YAR RAWA COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

YAR RAWA COMPLETE

YAR RAWA COMPLETE

- - Post a Comment

 YAR RAWA COMPLETE


Sannu Tabawa, Allah zai baki lfy, da kan ki za ki reni abinda kk haifa, shi ciwo ai ba mutuwa bane" Yana fada yana share kwallar dake maqale a manyan idanun shi, shigowar yar budurwar yarinyar su da bazata wuce shekaru sha 12 ba, ne yasa Tabawa ta daga kai da kyar ta kalle ta, miqa mata hannu tai akan ta isa gareta, da kyar cikin azabar ciwo da kanta yake mata, tare da zafin da take ji a qirjin ta, wanda ji take kamar hucin garwashin wuta take fiddawa, ta fara magana, bayan yarinyar ta bata ruwan da ta debo mata," Ameenee,..... ki ji tsoron Allah a duk inda kk,.... ki ma mahaifin ki biyayya, shida abokiyar zamana,....ki kasance yarinyar kirki da kowa zai sha'awar zaman ki tashi...... ki kiyaye dokokin Allah Ameenee.... Allah zai kiyaye ki da zuri'ar ki har qarshen rayuwar ki,.... Malam ka riqe amanar yarinyar nan,...... kar ka bari a cutar mana ita...... ka saka ta tai ilimi.... domin kai mai ilimi ne....." tari ne mai qarfi ya sarqe ta, yi take ba qaqqautawa, cikin tashin hankali, Malam Muhammad ya miqe ya dakko ruwan zai bata, sai yaji diyar su Ameenee, tana kalmar shahada,mahaifiyar ta na mainaitawa, idon Ameenee na zubar da hawaye, kamar an bude famfo, Malam kasa motsi yar, ganin dagawar da girjin matar shi yai, tare da jan wani nunfashi, ta kwanta, hannun ta Ameenee ta daga, ta ga alamar ya sake, kuka ta fara can qasan maqoshin ta, mara sauti, ta farama mahaifiyar ta addu'a" Ya Rab Ya ilahy, Allah ina roqon ka ka gafarta ma mahaifiyata, ka kai rahama qabarin ta, Allah ka tada ta cikin bayin ka muminai salihai, Allah ka bata ikon amsa tambayoyin qabari," Malam Muhammad da yai mutuwar durqushe ne , kama kanshi yana juya shi, hawaye masu mugun zafi, suke fama kwarara a idon shi, amsa addu'ar diyarshi yai wadda gaba daya bai san me take cewa ba sai daga qarshe ya fahimta, qanqame matar tashi yai kamar zai maida ta cikin shi, hawaye ke zuba, cikin ranshi yana nema mata rahamar Allah, daga baya ya sake ta ya kwantar da ita, ya rufe mata ido, sannan ya lullube ta da abin rufar da ta rufa da shi, tashi yai ya fita tsakar gidan nasu, wata gambasheshiyar mata na gani tana ma yaran ta wanda suke dika maza magana,akan suyi su gama cin abinci su debo mata ruwa, turo baki suke suna su ba inda za su, ganin malam ya fito cikin tashin hankali
DOWNLOAD HERE👈

Post a Comment for "YAR RAWA COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...