UQUBAR UWAR MIJI COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

UQUBAR UWAR MIJI COMPLETE

UQUBAR UWAR MIJI COMPLETE

- - Post a Comment

 UQUBAR UWAR MIJI COMPLETE


🐲🐲🐲
          HUQUBAR UWAR MIJINA
🐲🐲🐲
(Based On True Life Story)(Full of sorrow)

STORY Nd WRITTEN By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist.
GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION.

❄We are bearers of soo golden a pen, we write assiduously perceive no pain so magical our creative golden pen, be hold our words, A product of our pen savour our words for it will cause u no pain❄
Dedicated to


My Mother Za Arab lady Royal blood sayings

Alhamduliilah Allah na godemaka dakasake bani wani dama na sake wani rubutu,Masoya nadawo gareku da littafina mai taken HUQUBAR UWAR MIJINA,wannan labari ba k'irkira bane a gaske yafaru hakan saide abinda baza'a rasaba na k'ari amma tabbas hakan ya faru,masoya Ku biyoni donjin menake tafe dashi wane sak'o nakeson na isar,wane irin halayyane aciki.Ku kasance tare da YOUNG NOVELIST.+

A Kullum burina shine na faranta muku ,ni nishad'antar daku da fad'akar daku,Allah yabamu ikon k'aruwa da Juna Ameen.
(1)
Suana Fatima Abbakar ni Y'ar asalin garin Yobe ce,daga mahaifina har mahaifiyata duk Y'an yobe ne.

Ni farace kyakkyawa ajin farko ga diri ga kyau komai nawa dai-dai,Nima  Khadeejaht Nashaida hakan wlh,don gaskiya Anti Fatima badaganan ba.
Ita mutum ce mai son Addini ga kyauta ga fara'a,ga tausayin mutane ko nima Deeja nashaida,akwaita da son yara bak'adanba.

Inada shekaru 27 amma banyi aure ba saboda wasu kalubalen danake fuskanta,don Masha Allah inada farin  jini duk Wanda yace"...yana sona tofa ya dinga yimin hidima har Y'an uwansa suyi zaton nayi masa wani abun ne."
Mama ta kasancewata ya d'aya gareta yasa kullum tana cikin addu'ar Allah yabani miji nagari,ya kareni daga sharrin mutane.
Baba nama  ba'a barsa abayaba suna sona kuma sun bani tarbiyya  ta gari,nakasance cikin kamun kaii kullum.
Haka muke rayuwa acikin gidan dayake mallakin Baba na,gidane mai d'akuna hud'u,na Baba daya Mama daya sai nawa sai na bak'i,se Babban parlour da tsakar gida, Alhamduliilah Baba na yana rufin asiri yana bani duk abinda na buk'ta.

Toh fans ya kuka gani ne.
Miye ra'ayinku akan wannan littafin nawa.
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Royal blood typing
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

🐲🐲🐲

HUQUBAR UWAR MIJINA

🐲🐲🐲

(Based on true life story) (full of sorrow)


Story Nd Written By

Khadeejaht Hydar

Young Novelist

✍✍✍✍✍✍✍✍

GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION

✍✍✍✍✍✍✍✍


❄We are bearers of soo golden a pen, we write assiduously perceive no pain so magical our creative golden pen, be hold our words, A product of our pen savour our words for it will cause u no pain❄

Dedicated to

Abdallah Ibrahim

Tnx 4 everything.

(2)&(3)

To bana zuwa ko'ina daga makarantar islamiyya se gida,niko irin bikinnan ma bana zuwa.

Toh akwia wani saurayi a layinmu mai suna Khamis,tunba yau ba yanuna yana sona amma nak'i amincewa dashi saboda maganganun danakeji akan mahaifiyarsa.

Wata rana na dawo daga islamiyya ina tafiya cikeda nutsuwa ina maimaita hadda ta,kawai sainaga mutum a gabana.

Fuska na d'aure nace"....Malam lafiya ina tafiya zakana taremin hanya, se yace"...wlh yau ko marina zakiyi sekinmin magana."

Ganin yak'i bani hanya nawuce ga hankalin mutane yafara zuwa kanmu yasa nace"....yanzu me kakeso ?,yace"....yauwa so nake kibani numbarki."


Nace"...a gaskiya banda waya,saboda lokacin banda waya Sam banda ra'ayinta,yace"...tunda bakida waya kibani izinin zuwa gunki anjuma."

Dakyar na amince masa tukun yabani hanya nawuce,ina zuwa gida nayi ayyukana na kwanta.

Se bayan la'asar na farka da sauri na s'auka naje nayo alwala nayi sallah,daganan kuma nafara karatu har magrib tazo.


Bayan isha'i muna zaune a parlour akace ana sallama dani,abin mamaki tabawa su Mama wai yaushe nafara kula samari amma basuyi maganaba.

Hijab nasaka nafito waje,yana zaune akan wani dakali a k'ofar gidanmu, da sallama na k'arasa gun na zauna d'an nesa dashi tare da gaidashi.


Bayan mungaisa yace"....wato Fatima abinda nake shirin fad'amiki ba zancen wasa bane,Fatima tun ranarda naganki naji na kamu da sonki dafatan zakiyi na'am da zancena."

A hankali nace"...nagode da nuna soyayyarka agareni amma....,bank'arasa magana ba yace".....kinason kice matsalar Mahaifiyata ko?,to wallahi ta amincemin inhar ke zan aura."

Nace".....to shikenan Allah ya tabbatar da alkhairi nace"...Amin ngd,haba Fatima ai nine da godiya."

Kud'i yabani amma fur nak'i karba saida yace"...wato kinraina abinda nabaki ko to Allah yabani nabaki masu yawa,jin haka ne yasa na karb'i kud'in namasa godiya nashige gida."

Mama kawai na tarar a parlour nan nafad'a mata yadda mukayi dashi,Mama tace"..to Allah ya tabbatar da Alkhairi kuma kici gaba da Addu'a."

D'aki na shige nayi alwala na kwanta,kamar yadda Manzon Allah (s.a.w)yace"..... Duk wanda ya kwanta da Alwala ko macece wacce batada tsarki zata iya alwala to mala'ikun Allah zasu na nema masa gafara gun Allah harse gari ya waye.

Allah yasa mu dace Amiiin.

Toh magana ta kankama tsakanina da Khamis kuma tunda muke bantaba zuwa gidansu wai gaida mahaifiyarsaba,uhm Mata kuyi hattara gun zuwa gaida iyayen miji na farko bai kamataba na biyu wani zece muje ki gaida mamata ko saboda ansaka muku rana muje kiga gidan dazaki zauna,uhm Y'ar uwa ki gujema kanki asara.

A kwai wata yarinya saurayin da ankusa d'aura musu aure yazo har gun iyayenta wai yarinyar tazo suje ganin inda ya kama,Toh iyaye ganin aii yakawo komai se suka yarje masa,da'ita da k'awarta sukaje basu San hanyar dayabi ba.

Bayan sunje har zasu tafi seyacema yarinyar wai taje ta d'akko sak'o a d'aki bata kawo komai ba tashiga,dashigarta sai ya nuna mata bindiga ta kwanta yasaka maciji yashiga yafita ajikinta.

Yasakasu a mota suka koma toh yarinyar a hanya ta rasu, Ashe ta fad'awa kawarta meya faru,Apart from that namiji na'iya yaudarraka yasanka a matsayin y'a mace yana saninki zai fasa aurenki tunda dama abinda yakeso kenan.

Toh Iyaye mata da y'emmata ayi hattara,wata rana kema uwace yanzu ilimin Addini ya yawaita mukare mutuncinmu da darajarmu


ALLHA YA KAREMU DAGA DUKKAN SHARRI.

Manya sun shiga lamarinmu har ansaka rana,wata uku aka sa,don haka tuni anfara shirye-shirye saboda zasu aurar da Y'ar su d'aya tilo.


Nikuma nafarko na'a minta da Khamis ne saboda kowa ya masa shaidar kirki a unguwar kuma nima shaidace,kuma yana da sana'arsa Masha Allah.

Ga yacemin mahaifiyarsa ta amince,kuma dama itace matsalata.A sati sau uku yake zuwa fira saboda amfanin fira dayawa babu kyau,K'ira ga emmata Kada ki yarda mutum yana zuwa gurunki har nawani tsawon lokaci mai mike maganar aure ba kuma shi be bari kin saurari wani ba kawai yana b'ata miki lokaci a banza,daga k'arshema yak'i aurenki.


ALLAH YA KYAUTA.


To yau saura wata d'aya biki,kuma ayau aka Kawo lefe ba laifi kaya sunyi.

Kuma an musu tarba mai kyau,dukda ni ba gwanar kwalliya bace haka nad'anyi kad'an naje don gaida surukaina,Bayan mun gaisa na zauna shiru wata acikin su tace"...ah lalle amaryartamu mai kunya ce wata tace"...yo ai ta shafi Fulani."

Sallama na musu na koma ciki ina yaba kirkinsu,Toh Fatee Allah yasa hakane.


Vote.

Share.

Comment.

Like.

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

Royal blood typing

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎


Chocolate,Milk Lover.🐲🐲🐲

          UQUBAR UWAR MIJINA

🐲🐲🐲

(Based On True Life Story)(Full of Sorrow)

Story Nd Written By

Khadeejaht Hydar

Young Novelist


✍✍✍✍✍✍✍✍

GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION

✍✍✍✍✍✍✍✍

❄We are bearers of soo golden a gun, we write assiduously perceive no pain, so magical our creative golden pen, be hold our words, A product of our pen savour our words for it will cause u no pain❄

+

Dedicated to

ABDOOOUUL❤πŸ”₯One love 4 ur care nd prayers.

(4)&(5)

Ana saura sati d'aya biki ,lokacin angama wani shirye shirye komai ya kammala lokaci kawai  ake jira.

Yau takama laraba duk wani dangi nawa sun iso,wasuma daga guri mai nisa amma har sun iso,hak'ik'a naji dad'in ganinsu.

Washe  gari alhamis yakama saka lalle,haka akasamin lalle ma a al'adance.


Washe gari da safe ran juma'a jama'a suka shaida d'aurin aurena da Khamis Wanda d'aurin auren yasamu halartar mutane dayawa daga ko'ina saboda Alhamduliilah Baba na yanada jama'a.

Ba'ayi wata bidi'a ba  amma anyi walima anci ansha an k'ayatar,muna dawowa gida na shirya cikin shadda mai tsada da sark'ar gwal da d'ankunne da abin hannu duk iri d'aya.


Haka akazo tafiya dani amma fir nak'i fita ina kukan rabuwa da iyayena ,haka naje na rungumi Ummana ina kuka kamar anmin mutuwa itama kuka take tanamin fatan Allah yazaunar dani lafiya yakareni  daga sharri.


Haka aka turani cikin mota aka kaini gidana wanda babu nisa da na surukata,toh Bayan anshigar dani d'akina na shiga da k'afar da k'afar dama nayi nafila kamar yadda malamai suka nuna.


Bayan kowa ya wuce ne ango ya shigo tare da abokansa ,bayan sunyi nasihohinsu da sauransu suma suka wuce,bayan duk wani abinda musulunci ya tanada.

Alhamduliilah angona yasameni cikakkiyar budurwa,Wanda hakan yasashi k'ara mini wani girma a zuciyarsa.


Da safe daga gidan Mahaifiyarsa aka kawomana abinci,toh nikam ganin haka yasa naji inason uwarmijina nace"....Ashe abinda ake fad'a akanta ba gaskiya bane.

Uhmm karkiyi saurin yanke hukunci Fatee Ba'anan gizo ke sak'a ba


Haka rayuwa take tafiya cikin lafiya da kwanciyar hankali,har nayi sati Mahaifiyarsa ce ke aiko mana da abinci.


Bayan sati d'aya ne nafara girki,inda na girka abinci na aika mata dashi harta aikomin da sak'on gaisuwa.


Bayan wata d'aya da auranmu naje gaida uwar mijina,munsameta a zaune a parlour tana kallo.

Har kasa na tsuguna na gaidata ta amsa fuska babu walwala,gaba nane fad'i nace"....to meke shirin faruwa ne?.


Haka bandad'eba na koma gida saboda Sam kallon datake Nina dashi bangane masa ba,tundaga ranar bansake zuwa ba saboda ni mutum ce mai tsoron zuciya da hak'uri.


Cikin ikon Allah falalar arziki tafara bud'ewa mijina,to rannan yaje gun wani Malami don kaiwa sadaqa.


Bayan sun gaisa da Malamin,saboda a matsayin  kawu yake agunsa,se yace masa Khamis  zan fad'a maka wata magana matarka itace silar  da ubangiji yasa kakesamun falala matarka tana d'auke da arziki ga duk namijin daya aureta kuma Bayan haka matarka alkhairi ce ga rayuwarka don haka ka rik'eta hannu biyu don ita ba abin wulak'antawa bace.

Godiya ya masa yana mejin dad'i ya samu mata mai rik'on Addini ga sanin yakamata,daya dawo gida ma cikin farinciki yake.


Toh bayan Wata shida da auranmu  abubuwa suka fara canzawa daga uwar mijina saboda sam yanzu ta tsiri wani hali saita zo gidana tayini tana masifa,koda yayi niyyaryin magan sai inmasa nuni daya bari saboda ita mmahaifiyace,kuma ni duk abinda takemin bantaba nuna damuwa taba.


Toh akwai ranar datazo ta tarar banda lafiya,a maimakon ta tausayamin saita rufeni da duka wai tazo ko ruwa ban bataba.


Tana cikin dukana gashi ni nakasa tashi,sai Allah ya kawo Khamis tana ganinshi tafara kukan munafirci wai tazo nace ta koma ai ba gidan ubanta bane.

Sanin halinta kuma ana tsaye akayi batare da sanintaba yasashi fara bata hak'uri,dakyar ta hak'ura ta tafi.

Shikuma guna yazo a hankali yace"....Dan Allah Fatima kiyi hak'uri ban aureki ba saida uwata ta yarjemin kuma don ina sonki plss kina hak'uri WATARANA SAI LABARI.


A hankali nace ba komai ya wuce,yace"....meke damunkine?,nace"....ciwon ciki nake amma yanzu da sauk'i,shiya taimakamin na dafa mana abinci mai sauri sannan nasha magani muka kwanta.


Ku kasance tare da Young Novelist.


Comment .

Like.

Share.


🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

Royal Blood Typing

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«πŸ’«~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

+

🐲🐲🐲

          UQUBAR UWAR MIJINA

🐲🐲🐲

(Based on true Life Story)(Full of Sorrow)
Story Nd Written By

Khadeejaht Hydar

Young Novelist

Dedicated to

Zee xynab Ht u much,tnx 4 everitin. 1 love to u My Zeeta.


(6)&(7)


Da safe ciwona yayi tsanani hankali a tashe muka nufi asibiti, gwajin farko aka tabbatar mana ina d'auke da juna biyu har na tsawon sati uku.

Murna gun Khamis kamar ya zuba ruwa a k'asa yasha,ba laifi Mahaifiyarsa ma tayi murna da samun cikin wanda hakan yasa ta d'an sassauta mugun halinta akaina.


Wani gamin kuma tana aikomin da abinci ko na safe ko na rana wani gamin kuma na dare,Uhm ni Fatima da nasani dabanci  abincinba.


A rashin sanina ashe Uwar   mijina bokaye da Malamai take bi don ta raba aurena,da kuma tasaka rayuwata cikin garari da taskun bak'inciki da tashin hankali.

Ita a tunaninta wai ya koma k'ark'ashina yana bautamin yana kashemin kud'i,batasan  cewa bani k'adai zata cuta ba harma da d'anta amma tabbas tafi cutata.


Haka muke rainon cikinmu kuma tana kayomin abinci inaci,donma daga gida ana kawomin rubuta.

Ita ala dole kada na haifi abinda ke cikina,balantana na haifi namiji  yazama shine zaici gado ba'ita ba.


Fans kunji abinda yasa wasu basason uwarmiji fa,Ku kalli yadda take shirin tarwatsa Y'ar mutane.

Sai isa inzakiyi aure ka rok'i zabin Allah,don wasu uwarmijin su batada matsala ze iya kasancewa  Y'an uwan mijinne,kuma kome uwar miji zata miki ki kasance mai hak'uri kamar yadda Fatima tayi to inma ta cuceki Allah ze saka miki.


Amma tabbas uwar miji uwace,kuma abin ayaba mata ne,abin a kyautata matane,abin a tarayrayetane,kuma a kula da'ita Allah yabamu iyayen  MIJI na gari Masu maye mana gurbin iyayenmu.Cikin ikon Allah na haifi y'ata mace,kyekyawa kamar balarabiya saboda Khamis ma ba bayaba gun kyau da haske.


Ranar suna taci sunan mahaifiyata saboda Sam mahaifiyarsa tak'i yarda asa sunanta,ko miye dalilinta bansaniba.


Haka rayuwa take tafiyar mana cikin jin dad'i  har nayi arba'in,to lokacin ne Mama wutar  tsanar datakemin   tasake ruruwa.


Saboda ko zuwa gunta nayi bata d'aukar y'ata,hakanma yasa Khamis yahanani zuwa gidan ta.


Akwai ranar   datazo gidanmu da sassafe tanata fad'a, a lokacin Ilham tana rarrafe sai taje gunta tana tab'ata.


Wata tsawa ta daka mata saikace wata babba,wani razanannan ihu Ilham tayi sainaji tayi shiru ashe suma tayi.Tundaga rannan bansake bari Ilham ta sake zuwa gunta ba,amma bantaba fad'awa mijina ba saboda naga yana k'ok'ari ganin bantakuraba kuma banason hankalinsa  ya tashi.

Aranar da Y'ata ta shiga shekara d'aya,a ranar natafi gidanmu kuma aranarne uwar Mijina tasamu nasarar binne wani sihiri a k'ofar parlour na,kuma sihirin  bana mutum d'aya b.

Saboda daman tana neman hanya Malamai sunce mata asiri baze kama niba,aljani baze iya kusanta taba,saboda ina da addu'a   kuma Iyayena suna min Addu'a.


Saida yamma na dawo,saida na taka inda asirin yake tukun na naje inda zan bud'e na shiga parlour.

Ina shiga parlourn naji kaina yayi nauyi jikina yafara rawa,da sauri na zauna ina addu'a dakyar nasamu nutsuwa nashige d'akina.


Se bayan magrib yadawo Bayan na gabatar masa da abinci yaci,amma yanayinsa na yau ya canza ko d'aukar yarinyar beyiba ita kuma sai mik'a hannu take don ya d'auket,amma sam babu walwala a fuskarsa.


Gaba nane ya fad'i saboda be tab'ayimin haka ba,koda wani ya bat'a masa rai baya zuwa gida da fushi.

Bayan mun gama cin abincin mun koma parlour,na zauna kusa dashi nace".....Baban Ilham meyafaru ne yau naganka haka?,yace".....bakomai mekika gani. "


Tace".....naga kamar ranka a bac'e,yace".... A'a bakomai seda safe daganan yatafi d'akinsa."

Abinda be tab'a yiba kenan mu raba d'akin kwana,haka na kwanta zuciyata tana zullumin kode nice na masa laifi amma nayanke shawarar gobe zan tambayesa.


Da safe bayan nagama komai nayi wanka nayi kwalliya har k'arfe goma banga alamar saba,nan naje d'akinsa don naduba ko lafiya.


Da sallama nashiga amma me wayam babu kowa,na d'an saurara ko zanji alamar yana band'aki amma shiru kakeji.


Haka na fito jiki a sanyaye ina tunanin har girman laifin danayi yakai yafita babu sallama,nace"....ko de ya fita ina  barcine aikin  gaggawa Yaka masa?.

Haka muka wuni Allah ma yasa  munada kayan abinci,muna kwance nasaka k'ira'a a parlour naga mutum akaina.Da  sauri na tashi ina gaidata amma ko kulani batayiba se cewa tayi ina d'ana yake,nace"...Mama da sassafe ya fita,a tsawace tace"....inason ganinsa yanzu."

Zanyi magana se gashi ya shigo ,tace"....Alhamduliilah d'an albarka daman kai nazo nema, so nake yanzu base yau ba ka saki yarinyarnan.


K'arasowa yayi ya gaidata tace"....sannu d'an albarka,tace"...so nake ka saki wannan  Mara tarbiyyar mara mutuncin.


A hankali yace"....Mama dan Allah kiyi hak'uri inason matata,tace"....lallema ninakemaka magana  kakemin musu,eh hakane tagama dakai nayarda daganan ta juya ta fice tace"....zan dawo kuma saikinbar gidannan."


 

A hankali yace".....kiyi hak'uri Fatima nima daga jiya zuwa yau bansan meke damuna ba,nace bakomai Allah ya shige mana gaba."

Yace".....karki damu da maganar Mama muna tare  dake nace".... Insha Allah.

Muje zuwa.

Ku kasance yare da Young Novelist.

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

ROYAL BLOOD TYPING

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
🐲🐲🐲
         UQUBAR UWAR MIJINA
🐲🐲🐲
(Based on true life story) (full of sorrow)

Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist

Dedicated to  Granny May Allah s.w.t Continue to shower his mercy nd glory upun ur grief.I miss u Granny.Aliyu Muhammad Arab.Za Royal Hignezz.

+
This story is not dah Long so just Bear wit me,I saw ur msges fans tnx a lot,Alhamduliilah group dinmu na fb Zama Na Amana ya gyaru don haka aci gaba da gashi,kuna comment ina binku da ruwan typing loll.Tnx once again.
(8)&(9)
πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯
No matter how d circumstances,always Be prayerful.

Toh haka muka kwana raina ajagule donma mijina yana bani hak'uri da kwanciyar min da hankali, washe gari ma haka yafita  babu sallama se kud'i daya ajiye.

Alokacin ne nafara zargin kode girman laifin Dana masa ne yasa yake min hukunci batare da ya fad'aminba,amma nayi niyyar tunkararsa inya dawo yau.

Bayan nagama ayyukana da yamma nashirya cikin shadda pink mai kyau nayi kwalliya,bank'arasaba naji horn d'in motarsa bayan ya shigo namsa  sannu da zuwa.

Hak'ik'a kwalliya ta tamasa kyau amma ya kasa cewa nayi kyau ,ko ze fad'a se yaji kamar an hanasa,jiki a sanyaye nagabatarme da ruwa mai sanyi.

Bayan yasha na basa abinci har ya gama,bayan ya gama ne nak'ira sunansa dacewa Abban Ilham wai meke faruwa ne?.
Yace".....game dame ba,nace".....naga duk ka canza da safe saika fita batare da ka  nememu ba,ka dena kwana tare damu,kadaina cin abincina in laifi na maka kafad'amin se na gyara.

Kallona yayi na tsawon minti biyar amma ya kasa magana sema rungumeni da yayi ajikinsa still shiru,kamar kuma an tsikareshi saiya tashi da sauri yace".....nima bansan meke faruwa dani ba kinamin addu'a kawai."

Nace"...insha Allah zannayi maka addu'a kuma daman inayi."

To munkai wata uku a haka kullum abu sai dad'a gaba yake, babu sauk'i yanzu some times ma baya kwana a gida.

WATARANA Ranar da bazan tab'a mantawa a rayuwa taba,ranar da shima Khamis tazame masa ranar k'unci da duhu.

Zaune muke Bayan ya dawo daga inda yake Wanda seda ya kwashi kwana biyar tukun ya dawo,abinci yakeci muna fira don yau kam nagansa ba laifi.

Hannuna ya kama yace".....muje kitayani wanka nagaji yau fa,cikin jin dad'in ganin yafara dawowa yadda yake da nayi,da hanzarina na tashi  ina gaba yana bina abaya Ilham kuma tanagun Mama.

Bayan nataimaka masa munyi wanka,ya nemi ya raya sunnar manzo, wanka muka sake sannan muka shirya cikin kaya iri d'aya, kana ganinmu zakasan muna cikin farinciki.
Zama mukayi a parlour muna wasa,kawai se mukaji anbugo k'ofa da k'arfi,saurin sauka a jikinsa nayi ina gaidata.

Wani mugun kallo tabini dashi,sannan tace".....kai Khamisu yau base gobe ba,yanzu base anjuma ba kasaki yarinyarnan inba hakaba wallahi saina tsinemaka albarka."

Jiki na rawa yace"......Dan Allah Hajiya kiyimin rai kibarni da Matata,wani uban ashar ta yanko tace".... Allah ya......"

Da sauri yace".....Dan Allah kiyi hak'uri zan saketa karkimin baki,a hankali yakai dubansa kaina hawaye yakebin kumatuna."

Yace"....kiyi hak'uri Fatima ina sonki,nace".....bakomai Khamis nima ina sonka kabi umarnin Hajiya Allah yana tare dakai."

To in angama barikancin ina jira abarmin gidan d'ana,wucewa nayi ciki don d'akko hijabina,har ze bini tace"....ina zaka?,yace".....takarda da Biro zan d'akko,batayi magana ba illa kwafa datayi."

Hijab na d'auka ina hawaye,a bakin k'ofa mukayi karo dashi,rungumeni yayi ya fashe da kuka nima Inayi.

Yace".....banason rabuwa dake,nace".....dole mu rabu Khamis ka sakeni kar mama tayiwa rayuwarka illa,ni nayafemaka nasan ba'ason ranka bane.
A hankali yace".... Nasakeki saki d'aya, wani kuka ne y kufcemin a zuciyata nace"....daman haka saki yake,amma wasu matan sukeson asakesu.

Shigowa tayi tace"...kasa keta nace yanzunnan,yace"... Nasaketa tace"...wlh baka isaba saki uku zaka mata ba d'aya ko biyu ba."

Hankali a tashe yace"....Dan Allah Mama kiyi hak'uiri bazan iyaba,wani wawan mari takai masa tace"....kasaketa yanzu nace!!!,haka inaji inagani tarabani da Khamis yana kuka ina kuka yace ".....na sakeki saki uku amma kisani inasonki har k'arshen rayuwa ta."

Hannu ta tafa tace"....to Y'ar mayu se ki tattara kibarmin gidan d'ana na huta,Uhm da kinsan abun ba ita kad' ai ze shafa ba da baki rabasu ba.
Muje Zuwa fans.
Gida nakoma nasanar da iyayena,dukda sunji ba dad'i amma hakan be hanasu kwantar min da hankali ba,anan naci gaba da iddata Ilham na guna.

Bayan na gama idda ne aka kaiwa Khamis Y'ar sa,amma Mahaifiyarsa tace"....a maidota d'anta beda wata y'a.".

Haka aka maidota Wanda hakan yayi min dai-dai,saboda daman ina tunanin yadda zata rayu agunta cikin uquba da azaba.

Bayan nagama idda ne na koma gidan yayana,inda a wannan lokacin ne rayuwata ta tabarbare na koma wata kala kamar baniba,hankali kwata kwata baya jikina banma san wacece niba.kullum haka nake kamar wacce ake bawa umarni.

Bayan na barmata d'anta bata kyale niba taci gaba da bibiyar rayuwata saboda kawai burinta be wuce inta gayyaraba.

Aikin da tayi na k'arshe akaina gun wani malamine a nan garinmu,inda tasa yamin aikin da zan shiga duniya na ringa asarar,duk abinda nasakawa hannu ya lalace kuma inda k'arbar kud'in jama'a yana lalacewa aguna.
Uhm Wata shari'ar se lahira,,
Kuma gashi tamin asirin ko aure bazan sakeyiba.

A wannan lokacin ne na had'u da wani mutum Wanda me kud'i ne sosai,kuma ya nuna yana sona amma hakan besa nabasa fuska ba.

Ilham kuma tana gun Mama tana samun kulawa Alhamduliilah, Nikuma ina gun wani kawu na babu abinda nakeyi kawai naji unguwarmu ta fitarmin arai.

Muje zuwa
Ku kasance TARE DA YOUNG NOVELIST.

Vote.
Share.
Comment.
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
ROYAL BLOOD TYPING
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Alk'alamin Auta.
Ku biyoni don jin sabuwar rayuwar FATEEMA BAIWAR ALLAH.

Allah ka karemu daga sharrin duk abin k'i,Amin S Amin.
Pray 4 me Am sick,just type 4 ur calls nd msge🐲🐲🐲

           UQUBAR UWAR MIJINA

🐲🐲🐲

(Based on true Life Story)(full of sorrow)


Story Nd Written By

Khadeejaht Hydar

Young Novelist

Dedicated to.

My New Born Baby.

Allah ya rayamin ke cikin baiwa da hazak'a,yabawa mahaifiyarki lafiya da kwanciyar hankali duniya da lahiri,ya bud'ewa mahaifinki wato My best Broza,Allah ka rayashi tare da Anti deejersa,tnx 4 giving me a baby.

+

(10)&(11)


Uhm bayan rabuwa ta da Khamis da wata uku, yasamu karayar arziki inda duk wani duk'iyarsa ta lalace yazama babu komai se gidan dayake ciki.


Mama tana farincikin natafi zataci arziki ta aura masa wacce takeso,kwatsam saitaji labarin cewa aiii gobara ta kama gidan mai na Khamis, kuma b'araryi sunje company d'insa sunyi sata sun tafi da motar da'aka kawo masa kaya aciki.


Tashin hankali tashiga sosai,shi kuwa Khamis be wani damuba sosai,saboda rashin matarsa dayakejin zafinsa,kuma dama Malamai sunsha fad'a masa matarsa tana da arziki a jiki itace silar arzikinsa.


Zuwa tayi gidan tana kuka,tace".....Khamis kayi hak'uri da abinda yafaru,daman nasan tunda ka rabu da yarinyarnan nasan bazata barka a banzaba to nima nayi alk'awarin bazan zauna banza ba.Yace"....haba Mama kidaina cewa haka ni nasan Fatima bazatamin komai ba kawai de k'addarace Allah ya bamu ikon cinyewa."Da sauri tace"..... Kaide Allah yabaka ikon cinye  jarabawa,amma wannan ba k'addara bace,kuma wlh saina d'auki mataki akan yarinyar nan,fuu ta fice ta barshi cikin tunani."


Allah kabamu iyaye na gari Amin.

*************************


To mutumin damuka had'u dashi ya nacemin damaganar aure,nikuma sam aure baya raina,amma tsabar naci seda yaje har gun kawu na yamasa magana.


Daganan kuma kawu na yace"....dole nayi aure ko inaso ko banaso,haka na hak'ura na yarda da auren.Uhmm Mahaifiyar Khamis najin zanyi aure taje ta samu boka tace masa ya hana auren gaba d'aya,haka kuwa akayi har lokacin da'akayi zasu kawo kaya basu   kawo ba kuma har lokacin be daina zuwa guna  ba,nima kuma ban hanashi ba saboda nasan ina sonsa amma bada aure ba.

Uhmm Allah kamana mafita me kyau.

Shekarar mu d'aya da Ahmad amma babu maganar aure a junanmu,duk da muna mutuk'ar son junanmu amma ba halin auren juna.


Ana haka ne na tsinci kaina da samun juna biyu,wato inada ciki.

Tashin hankali na shiga Mara misaltuwa nan na sanar da Ahmad yace".....yana son abinsa amma na bijire nace wlhh saina cire cikin to na haifeshi da wani ido zan k'alli jama'a?"


Don haka naje na samu wani likita nace"....don Allah ya zubarmin da cikin,yace"....cikina yanzu watansa daya na bari se ya kai wata uku,haka na tashi na koma gida badon raina yaso ba.


Kuma banfad'awa kowa ba,saboda tsoron abinda ze biyo baya.


Cikina nakaiwa wata biyu na koma gun likitan,nan yabani wani magani yace nasha zai fita,duk da ina tsoro amma haka naje nasha maganin amma kusan kwana biyu magani yak'i aiki.


Na koma na fad'a masa yak'ara bani wani,amma the result is the same.

Don haka nakoma gun wani likitan saboda azatona wannnna bayason yamin abinda nakeso,Uhm anya Fatima daga gunsane kuwa.Sabon likitan Dana canzama haka the same thing,haka naketa canza doctors Amma duk d'aya, harna gaji nadaina zuwa gun likitoci kuma ko irin laulayin masu ciki banayi.Haka naketa zama sainaji Allah ya d'auramin son abinda ke cikina,don haka sena yanke hukuncin fuskantar komai akansa.Uhmmm Anya Fatima zaki iya kuwa.


To muje zuwa donjin abin al'ajabin dake gaba.


Taku a kullum:::Young Novelist.

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

Royal Blood Typing

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

Alk'alamin Auta

🐲🐲🐲
        UQUBAR UWAR MIJINA
🐲🐲🐲
(Based On True Life Story)(Full Of Sorry)

Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist.
Dedicated to
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«πŸ’«~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*+

Sayner Naseer Nd Aisha Abubakar(Dimple Deepika).
Anti Rabi'atul adawiyya Ina gaisuwa karki damu innazo Yola a gidanki zan sauka.
Welcome back Bandirawo am Bestie Aishat B Umar.

Pls amin uzurin rashin jina da'akayi ayyukane sukayi yawa amma insha Allah yanzu na dawo
(12)&(13)

Toh haka nake zaune a gidan yayana lokacin cikina nada wata biyu,to lokacin da matar yaya na tagane inada ciki ta tsorata sosai.
Kuka tasamin tana tambayata wayamin fyad'e,saboda ita a zatonta kamila irina  yazanyi  na yarda nayi zina harnayi ciki.
Uhm nace"...bakisan  jarabar dake jikinta ba bakisan aikin da'ke jikinta ba."

kuka nake nakasa magana saboda nima nasan wani abun yana bibiyar rayuwa ta,amma nakasa gane menene.
Dakyar nafad'a mata komai ina kuka sosai,kuka itama takeyi tace"....Fatima yazanyi da wannan abun Dan Allah karki fad'awa Mama kinga ke kad'aice gareta karki fad'a hankalinsu ze tashi."...

Cikin kuka nace"....Anti Hajara wlh in Yaya yasani nashiga uku kasheni zeyi,tace"....tashi muje asibiti a zubar dashi inba hakaba wlhh anshiga uku jama'a zasu sami abin fad'a a gari."

Tashi nayi  muka kama hanya batare da nace mata natab'a yunk'urin  zubarwa ba,muna zuwa wani specialist hospital.
Magunguna suka bamu sukace muna zuwa naci abinci nashasu cikin zai zube,muna zuwa gida naci abinci sosai nasha magani inajiran lokacin dasukabamu yayi cikin ya zube.

Da daddare bayan munci abinci muna fira yaya yashigo anti tamin saida safe tashige,nikuma dayake ana d'an zafi saina kwanta  da nufin anjuma innasha iska saina shige.

Ashe wannan kwanciyar danayi wani abin al'ajabine zai faru,Allah ne zai nunamin cewa komai saida izininsa yake afkuwa.
Ina kwance a tsakar gidan bacci yafara d'aukata sai naji k'asa tayi wata irin girgiza mai firgitarwa,bude ido nayi a zatona mafarki nake amma sainaga dagaske ne ba mafarki ba tsakar gidan duk jijjiga yake.
Take wani tsoro ya ziyarceni,at the same time kuma naji wani irin girgiza kamar wani babban  naman jeji yana  zuwa gareni,saboda ina  iya juyo takun abun kuma ko wane taku sai inda nake ya girgiza.

Nide tsoro ya rufeni kuma na kasa tashi na gudu,ga d'an k'aramin cikina yafara fitowa saboda inada girman ciki.

Abunne yake k'ara nufoni kuma a lokacin girgizar da k'asar takeyi tak'ara tsananta,cikeda tsoro nake k'ok'arin tashi saboda har nafara kuka ina karanto addu'oi.

Abunne yazo ya tsaya agabana kuma lokaci d'aya nadaina jin girgizar, kaina na d'ago a  tsorace don kallon menene.
Abin mamaki zakara (cock) nagani bawani mai girma ba, kuma fuskarsa tamk'e abun tsoro Yana tsaye akaina.

Cikin murya mai ban tsoro da tsawa  kamar ta mutum ya ambaci FATIMA!!!!! har sau uku,Kafin na amsa naji muryar yarinya k'arama tana amsawa,bangama tsinkewa ba saida nagane cewa daga cikina maganar ke fitowa.

A tsorace nakai hannuna  kan cikina inda abunda ke cikina yace"....Na'am,kuma duk wannan abun ba mafarki nakeba idona biyu kuma ko'ina da duhu se hasken farin wata dake haske tsakar gidan."

Muryarsace tak'ara dawo dani duniyar danaje,yace"....Fatima da fatan kina lafiya babu abinda yatab'aki?,amsawa tayi  tace"...Eh lafiyata kalau babu abinda yasameni."

Yace"...to Alhamduliilah nayi farincikin babu abinda yasameki,daganan kuma ya juya yafara tafiya nan take kuma ko'ina yafara girgiza kamar lokacin dayake zuwa.

Yana kaiwa k'ofar gidan naga ya bac'e,saboda daman bansan tayaya yashigo ba tunda an kulle gidan.

Wani wawan k'arfi ne yazomin bandamu da cikin jikina ba na antaya d'aki da mugun gudu nasaka sakata,kuma se alokacin jikina yafara rawa saboda gaskata cewa wannan abun   dana gani a zahiri ne ba mafarki ba.

Daganan na yanke shawarar bazan sake yunk'urin zubda cikin ba,da safe da anti ta tambayeni ko ansamu nasara  ban b'oye mataba nafad'a mata itama taji tsoro don haka tace"...mu bar cikin wata aya ce  wannan,kuma Insha Allah zata kula dani tasan ba halina bane k'addarace"...

Toh muje zuwa.
Taku a kullum.
Young Novelist.
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Royal Blood Typing
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Alk'alamin Autah✍

🐲🐲🐲
UQUBAR UWAR MIJINA
🐲🐲🐲
(Based on True Life Story) (Full of Sorrow)
Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist.

Dedicated to My gist patner,my abokin fad'a,my kinda hrt bro.
HAMZA.Tnx 4 d du'a,nd idea.+

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«πŸ’«~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

(14)&(15)

Haka na zauna ina rainon cikina Wanda yanzu yake da wata hud'u,kuma koda yayana yasani yaji babu dad'i amma yad'auki hakan amatsayin kaddara saboda lokacin dayafara min fad'a da Cewar saina fad'i Wanda yamin cikin.
Ganin yadda nake kuka nakasa maganane yasashi sassauta murya, cikin lallashi yace"...Y'ar uwata fad'amin waya miki wannan abun don nasan ba halinki bane."

Nan na sanar masa abunda yafaru,hak'ik'a yaji bak'incikin faruwar hakan amma yace"...badamuwa haka Allah yaso zan fahimtar dasu Baba,kuma nasan zasu fahimceni."

Ina kuka nace"....Dan Allah karka sanar dasu ,yace"....to Fatima inban sanar dasu ba haka kawai saisu ganki da yaro ko yarinya?, A'a baze iyuba karki damu zanyi k'ok'arin naga sun fahimta."

Nace"...to yaya nagode,daganan kuma nacigaba da rainon cikina kuma a lokacin nad'auki d'amarar haifar abinda ke cikina kuma na rungumesa hannu biyu."

Da yayana yasanar da iyayena sun kad'u matuk'a,amma haka suna danganawa Allah komai kuma suka k'ara jaddadamin nakula dakaina kuma narik'e mutuncin kaina nasan darajar kaina kada na na kuskura nasake tafka kuskure irin wannan.

Toh hak'ik'a ina cikeda danasani dukda nima bansan tayaya hakan yafaru ba,kuma har lokacin yakan zo gidan danake yakawomim abubuwan buk'ata harda kud'in zuwa asibiti da komai.

Kuma har yanzu munason juna amma dayamin maganar aure zan nuna Sam banyardaba,dukda nima wani gamin abun yana raina.

To yau cikina yakama wata 7 inda cikin yayi girma sosai kamar wacce zan haifi Y'an uku,gashi bana shan wata wahala sab'anin haihuwar Ilham.

Wani gamin nakan zauna ina tuna rayuwata ta da,sai na dinga cewa anya nice kuwa saboda nima ina ganin canji acikin rayuwata,amma nakasa gane hakan.

To wata rana muna zaune sai naji duk bayana yana ciwo,saboda dama tun safe nakejin ciwon Mara da baya amma nayi shiru aganina ai cikina bekai watan haihuwa ba.

Da safe natafi kauyen danginmu don kai musu ziyara duk da inajin ciwo anma bankai cewa haihuwa bace,ina zuwa na kwanta don hutawa.

ABINDA YA FARU KAFIN RABUWA TA DA KHAMIS SHINE.

Wata rana ina kwance sai nayi mafarkin ga wata bafulatana tana d'ebo zinare a kwarya tana zubawa ajikin gidan Khamis,tohm a lokacinne arzikin Khamis yaketa bunk'asa,ganin hakanne yasa mahaifiyarsa cin alwashin rabamu saboda tun farko bani taso ya auraba Y'ar aminiyarta taso ta bashi to hakanne yasa tace saita raba aurenmu kuma ta lalatamin rayuwa.
Hattara mata muguji zuwa gun bokaye da malamai,komai na Allah ne tana iyuwa kayi mugunta kuma ta koma kanka ko zuri'arka Ku biyoni donjin yadda rayuwar Khamis ta tagargaje sakamakon aikin uwarsa.

Da cikin Ilham ina kwance saiga wata baiwar Allah da Hijab d'inta fari har k'asa,tace"....Ki tashi kige gun Malam Ibrahim kice masa ya taimaka ya warware abinda ya miki,kuma ta nunamim kamannin Malamin da inda yake."

Muje zuwa .
Taku a Kullum Khadeejaht.
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎?
Royal Blood Typing
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«πŸ’«~*
*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~*

🐲🐲🐲
          UQUBAR UWAR MIJINA
🐲🐲🐲
(Based on true Life Story) ( Full of Sorrow)
+
Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist
Dedicated to
My 1 Nd Only Boo
Nisful Hayatee....
(16)&(17)

Da safe dana tashi na tambayi Khamis  cewa zanje gida, ya amince don haka ina gamawa nakama hanyar gidan da'aka sanar dani a mafarki.

Ina zuwa k'ofar gidan nayi sallama,wani yarone ya amsa,na tambayesa Malam yananan yace"...eh bari inmasa mgna."

Bayan Kamar minti 3 se yazo yace"....Ance kishigo ,shiga nay da sallama cikin parlourn."

Zaune yake da carbi a hannunsa mutum mai cikar haiba da kamala,bayan mun gaisa se yace"...baiwar Allah bangane kiba,tace"...nice Fatima surukar....nafad'a masa sunan surikata.
Ido ya zaro yace"...kece Fatima matar Khamis?,nace"...eh Dan Allah malam ka taimakamin ka warwaremin abinda kamin,ka tayusayawa mahaifana da rayuwar yaran dazan haifa."

Ajiyar zuciya yayi ya kalleni cikin jimami yace"...Allah Sarki Fatima kiyi hak'uri  a Yau nayi dana sanin aikin danayi miki,hak'ik'a UWAR MIJINKI tazo na mata aiki akanki kuma ba'aguna kad'ai ta tsaya ba tana kanyi miki aiki don ganin rayuwarki ta tagayyara,amma ina zuwa,ya tashi ya shiga wani d'aki ya fito."

Rubutu  yayi ya wanke yabani nasha,yace"....gashi Fatima nayi wanda zan iya nikam na warware wasu aikina akanki wasu kuma bazasu warwaru ba,amma Fatima keda kwanciyar hankali se a hankali wata k'ilama har kibar duniya bazaki zauna guri d'aya ba don aikinta kenan akanki kada kiyi amfani a rayuwa,Fatima kiyi hak'uri kiyafemin kitashi kije Allah yabaki lafiya.

Tashi nayi ina kuka,a zuciyata nace"...menayiwa  UWAR MIJINA ta tsaneni haka,to a washegarin  abun ne Khamis ya sakeni na koma gida,kuma a ranarne nayi mafarki ina kwance a gidanmu wai  matar danagani tana zuba zinare a jikin gidan Khamis tazo tana kwashewa tana tafiya dasu,to wannan shine silar karyewar arzikin Khamis.Muje zuwa.
CIGABAN LABARI.

Zuwana k'auyen danginmu da kwana d'aya na haifi y'ata mace kyekyawa kamar balarabiya ga gashi ga fari kamar ka latsa jini ya fito,duk da bata hanyar aure ja sametaba se naji inasonta son hak'ika haka ma mutane suna sonta kowa se so yake ya d'auketa.

Wani kawu nane ya tambayi wane suna nakeson asamata,har zance yasakamata sunan mahaifiyata se kawai sunan da zakaran yak'irata ya fad'omin,nace"....kawu asamata  FATIMA."

Yace"...to Allah ya raya ta yasa mai tausayin mahaifa ce,amin kowa ya amsa."

Ranar suna yarinya taci sunan Fatima,kuma Alhamduliilah komai anyishi a wadace.

Haka na zauna anamin wanka a k'auyen kuma ana kula dani sosai,kuma har lokacin Mahaifin Fatima yana zuwa guna ko ragon suna ma shiya  siya donshi a shirye yake ya amshi Y'ar sa.
To ana hakane naji labarin Khamis ya saida gidan mansa Wanda ya rage,gidan dana zauna acikima ya saida ya koma baida komai se ana taimak'onsa
Hartakai ta kawo  yaronsa Wanda shiyake  bawa mai ya saida yasamu riba,to yanxu shi yake taimakawa Khamis da abinci da kayan sakawa,Mahaifiyarsa kuwa a yanzu duniya ta mata zafi amma dukda haka bata daddara ba tananan tana bibiyar rayuwata.

To yau nayi arba'in kuma dangi sunyi abun sadaka harda Abban Fatima,and'anyi taro ba laifi akayi adddu'a aka tashi.
Toh haka nake rayuwa a k'auyen nida y'ata,Masha Allah Fatima se girma take Kamar ba Y'ar wata biyu ba.
Yau Kamar kullum mun kwanta bayan namana addu'a,acikin barci wani bawan Allah yazomin yana sanar dani na rik'e y'ata da kyau don Fatima Y'ar baiwace.

To daman ina sonta sosai fiyeda Ilham,uhmm yau kuma Fatima tacika Wata takwas inda har rarrafe take,jama'a se yaba wayo da girmanta suke.
Tana wata Wata goma sha d'aya tadaina shan nono,sede taci abinci ta k'oshi tayi bacci ga Allah yabata hak'uri da juriya Sam batada rigima.
Hakanne yasa kowa yakesonta kuma yakeson d'aukarta,kullum cikin bata kyauta ake,wani gamin in aka d'auketa tun safe se yamma za'a kawomin ita.

Uhm Ku biyoni donjin sabon kaddarar dazata riski wannna baiwar Allah n.

Ku KASANCE tare da YOUNG Novelist.

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Royal Blood Typing
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Alk'alamin AutaASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«πŸ’«~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u no pain.


🐲🐲🐲

         UQUBAR UWAR MIJINA

🐲🐲🐲

(Based On True Life Story )(Full Of Sorrow)

Story Nd Written By

Khadeejaht Hydar

Young Novelist

+

Dedicated to

Fans,Allah yabar k'auna, nagode matuk'a,banda bakin godemuku sede nace"...Allah yabar k'auna.🀝🀝.

(18)&(19)


Yau da safe bayan mungana ayyukanmu nace"...Goggo inaso naje nagaida su Mama,tace"...toh Allah yakaimu anjuman,Amin."

Tun alokacin nakejin gabana nafad'uwa nakejin sauyi ajikina,Amma sena alak'an tashi dacewa k saboda zan tafi da Fatima gidanmune abun yana bani kunya kuma dawani ido zan kalli su Baba.

Shiryawa nayi nad'auki  jakata Wanda kayanmu ne aciki ak'alla zasukai Kala goma,sallama na musu nafito cikeda kewarsu.


Harna fita senaji kamar namanta wani abun,komawa nayi nace"....Goggo anya banyi mantuwa ba kuwa?,tace"... Mantuwar me kuma Fatima to ki duba."

Zama nayi kamar karna tafi harseda  Goggo tace"....ko kunfasa tafiyar ne?.nace"...A'a zamu tafi daga haka na tashi nace"...toh Goggo ayafi juna nizan wuce Sena dawo,tamin adawo lafiya nafita."


Gun shiga motoci na nufa inaji  ana k'iran sunan cikin garinmu anma banshiga ba,kawai sena nufi inda naji ana k'iran kano.

Zama nayi kuma nandanan motar tacika muka kama hanya,a zuciyata nake tunanin to ina zanje kuma gunwa zan sauk'a nida banida dangi acan,Nide kawai zuciyatace take bani umarnin danaje kano.


Da yamma muka iso kano  saboda akwai tafiya tsakaninsa da yobe,bayan mun sauk'a a park sena nemi wani bench nazauna nasiya abinci mukaci.

Toh muna zaune har magrib  har isha'i har mutane suka fara bajewa,amma narasa inda zan nufa.

Goyon Fatima nayi nafara tafiya batare da sanin inda na dosaba,Can misalin k'arfe goma nazo gun wata bukkar mai shayi nazauna.


Mutane nagani suna isowa gunmu da sauri natashi nafara tafiya cikeda fargaba,wani lungu na lab'e sunzo wucewa  sai abunda yake cikin buhunsu ya fad'o.


Wani wawan ihu nayi ganin kan mutum aikuwa da gudu na fantama na jefar da wayata da kayana,aikuwa suka bini da gudu babban su yace"...Ku d'akko mana yarinyar Ku kashe uwar."


Jin an ambaci kashemin Fatima ne yasani k'ara speed harnazo bakin titi,wata motace tazo wucewa nafara d'aga musu hannu ina Neman taimako amma bata tsayaba kuma ga mutanen sun kusa kamoni.


Wata jeep nagani da gudu nashiga gaban na tsuguna nace"...Dan Allah a taimakamin,Wata matace tafito tace"....lafiya meyafaru?".Da hannu nake nunamata waenda sunkusa zuwa nace"....Zasu kasheni kitaimakeni,da sauri tabud'emin motar tace"....shiga muje ina shiga suka iso gun da gudu ta figi motar muka bargun."


Daya daga cikin sune ya jefi motar da wata adda,aikuwa yasamu glass d'in motar kuma dai-dai inda nake, aikuwa glass d'in yafashe yasamu fuskar Fatima nan da nan goshin Fatima yafashe.

Ihu nayi  nace"...innalillahi Fatima!Fatima!!Fatima!!!,amma ina ta suma,muna shiga cikin garin kano tayi asibiti damu."


Muna zuwa  aka k'arbeta akayi emergency da'ita,bayan kamar minti 30 aka fito da'ita harta farka kuma anmata dressing d'in gun.


Matar ce ta k'arbeta tana mata sannu,ta sallame su sannan tace"... Muje gida ku huta dare yayi.


Haka nabita muka shige motar,haka kawai naji matar ta kwantamin arai,kobabu komai  ai Allah ya aikota tacece mu.

Wata unguwar masu kud'i  muka nufa,unguwar babu gidaje sosai sai manya manyan gidaje tsirara.


Wani Babban gida muka nufa tayi horn aka bud'e babban gate d'in, shigar da motar tayi sannan ta umarceni dana  fito.

Wani Babban k'ofa ta nufa ina biye da'ita, Babban parlour ne mai cikeda kayan alatu ga manyan kujeru komai kana gani kasan na masu dukiyane.Zama nayi a k'asa ina rik'eda Fatima,tace"....Hau kujera ki zauna y'ata ina zuwa. "Abinci takawomin da ruwa,rabona da abinci tun safe kuma shima nacine ba cikin kwanciyar hankali ba saboda yadda gabane ke fad'uwa ashe abinda ze samemu kenan.


Abincin naci nabawa Fatima itama,sosai mukaci saboda muna tare da yunwa.


D'aki tanunamin tace"....kishiga kije kiyi wanka itama kimata wanka na ajiyemiki kaya akan gado."

Tashi nayi ina jinjina tausayawa irin na matar nan kuma tayarda dani batare da tasan ni wacece ba,haka na shige nayi wanka nayiwa Fatima nasaka kayan danagani akan gadon.


Kwanciya nayi  a makeken gadon dake d'akin, nandanan bacci mai dad'i ya d'aukeni.


To Asuba Tagari Fatima Anti Fatima Ummin Fatima.

Allah ya yayemiki abinda ke damunki aduk inda kike.😭😭😭😭😭😭

Taku a Kullum.

My New Fb Account For My fans,4 ur comment nd ideas.

(Hajaratou Bintu Muserh.)Add up u gonna get any answer to ur Questions.

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

Royal Blood Typing

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎


Alk'alamin Autah.

🐲🐲🐲
         UQUBAR UWAR MIJINA.
🐲🐲🐲
(Based on True Life Story) (Full of Sorrow).
Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist.
Dedicated to UQUBAR UWAR MIJINA Fans ina godiya matuk'a da kulawarku a gareni naga sak'onku kuma na gode,lokacin danaga yawan Msges dinku har kishi ya kamani don ganin duka msges d'in na Novel ne lol,Tnx daku nake tunk'aho Fans,Wannna page d'in na kune.+

Rashin lafiyace takamani kuma alhamduliilah naji sauk'i,Nagode da Addu'a.

Allah yabaki lfya Bestie Na'eema I miss u a lot.

Bestie Aisha karkiyi ciwo fa Kinga bame kawomin kindirmo fa,kuzo keda Yaya.
Anti Rabi'ah ina gaisuwa.

My Troublesome Sayner Happy Graduation Allah yak'ara lfya da Ilimi yasa ayi amfani dashi.Amin.
(20)&(21)

       Washe gari da safe bayan  mun tashi nayi sallah  a d'akin na fito waje,a parlour na tadda matar da wata budurwa a zaune.

Har k'asa na tsuguna na gaidata ta amsa fuska a sake tace"....Fatima ga k'anwarki mufeeda kuma inason sanin meyakawoki garin kano cikin dare har waennan miyagun ke Neman halakaki?."

Murmushi nayi na fara bata labarin rayuwata batare dana b'oyemata komai ba,hatta garinmu ban b'oye mata ba.
Jinjina kai tayi tare da share hawayen dake fuskarta tace"...insha Allah zan taimaka miki karki damu,haka rayuwa take kowa da abinda yake ganin yayi masa dai-dai."

Kwana na biyu da zuwa gidan tafiya takama Hajiyar zata tafi k'asar Togo da Ghana siyayar kaya saboda tanada kud'i, tana siyowa kayan tazo tasaida anan kano babbar Y'ar kasuwace.

Bayan ta tafi naci gaba da zama nida Y'arta Mufeeda wacce babu ruwanta gata da son mutane,Kuma tanason Fatima Sosai saboda in akaga Fatima a hannuna to Mufeeda na Makaranta,don ko makarantar Islamiyyace da'ita take zuwa haka intaje   zasu dinga d'aukarta.

Bayan kwana hud'u Hajiya ta dawo da siyyara kayan kasuwarta,haka tayi mana siyayya ba kad'an ba musamman Fatima wacce nata yafi na kowa kyau da tsada.
Godiya mukayi mata harta nuna bataso saboda Allah tayi,Kayan Fatima Mufeeda ta kwashe ta tafi dasu d'akinta tace"...Anti Fatima Munbar miki d'akin ki kije ki huta mukam munk'ama sabon d'aki."

Murmushi tayi tace"....to Allah ya kiyaye hanya daman ta hanani walawa a kan gadon, Hajiya tace"...A'a kam kar'ayiwa Y'ar uwata  Sharri kam don batada rigima ko kad'an. "

Bayan ta hutane washe gari tashiga garin kano don rabawa  Y'an kasuwa kaya,su Fatima kuma suka tafi makaranta.

K'irane ya shigo wayata,d'auka nayi naga sabuwar number amsawa nayi tare dayin shiru,muryar data doki dodon kunnenane yasani tashi cikin mamaki nace"...Khamis!!!,yace"...Na'am Fatima kina lafiya?nace"...lfya kalau ykk y hidima da aiki?,Be amsaba illa cemin dayayi ya Ilham nace"...tana lfya tana gun mama".
Da mamaki yace"...to ke kina ina?,uhmm ina kano gun Y'an uwanmu yace"...to ngd kibani izini inason naje naga Ilham nasan banmata adalciba dana watsar da'ita tun tana k'arama,Uhm aii bakomai komai ya wuce, godiya yamin sannan na katse k'iran.
To yau yakama watana biyar a gidan Hajiya kuma alhamduliilah tana kula damu sosai,Zaune muke a parlour Hajiya tace".....Fatima inaso kifara business banason zamanki haka don haka na yanke shawarar nan gaba idan zan tafi tare zamuje kiga yanayin kasuwar kuma kisan hanya daganan kuma zanbaki jari kema kifara kasuwanci dashi Allah yasa mu dace."

Godiya nayi mata sosai kuma naji dad'i.
Ashe wannan tafiyar itace silar  rushewar farincikina,itace sanadiyyar rashin zaman lafiya ta.
Tohm Ku kasance tare da YOUNG NOVELIST.

TAKU A KULLUM.
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Royal Blood Typing
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

Alk'alamin Auta ✍✍

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«πŸ’«~*
*~❄We beare's of soo golden a pen,We writer's assiduously percieven No pain,so Magical Our creative golden pen,Be hold our worlds,A product of our pen savour Our worlds for it will  cause u no pain~*

+
🐲🐲🐲
          UQUBAR UWAR MIJINA
🐲🐲🐲
(Based on True Life Story) (Full Of Sorrow)

Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist.
Dedicated to
Muhammad Muhammad Yusufari Nd Aliyu Haidar Muhammad  Family More grace to ur elbow,one love to mah sources I love u all my Family.
(22)&(23)

        To   yau yayi dai-dai da wata hud'u da dawowar Hajiya,kuma a yaune muke shirin tafiya tare da'ita kasuwar.
Tunda muka tashi muka kama hanya mukabar Fatima da Y'arta se masu aiki,seda mukayi tafiyar kwana daya tukun mukazo Lagos, daganan kuma muka shiga cotonue dayake basuda nisa haka mukayi siyyya ta nunnunamin gurare dayawa daganan kuma muk'a karasa Ghana muka sake siyayya dagaban muka dawo kano.
Mun dawo gida lfya bayan,dawowarmu da kwana hud'u ta tafi dani inda take rarraba kayanta donnima nagani,haka mukata zagaya customers d'inta tana nuna musu ni a matsayin wacce zatana kawo musu kaya a madadinta.

Uhm hak'ik'a na yaba da jarumta irin ta wannan baiwar Allahn,da kuma amana to inba hakaba mutumin dabaka saniba amma kayarda dashi ka nuna masa sirrinka harda gun waenda kake sayar da kaya,a raina na kud'urci niyyar bazan taba cin amanar taba.

Haka nake rayuwata nida y'ata a gidan Hajiya inda har yanzu Khamis yakan k'irani mu gaisa haka Baban Fatima ma,don yanzu Fatima Nada shekaru biyu(2)a duniya   kuma Allah yayi mata kyau na ban mamaki fara kyal da'ita kamar wata y'ar larabawa,ga farinjini,nikaina abin yana bani tsoro gani nake wani gamin har juyewa take don watarana se naga kamar ba'itaba.

Akwai wata rana damukaje supermarket nida ita da Y'ar Hajiya,bayan mungana siyayya  muka fito Fatima tana rik'e da k'atuwar teddy pink a hannunta.

Security d'in gun ne yahanamu wucewa yafara tambayar mu wai a'ina muka d'akkota?,dariya nayi nace"....she is my daughter yace"...wlh be yardaba dukda nima inada haske seda yasa akayi bincike babu Wanda ke neman yaronsa tukun yabarmu muka wuce Dakyar.

Toh tundaga ranar nadaina fita da'ita,sede na siyomata duk abinda takeso nakawo mata.
To rayuwa take tafiya inda maza dayawa nason su aureni kuma nima haka inason nayi aure,amma se anfara maganar aure dasu se d'ip su d'auke k'afa Wanda hakan ke sani cikin tashin hankali.

Akwai wani mutum mai suna abdur-rahman har anyi magana ance yaje yasamu iyayena,to shima tundaga  wannan maganar be sake zuwa ba,duk lokacin da irin haka yafaru sena shiga d'aki nayita kuka ina neman afuwa da sassauci gun ubangiji,haka Hajiya zata dinga bani kwarin gwuiwa tana bani baki tace"....kiyi hak'uri Fatima WATARANA SAI LABARI.kuma duk wane tsanani yana tare da sauk'i,dahakanne nakejin d'an sanyi araina.

To Har takai yanzuma  bana tanka maza bana kulasu kwata-kwata saboda duk iya son dazanyiwa mutum bazan aure shiba,anriga  anmin katangar k'arfe da aure sede nace"...Allah yabimin hakk'ina."

To yau takama ranar da zanje kasuwa nik'ad'ai saboda munyi zuwa kusan uku nida Hajiya kuma na gane hanyar sosai.

Tunda safe naji jikina babu  k'arfi gashi Fatima ta mak'alemin abinda batayi ada,kuma setadinga kallona tana min Murmushi, ni se duk jikina yayi sanyi don kwakwata nakasa ganema Fatima ta hanani sak'at anyi anyi tabarni amma tak'i,nima senaji son FATIMA yana k'ara huda zuciayata da gangar jikina senaji nak'ara sonta yadda bantab'a sonta ba abaya.
Ni na mata wanka a ranar abinda nadad'e banyimata ba saboda bata yarda,amma yau har wasa take acikin ruwan,a tare mukaci abinci acikin plate d'aya kuma da hannuna nake bata itama seta d'ebo tasamin abaki tana dariya,yau kuma naga tasake wani irin kyau na ban mamaki da kallo.
Bayan mungama  ne zan tafi se tazo ta tsaya tana d'agamin hankali,tace"....Mummy I love u cikin gwarancinta na yara love u too nace"....sannan nayimusu sallama nafita,har nakai bakin k'ofa na juyo na bud'e mata hannuna da gudu tazo ta fad'a jikina tana dariya wani sanyi naji araina a take kuma gabana ya fad'i, ajiyeta nayi nace"....Zahrata Allah ya kareminke se na dawo kiyi karatu dakyau kinji banda rashin ji,kiss tabani a kumatau sannna na wuce tana d'agamin hannu,a zuciyata  ina mamakin abubuwan da Fatima tamin yau,addu'a nayi nakoma hanya amma tunanin y'ata ne fal cikin raina,kuma duk tafiyar damukeyi bantab'a jin irin hakanba.
Tohm Anti Fatima Allah Yasa Alkhairi ne.😰😰

Taku a kullum
Young Novelist
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Royal Blood Typing
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

Alk'alamin Auta✍πŸ’✍

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«πŸ’«~*
*~❄We beare's of soo golden a pen,We writer's assiduously percieven No pain,so Magical Our creative golden pen,Be hold our worlds,A product of our pen savour Our worlds for it will  cause u no pain~*

+
🐲🐲🐲
          UQUBAR UWAR MIJINA
🐲🐲🐲
   (Based On True Life Story) (Full Of Sorrow)
Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist.
Dedicated to
My Noorul Huderh
Anti zaynerb.
Allah ya rayamana kai Baby Boo.
Maman Naeema Allah yabaki Y'an uku kisamin mai suna.lol
Bestie Aisha wish u khair  in yah lyf.
More lyf to fans ,Allah yasa kuyi growing kamar grass. Loll.
Tnx All for yah prayers am better nw.
(24)&(25)
      
             To Alhamduliilah munkai Lagos lafiya har nazo Cotonou daganan  nawuce k'asar Ghana nak'arasa siyayata.
Toh bayan na kammala siyayya,kaya na kusan na miliyan d'aya na kama hanyar Lagos.
To munbaro Ghana zuwa Cotonou lafiya,muna zuwa border wacce zata sadamu da Lagos  custom suka tsayar damu.

Dayake Duk tafiyar mu da Hajiya inmunzo sede a sallemesu muwuce se isa banji komai ba,bayan duka Y'an motar mun sakk'o muka nufi gun babban  custom d'in.
      Bayan munje gunsa muka gaishesa duk da ba mutumin da muka saba samu bane,kud'i yak'i karb'a mukayi ta rok'onshi amma fur yak'i yarda.

Nan hankalina ya tashi ganin munfi awa hud'u   muna abu d'aya  amma mutumin nan ko kallon mu ya k'iyi,k'arshe ma yace a kulle masa motar abasa key d'in.

Hawaye nafara ina rok'ansa amma yak'i kulani daga karshe ma yamana koran kare tare da d'aukar motar zuwa garage, haka naci kukana  amma banbar park d'in ba.

Da safe ma haka nazo inata rok'onsu amma sam suka k'i kulani,haka na Hak'ura  nakama hanyar Lagos ina  tunanin inda zan dosa.

Kano    na nufa amma banda niyyar zuwa gidan Hajiya,saboda bansan mezance mata ba.

Can nesa da unguwar na sauk'a gun wata mata wacce take kamar uwar d'akina, fad'a mata yadda akayi nayi kuma tamin alk'awarin bazata fad'awa kowa cewa ina  guntaba.

Haka na zauna agunta harna tsawon sati d'aya, to watarana tazomin da mummunar labarin cewa Fatima y'ata batada lfya tana kyanda.

Hankalina yayi mugun tashi amma bazan iya zuwa ba,kuma Hajiya tasanar mata cewa bandawoba ta nemeni ta rasa,kuma daga zuwa siyan kayane.

Dayake Hajiya akwai kawaici batace nagudu da kayantaba,inbaku mantaba anmin asirin komai na tab'a seya lalace.

Toh haka inaji inagani  y'ata wacce nake bala'in so batada lfya amma ba halin zuwa,sede wannan matar taje ta dubomin ita wani gamin tace"...da sauki jikinnata ko kuma tace"...sunje asibiti jikinde yak'i dad'i.

Watarana nafito zankoma Lagos ko zan samu subani kayan nadawo naga y'ata don har kamar zaucewa nakusayi,turus nayi ganin motar Hajiya a bakin titi ana k'ok'arin  fitowa da Fatima kamar wata gawa ana son sakata a motar asibiti.
Dayake akwai nikab a fuskata nayi saurin matsawa inda Hajiya ke cewa Dan Allah kutayani d'aukar ta,da sauri na tallabeta wani irin sanyi naji ajikina  kallon fuskarta nake kamar na k'ira sunanta.

Idona take kallo kamar taganeni a hankali takai hannunta takama hannuna takai bakinta ta sumbata,hawayen danake mak'ale wane ya fito nayi saurin sata  a motar nawuce ina kuka ganin halin da y'ata take ciki amma ba halin kulata.
Maganar da Hajiyar keyine yadawo min kunnena,naji tana  cewa ya Allah ka dawomin da Mamar yarinyar nan kada ta mutu a hannuna .
Tohm fans.
Kushana da wannan saboda farincikinku nayi wannan page d'in kad'an karkuce banyiba Ku saurarari na gobe.
Taku a kullum
Young Novelist.
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Royal Blood Typing
🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎
Alk'alamin Auta✍✍569379426621615/

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«πŸ’«~*

*~❄We beare's of soo golden a pen,We writer's assiduously percieven No pain,so Magical Our creative golden pen,Be hold our worlds,A product of our pen savour Our worlds for it will  cause u no pain~*+

🐲🐲🐲

          UQUBAR UWAR MIJINA

🐲🐲🐲

(Based On True Life Story(Full Of Sorrow).

Story Nd Written By

Khadeejaht Hydar

Young Novelist.

Dedicated to

  Granny Ummee Aysha.

Allah yak'ara lafiya yaci gaba da baki kwazo akan komai na.

Hmm inamatuk'ar ji da comment dinku fans,musamman Anti Fauziyya,Mrs Ridwan.

Safe trip Ummin Naeema,Allah yakaiku kuma yadawo daku lfya,gonna miss u.

(26)&(27)

     

               Ina zuwa bada b'ata lokaci ba naje gunsu amma kash anmusu transfer zuwa wani garin,tashin hankali nashiga sosai nabar gun jikina,kwakwalwata,zuciyata dama komai nawa ciyo suke min.

Haka nazauna a cotonue na sati d'aya amma narasa abin yi,bayan sati biyu na koma kano inda naji mummunan labari Wanda ya kusan tafiya da kwakwalwata dama rayuwata gaba d'aya.

Bayan na iso bantadda Baiwar Allahn  a gidanba,tana dawowa tafara cewa ina kikaje? haka nan nafad'a mata meke faruwa,zama tayi takama hannuna tace"...Fatima kiyi hak'uri da abinda zan fad'amiki Dan Allah kisama ranki ruwan   sanyi".

Tsoro ne yakamani nace"....meyafaru ne wai kiketamin waennan maganganun?,a hankali tace"...ke musulmace kinyi imani da k'addara,Allahn dayabaki Fatima ya karb'i abinsa,Allahn dayafiki sonta ya amsheta sede kiyi hak'uri. "


Nayi tsawon minti ashirin ban motsa ba tunanina ya tsaya cak, bana fahimtar komai kamar ma ba'a duniyar nakeba.


Jijjigani tayi sosai tukun na motsa,ina tuno abinda yafaru kawai senayi dogon suma.


Bantashi daga sumar danayiba seda nayi kwana uku,da kuka matashi inacewa Dan Allah Fatima karkimin haka wlh nayarda na  mutu ki rayu,Wayyo Allah na Fatima kidawo bazan....kawai senasake suma bansake sanin inda kaina yakeba se bayan kwana hud'u,Ashe allurar bacci akamin don likitan yabada tabbacin inhar na tashi to zaniya zaucewa.


Dana farka ina kuka ina r'okama y'ata gafara gun Allah,Matar ce ke bani hak'uri da lallami.

Gidnata muka koma nazama ba uhm ba uhm uhm,ko abinci setayi dagaske,danace zanje gun Hajiya tace".....ai  batanan tayi tafiya kuma natambaya bansan inda tajeba kuma randa akayi rasuwar ta tafi.


To bayan tafiyata abinda yafaru a gidan Hajiya inda Fatima take SHINE.


Wannan ganin dana musu randa zantafi  Cotonou, to bayan sunje asibiti akabasu gado,bayan kwana biyar ta warke sosai har sun dawo gida.


Kunsan yadda ciwon kyanda yake,to sanadiyyar sane ta rasa ranta.


Haka akamata sutura aka kaita gidanta  na gaskiya.


To ita kuma Hajiya tayanke  shawarar zuwa gun iyayena tunda tanada labarina kuma tasan garinmu,hotunana dake gunta ta d'auka se Wanda tayiwa gawar Fatima da wanda mukayi tare da'ita da Y'arta.


Batasha wiya gun gano gidanmu ba,bayan taje sun tarbeta hannu biyu suka nemi susan daga ina take kuma watake nema tunda basusan taba.Tafad'a mata komai nata sannan tasanar musu da abinda yake tafe da'ita,a razane Mama  tace"...Kina nufin Fatima Y'ar mu kinsan inda take?,tace"...a da ba amma yanzu sam bansan inda takeba,kuma ni wlh koda kayan da kud'in duka sun b'ata nayafemata ,saboda naji dai-dai lokacin data tafi customs sunyi kwacen kaya to ina tsammanin Harda ita,to may be abinda  yahanata dawowa kenan,amma muna addu'a tunda dukanmu munsan meke damunta Allah ya tsareta a duk inda take.


To rasuwar Fatima ce ta k'ara raguzamin rayuwa,saboda ina tsananin sonta har cikin raina,to a haka na baro kano nakama hanyar Lagos.


Acikin mota muka had'u da wata mata da yaranta, to dayake inda son yara akwai wata Y'ar k'arama acikinsu mai suna Fatima,haka kawai naji inasonta don haka ko'ina muka sauk'a innaga abu sena siyama yaran.


Gata yarinyar bazata wuce sa'annin Fatima na ba,gata itama kyekkyawa  da'ita, to ahaka harnafara  janta da wasa dayake kujerunmu na kusa.


Nace"....miye sunan ki cikin gwarancinta tace"...Fatima,sontane ya sake shiga ta a karo na biyu nace"....Allah ya rayaki ya miki albarka cikin gwarancinta tace"...mamin a raina nace"...itama tanada wayo Kamar Fatima ta.

Tohm kubiyoni donjin yazata kaya ne.


Taku a kullum Young Novelist.


🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

Royal Blood Typing

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎Alk'alamin Auta✍✍✍569379426621615/

*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONπŸ’«πŸ’«πŸ’«~*

*~❄We beare's of soo golden a pen,We writer's assiduously percieven No pain,so Magical Our creative golden pen,Be hold our worlds,A product of our pen savour Our worlds for it will  cause u no pain~*🐲🐲🐲

          UQUBAR UWAR MIJINA

🐲🐲🐲

(Based On True Life Story(Full Of Sorrow).

+

Story Nd Written By

Khadeejaht Hydar

Young Novelist.

Dedicated to

  Granny Ummee Aysha.

Allah yak'ara lafiya yaci gaba da baki kwazo akan komai na.

Hmm inamatuk'ar ji da comment dinku fans,musamman Anti Fauziyya,Mrs Ridwan.

Safe trip Ummin Naeema,Allah yakaiku kuma yadawo daku lfya,gonna miss u.

(26)&(27)

     

               Ina zuwa bada b'ata lokaci ba naje gunsu amma kash anmusu transfer zuwa wani garin,tashin hankali nashiga sosai nabar gun jikina,kwakwalwata,zuciyata dama komai nawa ciyo suke min.

Haka nazauna a cotonue na sati d'aya amma narasa abin yi,bayan sati biyu na koma kano inda naji mummunan labari Wanda ya kusan tafiya da kwakwalwata dama rayuwata gaba d'aya.

Bayan na iso bantadda Baiwar Allahn  a gidanba,tana dawowa tafara cewa ina kikaje? haka nan nafad'a mata meke faruwa,zama tayi takama hannuna tace"...Fatima kiyi hak'uri da abinda zan fad'amiki Dan Allah kisama ranki ruwan   sanyi".

Tsoro ne yakamani nace"....meyafaru ne wai kiketamin waennan maganganun?,a hankali tace"...ke musulmace kinyi imani da k'addara,Allahn dayabaki Fatima ya karb'i abinsa,Allahn dayafiki sonta ya amsheta sede kiyi hak'uri. "


Nayi tsawon minti ashirin ban motsa ba tunanina ya tsaya cak, bana fahimtar komai kamar ma ba'a duniyar nakeba.


Jijjigani tayi sosai tukun na motsa,ina tuno abinda yafaru kawai senayi dogon suma.


Bantashi daga sumar danayiba seda nayi kwana uku,da kuka matashi inacewa Dan Allah Fatima karkimin haka wlh nayarda na  mutu ki rayu,Wayyo Allah na Fatima kidawo bazan....kawai senasake suma bansake sanin inda kaina yakeba se bayan kwana hud'u,Ashe allurar bacci akamin don likitan yabada tabbacin inhar na tashi to zaniya zaucewa.


Dana farka ina kuka ina r'okama y'ata gafara gun Allah,Matar ce ke bani hak'uri da lallami.

Gidnata muka koma nazama ba uhm ba uhm uhm,ko abinci setayi dagaske,danace zanje gun Hajiya tace".....ai  batanan tayi tafiya kuma natambaya bansan inda tajeba kuma randa akayi rasuwar ta tafi.


To bayan tafiyata abinda yafaru a gidan Hajiya inda Fatima take SHINE.


Wannan ganin dana musu randa zantafi  Cotonou, to bayan sunje asibiti akabasu gado,bayan kwana biyar ta warke sosai har sun dawo gida.


Kunsan yadda ciwon kyanda yake,to sanadiyyar sane ta rasa ranta.


Haka akamata sutura aka kaita gidanta  na gaskiya.


To ita kuma Hajiya tayanke  shawarar zuwa gun iyayena tunda tanada labarina kuma tasan garinmu,hotunana dake gunta ta d'auka se Wanda tayiwa gawar Fatima da wanda mukayi tare da'ita da Y'arta.


Batasha wiya gun gano gidanmu ba,bayan taje sun tarbeta hannu biyu suka nemi susan daga ina take kuma watake nema tunda basusan taba.Tafad'a mata komai nata sannan tasanar musu da abinda yake tafe da'ita,a razane Mama  tace"...Kina nufin Fatima Y'ar mu kinsan inda take?,tace"...a da ba amma yanzu sam bansan inda takeba,kuma ni wlh koda kayan da kud'in duka sun b'ata nayafemata ,saboda naji dai-dai lokacin data tafi customs sunyi kwacen kaya to ina tsammanin Harda ita,to may be abinda  yahanata dawowa kenan,amma muna addu'a tunda dukanmu munsan meke damunta Allah ya tsareta a duk inda take.


To rasuwar Fatima ce ta k'ara raguzamin rayuwa,saboda ina tsananin sonta har cikin raina,to a haka na baro kano nakama hanyar Lagos.


Acikin mota muka had'u da wata mata da yaranta, to dayake inda son yara akwai wata Y'ar k'arama acikinsu mai suna Fatima,haka kawai naji inasonta don haka ko'ina muka sauk'a innaga abu sena siyama yaran.


Gata yarinyar bazata wuce sa'annin Fatima na ba,gata itama kyekkyawa  da'ita, to ahaka harnafara  janta da wasa dayake kujerunmu na kusa.


Nace"....miye sunan ki cikin gwarancinta tace"...Fatima,sontane ya sake shiga ta a karo na biyu nace"....Allah ya rayaki ya miki albarka cikin gwarancinta tace"...mamin a raina nace"...itama tanada wayo Kamar Fatima ta.

Tohm kubiyoni donjin yazata kaya ne.


Taku a kullum Young Novelist.


🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

Royal Blood Typing

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎Alk'alamin Auta✍🐲🐲🐲

          UQUBAR UWAR MIJINA

🐲🐲🐲

(Based On True Life Story)(Full Of Sorrow)

Story Nd Written By

Khadeejaht Hydar

Young Novelist.


+

Dedicated to

Uzair Basheer.

Moi Bro,za guy wit zero ego nd za caring hrt.

Can't say enough of u but always wish u Allah khair nd Rahma,may Allah  s.w.t bestow his mercy nd increase ur knowledge Amin.


Wish u Khair every one.

Zeeta where are u?,missing u iz not mah wish pls come back bae.

(28)&(29)


Fatima!Fatima!!Fatima!!!Firgigit natashi daga baccin danake,Hajiya ce ta tasheni tace".....Fatima!!!ke kuma daga dawowa dagakasuwa tun jiya da daddare baki shige d'aki ba har yanzu bayan kinsan bana fitowa da wuri  yau juma'a.Tashi nayi ina tuna mummunan mafarkin dana dingayi,a zuciyata nace"...Oh Allah daman duk wannnan mafarkine ya Allah kada ka rabani da Fatima don batason mafarkinnan yazama gaskiya kamar guntun mafarkayyan datakeyi."


A hankali nace"....Mama inasu Fatima?,tace"....inajin ko sun tafi islamiyya tunda ai lokaci ya ja,amma kekam wani irin baccine haka tun jiya se yanzu kalli lokacifa k'arfe sha d'aya na safe."Nace"....wallahi Mama nima banmasan nayi baccin ba,kawai senaji kina tashina."


Toh Allah ya kyauta,tashi nayi naje nayi wanka nayi sallar isha'i da asuba,sannan na rok'i Allah daya sauyamin akalar mafarkina yazama gaskiya don banajin zan iya rayuwa in na rasa Fatima.


Uhm nikuwa Deejerh Nace"...to Allah yasa kada mafarkin yazama gaskiya Amin."


To haka nake rayuwa a gidan Hajiya muna samun kulawa sosai,amma duk lokacin dana tuno mafarkinnan gabana na yawan fad'uwa seda na rik'ata addu'a.


Yau yakama wata uku da dawowarmu daga kasuwa,Hajiya take fad'amin cewa sati me zuwa zamuje Abidjan saboda itama tana harkar saida maganin mata to anan take sayowa.

To haka mukatafi  k'asar Abidjan tare da ita  muka sayo kaya masu yawa,da tsada.

To haka muke zuwa kasuwa tare da'ita mu dawo,cikin ikon Allah ba'a taba tsayar da muba saboda tasan customs sosai,dama kuma hanyar tane.Toh rannan tace"....Fatima tafiya takamani  zuwa cameroon kuma waencan sunce kayansu ya k'are don haka nakeso jibi zanwuce ke kuma gata seki wuce Abidjan d'in.


Gabana ne ya fad'i tuno da mafarkin danayi akan tafiyata, amma a zihiri se nace"...to Mama Allah yakaimu amin."


To sati bayan kwana biyu tawuce ,nima Washe gari natafi Abidjan,motar Lagos na hau saboda tanan yafi sauk'i daga Lagos nabi hanyar Cotonue naje Niger daganan kuma nawuce Abidjan.


Bayan mun shiga mota ne,ina kusa da wata mata da yaranta yarinyar dake hannunta k'arama ce take kuka tana rigima.


Juyowa nayi don nayima uwar magana ko bacci take,gabana ne ya fad'i  ganin Matar danagani a mafarki tare da yarinyar dana gani me kama da Fatima ta.

Kallonsu nakeyi cikeda tsoro da fargaba,a hankali nad'auki yarinyar ina mata wasa,daganan namik'awa uwarta tabata abinci.

Ana gama bata abinci tafara mik'omin hannu,d'aukar ta nayi ina mata wasa nace"...miye sunanki?,mamarta tace"...sunanta Fatima."


Shiru nayi ina tunani kada mafarkina yazama gaskiya,da sauri nace"...Allah ka tausayamin kabarmin y'ata mu rayu tare.


Nikuwa nace"... Uhm.

Haka mukazo wani park donmuyi sallah,tana hannuna muka sauk'a inda har munfara sabawa da Matar saboda na fuskanci matar tanada sauk'in kai.


Abinci dasu nama da kayan ciye-ciye na siyama yaran,muna shiga motar nabawa mamarsu nace"...gashi abawa k'annena,godiya tamin nace"....bakomai."


Cikin muna fira sama-sama ne tace"...ina nake zama a Lagos?,nace mata ga inda zanje sayan kaya,itama tafad'amin inda take zaune mukayi musayar  number.

A Lagos muka rabu dasu inda nayi mata godiya muka rabu kamar daman munsan juna.Hmm turk'ashi .

To kubiyoni donjin ya zata kaya.


Taku a kullum Young Novelist.


🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎

Royal Blood Typing

🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎🐎


Alk'alamin Auta✍✍

UQUBAR UWAR MIJINA
(Based On True Life Story)(Full Of Sorrow)
https://www.facebook.com/groups/
1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION
~*
*_~ We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain~_*
Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist.
Dedicated to my
Beloved Baby Fatima Sulaiman Allah ya rayamin ke.
(30)&(31)
To bayan naje border na shiga niger daganan nayi abidjan don sayo kaya,to Alhamduliilah nakai lafiya kuma nasiyo kaya na abinda yakai miliyan hud'u,
To abinda yafaru dani bazan tab'a mantawa dashi ba,shine silar rugujewar rayuwata.
Bayan nabaro Abidjan nazo border dake tsakaninta da Niger custom suka tsayar damu,suka k'arbe duka kayayyakinmu.
Tashin hankali Wanda ba'asa masa rana na shiga,don mafarkin danayi ne ya fad'omin.
Kuka na fashe dashi don ganin basuda niyyar bamu kayanmu,mun kwashe tsawon awa hud'u amma babbansu yak'i kulamu.
Hak'ura mukayi gaba d'aya muka bargun,zuciyata duk ta cunk'ushe don bak'in ciki.
Gabanane ya fad'i tuno da mafarkina,subhanallah na furto tare da karanta innalillahi wainna ilaihirraji'un Allah ajirni fil musibati haza wakhalifni khairun minha,wannan addu'ar ita yakamata mutum yana karantawa aduk lokacin dawani abun yasameka bawai mutum yana ihu ba,Allah yasa mu dace Amin.
Bayan nazo Lagos se wannan matar ta fad'omin,k'iranta nayi tasanar dani inda take,nacemata ganinan zuwa,tace"...se nazo."
Cikin mota ne nake tunanin abinda ke faruwa ga rayuwata,bangama tunani ba wayata tafara ringing,ganin wata y'ar uwarmuce yasa na d'aga,bayan mun gaisa takecemin Fatima yanzu haka ina gida wata mata daga kano takawo gawar y'arki Fatima,ido na zare cikeda fargaba nace"...shikenan narasata na rasa Fatima mafarkina yazama gaskiya,kawai sena saka kaina tsakanin cinyoyina ina kuka mai tsuma rai dasaka tausayi ga duk mai sauraronta,haka har muka iso unguwar.
Unguwace mai kyaun gaske kunsan de yadda Lagos yake da gina ginan manyan gidaje ga kyau da tsari,unguwar gaba da baya gate ne,bayan Na sauk'a nak'irata tamin kwatance har na iso.
Da fara'arta ta tarbeni tana mini sannu da zuwa,bayan mun gaisa tace"... yanzu har kin kai kayanne ko kinbadane?,kuka na fashe dashi nan na fad'amata abinda yake faruwa,hak'uri tabani kan cewa nayi hak'uri Allah yana tare da ni."
Na k'ara dace mata ina hanya aka k'irani aka sanar dani rasuwar y'ata, tace"... Dama kina da y'a?,nace".. Eh inada yara biyu,nan nabata labarin rayuwata ina kuka tana kuka,nima nayi kuka lokacin da take bada labarinta na rayuwa,ba'aiyawa mutum ko kad'an,wasu burinsu su lalata rayuwar jama'a to Allah ya karemu da mugun ji da mugun gani Amin.
Kuka naci gaba dayi saboda rasa Fatima danayi,haka matar tadinga bani hak'uri har nasamu na d'an tsagaita.
Tace"....toh Yanzu zakije yobe d'inne ko yaya?,nace"...inason naje amma ina tsoron kar akamani a kano saboda dukiyar Hajiya."
Tace"....insha Allah bazasu kamakiba kiyita addu'a,to bayan sati uku a gidan Matar nakama hanyar kano a sace a tsorace don tsoron kar'akamani a d'aure ni.
Bayan naje yobe ne natadda gidanmu yananan yanda yake,iyayena naganina suka fashe da kuka,Rungumesu nayi ina kuka suna kuka.
Mama tace"....Fatima haka Allah yaso sa rayuwarki zamuci gaba da miki addu'a,Allah yajik'an Fatima ya gafarta mata,magana ma kasawa nayi se kuka.
Mama tace"....satin dayawue ina zaune a gd ni k'adai naji sallama,bayan nafito naga wata mata mai kud'i ga babbar mota. "
Bayan mun gaisa ko ruwa batashaba,tafara mini bayanin abinda yakawota, tace"...kinzauna a gunta tunda kikabar gida,to bayan tafiyarki Abidjan Fatima ta fara k'enda Wanda hakan yayi sanadin rasuwarta"
Tazomana da gawar Fatima,kuma na tambayeta shin meyasa bata binneta acan ba?,setacemin ita mutum ce Wanda Allah yabawa arziki tana tsoron ranar da zaki waiwayeta ki tambayi Y'arki kinga batada hujjar gamsar dake cewa Y'arki ta rasu kar jama'a su d'auka nayi tsafi ko kud'i da'ita, to wannan dalilin ne yasata kawomana ita.
Kuka nake na jinjina hali irinna Hajiya,mutum ce mai amana kwarai da gaske,nima nan nafad'a musu abinda yasameni,Mama tace"...Uhm Fatima haka Allah yaso da rayuwarki ,inamiki fatan alkhairi a rayuwarki,kuma Hajiya ta tabbatar mana da cewa ita ta yafemiki duniya da lahira gashi Y'arki ta rasu a hannunta.+

~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION
~*
*_~ We beare's of soo golden pen,We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A product of our pen savour Our worlds for it will cause u no pain~_*
+
UQUBAR UWAR MIJINA
(Based On True Life Story)(Full Of Sorrow)

Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist.

Dedicated to
My Fans,Allah yabar k'auna ina godiya matuk'a.
Zeeta am in love wit ur comment.
Hauwa agabi kisani ina sane dake don haka inamiki jinjina.
(32)&(33)

Kuka nake kamar raina ze fita,saboda yadda y'ata ta rasu amma ko ganinta banyiba.
Haka mazauna agaban iyayena,kafin wani lokaci manema sun fara zuwa amma babu halin aure.
To a b'angaren Khamis kuwa yananan rayuwarsa ta k'ara k'unci,Hm se isa akace inzaka gina ramin mugunta to kaginasa dai-dai tsayinka,jama'a Ku kalli fa Mahaifiyarsa ce tayi sharrin amma yatab'a rayuwar d'anta.
Kinga duk uwa tagari bazataso abinda ze tab'a y'ay'an taba,to itama haka mahaifiyar Khamis Fatima tayiwa kuma yashafi d'anta,don nasan tabbas da tasan d'anta ze koma haka toda bazatayi hakan ba,duk da akwai wasu iyayen dababu ruwansu inhar sunyi kud'irin rusa rayuwar wani to ya shafi kowama ba damuwar su bane su burinsu buk'atarsu ta biya.
In iyayenmu basa karanta novels to mu muna karantawa kuma mu aii iyayen gobe near,kada kazamo me zagin y'ay'an wasu,saboda kana shafama zuri'arkane,in kaga d'an wani yana wani abu to kamasa addu'a ko nasiha ko kuma kayi shiru.
Kamar yadda yazo a hadithin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yake cewa(Falyakul khairan au liyasmut)Kafad'i alkhairi ko kayi shiru,To Allah yasa mufi k'arfin zuk'atanmu da harshenmu,saboda harshe gubace takan lalata rayuwar mutum cikin lokaci k'ank'ani Allah yasa mu dace Amin.
Ahakan nake zaune gaban iyayena harna tsawon wata biyu,to haka kawai naji zaman garin ya isheni bana buk'atar zama cikinsa gaba d'aya.
Amma abinda yake sani tsoron tafiya shine,karnaje akamani a hanyar kano saboda kayan mutane don ni aganina tasaka ido a kaina.
Please manage.Banjin dad'i sosai kuma banso kuji shiru.
Toh muje zuwa Fans.
Nakusa sauk'e muku novel d'innan meban tausayi da gararin rayuwa.
Urs Young Novelist.

Royal Blood Typing
Alk'alamin Auta

🐲🐲🐲
          UQUBAR UWAR MIJINA
🐲🐲🐲
(Based On True Life Story(Full Of Sorrow).

✍✍✍✍✍✍✍
  *GOLDEL PEN WRITER'S ASSOCIATION*  
✍✍✍✍✍✍✍

❄_We are bearers of sooo golden a pen We write assidiously percieven no pain Sooo magical Our creative golden pen Be hold our words  A product of our pen  Savour our words, for it will cause you no pain_❄

+
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
Story Nd Written By
Khadeejaht Hydar
Young Novelist.
Dedicated to
Oll Fans,ina sonku a duk inda kuke.
Nikam mezancewa Ubangiji na inbanda godiya,hakik'a nayi sa'ar fara rubutu inda first novel d'ina yajamin jama'a hardaga Niger.
Farinciki da kunya sukan dabaibayeni wani gamin,inda waenda suka girmeni suke girmamani da ganin k'imata sukecemin anti,ko yau nadaina rubutu Alhamduliilah Alhamduliilah Alhamduliilah nayi achieving d'in abubuwa dayawa,kuma yanzu nagane  cewa rubutu yana daga cikin top first abubuwan dake haskaka tauraron mutum,yakan saka samun farinciki saboda kullum burunmu shine mu fad'akar da alumma.
Some times inna tuna fans sainaji nak'ara jajircewa saboda rubuta,babu abinda zancema Allah se godiya,Kuma babu abinda zancewa Fans se Hamdala,Allah yabar k'auna.

(34)&(35)
LAST PAGE INSHA ALLAH.
To  haka kawai naji zaman yobe ya gundureni naji garin kwata-kwata yafita  araina,don haka nafara shirin barin garin batare da sanin kowa ba.
A d'an zaman danayi   naje k'auyen dana  haifi  Fatima,inda komai yadawomin sabo fil inda nadinga kuka Dakyar kawuna da matarsa suka rarrasheni nayi shiru.
Nayi sati biyu a gidan,nasakejin Kamar ana huramin wutar tsanar garin,don haka nayanke shawarar komawa gida daganan na wuce inda raina yake rayamin..
Bayan nakoma gida da kwana biyu na had'a kayana saboda daman basuda yawa,to nafito k'ofar gida na had'u da Ummin Khamis gaba nane yafad'i kawai senaji  hankali na ya tashi saurin komawa nayi cikin gidan ina jero addu'a.

To muna zaune nida su Mama a tsakar gida muna cin abinci,saboda daman al'adarmuce cin abinci a tare.
Bayan mungama Mama ta kalleni tace"....Fatima Dan Allah kada kisake barinmu muyi zaman mu,in an kwana biyu sai muje Lagos d'in  tunda kince kinason zuwa.
Amsa mata nayi da to Mama Allah yakaimu, daganan kuma muka nufi makwancinmu.
Da sassafe bayan sallah nafito don gaida su Mama,ganin basu bud'e kofa bane yasa nakoma donna kwanta amma me kawai sena samu kaina dahad'a kayana nafito kuma nayi sa'ar bansamu kowa ba a tsakar gida don haka nasa kai nafita nakama hanyar Lagos.

To Bayan na iso Lagos nazo gidan wannan baiwar Allahn damuka had'u a mota,tayi murnar ganina kuma ta tarbeni cikin mutunci da karramawa.

Haka nazauna gunta sama da sati agunta,mijintama Alhamduliilah mai son jama'a ne.

To matar takasance Y'ar kasuwa ita da wata Y'aruwarta duk sana'arsu d'aya, to ganina a zaune gabanta bana komai yasa  suka bani kud'i nafara  juyawa  karna zauna haka saboda sunajin tausayina akan abinda  yafaru dani amma me asirin da'akamin bai bari nacika alk'awari da rik'e amana ba.

Tohm bayana  bayin Allahn nan sunbawa Fatima kud'insu mai d'an yawa tafara juyawa,kwatsam rana tsak'a  suka nemeta  suka rasa ta gudu da dukiyarsu.

Dukansu dayake sunsan abinda ke tare da rayuwarta,sun yafe mata,saboda kaima me karatu zakaji tausayinta saboda komai nata bata d'aukaba,hatta da kayan Y'arta Fatima tabari dawasu kayanta,kaga hakan ze nuna maka kawai an lalata mata rayuwartane anmata abinda bazata'iya zama  a guri d'aya ba sede tadinga yawo,inbaku mantaba wannan malamin yace mata watak'ilama haka zata dinga yawo tana k'arbar kayan jama'a yana lalacewa  har mutuwa ce kawai zata rabata da wannan halin datake ciki.
To bayan tafiyarta,wani yaron matar ya tabbatar daya ganta a hanyar k'asar inyamurai a wata tasha,amma ita bata gansaba.

Daga baya anje hargun amma babu ita,da'aka tambaya akace daman wannan shine farkon zuwanta gun.

To har yau danake shirin     sauk'e muku littafinnan babu  labarin Anti Fatima babu ita,anyi nema har angaji,da wannan nake rok'an fans dan darajar ubangiji kunamata addu'a Allah ya kareta ya yaye  mata abundake damunta😭😭😭Amin S Amin.

To da haka ni Khadeejaht Musa Muhammad Hydar,wacce kuka sani da Khadeejaht Hydar Young Novelist, na sauk'e wannan littafin mai suna UQUBAR UWAR MIJINA.
Ina mik'a sak'on gaisuwata  ga uwa tagari Maimuna Hydar,Allah yak'ara nisan kwana da d'aukaka.Amin.

Post a Comment for "UQUBAR UWAR MIJI COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...