yana amsa sallamar, da mamaki afuskarsa ya kalli su Alh habibu yace,  " Alh barka da safiya "  barka ka dai yaro nan ne gidan me gari ko" cewar Alh habibu.


  " Eh nan ne, yana ciki bari namai magana " inji maahe.


Juyawa yayi cikin zuciyarsa yana mamakin zuwan wadannan 'yan birni gidansu, suna karasawa ya gayawa megari zuwan ba'kinsa, me gari shinfida yasa akayi musu asoron gidansa, yasa aka debo ruwa aka kai musu, da sallama megari ya shiga soron ya zauna yana me yi musu iso da su zauna suma, ba musu suka zauna suna gaisawa da me gari cikin mutumta juna.


      Daya daga cikin police din da suka taho me suna haruna shi ne ya fara magana, " megari dama gwamnati ce ta bullo da wani tsari na tallafawa likitoci da ma'aikatan jinya ta hanyar basu magunguna da kayan aiki, munabi gari-gari mu lissafa likitocin cikin garin mu dau sunayensu da adireshinsu idan kuma sunga da hali zasu iya binmu domin suje su karbi kayan aikinsu, sannan shi kansa me garin garin akan bashi wani tallafi da zai rabawa mutanen kauyensa, to yanxu munasan ka lissafa mana likitocin garin nan idan da halima munasan mu gana dasu muyi musu bayani yanda zasu fahimci abinda muka zo dashi "


    Ajiyar zuciya megari yayi sannan yace, " naji dadi kwarai da wannan tagomashi da ya zo mana kuma zamu baku goyan baya dari bisa dari, ehto' mudai nan gangaren hayi bamu da asibiti amma gaba kadan da garin nan akwai wani dan karamin asibiti wanda idan ta b'aci muke xuwa cen ganin manyan likitoci, amma muna likitanmu anan me suna dafta tanimu wanda wani tsohon  kansilanmu ya dauki nauyin karatunsa na likitanci, shi yake duba mu da duk abinda yake damunmu, amma kafin shi munyi wani likita dafta musa kai rayuwa kenan dafta musa likitan kwarai ne, domin yafi dafta tanimu sanin fannin lafiya wallahi watansa biyar kenan da Allah yayi masa rasuwa, sai bayan rasuwarsa ne ma dafta tanimu shima yayi kaurin suna, amma gaskiya munfi jindadin aikin dafta musa, kardai incika ku da surutu yanxu dai a dan kauyen nan likita daya muke dashi dafta tanimu " me gari ya karasa maganar yana yashe bakin cikin farin ciki.


     Gyaran murya Alh habibu yayi yace, " me gari yanxu a ina zamu samu shi wannan babban likitan naku, kasan akace da zafi kan daki karfe dan ba zama muka zo ba idan bakuyi da gaske ba to kuwa wannan tallafin zai wuce ku, dan garuruwan da zamuje suna da yawa "


    "  Ganin dafta tanimu baida wahala bari na tura yaron nan maahe ya kirawo muku shi, kayi wani zance da banji dadi ba Alh dan Allah karku sa mana rai kuzo baku aywatar mana ba " cewar megari.


    Gaba daya sai Alh habibu be ji dadi ba amma sai ya kauda maganar dan kar me gari ya fuskanci maganar shiri ce yace, " haba megari ay ba batun wasa akan abunda mukaxo muku dashi , ka tura yaron ya hanzarta "


   Maahe na fita gidansu dafta tanimu ya nufa, yana zuwa ya tarar baya nan wai yana gidansu dan asabe yaje yimasa magani, ( _Dan Asabe me amalenken shanun da ya ragewa su hjy iya hanya ya kaisu gidan megari_) da sauri maahe ya karasa yana zuwa ya tarar da feshe yan  gidan su dan asabe da ni'kakken rogo ana shirin yi musu surace da dafaffen ruwan hade-hade, maahe na shiga cikin d'oki ya sanar da dafta tanimu zuwan bak'in Alhazai, dama yana lab'e yanajin duk abinda su megari suke tattaunawa, tas ya bawa dafta tanimu labari, aykuwa basu dau lokaci ba suka yo gidan me gari, tafe suke suna sauri kamar sa tashi sama, da sallama ya shiga gurinsu Alh habibu yana sanye da dinkakkun kayan  buhu, tun daga sama suka fara kare masa kallo har kasa hakan ne yasa dafta tanimu yasha jinin jikinsa.


A sanyaye ya zauna jikinsa furu-furu duk garin goro, gaisawa sukayi suna kara kare masa kallo cikin zuciyarsu kowa da abinda yake ayyanawa.


Bayanin da sukayi wa me gari shi suka karayiwa dafta tanimu, da farko ya tsorata da ganinsu daga baya bayan yaji bayaninsu ya saki jikinsa cikin jin dadi yace musu, "  yallabai mungode kwarai da wannan abun arzikin, yanxu bari naje na sake kaya kuyi hakuri nazo muku a haka wallahi ina wani operation ne aka kirani, amma bari naje na dawo,  haruna har yace su tafi ahaka dayan ya kifta masa ido cikin hadin baki suka ce yaje ya shirya amma karya dade.


Gaba daya da ido suka bi dafta tanimu, ganin bilhakki shi ya dauki kansa amatsayin babban likita.


Megari ne ya zuba musu ido ganin haka yasa suka fito da wasy takardu acikin wani file sukace masa anan zasu dauki duk wani bayanin dafta tanimu.


Dafta tanimu be jima ba ya dawo cikin shiga ta kamala, sallama sukayiwa megari har bakin mota ya rakosu, sai da suka kammala komai sannan suka fito da ankwa suka sawa dafta tanimu, fisgewa ya shiga yi yana kokarin guduwa, cikin mota suka tura shi suka rufe.


Me gari dafe kirji yayi cikin tashin hankali da karfin hali yace, " bayin Allah ki suwaye ku dubi girman Allah da Annabi ku sako yaron nan wallahi iyayensa ba abinda suke dashi yanxu ku rasa dawa zakuyi garkuwa sai da mutanen kauye, gashi kun shafa mun bakar lamba mutanen garin nan cewa zasuyi da hadin bakina, dan Allah ku sako yaron nan " me gari ya karasa magana tana durkusawa agansu Alh habibu.


Gaba daya kofar gidan me gari ya cika da mutane, kasa-kasa kowa da abinda yake fada, Alh habibu ne ya kalli me gari da sauran yan garin ya fara yi musu bayanin musabbabun abinda ya kawo su game da dafta tanimu, ya kuma lallashe su akan su kwantar da hankalinsu domin bazasu cutar dashi ba, sunyi haka ne da gudun kar yaje yayi abunda zai halaka su, sun kuma basu labarin cewar su hjy iya ne suka sanar dasu duk abubuwan da dafta tanimu yake aykatawa.


Datfa tanimu ne ta window ya zuro kansa yana roko da magiya, " dan Allah kuyi hakuri wallahi nasan ni ba cikakken likita bane na tuba na daina duba mutane amma dan Amma dan Allah karku hadani da hukuna a birni, wallahi zan fada muku duk iya abinda na sani bayan tafiyata birni da tsohon kansila "


  Mutanen kauyen ne suka hau salallami suna mamakin dafta tanimu, su duk atunaninsu tanimu babban likita ne ashe ba abunda ya sani, gaba daya ta'ajibun dafta tanimu ya kamasu.


Cikin takaici me gari yace, " kai dai tanimu ka yaudaremu wallahi, kuma dole atafi da kai kaje ka girbi abinda ka shuka yanxu dama raina mana hankali kawai kakeyi, wato shiyasa kace ayi masa surace da ruwan tafarnuwa ashafe mana jiki da garin rogo, amma Allah wadaran naka ya lalace "


Me gari na rufe baki sukaji karar jiniyar motar yan sanda, adaidai gurunsu Alh habibu ta tsaya, aka ciro tanimu daga motar Alh habibu aka turashi motar yan sanda, dafta tanimu wannan karan harda hawaye shab'e-shab'e, suna gani motar su Alh habibu data yan sanda akayi gaba da tanimu, kowa sai kwashewa tanimu albarka yakeyi, mahaifiyarsa sai kuka takeyi tana rokon adawo mata da 'danta._nagaji wallahi shiyasa ban muku editing ba._


_Ina muku fatan Alheri koda yaushe_


_Vote_

_Comments_

_Share_


    _MUM ASLAM Ce_πŸ˜‰πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

       _17/8/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

    _AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*


                47&48


_ku karbeshi a haka ba editing_

Suna tafe a mota tanimu sai kwala ihu yake cikin kururuwa yana neman agaji, hawan su kan kwalta keda wuya ya kara kurma ihu cikin yekuwa yana bukatar ceto, daya daga cikin yan sandan ne ya buga masa tsawa cikin tsuke fuska yace, " kai rufe mana baki bamasan iskancin banza da wofi, jahilin banza kawai ni ban taba ganin dakikin likita ba sai kai, idan mukaje zakayi bayani, Allah ne ya rufa asiri da tuni ka kashe mutanen garinku wasu kuma ka nakasasu "+


Tanimu tsit yayi kamar ruwa ya cinye Shi, banda zare idanu ba abinda yakeyi bai taba dana sani arayuwarsa ba sai yau, tuno zamansa yayi abirni lokacin da suka taho shi da kansilan kauyensu da zimmar yayi karatun likitanci amma yasa san zuciya wanda gashi ya kaishi ga nadama.


Tafiya suke sosai ba wanda yake cewa  wani uffan sannu a hankali har suka iso cikin garin kano, sun danyi tafiya me nisa suka karasa police station din sharada.


     Keyar tanimu aka tasa cikin cell, DPO ne ya fito suka kara gaisawa da Alh habibu, tanimu ne ya ziro kai jikin window ya fara rokon Alh habibu, " Dan Alh ka taimaka mun wallahi na tuba bazan kuma ba zanyi muku bayanin duk abunda ya faru dani lokacin da naxo birni, amma dan Allah kumin rai karku kaini gaba wallahi ko kaza bazan kara bawa wani abu ba da sunan magani.


    Bayan Alh sun gama gaisawa da DPO sawa yayi aka fito da tanimu, tanimu ne zaune a kasa duk yayi wuri-wuri kamar wanda yayi jinyar shekara, DPO ne ya buga mai tsawa yana tambayarsa.

" kai, wanene kai meye matsayin karatunka a ina ka samu shaidar aikin likitanci, duk munaso muji daga gareka "

    Gyara zama tanimu yayi sannan yace,  " ni dai suna tanimu dahiru ni dan asalin garin gangaren hayi ne, mahaifina ya rasu tun ina karami, nayi makarantar arabi da boko, boko har primary na gama na shiga karamar sakandire, garin mu basu wani maida hankali akan karatun boko ba shiyasa ma bamu da wasu wayayyun yan boko, nima sai inshafe wata guda banje ba makarantar kuwa dama wani lokacin da kayan gida muke zuwa, alokacin da muka shiga aji biyu akaramar sakandire sai wani kansilan mu yayi shela yace,  karshen waccen shekarar da muke ciki zaisa ayi jarrabawa a makarantar mu wacce tayi dai-dai da kammala waec, amma bamu zaiyi wa ba yan babbar sakandire aji uku zaisa ayiwa, yayi alkawarin zai zabi mutum uku, acikin duk wanda ya rubuta dai-dai ya dauki nauyin karatunsu, mutum na farko shi zai karanci bangaren lafiya, na biyu ya karanci fannin tsaro na ukun kuma ya karanci bangaren koyarwa, haka akayi jarrabawa lokacin da kansilan mu ya bukaci abashi sunan wadanda sukaci jarrabawa sai aka sa suna na nine na faro, da wadansu mutum biyu hadi da nura, kanin mahaifiyata shi ne principal din makarantar kansancewar haka ne yasa mahaifiyata ta rokeshi alfarma akan yasa sunana, sun dan kai ruwa rana kafin ya amince daga baya kuma ya karbi bukatarta "


    Numfasawa tanimu yayi, Alh habibu yace " muna jinka cigaba da bayani "


     Tanimu yace,  "  akareshen shekarar gaba sai kansilanmu  ya taho damu birni ya kama mana wani shago a unguwar karkasara, duk wannan zancen da nake muku alokacin shekara ta goma sha takwas sauran abokan da mukazo dasu sun girmemun daga me ashirin da hudu sai me ashirin da biyar, mun samu wata biyu da zuwa wata rana yanka shi dade yace na shirya da wuri zai kaini makaranta, hakan kuwa akayi yazo da wuri ya kaini wata babbar makaranta wacce ake kira sch of nursing acikin Asibitin Aminu kano, duk abubuwan daya kamata yayi mun shi abunda yace mun yayi shige da fice akan komai ba abinda zanyi sai fara lecture itama idan lokacin yayi zai  gaya mun, ni dai ba baka sai inbishi da idanu babban farin ciki na da yace mun ba abinda zanyi sai zaman karatu, kanta kalmar lecture da ya bata ban ganeta ba sai da nayi wani dogon nazari sannan nafihimci inda ta dosa "


Tanimu ya cigaba da cewa,  " abokan karatuna ganin sun girmemun yasa basa shiga sabga ta kowa harkar gabansa yakeyi, suma muna nan yallabai ya nemar musu makarantun da zasu fara zuwa "

" Nura shi kaduna aka kaishi police college, yayin da hadi yasamu gurbi a sa'adatu rimi, tunda muka fara zuwa makaranta ba abinda nake fahimta, xo inkasheka da turanci bansani ba, sai dai idan malami ya shigo inzura masa ido kamar ina fahimtar Abinda yake koyarwa, ahaka har mukazo yin jarrabawa aykuwa tashin farko nasha kai muna da yawa wadanda aka kora sakamakon rashin maida hankali da bamayi, ganin irin kudin da yallabai yake bunjuma mun yasa naja bakina na tsuke bangaya masa cewar ankoreni ba duba da irin canjin rayuwar dana samu, hatta nura da muke kwana daki daya bangaya masa ba gari na wayewa zanyi wanka na shirya kamar me shirin zuwa makaranta, idan na fita saidai inta zaga gari ina yawo, ahaka ne har na dahu da wani aboki me suna  yemi, yemi ba musulmi bane amma yana dan jin hausa, haka muka cigaba da abotar mu har na fara sabo da yan gidan su duk da basa wani sakin jiki dani, sai da na shafe sama da shekara a kano yallabai baisan wainar danake toyawa ba, nayi fari nayi kiba wanda yasanni ada bazaice ni bane saboda yanda na mirje nayi kyau na kara wayewa ina shiga irinta yan birni, lokaci-lokaci nakan ziyarci garinmu idan zan taho sha tara ta azziki suke hadomun nida yallabai suce inkai wa iyalansa dake medile " cewar tanimu.


    "  Tas na kwashe komai na gayawa yemi abunda ya kawoni garin kano da halin da nake ciki na daina zuwa makaranta,  yemi wata shawara ya kawo mun da farko ban amince ba sai daga baya saboda ya nuna mun idan na koma garinmu bansan komai afannin lafiya ba zasu maidani wani sakarai ko su kyama ce ni, shawarar kuwa itace,  yace zai cewa babansa inasan koyan harkar abinda ya shafi fannin lafiya, inyaso ko wani dan kudi ne sai inbiya babansa tunda yace wata mata ma ta taba yin haka "


       Tanimu ne ya dago da kai yace yallabai dan Allah ataimaka mun da ruwan sha sai incigaba da bayani, ba musu aka mikowa tanimu pure water ya shanye sannan ya cigaba da cewa.


          " mahaifin yemi me suna victor kira na yayi na karayi masa baya ni, mutum ne me san kudin gaske, chemist gareshi yana saida magunguna cewa yayi saidai inbashi dubu hamsin sannan zan dinga zuwa shagonsa in Koyan yanda ake bada magunguna da allurai, marairai ce masa nayi da kyar muka tsaya akan dubu Ashirin da biyar, sannu a hankali haka na dinga zuwa gurin victor ina zama a chemist dinsa duk magungunan da za'a zo siya akan ido na, da haja da haka har na fara bayarwa nima sannu a hankali har yanda ake allura na fara koya "


    Kwatsam ba zato ba tsammani aka yi zabe bisa tsautsayi kansila mu beyi nasara ba, hakan ce ta fara sa tallafin da yake mana yayi

Kasa, daga baya ma yace bashi da halin da zai cigaba da daukan nauyinmu sai dai iyayenmu su cigaba da biyan kudin karatun mu, alokacin befi wata shida ya rage mu gama karatu ba "


  " nura da hadi bilhakki suke karatun su, ganin sunxo gangara yasa suka koma kauye suka saida dan abunda suke dashi suka dawo domin kamalla karatunsu, nikuwa kin komawa nayi ganin na abinci ma na neman ya gagare ni yasa ba shiri na koma kauye nace musu na kammala karatuna na aikin liktanci, murna gurun yan garinmu bata musaltuwa, bayan wani lokaci su nura suka kammala karatunsu, hadi tashi sukayi daga kauyenmu suka koma wani kauye dake bayan garinmu, nura shi kuma daukan mahaifiyarsa yayi ya koma da ita kaduna cen aka turashi a gurun aiki "inji tanimu.


" haka na dinga kwambo agarinmu ko kyakykyawar magana bana iya sakin jiki nayi da 'yan kauyen mu, yan mata kuwa haka suka dinga kawo mun kanta kowacce burinta ince ina santa, gaba daya cikin garinmu na fita zakka kallon babban likita suke mun, musamman da idan nayi magana zasuji na dan watso kalmar turanci wacce na koya daga bakin victor wadanda nakejin yana yawaita fadarsu, bani da makama ko kadan saboda banida wata sana'a da nakeyi shiyasa ma nayi tunanin saida gonar gadona tagun mahaifina ko na samu jarin da zan siyo magunguna nima na bude nawa chemist din, hakan kuwa nayi na bude chemist ajikin gidan mu cikin sa'a kasuwa ta bude mun, domin wasu ma domin suxo suyi magana dani ko kuma dan su samu damar kare mun kallo, saboda ko ahanya na hadu da mutum inyayi mun magana ko waiwaiyensa banayi, kai tsofaffun abokaina da sukaji labarin na dawo har gida suka xo mun sannu da zuwa amma nunawa nayi ma kamar dama bantaba saninsu ba, suna fara mun magana zanyi ta hada yan watsaltsalun turacina ni azuwan banajin hausa, ganin haka yasa duk kauyenmu suka fara shakkata kowa tsoron ya musawa magana ta yakeyi, amma fa duk wannan fiffikar da nakeyi koda wasa bantaba kuskuren zuwa shagon musa me chemist ba, saboda shi yayi karatu yasan me yakeyi ina ganin idan naje gurinsa zai iya kureni ko ya gano karatun bogin da nayi " tanimu ke ta zayyano wannan bayanin.


   DPO ne ya karewa tanimu kallo sannan yace, " lallai kai tanimu ka iya Drama na tabbata da zaka shiga wasan kwaikwayo sai ka zama babban jarumi, muje muna jin ka "


     Tanimu dan goge gumin fuskarsa yayi sannan ya cigaba da cewa, " ko da na bude chemist ina samun kasuwa daidai gwargwado kuma Allah ya aramun rana bantaba samun matsala ba ga duk wanda na bawa magani saboda victor yayi kokari wajen nuna mun magunguna masu kyau da saurin warkarwa, bansamu yanda nake so ba har sai da Allah ya dauki ran dr musa wato sai da dr musa ya mutu sannan naza babban likita agarin gangaren hayi, saboda daga baya wasu daga cikin yan garinmu haushina suka fara ji ganin irin girman kan da nake nuna musu, shiyasa suka daina zuwa gurina suna zuwa shagon musa likita "

  Tanimu ya cigaba da cewa, " kasuwa ta na dinga ci babu babbaka ina takun isa yanda naga dama, akan dole yan kauyen mu suka cigaba da girmamani suna kara bani babban matsayi, kaf fadin garinmu me gari ne kawai yake sani nayi ya hanani na hanu sai kuma mahaifiya ta, ana cikin haka ne wannan annobar ta shigo acikin wannan yanayin ne mukayi baki suka sauka agidan me gari, sunxo suna mura da tari nikuma naji ance alamomin corona akwai mura da tari sai sarkewae numfashi shine na jarraba hikimata ko Allah zaisa adace, kuma nayi haka ne saboda kar mutanen kauyen mu suga gazawata su daina girmami ko su rage hidimar da suke mun, tunda wasu har wanki kaya suke mun da goge takalma "


_lallai kaima tanimu ashe ka d'iga iya shegenka a gangaren hayi_ 🀣

_Wannan shafin naki ne fatima aduniyar wattpad kina ji dani ina godiya da kulawa._


_Vote_

_Comments_

_Share_

     _MUM ASLAM Ce_πŸ˜‰πŸ‘ πŸ‘ 

*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*

( _A hanyar lamba_) πŸ‘œπŸ‘œ

_19/8/2020_


*Written by*:- _Ameera Adam_

_AmeeraAdam60_

*@wattpad*


*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*

_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼


*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*

πŸ”šπŸ”šπŸ”š


49&50

Tanimu gyara zamansa yayi ya cigaba da cewa, " to akwai yan hikimomin da nayi nakesan gwada su akan bakin nan da me gari amma fir suka ki amincewa, shi kanshi me gari a yanda na fuskanta tawaye yake san yayi mun, ganin karna takura suyi saurin fuskanto ni yasa na kyale su, to bayan tafiyarsu da kwana biyu sai naji labarin dan asabe shi ya ragewa bakin nan hanya har ya kaisu gidan maigari shi ne naje dan inyi bajinta na tafi da kayayyakin aikina to shine na riski kiran ku da me gari, dan Allah ku mun rai kuyi hakuri sharrin shaidan ne "+


Ajiyar zuciya Alh habibu ya sauke yana kara karewa tanimu kallo, sannan yace , " tanimu yanxu kai duk wannan kayan haukan daka hada baka tsoron kaje d'an mutane ya mutu a hannunka, gaskiya kayi babban kuskure kuma acikin maganar nan bai kamata kace shaidan bane, tunda kaima ka sanya san zuciya alamuranka "


DPO ne ya fara magana, " Tanimu ka aikata babban kuskure kuma dole ne hukuma ta hukunta ka, yanxu idan kace kar mu kaika gaba muka sakeka mukasan abun da zaka kulla gaba, mukasan me zaka fadawa yan garinku idan ka koma, dole ne mu mika ka kotu ta yanke maka hukunci dai-dai da laifin da ka aikata, kuma zamu sanar da me garin garinku halin da ake ciki, amma idan muka sakeka mun bawa masu laifin irinka dama su yi ta aikata laifi yanda suke so, dan haka wannan izna ne ga masu shiga aikin ma'akatan da bana su ba, kai Cp sani kuxo ku maidashi kafin muyi refferral dinsu zuwa kotu " DPO ya bada umarni.


Tanimu kuka yake harda hawaye yana rokon ataimaka masa kar akaishi kotu, Alh habibu yaso ya sa baki asakeshi amma nazarin da yayi ya kamata ahukunta tanimu domin ba karamin laifi ya aikata ba, kusan wasa yayi da rayukan ai'umma.


DPO ne ya dakatar da tanimu sannan yace, " tanimu zansa ka raka yarana gidan shi wannan victor din wanda kace shi ya koya maka saida magunguna, shima bazamu barshi a baya ba sai ya fuskanci fushin hukuma " DPO na kammala yasa aka tasa keyar tanimu cikin cell aka rufe.


Sallama Alh habibu yayi masa kai tsaye gidan hajiya iya ya wuce, kamar kullin tana zaune a katafaren fallonta hannun rike da carbi tana ja, da fara'a ya karasa cikin falon har k'asa ya tsugunna ya gaida mahaifiyar tasa, cikin jindadi hjy iya take amsawa tana sa masa albarka, cikin kankanin lokaci su hansai suka cika gaban Alh habibu da kayan shaye-shaye.


Alh habibu cikin girmamawa ya fara yiwa mahaifiyarsa bayani, " hjy iya bamu dade da dawowa daga kauyen gangaren hayi ba, munje antaho dayaron nan da kika kwatanta mun shi, kuma har yayi mana bayani tas da irin tabargazar da yake aykatawa, lokacin da mukaje dama akan aikin shirmen nashi muka sameshi yanayi, gaskiya Allah ya rufa asiri hjy iya kin ceto mutanen garin nan daga cikin wani yanayi "


Hannuwa hjy iya ta d'aga sama tana fadin, " kai Alhamdulillah gaskiya naji dadi habibu da aka kamo yaron nan mara d'a'a, amma baka san wani abu ba habibu " hjy iya ta fada tana kallan Alh habibu.


Cikin kulawa Ya amsa, " sai kin fada hjy iya"


" Abu daya nake so kuyimun " inji hjy iya.


" Wane abu ne haka hjy iya, fadeshi ko mene ne " cewar Alh habibu.


" Habibu yaron nan akwai wasu abubuwa da ya hada lokacin da muna garin nan yace zai mana amfani dasu wai corona garemu, to so nake anemo su duka dan Allah shima yaron nan ayi masa haka kafin akaishi kotun, ja'ir har cewa yayi ayi mana siracen tafarnuwa da citta " inji hjy iya.


Alh habibu murmushi yayi sannan yace, " haba hjy iya ay baza'a biye ta tashi ba sai mu zama daya muda shi, kinsan kotu tafi karfin kowa zata hukuntashi dai-dai da abunda ya aikata, Allah ya kara kiyaye gaba dai amma hjy iya nan gaba ay bakya kara tafiya ke kadai ba ko " ya karasa maganar cikin zolaya.


Dariya hajiya iya tayi tace, " wane ni rufamun asiri ay dan ba kara, ko nan da shekara ne na yarda inka shirya ka kaini ko direba ya kaini amma wannan jalalar bada ni ba "


Dariya sosai Alh habibu yake wa hjy iya, sannan hjy iya ta kara cewa, " amma fa wannan ja'irin yaron so yayi ya kashe mu, yaron nan da ka dauko dashi me sun yusufa shine yayi mana dabara ya kubuto damu "


Dariya Alh habibu yakeyi sannan suka cigaba da hira daga karshe yayi mata sallama ya wuce gidansa.


Da shigarsa gida yana fitowa daga mota ladidi yaci karo da ita rakabe ajikin fulawowi, fuskarta shabe-shabe da hawaye, Tambayarta Alh habibu yayi aykuwa ta kara rushewa da kuka, umarni ya bata da ta biyoshi falo, yana tafe zungwi-zungwi ladidi na biye dashi har suka shiga kamar ko yaushe duk suna zaune a falo, suna ganin ladidi kowa ya hau watsa mata muguwar harara.


Gefe ta samu ta tsugunna, bayan duk sun yiwa Alh habibu barka da zuwa, ya fara agana, " me kuka yiwa ladidi ne naga tana cikin damuwa, wai me yake faruwaa ne acikin gidan nan jiya naji kuna wasu maganganu me kuke ciki ne? "


Mami ce ta zayyanewa Alh habibu duk abunda ya faru, jinjina kai yayi yana kallan ladidi da take ta zubda hawaye cikin kuka tace, " wallahi karya yaran nan sukaimun wallahi duk sharri ne " sai ta kara fashewa da kuka.


Numfasawa Alh habibu yayi sannan yace, " ya'isa haka banasan cece kuce haka, kudai ba kananan yara bane da zaku zauna kuna jan magana daya, ladidi dai ba yau muke tare da ita ba dan haka bai kamata tashi daya mu ce zamu yakice ta mu koreta ba, ke ladidi ki dinga iya bakinki ki kuma kama girmanki, ki dinga sanin abubuwan da zaki dinga furtawa na kashe maganar daga yanxu kar inkara jin wasu maganganu na yawo agidan nan, ku kuma kuyi hakuri komai ya wuce, ubangiji ma muna masa laifi kuma ya karbi tubanmu dan haka kowa yayi hakuri "


Sumi-sumi ladidi ta tashi kafin ta fita saida ta kara bawa su mami hakuri, bayan fitarta Alh habibu ya kallesu cikin zolaya yace, " naga duk kun tsuke fuska mana wai kishi kuke ne naga duk hankalinku ya tashi? To idan nine ma ku shirya akwai wata yarinya dana samu batafi sha biyar ba, na yaba da hankalinta zan aurota inkawota " ya karasa maganar yana kallansu dan jin me zasu fada.


Kamar hadin baki suka bashi amsa, " to Alh ka aurota mana mu meye namu aciki " suna gama maganar kowacce ta mike alamar zasu tafi.


Da dariya yace, " a'a da wasa nake muku ku dawo mu cigaba da hira, dama naga kun dau zafi da maganar ladidi ne "


Akunyace kowaccen su ta nemi guri ta zauna, suka cigaba da hira cikin nishadi.


Lokacin da ladidi ta koma sashensu su ta rasulu ta samu suna hira, cikin sakin fuska tayi musu sallama hade da barka da gida, dan tun lokacin zuwansu suwaiba kadarin ladidi ya karye har dan shakkar su tarasulu take yi, sam bata da wata power harda zata wani mulkesu.


_Washegari_


Yaran DPO ne suka shirya aka tasa keyar tanimu tiryen-tiryen har gidan victor aka kamoshi, tare aka hadasu da tanimu aka rufe, da farko victor cewa yayi baisan tanimu ba sai da yaji matsa sannan yayi wa police karin bayani.


_BAYAN WASU KWANAKI._


Duk abunda yake faruwa saida aka sanarwa da me garin gangaren hayi har ranar da za'a zauna akotu duk anyi musu bayani, hakan ce tasa megari shi da limamin garin suka kuduri niyyar zuwa suga irin hukuncin da za'a yankewa tanimu.


_RANA BATA KARYA_

Kotu ta cika makil kusan rabinta yan kauyen gangaren hayi ne, bayan gabatar da masu laifi da laifin da suka aikata Alkali ya yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara guda batare da zabin tara ba, da aiki me wahalar gaske sannan Alkali yaja kunnuwansu akan duk wanda ya kuma maimaita laifin da aka kawo su dashi zai yanke musu hukuncin me tsanani fiye da wannan, haka aka tasa keyar su tanimu mahaifiyarsa sai share kwalla take.


_BAYAN KWANA BIYU._


Yusuf ne ya shiryo takanas yaxo gidan Alh habibu, kasancewar sunyi waya da Alh habibu ya bukaci ganinsa, yusuf sakin baki da hanci yayi yana kallan yanda dukiya ta samu masauki tayi kwance agidan Alh habibu, kira yaji ana kwala masa da sauri ya karasa cikin falon baki aka kai yusuf, gaisuwar mutumci sukayi da Alh habibu, kafin wani lokaci aka cika gaban yusuf da lemukan kwali.


Alh habibu ne ya fara tambayarsa, " malam yusuf na sandai kurna itace unguwarka shin ko kanada aikin yi ?"


Yusuf cikin zakuwa yace, " ehto, sana'ar dai bunburutu nakeyi dan benci nake ajiyewa ina saro mai galan daya zuwa biyu ina saidawa, saboda nine babba agidanmu kuma mahaifina ya rasu "


" Allah ya jikansa da rahama " Alh habibu ya fada ya cigaba da cewa, " mene ne matakin karatunka ?"


" ni a diploma na tsaya banyi wani karatu me zurfi ba " inji yusuf.


Zabi biyu Alh habibu ya bashi ya kara masa jari ko ya daukeshi aiki a kamfaninsa, yusuf beyi jinkiri ba ya amince da aiki a kamfanin Alh habibu, ya shiga zabga masa addua kamar ba gobe, sun dan taba hira daga karshe sukayi sallama yusuf ya tafi gida, daka ga yanayinsa kasan yana cikin nishadi


_BAYAN WATA BIYU._


Ranar wata asabar Alh habibu yaje gaida hjy iya suna cikin hira, wata bakuwar lamba ta shigo wayarsa har ta kusa tsinkewa ya dauka da sallama.


" Assalamu alaikum "


Daga dayan bangaren aka amsa, " wa'alaikas salam habibu d'ana, kabiru ne yake magana "


Cikin rashin fahimta Alh habibu yace, " bangane waye kabiru ba baba ko akasi aka samu ne? "


" haba habibu ba wani akasi da aka samu, bari nayi maka gwari-gwari, ni ne dan tsoho da muka hadu da hadixatu a cikin mota har ka saukeni ka bani abun arziki "


Cikin sakin fuska Alh habibu yace, " baba dama kaine? Wallahi ban zata ba da naji shiru ko sau daya baka taba nema na ba, baba ya bayan saduwa "


" sai alheri habibu, ina hadizatu? Dama bugowa nayi inyi mata albishir na dai samu matar aure, rana ita yau daurin aure " inji dan tsoho.


" Masha Allahu, Allah sa ayi da mu insha Allahu zan halarci daurin auren kuwa, ay ina gidanta ma bari na bata ku gaisa "


Alh habibu mikawa hjy iya waya yayi, da farko bata fahimci waye ba sai da suka fara gaisawa ta dau muryar dan tsoho me buhu, Allah sanya alheri tayi masa kuma ta shaida masa zuwanta dan tace masa zata biyo habibu su je tare, sun dan jima suna waya hjy iya sai tsiya take yi masa awaya, daga karshe sukayi sallama.


Bayan sun gama waya, Hjy iya tacewa Alh habibu, " habibu idan zakaje daurin auren nan zan bika mu tafi inyi masa Allah sanya alheri "

" Ba damuwa hjy iya, kinga daga nan sai na kaiki rigana ki gaisa da su ko ?"


Cikin jin dadi hjy iya tace, " haka ne habibu ka kyauta Allah yayi maka albarka "

Murmushi Alh habibu yayi yace, " Aameen ya rabbi hjy iya ni bari na wuce, sai munyi waya "

Sallama sukayi Alh habibu ya tafi hjy iya ta kwalawa hansai kira, tana karasowa hjy iya ta bata umarnin da a dama mata kunun tsamiya.

Cikin zuciyar hansai tace, " to fa hjy iya andawo sarkin sa aiki, kwana biyu mun huta dai da bakya nan "


_Ranar daurin Auren dan tsoho._


Su hjy iya sun shirya tsab ita da Alh habibu sai khaleed da Ameer, kaya suka hadawa dan tsoho sha tara ta arxiki harda su kayan abinci hjy iya tasa Alh habibu ya hadawa dan tsoho dasu, tafiya sukeyi suna bin kwatancen da dan tsoho Yayi musu, sannu Ahankali har suka karasa, dan Autan dan tsoho me suna huzaifa shi yaje ya taho dasu, zuwansu keda wuya aka daura auren dan tsoho da amaryarsa mariya.


_Mariya dattijuwa ce mijinta mutuwa yayi da jimawa, taxo bikin d'an yayanta suka hadu da dan tsoho da yake yayan nata abokin dan tsoho ne_.


Dan tsoho saboda murna fashewa yayi da kuka ganin irin abun arxikin da su hjy iya suka kawo masa, yayi godiya har ya rasa kalmar da zai gode musu da ita.


Bayan sallah azahar sukayi wa dan tsoho sallama suka dauki hanyar rigana, tafiya suka yi me nisa sannan suka shiga cikin garin rigana, yan uwa da Abokan arziki sai murna suke da ganin hjy iya ina ka saka ina ka ajiye haka suka dinga yiwa hjy iya, kafin kwabo anciga gaban su hjy iya da abinciccika kala-kala.


_dama kuma ba bakwan abu bane agurin mutanen rigana, suna da karamci da karrama baki, wannan shaidar su ce._

Sai da Alh habibu yaci yayi kat sannan ya tambayi hjy iya ko kwana nawa zatayi, sati guda ta dauka da haka suka yi sallama da ita, ya dauko abun alheri ya rarrabawa dangi sannan ya shiga mota shida su khaleed suka wuce kano.


Kamar yanda hjy iya ta bukaci sati guda zatayi a rigana hakan ne ya faru, ranar da ta cika sati guda Alh habibu yasa driver ya daukeshi suka tafi rigana, sai yamma likis suka dawo suna shiga harabar gidan hjy iya taci karo da takalman mutane birjik, da mamaki ta kalli Alh habibu tace.


" Habibu kaga abunda na gani kuwa? Ji fa takalma da yawa ko yaran nan ne suka kawon ziyara ? "

" to wata kila dai hjy iya, shiga muje mu gani kila sune " Alh habibu ya fada.


Su Hjy iya na shiga falon da mamaki ta tsaya tana karewa mutanen dakin kallo, ganin dakin cike da 'ya'ya da jikokinta uwa uba harda matansa, tana kokarin yin magana suka katse da tafiπŸ‘πŸΌ suna fadin.


" _Happy brithday to uπŸ§€, happy brithday to uπŸ§€, happy brithday ! happy brithday !! happy brithday to u !!!_πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚


Manyan jikokinta maza ne suka karasa suka riko hannun hjy iya hawaye ne ya gangaro mata na farin ciki, Alh habibu ne ya yanko cake din dake falon da hannunsa yacewa hjy iya.

" hjy iya ta bude bakinki, ina miki murna da zagayowar shekara Allah ya kara girma hjy iya da jinkiri me amfani "

Ba musu hjy iya ta bude baki Alh habibu ya sa mata cake, lokaci daya suka dau ihu ana tafi hakan ne yasa hjy iya jin wani hawayen na kara kwaranyo mata, gam ta rike hannun habibu kamar wani zai kwace shi tace.


" habibu kaima Allah ya ja da kwananka cikin iyalanki kamar yanda nayi tawon rai " gaba daya dakin suka amsa da, " Aameen "


Elaf ce ta kalli hjy iya tace, " hjy iya wai kuwa kinsan mu nawa ne gaba daya 'yaya da jikokin daddy? "

Dan jim hjy iya tayi sannan tace, " ay inajin zakuyi arba'in ko? "


Dariya suka sa gaba daya sannan Elaf tace, " haba hjy iya ya zaki dinga rage mu, gaba daya 'yaya da jikoki fa mu hamsin da biyu ne (52).

Murmushin jin dadi tayi ta kalle su tace, " Allah ya albarkace ku ya raya ku, ya shirya munku bissa sunnar Annabi muhammad (S.A.W)


Gaba daya suka amsa da Aameen.


_Tammat bihamdulillah_

_Alhamdulillah Alakullihal_


_Anan na kawo karshen littafin YAWON SALLAR HJY IYA, inda nayi kuskure Allah ka yafe mun._ 🀲🏻

Post a Comment for "YAWON SALLAR HAJIYA IYA COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...