WANNAN RAYUWAR CHAPTER 10 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

WANNAN RAYUWAR CHAPTER 10

WANNAN RAYUWAR CHAPTER 10

- - Post a Comment

 WANNAN RAYUWAR CHAPTER 10"Ummu ki fito me kike yi ne? Ko so kike mu rasa flight ne?"

Anty Zainab ta fada.


Ummu dake daki tace

"Anty gani nan!"

Ta fito sanye da dogowar riga yar saudi maroon kala. Wacce ta amshe ta ta kara fito da hasken fatar ta. Yadda Ummu tayi kyau fatar ta ta kara haske da taushe saboda gyara da ta samu.


Nikaf ta fara kokarin sakawa Anty Zainab tace

"Wato shi kika tsaya nema zaki makarar da mu ko?"


"Sorry Anty!"

"To ba zaki saka ba. Ai kinsan facemask zasu ce ki saka dan ki sa su tsaida mu suna magana ko? Maza ki cire malama!"


Fuska ta bata tace

"Kai Anty dan ai ta kallo na?"

"Menene dan an kalle ki to?"


"Haram dai gashi kin sa na kara kyau!"

Ta kara magana tana turo baki!

"Au haka kika ce ko?"

Tayi kwafa tayi gaba.


Ummu ta bita a baya tana turo baki. A compound suka samu su Yaya Suleiman a mota. Kan Ummu ta karaso Anty Zainab har ta shige mota.


Yaya Suleiman dake zaune kusa da driver ya juyo yana fadin

"Ya kuka dade?"


"Ga yarinyar da ta zaunar damu nan!"

Ummu ya kalla yaga yadda take turo baki ya saki murmushi yace

"Yau ina Nikaf din nata."


Dai dai zuwan Ummu ta bude mota ta shiga ta zauna.

"Wa ya taba amarya ne?"


Yaa Suleiman ya fada idon ta ne ya kawo kwalla tace

"Ba Yaya Zainab bace."


"Yaya Zainab baki kyauta ba me kikai mata."

"Wai sai ta saka nikaf sai kace wani zai kalle ta ita kadai ce mai kyau da za a kalla akan neman nikaf fa duk ta zaunar damu kuma ta fison muje ai ta magana ta cire nikaf tinda yanzu abun facemask ne ba sai ta saka ba dan Allah!"


Kai ya gyada yace

"Yi hakuri kanwata rabu da Antyn nan taki ita da zata lallabaki zaki barta shine take miki haka ko? Rabu da ita ai zata zo tana missing ne."


Driver ya tada mota suka fice suka nufi airport suna zuwa kowa ya fito. Facemask kowa ya saka sannan Ummu ta ja mayafin ta ta rufe fuskar ta ruf. A haka ta fara tafiya a hankali Yaya Suleiman ne ya kalle ta ya saki murmushi ya karasa ya kama hannun ta yai mata jagora. A haka suka shiga akai screening sannan suka wuce dan shiga. Sai da suka shiga suka zauna sannan ta sauke rufe fuskar ta bar facemask din kawai.

Suna sauka kano ma a haka ta fito tana rurufe fuska driver da yazo ya dauke su ne ya wuce dasu gidan su Yaa Suleiman dake nan kano dan in sun zo in zasu dade a gidan suke sauka.


Suna shiga ta wuce dakin ta tayi wanka sannan ta kwanta dan bacci take ji. Tana kwanciyya wayar ta ta hau kara dauka tayi taga mai kira ta saki murmushi tana fadin

"Ba zan baccin ba dai kenan."


Dagawa tayi tai sallama. Ido ta lumshe tana fadin

"Yanzu muka sauka!"


"Sannu ai nasan daman by now kun sauka shiyasa na kira naji ya kuka sauka ina fatan baki gaji ba dai ko?"

"Eh!"


STORY CONTINUES BELOW

"Masha Allah! Na kusa na dawo naga Ummu na the Apple of my eyes!"

Murmushi tayi tace

"Kullum zancen kenan Yaa Muhammad!"


"Au kada nayi kisan irin hakurin da nayi kuwa shekara nawa ba matata a kusa ai nayi hakuri Ummu kinsan wannan kwanaki bakwan da suka wuce ganin su nake kamar shekara bakwai ne am eager to see you Ummu. Bansan wane hali zan tsinci kai na ba sai kin min uzuri fa dan ba wani daga miki kafa da zanyi da fatan zaki welcoming dina a duk yadda zan zo miki?"

Shiru tayi tana lumshe ido kirjin ta na bugawa da sauri da sauri.

Kamar yasan a halin da take ciki yace

"Ummu na kenan ki kwantar da hankalin ki zan tafiyar dake a sannu kinji. But kada ki manta kome kika ga nayi miki ko ya faru saboda sonki ne i love u Ummu i really love u ba abinda nake bumata a yanzu sai naganni gani gaki."


Idon ta na a rufe in banda murmushi ba abinda takeyi. Yace

"Amman ya kamata ayi walima ko Ummu?"


"Kai Yaa Muhammad kada ka daurawa kan ka wahala dan  Allah!"

"Menene wahalar Ummu aure ne fa mukai ya kamata ayi ko da walinar ce ta godiya ga Allah ya kika gani kan mu tare ko after?"


"Yaa Muhammad duk yadda kace!"

"Shikenan zan yiwa Anty Zainab magana muji me zata ce amman gaskiya sai dai a ranar da na dawo dan a ranar nake son na tare da matata!"


Murmushi kawai tayi yace

"Uhmm ni sai naga kamar bakya daukin dawowa ta Ummu?"


Ido ta zaro tace

"Haba dai Yaa Muhammad na matsu mana nima na kasance da miji na ko shima hankalin sa ya kwanta na samar masa farin ciki na fara aikin lada nima da za a na rubuta min wanda komai nayi zan samu lada na kasance mai saka ka farin ciki da baka farin ciki da baka nustuwa. Kai a baki kafi fada Yaa Muhammad ni kuma a zuci na fika zakuwa da dawowar taka ne. Kawai dai ni ina jin kunyar kane!"


Dariya yayi yace

"Da gaske Ummu.?"

Shiru tayi tana murmushi yace

"Shikenan nagode amman wannan kunyar in muka hadu sai na zane ta."


Dariya Ummu tayi tace

"Ita kunyar?"

"Eh mana tana hanaki fadan wasu abu da zasu saka naji kamar nayi tsuntsuwa na taho wajen ki."


Murmushi tayi tace

"Ai ka kwantar da hankalin ka in muna tare zata tafi da kanta ko?"

"Wannan haka yake Ummu nah. Ina son ki da kaunar ki Ummu!"


"Nima haka Yaa Muhamamd!"

"Kema me?"


"Uhmm!"

"Ki bude baki ki fada min mana."


Shiru tayi yace

"Please queen of my heart!"

Ido ta runtse tace

"I love you!"


Wani numfashi ya sauke yace

"I love u more Ummu in barki ki huta ko?"

Shiru tayi yace

"Yanzu ki kwanta ki huta kiyi ma bacci kinji sweetheart!"


"To nagode!"

Ta fada tana kashe wayar. Ido ta lumshe tana mai murmushi ita kadai dan irin soyayya da kulawar da take samu daga Yaa Muhammad bata taba zato samun ta a gun wani da namiji ba bare kuma shi da auren yazo musu ahaka. A haka bacci ya dauke ta.

Anty Zainab ce ta shigo hannu ta rike da ledar takeaway da sukayo a hanya dan yaran sunce yunwa suke ji. Ganin tana bacci ta juya kawai ta koma wajen yaran nata.


Waya ta dauka ta kira Umma nan sukai magana duk akan tariyar Ummu. Tana gama waya kiran Muhammad ya shigo. Dauka tayi tana fadin

"Ango da kansa!"


Yai murmushi yace

"Ina yini babbar Yaya?"

"Lafiya lou ya kake?"


"Alhamdulillah kun sauka lafiya?"

"Alhamdulillah!"


"Masha Allah daman Anty akan tariyar mune!"

"Uhmm me ya faru?"


"Gani nayi yadda akai aure nan ba wani taron mutane kuma kinga Ummu dai budurwa ce ba bazawara ba nace me zai hana kan a tare ayi walima."

"Muhammad ba zaka daurawa kan ka nauyi ba."


STORY CONTINUES BELOW

"Anty ba  wani wahala!"

"To shikenan kenan idan ka dawo sai ayi washe gari ko?"

"Duk yadda kika ce Anty!"


"Gaskiya dai zaifi after one day of ur arrival kaga da dare sai a mika maka matar ka ko?"

"Godiya nake Anty!"


"Ba komai!"

"To Anty ayo min list din komai da kuke bukata dan Allah kada kuyi karancin komai ayi komai a wadace."


"To Muhammad insha Allahu."

"Ko zuwa anjima sai a turon!"


"To Muhammad!"

"Sai anjima ina yaran?"


"Suna waje suna wasa!"

"Agaishe su sai anjima!"


"Nagode!"

*

**

***

****

*****

******

*******


Suna zuwa aka amshi ta a emergency akai ciki da ita. Hajara da Hafsat ba abinda suke sai kuka dan sun tsorata ganin yadda jini ke zuba a jikin ta gashi bata numfashi ko kadan.  Shi kansa Kabir ya tsorata da ganin yanayin da take ciki.


Tin karfe uku da rabi na dare suka shiga har biyar basu ba alamun su ba karamin tsinkewa sukai ba kowa jikin sa yai sanyi. Suna zaune aka fara kiran sallah asuba ba yadda Kabir ya iya haka ya fita dan zuwa yayi sallah. A masallacin asibitin yai sallah ya jima yana addu'a Allah tashi kafadun ta. Sannan ya fito lokacin biyar da rabi har ta wuce cikin asibitin ya shiga direct.


Yana shiga suna fitowa daga dakin da aka shiga da ita. Can aka gunguro da gado aka wuce da ita wani daki Hajara tabi bayan su. Kabir da Hafsat kuma suka bi bayan babban doctor da ya shigo dasu.


Suna shiga office ya zauna ya zuba tagumi sannan ya dago yana kallon su kan yace

"Kaine mijin ta ko?"


Jikin sune yai sanyi. Doctor bai damu da rashin amsar da sukaki bashi dan ya lura suna cikin firgici yace

"Matar ka tayi bari..."


A zabure Kabir da Hafsat suka mike. Doctor yace

"Cool down ku zauna!"

Kallon Hafsat Kabir yayi sannan ya koma ya zauna itama zama tayi. Doctor yace

"kuma da na duba ta naga damuwa ita ce silar abin sannan an bata wani magani wanda bai kamata mai ciki ta sha shi ba dan haka shi yasa ta kara shiga wannan halin da ta shiga!"


Kai Kabir ya dafe zuciyar sa na bugawa da masa zafi. Hafsat kuwa in banda hawaye ba abinda yake zuba a idon ta. Doctor yace

"Yanzu ni lokaci na ya yi zan tafi amman na bar case din a wajen Doctor Fateema Umar dan da,  da rana kuka zo ita ce zatai handling case din dan ta kware a harkokin mata sosai in tazo duk abinda ya dace zata fada muku amman yanzu munyi kokari an tsaida jinin sannan an saka mata ruwa za ai mata karin jini dan haka gashi sai aje laboratory in siya za ai in kuma zaku samu mai bada dai duk in kunje shikenan. Allah bata lafiya."


Ya mike ya tattara takarfun sa sannan ya dauki waya ya kira daya daga cikin nurse din. Tana shigowa ya mika mata file din yace

"Take it to Dr Fateema's Office zan mata magana in zato zata ganshi."


Ya kalli Kabir yace

"Kayi hakuri aboki na komai zai zama dai dai sai dai dole ka bata tayi bedrest sannan yana da kyau kan ta kara daukar wani cikin ta samu hutu na lokaci mai tsawo a kalla na wata shida insha Allahu by then sai kaga anyi dace an samu zaunanne ayi hakuri haka Allah ya tsara."


Mikewa Kabir yayi ya mika masa hannu yace

"Nagode!"

Sannan suka fita shi da Hafsat. Suna fita Hafsat ta kure shi da ido tace

"Kai kayiwa Halima ciki kenan?"


A zabure ya dago yana kallon ta. Hawaye ya gani yana bin fuskar ta ta zube a kasa tana fadin

"Yaa Allah mun tuba me mukai Allah kake jarabtar mu da rayuwa haka. Yaa Allah ka yafe mana ka tsayar iya haka Yaa Allah ka shirya mu."


Ta hade kai da gwiwa durkusawa Kabir yayi yace

"Kiyi hakuri amman..."


"Amman me? Sai da ka cuce ta sannan zaka zo kana fada min wani nonsense!"

"Ki tsaya ki saurare ni."


"Bayan ka lalata mata rayuwa. Me Halima tayi maka da kai mata haka  arayuwar ta shin ta cacanci haka daga gareka yarinya karama!"

Ta fadi tana kara fashewa da kuka.


Juyawa Kabir yayi zuciyar sa na kuna abinda bai taba ba a rayuwa shine zina shi ko mata bai kulawa ko hannun mace bai taba tabawa ba amman yau shi ake kira da wanda yayi wa wata cikin shege Isma'il ya ja masa bala'i. Idon sa ya kada yai jajir

Ganin Hafsa ba zata saurare shi ba yasa ya juya ya nufi dakin da aka kwantar da Halima. Hajara ya gani zaune a gefen gadon. Shiga yayi yace

"Ya jikin nata?"


Ta dago da sauri tace

"Da sauki bacci take."


"Ok bari naje na kawo muku wani abun ko?"

"Mungide!"


Ya juya ya fita a bakin kofa suka hadu da Hafsat zata shigo. Tsayawa tayi a kofa tana kallon cikin dakin. Zuciya ta ta karaya sosai.


Yana fita ya shiga wani supermarket dogayen riguna ya kwaso musu kala bibbiyu ya daular musu sabulu, toothpaste da toothbrush sannan ya wuce ya siya musu kayan tea.


Wani resturant ya biya aka yo masa take away na breakfast har da tea ya amso musu. Ya dawo asibitin dakin da suke ya nufa. A kofar dakin ya samu Hafsat zaune ta hade kai da gwiwa. Kofar ya bude ya shiga.


Hajara ta dago yace

"Gashi nan bari naje gida nai wanka yanzu zan dawo kan doctor ta shigo."

Kai ta gyada ya juya ya fita.


Kayan ta bude taga abinda ke ciki sannan ta maida ta ajiye. Suna zaune har karfe takwas ganin bai dace zaman su da kayan bacci ba yasa Hajara ta shiga tai wanka ta fito ta sauya kaya sannan ta zauna Hafsat ce ta shigo. Hajara tace

"Anty kema ki shiga kiyi wanka ki sauya kayan nan."


"Da gida nace zani na dauko mana kaya da abinci."

"Ga Yaa Kabir ya kawo mana."


Kallon kayan tayi tace

"Banaso."


"Haba Anty saboda me?"

"Waye wannan Kabir din?"


"Abokin saurayin Yaya Halima ne!"

"What? Abokin saurayin Halima shi ina saurayin nata?"


"Nima ban sani ba amman abinda muke zarga ni dashi sun samu matsala tsakanin su."

Shiru Hadsat tayi tana nazari akan abun. Shin me ya hada su ko yana da masaniya da cikin jikin Haloma kenan. Kai ta girgiza tana fadin bari ya dawo na tambaye shi menene alakar su da Halima


Hajara ce ta dafa Hafsat tace

"Lafiya Anty?"


"Lafiya lou bari nayi wankan!"

Ta shiga tayi wanka ta fito ta saka kaya. Kadan sukaci abibcin suka zauna jimami.


*To fah! Muje zuwa dai.....*

Wajen karfe goma ta fito daga bandakin gidan senator Lawal daure take da towel ya kalle ta yace
"Wai ke dole sai kinje gida ne?"

"Kasan me zanje nayi tinda kaji na matsa zani gida akwai abinda zanyi mai mahimmanci."
"Yaushe zaki dawo dan ina son wannan karan mu fita tare dan ba zan iya missing naki ko na kwana daya ba yau ma bansan ya zanyi ba."

Murmushi ta saki tace
"Sai ka tafi gun matar ka ai!"
"Ta bani me?"

"Abinda ta saba baka."
Ta fada tana zama a gaban dressing mirrow. Bayan ta yaje ya tsaya yana fadin
"Ai kuma tin da na hadu dake ko wacce mace lami nake jin ta."

Juyowa tayi tace
"Haba?"
"Kema kin sani Farisa!"

Wani murmushi tayi tace
"Ina yawan fada maka ka saba da wasu matab domin ni ba dauwamammiya bace."

"Farisa ba zan iya barin ki wallahi!"
"Kana da aiki!"

"Ke kike ganin haka ki daure ki auren dan Allah."
"Aure Lawal?"

Kai ya gyada yana dafa kafadar ta. Yace
"A yanzu ba aure a gaba na."

"Saboda me Farisa?"
"Saboda abu biyu zuwa uku."

"Ina jin ki!"
"Kaga na daya halin ku!"

"Menene da halin mu."
Ya fada yana mikar da ita tsaye. Tace
"Da kun auri mace kun daina nuna mata soyayya sai ta zama shara a gunku sai ku fita neman wasu matan!"

"In na same ki ni wacce mace zan fita nema?"
"Hmmm Lawal kenan!"

"Da gaske nake.bayan shi sai me?"
"Ban gama tara abinda nake so na tara ba."

"Kamar?"
"Dukiya mana."

Yace
"Ki fadan ko me kike so zan baki."
Wani murmushin rainin hankali ta saki tace
"So nake nafika kudi gaba daya ma kai kan ka dan ban dauki abinda kake dashi a bakin komai ba."

"Farisa daru Baby!"
Tai murmushi yace
"Kin fi karfi na dai kenan ko?"

"Ba haka bane. Matsala daya ita ce ba zan iya auren wanda mukai *wannan rayuwar* dashi ba."
"In na tuba fa!"

"Sai gaba dai amman kasan me?"
"Sai kin fada!"

"Kai ba sona kake ba."
"Saboda me kika ce haka?"

"Saboda nasan haka ne. Kana son jiki nane kawai!"
"Haba Farisa wallahi da gaske ina son ki ba dan abinda kike dashi ba."

Wata dariyar rainin hankali tayi ta mike tace
"Hmmm ban yadda da dadin bakin ku ba Lawal!"

"Ki yadda dani Farisa ina son ki dan Allah ba dan ni'imar ki ba zan iya zama dake a ko da wane hali."
"Ina jin kalaman nan agun maza da yawa amman narasa gane na gaskiya."

"Lokaci zai zo da zai nuna hakan!"
"In yayi na tabbatar!"

"Kefa kina so na?"
Dariya tayi tace
"Ni bana son kowa yanzu tukunna amman kana daya daga cikin wadan da ke burgeni da jin zan iya rayuwa dasu."

STORY CONTINUES BELOW

"Nagode da wannan matsayin da kika bani."
Ta saka kaya ta kalle shi tace
"Ni zan tafi sai naji alert!"

Janyo ta yayi yace
"Please kada ki wuce kwana dayan wallahi i will miss you."

"Naji!"
Waya ya dauka yai danne danne sannan ya mika mata yace
"Put the amount!"

Amsa tayi ta saka ta mika masa yace
"Put the pin."
Kai ta girgiza ta mika masa wayar tace
"Saka abinka."

Ta mike ta dauki handbag din ta da trolley din ta. Ya mike ya rakota compound driver ya kira yace
"Ka kai ta gida."

"To ranka ya dade!"
Ya fada yana tafi dan fito da mota. Har bakin mota ya rakata ya bude mata kamar kar su rabu sannan ta shiga ya rufe aka fice da ita.
*
A kofar gida aka dire ta ta fito tace
"Nagode!"
Ya juya ya tafi. Gidan ta shiga da sallam. Gidan yana nan inda yake. Dakin su ta shiga ta ajiye jakar ta sannan ta fito ta shiga dakin Umma. Zaune ta same su ita da Sakina.

Dagowa sukai suna amsa sallamar ta ta shiga ta zauna tace
"Ina yini Umma?"

"Lafiya lou ya kike?"
"Alhamdulillah!"

Tafawa sukai da Sakina tana fadin
"Yaushe kika shigo gari?"
"Dazu na shigo nake tambayar ki ma Umma tace kwana biyu baki shigo ba."

"Wallahi ya kike ya kasuwanci?"
"Alhamdulillah!"

"Ina Hafsat da Halima ne?"
"Wallahi Halima ce ba lafiya tin jiya suna asibiti basu dawo ba."

"Allah bata lafiya."
"Amin!"

Ta mike tace
"Zo muje Sakina."
Mikewa tayi ta fita tabi bayan ta. A dakin su ta zauna tace
"Ya labari ne?"

"Farisa ni duniyar tsoro yanzu take bani!"
"Bangane ba kema zaki bi layin su Yaya Fauziyya ne?"

"Ba haka bane Farisa!"
"To yaya ne?"

"Hajiyar da nake jin dadi da ita itace dan take so na fa?"
"To menene jici uwa kici 'da."

Tsaki Sakina ta saki tace
"Aure fa yake so muyi!"
"What?"

"Aure nace miki!"
"Tab din Wallahi kada ki soma daga nan rayuwar ki zata lalace."

Shiru Sakina tayi Farisa tace
"Kina tsaka da jin dadin ki kike son kiyi aure wallahi kada ki soma ki kada shi kawai."

"Amman Farisa rayuwar ta fara bani tsoro fa yaci ace mu tuba muyi aure kuma kada mu mutu a haka!"
"Ke ana magana zaki kawo mana wata zancen mutuwa. Kije kiyi duk abinsa kika ga dama amman ni dai aure ba yanzu ba."

"Shikenan amman fa ki sani duniya ba mattabaciya bace kwana nawa ya rage ki tuba."
"Dan Allah Sakina ki min shiru ya isa ai kinsan na sani ko?"

"Haka ne Allah ya shirya."
Ta mike ta fita. Farisa ta bita da kallo tana fadin
"Yan yan yan !"

*
**
***
****
*****
******
*******
Yana shiga gida ya shiga wuce part din sa. Wanka kawai yayi cikin sauri ya fito ya shirya cikin wata milk kalar shadda yasa ya bade jikin sa da turare bangaren Mahiafiyar sa ya nufa.

A falo ya same ta akan sallaya har kasa ya durkusa ya gaishe ta. Ta amsa tana fadin
"Ka tashi lafiya? Jiya baka dawo da wuri ba sannan ka fice tsakar dare yanzu kuma naga ka shirya ina zaka meke faruwa ne?"

Kai ya sosa yace
"Mami wallahi yariyar da nake so ce bata da lafiya! Jiya da dare da na fita kira na akai akace bata da lafiya shine na kai ta asibiti acan muka kwana yanzu ma suna can nazo nai wanka ne na koma!"

"Ya salam amman shine baka fada min ba. To Allah sauwake in ba a sallame su ba anjima zan saka Arfat ya kawo ni."
"To Mami nagode. Bari naje!"

"Amman ai kaci abinci ko?"
Kai ya sosa. Hajiya tace
"Ka daure kasha ko tea ne ai ba ka zauna haka ba."

STORY CONTINUES BELOW

Tea ya sha ya dan ci bread sannan yai mata sallama tai masa addu'a ya tafi yana jin sauki a ransa. Hajiya kuwa yana fita ta rike haba tana fadin
"Daman Kabir na da budurwa Alhamduliah. Allah tabbatar da alheri."

*
Yana fita asibitin ya nufa ya shiga dakin da aka kwantar da Halima ya samu Hafsat da Hajara suna zaune. Hajara na ganin sa ta mike yace
"Ya me jikin?"

"Da sauki!"
"Doctor tazo?"

"A'ah!"
Agogon hannun sa ya kalla yaga karfe tara har da kwata. Zai magana aka yi knocking bude kofa tayi ta shigo sanye take da doguwar riga ta less tayi rolling kanta da mayafi purple kalar kayan jikin ta sai bakin takalmi da ta saka. Yarinya ce ba wata babba ba amman sai ilimi. Nurses ne guda biyu a bayan ta.

"Sannun ku!"
"Yauwah!"
Kabir ya fada.

Tace
"Nice Doctor Fateema da zan amshi case din Halima wanda Doctor Auwal ya bani shi." (Dr Fateema Umar mai Umar Specialist Clinic USC ta cikin littafin WA NAKE SO?)
Murmushi Kabir yayi yace
"Gosiya muke!"

Ta kalle au tace
"Zaku bamu waje!"
"Ok!"
Kanir ya fada suka fice. Ta karasa wajen gadon ta farai mata aune aune.

*
Suna fita Hafsat ta kalli Kabir tace
"Ina son ganin ka please!
Ta fita. Bin bayan ta yayi a compound din asibitin suka tsaya. Tace
" ka fadan gaskiya waye kai?"

"Bangane ba?"
"Kai ne wanda yayi wa Halima ciki ko kuwa?"
Shiru yayi can yace
"Halima ba budurwa ta bace tayaya zan mata ciki!"

Ajiyar zuciya ta saki tace
"To menene hadin ka da ita?"
"Saurayin tane aboki na!

" kenan shi yai mata cikin?"
"Ni ban sani ba!"

"Please Kabir kar ka raina hankali kasan kome in ba dan haka ba saboda me zaka tsaya akan ta."
Shiru yayi sannan yace
"Isma'il aboki nane kawai."

"Shine kake tsaye akan budurwar sa shi yana ina?"
Shiru yayi can yace
"A gaskiya na fada miki Isma'il abokina shine saurayin Halima sai dai Halima tin farkon gani na da ita na fara son ta. A gaskiya ban san cikin waye ya zube ba amman ni ba ciki na bane dan Halima bata san ma ina son ta ba. Amman in ta tashi ita sai muji na waye."

"Ban gane wannan bayanin naka ba!"
Nan ya fara fada mata tin farkon haduwar su da yadda Isma'il ya shige mata sam bata fada masa komai akan halaiyar Isma'il ba. Shiru tayi tace
"Kayi hakuri na dauki hakkin ka dazu."

"Ba komai kowa ma abinda zai yi kenan in haka ta faru."
"Yanzu ina Isma'il din?"

"Baya gari ne amman ina jin yau zai dawo!"
"Ok! Mu koma ciki!"
Tabi bayan sa.

A inda suka bar Hajara anan suka dawo suka sameta. Basu jima ba Doctor Fateema ta fito ta kalli Kabir tace
"Bismillah"

Shiga yayi ta  kalle sa tace
"Zamuyi mata wankin ciki ne insha Allahu komai zai dai dai ta muna son muji yaddar ka."

"Ba matsala Allah bada sa'a."
"Amin! Shikenan!"
Fita yayi ya koma gun su Hafsat yace
"Wankin cikk zasuyi mata sai batun karin jinin zani laboratory in nawa yayi dai dai shikenan in bai ba sai a siya mata."

"Mugode Kabir Allah saka."
Kofar dakin aka bude Dr Fateema ta fito tare da nurses suna tura gadon da Halima take kai.

Bayan su suka bi wani daki aka shiga da ita sannan Dr Fateema ta aiko wata nurse zuwa tayi ta kalli Kabir tace
"Wai tace aje a kawo jinin da aka bukata."

"Insha Allahu!"
Ya juya zai tafi Hafsat tabi bayan su. Suna zuwa aka dibi nasa da na Hafsat aka auna sai akai dace na sa yayi dai dai da nata nan aka kwantar dashi aka dibi leda biyu.
*
Yana kwancen wayar sa ta dau kara dauka yayi ya duba Isma'il ne dauka yayi yace
"Ya akai ne?"

"Kana ina?"
"Ina asibiti!"

"Wane asibitin waye ba lafiya."
"Umar specialist clinic!"

"Gani nan!"
Ya kashe wayar. Yana kwance bayan thirty minutes ya mike yace
"Ai zan iya tafiya ko?"

"Eh!"
Fita yayi ya samu Hafsat zata shigo yace
"An gama?"

Kai ta gyada tace
"An maida ita daki ana kara mata jinin!"

"Masha Allah. "
"Doctor tace kaje!"

"Ok!"
Ya fada yana fita. yana fita compound din asibitin zai tafi wajen Dr Fateema kenan ya hangi Isma'il yayi parking tsayawa yayi ya fito ya fara kiran sa.
"Ka ganni nan!"

Ya fada masa yayi gaba. Bayan sa yabi yana fadin
"Me ya kawo ka asibiti ne?"
Office din Dr Fateema ya tambaya aka nuna masa suka shiga tare da sallama.

Tana zaune ta amsa musu shiga sukai ta basu waje suka zaune. Kallon Kabir tayi tace
"Alhamdulillah an gama komai yanzu sai shawarwari da zan baka akan kula da ita. Kaga nata sanadin yana da nasaba da rashin kula kamar dan tana tare da damuwa sai maganin da tasha ya kawo mata matsalar dan haka dole a kiyaye ana rage mata damuwar da take tare da ita dan jinin ta ya hau sosai bayan nan dole ka daga mata kafa ta dan huta sannan kan ta samu wani cikin yana da kyau ta dauki a kalla 6month dan ta samu ta warware garkuwa jikin ta ta dawo Allah bata lafiya. Ga bill din nan!"

Amsa yayi yace
"Nagode Doctor!"
"Ba komai Allah bata lafiya."

Mikewa Kabir yayi isma'il ya bi bayan sa yace
"Waye ba lafiya ne?"
"Wata ce."

Kudin yaje ya biya kusan dubu hamsin da biyar sannan ya wuce zai tafi dakin da aka kwantar da Halima. Isma'il yace
"Wai ka tsaya muyi magana mana."

Kudin yaje ya biya kusan dubu hamsin da biyar sannan ya wuce zai tafi dakin da aka kwantar da Halima. Isma'il yace
"Wai ka tsaya muyi magana mana."
Tsayawa yayi yace
"Menene?"
"Akan Waccar yariyar mana!"

"Wa fa?"
"Wacce na hada ku!"

"Oh Sadiya?"
"Sunan ta kenan!"

"Yes!"
Kabir ya bashi amsa. Isma'il
"Wow nice name."
"Eh mijin Halima da Sadiya ba!"

Fuska ya dan bata yace
"Ya kukai?"
"Uhmm nothing mun gaisa ne kawai. Isma'il Halima fa ba lafiya!"

"Allah sauwake!"
Kallon sa Kabir yayi yace
"Kamar ya Allah sauwake. Ko da yake Amin sai me kuma?"

"Shikenan me zan mata ni na daura mata ciwon!"
"Isma'il kasan ba zan shige maka batun auren Sadiya ba sai ka fara auren Halima!"

"Akan me?"
"Saboda ita ya cancanta ka fara aura."

"To uba na."
"Me...?"

"Eh nace to uba na!"
"Me kake nufi?"

"Abinda nace ka sani wallahi baka isa ka sa na auri Halima ba dan yanzu bana son ta."
"What?"

"Eh bana son Halima ba zan aure ta ba Sadiya nake so!"
Wani murmushi Kabir yayi yace
"No wonder! Mu shiga daga ciki na kai magunguna nan!"

Wani kallo yaiwa Kabir sannan yabi bayan sa suka shiga dakin. Yana ganin Hajara yaji jinin jikin sa ya tsinke. Kabir ya mika mata ledar maganin yace
"Ya jikin nata?"

"Da sauki."
Wajen gadon ya karasa ya ganta tana bacci kana gani kasan ba baccin dadi take ba. Duk ta rame.
"Ina yini Yaa Isma'il?"

"Lafiya lou ya kike?"
"Alhamdulillah kaga Anty Halima ba lafiya ko?"

"Allah sauwake ai ban sani ba me yake damun ta?"
"Nima ban sani ba"

Kai Kabir girgiza kawai ya dago daga kallon Halima dai dai fitowar Hafsa ta fito daga toilet kenan tace
"A'ah har ka dawo Kabir?"

"Eh! Ya jikin nata?"
"Da sauki me tace maka?"

"Bill ne daman sai jan hankali akan kula da lafiyar ta da rage mata damuwa sannan a kula da kalar maganin da zata na sha."
Yai dan murmushi yace
"Sai batun bedrest da suke ta bayar wa wai a barta kar ta kara samun wani har sai na da six month."

Itama murmushin Hafsat tayi tace
"Allah sarki. Allah bata lafiya angode nawa ne bill din?"

"An biya ai ayi ta addu'a Allah bata lafiya kawai."
"Insha Alahu amman Kabir ai dawainiyyar tai yawa."

"Ba komai."
Wayar sa ce tai kara ya dauka ba tare da ya lura da mai kiran ba. Tace
"Assalamu alaikum!"

"Wa'ailkun salam wacece?"
"Sadiya ce!"

"Sadiya kuma?"
Tace
"Wacce muka hadu jiya!"

"Oh Sadiya ya kike ya gida?"
"Alhamsulillah ya kake?"

STORY CONTINUES BELOW

"Lafiya Alhamdulillah. Nace kana ina ka zo mu hadu a inda muka hadu jiya!"
Kai ya shafa yace
"Ayyah wallahi kinga ina asibiti!"

"Ya salam me yake damun ka?"
"No bani bane!"

"Ayyah wacece?"
" kanwata ce."

"Allah bata lafiya wane asibitin ne inzo in dubata."
"US Clinic!"

"Ok shikenan ai mata sannu!"
Ta kashe wayar. Kallon Hafsat yayi yace
"Wannan ne Isma'il."
Ya kalle ta yai kasa da kai yace
"Ina yini ya mai jikin?"

"Da sauki!"
"Allah sauwake"

"Ameen ashe ka dawo ai dazu yake fada min baka gari."
Kallon Kabir yayi ya shafa kai yace
"Eh wallahi."

"Angode Allah ya bada lada."
"Amin."
Kansa ne ya daure yaja hannun Kabir suka fita.

A bakin kofar dakin ya tsaya yace
"Wai me yake faruwa ne?"
Wani kallo Kabir yai masa yace
"Isma'il meyasa kayiwa Halima haka?"

"Me nai mata?"
"Na tabbata cikin ka ne a jikin ta!

"What?"
"Eh! Kar ka rainan wayo waye yake mu'amala da ita wa take kulawa bayan kai?

"Ba wani nan ni zatayiwa sharri ta makala min ciki?"
Wani kallo Kabir ya watsa masa yasa
"Kar fa ka rainan hankali Isma'il nasan waye kai nasan me zaka aikata nasan wanda ba zaka aikata ba wannan ciki na kane ni nasan da wuya ka rabu da halima tinda ka santa nasan da wuya kuma illai shine dan ka gama morar ta kake son ka rainan hankali kace zaka aure su ita da Sadiya ni nasan karya kake so kake na hada ka da sadiya ka samu ka cika burin ka to kasani in har ina numfashi ba zaka taba auren sadiya ba. Sadiya tafi karfin ka ba ajin ka bace wallahi ba zaka aure ta ba."

Idon Isma'il ne yai ja ya ture Kabir yace
"Me?"

"Eh kaji me na fada maka ai. Kuma sai ka auri Halima!"
Wata dariya ya saki yace
"To uba na wallahi sai na auri Sadiya kuma ba wanda ya isa yasa na auri Halima in ma ciki na gareta dole nai mata kome. Kasan ni ai kamar yadda ka fada kana tinanin zan auri wacce na gama sani awaje ne never wallahi sabuwa dal zan dauka a leda kuma Sadiya da kake fada kana tsaye kana kallo zan aure ta sai dai ka mutu!"

Ya juya zai tafi ya dawo yace
"In ka isa ka hanani auren Sadiya sannan in ka cika mai tausayi da taimako a auri Halima!"

*
**
***
****
*****
******
"Baby baby!"
Ido ta bude a hankali. Ya shafa fuskar ya yace
"Asuba fa tayi!"

Mika tayi yabi krjin ta da kallo wanda ta bankaro su garin yin mika. Batai aune ba sai jin Muhammad tayi ya rumgumo ta. Kan ta ta kwantar a jikin sa tana dan lumshe idanun ta.
Kanta ya shafa yace
"Kada mu makara sallah fa."
Daga shi tayi ya mike ya fita ya daura alwala ya dawo ya kamata suka fita sai da tayi alwala ta koma daki sannan ya tafi massalaci.

Tana idar da sallah tai azhkar sannan ta haye kan gado kan kace mene bacci ya dauke ta. Karfe shida ya shivo gidan. Dakin su ya shigo ya same ta kwance tayi dai dai tana baccin ta hankali kwance. Ji yai wani abu ya tayar masa bama ganin cibyar ta da yayi a waje.

Kan gadon ya nufa ya kwanta agefen ta. Hannu ya saka akan cinyar ta yana mata tafiyar tsutsa. Hannun ta ta saka ta ture hannun sa tana gyara kwanciyya. Ido ya lumshe yana jin wata bukatar ta na taso masa.

Hannun sa ya daura akan kirjin ta yana wasa dashi. Taushin kirjin ta yasa har wani lumshe ido yake bacci take sosai amman jin abu na mata dadi sai kara bankare masa takeyi wanda shi kuna ya samu damar yin abinda yake so. Bakin sa ya saka yana sucking kirjin ta. Wani yarr taji a take ta bude ido.

Ganin abun da yake faruwa yai bala'in tsorata ta da daga mata hankali jikin ta ta fara janyewa amman ina Muhammad ya tashi sam bai gane me take yi in ban da laluben ta babu abinda yake yi duk yadda take ture shi yaki sakin ta rokar sa ta farayi amman sai ya hafr bakin su ma dan tai masa shiru.

STORY CONTINUES BELOW

Tana ji ya a sarrafata tana jin a daura hannu akan pant din ta ta zare bakin ta daga nashi da sauri ta sakar masa kuka mai karfi a take ya ji ya dawo hayyacin sa amman kuma yadda yake jin sa a matukar bukace yasa ya fara lallashin ta dan ya samu ya cika burin sa. Amman ina Fauziyya ba abinda take sai kuka jikin ta kuwa sai rawa yake.

Ganin ta firgita yasa ya rumgume ta kawai yana lallashin ta. Shiru tayi kamar mai bacci can ta zare jikin ta daga nashi ta mike ta fita. Falo ta koma ta zauna ta hade kai da gwiwa tana kuka ba kukan komai take ba sai na tunani lokacin da Muhammad zai tara da ita bata san wane irin kalubale zata fuskanta ba duk da tasan yasan ita ba virgin bace amman tana tsoron kar abin ya buge shi.
Kuka take sosai tana mai fadin
"Na cuci kaina na cuci kaina. Mama kin cuce mu."

Muhammad yana kwance sai da ya samu nutsuwa sannan ya mike a hankali ya fito falo yana ganin ta a durkushe tana kuka ya karasa wajen ta yana fadin
"Subhanallah me ya faru Baby?"

Jikin sa ta fada taba fadin
"Ka yafe min miji dan Allah ka yafen na kasa biya maka bujatar ka ka yafen kada mala iku suyi ta tsine min!"

Bayan ta yake shafawa a hankali yana fadin
"Haba Baby na na yafe miki dan Allah ki daina kuka ki sani ni ban rike ki ba kuma ba zaki tabai min laifi ba duk abinda zaki min na yafe miki kinji ki daina kukan nan!"

Kai ta gyada na ya dinga lallashin ta daga nan kuma suka fara yar soyayyar su. Tare suka gyara gida sannan suka shiga kitchen ta kalle shi tace
"Me zan dafa maka?"

"Kome kika dafa min ina so Baby na."
Dankali ta diba ta fara ferayewa ya dauki wuka yana taya ta suka gama ta soya tayi musu source din egg sannan ta dafa ruwan tea.
Wanka sukayi a tare suka fito suka shirya kowa yai kwalliya yana daukar kamshi. A falon su suka zauna suka karya bayan sun gama suka zauna hira.

Karfe daya da rabi ya tafi masallaci yai sallah yana dawowa ya dauko mata hijab har kasa ya bata ta saka suka fita ya rufe gidan.

"Ina son na kai ki ki shakata amman ban da kudi mai yawa duk inda na kai ki zaki so shi?"
"Me zai hana miji na."

Gidan zoo suka shiga nana suka zaga sai da suka zaga sosai yaga mai yoghurt ya siya mata da cake taci haka suka dade suna zagawa da suka gaji suka samu waje suka zauna. Har akai la'asar sukai sallah sannan suka cigaba daga inda suka tsaya. Sai karfe shida suka fito daga wajen.

Gida sukayo suna shiga ana kiran sallah dan haka ya fice itana sallah tayi bata tashi a gun ba sai da akai isha'i ta mike tayi. Tana idarwa ta shiga tai wanka ta fito ta shirya cikin wasu english wear da ya siyo mata masu kyau.
Wandon tie ne three quarter sai rigar wacce a sauka kan hips din ta tai mata kyau kayan fari da pink ne tagyara kanta ta fakashi ta feshe jikin ta da turare masu dadi zaman jiran sa ta zauna.

Karfe takwas ya shigo gidan ya saka sakata tana jin sa ta fito daga daki da sauri ta karasa tana tafiya mai kyau da daujar hankalin sa. Tsayawa yayi ya kasa koda motsi tana karasaaa ya bude hannun sa ta fada jikin sa rumgume ta yayi ya daga ta yana juyi da ita. Tare da kissing dinta.

Da kyar ya dire ta ta dauki lear da ya jefar suka shiga daki ruwan wanka ta hada masa ya shiga yayi yana fitowa ya shirya cikin wani threequater da riga armless yai kyau yana ta zuba kamshi.

Anan falo suka baje ya bude musu ledar da ya shigo da ita nama ne a ciki sai gurasa da lemo su sukaci suka koshi.

Baki suka wanke suka koma daki suka hau gado Kwanciyya yayi ta haye kan sa. Nan ta kwanta a kirjin sa yana wasa da gashin kanta. Dago ta yayi ya rumgume ya dago habar ta ya fara kissing bakin ta itama.kissing nasa back ta fara daga haka ya fara romancing nata sosai tama tana biye masa. Sun jima suna yi sannan ya haye kanta ya kamkameta har sai da yayi releasing sannan ya sasaauta rikon da yai mata. Ita kuma tayi likimo a jikin sa domin itama ba karamin bujatar sa take ba tana tsoro ne kawai amman da yau ta nunawa Muhammad Soyayya uar gaske.

Sai da ya samu nutsuwa sannan ya dago kanta yana kallon ta yace
"Baby!"

A hankali ta bude idon ta da yake cike da bukata da muradin mijin ta. Sannan ta mai da idon ta rufe.
"Baby na menene?"

Shiru tayi yace
"Are you ok?"
Kai ta girgiza yace
"To fada me kike so me zan miki!"

Mika tayi ta farai masa magana a kunne tana yi tana jan nunfashi kamar wacce taci yaji tace
"Uhm uhmm i need you but ina tsoro ni dai kai min abu mai dadi kawai!"

Ta fadi tana kamkame shi. Murmushi ya saki ya zare mata riga sannan ya zare mata tie din jikin ta. Kissing nata ya fara yana lasar ta tin daga kafar ta har fuskar ta wanda abinda yake mata ba karamin rudata yake ba...........

Haka ya cigaba da bata caji har sai da ya gama burkitata ta haukace masa sannan ya fara sauko da ita da kansa. Bai bar ta ba har sai da ta gamsu itama tayi releasing ta kuwa kamkameshi kamar zata koma jikin sa.
Sai da yaji ta sassauta rikon ya lashi kunnen ta yace
"How did you feel Baby?"

A kunnen sa ta fara magana ciki murya mai dadi wacce take cike da farin ciki da gamsuwa tace
"Nagode Mijina ina kaunar ka hakika kai ma kana so na Allah ya barmu tare!"

Bakin ta ya tsotsa yace
"Amin Baby na. Allah nuna lokacin da zan nuna miki yadda kike da matsayi kuma nake son ki."

"Wane so zakai nunan bayan wannan kalli fa..."
Ya dora bakin sa akan nata ya tsotsa yace
"Wallahi ba ai komai ba Baby na. I love u."

Rumgume shi taui tace
"Love u more."
Wanka sukayo suka dawo suka kwanta rumgume da junan su a haka bacci mai dadi ya dauke su.

Ya juya zai tafi. Sadiya ya hango ta shigo asibitin sanye da riga da siket yan kanti  maroon kala tayi rolling kan ta da karamin bakin mayafi hannun ta rike da bakar jaka da bakin hill cover shoe tayi kyau tana tafe kamar ba zata taka kasa ba. Hannun ta rike da waya tana dannawa sannan ta kara a kunne.

Tsayawa kallon ta yayi ta kara wayar a kunne tana fadin
"Hello gani a reception din ina zanyo!"

Dagowa Kabir yayi yace
"Gani nan ina wajen nima."
Ya katse wayar ya karasa wajen ta. Tana ganin sa ta saki murmushi tana fadin
"Kabir ya me jikin?"

"Da sauki!"
"Allah kara sauki!"

"Amin muje ko?"
"Ok!"

Mutuwar tsaye Isma'il yayi a wajen to me hakan yake nufi kenan a ina Kabir yasan ta har suka saba haka anya kuwa yarinyar ce. Ido ya murje ya kara kallon ta ita ce dai dan haka sai ya koma ya zaune ya dafe kai. Can kuma yai murmushi yace
"Shiyasa yake cika baki ba zan aure ta ba. Lallai har yanzu Kabir baka san waye Isma'il ba mu zuba muga."

Ya mike sai kuma ya juyo ya gansu sun sha kwanar dakin da aka kwantar da Halima juyawa yayi yabi bayan su. Suna shiga dakin suka tadda Halima ta farka da sauri Sadiya ta karasa ta dago ta tana fadin
"Sannu!"

Ido ta lumshe ta gyara mata zama sannan tace
"Since when take kwance!"

"Tin jiya sai yanzu ta farka bari a kira Doctor!"
Hafsat ta fada ta fita. Sadiya tace
"Wanka ya kamata tayi sannan a bata abu mai dumi but bari doctor tazo."

Isma'il na tsaye ta window yana kallon ta. Ba a jima ba sai ga Hafsat da nurse dayar kuma ta tafi kiran Fateema. Dubata Nurse din tayi tace
"Ai naga komai ba is normal!"

Dai dai shigowar Dr Fateema kenan ta dubata taga ba matsala sannan tace
"Alhamdulillah a taimaka mata ta gasa jikin ta abata abu mai dumi taci sannan tasha magani Allah bata lafiya."

"Amin!"
Ta juya zata fita Sadiya tace
"Dr Fateema!"

Juyowa tayi ta tsaya tana kallon ta. Sadiya tace
"Baki sanni ba amman ni nasan ki kuma ina jin program naki am Dr Sadiya Muhammad a staff at Aminu Kano teaching hospital!"

Murmushi Fateema ta saki tace
"Nice to meet you ya aiki?"
"Alhamdulillah!"

Suka fita a tare suna dan tattaunawa akan aikin su. Sadiya tace
"Asibitin nan ya burge ni ko na dawo nan ne?"

"Zaki iya aiki a under private bayan kina karkashin federal!"
"Menene ai mu burin mu, mu taimakawa marasa lafiya ba kudun da zamu samu ba."

"Gaskiya ne wannan shine buri mai kyau ga dan kasa na gari."
Har office suka shiga suna tattaunawa akan aiki a haka sukai sallama bayan sunyi musayar number dan har Sadiya tace
"Zatana zuwa tana helping nasu kyauta voluntary."

Fateema tai godiya sannan suka rabu tafi tayi dan komawa dakin da Halima take. A hanya ta hadu da Isma'il yace
"Yan mata!"

Bata juyo ba kara bin ta yayi batai aune ba taga ya sha gabanta hannu ta daga ta zuba masa mari dai dai fitowar Kabir da Hafsat zai mai da ta gida. Ta nuna sa da yatsa tace
"Mind your business na maka kala da banzan yan matan nan ne? Matsan a hanya."

STORY CONTINUES BELOW

Da sauri Kabir ya karaso yana fadin
"Lafiya?"
Kallon sa tayi tace
"Sai wani bina yake sai kace wata yar iska."

"Haba Sadiya dan ya biki kuma shine ya zama an mai daki yar iska?"
"Hmmm Kabir kenan kasan me yake ce min wai yan mata ji wani kira fa. Mtszz!"

Ta saki tsaki ta wuce ciki kawai.
"Sorry!"
Yacewa Isma'il sannan yace
"Muje!"

Hafsat tabi bayan sa. Waya ya zaro ya fara kira Sadiya dauka tayi yace
"Cool Down Halimatus Sadiya haba baki kala da masu saurin fushi ba kiyi hakuri na fita zan mika Yayar Halima gida amman yanzu zan dawo in kuma kin tafi ne shikenan nagode!"

Ya kashe wayar. Wayar ta ajiye ta amshi cup din hannun Hajara ta fara bata tea din. Kadan ta sha ta bata magani ta gyara mata kwanciyya tana kwanciyya bacci ya dauke ta.
*
Isma'il kuwa cikin mamaki da kaduwa ya tsaya kallon duk abinda ya faru dan ba karamin daurewa kan sa yayi ba yau macece ta mare shi. Abinda ya kara bashi haushi agaban mutane da Kabir kuma ma wai Kabir ne ya bata hakuri. Baki ya cije ya fice a wajen kawai.

*
Yana dire Hafsat yace
"Ina jirannki!"
"Ba zan bata maka lokaci ba."

"Eh ba matsala!"
"Shikenan!"

Ta shiga ciki. Wayar sa ce ta dau kara yana dubawa yaga Mami ce dauka yayi yace
"Hello Mami!"

Tace
"Kana asibitin ne?"
"Eh amman na fita yanzu zan koma!"

"Ok muma gamu nan zuwa!"
"Alright Mami ki taho musu da abinci dan duk basuyi gurki ba suna tashin hankali yanzu na kawo yar ta gida ma zata dauki kayan su."

"Alright ba matsala ya jikin nata?"
"Da sauki!"

"Allah kara sauki."
*
**
***
****
*****
******
*******
Tana shiga gida Ummah da Sakina suka taso suna fadin
"Ya jikin nata?"

"Da sauki Mama ku kwantar da hankalin ku da sauki dan da na taho ma ta tashi yanzu abinci zata ci."
"Alhamsulillah."
Umma ta fada.

Hafsat ta kalli Sakina tace
"Yaushe Kika zo Yaya Sakina."

"Dazu Farisa ma tana daki!"
Ta mike da sauri ta fita sai ta dawo tace
"Tare muke da wanda ya kai mu asibti in zaku ku shirya sai muje kuga jikin nata kinga Hajara ma ta dawo ta huta sai mu zauna tare ko Yaya Sakina."

"Eh hakan yayi abinci fa?"
"Ya kai mana abinci ba matsalar sa."

"To gashi Umma ma tayi muku wani a tafi dashi ko?"
"Eh!".
Ta juya ta shiga dakin Mama.

Akan gado ta samu Farisa na waya ta daura kafa da kan daya tana lumshe ido.
" yaya Farisa!"

Hafsat ta fada. Ido ta bude ta kalle ta ta mike zaune tana fadin
"Mayi waya anjima kai ka fiya jaraba naga tare muka kwana kuma ni gaskiya sai gobe zan dawo."

Tana fadin haka ta kashe wayar ta.  Hafsa ta zauna tace
"Yanzu Yaya Farisa ba zaki bar wannan harkar ba kina gani duk mun ajiye gashi har Yaya Fauziyya tayi auren ita ta huta!"

"Wai da gaskie Yaya Fauziyya tai aure!"
"Wallahi  tayi Aure Yaya baki ga mijin ta ba mai sonta da kaunar ta tayi dacen miji!

"Tayaya Baba ya yadda tai aure!"
"Uhmm muma cewa yayi kawai ya daura mata aure bamu san komai ba sai kuma mijin yazo ya dauke ta."

"Ina ne gidan ta?".
" Nima ban sani ba."

"Lallai ke kika bata shawarar tayi aure ko?"
"To menene gatan namu in ba aure ba."

"Amman me kuka tara da zaku zauna dashi ku bawa ya'yan ku in halin su irin na mahaifin mune fa?".
"Bama fata Yaya Farisa muna fatan Allah ya bamu masu jin kanmu."

Baki ta tabe. Hafsa ta mikr tana fadin
"Na bar mutum a waje Halima ce ba lafiya tana asibiti shine nazo mu tafi da su Ummah."

"Haka suka ce min zuwa yamma zan shigo insha Alahu!"
"Allah ya yadda "

Ta zare wayar ta dake jikin charger tace
"Sai anjima!"
Ta bita da kallo tana kallon wayar hannta. Dakin su ta shiga ta same su sun canja kaya ta dauki kwadon da suka zuba kayan abincin suka fito.

Kabir na ganin Ummah ya fito ya durkusa har kasa ya gaishe ta. Ta amsa tana masa godiya ya gaida Sakina ta amsa itama tana masa godiya gidan baya ya bude musu suka shiga Hafsa ta shiga gidan gaba ya tada motar suka nufi asibiti.
Suna zuwa suka shiga shi kuma ya tsaya a wajen da Mami ta kira shi suna hanya. Sadiya na zaune a gefen Halima tana ta matsa mata kafafun ta dake mata ciwo tace. A dai dai lokacin da suka shigo. Hajara ta mike ta fada jikin Umma tana fadin
" Sannu da.zuwa!"

"Yauwah Hajara ya jikin yayar taki?"
"Da sauki."

"Allah kara sauki."
"Amin."

Sadiya ta mike tace
"Ina yini?"

"Lafiya lou!"
"Ya mai jikin?"

"Da sauki!"
"Allah kara sauki."

"Amin!"
Ta kalli Sakina suka gaisa sannan ta kalli Hafsa tace
"Ina yake?"

" yana waje!"
Jakar ta ya dauka tace
"To Allah kara sauki sai na dawo gobe!"

"Amin mun gode!"
Sukai sallama ta fita tare da Hafsat da ta raka ta a bakin reception ta bar ta ta koma.

A parking space ta same shi ta karasa tace
"To Kabir ni na fito zan tafi sai anjima Allah kara saiki "

"Amin nagode Sadiya Allah saka."
Tai murnushi tace
"Ba komai!"

Ta juya ta shiga cikin motar ta ta tada ta fita. Kan mai gadi ya rufe gate motar su Mami ta kunna kai. Suna parking ya karasa Arfat ya fito ya budewa Mami ta fito. Kwaso basket yayi da manyan ledoji. Kabir ya asmhi ledojin ya yi gaba sukabi bayan sa. Dakin suka karasa suka shiga.

Kujera suka bawa mami ta zauna suka gaishe ta tai musu ya mai jiki sannan suka gaisa da Umma tana godiya. Kayan suka ajiye Umma ta kara godiya.

Fita Arfat da Kabir sukai suka zauna a waje. Bayan thirty minute Arfat ya dawo dakin yace
"Mami zamu iya wucewa."

Ta mike tace
"Eh muje."

Ta kalli Ummah tace
"to Allah kara sauki yasa kaffara."
"Amin mungode!"

Ta fita Umma ta bita ta karata har bakin mota tana godiya sannan ta dawo. Kabir yace
"Nima zan shiga kasuwa yanzu."

"To Allah bada sa'a ina Isma'il ne jiya bansan tafiyar sa ba."
"Sai da na dawo ya fita dazu ma muna tare anan bai jima da tafiya."

Ciki ya koma ya durkusa yace
"Umma ni zan tafi Allah kara sauki."
"Amin amin mungide Allah saka da alheri."

Ya mike Hafsat tabi bayansa har wajen mota tace
"To Kabir mungode Allah saka da alheri."

"Amin nima nagode!"
Ya zaro kudi a aljihu yace
"Ki bawa su Ummah suyi kudin mota."

"Haba dai ai wannan ma mungode dan Allah ka barshi."
Durkusawa yayi ya zura a karkasin takalmin ta sannan yace
"Sai na dawo!"

Ya bude mota ya shiga ya tada ya bar asibitin. Durkusawa tayi ta dauka taga dubu biyar ta koma ta bawa Umma tace
"Wai kuyi kudin mota."

"Kai ke kuma kika amsa."
"Sai da nace a'ah amman ya dire min."

"To angode"
Halima ce ta farka sukai kanta suna mata sannu ta amsa. Fruit salad din da Mami tayo mata suka bata tasha kuma da dama. Ana magarib su Umma da Hajara suka tafi aka bar Hafsat da Sakina.

8:00pm ya shigo asibitin bayan yai sallah a masallaci cikin asibitin. Hannun sa dauke da ledoji guda biyu. Dakin da suke ya nufa yai knocking aka amsa masa sannan ya shiga. Idon ta biyu tana zaune akan gado bayan ta jingine da pillow ya shiga Hafsat ya sama tana salah Sakina kuma na waya.

Ledar hannun sa ya ajiye ya karasa kusa da gadon yace
" ya jikin?"

"Da sauki nagode Kabir ina Isma'il?"
"Bashi da lafiya ne!"

"Meyake damhn sa?"
"Zazzabi ne amman dazu ma ya shigo!"

Kai ta jinginar akan gadon tace
"Allah bashi lafiya."
"Amin ba abinda ke miki ciwo ko?"

"Babu!"
"To Alah kara sauki."

"Amin!"Yaya Zainab ce zaune ita da Umma. Umma tace

"Zainab naga kyaan kitchen kinyi kokari sosai wasu abun ai an siya anan ma Zainab."+


"Ba komai Umma rabon ta ne yanzu ma ga ragowar kudin da Yaya Suleiman ya bayar dan a mata siyayya nace me kike ganin za a siya mata!"

"Har nawa ne?"


"Million biyu ya bayar to mun kashe million daya dayar ma tace tana son a saka mata dining munyi ciniki da wani mai siyar da kaya shine nake so a bashi kudin yanzu dai dubu dari takwas ne a hannu na in an siyi dining table din."

"Ai ba sai an siya ba domin Abban ku ya mata kaya komai da kika san yarinya zata bukata yai mata. Dan komai daki biyu yai mata bedroom ma kuwa har uku ya siya mata kayan wani gidan sa yace zai basu bansan wannene ba dai amman a gaskiya Abban ku ma ya kashe kudi nima nan ya bani dubu dari biyar wai in tana bukatar wani abu a dada mata to ni kan me zan dada mata kaya har sun mata yawa."


"Allah sarki kanwata mahakurci mawadaci insha Allahu zataji dadin Muhammad za kuma tai alfahari dashi tai murna da zabin abban mu daman kuma can Ummu ai yar gaban goshin Abban muce!"

"Haka ne. Nima dai tunanin me zan wa Ummu nake!"


"Umma ni a ganina wadan nan kudaden a siya mata gida a zuba haya ragowar kuma a cigaba da juya mata a business din ta ko ya kika ce?"

"Hakan ma yayi Zainab!"


"Yauwah Umma, Muhammad ya kawon wata magana jiya!"

"Ina jinki!"


" wai walima yake so ayi kan ta tare!"

"To wannan ai sai dai muje ga Abban ku in ya yadda shikenan ko?"


"Haka ne!"

"Tashi muje!"


Ta mike suka fita. Mama suka sama a tsakar gida tana gyara kayan miya ta kalle su ta saki shewa tana fadin

"Ana ta kulla kulla kenan!"


Ba wanda ya kulata suka shige dakin Abban. Yana zaune akan carpet suka shiga. Ya mike zaune yana fadin

"Ina amarya Ummu?"


Zainab tai murmushi tace

"Au Abban ni ba tani kake ba sai ta amarya."


"Eh mana kinsan amarya da farin jini."

Zama Zainab tayi tace

"Lallai kam!"


Tayi kasa da kai tace

"Ina yini Abba?"


"Lafiya lou! Kunzo lafiya ina kishiyoyina aka barsu."

"Suna gun Ummu!"


"Madallah!"

Ummah ce tai masa bayanin kudin da Suleiman ya bayar da abinda akai har da ragowar. Abban ya jinjina kai yace

"Suleimanu kenan shi dai baya gajiya to madallah Allah ya saka yayi masa albarka shima Allah ya basa masuyi masa."


Duk suka amsa da

"Amin!"

Umma tace

"Sai wata magana da Zainab tazo da ita daga Muhammad!"


"To to me ya faru?"

"Daman jiya mukai waya yace yana son ayi walima kafin tarewar Ummu!"


"To shi ya nema ko ku kuka nema?"

"Abban sam bamu muka nema ba dan mu ba mu shirya komai ba in banda yan uwa suzo ayi yini akai ta."


"To in dai shi ya nema ai ba matsala zamuyi magana dashi Allah sanya alheri."

"Amin Abba!"


STORY CONTINUES BELOW

"Jiya ma na masa maganar kafi yace a dakata tukkun da tini yau kun tafi."

"Allah sarki Allah ya kaimu ko yaushe ne."


"Amin!"

"To ni zan tafi Abba!"


"To ki gaida Ummu tinda boye min ita ake."

"Zata zo ne Abba!"


"Sai tazo."

Ta mike ta fita. Ummah tace

"Madallah Alhaji muna godiya."


"Ba komai Allah yayi albarka."

Ta mike tabi bayan Zainab.


A falo ta samu Zainab tace

"To yanzu me kike ganin za a tsara?"


"Umma gani nake ayi snacks kawai da lemo sai a raba akwai wata kawata tana order kayan sai tayi mana zamuyi waya tayi list na mutum dari ai yayi ko?"

"Eh yayi!"


"To da safe kuma me kike ganin za ayi anan? Ni dai na bayar ayo fried rice da masa da sinasir da dambu!"

"To ainkin kwashe kayan Zainab."


"Ba komai Ummah! Lemo ma Yaya Suleiman yace za akawo da ruwa."

"Ikon Allah anan ayi me to? Bari sai ayi gurasa bandashe ko?"


"Yayi Umma!"

"To Allah kaimu ga kati can in zaki tafi ko zata bawa wasu kawayen ta."


"Muma zamu buga na walina ko?"

"Eh hakan ma yayi Allah yasa ayi taro lafiya a gama lafiya dai."


"Amin"

Zainab ta mike tace

"Umma zan tafi dan ina son a gama komai na walimar nan yau insha Allahu."


"To Zainab ki gaida yaran da Ummu."

"Zasu ji."


Ta fita ta samu Mama zaune tace

"Mama ni na tafi sai anjima"

"Mu jima da yawa!"


Ta fita ta hau motar ta sai gida. Ummu ta sama tana daki tana ta bacci. shiga tayi ta zauna ta ce

"Ummu!  Ummu!!"


Mikewa tayi tana mutsuka ido. Anty Zainab tace

"Wai wanna wane irin bacci kike ne?"


"Gajiya nayi ne Anty!"

"Jiya munyi magana da Muhammad wai walima yake so ayi naje gun Abban muyi magana shawara nazo muyi me kike ganin ya dace ayi?"


"Anty duk abinda kikai yayi Allah yasa albarka."

"Amin!"


Nan ta kira mai yin kayan sukai magana ta fada mata pieces nawa take so ta fada mata sannan ta kashe wayar Muhammad ta fadawa yace ta turo account number. Tana turawa taga ya ninka kudin da aka fada masa.


Waya ta kira tace

"Muhammad ai kudun sun yi yawa."

"Ba komai Anty a dada a hidimar wani abu. Za a kawo jaka da gift din da za a hada zuwa gobe ko jibi!"


"To Allah ya kaimu."

"Amin!"

Sukai sallama. Ta kalli Ummu tace

"Kinsan ya ninka kudin fa. Kuma yace za a kawo bags da gift!"


Shiru Ummu kawai tayi. Anty Zainab tace

"Wane kayan zaki saka ne a cikin wanda aka kawo?"

"Duk wanda kika zabar min!"


"Ke baki da zabi komai kice duk wanda na zabar miki!"

Kai ta gyada tace

"Bari na leka wajen masu printing din can su buga mana kati ko?"


"Toh Anty!"

Tana fita ta dauki waya da niyyar kiran sa sai ga kiran sa ya shigo. Dauka tayi tai sallama ya amsa yace

"Yau sauran kwana shida Amarya!"


Tai murmushi tace

"Bakwai dai!"

Yace

"Waya fada miki ai ranar da na dawo zan ganki"


Tai murmushi tace

"Gani kawai zakai ba tafiya da ita ba dai ko?"

"Au haka kika ce to kuwa tafiya zanyi da ita ayi walimar kina gida na."


"A'ah tuba nake ranka ya dade!"

"To ya kike?"


"Alhamdulillah kai fa?"

"Same Dear. Ya batun gyaran jiki?"


Shiru tayi yace

"Ban bada kudin sa ba ko?"

"Haba dai ai ba sai ka bayar ba Anty Zainab ta hutashar da kai."


"Godiya nake amman ai yanzu zaki lalle da sauran abubuwa ko?"

"Eh!"


STORY CONTINUES BELOW

"Nawa kike bukata?"

"Haba dai Yaa Muhammad ai ina da kudi zanyi ka bar su."


"Toh Hajiya nima ina bukatar kudin!"

"Nawa kake so?"


"Uhmm kinga ki turon account number ki yanzun nan ina jiran ki!"

"Dan Alla....."


"Kiyi shiru Ummu kawai kiyi abinda nace!"

Yana fada ya kashe wayar. shiryawa tayi tana tunani ta tura ko kuwa can kawai ta yanke shawara ta tura tana zaune taji alert tana dubawa ta zaro ido ganin abinda ya turo mata


Number ta fara nema yana dauka tace

"Yaa Muhammad ina zan kai kudin nan lallen yafi dubu uku. Amman ka turon wannan uban kudin!"


"Na sani Ummu kiyi lalle daga kan dubu daya zuwa dari Ummu haka gyaran gashi sauran kiyi bukatun gaban ki abinda ya rage ki rike rabon kine. Nagode sai anjima!"

Wayar ta bi da kallo. Text tai masa na godiya sannan ta tura masa. Yayo mata reply yana fadin

"Nauyi nane Ummu kada ki damu nike da godiya."


Komawa tayi ta kwanta tana mai lumshe idanun ta kawai salon Mubammad da koman sa na daban ne.


*

**

***

****

*****

******

Cikin farin ciki ya tashi daga bacci dan a jiya sun jima suna waya da Hafsat kuma ga dukkan alamu ta kara saukowa ta kamu da son sa. Dan haka yau wani sakayau yake jin sa duk da yana jin kewar ta kwanan sa bakwai yau amman ji yake kamar yai shekara bakwai bai ganta ba. Ba abinda yake son ya gani kamar ta haka nan ba abinda yake son yaji kamar muryar ta.


Makarar da yayi ne yasa bai kira ta ba da ya tashi har sai da ya shirya ya leka ya tadda Hannah na bacci sannan ya fito ya isa motar sa ya shiga ya tada ya hau kan titi.

Tin da ya hau kan titi yake neman layin ta yaki shiga har ya iso office amman a kashe wayar take duk sai ya rasa sukuni to lafiya Hafsat take ko kuma kashe wayar tayi dan kar ya dame ta. Kai ya girgiza kawai yace

"Ba zata kashe dan kar na same ta ba."


Shiru yayi yace

"To lafiya kuwa!"

Ya zuba tagumi. Da ka kalle shi zaka san bai cikin walwala ko jin dadi domin kuwa fuskar sa ta nuna karara. Da kyar yayi aiyukan sa duk yunwar da yake ji kasa cin abinci yayi sai ya rasa me yake masa dadi don ji yayi har wani zazzabi zazzabi na neman kama shi. Shawara ya fara yankewa a zuciyar sa ya tafi kano a lokacin sai dai ganin yamma tayi ya bar wa gobe dan ba zai iya zama anan ba tare da yasan a hali da Hafsat take ciki ba.


Da ya tashi a aiki ma jiki a sanyaye ya fita ya shiga mota ya tafi gida. Yana parking ya fito ya rufe ya dauki tarkacen sa yayi cikin gida. As usual a parlour ya sameta tana kallo. Kallo daya yai mata ya dauke kan sa ya shige daki. Da kallo ta bishi ta tabe baki tana fadi 

"Yau ba yan maganar bane aka ka kenan"


Yana shiga ya kwanta akan gado ya lumshe ido. Ya jima a kwance dan jin ana fara kiran sallah yasa ya mike ya cire kayan sa ya shiga ya watsa ruwa ya dauro alwala sannan ya fito. Jallabiya ya saka ya fito yana tafiya kamar ba zai taka kasa ba.


Da kallo ta bishi har ya fita. Yana idar da sallah ya zauna yana tasbihi da addu'a sai da akayi isha'i yayi sannan ya baro masalaci. A parlour dai ya same ta ya shige dakin sa. Lemo kadai ya sha ya koma ya kwanta ya dauki wayar sa yana mai kara trying number ta.

*

Tana zaune a daki bayan Kabir ya tafi wayar ta da kunnawa kenan ta fara kara mikewa tayi ta dauka murmushi ta saki ta dauka ta fita a dakin.

"Assalamu alaiku!"


Wata ajiyar zuciya ya sauke kan yace

"Wa'alaikum salam Hafsat ina kija shiga tin safe nake neman layin ki a kashe lafiya kuwa? A gaskiya na tsorota na shiga kuma wani hali sosai Hafsat hakika rashin ki babban tashin hankali ne a waje na."


"Haba Deedat kana daukar abu a sannu fa."

"Hafsat daga son kine komai a sannu nake masa amman daga yadda son ki ya shige komai ya canja ban da buri da muradi sai naki. Ki fada min me ya faru dan da ban same ki ba da gobe sammako zanyi sai gidan ku yanzun ma ina hanya in Allah ya kaimu gobe nazo naga me yake faruwa?"


"Hmm Deedat kenan ka kwantar da hankalin ka ina nan lafiya lou wallahi tin daren jiya ne muke asibiti kanwata ba lafiya shiyasa sai dazu na koma na dauko wayata amman ba wata matsala."

"To Alhamdulilah ya jikin nata?"


"Da sauki!"

"Alah kara sauki in Allah ya kaimu gobe zan shigo sai na duba ta."


"Haba Deedat ba munyi magana ba nace ka bari ka karasa sati biyun ka."

"Ai na fada miki ba zanyi ba Baby wallahi yau baki san halin da na shiga ha a rashin jin muryar ki gashi na tashi da tsananin muradin jin muryar ki dan Allah ki barni nazo Baby wallahi in ban zo ba hankali na bazai kwanta ba."


"Shikenan Deedat Allah kaimu."

"Amman my Baby yanzu ya kike?"


"Alhamdulullah!"

"Ba dai matsala ko?"


"Babu masha Allah. I miss you Baby!"

"Hmm!"


"Wallahi yau kowa ya ganni yasan ban da lafiya sai kiji ana fadi  me yake damuna sai dai nace ba komai kawai."

Cikin sa ne yai kara yace

"Kinji cikina ko rabon sa da abinci tin jiya tinda Baby na tana lafiya bari naje naci abinci ko tea ne nasha ko?"


"A'ah kaci abinci dai."

"Shikenan kamar me?"


"Abinda madam ta girka maka."

Shiru yayi dan yasan ba abinda Hannah ta girka tace

"kaje kaci kaji."


Ta kashe wayar tana mamaki akan me matar sa bata matsa yaci abinci ba. sai ta tabe baki tace

"Uhmm kila ma ni yake fadawa duk san dadin baki."


"Ba dai ki sani ba."

Wata zuciyar ya fada. Daki ta koma tana sake sake in kuwa haka ne abinda yake fada mata gaskiya Ahmad masoyin ta ne to amman ita fa tana tsoro domin itama tana son sa amman tana tsoron gaba in ya gane wacece ita.


Zama tayi ta zuba tagumi tana tuna rayuwar su ta baya da yadda son abin duniya ya rudeta ta fada ga halaka wanda yanzu take danasani wanda aka ce keya ce. Yanzu in ta auri Ahmad ta kai masa me da wane idon zatai masa bayani dan gaskiya ita ba zata iyai masa bayani a waje ba asirin ta ya tono yace ya fasa auren ya wanda daga haka aje ana fada a duniya in tayi kaza tayi kaza zata bari in sunyi aure daga baya tai masa bayani tasan Ahmad yana son ta zai saurare ta.

Ajiyar zuciya ta dauke bayan ta gama tunanin nan tace

"Allah ka dubeni "

Sai ta mike ta shiga bandaki ta dauro alwala ta dawo ta tada sallah tana mai addu'a akan Allah ya yafe mata ya rufa mata asiri.


Tin da ya fita kai Sakina airport hankalin ta ya kasa kwanciyya tai ta zarya a parlournta ta kasa zama ta kasa tsaye waje daya. Gashi ta kira wayar sa ya bar ta a cikin mota wacce ke hannun sa kuma bata da number sa. Haka tai ta zagaye dakin sai kuma ta leka window ko zai dawo duk ta damu ta rasa akan me.+


Tabbas ba zata taba yadda danta da ta fiso ya auri Sakina ba yarinyar da taga tsiraicin ta ina sam wannan ba zai yiyu ba da Sakina ta auri Khaleel gwara ta bar duniyar gaba daya.


Tana zaune ta kara daukar waya tana kiran sa kiran ne ya shiga tana addu'a allah yasa ya dauka ai kuwa taji ya dauka yace

"Hello Mom ya akai gani nan na taho ko akwai abinda kike bukata?"


Ajiyar zuciya ta sauke tace

"A'ah daman naga ka jima ne sai ka karaso."

Yai murmushi yace

"Ok thank you."


Ya kashe wayar yana murmushi shi kadai. Yana shiga gida yai parking sannan ya fito ya shigo fuskar sa dauke da murmushi. A falo ya samu Hajiyar tana zaune ya zauna a gefen ta yana fadin

"barka sa hutawa Mom."


"Yauwah ka dawo lafiya?"

"Alhamdulillah."

Ta kalle shi taga sai murmushi yake saki tace

"Lafiya naga kana murmushi."


Ya gyara zama yace

"Mom na wa Sakina magana ne tace ita bata da wanda take so shine nake murna kinga kenan tawa ce ko?"


STORY CONTINUES BELOW

Fuska ta daure kamar bata taba dariya ba sannan ta mike ta nuna sa da yatsa tace

"Ibrahim ka fita idona na rufe wallahi ni sa'ar wasan ka ce."


"Mom..."

Kai min shiru me zaka ce min. Na fada maka abu baka yadda ba shine ka tambaye ta ko?"


"Ba haka bane Mom gani nayi ina son ta i can't live wirhout her wallahi mum da aure nake son ta ba wani shashanci ko wasa."

"Ibrahim!"

Ta daka masa tsawa ya dago da sauri.


"Ni to ban yadda ba."

"Why Mom? Why? Ni bazan iya ba in har kina so na hakura da sakina ki fada min kome gareta ni kuma zan duba in har ya kamata na barta zan barta har abada in kuma bai kamata ba kiyi hakuri."


Wani kallo tai masa ta mike tayi sama da sauri. Tana shiga daki ta saki kuka tana fadin

"Na shiga uku "


Hajiya Habiba ta kira a waya tana dauka tace

"Habiba ya zanyi Khaleel na neman tsarwatsan rayuwa ta!"


"Meya faru?"

"Kinga kina gida yanzu."


"Ina nan."

"Ok gani nan "

Ta dauki mayafin ta ta fice a dakin a falo ta same shi ta fito yana ganin ta ya kike yace

"Where are you going?"


"Gidan Hajiya Habiba!"

"Mom!"

Ya kira sunan. Juyiwa tayi yace

"Please kiji tsoron Allah kada ki rabani da Sakina dan Allah "


Yana fadar haka yayi sama tabishi da kallo sai kuma jikin ta yai sanyi. Fita tayi driver ya kaita gidan Hajiya Habiba.

A babban falon ta, ta sameta da manya manyan hajiyoyi wanda harkar su duk daya ce neman mata dan sai abubuwa suke tinda ta shiga ta nemi waje daya ta zauna tana tunanin rayuwa wata Hajiya ce a cikin su ta kyalla ido akan Hajiyar nan ta koma kusa da ita tana tabo ta daga nan ta rinjaye ta dan ita kwarariya ce anan falo suka baje suna masha'a su gaban kowa daga baya suka mike suka shige dakin Hajiya Habiba dake nan falo na baki.


Sai da suka gama masha'ar sannan suka fito falo. Hajiya Habiba ta tado ta rumgume Hajiyar tana fadin

"Babbar Hajiya ya kike ya gida kwana biyu daga samun sabon jini kin ya dani ko?"


"Ba haka bane Habibiya wallahi abubuwan sai a hankali sabon jini zata ruguza min rayuwa!"

"Me ya faru?"


"Khaleel ne wai yake son ta."

"To ke me kika ce?"


"Na nuna mata an mata miji yaki yadda wai tinda ba a aura masa ba ai da sauki wayasani ko tashi ce. Da na nuna bana so ya nunan sai na fada masa dalili to tayaya ni kam zan fada masa dalili Habibiya."

"Haba Hajiyar kamar ba ke ba ai kawai ki fada masa cewa yarinyar bata da tarbiyya."


"Me kusan Khalrel da bincike kuwa wallahi tinda yace yana son ta bazai bar ta ba."

"Ni kawai a ganina ki fada masa me yarinyar take ai baki mata sharri ba."


Wata a wajen tace

"Haka ne amman ma ba za a barshi haka ba duk da haka dole a dauke masa hankali daga kan yarinyar."


"Haka ne kuma Hajiya Balaraba."

"Sannan dole ki kawap makusa akan yarinyar yadda zai tsane ta."


"To fah yanzu ni ya za ayi ku fada min."

"Kinga ki kwantar da hankalin ki next week zani china in kina da lokaci kizo mu tafi kinga ai na samu me deben kewa daga can sai mu biya ayi komai ko yaya kika ce?"


"Shikenan Hajiya Balaraba nagode."

"Kai Hajiyar kar kiji komai!"


Hajiya Hindatu da tinda suka fara magana bata tanka ba tace

"Ni a ganina mai zai hana ki barshi ya aureta kingqa ke kici shi yaci ko ya kika ce?"


Hajiya Habiba tace

"Kuma fa kin kawo idea."


"Wallahi in nice haka zanyi ya aure tan amman fa nima ina tare da ita ina kada shi can wani wajen."

"Haka ne amman zamu fara bin ta Hajiya Balaraba in bai ba ai sai a duba taki amman gaskiya da kunya Hajiya Hindatu ace matar dana gani nake ba zan iya ba duk abuna gwara na hakura Allah ma ba zai sa ya aure ta ba."


STORY CONTINUES BELOW

"To shikenan Allah bada sa'a. Yadda kike jin dadin mu'amala da ita ga aba a gida me yai miki zafi ku rufawa kan ku asiri."

"Kuma fa Hakane Hajiya Hindatu."


Hajiya Habiba ta fada. Hajiya Hindatu tace

"Wallahi ni inama dana zai ga wata yarinyar da muke mu'amala yace zai aura ai sai nayi ruwa nai tsaki abin ya faru. Allah dai ya kai damo ga harawa"

Suka saka shewa suna tafawa.

*

**

***

****

*****

******

*******

Zuwan su kano ma yadda ake mata gyara sai ta kara wani kyau ta kara haske fatar ta tai luwailuwai kamar ta jarirai har muryar ta kadai ta canja.


Zaune take a dakin ta tana zaune hannun ta rike da abinda Anty Zainab ta kawo mata kurba tayi taji da dadi wannan yasa ta kara kurba. Kofar dakin aka budo tana daga kai taga Anty Rukayya. Murmushi ta saki tana fadin

"Anty na sannu da zuwa."


Rukky ta kalle ta, ta tabe baki sannan ta shigo tace

"Amarya kinsha kyau fa. Wane mai kike shafawa."


"Kai Anty ki rufa min asiri kinsan ni ai bana shafa mai gyaran da ake min ne kawai."

"Uhmm ai gwara ki shafa mai yafi wallahi yanzu ni ya kika ganni."


Kallon ta Ummu tayi gaskiya ne ta kara haske sosai kamar ka taba jini ya fito saboda bleaching har wani green green tayi. Ummu tace

"Amman Anty Rukkaya ai kinfi kyau a da."


"Au Ummu da gaske kina bakin ciki dani ne."

"Kamar ya bakin ciki Anty?"


"To gashi nan duk wani mai sona in ya ganni a yanzu ya ficewa nayi kyau sabida nayi fari sannan nayi kiba."

"Haka ne amman ni nafi ganin kyan ki a baya wai wannan kibar fa."


"Kema kina so?"

Shiru Ummu tayi. Rukayya tace

"Ai batai yawa ba kawai dai jikin ya kara kyau ne ya kika ganni. Wani magani nasha shine kika ga na zama haka fa ke har farin allura akai min."


" kai Anty ba kyau fa!"

"To malama kinsan dai nw sani ko? Dadin abin tare muke zuwa isilamiyya dan haka ki min shiru."


"Shikenan ina Yara nane?"

"Ah lallai kuwa yaran ki zaki gansu soon tinda kin auri mahaifin su,  suna gun surukar ki."

"Allah sarki ya suke?"


"Tayaya zaki tambayi kaza hanyar rafi Ummu ki tambayi agwagwa kisha labari."

"Kai Anty na bakya zuwa ganin su."


"Akan me Ummu?"

"Haba Anty Ya'yan kine fa."


"Tab na bar miki su Ummu wai Ummu mai yasa kika yadda aka aura miki Muhammad me zakiyi da Muhammad sauran wata sauran yayar ki?"

"Anty kenan biyayya kuma nasan ba zan taba faduwa kasa ba. Da kike cewa saura saura ai abin ba anan yake ba."


"Me kike nufi?"

"A'ah nifa bance komai ba."


Kwafa tayi tace

"Kuna waya ne?"

Shiru tayi sai kuma tace

"Eh!"


"Meyake ce miki?"

"Muna gaisawa ne kawai!"


"Ummu kada ki bari Muhammad ya cuce ki kamar yadda ya cuce ni."

"Anty wacce cuta yai miki?"


"Na haifi yara biyu ya uban talauci."

"Haba Anty ko a yara da Allah ya baku ai babban arziki ne bakya ganin wasu neman haihuwar suke sun rasa. Talauci kuma ai na Allah ne dan haka Allah zai buda mana da izinin Allah bayan nan kuma kada ki manta nayi karatu shima yayi zamu taru mu rufawa kan mu asiri."


"Daman ke ai ba wayo ne dake ba!"

"Naji!"

Ta fada tana turo baki dan har ga Allah abinda take fada akan Muhammad ya bata mata rai. Abin hannun ta ta daga kai ta shanye tana lashe baki.


Rukky dake kallon ta tace

"Uhmm naga sai wani rawar kafa kike yi har da ciye ciye ko ayi dai a hankali kada kije ya farka ki dan kinsan ya saba ba kamar ke ba sabon shiga."


"In ya farka ni ai ana dinkewa ko?"

" Au rashin kunya zaki min!"


"No tambayar ki fa nayi."

"Eh ana dinkawa amman zakiji jiki!"


"In har zan samu albarka ba matsala Anty na. Ke ya naki ya kasance?"

" hmmm ummu nawa ba sauki duk da ya kasance sabon shiga amman na kusan mutuwa wallahi abin ba na wasa bane."


Murmushi Ummu tayi ta sake duk da a zuciya ta ta tsorata tace

"Kila dan sabon shiga ne yana dauki yaji me ake jine? Amman yanzu a sannu zai yi dan ya samu buduwar da ya jima bai samu ba."


Kallonta kawai Rukayya ta tsaya yaushe Ummu tayi baki haka. Ajiyar zuciya ta sauke tace

"Kuma wai ba laife ba wani abu."


"Anty duk kaya na in kai laife ina Yaa Suleiman baki ga kayan da yai min ba haka ma Abbah ga Anty Zainab wallahi kayan da sukai min sun fi wasu laifen ma."

"Nqsu daban nashi daban."


"Au haba ai sutura duk sutura ce ni kam nagode wallahi ya ajiye kudin sa yai wani abun."

"Hmm lallai Ummu baki da wayo ai hankali zaki tada masa kice sai yai miki kinga in ya turo kudin sai ki ajiye kiyi amfani."


"Kai Anty?"

"Wallahi."

Shiru Ummu tayi can ta saki myrmushi tace

"To haka za ayi."


"Yauwah yar gari. Wai yaushe za ai kafi ne naji Abbah yace shi yace a dakata ko bai samu gidan bane?"

"Nima haka naji. sai dai ki tambayi Abbahn ai."


Ido ta zaro tace

"Rufan asiri."

Tai murmushi tace

"To menene ba so kike ki sani ba."


"A'ah wai dan muje kafi ne."

"Oh ai in za aje za a sanar daku."


"Amman fa yau sauran kwana uku."

" eh!"


"Lokaci bai kure ba."

"Ko ranar ai za a iya kafi kinsan Anty Zainab ta dauko masuyi ku naku kallo ne in an gama ku rufe gida ku taho."


Haba ta kama tace

"Fi'ili Allah kyauta."

"Amin!"


"Yanzu ke Ummu ba za'ayi ko dan wani taro ba na musamman da angon."

Gaban Ummu ne ya fadi take kishi ya kamata ita kawai ama fasa walimar kar azo ana kallon mata miji. (Ah kunji su Ummu masu miji fa lol)


"Gaskiya ki tada masa hankali ko dinner ne ayi!"

"Bana ra'ayi Anty Rukayya!"


"Ke daman ai baki waye ba ina ganin kinyi karatu yaci ace ki waye amman ina."

"Anty kenan wayewa ai ba anan take ba."


"Uhmm ai shikenan."

"Hmm"


"Amman wallahi Ummu kinyi kyau fa. Nima in zan yi aure a min irin gyaran nan naki!"

"Zan dauki nauyi!"


"Amman kuwa da na gode."

Murmushi Ummu tayi. Rukayya tace

"Yanzu aikin ki kin barshi kenan wai!"


"Eh yanzu zanyi bautar ubangiji ba."

"Gaskiya Ummu in nice ba zan barshi ba kudi fa kike samu."


"To Anty yanzu kuma alvarka da lada zan samu ko?"

"Kudi ai yafi"


"Haba dai Anty kada son kudi yankai ki ga halaka mana. Lada fa aka ce tayaya zaki hada shi da samun kudi?"

"Uhmm Ummu kenan."


Anty Zainab ce tai sallama ta shigo hannun ta dauke da bowl na pepper soup da akayi yaji kayan kamshi. Su ne kullum abincin ta daga na kayan ciki sai na kaza taci tasha romo sai hadin kunu ko fruit da Anty ke mata kala kala.


Mika mata tayi tace

"Rukayya ki fito kici abinci."

"No Anty na koshi sai da naci na fito tafiya ma zan fito nayi."


"To shikenan."

Anty Zainab tace

"Maza ki cinye dan anjima ma akwai wanda za ayi miki."


"Kai Anty ni dai kun mai dani kura kawai."

Hararar ta Anty tayi kawai ta juya ta fita. Ajiyewa tayi a tsakiyar su tace

"Muci."


Dauka tayi ta fara ci tace

"Yar gatan Anty. Antyn ki sai gyara ki take yi. Ke kuma naga bakya so."

Shiru Umu tayi ta dauki spoon tana shan romon shi ta sha da yawa naman kuwa fin rabi Rukatya ce ta cinye kadan Ummu taci tama godewa Allah da Rukayya tazo ta taya ta ci.


Rukayya ta mike tace

"To Ummu ni zan tafi sai an kira mu tariyya in kuma sai ranar kai kin ne shikenan zamu shigo can gidan Allah bada sa'a."

Tin da Isma'il ya koma gida ya kasa tsaye ya kasa zaune gaba daya ya rasa nutuswar sa. Kabir ya bashi mamaki haka nan Sadiya ta kara shayar da shi ruwan mamaki domin daman ya gane ita macece mai aji ba kowa take biyewa ba. Amman lallai daga Kabir har ita zasu san waye Isma'il.

Dan shi Kabir zai nuna masa baya neman abu ya rasa zai auri Sadiya sai dai in zai mutu ya mutu. Ita kuma zata shigo hannun sa duk son da yake mata hakan ba zai sa ya hukuntata ba domin ba macen da ta taba ci masa mutunci kamar haka har da mari sai ya shafa wajen yana wani killer smile. Can yai kwafa yace
"Ba zaka burgeni ba Kabir sai ka sauri Halima na gama da ita bana kuma bukatar ta."

Mikewa yayi sai kuma ya koma ya zauna. Yayi haka yafi sau uku yana saka da warwara.
*
Kabir na komawa gida yai wanka ya canja kaya. Cikin gida ya shiga ya samu Hajiyar sa a falo ya gaisheta ta karai masa ya mai jiki sannan ya mike ya nufi dining abinci yaci ya koshi sannan ya mike yai mata sai da safe.

Yana komawa bangaren sa ya kwanta sai dai da ya rufe idon sa sai yaga Sadiya na matasawa Halima kafar ta. Take tunanin Halima kuma ya shiga kwakwalarsa. Tausayin ta kawai yake ji

Bazai ce laifin ta bane domun yasan Isma'il tantiri ne sai dai in bai so abu ba amman zai iya komai dan ya samu wannan abun. Haka nan na yasan kaddarar ta ce Allah ya daura mafa amman yanzu tayaya yarinya karama ta shiga wannan halin wane zata shiga gaba ya lura Halima na son Isma'il wanda shi duk so da kulawar da ya nuna mana na yaudara ne a yanzu babu.

Me zai yi dan ya taimaka mata? Abinda yake ta tambayar kansa kenan. Tuna statement din Isma'il yayi da yaxe
"Sai ka aure ta zaka burgeni."

Kai ya girgiza yana fadin
"Tayaya zan iya auren ta. Hakika ina son ta amman ina kishin ta in na aure ta kuwa ba zan zalunce ta ba dan duk lokacin da na tuna da abinda ta aikata zanji kamar in kashe kai nane zanji na tsani rayuwa ta. Zan sa ta shiga wani hali ne."

Zuciyar sa ya dafe yana fadin
"But i love her ba pride din ta nakewa ba ita kanta nakewa Allah shi yasan dalilin da ya dauran son!"

Hannu ya daga sama yace
"Allah kamar yadda ka dauran son Halima Alllah ka kawon mafita akan sa. Allah ka bani ikon taumaka mata Allah ka bani ikon share mata hawaye Allah ka bani ikon shiryar da ita. Allah ka bani ikon kulawa da ita da kare ta."
Sai ya shfa yana kwanciyya.  Rainin hankalin Isma'il kawai yake hangiwa ace ka lalata yarinya sannan ka guje ta shi kuwa tayaya zai tsaya Isma'il ya samu Sadiya.

Zaune ya mike da sauri
"Dole i tsairatar da Sadiya daga auren Isma'il dan ba mutum aure bane. Sadiya bata dace dashi ba."

"To tayaya?"
Shine shine abinda ya kasa ganewa. Ranar haka ya kwana bai runtsa ba daga tunanin Halima sai na Sadiya.
*
Tin da ta tafi yake neman layin ta amman yaki shiga duk ya sauya a cikin yini daya daka kalle shi zaka san yana cikin damuwa mai tsanani ma kuwa. Yana zaune tin safe bai fito ba.

STORY CONTINUES BELOW

Hajiyar ganin har rana tayi yasa ta nufi dakin sa. Zaune ta same shi rike da waya yana famman dailing number. Sai ya saka a kunne ace switch off sai ya sauke. Shiga tayi tace
"Lafiya Khaleel?"

Dagowa yayi ya kalle ta idon sa jajir yace
"Momy Sakina!"
Fuska ta tsuke tace
"Me ya samu sakinan?"

"Na kasa samun ta please Momy baki da wata number tata?"
Wani kallo ta watsa masa ta saki tsaki sannan ta juya ta fice a dakin. Da kallo ya bita yana mamakon Momyn sa. Komawa yai ya kwanta kamar maraya yana tunanin ta.
Ido ya lumhse ba abinda yake gani sai kyakyawar fuskar ta mai kyau tana masa murmushi murmushin ya saki can kuma ya bude ido yana fadin
"Allah yasa kina lafiya Baby!"

Ranar a daki ya yini har dare bai fita ba kan safiya kuwa wani ciwon kai ya saukar masa.
*
Washe gari ba sam bai fito ba har wajen sha biyu yana daki yana fama.da kansa dan yadda ya matsawa kan sa da tunanin Sakina ya saukar masa da wani azazabben ciwon ka.

Hajiyar kuwa ta tsinewa Sakina yafi sau nawa dan tazo ta lalara mata yaro sam Khaleel be son baccin ran ta amman yau aka Sakina baiya gudun yaga rai fushi da dane tai fushi da tini yazo yana lallashin ta ko da bashi yayi laifin ba.

'Da da uwa duk da haka ita sai ta kasa nutsuwa dole yasa ta nufi dakin nasa. Ko ina a rufe yake haka nan fitila ma a kashe take. Fitila ta kunna sai ta hango shi kwance akam gado yana sauke numfashi da kyar da sauri ta karaso tana ffdin
"Khaleel me yake damun ka."

Da kyar ya isa daga hannu ya nuna mata kan sa. Da sauri ta fita tana bari a kira river ya kaimu asibiti. Tana fita kiran driver mota ta shigo gidan kan ta motsa aka bude kofar. Mai gidan ta ne ya firto daga ciki tana ganin ta tafi a guje ta fada jikin sa tana fadin
"Welcome honey."

"Welcome my wife"
Yai kissing nata yace
"I miss you."

"Miss you more!"
"Ina zakije ne?"

"Honey Khakeel ne ba lafiya "
Da sauri yai hanyar cikin gidan yana fadin
"Since when?"

Bayan sa tabi tana fadin
"Yanzu na shiga na same shi kwance!"
Juyiwa uace
"Bangane ba."

Shiru tayi yace
"Kada kice min tin jiya rabon ki da ki duba a halin da yake sai yanzu."
Shiru tayi sai yayi gaba kawai ya dauki wayar sa a aljihu ya fara kiran docton su.

Yana dauka yace
"Its emergency ka samen a gida please."
Ya kashe yana shiga dakin da Khaleel yake.
Da sauri ya karasa ya dago shi yace
"Son!"
A hankali ya bude ido sai kuma ya rumgume Dadyn nasa yana sakin kuka.

"Sorry Son ga Doctor nan zuwa."
Wayar sa ce tai kara yace
"Just come in muna dakin sa."

Ya kashe wayar bai ai minti biyu ba sai ga Doctor ya shigo da wani dan akwati a hannun sa. Budewa yayi ya dauki abun auna Bp sannan ya karaso wajen sa. Bpn ya auna masa sannan yace
"Kana zazzabi ne?"

Kai ya girgiza. Yace
"Ok!"
Yayi rubutu a paper sannan ya dago ya kalli Dadyn sa yace
"Alhaji ga magungunan da za a samar masa."

Amsa Dady yayi sannan suka fita  tare Dady yace
"But me yake damun sa?"

"Jinin sa ne ya dan hau."
"Hawan jini Mu'azam din?"

"Ai ba wani abu bane a wannan zamanin,  ga magani nan in yasha zai sauka, zan shigo bayan magrib na duba shi."
Hannu Dady ya bashi sukai musabaha sannan sukai sallama yaran gudan ya bawa su siyo magungunan. Sannan ya juya ya koma dakin Khaleel.

Yana kwance ya koma yace
"Did you take youe bath?"
Kai ya girgiza ya mike ya shiga ya hada masa sannan ya fito ya taimaka masa ya shiga.

Dakin sa ya koma ya cire babbae riga sannan ya fito a stairs ya hadu da Hajiyar zaya hau hannun ta rike da tray da ruwa da lemo da cup akai. Tana ganin sa tace
"Alhaji na har ka gaji da jira ne?"

Murmushi shima yai mata ta ja hannun sa suka zauna a kujerun dake sama. Sannan ta bude riwan ta bashi yasha ta kara zuba masa lemon shima ya sha. Tace
"Yauwah sannu yanzu muje kai wanka sai kaci abinci ko dan har lunch is ready!"

Fuskar ta ya shafa yace
"Did he eat?"
Kai ta girgiza yace
"Samar masa abinda zai ci kan yasha magani."

"Ok!"
Ta mike ya fita.
Kitchen ta shiga ta samu masu aikin ra suna ganin ta da yake kuku ne suba zube. Da hannu tai nusu alama da su tashi sannan ta saka suka haka hado nasa abinci. Nan da nan suka hada sannan ta amso ta fito har ta nufi stair taji ana dannan bell ajiye kayan hannun ta tayi ta juya ta isa kofa ta bude taga yaran gidan ne yana ganin ta yace
"Ina kwana Hajiya?"

"Lafiya!"
Ledar hannun sa ya mika mata ta maganin ta amsa yace
"Alhaji ne ya aiken!"

"Menene!".
Ta fada tana kallon ledar sai taga ta phermacy ce. Dan haka tace
"Is ok!"
ta juya ta rufe kofar ta koma ciki.

Sama ta isa ta shige dakin Khaleel direct. zaune ta same shi da wando three quarter da riga marar nauyi. Kayan ta ajiye sannan tace
"Sannu Khaleel!

Kai ya gyada mata kawai. Ta hada masa tea Dady ya amsa ya bashi sai doyar da akayi kadan yaci yace ya koshi magani Dady ya bashi yana sha ya kwanta bai jima ba bacci ya dauke shi. Sai da baccin ya dauke shi sannan hankalin Dady ya kwanta.

Hajiyar yace
"Alhaji muje kai wanka ko?"
Zai magana ta kamo hannun sa binta kawai yayi suna shiga daki ta fara cire masa kaya sannan ta shiga ta hada musu ruwan wanka tare sukai wankan dan da tin daga can suka fara romaning junan su dan sai dauko Hajiyar yayi ya dire akan gado.
Bayan minti talatin suka kara wanka sannan suka shirya suka fito. Masallaci Dady ya wuce sai da yai sallah ya dawo. Nan Hajiyar ta tare shi suka wuce dining naga soyayya da kulawa domin abinci a bashi aka bashi da an bata masa baki zata saka harshen ta ta lashe  hajiyar kwararra ce sosai ta wuce tunanin mai tunani.

Sai da suka gama suka koma Falo Dady yace
"Me yake damun Mu'azam ne?"
Inda inda ta fara sai kuma tace
"Nima fa shiga ta krnan na same shi a haka ban sani ba."

Ajiyar zuciya ya sauke yace
"Jinin sa ya hau wannan ya nuna akwai abinda ke damun sa."
"Toh fah..."

"Yes and you know his condition!"
Kai ta gyada. Yace
"I hope the problem is not from you."

"Its not Alhaji."
"Allah yasa."

"Amin!"
"Allah bashi lafiya."

"Amin! Amman baka fada min zaka dawo ba."
"I just want to surprise you!"

"Ai kam you did dan i miss you badly!"
"I see ai! But you know i miss you too ba."

"Bai kai nawa ba."
"Yafi naki baki ga yadda na zauce miki ba. But ke sai baga...."

"Kaga me Alhaji! Kana can how did you know in which condition i am?"
"Hajiyar tawa!"

"Yes My Alhaji na ni kadai."
"Wannan haka take."

"I love you!"
"I love you more!"
Ya rungume ta a jikinsa suna shan soyayyar su.Ummu na shiga ta zauna anan falo tace

"Sannu Anty!"

"Yauwah me wanna shashashar ta zauna fada miki."+


"Kai Anty!"

"Ba sha shashar bace."


Fuska ta bata. Anty Zainab tace

"Da yake na taba uwar ki ko?"

"Ba haka bane."


"Ai shikenan saura ki dauki shawarar ta."

"Haba Anty nima fa ina da hankali."


"Au haba?"

"Wallahi Anty ai na gane me tazo min dashi burgar cikina ta dinga yi da son kushe min auren har da Yaa Muhammad ma fa. wai na yadda kaza kaza haka nan wai ana tarewa da aiki na. Kisan me haka fa tace wai nace sai tai min lefe ni kuwa na bida ita a to."


"Oh ai nasa zuwan nata auko ta akai Allah yasa baki fada mata komai ba."

"Hmm Anty nima fa ina da wayo ko walima ban fada mata da yin ta ba in sun zo saji ko a aika mata da kati ta gani daga sama amman kiji wai nace masa ayi dinner ziga dai kala kala."


"Kinsan Allah Ummu ban yadda in kin tare tana zuwa miki gida ba kada ki kuskusara ki sakar mata fuska bare ta samu wajen zuwa ta kashe miki aure."

"Haba dai."


"To ki zauna."

Shiru Ummu tayi tace

"Wai yaya zanyi da kudin da Yaa Muhammad da ya turon."


"Nakine Ummu ki ajiye su bayan biki maga mai ya kamata ayi dasu ko?"

"Yanzu ba abinda ake bukata. Kudin fa da yawa ni bansan ina zan kai su ba. Shima Yaa Muhammad dai."


Murmushi Anty kawai tayi tace

"Dazu kuna ciki da Rukayya aka kawo bags da gift din da za a bayar an saka sunan ku sunyi kyau suna store din daki na."


"Waye ya aiko?"

"Kanin Muhmmad ne yazo ya kawo kayan sunyi yawa ma wallahi kuma sunyi kyau daga ga ni da tsada."


"Allah sarki Allah kara budi ya rufa asiri."

"Amin!"


"Imaan ta aiko dazu an bata sauran invitation din."

"Ni Anty bana son ma yaje wajen!"


"Saboda me?"

Shiru tayi. Anty tace

"Ba magana nake miki ba."


"Saboda Anty Rukayya kar ta kalle ahi."

"Ummu kishi!"


"Kai Anty ina kishin yake kawai dai kawai dai."

Murmushi tayi tace

"Dole kuyi hakuri abu dai na rana daya Allah zai kiyaye miki shi kinji, ki kwantar da hankalin ki insha Allahu babu kishiya agidan ki"


Murmushi Ummu tayi tace

"Nagode Anty."

"Amman fa sai kin dage Ummu!"


"Dame?"

"Kula dashi mana ki kula da komai nasa cin sa shan sa suturar sa farin cikin sa da bakin cikin sa,  ki taya shi son abinda yake a so ki taya sa kin wanda yake so in har bai kaucewa kaida ba ki zama mai bashi farin ciki da kwanciyyar hankali mai kore masa damuwa. Dole ki ajiye kunyar nan ki tallafi mijin ki, ki bashi abinda ya rasa a baya wato soyayya da tausayi ki zama uwa, 'kawa, kanwa,  matar sa ki zama abokiyar shawarar sa mai masa addu'a. Ki kansance macen da zai kalla yaji sanyi.

Dole ki rike tsabta duk da nasan kina da ita amman ki rike ta kam da kalolin girki kwalliya da kamshi. Komai naki ya zama na daban yadda zakiyi tafiya a gaban sa ta zama daban yadda zakiyi magana  a gaban sa komai dai ina fada miki.

Sannan shiga kala kala mai kyau da jan hankali ta safe daban ta rana daban sannan ko ya fita kina kiran sa ko tura masa sakonni na ban gajiya da salon soyayyar ki.

Duk da na lura da ya kamu da son ki amman kema sai kin kara tusa masa son naki. Ta hanyoyi da dama Ummu. Ki kwaci yancin ki ke matar sa ce kuma ke macece kina da abin so dan kinfi Rukayga nesa ba kusa ba kinsan a gida duk kin fimu kyau to kiyi amfani da kyan ki ilimin ki da tarbiyyar ki ki kara damke zuciyar sa.

Ki so Maman sa nasan kina son ya'yan sa to ki kara dan dama nasan kema ya'ya kine gashi aure ya hada ku da baban su dole ki kara son su da yan uwan su.

Bansan ki da rowa ba dan haka kina bayarwa da kyautata wa idan kina da shi,  Ya'yan nan amana ne ki rike masa su amana Ummu.

Nasan ki kina da hakuri da juriyya dan haka ki kara zaman aure ba zaman wasa bane da za ace za a fara ga lokacin kare shi muna fatan mutuwa ce kadai zata raba ku dan baka dole ki  kara dantse da riko da hakuri da juriyya.

Ki riki ibada komai ya faru kai kukan ki ga Allah ba mai magance miki sai shi kowa kika fadawa da addu'a zai taya ki dan haka ki kara riko da ibada da karatun Alkur'ani.

A bangaren gyara kanki kada ki yadda da wasu maganin mata komai zan rubuta miki wanda zaki hada da kanki in ma kayan zaki siyo ki bayar a hada miki ki bada kada yafi wanda zai kara miki lafiya kuma ya zama kamar abinci da kariya ga lafiyar ki,  ki kama yawan shan fruit da pepper soup inda hali in babu su ko gyada da zogale da aya ma sun wadata.

Sannan ki kasance mai yin ado a jikin ki kada ki bari yasan lokacin zuwa unguwar ki ko da yaushe ya zata unguwa zaki. Lalle da gyaran kai kina yin su akai akai. Haka nan gyaran jiki kina gani duk wata sai an min dan Allah Ummu duk abinda kika ga ina yi mai kyau kiyi koyi dashi marar kyau ki watsar ki dauki halin Umman mu nasan zakici riba.

Sai abu na karshe da zan kara fada shine kayi hakuri zaman aure dole sai da hakuri.

Kunya na fada miki ki cire ta ki ajiye ta gefe indai a gun faranta masa ne akwai gun da zaki dauko ki saka dan ta zama ado amman a gado gun bashi hakki ki nuna masa ke gwana ce kinji ko.

Bayan kwana biyu zan rubutu miki abubuwa masu yawa wanda a lokacin da abun yazo ina nufin ki fara amfani dashi kenan. Allah baku zaman lafiya da zuria mai albarka. Allah ya baki ladan biyayya yasa kici ribar ta kema ya baki masuyi miki biyayya hakika ko mu yayyen ki muna alfahari dake bare iyayen ki kuma na tabbata ya'yan ki da mijin ki zasuyi alfahari dake ummu kamar yadda alumma muslumai ma zasuyi Allah ya miki albarka!"


STORY CONTINUES BELOW

Rumgume ta Ummu tayi tana hawaye tace

"Nagode Anty bani da kamar ki Allah saka miki da mafificin alheri nagode sosai ina kaunar ki insha Allahu zanyi aiki da amafani da duk abinda kika fadamin bazaki taba samu na da yin kuskure ba."


"Allah miki albarka."

Yaa Suleiman da shigowar sa kenan yace

"Ah ah yau an fara missing ne Sweet nah."


Janye Ummu ta farayi Ummu ta kara kamkame ta tana kuka. Zama yayi ya kalli Zainab yace

"Me kikai mata?"


"Me zan mata Yayan mu."

"Gashi nan tana kuka!"


"Kukan shagwaba ne kasan Ummun ai."

"Ummu fadamin me tai miki?"


Kai ta girgiza yace

"To zo nan."

Mikewa tayi ta koma kusa dashi ya sa handkerchief ya goge mata hawayen yace

"Menene na kukan Ummu ai muna tare kada ki damu ko yaushe kike son ganin Antyn ki zata zo kinji."


Kai ta gyada yace

"Allah sanya alheri ya bada zaman lafiya."

Anty Zainab ce ta amsa ita tai kasa da kai. Yai murmushi yace

"Ummu sarkin kunya akwai abinda kike bukata ne?"


Kai ta girgiza yace

"To dazu munyi waya da mai dinki yace ya gama anjima zai kawo."

"Allah kaimu."


"Muje ka watsa ruwa ko?"

Mikewa yayi ta bi bayan sa sukai cikin daki.


Akan kujera ta kwanta tana juya maganganun Antyn ta tana daukar su daki daki. Wayar ta dake daki ce ta fara kara dan Anty Zainab ya fito dan kawo mata.


*

**

***

****

*****

******

Da yamma bayan Khaleel ya tashi Dadyn sa ya shiga ya same shi a kwance. Zama yayi yana fadin

"Ya jikin Mu'azam?"


"Alhamdulillah!"

"Masha Allah yanzu fada min damuwar ka."


Kallon sa yayi kai Dady ya gyada masa yace

"Yes kasan condition din da kake baya son saka damuwa but saboda me baka kiyayewa?"


"Dad...."

Hannu ya daga masa yace

"Just tell me your problem!"


"Dady zan fada maka amman ina son ka bani lokaci!"

"Wane irin lokaci?"


"Zan fada maka i promise!"

"Why not now?"


"Please Dad!"

"Is ok amman ka daina saka damuwa a ranka ka sani duk abinda kake so zan maka shi sai dai in yafi karfi na ko ya sabawa Allah amman zan baka ko wanne irin farin ciki kake nema."


"Thank you Dad!"

"Kar ka damu in kana da damuwa ka fada min kawai."


"Insha Allah."

"To tashi mu sauka kasa ko?"


Mikewa yayi suka fito tare suka fito falo suna hira. Hajiyar dake zaune tana waya ta zuba musu ido tana fadin a ranta

"Like father like son!"


Saboda yadda suke kama komai na Khaleel irin na mahaifin sa ne kama murya tafiya komai dai. Itama shi yasa take son sa sosai.


"Ya jikin Son?"

"Da sauki!"


"Allah kara sauki!"

"Amin thanks!"


Mai aiki ta kwadawa kira tana fitowa tace

"Ki gyaro min fruit din nan ki kawon yanzu!"

"Insha Allah!"

Ta juya.


Ba ayi minti goma ba ta dawo da katon tray wanda akai akwai kwaton bowl sai kananun da fork. Ajiyewa tayi tai serving kowa sannan ta bawa Khaleel amsa yayi yace

"Sannu!"


Ta bawa Hajiyar wacce ita kuma ta mikawa Dad sannan ta amshi dayan da tayi serving.


Suna cikin sha Khaleel yace

"Dad ina son gobe zanje kano!"

"Kano?"


Kai ya gyada yace

"Yea Dad!"

"Me zakai a kano?"

Hajiyar ta fada zuciyar ta na bugawa.


"Neman aure zani. So please i need your prayer Allah yasa a dace!"

Dafashi Dad yayi yace

"Insha Allah but wacece wannan yarinyar!"


"Dad in na dawo zan fada maka."

"Ok amman ai da ka bari ka kara jin sauki ko?"


"Dad in na ganta zanfi jin sauki duk missing nata ke damu na!"

"Are you sure?"


"Yes!"

"Gud!"


"Ni dai bana so kaje. Ka fadi yar wacece sai a nemar maka auren ta."

Hajiyar ta fada.


"No ba haka ake ba yanzu ai. Ki barsa yaje su fara ganawa daga baya manya sai su shiga nima na kosa naga auren ai Yaro na ya girma."

"Amman Alhaji.."


"Kinsan bana son ana matsawa Khaleel ko ki barsa yayi abinda yake so."

"To daman tambayar sa zanyi a ina ya ga matar?"


Kallon Hajiyar Khaleel yake da mamaki sosai wai meyasa take tsoron relation din su da Sakina ne? Murmushi yayi yace

"Dad anan Abuja muka hadu bai fi two week ba ta koma gida so ni kuma da gaske i love her. Dad zaka shigen gaba"


"Why not? Indai tana da dabi'u masu kyau da asali anwuce wajen."

"Thank you Dad!"


"You are welcome."

Hajiyar dai shiru tayi. Ta rasa ta ina kuma zata fara.

Suna zaune aka kira magrib tare suka tafi da Dad da Khaleel Hajiyar kuma tayi daki. Waya ta dauka ta fara kiran Hajiya Habiba. Tana dauka tace

"Dear da matsala fa."


"Tame?"

"Akan Khaleel da Sakina."


Tsaki ta saki tace

"Ke fa dama an fadamiki ki kwantar da hankalin ki ko ta malamai sai an raba in abun yaki kuma akwai wata mafitar ki kwantar da hankalin ki."


"Alhaji ya dawo kuma nasan Khaleel zai fada masa. Kuma kinsan Alhaji zai yi kome Khaleel ke so."

"Kyale su daga Alhajin har shi Khaleel din duk zasuyu bagani.'


"Tayaya?"

"Kedai zamuyi magana kije kiyi sallah ana kira."


"Ok zan kira anjima."

Ta fada ta zuba tagumi sai kuma ta mike ta shiga ta dauro alwala. Sallah tayi ta zauna tana addu'a Allah yasa Khaleel ba zai auri Sakina ba.

Sai da akai ishai suka dawo anan falo suka samu Hajiyar ta kara cin wata kwalliya. Nan ta musu jagora zuwa dining suka zauna suka fara cin abinci. Suna gamawa suka koma Falo khaleel yai dakin sa.


Wanka yayi ya saka kayan bacci ya dauki waya yana kiran layin Sakina. Har lokacin a kashe wayar yai cilli da ita ya dafe kai.


Kofar dakin aka bude ya dago da sauri Dad ne da Doctor suka shigo. Dad yace

"Me yake damun ka Mu'azam ko kan ne?"


Kai ya hirgiza yace."bacci zanyi "

"Ok!"


Doctor ya kalle shi yace

"Ya jikin?"

"Alhamdulillah"


"Allah kara sauki. Kan yana ciwo?"

"A'ah!"


"Ok ka cigaba da shan maganin zan shigo da safe. Allah kara suaki"

Suka fita da Dad. Kan gado ya hau ya ja bargo ya rufe yana Allah Allah gari ya waye ya tafi kano neman Sakina.

Kwanan su daya aka sallamo su aka daura ta akan magunguna Kabir shi ya biya komai ya siya mata magani ya maida su gida. Daga Ummah har yayen ta kowa addu'a yake masa da saka masa albarka.


Halima kuwa jikin ta yayi sanyi tana tunanin ina Isma'il to ko shine ya saka Kabir yi musu wannan dawainiyyar.

Daki aka kai ta ta kwanta. Suna ajiye kanyan suka Hafsa tayi dakin Mamah bacci ta samu Farisa nayi. Dakin ta gyara ta shiga tai wanka ta fito ta shirya cikin doguwar rigar atamfa. Kan gado ta hau dan ta samu itama ta huce gajiyar asibiti.


Tana kwanciyya ya kira wayar dauka tayi ta kai kunne

"Sauran awanni naga my princess?"

"kai Deedat ai kaje gida ka huta ka gaida su Momy ko?"


"Bayan naga lafiya my wife ba."

"Wife naka tana Abuja fa."


"Soon you too will be my wife!"

"Hmmm!"


"Eh!"

"Naji ka bari kaje ka gaida su Momy nima yanzu muka dawo daga asibiti bacci nake ji!"


Agogo ya kalla yace

"Yanzu sha daya da kwata nasan nan da daya ina kano by then ai kin tashi ko?"


"Sai biyu zan tashi."

"Sallar fa."


"Ai ita zan tashi nayi!"

"Kenan ni sai after 2 za aganki!"


"After 4 dai."

"Haba dai ba zan iya ba. Ki shirya biyu ina hanya insha Allah."


"Allah kawo ka lafiya!"

"Amin my wife me kike son na kawo miki?"


"Bana bukatar komai nagode."

"Hmmm shikenan sai na karaso miss you."


Tai murmushi ta kashe wayar ido ta lumhse tana jin son Ahmad na kara yawa da shiga can kasan zuciyar ta. Gyara kwanciyya tayi ta fara baccin cikin nutsuwa da kwanciyyar hankali.

*

*

*

Kabir ya tafi da tunani kala kala a ransa na yadda zai yi da Halima. Office ya wuce yana zuwa Sadiya ta kira shi. Dauka yayi suka gaisa sannan tace

"Ya me jiki?"


"Da sauki an sallame su ma."

"Masha Allah anjima zanje sai kai min kwatance."


"Shikenan nagode."

"Amman kana lafiya kuwa?"


"Me kika ji?"

"Sai naji kamar kana da damuwa."


"Ban da ita kawai dai na gaji ne."

"Haba dai kai ragone kenan yaushe safiyyar tayi har zaka ce ka gaji "


Yai murmushi yace

"Sannu Jaruma."

Tai murnushi itama tace

"Fadi da kyau kuwa kasan acan na kwana sai 8am na dawo gida kuma ko bacci ban koma ba acan ma banyi ba."


"Masha Allah lallai jaruma ce ke."

Tai murnushi tace

"Ba sai ka fada ma. Bari naje na kwanta na huta zuwa anjima in leka me jikin kai mata sannu kan naje."


"Insha Allahu!"

Ya kashe wayar yana bin wayar da kallo. Shi dai Sadiya na burge shi kawai bai san dalili ba.


Waya ya dauka ya kira Hajara ta dauka ta kai kunne tayi sallama, bayan ya amsa yace

"Ya me jikin?"


STORY CONTINUES BELOW

"Tana bacci!"

"Ba abinda take bukata?"


"Babu!"

"To in ta tashi tana bukatar wani abu ki fada min."


"Insha Allahu!"

Sukai sallama ya maida kai ya kwanta a jikin kujera yana juya wani abu a ransa dashi kadai yasan menene.

*

*

*

Daya saura ya shigo kano gidan su ya isa ya kai tsaye yana zuwa yai parking ya fito ya bangaren Momyn sa. Bata nan sai Basma dan haka yace ta kai masa abinci bare yaje yai wanka.

Ya tafi dakin sa,  wanka ya shiga yayi ya fito ya tada sallah. Yana salah ta shigo ta ajiye masa abincin sa. Zama tayi ya idar tace

"Zuwa baka fada mana ba ina sister!"


"Tana gida nima ban san da zuwan ba sai jiya kuma ina busy shiyasa ya kowa da kowa."

Ya mike ya fara cin abincin sa Basma na masa hira. Bayan ya gama ya mike ya shirya cikin wata sabuwar ash kalar shadda yai fesa turare sannan ya murza hula da agogo yai kyau ya fto kamar ango.


Waya ya dauka ya fita. Cikin gida ya shiga ya samu Basma na zaune yace

"Wai ina Momy ta tafi ne har yanzu bata dawo ba."


"Biki taje."

"Ok ni zan fita."


"Amman Yaya ina zaka kaci wannan kwalliyar kamar wani sabon ango."

"Shine ai dan neman aure zani!"


"Aure kuma?"

"Haram ne?"


"A'ah amman yaushe kayi auren!"

"To ko yau nayi gobe nace zan kara ba kyau ne."


"A'ah Yaya amman..."

"Kimin shiru ki tayani da addu'a kawai."


"Insha Allah!"

"Yauwah Little sister zan je me zancewa Antyn taki?"


"Agaishe ta kan nazo da kaina."

"Gud girl."


Ya juya ya fita anan compound ya bude boot din motar sa ya saka masu aikin su dauki buhun dankali daya da kwaryar doya daya sauran kuma aka rufe ya bar gidan.

*

Karfe daya shima ya fito office sallah sukai sannan ya fito ya isa Yahuza suya ya siyo mata nama da kaza masu yawa sannan ya tsayaa a Rufaida yoghurt nan ma ya siyo mata a hanya ya siyi fruit sannan ya wuce gidan su Halima.

Bayan yai parking ya kira number Hannun Hajara ta dauka yace

"Ina waje kizo!"


Sannan ya kashe batai minti uku ba ya fito suka gaisa yai mata ya me jiki. Kayan ya kaso ya mika mata amsa tayi tace

"Muje ka ganta mana."


Kai ya sosa tace

"Ba komai muje."

Dan dai shima yana son yaga a wane condition din take ne yasa ya bi bayan ta. A falon Umma sukai sallama ya shiga kan daddumar da aka shimfida masa ya zauna kan sa a kasa suka gaisa da Umma da Sakina. Nan Umma ta karai masa godiya kan sa akasa ya kasa magana ma.

Suna shigowa Hajara tayi cikin daki. Halima dake zaune tana neman layin Isma'il ta kalla tace

"Kizo abokin Yaa Isma'il yazo."


Da sauri ta mike tace

"Tare suke?"

Kai ta girgiza sai murnar ta koma ciki ta koma ta zauna.

"Tashi muje mana"


Hajara ta fada mikewa tayi ta saka hijab sannan suja fito. Tana fitowa Umma da Sakina suka fice. Hajara ma fita tayi. Zama tayi tace

"Ina yini?"


Ya dago yana kallon ta yadda ta fada ta kara haske da kyau yace

"Lafiya lou ya jikin?"


"Da sauki!"

"Allah kara sauki!"


"Amin nagode Allah saka da alheri amman ina Yake?"

"Baya nan ne yana busy kwana biyu."


"Ina ya tafi bayan jiya na ganshi kuma fa bai daukar wayata dan Allah ka fada min in akwai matsala."


"Halima kina jina ko?"

Kai ta gyada yace

"Ki kwantar da hankalin ki ba wata matsala yanzu condition din da kike ciki baya bukatar kina saka damuwa dan haka ki kwantar da hankalin ki Isma'il na son ki kinji ko?"


Kai ta gyada tace

"To kace yana kirana dan Allah."

"Zan fada masa in nima ya dauki wayar tawa dan nima bai fiya dauka ba in ya tafi."


"To shikenan."

"Yanzu akwai wata matsala ne?"


"Babu komai!"

"Bakya jin komai?"


"Bana ji!"

"Ba abinda kike bukata?"


"Bana bukatar komai nagode."

Mikewa yayi yace

"Shikenan zan wuce!"

Ya saka hannu a aljihu ya ajiye mata dubu goma yace

"Ko zaki bukaci wani abu Allah kara sauki."


"Dan Allah ka barshi."

"Bana son inyi kyauta ace ba aso Halima."

Kai tayi kasa dashi tace

" kayi hakuri."


Yace

"Yauwah koke fa."

"Nagode!"


Ta fada. Yai murmushi yace

"Allah kara miki lafiya."


Ta amsa da Amin ya fice. Hajara dake tsakar gida tabi bayan sa tana dadai masa godiya


Yana fita Sadiya ta kira shi a waya dauka yayi tace

"Ka turon fa."

Tura mata yayi ya shiga mota ya bar unguwar.


*

Karfe daya ta farka ta shiga tayo alwala ta tada sallah tana zaune akan sallaya Farisa ta shigo ta zauna a gefen gado sannan tace

"Ashe an sallamo ku?"


"Wallahi na shigo naga kina bacci."

"Bacci  da ba dadi ba yar AC a dakin."


"Ai sai ki saka mana kan muyi aure ko?"

"Wai kema kin fara tunanin aure."


"To Anty Hafsat tunanin me zanyi in bashi ba ko wacce mace da ta girma sai wannan tunanin bama mu da va karatu muke ba shekarun mu sun kai kuma"

"Allah ko to me kika tanadar wa ya'yan naki?"


"In basu tarbiyya da uba na gari."

Tsaki tayi tace

"Baki tanadar musu komai ba kenan na jin dadin rayuwar duniya."


"Haba Anty Farisa ya zaki ce ban tabadar musu komai na jin dadin rayuwar duniya. A yara menene dadin rayuwar duniyar in ba iyaye na gari da tarbiyya ba sai ilimi wanda zasu tsaya tsayin daka dan ganin mun basu su tsira da kan su."

"Uhmm ko tayaya zaki samu kudin basu ilimin?"


"Allah zai bamu!"

"Meyasa yanzu ba zaki tashi kinema ba."


"Ina kokarin nema!"

"Tayaya bayan kin zubar da makaman yakin ki."


"Ni ba ta wannan hanyar ba."

"Ta wacce kenan?"


"Yaya Fauziyya ta siya mana jamb ni da ita da Yaya zamuyi mu koma makaranta."

Tsaki ta saki tace

"Its too late."


"Like how?"

"Kun girma"


"Haba dai Anty Farisa ai ba a girma da karatu kuma mu fa jami'a zamu shiga tinda mun gama secondary so ai ko secondary zamu ba za a ce ba za a dauke mu ba dai bare jami'a dan shekara arbain ma shiga yake."

"Ke kika sani. Neman kudi dai daya ne shine ki fita ki nema baki sha wahalar komai ba."


"Haba Anty akwai wahala mana kece kullum mu'amala da maza daga wanna  sai wancan!"

"Shine me?"


"Kaskanci."

"Ke kika ga haka ni cinyewa da waye wa nake gani."


"Haba Anty...."

"Bayan nan kuma ba wata wahala sai dadi a cikin ta da samun kudi ko?."


"Amman akwai dibar zunubi ko?"

Shiru tayi. Hafsa ta mike tace

"Bari naje naga jikin Halima!"


Jikin ta ne yayi sanyi amman bata jin niyyar da ta dauka zata ajiye ta.


*

Tana futa ta nufi dakin Umma ba kowa a falon sai Halima da ta jingina kan ta da bango idon ta a lumshe. Zama tayi tace

"Halima lafiya?"


Ido ta bude tace

"ba komai!"

"Ya jikin?"


"Da sauki!"

"Allah kara sauki."

Dakin ta kalla tace

"Waye a ciki?"


"Ba kowa!"

"Ok tashi muje akwai maganar da zamuyi!"


Gaban Halima ne ya fadi ta mike ta bi bayan Hafsa suka shiga bedroom din Umma.Gaban Halima ne ya fadi ta mike ta bi bayan Hafsa suka shiga bedroom din Umma.


Suna shiga ta zauna ta kalle ta tace

"Halima da wa kika taba kwanciyya a rayuwar ki?"


Ido ta zaro tace

"Me Anty Hafsa?"


"Ina nufin waye ya raba ki da mutuncin ki?"

Shiru tayi tace

"Ni ba kowa fa."


"Kinsan Allah duk da baki da lafiya zan balballa ki,  ki fada min gaskiya mu haka mu burne tare. Kinsan me?"

Kai ta girgiza. Hafsa tace

"Ciki jikin kine ya zube!"


Da sauri Halima ta dago tana kallon Hafsa sai kuma ta dafe cikin tana mamakin daman rashin ganin aladar ta da tayi na kusan wata biyu da yake yana mata wajen fourty days kan wani yazo sai ta kawo ko haka me ashe ba haka bane kenan ciki ne da ita. Jiya da ta tashi taji ciwon mara taje fitsari taga jini sai ta zata na period ne ashe bari tayi.

"Innalillahi wainna illahir rajiun."


Dakin ne yai shiru Halima banda innalillahi ba abinda take fadi a zuciyar ta komai nata ya tsaya mata jikin ta yai sanyi. Hafsa ce tayi karfin halin fadin

"Ni na rasa waye yai miki menene a lakar ki da Kabir abokin saurayin ki ya fada min komai amman ina son ki fada min kema da bakin ki."


Shiru tayi can ta ce

"Ba wata alaka tsakani na dashi domin kuwa ni a yadda na lura kamar baya sona ma da Isama'il shiyasa nima ban fiya son ma Isma'il  yana kawon maganar sa ba amman yadda Isma'il ke fada min Kabir mutumin kirkine sosai yana fada min ba halin su daya ba shi yana da tausayai da ilimi da aiki dashi. Ba wani abu tsakani na dashi nima nayi mamakin ganin yadda ya tsaya a kaina."


Ajiyar zuciya Hafsa ta sauke tace

"Cikin waye ya zube to?"


Shiru ta karayi tana jin tsoron fada

"Ina jinki!"

Hafsat ta fada.


"Na Isma'il ne!"

"Tayaya kika san nasa ne?"


Kuka Halima ta fashe dashi tace

"wallahi Anty Hafsa ni ba karuwa bace shi kadai muke mu'amala shima dan munyi alkawarin aure ne amman wallahi shima ba ason raina ba dan kar ya fada halaka ko neman matan banza."


Hannu Hafsa ta fara tafawa tana salati tace

"Dan haka ke kika fada halaka ko? Dan haka ke kika zama matar banza ko? Shin Halima ina wayon ki wane namiji ne zai fada miki haka ki yadda waya fada miki rayuwar yar gaskiya da gaskiya ce innaliahi wainna illair rajiun!"


Ta fada tana zuba tagumi sai kuma tace

"Shine ke kika zamar masa karuwar sa. To ysaya kiji duk dadin baki ne amman zan barki dashi zaki bani labarin komai nan gaba dan ke shasha ce wane namiji ne zai yi mu'amala da mace a waje sannan yace zai kai ta gidan sa? To wallahi dadin baki yai miki kawai, kuma tinda yai lalalta dake to ki tabbata ba akan ki ya fara ba da yake cewa zai tafi ya nemi matan banza yaje mana sai ke yar iska kika yadda ko? Zunubi ya kara daduwa ko? Ai gwara yaje ga wadan da suka saba akan a kara samun bata gari. Kai amman Halima me ya kai ki son abun duniya ko?"


"Wallahi a'ah Anty da gaske nake son sa shima kuma haka wannan yasa da yazo gun Baba yaki aminta ya zauna jira na duk da yana bukatar auren shiyasa fa yace in taimaka masa tinda ni yake jira in yadda dashi kuma ni na yadda Isma'il na sona dan lokacin da muka fara na daina kula sa wallahi Anty har ciwo yayi ya damu ga Hajara nan sheda ce har da kuka yazo yana min a kofar gida kuma kome ya faru Ai Baba ne ya janyo tinda yazo neman aure na wai yace nawa nake ban kai shekara goma ba dan Allah Anty wai haka. Ni nasan Isma'il yana so na zai soni a duk yadda nake."


STORY CONTINUES BELOW

"Gaskiya Halima baki da hankali kina so ki cemin kin yadda da duk abinda ya fada. Yanzu dai abu daya zuwa biyu zan fada miki ki koma ga Allah ki tuba kada ki kuma yadda in kuma yana son ki yake ta kara fitowa a karo na biyu kice Baba yace ya turo tanan zaki gane in da gaske yake. Dadin abun cikin nan ya zube yanzu inda bai zube ba wane hali kike taunanin zamu shiga? Ki godewa Kabir domin ya tsqyaa miki da kudin sa da jikin sa da aljihun sa Allah ne kadai zai saka mishi."


"Haka ne dan yanzu ma ya barnan!"

"Halima ki karatun ta nutsu Allah ne ya rufa miki asiri Kabir ne ya kaimu asibiti shiyasa suke zata mijin kine amman ai kinga da ansha kunya. Kuma ba komai yai sanadiyar zubewar cikin ki ba sai damuwar da kika saka a ranki da maganin da kika sha wanda Baba ya baki. Allah kiyaye gaba ya yafe mana ya shirya mu baki daya."


"Amin Amin Anty Hafsa na gode."

Ta fada tana kuka.

"Yanzu ba lokacin kuka bane lokacin neman gafarar Allah ne sannan ki nutsu a rayuwar ki kiyi hankali ki gane me son ki."


"Insha Allahu."

Ta fara goge mata hawayen tana fadin

"Ki daina kukan to."


Kai ta daga. Sallama Hajara tayi ta shigo ta tsaya kallon su tace

"Lafiya? Ko jikin ne?"

Kai Halima ta girgiza da sauki. Tace

"Ok Wannan ta jiyan ce tazo duba ki."


"Ok gamu nan!"

Suka mike suka fita. Sadiya suka gani zaune a inda Kabir ya tashi. Tana ganin su ta fara murmushi tace

"Ah ai patient ta warware masha Allah."


Zama sukai Hafsa na murmushi tace

"Gaskiya kam Alhamdulillah ina yini?"

"Lafiya lou ya me jikin?"


"Da sauki!"

"Masha Alah kara sauki."


"Amin!"

Halima tace

"Ina yini?"


"Lafiya lou takwara ya jikin?"

"Alhamdulillah!"


"Allah kara sauki!"

Suka amsa da amin dukka har Sadiyan. Umma ce da Farisa suka shigo. Nan suka gaisa tai musu ya mai jiki sannan ta tura musu manyan ledar da ta shigo dasu tace

"Ba yawa Allah kara sauki."


Suka amsa sa amin. Mintin ta goma ta mike tace

"Ni zan tafi."


"angode Allah saka da alheri. Allah kiyaye hanya."

"Amin!"

Hafsa ta mike ita da Hajara suka rakata har bakin mota sannan suka juyo bayan sun mata godiya.


Cikin gida suka dawo Hafsa ta shiga daki wayar ta tagani tana haske tana dubawa taga Ahmad ne dauka tayi tai sallama yace

"Ina kika shiga ne ina ta kira!"


"Wallahi na fita naje gun Halima ne!"

*

**

***

****

*****

******

"Aunty ana kira. Aunty ana kira zata tsinke!"

Da sauri ta mike zaune amman kan ya kawo ta tsinke tana cikin duba wanda ya kira kiran nasa ya kara shigowa. Mikewa tayi tai cikin dakin ta.

"Amarya ta!"

"Hmmm Yaa Muhammad nifa ba amarya bace wata nawa ko ince shekara nawa da aure?"


"Waya fada miki? Ai ni har abada ke amarya ce aguna Sweetheart."

"Hmmm!"


"Da gaske nake. Kuma ke banda abinki. ina kika taren ma da zaki tashi daga amarya Sweetheart."

"Hmmm bamu gaisa ba fa ina yini?"


"Lafiya lou ya gimbiyar tawa take. Jibi yanzu kila naganki!"

"Kai Yaa Muhammad ai ka bari sai a walima kawai."


"Ina ba zan iya ba."

"Hmm au dazu Antyn tace an kawo kaya Yaa Muhammad kashe kudin yai yawa ai."


"Haba dai me akai Ummu kin cancanci fiye da haka Allah dai ya buda mana in miki a abinda yafi haka."

"Nagode Allah kara bude."


"Amin!"

Nan ya dinga janta da hira sun jima sannan sukai sallama.


*

Yau Yaa Muhammad zai dawo Hajiyar sa sai murna take ita da ya'yan sa. Ta shirya masa abinci mai dadi wanda yake so.


STORY CONTINUES BELOW

Karfe daya ya sauka a gida Nigeria kanin sa ne ya isa ya dauko shi. Yadda Muhammad ya koma ya kara haske fatar sa ta murje yayi yar kiba mai kyau inka ganshi sai ka rantse ba shi bane.


Haka kanin sa ya dinga fadin

"Yaya kaga yadda ka kara kyau kuwa kai amman saudiyya ta amshe ka."


Yao murmushi yace

"Usman kenan"


Suna shiga gida yaran sa suka taho suka rungumeshi suna fadin

"Oyoyo Abbi!"


Ya dauke su daya bayan daya ya na kissing nasu. Sannan ya ajiye su ya gaisar da Hajiyar sa da taje ta murmushi. Gidan su da yasa aja rushe aja canja masa fasali ga bangaren Hajiya daban bangaren su shi da kannen sa daban duk dashi ba zama zai ba amman an ware masa dakin sa an zuba masa duk abin bukata. Daki daya ne da bandaki a ciki sai gado da kayan kallo.


Yana shiga ya cire kaya ya shiga yai wanka ya fito ya tada sallah. Yana idar wa ya fara neman layin Ummu. Amman bata dauka ba sai da ya kira sau biyu bata dauka ba sannan ya kyale ta.

Abinci Hajiya ta kawo mishi ya zauna yaci ya koshi. Tsarabar yaran ya kawo musu kowa ya dauka yana wasa da abin sa  na Hajiya ya bayar da kannen sa da wasu yan uwan nasa. Bayan ya gama sannan suka zauna shi da Hajiya yana nuna mata kayan da ya siyowa Ummu.


Hajiya tace

"Sunyi kyau"


"To Hajiyata ga kudi nan ina son a yau a hada mata kayan lefe gobe akai gida da safe kan ta tare ko?"

"Daman ina son nai maka maganar lefen kuwa!"


"Toh!"

"Ni da har na fara hadawa!"


"Haba dai A'ah Hajiyata ga kudi nan ki kwashe naki ki siyo abinda ya kamata ai da kinyi yanzu kuma ni ya kamata nayi."

"A'ah Muhammad kai fa da nane nauyin ka yana kaina dan haka dole na sauke."


"Hajiyata ai yanzu mun girma mu zamu dauki nauyin ki dan Allah kiyi hakuri tinda da akwai ba matsala da babu ne shine."

"To Allah yayi albarka."


"Amin!"

Ya dauko jaka guda yace

"Wannan na yayar Ummu ne da ya'yan ta."


Sai wata jaka yace

"Wannan kuma na Alhaji mahaifin Ummu ne da Umman ta."


"Masha Allah ai sun cancanci fiye da haka Muhammad dan Alhaji ya maka abinda ko uban ka sai haka. Allah ya kara girma ya baku zaman lafiya."

"Amin!"


"Yauwah Hajiyata munyi magana da su Ummu gobe za ai walima dan haka sai a fadawa yan uwa kuma ya kamata kuyi wani abun da zaku raba ko?"

"Muhammad ai da ka barsu su sunyin kawai mu ba sai an musu gayya ba."


"Kada ki damu Hajiya ai akwai duk abinda ake bukata ba matsala munyi magana da Usman za ayi order duk abinda za a raba dan haka ki a aika din kawai."

"To shikenan ya zancen gidan da zaku zauna."


"Hajiya na siyi fili a can rigiyar zaki babban fili ne na saka an mana gini har da sashen ki daman so nake na dawo na kaiki ki gani sai a miki jere sai suma su Ummun suje ayi nasu ko?"

"A'ah Muhammad ni ba inda zani ka barni anan kawai nan gida ya ishe ni nayi rayuwar ta."


"Hajiya dan..."

"Muhammad dan Allah ka kyale ni na karasa rayuwa ta a gidan miji na da ya gina ni gyaran da akai da tanine ma ba za ai ba ai tarihi ne nan gidan ko da yaushe ina tuna irin rayuwar da mukai da mahaifin ka gwara nai zamana akan me zan koma can wajen matan ka nai muku me? "


"Hajiya to menene a ciki!"

"A'ah ni dai a barni anan kawai Allah baku zaman lafiya ya sanya alheri."


"Amin."

Sallah la'asar akayi dan haka ya mike yace

"Zanje naga gidan daga nan zanje gun Alhaji na basu keys din aje ayi kafi."


"To sai ka tambaya yaushe za ai kafin dan mu musu abincin kafi ko?"

"Insha Allahu."


Ya fada yana fita. Sallah sukai sannan ya koma ya dauki kayan da yai musu tsaraba. Yace Hajiya ta fito dan tare zasu taga gidan. Usman ya kira yace

"Ina motar ne?"


"Tana can gareji."

"Muje mu dauka ko? Dan za muje can rigiyar zaki da gidan su Ummu!"


"To!"

Can suka nufa ya dauki sabuwar motar sa da sai daukar ido take golding kala mai kyau daga gani zatai tsada dan tayi kyau sosai kuma modern ce.


Suna shiga yai addu'a sannan suka nufi gidan ya dauki Hajuyar sa,  suna daukar ta suka nufi can gidan nashi dake can rigiyar zaki. Gida ne katon gaske yana dauke da part biyu daya na Hajiyar sa da tace bazata zauna ba sai nasu.

Compound din katon gaske ne an kawata shi da shuke shuke masu kyau inda da ka kalla sai ya burge ka ya baka sha'awa.

Sai bangarori dake can nesa da compound din da zai iya daukar manyan motoci fiye da guda goma. Bayan bangarori biyu a can gefe akwai boys quarters bayan gidan kuma akai dan karamin garden wanda akai shuke shuke da gun shakatawa har da su liluka.

In ka shiga bangaren nasu katuwar barrender ce da aka rufe saman ta da blue roofing sai tukunyar shukoki wajen yai kyau an dan saka kujeru a wajen ga iska dake kadawa. Kofa ce in ka bude zata sadaka da katon falo akwai kofofi biyu daga bangaren dama da hagu sai wasu dake facing naka guda biyu.


Wanda ke facing naka toilet ne da kitchen na bangaren dama bangaren mai gidan ne bedroom ne guda biyu da falo sai dan sitting room dake da kofa can main compound din.

Bangaren Ummu kuma two bedroom ne da two parlour ko wannen daki da bandaki sai wani karami shi kadai shima da toilet haka nan akwai wani kitchen karami a bangarrn ta.


Gidan yasha fenti ya sha tiles an saka masa AC da fanka da fitilu masu kyau tin kan ayi kafi gidan yai kyau sosai. Shi kan sa Muhammad gidan ya burge shi. Haka ma Hajiya sai saka albarka take tana masa addu'a.


Sai hudu da arbain da biyar ya maida Hajiya da Usman sannan ya wuce gidan su Ummu. A kofar gida ya tsaya ya aika a fadawa Abbah shine yazo. Abba da kansa ya fito yana fadin

"Lale marhabun Muhammad kuma sai ka tsaya shiga muje ai gidan kune."


Durkuusawa yayi zai gaishe shi yace

"Muje daga ciki kaji."


Mikewa yayi suka shiga har falon Abbah. Bayan sun zauna yai kasa da kai ya fara gaisar da Abbahn Abbah ya amsa yana fadin

"Ka dawo lafiya ya gajiya hanya?"


"Alhamdulillah Abbah ya gida da aiki?"

"Alhamdulillah."


Kayan ya ajiye yace

"Ga wannan ba yawa nasu Umma ne da naka!"


"Madallah Muhammad an gode Allah kara budi."

"Amin Amin."


Abbah yace

"Ya zancen kafi Muhammad nace za aje a yi a gidan da na baka kace a dakata."


Post a Comment for "WANNAN RAYUWAR CHAPTER 10"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...