TARAYYAH COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

TARAYYAH COMPLETE

TARAYYAH COMPLETE

- - Post a Comment

 TARAYYAH COMPLETE


Bayine da kuyangi bila adadin akowace kusurwa ta cikin babbar masarautar 

kowanne da aikin daya duqufa yanayi wasu nsu kuma a qaqqame suna gadin 

hanyoyin wucewa da kowace qofa ta cikin masarautar

Dukkaninsu kalar kayansu dayane mazansu da matansu kalar dark blue Wanda 

zaa iya kira da uniform.

Ahankali kowannansu yafara aje aikinda yakeyi yana ra6ewa gefe tareda 

sunkuyarda kai qasa sbd takun tahowar sarauniya Wanda sautin anklets din 

zinarin dake qafarta shine yake sanarda isowarta ko tahowartar tundaga nesa 

wanda tunda ta tashi arayuwarta ta taso agidan sarauta tasaba duk inda take sautin 

sarqar ke sanarda tahowarta harzuwa yanxu data manyanta sbd mulki a jininta 

yake.

Tana qarasowa hanyar dazata shigarda ita 6angaren mai martaba sarki ta tsaya cak 

batareda tace qalaba tareda juyawa ahankali tadan kalli gefenta da dama.

jakadiyarta dake gefenta tayi saurin matsowa tareda juyawa takalli kuyangin dake 

take musu baya kusan su shida kallo daya tayi musu suka ja baya ahankali suka 

tsaya tareda sunkuyarda kai.

Boyayyar ajiyar zuciya tasauke ahankali tareda shiga qofarda aka jima da wangale 

mata jakadiya tabita abaya aka rufo qofar.

Parlour ne mai wani irin girma da tsari dayaji adon royal chairs red and golden 

kamar zinari sai qyalli suke sai komai daya qawata palon yazamto shima red and 

golden dinne splits aircon kusan guda biyar sai aiki suke sanyi yakama palon 

takoina sbd wata irin dukiyace ta musamman aka narkar a palon.Babu kowa a palon sbd palon farkone dazai sadaka da palon sarauta harzuwa 

turakar sarki 

Ta sake tsayawa cak tareda sake sakin wata sahirtacciyar ajiyar zuciya akaro na 

uku zuciyarta na harbawa batareda tajuyo bangaren jakadiyaba murya a karye 

tace,

Wannan saqon na sultan(sarki) yana matuqar girgixa zuciyata sbd saqone daya 

zamto na baqin ciki agaresa,

Duk wani bawa ko bafade yakai wannan saqon abakacin rayuwarsane shiyasa 

nazabi nazo na isardashi dakaina,

Ajiyar zuciya mai nauyi jakadiya ta sauke tareda kallon sarauniya zaarah din cikin 

tausayawa acikin aranta afili tace,

Allah yataimaki sultana yakuma sanyaya ranki badan kinyi rashiba yabaki ikon 

isarda saqon sarkin sarakuna....

Katseta sultana zaraahtayi da cewa,

Haihuwa tazamar mana abar fargaba maimakon farin ciki.

Uwargijiyata Allah ya sassauci fargabarki amma dakin sake kin nunawa yarima 

farin cikinki da qaruwar dayasamu tunda shi yanaso ahakan kuma yana godiyar 

Allah da arzikin qaruwa daya basa

Allah ya raya abinda aka Haifa din yasa ayi alfahari da hakan gaba.

Ajiyar zuciya sultana tasake tareda furta amin qasan maqoshinta kafin ta tattaro 

jarumta da qarfin gwiwa ta gyara zaman gyalen kanta daya rufo dogon gashinta 

dake kwance har bayanta Wanda shima gashin harzuwa goshinta adone na wata 

kyakkyawar sarkar zinari ta kai sai aka rufo gyalen doguwar rigarta dark purple 

dataji adon duwatsu masu shegen kyau da kyalli gyalen naja har qasa kadan.

Ratsa dogon palon tayi jakadiya na bayanta ta nufi qofarda zata kaita ainihin 

palonsa na musamman tana zuwa wanda ke tsaron qofar ya wangale mashekarar

ahankali tashiga jakadiya takoma gefe ta toge itama tana jiran fitowar uwar dakin 

tata.

Wani palon ne na alfarma babu kowa sai qarar ac dake tashi ahankali 

Zaune yake cikin shiga ta alfarma 

Dattijone sosai da Hutu da mulki na jinin sarauta daya ratsasa,

Kallo daya yayi mata da idanuwansa masu tsananin kwarjini da firgitarwa taso 

rudewa tayi saurin daidaita kanta ta tattaro nutsuwa da qarfin hali.

Qarasowa tayi cikin sanyin jiki da fargaba ta kallesa ta rufe idanuwanta dasuka 

fara canxawa murya na rawa tace,

Allah yataimakeka saqo daga GEORGIA.....

Idanuwan daya sake watso matane yasa taso daburcewa tayi saurin gyara murya 

cikin nutsuwa ta dauke idanuwanta daga kallonsa murya na rawa tace,

Yarima yabugo yasanarda saqon matarsa ta sauka ansamu 'YA MACE.

Sake dauke kai tayi sbd gudun ganin yanayinsa sbd kodagajin yanda ya dauke 

wuta tasan ran maza ya baci babu jin dadi ko alamar farin ciki dagajin saqonta.

Tsawon mintuna ashirin shiru 

Kamar daga sama taji dakakkiyar muryarsa cikin ikon mulki yace,

Kin isarda saqon yarima Dan haka kisanardashi saqonsa ya iso 

Ke kuma tukuicinki na sanarda saqonsa bazaki sakashi a idoba sai bayan shekara

daya,

Karya dawo harsai matarsa tasake samun wani cikin wannan karon anan zata 

haihu

Zata haifi yariman da ubansa yaqi amsa.

Yana gama fadar haka ya miqe zai shige turakarsa

Dagowa tayi takallesa idanuwanta na canxawa zuwa kalar tausayin kanta 

dabazataga 'dantaba ko awannan shekarar

DOWNLOAD HERE👈

Post a Comment for "TARAYYAH COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...