SANNU SANNU BATA HANA ZUWA COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SANNU SANNU BATA HANA ZUWA COMPLETE

SANNU SANNU BATA HANA ZUWA COMPLETE

- - Post a Comment

 SANNU SANNU BATA HANA ZUWA COMPLETE[6/15, 11:34 PM] My S Nomba: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž+ _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___3πŸ’Ž Murmushin da bai kai ciki ba shurahbil yayi masa yana kallon yaran da suka duqufa suna kallo abunsu hankali kwance, bud'e gambun motarsa yayi yafito tare da miqa masa hannu suka gaisa, fuskar shurahbil a d'aure yace "ammm.......kamar naso nawayi fuskarnan, waye kai? ya tambayeshi Kai tsaye batare da wani shayi ba. "Ni ba kowa bane" shima ya bashi amsa atak'aice, "Ok meya kai yarannan acikin motarka bawan ALLAH?" Yasake jefa masa wata tambayar batare daya dubi girman saba, Yana tunanin wane daliline zaisa daga ganin yara ya d'aukesu yatura cikin motarsa, ko dai so yakeyi ya sace sune, muryarsa yajiyo yana cewa, "Ganin yanda kabar motarka abud'e sun fito batare da sanin inda zasu nufa ba shine dalilin da yasa nayi tunanin tsayawa na taimakeka ta hanyar tsaidasu har sai kadawo, yakamata kasan cewa wannan abun da kayi sakaci ne babba kuma kuskurene? qananan yarane su dake buqatar cikakkiyar kulawa, don haka yakamata akula dasu sosai" bai jira me zai ceba ya sake bud'e gambun motar yace dasu, "Yawwa yaran baba, kuzo ga baba nan yadawo kunji ko?." Maqale kafad'a sukayi sunaci gaba da kallonsa yayi murmushi tare da cewa, "yatafiyarsa kenan kun fasa zuwa wajen dady da ummie ko?" "Laa..a'a nidai zanje." hassana tafad'a, hakan yasa itama hussaina ta taso tana fad'in, "nima zanje wajen dady da ummie." Fiddosu ya dingayi d'aya bayan d'aya daga cikin motar ya diresu qasa had'e da juyowa yana kallon shurahbil daya saki baki yana kallonsu yace, "ga yaranka nan, amma don ALLAH yakamata adinga kulawa" sannan ya shiga motarsa ya tayar yaran na d'aga masa hannu suna yimasa byebye, yana qoqarin barin wajen da sauri shurahbil ya iskosa tare da duqowa ta saiti jikin glass d'insa yace "afuwa alhaji, dama kasan yaran nan ne?" Girgiza kai mutumen yayi don yafahimci gaba d'aya shurahbil qurciya na damunsa, girmane kawai ya rigayi hankali saboda yanayin yanda yake magana, abun nasa kamar rashin iya magana kamar kuma isa da jijji da kai a tattare dashi, kallonsa yayi sannan yace, "Ban sansu ba kuma ban san ko suwaye su ba, Amma abu d'aya nasani shine tun wajen da sukayi accident dana ganesu jikina yabani cewa kamar akwai wata alaqa tsakanin ni dasu kuma araina naji ina sonsu har acikin zuciyata hakan yasa nabiyo bayanku lokacin da kuka taho dasu, ina fatar jikin iyayen nasu da sauqi saboda tsaurin tambayoyinka d'azun sun kasa barina na tambayi hakan tun farko" sinne kai qasa yayi yana sosa qeyar kansa had'e da cewa "kayi hak'uri Alhaji naji tsorone araina saboda yanda duniyar tamu ta koma." "Babu komai in sha ALLAH ka gaida iyayen nasu, in sha ALLAH gobe zanzo nadubasu saboda marece yayi yanzu." "Shikenan Alhaji Amma shi mahaifin nasu ALLAH yayi masa cikawa, mahaifiyarsu kuma anyi nasarar yimata tiyata anciro wasu 'yan biyun" da motar na slow amma alhaji najin haka ya kashe motar yana sallallami kai kace wani shaqiqin sane, yajima yana jajanta abun aransa tare dayi masa addu'a sannan yabar wajen bayan ya bashi complement card d'insa. Yana barin wajen yanufi inda twins d'in suke zaune agaban motar suna wasarsu hankali kwance yaje yaja hannuwansu ya nufi inda su Abba suke riqe dasu... Suna isa Abba ya miqa masu hannuwa alamar suje wajensa, da gudu suka isa tamkar sun sanshi ya rungumesu yana kallonsu d'aya bayan d'aya yana jin wani irin sonsu da k'aunarsu nashiga zuciyarsa, kallo d'aya zakayi masu kasan kamarsu sak da mahifinsu tamkar an tsaga kara hasken fatar mahaifiyarsu ne kad'ai suka d'auko, hawaye ne suka zubo masa a idanuwa yagoge had'e da cewa. STORY CONTINUES BELOW "ALLAH sarki batool, Ashe rabon wu 'yannan jikokin nawa yasa kika iya jurewa rabuwa dani bayan kinsan irin tsantsar so da k'aunar da nanuna maki acikin 'ya'yana, wacce har takasa b'oyuwa azuciyata, har kikayi nesa dani ban dena jin wannan qaunar taki araina ba, ubangiji ALLAH ya tashi kafad'unki, ALLAH yabaki lafiya kiga yanda soyayyarki ta dinga lunkuwa a kowace rana cikin shekarunnan da bakya tare dani." Haka Abba yayita suruttansa tamkar wanda yafara zarewa yayinda yaran daya d'ora saman qafafuwansa suke jan d'an farin gashin dake shimfid'e a fuskarsa. Tuni su uncle h suka kira matansu suka sanar dasu halin da ake ciki wanda nan take family da suka had'u don walimar tarbarsu da Abba ya shirya suka fara koke koke, baran mahaifiyar batool da kad'an yarage itama arasata saboda matsananciyar fad'uwar da tayi a some, tajima kafin asamu ta farfad'o, kuka takeyi sosai tana roqon ALLAH ya sassautawa 'yar tata kuma yajiqan mijinta, nan take duk aka watse jikin kowa a sanyaye, asibitin wasu suka nufa wasu kuma suka wuce gidajensu saboda basu sanar da mazansu ba, kafin kace me tuni asibitin tafara samun halartar 'yan uwa da abokanan arziqin Abba da 'yan uwansa tako ina, duk wanda yaji labarin abunda yafaru saiya zuddarwa da yaran hawaye domin har zuwa lokacin ita batool d'in bata farfad'oba, Dr sadeeq ne yadawo wajensu uncle akan zancen gawar Abu sumayya da suka buqaci abasu akace sai zuwa gobe idan police d'in da suka tsaya sunzo sunsa hannu, hakan yamatuqar qonawa Uncle Hassan rai da yasa yanata fad'a har saida Abba yabashi haquri shida Dr sadeeq sannan yayi shiru. Ita dai mahaifiyar batool hajia salmah abu yakashe mata biyu, nafarko damuwar halin da 'yarta ke ciki na biyu kuma maraicin da wud'annan qananan yara har su hud'u zasu fuskanta, tayi farincikin kyauta da kuma ni'imar da Allah yayiwa 'yar tata amma sam damuwa takasa barin haka ya bayyana a fuskarta, ita da mahaifiyar shurahbil ne suka zauna zaman jinyar batool da kuma kula jariranta, yayinda Abba yace matar uncle hussain da kuma abokiyar zaman hajia salmah wacce ake kira da Rabi'atu su zauna gida sukula da yara da hidimar abinci, Tun daga Abba har su uncle h babu wanda yakoma sakama bakinsa wani abun tun safe, hakan yasa bayan sallar magrib hajia salmah da suke kira da hajia mama ta kallesu had'e da cewa, "ya kamata ace damu daku duka mun fawwalawa ALLAH komai, mudangana da tsarin da yayo mana domin bamusan dalilinsa nayin haka ba, don ALLAH ku daure ku zauna kuci abinci kada kuma wani abun ya sameku." Wata qatuwar kula tajawo ta mik'awa shurahbil da isowarsa kenan shima yadawo daga masallaci tace, "ungo nan shurahbil je kazubawa iyayenka abincinan suci kuma kaima don ALLAH ka tabbatar ka zauna kaci naka" "To hajia mama, Ina yarana suke?." "Kagansu nan har sunyi bacci." Tafad'a tana miqa masa plates da spoons, karb'a yayi had'e da cewa, "yakamata hajia akirawo zainab tawuce dasu gida ta watsa masu ruwa, yau sun matuqar jigata sosai, donma yaro yana yaro ai da sai jikinsu yafad'a masu, amma kingansu nan yau sau uku suna barci suna tashi wannan shine na hud'u." "Hmmmm! Shurahbil kenan!, ai dolene suyishi, baccin rashine ALLAH dai yajiqan mahaifinsu." ya amsa da amin sannan ya wuce inda ya hangosu acan cikin wata runfa da aka tanada domin patient relatives. Gaida iyayen nashi yayi tare da qoqarin bud'e kular bayan ya ajiye uncle hussain ya dakatar dashi, "kaje dashi can cikin mota saboda bazan iya ci anan ba sai dai kosu alhaji idan zasu iya su." kallonsa Abba yayi sannan yace, "Kana tunanin abunda duk baibar kaba zai barmune mu?, Aje dashi duka cikin motar gamunan zuwa." Haka shurahbil ya sake kinkimar kular abincin da plates yakai cikin mota ya d'ibi nasa a plate ya rufe da wani plate d'in sannan yabaro wajen, masallaci yakoma yaci nasa duk da bawani ci yayi ba d'an tsakurane kawai yayi saboda hajia mama data had'asa da ALLAH, badon haka ba bazai iya cin abinci acikin asibiti ba. Saida ya kwatanta sun kammala ci suma sannan yaje ya d'auko masu lemu da ruwan da a kazo dasu na gora ya kai masu ya kwaso kayan da suka gama cin abincin ya maido wajensu hajia mama. STORY CONTINUES BELOW Sosai Abba yaso yaji takamammen bayani akan lafiyar batool amma hakan ya cutara saboda tsoron yanayin da zai iya shiga, tamatuqar wahala saboda ana gama mata tiyata lumfashinta ya d'auke, kusan likitoci bakwaine suka taru akanta kafin su samo da taimakon ALLAH lumfashin ya dawo, shima d'in da qyar take fiddashi wanda sanadiyar hakanne ake shiga da Oxygen aguje saboda ya taimaka mata, daga lokacin da akayi mata aikin zuwa dare ta shanye tukunya hud'u na oxygen, sai bayan sunga lumfashin nata ya daidaita ne kuma suka fara qoqarin treatment d'in raunin da taji a fuska duk da dai and'an bata emergency care kafin akawota nan. taji rauni sosai sabod duk glass d'in mota ya yanke mata fuska har saida aka ciccire mata wani da ya shige, idanuwanta kad'aine ALLAH ya kare basu samu wata matsala ta sokewa a xahiri ba ko kuma wani internal injury aciki ba, Amma hatta kanta ya bugu sosai wanda Dr odugun ya sanarwa dasu uncle h sai ta farka za'a iya gano cewa bata samu wata matsala acikinsa ba idan anyi gwaje gwaje, kallo d'aya zaka yimata kasan tanajin jiki saboda yanda aka nannad'e mata fuska da bandage ba'a bari kowa yashiga d'akin sai nurses da kuma masu jinyarta suma d'in saida dalili. Jariran kuwa tunda aka cirosu Dr imaan ta karasu ga nonon mahaifiyarsu suka d'an tsots-tsotsa har yanzu ba'a basu komai ba, sunyi kukan har sun gaji amma Dr tace kawai asa masu drip zuwa gobe tunda har lokacin mahaifiyarsu bata farko ba, Abba dasu uncle basu bar asibitin ba sai misalin qarfe sha biyu da rabi na dare bayan shurahbil yaje gida ya watso ruwa ya dawo shi da zainab sister d'insa ta d'auki su hassana sannan su Abba suka wuce da ita gida saboda anan shurahbil zai kwana Koda za'a buqaci wani abun.... _*ALLAH KAJIK'AN IYAYEN MU*_πŸ‘πŸ»πŸ˜­ [6/15, 11:34 PM] My S Nomba: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKIN KINE SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO (OUM AFFAN)*❤️ _ALHAMDULILLAH INA GODIYA GA RABBIL IZZATI WAL JABARUD DAYA BANI IKON SAKE DAWO MAKU DA WANNAN SABON LITTAFI NAWA DAKE CIKE DA 'DIMBIN DARUSSA DA NAKE FATAN SUZAMO TSANEN DA ZAMU IYA TAKAWA WAJEN GYARA KURA-KURANMU, WANNAN LITTAFI GABA 'DAYA QIRQIRARSA NAYI BISA LA'AKARI DA WASU ABUBUWAN DAKE FARUWA ACIKIN RAYUWARMU TA YAU DA KULLUM DON HAKA IDAN KAGA YAYI KAMA DA RAYUWAR KA/KI TO AKASINE KAWAI, SAI MUYI QOQARIN GYARAWA, FATANA ALLAH YA YAFEMUN KURAKURAN DA ZASUZO DAGA CIKINSA KUMA YASA DANI DAKU MUYI TARAYYA ACIKIN LADAR DA ZATAZO ACIKIπŸ‘πŸ», HAR ILA YAU BAZAN MANTA DA ADDU'AR FATAN ALKHAIRI AGAREKU BA *YA HAJJA CE* DA KUMA TAWAN *SALMA ABALI (LITTLE PRINCESS)* INA ROK'ON ALLAH DA YATABBATAR MAKU DA ALKHAIRANSA KUDA AHALINKU ADUK INDA KUKE, *MLF*_πŸ’‹πŸ‘πŸ» Page___1πŸ’Ž Tafe suke cikin wata kyakkyawar mota k'irar BMW da kallo d'aya zakayi mata kasan cewa sabuwace dal da ba'a dad'e da fiddota acikin ledar taba saboda yanda take faman sheqi da qyalli, cikin natsuwa matuqin motar ke tuqinsa yayin da wacce ke zaune agefensa da tsohon cikinta dake nuna alamar ko meye aciki neman fitowa yakeyi akoda yaushe, muskutawa tayi sannan tajuyo cikin zaquwa had'e da kallonsa tana cewa, "Abu sumayya wai wannan wace irin tafiya ce kakeyi haka?, Don ALLAH kataka motar nan da sauri, wlh namatsu naganeni agaban Abbana da kuma ummata." yanayin yanda take maganar kad'ai tana faman kashe murya shi zai tabbatar da cewa ita d'in matarsa ce, cikin k'warewa da iya tuqi ya juya sitarin motarsa ya shiga kwanar dake gabansa tare da d'an qara gudun motar kad'an sannan yace, "Gimbiya! haka yayi maki?." Yafad'i hakan batare daya d'auke idanuwansa daga kan titin da yake kallo ba "kad'an qara mana." tafad'a tare da juyawa ta sit d'in bayansu tana kallon yaransu 'yan mata su biyu dake kwance bacci ya d'aukesu, kallo d'aya zakayiwa yaran katabbatar da cewa 'yan biyune saboda tsantsar kamar da sukeyi da junansu, wata kyakkyawar ajiyar zuciya tayi had'e da shafa tulelen cikin dake jikinta tace, STORY CONTINUES BELOW "Alhamdulillah, Abu sumayya namatsu mu isa gida naga farincikin da zai bayyana a fuskar Abbana idan yaganeni tare da wud'annan kyawawan jikoki da ALLAH ya albarkacesa dasu bayan rabuwarmu dashi na tsawon shekaru bakwai, ga kuma wata kyautar agefe tare dani wacce nake fatar Allah yasa takwaransa ne aciki, natabbata hakan zai qara sakasa cikin farinciki sosai, Kuma yasake gusar masa da abun da nayi Masa azuciya" "To ALLAH ya saukeki lafiya gimbiya kuma yabamu abunda muke fata don cikar burinmu da kuma tabbatuwar farincikin Abban da kike hasashe." "Amin Abu sumayya." tafad'a tare da d'ora kanta saman kafad'arsa, shirune yabiyo baya na tsawon mintuna biyar kafin tasake cewa, "Wlh gani nakeyi kamar bama tafiya, hanyar tamkar ana qaramata tsawo, wataqil don na jima ban bita neba?." murmushi yayi had'e da cewa "Kai gimbiya d'oki dai ne kikeyi, Amma ai ba laifi ina tafiya sosai, kiyi hak'uri, ai sannu a hankali zamu isa in sha ALLAH kilometers biyar ne yarage mana, kinji hausawa nacewa SANNU SANNU bata hana zuwa...." Kafin yarufe baki yaji tace, "Sai dai adad'e ba'a kai ba, kuma ni shine bana so." taqarasa maganar tana turo baki had'e da mik'ewa zaune daidai, "Abu sumayya naji marata tad'an murd'a." Rage gudun yayi had'e da cewa, "Subhanallah Gimbiya ko abun yazo ne?." Yafad'a tare da juyowa yana kallonta a d'an firgice, yatsina fuska tayi sannan tace, "Bana tsammanin hakan, saboda idd na sai next month on 13 yanzu kuwa kaga muna 25 ne dis month." Tana rufe baki wata qatuwar mota tayo cikinsu aguje tare da gittawa agabansu, ji kakeyi qiiiiiiiiii...gigigigif..karaf, tabugi motarsu tafad'a jikin wata motar dake tafe bayansu itama tana k'ok'arin kaucewa ta d'ayan gefen, sosai yake qoqarin juyar da staring motar da dukkanin k'arfinsa da kuma gwanewarsa amma da yake duk qaddarar da ALLAH yatsaro akan bayinsa ko suna so ko basa so sai wannan alqalamin da aka dad'e da rubuta qaddarsa ya tabbatar da ita agaresa, duk iya qoqarinsa kasa iya sarrafa motar yayi balle ya samu nasarar tsaida ita waje d'aya, ganin haka yasashi qoqarin riqo matarsa da tuni kanta ya bugi glass d'in motar yafita tacan waje yayin da gangar jikinta na acikin motar, cikin yanayin fad'uwar gaba da kuma firgici yafara k'ok'arin jawota sai ji yayi sun bugi wani abu da yasa motar tasu tsayawa cak, daidai lokacin shi kuma kansa yabugi dashboard d'in motar da k'arfi wanda yasa nan take yaji gaba d'aya na'urorin dake aiki a sassan jikinsa sun tsaya cak, hatta jinsa da ganinsa ji yayi suma sun d'auke alokaci d'aya, cikin tashin hankali mutanen da suka tsaitsaya akan titin suna salati ganin yanda wannan tashin hankalin ke faruwa sukayo kansu ganin motar ta tsaya don kawo masu d'auki, gaba d'aya motar ta nad'e waje d'aya sanadiyar wani makeken dutsi da suka buga, kallo d'aya zaka yiwa motar ka rantse baza'a samu rayuwar ko d'aya daga cikin mutanen dake cikin taba, ganin jini na malalowa tak'ark'ashin motar ya sanya mutanen himmatuwa wajen b'alla gambun motar ta kowane gefe, shi suka fara jawowa kafin suyi nasarar fiddo da matarsa fuskarta gaba d'aya jini ya wanketa ta yanda bazaka iya gane ko wace itaba, cikin tashin hankali suka ida fiddo da ita daga cikin motar tamkar gawa saboda ko motsi ba tayi, hankalinsu bai tashi ba sai lokacin da suka lura da tulelen cikin dake jikinta sai faman motsi abunda ke ciki yake ga kuma jini d'aya b'alle mata na faman kwararowa daga k'asanta, cikin rud'ewa wani daga cikinsu ya d'ago kai yana kallon wud'anda ke kan mijin nata yace, "Matarnan tana buqatar taimakon gaggawa." Bai rufe baki ba mijin nata da tun d'azu ake faman yayyafa masa ruwa ya farfad'o tare da bud'e ido, ko kad'an babu alamar k'warzane ajikinsa da zai nuna yaji ciwo wanda hakan yaja hankalin mutanen akan doguwar sumace yayi suka fara yayyafa masa ruwa, k'ok'arin bud'e baki yayi yayi magana amma yakasa saboda lumfashinsa da yakejin yana qoqarin fin qarfins, yana gani aka tallabi matarsa aka nufi cikin wata motar da ita don ceto rayuwar abunda ke cikinta don gaba d'aya alokacin bata rayuwarta suke ba saboda ganin yanda cikin nata ke motsi kamar zai fasa cikin ya fito, sake yunqurawa yayi zaiyi magana idanuwansa na hawaye yana kallon yanda cikin nata ke motsi amma yakasa, kamar wanda aka tsikara da qarfi yajuyo ya maido kallonsa awajen motar tare da d'aga hannu yana nuna masu, da k'yar yabud'e baki yace, "'ya'yana..." Bai k'ara saba jini yafara fitar masa abaki tare da sakin hannunsa ya fad'i qasa, da gudu wasu suka d'aukesa suka nufi motar da akasa matarsa aciki lokacin har ana qoqarin barin wajen aka sakashi shima cikin motar tabar wajen dasu aguje, yayin da wasu suka nufi wajen motar suka fara qoqarin b'alla gambunanta na baya, koda sukayi nasarar b'alle gambunan motar basu ga komaiba a saman sit d'in sai da suka leqa a k'arqashin motar sannan suka hango qananan yara a qarqashi, gashi motar ta molak'e waje d'aya babu isasshen wajen da za'a iya jawosu hakan ya matuqar tayarwa da mutanen wajen hankali saboda rashin sanin makomar yaran da kuma sanin ko awane hali suke ciki awajen. STORY CONTINUES BELOW Anan sukayi cirko cirko suna shawarar yanda za'ayi a fiddo yaran, wani mutumne daga cikinsu yabada shawarar tunda akwai wani gari dake nan gaba kad'an aje asamo k'wararrun masu gyaran mota da suka iya kwanceta da had'ewa suzo su kwance motar gaba d'aya a fiddo yaran ko nawane shi zai biyasu, haka kuwa akayi cikin mintuna ashirin wane yaje yazo dasu su biyu d'auke da kayan aiki, nan take suka fara aikinsu cikin k'warewa wanda cikin minti 30 sai gashi sun raba body d'in motar da shimfid'ar qasanta, da sauri aka ciro yaran har lokacin gaba d'ayansu bacci sukeyi, bazaka tab'a cewa daga cikin motar aka fiddosu ba saboda ba wadda tayi ko qwarzane acikinsu inba d'ayar data d'an karce agefen kuncinta ba wanda ga alama wani qarfene ya karjeta, "ALLAHU AKBAR" wud'an ke wajen suka fad'a cikin mamaki da kuma tsoron ALLAH da gasgata ikonsa don gaba d'aya babu wanda yasa ran za'a fiddosu da rayuwa saboda la'akari da yanda motar ta mokad'e waje d'aya, ana hakane suka jiyo qarar waya acikin motar a gefen da aka ciro matar, d'aya daga cikin sune yaje yana bin sautin qarar wayar dake cikin jikkar ya d'auko tare da ciro wayar ya d'aga. "Assalamu alaikum." Shine abunda yafad'a kafin yaji an amsa masa ta d'aya b'angaren da, "wa'alaikassalam." Cire wayar yayi a kunnensa ya duba sunan dake yawo a screen d'in wayar yaga ansa _ABBANA_ hakan yasa yayi saurin maida wayar a kunnensa yana kallon sauran mutanen dake wajen tare dashi sannan yayiwa mutumen da tun d'azu sai faman tambaya yakeyi ina mai wayar bayanin abunda ke faruwa, Nan take yarud'e yafara tambayarsa adaidai wane wajene abun yafaru, cikakken bayanin yayi masa don akwai buqatar yazo yakarb'i yaran dake wajensu kafin yasan da komai sannan ya kashe wayar, Kallon wud'anda suka kwance motar mutumen da yasa aka kirawosu yayi had'e da cewa, "bayin ALLAH nawane za'a biyaku?." Gaba d'aya suka amsa masa da "A'a alhaji, kabar kud'inka don ALLAH mukayi, ubangiji ALLAH yatsare kuma yatashi kafad'un iyayen yaran nan," suna gama fad'ar haka suka d'auki kayan aikinsu fuskokinsu cike da tausayin halin da akace masu iyayen yaran na ciki sannan suka wuce, duk mutanen dake wajen godiya tare da addu'ar fatan alkhairi suka yimasu saboda karamci da 'yan uwantakar addini da suka nuna. Kasan cewar kilometers biyar ne yarage a tsakanin inda akayi had'arin da kuma cikin garin kano inda iyayen wud'annan yaran suka nufa yasa Abban nata d'aukar dogon lokaci kafin ya iso wajen, hakan yasa mutanen duk suka fara watsewa d'aya bayan d'aya lokacin har yaran sun farka sun fara kukan ina iyayensu suke, A b'an garen sauran motocin da akayi had'arin dasu kuwa dama shi drivern babbar motar daya bugi motarsu tafad'a can gefe koda aka fiddosa yarasu, haka itama qaramar motar dake gefensu da yake irin golb d'innan ce ta haya mutum hud'u sun rasu, uku kuma sunyi rauni sosai ciki hadda drivern motar suma anwuce dasu assibiti tun d'azu, Sosai yaran ke kuka anyi rarrashi har angaji amma sunqiyin shiru har saida wannan mutumen yaje yabud'e cikin motarsa ya d'auko gorar ruwa yadawo da ita riqe ga hannunsa ya nunama d'ayar yace, "Zaki sha ruwa?" Batayi magana ba amma yanda take kallon gorar ruwan shizai tabbatar maka da tanada buqatarsu, bud'e murfin gorar yayi sannan ya azamata abaki ba musu tafara sha, saida tasha sosai sannan ta jaye bakinta daga gorar tana sauke ajiyar zuciya, 'yar uwarta ya nufa da gorar Amma ga mamakinsa sai yaga ta sake fashewa da kuka sosai fiye da wanda takeyi farko tare da kauda kanta gefe, hakan yasa ya janye gorar, yamiqa hannu tana shessheka ya karb'eta, ajiyar zuciya ya sauke don ko kad'an baya son kukan yara, kallonta yayi ya sake kallon 'yar uwarta da itama sai faman ajiyar zuciya takeyi tasa hannunta cikin baki tana tsutsa yaji inama ace wud'annan yaran nasa ne, kamarsu d'aya babu inda suka banbanta inba yanzu da d'ayar ta karce a gefen kuncinta ba bazaka tab'a iya banbancesu ba, wanda hakan zai tabbatar maka da cewa su d'in 'yan biyune, 'yan biyunma irin wud'anda ake kira da (identical twins), gaba d'aya shekarunsu bazasu wuce 3 ba aduniya Amma kana ganinsu zakasan suna da d'an banzar wayau sosai, yana wannan tunanin ne wayar da aka ciro acikin motar dake hannun wanda ke riqe da d'ayar tayi qara, d'agawa yayi yaji Abban yace, "bawan ALLAH gani na iso wajen." Yafad'a muryarsa na rawa tare da yin parking motarsa daidai inda yaga babbar motar tafad'i da d'ai d'ai kun mutane a tsaitsaye awajen, wani kyakkyawan dattijo ne fari tas yafito daga cikin motar riqe da sanda qafafuwansa na rawa ko d'aukarsa basayi sai wani saurayi daya fito daga mazaunin driver da alama shiya tuqo motar tare da wasu maza su biyu kamarsu d'aya da alama suma tagwayene ko kuma wa da qane suka fito daga cikin bayan motar suma dai d'in sun manyanta amma ba kamar tsohon daya fara fitowa ba da gaba d'aya gashin dake kansa da fuskarsa farine tas ya cika da furfura, har lokacin wayar na akunnensa suna magana da mutumen, juyawa yayi ya hangosu tare da d'aga masu hannu da sauri duk suka nufo wajen in banda d'an saurayin daya tsaya yana tattakawa tare da tsohon, bayan sun iso wajen duk aka mimmik'a hannuwa aka gaggaisa ya nuna d'ayansu yace, STORY CONTINUES BELOW "Ranka ya dad'e kaine Abba ko wannan?." Da sauri duk suka juya suna kallon tsohon dake takowa riqe da sandarsa sukace "wancan shine Abba kuma yayanmu, Ina bayin ALLAHn da kukace sunyi had'ari suke?." Saida ya qaraso aka sake gaisawa sannan yace, "kuyi haquri anwuce asibiti dasu, Amma ga wannan itace wayar da aka gani acikin motar tare da wud'annan yaran" yaqarasa maganar tare da miqa masu wayar sannan suka ajiye yaran agabansu shida d'ayan mutumen dake riqe da d'ayar yarinyar." Sai alokacin suka lura da qananan yaran 'yan mata dake wajen, cike da mamki suka bisu da kallo saboda tsantsar kamar da sukeyi da mahaifinsu tare da girmama ikon ALLAH ganin yadda motar tayi amma yafidda yaran lafiya klw batare da sunji ciwo ba, kad'an ya rage tsohon da ake kira da Abba yafad'i saboda tsantsar kamar yaran da mijin 'yar tasa daya gani, da sauri suka riqesa cikin kuka yace, "Ina 'yata da kuma mijin nata suke?." "Haba Yaya kabi ahankali mana kada kafad'i, suna assibiti wud'an yaransu ne akace" "Innalillahi wainna ilaihirrajiun, nagani hussaini ga kamar yaron nan sak atare dasu, don ALLAH ku kaini asibitin inga halin da 'yata take ciki, shekara bakwai kenan ina son ganinta Ina mararin had'a idanuwa da ita, ku kaini kona samu inroqi yafiyarta" yaqarasa maganar yana kuka jikinsa na rawa, Ganin haka yasa suka nemi da akaisu asibitin da aka nufa dasu ko kuma afad'a masu suje saboda yanda tsohon ke neman birkice masu awajen duk su kace basuda masaniya akan kowace asibiti ce amma suna da tabbacin kano aka nufa dasu. Wani daga cikin wud'anda ke can gefe tsayene yace abari yakira d'an uwansa yaji ko wace assibiti ce saboda da motarsu ce aka d'aukesu, bayan yakira sane ya sanar masa da cewa suna Aminu kano teaching hospital sannan yafad'a masu, godiya suka yimasu sosai tare da fiddo da kud'ad'en da basusan ko nawa bane suka basu sannan suka d'auki yaran da sauran abubuwan da aka basu da aka gani cikin motar suka kama hanyar kano kowanensu hankalinsa atashe, Banda kukan Abba babu abunda kakeji acikin motar hatta yaran ana shiga mota suka koma bacci, Shikuwa mutumen daya d'aukowa yaran ruwa daga cikin motarsa ji yayi bazai iya tafiyaba saboda wata irin soyayyar yaran da yaji tashiga ransa, ji yayi yana kwad'ayin sanin ko suwaye su da kuma halin da iyayensu ke ciki hakan yasa shima yaja motarsa yabi bayansu... _Hmmmm....! tirqashi!πŸ’” Shin kuna so kuji yanda cigaban wannan labarin zai kasance? Shin ko zaku iya bani had'in kai tare da guntun lokacinku da kuma qarfafamun guiwa wajen warware maku bakin zaren wannan labarin cikin sauqi kuma daki daki yanda zaku fahimta? Comment d'inku shine amsar tambayoyina kuma shine zai tabbatar mun da cewa eh kuna buqata kuma kuna tare dani😍, shiiiii🀫 nasan zukatanku cike suke da tarin tambayoyi acikin wannan labarin kamar haka_ *WAYE ABU SUMAYYA DA GIMBIYARSA?*πŸ˜… *MEYE ALAQAR ABBA DA GIMBIYAR ABU SUMAYYA?*😑 *MEYA RABA GIMBIYAR ABU SUMAYYA DA IYAYENTA NA TSAWON SHEKARA BAKWAI?*😱 *AWANE HALI ABU SUMAYYA DA GIMBIYARSA KE CIKI?*😰 *MEYE TUSHEN WANNAN LABARIN?*πŸ™‡πŸ»‍♀️ *SHIN WANENE MUTUMEN DA YABI BAYANSU ABBA DA MOTA?*πŸš™ _Relax! kubiyoni sannu a hankali zaku samu duka amsoshin wud'annan tambayoyin acikin wannan sabon labari nawa dake cike da sabon salo mai suna *SANNU SANNU* Bata hana zuwa...🚢‍♀️🚢‍♀️🚢‍♀️_ *_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_* [6/15, 11:34 PM] My S Nomba: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ STORY CONTINUES BELOW _Jinjina agareku masoyana, fatan alkhairi da kuma fatan tabbatuwa cikin amincin ALLAH da yardarsa akoda yaushe Kuma cikin kowane hali shine addu'ata agareku, tabbas naga karamci, halacci, yarda da kuma zallar soyayya agareku, nayi farinciki da kuma murna ganin irin kyakkyawar tarba dana samu daga wajenku akowane group wanda hakan yatabbatar mani da cewa nid'in takuce akoda yaushe, ngd ngd ngd sosai ALLAH yadubi zuciyar kowanenku yabiya masa da buqatunsa na alkhairiπŸ‘πŸ» Ina farinciki da kuka nuna mani cewa yanda nake ikirarin cewa ina sonku FILLAH kuma kuna so na FILLAH😍 in sha ALLAH zan zage damtse wajen ganin kun ilmantu kuma kun nishad'antu da wannan littafi,πŸ˜…fatana shine ku juri bina daki daki tare da qarfafamun guiwa, ni kuma in sha ALLAH nayi maku alqawarin da *SANNU SANNU* Zaku samu tarin fad'akarwa da kuma farinciki marar misaltuwa acikin wannan labarinπŸ₯°MUCH LUV FILLAH na wajena😘❤️_ Page___2πŸ’Ž Aguje matashin saurayin ke tafiya saboda yanda Abba ke faman reren kuka tare da azazzalarsa akan yayi sauri, kusan minti ishirin da biyar suka d'auka kafin su isa cikin garin kano, Hanyar asibitin suka nufa zuciyoyinsu cike da fargabar abunda zasu riska, suna isa ko daidaita parking basuyi ba Abba yafara kiciniyar bud'e gambun motar da sauri saurayin ya danna lock d'in motar had'e da cewa, "Haba Abba! Me kake shirin yi hakanne, karka manta babu abunda muke iya canzawa daga qaddarar da ALLAH yatsaro agaremu da kuma sauran bayinsa, kabi ahankali in Sha ALLAH babu abunda ya samesu." ko jin abunda yake fad'a Abba ba yayi sai faman kica niyar bud'e motar yafita kawai yakeyi amma yakasa saboda lock d'in daya saka mata, ganin haka yasa wanda d'azu Abba yakira da hussaini ya dafa kafad'ar matashin had'e da cewa, "Shurahbil bud'e masa kaji ko!." "Amma uncle h...." Bai qarasa ba yayi saurin d'aga masa hannu da sauri shurahbil yacire lock d'in ba tare daya sake cewa komai ba suka fito tare da bud'ewa Abba da tuni yakai maqurar b'acin rai da hasala kawai yanayin da yake jin kansa acikine yasa bai tsaya bi takan saba, fitowa yayi har yana neman fad'uwa sukayi saurin riqesa ba tare da sunce dashi komai ba suka nufi emergency ward, girgiza kai shurahbil yayi tare da bin bayansu hannunsa na riqe da 'yan biyun da tunda sukaji tsayawar motar suka tashi daga baccin da sukeyi atare, Har sun kusa shiga emergency d'an uwan uncle hussain wanda shine hassan Kuma mahaifin shurahbil ya juyo yace, "katsaya daga waje kafin muji halin da suke ciki, idan zai yuyu ma ka koma cikin mota da yaran nan, idan akwai buqatar kazo zamu nemeka." Babu musu yakoma cikin motar shida yaran tare da ciro wayarsa yajawo game d'in race na motoci yanayi, dama aikinsa kenan aduk lokacin daya kad'aita shi kad'ai, yaran na ganin haka duk suka dawo daga inda suke zaune baya zuwa gaba inda yake zaune suka haye masa jiki suna kallo shi kuma mahaifinsa ya ida qarasawa can cikin emergency ward d'in tare dasu Abba suna tambayar mutanen da sukazo daga k'auyen da accident d'in yafaru, sunfi minti goma shabiyar kafin su samu su had'u da d'aya daga cikin wud'anda suka kawo su Abu sumayya d'in wanda shikad'aine ya tsaya awajen, sauran kuwa tuni suka wuce bayan sunga likitocin sun karb'esu, shima d'in saida wannan bawan ALLAHn yaje yakirawo police tukuna suka amshesu. Hannu yabasu suka gaisa kafin yace, "kune iyayen bayin ALLAHn da mukazo dasu?." Cikin rawar murya Abba ya amsa masa da "eh bawan ALLAH mune, Ina zamu ganesu ne, suna ina?." Shiru mutumen yayi kafin ya d'an nisa fuskarsa cike da damuwa yace, "likitoci nakan duba su amma suna buqatar addu'ah sosai, shi namijin sun wuce da shi ICU (internatal care unit) ita kuma macen suntafi da ita gyni emergency." Shiru yayi tare da ciro gilashin idanuwansa yasa gefen babbar rigarsa ya goge k'wallan da suka zubo masa sannan yaci gaba da cewa, "dukkaninsu suna cikin wani mawuyacin halin da addu'armu kawai suke buqata, amma har yanzu ina kallon yanayin da naga baiwar ALLAHn nan aciki kafin suwuce da ita, abun gwanin ban tausayi yanda abun dake cikinta ke faman motsi Yana neman taimako yayin da ita d'in takasa d'aga ko d'an yatsanta da zaya iya bashi koda k'warin guiwa ne na second d'aya, Ina addu'a ubangiji yadubi karamci da tausayi irin na uwa alokacin da rauni yasa takasa bawa d'an dake cikinta taimako da yakawo masu tallafi da kuma agajinsa domin ceto duka rayuwarsu." STORY CONTINUES BELOW Wani irin jirine ya d'ibi su uncle hussain jin yanayin da 'yar d'an uwan nasu ke ciki daya sasu ja da baya tare da fad'awa zaune saman kujerun dake bayansu saboda tsananin tashin hankali suna furta kalmar, "innalillahi wainna ilaihirrajiun." dama shi Abba tunda sukazo suka samu suka lallab'asa ya zauna saboda bawata lafiyar qafafune keda shiba balle yajuri iya tsayuwa na tsawon lokaci, lokacin da yaji wannan labarin sai kawai ya sake fashewa da wani sabon kukan da dama tun d'azu yake yin abunsa saboda rashin sanin awane hali gudan jinin tasa take ciki, kalmar shahadar shima ya Fara maimaitawa had'e da cewa, "Amantu billahi, qadarallahu wama sha'a fa'ala." cikin tausayawa mutumen ke kallonsu kafin yace, "hak'uri zakuyi tare da addu'a kuma kusamu ku matsa inda suke nasan gab ake da anemi 'yan uwansu, ni ina kan hanya tane ta zuwana garin minna, dama tsammanin jiran isowarku anan kamar yanda d'an uwana ya sanar mun awaya shine dalilin daya tsaidani anan saboda nasan kuna isowa dole direct nan (emergency) zaku zo, don haka ni zan wuce, ga wud'annan takardun acikin aljihun namijin aka tsincesu" yaqarasa maganar tare da miqawa Uncle Hassan takardun, har zai tafi saiga wani Dr da shine suka karb'i case d'in anan emergency ya iso wajen had'e da kallonsa yace "Ahhhh, ranka ya dad'e baka wuce bane?" "Eh Dr sadeeq Amma yanzunnan zan tafi in Sha ALLAH, wud'annan sune patient relatives na mutanen da muka kawo" yabashi amsa tare da nuna masa su Abba dake zaune kamar ruwa yacisu. "Masha Allah, ranka ya dad'e to ALLAH ya kiyaye ya kuma saka da alkhairi" "Amin ya rabbhi" yafad'a tare da bashi hannu sukayi musa baha, kallon su uncle h yayi tare da cewa "duk wani abu daya kamata wannan Dr zai taimaka maku insha ALLAH, aminina ne sosai don haka ku kwantar da hankalinku, pls Dr you should consider..." har lokacin suna riqe da hannuwan juna. "I will in sha ALLAH" yabashi amsa sannan suka yimasa godiya ya wuce, Dr yace sutashi yayi masu jagora zuwa can ICU d'in sannan suje gyni emergency, juyowar da zasuyi wajen Abba sukaga wayam babu kowa a mazauninsa, hankalinsu tashe saboda sanin yanayin da yake ciki suka fara duddu basa acikin wajen basu ganesa ba, cikin tashin hankali suka yiwa Dr bayanin ko wayeshi da matsayinsa ga patient d'in yace, "karku damu, inaga yakasa jurewane yanufi can, kuzo mutafi can d'in." A b'angaren Abba kuwa kamar yanda Dr yafad'a kasa jure zama awajen yayi hakan yasa yamiqe lokacin da suke magana ba tare da sun lura ba yakamo hanyar gyni emergency jikinsa na rawa sai faman had'a hanya yakeyi, babu abunda yake buqata alokacin irin yaga 'yarsa kuma yasan ko awane hali take ciki, kasancewar dole sai yafito tacikin emergency ward d'in zai iya isa gyani emergency dake can gefe dasu yasa shurahbil ya hangosa yana harhad'a hanya tare da neman fad'uwa, da gudu yafita cikin motar ba tare da ya tsaya kula yaran dake tare dashi ba yanufi inda yake, da sauri ya qarasa wajen tare dasa duka hannayensa biyu ya rungu mosa yana fad'in, "Abba ina kuma zakaje haka kai kad'ai, Ina su uncle ne?." 'Dago kai yayi ya kallesa ba tare daya iya furta masa komai ba sai dai ya nuna masa gefen da gyni emergency take da yake ana iya hangota daga nan inda suke, jujjuyawa shurahbil yayi yana kallon ta gefe gefensu ko zai hango su uncle h amma ko alamarsu babu, hakan yasa yariqasa suka nufi wajen, sukuwa 'yan biyun ganin yabar gambun motar abud'e yasa suka fito suma suna 'yan dube dube ta gefen, dai dai lokacin mutumen daya biyo bayansu Abba da mota shima yayi parking motarsa wajen tare da fitowa da sauri, cike da mamaki ya nufo wajensu tare da kamo hannun d'ayar yace, "Ina zakuje ne?" "Baba zamuje yabamu game." Tafad'a tana tsalle tsalle, tashi yayi ya leqa cikin motar yaga babu kowa aciki gashi kuma anbarta abud'e, gefe da gefe yakalla kuma baiga su uncle ba, hakan yasa ya rufe motar tare da ce masu, "to ina baban naku yaje?." hanyar da shurahbil yabi suka nuna masa. Kallonsu yayi yaga yanda suka jigata yace "Zakuci abinci?" "Eh zamuci dama yunwa mukeji" suka fad'a atare "To kuzo muje" yafad'a tare da riqo hannuwansu, d'ayar ce ta wafce hannunta had'e da cewa, "ni bazan jeba." Itama d'ayar ta wafce hannunta had'e da cewa "nima bazan jeba" haddasu maqale kafad'a, tsaye yayi yana kallon su cike da burgewa kafin yace, STORY CONTINUES BELOW "To zaku zauna anan inje inkawo maku abinci?." "Mu baba zamu bi." "Haba yaran baba ai bakusan inda zaku ganesa ba tunda yayi nisa, ku zauna anan karkuje ko ina bari naje nakawo maku abinci kuci kunji ko?" "A'a sai dai ka kaimu wajen dady da ummie zasu bamu abinci muci ko hassana!" d'ayar tafad'a tana kallon 'yar uwarta, "Eh, ke ummie ke baki ni kuma dadynah take bani abaki ko" Tsayawa yayi yana kallonsu cike da jin wani farinciki aransa wanda baisan dalilin saba, yanayin surutunsu na matuqar burgesa wanda yanzune ya gano wacce taqi karb'ar ruwa a hannunsa d'azu itace hassana kuma itace tafara cewa baza take ba, d'ayar kuma itace hussaina wacce ta d'an karce a gefen kuncinta na dama, wani irin tausayinsu ne yaji ya rufesa tunawo da halin da iyayen nasu keciki yayi tare da addu'ar ALLAH yatashe masu da kafad'unsu, juyawa bayansa yayi ya hango d'aya daga cikin security d'in asibitin yamik'e tare da isa wajensa yabashi hannu suka gaisa sannan yace "Don ALLAH ko zaka iya kula mani da yaran can kafin inje indawo?." Ganinsa babban mutum yasa yayi saurin cewa, "Babu damuwa Alhaji indai zasu zauna." Don yasan dole za'a shafa masa wani abun, komawa wajensu yayi yariqo hannunsu yace, "Yawwa yaran baba, kuzauna anan kafin babanku yadawo zanje nakawo maku abinci kunji ko?." Da sauri yabar wajen yanufi wani waje da ake saida abinci cikin asibitin aransa yana addua'ar yana saqa wasu abubuwa. Cikin mintuna biyar yaje ya siyo abincin ya dawo ya taddasu tare da security d'in sai faman surutu suke yimasa tamkar sun sanshi, murmushi yayi sannan ya bud'e bayan motarsa ya d'auko wata carpet mai girma ya shinfid'a cikin inuwar tare da aje abincin hannunsa sannan ya jawosu ya zaunar dasu ya bud'e masu abincin ya tura masu a gabansu, d'aya daga cikin take away d'in da yayo ya sake d'auka ya miqawa security d'in dama donsa ya siya tare da gorar ruwa d'aya da kuma lemu yanata godiya. Kallonsa sukeyi sana kallon abincin batare da kowacensu tasa hannu ba yace, "kuci mana." Girgiza masa kai sukayi alamun bazasu ciba yace "Meyasa" atare sukace "dady yake bani idan zanci" itama d'ayar tace, "ummie take bani abaki." Shiru yayi kafin yajawo gorar ruwan d'aya ya wanke hannunsa tare da d'ibar abincin yafara basu abaki ahankali, idan yaba wannan yaba wannan yana jin wani irin farinciki ya mamaye masa zuciya. Shurahbil kuwa suna isa gyani emergency sukaga wasu nurses aguje sun wuce da oxygen cikin theater room d'in dake laqe da wajen, bayan kamar mintuna bayar suka wasu sun sake wucewa da wani aguje, tsaye sukayi tare da rashin sanin abunyi data inda zasu fara, sunyi minti uku a tsaye kafin suga wata docter tafito daga cikin wani office dake kallon d'akin theater d'in da sauri shurahbil ya tareta had'e da cewa, "Assalamu alaikum, don ALLAH Dr ko nanne aka kawo wata patient da suka samu accident mai juna biyu?" Don kallo d'aya zakayiwa matar katabbatar da cewa ita d'in cikakkiyar likita ce, "Eh nanne, yanzu haka ita aka gama yiwa tiyata, ko kune relatives nata?." Ta tambayesa atak'aice "Eh mune Dr yafad'a tare da gyara tsayuwarsa da alama yana son jin qarin bayanine daga bakinta, amma ga mamakinsa sai yaga tawuce cikin d'akin ba tare data sake cewa komai ba, Dr sadeeq kuwa koda sukaje ICU d'in yashiga d'akin da ake duba Abu sumayya ya tarar ana k'ok'arin gyarasa saboda mai kowa mai komai ya amshi abunsa wato dai ALLAH yayi masa rasuwa, rufe idanuwa yayi cikin jimami tare da girgiza kai sannan yanufi wajen wani dr dake tsaye akan gawarsa yana qoqarin had'a bayanan tabbatar da mutuwarsa bayan dogon bincike da suka gudanar akanta, kallonsa yayi yace "Ahh..Dr sadeeq kadawo? Kadai ga yanda ALLAH yayi ikonsa akan wannan bawa nasa ko, ya samu internal injury ne cikin k'wak'walwarsa haka kuma zuciyarsa tabuga a sanadiyar tsoro da kuma fargabar daya ziyarcesa a lokaci d'aya Kuma sai akaci sa'a yana d'auke da hawan jini wanda shine ya qara tasiri wajen bugawar zuciyar tasa har tafashe" girgiza kai Dr sadeeq yayi had'e da cewa, STORY CONTINUES BELOW "ALLAH sarki, ALLAH yajiqansa yayi Masa rahama, dama relatives d'insa ne suka iso" "Ok zaka iya sanar dasu." "Nooo..bazan iya ba Dr naseer i feel their pain." "Ba damuwa, bari naqarasa had'e bayanan sai naje na sanar dasu, hak'uri zasuyi don dukkaninmu ita muke jira" Sai bayan kusan mintuna biyar sannan suka fito tare da Dr naseer d'in suka nufi wajen da su uncle h suke tsaye, gaisawa suka farayi dashi sannan yayi masu bayanin ALLAH yayiwa patient d'insu wato Abu sumayya rasuwa...salati suka farayi tare da jinjina al'amarin, tabbas sunji ba dad'i rasa nagartaccen mutum irin Abu sumayya adaidai wannan lokacin da suke tunanin shine cikar burinsa da kuma farincikinsa don uncle hussain ahadda hawayensa, haquri suka basu sosai tare da addu'ar ALLAH ya gafarta masa sannan Dr sadeeq yace suwuce gyni saboda ga alama Abba baizo nan ba, Jikinsu a sanyaye suka bar wajen suna tuna irin muqabalar daya fuskanta kafin su bashi auren 'yar tasu. Suna isa Dr da d'azu suka magantu da shurahbil nafitowa wasu nurses su biyu na biye da ita abaya d'auke da jarirai guda biyu a hannunsu, kallonsu tayi tace "A'ah Dr sadeeq barka da Rana, yau kaine a ward d'inmu?" "Barka Dr imaan, ya zamuyi nabiyo patient d'inmu da muka kawo anan wacce tasamu accident, so dama d'azu da mukazo ake fad'amun kece on duty keda su Dr odugun da Dr na'eem hop anyi nasara wajen aiki" "Yeah upcouse, Ashe kaine Dr na'eem ke kwatantamun, ya aiki?" "Alhamdulilah Dr." Tafad'a tare da kallonsu uncle h dasu Abba dake tsaye suka gaisa sannan tace "Ok Dr wud'annan sune relatives d'in patient d'inka" "Eh Dr imaan" "Ok congratulation Alhaji anyi nasarar ciro mata 'yan biyu macce da namiji amma.." kafin ta iyar Abba yafashe da kuka yace, "Shikenan dama nasan hakan zata faru, ya ALLAH kayafemun, yau gashi nayi sanadiyar jefa kaina cikin huznu dalilin nisanta kaina da ita da nayi, ta tafi tabarni da mikin da har lokacin da za'a karb'i tawa rayuwar bazai warkemun ba." Dafa kafad'arsa Dr imaan tayi had'e da cewa "Haba baba! Waya fad'a maka 'yarka tarasu, 'yarka na a raye saidai ba wannan kukan naka take buqata ba, kayi hak'uri addu'arka ita take so yanzu kaji" wani irin sanyi yaji azuciyarsa wanda saida hakan ya bayyana qarara a fuskarsa ya juya gabas yayi sujudush shukur had'e da kallonsu uncle h da fuskokinsu suka kasa bayyana farinciki ko kuma damuwar da suke ciki yace, "Alhamdulilah, Hassan hussaini 'yarku naraye bata mutu ba, kuzo kuyiwa ALLAH godiya kunji ko." ganin yanda fuskokinsu suke yasa hankalinshi ya koma akan mijinnata da sauri ya qarasa inda Dr sadeeq yake yace, "Dr ya jikin mai gidan nata?" "Sai hak'uri Alhaji shikam ALLAH yayi masa cikawa" "Innalillahi wainna ilaihirrajiun" Abba yafad'a da k'arfi tare da fad'uwa zaune, duk wanda ke wajwn jikinsa yayi sanyi jin cewa Abu sumayya ya rasu, hatta Dr imaan saida taji shock atare da ita saboda tunowa da halin da matar ke ciki, "ALLAH yajiqansa tafurta tare da juyawa ta koma cikin d'akin tiyata" Su uncle h suka karb'i yaran suna kallo tubarkallah masha ALLAH dasu, kyawawa dasu sak kamar mahaifiyarsu gasu da girma sosai, hud'uba suka yimasu sannan sukaba nurses d'in su aka koma dasu ciki saboda ga alama basuda lafiya don gaba d'aya hannuwansu saye suke da calular irinta qarin ruwa, Shurahbil kuwa jiyayi tamkar kar arabashi da jaririyar dake hannunsa wacce itace hussaina d'an namijin kuma shine hassan yana ta kallonsu har suka shige dasu ciki, hakan ne yasa ya tuno da yabaro 'yan uwansu a mota d'azu kuma bai rufeba, ai da sauri ya juya yamik'i hanyar inda suka ajiye motar, STORY CONTINUES BELOW Yana zuwa ya tarar basu cikin motar, nan take duk hankalinsa yatashi yafara dube dube harda qarqashin mota, kamar ance ya juyo ya hangosu cikin motar mutumen ya kunna masu laptop suna kallo hankali kwance, zaro idanuwa shurahbil yayi tare da qarasowa wajen yafara bubbuga glass d'in motar saboda duka a kukkulle suke saboda a.c da aka kunna, a hankali mutumen yafara sauke glass d'in motar tare da juyowa yana kallon shurahbil... *_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_* [6/15, 11:34 PM] My S Nomba: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___4πŸ’Ž Suna isa gida zainab tawuce dasu part d'insu yayinda uncle hussain ya ciro wayar batool da aka basu da kuma takardun da alhajin daya kawo su Abu sumayya asibiti ya basu ya mik'awa Abba yana fad'in, "Alhaji ga wud'annan takardun da wayar fatima" "Karik'esu hannunka hussain, Amma yakamata ace antuntub'i iyayen yaron nan an sanar dasu halin da ake ciki koba haka ba?", "Eh hakane gaskiya, dama tun d'azu ake kiran wayar narasa qwarin guiwar d'agawa, bari naba yaya sai ya lalabo lambar wanda yakamata." Mik'a masa wayar yayi ya karb'a tare da fara duba sunayen missed call d'in da yagani saboda yanada tabbaci akan nakusa da su d'inne suka kira, lamba uku ya gani, tafarko ansa gwoggwo, ta biyun kuma sister, sai ta ukun barrister kamal, shuru yayi yana nazarin wacce yakamata ace yakira Abba yace, "malan Hassan lafiya kuwa?." "Lafiya klw alhaji. Kawai Ina nazarin lambar kdaya kamata inkira cikin ukunnnan da aka yimata missed call dasu, wannan ta farkon Ina tunanin qilan mahaifiyar sace wato surukar ita fatima ta biyun kuma qilan qanwar sace, sai ta ukun wacce nakasa fahimtar waye shi!, gashi dare yayi kada a d'aga masu hankali" "Malan Hassan kenan! d'aga hankali kuma har na nawa agaresu?, ai tunda suka kirawo wayarsu sukaji basu same suba dole hankulansu su tashi, Ina tabbatar maka da cewa dakyar daga cikinsu in akwai wanda zai iya bacci matuqar Basu samu wani labari akansu ba, ya zamuyi tunda mai faruwa tariga da tafaru, ko ance abari sai gone babu abunda zamu iya canzawa don haka ka kira a sanar dasu shine daidai domin hakan zai sama masu natsuwa koda kad'ance, kaga at least tunda akwai 'yar tazara a tsakaninmu (kano da borno) idan aka sanar dasu tun yau zasu samu tasowa da wuri gobe" Abba yafad'a cike da damuwa, ganin shima gaskiya yafad'a yasa ya danna lambar barrister kamal kasancewar shine namiji aciki kuma shi zaifi iya karb'ar abun cikin kwanciyar hankali duk da dai bai san kowaye shiba, ringing d'in farko bai ida shiga ba yaji yad'aga Kiran da alama jiraye yake da hakan, lokacin shikuma yana part d'insu Abu sumayya don agida d'aya suke amininsa ne sosai wani aikine yakawosa agarin borno shida iyalinsa shine Abu sumayya yabashi wani b'angare daga cikin gidansa ya zauna har zuwa lokacin da zai gama, tunda rana mahaifiyarsa tayi masa waya hankalinta atashe tasanar dashi halin da ake ciki akan rashin samun lambar aminin nasa da takeyi ita kuma ta matarsa idan takira ba'a d'agawa, Nan shima yakira lambarsa bai samesa ba hakan yasa yakira ta batool ita Kuma bata d'aga ba, yanda hankalin mahaifiyar aminin nasa ya tashi tanata kuka yasa d'aya dawo sallar isha'i yawuce wajenta yana rarrashi tare da kwantar mata da hankali amma har tsawon wannan lokacin takasa dena kukan wanda hakanne yasa shikuma yakasa komawa part d'insa wajen iyalinsa, "Assalamu alaikum" Yaya hassan yafad'a ya amsa masa cikin natsuwa tare da fargabar abunda kunnuwansa zasu jiyo masa, runtse idanuwa yayi cike da rashin sanin ta inda zai fara sanar dashi wannan mummunan awannan lokacin, karb'ar wayar Abba yayi ahannunsa tare da duba lambar sannan yakara a kunnensa had'e da cewa, "da barrister kamal nake magana?." cikin i'ina yace, STORY CONTINUES BELOW "E..e...eh shine." "Kana magana da mahaifin batool ne wato alhaji Umar fari" wata irin ajiyar zuciya yaji ya sauke had'e da cewa, "Alhamdulilah!." sannan yace dashi, "Masha Allah, Abba ya gidan anwuni lafiya?." "Lafiya klw barrister kamal, ya.." kafin ya ida abunda zaice cikin zaquwa barrister kamal yace "Alhaji yasu batool suke!, sun dai iso lafiya ko, saboda tun d'azu muke nemansu awaya bamu samu gaba d'aya hankulanmu sun tashi." Gwaggo najin cewa da mutanen kano ne yake waya ta dakata da kukan da takeyi had'e da kashe kunnuwa tana sauraren yagama waya taji halin da ake ciki, Abba kuwa sai daya nisa sannan yace "To alhamdulilah don aduk halin da bawa ya tsinci kansa dole yayiwa ALLAH godiya." Wani irin fad'uwar gaba barrister kamal yaji kafin cikin sanyin murya da sarewa yace, "Hakane Abba injin dai lafiya?." "Lafiya barrister saidai ALLAH ya jarabcesu dayin hatsari gab da hanyarsu ta shigowa kano, wannan shine dalilin da yasa kika nemesu awaya kuka rasa, wayar batool kuma da muka samu bama cikin kwanciyar hankali tun lokacin shiyasa kukaji ba'a d'aga ba, yanzu haka duk suna asibiti wanda ALLAH mai kyauta da dad'i ya qaddara ita batool d'in saboda yanayin da take ciki anyi mata tiyata don ceto rayuwar abunda ke cikinta anfiddo mata da 'yan biyu macce da namiji, amma shi nuruddin (Abu sumayya) saidai muyi hak'uri domin ALLAHn daya haliccesa kuma yafimu sonsa ya karb'i abunsa." Cikin tashin hankali da kuma razana saboda yanda barrister kamal yaji dirar maganar kamar sakin aradu yasa ya saki wayar tafad'i k'asa yana fad'in "innalillahi wainna ilaihirrajiun, innalillahi wainna ilaihirrajiun" haka yayita maimai tawa na tsawon sakanni kafin ya lura da yanda hankalin gwaggo yatashi cikin rud'ewa tana tambayarsa, "lafiya kamal, meyake faruwa ne, meyasa mu 'ya'yana da kuma jikokina, ka amsa mun kamal meya samesu ne nace?" Sai as lokacin ya tuna da yaran cikin sauri ya daidaita kansa tare da goge hawayen da suka zubo masa yace, "Kikwantar da hankalinki gwaggo ba wani abu bane." Tare da duqawa ya d'auko wayar tasa da harta mutu, "Karka yimun qarya kamal kafad'amun halin da suke ciki, dama tunda naji wannan kiran awannan lokaci jikina yabani da akwai matsala, baranma da naji cewa da abbanta kake waya" tafad'a tare da sake fashewa da wani kukan. Kamo hannunta yayi ya zaunar da ita akan kujera tare da riqo hannuwanta biyu yana kallonta cikin tausayawa yace, "kiyi hak'uri gwaggo bazan b'oye maki komai ba domin waji bine agareni na sanar dake." shuru yayi sannan yaci gaba da cewa "mahaifin batool ne yakira yake sanar dani cewa gab dasu nuradden su shiga kano sun samu accident yanzu haka suna asibiti Kuma a sanadiyar hakan ita batool anyi mata tiyata anciro mata 'yan biyu macce da namiji, don haka suna buqatar addu'ar mu saboda sun d'anji rauni." Sai yab'oye mata zancen rasuwar Abu sumayya saboda tsoron yanayin da zata shiga kafin safe, gashi kuma babu kowa atare da ita sai jidda qanwar nuradden 'yar kimanin shekara goma sha shidda wacce itace batool ke kira da sister, sallallami gwaggo tashigayi tana kuka tana fad'in "Saida nace su haqura da tafiyarnan har sai bayan ALLAH ya sauketa lafiya Amma shauqi da soyayyar mahaifin yarinyar nan yasa suka kasa hak'ura, hazbunallahu wani'imal wakeel, ya Allah ka rangwanta masu halin da suke ciki." Kuka tayi sosai yayinda tunanin halin da zata shiga idan tasan gaskiyar al'amarin yasa barrister kamal Fara zagayen d'akin, message yaga yashigo awayarsa yayi saurin dubawa, still no batool d'ince uncle hussain da yaga Abba yajaye akunnensa shima yana kukan ya karb'a ya sake kira amma yajita switch shine yaturo message kamar haka, _muyi hak'uri da rashin nuruddin domin dukkaninmu ita muke jira, kuma mugodewa Allah daya bashi wud'anda zasu bishi da addu'ah yaransa duka nanan cikin k'oshin lafiya hadda wud'anda ya bashi ayau bayan shi ankarb'i tashi rayuwar, mahaifiyarsu ce kawai kejin jiki itama rai ahannun ALLAH, da fatar zaka sanarda wannan sak'on ga sauran ahalinsa Kuma sunce gobe in sha ALLAH zasu bada gawar tasa, ALLAH ubangiji yajik'ansa kuma ya gafarta masa_ STORY CONTINUES BELOW Awannan karon hatta shi kansa barrister kamal zaune yayi yana sharar k'wallah tare da jinjina girman izza da kuma iyawar ubangiji, yakarb'i rayuwar Abu sumayya alokacin da yabawa 'ya'yansa rayuwar zuwa duniya, ya tsara al-amarinsa tayanda ajalinsa ya riskesa adaidai inda yake so bayan shekaru bakwai, wasu zafafan hawayene suka zubo masa aransa yana cewa, "Tabbas ALLAH baya barin wani don wani kuma duniya ba abakin komai take ba, wanda ya d'auka da zafi zai b'ata lokacinsa batare daya ankara ba mutuwa tazo tayi gaba dashi, kana naka ALLAH yariga daya gama tashi tuntuni, kayita hauka kana qirgawa kanka shekaru batare da kasan mutuwa na gab da d'aukarka ba, kayita hauka kana kumfar baki akan qanqanen abu daga qarshe ALLAH yasa azo azare ranka, lallai duk wanda ya shiryawa zaman duniya to tabbas yayi ganganci domin duk tsawon sjekarun da ALLAH ya ibar masa to da sannu zasu qare mutuwa ta riskesa saboda duk nisan abu da SANNU SANNU yake qarewa, girman iko na ALLAH zakaga yanzune zaka rabu da mutum sai kaji ba zato ba tsammani ance maka yamutu, don haka duk musulmin k'warai dole ya farka yasan cewa ita mutuwa gaskiya ce kuma idan lokacinka yayi duk gimanka, duk matsayinka ko mulkinka zata riskeka aduk inda kake kuma aduk akowane lokaci, babu ruwan Allah da cancantar ka wa'adinka nayi za'a zare maka rai." _ubangiji Allah yakarb'i rayukanmu Muna musulmi kuma mumunai na k'warai, yajiqan wud'anda suka rigamu gidan gaskiyaπŸ‘πŸ»πŸ˜­_ Yajima awajen zaune har gwaggo ta gama kukanta taje ta d'auro arwala tadawo, kallon agogo tayi taga har k'arfe 1:25 na dare yayi tace "Kamal katashi kaje ka kwanta iyalinka najira, hak'uri zamuyi murok'i ALLAH da yabasu lafiya kaji ko?" Nisawa yayi tare da cewa, "to gwaggo." Sannan ya tashi zai fita jiki a sanyaye, har yakusa fita ta sake cewa, "Kamal basu yimaka zancen ko awane hali yaran nasu suke ba?." "Sunan lafiya gwaggo sunce babu abunda ya samesu" "Alhamdulillah, to saida safe" tafad'a tare da saka hijabinta sannan ta shimfid'a abun sallah ta tayar... A yanayin da barrister kamal yashiga wajen iyalinsa dake zaune a babban falon dake tsakiyar d'akunansu suna fira ya tabbatar masu da cewa akwai matsala, hakan yasa amaryarsa meenatu dake d'auke da tsohon ciki wata takwas miqewa da nufin barin wajen saboda 'yar uwar tata sajida da yake d'akinta tasamu damar rarrashinsa da kuma kwantar masa da hankali, kirawota yayi cikin sanyin murya yace+ "Ina kuma zakije?." "Zanje na kwanta dama muna jiran dawowar kane munji shiru." "Shine kuma zaki tafi baki jira jin dalilin daya dad'ar dani ba?." "Kayi hak'uri, baccin ne yariga yazo kuma kasan yanayin jikin nawa" tak'arasa maganar tana faman lumshe idanuwa irin na masujin baccinnan, hannunta yariqa tare da rakata har cikin d'akinta yasa taje tayo arwalar bacci sannan ta kwanta ya lullub'amata bargo tare da kashe mata fitala sannan yafito. Zaune ya isko sajida takawo masa abinci da ruwa don gaba d'aya yau ko lunch besamu yayi ba saboda tashin hankali tana jiransa, qarasaw yayi tare da zaunawa k'asan kujera ya mik'e k'afafuwansa sannan yace, STORY CONTINUES BELOW "Sannu nabarki kina jirana ko, kinsan halin 'yar uwar taki..." "Ba komai." tafad'a batare da tabari ya iyar ba ta tsiyaya masa ruwa masu sanyi a cup ta miqa masa, karb'a yayi ya kurb'a ruwan sannan ya ajiye agefe, k'ok'arin rik'e hannunta yayi lokacin da takai hannuwanta saman kular abincin yace, "Kibarshi wifey, bazan iya ciba." "Subhanallahi! Kayi hak'uri kaci kad'an kada yunwa ta kamaka" "Bana cikin yanayin da abinci zai iya shiga cikina sajida..." Nan ya sanar da ita abunda kefaruwa da kuma rasuwar Abu sumayya. Hannu biyu biyu tad'ora abaki tana qoqarin danne sautin kukan daya zo mata saboda ba b.kamal kad'ai ba hatta su da suke matansa sunsan da karamci da kuma kyautatawa irin ta abu sumayya, mutumne Mai mutunci da kuma tausayi da sanin haqqin musulmi d'an uwansa, rungumota yayi yana rarrashinta tare da cewa, "Nayi rashin aminin qwarai daga cikin aminaina, yanzu babu abunda yarage awajena tsakanina dashi kamar inbisa da addu'a, haka kuma, domin shine zai tabbatar da soyayyarmu agaresa bisa kyautatawarsa agaremu." Addu'a tayi masa sosai tana kuka kafin yatayar da ita suwuce d'aki, har zasu shiga yaja hannunta suka shiga d'ayan d'akin da yaransu ke ciki ya kunna fitila yaga duk suna lafiya sannan ya sake gyara masu kwanciyarsu suka yimasu addu'a sannan suka wuce d'akinsu, kamar yanda yayiwa meenatu haka yayiwa sajida itama sannan yadawo falo ya zauna tare da rafka tagumi yana tunano hirarsu taqarshe kafin sutafi da kalar dariyar shaqiyancin da yatayi masa akan yanda yaga yana nan nan dasu meenatu saboda kada ran kowacensu ya b'aci, maganarsa zancensa na qarshe shine. _ni dai Gimbiya ta isheni anan duniya babuni babu yimata kishiya balle inyi tunanin raba mata soyayyata da kuma kalaman bakina da zuciyata ita da wata, nayarda da ita da kuma nagartacciyar soyayyarta agareni, Ina fatar kuma ALLAH ya yarda da ita kuma ya sota, nine noora amma azahiri batool itace wannan sunan hasken da ake kirana dashi, wlh badon ALLAH yatsaro a aljannah dolene za'a bamu wasu matanba da ni Abu sumayya nace ALLAH yabarni da gimbiyata ta isheni, ALLAH kasa gaba d'aya matan hurul ayni da za'a bani kamanninsu da komai nasu irin na gimbiyata ne._ Girgiza kai yayi had'e da cewa, "ALLAHU akabar, duniya kennan, ya ALLAH ka amintar dashi ga dukkanin muradansa na alkhairi." Sannan yamik'e shima yayo arwala ya tayar da sallah, haka shima Abba kasa kwana yayi banda tunanin abubuwan da suka faru a shekarun baya da kuma tunanin halin da 'yarsa take ciki Babu abunda yakeyi, hakan yasa yayo arwala ya fuskanci gabas don samun sassauci, a b'angaren hajia mama ma dake asibiti itama d'in hakan tayi don samun sasauci acikin yanayin da suke ciki. Daren ranar kam gaba d'aya wud'annan ahali guda biyu kasa bacci sukayi musamman Abba da gwaggo da hajia mama da kuma barrister kamal cikakken aboki managarci awajen Abu sumayya, kwana sukayi bisa abun sallolinsu suna addu'ah ALLAH yagafartawa Abu sumayya kuma yaba iyalinsa lafiya ya albarkaci abunda yabari, banda gwaggo da addu'arta ta tafi wajen ALLAH yaba yaronta lafiya ya tashi kafad'unsa shima yasamu cikar farincikinsa kuma yaraya masa abunda tahaifa yabata lafiya. Tun da asubar fari ya kirawo abokanansu na kusa dana nesa ya sanar dasu rasuwar aminin nasu tare da tabbatar masu da cewa yanzu haka suna shirin tafiya can kano saboda acan yarasu kuma yanasa ran acan za'ayi jana'izarsa, rana nafitowa ya iske gwaggo bayan sun gaisa yace yakamata tashirya suje kano, hakan kuwa ya matuqar yimata dad'i saboda jiya zaune takwana ana nuno mata fuskar d'anta tare da hakaito mata yanayin da yake ciki, duk hankalinta yabi ya tashi taga nawar safiya tawaye, saboda yanayin da meenatu ke ciki yasa yace sajida tayi hak'uri tazauna gida Idan sun dawo shida gwaggo sai yakaita tayowa batool gaisuwa kafin itama meenatu ALLAH ya sauketa lafiya. Haka kuwa akayi sajida ta gyara masa kayansa meenatu nata kuka don sai alokacin yasanar da ita abunda kefaruwa suka kama hanya shida gwaggo da wani mak'wabcinsu babban mutumne sosai tare da matar da kuma zainab da itama kukan takeyi jin d'an uwanta na kwance aadon asibiti shida autynta da take matuk'ar k'auna, abunda bata sani ba shi gaba d'ayama yabar duniya. STORY CONTINUES BELOW Koda k'arfe d'aya na rana tayi har sun isa garin kano dama yakira yasanar dasu Abba suna kan hanya, suna isa ambulance na ajiye gawar Abu sumayya a k'ofar gidansu Abba, tsayawa fad'ar halin da gwaggo tashiga ciki abun zubarwa hawayene sosai amma daga qarshe ta dangana tabarwa Allah, Bayan kwana uku Abba yasa aka kirawota ya bata takardun da aka samu acikin aljihun Abu sumayya bayan ya sake bata hak'uri da kuma yimata gaisuwa akan rashin da sukayi, karb'a tayi taduba takardun ta farko takar dace data qunshi address d'in data bashi daren da zasu zo, dake d'auke da sunan malan NURADDEN IDRIS ALIYU, tare da address d'insa ak'auyen bebeji, tabiyu kuma takardun wata makaranta ce daya siya ahannun wani mutum acan borno d'auke dasa hannunshi da kuma na mutumen, ranar da zasuzo ya tsaya ya karb'i takardun wajensa wanda shine dalilin da yasa ya sanyosu aljihu suka wucikke. Kallon Abba tayi had'e da cewa, "Wannan takardar adreshin qauyen da nake tunanin zai iya gano mahaifinsa ne daka dad'e kana tambayar waye ubansa har kana jifarsa da cewa shi shegene, na qyalene alokacin saboda yanda naga qarfin soyayyar d'ana a idanuwan 'yarka shiyasa banyi yunqurin sanar dashi inda zai iya nemo saba idan har yana raye, shine awannan karon nayi tunanin fad'a masa inda zai iya nemosa don in tabbatar maka da cewa shid'in d'an halak ne gaba da baya, Amma cikin ikon ALLAH Sai gashi hakan bai faruba ya karb'i abunsa" ta qarasa maganar tana kuka. Shiru Abba yayi kamar wanda aka zarewa lakka yana mai nadama da baqin cikin abunda yayi, saida tayi kukan mai isarta sannan taci gaba da cewa, "wannan kuma bansan kota meye ba, a ajiye har zuwa lokacin da ALLAH zaiba iyalinsa lafiya mai yuyuwa ne ita tasan kota meye." Hak'uri su uncle Hassan dake gefenta suka shiga bata tare da ban magana tace, "Aini ku bakuyi mani komai ba tunda kuka nunawa d'ana gata aduniya kuma banida bakin da zanyi maku godiya saidai ALLAH yasaka da alkhairi, shima d'in daya yimana bawai nariqesa araine ba, kawai ina tuna masane." Da haka dai suka samu suka sake bata hak'uri tare da tausarta sannan ta ajiye masu takardun tawuce tabar d'akin tana sharar k'wallah. Tun ranar da aka yiwa batool aiki har zuwa yau kimanin kwanahud'ubata farfad'o ba, tun anasa ran yau zata tashi gobene har iyayen sun fara sarewa akan al'amarin tare da fargabar abunda kan iya zuwa ya dawo, ana gobe gwaggo zata wuce gida sunje asibitin ita da barrister kamal da kuma zainab suna zazzaune cikin d'akin da aka kwantar da batool riqe da jariran da aka faraba madara yanzu sukaga ga hannunta yafara motsi, cikin farinciki duk sukayo kanta yayinda tafara bud'e idanuwa ahankali tana kallonsu d'aya bayan d'aya tamkar wud'anda bata tab'a gani ba, wani irin farinciki ne ya rufe gwaggo da hajia mama suka rungume juna suna hawaye tare da yima ALLAH godiya, barrister kamal ne yayi saurin fita sai gashi yadawo tare da likita, matsawa yayi kusa da ita yana duddubata sannan yace su tayar da ita zaune, ahankali yafara kiran sunanta kanta na duqe a k'asa, "batool, batool, batool" yakira sunan har sau uku, anan ukunne ta d'ago kai tare da kafesa da idanuwa, biron dake hannunsa yafara nuna mata saiti idanuwanta yana yawo dashi a fuskarta. Ahankali take bin biron da idanuwa aduk inda yayi dashi kafin likitan ya maidashi cikin aljihu yana murmushi had'e da juyowa yana kallon barrister kamal da shurahbil dake gefe a tsaye yace "Alhamdulilah, ansamu tafarfad'o kuma in Sha ALLAH babu wata sauran matsala, yanzu abunda ya kamata ahad'a mata ruwan tea abata tasha." sannan ya rubuta wasu magunguna yabasu yace aje asiyo akawo idan tagama shan ruwan tea sai akirasa, juyowa yayi yasake kallonta har lokacin idanuwanta na saman aljihunsa da taga yasa biron aciki yayi murmushi sannan yafita. "Sannu maman twins" barrister yafad'a sannan ta maido idanuwanta akansa daga kallon likita da takeyi shima tanata kallonsa harda karkace kai, K'ok'arin had'a ruwan tea d'in hajia mama tafarayi yayin da gwaggo dake rik'e da maccen tamatso kusa da ita cike da tausayawa tace, STORY CONTINUES BELOW "Sannu uwar biyu, ubangiji ALLAH ya baki lafiya" kamar da gaske batool ta d'ago kai tace "Amin." tare da mik'a mata hannuwa, hakan yasa gwaggo ta mik'a mata jaririyar had'e da cewa zainab ta kawo mata d'ayan jaririn aka aza matasu saman jikinta tabisu da kallo d'aya bayan d'aya, so takeyi ta tuna kosu waye atare da ita amma takasa, hakan yasa taji kanta yafara jujjuyawa kamar ana yawo da ita cikin wata duniyar, dariya dariya kuka kuka tafarayi kafin can tasaki wata irin qara had'e da ture yaran daga jikinta tana wani ihu wanda nan take hankalinsu ya tashi, badon zainab tayi sauri taro yarinyar ba da tuni tafad'a akan k'arfen dake gefenta na qarin ruwa yayinda shikuma d'ayan tuni yafad'o k'asa tare da tsanyara ihun kuka da sauri gwaggo ta d'aukesa tayi waje tana k'walawa nurses kira ita kuma banda buge buge da takeyi tana sakin wata irin qara da duk wanda yaji sai tsikar jikinsa ta tashi, hajia mama na kuka tafara qoqarin riqota saboda kada tajima kanta takaimata wani irin cizo da yaga amma hakan bai hanata takamata tariqeta sosai tana maimaita kalmar "innalillahi wainna ilaihirrajiun, allahumma ajirni fi musi bati wa ahlifni khairan minha, ya ALLAH muntuba kayafe mana kada kajarabcemu da abunda bazamu iyaba." Dukanta takeyi da dukkanin qarfinta amma taqi sakinta saima sake rungumeta da tayi sosai tana kuka, itama zainab d'in kuka takeyi tana riqe da jaririyar agefe, saiga shurahbil da barrister kamal da sukaje wajen sayo magani sun dawo, da gudu suka ida qarasowa wajen suka kamama hajia kaka ita suka rirriqeta tana kucce kucce saiga wasu likitoci harsu uku sun shigo gwaggo na biye dasu abaya tana sharar k'walla saboda nurses sun karb'i jaririn yana can suna dubashi. Nan take sukayi mata allurar bacci sannan sukace su saketa sufito, taimakon gaggawa suka fara bata tare da yimata binciken daya kamata, sannan suma suka fito fuskokinsu cike da damuwa, da sauri hajima mama tanufi inda suke tace, "Don ALLAH likita awane hali 'yata take ciki" gaba d'aya kasa tanka mata sukayi suka shige cikin wani office, turowa sukayi aka kira masu shurahbil alokacin Abba da uncle Hassan sun iso saboda wayar da shurahbil yayi masu ya sanar dasu halin da ake ciki hakan yasa uncle hassan ya dakatar da shurahbil d'in suka shiga shida Abba, wata takarda suka mik'o masu bayan cikin natsuwa Dr na'eem wanda yana d'aya daga cikin likitocin da sukayi mata operation yayi masu bayanin cewa, "Alhaji kuyi hak'uri akan abunda zan sanar daku amma patient d'inku tana cikin wani mawuyacin hali sakamakon buguwar da tayi ga kai, bincikenmu ya tabbar mana da cewa tasamu matsala a kwakwalwarta, dama tuni wannan muke tsoro ga farkawar tata tun lokacin da aka gama mata aiki but alhamdulilah tiyatar tata tawarke sai d'an abunda ba'a rasa, don haka yanzu wannan takardar zakuje kubiya kud'in wani scanning ne da za'ayi mata zuwa anjima. Yanda abun ya matuqar girgza Abba yasa daga nan inda yake zaune sukaga ya b'ingire sanadiyar hawan jinin da yake dashi, dole shima nan take aka bashi gado kafin kaceme 'yan uwa sun taru a asibitin cike da jimamin wannan irin jarabawa da Allah ya aikowa familyn nasu acikin wannan lokacin. Little Hassan kam babu abunda ya sameshi don anyi masa checkup sosai, haka Abba shima yasamu sauqi duk da dai har yanzu yana qarqashin kulawar liikitocin, gwaggo kam fasa tafiya tayi saidai tace barrister kamal yawuce ita zata jira har nan da kwana biyu, al'amarin batool kam ya tsananta, hauka tuburan takeyi wanda likitocin suka tabbar masu da basusan iya adadin lokacin da zata iya warkewa ba sai dai kawai suci gaba da addu'a da kuma nemar mata magani, yanzu haka dalilin daya hana suyi deparing nasu zuwa asibitin mahaukata saboda sauran raunukan dake jikinta ne da kuma tiyatar dake jikinta da suke treating badon haka ba ayqnayin da take bai kamata ace an ajiyeta nan ba, shiyasa kullum cikin yimata allurar bacci suke kuma tahakanne kad'ai yaran kesamu suna shan nono awajenta. Rayuwar batool tazama abun tausayi musamman idan ka kalli jariran dake gabanta da kuma yanayin da take ciki, su hassana kam tuni sun samu sababbin iyaye saboda kulawar da zainab ita da d'an uwanta shurahbil ke basu, abunka da yaro rayuwarsu sukeyi cike da farinciki cikin sauran 'yan uwansu yara sai baka rasa bane zakaga sun aza rigama suna kuka sai ankaisu wajen dady da ummiensu, musamman cikin dare ko kuma lokutan da zasuci abinci sai kaji suna rigima waisu bazasu ciba sai I idan dady da ummie ne zasu basu, Abba kuma yasamu sauqi sosai har anbashi sallama amma yanda yayi rama saboda tsananin baqinciki da damuwar da yake ciki kallo d'aya zaka yimasa ka zubar masa da hawaye, yayi kuka, yayi nadama tare dayin tir da zuciya irin tasa, tabbas yayi dana sani abu adadi alokacin da SANNU SANNU yafara karb'a sakamakon abunda yayi, dama anfad'a masa cewa but khairan da sharran wanda duk ka aikata da SANNU SANNU zai riskeka, dama SANNU SANNU bata hana zuwa.....gashi yanzu anzo wajen da abunda ya aikata ya riskesa. A 'bangaren mutumen dake iqirarin soyayyarsu hassana da hussaina kuwa tun ranar da yaji kalaman da suka fito abakin shurahbil yadena bayyana agaresu amma hakan bai hanashi bibiyar rayuwarsu ba akoda yaushe hatta rasuwar Abu sumayya dashi akayi jana'iza saidai ko kad'an bai bari sukayi arba da shurahbil ba saboda tsoron kada wancan tunanin ya zauna aransa, haka kuma yakanzo asibiti duba jikin batool saidai baya zuwa sai lokutan daya tabbatar su shurahbil basa wajen ko sun shiga sallah tukuna, hajia mama na lura dashi Idan yashigo amma bata tab'a kawo komai aranta ba,saboda aduk sadda yashigo sai yafara zuwa ya dudduba marasa lafiyar dake ward d'in tare da yimasu alkhairi sannan yake zuwa wajensu hakan yasa tunaninta yatafi akan qila irin mutanen nanne dake zuwa dudduba marasa lafiya suna yimasu alkhairi don suma duk sadda yashigo dubo goma yake ajiye masu, har ta tab'a nunawa Abba dasu Uncle h shi, Amma ALLAH bai tab'asa suka gane saba ko kuma suka had'u da shurahbil ba sai yau, shurahbil na shigowa da motarsa asibitin ya d'auko su gwaggo da matar uncle hussain yaga shikuma yafito, hakan ya matuqar d'aure masa kai har yafara tunanin ko waye wannan mutumen, tunowa da compliment card d'in daya basa ranar yayi da sauri ya ajiyesu gwaggo yajuya motarsa yakoma gida, yana zuwa yanufi wajen daya sargafe kayan dayasa ranar ga hanger yafara laluben aljihun rigar, cikin sa'a yanasa hannunsa cikin aljihun rigar na gefe yaci karo da compliment card d'in, Wata irin ajiyar zuciya yayi don dama tuntuni ALLAH ALLAH yakeyi inbai yadda shiba, rubutun da akayi jikinsa yafara karantawa kamar haka, [6/15, 11:34 PM] +234 703 729 2170: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___6πŸ’Ž Rubutun dake jikin compliment card d'in shurahbil yaqurawa idanuwa kafin yafara k'ok'arin karantosa cike da mamaki, " _DR. N.I.ALIYU (PSYCHATRIC DR.)_" ya sake maimaitawa aransa, sannan yabi sauran address d'in dake rubuce da kuma numbobin waya har guda biyu da kallo, jujjuya card d'in yafarayi yana son tunano inda ya tab'a jin wannan sunan, Nan take yatuna cewa ai babban likitan da yasha ji ana zance agarine akan k'warewarsa wajen iya kula da mararsa lafiya musamman masu fama da matsalar k'wak'walwa ya matuqar sanin aikinsa tare da tausayawa mararsa lafiya sosai wanda wannan dalilinne yasa nan take yasamu d'aukaka cikin qanqanen lokaci, shekararsa hud'u kenan da yasa akayo masa transfer daga minna zuwa kano, kuma cikin ikon ALLAH yanzu babu inda labarinsa bai kaiba acikin garin saboda tausayi, kamanta gaskiya da kuma taimako acikin aikinsa, ajiyar zuciya yayi tare da cewa "tabbas babu ko shakka wannan mutumen shine likitan da naji ana zance agari, idan kuwa hakane yazama dole na samesa har gida saboda matsalar auntynah tunda ance shi mutumne mai sauqin kai wataqil zai iya bamu wani taimako kodon saboda soyayyar da yake yiwa yaranta" haka yaqarashi zancensa shikad'ai yana safa da marwa acikin d'akinsa kafin ya kad'a katin a aljihu yabar d'akin, yana fitowa yaci karo da zainab tafito ita da twinse zasuji wajen bukin wata qawarta, da gudu suka nufi wajensa kowacensu na Kiran "oyoyo uncle" tare da bud'e hannuwa, shima bud'e nasa yayi suka shige Yana dariya yace,+ "Iyyeee 'yan matan aunty Ina zuwa akaci wannan gayu haka?." "Party zamuje" hussaina tafad'a tana kallon zainab data qaraso wajen, duka hassana ta kaimata had'e da cewa "ke kuma bikine zamuje ba party ba ko aunty zee" tafad'a itama tana kallonta. Dariya zainab tayi sannan tace "Gaskiya kam hassana fad'amata mu biki zamuje ba party ba, haba hussaina wane party ana zaune lafiya, ai sai kija uncle hussain ya kakkarya mu idan yaji haka!." Kallon shurahbil da shima dariyar yakeyi tayi sannan tace "don ALLAH ya shurahbil Ina zakajene?." "Ya akayi ne?" Ya amsa mata atak'aice tare da mik'ewa tsaye daga duqen da yake zai wuce don yasan halinta, yanzunnan me zatace ya ajiyeta, bai qarasa fitaba ta biyoshi da sauri tana fad'in. "Emm.emm dama cewa nayi ko zaka rage mana hanya pls" "Ok, dama nasan shine zancen" yafad'a tare da ficewarsa, da sauri ta dawo baya tariqa hannuwansu sukabi bayansa suna yimata 'yan tsalle tsalle. Bayan sun shiga mota shurahbil ya tayar suka bar gidan ya juyo Yana kallon zee da tasha kwalliya qamshin turare na tashi ajikinta tako ina yace, "Zainab kinji fitinannen qamshin da kikeyi kuwa?" "Eh ya shurahbil turaren yayima dad'i ko?." Saida yamere baki tare da yin kwana ya hau titi daidai sannan yace "Wane dad'i, turare na hawan kai haka?, Meyasa Wai ku bakwa fahimtar cewa annabi yafaku, fisabilillahi wannan qamshin turaren da kikeyi yayi yawa, zai iya jawo hankalin maza akanki, ga wannan baqar kwalliyar da kika b'ata fuskanki da ita, gaba d'aya ta maidaki wata irin halitta daban sai kace dodo ko kuma aljana. dubi d'inkin dake jikinki zainab inada tabbaci akan ko lumfashi maikyau baya barinki gashi kin d'auko mayafi sai kace abun tatar k'ullu kin d'ora akai, gaba d'aya kincika duk wasu sharudd'an da zasu iya jefe rayuwarki cikin halaka" turo baki tayi ranta ab'ace saboda jin yanda take faman kushe mata kwalliya da kafin tace, STORY CONTINUES BELOW "Haba ya shurahbil meye aibun turaren dana saka?, meye laifin kwalliyata da zakace haka?, ALLAH a zamaninnan da kake gani wlh mace idan bata gayu tana gyara jikinta da iya d'aukar dress to ALLAH yasani sai miji yayi mata wuya, saboda yanda idanuwan mazan suka bud'e yanzu" "ALLAH?." "Eh mana, kaima kasan hakan!" "Hmmm nikam bansan komai ba inba kuskuren da nake ganin 'yan mata ire irenki na tabkawa ba, turare da kike gani manzon ALLAH sallalahu alaihi wasallam ya haramta mace ta sakashi idan zata fita domin yin hakan daidai yake da tayi zina, wasu matan na kuskuren fahimtar cewai wai sai ga matar aure wanda shi manzon ALLAH bai banbace matar aure ko budurwa ba, jam'ine na duka mata yayi, ita kuma wannan kwalliyar da kukeyi wlh da kunsan yanda take maida wasunku to da kun hutar da kanku domin asalin kamanninku sunfi sha'awa da burgewa akanta, ni anawa ra'ayin nafiso naga mace tayi kwalliyar da bazata canza mata kamanni daga yanda take ba wannan shike tabbatar mani da cikar hankalinta, banace kuskure ne yin kwalliyar ba, Amma yakamata kudinga yin mai ma'ana, zancen d'inki kuwa a yanda ya matseki d'innan kuma kika fito haka to ina tabbatar maki da cewa kin sake shiga jerin matan da annabi ya tsine masu wato kasiyatun, ariyatun, ma'ilatun, mumilatun....har dai zuwa qarshe akan sakin tsiraicinsu da sauransu, don haka tun wuri kiyiwa kanki fad'a, wannan d'abi'ar ba zata baki mijin aure ba sai shashasha kamarki, ammadai wanda yasan ciwon kansa bazai d'aukeki ba da duk wasu masu irin d'abi'arki domin shike yawan haifar da zinace zinace, bayan ALLAH da kansa yace _'wala taqrabuzzina...'_ kada ku kuskura ku kusanci zina domin takasance alfasha ce, wlh wannan sakin jikin da kukeyi baya haifar maku da kima awajen maza asalima shikesa namiji yaga arharku yaga sauqin fuskantarku da maganganun banza da kuma na fasiqanci, kujurewa rufe jikinku kamar yanda ALLAH ya umurci annabinmu daya sanar da matansa da 'ya'yansa da kuma mata muminai cewa _'yudnina alaihinna min jalabibihinna'_ surufe dukkanin jikinsu da jilbab (hijab) hakan zaisa suyi kima da daraja a idanun ALLAH da manzonsa da kuma duniya, shizai kare masu martabarsu ta 'ya'ya mata kuma yazab'a masu mazaje nagari, ba laifin idan har kinada sha'awar yin wud'ancan abubuwan kiyisu acikin gidanki/ku yanda bazaki d'ibarwa kanki zunubi ba, Idan kuma ke matar aurece sai ALLAH yabaki tarin lada mai yawa saboda kinfaranta zuciyar mijinki don haka ni Ina baki shawara akan cewa wannan ba burgewa bace Idan Zaki gyara kigyara, ke yanzu ko d'aukar aya bazakiyi ga 'yar uwarmu dake can kwance cikin wani hali ba, bazaki wa'aztu da cewa mutuwa na d'aukar ran bawa aduk lokacin da takeso Kuma akowane yanayi yake ba har kike yiwa rayuwarki wannan izgilancin, yanzu Idan aka zare rayuwarki acikin wannan yanayin mezaki je kicewa ALLAHnki" Shiru zainab tayi domin gaba d'aya yau ya kashe mata jiki, tabbas zata gyara kodon samun gobe mai kyau da kuma barranta daga cikin matan da aka tsinewa tun aduniya, ajiyar zuciya ta sauke had'e da cewa "nagode ya shurahbil daka fahimtar dani abunda uncle hussain akoda yaushe yake son nafahimta Amma nakasa saima kallon abun da nakeyi a matsayin takurawa, in Sha ALLAH daga yau nadena bazan qara ba, yanzu kamai damu gida nafasa zuwa bukin" Murmushi yayi tare da jin dad'in yanda ta karb'i gyaransa da hannu biyu sannan yace "A'a basai anyi hakan ba, tunda kinriga kinfito Bari mutsaya shagon d'and'a investment saina saya maki wani mayafin da zai rufe maki jiki kinji ko" cikin jin dad'i ta amasa dasa da "shikenan yayana Ina alfahari dakai" haka kuwa akayi suna kaiwa bakin shagon yayi parking sannan yashiga ya siyo mata wata wani mayafin mai kabri dazai kai mata har guiwa kalar touch d'in kayan dake jikinta, b'ata rai tayi had'e da cewa "a'a yaya ka d'okomun hijab nafi sonsa tunda kayan sun matseni da yawa" "Karki damu in sha ALLAH, wannan ma zai wadatar kedai kisa aranki tubar gaskiya kikayi kuma zaki gyara" "In Sha ALLAH Yaya" tafad'a tare da karb'ar mayafin a hannunsa sannan ta canza, Yana ajiyesu ya nufi gidan Dr.N.I aliyu a anguwar nasarawa kamar yanda yagani rubuce a card d'in, Yana isa ya yakira lambarsa da yayi copy a wayarsa amma yajita switch up, yakira duka biyun yafi ak'irga akashe gashi baisan gidan ba kuma anguwar tsit take balle ya tambaya, hakan yasa yajuya kan motarsa yakoma asibiti, STORY CONTINUES BELOW Yana isa ya tarar anyi transfer d'insu zuwa psychiatric clinic Amma saboda ta tashi daga baccin sai kuka su Abba da hajia keyi saboda yanayin da take ciki, gaba d'aya ta yayace ward d'in da qara tana buge buge, hatta nurses d'in dake kula da ita sun fara jin tsoronta hakan yasa suka kasa matsawa kusa da ita balle su samu damar yimata allurar da aka saba yimata, umurni wani likita yabasu dasu taru sufara d'aureta sai suyi mata allurar, tana ganin sun nufota da igiya tayi wani irin qaraji daya sasu saurin watsewa gaba d'aya, tana ganin haka ta tashi da gudu zata fita suka kamota, yunqurawa takeyi da duka qarfinta tana son kwacewa daga hannunsu amma da yake su kusan biyar ne takasa saidai takoma tana wani gumza kamar zakanya, kasa kallon yanda suke d'aureta Abba yayi da sauri ya qarasa wajen yana kuka tare da d'an doddo kawa nurses d'in sandar da yake tokarawa yana fad'in, "Kucika mun 'yata, kada wanda ya d'aure mun ita, kubarta don ALLAH ku k'yaleta nace" dakatawa batool tayi daga kucce kuccen da takeyi tana sauraren muryarsa tare da k'ura masa idanuwa, hakan yasa sukaga damar da zasu ida d'aureta Amma kafin kace me har batool ta ankara, yayumo wacce ke kusa da ita tayi tare da cijeta ga hannu har saida taciro fatar jikinta, fad'a Dr. Yafara yiwa Abba akan yabari suyi aikinsu Amma yaqi gashi har yajawo ta jima d'aya daga cikinsu, haquri hajiya mama tabashi sannan tarik'o hannun Abba had'e da cewa "alhaji don ALLAH kayi haquri kabarsu suyi aikinsu" kwace hannunsa yayi daga riqon da tayi masa ransa a b'ace yace "Bazan iya kallonsu suna cigaba da d'auremun 'ya haka ba sai kace dabba." Kallon likitan yayi had'e da cewa, "Kai dr, Ina kun sallamemu ko? To kubarni ni nasan yanda zanyi da 'yata koda zata kasheni Amma kar wanda ya sake d'aureta" yana rufe baki ya duqa kusa da ita tare da cire mata igiyar ya jefa masu sannan ya fara yimata magana a hankali "batool, batool, zakije gida?" Bai rufe baki ba tajawo qarfen qarin ruwa dake gefenta ya fad'o masa saman kai har saida yafasa masa goshi, da sauri shurahbil yanufo wajen amma Abba ya d'aga masa hannu, hannu takai da niyara chakumo wuyansa amma jinin da tagani nafita a goshinsa yasa tadakata, ja da baya tafarayi a tsorace kamar wacce kejin tsoron a doketa, batare da Abba ya damuba ya mik'a mata hannu ta k'ara matsawa a tsorace, haka yadinga matsawa wajenta tanaja da baya har ta isa jikin gadon ta runtse idanuwanta, ganinsa gab akusa da ita yasa tafara bud'ewa ahankali, ga mamakin nurses da likitan dake wajen sai sukaga Yana mik'a mata hannu tariqo ya mik'e da ita tsaye har lokacin yana riqe da hannunta, juyowa yayi zai fito da ita suka dinga jayewa suna kallon ikon ALLAH, biye take dashi amma ta tattakure kanta abayansa tana nonnoqe kai yace "Kungani ko, nasani qarfin soyayyar da 'yata keyimun bazai bari ta watsamun qasa a idanuwa ba duk dako bata cikin hayyacinta, shurahbil zo mutafi." Cike da farinciki hajia mama takai hannunta zata rik'ota ta bugemata hannu tana k'ara shigewa bayan Abba, juyowa Abba yayi yace ma hajia mama "kik'yaleta kada ta sake birkicewa kuma" "Amma yakamata katsaya aduba maka goshinka" "Babu komai tunda jinin ya tsaya nadawo daga baya a gyaramun ko kuma naje chemist" Shurahbil dake neman shiga a gabansu ne yace "Abba acan clinic d'in zamuje ne" "A'a gida zanje da 'yata, matuqar ta wannan hanyar da naga sunbi zasu kula da ita to bazan barta anan ba, zantafi da ita gida inbata kulawar daya kamata kuma nasamo manya manyan likitocin da zasu dinga duba mani ita" Ai kuwa haka akayi babu yanda Dr. Bayyi dashi akan kada yatafi da ita gida ba Amma yaqi, dole suka barshi ya wuce da ita don rigimar tsohon tafi k'arfinsu Babu yanda zasuyi, sunyi fad'a har sun gaji saidai shurahbil yayita basu haquri. Wajen shiga mota ma haka Abba yayita fama da ita don k'in shiga tayi sai da yayi ta mata dubaru sannan ta amince tashiga motar, Amma duk wanda ya aza qafa da sunan ya shiga ciki sai tayo kukan kura akansa, hakan yasa daga Abba sai kuma shurahbil dake jan motar suka shiga, hajia mama da kuma mahaifiyarsu shurahbil da gwaggo dake rik'e da jariran saidai abba yakira uncle hussain yace yazo ya d'auki da motar sa daya bari don data shurahbil ce su suka tafi.... STORY CONTINUES BELOW _AFUWAN DA JINA SHIRU BAYAN KWANAKI, NAJE GANIN GIDANE 'YAN UWA DA KUMA ABOKANAN ARZIK'I SHIYASA KUMA KUNGA SUMA AKWAI BUQATUWAR ACE SUN SAMU LOKACINA, NGD DA SAQONNINKU DA ADDU'O'IN ALKHAIRI ALLAH YABIYAKU DA ALJANNAH FIDDAUSI,πŸ‘πŸ»πŸ˜KUCI GABA DA BIBIYAR WANNAN LABARIN AHANKALI DOMIN *SANNU SANNU* BATA HANA ZUWA SAIDAI ADA'DE BA'A KAIBA🀣ONE LUV FILLAHπŸ˜‰πŸ€žπŸ’‹❤️_ *_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_* [6/15, 11:34 PM] +234 703 729 2170: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___7πŸ’Ž Al-amarin batool kam sai addu'a saboda ako yaushe sai qaruwa yakeyi, gashi Abba yabuga kai ga qasa shi baza'a kaimasa 'ya asibitin mahaukata ba, mutum ne shi mai kafiya da kuma zuciya hakan yasa su uncle h suka zuba masa idanuwa domin babu rarrashin da basuyi masa ba da kuma lurar dashi amma yakafe kai da fata, musamman yasa aka gyara mata d'aki d'aya yasa duk aka ciccire abubuwan da suka shafi qarfe da zasu iyasa tajima kanta aka fiddasu sannan ya d'auko wani k'warraren likitan k'wak'walwa yafara dubata, wasu allurai likitan ya rubuta da za'a dinga yimata kullum ko wace k'waya d'aya dubu ashirin kuma Abba ya amince, lokacin dasu Uncle h sukayi yunqurin dakatar dashi da kuma nuna masa cewa kud'in sunyi yawa rufesu yayi da maseefa har Saida suka koma bashi hak'uri, Kimanin watanni biyu kenan ana Abu d'aya amma babu wani sauyi, babu wanda ke matsawa wajenta tak'yalesa idan ba Abba ba hakan yasa kullum cikin hidimarta yake gwanin ban tausayi, abincinta da abun shanta duka shine hakama idan za'aba yaran nono shike karb'arsu yaje dasu cikin dubara ya lallasheta tabasu kuma batayi masu komai indai yana tsaye, duk da k'wak'walwarta bata aiki tana matuqar jin tsoronsa, zancen wanka ne kawai ba'a yimata saboda bazata bari ba shi kuma Abba babu kyautawa ace shi zai yimata, sau d'aya yasa su hajia mama suyi mata yana bakin toilet d'in ya tsareta ai kuwa sunsha cizo da yakushi, tun daga ranar sukace bazasu koma ba, gwaggo ma m takoma tun ana sati d'aya da sallamosu, lokaci lokaci takan kira hajia mama ta tambayi lafiyar jikokinta da kuma ta batool tayita kuka tana addu'ar ALLAH yabata lafiya, haka barrister kamal shima yakan zagayosu idan yasamu sarari wajen aikinsa tare da kayayyaki masu yawa yace aba yaransa. Shurahbil kuwa ko yaushe yana bisa hanyar neman Dr. N.I na kimanin wata biyu kenan bayada labarinsa kuma baya samun lambobinsa idan yakira, yau kamar an tsunkulesa yana kwance ya tashi had'e da zura jallabiyarsa ya nufi asibitn da Dr. N.I ke aiki don duk bid'ar daya yimasa hankalinsa bai tab'a kawo masa da yaje can ba. Yana zuwa ya tambaya aka kaishi har office d'insa, cikin sa'a kuwa ya iskota, ajiyar zuciya yayi tare da yiwa ALLAH hamdala sannan yatura gambun ya shiga, Dr.N.I na ganinsa ya mik'e cikin fara'a yana fad'in, "Ahh! Baban yara kaine a office d'ina?" tare da mik'a masa hannu suka gaisa, murmushi shurahbil yayi tare da sosa qeyar kansa sannan ya zauna saman kujerar da yake nuna masa yana fad'in, "Ya zanyi Dr tunda kab'oye mana, nayi nemanka har nagaji ban sameka ba, har nasarawa anguwarku naje amma nakasa samunka sai yau nayi tunanin zuwa nan asibiti kozan sameka." "Ayya malam shurahbil, ai kayi raggon azanci, kaida har unguwar mu kaje meyasa kak'i tambayawa, ai ko qanqanen yaro katambaya akaika gidana za'a nuna maka, duk da dai nad'anje qauyene wajen wani bincike sai jiya nadawo, yanzu nake cewa anjima Idan narage abubuwa zan shiga asibitin, ya masu jiki hop dai da sauqi ko?" STORY CONTINUES BELOW "Eh alhamdulilah za'a ce amma ambamu sallama ko ince transfer zuwa psychiatric clinic sai dai Abba bai amince mukaje ba, marar lafiyar na nan gida" "Subhanallahi meya faru da itane?." Shiru shurahbil yayi kafin yafara labartawa Dr.N.I halin da batool ke ciki, bai b'oye masa komai ba hatta likitocin da Abba kefaman d'aukowa da allurorin da akeyi mata duk saida yafad'a masa, ya matuqar tausayawa halin da batool ke ciki da kuma yaranta, yajima zaune batare da cewa komai ba kafin yace, "Shurahbil karka damu in Sha ALLAH zan taimaka maku kuma kakwantar da hankalinka da yardar ALLAH zata samu lafiya." "ALLAH ya yarda Dr. Nagode sosai" Shurahbil yafad'a Yana goge k'wallar data zubo masa a idanuwan, "Badamuwa, anjima da marece zanzo saika sanarwa da iyayen naka idan sun amince saika kirani tunda kana da lambata kafin lokacin yayi" "Shikenan Dr. Amma wud'annan lambobin sun dena aiki ko zaka bani wadda zan iya samunka direct" dariya Dr. N.I yayi kafin yace "Ka kira in sha ALLAH zaka sameni yanzu" dama rufe wayoyin yakeyi duk lokacin daya je k'auyen saboda muhimmancin abunda yaje yi, shikesa Idan yatashi hutun wata d'aya yake d'auka don yasamu isasshen lokaci, har sunyi sallama da shurahbil zai fita ya dakatar dashi tare da d'aukar biron dake gabansa da Kuma 'yar guntuwar takarda ya sake rubuta masa wata private no d'insa da bakowa ya sani ba yabashi had'e da cewa "Ka gaida mani da twins da kuma qannensu" "Zasuji in sha ALLAH nagd sosai Dr " sannan yawuce zuciyarsa cike da farinciki sai kace wanda aka tabbatarwa da cewa zata samu lafiya. Kai tsaye gida ya nufa, yana shiga ya hangosu uncle h tare da Abba rik'e da little hassan zaune saman wasu kujeru dake can gefe cikin wata 'yar rumfa, parking yayi sannan yafito cikin motar yanufi inda suke ya gaishesu sannan ya sanar dasu zancen Dr. N.I da batun zuwansa anjima, aikuwa nan mahaifinsa ya titsesa da tambayoyin a ina yasanshi?, waya sanar dashi cewa cikakken likitane da har zai kwashi jiki yaje wajensa bayan bashida tabbacin cewa shid'in likitan k'wak'walwane ko akasin haka, nan yaciro compliment card d'in daya basa ya mik'a masu, sosai Abba yaji dad'i kuma ya amince Dr yazo saboda ahalin yanzu ko qanqanen yaro yakawo masa magani ko kuma wanda zaiba 'yarsa magani tawarke zai karb'esa hannu biyu matuqar ya tabbatar da nagartarsa balle d'an gida da bazaya tab'a cutar da ita ba... *_WAI WAYE (TUSHEN LABARI)_* _WAYE ABU SUMAYYA_ 'Dah ne tilo awajen mahaifinsa malan Idris Aliyu, ya had'u da mahaifiyarsa awani k'auye da ake kira k'auyen yarimawa dake cikin garin kano alokacin an turasa makarantarsu wajen koyarwa, kasancewar shi mutumne da baya son ganin anbar d'alibinsa ko d'aya abaya ta fannin karatu yasashi maida hankali gaba d'aya wajenta saboda rashin son karatu, Rashida Basharu shine sunan mahaifiyarsa takasance batason karatu ko kad'an tun tana 'yar qanqanuwa har takai 'yar kimanin shekaru goma sha biyar Amma babu abunda yacanza, tsabar repeating d'in da akeyi mata yasahar awud'annan shekarun nata take a matakin aji biyar primary shima d'in daqyar da sud'in goshi akasamu takaisa, social studies shine darasin da take d'aukarsu kuma gwargwado d'alibban nasa suna fahimta inbanda Rashida da akoda yaushe batada wajen zama irin kujerar baya tana sharar baccinta, yafahimci hakanne ta dalilin yawan tambayoyin da yakeyiwa d'alibansa kuma suna bashi amsa daidai gwargwado amma ita saida tazuba masa idanuwa, gashi kusan tafi duka d'aliban ajin be nasu girma, hakan yasa ranar da abun ya fara bashi haushi ya maidota sit d'in gaba inda monitor d'insu yakeyi, cikin b'acin rai dajin takaici yace da ita "as from today this is your sit, I don't wanna be see you sitting back again you here me ko?." yaqarasa maganar cike da fad'a tare da rik'e kunnensa d'aya alamar jamata kunne, Rashida da batasan komai yafad'a ba tana ganin yariqe kunne da sauri tamik'e takama kunnuwanta cike da tsoronsa saboda ganin yanda ya d'aure fuska, gaba d'aya 'yan ajin suka sa dariya har dashi, saida yayi mai isarsa sannan yajuya yabar ajin dama period d'insa yaqare, tana ganin haka ta d'ago kanta had'e da cewa STORY CONTINUES BELOW "Malan in tashi?" Juyowa yayi had'e da cewa, "Dama ai bani na saki ba ke kikasa kanki, don haka zaki iya tashi idan kin gaji." "Malan kaifa naga kayi mani na kurmaye kace nakama kunnuwa na." Dariya yayi sannan ya girgiza kai had'e da cewa monitansu "na'ima tashi kifad'a mata abunda nace." Ai kuwa na'ima cikin irin zaqewa d'innan tamik'e tana fad'in "cewa yayi daga yau nan shine mazauninki baya son yakoma ganin kin zauna abaya kiji ko?" da sauri rashida ta d'aga kai tana fad'in "yes" suka sake kwashe mata da dariya hadda monitor d'insu dake yimata gwalo, "Keep quiet" yafad'a in a serious tone kafin nan kowanensu yakama bakinsa, harara ya maka mata had'e da cewa, "shemless thing to you" washe baki tayi had'e da cewa "thank you sir" cike da jin haushi yabar wajen yana tunanin ta ina zai fara saitata akan layi. Duk iya dubarar daya kamata yayi wajen ganin itama tamaida hankali wajen fahimtar karatu kamar sauran d'aliban yabi amma abun ya cutara, yabi mata tahanyar yawan yimata tambayoyi ko zataji haushi tamaida hankali amma taqi, yayi zaunar da ita yakoya mata ita kad'ai shima ta gagara fahimta, hakan yasa aka kirawo masa ita a office d'insa don ba qaramin tausayawa rayiwarta yakeyi ba, bayan tazo tagaishesa ya amsa cikin natsuwa sannan yace, "Rashida meyake damunki" shiru tayi har saida ya sake cemata, "meyasa kike son wahalar da mahaifinki bakyason karatu?" Cikin amsar da baiyi be tsammanin jinta daga bakin taba yaji tace, "Malan ni bana sone kuma bana ganewa shiyasa." "A'a Rashida baki sawa ranki zaki gane bane, Amma inada yaqini akan idan kika jajirce Kuma kika maida hankali da SANNU SANNU zaki iya." "Bazan iya ba malan." "Saboda me kikace haka?." "Saboda aure nake so malan!" Bata qarasa rufe baki ba yayi saurin zamewa daga riqe da fuskansa da yake da hannu ya tokare ga bencin dake gabansa yana mamaki, yajima bai sake cemata komai ba yana nazarin kalamanta masu ban al-ajabi har bayan wasu mintota kafin yace, "Amma Rashida kinsan meye aure kuwa, kinsan illar dake cikin jahilci da rashin ilimi acikin rayuwar d'an adam da kika zab'awa kanki shi?." "A'a ko d'aya, Amma nidai kawai natsinci rayuwata abisa turbar son aure, wannan kawai shine dalilina." Wata irin ajiyar zuciya ya sauke sannan yace, "Shikenan tashi kitafi, ALLAH yakyauta yazab'a mana mafi alkhairi?." "Amin malan" ta amsa masa sannan tamik'e zata fita, har takai bakin qofa ya tsaida ita had'e da cewa "menene cikakke sunan mahaifinki Kuma awace anguwa kuke da zama?" "Sunansa malan bashar mai takalma, anan anguwar muke kusa ga masallacin juma'a dake nan gefen makarantar nan." Jinjina mata kai yayi sannn ita Kuma tafita abunta hankali kwance.... _don Allah kutayani turawa a groups, gaba d'aya nayi missing nawa kafin komai yayi settling up_πŸ‘πŸ» *_ALLAH KAJIK'AN IYAYEN MUπŸ‘πŸ»πŸ˜­_* [6/16, 11:45 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ STORY CONTINUES BELOW Page___8πŸ’Ž Bin bayanta yayi da kallo har saida tafice sannan yayi ajiyar zuciya, azahirin gaskiya yayi mamakin yanda Rashida ta iya bashi amsa kai tsaye batare da tayi shayin komai ba, amma azuciyarsa yaga nagartar da kuma ingancinta data iya bayyana abunda ke cikin zuciyarta wanda da yawan 'yammata irin wannan nadamunsu amma sai su gagara furtawa balle har asama masu mafita, Wanda kuma yin hakan kuskurene dake haifar masu da jefawa cikin halaka, koda yake mafiya lokuta iyaye sune sila saboda rashin sauraren 'ya'yan nasu da wani dogon buri da suka d'orawa kansu, mik'ewa yayi tare da d'aukar littafin dake gabansa yanufi ajin da yake da darasi da d'alibansa. Yinin ranar abu d'aya ya dinga tunani shine kalaman d'alibar tasa, bayan yayi nazari da Kuma dogon tunani ya yanke shawarar iske mahaifinta yauidan an tashi makaranta, ana tashi kuwa ya hangota bakin gate ita da abokananta zasu fita da sauri yaturo wata d'aliba be takira masa ita. "Rashida malan Idris nakira ki" yarinyar tafad'a had'e da ficewarta don dama gida tanufa, kallon Rashida meenah qawarta tayi sannan takalli sauran friends d'insu had'e da cewa, "Anya rashida malan Idris ba sonki yakeyi ba?" "Wlh Nima haka nake zargi shamsiya" duka takaimasu had'e da cewa, "Bana son sa'ido, ni malaminane babu komai tsakanina dashi" "Hmm mudai bari muwuce kya cimmana" "A'a don Allah kujirani ba jinawa zanyi ba yanzu zan dawo." tana gama fad'ar haka bata jira mezasu ceba tanufi wajensa, tana isa inda yake tsaye wajen iccen dalbejiya tace, "malan gani" "Yawwa Rashida dama akan maganar da mukayi dake jiyane." "Meyafaru malan" tafad'a had'e da duqar da kanta qasa, murmushi yayi sannan yace "Babu abunda yafaru, Amma kin tab'a sanarwa da mahaifinki abunda kika fad'a mani?." Saida tagyara zaman jikkar dake saman kafad'arta sannan tace "Nafad'a amma sai yayimun fad'a sosai tare da gargad'ina akan cewa kada insake inqara yimasa wannan maganar, inajin mahaifiyarsa nayi masa magana amma sai yace tafita batuna ai banida hankali karatu yakamata ace nayi yanzu, ni kuma daga lokacin ban sake yin maganar ba." Girgiza kai yayi sannan yace ta tafi, koda takoma ta samu har lokacin suna nan a tsaye bakin gate suna jiranta, tambayoyi suka fara jefo mata amma ko kad'an batabi takansu ba tawuce abunta tana dariyarsu, Anayin sallar la'asar yaje gidansu had'e da yiwa mahaifinta sallama ya fito, dattijo ne sosai amma saboda yanada yalwar wadatar da za'a iyaci sau uku agidansa kowace rana bazaka iya fahimtar hakan ba, kujeru yasa aka kawo masu guda biyu qofar gida, bayan sun zauna suka sake gaisawa sannan malan Idris yayi masa bayanin koshi waye tare da cewa "Dama nazone akan batun Rashida 'yarka" "Tofah injin malan bawani shashancin ta aikata ba?." Mahaifin nata yafad'a tare da muskutawa ya gyara zamansa, "ko kad'an baba, kawai yanayin yanda take karatune yasa nace bari na bincika ko akwai wata matsala da kukasan tana fama da ita don asan wane irin taimako yakamata a matsayinmu na malamai mubata awannan gab'ar, saboda idan kalura awud'annan shekarun nata kamata yayi ace yanzu tana makarantar gaba da primary wato secondary amma ace gatanan har yanzu a primary kuma bata fahimtar komai kaga wannan matsalace da yakamata ace anbinciki dalilin da yasa takeyin haka." jinjina kai mahaifin nata yayi tare da fitar da wani iska abakinsa sannan yace, "Hmmm! Malan karabu da wannan yarinyar, babu wata matsalar dake damunta in banda daqiqanci da kuma shashanci, ko kad'an bata son karatu tuntana 'yar qanqanuwarta, haka mukayita fama da ita har takai wud'annan shekarun, hatta aji shiddan da kagata saida nabiya kud'i masuyawa sannan nasamu akaturata saboda tasamu takardar shedar qare primary don insamu inkaita tagaba da ita wato secondary, alokacin tana qarama na d'auka quruciya ce sai yanzune data girma na fahimci cewa abun nata iskancine da rashin maida hankali wajen karatu, ko kad'an ba tason karatun shiyasa takeyin hakan." STORY CONTINUES BELOW "Amma baba ai wannan babbar matsalace da yakamata ace kazaunar da ita katambayeta saboda ataimakawa rayuwarta, duk yaron da kake gani anhaifesa da baseera, kawai rashin samun daidaituwar layin d'aya kamata su haune kansa kaganesu haka, inada yaqini akan da za'a fara magance mata matsalar da kesa ta kasa maida hankali ga karatu to da tabbas za'asha mamakin ganin baiwar da ALLAH yayi mata," "Taya zan iya magance mata matsalarta malan bayan bazata yuyu ba?, Shekarunta duka sha biyar aduniya yanzu tashigo shekara ta sha shida, taya zan iya aurar da ita awannan lokacin? Yarinyar da batasan komai ba aduniya ga kuma rashin ilimi da yake d'awainiya da ita, wakake tunanin zai iya karb'ar amanarta idan na damk'a masa?" "ALLAH shine masani baba, tunda wannan itace matsalarta zaifi kyau ace anyi mata auren da ace anbarta ga tutar babu, ba ilimin kuma babu auren daga qarshema inba ALLAH yakare ba abunda ba'aso yabiyo baya, ni Ina ganin da zakayi hak'uri kayi mata auren da yafi, shekarunta basuda illar da zasu hanata aure saboda ada iyayenmu da shekaru goma sha biyu ake aurar dasu kuma su zauna lafiya har su haifemu ba tare da sunyi wani karatu ba." Rai b'ace mahaifinnata ya mik'e had'e da cewa, "ni bazanyi hakan ba, domin wancan zamanin daban wannan ma daban saboda haka idan wannan yakawoka tashi katafi don wlh ko bataso dole sai tayi karatu, wayasani ko kune kuke b'ata mana yara kuna juya masu ra'ayi saboda son kanku." "Subhanallahi, gyara kayanka baba ai bazai zamo sauke muraba ba, a matsayina na malami don na bibiyi matsalar dake jawowa d'alibina rashin fahimtar karatu bazai zama illa ba, kuma wannan ai shawarace nabaka saboda kasamawa 'yarka maslahar rayuwa da kuma kai kanka, idan kana ra'ayi saika d'auka idan Kuma baka ra'ayi kanada damar da zaka ajiyeta, meye abun b'acin rai da har zaikai ga wud'annan kalamai haka!." "Naji kuma nagode kama hanya katafi." Mik'ewa malan Idris yayi ransa duk babu dad'i had'e da gyara tsayuwarsa sannan yace "Zan tafi kayi hak'uri don ALLAH bisa shiga rayuwarka data ahalinka da nayi amma karka manta annabi yace _kullukum ra'in wa kullukum mas'ulun an ra'iyatihi_ damu malamai da kuma ku iyaye dukkaninmu makiyayane kuma dukkaninmu abun tambayane akan abubuwan da aka bamu kiwo, kayiwa ALLAH godiya daya baka 'yar da zata iya fad'a maka gaskiyar abunda ke ranta sab'anin wasu 'ya'yan da saidai iyaye suganesu da abun kunyar da son ransu ne ya jawo hakan." Yana gama fad'a yabar wajen cike da mamakin iyayen dake tafka kuskure irin haka da zai kaisu ga dana sani.... *_ALLAH KAJIK'AN IYAYEN MU_*πŸ‘πŸ˜­ [6/17, 11:38 AM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___9πŸ’Ž Yana barin wajen saiga Rashida tafito zataje islamiya, kallo d'aya tayiwa mahaifin nata dake faman fad'a yana suruttai ta d'auke kai saboda sanin halinsa, ta gabansa tabi zata wuce ya daka mata tsawa yana fad'in, "shashashar yarinyar zo nan." dawowa tayi agabansa ta durqusa kanta sunkuye ak'asa yaci gaba da cewa, "wane d'an iskan malamine kika turomun har gida ya titseni yana nema yafad'a mani maganganu akanki." Cikin rashin sani tace, "malami kuma baba?, Wlh ni ban turo maka kowa ba." Aharzuqe yayo kanta yana fad'in "wato baki san ko waye ba ko? Maza shiga cikin gida idan jikinki yafad'a maki zakiyi bayani daqiqiyar yarinya kawai da batasan abunda takeyi ba." STORY CONTINUES BELOW "Baba makarantar islamiya zanje fa." Tafad'a tana turo baki had'e da ja baya daga durqushen da take, ganin yayo kanta yasa ta tashi tanufi cikin gida da gudu, bayanta yabi yana cigaba da fad'an har ya shiga cikin gidan, hangota yayi tab'uya abayan mahaifiyarta dake shara tsakar gida tana fad'in, "don ALLAH Baba kayi hak'uri ni bansan kowaye ba." "Koma waye shi ni bai isa ya canjamun ra'ayi ba, karatune sai kinyi ko bakyaso har gaba da secondary in Sha ALLAH, don haka idan zaki dage kimaida hankali kiyi karatu ki dage donni bazan aurar dake yanzu ba har sai kin kammala degree." Bubbuga qafa Rashida tafarayi tana kuka yayinda mahaifiyarta da baba sukayi tsaye suna kallon ikon ALLAH cike da mamakin wai meyake damun tane da gaba d'aya ta zubar da kunyar da aka san 'ya mace da ita agabansu tana kukan aure take so, wani irin takaici ne yarufe baba ya karb'e tsintsiyar dake hannun mahaifiyar tata yafara zabga mata jiki tasa ihu tana tsalle tsalle tana fad'in, "wayyo baba kayi hak'uri, ni ban turo kowa ba wlh, malan Idris kad'ai ne ya tambayeni a ina ne gidanmu na fad'a masa amma daga haka bance masa komai ba, wayyo umma kice yadena dukana da tsintsiya fa babu kyau" kad'an yarage ita da baba suyi dariyaganin yanda take tsalle kabar d'an biri, cikin gimtsewa baba yace "Ai k'wanda nadukeki da ita ko kyabar wannan zancen banzar da kikeyi kinatsu kiyi karatu." "Ni bana son karatun nan baba wlh..." Bata qarasa ba umma tayo kanta da sauri tarufe mata baki gudun kada tajawo mata abun fad'i a makwabta, jefarda tsintsiyar baba yayi yafice gidan yana wani huttai sai kace namijin zaki yabar umma da ita tana yimata fad'a. "Haba Rashida! Haba Rashida! wannan abu dame yayi kama, don ALLAH meyasa bazaki natsu kiyiwa kanki fad'aba, yanzu meye illar mahaifinki don yace kiyi karatu?, 'yafa mace kike kuma haihuwa zakiyi, da wane ilimin kikeso kiyiwa naki yaran tarbiya idan har bakiyi karatu yanzu ba?." Ita dai banda dudduba jikinta da shacin tsintsiya duk yabi yakwanta mata babu abunda takeyi, asalima ba sauraren umma take yiba balle tasamu amsoshin tambayar da take yimata, "umma dubi yanda baba ya fasamun jiki da tsintsiyar nan bacin yasan duka da ita babu kyau?" Tafad'a hawaye kwance a fuskarta tana kallon umma, tsabar takaici yasa umma mik'ewa had'e da zungureta tabar d'akin tana fad'in, "ai shikenan ke kika sani tunda bakisan ciwon kanki ba sai kije kiyi abunda kike so, ana yimaki magana don kin raina wayon mutane kin maidani mahaukaciya nakiyi kikeyi, in akwai abunda yafi aure kije kiyi idan kina iyawa, shidai ilimi da kike gani garkuwane acikin kowace irin rayuwa tad'an adam, wanda kuma duk baya dashi babu banbanci tsakaninsa da dabba." Acan cikin d'aki Rashida tace "Haba umma, haba umma dabba fa kikace, ALLAH dai yatsareni," "Eh dabba mana, meye banbancin tunda bazai iya fahimtar duk abunda rayuwa take ciki ba balle ya banbance tsakanin baqi da fari acikin al'ummar dake zagaye dashi, matuk'ar baki sauka akan dokin naqin da kika hauba kika natsu kikayi karatu to tabbas kema d'in bakida banbanci da wannan akuyar da kike gani d'aure" tak'arasa maganar tana juyawa akuyar k'asarin dake gabanta, d'ago kan da zatayi taga Rashida tsaye agefen k'ofar d'akin kumbure da fuska tak'urawa akuyar idanuwa, harara ta cillama ta sannan tace, "ki kalleta dakyau kigani k'ilan har saita fiki gata saboda ita babu mai takura mata kuma dole abata abinci taci batare da zagi ko duka da tsangwama ba Amma kefa? Wayasan me gobenki zata haifar maki." "Kai umma nifa inada ilimin arabi, taya zakice d'aya muke da wannan abar dako tsarki batayi balle tasan farillan arwala dana sallah kuma har kice saita fini gata wai don d'ai banida ilimin boko, nidai don ALLAH kubarni bana son karatunnan wlh nafison aure akansa" awannan karon kasa cewa komai mahaifiyar tata tayi harna tsawon wasu lokuta maganganunta kad'ai take ji nayi mata yawo a k'wak'walwa, a inda take tadawo tarik'o hannuwanta ta zaunar da ita sannan itama ta zauna suna fuskantar juna tace "Rashida kifad'amun gaskiya, meyasa kike son ayi maki aure ba tare da kinyi la'akari da wud'annan qananan shekarun da kike dasu ba." "Umma nima ban sani ba, kawai ji nakeyi ina tsintar kaina a wasu lokutan cikin yanayin sha'awar son yin auren." "Rashida kin kuwa san me kalmar aure kenufi?" STORY CONTINUES BELOW "Eh malamin islamiyarmu yace mana shine kasantuwar mace da namiji a inawu d'aya bayan angabatar da sadaki da kuma waliyai da shedu, sannan yace ashari ance shine idhalu shai'i fishshai'i wato shi..." Saurin dakatar da ita umma tayi gabanta nafad'uwa had'e da cewa "Ya isa Rashida na yarda kina da ilimin arabiy kuma ke ba daqiqiya bace kamar yanda muke fad'a amma da kin amince dayin karatun bokon ma koda secondary ne saboda shi yana taimakawa wajen iya zaman takewa da mutane, ayanda kikayi bayani aure baya kasancewa har saida samuwar namiji da mace, to ke yanzu ina namijin da kika tanada ayi maki auren." "Umma akwai wani Rabe d'an gidan mai koko dake sona idan kuma bakwa sonsa zaku iya zab'amun duk wanda kuke so" Wata irin ajiyar zuciya iya ta sauke don tasan abun da kamar wuya mahaifin nata ya amince da auren yaron saboda rashin cancantarsa, tashi tayi ranta adagule taci gaba da aikace aikacenta batare da tasake bita kanta ba. Adaren ranar kasa bacci mahaifiyar tata tayi saboda tunanin maganganun 'yarta, in banda juye juye babu abunda takeyi domin tasan mahaifinta bazai yarda yayi mata abunda take so ba kuma ab'angaren yarinyar tafahimci kalamanta da gaske takeyinsu har cikin zuciya, tanajin tsoron kada rashin yimata abunda take son ya jefata cikin wani mugun hali ko iftila'in rayuwa da zai kaita yabaro ko kuma yatab'a mata mutunci da kuma kimarsu, fashewa tayi da kukan da yasa baba farkowa daga baccin da yakeyi a tsorace had'e da cewa "subhanallahi maman Rashida lafiya kike kuka awannan tsohon daren haka, me akayi makine, meke faruwa dake ne?" Cikin shesshekar kuka tace "Babu komai malan, kawai Ina sone don ALLAH kabar yarinyar nan tayi aure shine alfarmar da zan roqa awajenka amatsayina na mahaifiyarta." Tsaki yayi had'e da jan mayafinsa ya komawarsa yakwanta yana fad'in dama wannan maganarce ta zaunar dake kina kuka?, To wlh kinji na rantse bazanyi mata aure yanzu ba dole sai tayi karatun da nake so." "Kada kace haka don ALLAH, bamusan awane yanayi take acikiba wanda yasa ta furta hakan, katunafa mu iyayene daya kamata ace 'ya'yayenmu na alfahari dasu, kuma kada kamanta su amana ne da ALLAH yabamu ahannayenmu bai kamata ace munwofantar da buqatunsu da ALLAH yad'ora akanmu ba, don ALLAH tunda bata son karatunnan kayi hak'uri muyi mata auren tunda bamusan abunda ALLAH kenufi ba." Fita batunta yayi yaci gaba da baccinsa tanata faman basa hak'uri da rok'onsa, tun yana jinta har yadena bacci ya d'aukesa, data fahimci hakan taje ta d'auro arwala ta tada sallah tana fad'awa ALLAH daya sauko da zuciyar mijin nata ya amince da yima 'yar tasu aure, Haka yatashi da asuba ya sake tadda ita tana kukan, shiru yayi yana kallonta na tsawon mintuna kafin yayi tsaki had'e da mik'ewa yabar d'akin, arwala yayi lokacin har antada sallah anan masallacin dake kusa dasu yafice da sauri, be dawo gidan ba har saida rana tafara fitowa nan ma sake iskota yayi tana kukan, tsaki yaja sannan ya zauna agefen gado yana kallonta yace, "Yanzu wannan kukan da kikeyi tun jiya fisabillahi bai isheki ba?" "Taya zai isheni bayan fargaba da tsoron halin da 'yata zata shiga ciki yana dasqare azuciyata," girgiza kai yayi had'e dayin wani tsakin na ba adadi kafin yace "to yanzu ya kike son ayi?." "Kayimata abunda take so tunda bai sab'awa shari'a ba." "Ita fa rantsuwar da nayi?." "Zan fidda maka da kono." Kallonta yayi cike da tausayin yanayin data koma tsakanin jiya da yau, macece ita mai hak'uri da kuma juriya, iya kyautatawa da kuma biyayyar aure tana yimasa, ko kad'an bata son taga ransa yab'aci shiyasa shima bayason ganin nata b'acin rai, matuqar yin hakan zaisa tayi farinciki kamar yanda take faranta masa to zai amince da buqatar yarinya, nisawa yayi sannan yace taje takirawo masa ita, mik'ewa tayi duk jikinta ba k'wari taje takirawota, bata jima da dawowa ba sai gata tashigo, gaidasu tayi suka amsa mata sannan tanemi waje tazauna, STORY CONTINUES BELOW Gyaran murya mahaifin nata yayi had'e da cewa, "Rashida naso inbaki ilimin dako bayan ranmu zai amfaneki kuma kiyi alfahari dashi amma hakan ya cutara saboda wani buri da kike dash a ranki, mahaifiyarki nagartacciyar matace da tasan dukkanin haqqoqan zaman takewa da bazan iya jurar halin dana ganta daga daren jiya zuwa yau ba, don haka bisa roqo da tayi nahak'ura da ra'ayina na amince da naki kuma zanyi maki abunda kike so saboda wanzuwar farincikinta amma Ina so kisa aranki kuma kirubuta ki ajiye azuciyarki cewa ilimi shine gishirin zaman duniya da bawa kan ribatu dashi adukkanin tsawon rayuwarsa kuma ko yaushene zaki dawo da kanki kinemesa" Shiru yayi na wani d'an lokaci sannan yace, "Don haka idan kinada wanda kike so na amince ki sanar dashi cewa yaturo iyayensa." "Baba kayi hak'uri amma ni banida wani masoyi sai Rabe na gidan hajia mai koko." Dariyar takaici yayi sannan yace, "wannan baiyimun ba kicanza wani, domin yaron duka duka shekarunsa basu wuce ashirin ba taya zai aureki har ya iya kula dake, yanzu haka yana can makarantar kwana aji biyar shi yaje yanemi ilimin, to ta ina yaga inda zai ajiyeki." "To shi kad'aine ke sona baba Amma zaka iya zab'amun duk wanda kaga ya dace." Cike da mamaki yake kallonta kafin yace, "kinsan me kike fad'a kuwa." "Eh baba nasani kazab'amun ko waye zanyi masa biyayya kuma zan zauna dashi." "Shikenan tashi kitafi." Yafad'a yana murza hannayensa daya had'e waje d'aya, Bayan tafita yakalli mahaifiyarta yace "Kingani abunda nake son kigane kenan, tadami mutane da aure take so amma gashi takasa fiddo da wanda zata aura, ina tausayin rayuwarta saboda nasan SANNU SANNU bata hana zuwa..., ba baki nayi mata ba amma duk daren dad'ewa inada yaqini akan sai taga illar rashin tsayawa tayi karatunnan, kiduba fa ko had'a haruffan hausa bata iyayi taya rayuwa zata zauna ahaka." "Gaskiyane malan amma mubita da addua shiyafi, yaran zamanine kahaifesu baka haifi halin suba" Anan ya zauna yana bata labarin abunda yafaru jiya tsakaninsa da malamin makarantarsu d'aya iskosa akan matsalar rashin gane karatunta sannan yafad'a mata shawarar daya yanke akan mijin da zai aura mata, fatan alkhairi umma tayi had'e da fatan Allah yasa wanda aka zab'a mata d'in ya amince da ita.... _Note_ _A wannan gab'ar yakamata iyaye su fahimci cewa duk wani kalami da 'ya'yansu zasuyi yakamata ace sun natsu kuma sun zauna sun fahimcesa kamar yanda mahaifiyar Rashida tayi domin kowane yaro yanada k'wak'k'warar hujja da dalili akan kowace irin kalmace da zai fad'a Wanda sune zasu iya banbance mai kyauce ko kuma akasin haka, kamar dai Rashida ga bayanin data zauna tayiwa mahaifiyarta duk mai hankali yasan cewa zancen auren da take fad'in tana so har azuciya ne bawai abaki kad'ai ba, kuma kowane yaro da yanayin qaddarar da Allah ked'orasa akai tun yana qanqaninsa wacce iyayene solar tabbatuwarta akansa, don haka iyaye mudinga natsuwa muna nazartar kowane harafi kuma kowace kalma tare da kowane muradai na 'ya'yanmu don sama masu mafita akan abubuwan da zasu iya jefasu da uma mu cikin nadama da dana sani nahar abada, ilimi nada amfani sosai amma idan jiran asamesa zai iya jefa rayuwar 'yarki/ka cikin wata matsala za'a iya jinginesa har sai bayan an kauda waccan matsalar sai aci gaba da nemansa, ubangiji ALLAH yasanya muradanmu na alkhairi su daidaita dana 'ya'yanmu domin tabbatuwar farincikinmu da kuma samuwar ingantacciyar rayuwarsu, ba abun mamaki bane abunda Rashida ta aikata domin yasha faruwa ga wasu 'yan matan kuma yakanci gaba da faruwa, wasu kan furta da baki wasunsu kuma kannuna alama, amma sai kaga iyaye sun kasa fahimtarsu tare da kauda idanuwansu akan abunda suke son (aure) sai kaga sun lalace daga qarshe ma sun jawo masu abun fad'i aduniya wal iya zubillahi ALLAH kashirya mana zuri'armu_ *_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ˜­_* [6/18, 6:47 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž STORY CONTINUES BELOW _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___10πŸ’Ž Misalin qarfe goma na safe baba yanufi makarantar su Rashida yasa aka aka kirawo masa malan Idris, cikin girmamawa yayi masa sallama tare dasa wata d'aliba ta d'auko masu kujeru guda biyu ta aje masu a k'ark'ashin inuwar wata bishiya dake a tsakiyar compound d'in makarantar, hannu ya basa suka gaisa had'e da cewa "bisimilah baba" yana nuna masa kujerun, tare suka jero har suka iso wajen, saida ya zauna sannan shima yazauna yana nazarin abunda yakawoshi bayan jiya sun rabu baran baran dashi, shiru yabiyo bayan gaisawar tasu kafin can baba ya nisa yace "Ina fatar kaganeni malan?, nine bashar mai takalma wato mahaifin Rashida wanda jiya kaje wurinsa" murmushi malan Idris yayi kafin yace "naganeka baba, ya gida? Ya iyalin?, Injin dai ko lafiya naganka yanzu?" "Eh lafiya klw alhamdulillah, dama nazone inbaka hak'uri bisa abunda yafaru jiya, sai daga baya dana zauna nayi nazari nafahimci nayi kuskure akan abunda nayi maka, saboda shi gyara kayanka bazai zama sauke muraba ba, zuciyata ta gamsu kuma ta amince da shawararka don haka nazo inbaka hak'uri, don ALLAH kayi hak'uri bisa kausasan kalaman da nayi agareka, kasan duka mai rai ajizine" kansa na aqasa yana murza 'yan yatsun hannunsa ya d'ago yana kallon baba sannan yace "Karka damu baba, wlh babu komai ai haka rayuwar tagada, wasu mutane nada saurin fahimta da kuma yarda wasu kuma akasin haka, koma dai meye ni babu komai araina nayafe maka, saboda haka kamanta da komai babu wata damuwa, mukan yiwa ALLAH laifi ya yafe mana balle mudaya halitta." Jinjina kai baba yayi yana qara yaba hali irin nasa tare da tunanin ta inda zai b'ara b'ullo masa da d'ayan zancen daya kawoshi, cikin dakewa yayi gyaran murya had'e da cewa "madalla malan naji dad'i sosai kuma nagode, Allah yayi albarka yasa agama lafiya, hak'ik'a samun mutum irinka awannan duniyar da za'ayiwa laifi kuma adawo arok'esa yafuwa kai tsaye yayafe nada wahala, nagode sosai" "Babu komai ba ai yawuce" "To bari natashi natafi nasan bazaka rasa ajin da zaka shiga koyarwa ba yanzu" "Ai yau aji d'ayane agareni baba kuma tun safe nagama dasu saboda first period ne, Bari dai akirawo maka Rashida ko?" "A'a kyaleta kasan yau juma'a bawani dogon lokaci bane gashi lokacin zuwa masallaci na gabatowa" mik'a masa hannu yayi suka sake gaisawa sannan yajuya zai tafi, har yayi taku biyu sai kuma ya tsaya had'e da juyowa yace "Emm nace bakaji ba?." Juyowa malan Idris da har yafara tafiya shima yayi had'e da cewa "Na'am baba, magana kakeyi?." "Eh, dama nace baka fad'amun sunan kaba da kuma inda kake don da alama bautar qasa takawoka nan!." Saida yayi murmushi sannan yace, "Sunana Nura idris aliyu, Amma anfi sanina da Idris aliyu saboda da haka abokanan karatuna suke kirana a makaranta shiyasa sunan yabini, ni d'an garin nanne a qauyen bebeji." "Ikon ALLAH, inada aboki acan kuwa, sunansa malan idi ko kasanshi, muna had'uwane idan munje cin kasuwanne dashi." Dariya yayi had'e da cewa, "in dai malan idi mai awaki kake nufi toshi d'in ai mahaifina ne." "Allahu akabar malan dawo mu zauna." Baba yafad'a yana maijin cewa in sha ALLAHU haqarsa zata cimma ruwa, dama shi kuma malan idris kamar yanda yafad'a bayada wani ajin yanzu don haka ya sake dawowa suka zauna, "Aikuwa aminina ne sosai, sharabona dashi tun watanni biyar da suka wuce yacemun zaiyi tafiya to har yanzu kuma bamu sake had'uwa ba, ko har yanzu bai dawo bane?" STORY CONTINUES BELOW "A'a baba yadawo amma a hanyarsa tadawowa yasamu had'ari yanzu haka yananan gida zaune ana jinya yau sauqi gobe ciwo, wannan watansa na hud'u kenan baya zuwa ko ina" "Subhanallahi, gaske mukajisa shiru kuma gashi ALLAH baisa mukabi bayansa ba muji ko lafiya? Sai satinnan daya wuce muka fara shawarar zuwa nemansa don munzata tafiyar tasa mai dad'ewa ce shiyasa muka jisa shiru, ubangiji ALLAH yabashi lafiya yasa kaffarane, insha ALLAH ranar lahadi munanan tafe mudubashi, bawan ALLAH! malan idi ai mutumen kirkine." "Amin baba ALLAH ya yarda." Wannan zancen da baba yaji shine yahana yayiwa malan Idris zancen Rashida alokacin amma sosai yasake samun natsuwar mik'a aurenta a hannunsa kodon nagartar mahaifinsa da kuma tasa, sun d'an jima suna hira anan yake sanar dashi yau d'innan in ALLAH yaso zaije can qauyen yadubo mahaifin nasa kuma insha ALLAH zai fad'a masa cewa yana gaisheshi sannan baba yawuce bayan yakarb'i address d'insa. Bayan yawuce malan Idris yayi dariya tare da cewa "ALLAH mai iko!haka rayuwa take shiyasa akeson kazauna da kowa lafiya, da ace jiya bayyita tausar zuciyarsa ba akan abunda baba yayi masa daba qaramar kunya yau yajiba kasancewarsa abokin mahaifinsa." Sake murmushi yayi sannan yakoma cikin office d'insa Rashida kuwa tuni cikinta yad'uri ruwa ganin mahaifinta a makarantar, atunaninta yazone saboda abunda yafaru jiya, tsoronta d'aya kada yauma idan takoma gida ya doketa idan malan idi yafad'a masa sauran abunda tace, jikinta har rawa yakeyi atashi taje wajen malan Idris taji abunda yakawo mahaifinta don gaba d'aya ta manta da zancen da tayi dashi da safe akan yazab'a mata duk mijin da yaga dama kuma tunaninta bai kawo mata baba zai iya nema mata malan Idris ba, ana tashi tanufi office d'insa har suna cin karo dashi yana qoqarin rufe office d'in batare data damu ba cikin turo idanuwan dake nuna tsoro qarara a fuskarta tace "don ALLAH malan meya kawo baba makarantar nan!? Wlh inajin tsoron kar ace ka koma cemasa wani abun akaina ya sake dukana, ko ranar da kaje gidanmu saida yazaneni sosai da tsintsiyar shara" qura mata idanuwa yayi yana kallon yanda bakinta ke motsawa da yanda idanuwanta suka firfito saboda tsoro, ji yayi kamar ma bai tab'a ganinta ba sai yau saboda yanda yanayin tsoron nata ya bada wani fasionable atattare da ita, yanda take game hannu tana tambayarsa yasa jikkar hannunta fad'uwa da sauri ya duqa zai d'auko mata itama alokacin taduqo sukayi karo da juna, "Yi hak'uri malan." tafad'a had'e da d'aukar jikkar ta rataya akafad'a, girgiza kai yayi kamar wani soko sannan yafara tafiya yana murmushi had'e dajin wani abu akanta, da gudu ta cimmasa tace, "malan baka fad'amun kome mahaifina yazoyi anan ba." "Kashi yace abaki." Shine amsar daya Bata atakaice yanaci gaba da tafiyarsa, tsaye tayi kamar andasata awurin kafin tasake rugawa ta cimmasa, "malan, malan kashi fa kace!, to ni menayi kuma.?" "Saboda bakyason karatu." "Amma ai d'azu shiyace ya amince tunda aure nakeso zai yimun!" Tsaye malan yayi zuciyarsa nabugawar da baisan dalilinsa ba kafin yajuyo yana kallonta had'e da cewa, "waza'a aura makine?" gyara jikkarta tayi had'e da ware hannuwanta tana fad'in, "Ban sani ba, da akwai wani Rabe dake sona amma baba yace beyi masa ba, don haka shizai zab'ani miji da kansa" ajiyar zuciya ya sauke had'e da cigaba da tafiya tana biye dashi agefensa yaci gaba da cewa "Kuma ke kin amince?" "Eh, ni nace ya zab'amun duk wanda take so" "Kuma duk wanda aka zab'a makin zaki yarda ki auresa?." "Eh mana zan yarda tunda ni nace na amince." "Ko waye shi?." "Eh, kowaye shi" "Koda ace nine? zaki yarda" "Eh, zanyarda man.." Bata ida fad'aba tayi saurin rufe baki tare da zaro idanuwanta tana kallonsa jin abunda yafad'a, juyowa yayi shima yana kallon cikin idanuwanta d'aya bayan d'aya sannan jinjina mata kai tare da sakar mata murmushi yace "ina sonki! Zaki aureni!" Yaqarasa maganar yana dariya tare da barin wajen batare daya jira jin amsar da zata bashi ba yana jin wani shauqi da kuma farinciki atattare dashi, Ita kuwa Rashida gaban tane yayi mugun fad'uwa tare da sakin jikkar dake sagale a kafad'arta tafad'i k'asa, kallonsa takeyi har ya qurewa ganinta kalmar Ina sonki d'aya fad'a nayi mata yawo a k'wak'walwa, tafi mintuna biyar awajen tsaye kafin tad'auki jikkarta tanufi hanyar gida jikinta kamar wacce aka zarewa lakka, A ranar yini tayi data motsa fuskarsa take tunanowa da kalamansa tayita murmushi, ganinta cikin wannan yanayin yasa umma ta sake tsorata da al-amarinta, don atunaninta tsabar farincikin amincewar da mahaifinta yayine akan zaiyi mata auren kesata wannan nishad'in, d'azu garin kallonta har k'walewa tayi ajikin bangon qofar shiga d'aki, Haka ab'angarensa daya rufe idanuwa babu abunda yake gani sai yanda bakinta ke motsawa da idanuwanta, ahankali yakejin sonta nashiga acikin zuciyarsa da kuma sauran sassan jikinsa, Rashida kyakkyawar yarinya ce irin black beauty d'innan, tanada tsayi sosai don takusa kaimasa a kafad'a, tanada manyan idanuwa da zarazaran gashin ido hancinta bayada wani tsayi sosai amma saboda ramin idanuwa da take dashi zaka d'auka dogon hanci ne da ita hakama bakinta d'an madaidaicine ciccif fuskarta, bai tab'a lura da hakan ba sai yau daya qura mata idanuwa, Daga shi har ita matsuwa sukayi weekend taqare saboda mararin son ganin juna sai dai ab'an garenta takan shiga damuwa idan tatuna da cewa tariga da taba mahaifinta damar zab'a mata mijin da zata aura, gashi ba zato ba tsammani malaminta ya dasa mata soyayyarsa azuciyarta, duk wani motsi da zatayi tsananin sonsa ke sake shiga ranta, kuma ayanda tasan halinsa tunda har tafurta da bakinta kuma ya tambayeta ta amince da duk zab'in da zaimata to bata isa yanzu taje masa da wani sauyin magana ba, Shikam malan idris safiya na wayewa ranar asabar ya isko mahaifinsa ya sanar dashi komai ba tare daya b'oye masa ba akan aminin nashi da suka had'u da kuma zancen 'yarsa d'aya gani yana so wacce ayanzu yake da nufin aurarwa, sosai mahaifinsa yaji dad'i kuma yayi murna ya tabbatar masa da cewa idan ALLAH yabashi lafiya nan da sati mai zuwa zaije suyi zancen ko yatura qannensa suyo masa maganar, anan yake sanar dashi cewa ai yasan halin aminin nasa yanada matuqar kirki amma akwaisa da zuciya da kuma kafiya, shiru malan idris yayi tuna yanda suka fara kwashewa dashi shekaran jiya wanda yatabbatar zuciyace tasa yayi hakan, nisawa yayi kafin yace "To baffa don ALLAH kayi masa magana dawuri saboda ko yaushe zai iya bada aurenta ga wani, gashi kuma kace yacika kafiya da yawa" dariya baffa yayi tare da bubbuga kafad'arsa yace "To Nuraddeen, ka kwantar da hankalinka in Sha ALLAH bazan bari haka tafaru ba, bari idan sunzo gobe d'in sai nafara b'ulguta masa maganar sai muji me zaice kaji ko?." haka sukaci gaba da tattaunawa akan matsalar ciwonsa har yake cemasa shi dai yaso ace cikin 'ya'yansa wani yayi karatun kiwon lafiya kodon taimakon gida da waje, gashi yanzu sai faman kashe kud'i akeyi akan matsalar ciwonsa kuma sunk'i fad'a masu gaskiyar abunda ke damunsa balle a tsammani waraka nan kusa ko kuma nesa. Ranar lahadi misalin karfe sha biyu na rana, baba da wasu abokanan kasuwancinsa su uku da kuma qanensa da shima duk tare ake akasuwa suka kama hanyar bebeji don gano malan idi, basu kaiba sai misalin k'arfe biyu na rana saboda yanayin injinin motar da sukaje da ita Bata cika kyauba sai an lallab'a, qannen malan idi su biyune suka tarbesu tare da shigowa dasu cikin gida inda yake zaune saboda hatta qugunsa yasamu matsala be iya tafiya. Sosai farincikin ganinsu ya bayyana a fuskarsa kamar yatashi sama don murna, haka suma saidai su nasu farincikin ya surku da tausayinsa ga yanda fuskokinsu suka nuna, saboda malan idi mutumne mai dad'in sha'ani da kuma hak'uri, kusan ma halin sane malan Idris ya gado, murmushi ya dinga yimasu yana fad'in "karku damu alhamdulillah Ina samun sauqi, muyiwa ALLAH godiya da yasa fuskokinmu suka sake had'uwa badon haka ba ai shikenan rabuwarmu kenan tun ranar." Abinci aka kawo masu yasa malan Idris daya shigo gaishesu ya zuzzuba masu abincin, bayan sunci sun sai gashi yasake shigowa da gorunan lemu da ruwa yakawo masu hadda mahaifin nasa da qannensa, har zai fita baffa ya kallesa had'e da cewa, "Dawo nan kazauna" yana nuna masa gefen da baba take zaune, gaban sane yafad'i tare da sadda kai qasa sannan ya qaraso ciki ya zauna amma acan d'an nesa dasu, gyaran murya baffa yayi sannan yace.... _Tofah baffa zai fasa kwai agaban kowa🀣 Bari in gudu kafin kaina yayi girma saboda kunyar da zan tayasa jiπŸ˜… don son jin abunda baffa zai fad'a yau to inji ruwan comment idan ko ba haka ba kuda new update sai upper weekπŸ˜’_ *_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU_*πŸ‘πŸ˜­[6/19, 9:17 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___11πŸ’Ž Gyaran murya baffa yayi yana kallonsu baba kafin yace, "Malan bashar nasan kai kasan wannan" yana nuna d'an nasa sannan yaci gaba da cewa "don haka Babu buqatar in sake gabatar maka dashi saidai ko in wud'anna 'yan uwan nawa, amma ku su alhaji surajo, malan hashimu, sa'idu, malan shu'aibu da malan balarabe ga d'anku nan Nuraddeen wato d'an wajena koda ALLAH zaisa wata rana a had'u zaku iya ganesa shima yagane ku, wud'annan su biyun da kuke gani kuma qannena ne uwa d'aya uba d'aya wato Usman da aliyu, inafatar ko bana raye ace abota da kuma mutuncin dake tsakanina daku bai yanke ba, inaso ya zamana cewa idan anhad'u da juna za'a iya gaisa har kudinga tunowa dani kuna yimani addu'a"+ "Ashsha malan idi! don ALLAH kadena fad'ar haka domin ita cuta ba mutuwa bace, mudai fatanmu d'aya shine ubangiji ALLAH yabaka lafiya kuma ALLAH yaraya manasu shi da sauran 'yan uwansa ya tashi kafad'unka acikin iyalinka." Haka suka dinga fad'a tare da yimasa addu'a, Shiru baffa yayi yana kallonsu d'aya bayan d'aya nan take yaji wasu hawaye sun cika masa idanuwa, tari yafarayi wanda hakan yabawa hawayen dake maqale a idanuwansa damar zubowa, sannu duk suka dinga jero masa cikin jin k'warin guiwa ya kaikaita idanuwansu yana goge hawayen had'e da amsa masu, Bayan tarin ya lafa masa ya maido kallonsa ga 'yan uwansa da kuma d'an nasa suma ya gabatar masu da aminan nasa inda har yak'ara masu da cewa shi awajensa abokan nasa sunfi qarfin yakirasu da abokanai ko aminai saidai yace sud'in 'yan uwan sane shaqiqai, don haka yana roqonsu dasu riqesu hannu biyu bisa kyautatawa da kuma girmamawa, gaba d'ayansu ji sukayi jikinsu yayi sanyi saboda yanayin yanda yake magana tamkar wanda ke barin wasiya, murmushi yayi ganin yanda fuskokinsu suka canxa had'e da cewa "kada kusaka kawunanku cikin damuwa akan maganganun dake fitowa abakina domin natabbata daga cikinsu akwai wud'anda zasu sanyaya zuciyoyinku kuma su sakaku cikin farinciki marar misaltuwa" juyowa yayi inda d'an nasa me zaune yace, "Nuraddeen tashi katafi, ALLAH yayi maka albarka" ajiyar zuciya malan Idris ya sauke had'e da mik'ewa tsaye yad'an sunkuyar dakai agabansu alamar girmamawa sannan yafice daga d'akin, Bayan yafita baffa ya kalli 'yan uwansa yace, "usman, Aliyu Ina son kunemawa d'anku Nuraddeen izinin neman auren Rashida 'yar gidan malan bashar a hannun iyayenta dake zaune agabanku idan har ba'a tsayar mata da miji ba kamar yanda d'annaku yabuqata cewa yana sonta" Wani irin annurine da farinciki ya bayyana a fuskokinsu gaba d'aya jin kalaman dake fito daga bakin aminin nasu in banda baba da kuma aliyu qanen baffa, shidai baba tsantsar farincikine da kuma mamakin jin cewa wai malan idris nason 'yarsa Rashida, shikuma Aliyu tsananin bak'inciki da takaicin hakanne da yaji yasa yakasa b'oyewa saboda 'yarsa muneera yaso ya had'a aurensu da shi saboda yanda take tsananin sonshi. Sosai baffa yalura da sauyawar fuskar da d'an uwansa tayi Amma sai ya basar saboda jin Usman na fad'in "Masha Allah, alhamdulillah, agaskiya haka yayi kyau kuma shizai k'ara dank'on zumunci a tsakaninmu, don baka iyayen rashida kunji buqatar d'anku idan har yarinyar nan ba'a tsaida mata da miji ba, to muna nema masa izinin yafara zuwa wajenta donsu daidaita" Gaba d'ayansu suka had'a baki wajen cewa, "to aimu da Nuraddeen da Kuma Rashida duk 'ya'yanmune, saboda haka indon ta tamu bamuqi jinin yau a d'aura masu aure ba, don haka mu tabakin malan bashar muke jira sai muyanke hukunci" STORY CONTINUES BELOW Murmushi baba yayi sannan yace "hak'ik'a nayi farinciki, farinciki kuma marar misaltuwa akan wannan al-amarin, narigaku azuciya ne sai kuma ALLAH yasa yaron ya rigani abaki, Amma ALLAH shine shedar azuciyata nayi niyar bawa Nuraddeen auren Rashida saboda yanda nayaba da halinsa da kuma nagartarsa, dad'in fad'awa da naji cewa shi d'an amininane kuma d'an wannan ahali masu d'inbin karamci da kyautatawa, saboda haka kamar yanda kukace ku iyayen duka biyunne to nima haka, gaba d'ayansu 'ya'yana ne don haka ga mahaifinta nan malan balarabe sai muji tabakinsa." Yaqarasa maganar yana nuna inda qanen nasa kezaune, murmushi malan balarabe yayi had'e da cewa, "to madallah tunda duk kunbar mani 'yar tawa nagode kuma ni balarabe Ina so ku sheda cewa ba izini kad'ai ba hatta auren 'yata Rashida nabawa d'ana Nuraddeen duniya da lahira, don haka duk sadda kuka so asa rana da kuma yanka maku sadaki sai ku nememu in sha ALLAH ko yaushene mu a shirye muke" "Alhamdulillah" kowa yafad'a, baffa yace "Tunda hakane mezai hana ayanka sadakin kuma asa ranar yanzu sai ahuta ko me kukace?" Cikin rawar murya anensa Aliyu yace, "A'a yaya abari har sai sunje sun tambayi yarinyar idan ta amince ina ga hakan zaifi." "Indai ta b'angaren yarinyar mune babu wata matsala koda had'asu mukayi munyarda da tarbiyarta zata amince ballema shi yaron yaganta yace yana so, don haka ayi abunda yakamata babu damuwa in Sha ALLAH" malan balarabe yafad'a cike da nuna yarda akan 'yar tasu,ko kad'an ran Aliyu bi yimasa dad'i ba Amma babu yanda zaiyi dole ya haqura tunda duk 'yan uwan nasa sun nuna amincewarsu, kafin kace me aka yanka sadaki dubu hamsin , nan take abokanan iyayen nasu su hud'u suka had'a kud'in suka ba qannen mahaifin Nuraddeen a matsayin tasu gudun mawar ga d'an nasu, Hakan ba k'aramin sake farantawa baffa zuciya yayi ba tare da yiwa ALLAH godiya daya basa nagartaccin abokanai irinsu, Abunda ALLAH yaso kuma yariga ya had'a ko ana so ko ba'a so to sai ya tabbata, a ranar su baba basu baro garinba har saida aka dindince ranar d'aurin auren nan da sati biyu masu zuwa tare da sadakin Rashida a hannunsu zuciyoyinsu cike da farinciki, nisawa mahaifin Rashida yayi yace "ALLAH mai iko kuma mai yin yanda yaso, mu da mukaje gano marar lafiya sai gashi mun dawo da sadakin 'yarmu a hannu, tabbas komai nada sanadi arayuwa, ubangiji ALLAH yasa hakan shi yafi zama alkhairi kuma ya had'e hankulansu waje d'aya" kowanensu ya amsa da "Amin" suna masu jinjina al-amarin ubangiji. Aliyu kuwa suna tafiy bai zame ko Ina ba sai d'akin mahaifiyar Nuraddeen wato matar yayan nasa yay hawwa kmar yanda suke kiranta yana cika yana batsewa, nan ta taso tana tambayarsa ko lafiya ai kamar jira yakeyi ya zayyane mata qarya da gaskiya, ashar ta lailayo ta dire tna fad'in "ai wlh ba'a isa ba, yaushe har shi nuran yayi girman da ya isa yace ga wadda yake so da har za'aje ayo masa qulle qulle a aura masa wata can bare, to wlh bazan tab'a lamuntar wannan abun gori acikin dangi ba, haka kurum ajawo mani abun kunya da fad'a acikin gari, kowa yasan awannan garin namu auren zumunci akeyi, bamuda bare kuma ba'a tab'a kawo mana ita acikin gida ba, shikenan sai yanzu ace akan d'ana za'a fara?to wlh haka bazata sab'uba wai bindiga aruwa" wani farincikine ya rufe Aliyu yaci gaba da ingizata yana zugata haddasu cewa "Nima haka nagani yaya hawwa, Ina laifin ace ko muneera ce an had'asa da ita tunda tana sonsa amma wai antashi an had'asa da wacce batasan kimarmu da darajarmu ba, ga yaran cikin garin basuda mutunci da girmama na gabansu" "Kai rufamun baki, muneera ko shashasha, tun yaushe nake cemata tadinga oqarin jawo hankalinsa amma takasa, shegiya mai gwalmad'ad'd'in qafafuwa ai koma meye laifin tane" "Amma yaya hawwa kemafa kinsan yaronnan da baqin rai yake, har yaushe tag fuska balle taje tayi masa karairayar da zata jawo hankalinsa, yanzu dai ya kamata kisan abunyi kafin yarinyar nan tazo tarabamu da d'anmu ta tsigemu gaba d'aya" "Kai Aliyu tofar da mugun yawun bakinan naka, wannan baqar fata har Ina, Bari naje wajen malan dole a ajiye wannan maganar" fiiiii...tanufi shigifar da baffa ke kwance ta iskosa yana jan carbi, masifa tafara zuba masa yana kallonta har ta gama sannan ya ajiye carbin agefe yace "yanzu ke hawwa awannan yanayin da nake ciki har kinada k'warin guiwar zuwa kiyi tsaye agabana kina wud'annan maganganun, to bari infad'a maki ko kina so ko bakya so sai anyi wannan auren tunda yana son yarinyar" STORY CONTINUES BELOW "Ni kuma bana son yarinyar, don haka bazai aureta ba" "Saboda meye?" "Saboda ita d'in barece" "A'ina aka fad'i hakan, qur'ani yafad'a ne ko a'a?" "A al'adar garinmu dai ce ba'a tab'a yin hakan ba kuma baza'a fara akan d'ana ba" "Kaji shirmen banza, al'adar tafi alqur'anin ne? To Bari kiji wannan aure kamar anyi angama ne da yardar ALLAH" "Amma malan inkayi mani haka bakayi mani adalci ba sabo..." Bata qarasa rufe baki ba yace "Eh jeki naji d'in ni yanzu barci nakeji bana son wannan hayaniyar!" Duk inda ran hawwa yake inyayi dubu yab'aci, tafice buuuu.kamar zata tashi sama tana maseefa, karo tayi da Usman akan hanyar tsakar gidan da yake family ne duk anan suke zune tafara yimasa qorafi, murmushi yayi sannan yace, "ikon ALLAH, to aike yaya hawwa banda addu'a babu abunda yakamata kiyi tunda shi yaganta kuma yace yana sonta, don ALLAH don annabi ki kwantar da hankalinki, mai k'aya ya daure kuma sai ace mai cira na kuka!?" Aifa nan shima tayi masa tatas har tana k'arawa da cewa ai duk munafuccin da akayi dashi akayisa, shidai murmushi kawai yayi yawuce abunsa batare daya sake tankata ba, Aliyu ne ya iso wajen yana kallon irin hararar data raka d'an uwansa da ita yace, "Ahaf! Ai infad'a maki yaya hawwa duk munafuccin agindinsa yake, shine nan ya qulla komai." Tsaki taja had'e da barin wajen tana fad'in, "sakarci, to kai meya hanaka kwancewa daya qulla, ai wlh duk sai nayi maganinku ga baki d'aya." 😨 _TIRQASHI! RASHIDA KINA CIKIN MATSALA, GASHI KEBA ILIMIN ZAMANI BALLE KI KWACI KANKIπŸ€”πŸƒπŸ»‍♀️πŸƒπŸ»‍♀️πŸƒπŸ»‍♀️πŸƒπŸ»‍♀️_ *_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ˜­_* [6/21, 10:25 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___12πŸ’Ž Kallo Aliyu yabi yaya hawwa dashi kafin yace "Kai wannan mata anyi fitinanniyar halitta anan, duk girmanka baza katab'a gwaninta awajenta ba, jarababbiya da ganinta kasan ba qaramin haquri yaya keyi da ita ba." Kasa zaune da tsaye yaya hawwa tayi saboda tunanin hanyar da zatabi ta hana auren, in tayi nan tayi can kamar mai jiran sauraren wani sak'on, cije baki tayi aranta tana mai ayyana kalar uqubobin data tanadawa yarinyar matuqar bata samu nasarar ruguje auren ba, Baba kuwa yana isa gida bakinsa ko rufuwa bayayi saboda tsananin farinciki yafara k'walawa Rashida kira alokacin ita kuma tana bayi tana wanka, "A'a sannu da zuwa malan,lafiya naji kana k'wallawa 'yar taka kira tundaga zaure" tak'are zancen had'e da jawo tabarmar dake gefen d'aki ta shimfid'a masa sannan takoma d'aki ta d'auko ruwa masu sanyi takawo masa, fuskarsa cike da annuri ya nemi waje ya zauna sannan yace, "Yawwa maman Rashida lafiya klw muka dawo, Ina ita Rashidar take, ko tayi islamiya ne?" "A'a yanzunnan tashiga wanka, inaji yauma tayi latti ALLAH yakareta daga dukan malamai." "Amin ya ALLAH" Yafad'a had'e da d'aukar ruwan data ajiye masa agabansa yasha, "Malan shin ko abun sirrine tsakanin uba da 'yarsa naji kayi shiru, kai da naga kashigo da azamarka kamar Wanda akaba saqo yakawo mani." Murmushi yayi mata sannan yace STORY CONTINUES BELOW "To kusan dai kamar hakanne amma sak'on Kuma bake aka bawa ba 'yarmu aka ba." "Tooo...! Kace dai harkar tason kaice, to bari nakama bakina, inbar uba da 'yarsa susha sha'aninsu" "A'a ranki shidad'e ai abun bai kai can ba, ungo wannan riqe inyi maki bayani" ya ciro kud'i a aljihunsa ya mik'a mata, ansa tayi tana bin kud'in cike da mamaki kafin tace, "malan a ina kasamo wud'annan? Ina wajen ganin marar lafiya kuka tafi ko?" "Eh a can mukaje?" "To wud'annan kud'infa a ina aka samosu?" "Kai maman Rashida wud'annan tambayoyin sunyi yawa, sai kace wanda yasato" "To ai dole na tambaya saboda abun da mamaki!." "kwantar da hankalinki to wannan sadakin Rashida ne kuma nan da sati biyu za'a d'aura auren in sha ALLAH..." bai qarasa zancen ba sukaji qarar fad'uwar bokiti daga toilet Rashida ta saki jin abunda kefitowa daga bakin mahaifin nata, atare umma da baba sukace, "Ke lafiya?" K'ok'arin maida hawayen da suka zubo mata tayi tare da ciro zanenta dake rataye ajikin k'usa ta d'aura sannan ta yafo towel d'in da tashiga dashi yarufe mata daga samn kai zuwa qirji tafito kanta na sunkuye qasa tawuce d'akinsu, Kallo suka bita dashi kafin baba yace "ALLAH ya kyauta, ni bari inje muyi magana da balarabe yana waje yana jirana.!" "Shine bakace ya shigoba zaka barshi zaune awaje sekace wani baqo" "Bari dai natafi kije ki ajiye kud'innan idan nadawo ma k'arasa maganar." "To ALLAH ya kiyaye kuma yasa adawo lafiya, ka gaidashi" Yana fita itama Rashida tafito saye da hijabinta na islamiya tace "umma natafi" batare da tabari sun had'a idanuwa da ita ba don kada ta fahimci halin da take ciki, "To adawo lafiya" itama tabata amsa atak'aice, sannan tamik'e tawuce cikin d'aki. Rashida kam tana cikin yanayin da ita kanta batasan taya zata fassarashi ba, karatu akeyi amma tayi zaune tahad'a tagumi tana tunani, gashi dai auren da takeso za'a yimata amma damuwarta d'aya shine yanda alokaci guda soyayyar da malaminta ya dasa azuciyarta cikin kwana biyu tayi tasiri aranta har tana tunanin yanda zata iya auren wani idan bashi ba, ji tayi tafashe da kukan da batasan lokacin da yazo mata ba saidai taji malami na fad'in "Ke Rashida me yake damunki ne?" Firgigit tadawo cikin hayyacinta tana zarar idanuwa had'e dasa hannuwa tana goge hawayen da suka zubo mata, "Mik'e tsaye." Taji ya sake fad'a tare da nufo inda take riqe da bulala, mik'ewa tayi da sauri tana runtse idanuwanta don duk duniya babu abunda ta tsana kamar a tab'a mata jiki da sunan duka, "Me kike tunani!" "Babu malan" tafad'a atsorace har lokacin idanuwanta na arufe, har zai dukanta sai kuma ya qyaleta had'e da cewa tafitar masa daga aji, maimakon tabashi hak'uri kawai sai taja jikkarta tafice daga dama tun d'azu hankalinta baya wajen balle ta fahimci karatun da yakeyi, acan bayan wasu azuzuwa taje ta zauna, ta d'ora daga inda ta tsaya ga tunanin da yakeyi, Bata bar wajen ba har sai da taga antashi sannan tabi sauran d'alibai suka wuce gida, Tana isa gida ta isko umma na waya da 'yan uwanta dake borno akan zancen aurenta tana fad'a masu ai har ankawo mata sadaki an kuma sa ranar aurenta nan da sati biyu hakan yasake dagula mata lissafi tawuce d'akinta da sauri, kasancewar dama tana fashin sallah yasa batabi takan kiraye kirayen sallar magrib da akeyi ba tayi kwancenta, ita kuma umma kota kanta batabi ba tad'auki butarta tayo arwala sannan tawuce d'aki ta tayar da sallah. Can misalin qarfe tara nadare bayan baba yadawo sun gama tattaunawa da umma sannan yayi mata bayanin cewa ai bayan sun gama dubiyar da sun kajene aminin nasa ya bijiro da maganar nemawa d'ansa auren Rashida ashe cikin ikon ALLAH ganin da yake yimata a makaranta yaji yana sonta tun kafin inyi masa magana sae gashi yafad'awa mahaifin nasa cewa ya nema masa aurenta." nan dai ya fayyace mata yanda komai yafaru, ajiyar zuciya tayi had'e da cewa "Alhamdulillah, aini sai yanzu nasamu natsuwa, amma tunda kabarni nake wasu wasin wannan al-amarin tare da taraddi jin kace nan da sati biyu za'ayi auren, amma yanzu Alhamdulillah, ALLAH yatabbatar mana da alkhairi, naji dad'i kuma nayi farinciki sosai ai malan idi mutumen kirkine da kowa zaiyi sha'awar had'a zuri'a dashi, ubangiji ALLAH ya bashi lafiya kuma yasa ayi munada rayuwa." STORY CONTINUES BELOW "Amin ya rabbi, ai don ma bakiga yaron ba, ALLAH dai ya tabbatar da alkhairi, tashi kije ki kirawomun ita" cike da farinciki umma tanufi d'akinta ta tsaya abakin k'ofa tana fad'in "Rashida, Rashida.." jin bata amsa ba yasa taqarasa cikin d'akin, kwance ta hangota saman katifarta, kallo d'aya tayi mata tasan da cewa ba bacci takeyi ba kawai idanuwan natane kad'ai a rufe, matsawa jikin katifar tayi had'e da cewa, "Ke Rashida lafiya kikekuwa?" Firgigit tabud'e idanuwanta had'e da saukar dasu akan nata, "lafiya kike?" Tasake maimaita mata akaro na biyu, qoqarin miqewa zaune tayi had'e da sauko da k'afafuwanta k'asan katifar sannan tace, "Umma kainane yake yimun ciwo." "Ashsha shiyasa yau najiki shiru tunda kika dawo makaranta baki fito ba balle kid'auko abincinki kici, daure kitashi mahaifinki nakira inyaso daga can sai kici abinci kisha magani kinji ko" Kai tad'aga mata ita kuma tajuya tabar d'akin tana fad'in "ALLAH yasawaqe ciwon kai kam ai babu dad'i" Ko minti biyu umma batayi da zaunawa ba Rashida itama tashigo cikin d'akin tajawo hular hijab d'inta ta lullub'e mata rabin fuskarta tanemi gefen qofar d'akin daga ciki ta zauna, "Baba ina wuni andawo lafiya?" Tafad'a tana gyara hular hijabin zuwa kanta." "Lafiya klw Rashida, lafiya kike kuwa?" Kafin tace wani abun umma tace "Au kagafa na manta infad'a maka ba tajin dad'i, na iskota kwance shine dana tambayeta take fad'amun kanta ke ciwo don tunda suka dawo islamiya banga tafito waje ba balle ko abinci tasamu ta d'auka taci." "Subhanallahi, injin to da sauqi" yafad'a yana kallon Rashida "Eh da sauqi baba," tafad'a tana goge zufa a goshinta, wani d'an guntun tsaki yaja had'e da cewa "Matsalar ku kenan mata baku fiye kula ba wani lokacin, shiyasa ake ganin sakacinku yayi yawa ace mutum nada d'a yaga yayi awa kusan biyu a d'aki bai fitoba kuma bazai je yaduba halin da yake ciki ba sai mai faruwa tafaru kaji ana fad'in ai kuwa tun d'azu najishi ko najita shiru ad'aki ashe kaza da kaza yafaru bamu sani ba, to meye amfanin hakan? Kin jita shiru amma kin kasa dubota kiga ko lafiya take sai yanzu da nace ki kirawota, ALLAH ya kyauta" "Ayi hak'uri malan in sha ALLAH za'a dinga kula" Hannunsa yamik'a gefensa a qarqashin pillow dake kan gadon ya d'auko kud'in da yakarb'a a hannun umma ya mik'awa Rashida had'e da cewa, "Ungo wannan ki k'irgamun su nawa ne?" Mik'o hannunta tayi yana makarkata ta karb'a sannan tafara k'irgawa d'aya bayan d'an shi kuma yana kallonta, saida tagama sannan ahankali ta d'ago kanta tace, "Dubu ce guda hamsin" murmushi yayi had'e da cewa, "ban fahimta ba" "Ina nufin naira dubu ce sau hamsin " girgiza kai yayi cike da takaicin dubu hamsin ma 'yarsa bazata iya fad'a daidai ba, wannan wane irin rayuwace, kallonta yayi yanaji kamar ya maketa kafin yace, "Rashida kenan, ai bahaka ake fad'aba, naira dubu hamsin zakice a hausance kinji ko?." 'Daga masa kai tayi tare da sake mik'a masa kud'in, "A'a kiriqesu a hannunki, nakine mallakinki duniya da lahira" d'ago kai tayi tana kallonsa cike da alamar tambaya atattare da ita, "Eh, kud'in kine na sadaki da aka bayar kuma a musulunce bai halatta kowa yayi amfani dasu ba idan ba keba koda kuwa mune saboda hak'k'in k'ine shiyasa na hannunta makisu a hannunki duk abunda kike so kiyi dasu, mudai munfita hak'k'inki koba haka ba?" Yaqare maganar yana kallon umma, jinjina masa kai ita Kuma tayi alamar tabbatar da zancensa. Muryarta na rawa tace "Babu abunda zanyi dasu baba don ALLAH ku karb'a umma" "A'a kirik'e hannunki abunda babanki yafad'a shine daidai kinji ko?" STORY CONTINUES BELOW "Umma nifa babu abunda zanyi dasu, baba.." dakatar da ita yayi had'e da cewa, zaki iya ba ummanki ta ajiye maki, tashi kitafi ALLAH yayi maki albarka" Mik'awa umma kud'in tayi sannan tamik'e zata fita, har ta aza k'afarta abakin k'ofar mahaifin nata yace, "Rashida bazaki tambayi ko wanene na zab'a maki ba?" "A'a baba, babu buqatar hakan domin nasan bazaka tab'a yimun zab'in daba daidai ba." Tana gama fad'ar haka tafice idanuwanta na hawaye, tabbas tasan takamu da soyayyar malaminta amma bazata iya yiwa mahaifinta musu ko kuma gardama akan zab'in da yayi mata ba, kawai zatayi k'ok'ari ta yakisheshi aranta kafin lokacin auren. Shikuwagogan naka matsuwa yayi safiya tawaye yaje makarantar saboda yaga sahibarsa, wacce ke Shirin zamowa matarsa kuma uwar 'ya'yansa, cikin daren yaje yasiyo mata waya k'irar tecno L7 saboda ya dinga jin muryarta duk da dai gaba d'aya wannan satin zai ganta har yagaji. Tunda sassafe yatashi yayi wanka sannan yaje wajen mahaifiyarsa ya gaisheta tare da cemata zai wuce, ciki ciki ta amsa mata saboda fushin da takeyi dashi akan zaije ya auro masu bare, cikin sanyin murya yace, "Inna har yanzu fushin kikeyi dani?" "Ai dole inyi fushi da kai nura zaka jawo mani abun kunya." "Kiyi hak'uri inna da kin fad'amun tun farko bakyason in auro maki bare agidan nan da bazanyi ba, amma yanzu kinga su baffa sunyi magana bai kamata ace anwatsa masu qasa a idanuwan duniya ba." "Aiho shiyasa ni kuma aka watsamun qasar, shikenan tashi katafi." "Taya zantafi inna fuskarki ahaka, kiyi hak'uri don Allah kiyafemun, natabbata idan kikaga yarinyar kema zaki sota kamar yanda nake sonta" Saida ta sheqe da wata dariyar shaqiyanci kafin tace, "ALLAH natuba kayafemun ni hawwa, ai har abada bazan sota ba, kaidai tashi katafi ALLAH yatsare hanya." Jikinsa ya matuqar mutuwa dajin kalamanta amma babu yanda ya iya saboda ALLAH shine shedar yanda take jin soyayyar yarinyar bazai iya rabuwa da ita ba, fatanshi dai ALLAH yasawa inna sonta kamar yanda yake sonta, "Me kake tunani haka!" tafad'a a d'an tsawace da yasashi saurin mik'ewa tsaye yana fad'in "Natafi." "Adawo lafiya," tafad'a tare da mik'ewa ta rakosa har bakin qofa. Adaidai bakin k'ofar fita gidan bayan yaje wajen mahaifinsa shima sun gaisa yafad'a masa zai wuce ya had'u da qannen mahaifin nasa baffa Ali da baffa Usman kamar yanda suke kiransu, duqawa yayi har k'asa ya gaishesu, baffa Usman ne yafara amsa masa kafin baffa Ali dake gugar bakinsa da ashuwaki ya tofar da yawu agefe yace, "A'a malan nura zaka tafi" "Eh baffa Ali nama yi latti sosai yau gashi inada daraai qarfe takwas naga har bakwai da rabi tayi" "Eh gaskiya kama tashi katafi, ALLAH yatsare hanya." "Amin baffa Ali nagode." Har yafara tafiya yakira sunansa ya juyo zai dawo inda suke yace "A'a basai kadawo ba, cewa nayi to adai kula kasan halin mata kar ake kabiyewa shashancinsu suhanaka yin abunda ya kaika kaji ko?" Shiru yayi yana nazarin kalamansa kafin yace, "to baffa Ali in Sha ALLAH." Sannan yawuce cikin sauri. Girgiza kai baffa Usman yayi had'e da kallonsa kafin yace "Yanzu kai Ali meye amfanin abunda kayi, karkamanta yaronnan d'anka ne bai kamata kana yimasa abubuwan da basu dace ba gudun kada yadena ganin girmanka da kimarka, kaga daga lokacin fa girma yafad'i." "A'a meye rashin dacewa anan, gaskiyafa nafad'a masa, zamu saki yaron namune sagaga alalata mana shi acan" "Ikon ALLAH, yanzu Ali aganinka har abun yakai ga mata ke lalata maza?" STORY CONTINUES BELOW "Ahaf nawa akayi, ba shiyasa qara mutum ya nemawa d'ansa mata acikin dangi ya huta ba, Amma meye amfanin kwashe kwashe awaje." "Oho!.. yanzu nagane inda zancenka yayi, wlh kaji tsoron ALLAH kabar yaronnan yazauna lafiya da mahaifiyarsa, meye amfanin sonkai Ali?, Tunda yaron nan yakawo wacce yakeso don me da baza'a haquraba abarsa?" "Mtssss..." Baffa Ali yaja tsaki tare da barin wajen yana suruttansa. Malan Idris kuwa duk da yana cikin damuwar maganganunda baffa Ali yayi masa hakan bai hanasa fad'ad'a fara'ar saba alokacin daya iso makarantar, Kai tsaye ajinsu Rashida yanufa saboda yanda yake mararin ganinta, duk da itama tana son ganin nasa hakan bai hanata b'uya a qarqashin kujeraba alokacin data hangosa saboda yanda take son samawa kanta mafita tahanyar yakicesa aranta, dube dube yafarayi lokacin daya iso qofar ajin batare daya damu da malamin dake ciki yana yimasu mathematics ba yayinda itako banda fad'uwa babu abunda gabanta keyi,.... *_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ˜­_* [6/23, 11:14 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___13πŸ’Ž Jin kamar motsi abakin k'ofar ajin yasa malamin dake cikin juyowa, "A'a malan Idris barka da safiya" yafad'a tare da qarasowa wajen ya mik'a masa hannu suka gaisa, "Yawwa malan sale an shigo?" "Eh wlh, wani abu kake nema ne?" "Eh kusan haka dai Amma bari naje zuwa anjima na dawo saboda inada aji yanzu." "Ok to, Masha Allah" suka sake gaisawa sannan yawuce, yana wucewa tasaki wata irin ajiyar zuciya tare da fitowa a qarqashin kujerar data b'uya tana watsawa nakusa da sit d'insu wani mugun kallo saboda yanda taga sun maido hankalinsu gaba d'aya akanta, da sauri suka d'auke idanuwansu daga kallon da sukeyi mata gudun karta tata masu rashin mutunci, wani juya idanuwanta tayi had'e da aza kanta saman bencin dake gabanta tayi kwancenta, malan Idris nafita yanufi ajin da yake da period ransa duk ajagule, yaso ace yana shigowa yayi tozali da fuskarta saboda yanda yayi matuqar kewarta sai gashi hakan yacutara, haka nan ya daure yana koyarda d'aliban nasa sama sama amma gaba d'ayan tunaninsa da natsuwarta na wajen d'alibar tasa akan dalilin daya hanata zuwa makaranta yau duk da dai wani gefe na zuciyarsa na tabbatar masa da cewa tana cikin makarantar kawai biyi nasarar ganinta bane, adaddafe yasamu period d'insa ta k'are yafice daga ajin, wata d'aliba yakira yace taje ajinsu Rashida tace yana kiranta duk dako agaban idonsa wani malamin ya sake shiga cikin ajin nasu bayan nafarkon yafita. Daidai bakin qofar yarinyar ta tsaya tare da cewa "escuse sir, malan idris yace yana kiran Rashida bashar." ai Bata rufe baki ba rashida tasake shigewa qarqashin kujerar, dube dube malamin yafara yana kiran sunanta amma taqi amsawa, sukuwa ajin gaba d'aya tsoronta sukeyi saboda sanin halinta shiyasa babu wanda yayi yunqurin tonata gudun kada ta taresaidan antashi tabashi kashi don haka takeyiwa duk Wanda ya takaleta acikin aji. Juyowa malamin yayi had'e da cemata, "kije kifad'a masa bata zo ba." Yana nan a inda take zaune yarinyar tadawo tafad'a masa cewa, "malan ance bata zoba" yace "Ok wuce aji Kuma karki sake ink'ara ganinki waje kafin afito breakfast kinaji na ko." "Eh malan" tafad'a tare da rugawa tashige ajinsu, STORY CONTINUES BELOW Tunanin zuwa gidansu yayi ya dubota, sai kuma yaga kamar hakan ba daidai bane tunda bai tabbatar da batazo ba d'in, don shi har yanzu jikinsa nafad'a masa tana cikin makarantar saidai in akwai wani abu dake faruwa, hanyar clinic d'insu ya nufa ko tana can Amma ga mamakinsa bai iskota ba hakan yasa yawuce dining hall d'insu da kitchen duk bata can, wasa wasa malan idris ya zagaye duk wasu building na makarantar amma baiga Rashida ba, hankalinsa ya matuqar tashi da hakan, don bai tab'a ganin tayi fashin zuwa makaranta ba duk da rashin son karatunta saboda yanda baba keson tayi karatun shiyasa baya d'aukar mata hakan, office d'insa yakoma ya zauna tare da aza kansa saman jikin kujerar yana jin rayuwarsa duk ba dad'i, tun lokacin bai sake leqawo wajen harabar makarantar ba sai da yaji antashi breakfast, miqewa yayi da sauri yakoma jikin tagar office d'in nasa yana kallon qofar ajinsu yanda d'aliban kefitowa d'aya bayan d'aya Amma har suka gama fitowo ko mai kama da ita bai gani tafito ba balle itad'in, cike da takaici yakaiwa jikin bangon naushi had'e da juya zai bar wajen, kamar ance ya sake juyowa ta tagar ya hango ta azo qafarta sannan yaga ta leqo da kanta tana kalle kalle kamar mai neman wani abun, ganin yayi tana yiwa meenah qawarta magana ga kunne had'e nuno office d'insa wanda yasa aransa yaji dad'i atunninsa maganarsa takeyi, abunda bai sani ba Rashida tasa aduba matane idan yana cikin office don tasamu tafito ta sayi abunda zata saya kafin ya rutsar mata, yana kallo tafito tana d'an waige waige har ta isa inda zatayi sayayyar tasaya da sauri kuma tajuya tabar wajen, a maimakon takoma cikin aji sai yaga tanufi bayan class d'in da sauri meenah na biye da ita. Murmushi yayi had'e da sauke wata irin ajiyar zuciya sannan yakoma bisan kujerarsa ya zauna yana dariya saboda yagano dalilin da yasa tab'uya bai gane taba, dariya yasakeyi had'e da cewa, "kunyata Rashida keji kenan!?" Jikkar da yazo da ita yajawo yaciro kwalin wayar daya siyo mata yana kallo sai kace shine ita, a hankali yafurta da taimakon wannan wayar zan tabbatar matar maki da irin soyayyar da nakeyi maki, zanyi iya qoqarina wajen yakice maki wannan matsananciyar kunyar dake nema tazama shamakin da zaya zamo silar takurawa rayuwar aurenmu, maida kwalin wayar yayi cikin jikka ya rufe sannan yamik'e yafito daga office d'in, Saida yad'an jawosa sannan yamik'e ta d'ayar hanyar da zata sadashi da bayan ajinsu Rashida, zaune ya iskota saman wani dutse sunacin dankali da awara sai zob'o da ruwan sanyi dake ajiye gefensu ita da meenah qawarta dake fad'in, "Waike Rashida lafiya malan Idris yazo nemanki d'azu kika b'uya kuma ya sake aikawa akiraki kikaqi zuwa? Naga dai kuna shiri dashi balle ace wani abun, kodai laifi kika yimasa." Saida ta d'auki ledar ruwan tafasa tasha sannan tace, "wlh meenah babu wani abun dana yimasa kawai Ina cikin damuwane kuma kinsan halinsa ko kad'an baya son ganin d'alibinsa cikin damuwa, bansan irin amsar da zan bashi bane idan ya tambayeni." "To amma ai wannan shiya Aiko kiranki ma'ana shike nemanki, bakya tunin ko akwai dalilin da yasa yake nemanki?." Tana rufe baki kamar ance ta d'ago kanta tahangosa tsaye ajikin bangon ajin ya nad'e hanneyensa akan qirjinsa yana kallonsu, k'ok'arin yin magana tayi ad'an tsorace yabud'e mata idanuwa had'e dasa yatsansa akan bakinsa alamun tayi shiru, ita kuwa Rashida dama kanta naduk'e tana cin abincinta don haka bata masan abunda ke faruwa ba, alama ya sakeyiwa meenah da hannu ta tashi ta tafi, cikin tarin qarya data k'irk'iro tace "Emm...Rashida Bari naje naqaro mana ruwa qwaya biyu don wud'annan bazasu ishemu ba" takarb'i sauran nahannunta data fasa tasha tabar wajen, tana wucewa yayi gyaran murya had'e da dawowa tagabanta ya tsaye, a tsorace ta d'ago kai jin murya da qafafuwan data gani agabanta wanda bako shakka ta tabbatar namijine, suna had'a ido dashi tayi saurin mik'ewa tsaye tare da duqar da kanta tana qoqarin rab'awa ta gefenshi tawuce, hannunsa ya d'ora ajikin bangon ya tare ta inda zata wucewa had'e da cewa. "Ina kuma zaki jene?" "Aji zan koma." Tafad'a har lokacin kanta na sunkuye a qasa, gyara tsayuwarsa yayi sannan yaci gaba da cewa, "to ki zauna ki qarasa cin abincinki mana." STORY CONTINUES BELOW "Naqoshi." "Saboda nazo?" "A'a" "To meyasa?, Bakya son ganina anan ne?." "A'a" tasake bashi amsa atak'aice, "Meyasa naje nemanki kika b'uya kuma na aika akiraki kikak'i zuwa?." Shiru tayi saboda bata san ta Ina zata fara bashi amsa ba, har zai sake jefo mata tambayar yaji anbuga qararrawar komawa aji hakan yasa yace, "ki tabbatar kin jirani idan aka tashi ina son magana dake kinji ko?," yafad'a yana kallonta, kad'a masa kai tayi alamar eh sannan ya koma tahanyar daya biyo ya wuce, ahankali tajuyo tana kallonsa har ya b'ace kafin takoma saman dutsen data tashi ta zauna, hannuwanta tasa ta dafe kanta dasu wasu zaffan hawaye na zubo mata, tambayar kanta tashigayi akan meyasa malan idris ya shigo rayuwarta a daidai wannan lokacin, meyasa yafurta mata kalmar da zata saurin narkar mata da zuciya alokacin da batayi zato ko tsammani ba?, Meyasa tabari zuciyarta tafara sonsa bayan tasan batada iko akan zab'awa kanta abokin zaman da zatayi rayuwa dashi alokin?, Wani irin kuka ta fashe dashi tana mai jin rad'ad'i da kuma zugi acikin zuciyarta, Tafi mintuna biyar zaune ahaka tana kuka har saida tayi mai isarta sannan ta tashi tawanke fuskarta da sauran ruwan dake wajen ajiye takoma cikin aji. Ana tashi tayi saurin d'aukar jikkarta tagudu don batasan abunda yake son fad'a mata ba, Bata so yasake jifarta da wasu kalamai da zasu tunzura zuciyarta har sukaita ga bijirewa zab'in da mahaifinta yayi mata, Amma sai dai kash! cikin rashin sa'a tasamu yana nan tsaye abakin k'ofar ajinsu yana jiranta, k'ok'arin shigewa cikin 'yan uwanta d'alibai tayi tagudu yayi saurin riqo jikkarta dake sagale a kafad'arta, tsaye tayi cak batare data juyoba yace, "Ina kuma zaki je?" Juyowa tayi saboda d'aliban dake wucewa kada suyi zargin wani abun ta jaye jikkarta ahankali daya rik'e sannan tace, "Gida zanje." Yanda yaga wasu d'alibban sunyi tsaye suna kallonsu yasa ya shafa kansa yana fad'in muje inrakaki dama tuni ya d rufikke office d'insa ya tsaya nan zaman jiranta don yasan zata iya guduwa, babu yanda ta iya dole tabisa suka nufi gate d'in zuciyarta na harbawa da sauri da sauri, meenah dake can gefe tana jiranta na ganin haka tawuce abinta zuciyarta cike da tambayoyi akan meye tsakanin qawar tata Rashida da kuma malan Idris. Tafiya yakeyi ahankli tamkar wanda baya son su isa gidan yana tambayarta meye dalilin da yasa gaba d'aya yau ta sauya masa ba kamar yanda suka saba ba amma takasa cemasa komai, adaidai bakin wata bushiya dake kan hanyar ya tsaya tare da cewa, "Rashida meyasa inata yimaki magana kika yimun shiru? shin ko bakya sona ne shiyasa kika zab'i wannan hukunci a matsayin amsar da zaki bani don tabbatar mani da cewa bakya sona d'in." Yaqarasa maganar cike da damuwa a fuskarsa, da sauri ta d'ago kanta tana girgiza masa idanuwanta cike da k'walla kafin tace, "Ko kad'an malam ba haka bane, asalima azuciyata babu wani namiji da nake so kuma nake burin qare rayuwata atare dashi kamarsa, Amma kash kazomun a qurarren lokaci, kazo alokacin da banida ikon zab'awa zuciyata abunda take so face wanda aka zab'o mata, tabbas ina sonka amma nasan wahalace kurum zansha don bazamu tab'a kasan cewa a inuwa d'aya ba" taqarasa maganar tana share hawayen da suka zubo mata a fuska, cike da mamaki yake sauraren kalamanta kafin yace "Rashida ban fahimceki ba, kamarya bazamu lasance a inuwa d'aya dani dake ba bacin kince kina sona kuma kinsan nima Ina sonki, to meye kuma zai dakatar damu daga cimma burukanmu." "Nauyin bakin da kayi wajen sanar dani soyayyarka har sai dana sallamawa mahaifina akan duk zab'in daya yimun, wannan shine dalilina domin jiya mahifina yazab'o mun wanda zai aura mani kuma har yabiya sadakina, yanzu haka kwanaki goma sha biyune suka ragemun nazamo mallakinsa kuma ni bazan iya hana hakan ba." Dariya yafara mata har yana riqe ciki don gaba d'aya ya fahimci batasan cewa shine mijin da take iqirarin mahaifinta ya zab'a mata ba, yana kallon yanda ranta yab'aci amma yakasa tsaida kansa har saida yayi mai isarsa sannan yace " yi hak'uri ranki shidad'e abunne dole inyi dariya.." yaqarasa maganar had'e da d'ago kansa amma ga mamakinsa sai ya hangota ashe tuni har tabar wajen tana gab da isa gida, STORY CONTINUES BELOW Da sauri ya cimmata yana kiran sunanta, tsayawa tayi tanajin zuciyarta kamar tafad'o saboda takaicin fad'a masa sirrinta da tayi Ashe dama shi ba sonta yakeyi ba tunda har ya iya yimata dariya a daidai wannan lokacin daya kamata ace dukkanin su suna cikin damuwa, qarasowa wajen yayi had'e da rik'e kunnuwansa yana gumtse dariyar dake neman sake fito masa yace "yi hak'uri matata natuba kinji" K'walalo idanuwa awaje tayi had'e da girgiza kai irin bakasan abunda kakeyi ba tace "malan matar kafa kace? Karka manta yanzu nagama fad'a maka cewa antsayar mani da mijin da zan aura kuma har yabiya sadaki kwanaki kad'an suka rage a d'aura mana aure amma ka aza mani dariya saboda kasan Kai d'in bada gaske kake sona ba shiyasa bak damu ba, dama nasan bazaka iya aurena ba tunda banida ilimin boko kawai kafad'i hakanne don ka yaudareni." "Subhanallahi Rashida mekike cewa hakan, nifa Ina mamakine akan yanda bakisan cewa nine mijin da zai aureki ba, kituna ke d'alibata ce, idan babu soyayya taya kike tunanin zan iya zaunawa ina bibiyarki haka? Ni da kike gani bantab'a soyayya ba kuma ban tab'a bawa wata mace dama ba tashiga rayuwata sai ke, to don me da zan yaudareki Rashida, ita soyayya Babu ruwanta da ilimi ko akasinsa kawai shiga takeyi a zukatan da ALLAH yaga cancantarsu da juna, kiyi hak'uri da banjira amsar da zaki bani ba na gabatar da kaina awajen iyayenki, wlh Rashida sonki nakeyi da gaskiya Kuma aurenki nakeso nayi kizamo mallakina kuma uwar 'ya'yana" "Don ALLAH malan kadena fad'ar haka, kadena k'ok'arin cusamun sonka azuciya, wud'annan kalaman naka zasu iya sake jefani cikin maraicin rashinka alokacin dana zamo mallakin wani, tun ranar daka furta mani kalmar so nake shan wahala domin duk motsin da zanyi Ina tsinkayo sautin kalmomin a kunnuwana, meyasa zaka nemi sake turani cikin damuwa da wud'annan zantuka naka." "Amma Rashida meyasa baki tambayi baba kowaye yazab'a maki?" "Saboda bana son nasan koshi waye?" "Koda nine Rashida?." "Taya zaya zamana cewa kaine" tunanin fad'a mata komai yayi saboda yakawo k'arshen wannan jayayyar tasu tunda ya fahimci batada wata masaniya akan komai gyara tsayuwarsa yayi sannan yashiga labarta mata abunda yafaru ranar da yazo gidansu wanda shine silar daya kai mahaifinta aranar makarantarsu daga nanne ya gano shid'in abokin mahaifinsa da bashida lafiyane har zuwa jiya da sukaje dubosa shi kuma dama ya sanar da mahaifinsa cewa yana son yanema masa aurenta Kuma kasancewar aminaine sosai yasa mahaifinta ya amince, nan take akayi komai aka gama bisa amincewar iyayenta da kuma nasa, yana kaiwa nan ya lumfasa had'e da cewa, "to Rashida kinji abunda yafaru kuma Ina fatar zaki amince dani d'ari bisa d'ari ki aureni, cike da mamaki wata irin kunya tarufe Rashida don gaba d'aya yanda yabata labarin haka taji baba yana bawa ummashi amma arayuwarta bata tab'a kawowa shi d'inne ba, wani irin farinciki takeji aranta marar misaltuwa, ahankali tabud'e baki tare da sunkuyar da kanta k'asa tace, "Kayi hak'uri malamina" sannan tabar wajen aguje, dariya yayi yana binta da kallo har tashige gida, wani yaro yakira tare da bashi ledar dake hannunsa yace yashiga wancan gidan yakaima Rashida sannan shi kuma yawuce zuciyarsa fal cike da farinciki. ••• ••• ••• A b'angaren yaya hawwa kuwa wato mahaifiyar Nuraddeen kasa amincewa da kuma natsuwa tayi akan komawar yaronta garin saboda yarinyar da zaya aura se take ganin kamar duk abunda yasamu yanzu ita da iyayenta zai baiwa, hakan yasa tayanke shawarar zuwa wajen wani malamin tsibbo tace tana son tunkafin ayi auren a tabashi da ita a saka mashi tsanarta ta yanda koda ranar d'aurin aurensu ne bazai yarda ya aureta ba sai a maye soyayyar da yake yimita akan 'yar qanen mahaifinsa wato muneerat, duk iya tsibbo da bugun k'asar da malamin zaiyi yayi don ganin kozai iya cin nasara Amma ya kasayi daga k'arshe sema cemata da yayi ta tashi tatafi don babu abunda zai iya, domin wannan auren ko tana so ko bataso dole sai anyisa saboda arubuce yake acikin qundin qaddarar yaronta da babu wanda ya isa ya hana ko kuma ya sauyasa hakan, Wanda kuma duk yayi yunqurin hanawa to tabbas babu ko shakka dole zai mutu don bazai iya ja da alqawarin ALLAH ba. STORY CONTINUES BELOW *_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ˜­_* [6/24, 9:08 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___14πŸ’Ž Cikin rashin amincewa da zancen malamin Yaya hawwa tace, "Haba malan, cike fa da yarda da aminci muke kawo buqatunmu zuwa gareku, sai kuma ace da kanku zaku wargaza wanan yardar da muke da ita akanku, wlh no bana son ya auri yarinyar nan don ALLAH kasake dubawa ko akwai yanda za'ayi" jinjina kai ya shigayi yana kallon gefe gefensa kafin yafara kiran wasu kalar sunaye, yajima yana suruttansa kafin yasake baje duwatsun dake gabansa, d'ago kansa yayi fuskarsa a d'aure yace da ita "d'auki d'aya" hannunta narawa tad'auka ta mik'a masa ya jawo wani tray dake cike da qasa ya ajiye agabansa, tsakiyar tray d'in ya aza dutsin tare da yin rubutu saman qasar, ya kwashe fiye da mintuna biyar yana abu guda sai faman zufa yakeyi, can ya shafe rubutuna yayi tare da d'ago kansa yana nuna Maya qasar dake cikin tray yace, "duba nan kigani" Tana dubawa taga hoton Nuraddeen shida Rashida lokacin daya riqe kunnuwa yana bata hak'uri, da sauri tadafe qirji tana fad'in "nashiga uku ni kuluwa, malan kaga abunda yaronnan keyi agabanta tun ba'aje ko ina ba, don ALLAH malan kayi wani abun, bazan iya jurewa ganin haka ba" Murmushi malamin tsibbon yayi kafin yace "fiye da haka sai kingani, kawai kitashi kitafi, bayan auren kidawo masan abunda zamuyi amma wannan bazamu iya komai ba" Babu yanda zatayi dole tamiqe jiki ba k'wari taji yace "An buqaci ki ajiye kud'in sadaka kafin kitafi" Cikin jin zafi da takaici tabud'e jikkarta taciro naira dubu uku ta ajiye masa sannan tafito kamar zata tashi sama tana fad'in, "wannan ai shi ake kira da asara, maqaryacin banza da wofi meye bazai yuyu ba aduniya, ai wlh banda wancan shashan Aliyun daya kwatanta mani wajenka kuma yace aikinka sha yanzu magani yanzune babu abunda zai kawoni nan don nasan dama bakomai irinku suka iya ba, malan bakada imani shiyafi dacewa da wannan aikin nazo nan nayi asarar kud'ina ga banza." Har ta isa gida fad'a takeyi tana qarawa saboda jin zafin kud'inta da aka amsa ga banza kuma ba'ayi mata aikin da take so ba, nafef na ajiyeta tabud'e jikka taciro kud'i taci karo da baffa Ali daya fito daga masallaci, yana hangota ya washe baki had'e da nufo inda take yana fad'in "sannu da zuwa Yaya hawwa" rufe jikkarta tayi had'e da banka masa wata irin muguwar harara sannan tace, "kasallami mai napep d'in nan acikin kud'ina" tawuce abunta, babu yanda ya iya tunda ta tafiyarta dole yaciro wata damuqaqqar d'ari biyar ya miqawa mai napep d'in yace, "ungo bawan ALLAH cire kud'inka kabani canji" mai napep d'in na amsa yatada kekensa had'e da cewa "ai ahaka na d'aukota." "'Darin d'in." "Eh wlh, don ma bance da hamsin ba wannan tsayin da aka sani." Yana gama fad'a yaja kekensa yabar wajen, da sauri baffa Ali ya cimmata daidai qofar shiga gida yana fad'in "Yaya hawwa wud'an ne kud'i kuma kike biyata da kika sani asarar miqa kud'in da nake dasu gaba d'aya, shi kuma tsabar rashin mutuncin wai har nera d'ari ya karb'a, kuma wlh ita kad'ai ce gareni yau ina zancen nakai ad'an silala mana wake da mai sai gashi anrabani da ita." "Ai ni be burgeni ba don ba haka naso ba, so nayi ya karb'i d'ari biyu a hannunka, idan kahanashi ciko yacire hularka yaje da ita" "Yaya hawwa meyayi zafi haka?, ALLAH baki haquri, yanzu dai mu ajiye wannan maganar, ya kikaga malamin inadai komai angama ko?" Kallonshi tayi had'e da yaqe hauru hakan yasa shima yasaki murmushi azatonsa andace, ji yayi tace STORY CONTINUES BELOW "Anko dace Ali, ai har an rabasu yanzu kawai ka qaddarama har ya auri 'yarka ya gama" Sake washi baki yayi yayi had'e da cewa "ai nafad'a maki aikinshi Sha yanzu magani yanzu, dako kinata faman kunfar baki ga inda za'ayi maki maganin matsalarki cikin sauqi." Saida tad'aure fuska sannan tajuyo tana kallonsa ido cikin ido ranta ab'ace tace, "Eh nako gani Ali, amma ina tabbatar maka da cewa nima cikin sauqi nima zaka biyani kud'ina da kasa nayi asararsu ga banza ga wofi, saboda rashin mutuncin Ali ni zaka yaudara, ka turani wajen matsiyaci talaka da baisan komai ba akarb'e mani kud'i ga banza kuma ace abunda nake so baze yuyu ba, to wlh kaji narantse maka kud'ina ko sisi bazaiyi ciwon kaiba saika biyani" tana gama magana tawuce abunta, tsaye baffa Ali yayi yana kallonta cike da mamaki kafin yayi hanzarin bin bayanta, "Yaya hawwa nifa ban fahimci me kike nufi ba" "Oho! Ni ba abinda ya dameni kaji nafad'a maka saika biyani kud'ina ko in d'ibesu ajikin waccan gwalmammiyar 'yar taka kona rage zafi." "Haba Yaya hawwa, meyakawo zancen 'yata anan, don ALLAH kiyi shiru kada afahimci abunda ke faruwa." "Meya dameni ko anji, d'a dai nawane kuma nace bana buqatar wacce za'a aura masa amma anqi afahimceni, to Ina ruwan mutum da duk matakain dana d'auka, kaga ni kaje duk yanda zakayi kahad'o mani kud'ina in koma wajen malan bakada imani, nasan shi kad'aine ke iya maida abunda bazai yuyu ba ya yuyu." ( _wal iya zubillah, yya haww kam kinyi nisa kina buqatar addu'a, duk wani mai sab'o yakan b'oye baya son kowa yasani amma ke qarara kike nunawa mutane ke bakya tsoron ALLAHn da yayiki ma balle d'an Adam, ubangiji ALLAH ya shiryeki da duk masu hali irin naki_). ••• ••• ••• Da gudu taqarasa cikin zauren nasu tare da tsayawa tana fitar da nishi ahankali, murmushi tayi had'e dasa hannuwa tasake rufe fuskarta, "Alhamdulillah" tafad'a tare da sake leqowa tana hangosa daidai lokacin daya miqawa yaron ledar sannan ya juya yakoma tahanyar da suka biyo, da sauri takoma itama cikin gida tana fad'in "wai kodai mafarki nakeyi?" Daidai lokacin ta k'araso tsakar gidan umma najin me take fad'a tace "meye kuma kike tambayar ko mafarki kikeyi." Cikin farinciki taqaraso inda take zaune tana gyaran wake tace, "Babu komai ummata" "Anya Rashida?, gaskiya da walakin goro acikin miya wannan farinciki da naga kinayi" kafin tarufe baki sai ga yaron da malan ya aiko yayi sallama had'e da cewa, "wai gashi inji malan idris yace abawa Rashida" kallon yaron umma tayi sannan tamaido kallonta ga Rashida data sunkuyar da kai qasa, murmushi umma tayi sannan tamik'a hannu takarb'i ledar had'e da cewa, "kace angode." Har yajuyazai fita umma takirasa ta warware hab'ar gefen zanenta taciro naira hamsin tamiqawa yaron tace, "kace masa angode kaji ko." "Kibarsu umma ai har yawuce nagode." Yaron yafad'a tare da ficewarsa da gudu"ikon ALLAH, kaga yaro mai tarbiya, ubangiji ALLAH yai maka albaraka kaji.!" Acan cikin zauren ya amsa da "Amin" sannan yaficewarsa, juyowa umma tayi tana kallon Rashida dake duk'e tana tayata tsince waken, tanaji zatayi magana da sauri tamik'e tana cire jikkarta dake kafad'arta tashige d'aki don tasan babu abunda umman tata bata sani ba, ita dai umma abunma dariya yaso yabata wai yau Rashidar tace dajin kunya, "ALLAH ka sake shirya mana" tafad'a sannan taci gaba da gyaran wakenta, acan cikin d'aki kuwa Rashida kasa tsaida kanta daga murmushin da takeyi tayi tafad'a akan katifarta tare da mulmulawa tajawo pillow tarungume tana dariyar da umma bazata iya jiba ta runtse idanuwanta had'e da furta "I luv you malamina, I luv you Nuraddeen" Saida tagama sabbatunta tukuna ta tashi tacire uniform d'inta ta sanyo doguwar riga tafito don taya mahaifiyarta aiki, sosai umma ke kallie da sauyin walwalar da 'yar tata ta samu tare da farincikin da take ciki wanda bako shakka tasan abunda take tsammanin rasawane akwanakin baya tasamu tabbacin samunsa, dariya tayi cikin tsokana da nuna cewa bata san abunda ke faruwa ba tace "Rashida nikuwa wai meye tsakaninki da wannan malamin naku daya aiko maki da saqo d'azu, gashican ma akan kujera na ajiye har babanki yadawo" Saida tayi dariya sannan tace STORY CONTINUES BELOW "Kai ummata ai kunsan komai?" "A'a nikam ban san komai ba amma dai yanzu abani labari insha, don naga alamar farinciki ya banbanta ranar yau data sauran ranaku ukun da suka gabata, fad'amun meye sirrin 'yatah." Dariya ta sakeyi had'e da cewa. "Kai ummata, nafahimci komai nakeyi kina sane dashi qyalewa kawai kikeyi." "Eh mana, ai duk uwa takan banbance tsakanin farinciki da kuma damuwar 'ya'yanta, wasu lokutan kawai tanayin shirune har zuwa lokacin da take tunanin gazawa zata iya bayyana atattare dasu, awannan lokacinne take zamewa jigo kuma garkuwa agaresu har zuwa lokacin da jarumta zata zamo mabayyaniya agaresu. Duk da ban takura kiba wajen sanin halin da kike ciki, akoda yaushe nakan roqi ALLAH d'aya gaggauta yaye maki damuwarki kuma ya matso maki da farinciki marar misaltuwa Kuma alhamdulillah yau natabbata ubangjina ya karb'amun" "ALLAH sarki umma, tabbas ubangiji ya amsa maki addu'arki ga 'yarki don kuwa ya yae mata damuwarta Kuma yasakata acikin farincikin da baya misaltuwa, ada bana iya banbance soyayya da shaquwa sai ranar da malam idris ya furta kalaman soyayya agareni, aranar ne nasan meye so kuma meye shaquwa, na fahimci gaba d'aya soyayyata da Rabe koda na auresa babu so da qauna aciki shirmene kawai nakeyi gashi najayewa kaina damar da zan iya zab'ar wanda nake son rayuwa dashi tahanyar bawa baba zab'i akan duk mijin daya auramun, hakanne ya jefani cikin matsananciyar damuwa da kuma rashin madafa har nake tunanin farincikina yatafi kenan har abada, ashe bansan cewa wanda yakawo sadakina kuma nake kallo a matsayin zab'in da mahaifina yayi mani shine wanda zuciyata keso, nan take na yankewa kaina hukuncin nesanta kaina da muradin zuciyata saboda insamu damar yiwa mahaifina biyayya, aqoqarin yin hakan ne malan Idris ya walwalemun zare da abawa har nafahimci cewa shine wanda yakawo sadakina kuma shine wanda zan aura" taqarasa maganar tare da miqewa tana kwashe kwanonin data gama wankewa, murmushi umma tayi sannan tace, "Ikon ALLAH, ai abunda baki sani ba tun kafin mahaifinki yasan alaqar dake tsakaninsa da mahaifin yaron ya yanke shawarar bashi aurenki, kuma ranar juma'ar daya je makarantarku wannan maganarce takaishi wajensa amma saboda ALLAH yariga ya tsaro komai yanda yake son yinsa si gashi kafin yasanar masa da cewa yabashi auren 'yarsa shi da kansa yafad'awa iyayensa anema masa aurenki" "Tabbas ALLAH shikeyin al-amarinsa ayanda yakeso akuma lokacin daya dace, domin aranar ne nima malan Idris yafurta cewa yana sona wanda aranarne kuma nace baba yazab'amun duk wanda yakeso zan aura." "To kingani yanda komai yafaru cikin sauqi, kece kawai kika wahalar da kanki, da ace ranar kin sanar dani komai to da bakisha wahala ba, ubangiji ALLAH yatabbatar da alkhairi atsakaninku." "Amin ummata" tafad'a tare da rungumeta, girgiza kai umma tayi had'e da nad'a mata hannu abaya tace "Ja'irar yarinya ni cikani tunda ke kin zama ruwa biyu, yau kunya gobe rashinta, ALLAH ya shiryeki" haka suka cigaba da aikace aikacen gidan abun gwanin sha'awa tamkar ba 'ya da mahaifiya ba saboda yanda umma ta sakar mata fuska tabata damar yin fira da ita sosai saboda tasamu damar nazartar kalaman 'yar tata acikin maganganun da sukeyi. Bayan la'asar baba yadawo yaci abinci ya huta umma ta d'auko masa saqon da malan idris ya aikowa Rashida dashi, karb'a yayi had'e da bud'ewa yaga kwalin wayane da kuma wata leda daban, sa yayi aka kirata yace taciro wayar yagani taciro tana wani sissinne kai yace tabud'e kwalin, Wayace qirar techno L7 sabuwa dal harda charger d'inta da earpiece, karb'a yayi yaduba had'e da kunna wayar yaga har layi akwai ciki yace "To ki kula Kuma kiji tsoron ALLAH, ubangiji ALLAH yatsare kuma yasanya albarka" sannan ya miqawa umma itama tasa albarka tamik'a mata, Sai da suka yimata jan kunne akan matsalolin waya da kuma rashin alfanun da take jawowa idan mutim baiyi tak tsantsan ba sannan suka sallameta, har zata wuce baba yasake kiranta had'e da cewa d'auki wannan ledar ki wuce batare daya damu da sanin ko menene acikin d'ayar ledar ba, umma ce tace "malan to kaduba sauran kayan?." STORY CONTINUES BELOW "Indai ke kinduba alhamdulillah ya wadatar." "A'afa nikam mezai sani bincikarsu batare daka gani ba!." "To k'yaleta can dasu bazai wuce 'yan turarukka bane da sauransu, Kuma kema kinsan nasha yimaki irinsu ko kuwa?" Yaqarasa maganar cike da tsokana yana yimata dariya, murmushi kawai tayi had'e da kauda kai gefe tana k'ara gyara zamanta. Aikuwa kamar baba yasani koda Rashida tabud'a ledar turarukkane guda uku sai tarkacensu sweet da cingwam, sosai taji dad'in kyautar don ba qaramin son sweet take dashi ba, Bayan sallar magrib baba yashigo ya leqa d'akin Rashida had'e da cewa takula da gidan zasu fita sannan yaje yacewa umma tafito suje, dama d'azu sunyi magana akan bayan magrib zai kyaita taga kayan d'akin daya siyawa Rashida idan sunyi gobe sai akwasosu, Basu jima da fitaba wayar Rashida tafara ruri wanda har saida yasa taji tsoro, kasancewar tana yawan amfani da wayar ummanta yasa duk tad'an San wasu abubuwan amma wasukam saiya zauna zaman koya mata saboda bata sani ba, gashi ita wayar daya sawo matama touching ce ita kuma tafi iya mai keypad, ta dad'e wayar na ruri kafin tasamu daqyar ta d'aga, "Assalamu alaikum." Tafad'a kamar mai koyon magana kafin taji ta d'aya b'angaren an amsa mata da, "wa'alaikissalam d'alibata, ya akayi baki d'aga watar da wuri ba" "To malamina ban iya bane, ko yanzu ALLAH ne yataimakeni hannuna yakai inda ake d'agawar badon haka ba saidai ta qaraci kukanta tagama" tabashi amsa kai tsaye ba tare da wata kunya ko shayi ba, saida yayi dariya sosai sannan yace "Kai d'alibata, sedai kice naqarashi kirana nagaji nagama, oh ni Nuraddeen ya zanyi da d'alibata?" "Haquri zakayi tunda ba tason bokon." Tafad'a tana dariya. "Hmmm ALLAH dai yakai damo ga harawa, boko kam ai kamar kinyishi kingama..." "Tirqashi! Ashe kuwa akwai 'yan kallo, Allah yabani kon koya to." "Amin, ya kike?." "Lafiya klw malamina." "Masha Allah, haka nekeson akoda yaushe kunnuwana sudinga ji, ya baba da umma duk suna lafiya?" "Eh suma lafiya klw yanzunnan suka fita." "Allah yadawo dasu lafiya." "Amin." Shirune yabiyo bayan gaisawar tasu kafin yace, "Rashida nifa har yanzu nakasa samun natsuwa wajen tabbatar da wane irin so kike yimani, sai nake ganin kamar zuciyarki bata yarda da soyayyar da nake yimaki ba." "Meyasa kace haka bayan Kai tsaye n nuna maka raunin da zuciyata tayi saboda yanda zantuka da kuma kalamanka suka narkar da ita, kamata yayi ace nice nake shakkun haka saboda banida wata nagartar daya kamata ace na cancanci samun soyayyarka." "Hmm d'alibata kenan! Ai ita soyayya Bata dubin nagarta ko kuma dacewa da cancanta, kawai had'uwar jinice da kuma zukata da ALLAH kehad'awa lokacin daya so, karki sake tunanin cewa baki cancanci soyayyata ba domin hakan zi iya tarwatsa mani zuciya, Ina so koda zamuyi aure ya kasance mungamsu da qaunar da muke yiwa junanmu ta yanda bazamu tab'a bari wani abu yashiga tsakaninmu ba balle har wata rana aganmu arana ko kuma muyi yunqurin rabuwa da junanmu, Ina matuqar sonki da qaunarki wanda natabbata hakn daga ALLAH ne, zan tsaya maki wajen ganin nariqeki hannu biyu batare da nabari kin koka ba." "Hmm! Malamina ai wannan abune mai wahala matuqar mutum naraye, zanyarda akan bazaka sakani koka waba amma indai wannan rayuwarce da wataran farinciki wataran Kuma baqin ciki to dole zan koka tawani b'angaren, babban burina shine ace ka so ni ayanda nake d'innan koda bazan samu ilimin bokon da kake muradi ba sannan kayi hak'uri da raunina alokacin dana gaza, ni kuwa nayi alk'awarin riqeka kai kad'ai acikin zuciyata batare dana had'aka da kowa ba, zanyi jarumta wajen kula da kai da kuma baka farinciki har iya qarshen rayuwata." Shiru yayi yana sauraren kalamanta da yakeji tamkar karta dena, tabbas yayarda kowane bawa da irin baiwar da ALLAH yayi masa, Rashida batada ilimin boko amma duka kalamanta cike suke da fikrah da kuma ma'ana, a 'yan shekarunta baiyi tsammanin zai iya samun nagartaccin kalamai daga wajen taba, asali ma yad'auka wayayyiyar mace 'yar boko ita kad'ai tasan yanda ake sarrafa harshe wajen furta kalmomin soyayya, murmushi yayi sannan yace STORY CONTINUES BELOW "Indai wannan ne muradinki da Kuma burinki to ki kwantar da hankalinki, ni Nuraddeen nayi alqawari zan soki so mai tsanani Kuma zan d'aukaka darajarki acikin 'yan uwanki mata." "Ina godiya da hakan malamina" tafad'a cike da farinciki, firarsu sukasha sosai kafin ya canxa akalar firra zuwa wajen koya mata yanda zatayi amfani da wayar, dariya tayi sannan tace. "Malamina kahutar da kanka don bana fahimtar komai ahaka, inda ma ace a ikacene kake nuna mun to da zanfi fahimta amma wannan left da right da kake fad'a awajen asambuli kawai nake ganesa." Dariya yayi sosai kafin yace "shikenan gobe kifito da wayar sai innuna maki wasu abubuwan a aikace kinji ko?." "To shikenan, seda safe naji motsi qila su baba ne suka dawo" "Ok. To kigaishesu." "Zasuji in sha ALLAH malamina." murmushi yayi ahankali ya furta mata "I love you so much Rashida." Dariya kawai tayi had'e da ajiye wayar tayi tsakar gida, "hello, hello." Yadinaga fad'a amma ga mamakinsa yaji shiru, yatabbata ajiye wayar tayi batare data kashe ba ta tafiyarta, dariyar shima yayi sannan yakashe wayar ya ajiye, ji yakeyi Ina ma rashidarsa zata iya karanta message day tura mata dad'ad'an kalaman da zasu dad'a sanyaya mata zuciya kuma suqara mata qaunarsa, amma kash yasan dole soyayyarsa tasamu tawaya tawannan gefe. ••• ••• ••• Baffa kuwa tuni yaba baffa usman shanunsa guda biyu yace aje asayar dasu kud'in afara sawo kayan aikin da za'a fitarwa da Nuraddeen sashen da zai ajiye matars, kafin kace me tuni baffa Usman yayi yanda yace har anfara aza gini mai kyau, wanda duka baffa Usman ne yakira wud'anda suka fitar da zanen yanda za'ayi ginin, ciki da falo sai toilet da kitchen duk acikin sashen da aka d'ibar masa tsakankanin shiyar mahaifinsa data baffa Ali.... *_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ˜­_* [6/25, 9:34 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___15πŸ’Ž Wasa wasa gini yafara girma saboda aikin akeyi ba dare ba rana, duk wani tanadi da baffa yayi sai daya fiddosa yabawa baffa usman yace ayi duk abunda yakamata kafin lokaci yayi don baya son aikin yakai har lokacin da za'a kawo amarya, acewarsa hakan yafi da ace ankawo yarinyar mutane cikin matsuwa inda bazata samu sakewa ba, sosai duk wanda ya kalli baffa cikin natsuwa zai fahimci bakad'an yake matuqar jin jiki ba, ammasaboda qarfin hali akoda yaushe qoqarin b'oye hakan yakeyi don gudun kada adakatar da auren. Ita kuwa yaya hawwa kullum cikin masifa take wai ama faman kashewa k'asa kud'i a banza anqi atanada Amma tun daga baffa har zuwa baffa Usman Babu wanda ya tankata inba baffa Ali dake sake zugata akan ccewa inbatayi da gaskeba duk nan baffa zai qarar da kud'in gashi yana jinya abarta da wahala, sake rufe idanuwa tayi ita ala tilasa a ajiye ginin inyaso Nuraddeen d'auki shigihwa guda a cikin shigihun dake sashen nasu a gyarawa yarinyar, nan ma baris baffa yayi da ita saima cigaba da bada kud'i da yakeyi ana cigaba da aikin, tayi masifar tayi har tagaji don kanta tabari amma babu abunda ke dad'a b'ata mata rai irin yanda taga ana narkewa wajen kud'i da irin manyan shanun da yasa aka kama aka sayar, hakan ba k'aramin takaici da bak'inciki yake sata ba idan ta tuna, gashi har yanzu takasa had'a kud'in da malam bakada imani yace tahad'o wajen yimata aiki balle tasan ko meye madafarta, wata shawara ta yanke aranta na zuwa wjen baffa ko zata samu cikon kud'in da take nema wajensa, kwance ta iskoshi duk ya had'a zufa saboda wutar da aka d'auke sai zafi ya taso masa, "A'a malan kaid'ai kake a d'akin ba kowa? Sukuma 'yan albarka sun d'auke wutar duk zafi yataso, kai ALLAH dai ya rangwanta mana" tafad'a tana jaye labulayyen taga saboda iska yashigo sannan taqaraso wajensa ta tallabosa ya tashi zaune yana fad'in "wash! bi ahankali hawwa, bayannan inajin yana yimun zafi sosai" "Sannu malan, sai hak'uri kasan dama shi sauqi ahankali yake shiga, ALLAH dai yabaka lafiya." "Amin hawwa." Yafad'a yana kallonta cike da mamaki don yasan wani abun take so, bai qarasa tunanin da yakeyiba yaga ta d'auko mafefeci tafara yimasa fiffita had'e da cewa, "malan kaga aurennan ya matso gashi babu fashi sai anyisa kuma inada buqatar inyi wasu 'yan gyare gyare, shine nace mezai hana ko 'yar dubu goma ka qara mani insamu in gyaggyara kafin lokacin ya qaraso" murmushi yayi don dama uasan za'a rina, indai hawwar daya sani ce Babu yanda za'ayi kaga tana yimasa wud'annan abubuwan batare da tana son wani abu daga garesa ba, d'an nisawa yayi sannan yace, "Hawwa dubu gomafa kikace?, Yanzu ke ko hidimar gyaran inda yaronnan zai zauna da nakeyi bakya gani har zaki zomun da wannan zance, haba hawwa ai kamata yayi ace kinkawo nahannunki anqara dasu bawai kinemi karb'a ba" "Amma naga ainima duk hidimarce zanyi ko malan, ko kafiso akawo yarinyar nan babu wani abun kirki da aka tsinana agidan?." "To meza'ayi tunda dai naga ba kishiyarki bace balle kice haka, in Kuma maganar abubuwan da za'aci a rarrabane to kibari lokaci yayi ina sane dasu, mufa wajen ango muke ba amarya ba balle muce wata hidima zamuyi." "Dakata malan kawai idan bazaka bayar bane kafad'amun Amma bazai yuyu kazauna kana fad'amun yanda ranka keso ba." Taqarasa maganar had'e da miqewa ta jefar da mafefecin gefe, "Meyayi zafi haka daga magana hawwa karki manta yaronnan d'an mune mu muka haifesa kinga kuwa gaba d'aya hidimar tamuce dani dake kuma yakamata ace kema kin kawo taki gudun mawar, ni nazatama kina can kina qoqarin had'a masa lefe ashe aiki nizai qararwa." Ya iyar da zancen yana dariya, wani irin mugun tsaki taja sannan tabar d'akin, girgiza kai yayi yace "ALLAH ya shiryeki hawwa." ••• ••• ••• Ta b'angaren baba kuwa tuni yaga yakammala had'a kayan d'akin Rashida da taimakon d'an uwansa malan balarabe, haka itama umma bisa amincewar Rashida tasa 'yan uwanta sukazo tabasu sadakin Rashida da kuma abunda ALLAH ya hore mata da wanda suka kawo mata tace suje tare da rashidar duk abunda takeso ta fannin kayan kici dana aikace aikacen gida asawo mata, tun safe suka fita basu dawo ba har sai qarfe biyar na marece, sosai umma taji dad'in sayayyar da sukayo mata don Babu abunda basu siyoba sai wanda aka manta, shire shiren auren sukeyi sosai don tuni sun fara rabon minti da cingwam, soyayya kuwa tsakanin Rashida da Nuraddeen sai wanda yagani, cikin sati d'aya suka d'inke waje d'aya tamkar wasu masoyan da suka jima da shekaru suna soyayya, kullum cikin satin sai yaje wajenta fira da daddare wani lokacin kuma da marece, tuni d'aliban makaranta da kuma malamai suka sanda alaqar dake tsakanin malam Idris da Rashida wanda mafi yawansu sunsha mamakin yanda malam idris yake d'an kwalisa kuma wayayye da yasha boka zai auri Rashida wacce kaf makarantar babu wanda baisan da zaman taba saboda tsabar takkwalci, wasu kanyi fatan alkhairi gareta akan ALLAH yasa ta sanadiyarsa tamaida hankali ga karatu wasu kuma kanyi dariya had'e da cewa ya kwasarwa kansa daqiqiyar yarinya kuma jahila, duk abubuwan da mutane kefad'a suna dawo masa a kunne amma ko sau d'aya bai tab'a jin damuwa akan haka ba, yariga yaji ya gani aduk yanda Rashidarsa take yana sonta kuma yana qaunarta ahaka, ana gobe juma'a da zai koma gida yazo fira wajen Rashida da daddare bayan tafito tayi masa shimfid'a a zaure ya zauna takoma cikin gida ta kawo masa ruwa yasha sannan itama tazauna saman kujera irin tazaman gida dake facing d'insa, "Sannu da zuwa malamina." Tafad'a tana jujjuya wayarta dake hannunta kafin shi kuma ya amsa mata da "yawwa habibty, kina lafiya?." "Lafiya klau alhamdulillah, ya shire shiren tafiya?, gobe sai gida ko?" STORY CONTINUES BELOW "In sha ALLAH, ko Zaki rakani?." K'walalo idanuwa tayi waje had'e da cewa "na shiga uku ni 'yar babanta, rufan asiri kada kasa abugani ajaridu" "Saboda kinje gidanmu ana saura sati d'aya bukinmu?, Ai ni kuwa sai nake ganin da nan da can duka d'ayane Babu wani abun aciki!." "Hakane, Amma dai kasan hakan ma bazata faruba gaskiya." "To naji, nima dai da wasa nakeyi amma Ina so ne idan Allah yasa nakoma ranar lahadi za'azo akawo lefe" "ALLAH yakai ranmu kuma yasa ka isa lafiya." "Amin habibty, amma Ina so don ALLAH kiyi haquri da duk abunda kika gani, ba haka naso ba yanayin abunne yazo ahaka." "Malamina kenan! Ni koda duka lefenne baka samu damar yiba bazanji komai ba saboda inada yaqini da kuma tabbaci akanka, nasan idan nazama mallakinka zakayi mani fiye da abunda bana tsammani don haka ka kwantar da hankalinka, bakada damuwa akan haka." Yaji matuqar dad'in kalamanta kuma yasake samun natsuwa akan halayyarta donmin ayanda halayyar 'yan matan yanzu take basa da fahimta wajen maganar aure balle uzuri amma ita gashi cikin sauqi ta fahimcesa kuma ta amshi uzurinsa, bai wani jimaba yakoma had'e da yimata bankwana don gobe tun da wuri zai wuce saboda akwai abubuwan da yake tunanin yi idan yakoma, har bakin qofa tarakosa tare da yimasa ALLAH ya kiyaye sannan tajuya takoma cikin gida, yana barin wajen yanufi wani shagon sayarda kayan sawa da sauran abubuwa dake cikin gari don dama tun jiya ya amshi kud'in adashin da suka had'a shida sauran malamai sunayi dubu d'ari da hamsin, akwatunansa yasaye guda biyu da d'an qarami na sama naira dubu goma sha biyar sannan yasayi atamfuna guda goma masu sauqin kud'i da kuma lace guda biyu na dubu goma sha uku uku, sai shadda d'aya da material yard shima mai sauqin kud'i k'waya uku da doguwar riga k'waya biyu itama da qananan kaya suma kala uku, ya kashe kusan dubu hamsin da wni abu a fannin kaya kawai sannan yasake cire wasu dubu talatin yace ahad'a masa kayan shafa da hijabai da mayafi, kud'in sunyi kad'an sosai amma yace ahad'a mashi su yanda suka samu, takalmi da jaka kala biyu ya siya sai sauran tarkacen underwears kud'in suka qare ya rage dubu d'aya ce ta rage masa a aljihu, hakanan yakwashi kayan yakoma d'akinsa yana mamakin yanda kud'in suka shige kaf cikin 'yar wannan qaramar sayayyar gashi kuma bai qarasa had'a sauran kayan ba, dama zancen inda yake tunanin gyarawa da ya ajiyeta tuni baffa ya sanar dashi yakwantar da hankalinsa duka abunda yakamata ayi za'ayi kawai yaji da had'in lefe da kuma abunda zaiba yarinyar nabuki, hakan yasa yasamu natsuwa sosai har yasamu damar yin wannan sayayyar, safiya na wayewa ya kama hanyar zuwa gida tare da akwatunansa yana tunanin abunda zai iskowa wajen mahaifiyarsa idan taga kayan... *_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ˜­_* [6/26, 11:11 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___16πŸ’Ž Tun daga qofar gida da mashin ya ajiyesa yaga alamar cewa aiki akeyi agidan nasu saboda tarin yashi daya gani da masu aiki da sai faman shige da fice sukeyi da kayan aikinsu, yaran gidansu dake gefe suna buga k'wallone suka hangosa da gudu suka nufo inda yake suna fad'in "oyoyo yaya nura, ya nura oyoyo" suka qaraso wajen su kusan bakwai suna ruguguwar d'aukar kayan, cikin tsawa ganin yanda suke jan jikkunan akwatayyen suna ruguguwar d'auka yace "ha'a kai kunada hankali kuwa! Ji iskanci zaku lalata kayan mutane, maza ku ajiye kubani waje." Dariya suka aza masa ganin yanda ya zazzare masu idanuwa, kansu yayo ahasale kamar zai dokesu suka bar wajen aguje sunaci gaba da dariya, d'aya daga cikin sune daya d'arasu hankali ya tsaya yana had'e da cewa "yi hak'uri yaya nura" kwafa yayi kafin ya d'auki d'ayar jikkar da tafi girma da qarami yacewa yaron, "yusuf d'auko mun wannan d'ayar." Cikin jin dad'i yaron ya tallabo jikkar ahankali tamkar wanda ya d'auko k'wai yabi bayansa, Kai tsaye shigifar da baffa ke kwance yanufa da kayan yaron nabiye dashi sukayi sallama suka shiga, baffa na ganinsa ya washe baki had'e da cewa, "Kai agaida mutanen yarimawa, sannu da zuwa sannu da zuwa." STORY CONTINUES BELOW "Yawwa baffa, munsameku lafiya" Nuraddeen yafad'a yana ajiye kayan had'e da komawa kusa da mahaifinnasa ya zauna, shima yaron ya ajiye ta hannunsa inda yaga ya ajiye sauran sannan yafita, binsa da kallo baffa yayi kafin yajuyo ya maido kallonsa ga Nuraddeen yace "lafiya klw Nuraddeen yaron can nake kallo kaf cikin yaranmu shi kad'ai ALLAH yayiwa natsuwa sak irin taka, shiyasa yake matuqar burgeni, gaba d'aya halinsa ba irin na sauran yaran bane da kuma mahaifinsa, kaga ikon ALLAH bazaka tab'a ganinsa kace yaron Aliyu bane don gaba d'aya tun daga kamarsa da halin kai hatta tafiyarsa duk irin na Usman ne kai kace shiya haifesa" murmushi yayi had'e da cewa "ALLAH sarki baffa, ao dama zumunka ka haifa maka, ni kaina jinina yafi had'uwa da nasa akan sauran yaran, yanzu nagamo dasu abakin gida gaba d'ayansu basajin magana baffa saidai addu'ar ALLAH ya shirya." "Amin fatanmu kenan!, Kai dai ka kula kuma dikkaninsu ka rik'esu gaba d'aya da zuciya guda saboda abu d'aya like kuma duk lalacewarsu bakada wud'anda suka fimaka su aduniya don haka kayi haquri da yanda halinsu yake ka sosu ka qaunacesu don bazaka iya canzasu ba, ubangiji ALLAH yayi maku albarka ku duka" "Amin baffa, insha ALLAH zan kula da hakan har qarshen rayuwata." "Masha ALLAH da kuwa naji dad'i sosai." Juyawa gefe yayi tare da jawo ledar magungunansa yana duddubawa sannan yace "Baffa ya qarfin jikin naka?" "Alhamdulillah ina samun sauqi sosai." "Amma baffa jikinka ya gagara nuna haka har yanzu, kodai canza maka maganukkan nan za'ayi?." "A'a nace maka nasamu sauqi sosai, yakabaro can wajensu 'yar tawa, suna lafiya?" "Duk lafiya klw baffa" "Madalla kasamu kaje kawatsa ruwa daga nan sai kashiga kagani komai yakusa kammala." "To baffa, dama cewa nayi ga kayannan nagama had'awa sai 'yan abubuwan da baka rasa ba." "Ahhh to masha ALLAH, ai wannan Bari kakeyi har saika huta sai ka kirawo ita mahaifiyar taka da sauran dangi abud'a agani, agaisheka ALLAH yayi albark." "Amin baffa." Yafad'a tare da miqewa ya nufi sashen da mahaifiyarsa take, har ya aza qafa zaishiga cikin rumfar d'akin nata ya hangota wajen da dabbobi suke tana dama masu qasari, juyowa yayi tare da nufo inda take yana fad'in, "Ahhh..innarmu ashe kina nan." Dayake kanta aduqe yake batama lura da shigowarsa ba sai yanzu da taji maganarsa ta d'ago kai da sauri had'e da cewa. "A'a oyoyo oyoyo, d'an baffansa shigowar yaushe?" Takwankwahe hannun rigarsa yayi had'e da saka hannunsa cikin bahon da take had'awa dabbobin qasari yayi yana murmushi yace, "banjima da isowaba innarmu, ai nazata yarannan sunshigo sun fad'a maki, wajen baffa kawai nafara isa na duboshi da jiki." "Rabu da ja'iran banza, yanzu haka wasa ta d'auke masu hankali basu shigo suka fad'a munba aida tuni na isa wajen kafin ka zazzagewa mahaifin naka aljihunka, gashi yanzu sun jamun tsiyar da k'ilan ko sisi bazan samu ahannun kaba." "Kai innarmu! Ai kinsan yanzu ba'ayi albashi ba ko sisi banzo dashi ba balle baffa klya karb'a." "Kai ni rufemun baki, kai da baffan naka ai ba'a gane kanku, Ina dai lafiya naga yau ka iso kafin a hau masallaci kai da baka isowa gidannan sai bayan sallar juma'ah wani lokacin ma har ana gab da sallar la'asar.?" "Lafiya klw innarmu kinsan yanayin yanda rayuwar take, balle yanzu da abubuwa suka shigo gabana." "ALLAH yakyauta, tashi kaje ka watso ruwa kaci abinci kafin afara kiraye kirayen sallah." "To innarmu, wai kije baffa na nemanki." "Kai nifa akwai aikace aikacen da nakeyi bana so inje yafara mani suruttannan da basuda gaira balle dalili." Kasa cewa uffan yayi ya girgiza kai cikin ransa yana mai addu'ar ALLAH ya shirya masa mahaifiyarsa. STORY CONTINUES BELOW Har yayo wankansa ya sauya kaya tana nan zaunenta ita da wata mata da tazo wajenta suna fira, wannan karonma girgiza kai kawai yayi yawuce abunsa, har yad'anyi nisata k'wala masa kira yazo, "Kashiga kitchen akwai sauran d'imame ka kad'auka kaida mahaifinka don namanta bansamu tun d'azu nasa ankai masa ba." agogon hannunsa ya duba yaga sha biyu saura amma ace har lokacin mahaifinsa bai karyaba wannan wace irin rayuwace mahaifiyarsa keda ita bayan tasan ko cikakkiyar lafiya bayada, kamar zaiyi kuka yace. "Innarmu badai sai yanzu baffa zai karyawa ba?" "Eh mana, ai kaji nafad'a maka mantawa nayi, kaje ka d'auka katafi in kuma so kakeyi saika gama tuhumata to bisimillah." "Bahaka nake nufi ba innarmu, kinsan ba cikakkiyar lafiya yake da ita ba ko kad'an bai dace ace yakai wannan lokacin bai karya ba domin hakan zai iya shafar 'yar sauran lafiyar data rage masa," mik'ewa tsaye tayi had'e da dukan qirji tana zaro idanuwa tace "Nashiga uku ni kuluwa, yanzu yaronnan nizaka qarewa magana akan mahaifinka, eh lallai ta tabbata za'a rabani da d'ana tun ba'aje ko Ina ba, to tunda nabar ubanka da yunwa zoka dokeni kaji ko nura?." "A'a innarmu ai batakai can ba ALLAH yabaki hak'uri." Yafad'a tare da shiga kitchen ya d'oko abincin sannan yawuce, yanaji matar dake zaune tare da ita tana fad'in. "Kai hawwa! Haka nura yakoma maki marar kunya daga jin zancen aurensa?, To wlh sai kintashi tsaye inba haka ba da ankawo yarinyarnan yasan yanda lamarin yake shikenan kashinki yabushe, dubi wannan rashin kunya daya zuba maki daga ganin zaiyi aure to inata da anyi auren, gaskiya akwai aiki babba e'ehhhmmm nura kam ya lalace" cike da takaici ya qarasa barin wajen ba tare da yaji amsar da zata fitowa daga bakin mahaifiyar tasa ba, yana kaiwa bakin qofar shiga d'akin da baffa yake yaci karo da baffa Ali shi kuma zai fitowa, yana gaishesa amma kota kansa baibi ba jikinsa har rawa yakeyi ya isa wajen yaya hawwa ya kwarmato mata duk da dai baffa yace yaje ya kirawota, binsa da kallo yayi sannan yawuce cikin d'akin ransa a dagule, baffa isman daya gani zaune ya sashi sakin murmushi had'e da duqawa har qasa ya gaisheta bayan ya ajiye kwanon tuwon agaban baffa, Baffa Usman na murmushi ya amsa masa cikin fara'a had'e da cewa, "Agaida ango d'an gidan baffa, sannu da qoqari, ashe da tsiminka ab'oye kasa yayana yanata wahala." Cike da kunya ya noce kai qasa yana murmushi baffa Usman yaci gaba da cewa, "Madalla to ai ka kyauta, ALLAH yayi albarka yaqara bud'i." "Amin baffa Usman." Ya amsa masa a kunyace, jiyayi baffansa yace, "Meye nan ka ajiye nura." "Tuwone innarmu tace akawo maka." "Kai kaci naka.?" "A'a baffa alhamdulillah naqoshi.?" "To Nima dai Alhamdulillah don qanena ya sawo mani abunda na samu na karya kuma har nasha magani, ubangiji Kuma ALLAH ya shirya yaganar." Dashi har baffa Usman sun fahimci yanayin damuwar da yashiga yanzu amma saboda shi mutumne mai haquri da rashin son aibata babba gaban qarami a maimakon yayi fad'a sai ya sauya maganar ta hanyar addu'a." Kamar iska haka sukaga yaya hawwa tashigo d'akin rai ab'ace tana dube dube ALLAH kad'ai yasan abunda baffa Ali yafad'a mata wanda shi ya haifar da shigowar tata ahaka, tsaye tayi cak ganin akwatunan tana cika tana wani batsewa kafin ta kalli Nuraddeen tace, "Amma kai wannan yaro munafuki ne, yanzu kasan da wud'annan kayan kazo a matsayina na mahaifiyarka a maimakon ka kaisu can saika tsaya anan dasu ka ajiye don d'ai munafucci, to meye alaqar uwaye maza da kayan lefe indai ba k'ulle k'ulle ake son ayimun ba wai don har ka renamun da wayo ina yimaka magana kace ba'a wani yimaku albashi ba, to su wud'annan uban kayan daka jido uban waye yabaka kud'in...." Bata qarasaba taji baffa yace, STORY CONTINUES BELOW "Ubansa ne yabasa ko bai isa ba?" Shiru tayi tare dayin tsaye tana girgiza jiki ita mai zuciya, cikin b'acin rai da takaici baffa ya katsa mata tsawa had'e da cewa "maza kizauna kafin ranki yab'aci." Cikin tsiwa tazauna saboda sanin halinsa kafin nan baffa Ali yashigo tare da sauran matan, shidai baffa Usman dama tunda tashigo ya noce kai qasa yana karanto addu'o'in daya sani abakinsa, shid'in mutumne mai sanyin hali da kuma haquri tamkar yayan nasa amma ko kad'an bai iya b'acin rai ba, shiyasa ba kasafai yake kula wasu abubuwan ba don gudun b'acin rayuka, batare da baffa yanuna komai aransa ba yasa matan qannen nasa suka jawo kayan aka shiga bubbud'awa kowanensu na yaba kyawon da sukayi tare da ALLAH yasanya alkhairi, har aka gama Yaya hawwa batace uffan ba sai da taji matar baffa Usman tace, "Nura kam kayi qoqari sosai kuma kaya sunyi kyau amma ni banga sarqoqi da ribon ribon d'in 'yar tawa ba ko ka mantane.." ai kamar jira takeyi kafin tarufe baki tace, "To tsohuwar munafuka, irin kune masu qaryar arziqi alhalin bakuda komai, da zakice babu kaza da kaza duk wud'annn kayan da yayi inba raahin imani ba ace har sai yaqaro wasu ko don bake kika haifesa ba ba'asan amshi ba sai dai karb'a zakice hakan." Tabud'e baki tabata amsa baffa usman yace, "kul..bilqeesu karki fara." tashi Nuraddeen yayi yabar d'akin ransa ab'ace yayinda matar baffa Usman tace, "Haba maigida, yanzu meyayi zafi acikin wannan maganar da zata jefomun wud'annan kalamai, inadai 'ya'yane nima ina dasu kuma Alhamdulillah idan amshi kad'ai nasani tunda 'ya'ya mata nake dasu banida takaici dama haka ankasan macce da abata, ita kuma dake alfaharin.." Bata qarasa ba yace tabar d'akin tunda tayi ALLAH sanya alkhairi shi dai baya son fitina, dole tafita tanajin wani sululi aranta saboda Babu ranar da Yaya hawwa bata goranta mata rashin d'a namiji saboda gaba d'aya 'ya'yanta biyar duk matane har sun aurar da biyu saura uku. Tana wucewa baffa Ali yace, "amma dai Usman yakamata ka tsawtarwa matannan taka, ni bansan abunda yaya hawwa ta tare mata ba duk tabi ta renata, Wlh yaya wannan balkisun da kake gani so takeyi tawatse mana zuria amma inba haka ba daga fad'ar gaskiya saita rufe yaya hawwa da baqar magana, ai wannan rashin mutuncin ne.." yana rufe baki matarsa da tuni tuquqin baqincikin ganin wud'annan kayan bana 'yarta bane ya mamaye mata zuciya taja wani irin dogon tsaki tabar wajen, "Itafa wannan kace me?" Baffa Usman yafad'a yana nuna masa hanyar data fita, tsuru tsuru yayi da idanuwa tare da noce kai qasa baffa yyi murmushin da yafi kuka ciwo sannan yace "Ubngiji ALLAH yaganar damu muduka" Mere baki Yaya hawwa tayi kafin tace, "Amin, Ali kwasomun kayannan tunda angama gani gobe akirawo makwabta suma su gani kafin atashi kaiwa" tana gama fad'a tawuce abunta don kar wnda yaga damarta, jiki narawa baffa Ali yanufi kayan baffa yace... *_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU_*πŸ‘πŸ˜­ [6/27, 10:52 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___17πŸ’Ž Kul Aliyu kada kasake inga hannunka yakai ga kayannan, Babu inda za'aje dasu anan za'a barsu har zuwa jibi, inyaso kyasanar da 'yan uwanki ko mutum d'ayane sai yazo aje akai kayan tare dasu bilkeesu, har tafidda qafarta d'aya awaje tana shirin aza d'ayar tajuyo da qarfi jin abunda baffa ke fad'a. STORY CONTINUES BELOW "Malan menaji kana fad'i?" "Abunda duk kunnuwanki suka jiyo maki kuma maza kifice mun da gani." Fita tayi ranta ab'ace ta tsaya abakin qofa tana zazzaga maseefa ita kad'ai yayin da baffa yace su baffa Usman suriqasa yana so yashiga ban d'aki suka barta can tanata kumfar baki, wunin ranar kusan aqofar d'akin ta wuni tana zazzaga masifa inda taka shiga ba nan taka fita ba tana nemn wanda zai tankata, sai akayi sa'a hatta baffa Alin dake biye mata baice da ita uffan ba ya shirya yawuce masallaci wajen sallarsa ta juma'ah, bayan sun dawo Nuraddeen ya nufi sashen da ake gyara masa cike da farinciki duk da kuwa zuciyarsa dasqare take da damuwowi kala kala, Ba kad'an tsarin part d'in nasa ya burgesa ba, baran ganin kitchen d'insa da toilet ba'a waje suke ba, hakan ya matuqar yimasa dad'i arai, tuni an kammala komai fentine kurum ya rage, sai wearing na wutar nefa da ba'ayi ba, suma akwai komai aqasa nan da kwanaki za'a ida kammlawa, ya jinjinawa qoqarin mahaifin nasa sosai tare da yimasa godiya da addu'ar ALLAH yaqara masa lafiya da tsawon rai. Yaya hawwa kuwa duk iya dubarunta da kinibibin da zatayi wajen gani kayan sun dawo hannunta tayi amma takasa samun nasara saboda yanda baffa yakasa ya tsare daga qarshema cewa yayi kar wanda takoma kawo masa da sunan yazo ganin lefe saboda gobe za'a kai lefen, annan ma taso tayi maseefa amma tayi shiru don taga take taken yanzu baffa daidai yake da ita, kad'an yake jira yayi mata rashin mutunci shiyasa ta aminci da abunda yace, gashi tagama zagaye anguwa da makwabta azo aga lefen d'anta takoma saidai duk wacce tazo ganin lefen sai tace mata anrufe, haka sukata fita kowa da kalar tsogumin da yakeyi akan ta aika masu suzo ganin lefe kuma tace anrufe qilan bawani abun azo agani d'an nata yayi ba shiyasa takasa gwada masu gudun kar tayi abun kunya, duk wud'annn suruttai da akeyi suna dawoma kunnuwanta wanda hakan yamatuqar b'ata mata rai, qwafa tayi had'e da cije baki tana girgiza qafa daga zaunen da take kafin tace, "Wlh malan kayi da gwana, sai kace wannan abun daka yimun da bakayi shiba, yanzu banida lokacinka, Amma kabari idan nagama da wannan figaggiyar yarinyar da za'a kawo nadawo kanka, alokacin zaka gane cewa ka tabka babban kuskure." Ita kad'ai take suruttanta ad'aki wanda abun har ya riga daya zame mata jiki ka, sallamar Nuraddeen tajiyo abakin k'ofa tana hango yana cire takalmansa kafin yashigo, ciki ciki ta amsa masa sallamar don yanzu gaba d'aya tamaida laifin akansa tad'ora, waje yanema ya zauna ita kuma tajuyar da kai gefe, sunkuyar da kansa yayi qasa cikin damuwa kafin yad'ago had'e da cewa. "Innarmu barka da marece" "Yawwa" tafad'a adaqile batare data juyo takallesa ba, "Innamu don Allah kidena wannan fushin inba so kikeyi infad'a cikin fushin ALLAH ba, don ALLAH kiyi haquri kifad'amun duk abunda kike so zanyi maki amma don ALLAH kidena wannan fushin dani" jin abunda yace yasa tad'anyi ajiyar zuciya had'e da juyowa tace, "Duk abunda nikeso zaka yimun?" Cikin rawar muraya yace "e..e.eh zanyi maki indai bai sab'awa ALLAH ba." Fad'a murmushinta tayi sannan tace "Ka kwantar da hankalinka bazansa kasab'awa ALLAH ba, so nakeyi ka nunamun cewa ni mahaifiyar kace, ka d'auko lefencan yadawo d'akinnan saboda nagaji da abun gori da kunya da makwabta keyimun, yanzu fisabillahi inba mahaifinka da iyayi ba, Ina ruwansa da harkar mata, Ina lefe sha'aninmu me na mata don me zaiyi wani kane kane aciki, Nima ina so ingwadawa duniya jarumtar da d'ana yayi amma gaba d'aya yazo ya hana" "Amma innarmu naga da nan da can wajensa duka d'ayane kuma ai kayan gobe ma za'a kaisu tunda har na sanar da ita tafad'awa iyayenta." "To.to shikenan tashi katafi, don kasanar da ita sai me, Ina ni nahaifeka Kuma nafad'a maka kayannan wasu 'yan uwana duka basu gani ba sai faman yab'a mani magana sukeyi akan haka, ai shikenan ka kyauta tinda so kakeyi nazama abun nune a anguwa" taqarasa maganar tare da fashewa da kuka, Babu banban burinta kamar ace kayan sun dawo d'akinta, don tad'au alwashin zabce rabi tabar mata rabi, don bazata yarda ba ace kura da shan bugu...ita da d'anta ace wata tafita moriya dashi tun ba'aje ko ina ba, sau biyar kad'ai yatab'a siya mata atamfa amma gashi kusan kala ashirin da wani abu yahad'awa wacce zai aura, shiru yayi cike da mamakin meye abun kuka anan da har mahaifiyar tasa zata fashe masa dashi, cikin sanyin murya yace STORY CONTINUES BELOW "Kiyi hak'uri innamu bari nakira yarinyar nafad'a mata cewa amfasa kawo lefen gobe, shikenan haka yayi maki." Da sauri tace "eh yayi, kirata yanzu agabana kafad'a mata" ba musu ya ciro wayarsa yakira Rashida, bugu d'aya ta d'aga had'e da cewa "hello malamina." Cikin jin dad'in sauraren muryarta yace "Habibty ya kike? Kina lafiya?." "Lafiya klw, ya naji muryarka bayanda nasanta ba, ko kana kewatane. Taqare zancen cike da zolaya tana dariya, murmushin yayi shima had'e da kallon mahaifiyar tasa data kafesa da idanuwa tana harara suna had'a idanuwa ta d'aure fuska tare da kauda kanta gefe, murmushin ya sakeyi sannan yace. "Sosai habibty I really missed you." Murmushi tayi don tafajimci meyake nufi saboda duk k'ananan kalmomin nan na soyayya yafara koya matasu kuma tana saurin fahimta da kuma haddacewa, matsalarta d'aya bata iya rubutawa balle takaranta sai dai inda ajami za'a rubuta mata, sanin har izuwa lokacin tana kan layi yasa yaci gaba da cewa, "habibty zancen kawo lefe da za'azo gobe odan baki fad'awa su umma ba to kifad'a masu sai ranar attanin za'a kawo saboda wani dalili kinji ko." "To shikenan, dama ban fad'aba sai yau nake tunanin fad'a masu don haka babu matsala." "Yawwa nagode sai anjima idan nakira" da haka yakashe wayar yana kallon umma da farinciki kwance a fuskarta fal tace. "To ko kaifa, yanzu kaga sai ad'auko lefen akawo zuwa gobe 'yan uwana sun gani an uma tsaida wud'anda zasuje jebi sai akai ko kuwa" "Hakane innamu ALLAH yatabbatar da alkhairi." Qirikiri tayi mui da baki batare data amsa masa da abin ba don itakam Bata fatan yazauna da yarinyar ballantana tayi fatan wani alkhairi a tsakaninsu. Mik'ewa yayi zai fita tabiyo bayansa had'e da cewa "Nace babu d'an wani abu a hannunka nan, kasan kullum mahaifin naka nanan zaune waje guda sai abunda 'yan dubiya suka bashi, d'an tanadin da yayi kuma ya lalatashi wajen wannan ginin wahala, baice komai ba yasa hannu a aljihu yaciro d'ari uku a aljihunsa ya miqa mata had'e da cewa, "kiyi hak'uri da wannan innarmu sukad'ai suka ragemun" karb'a tayi ta saka a hab'ar zane ta d'aure tana biye dashi har waje tace "ba laifi, ALLAH yayi albarka" "Amin innamu," inna balkisu ce taqaraso wajen riqe da leda irin poly bag d'in nan tana murmushi "A'a malan Nuraddeeni fita za'ayi" tafad'a batare data kalli gefen da yaya hawwar takeba, cikin sakin fuska da girmamawa yace "Eh inna bilkisu fita zanyi in ALLAH ya yarda, ina wuni?" "Lafiya klw yaron kirki dama saqone 'yan uwanka saleema da kareema suka aiko dashi sukace akawo maka ka k'ara a lefe." Washe baki yayi yana kallon mahaifiyarsa tasa da tunda taga inna bilkisu taqaraso wajen ta d'auke kai ko zata juya, karb'ar ledar yayi tare da komawa cikin rumfar d'akin mahaifiyar tasa ya jawo tabarma had'e da zazzage kayan, cike da mamaki yace "Kai kai kai inna bilkisu kice hidima na d'orawa 'yan uwana, wannan irin abun arziqi har ina, gaskiya nagode sosai wlh ALLAH yabar zumunci km yasaka masu da alkhairi." "Amin ya rabbhi ai ba komai yiwa kaine, kadaici da haquri abunba yawa kasan d'iya mata ne basu san amshi ba saidai karb'a" murmushi yayi yana kallon mahaifiyar tasa da tabbas yasan maganace inna bilkisu tasakar mata amma hankalinta nawajen kallon kayan dasu kareema suka aiko dasu atamfa biyu sai sarqoqi kala biyar da jikkar ribon dozin biyu da kuma hulunan sawa masu kyau qwaya biyar, murmushi inna bilki tayi ganin yanda Yaya hawwa tasaki baki sannan ta sake fiddo da wasu bugaggin shaddodi irin wud'anda akeyiwa rini har guda biyu ta sake miqa masa tace, "Nima ga tawa gudun mawar aqarawa 'yata dasu, ALLAH ya sanya alkhairi kuma yakauda idon maqiya." Tana gama fad'a tajuya tayi tafiyarta don gurinta ya gama cika, damuwar da takeso tagani a fuskar Yaya hawwa da takaicin da take son tusa mata arai tagansu qarara kuma taji dad'i, STORY CONTINUES BELOW Godiya ya dinga yimata yana fad'in ALLAH yabar zumunci kafin yajuyo wajen mahaifiyar tasa amma ga mamakinsa sai yaga tayi fuuuu..tabar wajen ranta ab'ace, kwashe kayan yayi yanufi wajen baffa dasu yana mai yabawa qoqarin 'yan uwan nasa, sunyi masa abunda kaf dangi babu wanda yayi tunanin yimasa kuma yaji dad'i sosai, haka shima baffa cike da jin dad'i yayita sanya masu albarka, Yaya hawwa taci alwashin cewa koda ansa kayan alefen d'anta saita ciresu a gaban bilkisu tasa masu kalanzir ta qyasta ashana ta qonesu, ita ba ayi mahaluk'in daya isa ya nuna mata cewa ita da d'anta gajiyayyu bane balle ace za'a wani taimako masu har ayimata gori agabanta, ALLAH ALLAH ta dingayi gobe tayi kayan sudawo hannunta don tagwadawa inna bilkisu ita bata isa amma kash koda k'arfe 10 na safe yayi har baffa yasa ankira masa wani mak'wabcinsa dake da mota gwab irin ta haya d'innan yace da baffa Usman da kuma baffa Ali suje sukai kayan babu buqatar sai ankwashi ayarin mata guda anje kai lefe don d'ai d'orawa mutane hidima, duk yanda baffa Ali yaso zagayawa yazo ya sanar da yaya hawwa abun yacutara don baffa zaunar dashi yayi cikin d'akin yace karya kuru yatashi har sai angama kammala komai, baffa Usman shiya kwashe kayan yana kaiwa cikin mota yana dariyar yanda yaga baffa Ali na faman mutsu mutsu da qafafauwa yana son tashi amma baffa ya hanashi, bayan angama kaf baffa yaciro dubu goma aqarqashin katifar da yake kwance yaba baffa Ali yace idan sunkai lefen subayar asayi kayan wanka da ake kaiwa a al'adance. Kallon baffa Ali yayi had'e da cewa "tashi kutafi kuma wlh karka sake inga kanufi cikin gidannan ina kallonka babban kwabo kawai" Baice komai ba yamiqe yafita yana waiwayen cikin gida, ji yakeyi har wani cizonsa maganar keyi amma baffa ya kasa ya tsare ga kuma baffa Usman biye dashi yana gimtse dariyar dake cinsa, kamar yaro haka ya dinga kumbure fuska har suka bar qofar gidan, Hamdala baffa yayi kafin nan yatura yusufa daya hango zai shiga cikin gida yace yakirawo masa Yaya hawwa, da qunquni tashigo cikin d'akin tare dayin tsaye bakin qofa fuskarnan ba annuri ko kad'an saboda fushin da takeyi dashi akan abunda yayi mata tace "gani lafiya?" Shikam dariya ma tabashi ganin yanda take cika tana batsewa akan d'an qaramin abunda yafaru tun kwana biyu da suka wuce, to inata da wannan baisan mezai faruba shiyasa yace qara yafad'a mata da kansa da ace taji ga wani, wannan dalilinne ma yasa yahana baffa Ali komawa cikin gidan don yasan halinsa tsab zai iya qarawa wutar fetur, cikin tsokana yace, "Haba hawwa wannan irin cika da batsewa da kikeyi haka sai kace ba uwar ango ba, yihaquri zo muyi magana fushi ba naki bane kinji." "Malan nifa inada aiki cikin gida inzaka fad'amun abunda zaka fad'a to kafad'a sauri nakeyi." "To yihakuri kishigo mana." Badon taso ba haka taqaraso cikin d'akin tayi masa tsaye qiqam akai, murmushi yayi sannan yace, "Dama zancen lefennan ne.." bai qarasa ba tace, "Sai akayi me, ai jiya munriga mungama magana da yarona baza'a kaishi yauba sai gobe don haka nima inada hakk'i da d'ana yau nakira 'yan uwana abamu lefe suma sugani daga nan zamu fidda wud'anda zasuje kai kayan gobe in ALLAH yakaimu don wlh baza'aje da kowace shegiya acikin gidannan ba naji kana kawomun wasu kalan dangi ehe." Baki bud'e baffa ke kallonta har ta dasa aya kafin yace, "ikon ALLAH, waike kam hawwa har yaushe zakiyi hankaline?, Meye amfanin maido da hannun agogo baya da kikeyi yanzu bayan da yardar ALLAH nasan lefennan da kike magana har yakusa isa inda yakamata, don ALLAH kidinga tunani kirege fitina domin in mune aduniya gobe bamu bane, mutuwa na tare damu akoda yaushe saboda haka muzama masu hak'uri.." bai rufe bakiba yaga tajuya da qarfi tana kallon inda aka ajiye akwatunan had'e da lailayo asshar ta tule saboda ganin wurin da tayi wayam shiya tabbatar mata da abunda yake fad'i gaskiya ne, dole yariga da yasan hakan saita faru don haka ya gyara qafafuwansa had'e da mik'esu yayi kwanciyarsa, Masifa tadinga zazzaga masa had'e da miyagun kalamai tana bubbuge abubuwan dake cikin d'akin tamkar wata mahaukaciya yayi tamakar baisan tanayi ba har tagaji don kanta tabari, amma yinin ranar mutanen gidan sunsha zagi manya da yara acewarta duka sunsan da zancen suka munafucceta, shi kuwa Nuraddeen da mahaifinsa sunsha tsiga da miyagun kalamai kala kala, Kai inkaji kace ba d'anta da mijinta take yiwa suba, yayi mata ranstuwa yana magiya akan baisan da baffa zaisa su baffa Usman suje kai lefen ba yafi aqirga amma fir taqi yarda, saboda tsoron fushinta har kuka yadinga yi yana roqonta Amma tace yafice mata daga d'aki Bata son ganinsa, itama saboda takaici da baqincikin rashin cikar muradinta har da k'walla tayi tana tsinewa yarinyar albarka.🀭🀣 STORY CONTINUES BELOW ••• ••• ••• A can garin yarimawa kuwa tarba tamusamman baba da qanensa malan balarabe suka yiwa su baffa Usman, sosai sunji dad'in karramawar da aka yimasu don musamman baba balarabe yasa aka gyara masu kaji ga fura da nono mai sanyi sannan aka yimasu abinci da abunsha musamman, ko kad'an baffa Usman baiso tsayawaba bayan sun bada kayan amma malan balarabe yayita roqonsu dole ganin girmansa yasa suka haqura suka tsaya, sunci sun sha sunyi nak sannan su baba sukayi masu godiya, musamman baffa Ali da har saida yayo guzurin nama a aljihunsa don yaji dad'in bawa yaya hawwa labari, dubu uku malan balarabe yabasu yace susha mai ahanya angode sosai baffa Usman yace bazasu karb'a ba hakan kuwa ba qaramin b'atawa baffa Ali rai yayi ba don har yafara hango lalurorin da zaiyi da nasa kud'in idan anbashi, haka aka rabu cikin farinciki da murna tsakaninsu baffa Usman da iyayen Rashida kowanensu na yabawa karamcin da suke dashi. Duk da ba wasu kayane masu yawa ba ayanda ake qaryar lefe azamaninnan duk wanda yaga lefen sai ya yaba kyansu tare da qoqarinsaa matsayinsa na malami kuma mai matsakaicin k'arfi, *A gurguje* Acikin kwanakin da suka rage a d'aura auren Rashida da malan Idris abubuwa da dama sun faru musamman ta b'angarensa don kusan Yaya hawwa fidda hannuwantatayi a sha'anin auren Saida 'yan uwa da abokanan arziqi aka had'u akayita bata haquri sannan ta haqura gaba d'aya gidan bata magana da kowa duk gaba takeyi dasu akan haka har lokacin da auren ya matso ana saura kwana biyu, babu wani shagali da akayi inba walima ba wacce itama ab'angarensu Rashida aka shiryata don sukam suna cikin farinciki sosai musamman iyayen Rashida da ita kanta, shima Nuraddeen ba'a barsa abaya ba amma idan yatunada matsalolin mahaifiyarsa duk sai yaji auren ya fice masa arai saboda tsoron abunda masoyiyar tasa zata fuskanta acikin gidan musamman wajen mahaifiyarsa da kuma baffa Ali, ko ranar da akazo jere yana jin irin walaqancin dasu muneera da baffa Ali sukayi masu banda inna balkisu da tazo ta jajirce wajen da ba qaramin kunya tasu akayi ba hakan yasa baffa yakirata ya damqa mata ragamar kula da mutanen amaryar da zasu zo har zuwa lokacin da za'a kammala shagalin, Anyi walima taji da gani don su baba balarabe sun taka rawar gani sosai kuma sunyi duk abunda yakamata ayi tun daga kan abubuwan ciye ciye dana lashe lashe, musamman aka yanka rago ranar walimar saboda had'ewa akayi haddata saukarta ta alqur'ani, malamai da dama sun halarci walimar sunyi nasihohi kalakala akan zamantakewar aure da kuma biyayya ga ALLAH da manzon tsira, baqar abayace mai kyau da tasha duwatsu ta ko ina jikinta da Kuma farar alkibba ta saka gashi tasha kwalliya had'e da lalle tayi kyau sosai kamar ba itaba, wani abu da zai qara burgeka ga walimar shine yanda malan Idris da abokanansa da sukayi zuwan bazata awajen walimar Jim kad'an da farawa yasha shaddarasa fara qal d'unkin riga da wando kaftani, nan take aka halarto masa da kujera kusa da inda Rashida ke zaune, wani irin farincikine ya lullub'eta a hankali tad'ago kai takallesa tayi murmushi shima yayi mata sannan tamaida kanta qasa, sosai iyayenta sukaji dad'in halartarsa wajen domin hakan yanuna masu irin muhimmancin da take dashi awajensa, nan aka cigaba da gabatar da nasihohin amarya da ango na saurare wasa wasa Rashida tafara jin gabanta nafad'uwa kafin can kuka ya kubce mata wanda ba sau d'aya aka saba ganin amare nayin hakan ba, anyi komai lafiya anqare batare da wata matsalaba kuma anyiwa amarya da ango fatan alkhairi tare da zaman lafiya da zuria masu albarka sannan kowa ya watse, yanda Rashida ke kuka sosai ba qaramin tab'awa malan Idris zuciya yayi ba don har saida yaso ya keb'e da ita don ya lallasheta amma kunya ta hanashi saidai akan hanyarsu ta komawa gida yakirata awaya ya lallasheta, Saida yaji tayi shiru tadena kukan sannan yakashe yana fad'in, "Sai gobe habibty idan nazo d'aurin aurenmu.." bai qarasa ba takashe wayar tana dariya don tasan wannan tsokanar da biyu yayita, dariyar shima yayi sannan yakashe wayar yanajin wani irin farinciki marar misaltuwa aransa... Bayan yakoma gida ya tarar da mahaifiyarsa nafad'a ita da inna bilkisu akan jagorancin da baffa yabata tayi mata tas had'e da cin mutunci kala kala, tun inna bilkisu nahaquri har taji bazata iyaba ta tanka mata sunata zubar da rashin arziqi kala kala, mutanen gida sunyi basu haquri har sun gaji amma sunqi su dena, kowacensu jitakeyi zuciyarta abaki tamkar ta kashe 'yar uwarta, gashi baffa Usman bayanan shi kuma baffa baya iya tafiya balle yatashi ya tsawatar masu, yayi kiransu har yagaji amma babu wacce ta tanka masa balle yasaran zasu dena, ga 'yan uwa da abokanan arziqi da sukazo bikin da mak'wabta duk sunyi cirko cirko suna kallon ikon ALLAH, abunda zaifi baka haushi ma yanda hatta 'ya'yansu manya da yara duk suna wajen a tsaye, wani irin baqin cikine da damuwa suka taso masa waje d'aya suka turnuqe masa zuciya, ji yakeyi babu babbar damuwarsa aduniya yanzu irin wannan jarabawar da yake ciki kasancewar gashi da ransa ba mutuwa yayi ba amma yakasa iya dakatar da fitina acikin ahalinsu a lokacinda 'yan uwansa basa gida, hawayene suka zubo masa daga cikin idanuwa ahankali ya rufesu yana karanto sunayen ALLAH, cikin ikon ALLAH kuwa yaji wani k'arfi da kuzari sunzo masa yafara jan gindi yana nema yasamu ko bakin qofane yakai wataqil ganin idanuwansa susa sudena, cikin azabar da shikad'ai yasan ko meyakeji ya iso bakin qofar d'akin jikinsa na rawa lumfashinsa na fita sama sama da qyar yabud'e baki yace, "Bilkisu" saiga Nuraddeen yashigo cikin hanzari saboda hayaniyar da yaji tana tashi, da sauri yayo kansa yana fad'in, "Baffa lafiya? Ya akayi kazo nan da kanka." Cikin zubar hawaye ya d'ago kansa yana nuna masa tsakar gidan daya hango anyi dandazo ana sauraren fad'an inna bilkisu da Yaya hawwa ga mamakinsa kawai sai ya hango baffa Ali gefe zaunensa yana sharb'ar tuwo ita kuma matarsa agefe tana tintsirar dariya, baisan lokacin daya dafe saiti zuciyarsa yan bud'ar baki saboda lumfashinsa dake neman d'aukewa, kan Nuraddeen yayi wani yunqurin lumfashin baffa ya d'auke tare da langab'ewa daga jikinsa da yake, "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun" yafad'a da qarfi tare da fashewa da kuka yana girgizarsa yana fad'in, "baffa, baffa, baffa don ALLAH kada katafi kabarni." Jin hakan ya maido hankalinsu bakin qofar d'akin da Nuraddeen ke rungume dashi, da gudu baffa Ali yayi kansa daidai lokacin shima baffa Usman yashigo gidan sargafe da kwashensa a kafad'a, jefar da ita yayi yanufi wajen d'an uwansa tare da jawosa ga jiki daga rungumen da yake ga Nuraddeen. Girgizas ya shigayi yana fad'in, "yaya, yaya" alokaci guda yana tattab'a tafin hannunsa, gefen wuyansa da kuma k'asan hancinsa inda lumfashi kefita, jin fitar iska kad'an daga hancin nasa ya tabbatar masa da cewa yanada sauran lumfashi ya kinkimesa yayi cikin d'aki dashi had'e da cewa Nuraddeen yakawo masa ruwa, dama tun a bakin gida da yaji hayniya nafitowa daga cikin gidan yatambayi Yusuf d'an baffa Ali abunda kefaru, jin da matarsa ake fad'an yasa yashigo ransa ab'ace sai gashi ya isko wannan tashin hankalin, muryar Nuraddeen daya dawo riqe da cup da ruwa yana fad'in, "baffa gasu." Yasashi fitowa daga tunanin daya shiga, karb'ar ruwan yayi ya yayyafawa baffa a fuska har sau biyu amma bai farfad'oba, Yaya hawwa dake tsaye abakin qofar ita da suran mutanen gidan suka fashe da koke koke suna wayyo, a fusace baffa Usman yajuyo yace, "gaba d'ayanku kub'acemun da gani, kuma dake dake duk sai nayi qararku idan kuka sake yayana yamutu, shashashun mata kawai, ku b'acemun da gani" yaqarasa maganar cikin tsawa yana nunasu da yatsa idanuwansa sunyi jajur tamkar wanda aka zubawa yaji aciki, jiki ba qwari kowa yabar wajen tare da komawa cikin gida sukayi jigum jigum tamkar basu bane suka gama cacar baki ba yanzu. STORY CONTINUES BELOW Sake d'ebo ruwan yayi ya sake shafawa baffasu har sau uku a fuska yana mai addu'a ALLAH yasa yafarfad'o, cikin ikon ALLAH sukaji yaja wani dogon lumfashi cikin dasashshiyar muryar da babu wanda kejinsa saidai sukaga bakin namotsi yana fad'in "hazbunallahu wani'imal wakeel" wani irin sanyi da farinciki baffa Usman yaji azuciyarsa ya runtse idanuwans a hawayen dake maqale suka zubo, ahankali yafara bud'e idanuwansa ya saukar dasu saman na baffa Usman dake hawaye ya riqo hannunsa, "Sannu Yaya" baffa Usman yafad'a yana murmushi kafin suma su Nuraddeen da baffa Ali suyi masa sannu fuskarsu cike da farincikin farfad'owar tasa, cikin rawar murya had'e da damuwa baffa Usman yace "Yaya bari naje wajen musa ya aro mana mota akaika asibiti" yana k'ok'arin d'agasa daga jikinsa ya kwantar dashi akan katifa, cikin muryar dake nuna yana jin jiki yace, "A'a Usman ba sai munje asibiti ba Alhamdulillah nasamu sauqi, amma Ina so don Allah Aliyu yafita daga d'akinnan bana son ganinsa yanzu, bantab'a tsammanin cewa duk wannan fitinar dake faruwa acikin gidannan ba yana ciki kuma koda fad'amun akayi wlh bazan yarda ba, amma sai gashi da idona nagansa zaune shida matarsa iyalinmu nafad'a anrasa wanda zai rabasu shida ita, wannan wace irin rayuwace haka ace d'an uwan bazai iya karewa 'yan uwansa mutuncin suba, da ranmu kenan yayi haka inaga bama raye." 'bata rai yayi yana qunquni wai aishi baisan yanda zaice masu ba tunda duka matan yannens ne Amma anaso aga lifinsa, cike da takaici baffa Usman dake kallonsa yace, "Bakomai Aliyu duniya ce, idan mutum ya gyara kansa, idan kuma ma yab'ata kansa, rayuwa da kake gani batada tabbasa kuma shi zumunci ba wasa bane, don haka duk abunda kayi don kanka, mudai iya fatanmu da kai ALLAH yagyara maka halinka" juyowa yayi wajen baffa yaci gaba da cewa "ka k'yaleshi yaya indai duniyace ta ishesa riga da wando" mik'ewa yayi ransa ab'ace yabar d'akin yanaci gaba da qananan maganganunsa, baffa ya kalli Nuraddeen dake gefe idanuwansa sunyi jawir saboda b'acin rai da kuma kukan da yayi yace "Nuraddeen ya hidima?" Murmushin qarfin hali yayi masa sannan yace "Alhamdulillah baffa, ya jikin naka?" "Alhamdulillah Nuraddeen, ubangiji ALLAH yayi maka albarka ya albarkaci zuriar da zaku samu, gobene d'aurin auren ko?." "Amin baffa, Amma don ALLAH a d'aga d'aurin aurennan har kasamu lafiya, kaga sai muje asibiti gobe adubaka tunda yanzu marece yayi sosai" "Hakane yaya, gaskiya yakamata muje asibiti, zamannan gida naga babu wani sauqi da ake samu abunma sai qara tsamari yake." Baffa Usman yafad'a had'e da kawo mafici yana yimasa fiffita. "Kul! Usman kada in koma jin zancen d'aga auren nan yakoma fitowa daga bakinku da kai har Nuraddeen, wlh ko rasuwa nayi banyafe ad'aga d'aurin aurennan ba kunji nafad'a maku, lafiya da kuma rashinta duka daga ALLAH ne haka itama rayuwa da mutuwa duk ahannun ALLAH suke, aure kuma hukuntawarsa ce adaidai lokacin daya so, don haka ban lamunta ad'aga aurennan ba saboda rashin lafiyata, mutuwa da kuke gani bata hana komai aduniya balle rashin lafiya, don haka abar komai ynda aka tsarashi da yardar ALLAH Kuma zan samu sauqi kunji ko nafad'a maku?" "Eh Yaya" suka amsa masa atare kowane najin wani abu azuciyarsa. Sosai baffa yasaki jiki don ya nuna masu yaji sauqi sosai sukayita fira har bayan isha'i, amma cikin jikinsa shikad'ai yasan meke damunsa, duk wannan hali daya shiga Yaya hawwa bata koma tunanin koda leqa ta gefen da d'akin baffa yake ba balle taje tadubo sa saboda fad'an da baffa Usman yayi masu wanda hakan ba qaramin sake qonawa baffa rai yayi ba har yake tunin tabbas koda mutuwa yayi yasan hawwa bazata tab'a damuwa ba balle yasa ran zata tuna dashi tayi masa addu'a, hawayene suka gangaro masa a fuska yayi saurin gogewa don kada sugani, baffa Usman bai bar d'akin ba sai kusan qarfe d'aya na dare shi kuwa Nuraddeen kwancensa yayi wajen baffa sukaci gaba da firarsu wacce rabinta duk nasihace yakeyi masa akan rayuwar aure da kuma amana da hak'k'ok'an da ALLAH ya d'ora masa na matarsa, yayi mashi nasiha sosai akan muhimmancin hak'uri da iyali da kuma kyautata masu har aka kira sallar asuba, da kanshi ya riqasa sukaje baye yayo arwala sannan ya maidosa shikuma ya koma yayo tasa had'e da wucewa masallaci acan sukaci karo da baffa Usman shima ya zauna bayan anyi sallar asuba yayi masa nasiha sosai, bayan sun dawo ne masallaci lokacin rana tafito baffa Usman yasa aka kirawo masa yaya hawwa da bilkisu anan d'akin da baffa yake, Amma har matarsa bilkisu tazo Yaya hawwa nacan abunta zaune don cewa tayi baza tajeba saboda jiya agaban mutanen gida yara da manya ya wulaqantasu don haka Babu inda zataje tunda bashi ya ajiyeta ba. STORY CONTINUES BELOW Sun jima suna jiran isowarta amma fiye da minti talatin babuta ba tsammani, hakan yasa baffa Usman ya maido hankalinsa ga bilkisu batare da yajira bayanin komai abakin taba yayi mata tas dama tun jiya da daddare yafara sauke fushinsa akanta yau kuma yasake d'orawa hak'uri tayi ta basa tana roqonsa gafara ya katsa mata tsawa had'e da cewa, "Kiyimun shuru ba wannan nake son ji daga bakinki ba, wlh daga yau nakoma jin kin tankawa yaya hawwa acikin gidannan sai ranki yayi mummunan b'aci don bazan lamunci garin shashanci irin naki kibiye mata kuna fitinar da zata haifarwa da d'an uwana matsala ba, daga yau duk abunda zatayi maki Ina so taci albarkacinsa matuqar ni inada muhimmancin agareki a matsayinsa na yayana." "Shikenan zanyi yanda kace in Sha ALLAH, Yaya kai Kuma don ALLAH kayi hak'uri bisa damuwar da muka haifar maka da ita jiya" tafad'a tana goge hawayen jin d'acin hukuncin da maigidan nata ya yanke mata, taso ace yabarta takoyawa Yaya hawwa hankali idan ita mahaukaciyace amm dole tabar maganar ko don yiwa mijinta biyayya, girgiza kai baffa yayi don baiso baffa Usman yayi mata hakanba agabansa, yaso ace amtsayinsu na miji da mata sun kashe sun binne a d'aki amma sanin yanda zuciyar d'an uwan nasa take idan ransa ya b'aci yasa bai dakatar dashi ba, cikin taushin murya baffa yace, "Babu komai bilkisu, kiyi hak'uri kema nasan duk dalilin jagorncin dana azaki ga aurennan ya haifar maki da wannan fitinar awajen iyalina, don ALLAH kuci gaba da hak'uri da ita kunsan hali zanen dutsi, ubangiji ALLAH ya shiryeta kuma ya ganar da ita, Usman don ALLAH kada kasa bilkisu tacire hannunta awannan hidimar domin burinta aduniya bai wuce a kunyata a wannan al-amarin ba, don haka Ina baku haquri na yau d'ai kujurewa duk abunda zatayi har agama lafiya kaji ko?" yaqarasa maganar yana kallon baffa Usman da gaba d'aya yaso iyalinsa tafita harkar sha'anin auren saboda matsalolin hawwa, wata ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kalli d'an uwan nasa yace "Duk abunda ka yanke Yaya shine daidai kuma dole ayisa ubangiji ALLAH ya kauda fitina kuma yasa agama taro lafiya." "Amin ya rabbhi Usman nagode, ALLAH ya zaunar dakai lafiya da iyalinka kuma yanda kake kula dani tare da yimani biyayya kaima ALLAH yabaka mai yimaka haka, yanda ka kula da sha'anin Nuraddeen kaima ALLAH yakula maka dana dukkanin zuri'arka nagode nagode sosai.." yaqarasa maganar yana mai fashewa da kuka saboda tunanin abunda zai faru bayansa don shikad'ai yasan yanda yakeji acikin jikinsa, Abunda duk ALLAH yatsaro babu wani mai iya hanashi sannan ita matar mutum kabarinsa yau misalin qarfe biyu da rabi na rana masallacin juma'a na unguwar yarimawa yacika da tarin dan dazon mutane 'yan kasuwa da malamai don sheda d'aurin auren MALAN NURADDEEN IDRIS ALIYU (MALAN IDRIS) da kuma amaryarsa RASHIDA BASHAR MAI TAKALMA, inda nahango baffa zaune agefe sai kuma baffa Usman tsaye agefensa yana gaggaisawa da mutane cikin farin yadinsu boyel d'unkin babbar riga sunyi matauqar kyau kai kace tagwayene kowanensu sai fara'a yakeyi saboda tsammanin cikar burinsu, haka baba da qanensa malan balarabe suma sunsha manyan rigunansu kalar ruwan omo iri d'aya fuskokinsu cike da annuri suna yiwa baqi masauki kafin isowar ango, Nuraddeen na hango tare da abokanansa sai wasar hauru yakeyi cikin had'ad'd'iyar shaddarsa milik suna tahowa shima d'unkin babbar rigane ajikinsa ya matuqar zauna masa had'e da yimasa kyau sosai wanda ko ba'a tambaya ba kasan cewa shine ango, suna qarasowa aka nuna masu masaukinsu acan gefen dake tsakanin iyayensa dana amarya limamin masallacin juma'ar yafara gabatar da sigar aure kamar yanda yazo a musulunce sannan aka gudanar da yarjejeniyar karb'arwa Nuraddeen auren Rashida daga hannun iyayenta bisa sadaki dubu hamsin laqadan ba ajalanba yayin da iyayenta suka damqawa nuradden amanar aurenta tahannun iyayensa bisa yarda da amincewar cewa zai kula da cinta, shanta, suturarta da kuma lafiyarta sannan aka tofa addu'a, wani murmushi baffa yasaki had'e da cewa, "Alhamdulillah, dama sannu sannu bata hana zuwa saidai adad'e ba akaiba, ubangiji ALLAH ka amintar da wud'annan bayi naka bisa dukkanin alkhairanka awannan rana da dukkanin ranakun da zasu biyo bayanta har iya qarshen rayuwarsu" baffa Usman dake gefensa ya amsa masa da "Amin Yaya" yana dariya, shikuwa gogan naka ana gama d'aura auren lumshe idanuwansa yayi yanajin wani irin farinciki na ratsa dukkanin sassan jikinsa da kuma rouhinsa, yajima ahaka kafin d'aya daga cikin abokanansa ya zunguresa suka bushe masa da dariya suna yimasa sheri. STORY CONTINUES BELOW ••• ••• ••• Acan gida kuwa bebeji gaba d'aya anguwar mutanen arziqi suna wajen d'aurin auren Amma banda baffa Ali da tun jiya da yayi fushi akan maganar da baffa suka yimasa yasha alwashin ko d'aurin auren bazai jeba, Babu yanda baffa Usman baiyi dashi ba amma yace babu inda zaije tunda suka had'e masa kai suka nuna masa cewa shi bawani tsiya bane acikinsu, ganin lokaci na qurewa yasa ya ajiye masa kayan da suka d'unka su uku suka wuce cike da tsammanin cewa zai biyosu abaya, Amma ga mamakinsu har aka gama d'aurin auren bai jeba wanda hakanma yasake tab'a zuciyar baffa sosai ganin cewa idan baya raye sukad'aine zasu iya karb'arwa 'ya'yansa aure amma ace yaqi halartar auren d'an nasa, awannan karonma sake danne damuwarsa yayi saboda gudun haifarwa da d'ayan d'an uwan nasa damuwa. Bilkisu ma sake zage damtse tayi cike da farinciki tamkar wani abun bai tab'a faruwa ba jiya tayi duk abunda yakamata, duk wasu baqi da zasuzo kai tsaye Yaya hawwa kace masu suje wajen qirjin biki wato kinfi uwar ango bilkisu don ta tozartata amma ita hakan ko ajikinta don baffa Usman yabata isasahin kud'i tayi abinci ita da 'ya'yanta su kareema da sukazo, koda suka jewa Yaya hawwa yimata fatan alkhairi ko kallon banza basu isheta ba balle ta tankasu suka juyowarsu batare da sun damu ba don dama saida bilkisu taja masu kunne kafin sutafi, baffa Ali kuwa shida matarsa bini bini sun fito tsakar gida ko kunyar mutane basaji sun yadawa bilkisu magana au da Yaya hawwa itako tayi kamar bata masan sunayi ba. Kasancewar akwai 'yar tazara tsakanin garuruwan guda biyu wato qauyen yarimawa da kuma bebeji yasa su baffa suka roqi alfarmar abasu amaryarsu suwuce da ita don tuni suka zo da motocinsu k'waya biyar da za'a d'aukar amaryar, ko kad'an baba bazasu iya yimasu musu b saboda tsananin girmama juna da sukeyi don haka sukace abasu mintuna ashirin za'a fito da amaryar su baffa nata godiya tare da yaba karamcin da suka yimasu... *_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ˜­_* [7/1, 11:24 AM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___19πŸ’Ž Cike gidan yake maqil da 'yan uwa da abokanan arzik'i na nesa dana kusa da suka zo taya umma da baba murnar aurar da 'yar tasu tilo, duk wanda ka kalla awajen kasan cewa cike yake da tsantsar farinciki saboda yanda fuskokinsu ke d'auke da annuri anata gudanar da buki wan shagali. Fuskar baba cike da fara'a ya shiga cikin gidan bakinsa d'auke da sallama yana rarrab'awa ta gefe gefe saboda yanda gidan yacika maiqil da 'yan buki sai faman shiga raha akeyi wasu na shiga wasu nafita, duk inda yabi sai faman gaishesa akeyi ana tayashi murna tare da ALLAH sanya alkhairi, da qyar ya samu ya shiga ciki had'e da nufar wani d'aki da suke ajiye kayayyaki aciki yasa wata tobashiyarsa ta kirawo masa umma dake can tsakar gida tasha adonta cikin wani had'ad'd'en leshi wanda saika duba da kyau zaka iya gane itace, yajima zaune cikin d'akin yana tunanin shikenan yau zai rabu da 'yarsa tilo da yakeji har cikin qoqon ransa kafin umma tasamu takuccikke daga baqin dake dad'a shigowa tanufo inda take, a jigace tashigo cikin d'akin tana fad'in, "ai sai kuyi babu wanda zan sake d'ebowa abinci in zaku tashi kuje kud'ebo da kanku ku tashi, ai Kuma 'yar takuce bani kad'ai nahaifeta ba balle kubarni da aiki, don haka ni nagaji bazan qara yimaku wani abunba, shikenan daga kara saiku barni da aiki." Murmushi baba yayi yana kallon fuskarta sannan yace, "haba uwar amarya, wannan irin fad'a haka da kikeyi halan keda wa." "Nida matan balarabe mana, su daya dace ace suke tarbar baqi suna kai masu abinci shine sunka koma gefe kowace ta hakince sai kace tukane suna kiran akawowa wance da wance abinci, sun barni ni kad'ai ke hidimata sai kuma fareeda 'yar wajen yaya maryama." STORY CONTINUES BELOW "A'a'a to wannan maganar tafi qarfina tsakaninki ne da qannenki ba Mai shiga tsakani, ni dama zancen kai amarya ne yakawoni kinga gari ba guda ba.." kafin yaqarasa tayi saurin cewa, "To ai sai anyi sallar la'asar za'aje ko kuwa?" "A'a, bayin ALLAHn nan sun roqi alfarmar abasu amaryarsu su wuce da ita don gaba d'aya suka zo d'aurin auren tare da motocin d'aukar amarya, don haka kishiryata in sha ALLAH yanzu zasu wuce da abussu" "Amma malan bamuga 'yan biko ba haka zamu miqa masu ita kamar..." "Haba maman Rashida kada kice komai da yanzun da anjima duka d'aya ne, kuma shi biko ai al'adace ba addini ba don haka kiyi hak'uri tunda har iyayensa maza sukayi magana tamkar sun turo bikon ne, aje ashiryota gamunan muna jiranta muyi mata hud'u ba sai suwuce." Jiki a sanyaye umma tafita tamkar wacce k'wai ya macewa a ciki, duk tsawon kwanakinna bata tab'a d'aukar cewa tabbas zata rabu da 'yar tata ba sai yanzu, cikin k'arfin hali tanufi d'akin da Rashida ke ciki kwance tana kuka bayan andawo da ita wajen wanka ita da 'ya'yan malan balarabe qanen mahaifinta su uku, sunyi lallashi har sun gaji sun qyaleta suna ganin umma tashigo duk suka mik'e suka fita, dai dai wajen kanta umma taje ta zauna tare dasa hannuwa ta d'ago kanta, cikin kuka tafad'a ajikinta tana sheshheka, ko kad'an umma ba tayi yunqurin hanata ba domin itama kanta kukan ne yazo mata, saida sukayi mai isarsu sannan cikin muryar dattako umma tafara yimata magana har lokacin tana jikinta. "Rashida kuka bai kamaceki ba, domin wannan ranar farinciki ce agareki da kuma mu iyayenki da Allah yabamu ikon ganin mun sauke d'aya daga cikin haqqoqanki daya d'ora mana kuma ranace da kika dad'e kina jiran zuwanta don haka kinatsu ki saurari abunda zan fad'a maki amatsayina na mahaifiyarki." Share hawayen da suka sake zubo mata tayi sannan tasa hannuwanta ta tallafo fuskarta tana share mata qwalla had'e da cewa. "Rashida! Ina so kibud'e kunnuwanki kiji abunda zan fad'a, gidan aure da kike gani ba wajen zaunawa kace zaka huta bane ko kace kayisane don kasuwanci, wajene na gwaggar maya don meman lada da kuma aljannarki, shi gidan miji wajene da zaki jajirce wajen nunawa duniya nagartar gidanku da kuma ahalinki, duk wata kima da darajarki annan ne zaki tabbatar da ita ta hanyar nuna kamalarki ga ahalinda zaki riska ku zauna dasu, mijinki shine aljannarki kuma shine farincikin ki na duniya da lahira, haquri da kike gani shi ginshiqine na tabbatuwarki isashshiyar mace awajen mijinki, shi kuma ladabi da biyayya sune zasu zamo maki tubalin da zai mai dake kasaitacciyar mace awajen mijinki, girmama iyayensa abune da zai qara maki kwarjina da tarin soyayya azuciyar maigidanki, kauda kai kuma da iya dad'ad'an lafuzza ga 'yan uwansa shi zaisa su soki har su zauna dake lafiya, kwanciyar hankalin da zaki bawa mijinki ita kuma jigoce ta yalwatuwar arziqinsa, kyautatawa da yin alkhairi ga mutane shizai jawo maki girmamawa ga manya da yaran da kike tare dasu, kiriqe ALLAH, ki guji abun hannunki, kibi mijinki kiyiwa mahaifiyarsa biyayya tamkar yanda kike yimani ga duk abunda bai sab'awa ALLAH ba, rashin kunya, tsiwa da sakin baki acikin mutane sukan xubarwa da mutum kima da daraja don haka ki nisancesu, Ina mai roqonki da duk k'arfin tsanani da wahala kada kid'aga harshenki akan na mijinki, idan son samune kada ki zalinci kowa kibari ke azalinceki da SANNU SANNU ALLAH zai yi maki sakayya, shi khairan da sharran duka 'yan aikene duk inda ka aikesu za suje kuma su dawo maka, kiyi k'ok'ari kishuka alkhairi don ki girbesa, kizama mai haquri da juriya sannan kizauna da kowa lafiya, kiriqi tsafta nasan kinada ita amma ki qara haka girki shima duk da bani da wani haufi akai amma ki kula sosai wajen kiyaye lokacin yinsa da wajen dafasa, banda almubazzaranci ko rashin yiwa miji godiya ga duk abunda yakawo, kiriqi addu'a da azkar na safiya da marece da lokacin kwanciya insha ALLAH zasu zamo maki fitila arayuwarki, ki guji fushin mijinki, ki nesanta da duk abubuwan da kikasan baya so ta hakanne zaki samu cikakkiyar natsuwa a gidan aurenki, Ina roqon ubangiji da yayi maki albarka, yakare mani ke aduk inda kika shiga ga sharrin mutum dana aljani, ALLAH ya albarkaci dukkanin zuri'ar da zaki samu ya kareki daga fad'awa ko wace irin fitinar rayuwa ta duniya da kuma lahira." STORY CONTINUES BELOW Duk da Rashida nacikin damuwar rabuwa da iyayenta hakan bai hanata jin dad'in lafuzzan mahaifiyarta ba agareta, gaba d'aya zuciyarta da kuma qwaqwalwarta sun gamsu da nasihohin data yimata kuma tayi alqawarin zatayi aiki dasu komai rintsi komai wuya, cikin sheshhekar kuka tace, "Amin ummata, zan kula da duk abubuwan da kika fad'a mun kuma nayi maki alqawarin zamowa mai tsananin haquri da yiwa mijinta biyayya tamkar yanda naga kinayi." Rungumeta umma tayi tana murmushi had'e d cewa, "A'a Rashida, bana so kiyi yanda kikaga inayi nafiso kiyisu fiye da yanda nakeyi kinji ko?." Cikin kuka tace, "In sha ALLAH, ummata zanyi, don ALLAH kiyafemun duk wani abu Dana yimaki, ummata Ina matuqar jin kewar rubuwa dake." Taqarashe maganar tare da naniqeta ajiki tamkar zata tsagata ta shige tana mai k'ara tsananta kukanta, "Rashida kenan! wake maganar yafiya anan bayan ummanki cike take da soyayyarki da kuma alfaharin samunki taya har za'ayi kiyi wani laifi kome qanqantarsa agareta kuma har yasamu muhalli acikin zuciyata?, Babu komai tsakanina dake face tarin d'inbin albarka da nake yimaki fata awajen ALLAH" cireta tayi daga jikinta sannan tamik'e taci gaba da cewa, "kije kishirya Rashida mahaifanki na jiranki a d'akin kaya kinji ko?." Tana gama fad'ar haka tajuya tafice daga d'akin, wajen qanwarta aunty marwiyya tanufa tayi mata magana akunne sannan tawuce wajen bak'in da suka shigo yanzu, da sauri ita kuma aunty marwiyya tashiga d'akin da Rashida take tasa ta tashi tashiga toilet tayo wanka da ruwan turarukka masu qamshi sannan tasa ta tsuguna saman turaren wutan da tana fitowa ta isko tahad'a mata, bayan yagama shiga jikinta tabata wani had'in madara daya sha kayan gyaran ni'imar jiki tace tashanye sannan tahau kimtsata yanda ya kamata, ba'afi mintuna ishirin ba sai gashi tafito da ita cikin had'ad'd'iyar shiga mai kyau da kuma d'aukar hankali, duk inda Rashida ta gotta sai zuba qamshi takeyi fuskarta a lullub'e, daidai lokacin malan balarabe yashigo cikin gidan yana fad'an afito da amarya anbar mutane zaune suna jira, ganinta yasa yayi shiru tare da nufar d'akin da d'an uwan nasa ke ciki suna jira, acan aunty marwiyya tanufa da ita suka shiga kan Rashida naqasa har lokacin tana zubar da k'walla, Saida ta duqar da ita agabansu sannan ita kuma tajuya tabar d'akin, naseeha sosai suma suka yimata sannan suka aika aka kirawo umma itama ta sake yimata wata sama sama, rungume baba tayi tana kuka mai tsima rai tare da roqonsa gafara nan take shima yaji kukan na nema ya kucce masa, da sauri yamiqe yana fad'in "nayafe maki Rashida ALLAH yayi maki albarka" ya fice daga gidan yana goge hawayen da suka zomasa, wajen umma tanufo ta sake rungumeta tana kuka umma ta dafa kanta had'e da cewa, "Kitafi gidanki cikin amincin ALLAH da kuma yardarsa Rashida, ALLAH ya albarkaci rayuwarki yakareki ga dukkanin sharrin shaid'an da kuma ahalinsa" tana gama fad'a itama tajuya tayi cikin gida tana hawaye. Aunty marwiyya ce tazo tarik'ata sai kuma yaya Maryam (yayarsu baba) dama tuni ansanar da 'yan bukin duk mai halin zuwa kai amarya ya gyara yanzu za'a kaita ba sai anjima ba kamar yanda aka tanada, Kai tsaye aka fiti da Rashida tana reren kuka yayinda suna isa bakin gida suka tarar da motar da aka tanada don amarya har anbud'e ana jiran isowarta, aunty marwiyya ta duqar da ita tana mai rad'a mata akunne cewa ta tashiga da _"Bismillah tawakkaltu alallah wala haula wala quwwata illah billah"_ Cikin zuciya tadinga karantota duk da kuwa kukan da takeyi na nema ya rinjayi zuciyar tata sannan sukuma sauran mutane suka shiga sauran motocin aka tayar, dama mota biyarce aka kawo takai amarya sai motarsu baffa sukuma tuni ana fitowa da ita sukayi musabaha da malan balarabe da kuma baba had'e da yin godiya suka wuce gaba, saida mota biyu tashiga gaba bayan tasu baffa sannan wadda rashida keciki tabi bayansu sannan biyun suka bi bayanta suma, wani irin kuka mai tsimarai Rashida keyi tana nazarin kalmar da akoda yaushe take d'auka mai sauqi wajen furtawa (aure nake so) wacce gaba d'aya bata natsu wajen fahimtar kome take nufi ba sai yanzu da aka rabata da iyayenta, tabbas tana farincikin samun muradinta da kuma auren amma rabuwa da iyayenta gaba d'aya ya shamakance ta da bayyana wannan farinciki, tafiya mai d'an nisa sukayi kafin su isa garin bebeji lokacin har anfara kiraye kirayen sallar magrib amma koda suka isa dandazon yaran shiyar dake qofar gidan suna ihun ga amarya bazai bari kaji sautin kiran da akeyi ba, motar da take ciki na tsayawa gabanta ya fad'i da sauri tafad'a jikin aunty marwiyya tana kuka, STORY CONTINUES BELOW "A'a Rashida wai kukannan naki bazai qare bane? Yakamata kiyi hak'uri haka domin duk wata d'iya mace dake gidan mijinta saida ta fuskanci hakan." A hankali ta tsagaita kukan sannan yaya maryam tarik'ota tafito daga cikin motar tana fad'in kiyi addu'ah _"hazbunallahu wani'imal wakeel"_ Rashida tafad'a acikin zuciyarta kafin ta azo qafarta tafito daga cikin motar fuskarta a lullub'e, ihu yara suka hau suna fad'in, "yeeee.. amarya, amarya, ke kicce kinaso da bakice kina so ba da ba'a baki shiba." ahankali suke tafiya da ita tamkar k'wai har sukazo bikin k'ofar shiga gidan, qafarta ta dama ta aza tana karanto addu'ar " _"Allahummah inna naj'aluka fi nuhirihim, wana uzu bika min shururihim"_ ma'ana (ya ALLAH! mu muna sanya ka a gabansu, kuma mina neman tsarinka daga sharace sharracensu.) sosai taji tasamu 'yar natsuwa daga ynayin da takeji suka shiga da ita, cike da farin ciki Yaya balkisu ta tarbesu hannu biyu ita da sauran 'yan uwa dasu kareema 'ya'yanta suna "sassannuku da zuwa, ku wucikke, masha ALLAH, kuwucikke da ita nan." Ana nuna masu shiyarta wacce koba tambaya kasan b'angaren amarya ne, suna tsaye kafin su shiga suka jiyo muryar matar baffa Ali tna fad'in, "To mudai gidannan bamu da bare sai yanzu, ALLAH kasa ba'a d'ebo mana miyagun dangi ba.." kafin wasunsu su ankara da abunda tace inna bilkisu tace dasu "kuwucikke mana kun bar mana amarya tsaye kada qafafuwanta suyi ciwo." Murmushi aunty marwiyya tayi had'e da cewa "A'a muna jiran agwada mana sashen uwar mijin tatace mukaita wajenta tukuna." "Ahaf illar bare kenan komai nasa daban yake, To mudai ba haka mukeyi ba anamu al-adar, kufara shiga da ita d'akinta tukuna sai tafito da kanta tagano d'akin uwar mijin nata donmu auna hankalinta, mu haka mukeyi inyaso ku kwa jirata anan har tafito" suka sake jin matar baffa Ali dake can bakin k'ofar d'akinta zaune saman wata kujera tafad'a tana tamnar cingwam, cikin sakin fuska Yaya Maryam tajuyo had'e da cewa. "To kuyi hak'uri tunda har bare nada wata illa Kuma ahaka kuka gani kukace kuna so, kuma mu al'adarmu zamubi ba taku ba tunda bare muke." Wani irin dad'i inna bilkisu taji da amsar da Yaya maryam taba matar baffa Ali kafin tace dasu "kuwucikke ga shiyarta can" tana murmushi ta wuce gaba suka bi bayanta, sallama sukayi Yaya hawwa nakwance saman gadonta d'an bono tana jinsu fiye da minti biyu Amma bata msa ba balle ta taso hakan yasa inna bilkisu leqawa taciki tana fad'in. "Assalamu alaikum Yaya hawwa ga bak'i nan sun iso." Tana qoqarin shiga ciki, wata irin tsawa Yaya hawwa ta dakawa inna bilkisu da tasa saida Rashida tazabura had'e da rik'e Yaya Maryam tana fad'in, "Kul! kada wanda ya sake ya shigomun d'aki, bak'i ai nakine don haka kiyi qoqari ki karramasu ki zame mata uwar miji hakan zaisa nasan cewa ked'in 'yar kanzagice lamba d'aya." Shiru bilkisu tayi tanaji kamar ta zubar da kwallah saboda walaqancin da yaya hawwa tayi mata agaban mutane gashi tayi alqawarin bazata sake kula ta kanta ba balle tamayar mata da magana daidai yanda tayi mata, murmushin dake cike da takaici tayi tare da juyowa tana kallon 'yan kawo amarya da sukayi cirko cirko suna sauraren ikon ALLAH, cikin qarfin hali tace, "Kuyi hak'uri kuzo muje akaita d'akinta ga motocican suna jiranku naji sunata faman yimaku oda" taqarasa maganar tare da juyawa tana qoqarin b'oye damuwarta. Adai dai bakin k'ofar shiga sashen Rashida inna bilkisu ta tsaya, sunaji matar kawo Ali ta tintsire da dariya tana fad'in "Yaya hawwa tayi tsiyar kenan ko bilki." Had'e da tuntsirewa da wata dariyar, gab d'ayansu babu wanda ya tankata suka wuce ciki bakin Rashida d'auke da addu'a jikinta har wani rawa yakeyi sannan tashiga haka lokacin da zata shiga d'akinta har ta aza qafa aunty marwiyya tadawo da ita baya had'e da aza qafarta ta dama tace, "kiyi bisimillah da ayatul kursiyu, sannan ki karanta _allahummak finihim bima shi'ita_ (ya ALLAH ka isar mani su da abinda kaso) don wannan gida da kike gani sai kinyi hak'uri, baiwar ALLAH nan kad'aice nagani da alamaun mutunci." STORY CONTINUES BELOW "Marwiyya menene haka!" Yaya Maryam tafad'a tana kallonta, "Hmm Yaya Maryam kenan! Wlh tunanin abunda zan barwa yrinyarnan yasa nakasa tankawa da wllh tundaga waccan angulun har uwar mijin tata saina yimasu wankin babban bargo." "Ya isa haka marwiyya ALLAH yakyauta." Lokacin Rashida tagama addu'arta sannan suka shiga, nan kallo yakoma cikin d'akin don ba qaramin k'ok'ari baba yayi ba, hatta tv da vedio da fridge duk saida yasa aka sakawa Rashida, komai yayi kyau gwanin burgewa, nasiha suka sake yimata da tayi taka tsantsan da sha'anin mijinta da kuma duk wani abu da zai had'ata da mutanen gidan don kaucewa rashin mutunci sannan sukace tarik'e inna bilkisu hannu biyu ta d'auka 'yar uwarta ce da zata dinga magance matsalolinta kafinsu don sun yaba da halinta, daidai lokacin inna bilkisu tashigo sashen ita da 'ya'yanta salame da kareema d'auke da ledojin ruwa dana muhallip da kuma wani kwali babba dake cike da tarkacen biskit da mintuna da cingwam wanda bafffane ya aiko dasu yace abawa 'yan kawo amarya, sake gaggaisawa akayi ta sake basu hak'uri bisa abunda yafaru sannan ta basu kayan, cikin jin dad'i sukayi godiya sannan yaya maryam tace. "To bilkisu ga amanar Rashida nan mun baki, duniya da lahira mun amince kiyi mata hukunci daidai yanda kike yiaw 'ya'yanki idan tayi ba daidai ba, mun baki amanarta ki kula da ita batada kowa saike don ke muka sani yanzu, Rashida qaramar yarinya ce da hankalinta bai isa banbance daidai da rashinsa ba don haka kiyi mana taimakon d'orata akan hanya aduk lokacin data kauce, mungode mungode sosai, ALLAH yasaka maki da alkhairi kuma yabaku haqurin zama." "Amin nagode nima, karku damu da abunda yafaru sharrin shed'annne kunsan halinsa la'ananne ne, dukkaninmu abu d'aya muke kuma in sha ALLAH zamu kula maku da amanar Rashida domin itama 'yar muce." Sosai su aunty marwiyya sukaji dad'in kalamanta kuma sun samu 'yar natsuwa akan d'azu, mik'ewa sukayi da zimmar fita don tuni sauran mutane da yaran sunfita sukad'ai ake jira Rashida tarik'esu tanata kuka, duk qarfin zukatansu suma saida suka zubar da kwallah saboda tausayinta, so suke sutafi amma tariqesu gam saida su kareema sukazo suka b'anb'areta ajikinsu sannan, riqeta sukayi suna lallashinta su kuma suka wuce inna bilkisu na biye dasu kowacensu na k'walla, Suna fitowa matar baffa Ali ta toshe hanci had'e da rangad'a uwar gud'a tana fad'in, "wayyo duniya budurwar wawa, wai iyayen amarya da kuka wannan ai anyi abun kunya, koda yake qila amaryar tasu ta gagara yi abunka da yaran zamani shine su suka yimata." Wucewarsu sukayi suna tir da halin fitinanniyar mat irinta inna balkisu nata basu hak'uri har bakin k'ofar gida, sunaji tana fad'in. "Munafucci dodo akan wasu yake qarewa" Wanda bako shakka sunsan da inna balkisun take... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/3, 11:01 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___20πŸ’Ž Bayan sun tafi Inna bilkisu tadawo tare da tsayawa tsakar gidan saitin da matar baffa Ali ke zaune ta rangad'a wata uwar gud'a tana fad'in. "Alhamdulillah ALLAH kaine abun godiya, ita dai hassada ga mai rabo takice kuma duk hassadar mai hasada bai isa ya canza abunda ALLAH ya qaddaro ba sannan shi son kai baya tab'a kai mutum ga nasara, sannan kuma tabbas shi naka sai naka amma dad'in zama sai bare, yarinya dai tashigo gidan mijinta kuma ko ba'aso dole akirata da matar Nuraddeen, uwar gidansa kuma uwar 'ya'yansa suruka a wannan gida, masu had'e had'e da kuma qulle qulle sai su canza dabara domin ruwa kam ya riga daya qarewa d'an kada..sai ayi sauri acanza dabara, yarinya dai ALLAH ya mallaka mata Nuraddeen a matsayin miji domin shi tariqe tun farko kuma shi zai tayata fad'a su ko 'yan baqinciki sai dai su mutu don nagaba yariga da yayi gaba." STORY CONTINUES BELOW Tana gama fad'ar haka tawuce d'akinta tana jin wani sanyi aranta, koba komai tasamu zuciyarta ta rege nauyin da tayi mata akan maganganun da suka ta cab'a mata ita da Yaya hawwa. Wani irin mugun ashar matar Baffa Ali ta lailayo mata had'e dayin kukan kura tanufi wajen qofar d'akinta tana rafkar mata gambu. "Bilki, Bilki, Bilki tsakanina da ALLAH tun wuri ki kama kanki ko in tata maki rashin mutunci, ki kama bakinki kafin inyi maki wankin babban bargo agidannan, yo da kike zancen ruwa ya qarewa d'an kada ai bakiga k'arshen wasan ba, in dai nice ruqayya matar Ali gadanga tunda kika shigarmun hanci wlh saina nasa zaman gidannan ya gagare ki dake har 'yar koron taki da aka kawo, kwad'a yayyiyar banza da wofi anga yarinya masu maiqo shine za'a maqale mata, to daga ke har ita sai nasa kun kuka da kanku." Tana gama fad'a ta banka gambun qofar da qarfi cike da jin haushin rashin tanka mata da batayi ba tajuya tabar wajen, Yaya hawwa najinsu daga kwancen da take taja tsaki had'e da cewa. "Sakarkarin banza duk kuyi ku gama zan dawo takanku, don da d'ai d'ai zanyi maganinku acikin gidannan." Ita dai Rashida tun tana kukan har ta dangana ga ALLAH tayi kwancen tana tunanin wannan sabuwar rayuwar da zata fara a d'aya b'angaren tana sauraren firar dasu salame da kareema keyi, muneera ce tafad'o cikin d'akin ko sallama babu tayi tsaye qiqam tana raba idanuwa batare da takalli wud'anda ke wajen ba da alama itama rashin mutuncin tazoyi saboda yanda take bud'ar hanta, sudai su salame na kallonta basuce da ita uffanba ta rab'a tagefensu tanufi uwar d'akin, kallon kareema salame tayi ta d'auke fuskarta tana kallon muneera dake qoqarin hankad'a labulen ta d'aure fuska had'e da cewa, "Ke malama Ina zuwa?" Juyowa tayi cikin ba'acin rai itama had'e da cewa "to sa'idanawa masu barci da ido d'aya Ina ruwanku da inda zani, Ina dai amaryar nan ba 'yar uwarku bace balle kuce zaku hanani shiga" "Bashi aka tambayeki malama ba, amsa zaki bamu ba rashin kunya ba don kinsan nan gidanta kika zo" kareema tafad'a a tsattsaye, tsaki muneera tayi had'e da kutsawa tashiga cikin d'akin Rashida na kwance saman gado fuskarta lullub'e da mayafin da aka rufo mata tasa hannu ta yayeshi da qarfi, da sauri Rashida tamiqe zaune tana kallon muneera dake riqe da mayafinta data cire, idanuwa muneera ta qura mata tana kallon gashin kanta daya zubo har gadon bayanta sanadiyar jawo mayafin da tayi ribon d'in ya cire, kyakkyawar fuskarta ta qurawa Ida kafin can kamar an tsunkureta ta zabura had'e da cewa, "Au yihakuri fa na manta ke amarya ce Saida lallab'awa.." mere baki tayi sannan tafara takawa tana qarewa d'akin kallo kafin ta maido hankalinta gareta, "Dama kece ya nurana keso? kece ya zab'o a matsayin mata bayan yasan Ina qaunarsa, dama kece kika zamo katangar data shiga tsakanina dashi Kuma har kika datsemun duk wani mafarki da kuma burin mallakarsa dana dad'e inayi, kika wargazamun farinciki tare da sani zubar da k'wallah acikin kowane dare?, Hmmm to kinyi kuskure yarinya a wud'annan qananan shekarun naki baki kai matsayin da zaki mallaki ya nura naba kuma na hak'ura, domin na d'au alwashin shid'in mallakina ne ni kad'ai, kid'auka wannan auren jeka nayi kane kukayi saboda dole kirabu dashi ko kina so ko bakyaso, mallakina ne shi Kuma ki kalleni da kyau kigani nice daidai shi saboda nid'in 'yar uwar sace kuma jininsa don haka d'an uwa sai d'an uwa badai bare ba."+ Taqarasa maganar tana wani kallon sama da qasa irin ita wayayyiyar nan , sai alokacin Rashida ta d'ago kai cikin mamaki tana qarewa muneera kallo wacce tun shigowarta data kalleta ta aza itama cikin matan gidanne saboda yanda taganta ajeme cikin wata kod'ad'diyar atamfa wacce duk da itama a qauye take bazata iya ko gugar leda da ita ba, sak kamar muneera irinta 'yan matan qauyennan ne da suka jima basuyi aure ba ga wasu uban qassan wuya da suka taso mata fuska cike da jar foda, kallo d'aya zakayi mata kasan cewa ba yarinya bace zata kai shekaru 20 aduniya ga matsalar qauyanci da rashin wayewa da suka taru suka sake jemeta waje d'aya sai kace wacce tashekara aru aru d'in nan, watanni ne tsakaninta dasu kareema wanda hakanne yasa babu wata girmamawa tsakaninta dasu sai reni, shiyasa da sukayi mata magana bata sauraresu ba hakan yasa salame tamiqe taje d'akinsu ta d'auki wayarta takirawo Nuraddeen ta sanar dashi abunda ke faruwa dama yana bakin gida baiyi nisa ba sai gashi ya shigo da sauri, yana shiga kareema na qoqarin shiga uwar d'akin saboda yanda taji tana yab'a mata maganganu da sauri yariqo hannunta yace tawuce, abakin qofar shigowa taci karo da salame tadawo zata shiga tariqe hannunta tana fad'in. STORY CONTINUES BELOW "Muje salame ai yayan yadawo, barta dashi." Wucewarsu d'akin mahaifiyarsa da tagama had'a masu 'yan abubuwan da zata basu tana fad'a suzo suwuce gidajen mazansu dare yayi don har ankira sallar isha'i, nan suka fara bata labarin abunda kefaruwa tace. "Hmm! ALLAH dai ya kyauta, Amma ni wlh har yarinyar nan tafara bani tausayi, koni nan dana girmeta nesa ba kusa ba ya naqare da matsalar Yaya hawwa da ruqayya da kuma rashin kunyar yaransu inba Nuraddeen da Yusuf ba, sukad'aine nake jin sanyinsu amma kaf gidannan babu wanda keda ragi, sudai iyaye kishi suke dani gashi kowacenmu da mijinta balle ace ai saboda haka, sukuma yaran iyayen ke lalatasu shiyasa Amma banda haka har ina za'ace muneera ta isko matar yayanta tana yimata rashin kunya, zumuncine da yariga ya lalace saidai ALLAH ya kyauta." "Hakane inna, amma kema da alifinki? Kidena biye masu balle shiga harkarsu, inaji d'azu kin dawo kina maidawa Inna ruqayya da maganganu ai kinga hakan bai dace ba, ka kyale mutum duk abunda zaiyi tunda dai kasan adoke bai isa ya dokeka ba amma saikiyita biye masu ana fitina." Kareema tafad'a ranta a d'an b'ace, shiru Inna Bilkisu tayi tana nazarin kalamanta don tasan gaskiyane tafad'a kawai dai abun da ciwone shiyasa bazaka iya haquraba wataran, muryar salame taji itama tana fad'ar. "Eh Inna ALLAH gaskiya kareema tafad'a don ALLAH kidena biye masu, kinsan abun fad'i agarinnan baya k'arewa, kuma mu kece mutuncinmu da kimarmu agidajenmu, da wani abun yafaru agidannan akaji dasa bakinki ba zamuji dad'i ba, don ALLAH kiqara haquri dasu wata rana sai labari" "Shikenan, ALLAH yaganar damu kutashi kutafi" tabasu amsa atak'aice. Acan sashen Nuraddeen kuwa tsaye yana qoqarin shiga yaji maganganun muneera sun dakar masa kunne a lokacin da take cewa d'an uwa sai d'an uwa badai bare ba da sauri ya qarasa shigi ciki tare da fizgota ya jefota falo yana fad'in "uban waye ya fad'a maki d'an uwa sai d'an uwa, itama yanzu 'yar uwace awajenmu tunda na aurota na kawota a gidan nan don haka maza kifice kibani waje ko in tattaka ki awajennan wawiya kawai da bata iya magana ba" turo baki tayi tana susar kai had'e da cewa, "Kai ya nura nizaka yiwa walaqanci akan wannan 'yar yarinyar.." kanta yayo da gudu tafita ta tsaya bakin qofar d'akin tana cigaba da fad'in "Wlh ALLAH ya nura ni bazan yarda ba ai kasan ina sonka sosai shine kaje ka auro wannan abar.." Bata rufe baki ba cikin tak'a biyu ya cimmata a bakin qofar d'akin had'e da sakar mata wani mugun rank'washi akai, ihu ta saka tare da dafe kanta tabar shiyar aguje tana kuka, rumfar d'akinsu ta shige tafad'i qasa tana murje murje da qafafuwa tana wayyo Inna zai kasheni, aguje tafito d'akin tanufi wajenta yanajin haka ya koma Uwar d'akan Rashida na zaune a gefen gado kanta qasa idanuwanta na zubar da hawaye, durqusawa yayi a gabanta tare da tara hannusa hawayen dake neman saukowa daga idanuwanta suka sauka akai, cikin rashin jin dad'in abubuwan da suka faru yace, "Habibty kuka kikeyi?" Shiru tayi tare dasa hannunta akan hanci taja majina sanna a hankali ta d'ago kai tana kallonsa, ganin yana qoqarin saka idanuwansa acikin nata yasa tayi saurin maida kan qasa, magana yaci gaba dayi cikin tattausan lafuzza, "Habibty kidena wannan kukan bana so, akwai basosa masu girma da kike bina wajen rarrashin zuciyarki daga abubuwan da nine silar data b'aci har ta tinzira kyawawan idanuwannan naki fitar da wud'annan tsadaddin wayen, kiyimun afuwa kada kisa zuciyata tayi mani tsattsauran hukunci akan haka, kinfi kowa sanin tarin qaunar da nakeyi maki azuciyata saboda haka gada kibari shaid'an da sharrin zuciyar wasu yasa maki kokwanto ko wani shakku akaina, muneera yarinyar baffa Ali ce, tana matuqar sona amma ban tab'a jin qaunarta azuciyata ba shiyasa tazo tana maki wannan haukar, kiyi haquri daga yau nayi maki alqawarin bazata sakeba kinji?." Saida ta share hawayen da suka jiqa mata fuska tana sake jan majina sannan tace "Amma meyasa ka aureni bayan kasan tana sonka.?" STORY CONTINUES BELOW "Saboda ke kad'ai nakeso habibty, ke kad'aice keda mallakin dukkanin wani sansani dake cikin zuciyata, gangar jikina, zuciyata da Kuma rouhina duka mallakinkine babu wani qanqanen fili daidai da k'warar zarrah da zan iya baiwa wata aduniya, Wannan dalilin shiyasa ban aureta ba." "Amma ai 'yar uwarka ce, inaga kamar ita tafi dacewa ka aura." Murmushi yayi tare da kamo hannuwanta biyu ya riqe yana murzawa a hankali yace. "Idan ita 'yar uwatace ke Kuma rayuwa tace habibty, shin da d'an uwa da rayuwa wayafi dacewa ace mutum yariqa da kyau da kuma muhimmancin da zai zamo masa abokin zama" "Rayuwa mana" Ta furta ahankali tana murmushi, murmushin shima yayi had'e dasa yatsa ya lakutar mata hanci yana fad'in "Gud gel" Da sauri tasa tafin hannayenta tarufe fuskarta, "yawwa bari naje nadawo yanzunnan kinji habibty, kada kisake kuka daga wannan lokacin saboda yau ranar farinciki ce agaremu." Kad'a masa kai tayi sannan yafice daga d'akin bayan ya d'auki makullan shiyar tasa dake gefen bedside d'inta, yana fita yajawo qofar yasa makulli had'e da juyawa zai bar gidan, yanaji Inna ruqayya matar baba Ali na zage zage harda fad'in. "Lallai nura ya lalace yanzu ya dakeki akan bare, kina 'yar uwarsa zai walaqantaki akan matarsa lalle dole Yaya hawwa tasan abunyi, ke ya dokeki?" Tasake nana tawa tana d'agowa muneera kanta, murmushi yayi tare da kad'a kai sannan yawuce abunsa, ita kuma tab'are baki tare da nunawa inna ruqayya tsakiyar kanta, "Yishiru taso muje wajen yaya hawwa, wlh yau sai ranar nan tazamo masu ranar bak'inciki, yishiru nace maki" taja hannunta suka nufi sashen Yaya hawwa lokacin tana zaune bisa abun sallarta Bata dad'e da gamawa ba, kukan muneera da taji yasa yasa tayi tsaki tare da ajiye tasbahar hannunta gefe kai kace tasan ALLAH tana tofe addu'a had'e da shafewa a fuska. "Ke.ke. lafiya aka zomun qofar d'aki ana mani reren kuka sai kace munafukar amarya!." Tafad'a tana lunke sallayar had'e da komawa saman gadonta zata kwanta, "A'a Yaya ai kwanci bai ganeki ba saboda waccan itace munafukar amaryar da naji kina fad'i, fisabillahi ace daga kawo yarinya yau har tajawa yarinyarnan duka awajen d'an uwanta don tana muna fuka...zonan nuna mata inda ya dokeki muneera don bazan yarda ba." "To sakaryar uwa mai malalaciyar 'ya yanzu akan d'an rank'washin da yayi mata akai zaki zomun kawo qara don rashin mutunci ko nace takakka." Yaya hawwa tafad'a tana kallon Rashida da tawani duqo Kai tana nuna mata da yatsa tanaci gaba da reren kuka "ke dallah rufemun qaton bakinnan naki kamar rijiya kona ci ubanki, ca nake uban waye yakaiki shiyarsa har ya rankwasar maki kai." turo baki tayi tana susar kai had'e da cewa. "To ba amaryar naje gani ba, shine nake jamata fad'amata ni 'yar uwarsa ce Kuma ni nake sonsa..." Bata k'arasa ba Yaya hawwa ta kwatseta tana fad'in "maza fitarmun d'aki shashasha mai gwalmammin qafafuwa ke kuma da bakisan abunda kikeyi ba kika kwasota kuka iskeni ko yanayin da nake ciki bakya tunani ke tama 'yarki kikeyi, to idan kinfita kijamun qyaurena zanyi lokacinsu su kuma." "Amma Yaya hawwa ya zakiyi mani haka?" "Kije kafin dukkanin damuwata taqare akanki rakkiya." Afusace tafita tare da rafko qofar d'akin tana suruttai jar ta iso shiyarta, tun tana tsammanin wani zai tankata har tagaji tahaqura saboda rashin samun wanda ya kulata. ••• ••• ••• Acan b'angarensu umma da baba kuwa tun cikin mota yaya Yaya maryam ta gargad'i kowa akan kada atada zancen abunda yafaru saboda kada atayarwa mahaifiyarta da hankali, haka da akazo qofar gida saida tasake gargad'insu, kasancewar itace babba yasa kowa kama bakinsa aka shiga ana fatan Allah yasanya alkhairi, aunty marwiyya kuwa da zata tafi Saida tacewa umma "to aunty bawai kinnrabu da 'yarki ba Kuma shikenan, a'a tashi tsaye zakiyi wajen yimata addu'a da nema mata kariya wajen ALLAH daga sharrin miyagu da mahassada." Gaban umma ne yafad'i tace. STORY CONTINUES BELOW "Marwiyya injin dai ko lafiya kika fad'i haka.?" "Lafiya klw aunty kinsan dai halin gidan yawa dole baza'a rasa gutsiri tsoma aciki ba, amma babu komai." Wata ajiyar zuciya umma ta sauke duk da dai bata natsu da amsar da tabata ba had'e da cewa. "Shikenan marwiyya, Allah yatsare da tsarewarsa amma addua'a dama ai baza'a dena ba, ngd sosai Allah yabar zumunci, ki gaida mun da alhaji." "Amin aunty zaiji in sha ALLAH, ALLAH yahutar da gajiya." "Amin seda safe a gaida yara." Tunda tafita umma taji ta kasa samun natsuwa har baba yadawo, cikin gajiya had'e da nuna kasalar dake tattare dashi yafad'a gefen gado yana fad'in. "Wayyo ni bawan ALLAH." Murmushi tayi jiki a sanyaye had'e da mik'ewa takoma ta gefensa ta zauna tana d'an mammatsa masa k'wandunansa, "Sannu da hidima malan." "Sannu mamn Rashida ya gajiyar taku hidimar.?" "Alhamdulillah, saidai Ina matuqar kewar yarinyata sosai." "Naga hakan atattare dake amma ya zamuyi tunda ita mace dama 'yar gidan wani ce, ni kaina ina kewarta sosai, ki kwantar da hankalinki addu'armu kawai itace ubangiji ALLAH yabasu zaman lafiya." "Amin ya gaffar." Tafad'a tana goge 'yan qwallan da suka zomata. ••• ••• ••• Nuraddeen nafita yanufi wajen masu saida naman kaji dana rago ya siyo namansa na kaza sannan yasa akayo masa d'aurin naman rago guda biyu, da gorar fresh yaghouth guda biyu, uku wajen baffa yanufa ya kaimasa qulli d'aya sannan yanufi sashen Yaya hawwa bakinsa d'auke da addu'a, tura gambun yayi ahankli daga can kwance tace "Waye?" "Innar mu nine yafad'a yana qarasowa cikin d'akin, gefe ya zauna tare da gaisheta ta amsa daga kwancen da take batare da ta taso ba, shiru yayi na mintoto kafin yace "Innar mu ga wannan?" Ya ajiye ledar abakin gadon, "ALLAH amfana." tafad'a tana qyaren d'ayar ledar dake hannunsa, "Saida safe innarmu." Yafad'a tare da miqewa ya nufi qofar fita, har ya aza qafarsa tace, "Miye wannan a d'ayar ledar?" Shiru yayi yakasa Bata amsar don baisan me zaice mata ba, "Dawo itama ka ajiye." "Innar mu.." "D'auka duka biyun ka b'acemun da gani" tafad'a a fusace, cike da mamakin mahaifiyar tata ita dako bud'a abunda ya kawo mata batayi ba amma tace a ajiye mata duka, duk ya zatayi dasu, dawowa yayi ya ajiye ledar sannan yace. "Kiyi hak'uri innar mu seda safe" sannan yafice kamar zaiyi kuka, gashi gaba d'aya duka kud'in ya kashe naira d'ari biyu kacal ta rage masa, tsaye yayi bakin rumfar yana tunanin yanda zaiyi ya samu wasu kud'in gashi abokanansa duka sun shige Kuma bazai iya iske baffa yace masa yabashi kud'i ba bayan duk wannan jidima daya yimasa, yanke shawarar zuwa ya siyo naman d'ari biyun yayi ko kuma idan abule Mai naman ya amince ya karb'i bashi har gobe don bazai iya koma mata babu komai a hannu ba, daidai ta wajen d'akin baffa zai wuce yaji yakira sunansa, shiga yayi had'e da cewa. "Gani baffa lafiya." "Lafiya klw Nuraddeen, wai wannan tsumuiniyar da kakeyi ta lafiya ce kabaro yarinyar mutane ita kad'ai zaune, daga Ina kake yanzu kuma Ina zakaje?." d'an sosa kansa yayi had'e da cewa, "Daga wajen innar mu nake baffa yanzu zan dawo bajimawa zaniyi ba." Yaqare maganar yana kallon agogon hannunsa saboda lokacin tashin abule ya kusa, daga cikin idanuwansa da Kuma yanayinsa baffa ya fahimci komai, aransa ya tabbatar da cewa Yaya hawwa tayi tsiyar don zata iya komai don ta quntata masu awannan ranar, "tashi katafi" yafad'a yana mai addu'ar ALLAH yaganar da ita, har zai fita sai Kuma baffa yace, "Yawwa Nuraddeen zo d'auke ledar nan naman nan yayimun qarfi bazan iya ciba." "Amma baffa mai taushi nace yasa maka bansan ya akayi yasa mai qarfi ba." "To nidai naci d'aya hakanan ALLAH yayi albarka d'auka katafi dashi." d'auka yayi don yasan halinsa baya son gardama yaji yace. "Had'a da madarar nan tayimun sanyi sosai naga har qanqara gareta, gobe kasiyomun fura da nono nafi gane masu." Shiru Nuraddeen yayi don yagama fahimtar mahaifinsa ya gano komai shiyasa yayi haka, "Baffa ka ajiye ko zuwa gobe sai asake dafa maka, ita madarar Kuma dama kamar nono take tahuce sai kasha." "A'a d'auka tafi dasu nace maka" dole ba yanda zaiyi ya d'auka had'e da yimasa saida safe ya fice, baffa na kallonsa ya koma cikin gida batare da ya fitar daya tashi yiba, murmushi yayi yace, "ALLAH ya kyauta sannan ya komawarsa ya kwanta, sashensa yabud'e ya shiga tare da karanta addu'a ya rufe. Koda ya shiga ya tarar har tayi bacci ya ajiye ledar hannunsa had'e da nufar inda take kwance da alama sallolin magrib da isha'i tagama bacci ya d'auketa, hannuwansa yasa ya tallabota tare da cire mata hijabinta ya dinga hura mata iskan bakinsa a fuska, ahankali tafara bud'e idanuwanta suka sauka saman fuskarsa ai kamar wacce aka mintsila tayi saurin zamewa daga hannunsa tana tattaro hijabinta tana rufe jikinta, murmushi yayi daga duqen da yake tare da cewa "tashi muje ki wanko bakinki a toilet." Yaqare maganar had'e da mik'ewa ya riqo hannunta suka nufi toilet d'in tana biye dashi tana kallonsa, bata tab'a kula da kyan da ALLAH yayi masa ba sai yau... [7/5, 7:07 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___21πŸ’Ž Murmushi yayi don yakula da kallon da take yimasa saboda hasken wutar lantarki data haskesu lokacin da suke qoqarin shiga toilet d'in, seda yashiga sannan ya sake mik'a mata hannusa tariqo ya shigo da ita cikin toilet d'in, alama yayi mata data iso gaban fanfon dake tsaye ciki irin na qarfe d'innan da xaka gani a tsakiyar gida ko anguwanni ana d'ib'ar ruwa, ahankali tafara takowo kanta na sunkuye a qasa, cikin takun da baiwuce biyu zuwa uku ba ta isa gaban fanfon had'e da duqawa wajen, d'ayan hannunta ta d'ora saman kan fanfo zata kunna taji shima ya d'ora nasa akai da niyar kunna mata, d'ago kai tayi ta kallesa suka had'a ido ya sakar mata murmushi, da sauri ta sinne kanta qasa itama tana mayar masa da murmushin, ahankali yafara juya kan fanfo har lokacin hannusa na saman nata, ganin ruwan sunfara zubowa yasa ta tara d'ayan hannunta tana d'ibar ruwan tana kuskure bakinta had'e da wanke fuskarta, qoqarin jaye hannunta tayi yariqesa gam tamkar wanda za'a kwacewa hakan yasa ta kasa tashi tayi duqenta awurin, tanaji yana wasa da hannunsa akan nata kafin yacirosu akan fanfon bayan yasa d'ayan hannun nasa ya kashe batare da yasaki hannunsa sake riqe da nata ba,+ Bayan sun fito toilet yanufi falo da ita ya zaunar da ita qasan center carpet d'in dake shimfid'e ya d'an tura center table d'in dake tsakiyar don sud'an samu isashhen fili da bazasu matsuba, ledar daya shigo da ita yaje ya d'auko tare da shiga kitchen ya d'auko wani d'an k'aramin tray da cup d'aya ya d'aurayosu ya kawo agabanta yana fad'in. "Washh amarya bakya laifi." yana kallon yanda ta noce kanta qasa tana wasa da 'yan yatsun hannunt, riqo hannun yayi yanabin 'yan yatsun da kallo had'e da cewa. "Habibty lallen nan yayi kyau sosai gashi garin wannan wasar taki kina nema ki gogemunshi da wuri haka." Tana qoqarin janye hannun yayi 'yar dariya tare da yimasa kiss wanda yasa Rashida jin wani yanayi atattare da ita, ja baya tayi kad'an kafin ya saki hannun yana mai basawa kamar baisan me tayi ba, naman ya zube masu a plate had'e da ciro gorar fresh youghout d'in acikin leda ya tsiyaya a cup, "Habibty matso kici abinci nasan bazaki rasa jin yunwa ba." Yafad'a tare da nufo bakinta da yankan naman daya d'auko, kauda kanta gefe tayi alamun bazata ciba shima yasake maida hannunsa a gefen yana fad'in. "Haa mana." Kamar yanda akeyiwa yara harda d'an bud'e bakinsa murmushi tayi tare da girgiza masa kai tace. "Naqoshi malamina." Harararta yayi da wasa kafin yace, "Ai baki isa ba.maza kibud'e bakinki bana son musu Kuma." Ganin ya d'aure fuska yasa tabud'e bakin ya tura mata naman ciki yana fad'in "gud gel" haka yayita bata tanaci har naman yakusa qarewa, riqe masa hannu tayi lokacin da yasake d'auko wani yankan cikin marairaice fuska kamar zatayi kuka tace. "Kayi hak'uri malamina naqoshi tun d'azu ci kawai nakeyi saboda kace baka son musu amma ALLAH idan naqara wani akai yanzu zan iya yin amai." "Kin tabbata." "Sosai malamina" "Ok bari nima na tabbatar idan har da gaske kikeyi" noce kanta qasa tayi ganin yasake matsowa kusa da ita gabanta na dukan uku uku taji ya d'ora hannunsa saman cikinta da saurin ta rintse idanuwa yanda yake shafa cikin ahankali yasa dariya ta soma zomata da sauri tariqe hannun tana fad'in. STORY CONTINUES BELOW "Don ALLAH kadena, ALLAH kayar da Dani na qoshi sosai" tana 'yar dariyar da saida haqoranta suka bayyana. "Eh to na amince amma har yanzu da akwai inda bai ida cika ba, ungo wannan ki shanye saiki cike wajen kinji ko d'alibata." Yafad'a tare da mik'a mata cup d'in daya tsiyaya fresh youghout d'in, ba musu takarb'a tunda yariga yafad'a mata cewa baya son musu shi kuma yafara cin sauran naman daya rage yanayi yana kallon yanda take kurb'arsa ahankali, murmushi yayi don gaba d'aya komai na yarinyar na burgesa musamman yanda take motsa bakinta, nad'e takardar naman yayi bayan ya cinye ya ture ta a gefe tare da jawo sauran da kecikin gorar yafara sha shima, saida ya kusa shanye sa sannan ya ajiye gorar da sauran da ke ciki ko rabin gora beyi ba a lokacin itama ko rabin nata bata sha ba, miqewa yayi ya d'auke late d'in tare da ledar naman da kuma gorar youghout d'in daya rage ya nufi kitchen dasu, ledar ya kad'a a dosbin ya d'auraye plate d'in ita Kuma gorar ya ajiye a gefe don har lokacin ba'a cire fridge d'inta acikin kwali ba balle a jona, A inda ya barta anan ya sake iskota zaune tana jujjuya cup d'in da sauran youghout d'in dake ciki, kallonta yayi had'e da cewa. "Habibty dare fa yayi ko bakyajin bacci ne?" Miqewa tayi taje ta d'auraye cup d'in tare da wanko bakinta shi kuma yawuce toilet don ya watso ruwa, koda tadawo falon tajiyo motsin ruwa a toilet komawarta inda take tayi ta zauna tana kallon tsarinfalon nata da kayan da iyayenta suka zuba mata, sosai ta jinjina masu sabo kyan kayan da kuma yanda aka qawatashi da frem masu kyau kalar coppy colour, kujerunta da labulayenta duka suma kalarne sai 'yar madai daiciyar tv dake ajiye saman tv stand da qatuwar flower acan gefen falon daga kudu tana wannan tunaninne taji ya shigo falon saye da doguwar jallabiya yace "Habibty je kiyo arwala muyiwa ALLAH godiya daya nuna mana wannan ranar." Bayan tafito ya jasu sallar raka'a hud'u sannan ya sallame, addu'o'i yayita kwararo masu na samun zama lafiya da kuma zuri'a masu albarka, bayan yagama yajuyo yayi mata tambayoyi akan abunda ya shafi tsarki da kuma wanka, yasha mamaki sosai yanda yaji tabashi amasarsu yanda ya kamata hakan yasa baiyi zurfi ba wajen yimata tambayoyin saboda kusan qarfe sha biyu harda rabi tayi, miqewa yayi ya nufi tsakar gidan ya kashe fitila sannan yadawo cikin falo itama ya kashe har lokacin tana nan zaune gabanta na fad'uwa duk da dai bata san gaskiyar abunda zai biyo baya ba Amma keb'antarta daga ita sai namiji awake d'aya abune da Bata tab'a yiba don haka dole tsoro da fad'uwar gaba su kamata, tana jinsa yana kiran sunanta tamakure a gefen kujera jikta na rawa. "Habibty taso muje mu kwanta." Yafad'a yana qoqarin had'iye dariyarsa ganin yanda ta sake shigewa can bayan kujera, "Habibty, habibty..." yaci gaba da fad'a ahankali yana qoqarin isa inda take, a hankali hannunsa yakai saman kafad'arta tazabura tana shirin yin qara ya jawota ta fad'o jikinsa, "meye haka habibty? Nifa mijinkine da ALLAH ya halatta maki kiyi duk yanda kikeso dani da kuma gangar jikina haka kema ya halasta mani ke da duk wani abunda ke tattare dake, Ina sonki kina sona, menene abun tsorata da juna, karki manta nayi maki alqawarin zan kula dake Kuma zan baki farinci mai d'orewa matuqar Ina raye, zan soki soyayya mafi girma aduniya, irin soyayyar da zatasa harna mutu bazaki manta dani ba, Rashida kece duk wani bugun lumfashina don haka kiyarda dani bazan tab'a bari kicutuba aduniya, Ina so matuqar zuciyarki ta amince da kalaman dake fitowa daga qarqashin zuciyata ki kwantar da hankalinki muje mu kwanta abunmu kinji ko?." Ahankali ta d'aga masa kai jikinta narawa jin yanda nasa jikin ke gugar nata tana qoqarin zamewa, riqeta yayi sosai sannan ya d'agata cak ya d'auketa yawuce uwar d'aka da ita, bai direta ko ina ba sai tsakiyar gadon ya zagaya ta gefe yacire jalabiyar dake jikinsa had'e da kashe fitilar ya hau saman gadon shima, jawota yayi ajikinsa yaji ko Ina rawa take na jikinta, ahankali ya sake mannata aqirjinsa sosai cikin kwantar da murya ya rad'a mata a kunne. STORY CONTINUES BELOW "Don ALLAH kinatsu habibty? Nayi maki alqawarin bazan cutar dake ba ko kad'an, kinga gidan yawa muke kada muyi abunda zaisa aganomu kinji ko?" A hankali ta d'aga masa kai cike da tsoro hawaye na zubo mata, "Kin amince?." Nanma d'aga masa kai yasakeyi, cike da jin dad'i yakai bakinsa a goshinta yayi mata kiss, don aransa ya raya matuqar Bata amince ba bazai tab'a yimata dole ba saboda yanayin inda suke ciki zai iya zame mata abun gori idan har wajen tilastata yasa tayi abunda zaisa ajiyosu, ita kuma ta amsa masa ta amincene atunaninta na yakwana d'akin da ita badon tasan meye ainahin abunda yake roqon amincewarta aciki ba. ( _Karku manta Rashida yarinya ce, ba lallai bane don ta furta kalmar aure takeso kuma tasan me ake aikatawa acikin aurenba, batada wasu cikakkin abokanai inba meenah ba kuma a qauye ta tashi ba dolene ace tanada wayewar sanin ko meye ba don haka kada kuyi mamakin jin nace batasan me yake shirin yimata ba da har yake neman amincewarta ba da Kuma yanda ta tsorata har dasu rawar jiki saboda abune da bata tab'a yiba arayuwarta balle ace tasaba, tanada ilimi akan aure amma batada ilimin auren a aikace ko zahirance, sab'anin 'yan matanmu na yanzu da tun kafin akai yarinya tasan meza'a aikata_). Bakinsa ya d'ora akan idonta d'aya yayi mata kiss haka ma ga d'ayar kafin ya gangaro ga abu mafi burgesa atattare da ita shine bakinta ya d'ora nasa akai da sauri tajaye tana hawaye, "Don ALLAH kadena bana so?" "Kiyi haquri habibty wannan shine fa auren." Bil haqqi ta wangame baki zata saka masa kuka yayi saurin rufesa da nasa yana tsutsa ahankali, tun tana qoqarin kwacewa har ta gaji tafara lumshe idanuwa tana karb'ar saqon yanda ya kamata, jinta tayi awani baqon yanayi tare da kasa attaka komai saboda yanda jikinta ya mutu had'e da yin sanyi, hakan yabasa damar cigaba da aika zafafan sak'onnin da zuka dad'e yana son isarwa azuciyarta hannayensa kuwa nak'ara taimaka masa akan dukkanin muradansa naganin ya maida ita cikakkiyar mace a wannan daren, sosai take amsar saqwanninsa tana fitar da lumfashi a hankali, cikin tausayi da nuna jinqai yafara qoqarin sarrafata had'e da karanto addu'ar saduwa har ya cimma burinsa. Kasancewar bai zomata cikin tashin hankali ba yasa yayi nasarar rabata da budurcinta duk dai shima kansa saida ya wahala wajen qoqarin samun hanya, Rashida kam tasha kuka sosai, tayi dana sanin furta kalmar aure takeso don har seda taroqesa a maidata makaranta zatayi karatu sosai, wannan abun ba kad'an yabashi dariya ba hakan yasa yahaqura duk da bawani jimawa yayi ba balle gamsuwa, saboda duk duniya bayada burin daya wuce Rashida ta samu cikakken ilimin boko kamar yanda take dana arabiya, Wannan dalilin yasa yanaji yana gani ya haqura tare da komawa rarrashinta, da qyar yasamu taui shiru bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita, amma kallo d'aya zaka yimata kasan baccin bana dad'i bane, Jin alamun gari yayi sanyi da iskan da ake kad'awa sosai yasa yafahimci ruwa za'ayi don haka ya gyara kwanciyarsa tare da jawota ajikinsa yanajin wata sabuwar sha'awarta na taso masa, murmushi yayi cikin farinciki da jin dad'in yanda yasameta sannan ya ja masu bargo suka lullub'a. ••• ••• ••• Yaya hawwa kuwa yana fita ta tashi zaune had'e da jawo ledojin guda biyu tafara bud'e tafarkon, ganin naman ragone yasa ta turesa gefe tajawo dayar tabud'e, wahe baki tayi had'e da cewa "d'an kwal uba ga naman kaza zaka bani na rago, duk da dai naga irin wanda nake so ne Mai kitse kasiyo." Zaunawa daidai tayi tabud'e qafafuwanta tasa naman a tsakiya tayago naman kaza taci sannan ta d'auko yankan na ragon Mai kitse bayan ta birkid'eshi da yaji taci, haka tayitayi har ta canye naman ragon da kaza d'aya sannan tajawo gorar youghout d'in ta aza asama, wata uwar gyatsa tayi had'e da cewa "d'an buhun uba, wato inana kwance turus kashige d'aka da mata kusha wannan uwar dad'in ni kuma ka had'ani da mai kitse kad'ai, yo waya fad'a maka shikad'ai nake so bana son ita wannan abar mai fika fikai. STORY CONTINUES BELOW Nad'e d'ayar kazar tayi ta tura aqarqashin filo tare da gorar youghout d'in d'aya, shi kuma sauran takoma ta kwanta tana sha tana suruttanta har bacci ya soma d'aukarta, can cikin bacci taji kamar ana Kiran sallar asuba da sauri tamiqe tanufi sashensu Nuraddeen tafara bubbuga qofar, kasancewar baaccin ya soma yimasa nauyi sosai shiyasa baiji ba saidai baffa Usman ne yaji qarar ana dukan qofa daga wajen sashen Nuraddeen da sauri yafito don ya zata shine, ganin Yaya hawwa tsaye bakin qofar yasa yaqarasa wajen yana murzar idanuwa cikin rage murya yace "Lafiya Yaya hawwa kike buga masu qofa awannan lokaci?." "Aiho Usman ashe kaima kafito, ja'irin yaro kaji har ankira sallar asuba bai fitoba shine nace Bari na tadashi don Karya makara" kallon sararin samaniya baffa Usman yayi kafin yace. "Ikon ALLAH! To aike yaya ba'a isa kiran sallar asuba ba, qarfe uku da rabi yanzu ko baki duba agogo bane." "Kace wlh, Niko naji kiran sallah yanzu shiyasa nataso." dariya yayi don ya fahimci zallar damuwane yasa kunnuwanta ke hakaito mata kiran sallah awannan lokacin, dariya suka jiyo shiyarsu baffa Ali wanda har da zai fito Inna ruqayya tariqesa ta hanasa fitowa. "Wlh waccan yayar tashiga uku, mace baqin hali sekace gareta farau suruka, shiyasa naso muneera ta auresa don ta gyara mata zama wannan takurawa har Ina, fita batunsu baban yusufa koma ka kwanta." Tafad'a tana dariya had'e da kashe wutar d'akin, Girgiza kai baffa Usman yayi had'e da cewa "ki koma ki kwanta Yaya hawwa idan asuba tayi zan tashesu." "Asubar batayi ba kenan!" "Eh" yafad'a tare da juyawarsa yakoma d'aki, Daren ranar kam kasa komawa bacci tayi in banda saqawa da kuma warwarewa azuciyarta babu abunda takeyi, Baffa shima kansa abun dariya yabashi don duk abun dake faruwa akunnensa yanaji saboda alokacin shima ba bacci yake yiba, zaune take abunsa yana karatun al-qur'ani kafin yafara sallolinsa daga zaunen yajiyo bugun qofarta, rashin qafafuwa ya hanasa tasowa da sai ya riga baffa Usman fitowa, sosai matar tasa tabashi dariya ya d'aga hannuwa sama yana addu'a ALLAH ya shirya masa ita yaganar da ita kura kuranta tun wuri bai qure mata ba sannan yaci gaba da ibadunsa tare da roqawa d'an nasa samun dukkanin bud'i na duniya da zaman lafiya had'e da 'ya'ya nagari... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/5, 11:35 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___22πŸ’Ž Yaya hawwa kuwa har akayi kiran sallar asuba na farko idanuwanta biyu tanaji anfara kiraye kirayein sallar tamik'e had'e da azo qafarta bakin qofar d'aki kawai taji saukar ruwan sama ya kuccike ba zato ba tsammani don tun wurairan biyu da hadarin ya kankama iska ya taso ta ko Ina sai kuma daga baya ya kwanta hadarin kuma ya wargaje cikin ikon ALLAH nan take kuma da asubar ya sake had'uwa saiga ruwa, tsaye Yaya hawwa tayi kamar tafashe da kuka tana kallon sama, wata irin walk'iya akayo da tsawa alokaci d'aya da gudu takoma cikin d'akin tanemi waje ta zauna gefen gado idanuwa sunyi mata qululu, yau take jiran ad'auke ruwa gobe take jira amma sai sake sauka sukeyi kamar da bakin k'warya, hakan yasa kosu baffa Usman basu samu fita masallaci ba balle malan Nuraddeen ango sai dai kowanensu yayi sallarsa a d'aki tare da iyalinsa, STORY CONTINUES BELOW Nuraddeen kuwa saboda sanyi da qyar yasamu yayi wankan tsalki ba tare daya tayar da Rashida ba da sai faman yatsine fuska takeyi cikin baccin saboda babu ruwan zafi, sallarsa yayi sannan ya shiga cikin kicin d'inta ko zaiga inda aka ajiye rishow d'inta, cikin sa'a ya hango kwalin electric stove ya jawo had'e da cirosa daga ciki ya jona ga socket d'in kitchen d'in sannan ya ciro tukunya cikin kwalinta itama ya d'ora bayan ya d'an kara hannunsa saitin electric d'in yaji yafara zafi ya d'ebo ruwa ya zuba sannan yakoma cikin d'akin, gefen gadon ya zauna tare dasa yatsansa yana d'an shafa lab'b'anta, ahankali yaga tafara bud'e idanuwanta suka sauka akan nasa daya qura mata, suna had'a ido tayi saurin rufewa had'e da cuno d'an k'aramin bakinta ta kauda kanta gefe, dariya yayi kafin yace "haba ta malan nura fad'amun waya tab'amun ke kike juyamun kai haka." Shiru tayi batare data amsa masa idanuwanta na arufe, hannunta ya cire daga saman qirji da yake ta riqe bargon yana shafa lallen dake jiki a hankali tare da yimasa kiss, jaye abunta tayi da sauri tana fad'in "kadena bana so.." Kafin tarufe baki taji ya had'e bakinsa da nata ya sakar mata wani irin sihirtaccen kiss. Idanuwanta ta lumshe tanajin tamkar na'urar jikinta ta d'auke ta had'e da dawowa. "Morning habibty kin tashi lafiya?" Kad'a masa kai tayi tana tunani abubuwan da suka faru jiya tsakaninta dashi kawai saita tsinci kanta cikin matsananciyar jin kunyarsa, "taso muje kiyi wanka yafad'a had'e da miqewa, har zai d'aukarta sai Kuma ya tuna bai had'a ruwanba ya. "Afuwa habibty bari naje na had'a maki ruwan wankan tukunna." Yaqarasa maganar tare da barin d'akin koda yaje ruwan har sun tafasa ya juye a boket yakai toilet, wani bokitin ya sake d'auka yahad'a mata ruwan tare da detol sannan yakoma ya d'aukota tamkar wata baby, Cikin jin kunya tace "don ALLAH ka ajiyeni zan iya tafiya da kaina." Zaro idanuwa yayi yana kallonta had'e da cewa. "Da gaske kike?" "Eh ajiyeni kagani mana." Tana turo baki agaba, Saida yayiwa bakin kiss sannan ya ajiyeta qasa tafara takawa ahankali yana biye da ita har takai bakin qofar shiga toilet d'in, tana aza qafarta d'aya ta d'ago d'ayar ta aza tayo baya baya zata fad'i da sauri ya tareta tafad'a akan jikinsa saboda wani irin masifaffen zafi da taji a tsakiyarta don ma ALLAH ya taimaketa bai jimataba saboda ba duka ya shigeta ba, binta da kallo yayi ganin yanda tsoro yasa taturo idanuwanta da suka cika tab da hawaye tana shirin yin kuka yace "Sorry habibty, kibi a hankali mana kinga da yanzu kin fad'i" kafin tace wani abu ya d'auketa ya qarasa shiga da ita ciki, qasa ya direta sannan yajawo wata 'yar kujerar da kecikin bayin ya zaunar da ita had'e da nad'e hannuwan rigarsa yasa cup yafara d'ebo ruwan yana yimata tsarki dasu, ture hannunsa takeyi tana had'e qafafuwanta Amma yayi kamar bai ganta ba saida ya gasata sosai sannan yace tayi wankan tsarki sai tafito, Ita kam banda satar kallonsa tana mamkinsa babu abunda takeyi, wai yau itace malaminta ke d'auka hadda suyimata tsarki, lalle aure wani babban alamarine daban, da sauri tasa hanuwa tarufe fuskarta tana dariya alokaci d'aya kuma tanajin qaunarsa naqara ruruwa azuciyarta, tajima zaune tana wud'annan tunanin kafin tayo wankan tafito tasamu harya shimfid'a mata abun sallah tare da fiddo mata da doguwar riga da hijabi yabata tasa ta tada sallah, waje yake son fita amma har lokacin ruwa akeyi sosai gashi har goma da kwata tayi yarinyar mutane bataci komai ba, Yanke shawarar fita haka yayi sai gashi yaji qarar wayarsa dake ajiye saman bedside, da sauri yaje ya d'auka yaga lambar baffa Usman duk sai yaji wata irin kunya ta kamasa, kasa d'agawa yayi akaro na farko har sai akaro na biyu ya d'aga had'e dayin sallama ya gaishesa. murmushi yayi sannan yace "Lafiya klw Nuraddeen, katashi lafiya." "Lafiya klw baffa Usman." "Ya kwanan iyalin naka? Yau mun tashi da ni'ima." STORY CONTINUES BELOW "Alhamdulillah kam ga ruwa nan masha ALLAH sai fatar alkhairin dake cikinsu" yafad'a tar da basar da d'ayar maganar, murmushi baffa Usman ya sakeyi kafin yace, "Kabud'e k'ofa ga abun karinan Aysha zata kawo maka da sauri kasan ruwan nada qarfi kada su dokarmun auta tayi ciwo.." 'yar dariya Nuraddeen yayi had'e da cewa. "To baffa Usman, ko abari inzo in karb'a kada ruwa sudoketa nayi laifi, dama yanzu nake Shirin fitowa." "A'a jira gatanan zuwa, ai babban d'a baya laifi," "To baffa Usman mungode." "Masha ALLAH ka gaida iyalin naka" Yakashe wayar don yasan bazai amsa ba saboda kunyar da yake da ita, miqewa yayi had'e da zuwa bakin qofar don har yaji isowar ta, yana bud'ewa yace "Aysha shigo da sauri mana kada ruwan ya jiqaki." "A'a Yaya Inna tace inyi maza indawo kada natsaya, Ina kwana?" "Lafiya klw autar baffa yasu Inna?" "Duk lafiya klw suke, Ina aunty." Juyawa yayi yakalli qofar d'akin bayan ya anshi kayan hannunta sannan yace "shigo mana tana ciki ku gaisa ko bakya sonta?" Rufe baki tayi sannan tajuya da gudu tabar wajen tana fad'in "Ina sonta mana Yaya ka gaisheta anjima zamuzo ni dasu aunty fadila." Juyawa yayi ya koma ciki ya tarar har ta sake gyara d'akin ta koma ta kwanta, amaimakon ya tada ita sai kawai shima yabi bayanta yakwanta abinsa had'e da jawota ajikinsa, tanaji yafara shafo cikinta yana yawo da hannunsa ta rintse idanuwa sosai irin tayi baccin nan, cakulkuli yafara yimata yana fad'in "kima bud'e idanuwanki nasan ba bacci kikeyi ba." Yanaci gaba da yimata cakulkulin, juyowa tayi tana dariya tashige jikinsa tana fad'in "don ALLAH kadena bana so." Cikin kwaikwayon muryarta shima ya maimaita abunda tace. "Shikenan to ni kiyimun Ina so." Aikuwa ta taqarqare tana yimasa cakulkuli tana dariyar shima yanayi, jawota yayi ya rungume jikinsa sosai yana fad'in "to ya isa haka kibarni nima bana so" yana rirriqe mata hannuwa ita kuma tana qoqarin kwacewa, da wayo da wayo yasamu ya sake biyan buqatarsa amma awannan karon Mai gaba d'aya yayimata don seda yaji yasamu natsuwa sosai, Kuka kam Rashida tashashi har dasu majina, sai faman rarrashi yakeyi fiye da jiya yana qoqarin jawota ajiki turesa ta dingayi tana fad'in "ni ka qyaleni tunda wayone da Kai bazan sake yarda da kaiba." Dariya ya dinga yimata yana cewa. "Yi hakuri nadena bazan sake ba." Saida yaga tayi shiru sannan ya tashi yaje ya juyo sauran ruwan zafin d'azu yakai masu toilet yadawo ya sake d'aukarta izuwa toilet d'in, nan ma saida ya cukulkulata sannan ya taimaka mata tayi wankan shima yayi suka fito, ji yake wani irin sonta na qara ruruwa azuciyarsa da bayajin zai iya rayuwa idan babu ita. Saida suka shirya tsaf sannan ya d'auko abun karin da baffa Usman yasa Aysha takawo masu ya ajiye agabanta, soyayyen kwaine sai ruwan tea da kuma qaton burodi guda sai suga da gwangon madarar ruwa guda biyu tare da bonvita, qananan cups ya d'auko a kitchen tare da plate yajuye soyayyen qwan akan yahad'a mata tea mai kabrin gaske yabata, tana jin yunwa sosai hakan yasa ba musu ta karb'a tafara sha tana had'awa da soyayyen qwan tak'i cin biredin, Babu yanda beyi da itaba akan taci tace taqoshi don dama ita ko agida biredi bai shamata kai ba. *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/6, 10:32 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž STORY CONTINUES BELOW _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___23πŸ’Ž Haka yagaji ya qyaleta yaci gaba da cin biredinsa tare da kora ruwan tea kafin can ya turesu gefe yana kallonta, murmushi tayi ta tura soyayyen k'wan data d'ebo cikin baki had'e da sunkuyar da kanta k'asa. "Malamina wannan kallo haka fa?." Tafad'a tana kai ruwan tean abakinta, "Ke d'ince indai kina agabana bazan iya dena kallonki ba, musamman idan kina motsa wannan d'an mitsitsin bakin naki dake d'auke da tausasan lab'b'a tamkar tuffa sai inji bana gajiya da kallonki." "Ehhm." "Baki yarda bane?" "Haba! Nayarda sosai kuwa." "Habibty! Hak'ik'a ba k'aramar sa'a nataka ba da ALLAH ya mallaka manike a matsayin matata kuma asusun ajiyar 'ya'yana har nakanj alfahari araina tare da ganin babu abunda yai sauran mani aduniya face naci gaba da yiwa ALLAH godiya bisa wannan kyauta da yayimun, haqiqa kowace mace da irin baiwar da ALLAH yayi mata aduniya amma inada yaqini akan cewa taki baiwar ta musammance, nayarjewa kaina in rayu rayuwa ta har abada a qarqashin inuwarki ke kad'ai batare dana kwad'aita izuwa wata inuwar ba." Yanda taqura masa ido tana sauraren kalamansa ya sashi jinjina mata kai had'e da rufe idanuwansa yabud'e alamun tabbatar mata da zancensa sannan yaci gaba da cewa. "Kiyarda dani Rashida Kuma kibani damar d'awainiya da dukkanin murdanki da burukanki aduniya natabbata zanyi qoqarin cika makisu koda kuwa zan rasa raina, ni Nuraddeen nayi maki alqawarin zan kula dake, zan tarairayeki zan bud'e maki dukkanin qofofin zuciyata kiyi duk yanda kike so aciki, zan mallaka maki dukkanin sassan jikinsa da kuma rouhina, zanyi maki uzuri acikin lafuzzanki da kuma ayukkanki agareni, zan killaceki tayanda Babu wani mahaluqin daya isa yacutar mani dake, zan d'aukaka darajarki da martabarki acikin 'yan uwanki mata, burina d'aya shine ki soni so mai girma kuma ki qaunaceni tayanda duk tsanani bazaki tab'a yarda arabaki dani ba domin farincikina yana wan zuwane matuqar kina tare dani to tabbas zan kasance mai alfahari da rayuwata har abada, Rashida Ina sonki so marar misaltuwa, Ina qaunarki qauna mai tsananin da zan iya sadaukar da dukkanin farincikina akan naki farincikin." Murmushi tayi tana maijin wani sanyi na ratsa zuciyarta da kuma sassan jikinta, tabbas tayarda cewa idan ALLAH ya jarabci bayinsa awanI b'angaren to yana kawo masu mafita a ta wani b'angaren daban, daga daren jiya zuwa wayewar safiyar yau cike take da tsoro da kuma tashin hankali ganin yanda mahaifiyar mijinta da wasu 'yan uwansa suka nuna qarara cewa basa farinciki da aurota wanda hakan ba qaramin jefata cikin damuwa da karaya yayi ba amma ayanzu ganin tsantsar soyayyar da mijinta keyi mata acikin idanuwansa da saqon da bakinsa ya isar Kai tsaye daga zuciyarsa yasa tasamu natsuwa da qwarin guiwa d'ari bisa d'ari wajen jajircewa ta nayarda martani akan soyayyar da mijinta keyimata kuma tashirya tsaf wajen yaqar duk wani shamaki da zaizo ya shiga tsakaninta dashi, zata lullunka dukkanin haqurin da akace tayi tare da jurewa dukkanin b'acin ran da zata fuskanta don ganin sunyi rayuwarsu yanda suka tsara cikin so da qaunar juna. Wata kasalalliyar ajiyar zuciya tayi had'e da riqo hannayensa biyu tana kallon cikin idanuwansa tace. "Ka kwantar da hankalinka malamina domin kai kad'aine zuciyata keso, Kai kad'ai taquduri alqawarin yiwa hidima har qarshen rayuwarta, bazan gujeka ba komai rintsi komai wuya, zanyi maka biyayya iya qarfina, zan kula da kai iya qoqarina sannan zan baka farinciki daidai iyawata, zan zauna da 'yan uwanka lafiya zan Kuma kyautawa iyayenka tamkar nawa iyayen sannan zanyi fad'a da qarfin ALLAH ga duk abunda zai rusa rayuwar aurenmu, abu d'ayane bazan iya yimaka alqawari ba, shine na baka soyayyata tahar abada." STORY CONTINUES BELOW Taqare zancen tana sinne kanta qasa had'e da qumshe dariyar da tazo mata saboda ganin yanda ya turikke idanuwansa awaje, cikin rud'ewa ya rumk'e hannuwanta sosai kamar zaiyi kuka had'e da cewa. "Why Rashida!. Meyasa bazaki iya bani soyayyar kiba tahar abada?" D'ago kanta fuskarta ad'aure tana kallonsa tace. "Kayi hak'uri saboda gaba d'aya nariga da nabaka ita tunda dad'ewa har agaban Aabadan kaga kuwa bazan iya sake baka itaba tunda tuni tana hannunka." Taqare maganar tana dariya had'e da kallon yanda ya dafe saiti zuciyarsa da hannayensa biyu yana murmushi, cikin wani irin shauqi yariqo gefen kuncin ya d'aga d'ayan hannunsa kamar zai mareta yana fad'in. "Ke ko!" tayi saurin runtse idanuwanta tana dariya, ji tayi ya rungumeta had'e da sumbatar goshinta yace. "Kai habibty Zaki kasheni da soyayyarki, waya koya maki soyayya haka." Yana sake sakar mata kiss agoshi, gyara zaman kanta tayi a qirjinsa had'e da cewa. "Malamina mana.." duk sukasa dariya, atak'aice dai ranar sun faranta zukatan junansu da dad'ad'an kalamai dake d'auke da nagartacciyar soyayya. Ganin ruwan basuda ranar d'aukewa yasa qarfe d'aya da rabi nayi na rana ya fito haka don gabatar da sallar azahar, kallo d'aya zakayi masa katabbatar da natsuwar dake cikin zuciyarsa saboda farincikin dake shifid'e a fuskarsa, kasancewar ruwan sun d'an rage yayyafine akeyi amma mai d'an qarfi yasa bai tsaya yin sallarsa b'angaren baffa ya wucewarsa masallaci, bayan yadawo yashiga inda mahaifinsa yake cike da jin kunyar rashin fitowarsa da safe ya gaishesa, sallama yayi baffa ya amsa masa sannan yashiga yana zaune riqe da littafin majma'ul baharaini yana tilawarsa, kallo d'aya yayi masa ya d'auke kansa ya mayar ga littafin yana murmushi ganin yanda yake wani faman sissinne kai qasa. "Baffa Ina wuni?" Yafad'a kamar zai nutse aqasa saboda kunya, batare da baffa ya d'ago kansa ba yace. "Lafiya klw Nuraddeen, ya yinin iyalin naka duk lafiya kuke?" "Lafiya klw baffa ya ruwa?." "Ruwa kam gasunan Masha ALLAH sun sauka, kaga badon rashin qafafuwannan nawa ba da sai gona." "To baffa ya za'ayi sai haquri, in sha ALLAH ijaba takusan sauka, inaji ajikina ka kusan miqewa da qafafuwanka da yardar ALLAH" Murmushi yayi irin nasu na manya tare da rufe littafin sannan yace, "Hmm! Nuraddeen kenan! Kai yanzu kana tunanin zan miqe awannan halin da nake ciki?, Duk da dai shi ciwo da mutuwa duka a hannun ALLAH yake bana tunanin zan wud'an qafafuwan nawa zasu sake taka qasa" _Laa taqnad'u min rahmatillah (kada ka yanke tsammani ga rahamar ALLAH)_ sukajiyo baffa Usman dake qoqarin shigowa yafad'a had'e da yin sallama, murmushi baffa yayi had'e da cewa. "Malan Usman uban ango yau Ina kashige tun safe ban sake ganin kaba sai yanzu?, kodai d'an naka kake tayawa angwanci?" Sosa qeya Nuraddeen yashigayi yana murmushi tare da kallon baffa Usman dake qoqarin zaunawa kusa ga d'an uwan nasa yana dariya yace, "To Yaya idanma nayi ai ba garemu farauba balle ta qare kanmu, in banda abunka Yaya duka duka shekarun naka nawane da kake zancen mutuwa koda yake ita batada takamammen lokaci amma muna fatar ba jikoki kad'ai ba har 'ya'yansu kariqa a hannu kafin wannan lokacin har su girma suna biye da kai kuje gona, rayuwa dai muke fatan tayi mana fad'a." "Usman kenan tunda ALLAH kace nayi shiru, Amma karka maanta shekaruna fa yanzu sun haura hamsin da wani abu aduniya, idanma ALLAH bai nufi nagani ba ina roqon kai da d'an uwanka yagwada maka." Yafad'a yana sharar k'wallah ganin haka yasa baffa Usman ya kauda zancen had'e da cewa, STORY CONTINUES BELOW "Ya qarfin jikin naka? Kasha maganinka?" "Eh yanzu da hawwa tashigo tabani nasha, jiki kam gayanan Alhamdulillah, yawwa kai namanta infad'a maka maman taka ba tada lafiya, shine dalilin shigowarta tace mun tana fama da ciwon ciki da gudawa don haka ka aika ko filagin da limotin ne asiyo mata ko kuma kaje da kanka." Baffa yaqarasa fad'a yana kallon Nuraddeen Baffa Ali ne ya d'ago labulen qofar had'e da kallon Nuraddeen sannan ya kalli baffa daga bakin qofar yace, "Ya jikin?." "Da sauqi Aliyu bazaka shigo ba?" "A'a sauri nake zanje gona nad'an duba wasu abubuwan kasan zaman gida bana namiji bane sai mata." Batare da baffa yadamu da maganar daya soka masa ba yace. "To ALLAH yayi taimako yadawo da kai lafiya." Shidai baffa Usman na zaune yana kalonsa don tun jiya take d'aure masa fuska had'e da rashin yimasa magana. "Baffa Ali ina wuni?" Nuraddeen yafad'a daidai lokacin da yake qoqarin barin wajen batare data kalli ko gefen da baffa Usman yake ba, dawowa yayi had'e da sake d'ago labulen sosai yanda zaiga fuskar Nuraddeen d'in snnn yace, "Af..shin nura ne? Ai ban lura da kaiba, ashe kasamu damar fitowa yanzu, to agaisheka." Baice masa komai ba saima noce kansa qasa da yayi shi kuma yawuce yana dariyar qeta don acikinsu yasan babu wanda bai b'atawa raiba da kalamansa. Murmushi baffa yayi sannan ya fara ba baffa Usman magana akan yaci gaba da haquri da halin d'an uwansa, in Sha ALLAH da SANNU SANNU zai gane dukkanin kuskuren da yakeyi. Miqewa Nuraddeen yayi had'e da cewa. "baffa Bari naje na siyowa innar mu maganin" "To adawo lafiya." Yabashi amsa atak'aice tare da maida hankalinsa wajen baffa Usman sukaci gaba da firarsu. Bayan mintuna biyar da fitarsa sai gashi yadawo da ledar magani a hannunsa yanufi sashen mahaifiyar tasa yana isa tana fitowa da sauri daga d'aki had'e da cewa, "Miqomun butar nan Nura." tanufi bayin aguje, kad'an yarage dariya tafito masa yayi saurin d'aukar butar yabita da ita yakai mata abakin toilet sannan yadawo, juyawa yayi da niyar fita tayi masa tari alamun ya jirata, tafi minti biyar acikin toilet d'in kafin tafito riqe da ciki, daddafe ta iso cikin d'akin yana zaune yana daddanna wayarsa tace. "Nura banda lafiya." "Subhanallahi innar mu meyake damunki?" "Bari nura d'azunnan naji cikina ya murd'a nashiga bayi basai ga gudawa ba, ciwon ciki uwa zan mutu gashi kai kashige abunka kamar bazaka fitoba balle kasan halin da nake ciki." "Yi hak'uri innar mu, yanayin uwan da aka tashi da sune na d'auka kema kina nan abunki kwance saboda qarfin ruwan." "Kai! haba nura ina naga takwanciya awannan halin, ai mayata bayi tafi biyar acikin ruwannan, inaji nura naman nan bayada kyau, kodai wani abun kasa aka saka maka aciki?" Tafad'a tana qoqarin zaunawa saman gadon, Bata qarasa zaunawa ba tasake fita aguje zuwa bayi, duk da mahaifiya ce amma abun dole ya basa dariya, yana zaune tadawo tana "wash ALLAH na, nura kaji tsoron ALLAH anya da zuciya d'aya kabani naman nan? Wlh gudawarnan tayi yawa ko qarfin jikina banaji, gaba d'aya ruwan jikina sun qone qurmus nura." Kauda kansa ya dingayi yana basar da dariyar tare da cewa. "Sannu innarmu, wlh da zuciya d'aya na ajiye maki, kefa mahaifiyata ce, taya zanso abunda zai cutar mani dake?" STORY CONTINUES BELOW "To Ina nasani nura ko kazab'i matarka akaina shiyasa kayimun haka! Ko ko dai kitsennan ne yatab'amun ciki kasan sonshi nake Amma baya shafamun lafiya." Ledar hannunsa ya bud'e ya d'auko maganin daya siyo mata ya b'alla matasu tare da d'ebo ruwa atukunyar dake cikin d'akin bayan gambu ya miqa mata, "Gashi innar mu kisha, maganine baffa yace naje nasiyo maki dana shiga wajensa. Idan anjima kikaji ba canji sai inje inkirawo maki Ibrahim mai allura aqara maki ruwa" "Yawwa agaisheka ALLAH yayi albarka." Tafad'a tana karb'ar maganin ta afa abaki sannan ta kora ruwan sama tana b'ab'bata fuska. "Wannan magani sai d'acin tsiya, shiyasa nafi ganewa maganin gargajiyar nan na basir." Tana gama fad'a ta d'aga gefen filonta tajawo sauran kazar d'aya data rage jiya tare da gorar youghout d'in tace. "Ungo nan nura kaje da ita ku silala, batayi komai ba saboda sanyin da kayi." "Innar mu bari dai agyaro maki ita tunda kinga bakijin dad'i sai anjima kici." Daqquwa tayi masa had'e da cewa, "Zaka karb'ane ko saina b'ata maka rai, ai duk wannan namanne da naci yajawomun wannan wahalar, tashi kaje dashi can ni bazan ciba ta sake kawomun wahala, gaba d'aya tama fita raina, ungo had'a da wannan gorar madarar ta wahala ku qara can." Duk qoqarinsa wajen ganin ya danne dariyar karta fito saida tafito a wannan karon ta jefesa da gorar had'e da cewa, "'dan buhun uba, dariya ma zaka azamun taahi ficemun da gani ja'irin banza da wofi.." Da sauri ya miqe yafita riqe da sauran naman bayan ya d'auki gorar youghout d'in data jefomasa yana dariya. "Oh ALLAH! ALLAH yaqara yawancin rai innar mu nikam naga yanda Zaki kwashe da 'yan jikokinki!" "Innar mu sanni ALLAH yakyauta Kuma yabaki lafiya." "Amin, zaka gane bari dai insamu lafiya d'an buhun uban nan duk sai naci mutuncinku da Kai har wannan tsigi tsilar yarinyar." Shiyarsa ya shige ya tadda Rashida dasu Aysha zaune suna tayata fira bayan sun kawo mata abincin da baffa Usman yasa aka dafa masu, suna ganinsa suka miqe had'e da gaishesa suka fita, bud'e hannuwa yayi yana fad'in "baza'a yimun oyoyo ba?" Tasowa tayi ahankli tana tafiya tashige cikin hannayen nasa, har zai maida ya kulle ta duqe ta qasa had'e dayin zaunenta qasan carpet d'in ta jingina ga kujera tana dariya, "Kazo kaci abinci qarfe uku ke shirinyi kada yunwa takamaka." Tafad'a tare da jawo kular jallof d'in shinkafar da su Aysha suka kawo mata tasha kayan ciki.... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/7, 7:47 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___24πŸ’Ž Zaunawa yayi tare da tankwashe qafafuwansa yana bud'e kular dake gabanta, "munzama 'yan gatan baffa Usman meye yasa aka kawo mana" STORY CONTINUES BELOW Yafad'a yana qarasa bud'e kular, "wow my fav..." "Kana son jalop rice kenan?" "Sosai kuwa habibty musammamn idan tasha kayan ciki, wannan aikin Inna Bilkisu ne don tafi kowa sanin abubuwan dana fiso aduniya in kika cire su baffa da innar mu agidannan." Murmushi tayi had'e da mik'ewa taje ta d'auko plate da cokula biyu ta zuba abincin ta ajiye masa agabansa, ledar hannunsa ya miqa mata had'e da cewa. "Ungo wannan kisa a electric tunda naga akwai nepa sai ki gyara mana." Hannu biyu tasa ta karb'a tana fad'in "Angode ALLAH ya qara bud'i." "Amin ya rabbhi, amma jeki ki ajiyesa kitchen sai kidawo muci abincin." Bayan sun kammala ya shiga toilet don ya watso ruwa ita kuma tawuce kitchen wajen aikinta, yana fitowa yadawo falo yacire fridge d'inta dake cikin kwali ya jona, cikin 'yan sakanni yafara sanyi yaje ya d'auko sauran youghout d'in da suka rage jiya tare da wanda yazo dashi daga wajen Yaya hawwa yasa a fridge, tsakar gidansu ya leqo yakira Yusuf yabashi nira d'ari yace yaje ya siyo masa ledar package water sannan yakoma ciki, kitchen yanufa ya samu tana yanka albasa ya rungumota tabaya had'e da turo kansa ta wuyanta ya yimata kiss, murmushi tayi ta d'ago kai tana kallonsa, "cikani mana kada in yanke." "Bazaki yanke ba tunda ina wurin, natabbata kaifin wuqa bazai iya cutar dake ba agabana." "Hmm to ai shikenan." Tafad'a tare da ajiye wuqar agefe, "Aw baki yarda bane?." "A'a nayarda, kawai nagama yankan albasarne Bari in zuba kafin ruwan su ida tsanewa." Had'e da jaye jikinta daga riqon daya yimata, daidai lokacin yusuf yayi sallama yana fad'in, "Yaya ga ruwan." Fita yayi ya karb'a tare da cemasa "Yusuf ba zakazo kugaisa da auntyn taka ba?." Qarasa shigowa yayi tare da d'an d'aga muryarsa yace "Aunty ina wuni?" Rashida dake kitchen tajiyo ana gaisheta tafito had'e da cewa, "Lafiya klw, kana lafiya." "Lafiya klw" yabata amsa sannan yawuce abunsa, "Yusuf kenan d'an gidan baffa Ali." Nuraddeen yafad'a yna kallonta, "ALLAH sarki yaron tubarkallah kyakkyawa dashi kamar kai." Taqarasa maganar tana dariya tare da komawa cikin kitchen ganin yanda ya juyo yana harararta irin da wasa d'innan. Kai ruwan yayi yasa a fridge sannan yadawo cikin kitchen d'in tare da jinginawa ajikin qofar yana kallonta, "me kikace? Yusuf mene?" "Ni! Bance komai ba fa." "Banyarda ba ALLAH sai kin sake maimaita abunda kikace" Yafad'a tare da fizgota tafad'o jikinsa, qurawa idanuwanta kallo yayi itama tabishi da kallo hannunta na dafe da qirjinsa, "maimaita abunda kika fad'a." Taji yasake furtawa cikin wata kasalalliyar murya, turo d'an bakinta tayi zata jaye jikinta daga riqon daya yimata ya sake matseta sosai, "Karfa naman yaqone." Tafad'a tana cuno baki gaba, tagefen da tukunyar take yad'e karkata kansa yana kallo kafin yace. "Ok inajinki, maimaita nace," "Kai malamina, cewafa nayi kyakkyawa da..." Kafin ta qarasa ya game bakinsa da nata yana sakar mata wani irin passionate kiss, kafin nan yace, STORY CONTINUES BELOW "Daga yau bana son inji wannan bakin naki ya yabi kowane irin namijine agabana kinji ko?" Jikinta a mace ta d'aga masa kai had'e da cewa. "Kayi hak'uri baza'a sake ba." Kiran sallar la'asar da yaji yasa ya kauda zancen had'e da cewa. "Habibty bari naje nayi la'asar idan kin qarasa Aysha zatazo ta rakaki cikin gida kigaishesu daga nan siki dubo innar mu da jiki don batajin dad'i ni Kuma daga cn zan biya wajensu kamal zasu rakani yarimawa wajensu baba balarabe nayo godiya" "Don ALLAH in shiraya zakuje dani nagano ummata?." Tafad'a had'e da marairaice fuska kamar zatayi kuka, bayason ranta yab'aci don haka kawai yace tashirya, amma yafad'i hakanne bawai don zai dawo ba sai don karta aza masa rigimar da zata jawo b'acin ranta. Cikin d'oki tarungumesa had'e da cewa "Sai kadawo bari nayi sauri naqarasa aikin." "Ok amma kifara shiga kigaishesu tukuna kafinna nadawo d'in kinji ko." 'Daga masa kai tayi ya sakar mata murmushi tare da yimata kiss a goshi sannan yawuce d'aki yayo arwala tare da sauya kayan jikinsa izuwa manyan kaya ya feso turare yafito yana gyara zaman hular kansa, kallo d'aya tayi masa taci gaba da kwashe naman tana fad'in "Tubarkallah malamina kayi kyau." "ALLAH habibty?." "Sosai kuwa, adawo lafiya nima bari naje na shirya kafin kadawo." Murmushi yasakar mata sannan yafice daga sashen, inda Yaya hawwa yasake shiga ya dubota da jiki sannan ya shiga shiyar baffa Ali har lokacin bai dawo ba Inna ruqayya kad'aice zaune tana yiwa munira fad'a akan tazo ta tsefe kanta, tana ganinsa tayi shiru tare da d'auke kai gefe. "Inna ruqayya ina wuni?." "Lafiya" Tafad'a tana sake juyar da qeyar kansa gefe, idanuwansa ne suka sauka akan muneera data wani dashe haqora tana susar kai had'e da kallonsa ya zabga mata harara yana fad'in. "Ke lafiya wannan kallon?." "Ina wuni yaya." Tafad'a tana sake bayyana fara'arta garesa, tsaki yaja had'e da miqewa yabar wajen, yana jin inna ruqayya na fad'in. "Iskancin banza da wofi, har ni za'a gwadawa cin gira kusa da ido, yaro da SANNU SANNU zaka zo hannuna da Kai har waccan 'yar iskar jarababbiyar yarinyar daka kawo sai kun yabawa aya zaqi, ke kuma zaki tashi ki tsefa kan ko sai nasa wannan tab'aryar na makeki." Tafad'a tare da jawo tab'aryar dake gefenta, "Kai Inna don ALLAH abar tsifar nan zuwa jibi..." Bata rufe bakiba taga tayo kanta da tab'aryar ta tashi da gudu tabar wajen tana susar kanta. Shiyar baffa Usman yanufa Inna Bilkisu na tankad'en gari shi kuma baffa Usman na arwla da sauri saboda jin ana qoqarin tada sallah, a tsaitsaye ya gaisheta ta amsa cikin fara'a tare da tambayarsa iyalin tasa, murmushi kawai yayi yace. "Inna sannu da hidima ALLAH yasaka da alkhairi ya qara bud'i." "Amin nura, ai babu komai d'a nakowa ne, kaidai kakula da amanar yarinyar mutane daka karb'o, ALLAH yabaku zaman lafiya, "Amin inna dama cewa nayi ko Aysha zata rakata cikin gida tagaishesu?." "Af kaji nura da wata magana, Aysha ai qanwar kace ko bak fad'amun ba kanada ikon aikinta duk inda kaga dama balle nan cikin gida maza ka hanzarta kaje kasamu sallah kada jam'i ya wuceka in sha ALLAH babu wata matsala." Kusan tare suka fita da baffa Usman cikin sauri sauri don su samu ayi jam'in dasu, Duk inda yakamata akai Rashida acikin gidan Aysha ta kaita in banda wajen yaya hawwa da baffa, shima d'in Inna Bilkisu ce tace tabari idan nurah yadawo sai sutafi tare, duk cikin gidan babu inda Rashida tasamu matsala hatta ga 'yan uwansa da suke uba d'aya Wanda b'angarensu nacan gefe sai wajen Inna ruqayya, tasha tambayoyi da maganganu kala kala da kallon banza amma da yake gaba d'aya hankalinta baya wajen saboda ganin yanda magrib ta gabato bai dawo ba zancen zuwansu gida tagano ummata, shiyasa ko ajikinta don bata maji wasu maganganun ba Aysha ce kawai taji itama taja bakinta ta tsuke tamkar bataji ba. STORY CONTINUES BELOW Har akayi sallar isha'i Rashida nazaune tana jiran dawowarsa amma shiru hakan yasa tad'auko wayarta da tunjiya data ajiyeta cikin jikkar hannuta bata sake waiwayarta ba sai yanzu da yake tasan wayar akashe take shiyasa tana d'aukowa tayi saurin kunnawa, tana gama logging tafara qoqarin lalubo lambarsa saiga kiransa ya shigo, cuno baki tayi sannan ta d'aga wayar kamar zatayi kuka tace. "Shine kayi tafiyarka kabarni ko?" 'Dan murmushi yayi don dama uasan za'ayi hakan sannan yace. "Yihaquri habibty koda nakammala sallah nasamu suna jirana a mota kinga bazai yuyu in b'ata masu lokaci ba, amma nayarda nayi laifi ayimun afuwa ga munan munkusa qarasowa gida." "Ai dama nasan haka zakace, shikenan ALLAH yakawoku lafiya, ya umma dasu baba?" "Lafiya klw suke ga saqonan sun bayar akawo maki," "To shikenan sai kadawo." "Yawwa habibtynah I love you." "I luv you too" itama tafad'a akunyace sannan takashe wayar, Bayan yadawo yaci abinci ya watso ruwa ya huta lokacin har qarfe tara na dare yayi suka fito tare da rufo qofar tana saye da hijabinta, d'akin Yaya hawwa suka nufa yayi sallama tana kwance tabashi izinin shigowa tare da qara nishin da takeyi, "Shigo nura har yanzu dai jikinnan ya qiyamun duk da dai ciwon cikin yafad'a gudawar daice har yanzu." Tafad'a tana qara mimmiqewa akan gadon batare da tasan tare yake da ita ba sai daya koma gefe yana cewa Rashida dake lab'e bayansa gabanta na dukan uku uku. "shigo mana" Wata irin zabura Yaya hawwa tayi sai kace ba itace tagama nishi tana fad'in har yanzu jikin nata yakasa koma mata daidai had'e da cewa. "Fita, fita, fita tsaya can bkin qofa Ina zuwa, Kai ma tashi fita tabarma na nan gefe ka shinfid'a ganinan fitowa" tana nuna masu qofar fita da hannu, jikin Rashida na rawa tajuya zata fita da sauri yariqo hannunta, "Haba innar mu keda bakida lafiya mezaisa sai kin wani fita, Rashida cefa ba wata ba ni kuma d'anki ne, me zaisa kice muzauna awaje." "Kaga kayi abunda nace maka, idan Kai d'ana ne ita wannan abarfa, karka manta shifa bare ba'a bashi amana Taya za'ayi inbarta tashigo tagane mani sirrin d'aki asamu damar cutar dani, maza kufita nace." Juyawa yayi yana riqe da hannunta yana d'an mammatsawa ahankali saboda tasamu suka fito d'akin, Tabarmar dake gefe Rashida tajawo yana kallonta ta qaqaro murmushi ta sakar masa had'e da shimfid'awa ta suka zauna, murmushin shima ya sakarmata kafin Yaya hawwa tafito a dudduqe ta zauna abakin qofar shiga d'akin nata, kallonta yayi yace "Ina wuni innar mu, ya qarfin jikin?" "Lafiya klw" tafad'a fuskarta ad'aure tana qarewa Rashida data sinne kanta qasa kallo da yake akwai wuta, d'ago kai Rashida tayi batare da tasan tana kallonta ba tace, "Ina wuni? ya qarfin jiki." "Lafiya" ta amsa mata tana dalla mata wata irin muguwar harara, addu'a ta shigayi cikin zuciyarta saboda tasamu sauqin yanayin da take jin kanta aciki, can tajiyo dirar muryar Yaya hawwa akunnuwanta. "To atashi atafi idan shikenan Ina so inyi magana da d'ana." Jiki ba qwari Rashida tamiqe tabar wajen. "Kai nura nifa inkan bid'ar lafiya ga yarinyar nan kada ka koma kawo man ita shiyata saboda natsaneta bana son ganinta ko kad'an." "Haba innar mu, ai yakamata ace ko albarkaci na taci, bai dace ace kinyi mata haka ba ko kad'an, don ALLAH kicire wannan tsanar da kikayi mata tunda batada dalili." STORY CONTINUES BELOW "Iyyeee lallai nura kace wani abu, wato ni zaka gwadama cewa kaima cikakken namiji ne yanzu saboda waccan 'yar abar, koda yake bansan wane kalar surk'ulle akayo maka ba kabi ka lashe dole kafad'a mani magana, to bari kaji nafad'a bana sonta zo ka dokeni, yarinya bare da ita har kace banida dalilin tsanarta bayan ta ruguje mana al'adar gida." "Haba innar mu, al'adafa ba addini bace.." "Kai ni tashi tafi kabani waje ban iya sauraren wud'annan suruttan naka." "To jikin fa?" "Nawarke tashi kaje."tafad'a cike da takaicins. "ALLAH yabaki hak'uri innar mu seda safe." Yafad'a tare da miqewa yafice, yanaji tasaki wani uban qyacci dake nuna akwai wata aqasa amma ransa yaroqi ALLAH ya fahimtar da mahaifiyarsa taso matarsa farincikin sa... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/7, 10:03 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___25πŸ’Ž Koda yafito yasamu bata wajen kuma babu alamar takoma part d'insu don arufe yake, shiyar Inna Bilkisu ya leqa ko zai gata acan, cikin sa'a ya hangota gefe zaune ita dasu na'ima da fadila yayun Aysha suna fira ita kuma Inna Bilkisu na d'aura jiqaqqar ayar da take sayarwa, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya gaida Inna Bilkisu had'e da cewa Rashida. "Ashe nan kika shigo?" "Eh nafita d'auko ayar nan ne naganeta tsaye abakin qofar shiga shiyarku shine nace tazo nan tajira kafito saboda wajen akwai sauro sosai." Inna Bilkisu tafad'i haka tana kallon Rashidar data noce kanta qasa tayi kamar batasan da shigowarsa ba saboda kunya. Sosa d'an qeyar kansa yayi had'e da cewa "eh da yake munshiga gaida innarmune shine nace tajirani muje wajen baffa." Tashi kuje Rashida kinbar mijinki tsaye, miqewa tayi tayi mata seda safe itama su aysha nace mata "aunty seda safe" suka wuce. Kafin su isa wajensu baffa don da alama duk suna can d'akin da yake ya kalli fuskarta da yake akwai hasken wutar nefa ko Ina agidan yace "habibty kiyi hak'uri da abunda innar mu tayi maki kinji ko?" "Laa..bakomai mai malamina ai don ta isa ne, karka damu ni banji komai ba tunda mahai fiya take agaremu." Murmushi yayi yan qara jin qaunarta aransa kafin ya jawota ajikinsa "Ina sonki sosai d'alibata." dariya tayi tare da k'wace jikinta daidai lokacin suka iso bakin qofar shiga d'akin baffa sunajin tashin firarsu, sallama yayi suka amsa sannan yashigo ita Kuma tayi tsaye abakin qofar, Sosa kansa ya shigayi had'e da kallon baffa Usman yace, "Baffa zuwa tayi tagaisheku." "A'a'ah to to Masha ALLAH, shigo da ita." Leqowa yayi had'e da cemata tashigo, tashigo bakinta d'auke da sallama kanta na qasa a duqe ta duqa har qasa tana gaishesu, daga baffa sai baffa Usman suka amsa mata shikuwa baffa Ali gefe ya koma abunsa tare da d'aukar redion baffa ya kara akunne don kar yaji abunda suke fad'a, ya jiki tayiwa baffa had'e da yimasa addu'ar ALLAH yabashi lafiya, STORY CONTINUES BELOW Ba baffa kad'ai ba hatta baffa Usman sun yaba da Rashida sosai tare da yimata nasiha akan tabi mijinta akan dukkanin abunda bai sab'awa ALLAH ba, kafin su sake had'asu subiyun suyi masu nasiha sosai akan haqqoqin junansu dake kansu, har suka gama baffa Ali baice komai ba saida baffa yace "To Ali kai bakace masu komai ba, yakamata a matsayinka na mahaifinsu kasa masu albarka da 'yar nasiha ko kuwa?" Ganin Babu alamun wasa a fuskar baffa Yasa ya ajiye redion had'e da cewa. "To duk abunda yakamata ince ai kunce sai dai nayi d'an qari akai, Kai nura kasani zumunci ba wasa bane don haka kanunawa matarka tariqe maka 'yan uwa da daraja kada ta walaqan tasu haka kaima, kada kanunawa matarka fifikonta akan 'yan uwanka don ana rabuwa da mata amma ba'a rabuwa da 'yan uwa, 'yan uwa da kake gani duk inda suke sunfi bare.." "Haba Ali.." baffa Usman yafad'a ransa ab'ace da zimmar dakatar dashi baffa yariqe hannunsa alamar ya qyaleshi. Cikin isa yaci gaba da cewa "Kuma kar inji kar ingani kisake inji ance kin ware mana d'aya acikin 'yan uwa duk d'aya muke, bama son had'e had'e balle anyi ance don cikin ahali guda kika shigo bamu yarda kiraba mana d'aya biyu ba, yanada 'yan uwansa mata da kika iskosa dasu don haka kada mugun kishi yasa inji ance kin rabashi dasu ko kin hantaresu kinji nafad'a maki?." "In sha ALLAH baffa nagode sosai" Rashida tafad'a cikin girmamawa da kuma sakin fuska, Hakan baqaramin yiwa su baffa Usman dad'i yayi ba don azatonsu nan take yarinyar zata nuna b'acin ranta wanda da wannan baffa Ali zai samu damar cusguna mata akoda yaushe, "To Rashida munsan gidanku Kuma munsan tarbiyarki don haka kiji kiqi ji ki gani kiqi gani, duk idan akace akwai taron mutane to dole saida hak'uri saboda sai kaga mabanbantun halayye da Kuma d'abi'u don haka kisa haquri kuma kiriqi ALLAHn ki ubangiji ALLAH yayi maku albarka ya zaunar daku lafiya kuma yabaku zuri'a masu albarka." "Amin baffa ngd" tafad'a tana maijin dad'in addu'arsa. Miqewa Nuraddeen yayi aransa yana mai godewa ALLAH daba baffa Ali kad'ai yabashi a matsayin qanen mahaifi ba badon haka ba da baisan meye makomar rayuwarsa data iyalinsa acikin gidannan ba, amma yanzu koba komai yasan idan yaji d'aci awani b'angaren to zaiji dadda'an zaqi awani b'angaren guda. Saida safe yayi masu sannan yawuce agaba tana biye dashi abaya, adarare baffa Ali ke satar kallonta aransa yaji natsuwar yarinya ta kwanta masa arai duk da dai zuciyarsa bata buqatar haka, Amma Babu yanda zaiyi don yabon gwani yazama dole, ko maqiyin ALLAH ya kalli Rashida yasan batada makusa ta ko ina gata da shawar kallo a fuska, kallo d'aya zakayi mata taburgeka idan kuma ka zauna da ita cikin qanqanen lokaci zata shiga ranka wanda hakanne yasa cikin lokaci qalilan soyayyarta tayiwa Nuraddeen mugun d'auri azuciya. Kwanci tashi babu wuya awajen ALLAH tuninrashida tabuge sati d'aya agidan, abubuwa da dama sun faru na b'acin rai gareta amma bata tab'a tada kai ta kalla ba, kullum addu'arta shine kada ALLAH yabarta da dubararta acikin alamurranta kuma yabata haquri mai yawa agidanta, tana samun kula sosai awajen Inna Bilkisu dasu baffa Amma awajen yaya hawwa banda tsangwama da kyararta babu abunda takeyi, Babu ranar da zatazo bataje ta gaisheta ba kuma duk take saita b'ato mata rai, hakan kuma bazai hana gobe ta koma ba, musamman tacire kular da take zuba mata abinci kullum safiyar ALLAH Amma bai hana ta iskota da kwano tace tazubo mata abinci, wanki da sharar gida duka yimata takeyi amma koda yaushe dad'a tsigarta takeyi, kulawa da tarairayar da take samu awajen Nuraddeen yasa bata ajiye abubuwan agabanta balle su dameta, gashi akullum idan umma takirata cikin yimata wasiya da haquri take Wanda hakan yaqara zame mata linzami wajen gudanar da rayuwarta agidan, baffa kuwa tun tana jin kunyarsa har tadena ta d'aukesa tamkar mahaifinta, lokuta da dama takan shiga wajensa idan Nuraddeen baya nan da littafanta na arabiya ya dinga qaramata daga inda ta tsaya agida, wasu lokuttan kuma tayi masa gyaran d'aki ta share ta kawo masa abinci yaci, hakn kuwa ba qaramin tai maka masa yayi ba don daka kallesa zaka fahimci yasamu sauyi arayuwarsa, Wannan dalilin yanqara haifar mata da tsana mai qarfi azuciyar Yaya hawwa fiye da wacce take yimata ada, hakan yasa tasake d'aura d'amarar ganin tafidda ita gidan tako wane hali, duk ranakun da Nuraddeen yake gida Yaya hawwa batada wajen zama imba shiyarsu ba, haka zata ararrashe akan kujera tace akunna mata kallo adafa mata wannan a soya mata wancan, duk wani motsi da zasuyi akan idonta basuda wani shaqat, ga Nuraddeen mayen soyayyane yanaso akoda yaushe yadinga rab'ar jikin matarsa Amma bayada wannan damar saboda yanda tayi masu kane kane, tun Rashida Bata damuwa har taso ma jin daban saboda tun hutun sati biyun daya d'auka yagama sangartata da kuma lalatata da kalolin soyayyarsa, sun koma saidai suyi soyayyar a kitchen idan tace ta d'ago mata wani abun sai yayi kamar zai fita shi kuma anan yake samu ya lallab'a sushige suyita soyayyarsu kamar wasu munafukai, randa Yaya hawwa tagani kusan Tara masu jama'a ta tashiyi saboda masifa sai kace ba miji da mata ba, wai sun maida ita 'yar iska sun barta a d'aki ita kad'ai, A ranar baffa yakirata yayi mata fad'a sosai akan taqyale yaran nan tadena shiga shiyarsu inbada qoqqwaran daliliba kada mutuncinta yazube, ai kuwa tayi masa tas tace bazata Dena ba in ya isa ya taso ya riqe mata qafafuwa ta hanata shiga, tsananin b'acin rai ranar daqyar yayi bacci saboda ciwon daya nemi taso masa kamar zai kashesa. Haka aka d'aukesa akayi asibiti dashi da safe aka duddubasa had'e da yimasa allurai sannan suka dawo, Aranar data tashi shiga shiyar duk saida tasa aka kirawo mata yaran gidan tace su ahigo suyi kallo suma su d'ebe qeyar ido, adako korarsu takeyi tana hantararsu muneera ba kunya itama tabisu sukaje suka cika d'akin tab ko masokar tsintsiya babu banda hamami babu abunda ketashi aciki, da yake lokacin har tagama girki kawai ta d'auki na baffa tanufi qofar fita riqe dashi zata kaimasa bayan tasa takunna masu kallon, tana wucewa Yaya hawwa tayi tsaki had'e da cewa "yarinya indai wannan gidanne sai nasa kinficesa da kaifin qafafuwanki." Nuraddeen kuwa dama yana uwar d'aki kwance yana bacci sai dai kawai yajiyo yayar yara afalo da sauri yafito don ganin ko lafiya, Tsaye yayi cak yana kallon ikon ALLAH sake da baki tare da kallon mahaifiyar tasa data ashisahire saman kujera, tsabar b'acin rai baisan sadda yayi kukan kura ba yafara fatattakar yaran daga d'akin, aguje duk suka fita in banda muneera da tayi tsaye tana kallonsa had'e da susar kanta, wani irin zazzafan mari ya d'auketa had'e da cewa. "Uban me kikeyi anan." Kallon yaya hawwa data miqe tsaye tana gyara zanenta tayi dafe da kunci tana kuka tace, "Inna ce.." tare da nunata, "Buhun uba!, yaushe nace kishigo ba yara nakira ba kika taso da wud'annan gwalmammin qafafuwa naki kika biyosu don kina sakarai, Kai kuma akan me zaka koresu suna kallonsu." Shiru yayi hannunsa riqe da kunkuru ya sa d'ayan ya shafo kansa sannan cikin b'acin rai ya sake d'auke muneera mari yana fad'in, "maza kibar d'akinnan kafin naji maki" b'are baki tayi tare da fad'uwa zaune wajen tasa wata irin muguwar qarar da saida Yaya hawwa dake shirin komawarta tazauna akan kujerar tazabura tana fad'in. "Ke munafukar ALLAH tashi kifita kafin nima naqara maki." Rashida, Rashida, Rashida, Nuraddeen yashiga k'wala mata kira ransa ab'ace, dama gashi cikin b'acin rai ya wuni saboda halin da mahaifinsa ke ciki, basu jima da dawowa daga asibiti bane yasamu ya kishin gid'a sai ga wani b'acin ran mahaifiyarsa na neman qara masa.... [7/9, 12:00 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___26πŸ’Ž Rashida kuwa dake can d'akin baffa takai masa abinci bata san wainar da ake toyawa anan ba saida Aysha yarinyar Inna Bilkisu ta iskota aguje tafad'a mata, murmushi kawai tayi batare data nuna abun yadameta ko kad'an ba taci gaba da yiwa baffa yankan farcen da take yimasa don koda tashigo ta iskosa yagama cire na hannuwa yana dubarun yanda zai duqo ya cire ta qafafun shine takarb'i rezar tana qarasa masa suna d'an fira jefi jefi.+ Muryar Aysha dake a tsaye har lokacin ta tsinkayo daga dogon tunanin da take akan ynayin rayuwar da take ciki dangane da matsalolin uwar mijinnata na yau da kullum tana fad'in, "Aunty fa Yaya nakiranki." Adai dai lokacinne tariqe farcen qarshe da zata qarasa cirewa baffa akaifar, saida tacire sannan ta d'ago kai tana kallonta had'e da cewa. "Jiki ganinan tafe kinji." Kallonta baffayayi lokacin tana mik'ewa daga zaunen da take bayan ta d'auki k'yallen data aza qasan qafafuwan nasa qumbar da take yankewa na zuba akai ta kakkab'ik kesa awaje tadawo ta lunkesa ta mayar a inda yasa tad'aukosa d'azu. "A gaida Rashida ALLAH yayi maki albarka, sai nakeji gaba d'aya jikina yayimun sayau tamkar an d'auke mun wani abu akai." Baffa yafad'a yana jujjuya yatsun hannuwansa, dariya tayi had'e da cewa. "Kasan dattice idan ta tararwa mutum shiyasa wanda suka saba yankawa idan tataru basajin dad'in zama da ita ajiki, baffa bara naje nadawo nazuba maka abincinka kaci sai kasha magani." Yana kallon qafafuwansa yanda faracen sukayi masa tas saboda shi mutumne mai tsananin zafta da son gyara jiki yace. "To jeki, ALLAH yasa kigama lafiya, yakawo maki rabo Mai albarka." Akunyace tabar d'akin batare data amsaba tana murmushi tanufi qofar shiga part d'insu, tana kawowa Inna ruqayya nakawowa itama saboda qarar 'yarta data jiyo, qoqarin kaucewa Rashida tayi ta bata hanya tawuce amma saboda rashin imani irin na Inna ruqayya tasa kafad'a da qarfi ta mangajeta tafad'a ajikin ginin shiyar tasu kanta kuma yabugi gambun qofar tayi baya baya tafad'awa sauran buloluwan da akayi aikin sashensu dake ajiye gefen jikin ginin. Cike da azaba zafin buguwar da tayi tasaki wata irin qarar da saida Nuraddeen dake falo zaune ya dafe kansa zabura, da sauri yafito sukaci karo da Inna ruqayya da babunko d'igon imani da tausyi atattare da ita tabaro Rashida can kwance ta tahowarta tana masifar waya tab'a mata 'ya, ko kallonta beyi ba shima ya wucikke warsa tare da tsayawa bakin qofar ya leqo don ganin ta Ina yaji muryar qarar Rashida, daidai lokacinne yaga Inna Bilkisu tarugo aguje tare da 'yarta fadeela tana fad'in. "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun Kai ruqayya wannan wane irin rashin imanine haka ki bangaje yarinyar mutane tafad'i kuma duk da kinji qararta bazaki tsaya kiduba halin da take ciki ba." Har ta aza qafarta tashiga d'akin tajuyo cike da maseefa tadawo don dama jiraye take da inna Bilkisu, bangaje nura tayi dake tsaye bakin qofar kamar an dasa yana kallon ikon ALLAH, gaba d'aya saboda yanda gaskiya tayi masa yawa kasa cewa komai yayi sai bin Inna Bilkisu data tallabota tana d'an bubbuga gefen uncinta had'e da kiran sunanta yakeyi. "To munafuka algunguma, sarkin ashibanci da son yabo, fad'i ba atambayeki ba tsabar kicifi da iyayi ina ruwanki, meya shafeki no aciki ko dake akeyine da zakizo kisamun baki, kinsan me tayi manine da zakizo kisamun baki, Ina yanzu kika jiyo qarar muneera acikin d'akin nan Amma tsabar mugunta Ina kallonki ko ajikinki tunda ba 'yarki bace, sai yanzu don antab'a bare Zaki taso mana da wani migun bakinki kisa mani baki, to wallhi ahir d'inki Bilki da shiga sabgata ko inyi maki rashin mutunci, ni uban waye nasakawa baki da aka tab'amun tawa 'yar." Inna ruqayyace tafad'i haka tare da fitowa tayi tsaye akansu batare data damu da ganin halin da Rashida keciki ba. "Fadeela jeki d'ebo mun ruwa ki kawo inaga yarinyarnan suma tayi." Da sauri fadeela tabar wajen taje ta d'ebo ruwan takawo Inna Bilkisu ta karb'a ta yayyafawa Rashida. "Mtssssss.. ALLAH ma yasa tamutu idan taso ba abunda yashamun kai iyayenta keda asara bani ba." 'dago kai Inna Bilkisu tayi had'e da kallonta hawaye cike da idanuwanta, kasa magana tayi ta maido kanta had'e da sake zuba ruwa a hannunta tashafawa Rashida, wata irin doguwar ajiyar zuciya Rashida tayi tare da dafe goshinta dake mata rad'ad'i tana fad'in. "Wash.." "Sannu Rashida." Inna Bilkisu tafad'a tana kallon inda ta dafe goshin nata ya kumburo, sai alokacin nurah ya qaraso wajen idanuwansa sun kad'a sunyi jawur kamar an watsa masa barkono aciki, wani irin zugi da rad'ad'i yakeji kallon halin da matarsa keciki amma yakasa tab'uka komai saboda jin nauyin Inna Bilkisu dake wajen tana kula da ita, had'a idanuwa yayi da ita ta sakar masa murmushin daya tabbata cikin qarfin hali tayisa don takwantar masa da hankali, "Nura d'auki matarka kushiga ciki, kaga goshinnan nata yabugu kad'an lullunda matashi koya saki, ALLAH yasawaqe kuma yaqara maku hak'uri." STORY CONTINUES BELOW Ya tsinkayo muryar Inna Bilkisu nafad'a cike da damuwa, duqawa yayi da niyar riqota, Inna ruqayya tariqo wuyan rigarsa had'e da cewa. "Ai wallahi baaka isa ba, mutum befi mutum ba balle ka dakarmun 'ya na qyaleka, wuce muje naga ubanme kayiwa 'yar tawa take wancan reren kukan." Ta jasa suka nufi cikin sashensa yana biye da ita, wani irin tuquqi yakeji aransa da badon matar qanen mahaifinsa bace ko wace yau sai ya koya mata hankali, qoqarin miqewa tsaye Rashida tayi hawaye na zubo mata daga cikin idanuwanta Inna ruqayya tayi saurin d'agata had'e da riqota sosai tanufi cikin shiyar tata. "A'a Inna Bilki bana son ganin abunda zai faru tunda tsakninsa ne da 'yan uwansa, kawai ki kaini shiyarki" Rashida tafad'a tana sake goge hawayen dake faman kaida kawo saman fuskarta akaro na ba adadi, Kiyi hak'uri Rashida in sha ALLAH komai zai wuce." Sashenta tanufa da ita suna kai bakin dangaramar da zaka taka su ahiga cikin d'akin jiri ya sake d'ibarta da kad'an tafad'i, da sauri fadeela tariqota ita da Inna Bilkisu tana dafe da kanta sukaqarasa shiga da ita. Acan cikin d'akin Rashida kuwa yaya hawwa na can hakince saman kujera tana kallonta, ita kuma muneera na zaune sai faman reren kuka takeyi tana susar kai sai kace wata sabuwar amaryar da akayiwa auren dole, duk abunda akeyi tana jiyosu daga tsakar gidan amma tayi kamar batasan anayi ba, bini bini take juyowa tana kallon muneera dake kuka can kuma sai tayi shiru ta qurawa tv ido tana susar kai tace. "Au munafuka dama kukan na qaryane! Wato anga abunda sai gidan masu kud'i ake gani d'an ba'a saba ba kin baza idanuwa sai kallo kike yi, ja'ira kawai." Ta kaimata dunguri a qeyar kai, sake fashewa da kuka tayi tana cije gefen d'an kwalinta had'e da sosa qeyar kan nata data daka, Inna ruqayya ce tashigo d'akin har lokacin tana riqe da kwalar rigar Nuraddeen tana fad'in. "Wato kasan matar taka bata cikin d'akin shine ka kamamun 'ya ka zalunta to wlh bazan yarda ba, ai kana ganinta ka zame kaje ka auro wata shine yanzu kake nema ka cuceta don baka samu yanda kake soba, wuce muje naga abunda kayimata" muneera naganinta ta taso tanufo inda take tana sake tab'e baki. "Buhun uba me zan gani haka ruqayya, d'an nawa kika shaqowa wuya haka sai kace wanda yayi sata! Uban me yayi maki." Cikasa Inna ruqayya tayi kafin tariqo mueera tana fad'in. "Aiho dama kina cikin d'akin Yaya hawwa?, Kukan muneera najiyo nazata shikad'aine aciki shine na tasosa agaba yazo ya fad'amun abunda yayi mata gabanta har take wannan reren kukan saboda nasan duk abunda yasata kuka to ba kad'an bane" Tafa hannuwa Yaya hawwa tashigayi tana sallalami had'e da gyara d'aurin zanenta kafin tace, "Ke ruqayya sharri zakiyiwa yaron nawa don kinga bayyi magana ba?, shi dake da matan mezaiyi da 'yarki yarinya kamar an tsoma kaza acikin ruwan zafi anfiddata, tsigalalliyar yarinya munafuka kawai da ita, mai yagaggen baki zakuyi masa sharri, to maza kufita kafinna karya mata wud'annan gwalmad'ad'd'in qafafuwan nata." "Dakata yaya hawwa gaskiya nagaji da wannan cin kashin naki, aci zalin yarinya agabanki bazakiyi magana ba kuma sai kiqara mata da kushe mata halitta, gaskiya nagaji kidena don nima ina son abuta a haka, shikenan daga zuwa tambayar meyayi mata sai kidinga cab'a mani magana..." Bata rufe baki ba ta Nuraddeen yafito a fusace riqe da belt a hannunsa dama tuni tsananin b'acin rai yasa ya shige uwar d'aki yayi zaune bakin gado yana tunanin ko meyi zai yimata ya rage rad'ad'in abunda tayiwa habibty d'insa, babban takaici ma wai shi Inna ruqayya ke zargi akan muneera ko mezaiyi da ita, meye ma zai tsinta ajikinta da zatayi masa wannan sharrin, yana zuwa ya finciko muneera daga jikinta idanuwansa jajir ya jefar da ita a qasa had'e da nuna Inna ruqayya yace. "So kikeyi nafad'a maki abunda nayi mata ko, to bari kigani na nuna maki, bari kiga kome nayi mata yanzun nan." Jibgar muneera yafarayi da belt d'in yana watsa mata tako ina tana ihu, sheqeqe Yaya hawwa takalli Inna ruqayya data turo idanuwa waje tana kallonsa tace "yawwa qarawa shegiyar, yimata lilis munafukar yarinya kawai, daga mari sai uwarki tabisa da mugun sharri, yita jibgarta sai tagane shayi ruwane?" Tafad'a tare da rab'awa ta gefensu tayi tafiyarta, qoqarin riqesa Inna ruqayya ta shigayi tana tsigarsa amma da yake zuciyarsa tariga tarufe a fusace ya d'ago kai yana cewa. "Wlh kibar ganin ke matar qanen mahaifinace duk kika matso wajennan saina had'a dake." Ganin yanda fuskarsa ta sauya yasa tayi gum da bakinta tayi waje tana haragagon neman taimako, duka kam ranar muneera tashashi tun tana ihu har takasa shi kuma yace bazai dena dukan taba har sai lokacin data bar d'akin da qafafuwanta yanda gobe koda wasa akace tashigo shiyarsa bazata shigoba, Inna ruqayya kuwa tayi ihun neman taimakon har tagaji babu wanda yazo ai kuwa tana ta zundumawa mutanen gida zagi wai duk munafukaine sunaji za'a kashe mata 'ya kowa ya qyale, STORY CONTINUES BELOW Inna Bilkisu kuwa ji tayi kamar ta taka tsabar farinciki don koda baiyi komai akai ba ta d'au alwashi akan sai tayi mashi fad'a daya tashi tsaye ya qwatowa matarsa 'yancinta a gidan matuqar shi ba lusarin namiji bane, sai gashi da kanshi yayima kansa fad'a. Yaya hawwa kuwa dama sashenta tawuce tashige d'aki had'e da haye gadonta ta soma bacci batare data sakebi ta kansu ba, su baffa Ali da baffa Usman su kuma basa gida balle su kawo mata d'auki , Sai da jikin muneera yayi tib'is tukuna tafara qoqarin k'watar kanta daga hannunsa ganin babu sarki sai Allah, da jan gindi tafito shiyar Inna ruqayya na tsaye bakin qofar takasa komawa sai faman zunduma masa zagi takeyi, da sauri ta riqota had'e da ida jawota tafito sukayi shiyarsu tana kuka yace. "Wannan shine abunda nayi mata, kuma kad'an tagani, idan nakoma ganin qafarta cikin shiyata saina maida ita gurguwar qarfi da yaji." Sannan ya juya yakoma ciki, Toilet ya fad'a had'e da d'ibar ruwa acikin durom d'in dake ciki yafara sakarwa kansa yana sakin wata irin ajiyar zuciya. Yajima aciki kafin yafito ya hau gyaran falon had'e da sharesa tass, feffesa room freshener yayi soboda tsamin da yaji d'akin nayi sannan yanemi kujera mai zaman mutum uku ya kwanta rigingine kansa na kallon silin zuciyarsa cike da matsananciyar damuwa Acan shiyar Inna Bilkisu kuwa saman gadonta suka kwantar da Rashida, hannuwanta da idanuwanta tashiga duddubawa tana son gaskata abunda zuciyarta ke rayamata akanta tun kwanaki biyu da suka wuce saboda yanda ta canza, murmushi tayi had'e da cewa, "Alhamdulillah ALLAH kaine abun godiya." har lokacin takasa Dena murmushin da takeyi, kallonta fadeela tayi had'e da cewa, "Inna menene?." Bata tanka taba saidai kallon Rashidar data koma yi tana qoqarin rufe idanuwanta saboda baccin da take ji, baccinta mai isarta tayi kafin nan tafarko tana jin wata irin matsananciyar yunwa dama d'azun data gama abinci bata samu taci ba saboda tare sukeci dashi shikuma alokacin bacci yakeyi, Kasancewar koda ta tashi bakowa ad'akin yasa tasauko saman gadon had'e da fitowa bakin qofar d'akin ta saki wata uwar hamma dake nuna ba qaramar yunwa take jiba. "A'a Rashida har kin tashi?." Inna Bilkisu dake sharar cikin rumfar tasu tafad'a tare da d'agowa tana kallonta. "Eh inna barka da marece, shara kikeyi?." "Eh wallahi wajenne ya d'anyi datti ga baffanku yana kan hanyar dawowa ke sanshi baya son datti ko kad'an, ya qarfin jikin naki?" "Alhamdulillah da sauqi Inna bari na riqa maki." "A'a ki barshi ai nakusa qarasawa, maza jeki tun d'azu mijinki na ciki nasan ran nan nasa a cunkushe uake yanzu, kuyita haquri har ALLAH yakawo qarshen wannan al-amarin kinji ko." Duqar da kanta qasa tayi tana wasa da 'yan yatsun hannunta tana murmushi sannan tabar wajen, har takusa shigewa Inna Bilkisu tace, "Au Rashida." Juyowa tayi tana kallonta taci gaba da cewa "dama nace ki kula da kanki saboda yanzu bake.." Bata qarasa ba saboda hango Inna ruqayya da tayi nafitowa daga cikin d'akinta sai tayi shiru had'e da cewa "Jeki rashida maya magana dake anjima" "Mtssss...munafucci kunun kanwa!." Inna ruqayya tafad'a tana jefo wata tasar Inna Bilkisun data gani cikin rumfarta. Batace mata qanzil ba taci gaba da shararta ita kuma tawuce shiyarta batare data fahimci kome Inna Bilkisun ke nufi ba. *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/9, 10:52 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž STORY CONTINUES BELOW _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___27πŸ’Ž Tana shiga Kai tsaye kitchen tashiga ta d'ebo abincin a plate, tun kafin taqaraso cikin d'akin tasomaci saboda azabar yunwar da takeji, kwance ta iskosa idanuwansa arufe amma babu alamun bacci yakeyi saboda yanda k'wayar idanuwansa ke rawa, qasan carpet a bakin kujerar da yake kwance ta zauna tana cigaba da cin abincinta hannu baka hannu akushi, a hankali ya jaye hannusa dake saman goshinsa yana kallonta fuskarta a sake tamkar babu abunda yafaru, abincin dake gabanta ya kalla sannan ya kalleta cike da tambaya, saboda iya saninsa tunda tazo gidan tare suke cin abinci yazu ko kimanin tsawon watanni hud'u kenan, to meye dalilinta nayin haka kenan ko haushinsa takeji ya tambayi kansa had'e da tashi zaunne yana kallonta. 'Dago kai tayi ta kallesa tare da sakin murmushi daga haka Bata cemasa qanzil ba Kuma shima bai cemata ba sai data canye abincin tas had'e dayin gyatsa. "Alhamdulillah" tafad'a tana lashe yatsun hannuwanta har lokacin idanuwansa nakanta, turo baki tayi yasakar mata murmushi tare da miqewa ya d'auko mata ruwa a fridge ya miqa mata, karb'a tayi tasha sannan tamiqe tare da d'auke plate d'in takai kitchen, tray d'in data had'a abincinsu akai ta d'auko takawo agabansa ta ajiye sannan takoma saman kujerar kusa dashi ta zauna had'e da d'ora kanta saman kafad'arsa. "Malamina ka sauko kaci abinci, nabarka da yunwa ko?." Seda yad'an harareta sannan yace. "Bazanci ba!." 'Dan turo idanuwanta tayi awaje tana qyaqqyaf tasu had'e da cewa, "meyasa?. Abincin da kafiso ne nayifa!" Taqarasa maganar tana b'ata rai tare da nad'e hannuwanta saman qirjinta, mintsili ya kaimata a kumatu had'e da cewa. "Saboda bakya son naci shiyasa kikaci naki bayan kinsan tare mukeci ko fushi kikeyi da nine akan abunda yafaru." "Laaaa...wlh ba haka bane malamina, kawai yunwa nakeji sosai shiyasa na fara ci, atunanina ma bacci kkeyi, kayi hak'uri nazuba maka kaci nasan kana jin yunwa kaima." "E.ehm bazanci ba." Yasake fad'a yana nad'e hannayensa akan k'irji kamar yanda tayi d'azu ya juya mata baya, saqalo hannayenta tayi ga wuyansa ta rad'a masa akunne, "afuwan habibyyy.." taja qarshen cikin wani salo daya sashi juyowar da bai tashiba cike da mamaki don bai tab'a jin takirasa da wani suna ba inba malaminta ba, "me kikace habibty?, Pls sake fad'a naji." Maqe kafad'a tayi had'e da cewa, "o'oh sai in kaci abincin tukuna zan fad'a har sai kace ya isa" zamewa tayi daga kan kujerar tana dariya ta zubo masa abincin a plate, jallop rice ce tasha kayan ciki da kifi dasu irin baqin kifinnan gasashshe mai d'an karen dad'i, saman kujerar tadawo tana riqe da plate d'in abincin da cokali aciki, d'ebowa tayi a spoon takai masa abakinsa ya juyar da kai gefe, "Meye?" "Kifad'a mana." Yafad'a had'e da d'an d'aure fuska, dariya tayi sannan tace, "Shikenan! Nafad'a habiby, habiby, habibyyy.." bud'e baki yayi zaiyi magana ta tura masa cokalin abincin abaki had'e da sakin dariya, murmushi yayi tare da nunata da yatsa. "Ke ko?" Haka tadinga bashi abaki yanaci har yaqoshi ta tattara kayan takai kitchen ta dawo, miqa mata hannu yayi ya zaunar da ita a tsakankanin kafafuwansa ya turo kansa tagefen wuyanta. "Habibty!" Yafad'a cikin wata irin kasalalliyar murya, "uhmm, habibyn habibty!." Shiru yayi na wasu mintota yana nazarin irin kalaman da zaiyi amfani dasu wajen bata hak'uri akan abunda yafaru, juyo fuskarta yayi yayi mata kiss saiti inda ya d'an kumburo a goshinta sannan ya sake maida kansa agefen wuyanta yace, "kiyi hak'uri, kiyi hak'uri, kiyi hak'uri bisa abubuwan dake faruwa, nasan cewa ba kad'an kike kauda kanki ga abubuwan da mahaifiyat da kuma wasu 'yan uwan keyi maki ba, kwata kwata banajin dad'insu har ga ALLAH domin ke amanace agareni, nakan tsinci kaina cikin damuwa mai tsanani aduk lokacin da naga ana cutar mani dake, zuciyata na quna inajin wani d'aci a maqoshi domin babu abunda nake so araina duniya fiye da inganki cikin farinciki, zallar hak'urinki da tarbiyarki suke galaba akaina wajen kawar mani da damuwa badon haka ba inada tabbaci akan da tuni zuciyata da kuma rouhina sun daina aiki ajikina saboda kasa jurewa ganin duk wani abu da zai cutar dake, nayarda cewa shi so sa'ane kuma dacene tun a ranar dana had'u dake, domin kin zame mani gwana takowane fanni, a kyau kece gwanata, a hak'uri Banda yake, a iya kula da tarairayar miji kinfi mata dubu, girki tsafta da kawaici sai dai nace Masha ALLAH, Alhamdulillah domin duka nasamu awajenki, na tabbata kece alkhairina na duniya da kuma lahira don haka Ina mai sake baki haquri ga yanayin da muka tsinci kanmu aciki, natabbata wata rana zai zamo labari." Tunda abubuwannan kefaruwa bata tab'a zaunawa ta zubar masu da hawaye ba sai yau, koshi saboda wani nauyine da takeji azuciyarta taji ya sauka saboda dad'ad'an kalaman daya fad'a mata hakan shine yayi silar zubowar hawayenta batare data shirya ba, wud'anda batasan da wace kalma zata fassarasu ba, na bak'in cikin abubuwan da suke faruwa da itane ko kuma na farincikin soyayyar mijinta dake lunkuwa azuciyarta. hannu yasa ya juyo da ita gaba d'aya suna kallon juna tare da tallabo fuskarta yana kallon kyawawan idanuwanta dake zubar da hawaye, bakinsa ya nufo dashi wajen fuskarta tayi saurin rufe idanuwanta hawayen dake maqale aciki suka samu damar gangaro, jira takeyi taji saukarsa akan nata amma sai taji akalarta sauya saboda harshensa da taji saman fuskarta yana lashe hawayen, sannan yadawo ga bakinta ya sakar mata wani irin french kiss daya sa ta sake lumshe idanuwa tana mayarnmasa da martani. Sunfi tsawon mintuna biyar ahaka kafin ya zare bakinsa daga nata had'e dasa hannuwa yariqe fuskarta yana kallon idanuwanta d'aya bayan d'aya, STORY CONTINUES BELOW "Habibty kidena zubar da hawayenki domin duk d'igar da zasuyi suna yintane tamkar d'igar ruwan wuta abisa zuciyata, nasan ke jarumace kuma akoda yaushe nasara natare dake don haka kikara hak'uri kafin ALLAH ya yalwata mana mutashi nan kinji ko?" "Habiby ba Ina zubar hawayene akan abubuwan dake faruwane ba, hawayena na zubane adalilin samun nagartaccen miji kamarka, kalamanka nada matuqar tasiri agareni domin ako yaushe d'auke suke da saqonni masu ma'anar dake gamsar dani irin soyayyar da kake yimani Wanda hakan shine babban burina arayu, bana son wannan haqurin da kake bani domin mahaifiyarka ai mahaifiyatace hakama 'yan uwanka nawane don haka duk runtsi zai jure komai akanka matuqar kana tare dani." "Habibty bakyajin zafin abubuwan da ake yimaki ne?." "Inaji mana amma girman soyayyarka bata barin hakan yayi tasiri azuciyata." Tafad'a tare da rungumesa. Rungumeta shima yayi sosai tamkar wanda za'a k'wacewa ita yace. "I dont want to miss you in my life..., I love you for ever and ever and ever.." Rashida da wasu kalaman tafahimta wasu kuma bata fahimcesu ba tayi murmushi itama tace "Nima haka." dariya yayi don yanada tabbacin ba duka ta fahimci meya ce ba amma tace itama haka duk da dai dad'ad'an kalamaine yayi bamasu illa ba. "Habibty kema me?" Yafad'a yana sake shigar da ita ajikinsa sosai. "Yanda kace mana." Tabashi amsa atak'aice itama tana dariya, "Tom nagode gobe kishirya zamu fara lesson in sha ALLAH." "Ni bana so." "Ai baki isa ba." Nuraddeen yafad'a had'e da sakinta yana yimata cakulkuli, cikin mintuna qalilan ya mantar da ita duk wani b'acin rai da takeji azuciyarta. Rayuwa kenan haka ALLAH ke jarabtar bayinsa da sukayi imani dashi akoda yaushe, baffa dai gashi da rai amma wasu abubuwan sun buwayesa, duk fitinar da akeyi yanaji Amma Babu halin tashi, ahankali yaji damuwa naneman tayar masa da ciwonsa yayi saurin jawo hisnul muslim d'insa yana karanta addu'o'in hammu wal hazan (damuwa da baqinciki) cikin ikon ALLAH yaji komai na gushe masa, Saida yaji yasamu sassauci da salama acikin ransa sannan ya ajiye yaci gaba da ambaton ALLAH. Bayan sallar magrib su baffa Ali sun dawo don basu shigo gidan ba saida suka gama sallah, baffa ya zayyane masu duk abunda yafaru agidan wud'anda kunnuwansa suka jiyo masa, sosai baffa Usman yaji ba dad'i sab'anin baffa Ali da yace. "Ni wlh Yaya nazata wani abun mai muhimmancin ne yasa ka tsaidamu gashi tun d'azu yunwa nakeji, ai indai muneera ce da uwarta abunda ma yafi haka zakaji, ni bari inje inci abinci inaga yafimun." Yana gama fad'a yamik'e ya wuce sashensa, cike da mamaki suka bishi da kallo kafin su ahiga tunanin nemo mafita, Baffa Ali na shiga ko sannuda zuwa babu inna ruqayya da tun d'azu take zaman dakon isowarsa tace. "Alhamdulillah muje malan, wlh yau saika qwatarwa 'yata haqqinta akan cin zalun da aka yimata." "Ke ruqayya fara bani abinci tukuna yunwa nakeji." Yafad'a yana zaunawa saman tabarmar dake shimfid'e abakin qofar d'akin, sanin zai iya birkice mata idan tamatsa masa da zancen yasa taje takawo masa abincin ta ajiye agabansa, ruwa taje ta d'ebo takawo masa jikinta har tsima yakeyi ta zauna tabasa labari, Yana gamawa tashiga bashi labarin qarya da gaskiya ya mik'e cikin b'acin rai yanufi shiyar Yaya hawwa yana k'walla mata kira, iskota yayi zaune tana cin abinci bisa 'yar barandar dake cikin rumfarta akan kujerar tsugunno ta tsakar gida shima yanemi waje ya zauna. Saida takai loma abaki ta had'iye sannan yace. "Ina jinka Ali mike faruwa?" Cikin kwantar da kai yace. "Haba Yaya hawwa yanzu ace agabanki yaron nan zai kama 'yar uwarsa yayi mata mugun duka baki d'au mataki ba." STORY CONTINUES BELOW "Uwarta taja mata." tabashi amsa atak'aice tanaci gaba da tura lomar tuwonta hankali kwance. "Koma dai meye ai kamata yayi ace kin hanasa tunda 'yar tawa ba jaka bace kuma ko meye ai kece kika jamata, babban abunda kebani takaici shine keda kikace bakyason yarinyar nan kin tsaneta meye na wuni kullum a d'akinta? Kodai yanzu kin fara amincewa da zab'in barene." "Hmmm! Ali kenan, wai ku atunaninku zuwa d'akinta da nakeyi na ALLAH ne? Yaro man kaza ai duk wanda yace baya sonka to tabbas har amutu bazai tab'a sonka ba, ai tsuntsu biyune nake jifa da dutsi d'aya don haka ka kwantar da hankalinka, wannan shashashar 'yar taka ita nakeyiwa yaqi amma ita da mahaifiyarta suna neman b'atawa shiyasa na zura idanuwa saboda kada ad'agoni, duk wani shiri nawa ya kammala don gaba d'aya nagama aiwatar da abunda na karb'o wajen malan bakada imani, k'waya d'aya yarage ina kammalasa zakaga aiki da cikawa.." Yaya hawwa taqarasa maganar had'e da miqewa tana d'auraye hannunta agefen d'akin. dashe hauru baffa yayi had'e da cewa. "ALLAH yaya hawwa?" "Naka wasane Ali, an fad'a maka ja da baya tsorone, ai tuni nashirya maka maina tsaf da zan yaqi waccan yarinyar mai kama da miyagun mayu, yanda nakejin natsaneta yanzu bana tunani zan iya d'aga mata qafa har sai tabar gidannan don haka idan harkana son gurinka yacika dole kadakatar da uwar iyayin nan da muneera daga shiga sha'anin Nuraddeen, inba haka ba kuwa to dasu b'ata mun aiki k'wanda na tabbatar na dakatar dasu nida kaina."... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/11, 2:50 AM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___28πŸ’Ž To shikenan Yaya hawwa yanzu nai magana, amma tuntuni sai zuba idanuwa nakeyi naga matakin da kikace zaki d'auka amma shiru yau gshi kimanin watanni hud'u kenan da kawota. "Kaji dai abunda nafad'a maka koma meye kawai kazuba idanuwa kagani." Tafad'a tana qoqarin shigewarta d'aki, seda safe yayi mata sannan ya wucewarsa yana ayyana abubuwan da zasu faru idan burinsa ya cika. Yana fita Kai tsaye waje yayi sai bayan sallar isha'i lokacin har karfe 9 tawuce, yana shiga sashensa inna ruqayya ta sake tarbarsa da maganar cewa yayi "Kai ruqayya matsalata dake rashin hak'uri, yanzu dai ki kwantar da hankalinki munyi magana da Yaya hawwa kuma tace tana nan ta d'aukar mataki akan al-amarin." "Hmm wane mataki zata iya d'auka akai bayan duk abunda yafaru dasa hannunta itace ummul aba isu tana kallo ya narkarmun yarinya agabanta batace komai ba, Kai nifa wlh nagama gano bata son auren yarinyar nan da yaronta, kaduba yanda take kashe wuni ashiyarta kuma wai don ta Rena mana da hankali tace bata sonta." "Ashsha ana baki kina roqo, Bari in fad'a maki wlh yarinyar nan Yaya hawwa bata qaunarta tuni taje takarb'o magani wajen malan bakada imani..." Nan ya kwashe duk yanda sukayi da Yaya hawwa ya sanar da ita, lokacin muneera na kwance can acan gefen gado kafin takoma d'an d'akin da take kwana, Inna ruqayyace tace tabari har mahaifinta yadawo taji matakin da aka d'aukar masa na dukan daya yimata, wannan dalilin yasa tayi kwancenta nan ita da qannenta maza su uku ciki harda yusuf tana jiran dawowarsa. Baffa Ali daya saki baki yanata bata labari kawai sai yaga muneera ta taso tana susar kai tanufo inda suke zaune gefen gado tana fad'in. "Baffa ni babu ruwana da matarsa kawai so nake ku a auramun shi, wlh baffa Ina son ya nura sosai." Zarar idanuwa baffa Ali yafarayi don bai zata muneera na cikin d'akinba da ko kad'an bazaiyi wannan maganar agabanta ba, STORY CONTINUES BELOW "Yi haquri muneera, ai zancen yanda za'ayi aurenne muke tattaunawa." Inna ruqayya tafad'a had'e da riqo hannunta, turo manyan lab'b'anta tayi cike da rashin iya magana tace, "Wallahi Inna qaryane, ai duk Ina jinku maganine zakuyi ko korar masa mata, yo a maimakon haka kuyi mani magani na auresa kurum.." da sauri tajawota had'e da toshe mata baki shi kuma baffa Ali ya dafe kai don yasan ALLAH kad'ai ke hana muneera taje ta watsa wannan magana, abunda basu sani ba hatta Yusuf idanuwansa biyu basuyi bacci ba qannensa ne kawai baccin ya d'auka. "Shiii muneera kirufa mana asiri kidena wannan zancen kada wani yajiki, yanzu da kike wannan maganar mu ba yarinyar mukeso tafara fita ba sai ke kuma ki auresa, kinjimun shashashar yarinya." Inna ruqayya tafad'i hakan tana murgud'e mata bakin da hannu data toshe mata shi. "Kai Inna da zafi." Muneer tafad'a itama tana jaye mata hannun sannan taci gaba da cewa, "ni ku aura munshi a haka ko mata dubu garesa ALLAH zan auresa balle d'aya, so kukeyi sai na sake shekarewa aci gaba da cemun kwancen gidansu nura wlh ALLAH ni nagaji da jira." Taqarasa maganar tana fashewa da kuka, takaici ne yarufe baffa Ali kamar yatashi ya rufeta da duka shima, Amma yasan hakan na iyasa tafallasa komai don ba qaramar sakarya bace, lallashinta suka shigayi tare da tabbatar mata da cewa itama wannan shekarar kota halin qaqa saita auri masoyinta ya nura sannan suka samu tawuce d'akinta takwanta, fad'a baffa Ali ya shiga yiwa Inna ruqayya akan meyasa bata sanar masa da muneera na d'akinba ai da bai d'auko zancenba agabanta. "Yo kukan da taci yau ai sanin matakin da aka d'auka akansa kad'ai zaisa taji sanyi azuciyarta shiyasa nace ta zauna har kadawo." Tsaki yayi had'e da juyawarsa ya kwanta cike da takaicinta da ita har 'yar tata. A 'bangaren su Nuraddeen kuwa ana gama sallar isha'i yadawo gida, d'akin baffa ya shiga ya gaishesa tare da yimasa ya jiki lokacin suna zaune shida Rashida tagama b'ab'balla masa maganinsa yasha bayan tazuba masa abinci yaci tana karanta masa wasu addu'o'in dake cikin littafin (adda'u wad dawab) littafin daya qunshi nau'o'in cutuka da kuma kalolin maganukkan da za'asha ayi amfani dasu don samun waraka, d'aya daga cikinsu take fad'awa baffa alokacin, wuri yanema a gefe ya zauna yan sauraren bayanin da take yiwa baffa. "Baffa kaga wannan addu'ar ana karantata ga duk wanda ciwo yayi masa tsanani kuma aka rasa gano kowane irin ciwone ke damunsa, sai a nemi ruwa masu kyau acikin madaidaicin kwanon shan ruwa, sai a nemo kanwa da gishiri a zuba aciki, anemo albasa itama a yayyanka ta aciki sai marar lafiyar yasa duka hannayensa acikin ruwan bayan ya saka duk wud'ancan abubuwan da aka buqata sai ya karanta qula quzzai (falaq, nasi da kuma ikhlas) kenan, sannan yakaranta ayatul kursiyu karatun na sauka acikin ruwan da hannayensa ke ciki, sannan sai ya karanta wannan addu'ar kamar haka ( _Bismillahi arqiq, wallahu yashfik, min kulli da'in mardud, wamin kulli aynin au aynil hak'k'imu ALLAHU yashfik, allahummah rabbannas, ashfi bil ba'as washfi antashshafi'i laa shifa'a illa shifa'uka, shifaa'allahu laa yugadirus saqama_). sai atofa acikin ruwan acire hannayen daga ciki, sai a d'ebi ruwan marar lafiyar yasha sannan ya tauna albasar dake ciki, asake d'iba yayo wanka dasu sauran sai a dinga watsawa ko ina a cikin d'akin da yake ciki ana fad'in ( _ikhrij aduwwallah_) har ruwan su qare, to da yardar ALLAH duk marar lafiyar da aka dage anayi masa haka ko ya dage da kansa yanayi zai samu sauqi da ikon ALLAH, kaga zuwa gobe idan ALLAH yakai ranmu sai mufara baffa saboda ba'asan in da dace yake ba ko ba haka ba." Cike da farinciki baffa ya dafa kanta had'e da cewa. "Hakane 'yata, ALLAH yayi maki albarka kuma yasa adace." "Amin baffa." Tafad'a tana rufe littafin fuskarta d'auke da murmushi, juyowa tayi gefen da Nuraddeen ke zaune ta gaishesa had'e da yimasa sannu da zuwa sannan tamik'e tabar d'akin tana yiwa baffa seda safe. Bin bayanta da kallo baffa yayi kafin yayi ajiyar zuciya yace. "Alhamdulillahillazi bini'imatihi tatimmusswalihat, haqiqi Nuraddeen Ina tayaka murna da kuma alfaharin zab'in da kayowa 'ya'yanka, banida shakku akan cewa ALLAH yagama mallaka maka rabin addininka yanzu yarage wajenka kanemi rabin don samun kyakkyawar makoma, Ina roqon ALLAH nima daya dubi zuciyata ya shirya mani mahifiyarka, bansan meyake damunta ba da har zata d'auki karan tsana ta azawa wannan nagartacciyar yarinya wacce samunta tamkar samun zinarine acikin qasa, narasa wane irin zunubi na aikata da har iyalina ta kasance ahaka, ubangiji ALLAH kaganar da ita tun aduniya basai ranar da nadama baza tayi amfani ba." Nisawa nuraddin yayi yana d'an muskutawa sannan yace, "Amin baffa." Sun d'an jima kad'an suna fira kafin yayi masa saida safe snadiyar baffa Usman daya shigo d'akin riqe da 'yar ledarsa wacce tazamo masa jiki duk daren ALLAH sai ya riqowa baffa ita, wani lokaci gasashshen nama ne aciki, wani lokaci kuma kifi ko kuma sharare (had'in dankali da kifi). 'Dakin Yaya hawwa yashiga itama ya gaisheta sannan ya d'auko mata zancen abunda yafaru d'azu, duk da cikin girmamawa da kuma tausasa harshe yake yimata maganar hakan bai hanata yimasa tas ba sannan ta jadda masa cewa bazata dena abunda take so ba tunda gidansa ne kuma ita ta haifesa duk yanda taga dama haka zatayi, daga qarshema korarsa tayi tace yaje yabata waje bacci take ji, haquri yabata sannan ya tashi yawuce sashensa, ruwa yafara watsowa sannan sukaci abinci bayan sun gama itama tashiga toilet ta watso ruwan had'e da yin shirinta na kwanciya tahaye gadonta, duk abunda takeyi yana zaune gefen gadon yana kallonta da gefen idanuwa saida ta kwanta ya mulmula tare dasa hannu ya jawota yana fad'in. "To ranki ya dad'e ai baki isa ba, kin manta karatu zamuyi ne?". STORY CONTINUES BELOW Jan abun rufarsu tayi had'e da rufe fuskarta "habiby kabarni bacci nakeji don ALLAH." "Tab..ina yimasa Amma kinsan ALLAH bazaki kwantaba, kawai kitashi, Yanzu muna qarfe tara awa d'aya da rabi kacal zamuyi seki koma ki kwanta abunki kinji ko, daure kitashi mana habibtyn habibyyy." yafad'a yana d'agota daga kan filo, wartsake idanuwanta tayi don tasan tunda yafad'a to dole haka za'ayi tajuyo tana d'an harararsa. "Naji dai ko mai zaki mun bakomai." Yafad'a yana ciro littafi da biro a gefen bedside loka, murmushi tayi ta aza kanta saman kafad'arsa yace. "Karki damu, zan baki abunda kike so." Hakan daya fad'a yasa ta zauna daidai, cikin qwarewa yafar koya mata qananan kalmomin turanci da kuma hausa irinsu (I, you, she, we, he, they, them, us, e.t.c) (ni, ku, ita, shi, su, mu da sauransu.) Gwargwado kuma ta maida hankali tana fahimta sai dai bini bini tanayi tana duba agogo, awa d'aya na bugawa tayi baya da jikinta zata kwanta ya tarota yana dariya. "A'a habibty kiji tsoron ALLAH saura rabin awafa." "Bacci nakeji habiby." "Kiyi haquri, rabin awar tawace addu'o'i zaki koya mun, kinga sai kema kizama malamata." "Habiby mubarshi sai gobe." Rashida tasake fad'a tana zamewa daga riqon daya yimata tayi kwancenta, a 'yan kwanakin nan yarasa meyake damunta take yawan bacci, gyara mata kwanciyarta yayi sannan ya miqe yaje yayo arwalar bacci ya kashe masu wuta shima ya kwanta, addu'ar bacci yayi masu ya shafe mata jikinta sannn ya jawota ajikinsa ya rungumeta sosai sukaci gaba da baccinsu hankali kwance. Misalain qarfe shabiyu biyu da rabi na dare Rashida n bacci taji wata irin qara da kururuwa na fitowa daga cikin falonta, addu'o'in data sani tafara karantowa abakinta sannan ta sauko kan gadon, fitilar d'akin ta kunna had'e da kallon yanda Nuraddeen ya qaqume abun rufarsu yana baccinsa hankli kwance, toilet tawuce tayo fitsari had'e da d'auro arwala akai tanufo falon, wani irin qugi taji yna tashi cikin dakewa takoma ta d'auko wayar Nuraddeen ta kunna karatun k'ur'ani tanufo falon dashi, tana shiga taga wata irin qatuwar mage tayo kanta tadake tana kiran sunan ALLAH tare da runtse idanuwanta, tsaye tayi tana jiran taji mezai faru da ita amma sai taji wani iska maiqarfi kamar guguwa yayi wani qugi daidai saiti kunnenta sannan yayi shuuu...yawuce ta gefen labulen tagarta. Sautin karatun ta sake qarawa sannan ta shimfid'a abun sallah ta kabbarta sallarta cike da yaqini da kuma miqa dukkanin al'amurranta ga ALLAH, hankali kwance take gudanar da sallolin nata na nafila kamar yanda tasaba duk daren ALLAH matuqar tanada tsarki har aka kusa kiran sallar asuba, daidai lokacin Nuraddeen ya farko tare da laluba gefen da take kwance yaji ba kowa, d'an shafa goshinsa yayi cikin yanayin bacci tare da jaye mayafin da suka lullub'a ya sauko akan gadon, falon yanufo ya tarar da ita zaune ta d'aga hannayenta tana addu'o'inta kamar yanda tasaba, murmushi yayi tare da komawa toilet ya d'auro arwala shima yayi raka'o'insa biyu na raka'atanil fijir sannan ya zauna yana jiran atada sallar asuba. Tana gama sallar asuba tayi zaunenta tana karanto azkar d'inta na safiya da marece har rana tafito sannan tawuce kitchen tad'ora dahuwar indomie kafin ta d'ora abun kari saboda yunwar da takeji shi kuma ya riqa mata gyare-gyaren uwar d'akin dana falo yana gamawa ya iskota kitchen zaune da plate gabanta tana cin indomien data gama dafawa. Cike da mamaki yake kallonta kafin yace. "Habibty lafiyarki kuwa? Qarfe shida da rabi na safe yanzu, sekace wacce takwana da yunwa..." Bai qarasa rufe baki ba ta tashi aguje tayo waje wajen makwarara tana sheqa amai, da sauri yayo kanta ya riqeta, gaba d'aya indomien da taci saida ta amayeta abun gwanin tausayi, kujerar tsugunno ya d'auko mata a kitchen ya zaunar da ita sannan yaje ya d'ebo ruwa ya wanke mata bakinta da inda ya b'ata mata hijabin dake sanye ajikinta, d'aki ya kaita ya zaunar saman kujera had'e da cire mata hijabin sannan yadawo tsakar gidan ya wanke bakin makwararar da tayi aman ya sake d'ebo wasu ruwan ya wanke hijabin ya shanya sannan yakoma cikin falon yana jero mata sannu, kuka ta saka masa kai kace wata qaramar yarinyace sosai. "Habibty meye haka, laifinki ne fa, kinsan bama Kari dawuri don me zakici abinci yanzu beside kofa brush bakiyi ba ba dole k'wayun cutukan da suka zauna maki a baki su sakaki amai ba." Nuraddeen yafad'a yana qoqarin jawota ajiki, k'wacewa tayi tana fad'in. "Ko ba yunwa nakeji ba, kuma cikina duk a toshe yake bana jin dad'insa." STORY CONTINUES BELOW "Ayya yi haquri habibty, amma anya wannan ci da kikeyi a kwanakinnan ba macijin cikine ke damunki ba, ga yawan bacci dana lura kinayi gaskiya yau zanyiwa baffa Usman magana idan yaje daji yasamo maki maganin macijin ciki da basir." "Wlh kuwa habiby nima nafara jin tsoro kada yafara cimun hanji kaga yanzu banci komaiba." Rashida tafad'a tana yamutsa fuska, daidai lokacin taji ana yimata motsi aciki, wuntsil wuntsil, da sauri tamiqe tsaye tana zaro idanuwa tare da dafe saiti inda taji motsin kamar zatayi kuka yace. "Habiby wallahi macijinnan da gaskene, kaji yafaramun motsi, wayyo ummata, wayyo zan cinyemun hanji." Da gudu takoma kitchen d'in ta d'auki sauran indomien ta qarasa cinyewa shi kuma yana tsaye yana kallon ikon ALLAH, duk Wanda yasan ciki kallo d'aya zaiyiwa Rashida ya fahimci tanada shi saboda hasken da tayi ga breast d'inta suma duk sun cicciko duk da bai sata laulayi ba yakan sata jin matsananciyar yunwa da Kuma yawan bacci wud'an gaba d'aya Nuraddeen ya ta'allaqasu da cewa yawan bacci basirne ke damunta shi kuma yawan cin abinci macijin ciki ne da ita sabod ko kad'an ransa bai kawo masa zancen cikine da ita ba, be side bema San yanda ake gane cikin mace ba idan tanada shi, ko amai da yaga tayi a tunaninsa rashin brush ne da batayi ba kafin taci abincin.... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/11, 11:57 AM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___29πŸ’Ž Bayan tagama tayi gyatsa had'e dayin hamma sannan yace. "Habiby bacci?" "Kuma?" Yafad'a yana kallonta, kashe electric d'in tayi sannan tajuyo ta d'ora kanta saman qirjinsa tana sake sakin wata hammar akaro na biyu ta sake cewa."bacci nakeji." Muje nima shi nakeji, Nuraddeen yafad'a tare da sunkutarta yanufi d'aki da ita, cikin muryar dake nuna baccin takeji sosai tace. "Habiby jiyafa tsoro aka bani a falon nan!." "Kamarya habibty, tsoro anan falon Kuma? to sai Kikayi qaqa." Yafad'a tare da direta saman gadon, Saida tasaki wata hammar sannan tace. "Addu'a nayi." "Shine baku tasheni ba yafad'a yana kwanciya bayanta tare da jawo masu mayafin lullubinsu ya lullub'esu, cikin nauyin baccin dake d'ibarsa take basa labari shikuma yana isar da saqonsa ba tare daya fahimci sauran abubun da take fad'a masa ba har ya cimma burinsa, gyara kwanciyarta tayi yace. "Yihaquri Bari muyi wanka tukuna saikiyi baccinki" daqyar yasamu ta tashi suka tsarkakikke jikinsu sannan suka koma sukayi kwanciyarsu. Kamar yanda Nuraddeen ya fad'a haka akayi, ya sanarwa baffa da cewa ya samoma Rashida maganin macijin ciki dana basir take fama dasu, da baffa yasamo yazo ya gyarasu Inna Bilkisu na gefe tana gyaran ayarta ya miqo mata, "ungo maganin nan ki kaiwa yarinyar nan Rashida tun shekaranjiya Nuraddeen yafad'amun tana fama da matsalar macijin ciki da basir asamo mata, to bansamu shiga dajin ba sai yau, wannan ganyen dafashi zatayi tasha, shi kuma wannan sassaqen ta dakesa sai tarinqa sha tare da hura ko kunu, yarane basuda aiki sai cin maiqo ALLAH dai ya kyauta." Dariya tafaryi had'e da cewa, "yanzu shi nuran yafad'a maka cewa tana fama da basir da macijin ciki?" "Haka yace mun mana tunda tana yawan bacci da cin abinci sosai bini bini yace taji yunwa, ai kinga wud'an matsalolin ke damunta ko kuwa.?" STORY CONTINUES BELOW "Ikon ALLAH, malan kenan sake dai tunani, ai akwai d'ayansu dake iya haifar da irin wud'an matsalolin koma fiye dasu, be cemaka yaga tana haskeba ka had'o mata da maganin shawarah ba?" Inna Bilkisu taqarasa maganar dariya na kuccikke mata cike da mamakin Nuraddeen daya kasa gane matarsa nada ciki, kodon yaga ALLAH yabata lafiyayyene, shiru baffa Usman yayi na tsawon mintota kafin yagano inda zancen Inna Bilkisun ya nufa, murmushi yayi irin nasu na manya sannan yace. "To.to..to haka ankayi? Masha ALLAH, ubangiji ALLAH ya inganta, ja'iri zaisa in tafkawa kaina b'arna." "Ai kuwa dai, Ina ruwan malan Nuraddeen, to bai d'au hannu ba shiyasa." Tafad'a tana dariya. Daidai lokacin Nuraddeen yafito sashensa yayo inda Inna Bilkisu take a hirgitse, "Inna Bilki Rashida ce ba lafiya tun jiya da daddare take fama da zazzabi mai zafi yanzu haka gata can sai amai take faman yi ko za'a kaita asibiti ne?" Kallonsa baffa Usman yayi had'e dayin murmushi cikin xolaya yace. "To ko dai macijin cikinne yataso mata Nuraddeen?" "A'a inaga dai wannan karon qila shawara ce ko?" Inna Bilkisu tafad'a tana kallonsa, "Inna Bilki inaga itace ko akwai sauran maganin da baffa ya d'ebowa fadeela kwanakki abata har zuwa anjima inga ko zamu samo aron mota muje asibiti..." Bai qarasa ba Inna Bilkisu tace "Kai don ALLAH rufemun baki, ba don dai nasan kayi boko ba da nace maka takkwali kuma Mai qaton kai" tana gama fad'a tanufi sashen nasa baffa Usman na dariya ya shige d'aki suka barshi tsaye yana bitar kalaman Inna Bilkisu, can ya zaro idanuwa cike da mamaki har yana rufe baki yabi bayanta da sauri don samun qarin bayani cike da jin dad'i. Kwance ta iskota saman kujera mai zaman mutum uku cikin bargo sai rawar sanyi takeyi, sannu tayi mata sannan tajuyo ta kallesa tana fad'in, "yanzu kai Nuraddeen kan shirin zama baba amma har yanzu akwai wauta atare da kai, tana cikin wannan hali tun jiya ko ince kwanakin baya amma ka kasa kaita koda nan chemest ce adubata sai kira mata basir da macijin ciki kakeyi?" Cikin jin kunya yashiga sosa k'eyar kansa yana sissinne kansa qasa, murmushi tayi kafin suga Rashida tamiqe tayi waje da gudu da d'an sauran qarfin da take dashi, da sauri yaje ya kamata tana kwarara amai tamkar zata amaye hanjinta, ji yakeyi kamar yayi kuka ko ya maido da ciwon ajikinsa saboda tsantsar tausayinta, rungumota yayi gaba d'aya ajiki yana zuba mata sannu jikinta duk yayi yaushi, ruwan daya ajiye gefe abokiti ya d'iba ya wanke mata bakinta sannan ya d'agota tamkar 'yar baby ya maidota d'aki tana sakin lumfashi da qyar, gaba d'aya ya mance da zancen Inna Bilkisu awajen sai daya gama gyara wajen yakoma cikin d'akin tace. "Idan akwai 'yan ruwan zafi ka d'ebo mata ka lallab'ata tasha ko kad'anne in sha ALLAH Aman zai tsaya, bari naje nadubo maqwabcinnan namu idan motarsa nanan kayi masa magana kuje asibit, sannu Rashida sai hanquri Kuma yanzu har lokacin da ALLAH yarabaku dashi lafiya, ALLAH ya inganta kuma yaqara sauki." Tana gama fad'a bata jira me zaice ba tafito tazari hijab d'inta, baffa Usman ta tarar bakin gida zaune ta sanar dashi halin da ake ciki, cikin sa'a mutumen nana yajawo motar Inna Bilkisu ta taimaka masa aka fito da Rashida, har zata bisu baffa Usman yace a'a tadawo taje can cikin gida ta sanar masu da halin da ake ciki, su kuma yace su wuce idan akwai buqatar wani yazo to yakira sai Inna Bilkisu tabiyosu a baya tunda nan cikin garine ba nesa ba. Suna isa nan take aka d'ebi jininta don ayo mata gwajin ciki bayan an bata taimakon gaggawa irin nasu na qauye, tashin farko ana aunawa a kaga tana d'auke da ciki har na tsawon wata hud'u da sati d'aya, duk da Nuraddeen yasan da haka tun gida da Inna Bilkisu tafad'a masa Amma bai gasgata hakan ba sai yanzu da likita ya tabbatar masa, tsabar farinciki ji yakeyi yau tamkar ya take kan jariri sai faman washe haqora yakeyi yana yiwa yiwa likita godiya, likita kam abun har dariya ya soma bashi ganin yanda gaba d'aya murna da farinciki suka rud'ar dashi,. Girgiza kai yayi yana dariya yace "malan Nuraddeen wanna irin farinciki haka inaga haihuwar farko ce za'ayi maka ko?" Murmushi yayi yana sosa kai likitan yaci gaba da cewa STORY CONTINUES BELOW "Ahhh.. Masha ALLAH Ina tayaka murnar zama fresh baba, ALLAH ya inganta." "Amin Dr. nagode sosai" Nuraddeen yafad'a yana miqa masa hannu cike da farinciki. Takardar magani da ruwan da za'a qara mata da allurai ya miqa masa yana fad'in. "Amma zakuyi haquri zuwa nan da anjima koda za'a sallameku don tana buqatar qarin ruwa sosai, ALLAH yaqara sauqi" "Amin Dr mungode" Nuraddeen yafad'a tare da ficewa daga cikin d'an office d'in nasa. A can gida kuwa koda Inna Bilkisu ta sanarwa da Yaya hawwa dasu Inna ruqayya babu wacce ta nuna tadamu acikinsu don duk a tunaninsu aikin bokansu ne yafara aiki, tana fita sashen Yaya hawwa ta kece da dariya tana fad'in. "Wani aikin sai malan bakada imani, ba kince ke taurin kaiba yarinya, anturo maki su mutsibbata da janjabilu su tsorataki yanda bazaki iya zama a d'akin ba sunce kinfi qarfinsu, anturo maki ashiq ya shiga jikinki amma yayi duk shawaginsa da dubarunsa shima ya kasa, na dasa na binne don ashiga tsakaninki da d'ana ya dakeki muhuta duka shima mun kasa nasara saboda baqin naci irin naki, shiyasa nace ayi maki mai kankat aturo maki mugun ciwon da zaisa kidinga wari kina sakin quraje dole ko baiso ya gujeki, kuma da dukkan alamu malan bakada imani yasa munyi nasara a kanki wannan karo, shegiya tsigitsila sai kinbar gidannan tunda bana ubanki bane, ba inda zanje ALLAH ma yasa kimutu. Haka kuwa akayi har marece yayi aka sallamota babu wanda yatafi daga cikinsu inba baffa Usman dasu Aysha da fadeela ba saboda Inna Bilkisu ta tsaya yin girki da gyara gidan sai Kuma yusuf d'an baffa Ali, Allah sarki baffa duk ji yayi ba dad'i da aka sanar dashi halin da take ciki, yaso ace lafiya take da babu abunda zai hanashi kai jiki asibitin, duk da yanzu sanadiyar addu'ar data bashi yanayi wata ran kuma tayi masa ko kuma baffa Usman yayi masa yafara samun sauqi sosai, Yaya hawwa kuwa sai yakwan biyu baiga ko qwayar idanuwanta ba, Inka gata tazo wajensa to wasu tarako cikin 'yan uwa dake zuwa dubasa ko intake karb'ar kud'in da zatayi abincin da zataci duk da kuwa ko yaushe Rashida na kai mata idan tayi. Addu'a yayi mata sosai akan ALLAH yabata lafiya yanajin wata irin qaunarta na ratsa zuciyarsa musamman ma da akayi masa albishir tana d'auke da juna biyu, sai yaji kamar ya taka saboda tsantsar farinciki, nan yasa aka kira masa Nuraddeen yace kada yasake yafad'awa kowa cewa tanada juna biyu koda mahaifiyarsa ce har sai cikin yafito, haka ma Inna Bilkisu da baffa Usman duk ya roqesu su b'oye wannan sirrin na jikansa domin komai zai iya faruwa dashi idan har wani abun ya Sami yarinyar da abunda ke cikinta. Baffa Usman dama ba mutumne mai surutu ba ita kuma Inna Bilkisu tafi kowa son a b'oye zancen cikin gudun kada acutar da ita. Bayan an sallamosu sun dawo gida baffa yasa su baffa Usman suka riqasa yaje har d'akinta yayi mata ya jiki, akunya ce ta amsa yayi mata addu'a tare da gargad'inta akan cikin sannan suka mai dashi, yanda take d'an miqewa yana d'an aza qafafuwansa a qasa shi zaisa kana kallonsa kasan ya samu sauqi sab'anin da dako tashi tsaye baya iyayi balle har ya iya aza qafafuwansa a qasa, dudduqe yake kuma bai iya miqewa tsaye koda an riqasa, Amma yanzu cikin yardar ALLAH yana miqewa yayi tafiya idan anriqasa saidai baya aza qafafuwan da kyau ya taka qasa shiyasa mutanen gidan keta kallonsa cike da mamaki suna jero masa sannu. Satinta d'aya cikin d'aki tunda aka salla mota bata fitowa ko bakin qofa tana jinyar jikinta don har yanzu bai koma daidai ba bata son cin komai sai fura da kwad'on zogale hakan yasa tadena girki don ko qamshinsa bata so, Inna Bilkisu kullum cikin sayen ganyen zogale take a b'oye tana aika mata dashi haka baffa duk yafita sai ya sawo mata damammiyar fura tasha nono, abunka da qaramar yarinyar dake taka matakin farko na cikar girmanta mace nan take suka karb'i jikinta ta murmuje tayi haske abunta, bata aikin komai saboda fadeela da aysha keyi mata share share da wanke wanke, shi Kuma Nuraddeen shike kula da gyara mata d'akinta da wankanta, sosai yake bata kulawar da baya barin kowa shigowa sai idan aikowa akayi ko kuma cikin matan gidanne sukazo dubata da jiki shima d'in sai ya tabbatar ya saka mata hijabi tukuna yake cewa su shigo. STORY CONTINUES BELOW Yaya hawwa kam ranar tunda safe ta shiga sashen daga tsakar gida tana qwalla masa kira da sauri yafito had'e da duqawa yana gaisheta, kallonsa tayi tun daga sama har qasa ta mere baki had'e da cewa. "Sannu bawan mata, wai ita har yanzu bata warke bane?" "A'a innar mu da sauqi dai." "Mtssa to ni nagaji da d'ora sanwar nan Ina jiran aminci don yau zanyi baqi, sai ka sanar da ita don kada ab'ata mani lokaci." "To innar mu." Yafad'a jiki a sanyaye yana mamakin wannan hali na mahaifiyarsa, tun ranar da abunnan yafaru tsakaninsa da muneera har zuwa ciwon Rashida bataxo sashen ba balle tazo ta dubata, amma yanzu rashin kai mata abinci na sati d'aya yajawo tazo tana qorafi akai, muryarta ya tsinkayo daga tunanin daya tafi tana fad'in. "Kaji ko." "E.eh innar mu." Nuraddeen yabata amsa da sauri cikin i'ina, Jan tsaki tayi tare da kallon qofar d'akin Rashida ta cije baki had'e da girgiza kai sannan tabar wajen, jiki sanyaye yabar wajen shima yakoma cikin d'aki yana kallon Rashida dake baccinta hankali kwance batare da tasan ma wainar da ake toyawa ba, K'arar wayarta dake ruri yasa ta motsawa had'e da bud'e idanuwanta suka sauka akan fuskarsa, murmushi yayi tare da mik'a mata hannu yariqota ta tashi zaune sannan ya d'auko wayar dake sake ruri akaro na biyu ya miqa mata, murmushi ne ya bayyana a fuskarta lokacin da idanuwanta suka sauka saman screen d'in wayar ta kalli Nuraddeen tace. "Laaaa..Habibi baba ne." "To kid'auka mana kada ta tsinke." yafad'a tare da miqewa yabar d'akin yana tunanin abunda yakamata ya dafawa Yaya hawwa tunda ko kad'an Rashida bata son qamshin girki shiyasa ta denayi, shi kansa saidai yanemi ruwan tea yasha ko kuma yaci abincin da Inna Bilkisu ke aiko mata dashi. Cikin jin dad'i Rashida ta d'aga had'e da gaisheda mahaifin nata da tuni labarin tana da ciki ya isa kunnensu... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/12, 10:35 AM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___30πŸ’Ž Cike da so da qauna ya amsa mata yana tambayarta ya qarfin jikin nata, a kunyace ta amsa da taji sauqi sosai, nan yayi ta saka mata albarka bisa zuwan da baffa Usman yayi wajensu amadadin baffa suna godiya bisa tarbiyar da suka bata tare da yabon kyawawan halayenta bisa haquri da juriya da take dasu da yanda take girmama kowa acikin gidan, hakan ba qaramin jin dad'i da alfahari ta sakasu ba shi da umma bugu da qari ga albishir da suka samu cewa sun kusa samun jika nan kusa bada jimawa ba, wannan dalilinne yasa yakirata da wannan safiyar don yanuna mata tsantsar farincikin data sakashi don har seda yayi qwalla. "Rashida Ina matuqar alfaharin kasantuwarki 'yata saboda kin janyo mani girma da kimata sun qaru a idanun duniya kin sakani farincikin da ko mai 'ya'yaye goma bai isa yanuna mun shiba, kin fahimtar Dani cewa ba ilimin boko kad'aine kesa kayi alfahari da d'anka ba matuqar kabashi tarbiya da ilimin addini, Ina mai addu'a ALLAH yakareki Kuma yafaranta zuciyarki kamar yanda kika faranta tamu nida mahaifiyarki, ki kula da kanki sosai kinga yanzu bake kad'ai kike ba, ki dage da yiwa abunda ke cikinki addu'a da neman tsari daga sharrin shed'an tun kafin yazo duniya domin shine hikimar ALLAH da yabar uwa tayi renon cikinta har na tsawon wata tara don samu isashhen lokacin yimasa addu'a badon haka ba da yanda akayiwa nana maryam kun fayakum haka za'a yiwa kowace mace saboda haka ki kula sosai kinji iko, kiqara hak'uri Kuma ki kai kukanki ga ALLAH da SANNU SANNU zai yaye mana damuwarmu, ALLAH yayi maki albarka, ga umman taki." Baba yafad'a yana miqawa ummu wayar, STORY CONTINUES BELOW "Ummata." Rashida tafad'a hawaye na biyo kuncinta saboda tausayin kanta da halin da take ciki da basu sani ba, goge hawayenta tayi wani b'angare na zuciyarta nafad'a mata cewa bai kamata tayiwa ALLAH butulci ba tunda iyayenta nacikin farinciki Kuma ako yaushe addu'arsu natare da ita. Muryar umma ta tsinkayo a kunnuwanta tana fad'in, "yarinyata ya kike?" "Lafiya klw ummata ya kuke kuma da wajensu aunty marwiyya da baba balarabe, kowa duk lafiya ko umma.?" Rashida tafad'a cikin sanyin murya tana qaqaro murmushi a fuskarta tamkar tana gabanta. "Kowa lafiya klw ya qarfin jikin naki, kinacin abinci kuwa?" "Naji sauqi ummata, abincin daine bana iyaci ummata.." saida umma ta kalli baba dake gefenta sannan yace "dama nasan za'ayi haka, ki daure kinacin abinci kada kirame shima yaron cikinki kisa yafito ba lafiyayye ba kinji ko, fad'amun me kike so inba malan Idris idan yashigo yakawo maki." Murmushi Rashida tayi aranta tana cewa, ALLAH sarki uwa, akoda yaushe kulawarta tamusamman take fiye da takowa aduniya, shiru tayi tana nazarin me zatace kafin can taji umma nafad'in "Akawo maki garin d'an wake kina so.?" nan take taji d'an waken yabiyo mata arai, "eh ummata Ina so, ahad'omun da busashshiyar zogale da kike ajiyewa kina yimana dambu shima inaso" "To kice dai a had'o har da tsakin yin dambun ko," "eh umma har dana fate fate.?" "Duk dai Rashida, wannan yaro ko yarinya anyi makwad'aita." Umma tafad'a tana dariyar, tamkar tana agabanta haka rashidar tayi saurin rufe fuska itama tana dariya, naseeha tayi mata sosai had'e da bata 'yan shawarwarin yanda zata reni cikin sannan sukayi sallama, wani farinciki Rashida taji ya mamaye ranta cikin jin dad'i ta yane zanen gadon dake jikinta ta sauko daga kan gadon. Falo tafito taduba bataga habibynta ba tafito tayo kitchen don tasan bai wuce can yana had'a masu breakfast, ai kuwa tana zuwa ta iskosa yana gyaran kayan miya har ya d'ora sanwar shinkafa ta tafaso saboda electric ne kuma wutar tanada qarfi sosai, qamshin shinkafar data tafaso ne yabugi hancinta lokacin data aza qafarta zata shiga kitchen da sauri takoma baya had'e da toshe hancinta amma ina tuni aman yaci qarfinta da gudu takai bakain makwarara tana sheqasa, ji Nuraddeen yayi kamar ya aza hannu akai yafashe da kuka saboda takaicin wannan abun da yaya hawwa tace ayi gashi aman datayi kusan sati da kwanaki batayi ba yau duk ta rankasa, sosai aman ya galabaitar da ita don tun tana durqushe saida takoma zaune hawaye nabimata a kunci, gashi daya matsota saita turesa saboda warin girkin da yakeyi, rufo kitchen d'in yayi da sauri ya d'ebo ruwa ya wanke mata baki zuwa lokacin batada sauran qarfin da zata iya hanasa rab'ar jikinta duk dako qamshin girkin dake jikinta da bata so, riqata yayi ya kaita d'aki ya kwantar da I bisa gado yana jero mata sannu yaje yacire kayan jikinsa ya watso ruwa sannan ya d'auko plaks d'in ruwan zafi dake kan fridge tare da kayan tea ya had'a mata mai kaurin gaske ya tadata zaune yadinga Bata tana sha, saida ta shanyesa cikin kofin tas tace yaqaro mata wani ta shanye sannan takoma ta kwanta tana fad'in "kayi haquri habiby, kagaji da rashin girkin da nake yimaka ko shiyasa kad'ora abunka yau..." Bata qarasa ba ya d'ora yatsans abakinta yana girgiza mata kai. "Ko kad'an habibtyn habiby bazan tab'a gajiya da halin da kike ciki ba tunda nine sila, don haka kidena fad'ar haka kinji ko.?" Ya qarasa maganar yana jan karan hancinta, hannunta tasa tariqo nasa had'e da cewa. Kaima kadena fad'ar cewa kaine sila domin yanayin wannan ibadar gidan aurence tazo mana a haka." 'Dan duqowa yayi ya sumbaceta agoshi yana murmushi ta wani lumshe idanuwa sannan ya gyara mata abun rufarta daidai qirjinta yace. "Kiyi baccinki kada kifito har in qarasa, kwana biyu naga yadace yau akaiwa su baffa abinci shiyasa kika ga nad'ora girkin tunda ke dake dafawar bakyajin dad'i." Yana gama fad'a ya juya zai bar d'akin tariqo hannunsa alokaci d'aya tana lumshe masa idanuwa bayan ya juyo tace. "Ina sonka malamina habiby nah." STORY CONTINUES BELOW Dawowa yayi yad'an shafa cikinta d'aya d'an fara tasowa sai dai ba sosai ba saboda tsawon da take dashi. "Ina sonki so mai yawa kuma marar misaltuwa habibty." Bai jira mezata ceba yayi saurin wucewa ransa cike da nishad'i, in dai soyayyace tsakaninsa da habibtynsa yasan basa gajiya kuma ba ranar gamata, yanzunan ne zasu qone abincinnan batare da sun ankara ba shiyasa yayi saurin baro d'akin, murmushi tayi tarufe idanuwanta nan da nan bacci yazo yayi gaba da ita, bai jima da d'aukar taba can cikin baccin aka fara nuno mata miyagun halittu kala kala suna neman firgitata amma sai taga wani glass yayi mata shamaki tsakaninta dasu sun kasa yimata komai, da wata irin kalmar shahada tafarko cikin matsananciyar qarar da tasa Nuraddeen shigowa cikin d'akin a rud'e riqe da ludayin miya a hannu, da alama ita yake motsawa yaji qarar sautin kalmar shahadarta. Saman madubi ya ajiye ludayin yanufi inda take zaune tana karanto addu'o'in data sani abaki zuciyarta cike da tsoro sai faman harbawa takeyi da sauri da sauri, tattab'a fuskarta da tayi sharkaf da zufa ya dingayi hankalinsa atashe yana fad'in "habibty lafiya?." "Lafiya habiby." Tabashi amsa tan dafe d'an cikinta da yaji yana motsi sakamakon firgitar da tayi, "Tashi mukoma falo." Yariqota ahankali yana kallon yanayin da take ciki, don riqotan da yayi yaji yanda qarar bugun zuciyarta ke tafiya da sauri da sauri sboda tsananin firgicin da tayi, ruwa ya d'auko a fridge yabata tasha bayan ya zaunar da ita, wayarsa ta karb'a ta kunna baqara tare da cewa yamiqo mata qillen tsamiyar dake ajiye saman fridge ta tsotsa saboda zuciyarta data fara tashi don har lokacin bai qarasa girkin da yakeyi ba. Bayan ya miqo mata tsamiyar yafice ya nufi can cikin gida da niyar kirawo fadeela tazo taqarasa aikin dama miya ce kad'ai bai qarasa ba. Yana fitowa yaci karo da muneera zaune bakin rumfarsu tana tsifar Kai, fiye da sati d'aya Inna ruqayya na fama da ita ta tsefesa sai yau da taga dama sannan ta zauna zaman tsifar, tana ganinsa ta dashe baki shi kuma ya d'auke kansa gefe cike da takaicinta, "ya nura." Muneera tafad'a tare da tasowa tabiyosa har lokacin hannunta nacikin kanta tana tsifar da yatsunta, bai tankata ba har yakai bakin qofar d'akin Inna Bilkisu had'e dayin sallama, juyowar da zaiyi ya jira fitowarta sukayi karo da muneera dake biye dashi kansa yabugi nata sosai tayi baya zata fad'i yayi saurin tarota tafad'a saman hannunsa, abunka da d'an uwa duk yanda take bazaiso abunda zai cutar da itaba har takai ga taji ciwo, muneera na ganin haka ta dashe baki tare da sake sakin jikinta. "Meye haka, dalla miqe sakarai, meye kike faman bina haka." ganin ko qwakkwaran motsi takasayi sai wni kafesa takeyi da idanuwanta irin na mujiya yasa cike da takaici ya saketa, tim kakeji qasa tamkar an yarda kayan wanki. "Wayyooo..quguna ya nura zaka karya ni." Tafad'a tana qoqarin tashi, daidai lokacin Inna Bilkisu tafito had'e da cewa."a'a Nuraddeen shine kayi tsaye anan sai kace baqo injin dai lafiya?." "Lafiya klw Inna Bilkisu dama fadeela nake son tazo tad'an qarasa mana wani aiki, jikin Rashidar ne yad'an motsa yau.." "Ya nura nizan qarasa maka kowane aiki ne basai fadeela ba." Muneera tafad'a tana wani turo lab'b'a ala tilas itaga mai kishi, "to Nuraddeen kuje ga muneera nan kaji tace zata qarasa maku." Muskutawa yayi had'e da gyara tsayuwarsa sannn yace. "Don Allah Inna Bilkisu kitaimaka kituromun fadeela." Batare daya damu da zancen muneerar da tayi masa ba, "Nuraddeen.." Inna Bilkisu tafad'a cikin sigar lallashinsa akan muneerar taje gudun wata matsala tafaru amma yayi saurin dakatar da ita tahanyar cewa "Don Allah Inna Bilkisu." Yana had'a hannayensa sannan yawuce ita muneera ta sake bin bayansa. Saida Inna Bilkisu ta sauke ajiyar zuciya sannan ta qwalawa fadeela kira. "gani inna" Fadeela tafad'a tana fitowa daga cikin d'aki da alama baccima ta farayi, "maza jeki yayanku nakiranku, kice ma Rashida Ina gaisheta da jiki." "To Inna." Fadeela tafad'a tare da komawa d'aki ta d'auko hijabi tasaka tanufi sashensu, tana isa baki qofar shiga shiyar muneera ta riqe mata hijabi. "Wallahi babu inda zaki shiga tunda yahanani nima, munafuka kawai sai wani shishshige masa kikeyi bacin kinsan nice zan qara aurensa." "Ha'a meye haka kuma aunty muneera, cikamun hijabina." "Bazan cikakiba, wuce muje kikoma inda kika fito." Nan rigima ta kaure tsakaninsu muneera tayi bake bake a bakin qofar shiga sahen nasu Rashida riqe da hijabin fadeela ta kafe akan ba inda zata fadeela sai kiciniyar k'wacewa takeyi ta shiga, hakan yajawo hankalin Nuraddeen dake cikin d'aki yafito had'e da katsawa muneera tsawa yace. "Waike wace irin marar kunya ce, zaki sake mata hijab ko sai nazo na takeki wajen." Yafad'a had'e da yowa kanta ransa ab'ace. Da sauri ta saketa tare da komawa gefe tana fad'in "ya nura to nima in shigo?" "In karya maki k'afa k'azama." Turo lab'b'a tayi tana fad'in. "Badai shiyar kane baka so nashigo ba, wallahi saina fad'a inna shima akaika wajen maln ba..." Bata qarasa maganar ba sakamakon wata uwar tsawa da Inna ruqayya dake fitowa daga b'angaren yaya hawwa tayo mata jin zata tona masu asiri, "kee muneera maza kibaro wajennan kafin ranki ya b'aci, yayan naki ke fad'a kina fad'a don rashin kunya, zaki jaye ko saina iskoki." Taqarasa maganar tare da nufar wajen, qafafuwa muneera ta shiga bubbugawa tana fad'in. "Inna shifa zan aura kukace Kuma zakice nabaro wajensa, ya nura ni takace kuma ko bakaso sai ka aureni, kashirya a wannan shekarar dole muyi aure." dariya Inna Bilkisu dake kakkamta kaya a cikin rumfarta tana sauraren suruttan muneera tayi aranta tana cewa tabbas iska na wahalda mai kayan kara, Nuraddeen dake tsaye shikuma yana kallon ikon ALLAH tsaki yaja tare da shigewarsa don bai fahimci ma inda zancenta yayi ba, a fusace Inna ruqayya taqaraso wajen taja hannunta tana d'imarta a baya "ke kam anyi samna anan, shin b'angaren nasa aljannah ne da zaki nace sai kin shiga, bana fad'a maki kifita shirginsa ba kafin yasake nad'a maki wani dukan?" Dai dai bakin shiga rumfar tasu ta tirje tana kuka had'e da fad'in. "Ni bazan fita harkarsa ba Ina sonsa, kuma ai keda baffa kunce zaku kaisa wajen malan bakada imani asa mashi soyayyata ya akayi har yanzu baya sona, ni bazan yarda ba kawai yau akaishi wajensa a d'aura mana aure gobe bana son aurensa qarshen shikarar nan don wallahi waccan munafukar zata iya aura masa fadeela gashinan sai faman tura masa ita akeyi tana shisahige masa.."[7/12, 10:22 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ _Hi fan's am so sorry akan yanda kuka matsu mukoma asalin labari, Karku manta ita SANNU SANNU bata hana zuwa..no matter how matuqar ALLAH yabani aron lumfashi da kuma rayuwa zan sadaku da farkon labarin da muka faro, karku manta *baku san ko waye Abu sumayya ba?, bakusan asalinsa ba? taya ya had'u da matarsa batool shima baku sani ba? meya jawo batooul tabar iyayenta har na tsawon shekaru bakwai? Shin Abu sumayya ya cancanci mutuwa adaidai lokacin da yakamata yasan ko waye mahaifinsa?, meyasa mahaifin batoul ya sheganta shi, Shin batool itama ta cancanci ta fuskanci jarabawar da take ciki adaidai lokacin da take d'okin sake had'uwa da iyayenta?* πŸ˜…Inada yaqini akan shima baku sani ba kuma bakuda duka amsoshin wud'annan tambayoyin, wannan waiwayen tushen labari da mukayi shi kad'ai zai amsa maku duka wud'annan tambayoyi kuma da sannu ya sadaku da farkon labarinku, saboda haka kujuri zuwa rafi na tabbatar ranar da tulun zai fashe na nan zuwa🀣Ina matuqar godiya bisa yanda kuke qaramun k'warin guiwa ta hanyar comment d'inku, nakanyi farinciki kuma na nishad'antu da hakan akoda yaushe, FILLAH INA SONKU OVERπŸ’‹πŸ˜_ Page___31πŸ’Ž Har Nuraddeen zai wuce yadawo yayi tsaye yana jin maganganun dake fitowa daga bakin muneera, tun daga farko har qarshe babu abunda baiji ba yafito ransa a'bace yana watsawa Inna ruqayya da tayi tsuru tsuru da idanuwa tana 'yan kame kame wani irin mugun kallo da yasa cikinta murd'awa, nunata da yatsa yayi yace.+ "Wai ni za'a kai wajen wani malami ko boka don in so wannan abar?" Yaqare maganar yana nuna muneera sama da qasa da hannu, murmushin gefen baki ya saki cike da takaici kafin yaci gaba da cewa. "To wallahi Inna ruqayya koda matan duk duniya zasu qare bazan tab'a auren muneera ba Kuma badon bana sonta ba sai don kawai kinzamo mahaifiyarta, duk da 'yar uwata ce ita bazan iya aurenta ba har duniya ta nad'e don haka idanma mafarki kukeyi to wlh kufarka kunema mata mijin daya dace da ita, wannan Nuraddeen da kike gani in sha ALLAH mallakin Rashida ne ita kad'ai, zuciya da kuma ruhi gaba d'aya natane bana tunani ko a mafarki kwakwalwata zata aminta da shigowar wata azuciyata ko wacece ita ciki kuwa har da muneera d'in da kuke qaqabar 'yar uwata ce domin bare tagama mani komai aduniya.." wata irin qara muneera tayi had'e da ciyo kwalarsa tana kuka, "wallahi ya nura baka isa ba, don ka kawai aka halitto ni bazai yuyu na auri wani inba kaiba.." Bata qarasa maganar sanadiyar wani zazzafan mari daya d'auketa yana kallon wuyar rigarsa data riqo, qafa yakai zai hankad'ata tayi saurin duqewa wajen tare da riqe masa qafafuwa tana kuka, "don ALLAH ya nura karka damu da inna, kafita batunta da halayenta ni kai nake so, zan zauna da kai ko mata nawa zaka aura amma karka yimani hukunci akan halin Inna ita da baffa sune basa son matarka haka ranar naji suna fad'a wai Inna hawwa takaita wajen malan bakada imani za'a dinga turo mata aljanu suna tsoratata, yanzu haka ciwon da takeyi sune sukasa yaturo mata shi.." baya baya Nuraddeen yayi kamar zai fad'i saboda tsorata da kalaman dake fitowa daga bakin muneera, duk da dai ciwon da Rashidarsa keyi ba irin wanda take nufi bane amma maganarta akwai qamshin gaskiya aciki idan yayi la'akari da tsoron da Rashida kecewa ana bata da Kuma yawan firgitarta acikin barci, kasa cewa uffan yayi har saida Inna Bilkisu dake tsaye cikin rumfarta tana sauraronsu ta matso wajen ganin yanayin daya shiga ta dafashi tana fad'in. "Karka kuskura ka amince da wannan soki burutsun na muneera kasan halinta da shirme, idan kuma har gaskiya take fad'a to kada ka tsorata domin da wannan tsoron naka za'ayi amfani wajen cutar da kai da kuma matarka kayarda ba mai yimaka sai ALLAH kuma Babu wanda ya isa ya cutar da kai sai abunda alqalamin qaddara ya rubuto akanka, maza kawuce kaje wajen iyalinka ba abunda zai sameku in sha ALLAH tunda kun riqe ALLAH, sharri shi Kuma d'an aikene duk inda kaje zai dawo ya sanar maka." STORY CONTINUES BELOW Taqare maganar tana kallon Inna ruqayya da tsabar kunya tasa tayi wuri wuri da idanuwa tana faman susar wuyanta. Wasu zafafan hawaye yaji son zubo masa wai ace qiyayyar da mahaifiyarsa keyima matarsa har takai ga za'a iya had'a baki da ita acutar mashi da ita don d'ai cikar burin wasu, cikin zafin rai ya dubi Inna Bilkisu yace. "Inna Bilkisu me yarinyar nan tayi masu da suke nema su cutar da ita, nine fa d'ansu duk wani abu na mataki daya kamata su d'auka akaina ya dace ba itaba." Girgiza kai Inna Bilkisu tayi had'e da cewa. "ALLAH dai ya kyauta, kawai kashiga ciki in sha ALLAH babu abunda zai sameta." "Munafuka! aikin kenan ko yaushe sa ido, to Ina ruwanki tunda duk abunda akayi d'in da sanin mahaifiyarsa ita data haifesa, meye naki nasa baki, ke kuma shegiya mai baqin baki kamar aku da yaushe akayi haka? wato ke uwar soyayya zaki qaqaba mana sharri tsakar rana, tashi muje yau sai kin gane kurenki" irin borin kunyar nan Inna ruqayya tafara wud'annan suruttan had'e da rufe muneera da duka tana janta, "Dakata Inna ruqayya! ku gaggauta zuwa kusa a kwance qullin da akayi maku akan matata idan ba haka ba duk abunda yafaru da ita to sai nayi shari'a daku.." kafin yarufe baki yaji saukar wasu zafafan marora har biyu a fuskarsa, Yaya hawwa ce da tun d'azu da taji muneera ta sako baki tana zuba tafito tayi tsaye tana qare masu kallo ta sakar masa wud'annan marora bazato ba tsammani, cikin d'aure fuska da rashin tsoron duk abunda zaije yadawo tace "Don buhun ubanka dake kwance anyi qullin kuma baza'a kwance ba kayi duk abunda ka iya, inkaga dama kaje koton duniya ni hawwa bana tsoron uban kowa akan wannan tsigalalliyar yarinya bare daka auro mani, Kai nifa nagaya maka natsani matarnan tun wuri ka rabu da ita ko agaban idanuwanka insa ta walaqanta, shashashan banza da wofi har kace zakayi shari'a damu akan bare." tunda Nuraddeen ya soke kai qasa bai d'ago ba sai hawaye dake faman kwarara daga idanuwansa, yarasa wannan wace irin qiyayya ce mahaifiyarsa keyi ma Rashida da har Bata shakkun kowa akan zata iya illatata. 'Dago kansa yayi yana kallon Yaya hawwa yace. "Innar mu kiyi hak'uri, aurena da Rashida muqaddirine daga ALLAH, Ina sonta sosai shiyasa nakasa haqura da ita tun farko, don ALLAH ko donni ki daure kisawa zuciyarki soyayyarta, inada yaqini akan zakiyi alfaharin samunta a matsayin suruka, kigujewa wannan mummunar al'adar da kike tunanin daidace kada ta jefaki cikin fushin ALLAH." "To saketa idan kana so kada nashiga cikin fushin ALLAH, idan bahaka ba nayi maka baki ka lalace." Taqarasa maganar tana gyara tsayuwarta da d'aurin zanenta, "Haba Yaya hawwa meyayi zafi haka keda d'anki, ai idan kikayi kuskuren yimasa baki damuwar akanki zata fad'a, don ALLAH da girmansa kiyi hak'uri kibar yaronnan tunda yana son matarsa, yaran zamani da kike gani bad'ai suke dana da ba zaifi kibarsu suyi rayuwarsu yanda sukesu ke Kuma iya naki kibisu da addu'a," Inna Bilkisu tafad'a tana kallon Yaya hawwa cike da girmamawa. "Bilki." "Na'am Yaya hawwa." "Bilki." Yaya hawwa ta sake fad'a akaro nabiyu tana kallonta, itama ta sake amsa mata kamar d'azu. "Ya isheki haka babu ruwanki da d'ana, kifidda bakinki a wannan maganar saboda ba huruminki bane, ni nahaifi d'ana baruwanki ko yankasa zanyi shishshigin naki ya isa haka kina jina, idan kuwa ba haka ba zan zageki tass awurinnan nayaga maki rigir mutunci ba abunda yadameni, ke kike da abun fad'i agari bani ba don haka bar wajen nan tun wuri kinaji na ko?" "ALLAH yabaki haquri." Inna Bilkisu tafad'a tare da barin wajen zuciyarta cike da tausayin Nuraddeen, wata irin gud'a Inna ruqayya tasaki had'e da cewa, "su uwar gulma andaiji kunya idan ansanta, sai aja tsomakaran qafafuwa asani inda akayi yau shishshigi baiyi rana ba." Bata tankata ba tawuce abunta Yaya hawwa tajuyo tana kallon gefen da Inna ruqayyace take tace. "Ai kece babbar uwar gulmar kuma zan dawo ta kanki." "Kai nadawo gareka zaka saketa ko kafiso sai naga walaqantata agidannan." "Innar mu don ALLAH kada kirabani da Rashida Ina matuqar sonta." STORY CONTINUES BELOW "Maida son akan waccan mai idanuwa kamar na mujiya koba komai 'yar uwarka ce" Yaya hawwa tafad'a tana nuna muneera dake jingine ajikin k'arfen rumfa ta takure waje d'aya, wani irin shu'umin murmushi Inna ruqayya ta saki tana ayyana abubuwa aranta, cikin katsa tsawa taji tace masa. "Ka saketa nace.." duqewa yayi agabanta yana fad'in "innar mu kiyi hak'uri bakina bazai iya furta wud'annan kalaman agareta ba." "Bazaka sake tab'a saina tsine maka?." Tafad'a tana qoqarin bud'e baki ta tsine masa, da gudu Rashida dake lab'e tafito ta durqushe agabanta itama tana hawaye. "Don ALLAH kada ki rabamu innarmu, kifad'i duk abunda kike so zamuyi amma kada kirabamu ko don albarkacin abunda ke cikina." Rashida tafad'a tana kuka, wani irin mugun kallo yaya hawwa tabita dashi tana kallon yanayinta da d'an cikin daya taso kad'an ajikinta kafin tace.... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/13, 6:45 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___32πŸ’Ž Buhun uba mezan gani haka?, Munafukan ALLAH dama cikine dake ake yimani rufa rufa agidan nan? tirqashi to idan tunaninki yabaki cewa wai cikin dake jikinki nada wata kima ko daraja awajena da har zai iya dakatar dani daga qudurina to kinsha qarya, dake har wannan abun dake cikinki bana sonku bana qaunar ganinku, don haka kai kasaketa kaji nafad'a maka kafin raina yab'aci" Yaya hawwa tafad'a cikin zaro idanuwa tana kallon Nuraddeen da izuwa yanzu gaba d'aya qasusuwan jikinsa sunyi sanyi, ga wani irin zazzab'i daya ji yana shirin taso masa, a hankali ya d'ago kai bakinsa na rawa yace. "Innar mu kidubi girman ALLAH kada kirabani da Rashida, wlh zan iya mutu idan kika rabani da ita, nayarda bakya son Rashida amma abunda ke cikinta bai kamata ki k'isa ba saboda jinin kine kuma jinina." Tana bud'e baki tayi magana taji muryar baffa da tun d'azu yake yaqar zuciyarsa dake Shirin mutuwa ta sanadiyar raunin daya samu tamaidasa marar amfani aduniya, bayan da rayuwarsa ba mutuwa yayi ba cikin qarfin hali da jajircewa da kuma miqa dukkanin yaqininsa ga ALLAH akan zai iya abunda yasawa ransa yafara qoqarin rarrafawa yana dafa bango, addu'a yake maimaitawa azuciyar yana ambaton dukkanin sunayen ALLAH abakinsa yashiga bin bango yana fad'uwa yana tashi, wani azababben ciwo yakeji na qara taso masa tun daga kan qugunsa har zuwa tsakiyar qasan tafin qafafuwansa amma haka yaci gaba da takawa saboda rad'ad'in da yakeji da ciwo azuciyarsa yafi ciwon da yakeji yanzu atattare dashi har ALLAH ya kawosa inda zasu iya ganinsa, fad'uwa yayi zaune zufa na tartsikke masa tako ina ajikinsa yana fitar da lumfashinsa sama sama, ji sukayi cikin d'aga murya baffa yace. "Karka kuskura kasaki matarka Nuraddeen ko bana raye aduniya, ke kuma d'anki ne bazan hanaki kiyi duk yanda kike so dashi ba amma Ina so kisani aduk lokacin da kikayi nasarar sa Nuraddeen yasaki matarsa to kisani ranar nima babu aure tsakaninmu kije kema na sakeki." Afirgice yaya hawwa ta d'ago kai tana kallonsa jin kalaman dake fitowa daga bakinsa cike da mamaki, shikuwa Nuraddeen duk da babu wani qarfi ajikinsa da gudu yataso yayo wajen mahaifin nasa da shed'arsa kefita sama sama batare daya tsaya fahimtar maganganun dake fita daga bakin saba, fuuuu.. Yaya hawwa tayi tawuce sashenta ranta ab'ace, ko kad'an bata damu da yanayin data gansa ba balle tayi tunanin taya akayi yazo wajen, amma gaba d'aya yara da manya dake gidan sunyi mamakin ganin baffa a wurin batare da kowa ya riqosa ba, kansa suka taru hadda muneera dasu Inna ruqayya ana yimasa sannu duk da Inna ruqayya bakad'an taji zafin bayyanarsa awajen ba saboda yanda ya b'ata mata masu tsarin, Rashida kuwa tunda tajuyo takalli baffa daga durqushen da take shima yana kallonta tayi murmushi lokaci d'aya kuma hawaye na yimata kara kaina a fuska kasa tashi tayi har saida Inna Bilkisu tazo ta riqata ta tashi tana mai godiya ga ALLAH daya hana faruwar abunda Yaya hawwa taso faruwarsa. STORY CONTINUES BELOW Wajen suka nufa lokacin Nuraddeen ya rungume Baffa yana kuka cike da tagwayen farin ciki da suka lullub'e masa zuciya, na farko ganin akaro na biyu ALLAH yasake bawa mahaifinsa damar sake taka qasa da qafafuwansa na biyu kuma yanda ALLAH yakawo masa ginshik'in daya shiga tsakanin hana faruwar rabuwarsa da masoyiyarsa, shi kansa baffan kuka yakeyi Amma nasa na takaici da baqincikin irin matar da ALLAH ya jarabcesa da ita, d'ago kansa yayi yana shafa kan Nuraddeen yace. "Kayi hak'uri dukkani tsanani yana tare da sauqi, Alhamdulillah wama sha'a fa'ala." 'Dago kai Nuraddeen yayi yana jin wani sanyi azuciyarsa ya kalli Rashida da har lokacin kuka takeyi ya girgiza mata kai alamun tayi shiru tare da sakar mata murmushi, hannu tasa tagoge hawayenta itama tana mayar masa da nata sannan tajuya tashiga sashensu ta d'ebo ruwa a joke, duqowa tayi tana karanta addu'o'in data iya had'e da tofawa tabawa baffa, murmushi yayi yakarb'a ruwan yana saka mata albarka yasha sannan ya miqawa Nuraddeen sauran yace ya shafa masa a qafafuwansa, bayan mintuna kad'an baffa ya gwada qoqarin tashi da sauri Nuraddeen ya miqa hannuwa zai riqosa ya dakatar dashi, su dai mutanen gida duk suna nan tsaye cirko cirko suna kallon ikon ALLAH, duk da baffa najin zugi da zafi atattare dashi hakan bai hanasa gwada miqewar da kansa ba yana cije baki saboda zugi da rad'ad'in da yakeji har ALLAH ya taimakesa ya miqe da kansa, rufe idanuwa Rashida tayi hawayen dake cikin idanuwanta suka samu damar zubowa sannan tabud'e tana fad'in "Alhamdulillahillazi bini'imatihi ta timmusswalihat, ya mujibudda'awat, Alhamdulillah kathiran." Ihu yaran gidan suka fara suna tsalle ganin yanda baffa yafara tafiya ahankali yana dafa bango batare da anriqasa ba, juyowa Nuraddeen yayi ya rungume Rashida agaban kowa yana fad'in. "Ke alkhairice arayuwata da kuma ta mahaifina, ya ALLAH kada kabani damar shaqar lumfashi a inda babu habibty d'ina." Cike da jin kunya Rashida ta notar da kanta qasa tana murmushi tare da d'an turesa daga rungumar daya yimata ta juya tabar wajen cike da farinciki azuciyarta." Juyawa yayi shima yabi bayan yaran dake biye da baffa suna tafi da ihun murnar ganin ya samu lafiya, Suna barin wajen inna ruqayya taja wani irin dogon tsaki cike da takaicin Rashidar babu babban baqin cikinta yanzu kamar cikin da tagani ajikinta wanda tamada yaqinin shizai qara zamowa shamaki kuma katangar da zata rugujewa 'yarta samuwar nata farincikin, cike da son muzanta Rashida daidai lokacin da ta aza k'afarta zata shiga sashenta tace "Aikin banza da wofi, zuri'ar 'yan tsibbu da mayu da gani anyo gadon buge bugen qasa." Tsaye cak Rashida tayi tana sauraren kalaman da take jifarta dasu kafin tashigewarta batare da tajuyo ba balle ta tankata zuciyarta fad'a mata kada ta tab'a damar da kanta don tace mata haka, dama shi d'an adam haka yake duk abunda yake aikatawa sai yayi tsammanin kowama yana yinsa, konkad'an baici ta damar da kanta ba tunda tasan sunan da tayi mata da ita yafi dacewa ba itaba. Da gudu muneera tabiyo bayan Rashida har zata aza qafarta ta shiga sai tatuno jan kunnen da ya nura yayi mata. "Rashida" muneera takira sunanta cikin sanyin murya, juyowa tayi tana kallonta, ganin tana son yimata magana amma takasa shigowa tace. "Aunty muneera shigo mana." "A'a bazan shigo ba ya nura na iskoni sai ya maidani tamkar jaki yasha Kara." Murmushi Rashida tayi tare da dawowa bakin qofar inda take tsaye tace, "to gani aunty muneera" susar kanta tashigayi kafin tace, "naji Inna tana cemaki wai zuri'ar 'yan tsibbu saboda kinyi wani abu aruwa kinba baffa yasha yawarke har yana tafiya, don ALLAH da gaskene shi kikeyi?" Murmushin da bai kai cikiba Rashida tayi tare da gyara tsayuwarta sannan tace "A'a muneera ba gaskiya bane, ni bana tsibbu kamar yanda Inna ruqayya tafad'a maki balle iyayena ko zuriarmu, Amma muna roqon ALLAHn daya halicci cuta kuma yayi maganinta cike da yaqini kuma ya karb'a mana, adduace nayiwa baffa d'azu don yasamu sauqin rad'ad'in ciwon da yakeji sai aka dace da ijaba ta sauka bayan jimawarsa azaune yana shan magani da kuma amfani da addu'o'i Wanda inada tabbaci akan tasirinsu ne yanzu yazamo silar samun sauqinsa bayan natofa masa addu'a aruwa yasha." STORY CONTINUES BELOW "Laaa ashe Inna qarya takeyi, don Allah Nima zakiyiwa ya nura aruwan yasha sai ya aureni." Muneera tafad'a had'e da matsowa kusa ga Rashidar bayan ta d'an sassauta murya, Saida Rashida tayi dariyar da duka haqoranta suka bayyana sannan tace, "a'a aunty muneera bazan yimaki ba domin duk son da kike yimasa baikai adadin wanda nake yimasa ba, saidai Ina baki shawara akan kema kije kiroqawa kanki ALLAH daya baki shi, amma nidai bazanyi ba." Taqare zancen cike da mamakin sakarci irin na Rashida, Ture lab'b'a muneera tayi cike dajin haushinta tajuya tabar wajen tana fad'in "'yar baqin ciki, ALLAH ko bakyaso saina auri ya nura, bazaki zauna ke kad'ai ashiyar nan ba tundanima Ina qaunarsa, shegeyw mai tsawo kamar na iccen rama" dariya Rashida tayi sannan tawuce abunta had'e da turo qofar. Na'ima da Aisha ma yaran Inna Bilkisu dake zaune dawowarsu daga wajen niqa kenan don duk abunda yafaru basa nan akayi suma suka sawa muneera dariya jin abunda yafaru tsakaninta da Rashida, kansu tayo tana susar kai suka tashi suka ruga aguje tabisu tana zunduma masu zagi dama Inna Bilkisu nacan d'akin baffa ana murnar samun lafiyarsa. Ita ko Inna ruqayya sashen Yaya hawwa tanufa ta iskota cikin d'aki in tayi nan tayi can tana daddagar hannu had'e da cizon baki tana girgiza kai, "hmmm yanxu fa shikenan bakida abunyi yariga d'aya jawo maki reni ga yarinya, ya zubar maki girma agaban idanuwan d'anki sai yanda sukaga dama zasuyi acikin gidannan." Ina ruqayya tafad'a tana watsa hannuwanta baya tariqesu tana jiran amsar da zata fitowa daga bakin Yaya hawwa don tasan yanda zata sake tunzurata idan ta zubar da maka manta a fusace Yaya hawwa tajuyo had'e da cewa "inaaa wallahi qarya ne, bai isa ba matuqar Ina raye, ai fad'a da aljani sai anshirya kuma duk lalacewar bushiya tafi qarfin a takata da qafa koda kuwa da takalmi ne, ni hawwa ban tab'a sawa raina abuba nakasa, atarihin zuriarmu ba'a tab'a sakin mace ba don haka baza'a fara akaina ba, badai ya hana nura ya saki matar saba, to ni kuma zansa matar nurah tabar nura nahar abada koda hakan na nufin zan mutu wlh sai tabar cikin gidan nan ita d'in banza da wofi." Murmushi Inna ruqayya tayi kafin yace, "ahh to Nima dai shi nagani, wallahi idan bakiyi da gaske ba saita rabakinda d'anki da mijinki, yanzu haka fa Ina kallon wasu surqulle da tayi da wasu sabbatu ta tofa masa aruwa yasha sai gashi ya tashi da qafarsa, ke wannan yarinyar itama Ina ganin da nata shirin take don ko yayan Bata barsa ba tunda kikaga kimanin watanni goma sha yana zaune duk rigima da fitintinun da akeyi agidannan bai tab'a tasowa ba sai yau don yaji ance a saketa, aikam kema kinsan sedai ALLAH ya kayauta Amma tagama da Yaya balle nura." Takai qarshen zancen had'e da fashewa da wani kukan munafucci, "Ke ruqayya fita, fita kibarni inji da abunda ke damuna don yau dole in koma wajen malan bakada imani, wannan shegen cikin dake jikinta dole adakatar da zuwansa duniya da ransa kafin ita Kuma musn nayi da ita." "Gaskiya kam Yaya hawwa, ai yarinyar nan wlhi tagama tona mana asiri." "Mtss..zan zageki ruqayya kitafi nace, akwai mai tona maku asiri kamar hasararriyar yarinyar dake gabanku, ai bakiga tonon asiri ba sai ranar data bud'e baki tafad'a duniya cewa iyayenta shashashune da basu san ciwon kansu ba tukuna, ni nafara tunanin bazan iya had'a zuria da itaba a haifo mun jika sak aku kuturu da gwalmammin qafafuwa." Yaya hawwa taqare zancen tana turo Inna ruqayya waje had'e da rufo qofar d'akinta. Tsaye Inna ruqayya tayi tana ayyana kalar abunda zata yimata duk ranar da burinta yacika akan wannan walaqancin da take yimasu ita da 'yarta sannan tawuce ranta ab'ace, d'akin da baffa yake tanufa fuskarta sake don kar afahimci yanayin da take ciki, lokacin mutane sun taru sai shigowa sukeyi suna fita ana yimasa barka da arziqi, baffa Ali da baffa Usman suma na zaune gefe fuskokinsu d'auke da farinciki duk da shi baffa Ali bahaka yaso aransa ba, yaso sai sungam shirinsu tsaf Mai faruwa tafaru koda zai samu lafiya gudun kada ya dakatar masu da shiri, yaqe kawai yakeyi amma haushi da takaicin taahin d'an uwan nasa yayi masa katutu azuciya, shi kam baffa yana tsaye yana gaggaisawa da mutanen dake shigowa, Kallo d'aya Nuraddeen yayiwa Inna ruqayya ya d'auke kai had'e da barin d'akin don yanzu shi ko ganinta baya son yi, bayan an watse yarage su kad'aine mutanen gida zaune baffa sai faman zagaya falo yakeyi yana yiwa ALLAH godiya, kallo d'aya zakayi masa ka fahimci tsantsar farincikin da yake ciki saboda ynda ya bayyana a fuskarsa. STORY CONTINUES BELOW Wata irin muguwar dariya sukaji baffa Ali ya kwashe da ita harda tuntsirawa yana nuna baffa cike da isgilanci sannan yace. "Ho.ho.ho Yaya kace yau ba zama, tun d'azu ka kasa zaune ka kasa tsaye sai faman zagayar d'aki kakeyi, halan tsoron zaunawa kakeyi gudun kada asake damqeka waje d'aya, koda yake gaskiya ka zaunu dole ka guji abunda zai sakesa ka zauna inba dole ba." Wani irin dimmm...baffa yaji har jiri na neman d'ibarsa jin kalaman dake fitowa daga bakin d'an uwan nasa, badon yasan lokacin da mahaifiyarsu ta haifi baffa Ali ba da tabbas yace daqyar idan shi jinin sane, saboda gaba d'aya halayyarsa kwata kwata batada kyawo, Babu hankali da lissafi acikin kowane irin zance da zaiyi, amma babu yanda ya iya dole yayi haquri dashi tunda jinin sane, fatarsa d'aya ALLAH ya ganar dashi matsalolinsa ya gyara kafin wuri ya qule masa, murmushi yayi sannan yakoma inda yake zama lokacin da yake jinyar yana kallonsa sannan yace. "Aliyu, ai ita jarabawar ALLAH takan zone ga bayinsa muminai, tabbas na zaunu anan wurin kuma nakanji na tawaya sosai, shiyasa yau da ALLAH ya yaye mun wannan lalurar nake ganin yakamata nayi farinciki na nuna masa cewa nagode da lafiyar daya bani, ba tsoro nakeji ALLAH yasake jarabtata ba domin shiyasan dalilinsa nayin hakan, nagode da irin naka farincikin daka nuna mun domin yasa nad'auki wani darasi aciki." Girgiza kai baffa Usman yayi had'e da cewa. "Ashsha Ali Kai kam wane irin d'an uwane haka? Shin kana ganin abunda kayi burgewa ne ko kuma zai samaa maka nishad'ine shiyasa kayisa? To kasani kayi kuskure mai girma domin kayi izgilanci da al-amarin ALLAH wanda shi keyin yanda yaso alokacin da kuma yaso. "juyowa yayi ya kalli baffa sannan yaci gaba da cewa. "kayi hak'uri da kalamansa in sha ALLAH zaiyi nadamar yinsu ko yaushene." Baffa Usman nagama fad'ar haka yabar d'akin dama tuni itama matarsa Inna Bilkisu takoma cikin gida don cigaba da aikinta saboda marecen dake gabatowa, nan take baffa Ali yaji jikinsa yayi sanyi kuma yafahimci bai kyauta ba. "Yi hak'uri Yaya." Yafad'a tare da miqewa shima yabar d'akin, Inna ruqayya nabiye dashi a baya... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/14, 6:58 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___33πŸ’Ž Ranar kam baffa kasa kwana yayi saboda abubawan da suka tarar masa azuciya, tsantsar farincikin samun lafiyarsa da irin kalaman da d'an uwansa ya jefesa dasu, Abu mafi cimasa rai shine yanda matarsa uwar d'ansa tayi biris da al-amarinsa, duk masoyansa na nesa dana kusa sunzo tayasa murnar samun lafiyarsa amma ita da take matarsa mallakinsa da tafi kowa ribantuwa da ita takasa zuwa ta dubasa balle tanuna masa farincikin da tayi, wasu zafafan hawayene suka zubo masa yana mai nadamar zab'enta a matsayin abokiyar rayuwarsa kuma uwar 'ya'yansa, ganin zai sake jawowa kansa wani b'acin rai da damuwa yasa yashiga bayi yayo arwala yatada sallah yana mai miqa godiyarsa ga ALLAH daya fitar dashi cikin jarabawar da take ciki batare da anrabasa da imanin saba, Bayan sati d'aya da samun lafiyar baffa duk masu zuwa dubasa sun gama zuwa ciki har da iyayen Rashida, baba da umma da malan balarabe da matansa sai yayarsu hajia maryama da kuma aunty marwiyya, haka sukayo mota guda sukazo dubasa wanda ranarce tafarko da umma tazo gidan, duk da tanajin 'yan wasu matsaloli da 'yarta ke ciki tayi farinciki sosai ayanayin da taganta, don ba qaramar kulawa take samu daga wajen Nuraddeen ba, lokacin ne cikinta yacika wata biyar dam, tayi haske ta murje ko Ina na jikinta ya cika fam sai sheqi da kyalli takeyi abunta, ga d'an cikin daya fito ya zauna mata d'agwas ajiki gwanin sha'awa, duk wani motsi nata na akan idanuwan Nuraddeen da baffa, duk abunda take so taci suna bid'o mata batada wata matsala saboda yanzu komai tanaci kuma tadena yawan aman da takeyi si can baka rasa ba. Rashida tayi farincikin ganinsu sosai har tanaji kamar takoma ciki, da zasu tafi baffa yahad'a masu sha tara ta alkhairi shida baffa Usman suka rakasu har bkin mota, haka kurum Rashida ta tsinci kanta da fashewa da kuka tanaji kamar karsu tafi subarta tariqe ummanta sosai, saida Nuraddeen yayi da gaske yasamu ya lallab'ata suka koma cikin gida sannan su kuma suka wuce cike dajin kewar 'yar tasu. Duk wasu abubawa da baffa yasan nashine a d'akin da yayi jinya yana cika satin nan guda da warkewa ya kwashesu yamayar asalin shiyarsu wato d'akin Yaya hawwa dama jinya ce takaisa can shiyasa yanzu da ALLAH yabashi lafiya ya dawowarsa saboda yasamu damar tsawatar mata, sosai hakan da yayi ya matuqar b'atawa Yaya hawwa rai har tana cewa ita ya komawarsa can d'akin kar yazo ya takurata, yi yayi kamar bai jitaba yaci gaba da kwaso kayansa yana maidowa nan cike da burin dakatar da ita ga dukkanin mugun nufinta. STORY CONTINUES BELOW Hakan kuwa da yayi ya matuqar yiwa Nuraddeen dad'i ya sake maida hankalinsa wajen renon cikinsu, wata irin mahaukaciyar soyayya yake nunawa Rashida wadda ko alittafan novel bata tab'a jin irinta ba balle a finafinan zamani, kusan ko yaushe yana gida idan yataso makaranta, tare sukeyin komai kuma yanaci gaba da koya mata karatunta, ba laifi tana fahimta sosai don yanzu karatun hausa kowane irine zata iya karantawa, haka shima na bokon don su ( _come, go, sit-down, walk, run, stop, shoutup, ask_) duk ta iya, haka ma fannin had'a jimloli da turanci irinsu, ( _I will be there soon, stop crying, don't worry, why do you ask, tell them e.t.c_) duk ta iya saboda yanda ya d'aukesu da muhimmanci shiyasa yafara koya mata ire irensu saboda yanda zai samu sauqin mu'amala da ita cikin sauqi idan suna cikin mutane, haka shima duk wasu addu'o'in da be iyaba yana koya daga wajenta, rayuwarsu cike take da burgewa gwanin ban sha'awa saboda yanda suke son junansu, qauna da kuma kulawa abun ba'a magana, kallo d'aya zakayi masu kafahimci yanda kowanensu ke shirye da sadaukar da farincikinsa akan d'an uwansa, furuci da kalamansu d'ai idan ka saurara zaka fahimci cewa shirya suke da su mutu wa junansu, daidai da qwarar zarra basa ba baqinciki damar da zai shigo masu cikin rayuwa, sun yarda da juna kuma sun amince akan zasuyi rayuwa tare kuma zasu mutu atare shiyasa sukeda tsananin fahimtar juna, cikin Rashida na tsufa qwaqwalwarta na dad'a bud'ewa wajen d'aukar karatun da Nuraddeen ke koya mata, Wanda si yanzu ne tafahimci cewa Babu wata wahala cikin karatun kamar yanda take tunani kawai rashin so da maida hankali yasa takasa natsuwa tayisa. Tuggu da makirci kuwa har yau Yaya hawwa takasa dena shiryawa Rashida shi, idan tayi wannan tayi wancan ta binne nan ta binne can amma duk wanda tayi sai ALLAH ya kubutar da Rashida, sau da yawa tasha zuwa tayi binne binnenta a bayan d'akin Rashida sai ALLAH yatura yara garin wasa su tonosa, musamman ta karb'o maganin da zai sawa Rashida baqin jini agun Nuraddeen ta zauna ta dama matashi cikin fura da nono saboda sanin yanda take matuqar son furar ta ajiye gefe da zimmar idan Rashida tashigo gaishesu zata bata tasha, malan bakada imani ya tabbatar mata da cewa matuqar ta shata Nuraddeen zai tsaneta da ita har abunda ke cikin cikinta kuma bazai qara ko awa d'aya da ita ba a matsayin matarsa zai saketa da kansa, kuskuren da tayi ta manta cewa da bakinta tasha fad'a agaban kowa cewa ba tason Rashida da ita har abunda ke cikinta, shiyasa lokacin da taba Rashida furar da tazo gaishesu baffa dake zaune yana karyawa yafahimci akwai wani abu ciki, har Rashida tamik'e cike dajin dad'i tana yimata godiya baffa yakirata, wata baqar leda yajawo agefensa dake d'auke da fura da nono da ba'a dama ba masu yawa ya miqa mata yace taje da ita tadama masu ita da mijinta sai tabashi ta hannunta yasha, yanda taga furar tayi kyau yasa taji tabiyo mata arai amma bazata iya musawa baffa ba tunda yace yana so, miqa masa furar tayi tana binta da kallo kafin takarb'i wacce ya miqo mata aleda tabar d'akin, tana fita Yaya hawwa tafara masifa akan ya za'ayi tabata abu ya karb'ar mata, murmushi kawai yayi tare da girgiza kai yace "hawwa kiji tsoron ALLAH, yarinyar nan da bakinki kike iqirarin baki sonta akan me zaki bata wani abu yanzu, shiyasa nafahimci akai wata badaqalar da kike shiryawa aqasa ni kuma na karb'e furar." "To amma ai badonta zanyi ba saboda abunda ke cikinta kuma naga tana sonta sosai." Saida ya mere baki sannan yace, "saboda abunda ke cikinta? Kin manta shima kince bakya sonsa bakya qaunarsa? Taya za'ayi yanzu kiyiwa mahaifiyarsa abu donsa baya baki sonsa." "Nifa malan kadena jifata da sharri ba abunda nasawa furar nan, kyautatawa ce kawai amma kana bid'a kamaida cibi yazama qari." "To fad'awa wani hawwa, Amma dai bani ba, kinfi kowa sanin nasan halinki kar babu abunda bazaki iya iyaw yarinyar nan ba tunda baki sonta baki qaunarta, idan kuma kince ba haka bane ungo furar kisha ke." Yafad'a yana miqa mata furar a hannunta. "Ungo riqa kisha nace." Yasake fad'a akaro na biyu yana kallonta. Ganin ta had'e rai tare da juyar dakai gefe yasa yayi murmushi cike da takaici yace. "Hmm! ALLAH yaganar dake hawwa, bakida gaskiya ko kad'an acikin alamurranki, zan so ace kin daure kin zibar da makaman yaqinki akan yarinyar nan tunda har rabo yariga yashiga tsakani, kiyaqi zuciyarki kiyarda da qaddarowar ALLAH acikin aurennan idan ba haka ba zakiyi babban dana sani da Kuma nadama lokacin da basa da amfani, yanzu haka hawwa zuciyata cike take da nadamar zab'arki da nayi amatsayina uwar d'ana gashi nadamar batada amfani tunda har rabo ya gitto a tsakaninmu, lokaci yariga yaqure mani da zan iya maida hannun agogo baya badon haka ba wallahi bazan zab'awa d'ana mahaifiyar da Bata tsoron ALLAH kuma take shirka dashi." Baffa nagama fad'in haka ya d'auki furar yaje toilet da ita yazuba da yake na qasane ya jefar har da kofin aciki sannan yafita yana mai neman sauqi da sassaucin jarabawar da ALLAH yayi masa da ita. STORY CONTINUES BELOW Ita kuwa kamar ta k'walla ihu haka taji don izuwa yanzu tafara fara kaiwa maqura bisa tufk'ar da takeyi baffa nayi mata walwala, gaba d'aya ya kasa ya tsare akan al-amarin yarinyar ko shine mahaifinta ai hakan ya isa, miqewa tayi had'e da riqe qugu tana hurar hanta tace, "Shikenan! Yanzu kam wasan yazo qarshe, zanyi amfani da dukkanin abunda na mallaka a duniya don cikar burina da nuna maka cewa baka isa ka dakatar dani ba." A fusace tajuyo ta d'auki mayafinta da sauri da sauri tabar gidan ta nufi jejen wani mugun boka da tuni taso zuwa rashin kud'i ya hanata ana cemasa boka mai abun mamaki wato (bargaji) kamar yanda kowa yasanshi dashi yau taquduri komai yakeso zata bashi matuqar zai fitar mata da waccan matsiyaciyar acikin zuri'a. Rashida kuwa na komawa sashenta ta kwab'e hijab d'in dake jikinta zuciyarta cike da farincikin tafara samun karb'uwa a wajen uwar mijinta ganin alkhairin data yimata, ALLAH sarki baiwar ALLAH bata san cewa yanzu haka tana can kan hanyar illatata ba da kuma tabbatar mata da tsanar da take yimata ba, kitchen ta nufa da tulalen cikinta daya shigo wata na tara, nan da kwana ashirin ko yaushe ana tsammanin haihuwarta, wani d'an madaidaicin bokiti ta d'auko taje ta dama furar da baffa yabata tasha sosai sannan taje toilet ta watso ruwa tadawo falon taqara shan furar sannan takai kitchen ta ajiye, tana fitowa saiga Nuraddeen ya dawo daga makarantar can yarimawa da yake koyarwa, don tunda cikinta ya tsufa yadena zuwa yayo kwanaki acan sai dai kullum yaje ya dawo, cike da yanga tanufo inda yake don ta tarbosa tana fad'in, "oyoyo habibynah welcome back my love my everything." Bud'e da baki yabita da kallo yana kafeta da idanuwansa maau matuqar d'auke mata hankali, murmushi tayi ganin yanda yake kallon takowarta izuwa garesa da d'an cikinta daya yimata kui, dama saye take da wata doguwar riga data d'ame mata jiki ko ina cikin yafito sosai ya matauqar qara mata kyau kamar ba ita ba, rufe idanuwansa yayi had'e da bud'ewa sannan ya bud'e mata hannayensa kafin taqaraso yana fad'in "thank you habibtynah kece haka kuwa?" tana qarasowa tarungesa ya mayar da hannuwansa yana shafa bayanta yana dariya, tace "Ni d'ince kuwa donma babynka ya b'atamun tsari." "Kai habibtyn habiby! ba ruwan baby na kyau ma naga ya qara maki sosai." Yafad'a yana janta zuwa d'aki, cuno baki tayi had'e da cewa. "Ba wani nan habiby wayau dai zaka yimun, Amma kabari nahaife maka babyn nan naka zakaga yanda zanyi fresh in koma 'yar gayu, baran ma idan nafara zuwa school d'in da kace zaka kaini, hmmm sai kasha mamakin ganin yanda habibtyn nan taka zata canza." Tak'are maganar tana aza kanta saman kafad'arsa riqe da hannusa, "ALLAH habibty nah?.." Nuraddeen yafad'a daidai lokacin da yake qoqarin zaunawa saman kujera had'e da turo idanuwa waje. turo nata itama tayi tana kad'a masa kai alamar tabbatar da zancenta had'e da cewa "serious habiby". Jawota yayi ya zaunar da ita saman cinyarsa yana shafa cikinta ahankali sannan ya d'ago kansa yana kallonta yace "you're serious ko? to nafasa babu inda zakije." Saida tayi dariya sannan tarungumosa ta aza kansa saman breast d'inta tace, "haba dai habiby!, kaima dai kasan wasa kakeyi, kaga! Mudai bar wannan maganar ka tashi muje na tayaka kawatso ruwa sai kaci abinci, duk da yau dai ba abunda kake so nadafa maka ba, Eba ce da miyar shuwaka nayi maka." Saida yayi kissing d'in cikin nata sannan ya d'ago kai ya lakuci hancinta sannan yace, "anything habibty indai daga wajen kine I luv it koda kuwa bana son sa." Yafad'a yana kashe mata ido d'aya. Jan hannunsa suka nufi uwar d'aka tana fad'in "you different habiby." Dariyar da saida haqoransa suka bayyana yayi had'e da jawota tafad'o masa ajiki ya jingina jikin wardrobe d'in dake cikin d'akin yana k'arewa kyakkyawar fuskarta kallo suna shaqar lumfashin juna yace "you're different zakice habibty ba you different ba kinji ko?." 'Dan turo baki tayi sannan yace, "koma yane ai kaine ka koyamun shi ahaka" tafad'a a shagwab'e tana b'alle masa mab'allin rigarsa, da haka Nuraddeen ya shiga zolayarta yana aika mata da wasu zafafan saqonni masu wuyar fassarawa har yasamu ya lallabata cikin azanci yabiya buqatarsa. STORY CONTINUES BELOW Tare suka shig wankan bayan sun fito ta kimtsa agurguje had'e da zuwa ta kawo masu abinci sukaci suka qoshi sannan yace ta taso suje tamotso jikinta don yaga qafafuwanta sun fara kumburi, Kitchen tafara shiga tasha ruwan farin zob'on da umma tabata satin daya wuce da sukaje dubosu tace tadinga sha zai taimaka mata wajen kakkatse tsak'in dake fita yayin haihuwa da wani wanda Inna Bilkisu tabata shi kuma tace maganin tsinkau tsinkau yakeye, Sha takeyi tan wani b'ab'b'ata rai yana tsaye yana kallonta har tagama sannan tafito. *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/14, 10:32 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___34πŸ’Ž Habiby wai har ina zamuje ne motsa jikinnan haka naga duk kabi ka kasa ka tsare." Rashida tafad'a tana cuno baki ba, jawo hannunta yayi had'e da cewa, "Idan mukaje ai kya gani, nalura bakya son kina motsa jikinki kuma kinsan ko awonmu na qarshe da mukaje saida likita ya jamana kunne akan kirinqa yawan motsa jiki zai taimaka maki wajen aihuwa, don haka dole yanxu kiyi hak'uri muje ko don chu luv d'inmu, mud'an zazzagayo" Zaro idanuwa tayi waje had'e da rufe baki tace, "don ALLAH karufan asiri habiby, wlh bazan iya ba, ka kuwa san halin mutanen garin nan naku kuwa?, Kawai kayi haquri zan motsa anan cikin gida karka jawowa kanka zagi." Zai sake magana ta aza yatsanta akan leb'ensa had'e da cewa. "Pls.. habibyyyyy." Tare da Jan k'arshen sunan cikin shagwab'a. Bayanda ya iya da ita dole ya hak'ura don aduk lokacin data yimasa irin wannan kiran ji yake baya iya musa mata akan komai, "To yanzu fad'amun ya kike so ayi, motsa jikinnan dai kinsan dole kiyisa ko saboda lafiyarki Kuma ina so ki haifomun my chubby luv very strong!" Yafad'a yana kallon cikin idanuwanta. "Muje ka rik'amun k'afa fuwana zanyi set back (wani salon motsa jikine da mutum zai kwanta ko kuma zaunawa yana yin gaba yayi baya na tsawon wasu sekonni sannan yadawo gaba, haka zai dingayi har na tsawon mintunan da yaji zai iya.)" "Anya zaki iya habibty." Ya tambayeta cike da tsoro, "o'oh zan iya mana, ai masu ciki nayi kuma babu abunda ke samunsu." Haka kuwa akayi suka koma falo ya taimaka mata sosai tayi set back d'inta fiye dana mintuna ashirin har tagaji ta dena saboda mararta da taji tad'an amsa mata, sake taimaka mata yayi ta watso ruwa saboda yanda zufa kefita jikinta sannan yariqota suka dawo falo ta zauna tare da miqe qafafuwanta ya shiga yimata tausa har bacci ya d'auketa. ••• ••• ••• Tafiya mai nisa Yaya hawwa tayi kafin takai cikin dajin boka mai abun mamaki (bargaji), tana kaiwa ana kiran sallar la'asar tayi tsaye abakin wani beji tana dube duben ta inda zata hango bukkar bokan da aka fad'a mata cewa daidai wajen yake zama sai gashi ta isko wanen wayam Babu alamar wata bukka awajen, tafi minti biyar kafin tajuya zata bar wajen cikin wani irin sauti marar dad'in ji taji ance. "Maraba dake hawwaaa.., maraba da zuwa gidan miyagun aljanu, gidan biyan buqatun shed'anu da bau tsoron ALLAH, gidan rashin tausayi da imani, gidan da babu kunya balle mutunci, gidan cin amana da mugunta, gidan da babu jin tsoron ALLAH wajen kashe mai rai ya zamo matacce, Mai lafiya mu maidashi naqasashshe, shikuwa mai hankali mu maidashi mara hankali, marabanki abokiyar ta'bewa da hasara, meke tafe dake." Cikin dakewa da rashin tsoro Yaya hawwa tace. STORY CONTINUES BELOW "ALLAH ya taimaki bargaji..." "Keee dakata, ba'a kiran sunan ALLAH anan domin wud'anda alqawarin tab'ewa ya tabbata akansu kad'ai ke zuwa wajen, yanda kika manta dashi kika zo nan haka zaki manta da sunan har saikin bar wajennan." Taji ankatseta cikin wata irin murya daban, "To boka mai abun mamaki Ina roqon ayi mani afuwa zan kiyaye haka." "An maki abokiyar b'acewa, muna sauraronki fad'i buqatarki." "So nakeyi a haukata surukata tabi daji Kuma kada takoma dawowa gidan d'ana har abada." "Bazai yuyu ba, kicanza buqata." Taji anfad'a tawni b'angaren, juyawar da zatayi sai ga bukkar ta hango gabanta da bai wuce taqa goma tsakani da ita ba. "Boka mai abun mamaki saboda me bazai yuyu ba, bana son takoma shiga rayuwar d'ana shiyasa nake son agusar mata da hankali na har bada.." bata rufe baki ba taji an d'auketa kyawawan maruka har guda biyu, tana shirin magana taji ana jawota zuwa inda bukkar take, Saida akazo daidai bakin qofar shiga ciki taji an durqusar da ita wajen ana zuba mata ruwan buloli tako ina ajikinta ana fad'in "kada ki kuskura kiyi kuka domin shizai qaro fushin alhajimalan akan tambayar da kika yimasa." Yaya hawwa naso tayi kuka amma ta kama bakinta tarufe da hannuwa, duk saukar bulalar da taji ajikinta saita turo idanuwa waje tana had'iye kukan har aka gama" Gaba d'aya jikinta saida yayi laushi sannan aka k'yaleta ana maimaita mata cewa "ba'a tambaya awajen." Kad'a kai tashigayi tana d'aga hannuwa alamun bada haquri kafin taji an sake janta an maidata ajikin bishiyar da take tsaye d'azu. "Ki canza buqata muna sauraronki." Aka sake fad'a, cikin rawar murya tace. "Du..du.duk yanda akayi mata boka mai abun mamaki." Wani irin iska taji ya taso had'e da guguwa taji ance "d'ago kanki." Tana d'agowa cikin guguwar aka nuno mata hoton Nuraddeen zaune alokacin da yake tattausawa Rashida qafafuwa, banda fuskarsa da hannuwansa da tagani bisa qafafuwa yana mammatsawa wud'anda ta tabbatar na Rashida ne bataga komai ba, duk iya leqe laqen da zatayi don taga fuskarta kasa gani tayi bokan ya kece da dariya had'e da cewa. "Bazaki ganta ba domin ko mu anyimana shamaki da ganinta, tanada matuqar riqon ibada da addininta don haka baza'a iya galaba akanta ba, wannan auren had'in mai sama da qasane don haka bazamu iya rabashi ba, kawai mafita d'aya itace zamu iya fitar da ita cikin gidan idan mukayi sa'a da tana cikin rashin tsalki kowane irine to zamuyi nasarar yimata kurciyar da zata b'ace tayi nesa dashi, iya qarfin addu'arta iya tasirin da kurciyar zatayi akanta." "To boka haka ma yayi, me zan.." bata qarasa ba tayi saurin rufe baki tunawa da dukan da tagama sha akan tambayar da tayi, dariya bokan ya kece da ita sannan yace. "Bama karb'ar komai anan, mun b'ace kuma dole mub'atar, juya can kafin kitafi kiyi sallar la'asar." Kafin tace wani abu taji an sake janta izuwa bakin wancan bukkar ta d'azu, jikinta ne yahau rawa tazata wani dukan zatasha taji cikin wata irin murya daga cikin rumfar ance. "Shigooo, shigoooo" Jiki narawa tamiqe tashiga cikin rumfar, wani irin mugun hayaqine da wari suka tarbeta nan da nan tafara tari, dishi dishi tafara ganin wani mutum marar ma'ana tamkar mahaukaci yace "kijuyo anan ki sallaci sallarki ta la'asar." Tsabar b'acewar Yaya hawwa da muguwar zuciya tanaji tana gani ta kabbarta sallah agaban wannan mutumen, ruku'inta da sujada gaba d'aya shi tayiwa su sannan ta sallame. Ji tayi ansake fizgota da qarfi anfito da ita izuwa bakin waccan bishiyar ta d'azu tashiga waiwaye waiwaye tana nemn inda zataga masu jan nata haka saboda tsavar bushewar zuciyarta. "Kitafi, ki saurari biyan buqatarki akoda yaushe kuma kitafi da baya baya har kifita jajin nan, rashin aikata haka kuma zai ruguza dukkanin murdanki." Taji ana fad'a cikin wani salon murya da tamkar mutum biyu keyinta, da haka Yaya hawwa tafita jejin duk da tsananin nisan da yake dashi kafin akai hanyar cikin gari, fad'uwa kam tashata tafi a qirga kafin tasamu tafito, gashi duk tabi ta guggurje a qafafuwa, amma da yake taji tagani tana fitowa tayi wata irin ajiyar zuciya had'e da cewa "wahala ruwace nasan watarana wucewa zatayi" sannan taja qafafuwanta tawuce gida. STORY CONTINUES BELOW Tana dawowa taci karo da baffa abakin gida suna tattaunawa akan wata magana wacce itace mafitar da baffa yasamawa kansa akan al'amarin Yaya hawwa da zata sama masa kwanciyar hankali dashi har dansa da iyalinsa. Shiru yayi yana kallonta tun daga sama har qasa lokacin da tazo wucewa don lokacin ana kiraye kirayen sallar magrib, cike da takaici ya katsa mata tsawar da saida tasata dawowa da baya har tana shirin fad'uwa saboda rashin kuzarin dake tattare da ita. "Daga gidan wa kike kuma da izinin wa kika fita?." Baffa yafad'a had'e da yawo kanta a fusace, d'aga hannunsa yayi da niyar marinta ko zai rage rad'ad'inta da yakeji azuciyarsa, baffa Usman ne da tun d'azu ya sinne kansa qasa duqe yayi saurin tasowa yariqe masa hannu, "Haba Yaya kada kayi haka domin kasani annabi ya haramta mana dukan matanmu musamman akan fuskokinsu, koda yaushe kaike tunasar damu akan haka taya za'ayi yau Kai kuma kayi yunqurin aikata hakan kuma awake, inaga hakan bai dace ba, don ALLAH kayi haquri ka had'iye fushinka." Wani irin kuka mai ban tausayi baffa yafashe dashi yana nunata da hannu. "Wannan wace irin matace Usman kadubeta sama da qasa batada banbanci da jakar da tagama birkid'a aqasa, dubi lokaci qarfe bakwai saura mintota ace mace Bata cikin gidanta, wannan wane irin sakarci da lalacewa ne?, Narasa wane irin girman zunubine dana aikata ubangijiya had'ani da wannan fitinanniyar mace da gaba d'aya bata san ciwon kanta ba, wlh da nasan haka rayuwarta zata kasance agidana da banyi fatar yin aure ba har nakoma ga mahaliccina." "Kayi hak'uri Yaya jarabawace, itama kayi qoqarin canyeta kamar yanda kacanye na bayan, ALLAH shine masani bisa dalilin jarabtamu ta hanyar abubuwan sonmu da kuma jin dad'inmu, muje muyi sallah kaji har anfara tayar da salloli" Bugun iska baffa yayi da bayan hannunsa had'e da cewa "tir! hawwa ubangiji ALLAH ya shiryeki ya ganar dake" sannan ya juya suka nufi masallacin. Cije leb'enta na qasa tayi had'e dayin k'wafa sannan tajuya tawuce cikin gida tana ayyana kalar matakin daya dace ta d'aukarwa baffa idan ta gama da Rashida... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/15, 10:27 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___35πŸ’Ž Bayan kwana biyu kullum Yaya hawwa cikin zuba idanuwa take taga abunda zai samu Rashida amma shiru har lokacin babu abunda ya sameta saima lafiya da take taqara samu, haka ma ta b'angaren boka bargaji duk iya sihirce sihircen da zaiyi yayi amma yakasa samun nasara ko daidai da qwarar zarra da zai iya cutar da, yatura baqaqen aljanu da mugaye kala kala don su juyar mata da qwaqwalwa saboda tsananin fusatashin da tayi nason ja dashi tahanyar nuna gazawarsa ga aikin amma duk wanda yatura a qone yake dawo masa ko kuma naqashe saboda qarfin addu'o'in da takeyi da yawan sauraren karatun alqur'ani, ko kad'an Rashida bata wasa da azkar kuma bata yadda tazauna babu arwala ba ko kuma cikin janaba balle yasamu damar aiwatar da aikinsa wanda hakanne yaqara mata matuqar tsaro da kariya daga sherin shed'anun, musamman ya tura mata aljanun da zasu dinga tsereta koda zatayi kuskuren mantawa dayin addu'a lokacin kwanciyarta ko kuma lokacin da zata Tara da mijinta, a tunaninsa yafi komai sauqi Amma sam agurin Rashida bata wasa da hakan, haka ma tsakar dare yakan turo wasu da zasu dinga zuwa suna tsoratata shima da sunje saisu tarar da ita tana nafilfili wanda takanyi hakanne aduk lokutan da tajita cikin tsoro ko miyagun mafalkai, ko kad'an nauyi da girman cikinta basusa tayi sakaci da ibadar taba domin ita tad'auka a matsayin jigon dake tafiyar da rayuwarta cikin aminci, babban farincikin ta d'aya aduniya shine yanda hankalin Yaya hawwa bai karkata wajen cutar mata da abunda ke cikinta ba wanda ako yaushe idan ta tuna da hakan takan yiwa ALLAH godiya, STORY CONTINUES BELOW Yauma kamar kullum tana zaune saman kujera taba qofar falonta baya tana karatun al-qur'ani saboda tuni ta kammala girkinta da kuma 'yan gyare gyaren gidan da takeyi sai ga Nuraddeen ya shigo cike da farinciki yana kiran, "habibty, habibty, habibtyyy..where are you my habibtynah?." Kasancewar takama farkon aya yasa takasa katsewa ta amsa masa har sai da takai k'arshen ayar, juyowa tayi daidai lokacin daya shigo yayi saurin zuwa yarungumota ta baya had'e da sumbatar gefen wuyanta yana fad'in, "Masha ALLAH da samun nagartacciyar mace ma'abociya riqo da addini kamarki, ALLAH yayi maki albarka momyn chuluv d'ina." Hannunsa dake saman kafad'arta tasa hannunta tariqo had'e da sumbatarsa tace. "Welcome habiby abban chubby d'insa, ALLAH yasa alkhairine wannan kira da naji kana yimun tun daga bakin qofa?." Dawowa gabanta yayi ya amshi qur'anin dake hannunta ya saka mata alama a inda take sannan yarufe tare da ajiyesa gefe, hannunsa ya d'ora akan cikinta yana murmushi, daidai lokacin abunda keciki ya motsa, da sauri yacire hannunsa yana zaro idanuwa awaje, dariya ta bushe masa da ita had'e da cewa. "Lafiya abban chubby d'insa?" "Kai!.motsifa naji yakeyi habibty.!" "Eh mana, baka tab'a ji bane?, Ai shine cikakkiyar lafiyarsa idan yana wannan motsin inji likita, ai wannan bashine karo nafarko daya fara motsiba, kaine kawai baka tab'a cin sa'a ganin saba alokacin da yakeyi." "Najifa tsoro!" Nuraddeen yafad'a cike da mamaki yana kallon idanuwanta, kallo d'aya zakayi masa kasan tsokana ce tasa yafad'i haka, dariya tayi had'e da cewa. "Tab lallema habibtyn! nan, to meye abun tsoro anan? Kenan ni da yake ajikina sai in mutu idan naji motsinsa?" "Ahh..rufamun asiri bance haka ba, to idan kika mutu ni kibarni Ina?, Yihaquri dama zolayanki nakeyi." Yafad'a yana dariya, Dukan wasa takai masa a gefen kafad'a had'e da d'an harararsa cikin shagwab'a tace. "Kai ko!" "Afuwan bazan qara ba, yanzu dai albishirinki?" "Goro fari qalqalqal." Yanzu muka gama waya da baba yace zancen komawarki gida wanka abarshi tunda anan kike awo har sai ALLAH ya saukeki lafiya sai amaidaki dake da babyn, kinga dai nima zan d'an qara morewa Ina dinga ganinki keda chuluv d'ina kafin lokacin.?" 'Bata rai tayi kamar zatayi kuka don har tafara shireshiren komawarta sati mai zuwa amma sai gashi yazo ya wargaza mata tsari, cike da jin haushi tafara kaimasa duka 'yan k'wallah nafito mata shi kuma yana dariya, "Wato zuwa kayi kafad'awa su baba kada abarni na koma?, Kuma shine za kazo ka aza mani dariya ko? Why habiby meyasa zaka yimun haka?." Tafad'a tare da fashewa da kuka, ganin da gaske takeyi saboda hawayen da suke zubowa daga idanuwanta yasa yatsaya da dariyar da yakeyi yana qoqarin riqe mata hannuwa. "Srry habibty ba haka bane, wlh bana son kiyi nesa dani ne?, Kuma idan kin lura duka duka kwanaki nawa suka rage ki haihu?, sati biyu kacal fane, ai kinga da ace kin koma can Kuma haihuwar tazo ankwasoki anyo nan k'ara kiyi hak'uri ki haihu nan abunki, kinga ranar da kika haihu idan an sallamome nayi maki alqawarin da kaina zan d'aukeki in kaiki gida kinji ko?." Yaqarasa maganar cikin sigar rarrashi, fad'awa tayi ajikinsa tana kuka ya rungumeta yana shafa kanta zuwa bayanta cike da mamakin yanda abu kad'an ke sata kuka yanzu, sun jima ahaka yana cigaba da rarrashinta tahanyar dad'ad'an kalamai masu sanyi da kwantar da zuciya kafin ya d'agota yana kallon idanuwanta, sadda nata tayi qasa yasa hannu ya tallabo fuskar yana goge mata hawayen. "Kina so in fad'a maki wani albishir da zai faranta maki rai.?" 'Dago idanuwanta tayi takallesa tare da cuno baki gaba tace, "ni bana so idan kasan zai sake b'atan rai." STORY CONTINUES BELOW "No..no..wannan nasan zakiji dad'insa Kuma zai saki farin ciki sosai." Yafad'a yana sumbatar 'yan qanan lab'b'anta, "ALLAH da gaske?" "Sosai kuwa." "Ok. Ina saurarenka." Tafad'a tana qarasa goge hawayen dake nema su bushe a fuskarta. Murmushi yayi yariqo hannuwanta had'e da cewa "Habibty!, nasamu gurbin cigaba da karatuna, sunana yafito ajerin sunayen wud'anda gwamnati ta d'auki nauyin zuwansu qasar malesia don suqaro karatu, baban farinciki anan ma shine dana dawo naje Ina sanarwa da baffa yake fad'amun cewa yasama mana gida haya da zamu zauna idan kindawo daga wankan biqi kafin nawuce, kinga sai musha soyayyarmu hankali kwance babu takurar gidan yawa." Cike da farinciki tarungumesa tana fad'in. "Alhamdulillahillazi bini'imatihi ta timmusswalihat, congrat habiby gaskiya nayi farinciki sosai, ALLAH sarki baffa ai da yabarmu anan d'in, kullum baya gajiya dayi mana hidima da son faranta mana, ALLAH yabiyashi yasaka masa da mafi qololuwar alkhairinsa." "Amin ya rabbhi habibty." Yafad'a yana dariya cike da jin dad'in addu'ar da tayiwa mahaifinsa, "Amma habiby yaushe ne zaku wuce?" Tafad'a tana d'agowa daga jikinsa, shiru yayi kamar mai wani tunani kafin yace "Ehmm..inaga kamar nan da wata uku sukace, amma ungo takardar kiduba kigani." Yafiddo takardar daga aljihunsa yana miqa mata. "A'a kabarta, Amma gaskiya abun ya matse sosai, kamata yayi ace ko nan da wata biyar ne, kaga lokacin chubby child d'inka yad'an saba da kai..." tafad'a tana d'an b'ata rai. "Karki damu zan iya cewa a d'agamun lokaci saboda matata da chuluv na buqatata akusa dasu koda nan da zuwa wata goma ne idan kina buqata." "A'a rufamun asiri, ai dama ce ta lokaci d'aya idan tasamu to yayi amfani da ita.. ALLAH yakaimu lokacin kuma yasa munada rayuwa." "Amin habibtynah. Shiyasa nake qara sonki saboda wannan kaifin fahimtar da kike da ita." "Bawni wayau da zakayimun, ALLAH zamuyi kewarka sosai idan katafi." Taqare maganar tana shafa tulelen cikinta daya qara girma sosai cikin kwana biyu d'innan. "ALLAH dai ya saukeki lafiya kuma yabamu rayayye mai albarka." "Amin habiby." "Yawwa nace wane suna kike so mu sakawa babynmu idan kin haihu?." "Emmm..idan macece sunan Inna nake so a saka mata hawwa'u mudinga kiranta (jiddah) idan kuma namijine sunan ka nake so yaci wato (Nuraddeen)." Tuni baffa yagama samarwa su Nuraddeen hayar wani d'an madaidaicin gida acan farkon gari kusa da asibiti mai d'auke da d'akuna biyu da falo d'aya sai kitchen da toilet, sai tsakar gidan da girmansa bai wuce iya mutum biyar su kwanta ba, yayi hakanne don su samu sakewa su huta da takurar Yaya hawwa shi kuma yasamu yaqaro aure ko yakoya mata hankali, wannan itace shawarar daya yanke tsakaninsa da baffa Usman da tuni yayi magana da Inna Bilkisu za'a bashi auren 'yar yayarta da ALLAH yayiwa rasuwa tagudo tadawo nan garin sanadiyar wahalar da take Sha a hannun 'yan uwan mahaifinta, qaramar yarinyace da Bata wuce shekara goma sha uku zuwa Sha hud'u ba da yake su can qauye basu d'auki abun wani abubu har da shekara goma zuwa goma sha biyu suna aurar da yarinya, cikin sa'a kuwa iyayen Inna Bilkisu suka yarda saboda yanda sukaga baffa Usman yariqe masu 'yarsu hannu biyu shiyasa suka yarda da nagartar yayan nasa suka amince da aura mashi yarinyar koba komai hakan zaisa idan 'yan uwan mahaifinta sukaji tayi aure su dangana da batun komawarta can. Duk wannan abun da akeyi Yaya hawwa batada labari tana can tana haukar rashin ganin aikin boka da bai kama Rashida ba, gashi wannan bokan ba'a yimasa katsalandan ko tambaya balle takoma taji ba'asi, gaba d'aya abu ya isheta ya sha mata kai tarasa yanda zatayi, Inna ruqayya kuwa tuni itam tabazama wajen bokaye tunda taji abunda Yaya hawwa tafad'a akan bazata had'a zuria dasu ba don arufe mata baki Kuma akarkato masu da zuciyar Nuraddeen ga muneera har sai ya aureta, Adaidai wannan lokacin da Rashida da Nuraddeen ke cikin halin tsaka mai wuya a hannun bokaye cikin Rashida ya cika wata wata tara dam da haihuwa, duk abunda yakamata Nuraddeen ya tanada na kayan baby da mamansa gwargwado ya tanada, haka kuma duk abubuwan da mahaifiyarsa keyiwa matarsa bai tab'asa ya yarda haqqinta ko d'aya ba akansa, duk wata kyautatawa yana yimata daidai gwargwado kuma kullum dashi har Rashida basu fasa zuwa gaisheta ba amma Rashida bakinta d'auke da addu'o'i take zuwa gaisheta ko yaushe sanin halin da ake ciki, musamman itama ya saimata kaya kala biyu ya kimata da zimmar taci suna dasu idan ALLAH ya sauki Rashida lafiya, yau tunda safe Nuraddeen yatashi da fad'uwar gaba wacce yarasa dalilinta amma yanata addu'ah batare daya bari Rashida ta fahimci halin da yake ciki ba, Da daddare suna kwance ta mulmulo wajensa had'e da d'ora kanta saman kafad'arsa tana yawo da hannunta saman qirjinsa, a hankali yayi gyaran murya had'e da cewa. "Habiby lafiya yau naganka sai ahankli, meyake faruwa da kaine?" Wata ajiyar zuciya yayi had'e da cewa. "Habibty babu b'oyo a tsakninmu domin kin zama ni nazama ke, nayi qoqari wajen ganin ban bari yanayin da nake ciki ba yayi tasirin bayyana a fuskata har kika fahimta, amma tsantsar kulawarki agareni yasa hakan ta gagara, bansan yau meke faruwa ba tun safe nake jin yanayina daban duk babu dad'i ga wata irin fad'uwar gaba dake damuna, addu'a nakeyi amma sai qara tsananta abun keyi narasa ya zanyi habibty, cikin kwantar da kai da sigar rarrashi tafara yimasa magana cikin sanyin murya tace. "Haba Nuraddeen, hasken idaniyata, zuciyata da kuma ilahirin gangar jikina, Kai kuwa meye zai tayar maka da hankali bayan kasan kanada ALLAHnka akoda yaushe kuma yana tare da kai, me zaka jiwa tsoro aduniya kai dake tare da sa albarka iyayenka, me kake shakku acikin rayuwarka bayan kana da yaqini akan zamu kasance atare, don ALLAH kadena fargaba akan komai koda kuwa wani abunne zai sameka ko kuma ya sameni, natabbata cewa tsantsar imaninmu da miqa wuya ga ALLAH shine kan iyasa ajarabcemu, muzama masu juriya cikin al-amurranmu alokacin da wani abu kenema ya gitto mana cikin rayuwa, sai musamu kanmu masu riskar ubangijinmu amadakata kyakkyawa, kacire komai aranka in Sha ALLAH babu abunda zai faru, nasan harda tunanin haihuwarnan yasa kakejin haka, to kasanyawa ranka salama in sha ALLAH zan sauka lafiya kuma zan haifa maka chuluv d'inkacikin qoshin lafiya kaji ko" taqare maganar tana sakar masa kiss ta ko ina afuskarsa har da saman tsinin hancinsa, cikin dariya ya rungumeta shima yana sumbatar goshinta yace. "Nagodewa ALLAH daya sanya cikakkiyar natsuwata a hannunki, ALLAH yayi maki albarka yasa kigama da duniya lafiya, nayarda da shawarwarinki da kuma duk tsarin da ALLAH yayi mani arayuwa, ALLAH kasanya farinciki ya zamo cikar gurbin yanayin da nake ji." "Amin habibynah jarumin mazan duk duniya." Karan hancinta yaja tare da lakatar kuncinta yace. "Abaki kenan amma idan nace ingwada jarumtar tawa yanzu ai bazaki yarda ba, chuluv d'innan nawa naga nema yake tun kafin yazo duniya yafara takuramin." "Karkai masa sheri domin Babu ruwansa, habibtynka ce kawai keyi maka rowa saboda nauyin da tayi amma yau bazata yimaka ba matuqar kanada buqata akanta." Tayi hakanne saboda ta tabbatar da tagusar masa da damuwarta amma ita tunda cikinta yashiga wata na tara takejin wahalar kwanciya da ita, hakan yasa shima yadena takura mata. Cike da farinciki ya mirgino fuskarsa na kallon tata yace. "Da gaske habibtyn habiby zaki iya jurewa?." Kad'a masa kai tayi alamar ta tabbatar da hakan, cikin dubaru da tausayi yafara sarrafata ta hanyar da yasan bazata wahala ba har ya biya buqatarsa, tun kafin yagama taji mararata na murd'a mata ga wani ciwon baya da taji yarufeta amma saboda qarfin hali da kwad'ayin samun natsuwarsa yasa tajure har saida yagama. "Habibty tashi muyi wanka." Yafad'a yana qoqarin saukowa saman gadon, Sai data cije baki cikin tsananin zafin da takeji tace. "Kaje kafarayi habiby daqyar idan zan iya yanzu saboda marata namun zafi." "Yi haquri habibty duk nine najawo hakan, Bari nad'aukeki sai muyo ko?." "A'a kafara zuwa kayi, idan kafito ko arwala ce nasamu nayi kafin asubar tunda annabi ya halarta yin hakan." Miqewa yayi har ya aza qafarsa zai shiga sai kuma yadawo had'e da sumbatar goshinta yace. "Ina matuqar sonki da qaunarki habibty and I dont want to loose you any more in my life, be couse you're my everything, if I say everything I mean everything including my entire life, I love you for ever and ever and ever." Cikin wani yanayi da ita kad'ai tasan ya takeji tayi masa murmushi tare da cewa. "me too all I have." Show some luv plsπŸ‘ #COMMENT #VOTE #SHARE *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/16, 10:46 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ 😭😭 _THE MOST BREAKING HEART & HEART TOUCHING PART OF THE BOOK_πŸ’”πŸ’” Page___36πŸ’Ž Sake miqewa yayi ya nufi toilet d'in bakisa d'auke da addu'a ita kuma ta lumshe idanuwanta tana jin wani irin azababben bacci na son d'aukarta, a wannan lokacinne madubin boka bargaji ya nuna masa cewa Rashida bata cikin tsarki, nan take yafara surqullensa yana turo mata miyagun aljanu masu matuqar qarfi, wani iskane yataso da qarfi cikin d'akin da sauri Rashida tafarko daga nannauyan baccin daya soma d'aukarta tana cije baki, kan kace me tuni tafara ganin duniyar na juya mata, qoqarin kama addu'o'i tafarayi abakinta amma duk wacce tajawo saita kucce mata, wasu Halittu tafara gani cikin iskan daya mamaye gabanta suna nufato inda take kowane da kalar sigarsa suna qoqarin illatata amma qarfin addu'o'in da takeyi ya shamakance tsakaninta dasu, hakan yasa suka gagara yimata komai saboda aduk lokacin da suka tunkarota wani irin gilashi mai qarfi suke ganin ya shiga tsakaninsu da ita, basu dena tsorata taba ita ma batadena karanto addu'o'in da suke bakinta ba har saida azabar ciwon da take ji ya tsanantar mata, gaba d'aya tarud'e tashiga tashin hankali, wani irin yanayi take jin kanta aciki wanda tunda aka haifeta bata tab'a jin kanta acikiba, yanayine da kallo d'aya zakayi mata kasan cewa naqudace ta taso mata adaidai wannan lokacin, tun tana jurewa har tafara gazawa idanuwanta suka fara zubarda k'walla tana kiran "ALLAH, ALLAH." don alokacin iya shi kad'aine bakinta ke iya furtawa. Ganin duk aljannun da bargaji keturawa sun kasa nasara yasa yakira wani mugun shed'anin aljani wanda aduk lokacin da aiki yayi masa tsanani ko yake nema ya gagareshi shi yake turawa kuma cikin ikon ALLAH zasuyi nasara saboda ALLAH ya riga daya sakar masu talala, cikin wani qamari da girgiza ya dumfaro Rashida da alokacin bata iya furta komai saboda azabar naquda data rufeta, wani surqulle boka bargaji ya sakeyi yanda idanuwan Rashida zasu bud'e, tun tana kwance saman gadon har tajid'o dafe da cikinta alokacin aljanin ya bayyana da wata irin mummunar siffa agabanta nan take ta some wajen ba tare data koma sanin inda take ba, duk iya abunda boka bargaji zai iyayi shida shed'anun dake taimaka masa wajen ganin ankawar mata da hankali ko mugun sammun da akayi mata yayi tasiri akanta sunyi amma cikin ikon ALLAH da nuna qarfin addu'a hakan ya cutara, nasara d'aya sukayi shine d'auketa da akayi akabar garin da ita, sanadiyar hakan aljanin ya dinga buga Rashida a jikin itatuwa yana wurgi da ita bisa duwatsuna, yamatuqar fusata ganin yanda yakasa aiwatar da aikin uban gidansa akanta Wanda wannan dalilinne yasa saida y azabtar da ita sannan ya Kai ya jefar inda suke sa ran bazata tab'a rayuwa ba kafin safe.+ ••• ••• ••• A 'ban garen Nuraddeen kuwa yana fitowa wanka riqe da d'an qaramin towel yana tsane ruwa akansa yace. "Habibty ki daure kitashi muje intayaki kiyo wankan nan, nasan yanda kika tsani kwana cikin irin wannan halin na janaba baccin bazai yimaki dad'i ba idan kikayi kwanciyarki a haka, gashi biyu har da rabi nadare ya somayi nasan lokacin tashinki shima yakusayi tunda ukku takusa. Pls daure ki tashi kinji?" Yaqare maganar had'e da juyowa yakai kalonsa inda take kwance, gabansa ne yayi mugun fad'uwa da sauri ya nufi inda yabarta kwance yana jaye mayafin da suke lullub'ewa don gaskata abunda idanuwansa kefad'a masa, a firgice yaja baya ganin bata wajen kwance da sauri ya nufi falo cike da fargaba amma ga mamakinsa nan d'in ma bata nan, kasa gasgata kansa yayi ya dinga d'add'aga pilows d'in kujeru da gefe gefen kujera cikin tashin hankali gabansa na bugawa da sauri da sauri, curtains d'in tagogi falon ya shiga d'ad'd'agewa yana kiran sunanta, babban taahin hankalinsa ma qofar falon daya gani kulle Wanda yatabbatar masa daba fita tayi ba, da gudu yakoma uwar d'akan yana rerrega qarqashin gado da bayan wardrobe yana sake kiran sunanta da qarfi, bud'e qofar toilet d'insu yayi yaqara shiga yana dudubata har bayan gambu kafin ya fito jikinsa na rawa yabud'e d'akin gaba d'aya, gaba d'aya ya manta darene haka yadinga kiran sunanta yana bud'e qofar kitchen, STORY CONTINUES BELOW Jin qarara muryarsa da baffa Usman yayi yana kiran sunan matarsa yasa shi fitowa da sauri sanin halin haihuwar da a ciki ko yau ko gebe, "Nuraddeen lafiya.?" Baffa Usman yashiga bubbuga qofar shiyar tasa yana tambayarsa. Sai a sannan Nuraddeen yanufo wajen da sauri yabud'e k'ofar daidai lokacin shima Baffa yafito, tare suka had'a baki shida baffa Usman lokacin daya bud'e qofar suna tambayarsa ko lafiya?. "Baffa Rashida!." "Me yasamu Rashidar?" baffa yatambayesa firgice ganin yanda yaga hankalinsa atashe, "Baffa ban ganeta ba..." Kafin ya rufe baki a tsorace baffa yatura kansa cikin shiyar baffa Usman na biye dashi yana fad'in "kamar ya baka ganeta ba, ita tsinken allurace da zaka nemeta cikin d'akin kuna tare k'arasa?." Bayansu yabiyo tare dayin gaba yana fad'in "wlh baffa yanzu nabarta anan kwance nikuma nashiga in watso ruwa koda nafito ban ganeta banganta ba, dube dube suka shigayi suna leqe leqen cikin d'akin cike da mamaki, Tare suka fito da fitillu a hannunsa suna dudduba cikin gidan amma babu alamun Rashida balle mafarinta, "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, Inna lillahi wa'inna ilaihirrajiuun.." Nuraddeen yashiga fad'i yanajin kansa na jujjuya masa, "Baffa nashiga uku, dama yau jikina nafad'amun wani abu zai faru dani, baffa ina Rashida zata shiga awannan cikin tsohon daren ba tare dana sani ba?, Wlh baffa akwai abunda ke faruwa ba daidai ba." "Nuradden ka kwantar da hankalinka za'a ganeta, abun tambayar a ina tashiga?" "Shine tambayar baffa, Kuma ko Ina akulle nagansa kamar yanda nabarsa, baffa kataimakeni inajin tsoro kada acutar mani da ita." Nuraddeen yafad'a yana goge hawayen da suka fara yimasa kwaranya a idanuwa, ko Ina na cikin gidan su baffa suka shiga zazzagayawa harda Inna Bilkisu data farko lokacin hankalinta atashe jin abunda ke faruwa, d'akuna tashiga bi tana tambaya jikinta duk amace har zuwa wancan d'ayan b'angaren 'yan uwansu dake cikin gidan amma amsar d'aya ce, ba'a ganta ba!. A cikin darenhankalin kowa yabi yatashi anata sallalami, baffa Ali kuwa kallon inna ruqayya da itama ta dan shiga tsinke yayi yana nuna mata Yaya hawwa dake tsaye ta rafka uban tagumi fuskata cike da damuwa kamar da gaske ammaqasan zuciyarta cike take da farinciki yace. "Dubi Yaya hawwa, narantse da ALLAH tasan komai, d'akin kalleta Zaki tabbatar da kawai tashuka tsiyar don farincikine tattare da ita bayan waccan damuwar da kika hangota aciki." Murmushi tayi had'e da cewa. "Ranar bayyanar asalin tata damuwar nakusa tunda tagama cimma nata burin." Ganin kowa yayi cirko cirko ana jajanta maganar b'atan Rashida yasa Nuraddeen yanufi qofar gida a hargitse yana sabbatu da sauri baffa Usman yariqesa yana fad'in, "Ina zakaje Nuraddeen acikin wannan tsohon dare, qarfe uku fa ake magana yanzu, kayi hak'uri har muga abunda safiya zatayi." Wani irin kukane yazo masa yana kallon baffa Usman cike da mamaki yace "Baffa da bakinka kake fad'in inbar iyalina acikin wannan tsohon dare batare da sanin awane hali take cikiba?, Baffa amana ce fa agareni, bayan haka katuna halin da take ciki idan akace salame ce baffa kanaga zamu iya runtsawa awannan daren muna jiran wayewar safiya sannan muje nemanta?, Don ALLAH baffa kabarni inje koma meye yasameni nida ita, zuciyata nayimun rad'ad'in da zan iya mutuwa awannan lokacin idan natsaya dakon jiran dawowarta." Yana gama fad'ar haka yabud'e gambun yafita batare daya jira amsar da zata fitowa daga bakin saba, dagudu ya fice cikin gidan ko fitila babu a hannunsa Saida yakusa kai farkon gari sannan yafara yawo yana kiran sunanta, inyayi nan yayi can batare daya damu da yanayin dare ko duhun dake da garinba., Idan yayi wancan lungu ya shiga wancan yakoma wannan haka yayita yawo yana kiran sunanta, kallo d'aya zakayi masa kasan kwanciyar hankali tagama gushewa a jikinsa, wasa wasa har qarfe hud'u tayi ba batun Rashida, kaf ya zagaye k'auywn nasu da qafa ko takalma bashida yana kuka yana ambatar sunanta tamkar wani k'aramin yaro duqewa yayi yasaki wata irin qara had'e da jin kansa yana jujjuya masa, yafi minti biyar ahaka kafin ya miqe tunawa da 'yar qramar kasuwar garin da yayi ya nufi can da gudu, rumfuna rumfuna yadinga bi yana leqawa amma began taba, hanyar asibiti yanufa lokacin biyar da rabi na asuba yafara zagayenta tamkar wani tsohon mahaukaci sannan yashiga ciki yana lelleqa d'akunan majinyata, ganin nan ma Babu labarinta yasa yafara shiga dazukka dake cikin qauyen tamkar wani mashayi saboda yanda yake tangad'i saboda tsananin tashin hankali da gajiya, tun yana kuka har hawayen nasa suka qare, haka suma su baffa suka shiga nemanta cikin qauyen Amma babu labarinta, misalin qarfe shida na safe ko salla basuyi ba suka wuce qauyukkan dake maqwabtaka dasu amma har qarfe bakwai na safe balabarinta, a hanyarsu ce ta dawowa suka cikaro dashi saman hanya yashe mutanen gari sun zagayesa, da gudu baffa yaqarasa kusa dashi cike da damuwa ya tallabosa, ckallon yanda yayi bijib bijib da jiki ga qafafuwansa duk sun yayayyanke qaya ta sossokesa yasa baffa ya fashe da kuka yana fad'in. STORY CONTINUES BELOW "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, allahummah ajirni fi musibati wa'ahlifni khairan minha." Cikin yanayin dake nuna Nuraddeen nacikin matsananciyar damuwa ya d'ago kansa yace, "Baffa kunga matata Rashida?. Baffa kubarni anan kuje kudubo mun ita, raina fansane agareta koda zan mutu kuje kutaimaketa, qarfina yaqare gaba d'aya, lumfashinanema yakeyi ya rabu da gangar jikina saboda rashin sanin a ina take, Kuma awane hali take ciki, baffa kutaimaketa jikina yana bani cewa Rashidata nacikin wani hali.." bai qarasa maganar ba sanadiyar lumfashinsa daya d'auke, jijjigasa baffa yashigayi yana kuku had'e da kallon baffa Usman da shima kukan yakeyi yace. "Usman kataimakeni kada inrasa d'ana da nafiso aduk fad'in duniya." Kan baffa Usman yaqarso wajen har baffa ya ciccib'o Nuraddeen da sauri baffa yaqarasa wajen ya kama masa shi suka nufi hanyar asibiti dashi asheme ko motsi ba yayi. Kan kace me batu ya gama zagaye qauyen nasu cewa matar Nuraddeen ta b'ata da tsohon cikinta wata tara. Baffa Ali kuwa fad'a yakamayi yana fad'in tun farko Saida suka guji wannan auren saboda Babu alkhairi acikinsa yanzu gashinan zasu jawo masu abunda yafi qarfinsu don yasan iyayen yarinyar nan dole suje su kaiwa 'yan sanda rahoto azo adamesu da 'yan tambayoyi, Su baffa na isowa asibiti likita yaduba Nuraddeen tare da yimasa wasu allurai ya fad'a masu sumace yayi amma yanzu zai farfad'o, yana rufe baki Nuraddeen na tasowa da qarfi daga kwancen da yake akan gadon asibitin cikin matsananciyar qara yana fad'in. "Rashidaaaa...." *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUπŸ‘πŸ˜­* [7/17, 11:04 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ _Amincin Allah ya tabbata agareku masoya littafin SANNU SANNU...haqiqa zan iya cewa tunda nafara littafinnan ban tab'a jin dad'in rubutunsa ba kamar jiya, saboda yanda naga ruwan comment d'inku har da wud'anda Raina bai tab'a kawomun cewa suna karatun saba, na matuqar jin dad'i har sai da zuciyata takoma tana rayamun cewa anya soyayyar da kuke yiwa Rashida batafi wacce kuke yiwa Billy ba?😰 What ever d case am feel a little jealous oo..πŸ˜‰lolz..nagode nagode sosai jazakumullahu bikhair, I LUV YOU ALL FILLAH_🀍❤️ Page___37πŸ’Ž Juyowa su baffa sukayi tare da likitan suna rigegeniyar isa inda yake, tsaitsaye sukayi gabansa fuskokinsu cike da tausayinsa ganin yanda nan take duk yabi ya zabge kamar wanda ya buge watanni yana jinya, riqasa likitan yayi daga zaunen da yake ya maidashi kwance yana fad'in. "Relax malan Nuraddeeni, in Sha ALLAH komai zai daidaita kaji ko?" A hankali yarufe idanuwansa wasu zafafan hawaye suka zubo masa afuska, juyowa yayi yana yabud'e idanuwansa suka sauka saman na baffa Usman, kamo hannunsa yayi yariqe sosai har lokacin hawaye nazubowa daga cikin idanuwansa yace. "Baffa kun ganta kuwa?." "Kayi hak'uri Nuraddeen, in Sha ALLAH za'a ganta, kafara qarfafa zuciyarka tukuna tayanda zaka iya fad'an nemo masoyiyarka aduk inda tashiga, kada kabari raunin zuciya ya bayyanarwa da duniya gazawarka ga masoyiyarka dake neman taimakonka takowane fanni." Baffa usman ne yafad'i hakan yana rumqe hannunsa sosai, cikin yanayin dake bayyana dukkanin raunin da Nuraddeen ya samu ta fannin zuciya, gangar jiki, kwakwalwa da kuma ruhinsa yace, "kaicona da riskar wannan lokaci da nayi, meyasa mutuwa batayi gaggawar d'aukata ba kafin wannan ranar tazo mani?, Meyasa rayuwa zata yanke mana wannan hukunci a daidai lokacin da muke tsananin buqatar juna?, Meyasa soyayya tayimun d'aurin goron dana kasa gano alfanun dake cikin komawar Rashida agaban iyayenta saboda kawai Ina buqatar kasancewa tare da ita akoda yaushe? Meyasa duniya zata juya mana baya a lokacin da ALLAH keshirin yimana kyautar da zata bamu jin dad'in zamanta?, Meyasa?, Meyasa baffa?" Yaqarasa maganar yana qara fashewa da wani irin matsanancin kuka maicin rai, da sauri baffa yajuya yabar d'akin saboda bazai iya jurar sauraren kukan d'an nasa ba, kowace hawainiya dake d'igowa daga cikin idanuwansa jinta yakeyi tamkar saukar qyanqyashe a saman zuciyarsa, baffa Usman kuwa sake rumqe hannun Nuraddeen yayi sosai cikin dakewa yace. STORY CONTINUES BELOW "Kayi haquri, kayi haquri, kajure kada zuciyarka tasa ubangijinka yayi fushi dakai, Babu dalilin dakesa ALLAH yayiwa bayinsa jarabawa kamar tsantsar imaninsu agaresa, wlh wlh Ina tabbatar maka da cewa duk inda matarka take bazata tab'a walaqanta ba domin ita yarinyace mai tawali'u ga ubangijinta, yarinyace mai tsananin riqo da addini da kiyaye dokokin ALLAH don haka dole ALLAH zai jarabceta harma damu dake tare da ita, saidai abu gudane nake da tabbaci akai da kuma kyakkyawan zato zuwa ga ubangijinmu cewa zai kula mana da ita aduk inda take fiye da kulawar da zamu yimata, mumunin k'warai shi ALLAH ke jarabtar kuma duk tsananin ibadarka da tsoron ALLAH bazai hana ajarabci imanin kaba saboda aqaramaka d'aukaka awurin ubangiji idan kaci jarabawarka, kayi haquri in sha ALLAH za'aganeta yau d'innan kaji ko?." Duk da dai babu wani rad'ad'i da ya denaji azuciyarsa da kuma quncin dake damunsa ya yarda da duka kalman baffa Usman kuma zai gwada amfani dasu, kalaman data dinga fad'a masa daren jiya ne suka shiga yimasa yawo a kwakwalwa _Haba Nuraddeen, hasken idaniyata, zuciyata da kuma ilahirin gangar jikina, Kai kuwa meye zai tayar maka da hankali bayan kasan kanada ALLAHnka akoda yaushe kuma yana tare da kai, me zaka jiwa tsoro aduniya kai dake tare da sa albarka iyayenka, me kake shakku acikin rayuwarka bayan kana da yaqini akan zamu kasance atare, don ALLAH kadena fargaba akan komai koda kuwa wani abunne zai sameka ko kuma ya sameni, natabbata cewa tsantsar imaninmu da miqa wuya ga ALLAH shine kan iyasa ajarabcemu, muzama masu juriya cikin al-amurranmu alokacin da wani abu kenema ya gitto mana cikin rayuwa, sai musamu kanmu masu riskar ubangijinmu amadakata kyakkyawa, kacire komai aranka in Sha ALLAH babu abunda zai faru, nasan harda tunanin haihuwarnan yasa kakejin haka, to kasanyawa ranka salama in sha ALLAH zan sauka lafiya kuma zan haifa maka chuluv d'inkacikin qoshin lafiya kaji ko_ Tsananin jin yanda kansa keyi masa ciyo tamkar zai tsage yasa yai saurin dafe kansa da hannu bibbiyu yana sakin wata qara, da gudu baffa yadawo cikin d'akin ya tsaya yana fad'in. "Nuraddeen kayi haquri karka jawo nima in rasaka." "Baffa kaina zai fashe." Nuraddeen yafad'a hawaye na dararo masa ta gefen idanuwa, juyowa baffa yayi yana kallon likita dake gefensa yace. "Likita don ALLAH kuyi masa allurar bacci koya samu koda 'yar qaramar natsuwa ce azuciyarsa." "Abunda nake tunanin yi kenan nima." Likitan yafad'a tare da ciro biro a aljihunsa ya rubuta masu allurar bacci yace aje asiyo, baffa Usman ne yakarb'a da sauri ya nufi gefen da pharmacy take acikin asibitin ya siyo yakawo masa, daidai bakin qofar da zai shiga d'akinne yaci karo da baffa Ali suka shiga tare, miqawa likitan dake can gefen wani marar lafiya yana sa masa drip allurar yayi yace yadwo nan inda Nuraddeen d'in yake ya jirasa, shi Kuma baffa Ali tsaye yayi saman kan Nuraddeen yana kallon yanda ya zabge lokaci d'aya, ajiyar zuciya yayi sannan ya maida kallonsa ga baffa dake tsaye yace. "Yaya Ashe jikin nura haka yazama, ni yanzu yaran gari sukaje suna fad'amun cewa ai kunanan asibiti da nura ya zauce saboda b'atan matarsa" "To kadai gani Ali, jarabawar da ALLAH yad'oro muna kenan! Ubangiji ALLAH yabamu ikon canyeta." "Amin Yaya, Amma to ba wannan ba yakamata yaronnan yasawa ransa salama, idan ALLAH yatsaro za'aga yarinyarnan to za'a ganta, in Kuma ALLAH be nufa ba to yayi haquri basai yaje ya illata kns ba zai samu wata matar tunda ba ita kad'aice mace ba, mata ne gasunan ko ina sai yazab'a ya darje, nan kusa ba nesa ba ga 'yar uwarsa nan muneera sai tamaye masa gurbinta ai inaga shikenan ko?" Cike da b'acin rai baffa ya nufosa had'e da shaqe wuyansa ya had'a da jikin bango. "Aliyu dama kai bakada hankali ban sani ba? Mekake nufi da idan ba'a ganeta ba? Wlh damuwata tafi yawa akan b'atar yarinyar nan fiye da halinda Nuraddeen ke ciki domin nasan cewa ganinta ne kad'ai zai kawo masa sassaucin wannan halin da yake ciki saboda itace farincikinsa, shine kake fatar kada aganeta saboda ita d'in ba 'yarka bace?, Yaqarasa maganar cikin d'aga murya tare da qara shaqesa tayanda ko lumfashi mai kyau baya iyayi, kakarin d'aya farayi ne yasa baffa da likita sukayo kansa suna rirriqesa amma suka kasa cire hannunsa daga wuyansa, cikin b'acin ran daya sauya masa kalar idanuwansa dake fari izuwa jajaye yace. STORY CONTINUES BELOW "Kaje ka muri sauran mintotan da suka rage maka kafin jami'an tsaro su iso gareka, Ina tabbatar maka da cewa dukkaninku sai nasa ansa kunfad'i inda kuka kai yarinyar mutane, idan ba haka ba zanyanke duk wata alaqa da Kuma 'yan uwantakar dake tsakanina dakai nasa akulleku har sai natabbatar da kunfad'i inda take tukuna." Yana gama fad'ar haka ya sakesa tare da wullasa gefe sannan yabar d'akin da asibitin gaba d'aya, baffa Usman ne ya tsaya har saida akayiwa Nuraddeen allurar bacci wanda duk abunda ke faruwa idanuwansa kad'aine arufe amma yana saurarensu. Take bacci ya d'aukesa bayan an laqa masa gorar ruwa guda. Juyowa yayi yana kallon baffa Ali da har lokacin ke zaune qasa yana lalubar wuyansa saboda azabar zafin riqon da baffa yayi masa a kuma lokaci guda yana fidda lumfashi d'aya bayan d'aya yace. "Ga d'anka nan ka kula dashi idan kaga dama, idan kuma baka gani ba zaka iya tafiya." Yana kaiwa nan shima yabi bayan baffa, har yakusa fita ya juyo had'e da cewa. "Yawwa Ali namanta in fad'a maka cewa zaka iya qarasa rayuwarsa idan kana buqata tunda bakwason ganinsa cikin farinciki balle raye." Sannan yawuce. ••• ••• ••• A gefen wani babban titi shed'anin da bargaji yaturo ya sace Rashida ya jefar da ita bayan yagama azabtar da ita lokacin qarfe hud'u da rabi na dare ko motsi batayi, abunda ke cikinta sai faman motsi yakeyi saboda azabar daya sha ga lumfashin uwa dake taimaka masa na neman yarabu da gangar jikinta, cikin iyawar ALLAH da nuna isarsa ga bayinsa da sukayi imani dashi kuma yake taimaka masu alokacin da suke neman taimako yasa sanyin asuba nafara sauka lumfashin Rashida ya daidaita ga gangar jikinta, wani dogon lumfashi taja had'e da qoqarin bud'e idanuwanta a hankali a hankali, ganinta agefen titi gashi duhu ya mamaye gari ko hasken mota bata gani saboda dogayen ciyawun da sukayi shamaki tsakaninta da titi balle ahangota yasa tafara qoqarin tashi, bataji wani dogon rauni ba a zahirance sai 'yar gugguljewar da ko ina ajikinta yayi da kuma azabar da takeji can cikin qashin bayanta da kuma mararta wanda in bata manta ba acikin wannan halin take kafin ta tsinci kanta acikin wannan yanayin da take kallo tamkar mafarki, jin an shureta cikin ciki ya tuna mata da d'an dake cikinta da sauri tasa hannu tana tattab'a cikin, duk inda taji alamun abunda ke ciki yayi motsi sai takai hannunta akai shi kuma sai ya janye yakoma wani gefen, haka ta dingayi tana murmushi kafin tafara qoqarin fitowa daga cikin ciyawun tana takawa da qyar saboda nauyin cikin. Hango wani haske da tayi acan tsallaken titi yasa tayi yunqurin tsallakawa don samawa kanta tsaro daga abun dakan iya cutar da ita awajen. K'iiiiiiiii...kakeji da qarfi motar dake tafe gabanta da gudu matuqin yaja burki ganin mutum ya gitta masa, nan take tsananin tsoro daya gama zama abokin rayuwarta yasa tasaki wata irin qara tare da duqewa wajen, k'iris kad'an ya rage Mai motar yabugeta Amma ALLAH ya taimakesa kafin motar takai ga jikinta yayi nasarar tsaida ita, qara hasken fitillun motarsa yayi don gasgata idanuwansa dake gane masa mace da tsohon ciki agabansa, da sauri ya bud'e motar yafito jin wata irin qara da Rashida tayi tana fad'in, "Wayyo ummata zan mutu." Saboda azabar naqudar da tataso mata lokaci guda, "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun., Baiwar ALLAH daga Ina? kike da asubancin nan haka?" Kasa magana tayi sai yarfi da hannu takeyi tana cizon baki, kallo d'aya yayi mata ya fahimci haihuwace zatayi saboda ganin ruwan dake bin qafafuwanta Wanda bako shakka fawace tafashe. Gabas da yamma, kudu da arewa yaduba Babu wani mahaluqi dake tahowa daga saman titin, shimad'in yayi sakkon fitowane saboda wani emergency operation da aka kirasa cewa zaiyi da safennan, shine dalilin fitowarsa cikin sauri zaije airport don ya hau jirgi sai gashi ya had'u da wannan tsotsayin, sake kallon Rashida yayi yaga she's too young da alama ma haihuwar farince duk rashin imaninsa bazai iya barinta awajen ba, gashi tana stage d'in da take matuqar buqatar taimako, bai tsaya saurarar zuciyarsa ba kawai ya runtse idanuwa yana karanto addu'a daga bakinsa ya tallabeta ya sakata cikin motar ya tayar ya nufi hanyar asibiti mafi kusa dasu acikin garin, kallon yanda take nishi da qarfi alamun haihuwar na kusa yakeyi had'e da qara gudun motarsa, A wata qatotuwar asibiti yayi parking had'e da fitowa da sauri ya bud'e bayan motar ya sake d'aukota yanufi cikin asibitin da ita yana kiran "nurse, nurse.." da gudu suka fito suka karb'eta suka nufi cikin wani d'aki da ita, wata nurse ce tashiga da sauri cikin wani office tayowa dr dake on duty magana suka fito tare da ita, har zasu shiga d'akin da aka shiga da Rashida yayi saurin tsaishesu yana fad'in STORY CONTINUES BELOW "Dr. don ALLAH ka taimakawa yarinyarnan, haihuwa ce zatayi kuma inaga wannan itace tafari, ga dukkan alama yamatuqar Shan wahala don tadad'e tana labour, yanayinta ya nuna tayi riching final stage da zata iya haihuwa wato 10cm don ALLAH kayi iya qoqarinka wajen taimakonta ta haihu lafiya." Yaqare maganar yana had'a hannayensa waje d'aya, riqa hannunsa Dr yayi yana mai bashi k'warin guiwar cewa zai iya sannan ya wuce batare daya tanka ba. Safa da marwa mutumen ya dingayi abakin d'akin yana mai addu'ar ALLAH ya sauketa lafiya kafin yaciro wayarsa yakira matarsa. Bugu d'aya ta d'aga had'e da cewa. "Swthrt har ka isa airport d'in." Cike da damuwa yace "A'a fatima banma je wajen ba, yanzu haka Ina asibiti.." miqewa tayi daga kwancen da take ta tashi zaune had'e da cewa "swhrt lafiya kuwa? meya same kane? Dama tunda zaka tafi Saida nafad'a maka hankalina bai kwanta da tafiyarnan ba qara kabari sai safiya tawaye ido naganin ido amma ka nace kai sai alokacin zaka tafi." Taqare maganar had'e da fashewa da kuka. "Haba Fatima meye haka kikeyi? Kinaji na ki saurareni kiji me zanfad'a, Babu abunda ya sameni kawai ansamu matsalace akan hanyata ta zuwa filin jirgin..." Nan yaciga da yimata bayani dalla dalla sannan takwantar da hankalinta, cike da damuwa yaci gaba da cewa. "Idan zaki iya munanan _mom maternity clinic_ kiyi sauri kizo kinji ko." "On my way Dr. In Sha ALLAH." Tafad'a tana goge hawayenta had'e da kashe wayar. Daidai lokacin shima yasaki wata irin ajiyar zuciya tare da runtse idanuwa saiga likitan yafito da sauri ya nufo inda yake tsaye. "Dr. Lafiya?." Mutumen yafad'a yana kallonsa cikin tashin hankali, shiru Dr. ya d'anyi kafin ya kallesa had'e da cewa. "Am sorry ansamu matsala. Dole zaka samana hannu anan." Yajuya wajen nurse d'in dake biye dashi ya karb'i takarda a hannunta yana miqa masa. "Zaka saka hannu saboda dole sai anyi mata tiyata bazata iya haihuwa da kanta ba." "Kamarya Dr.? Inada tabbaci akan takai adadin yanda ake buqatar ta haihu mezaisa kace Kuma bazata iya haihuwa ba yanzu." "Saboda yaron baizo daidai ba, ma'ana amai makon yazo takai sai yazo ta qafafuwa aturance muna Kiran irin wannan haihuwa da "breech presentation" wato haihuwar da tazo a baibai ba normal haihuwa ba." Shafa kai mutumen yayi had'e da cewa. "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun." Kafin yafiddo wasu i.d card guda uku had'e da license d'insa nazama likita a aljihunsa ya miqa masa da sauri, karb'a Dr. Yayi ya shiga dubawa, d'aya national i.d card d'insa ce, d'aya kuma i.d card d'in dake nuna yana aiki a qarqashin asibitin aminu kano ce dake garin birnin kano, d'ayar kuma shedar cewa shi qwararren likitane a fannin matsalar mata wato (gynicolgy) inda yaga an rubuta Dr. Nura ahmad. 'Dauke da lambobin dake nuna cewa shi cikakken likitane babba a fannin wato (consultant). 'Dago kai Dr yayi yana kallonsa ya jinjina masa kai alamar bashi tabbaci akan abunda yagani, cike da girmamawa Dr. Yasake bashi hannu suka gaisa saboda ganin shi babban sane. "Don Allah Dr zan iya shiga na taimaka mata?. Nasan insha ALLAH zata iya haihuwa da kanta basai anyi mata tiyata ba." Shiru Dr yayi kafin ya bashi hanya yana nuna masa qofar shiga d'akin, da sauri ya shiga ya tarar da Rashida kwance ta matuqar jigata, nan take yasa handglove batare daya cire kayan dake jikinsa ba ya nufi inda take kwance, Saida yafara zuwa saiti fuskarta yace. "Kiyi fad'a da kowace irin qadadara ce data fiddoki cikin dare awannan yanayin, ki qoqarta wajen ceto abunda kecikinki inada tabbaci akan komeye zai zamo sanyin idaniyarki, kada kibari qaddararki ta rinjayi nasararki wajen rasa abunda ke cikinki ta hanyar gazawarki, kiyi addu'a kuma ki jajirce kibamu had'in kai in sha ALLAH zamuyi nasarar wannan aikin da zamuyi." Binsa kawai Rashida tayi da kallo batare data iya tanka masa ba hawaye na tsiyaya tagefen idanuwanta, tabbas ba k'aramin tasiri kalamansa suka yimata ba hakan yasa taquduri bayar da rayuwarta ga abunda ke cikinta. STORY CONTINUES BELOW Nan take yafara ba nurses d'in umurnin miqo masa kayan aiki, cikin k'warewa da hikima irin wadda aikinsa ya koyar dashi yafar qoqarin jujjuya yaron da zimmar mayar dashi ya koma daidai, fiye da mintuna ashirin ya kwashe yana abu guda amma hakan ya cutara, kallon irin wahalar da tasha yayi amma duk da haka bata sare ba da sauri yasa hannu ya goge hawayen da suka zo masa tare daba nurses d'in umurni dasu canzo masa kayan aikin da zai karb'i haihuwar ayanda yaron yazo koda kuwa za'a rasa ranshi saboda aceto rayuwarta, Nan take aka had'a komai yashiga fara aikin cike da addu'ar ALLAH yasa ayi nasara, kusan wasu mintuna ashirin ya kwashe sannan yayi nasarar fiddo da yaron lafiya, yana fiddosa na'ura nagwajin d'aukewar lumfashin Rashida, haka shima yaron tsabar wahalar daya sha koda aka cirosa ko motsi baya yi, da sauri yajawo oxygen d'in dake can gefen gadonta ya harhad'a ya jona mata da taimakon nurses d'in dake wajen.... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/18, 10:56 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___38πŸ’Ž Juyowa yayi yana kallon Dr dake wajen tare dashi wanda yakamata ace shine ya karb'i haihuwar ya miqa masa hannu suka gaisa sannan yace. "Nagode sosai, in Sha ALLAH zata samu lafiya, ayanayin wahalar da tasha dole nasan hakan zata kasance, nayi abunda na Nemo alfarmaryi sauran kuma nagareku." Yaqarasa maganar yana cire handglove d'in dake hannunsa, murmushi Dr yayi yana yabawa qwarewar Dr. nura tare da jinjina masa akan namijin qoqarin da yayi, wanda badon haka ba babu ko shakka saidai suyi mata tiyata gudun abunda zai iya faruwa da ita ko d'anta, solutin nasa yayi shima had'e da cewa. "Weldone sir, sunana Dr sani Bilal Ina zaunene d'aya daga cikin gidajen dake cikin asibitinnan, naji dad'in had'uwa dakai sosai." "Masha ALLAH sunana.." saurin katsesa yayi tahanyar fad'o masa cikakken sunansa daya gani arubuce jikin i.d card d'insa ta asibiti wato "Dr. nura shu'aib k'wararren likita afannin matsalolin mata dake aiki da asibitin aminu kano dake garin kano." Murmushi yayi sannan yanufi gefen da nurses d'in ke gyara babyen har lokacin be koka ba, karb'arshi yayi ya d'aga qafafuwansa sama kansa na qasa yad'an twad'i d'uwawunsa sai gashi ya canyara ihu, murmushi farinciki yayi sannan ya miqa masu shi yana kallonsa, yaron kyakkyawane sosai gashi da girma tubarkallah, kallo d'aya zakayiwa jaririn kafahimci ba qaramin kulawa yasamu ba alokacin da yake cikin ciki, yana wannan tinaninne yaji wata nurse a firgice tace. "Dr...." Saboda ganin yanda yaron yafara amai yana fizge fizge, da sauri ya qaraso wajen ya karb'esa nan take yagano yaron yasha ruwan naquda, qoqarin zuqe masa su ya shigayi da taimakon Dr sani da gaba d'aya hankalinsu ya tashi, miqa masu shi yayi yace suyi maza maza su kaishi sashen ba jarirai taimakon gaggawa, haka kuwa akayi kafin kace me har sun isa wajen nurses d'in b'angaren suka karb'esa suka fara bashi kulawa kafin likitan dake b'angaren yaqaraso, yana zuwa yashiga duddubasa cikin k'warewa da iya aikinsa. Bayan komai ya daidaita shima yaron aka saka masa oxygen saboda yanda lumfashinsa ke kokuwar barin jikinsa. Dr. nura kuwa nurses nafita da jaririn ya nufi inda Rashida ke kwance ya qura mata idanuwa, gaba d'aya kamannunta dana yaron sunsha banban, wataqil shi mahaifinsa yabiyo, Yafad'a aransa, ficewa yayi daga d'akin yana tura hannuwansa cikin aljihu, sai alokacin ya tuno da wayarsa daya ajiye a can gefen gadon da Rashida take kwance da sauri yakoma ya d'auko, kusan 10missed call yagani Kuma duka na matarsa ne fatima wacce take da tabbacin tashigo asibitinne shine takirasa taji inda take, murmushi had'e da danna lambar ya sake kiranta, bugu d'aya ta d'aga tana fad'in. STORY CONTINUES BELOW "Swthrt kana inane? Tun d'azu kabarni a tsaye." Tafad'a cike da qorafi akan haka. "Fatima kenan! Yihaquri ki qaraso tanan gyani emergency Ina tawurin tsaye Ina jiranki." "To." Tafad'a had'e da kashe wayar sannan tanufi hanyar da zata sadata da wurin, daidai lokacin shima yanufo qofar fitowa daga wajen sukayi kicib'is da ita d'auke da kwandon kuloli har dasu qatuwar leda da flaks, zaro idanuwa yayi yana kallonta cike da mamaki yace. "Fatima duk meye haka?" dubon agogon hannunta tayi taga kusan qarfe goma da rabi na safe ta dafe kai had'e da cewa. "Kayi haquri nadad'e ban qaraso ba ko?, natsaya had'a mata wud'annanne, Ina jarin da aka haifa? tahaihu ko?" Tafad'a tana gyara zaman mayafinta cike da tausayi yabita da kallo, daga jin cewa ya tsinci maiciki a hanya suna asibiti zata haihu shine Fatima zata had'o wud'an abubuwa haka saboda tsananin son haihuwa da take da ita, ya ALLAH kadubemu da idon rahama muma kabamu namu masu albarka, yaqarasa fad'a aransa yana goge 'yan kwallan tausayinta da suka zubo mata. ••• ••• ••• Dr nura da Fatima mijine da mata dakeda matuqar kyakkyawar fahimta a tsakaninsu, kalla d'aya zakayi masu kafahimci aurensu auren soyayyane saboda yanda suke matuqar son juna, sunyi aure tun shekaru goma sha uku da suka wuce amma har zuwa tsawon wannan lokaci basu samu haihu ba, Fatima macece mai matuqar son yara amma jarabawa ta ALLAH ko b'atan wata bata tab'a yiba, anyi masu duk wasu gwaje gwajen da bincike bincike don agano dalilin rashin haihuwar tasu amma likitoci sun tabbatar masu dashi har ita duka lafiyarsu qalau basuda wata matsala data hanasu haihuwar kawai lokacine beyi ba, hakan yasa gaba d'aya suka tattara komai akan batun haihuwa suka watsar gefe suka rungumi junansu hannu biyu cikin so da qauna da kuma kulawar juna, fatarsu akoda yaushe da addu'arsu shine ALLAH ya basu masu 'ya'ya masu albarka aduk lokacin daya so kuma yanufa, Dr nura cikakken d'an asalin jahar borno ne amma wasu lokutan suna zama a kano saboda aiki daya kaishi can, dalilin fitowarsa yau tunda asuba shine kiran gaggawar da akayimasa tun jiya da daddare ne cewa ana buqatar ganinsa gobe qarfe takwas na safe akwai matar da zasu yiwa tiyata, shiya yayi asubancin tashi zuwa filin jirgin da zai tashi qarfe biyar na asuba don ya isa dawuri, ashe rabon ya taimaki Rashida a wannan lokacin ya fiddosa. ••• ••• ••• Wata irin ajiyar zuciya Dr. nura ya sauke had'e da riqo hannunta yace, "Kai fatima daga fad'a maki zancen matar nan zata haihuwa shine zaki tsaya kwaso kaya haka!." Dariya kawai tayi masa batare da tace komai ba saboda Babu abunda takeso alokacin irin taga matar da yace ya tsinta da babyn data haifa, d'akin da Rashida ke kwance yanufa riqe da hannunta har suka shiga. A bakin gadon Rashida yaja burki ya tsaya yana nunata da hannu. "Fatima kinga baiwar ALLAH da nake fad'a maki nagani tafito daga cikin wani daji tashigo gaban motata, badon ALLAH yatsare ba dana bugeta gata da tsohon ciki." Cike da tausayi tariqe hannunsa gam kamar zatayi kuka yace. "Swthrt meya fiddota waje a lokacin gata qaramar yarinya mai qanan shekaru, yanzu haka sharri da baqincikin d'a namiji yasata fitowa, kai walh wasu mazan basuda imani." "A'a fatima karkice haka tunda bamusan dalilin daya fiddota be daga gida ba, wataqil wata matsalarce daban." "Hmm! Bazaka gane ba swtht wlh yanzu hakan mijinne yakorota saboda wani banzan dalilinsa, ya ALLAH kadubi maraicinmu." Tafad'a tana d'aga hannuwanta sama hawaye nazubo mata daga cikin idanuwa, qara matsowa tayi kusa da Rashida taduqo had'e dasa hannu tana shafa fuskarta, "ALLAH sarki yarinya, ALLAH yatashi kafad'unki, wlh swthrt da ganin yarinyar nan akwai ban tausayi cikin al-amarinta, yanzu I babyn nata yake?" "Yana can shima anbashi gado bayada cikakkiyar." Yafad'a tare da juyowa yafito wajen tana biye dashi ya zuba hannayensa acikin aljifan wandonsa, kallonta yayi yaga yanda gaba d'aya jikinta yayi sanyi, murmushi yai sannan yaci gaba da cewa "muje can kiga yaron nata, so nake idan kin amince nabar komai ahannunki kafin nadawo nan da zuwa jibi idan yafarfad'o muji daga Ina take, thank God ma nayi waya da Dr qasim can wajen aiki yace anyi shifting theater da zanyi sai nan da 24hrs saboda jinin patient d'in daya hau sosai." STORY CONTINUES BELOW "Babu damuwa swhrt ALLAH yabasu lafiya, idan da imani da tausayi a qirjin bawa ko bakasan mutumba ai katausaya masa, shikuma taimako bakasan ta inda zai yimaka rana ba wataran, na amince Babu wata damuwa akan haka." "ALLAH fatina?" Dr nura yafad'a yana dariya. "Sosai kuwa, yanzu kafasa bin jirgi kenan?" "Eh da motar haya zanje sai inbar maki wannan koda wani abun zai taso, zan kira Salim ya kasance kusa idan kina buqata." "Noo..kabarshi kasan bama inuwa d'aya da qanennan naka yafiye reni da yawa." "To shikenan muje kigano yaron." ••• ••• ••• Baffa kuwa na fitowa daga asibiti kai tsaye gida yanufa ransa duk a dagule, gaba d'aya ya rasa mekeyi masa dad'i aduniya, yana shigowa cikin gidan ya tarar da yaya hawwa zaune a bakin rumfarsu Inna ruqayya takira mai tallar fankasu (na alkama) ta tasashi agaba sai ci takeyi tana dangwala yaji, tana ganin lokacin da baffa yawuce ta gabanta fuskarsa cike da damuwa amma ko kallon banza bi isheta ba, saida taci mai isarta taqoshi sannan tamiqe had'e da cewa yaron ya jirata tana zuwa ta karb'o masa kud'insa. 'Daki ta iskosa zaune abakin gefen gado ya rabka wani uban tagumi yana tunanin ta inda zai fara sanarwa da iyayen Rashida halin da ake ciki, cikin nuna halin ko inkula akansa tace. "Malan bani naira d'ari in biya yaron can kud'insa na fankasu dana ci." Tafad'a had'e da tura yatsa cikin baki tana qwalqwalo wanda ya laqemata a hauru, hannunsa yasa cikin aljihu yaciro d'ari biyu ya miqa mata ta amsa ba gode balle nagode taficewarta, ba'a jimaba tadawo tamiqo masa canjin naira d'ari ya sake miqa hannu ya karb'a yatura cikin aljihu, "Yawwa nace ina nura take?, Nifa tunda yafitarnan hankalina ba kwance yake ba kar yaje garin neman gira ya rasa ido..." Ai kafin tarufe baki baffa yamiqe tsaye yana nunata da d'an yatsa had'e da cewa. "Qarya kike, wlh qarya kikeyi kice kindamu da Nuraddeen, wai yanzu ke a tunanin ki ke uwace ahaka? tir da halin uwa ko in haka take, maqaryaciyar banza maqaryaciyar wofi, shashasha da batasan abunda takeyi ba, sakaryar uwa kawai to kitambayeni Nuraddeen damuwa kikayi dashine ko a'a?" "Ya haka malan sai kace wanda ke jiraye dani daga tambayarka yarona saika rufeni da kwandon fitina?" "Naji hawwa jiraye nake dake amma idan harda gaske kikeyi kina son ganin d'anki sai kifad'a mani ina 'yar mutane take tukuna, don bana haufi akan cewa duk inda yarinyarnan taje ko aka kaita kinada sa hannu aciki, don haka kifad'amun inda yarinyar mutane take naroqeki da ALLAH." "Buhun ubannan, lallai malan kace wani abu, meya dameni da wannan yarinyar da har zakace akwai sa hannuna aciki, to wlh kul kar inji..." Bata rufe baki ba ya d'auketa kyakkyawan marin da saida ta birkita, kafin ta taso yaqara mata wani, zuciyarsa na tafarfasa yace. "Anzo wajen hawwa, ahalin yanzu bana yimaki kallon daraja da kimar cewa ke matatace, baki isa kiyi mani jan kunne ba agabana, ayau kimanta da cewa ni Idris d'innan ne da kika sani mai sanyin hali da kuma haquri, wannan Idris d'in dake gabanki shirye yake daya sallamaki har abada, ahalin yanzu ba duka kad'ai da ALLAH ya haramta miji yayiwa matarsa ba hatta azabtarwar da zata iyasa kirasa rayuwarki na har abada zan iya yimaki saboda zaluncin da nake tuhumarki da aikatawa yarinyar mutane, don haka tun wuri ina fad'a maki kitanadi kalaman da Zaki fad'awa jami'an tsaro idan sunzo takanki don wlh bazan bar duk wanda keda hannu acikin b'atar yarinyar nan ba. Tsaye Yaya hawwa tayi tabisa da kallo cike da mamaki don ko amafarki Bata tab'a tsammanin cewa baffa zai iya yimata hakan ba, tureta yayi daqarfi daga gabansa da take yawuce yabar d'akin, yanajin yanda tafad'a akan qarfen gado kanta yabuge qum..amma ko juyowa beyi ba balle ya kalleta ya wuce abunsa zuciyarsa cike da tsanarta , Shikuwa Baffa Usman yana fitowa daga asibiti kai tsaye tashar mota yanufa ya shiga motar da zata kaishi cikin birnin kano, gidajen redio da telebijin yaje yabada iya kud'ad'en dake hannunsa don asa masa sanarwar b'acewar rashida ta kafafen labarai saida ya tabbatar anyi komai tukuna sannan yashiga motar da zata kaishi qauyen yarimawa, cikin sa'a ya tarar da malan balarabe yazo wajen baba, cike da karramawa suka tarbesa duk da dai fuskarsa ta gama nuna baya cikin yanayi mai dad'i. Bayan sun gaisane cikin natsuwa yayi masu bayanin halin da ake ciki ya qara masu da cewa yanzu haka shima Nuraddeen d'in yana asibiti rai a hannun ALLAH, STORY CONTINUES BELOW "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun" kad'ai baba ya iya furtawa daga nan bai koma cewa komai ba saidai sukaga ya b'ingire qasa daga zaunen da yake, ranar baffa Usman yaga tsantsar tashin hankali wanda ba'a samasa rana domin adaidai lokacinne itama umma data shigo d'akin kawo masa ruwa ashe duk abunda baffa Usman ke fad'a taji da kunnenta ne saidai sukaji fad'uwar kofin dake hannunta kan kace me itama tafad'i wajen a some... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/19, 6:49 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___39πŸ’Ž Cike da tashin hankali baba balarabe yaje ya d'ebo ruwa cikin gida aka yayyafa masu, kusan atare suka farfad'o amma babu wanda ke iya magana acikinsu, banda hawaye babu abunda kezuba daga cikin qwayar idanuwansu, ganin haka yasa malan balarabe yaje wajwn nemo mota don akaisu asibiti, yace wa baffa Usman dake gefe ya rabka uban tagumi cikin yanayi mai wuyar fassarawa yajirasa nan da mintota zai dawo. Kallo d'aya zakayi masu kasan akwai maganganu acikin bakinsu saboda yanda suka qurawa baffa Usman idanuwa Amma Babu bakin magana sai hawayen kawai da zasu iya fassara maka yanayin da suke ciki, ba'a jima ba malan balarabe yadawo da mota da Kuma matarsa d'aya don seda yakoma go ya d'auko kud'i, nan take suka d'aukesu suka nufi asibiti, Waya baffa Usman ya d'aga yakira baffa yace ya iskosa yarimawa ga abunda ke faruwa yanzu haka suna asibiti, cikin azama baffa yakamo hanya batare daya sanarwa da kowa halin da ake ciki ba, tafe yake yana addu'o'i abakinsa har yasamu mota, tund'azu ALLAH ne kad'ai yasan awane yanayi baffa kejin kansa saboda tunanin yanda zai fuskanci iyayen Rashida ya sanar dasu zancen b'atar 'yarsu ashe har d'an uwansa yaje yasanar dasu, saidai ayanayin daya ce suke ciki yanzu kuma shine babban abunda yafi d'aga masa hankali, har aka iso qauyen yarimawa baffa baisan an iso ba saboda tsananin yanda damuwa tayi awan gaba da dukkanin ilahirin natsuwarsa. Kai tsaye asibitin ya nufa yatarar dasu baba balarabe da baffa Usman tsaitsaye cikin halin jimami suna jiran fitowar likita, qarasowa wajensu yai jikinsa duk Babu qwari, cike da jin kunya had'i da damuwa yaba malan balarabe hannu suka gaisa, fuskarsa asake ya amsa masa yana mai tambayarsa halin da Nuraddeen ke ciki tare da jajantawa juna akan abunda yafaru, suna nan tsaitsaye likita yafito ya nufo inda suke, tambayarsa suka shigayi ya jikinsu baba da umma yace su biyoshi office tukuna, Baffa da malan balarabe ne zaune saman kujerun dake kallon likitan shi Kuma baffa usman na tsaye, seda Dr yayi gyaran murya sannan yafara fad'a masu halin da suke ciki, Sanadiyar tashin hankali da baba yashiga a lokaci d'aya ya haifar masa da ciwon hawan jini wanda ahalin yanzu yakamu da mutuwar sashen jiki ma'ana yasamu (stroke), ita kuma umma sun dubata amma sun kasa gano abunda kedamunta ba abunda take kira inba Rashida ba, wanda hakan yasa dole sai munyi mata gwajegwaje a qwaqwalwarta ko anan ne tasamu matsala. Wannan shine cikakken bayanin da likita yayi masu akan binciken da sukayi, gaba d'ayansu sun shiga tashin hankali jin abunda likita yafad'a "innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, ALLAH Kai kasan dalilin jarabta wud'annan bayi naka, ya ALLAH ka samasu hak'uri da juriya kuma kabayyana masu 'yarsu aduk inda take." malan balarabe yafad'a had'e da sakin wata irin ajiyar zuciya. STORY CONTINUES BELOW Baffa da Baffa Usman kuwa jin duniyar sukayi gaba d'aya tayi masu k'uncin da suka rasa sanin ina zasusa kansu. ••• ••• ••• A 'bangaren Nuraddeen kuwa tun safe bai farko ba har sai bayan sallar la'asar, ko daya farfad'o yad'an samu sauqi sosai amma yana tuna zancen b'atan Rashida zazzab'i yataso masa, cikin qarfin hali yamiqe ya sauko daga kan gadon yana yatsina fuska, ganin bakowa wajen yasa yamiqi hanyar fita cikin asibitin don baffa Ali da aka bari ya kula dashi tuni yabar wajen, acan bakin wata bishiya ya hangosa shida wasu yasa andamamasa furarsa hankali kwance yana sha suna fira, bai tsaya bi takansa ba ya wuce gida, tafe take yana harhad'a hanya har ALLAH yasa ya isa gida lafiya, sashensu yanufa ya shiga cikin d'akin, tsaye yayi yana kallon ko ina cike da fatar zaiga Rashidarsa ta iso gare adaidai lokacin, yafi minti biyar ahaka kafin ya duqe wajen yasaki wani irin kuka mai tsima ran duk wanda ke saurare, jin yayi andafo kafad'arsa da sauri yaciro kai yana kallon sama cike da zimmar ganinta amma sai yaga ashe Inna Bilkisu ce, hannu tasa tagoge masa hawayen da suka jiqa masa fuska sannan ta riqosa ya tashi ta azasa saman kujera, cikin sanyin muryar dake nuna tattare take da damuwa tace. "Nuraddeen bazan hanaka kuka ba, domin b'atan Rashida ba kai kad'ai yashafa ba har mu, Amma Nuraddeen Ina so infad'a maka cewa yanzu ba lokacin kuka bane agareka, lokacine da zaka tattaro dukkanin natsuwarka kayi yaqin gano matarka aduk inda take, Ina so kayi amfani da kud'in da kake dasu ahannunka, iliminka da kuma qarfin jikinka kaje kagano matarka aduk inda take, wannan kukan da wani kwanciya duk ba mafita bane agareka, kazuba kud'inka a kafafan yad'a labarai asa maka cigiyarta, kayi amfani da iliminka wajen tsananta addu'a kuma kasa malamai ayi maka, kayi amfani da qarfin jikinka wajen shiga lungu da saqo kadubo matarka, idan ALLAH yayi za'a ganta Ina tabbatar maka da zaka had'u da ita tunda baka zauna ba kaji ko, don ALLAH kadaure duk yanayin da kake jin kanka aciki kanunawa duniya cewa kana son iyalinka ko tana tare da kai ko bata tare dakai, damuwa dolece amma kada kabari tayi tasirin da zata cutarwa da Rashida kai, don na tabbata aduk inda take matuqar tana a hayyacinta kaine mutum nafarko da zatayi fatan kasancewarsa cikin qoshin lafiya da kwanciyar hankali, don haka kayi haquri kuma karb'i qaddararka hannu biyu ta hanyar qarfafa zuciyarka kaji ko?." "Eh Inna Bilkisu nagode." Yafad'a yana goge hawayen da suka jiqa masa fuska, miqewa tayi tafita tana fad'in, "Ina zuwa.?" Binta da kallo yayi aransa yana burin inama ace itace mahaifiyarsa, daya rungumeta yayi kukan sosai yanda zata fahimci yanayin da yakeji koya samu sassauci, yana wannan tinaninne Inna Bilkisu tadawo riqe da kwanon abinci da wani kwanon ruwa da damammiyar fura aciki, saida tad'an riqe fuska tukuna ta ajiye masa kwanon abincin agabansa tace "Maza sauko kaci abinci kaji." "Bazan iyaba Inna Bilkisu, wlh bana tunanin abinci zai iya shiga bakina bacin bansan halinda Rashida ita da abun cikinta ke cikiba." "Ungo wannan to kasha, ai haquri zakayi, idan bakaci ba taya zaka samu qarfi ajikinka har ka iya zuwa nemota. kadaure ko rabine kasha kaji ko." Inna Bilkisu tafad'a had'e da bud'e kwanon ruwan takai abakinsa, awannan karon Babu yanda zaiyi dole yafara tsutsar furar ahankali yana sha tamkar wani jariri, cike da tausayi ta raja'a akallonsa kawai sukaji anbuge kwanon furar yafad'i qasa gaba d'aya tazube, d'ago kai dashi har ita sukayi da sauri don ganin wanda yayi wannan aika aikar, dik da dama gaba d'aya zukatansu sun gama hakaito masu dako wacece, cike da masifa Inna hawwa tafara magana. "Kam buhun uban nan, Bilki me nake shirin gani anan?, So kikeyi shi kuma yaron nawa bayan halin da yake ciki ki hallaka mani shi ta hanyar asirce manishi sai yanda kikayi dashi don mugunta?, To wallahi jinina yafi qarfinki munafukar banza munafukar wofi, hadda wani d'auko abu kina bashi abaki, kai Kuma sakaran banza da bakasan inda duniya tayi ba kasaki baki kana sha." Yaya hawwa taqarasa fad'a tare da jawo hannunsa zatabar falon dashi tana cika tana batsewa, cike da tausayin mugun halin da ALLAH yayi mata yajarab tawar rayuwa dashi Inna Bilkisu ke kallonta kafin tace. "Dakata Yaya hawwa, kiji tsoron ALLAH, kiji tsoron ALLAH kitausayawa yaron nan halin da yake ciki, a matsayinmu na iyaye bamu kad'aine ALLAH ke hukunta 'ya'yanmu akan haqqoqan muba idan suka danne, hatta mu kanmu ubangiji na kamamu da haqqoqansu kuma yayi mana hukunci mai tsauri idan muka taushe masusu, su amana ne agaremu kuma ALLAH zai tambayemu, Nuraddeen d'anane duniya da lahira tunda nake auren qanen mahaifinsa, don haka banga ribar da zan samu ba idan nacutar dashi, dama haka rayuwa take idan kana abu sai kayi tsammanin kowa ma yanayi, kitaka sannu haqqin d'anki kad'ai ya isheki aduniya balle na sauran rayukan da basuji basu gani ba, agidannan Banda darajar mijina da yayansa da kike ci saita haihuwa da kikayi badon haka ba da saina koya maki darasin rayuwa, amma ko yanzu muje zuwa da sannu duniya zata koya maki." STORY CONTINUES BELOW Rab'awa tagefensu tayi tawuce bayan ta d'auko kwanon abincin data kawo masa tare da furar da Yaya hawwa ta b'arara, "Kagani ko shashashan banza da wofi, bakasan mai sonka ba, dubi yanda tayi tsaye ta cimun mutunci agabanka amma ka kasa cewa uffan saboda tariga data gama da kai, dallah wuce mutafi samna sakaran banza, biye yake da ita kamar hoto har suka fito sashen tana rafka uwar masifa da zagezage, daidai bakin qofa taci karo da fadeela Inna taturota tagyara inda furar tazube, hannu tasa ta bangajeta gefe da kad'an tafad'e da sauri Nuraddeen yariqe mata hannu. "Gidan ubanwa zakijene" Yaya hawwa tafad'a tana watsa mata wani mugun kallo, "Inna ce tace nazo nagoge inda fura ta zube.." "To ahalin kicifaffi anyo gadon ashibilanci da iyayi maza kiwuce kibar nan kafin in makeki, shegu d'iyan bani na iya.." Da sauri fadeela tabar wajen tun kafin tarufe baki ita kuma tajawo gambun qofar tarufe har lokacin tana riqe da hannunsa kamar wani qaramin yaro, 'Daki tashiga dashi ta zaunar saman gefen gado ta jawo wani kwano da dambu aciki sannan ta d'ebo ruwa ga kofi ta ajiye agabansa, "Maza kaci kada yunwa ta illataka, yanzu haka duk inda ta tafi tana can hankalinta kwance tabarmu da tashin hankali anan." 'Doga kansa yayi yana kallon mahaifiyar tasa had'e da cewa. "Kamarya duk inda tatafi innar mu, taya Rashida zata bar gidannan da tsohon cikinta haihuwa ko yau ko gobe?." "Eh mana, ai haka na iya yuyuwa idan taji tagaji da zama dakai, to don ta tayar maka da hankali tunda taga kana sonta, ya kamata kiyi tunani anya ba guduwarta tayi ba tunda auren naku na had'ine?." Murmushin da yafi kuka ciwo yayi kafin yace. "Innar mu kenan! Ai aurena da Rashida ba had'in iyaye bane balle tagudu tabarni, ni naganta da kaina nace Ina sonta kuma itama ba tilastata akayi sai ta aureni ba, ita da kanta taji tana sona kuma ta amsa mani, kinga batun guduwa anan ga masoyan da sukaji sun amince da juna ai bata taso ba, Rashida inada tabbaci akan d'auketa akayi amma su waye? Meyasa? Duka ban sani ba, tsorona d'aya aduniya kada ace mahaifiyata nada sa hannu aciki, Ina addu'a kar ALLAH yasa tsanar da kike yimata bata Kai mizanin da Zaki iya salwantar da rayuwarta ba." Hannuwanta yariqo had'e da durqushewa agabanta sannan yaci gaba da cewa, "innar mu duk duniya banida maccen da takai matsayinki araina domin ke kika haifeni, kikayi d'awainiya dani tun Ina cikin cikinki har zuwa girmana amma duk da haka farincikina da kwanciyar hankali na suna tattarene a hannun matata Rashida, don ALLAH idan kinada masaniya akan inda take don ALLAH innar mu kisanar dani kafin nakoma marar amfani adoron duniya." Wani banzan kallo tayi masa kafin a hasale tace. "Tashi fita kabani waje tunda naga kai bakasan abunda kakeyi ba." Tsom ya tashi ya miqe jikinsa ba k'wari ko kad'an ya koma sashensa, bai jima da shiga ba yafito sanye da wasu kaya yamiqi hanyar fita gidan. "Ina zaka?" Yaji muryar Yaya hawwa tana fad'a cike da gadara, batare daya juyo ba yace. "Zantafi nemo farincikina." Bai tsaya sauraron abunda zatace ba yaci gaba da tafiya, daidai bakin qofar fita gidan yaci karo muneera tashigo aguje da alama wani tajawo sauran k'iris ta bangajesa tawuce, jikinta na rawa tatsaya tana fad'in. "Don ALLAH ya nura kayi haquri" kota kanta baibi ba yawuce abunsa batare dama yasan da ita awajen ba, biyo bayansa tayi tana fad'in, "ya nura, ya nura." Ko juyowa beyi ba balle ma yakalleta har tasa ran zai tanka mata, hakan yasa tafashewa da kuka had'e da rugawa cikin gida, da sauri Inna ruqayya tafito tana fad'in. "Ya rasulu manzon ALLAH, muneera keda wa acikin gidannan, fad'amun inji waya tab'aki ne, qara tale baki tayi tana cigaba da rere kukanta wanda nan take yasa hankalin mutanen gida yadawo wajen saboda sanin halin da ake ciki, STORY CONTINUES BELOW "Ke muneera lafiya? Wata tsohuwa data dudduqo daga wancan b'angaren dake cikin gidan tafad'a tana tokare sandarta akusa da ita, "ke fad'amun waya tab'eki ko d'an gidan uban waye inje dashi har iyayen da suka haifesa inci masu mutunci tas, fad'i Ina jinki keda waye?" Cikin kuka tace, "Inna koba ya nura neba inayi masa magana ya qyaleni ko kallona beyi ba yai tafiyarsa." Kallon dan dazon mutanen gidan dake wajen Inna ruqayya tayi had'e da had'a wasu yawu masu kabrin gaske saboda sanin halin 'yar tata, hannunta tariqo tana fad'in. "To zo muje d'aka kiji kinsan yau yana cikin yanayi marar dad'i." "Wlh Babu inda zanje ai bani na b'atar masa da mata ba balle yadinga qyaleni yana fushi dani kuma Inna ai haka kukeso tunda kunce bakwa son ya aureni tana cikin gidan." 'Dago kai gaba d'aya mutanen gidan sukayi had'e da maido kallonsu ga inna ruqayya data fara kalle kallen gefenta, tsohuwar dake kusa garetace tace. "Ke muneera kirufa mana asiri gidannan, wannan sheri da kike neman qaqabawa uwarki har ina?" "Ai wlh basheri bane itama innar tasan gaskiya nafad'a, har magani suka karb'o aka barbad'awa ya nura saboda akarkato zuciyarsa yafara sona muyi aure amma gashinan beyi amfanin komai ba, ni wlh ALLAH bazan yarda ba sai an auramun ya nura." Taqare maganar tana bubbuga qafafuwa tana kuka. Ana haka saidai mutanen dake wajen suna tafa hannuwa suna sallallami sukaga Yaya hawwa da bawanda ya lura da lokacin data fito tayi tsaye wajen tana kallon sakarci irin na muneera tayo wani irin kukan kura ta damqi wuyan Inna ruqayya tana fad'in "Buhun uba, d'an nawa zaku kai ayiwa asiri don kuna munafukai algungumai, to wallahi ALLAH baku isa ba yau nafison garin bebeji ya tarwatse ya watse akan wannan rashin mutunci da kuka tafka mani matsiyata da bakusan abun arziqi ba." Taqare maganar tana kaimata naushi a gefen fuska, kokuwa suka shigayi ita da ita cikin sanyin muryar qasaqasa ta yanda baza'a jiba Inna ruqayya ta dinga bata haquri gudun kada suyiwa kawunansu tonon asiri, Amma saboda yanda Yaya hawwa taji zafin abun aranta ko saurarenta batayi taci gaba da tsigarta tana jifarta da miyagun kalamai, cikin b'acin rai da hasala Inna ruqayya tasa hannu biyu biyu ta tureta tana fad'in. "Ke hawwa bari nafad'a maki shuru shurufa ba tsoro bane, sannan shi abun fad'i kowa yana dashi qulle agindinsa saidai idan bai fito bane, karkiga na qyaleki kinemi maidani sakarai agaban mutane Ina d'an naki ba damuwa da rayuwarsa kikayi ba balle har kinuna mani cewa ke uwar sace, naji munkai nura wajen mlamin tsibbu a karkato da zuciyarsa ga muneera, ai nayine don farincikin 'yata, amma kefa? d'an naki kike zuwa kikai wajen bokaye don farin cikin kanki dana wasu, ko kina tunanin ban san cewa ke kika b'atar da yarinyar nan ba da har zakizo kina yimani cin mutunci agaban mutane, to anyi masa asirin duk abunda kika iya kije kiyi, in shed'anci kike taqama dashi na damaki na shanye Kuma wallahi da sannu zan koya maki hankali, banza ke atunaninki duk wannn walaqancin da kike yimani kinasa ran zan barshine yatafi abanza? Wlh kinsha qarya dama jira nake kigama yaqin ni kuma nakwashe ganimar, kuma tunda kika yimun wannan tozarcin wlh saina tabbatarwa da duniya cewa kece nan kika b'atar da surukarki kika sa ahallaka maki ita don bakya sonta." Inna ruqayya taqare maganar tana shed'a guda guda had'e da gyara d'aurin d'an kwalinta. "Kan hatta kazak kaza..ni zakiyiwa sharri ruqayya don 'yarki ta tona maki asiri, to baki Isa ba wlh..." Nan suka shiga tonawa kansu asiri mutanen dake wajen nata la'antarsu da miyagun halayensu. Inna Bilkisu kuwa fashewa tayi da kuka tashige d'aki tana mai tausayawa halin da Rashida keciki, baffa kuwa da tun d'azu suna bakin qofar shigowa tsakar gidan yanata ko kuwar shigowa ciki saboda abunda kunnuwansa suka jiyo masa lokacin da zasu shigo amma baffa Usman yariqesa yace yabari har sai sun gama fad'in komai da zai zamo masu hujja tukuna, kasa haquri yayi ya fizgikke daga riqon da yayi masa jikinsa narawa idanuwnsa na hawaye yashigo yana nuna yaya hawwa da hannu yace.... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [7/20, 9:15 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž STORY CONTINUES BELOW _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___40πŸ’Ž Kin cuceni hawwa kinci amanar zaman da mukayi dake, haqiqa ba qaramin kuskure natabka ba wajen zab'awa d'ana ke amatsayin uwa, gashi yanzu duk wani farincikin mu dani har shi kin rusa mana shi, naso nacigaba da haqurin zama dake ko don albarkacin d'anmu har lokacin da mutuwa zata rabamu, amma bazan iyaba, ko kad'an bazan iyaci gaba da zama da mushirikar mace da bata tsoron ALLAH ba kamarki, macen da batada imani da tausayi, son kanta yasa ta cilla mutane da yawa cikin wani hali, ALLAH yasani nayi iya qoqarin zaman da zan iya dake amma yanzu kitafi na sakeki, na sakeki hawwa saki biyu, keji duk abunda kika yimun nayafe maki duniya da lahira albarkacin yaronmu, Amma Ina so kisani bazan tab'a d'aga maki k'afa akan sauran haqqoqan bayinsa da kika zalunta ba, wlh ni da kaina zan tsaya na bimusu shi koda duka abunda ALLAH ya mallakamun aduniya zai qare musamman haqqin wannan qanqanuwar yarinyar da kika d'auka, yarinyar da zuciyarta bata san komai ba sai tarin qauna da soyayya agaremu, tayi mana halacci mai d'inbin yawa kama daga soyayyar da take yiwa d'anmu har zuwa kulawar data bani agidannan nasamu lafiya da haqurin cin kashin da kika tayi mata amma kikasa qafa kika shure duk wud'annan abubuwan keda marasa imanin da kuka had'a baki kuka cutar mana da ita, in sha ALLAH, ALLAH bazai barki ba har sai ya hukuntaki tun aduniya kafin kije lahira." Yana gama maganar yajuya yafice daga gidan ko gani bayayi saboda tsananin b'acin rai, tafiya mai nisa yayi baffa Usman na biye dashi kafin yasamu waje ya zauna, kuka ya shiga rerawa tamkar qaramin yaro cike da nadamar sanin Yaya hawwa da yayi aduniya, gaba d'aya ji yakeyi yatsani duk wani abu daya dangance ta balle ita kanta, Saida yayi kukansa mai isarsa sannan yamiqe suka nufi asibiti, akan hanyarsu suka gamu da baffa Ali sai faman sabbatu yakeyi wai Nuraddeen ya maisheshi d'an iska ya gudu daga asibiti yabarshi, gashi yasa agaban mutane likita yayi mashi wala qanci, har ya d'an gotasu zai wuce baffa Usman yajuyo don da alama duk kansu basuga juna ba sai yanzu. "Ali Ina kanufa kuma haka?, Ko har Nuraddeen d'in yatashi an baku sallama ne.?" "Af Yaya kun dawo? Injin an dace anga yarinyar?, " "Kai ka amsamun tambayar da nayi maka, yarinya kam idan da rabon agata ko anqi ko anso ai ganinta za'ayi da yardar ALLAH." Baffa Usman yabashi amsa yana kafesa da idanuwa, "Aw Nuraddeen kake magana?, ai kabarni da shashashan yaro, wai daga infita inyo sallah yaronnan ya gudu daga asibiti, sai dawowa nayi natarar da likaita na tambayarsa yarufeni da fad'a agaban mutane baka ganiba abunnan zak kunya." Shiru baffa Usman yayi cike da mamaki yana kallonsa kafin yaji muryar baffa yace "Ba komai Aliyu, Nuraddeen ai d'an kane duk abunda kayi masa ko kabari ya samesa kanka kayiwa, shidai zumunci yananan rataye aqasan al'arshi duk wanda ya gyara yaga da kyau wanda kuma ya munana yaga akasin haka, ni dai addu'a ta d'aya shine ubangijin dake tare da waccan yarinyar shima yakare mani shi aduk inda ya tafi, kuma Allah ya qaddara had'uwarsa da ita cikin amincinsa da yardarsa." Yana gama fad'ar haka yanufi hanyar gidan daya d'aukarwa su Nuraddeen haya yana fad'in. "Usman zo mutafi." Bayansa baffa Usman yabi shi kuma baffa Ali yawuce gida yana maijin d'acin maganganun da baffa yafad'a masa, "wato duk abunda nayi masa baiga qoqarina ba, amaimakon yaga laifin d'ansa laifina yake gani, ai shikenan gobema ranace" haka baffa Ali yaba hanya yana fad'a cike dajin haushin d'an uwan nasa har ya isa gida Cikin sa'a sukayi nasarar ficewa daga anguwar ba tare da kowa ya gansu ba, daga su sai jikukunansu guda biyu na kaya da kuma 'yar jikka ta ratayawa irin ta maza dake sagale a kafad'ar baba suka nufi tasha, sunjima zaune abakin wani shago kafin baba yatashi yaje ya d'ibi ruwa a randar dake ajiye bakin qofar masallacin dake cikin tashar yayi arwala, Saida ya d'ibi wasu a buta yaje ya kaiwa umma itama tayi arwalar had'e da ciro sallayar da sukazo da ita cikin kayansu ta shimfid'a sannan yabar wajen da sauri jin antayar da sallar yana fad'in, "Kibi jam'i maman Rashida Ina fitowa zamu shiga motar duk da muka samu tagama lodi." Ana gama sallar addu'a kad'ai yayi yafito da sauri da sauri tare da tallabar jikukunan nasu dake gabanta yana fad'in. "Hanzarta maman Rashida naji motoci sun fara tashi." Tofi tayi acikin hannayenta dake sama bayan tagama yimasu addu'ar ALLAH yazab'a masu wajen zuwa mafi alkhairi arayuwarsu had'e da shafawa sannan tamiqe tanad'e sallayar tabi bayansa, suna isa motar Niger na d'agawa wacce ita yaso su samu don d'azu yana arwala yaji drivern motar nafad'in passinger biyu ya rage masa tacika, sai gashi kafin ya d'oko kayan nasu su iso wajen har ansamu ciko, shiru yayi had'e da ajiye jikkunan yana kallon umma da sai yanzu ta ida qarasowa wajen, STORY CONTINUES BELOW "Ai har motar tacika, kingata can yanzu tawuce" yafad'a cike da damuwa don baya son abunda zaizo ya dakatar dasu daga tafiyar wanda hakanne yasa ma ya kasa sanar da d'an uwan nasa. Murmushi tayi tare da cewa, "ka kwantar da hankalinka, inda tanufa qilan zuwanmu can d'in ba alkhairi bane." "Hakane kuma." Yabata amsa tare da nufar rumfunan da motocin kowace jaha ke tsayawa lodi, duk motar daya duba bai wuce yaga mutum biyu ko ukku aciki har yawuce kusan motocin jahar, gombe, sokoto, katsina, adamawa da kuma bauchi babu inda yaga mota takusa cika balle tashi, har yajuya zai bar wajen yaji ana fad'in. "Borno mutum uku, mutum uku borno." Da sauri ya juyo yanufi inda motar had'e da cewa driver borno zaije. "To kashiga, saura mutum biyu." Karan motar yafad'a yana sake d'aga murya yana fad'in "mutum biyu borno." A sauri baba yasake matsawa kusa dashi yace "ai mu biyune nida matata." Yana rufe baki saiga cikon mutum d'aya an samu, da d'an gudu gudunsa yaje yakira umma tare da d'oko masu jiku_ kunansu, miqa hannu umma tayi takarb'i d'ayar ganin sunyi masa yawa saboda yanayin yanda yake tafiya tunda ba lafiya yacika ba yayi saurin wucewa yana fad'in. "A'a kedai d'aga qafarki muje." Suna zuwa akasa kayansu bayan mota suka shiga drivern ya tayar da motar suka bar tasha, suna hawa titi had'e da kama hanyar tafiya baba yarufe idanuwansa had'e da sakin wata irin ajiyar zuciya, kallonsa umma tayi itama tana ajiyar zuciyar tare da aza kanta saman kafad'arsa tana karanto addu'ar tafiya yayinda mutum ya hau abun hawa, wacce tafito daga bakin mafificin halitta kuma ya tabbatar mana da cewa duk wanda yayita alokacin daya hau abun hawansa zaiyi wata tafiya to ALLAH zaikaresa da ga sharrin duk wani abunqi dake cikin tafiyar da sharrin qarfe ko kuma had'ari, zai sanya tarin alkhairai masu d'imbin yawa acikin tafiyar tasa da yardar ALLAH. _"ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBAR, ALLAHU AKBARU subhanallazi sahhara lana haza wama kunna lahu muqrinin, wa inna illa rabbina lamunqalibuun, allahummah Inna nas'aluka fi safrina hazal birri wattaqwa, waminal amali ma tarda, allahummah hawwan ala safarana haza wad'wi Anna bu'udahu, allahummah antasswahibu fis safri, walkhalifatu fil ahli, allahummah inni a uzu bika min wa'thaa'issafri, wa kaabatil manzwari, wasuu'il munqalabi fil mali wal ahli."_ Domin samun fassarar wannan addu'ar zaku iya duba littafin hisnil muslim, addu'a ta tis'in da shida (96) don nemawa kai kariyar ALLAH daga sharrace sharracen miyagun mutanen dake kan hanya da kuma munanan had'urran da sukayi yawa alokutan tafiye tafiyenmu, Tana addu'ar hawaye nazubo mata a fuska, hannu baba yasa yagoge mata had'e da cewa. "Kinsan inda muka nufa yanzu?" Girgiza masa kai kawai ta iyayi tana mai tunanin yanda duniya tajuye masu daga farinciki Mai yawa na bayan shekaru zuwa baqincikin da basusan iya adadin lokacin da zasu d'auka dashi kafin yabarsu, "Jahar borno muka nufa kuma Alhamdulillah akwai wani babban mutum dana sani acan abokin alhajin da nake saro takalma a shagonsane ana cemasa alhaji shu'aibu maiglass, muna yawan had'uwa dashi idan yaje wajensa ni kuma naje kaimasa kud'insa in amso takalmi, yanda alhajin kejin dad'in mu'amalar kasuwanci dani yasa wata rana ya had'ani dashi muka gaisa har yake fad'amun ai aminin sane yana zowa daga borno me shima yayi sayayar kayan glass nayin qofofin zamani, to tun daga lokacin duk yazo in muka had'u sai yayi mani alkhairi don babban mutumne sosai, kinga idan munje sai munemi gidansa kafin musamu inda zamu zauna. "Shikenan duk da dai mutum bashida tabbas amma tunda ba muda wata mafitar ALLAH yasa hakan shiyafi zama alkhairi kuma yakaimu lafiya." "Amin, ki kwantar da hankalinki in Sha ALLAH babu wata matsala." STORY CONTINUES BELOW "ALLAH yasa." Tafad'a tana share qwalla a idanuwanta. ••• ••• ••• Baffa Ali kam yayi sanyi sosai akan abunda yafaru, yayi dana sani mai yawa akan biyewa harkar mata da yayi wacce ta jefasa cikin halin qaqa nikayi, yayi nadamar shiga al'amurran Yaya hawwa Amma duk da haka yana jin tsanar baffa mai tsanani azuciyarsa bisa abunda yasa akayi masa shida iyalinsa a matsayinsa na d'an uwansa, hakan yasa tunda suka dawo yafita harkar kowa yana rayuwarsa shi kad'ai, baruwansa da kafatanin mutanen gidan acewarsa suma munafukaine tunda aka kasa samun wanda zaiyi belinsa acikinsu, had'uwa dubu kuwa idan zasuyi da baffa bazai d'aga Kai ya kallesa ba balle yasa ran zai gaishesa, dama dama baffa Usman yakan d'an saki jiki dashi sugaisa yawuce shima d'in ba sosai ba, Kuma hakan ko kad'an bai dami baffa ba saima addu'ar neman shiriya daga ALLAH. Muneera kuwa tuni ta manta da babin ya nura rayuwarta takeyi kamar ba itace muneerar dake faman kukan son ya nura dare da rana ba, Amma tasha alwashin bazata tab'a sure ba inba saurayin birni d'an kwalisa ba irin ya nura, shiyasa takeci gaba da yiwa maqwabcinsu da yace yana sonta walaqanci kuma Inna ruqayya tagoyi bayan haka, saidai duk da haka yanzu basuda bakin fitowa tsakar gida suyi tijara kamar yanda suka saba gudun kada a mayar masu da jawabin abunda baffa yasa akayi masu wanda ita kanta tana kallon baffa amatsayin azzalumi wanda yaci amanar d'an uwansa, dama mai hali baya fasa halinsa. ••• ••• ••• Dr. Nura kuwa tunda safe yaso yin tafiyarsa zuwa kano amma yanda yaga Fatima takwana da tana fama da ciwon kai wanda dama lokaci zuwa lokaci yana taso mata yasa yafasa tafiyar, gashi sai kiransa akeyi wajen aikinsa akan wani emergency daya taso na gaggawa, Babu yanda batayi dashi ba akan yatafi kodon issue d'in Rashida amma ya kafe akan matuqar ba sauqi yaga ta samu ba babu inda zaije, hakan yasa tayi qarfin halin tashi taje tayo wanka tare da kiran mai aikinsu tace takawo mata abinci taci, bayan taci ya d'ebo mata magani tasha, a maimakon takoma ta kwanta sai tawuce part d'inta, zaune ta isko Rashida a palour rungume da little Nuraddeen tagama dama mashi madarar (NAN) da ake had'a masa da ita zata bashi. "ALLAH sarki aunty yanzu nake cewa idan nagama bawa yaronki madara zanje naduboki da jiki, injin da sauqi ko?" Rashida tafad'a tana qoqarin d'aurama little Nuraddeen dake qoqarin kamo fidan madarar abun tare abinci idan ya zuba awuyansa, murmushi Fatima tayi had'e da miqa hannu takarb'esa tana yimasa wasa sannan ta zauna takarb'i fidan tana bashi madarar, har kusan qarfe sha d'aya da rabi Nuraddeen yaji tsit har lokacin Fatima bata dawo ba, part d'inta yanufa ya iskota kwance little Nuraddeen nasaman cikinta yana bacci ita kuma da Rashida na zaune suna kallon wani wa'azi a tsahar sunnah tv, a daidai bakin qofa ya tsaya yayi gyaran murya yana kallonta kafin yace. "Iyyeeeee lalle kinsamu sauqi madam, shine kika barni acan Ina jiran tsammanin dawowarki ashe kuna nan keda maman baby kuna kallonku, ikon ALLAH, to wannan wace irin jinyace nakeyi, ga marar lafiya anan ni kuma mai jinyar anbarni acan." Ahankali ta tashi zaune don kada little Nuraddeen yafarka tana kallonsa had'e dayin murmushi tace. "To ai laifinka ne, nafad'a maka nasamu sauqi amma baka yarda ba ai yanzu ka ganewa idanuwanka ko?" "Eh to! Yanzu kam ai nayarda." Kallon Rashida da kanta ke qasa a sunkuye yayi had'e da cewa. "Mman baby Ina kwana antashi lafiya, tunda yau tunanin takwarana abban takwara bazai bari agaisheni ba."yaqare maganarcike da tsokana. "Laa..uncle jirafa nakeyi kugama magana sai nagaisheka, Ina kwana ya jikin aunty." Rashida tafad'a had'e da d'ago kai tana dariya. "Lafiya klw, auntynki kam aike zan tambaya tunda kinsa ta wartsake." Murmushi kawai tayi tare da maida kanta qasa ba tare da tace komaiba yace. "Madam tunda naga kin samu sauqi kuma akwai sauran lokaci bari kawai nawuce ko kuwa?" "Gaskiya kam." Fatima tafad'a tare da tasowa tabi bayansa sab'e da little a kafad'arta, "ALLAH ya kiyaye uncle." Rashida tafad'a tana kallonsu cike da burgewa, itadai a kullum rayuwar ma'auratan na burgeta don akwai fahimta sosai a tsakaninsu, hakan na yawan sa tanajin sha'awar kamanta irinta da habibynta amma da zaran ta tuna da mahaifiyarsa sai tayi saurin kauda wannan tunanin aranta. Akan gado ta ajiye little ta taimaka masaya shirya tsaf ta sake d'ebo masa breakfast ta tsaresa ya sakeci sannan tace. "To ranka shidad'e ALLAH ya kiyaye kuma yasa Kati tafiyar sa'a, kaje lafiya kuma kadawo lafiya tare da kyakkyawan albishir d'in had'uwa da iyayen maman baby, duk da inajin damuwa idan natuna zan rabu da kyakkyawan qaramin maigidannan nawa" taqare maganar tana kallon little Nuraddeen dake baccinsa hankali kwance, jawota yayi ajikinsa had'e da cewa. "Ki kwantar da hankalinki insha ALLAH muma namu natafe ga ALLAH kinji ko matar?" "Ina fatar ganin wannan ranar akoda yaushe." Sumbatar goshinta yayi sannan tasake sab'a Little Nuraddeen a kafad'a ta rakasa har bakin gate hannuwansu na sarqe da juna, dama tuni yakira qanensa ya fitar da motar waje yana jiransa, shi zai kaishi tasha ya hau mota sai yadawo mata da motar gida don dama yadena zuwa da ita tun lokacin da little na asibiti saboda tunanin ko wata matsalar zata taso da za'a buqaci motar, Saida taga tashinsu sannan ta d'aga masa hannu had'e da komawa gida, Suna isowa junction d'in da zasu juya su shiga tasha motar su umma na sauka, lokacin qarfe sha biyu saura minti biyar na rana, har zai shiga junction d'in dr.nura yace ya tsaya ya karb'o masa swan water gora biyu awani shago dake wajen, parking qanen nasa yayi agefe tare da rage glass d'in motar, adaidai lokacin su kuma su baba suka fito daga cikin tashar suna qoqarin tsallakowa titi zuwa d'ayan hannun da motar su Dr nura tayi parking.... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­[8/12, 10:06 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___51πŸ’Ž A qoqarin su na tsallakowa zuwa d'aya b'angaren baba na tallabe da jakunkunan su umma tamiqa hannu zata karb'i d'ayar dake sagale a kafad'arsa ganin yanda yake tafiya daqyar saboda yawan da suka yimasa tana fad'in. "Malan kenan! ALLAH kafiye qarfin hali da yawa, miqo wannan jakar ko itace in riqa maka tunda sunyi maka yawa." Maganar takeyi tare da qoqarin karb'ar jikkar ahannunsa har lokacin suna a tsakiyar titi kai kace cikin gida suke hankali kwance, wata motace tashigo ta junction d'in aguje tana yimasu oda amma saboda hankalin su gaba d'aya baya akan titin ba suma kula da zuwan nata ba balle suji odar da akeyi masu. abunka da mutumen qauye ba ruwansu da tunanin ai nan birnine akwai banbancin dake tsakanin titunansu dana qauye.+ Ganin motar na tunkarosu ka'in da na'in inda yasa dr.nura dake kallonsu tun d'azu ta cikin glass d'in motar yayi saurin fitowa tare da rugawa ya jayikkesu da qarfi, cikin tashin hankali duk suka saki jakunkunan nasu tsakiyar titi gabansu na matsanancin fad'uwa, yana jayesu motar na wucewa aguje kamar iska wacce kad'an ya rage ta buge Nuraddeen garin taimakonsu. Kallo d'aya zakayi masu kafahimci tsantsar tsoron daya ziyarto zukatansu alokaci d'aya, binsu yayi da kallo cike da takaici kafin yakoma yakwaso jakunkunan nasu dake tsakiyar titi. "Haba baba!, shifa titi da kuke gani ba gidajenmu bane da zamuyi yanda muke so akai ba, wajene da ke cike da barazanar d'aukar duk wata rayuwar da tayi kuskuren gittawa akai ba daidai ba sanadiyar ababen hawan dake kai da komo akansa, yanzu da wani abun ya sameku wani hali kuke tunanin zaku jefa halinku aciki, don ALLAH baba kudinga duba tituna dakyau idan zaku tsallaka saboda akwai banbanci tsakaninsu da naku na karkara." Ya qarasa fad'a ransa a d'an b'ace yana miqa masu jakunkunansu. "Kayi haquri yaro, injin bakaji ciwo ba." Umma tafad'a tana goge 'yan guntayen hawayen da suka zubo mata. "A'a baaba, Amma dai adinga kula saboda gujewa qananan had'urra da manyansu." "Mungode bawan ALLAH daka taimakemu, badon haka ba da mun afkama abunda mukayi qoqarin gujewa, mungode sosai da wannan taimakon da kayi mana, ALLAH ya saka da alkhairi yayi maka albarka." Baba yafad'a yana kallon Dr nura daya shiga duniyar tunanin muryar umma da yaji, tabbas yatab'a jin mai irin muryar nan tata amma a Ina ne? shine ya kasa tunawa. Daidai lokacin qanensa ya qaraso wajen riqe da gorar ruwan guda biyu a hannunsa daya siyo masa, "Yaya lafiya?." Ya tambayesa yana kallonsu umma had'e da yatsine fuska, halinshi kenan aduk lokacin da zai had'u da talaka saboda yanda yaqi jininsu, shiyasa basa wani shiri da yayan nasa da matarsa ko kad'an, don tsakaninsu da talaka d'an jimmane da d'an jummai injisa. "Ba komai, muje." Dr.nura yabashi amsa had'e da wucewa yana kallonsu, bayanshi yabi ummat nayita sa masa albarka suka nufi tasha ya ajiyesa sannan yajuya ya maida motar tare daba Mai gadi makullin motar yaba Fatima sannan yawuce gida. STORY CONTINUES BELOW ••• ••• ••• Ana gama sallar asuba bayan rana tafito bab balarabe ya gyara tare da fitowa yanufi kitchen inda uwargidansa ke ciki tana had'a abun karyawa. "Subhanallahi, hajia har yanzu baki gama had'a abun karinnan ba?, Kinfa sani babu kowa atare dasu kuma akwai magungunan daya kamata susha da safennan bayan sunci abinci, tun jiya saida nafad'a maki haka amma ace har qarfe takwas na nema tayi baki gama had'awa ba, kinsani badon wannan ba da tuni ni nabar gidannan natafi nadubo ya d'an uwana ya yatashi da jiki." Yafad'a ransa a d'an b'ace yana qoqarin rufe mab'allan gaban rigarsa, juyowa tayi had'e da gaishesa sannan tace. "Kayi haquri, na samune yarannan sun jiqamun gawayin da zanyi amfani dashi seda nakoma had'a itacen murhu, amma kad'an yarage na kammala sai naba Hassan shida Hussain subiyo bayanka dashi." "Mtssss.." tsaki yaja had'e da ficewa yabar gidan yana fad'in. "ALLAH ya kyauta." Ya matuqar shan mamaki lokacin daya isa qofar gidan yaganta kulle da kwad'd'o, maqwabtansu ya aika akayo masa sallama da maigidan ya tambayesa su yace shima baisan inda suka jeba, yafi qarfin Rabin awa abakin qofar gidan yana tambayar mutanen dake anguwar tasu amma wanda duk ya tambaya amsar d'aya ce shine basu sani ba, kan kace me qofar gidan tacika da mutanen anguwar ana ta'ajibin ina su baba suka shiga, shi kuwa baba balarabe banda aikin Kiran wayar baba da umma babu abunda yakeyi, cike da tashin hankali yake kiran lambarsa idan ya jita akashe sai ya kashe yasake kiran ta umma amma duka Babu wacce yayi nasarar samu, waje yanema ya zauna yaci gaba da sake gwada kiran nasu cike dasa ran cewa awannan karon zata shiga, Dafe kansa yayi da duka hannayensa tare da fad'in. "hazbunallahu wani'imal wakel." Duk mutanen dake wajen sun matuqar tausaya masa ganin yanda hankalinsa ya tashi alokaci d'aya kowanensu nafad'in albarkacin bakinsa akan tafiyar baba batare daya sanar da d'an uwansa ba, duk dako mafi yawancinsu sun san dalilin da yasa suka aikata hakan. Baki suka dinga bashi kafin sufara watsewa d'aya bayan d'aya ya rage daga shi sai su Hassan da hussaini da basu jima da isowa wajen ba d'auke da kwandon abun karin da aka had'o masu da flaks d'in ruwan zafin tea. Sai Kuma maqwabcinsu dake gefe zaune shima yana gwada kiran wayar baba. Auntynsu gaba d'aya Yaya maryam baba balarabe yakira ya sanar da ita abunda ke faruwa nan take ita da mai gidanta suka iso wajen cikin tashin hankali suma, nan ya shaida mata abunda yafaru jiya da iyayen Rashida sukazo wanda yake tsammanin shine dalilin da yasa suka yanke shawarar barin garin saboda baqinciki da quncin da suke ciki. Fashewa tayi da kuka tana fad'in "Amma wannan mata ta cucemu ta rabamu da 'yarmu da kuma d'an uwanmu, ubangiji ALLAH ka isar mana, ALLAH ka isarwa Rashida da iyayenta." Kasa cewa komai baba balarabe yayi sai jinjina kai da yakeyi, haka Yaya maryam taci gaba da kukanta tana yiwa Yaya hawwa ALLAH ya isa bisa rusa masu farinciki da tayi, wata irin ajiyar zuciya maigidanta ya sauke kafin yace. "A gaskiya wannan baiwar ALLAH tacutar da mutane da yawa kuma in Sha ALLAH haqqoqansu bazasu barta ba, yanzu Kai balarabe duk ka tambaya nan maqotansa basuda wani labari akan inda sukaje ko wani saqo da suka bari kafin sutafi.?" "Na tambayesu Yaya sunce basu san komai ba akan tafiyar tasu, ni ina tunanin tun cikin dare sukabar garinnan." baba balarabe yafad'a yana murza goshinsa saboda ciwon kan da yaji yana nema yarufesa, Kallon Yaya maryam yayi dake shartar majina tana dannar wayarta da alama itama gwada kiransu takeyi yace. "Yaya maryam kidena wahalda kanki bazaki samesu ba, nakira yafi a qirga amma ban samesu ba." To yakamata asa ab'alle gidan ko za'a samu wani saqo da suka bari don natabbata bazasu tafi haka ba har sai sunbar wani saqon," maigidan Yaya maryam ne yafad'i haka tare da zuba hannayensa a aljihu. STORY CONTINUES BELOW Maqwabcin su sake gefe zaune baba balarabe yayiwa magana da ataimaka masu da wani abun da zasu iya b'alle kwad'on dashi, cikin gidansa yashiga yake ya d'auko zarton ya kawo masu, kallon babban d'ansa da zai wuce da alama gona yayi had'e da cewa. "Qasimu zoka taimaka kayanke masu kwad'onnan." Baba balarabe yafara shiga bayan anyanke kwad'on sannan Yaya maryam Mai gidanta na biye dasu abaya, tsafa suka isko gidan babu alamar an hargitsa komai aciki kafin sutafi, Yaya Maryam tashiga dudduba ko ina cikin d'akin ta hargitsesa amma basuga komai ba, sallamar aunty marwiyya data shigo tana reren kuka tasata fitowa tsakar gidan dasu baba balarabe ke tsaitsaye, kuka takeyi had'e da lailayo miyagun addu'o'i kala kala tana yiwa Yaya hawwa, rarrashinta suka shigayi da bata magana kafin su yanke shawarar fara nemansu a tashoshin motar dake cikin qauyen nasu da zagaye. Wani yarone yayi sallama had'e da cewa. "Wai mai mashin yace yana jiran matar da yakawo takawo mashi kud'insa" sai alokacin aunty marwiyya ta tuna da aibata sallami mai mashin d'in ba, kawai yana ajiyeta ta tahowarta, nera d'ari baba balarabe yaciro ya miqawa yaron tace a'a yabari taje dakanata, a tsakiyar zauren gidan jikkarta takucce tafad'i wajen saurin taje ta sallamesa tare da bashi haquri, tana duqowa ta d'auki jikkar idanunta sukayi tozali da takardar da baba yarubuta duk an tattaketa. _KUYI HAQURI ZAN NEMEKU ADUK LOKACIN DA NAGA DACEWAR HAKAN, DAGA 'DAN UWANKU BASHAR"_ Shine abunda ta gani a qasan takardar da har tayi nufin wucewa tabarta, da sauri ta d'auka tana kakkab'e qasar dake jiki ta koma cikin gidan bayan taba yaron kud'in yakai masa tace yabashi haquri, "Balarabe, balarabe." Tadinga kiransa tun kafin takai cikin tsakar gidan tana gyara mayafinta da jikkarta dake nema su sub'uce mata. Kad'an yarage suyikaro dashi a daidai bakin qofar shigowa tsakar gidan da sauri yaja baya yana fad'in. "lafiya marwiyya ko sun dawo ne?" Takardar ta miqa masa hannunta narawa ya karb'a yana binta da kallon mamaki kafin ya maida kallon nasa ga takardar, saida ya karanceta tsaf sannan ya d'ago kansa yana kallon aunty marwiyya, "Waya baki?" Ya tambayeta don ya tabbatar da rubutun dake ciki nad'an uwan nasa ne. "A tsakiyar zauren nasameta ajiye a qoqarin d'auko jikkana data fad'i wajen saurin in sallami mai mashin." Juyawa yayi yana kallon Yaya maryam dake tsaye ita da maigidanta suna jiran jin ba'asi tare da takawa ya isa wajensu, cikin raunin muryar dake tabbatar da irin sanyin da jikinsa yayi yace dasu. "Wannan itace abinda mukayi tsammanin Yaya bashar zai barmuna muketa nema kuma Alhamdulillah gata mun samu." Da sauri Yaya hawwa takarb'i takardar don gaba d'ayansu sunyi boko saidai baiyi wani zurfi ba daga bakin sakandirene suke ajiyesa, wannan dalilinne yasa abaya baba ya kafe akan sai Rashida tayi karatu sosai saboda alwashin daya d'auka akan cewa zurfin karatun da bai samu yayi ba zaisa 'ya'yansa suyisa kosu nawane. Karanta takardar Yaya maryam tafarayi da qarfi kamar haka. _Assalamu alaikum 'yan uwana, fatan alkhairi mai yawa da kasancewa cikin amincin Allah arayuwarku har zuwa lokacin da ubangiji zai sake had'a fuskokinmu daku, haqiqa samun 'yan uwa kamarku abune daya isa mutum yayi alfahari dashi har iya qarshen rayuwarsa, Ina Mai godiya agareku bisa kulawa da d'awainiyar da kukayi nida iyalina, mungode ALLAH yabaku aljannah da rahamarsa, nasan alokacin da kike karanta wannan takardar kuna cikin halin tashin hankali da damuwa saboda rashin sanin inda muke, Ina roqonku daku kwantar da hankalinku, muntafine bisa Imanin cewa hakan da mukayi shine mafi alkhairi agaremu, shine hukuncin da zai sama mana sauqi da rad'ad'in abunda mukeji aranmu, don haka muna roqon addu'arku akoda yaushe, nagode 'yan uwana Ina alfahari daku, musamman balarabe daya zamemani ginshiqi arayuwa,_ _KUYI HAQURI ZAN NEMEKU ADUK LOKACIN DA NAGA DACEWAR HAKAN, DAGA 'DAN UWANKU BASHAR_ STORY CONTINUES BELOW Kusan atare sukayi ajiyar zuciya gaba d'ayansu kafin Yaya tace. "Assha bashar, meyasa zakayi haka?, Meyasa zaka jefa kanka da iyalinka uwa duniya don gushewar farincikinka? duka wannan damuwar tasu akan Rashida ce, to gashi sun gudu sunbar garin, idan ALLAH yakuma nufi farincikin nasu dawowa agaresu shikenan sun sake nisanta kansu dashi?." "Lalle kam Yaya sun ragon azanci duk da dai bamusan ya suke jiba, amma muyi masu addu'a kamar yanda ya buqata, ALLAH yasa rabon had'uwarsu da 'yarsu ne ya fishshesu." Baba balarabe yafad'a yana sake sakin ajiyar zuciya akaro na ba adadi. Sosai ganin takardar yad'an sa sun samu natsuwa, sun jima agidan suna jajanta abun kafin sufito baba balarabe yabayar asawo masa wani kwad'on ya kulle gidan dashi, bayan ya kulle ya miqama yaya maryam makullan tace yabarsu hannunsa kafin suyi tunani akan abunda ya dace suyi tunda baza abar gidan haka ba. Sai da mijinta ya goyata ga mashin d'insa suka wuce sannan yaraka aunty marwiyya bakin titi itama tahau mashin, suna wucewa shima shima yawuce yana maijin duniyar tayi masa wani iri daban. ••• ••• ••• Duk wani bayani daya kamata boka yayima su inspector najida yayi masu shi ba tare daya basu wata wahala ba, anan ya tabbatar masu da cewa shima baisan inda baqin aljanin daya turawa Rashida ya kaitaba, ataqaice ma shi aljanin baiyi nasarar shiga jikinta ba kuma ma yanzu baya tare dashi saboda anqoqqonasa ya bijire masa, shi kansa yanzu tsoronsa yakeji saboda yanda yake cutar dashi tare da azabtar dashi, koda inspector najida takira baffa yazo Police station d'in tayi masa bayani, ya matuqar jin dad'in cewa aikin shed'anunbaiyi tasiri akan Rashida ba, dama shi yanada matuqar yaqini akan hakan saboda riqon ibadarta, abunda kawai baiji dad'in jiba shine rashin sanin inda suka kaita lokacin da sukaci nasarar d'auketa, addu'a yayi had'e da roqon ALLAH ya gaggauta bayyanata. Nan yasaka hannu akan ayi releasing case d'in akayi komai aka gama, har ya juya zai tafi inspector najida tace. "Baba ya batun Inna hawwa.?" "Ku saketa kawai." Yabata amsa atak'aice tare da juyawa yabar station d'in. Har ya tare abun hawa zai hau sai kuma ya juyo ya dawo wajen inspector najida, koda ya shigo office d'in kanta na duqe tana ida cike sauran information d'in daya kamata kafin ya ajiye file d'in inda ya kamata. A hankali ta d'ago kai ta kalli baffa tace. "Baba ya akayi?" "Akan maganar hawwa ne, Ina so ku ajiyeta kafin nasamo asibitin da za'a kula da ita, koba komai ta haifamun d'a wanda nake alfaharin samunsa aduniya." Rufe file d'in dake gabanta tayi ta ajiye biron data gama rubutu sannan ta d'ora hab'ar bakinta akan hannuwanta data had'e waje d'aya tana kallonsa, murmushi tayi sannan tace. "Baba kanada zuciya mai kyau, haqiqa da maza zasu kasance masu duba alkhairin matansu komai qanqantarsa arayuwa koda sun rabu dasu, to ina da tabbaci akan mata bazasu wahala aduniya ba sosai, haqiqa kayi qoqari ubangiji ALLAH yasaka maka da alkhairi." Murmushi baffa yayi had'e da cewa. "Amin 'yata nagode ALLAH yayi maki albarka ya d'aukaki acikin al-amurranki," "Amin" ta amsa masa had'e dajin dad'in addu'arsa.... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [8/16, 11:24 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž STORY CONTINUES BELOW *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___52πŸ’Ž Baffa nashiga gida ya tadda Nuraddeen yafito daga wanka yana shiryawa, cike da girmamawa ya tarbesa tare da karb'ar ledar daya shigo da ita ga hannu yana fad'in. "Sannu da zuwa baffa." "Yawwa Nuraddeen, barka da rana wanka akayi?." "Eh baffa, Ina son inje dubo innar mu ne." Batare daya tanka saba yawuce bakin katifar dake cikin d'akin ya zauna. "Nuraddeen zubikke abinda ke cikin ledar nan awani kwano kazo muci yunwa nakeji" Acan gefen d'an madaidaicin durom d'in dake cikin d'akin Nuraddeen ya d'auko wani kwano cikin kwandon da suke kife kwanonin abincin da suke amfani dasu yazo ya d'auki ledar ya zube soyayyar doya da k'wai d'in dake cikin ledar daya zo da ita yana fad'in. "Ya akayi haka baffa?, Ga abinci nan Inna Bilkisu ta aiko yusuf ya kawo tund'azu." "Ai nasani Nuraddeen, wannan ina fitowa daga police station ne nagata ana siyarwa saita burgeni nace bari nasiyo mana." "To baffanmu, ALLAH yasaka maka da alkhairi." Nuraddeen ya qarasa maganar had'e da ajiye kwanon agabansa, saida yafidda ledar ya saka cikin shara tukuna sannan ya dawo ya d'ebo masa ruwa cikin durom d'in yazo ya ajiye agabansa, har zai juya baffa yace. "Zo zauna muci mana, ko kaci wancan d'in ne." Azahiri baiya jin cin abincin amma ganin yanda mahaifin nasa ya tsaresa da idanuwa yasa yaje ya wanko hannuwansa yasa hannunsa suka soma ci, tunda suka fara babu wanda ya koma cewa uffan har suka kusa gamawa, cire hannu baffa yayi ya d'auki ruwan yasha ya yiwa ALLAH godiya sannan yace. "Nuraddeen ya zancen tafiyarka? Naga lokaci sai sake gabatowa yakeyi" Da qyar Nuraddeen ya iya had'iye abincin dake cikin bakinsa kafin ya d'ago kai yana tankwashe qafafuwansa yace. "Baffa maganar tafiyar nanfa ni na haqura da ita gaskiya, bana tunanin zan iya sa qafa inbar qasarnan mahaifiyata na cikin wannan yanayin, bacin haka ma baffa nifa har yanzu bancire tsammanin cewa Rashida zata dawo ba, jikina yana bani cewa duk inda take Ina ranta kuma tana cikin damuwa kamar yanda nake cikinta, bana son lokacin da zata dawo ta isko bana qasar, hakan zai sakata cikin shakku da kokwanto cewa nadamu da b'acewarta, shiyasa kawai nake tunanin gwara inzauna in bawa mahaifiyata kulawa har zuwa lokacin da ALLAH zai dawo da Rashida agareni. "Nafahimceka Nuraddeen, Kuma nayarda da zancenka, Amma karka manta dama tana zuwa ga bawane sau d'aya arayuwa, sai kuma sa'a idan tasa ALLAH yasake baka wata damar, batun mahaifiyarka kabarshi a hannuna zankula maka da ita har lokacin da zaka dawo, zanyi hakanne don ALLAH da kuma zamowarta uwa agareka amatsayinka na d'a tilo da nake so fiye da komai arayuwata." "Ita kuma matarka Ina so kayarda dani, na d'aukarma alqawarin zanci gaba dasa anayi maka sauka da addu'a har zuwa lokacin da ALLAH zai bayyana mana ita, zanyi qoqarin fahimtar da ita komai alokacin da tadawo izuwa gareka kuma na sadaka da ita akaro na biyu, na tabbata zata fahimceni tunda yarinyar nada ilimi da kuma fahimta. Shiru yayi cike da son mahaifin nasa ya fahimci abunda yake nufi, baya son abunda zaisa Rashidarsa taji wani shakku azuciyarta akan soyayyar da yake yimata tahanyar barin qasar alokacin da bata tare dashi, nisawa yayi kafin yace "Baffa.." Da sauri baffa ya dakatar dashi tahanyar d'aga masa hannu yana fad'in. "Shikenan! Na fahimceka ALLAH yasa hakan shiyafi alkhairi, Yana gama fad'ar haka yamiqe zuciyarsa a cunkushe duk da yayi qoqarin hana hakan ya bayyana a fuskarsa amma saida nuraddin ya fahimci hakan. STORY CONTINUES BELOW Toilet baffa ya wuce shi kuma yamiqe ya d'auke kwanon sannan ya Ida gyarawa, yana tsaye baffa yafito ya watso ruwa tare da canza wasu kayan yace dashi. "To ni zan fita, zanje wajen baffanka akwai mganar da nake son tattaunawa akan mahaifiyarka dashi." Bai jira jin amsar da zai basa ba yafice don baya son ya fahimci rashin jin dad'insa akan hukuncin da yake qoqarin yankewa kansa wanda yazab'awa rayuwarsa. Zaune Nuraddeen yayi akan katifa yadafe kansa da hannayensa duka yana furta, "Rabbi yassir wala ta'assir." Yajima ahaka yana tunanin yanda rayuwa tayi masa d'aurin goro tahanyar rasa farincikinsa Rashida da kuma gudan jininsa dake jikinta, a b'angare d'aya kuma tsananin damuwar da yake ciki ta halin da mahaifiyarsa ke ciki dake neman tsaida dukanin al'amurransa, yanzu kuma ga fushin mahaifinsa na nema ya bayyana agaresa ta dalilin hukuncin da yaga yafi dacewa agaresa, miqewa yayi yabar gidan shima bayan yasa kwad'o ya rufesa sannan yanufi police station d'in, Bai wani sha wahala ba inspector najida tasa aka kaishi inda take don ancanza mata waje saboda yanzu Bata qarqashin kulawar hukumar, tamkar ajiya take a hannunsu shiyasa aka kaita can cikin wani d'aki abayan station d'in daya tab'a gobara ya qone, tun daga kan tagogin wajen da qofofi duk sun qone, haka ma samansa abud'e yake saboda qonewar da rufin yayi, asalima nan jami'an 'yan sandan ke zagayawa domin biyan buqatocinsu na yau da kullum wato fitsari da bayan gida, duk wata rana da iska ko ruwan sama da akeyi akanta suke qarewa gashi an d'add'aureta gudun kada ta tsere, suna nufo wajen Nuraddeen yafara yatsine fuska yana toshe hanci saboda tsananin warin da yakeyi yana bin d'an sandar da kallo Mai cike da tarin tambayoyi har suka isa inda take, da sauri ya saki hancinsa yana zaro idanuwa waje hangota da yayi kwance cikin wajen dake kama da juji hannuwanta da afafuwanta d'aure da gudu ya isa wajenta tare da tallabota izuwa jikinsa batare daya damu da yanayin da take ciki ba yana fad'in. "Innar mu, innar mu." A hankali ta d'ago kanta tana kallonsa kafin ta saki wata irin muguwar qarar da tasa baisan lokacin daya saketa ba ya koma gefe, wani qaqari tashigayi kafin yaga anfara juyata cikin qonanniyar dattin dake cikin wajen ana birgima da ita tamkar wata halittar da batada qaffuwa, qananun gilasaiyen dake wajen ne suka shiga yayyanke mata jiki tana cigaba da wata qara mai cike da nuna tsantsar azabar da take ciki, ganin haka yasa yasake zuwa ya tallbota yariqeta yana kuka yana fad'in. "Kidena innar mu, don ALLAH kidena innar mu kada kijima kanki." Rungumeta yayi tsam don kada ta kucce masa yana aza kansa bisa jikinta, ganin haka yasa tasa baki ta kaimasa cizo ahannu har saida taciro da naman jikinsa amma yaqi sakinta saima sake rungumeta da yayi sosai yana kuka yana fad'in "kibari innar mu." Yanayin qugi da gumzar da qarar da takeyi yasa inspector najida da sauran 'yan sandan zagayowa sukayi tsaye suna kallon ikon ALLAH, lallae duk lalacewar uwa uwace kuma baza'a tab'a iya shiga tsakaninta da d'an taba. Wani yunquri tayi da yasa d'aurin dake hannuwanta faccewa da qarfi ta turesa gefe har saida yabugi jikin bangon wajen ya dawo, 'yan sandan naganin haka suka shigo wajen had'e da qoqarin rirriqeta, ganin tana neman tafi qarfinsu yasa wani d'aya daga cikin 'yan sandan qaqqarfa ya d'auketa kyakkyawan marin da yasa saida ta kife qasa, wani irin kukan kura Nuraddeen yayo kansa had'e da cakumar wuyansa ya kaisa jikin bango ya shaqesa yana fad'in. "Kai waye da har zaka dakarmun mahaifiya agabana?, Kasan me ake kira da uwa kuwa?, Kasan muhimmancinta ga 'ya'yansa da zaka dokarmun abita?." Maganar takeyi idanuwansa sun kad'a sunyi jawur ga wasu irin jijiyoyi sun taso masa a goshi yana turo idanuwa awaje." Jin yafara kakari yasa wasu 'yan sandan dawowa wajen suna qoqarin janyesa amma gaba d'aya su ukun ya turesu yafara kaimasa naushi a fuska da ko ina ajiki, dukansa yakeyi yana fad'in. STORY CONTINUES BELOW "Wayace ka daki mhaifiyata?, waye yace ku d'auremun ita haka?, Akan me zaku kawota anan ita ba dabba ba?" Duk d'an sandan daya nufosa sai yakai masa duka hakan ya b'atawa inspector najida rai nan take tbasu damar suyi masa duka, ai kamar jira sukeyi suka rufar masa da duka Saida suka yi masa liqis sannan suka qyalesa tace a d'aukesa ajefasa cell. Ranta a b'ace takira baffa lokacin yana wajen baffa Usman suna tattaunawa akan asibitin daya dace akai Yaya hawwar ta sanar masa da abunda Nuraddeen yayi nayiwa 'yan sandansu duka a police station d'in. Jikinsu narawa shi da baffa Usman suka nufo wajen kowane da abunda yake saqawa aransa. ••• ••• ••• Kwanan Dr.nura biyu yana rage aikace aikacen daya isko sun tarar masa a asibitin tasu sannan ya nufi anguwarsu umma agarin yarimawa, awannan karon bisa mashin yake tunda baizo da motarsa ba shiyasa batare daya sha wata wahala ba yasamu wani mutum ya tambayesa zancen iyayen Rashida da har lokacin yaga gidan a kulle da kwad'o. Nan mutumen ya sanar dashi komai har yana d'ora masa da "yanzu haka ina tabbatar maka cewa babu Wanda yasan inda iyayenta suka nufa balle asan halin da suke ciki." Wani irin jiri ya d'ibesa da yasashi saurin dafe bushiyar iccen dake kusa dashi yana fad'in. "Hazbunallahu wani'imal wakeel, wannan wane irin mummunan labari ne kunnuwana suka jiyomun." "Abun gaskiya ba dad'i sai haquri." Mutumen yafad'a had'e da wucewarsa, koda ya d'ago kai daga jimamin da take ciki da niyar yimasa wata tambayar sai yaga har yabar wajen, bai bar anguwar ba har saida yasake tambayar mutum uku don ya tabbatar da abunda nafarkon yafad'a suna bashi amsa iri d'aya da tasa sannan yabar anguwar jikinsa a sanyaye, kwana biyu yaqara kafin yakoma borno cike da tunanin irin amsar da zai baiwa Rashida idan ta tambayesa iyayenta, daga qarshe dai ya yanke hukuncin zai bari har zuwa wani satin idan sunje taganema idanuwanta ammashi tabbas bazai iya fad'a mata ba. Sosai yayi qoqarin sakin jikinsa lokacin daya koma amma saida Fatima tafahimci akwai abunda ke damunsa, yanda ta tsaresa da tambaya yasa ya sheda mata komai ba tare daya b'oye mata ba tare da shawarar daya yanke, nan take tagoya masa baya tan kukan tausayin Rashida akan halin da zata shiga idan sukaje ta tarar iyayen nata basa nan. rungumeta yayi yana lallashinta don yasan halinta sai takai gobe tan kuka har yakai ga Rashida tafahimci abunda ke faruwa. A b'angaren little Nuraddeen kuwa yayi wayau sosai don har ya iya zama, sak kamarsa da Rashida ke dad'a fita da kagani babu tambaya kasan yaron tane. Wani irin so takeyi masa marar misaltuwa da yasa Bata qaunar abunda zai sashi kuka ko kad'an, duk Wanda ya kallesa sau d'aya sai yaqara saboda yanayin jikinsa da kuma tsabtarsa shiyasa duk wanda ya gansa sai yayi sha'awar d'aukarsa, a daddafe suka hau yima Rashida Shirin komawa gida ita da little sai murna takeyi, katsar watsar tasamu satin ya qare wani yashigo yakama gobe zasuyi tafiyar don harda Fatima za'a. Basu suka gyara ba sai kusan qarfe d'aya na rana saboda wasu 'yan abubuwa da Nuraddeen ya tsayayi, shidai Nuraddeen sai binta yakeyi da kallo yana jimamin abunda zata riska idan sunje, Saida yayi mata nasiha sosai akan rayuwa da kuma muhimmancin yadda da qaddara mai kyau ko marar kyau, sannan ya tabbatar mata da cewa sauran maganin little Nuraddeen na cikon wata d'aya daya rage in Sha ALLAH zai karb'a sai ya kaimata idan lokacin yayi tana tayi masa godiya harda 'yar qwallarta, haka ma Fatima tayi mata godiya sosai suka rungume juna kafin suwuce su d'auki hanyar zuwa kano tana murna tana qarawa. ••• ••• ••• A b'angaren su umma kuwa Saida suka kwashe kwana uku suna yawo acikin borno kafin baba yagano Wanda yake nema, haka suke buge yini suna yawon tambayarsa in kuma dare yayi sai suje asibiti su shige cikin majinyata su kwanta da safe kuma su sake fita nemansa har ALLAH yasa suka ganesa, hannu biyu mutumen ya karb'esu bayan baba yayi masa bayanin dalilinsu na zuwa garin saida, sosi ya jajanta masa tare da yimasa addu'ar ALLAH ya bayyana masa inda 'yarsa take, nan yabasu wajen da zasu zauna acikin gidansa acan baya inda d'akunan masu aikin gidan suke sannan yace suyi haquri zai sama masu abunyi nan da kwana biyu, bayan kwana biyu ya tambayi baba in zai iya zaman tsaron wani sabon shagonsa daya bud'e zai dinga biyansa albashi duk wata dubu goma idan ya amince bisa amana da Kuma yardar daya yimasa, nan take ya amince har yana duqawa had'e da yimasa godiya, ita kuma umma d'aya daga cikin matan alhajin taroqa ta dinga yimata aiki duk wata zata biyata dubu hud'u, daga alhajin har baba basuso hakan ba amma nan take umma ta amince da zatayi aikin, acewarta hakan zai d'an d'auke mata hankali da ace tayi zaune ita kad'ai bata komai sai aikin tunanin b'atan 'yarta. Babu yanda suka iya tunda ta amsa zatayi, ajiyar zuciya alhajin yayi kafin ya kalli matar tasa bayan sun wuce yace. STORY CONTINUES BELOW "Hajia nafeesa don ALLAH kada kiyiwa baiwar ALLAHn nan abunda kika saba yiwa sauran masu aikinki, mutanene masu kirki da daraja agarena don haka kada kiwatsamun qasa tahanyar tozartar dasu don suna aiki aqarqashinki, zamane zamuyi dasu nad'an wani lokaci kafin su koma inda suka fito, saboda haka Ina roqonki daki mutuntasu don girman ALLAH kinji ko." Saida ta yatsina fuska sannan ta mere baki had'e da kallon gefe tace. "Naji.." Hajiya nafeesa itace matarsa ta biyu, matada kirki ko kad'an ga son walaqanta mutane matuqar suka amsa sunan talauci atttare dasu kuma suka zamo qarqashinta, shiyasa yaja mata kunne tun kafin aje ko Ina saboda shi mutumne mai dattako, yau itace rana ta uku da umma tafara aiki a sashenta, Babu ruwanta da shiga sha'aninta iya karta tayi abunda tasata ta koma sashenta, kamar kullum yau umma tagama gyaggyara kitchen bayan aikin da tayi saiga baqi hajia nafeesa tayi, sai da aka kwashi mintuna uku sannan ta d'ibi ruwa da lemuna ta kaimasu a falo tare da russunawa ta gaishesu sannan ta koma kitchen, sake kirawota tayi had'e da cewa. "Umma jeki ki kawo masu fruit" Saida taje kitchen tabud'e fridge d'in taga babu komai sun qare sannan tadawo taduqa tare da cewa. "Hajia ba'a samu kawo wasu ba, Kuma naciki sun qare." Batare da hajia nafeesa ta damuba taje d'aki tad'auko dubu uku tadawo falon tare da jefowa umma kud'in tace. "Jeki kicewa driver nace ya kaikai inda aka siyo mana kisawomun, kiyi sauri Ina jira yanzu yanzu kinji ko." "To hajia." umma tafad'a tare da d'aukar kud'in tabar falon. Tafe suke ita da drivern har suka kai daidai wajen da zata siyo fruit d'in yayi parking acan gefen titin yana nuna mata tsallake inda suke yace "Umma ki tsallaka acan kice daga gidan alhaji aka turoki, zasu had'a maku duk abunda suka san ana buqata." "To" Umma ta and masa tare da bud'e marfin motar tafito tana waige waigen gefe gefe don tasamu ta tsallaka. A daidai lokacin motarsu Dr nura tazo wucewa yana sauri ganin har qarfe d'aya na rana yayi saboda bayason suyi dare ahanya gashi ko cikin garin basu fita ba...... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [8/18, 1:25 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___53πŸ’Ž Umma na tsallakowa a dai dai tsakiyar titin Dr. Nura na kawowa da sauri ya sakar mata oda yana qoqarin juya starring nasa wanda kad'an ya rage ya bugeta, daga Fatima har Rashida runtse idanuwa sukayi had'e da dafe kai suna fad'in. "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun." Ita kuma umma tsabar tsoro duqewa wajen tayi jikinta na rawa, gefe yayi parking had'e da fitowa ganin takasa motsawa daga duqen da take a tsakiyar titin ya nufi wajenta. Kafin ya isa har drivern da sukazo tare yazo ya jayeta ya nufi wajen motar yana masifa da ita, "Umma kar kizo ki jazamun bala'i, duka duka yau kwanana uku da d'auka aiki agidannan kizo kisa akoreni, fisabillahi idan kinsan bazaki iya tsallakawa ba ai saiki fad'amun, gashi yanzu da kinja mani fitina." Maganar yakeyi kamar zai doketa saboda tsananin takaici, ganin babu abunda yasamu matar yasa Dr nura juyawa yakoma wajen motarsa yana girgiza kai had'e da fad'in ALLAH ya sawaqe, kallon Fatima yayi dake faman jijjiga little Nuraddeen dake kuka saboda tsoron qararsu da yaji ta tadashi daga baccin da yakeyi yace STORY CONTINUES BELOW "Bari na tsallaka nabawa matar can haquri duk da dai naga bataji ciwo ba." "Haba saurifa mukeyi, tunda ALLAH ya kare kuma ba laifinka bane kawai mutafi ALLAH ya tsare gaba." "Amin ya amsa yana qoqarin bud'e marfin motar ya shiga sai yaga drivern ya iso wajen masu fruit d'in, fasa shiga yayi ya nufi wajensa ya bashi hannu suka gaisa sannan ya amsa gaisuwar da masu fruit d'in keyi masa dake nuna sun sanshi, "Amm..don ALLAH kabawa matar can da muka kusan samun tsotsayi da ita haquri, sauri nakeyi amma tunda ALLAH ya tsare naga dacewar nayi maka magana tunda tare kuke kabata haquri." "Babu komai ranka ya dad'e, ALLAH ya tsare gaba kuma ya kaiku lafiya." "Amin." Yafad'a tare da miqa masa hannu suka sake gaisawa sanna ya juya yashiga motar ya tayar suka kama hanya shi kuma drivern ya amshi fruits d'in ya tsallaka inda ya ajiye motar tasu, ta glass Dr nura ke kallonsa lokacin daya biyo bayansa don yayi utorn yace da Fatima. "Matar wai kinsan wani abun, ashema motar gidace, sai yanzu na hango lambar dady dake jiki, kingasu nan sun biyo bayan mu." "Allah sarki, to ko waye waccan matar?, Inaga dai sabon drive ne dady ya samu, Amma shima bayada mutunci, don me sunzo a mota bazai iya tsallakawa yayi parking acan ba sai dai ya tsaya acan tsallake kuma ya turo matar mutane a wannan babban titi hakan shi bazai iya fitowa ba sai ita." "Iskanci samarin yanzune, Amma zanyi magana da dad a dinga tsawatar dasu akan tsofaffin mutane, inaga d'aya daga cikin masu aikine hajiya nafeesa ta turo kinsan halinta." "Zata iya yuyuwa gaskiya, ALLAH ya kyauta." A daidai lokacin da suka tsaya a bakin junction suna jiran traffic tabasu hannu drivern yazo saiti dasu Dr nura ya juyo ya kallesa yana fad'in. "Kin gashi ko?" Fatima tajuya ta kalli drivern daya qore sautin kid'an motar yana kad'a kai, dai dai lokacin itama rashida ta d'ago kai ta gefenta tana kallon motar da taji suna fira akai, motace mai kyan gaske don zata iya cewa takusa kyn ta Dr.nura ko kuma suzo d'ai, matar dake ciki tajuyar da kanta can gefe take kallo da jikinta yabata kmar ta santa kota tab'a ganinta awani wajen amma rashin juyo fuskarta da tayi yasa takasa tantance haka, tan wannan tunanin ne little Nuraddeen ya tsanyara kukan da ya maido hankalinta agaresa tare da qoqarin turasa cikin mayafinta don tabashi nono, a lokacin ita kuma umma tajuyo fuskarta ta b'angaren tana qarewa yanayin kyawon garin da yanda motocin suka tsaitsaya suna jiran abasu hannu suwuce amma kasancewar glass d'in motar tasu Dr nura tinted ne yasa takasa hango 'yar tata dake ciki tana kicaniyar bawa little Nuraddeen har traffic d'in tabasu hannu, jin motarsu tafara tafiya yasa Rashida d'agowa tare da maida kallonta wajen amma sai taga wayam tuni har motar tajuya ta d'ayan hannun takoma baya sukuma suka miqe hanyarsu tabarin cikin garin. ••• ••• ••• Baffa ya matuqar tsorata da abunda yaji inspector najida tace Nuraddeen ya aikata, sukayita bata haquri shida baffa, daqyar suka samu tabasu belinsa saboda yanda ranta ya matuqar b'aci kafin tace. "Baba kaja masa kunne don idan ya sake maimaita hakan zamu kaishi a hukuntashi ne saboda babban laifine civilian yasa hannu ya bugi kowane irin kaki, don haka kajamasa kunne, kawai na qyalesa ne albarkacinka daya sai mun ganar dashi kuskurensa" "To 'yata nagode nagode sosai." Kallon Nuraddeen da duk yafita hayyacinsa yayi had'e da cewa "tashi muje." "Babu inda zanje baffa matuqar innarmu na wannan wajen." Nuraddeen yabashi amsa had'e da d'agowa yana kallonsa da ijiyarsa da aka bubbuge ta kumbure. Cike da mamaki suka bishi da kallo kafin baffa Usman yace. "Haba Nuraddeen, kayi haquri, zamu d'auke mahaifiyarka anan amma kasan komai sai anshirya, kabi komai ahankali insha ALLAH zamu fidda ita nan kuma zata samu lafiya, yanzu haka muna tattaunawa akan maganar ne inspector najida ta kirawomu, kayi haquri ka taso muje kaji ko." STORY CONTINUES BELOW "Baffa bazan iya ba." Yafad'a tare da miqewa zai koma cikin cell d'in baffa ya bishi da kallo, saurin dakatar dashi baffa Usman yayi had'e da cewa. "Dawo Nuraddeen za'a fiddo da ita kaji!" Baffa zaiyi magana baffa Usman ya dakatar dashi had'e da cewa "a'a ya kabarshi, inspector najida ya za'ayi kubamu ita." Baffa Usman ya qarasa maganar yana kallonta. "Bayada matsala baba, dama Bata qarqashin kulawarmu don haka zaku iya zuwa ku d'auketa ko yaushe, Amma d'aukarta akwai had'ari sosai saboda yanayin da take ciki bai kamata ace an d'auketa ankaita cikin mutane ba, wannan kawai shine matsalar." "To mungode, Kai Nuraddeen kaji abunda tafad'a, me kace." "Ni zan iya kulawa da mahaifiyata koma a inane, kawai ni bana buqatar zamanta ne a hannun wud'annan mutanen." Shiru sukayi kafin sufice waje suna tattaunawa akan inda yakamata akaita daga qarshe suka yanke shawarar ajiyeta can gida a d'akinta, ciro waya baffa Usman yayi yakira maqwabcinsu dake jigilar motar haya, Bayan mintuna sai gashi yazo da motarsa sukaje aka d'auko Yaya hawwa tana kucce kucce, aka sata baya sannan Nuraddeen shima ya shiga ya riqeta, kallon baffa Usman baffa yayi yace yashiga gaba, shi zai biyosu abaya ya shiga suka wuce, Godiya ya sake yiwa inspector najida sannan ya nemi Mai mashin ya hau yabi bayansu. Ba qaramar wahala Nuraddeen yasha ba kafin su isa gida don duk ta yakusheshi, haka ma da zasu shigar da ita daqyar da sud'in goshi yasamu yashigar da ita cikin gida har d'akinta don hana kowa ya tab'ata yayi ganin yanda sai ihu da dariya yaran shiya ke yimata. Baffa na saman mashin ya kira baba balarabe yana tambayarsa jikinsu baba balarabe, nan ya sheda masa halin da ake ciki na b'atansu, baffa yashiga tashin hankali sosai marar misaltuwa yashiga sallallami har ya iso gidan, yana isowa ya tadda baffa Usman tsaye shida baffa Ali yana surfa masa masifa akan don me za'a kawo masu mahaukaciya acikin gida tahanasu bacci ta illata masu iyali, yana ganin baffa ya d'aure fuska had'e da zunduma ashar sannan yabar wajen, baffa dake cikin alhini da damuwan b'atan iyayen Rashida kota kansa bebiba balle yadamu da abunda yayi masa yashiga yima baffa Usman bayanin abunda ke faru. "Astagfirullah, astagfirullah, astagfirullah ALLAH ka sassauta mana wannan jarabawar dake b'ullo mana d'aya bayan d'aya." Baffa Usman yafad'a yana zabga uban tagumi, ahaka Nuraddeen ya taraddasu baffa yayi masa bayani, awannan karon damuwa tayi masa nauyin da bayada kuzarin yin kuka balle ya zubar da hawaye, gefen baffa ya zauna ya d'ora kansa saman kafad'arsa ko zai samu sassaucin yanayin da yakejin kansa aciki, tabbas ubangiji baya zalunci kuma baya goyawa mai zalunci baya domin yayi hani da hakan, haqiqa halin da mahaifiyarsa ke ciki ta cancanci zama ciki fiye da hakan saboda haqqin wud'annan bayin ALLAH da tayi sanadiyar fad'awarsu cikin wani hali suda 'yarsu, A hankali ya d'ago kansa yana kallon baffa yace. "Baffana shin kana fushi da inna ne har yanzu?." "A'a Nuraddeen bana fushi da ita Amma aduk lokacin dana tuna cewa ita wani sashece acikin rayuwata kuma mahaifiyar d'ana nakanji ba dad'i." "Kayafe mata Baffa nasan hakan zaisa tasamu sassucin halin da take ciki." "Ko kad'an Nuraddeen bani tunanin haqina na daga cikin dalilan da ALLAH ke hukuntata domin tun aranar da ALLAH ya wanzar da tsinkewar alaqar dake tsakaninmu nayafe mata dukkanin haqqina dake kanta kuma ALLAH shine sheda akan haka." Sake maida kansa yayi saman kafad'ar tasa sannan yace. "Kayi haquri baffana, haqiqa dukanin mumini baya kaucewa jarabawarsa, in Sha ALLAH da sannu quncinmu zai koma farinciki." STORY CONTINUES BELOW "ALLAH ya qaddara hakan Nuraddeen." Cike da tausayi baffa Usman ke kallonsu, haqiqa ALLAH shi yake fidda farin tuwo acikin baqar tukunya kamar yanda ya fidda Nuraddeen acikin Yaya hawwa, Wanda gaba d'aya kyawawan halayensa na mahaifinsa ne ya gado, sunjima awajen kafin akira sallar la'asar suje suyo SALLAH sannan suka kama hanyar yarimawa. Gidan baba balarabe suka sauka suka jajanta masa akan abunda yafaru kafin sujuyo sudawo gida. Da daddare suna zaune sunacin abinci sukaji sanarwar batun tafiyarsu Nuraddeen nan da kwana uku ana masu aqa gargad'insu dasu kasance cikin shiri, Nuraddeen na kallon yanda yanayin fuskar baffa takoma lokacin da aka fara sanarwar har aka gama yana saurare yayi ajiyar zuciya had'e da cewa Allah ya sawaqe. Cikin kwanaki ukun da suka rage kullum Nuraddeen shike zuwa da kansa d'akin Yaya hawwa da aka kulleta ciki ya bata abincin safe rana da kuma dare, haka kuma yakanyi qoqarin gusar mata da duk wata najasa da tayi da dattin dake taruwa cikin d'akin, Bata barin qazanta ko kad'an atattare da ita koda kuwa tana dukan sane har sai yaga ya tsaftace ta. Shi kuma baffa tuni suka gama yanke shawarar Kai Yaya hawwa asibitin mahaukata ta uduth dake jahar sokoto wanda tafiyar takama ranar dasu Nuraddeen zasu wuce, shire shire kawai baffa keyi nakai Yaya hawwa asibitin batare daya koma kula zancen maganar tafiyarsu Nuraddeen ba saboda yanda yaga yafita batun abun, Da daddare awayi safiyar ranar baffa na zaune shida baffa Usman suna fira saiga Nuraddeen yadawo kayansa duk ajiqe sanadiyar ruwan saman da akayi suka yimasa duka, binsa da kallo sukayi har yaje yacire kayan jikinsa ya canzo wasu yazo ya zauna inda suke yana mai saqale hannuwansa waje d'aya ya d'ora akn qirji, "A'a, Nuraddeen daga Ina kake haka ruwa sukayi maka duka?." Baffa Usman yafad'a yana kallonsa, saida ya kalli mahaifinsa dake qoqarin had'o tea a cup sannan yace. "Daga wajen bankwana nake baffa Usman." Miqo masa cup d'in tea daya had'a Mai zafi har yana tururi baffa yayi had'e da cewa. "Bankwana fa kace Nuraddeen, Ina zaka jene?" Saida ya kurb'i tea d'in yana sake motsasa da cokalin dake ciki saboda zafinsa sannan yace. "Baffa kayi hak'uri bisa qin fahimtarka da nayi akan maganar tafiyata, a yanzu amince zanje saboda gujewa dana sanin rashin amfani da damar dake iya zowa mutum sau d'aya arayuwarsa, zanje nayi karatu, karatun da zansa kuyi alfahari dani har iya qarshen rayuwata, karka manta lokacin da kake jinya kaso ace d'aya daga cikin zuri'arku yayi karatu a fannin lafiya, to tabbas zan cika maka wannan burin da yardar ALLAH, al-amarin innar mu da Rashida kuwa, wa'ufawwidu amri ilallah, natabbata zai dafa maka wajen kula da komai, don haka shirin da nayi bazan warwaresa ba, da yardar ALLAH zantafi." Kallo baffa Usman baffa yayi mumushi d'auke da fuskarsa yace. "Kaji ko Usman, dama nafad'a maka bazan takura Nuraddeen ba, bazan tilasta saba amma ina da yaqinin bazai Bari wannan damar da ALLAH yabamu tawuce Saba." "Alhamdulillah haqiqa naji dad'in sauya wannan hukuncin da kayiwa kanka da kayi, ubangiji ALLAH yayi maka albarka yasa kaje cikin sa'a, ALLAH yafaranta zuciyarka ybka kariya aduk inda kake kuma yayi maka jagora.." Haka baffa yaci gaba da kwararo masa addu'o'i yana riqe da hannunsa baffa Usman na tayashi fuskokinsu d'auke da farinciki, murmushi Nuraddeen yayi ganin haka a fuskarsu had'e da cewa. "Saidai baffa nakasa zuwa wajen baba balarabe inyi masa bankwana saboda rashin sanin da wace irin fuska zan kallesa in iya fad'a masa cewa zanje karatu waje a daidai lokacin da nine na zamo silar b'atan 'yarsa da kuma iyayenta. STORY CONTINUES BELOW "Karka damu Nuraddeen nasan bayada matsala zai fahimceka, Amma yanzu lokaci yaqure saboda qarfe bakwai naji ance zaku had'u a babbar ma'aikatar jahar nan don qarfe takwas jirginku zai tashi, don haka ni zani magantu dashi da yardar ALLAH kaji ko?" "Shikenan baffa babu damu." Yafad'a tare da shanye sauran tea n ya ajiye cup d'in agefe, hannu yasa aljihu ya fiddo kud'i ya miqawa baffa. "Ga wannan baffa, Inna Bilkisu ce da sauran mutanen gida da naje yimasu bankwana suka bani, banso karb'a ba Amma sun tilasta adole na karb'a." "ALLAH sarki, angode ALLAH yabada ladar zumunci," "Amin baffa." "Yawwa Usman ka tayamu godiya idan kaje, ALLAH yasaka da alkhairi." "Amin Yaya Babu komai ai yiwa kaine." Baffa usman yafad'a yana murmushi. Nan suka shiga fira tare dayi masa nasihohi kala kala akan yariqe addininsa da al'adunsu nad'an bahaushe idan yaje kafin baffa yaje ya d'auko kud'ad'en da yake ajiya saboda tafiyar. Saida yasake qidanyasu dubu d'ari biyu da ashirin don ya tab'a wasu ma sannan ya miqawa Nuraddeen yace. "Ga wannan ka qara dasu, banida cikakken qarfi ko arziqi da na yimaka fiye da hakan, to kayi haquri dasu su kad'ai ALLAH ya horemun." Qin karb'a yayi had'e da cewa "A'a baffa kabarsu ai su zasu bamu duk abubuwan da muke buqata idan munje, muradinsu kawai muyi karatu sosai mudawo mutaimakawa qasarmu, don haka kabarsu akula da lafiyar innar mu dasu." Daqyar baffa suka tilastasa ykarb'i dubu d'ari suka ajiye d'ari da ishirin d'in kamar yanda ya buqata. Shirune yabiyo bayan wasu lokuta kafin Nuraddeen yace "baffa kuroqamun sa albarkar baffa Ali koda bayan natafine a matsayinsa na mahaifi agareni, naje nayi masa magana nafad'a masa zancen tafiyata amma ko juyowa beyi ya kalleni ba." Murmushin takaici baffa yayi zuciyarsa cike da damuwar halin da d'an uwansa ke nunawa, baffa Usman ne yace. "Kayi haquri Nuraddeen, in sha ALLAH komai zai wuce kaji?" "To baffa Usman ALLAH ya yarda." Miqewa baffa Usman yayi yace zai wuce baffa ya rakkosa har qofar gida suka yiwa juna seda safe sannan yatafi. Aranar kam zaune baffa suka kwana shida Nuraddeen suna firar bankwana cike da shauqin rabuwa da junan da zasuyi. Tunda asubar fari Nuraddeen ya ida shirya kayansa lokacin shima baffa yagyara tsaf suka nufi can gidan saboda Nuraddeen naso yayi bankwana da mahaifiyarsa, a kan hanya suka had'u da baffa Usman yanata sauri zaije can suka sake juyawa suka nufi gidan tare, a bakin qofar d'aki suka tsaya Nuraddeen yabud'e ya shiga Yaya hawwa na kwance tana bacci bisa tabarmar data rage kad'ai a cikin d'akin don gaba d'aya Nuraddeen ya kwashe kayan dake ciki saboda gudun kada tajima kanta ya mayar dasu acan d'ayan d'akinsa nada. A hankali ya qarasa ciki yaduqa saiti fuskarta yakai hannu zai shafa sai kuma ya fasa, wasu irin hawaye suka zubo masa a fuska yayi saurin gogege yana fad'in. "Innar mu ALLAH yabaki lafiya, ALLAH ya yaye maki wannan lalurar albarkacin haihuwa da tarbiyar da kka bani, ALLAH yasa kaffarar kankarar zunubbanki ne wannan hlin da kike ciki, Ina maibaqincikin barin qasarnan babu addu'arki da sanyawar abarkarki atttare dani, fatan alkhairi uwata kafin nadawo agareki." Yana gama fad'ar haka yamiqe da sauri yana hawaye yabar d'akin, kamar an tsinkili Yaya hawwa ta tashi da qarfi tanufo wajen qofar tana fad'in. "Nura, nura, kana Ina d'ana, Ina kake nura" Jawo qofar baffa Usman yayi da sauri ya rufe had'e da murd'a key. STORY CONTINUES BELOW Part d'insa ya bud'e har ya fara qura yana bin ko Ina da kallo, memory d'in da sukayi da Rashida tashiga dawo masa akai musamman daya kalli kitchen wanda ya zamomasu tamkar wani waje da suke d'ebewa juna kewa wajen aikawa da juna kalaman soyayya da kuma isar da saqon zuciya, bud'e cikin d'akin yayi ya shiga nan take yaji qafafuwansa na nema su gagaresa tsayi ya durqushe wajen yana kuka kamar ransa zai fita. Yanajin qarar sautin ihu da bugun qofar da yaya hawwa keyi tana Kiran sunansa Amma rad'ad'in da yakeji azuciyarsa yanzu daya dawo masa fal ba zaisa ya iya sake waiwayarta ba, Qarar wayarsa data fara ruri yasashi tsaida kukan nasa had'e da miqewa yashiga uwar d'akan ya jawo wata jikkar dake d'auke da pics d'in aurensu na ranar walima yaciro hotunanta inda take ita kad'ai tare da d'aukar wayarta data bari sannan yabar d'akin, Saida ya kulle part d'in yaba baffa makullan yana d'iba agogon hannunsa qarfe bakwai daidai ya d'auki butar dake gefe ya wanke fuskarsa su Inna Bilkisu na tsaitsaye suna kallonsa idanuwansa sunyi jawur saboda kukan da yayi har sun d'an kumburo. "Inna Bilkisu mu zamu wuce asamu a addu'a." yafad'a yana kallon muneera data rakub'e gefe ya sakar mata murmushi, dashire hauru tayi tana fad'in. "Ya nura ALLAH ya kiyaye hanya yabada ilimi Mai albarka, ALLAH yasa koda zaka dawo aunty rashidarka itama tadawo, akaro nafarko da yaji muneera tafara burgesa kenan yasake sakar mata wani murmushin had'e da cewa "Amin muneera, ALLAH yazab'a maki kema miji nagari kafin nadawo In isko kin haifi mani d'a ko d'iya." Washe haqoranta tayi gaba d'aya tana fad'in "amin ya nura amma d'an bunni irinka." Juyawa yayi yana kallon Inna ruqayya da tun d'azu ke zabga masu wata it muguwar harara had'e dayin tsaki yace. "Nawuce Inna ruqayya." Ko kallonsa batayi ba balle yasa ran zata tanka masa daga qarshe saima tashi da tayi tabar wajen, "Nuraddeen zo mutafi mana ga malan bello can a qofar gida da motarsa kai kad'ai muke jira." Baffa Usman yafad'a tare da bin bayan baffa daya fice daga gidan, rufa masu baya shima Nuraddeen yayi inna Bilkisu da sauran mutanen gida nabiye dashi suna yimasa addu'a, Koda suka isa har motocin wud'anda zasuje sun soma tashi zuwa filin jirgin aminu kano da sauri yafita shima yaje ya gabatar da takardar shed'arsa da i.d card d'in da suka bashi sannan akace yashiga motar dake qoqarin tashi wacce itace ta qarshe. Bayansu su baffa suka sake bi har suka isa filin jirgin, suna Isa aka fara kiran sunayen matafiyan kafin akai ga sunansa yaje ya duqa ya kwashi albarkar su baffa tare da rungumesu yana mai sake roqon dasu kula da mahaifiyarsa Wanda ananbaffa ya tabbatar masa da cewa kada yadamu suma dasun koma zasu wuce sokoto sufara amsar katin Kai mahaifiyar tasa asibitin ta mahaukata da sauran shire shire. Yaji dad'i sosai kuma yasamu qwarin guiwar tsayawa ya jajirce akan karatunsa don ya tabbata mahaifin nasa zaikula da mahaifiyarsa duk da kuwa bata a qarqashin inuwar aurensa. Basubar wajen ba har saida sukaga tashin jirginsu sannan suka juyo suka dawo gida cike da kewarsa.... _'yar uwa mekika fahimta acikin rayuwar littafin SANNU SANNU?, Nidai nafahimci girman uwa komai lalacewarta awajen nuraddin😍don haka bana wasa da mamana kaima karkai wasa da mamankaa,πŸ’ƒπŸΌπŸ’ƒπŸΌ domin itacee farincikinka duniya gabaa d'ayaaa (D.one voice)_ Kimanin awanni biyar da rabi suka shafe akan hanya kafin su isa garin kano, iya jigata Rashida tayita don ba kad'an ta tsargu da zaman na mota ba kasancewar bata tab'ayin koda makamancin irin sa bane, bini bini Fatima da Nuraddeen ke juyowa baya su kalleta har zuwa lokacin da suka iso.+ Kai tsaye gidansu dake unguwar sharad'a phase2 suka nufa, da sauri mai gadi ya taso ya bud'e masu had'e da russunawa yana gaishesu dr.nura ya d'aga masa hannu yana fad'in "ahh...malan sule sannu da aiki, kana lafiya?." "Lafiya klw ranka shidad'e barka da hanya an iso lafiya?" "Lafiya klw malan sule" Dr .nura yafad'a daidai lokacin da yake karya starring motar had'e dayin parking, Fatima ce tafara fitowa tana fad'in. "Ya ALLAH! Sweety wlh duk nagaji." Daga can cikin motar taji yace, "To matar ke kenan, inata ga mmn baby ko ba haka ba?" Ya qare maganar had'e da juyawa yana kallon Rashida dake qoqarin sab'a Little Nuraddeen a kafad'a zata fita, dariya Fatima tayi ta zagaya tacan gefe tabud'e mata gambun motar had'e da karb'ar little tana fad'in. "Sannu maman boy, ai ko da gani babu tambaya kinfini jigata, tafiya kam mai tsawo babu dad'i ko kad'an gaskiya in bata jirgi ba." Ita dai Rashida Banda murmushi da takeyi tana shaqar yanayin iskan garin tare da bin tsarin gidan da kallo babu abunda takeyi har yafito cikin motar ya kulle tare da wucewa gaba sukabi bayansa, Suna shiga duk suka zube tsakiyar falo a gajiya, Saida suka d'an huta sannan Dr nura yawuce part d'insa ita kuma Fatima tamiqe d'auke da little had'e da cewa Rashida tabiyo bayanta suka wuce part d'inta, har ga ALLAH Rashida ba hakan taso ba aranta, taso suna isowa sukaita wajen iyayenta duk da lokacin dare ya somayi don takwas na dare tawuce amma babu yanda ta iya dole tayi haquri idan talura da yanayin yanda kowanensu ya dawo agajiye, "Maman boy kishiga toilet kifara watso ruwa kafin nan nima naje na watso nawa, sai in kawo maki little shima ayi masa." muryar Fatima ce taji tadaki kunnenta tana qoqarin ficewa daga d'akin, sai alokacin tayi yunqurin fita daga tunanin data shiga tare da d'aga mata kai sannan tafice sab'e da little dake faman baccinsa hankali kwance. Rashida tajima zaune agefen gadon tana qarewa d'akin kallo kafin tamiqe tashiga toilet ta watso ruwan, A b'angaren Dr.nura kuwa koda Fatima taje har yafito wankansa, "sweety shine baka jira nazo nataya kaba?" Tafad'a cikin shagwab'e fuska. "Ina tuba matar kawo little maza kije kema kiyo naki musamu muranka sallolin dake kanmu mukai maman boy gida." Shiru tayi na tsawon daqiqa d'aya dake nuna damuwarta akan maganar, har ga ALLAH tanajin rad'ad'i aranta idan ta tuna halin da Rashida zataje ta riska na rashin iyayenta, ba wani dogon shiri yayi ba face doguwar riga jalabiya daya zura ajikinsa sannan ya karb'i little a hannunta yana fad'in. "Kidena bana son irin wannan dogon tunanin zai iya sakaki cikin damuwar da zata iya ankarar da ita halin da ake ciki." "Shikenan Dr, Amma kana ganin bazamu bari sai gobe muje kaita ba? Ni sai nake ganin kamar dare yayi yanzu. "Noo...hakan zaisa tayi kuka damu idan mukace mubari sai gobe, amma in mukaje yanzu mun kaucewa duk wani zargi daga gareta akan cewa rashin zuwanmu ne akan lokaci ya haifar da hakan kin gane?." 'Daga masa kai tayi sannan tashiga toilet, batafi mintuna biyar ba itama tafito tawuce falo tajawo akwatin kayanta dama tun d'azu Mai gadi ya shigo masu dasu ciki tawuce itama tashirya cikin doguwar rigar wani yadi marar nauyi, karb'arsa tayi takoma d'akin da Rashida ke ciki ta isko ita har tagama shiryawa tana ranka sallolin kanta tunda qasaru ne, tad'an jima zaune kafin taqarasa tamiqa matashi had'e da cewa. STORY CONTINUES BELOW "Ungoshi kiwatsa masa ruwa kifito falo muna jiranki." Karb'arshi tayi tana fad'in "sannu aunty yaron nan nabaku wahala, shikenan shi baza'a ajiyesa shi kad'ai ba sai an tsaresa?" "Ikon ALLAH! kin jiki da wata magana mmn boy, ai lalura ce takawo hakan, Amma badon haka ba mezaisa yana baccinsa ayita reto dashi hakan?" Fatima taqarasa maganar tana murmushi sannan tamiqe tafice daga d'akin, a falo taci karo da Dr nura yadawo daga wajen ba maigadi saqo ya sawo masu abinci a wani restaurant dake kusa dasu a can bakin titi. Hijab d'inta ta d'auko tadawo falon yana zaune ya miqe had'e da kabbarta sallah har suka gama ranka sallolin atare, suna zaune Rashida tafito d'auke da little ta gyarashi sai qamshi yake saye da hijab d'inta har qasa, duqawa tayi ta gaishesu suka amsa kowanensu fuskarsa d'auka da murmushi kafin Dr nura yamiqe had'e da karb'ar little d'in a hannunta ya zauna d'aya daga cikin kujerun dake falon, ita kuma ta zauna kusa da Fatima da har lokacin bata tashi daga inda sukayi sallar ba tana addu'a, sai da tagama suka shafa tare Rashida nafad'in. "Amin ya Allah masu albarka auntynah." Zaro idanuwa wje Fatima tayi had'e da cewa. "Nashiga uku ni batulu, yaushe kika fara shiga zuciyar mutane mmn boy kina gano sirrin addu'o'in da sukeyi." Dariya Rashida tayi sannan tace. "Ba shiga zuciya bane auntyna, abunda ya tsaya mani araine har yakai yasa bana iya gama duk wata ibada tawa ba tare dana roqi ALLAH daya kawo mana qarshen saba, balle ke da nasan duk yanda nakai ga jin zafinsa kinfini shiyasa natabbatar idan ni ina yin addu'ar samun yayewar wannan abun toke zaki fini yin hakan sosai, ubangiji ALLAH yanda kuke bawa yaron nan kulawa kuma ALLAH yakula daku yabaku zuri'a masu albarka." Tare duk suka had'a baki ita da Dr.nura suka amsa da Amin. Maigadi ne yayi sallama Fatima taje ta karb'o saqon ta kawo falo ta ajiye sannan taje ta d'auko plates guda uku da cokulla da wani tray babba da yuqa ta ajiye bayan ta d'aurayosu, zuzzuba abincin tayi dake cikin robobin take away sannan taje ta wanko fruit d'in Rashida takarb'a ta gyara masu, miqewa tayi taje ta d'auko little a saman jikin Dr nura dae kwance saman kujera tana fad'in. "Bisimillah yallab'ai." Saida sukaci suka qoshi Dr ya d'auki makullin motarsa tare da d'aukar little dake saman kujera yana 'yan wasanninsa da hannuwa sannan ya fice yana fad'in. "Ina jiranku a waje." Kwashe kayan suka farayi suka wawwanke komai had'e da gyara wajen sannan suka bi bayansa, dama kayan Rashida nacikin mota ba'a fiddo komai ba inba 'yar jikkar baby bag d'in little dake sagale a hannunta ba, shiyasa shikad'ai ta gyara ta sauyawa kaya ita kuma tamaida wud'anda ta cire ajikinta. Kasancewar akwai 'yar jayawa sosai tsakaninsu yasa koda suka isa anguwar tasu Rashida qarfe tara da rabi nadare har yayi, duk d'okin da Rashida keyi nason zuwa taga iyayen nata suna nufo anguwar taji gabanta yafara fad'uwa, a hankali tafara kirawo sunayen ALLAH tana mai neman tsarinsa daga dukkanin sharrin dake iya cutar da ita ko d'anta. A daidai bakin qofar gidan ya tsaya da yake akwai wutar nepa da d'aid'aikun mutane dake kai da kawo cikin anguwar, ko gyara tsayuwar motar beyi ba ta b'alle marfinta ta ruga aguje tanufi qofar gidan tana kiran "umma, ummaa." Turus ta tsaya ganin qofar rufe da kwad'o gabanta na tsananta fad'uwa, juyowa tayi jiki ba k'wari tace. "Uncle ya naga gidan arufe?." Tana qarasowa inda suke a firgice. Maqwabcinsu ne taga yazo wucewa zai shiga gidansa kafin dr yace wani abun tabi bayansa da sauri tana fad'in. "Baba, baba na kande!." Da sauri ya juyo yana kallonta cike da mamaki yaja da baya, ya matuqar tsoratar ganinta awannan lokacin ba zato ba tsammani, matsawa ta sakeyi kusa dashi jikinta na rawa tace, "baba nakande nice fa Rashida, nice Rashidar umma fa, don ALLAH baba kada ka gujeni ka tsaya kafad'amun Ina su umma da baba sukaje, Ina son nagansu baba nakande, Ina matuqar kewarsu, kafad'amun ina ne suka tafi don ALLAH." STORY CONTINUES BELOW Wata irin ajiyar zuciya ya sauke cike da ta'ajibi yace. "Rashida!" "Na'am baba nakande." "Rashida ke ce?" "Eh baba, Ina su ummata suka tafi?" Jinjina kai baba nakande ya farayi kafin yafashe da kuka yana fad'in. "Wayyo ALLAH na Rashida sai dai kiyi haquri..." Bata qarasa jin abunda zai fad'a ba tsabar fargaba da tsoron abunda take tunanin zai fad'a yasata fad'uwa wajen, da gudu su Dr. Suka qaraso wajen Fatima taduqa ta tallabota tana kiran sunanta, Dr nura dake riqe da little ya miqama baba nakande hannu dake kuka yace. "Assalamu alaikum, baba meye kafad'a mata halama haka?." "Yaro kaine?" Baba nakande yafad'a yana share hawaye don ya wayesa, "Eh baba." "Dama tana hannunka?" "Eh baba," "To meyasa bak sanar da ita komai ba?, Gashi yanzu tun kafin infad'i abunda zan fad'a tasome." Ganin halin da take ciki yasa Fatima takoma cikin mota ta d'auko gorar ruwan swan d'in dake ciki ta yayyafa mata had'e da shafa matasu ga fuska, Ahankali Rashida tabud'e idanuwa tare da fashewa da kuka tana fad'in. "Nashiga uku aunty don ALLAH kada kucemun iyayena sun mutu sun barni.." "Haba Rashida, waya fad'a maki cewa iyayenki sun mutu?, Iyayenki na raye amma bamusan inda suka dosa ba, sun bar garinnan kwata kwata saboda b'atanki.." Kan baba nakande yarufe baki tuni sukaga Rashida tafara fizge fizge idanuwanta sun kakkafe." Da sauri Dr yace Fatima takarb'i little da sai faman kuka yakeyi ya tallabi Rashida yasa cikin mota, "baba don ALLAH idan ka amince kazo muje asibiti dakai, nasan bazaka rasa sanin wasu daga cikin dangin taba." Duk da baba nakande najin tsoron halin mutunen duniya tausayin Rashida yasa bai tsaya tunanin komai ba yashiga motar ya bisu, da gudu Dr nura ke taka motar har suka isa asibiti, cikin gaggawa aka karb'i Rashida kasancewar wajen aikinsa ne ba tare da antsaya wani b'ata lokaci ba, ba'a jima ba likitan daya shiga dubata yafito had'e da tambayar Dr nura cewa dama tanada hawan jini (hypertension)?. Nan yabashi amsar cewa tana dashi lokacin data haihu amma yayi tsammanin cewa wannan is normal yariga ya wuce, "Noo..gaskiya ba haka bane, yanzu hakan shine ya tsar mata, sai dai baiyi mata worst sosai ba za'a iya shawo kansa da yardar ALLAH, inaga ko yanzu saboda bata jima da haihuwa bane hakn tafaru, amma in sha ALLAH komai zai dai daita don Babu wata matsala bayan shi, yanzu haka anyi mata allur bacci ne saboda tasamu isashhen hutu" "Alhamdulillah Dr. Ngd sosai." "Ba damuwa dr.nura, ALLAH yabata lafiya." "Amin Dr" Nuraddeen yafad'a yana kallon baba nakande dake zaune yayi tagumi..... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [8/20, 11:50 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ STORY CONTINUES BELOW _ASSALAMU ALAIKUM, GAISUWA DA FATAR ALKHAIRAN ALLAH AGAREKU MASIYANA, INA BAKU HAQURU AKAN RASHIN AMSA MAKU IDAN KUNYI COMMENTπŸ˜… KUYI HAQURI IN SHA ALLAH DAGA YAU ZAN GYARA, KUNA QORAFI AKAN HAKA ASHE ABUN SON KAINE WATO WANZAM BAKA SO GA KANKA,🀣 YO IDAN HAKAN NA BATA MAKU RAI ME KUKE TUNANI AGARENI NIDA NAZAUNA NAYIMAKU TYPING DON KU NISHA'DU SAI ACE ANWAYI GARI KO THANKS BAZAN SAMU AWAJENKU BA BALLE COMMENT, DUK DA DAI NI NASA KAINA AI KUNSAN BABU DADI DON NA TABBATA KUNA KARANTAWA, SHIYASA NIMA NA SHAREKU DON KUJI IDAN ABUN KWAI DA'DIπŸ˜‚ BUT TUNDA KUN QARA, TO ZAN GYARA KAMAR YANDA NAKEYI ADA, INA FATAR KUMA ZANGA CHANJI AWAJENKU TA HANYAR DA'DA'DAN COMMENT 'DINKUπŸ‘ NGD SSAI_ Page___55πŸ’Ž Tuni baba balarabe da Yaya maryam dasu aunty marwiyya suka isa asibitin cikin daren sanadiyar wayar da baba nakande yayiwa baba balarabe ya sanar dashi zancen dawowar 'yar d'an uwan nasa shi kuma yakira Yaya maryam takira aunty marwiyya ta sanar da ita, kowanensu cike da farinciki yake a zuciyarsa naganin 'yar tasu duk da dai a yanayin da take ciki na nema ya gusar masu da farincikin, Little kuwa yayi kuka har ya gaji saboda tsabar yunwar da yakeji, goyashi fatima tayi bacci ya d'aukesa shi kuma Dr nura ya koma gida don ya d'auko masu abunda zasu iya buqata kafin gobe don yasan bazasu wuce gobe ba shiyasa koda su baba balarabe suka iso asibitin Fatima kad'ai suka tarar sai baba nakande, ita tawuce dasu d'akin da Rashida take kwance tare da yimasu bayani ataqaice kafin Dr ya iso. Jugum jugum ya tarar dasu kamar wud'anda k'wai ya fashewa cikin ciki ya wuce ciki ya ajiye kayan dayazo dasu yana kallon gefen da Rashida ke kwance hannunta laqe da drip sun kusa qarewa sannan yajuyo yanufi inda baba balarabe ke zaune shida mijin Yaya maryam, "Assalamu alaikum." Yafad'a yana miqa masu hannu suka gaggaisa kafin baba nakande yayi masu bayanin cewa shine mutumen da yazo da Rashida, cike da girmamawa suka sake gaishesa kafin ya nemi waje yazauna yana fuskantarsu, matsowa su aunty marwiyya sukayi wajen suma suka gaisa sannan Dr nura yagabatar masu da kanshi ataqaice yaqare maganar yana nuna masu Fatima. "Waccan kuma iyalina ce." "Masha ALLAH." Baba balarabe yafad'a sannan yace. "Ni sunana malan balarabe, qane ga mahaifin ita waccan yarinyar Rashida, ita Kuma wannan sunanta Maryam wato Yaya agaremu nida mahaifin Rashida, wannan qanwar mahaifiyar tace sunanta marwiyya sai kuma shi wannan mijine ga ita yayar tamu wato alhaji ubale." "Dukkaninmu da kake gani abu d'aya muke babu banbanci, Kuma mukad'aine iyayen Rashida acikin wannan garin, munyi baqin ciki sosai alokacin da muka rasata wanda sanadiyar hakanne ya haifar mana da shiga matsanancin damuwa kala kala har yakai ga su iyayenta da suka haifeta sun kasa jurewa rashinta sunbar garin bayan doguwar jinyar da sukayi a asibiti." A yanayin bayanin da baba balarabe keyi yasa Dr nura gamsuwa akan cewa su d'in shaiqanta ne na jini don haka yasaki jiki sosai dasu had'e da yimasu bayanin yanda suka tsinceta dalla dallah da irin wahalar da yaronta yasha wanda shine sanadiyar da yasa basu nemesu ba tun wuri, duk da dai yayi qoqarin ganin yasamu iyayenta alokacin Amma ALLAH bai yarda ba, gaba d'ayan su kuka da tausayin halin da Rashida tashiga ita da yaronta suka shigayi suna Mai godewa ALLAH daya miqata ga hannun mutane nagari masu d'imbin karamci da halacci, a daidai lokacin little dake goye a bayan Fatima ya tashi yafara mutsu mutsu yana neman yin kuka Nuraddeen yamiqa mata hannu ta sancikke masa shi, miqasa yayi hannun malan balarabe had'e da cewa. "Wannan shine abunda ALLAH ya albarkaceta dashi wanda muka rad'a masa suna Nuraddeen bisa yardarta da kuma amincewarta." Hannun baba balarabe na rawa ya karb'esa yana qare masa kallo don wajen d'auke yake da hasken wutar lantarki kamar rana, tabbas ko ba'a fad'a ba wannan yaron jinin sune don kamarsa sak da d'an uwansa wanda itama mahaifiyar tasa wato Rashida dashi take Kama, wasu zafafan hawayene suka zubo masa yana maijin inama d'an uwansa bai tafi ba yaga irin kyautar da ALLAH yayi masa ta hanyar dawo masa da 'yarsa da kuma jikansa a hannunsa. STORY CONTINUES BELOW Rungume yaron yayi yanaji tamkar d'an uwan nasa ne kafin yaji hannun Yaya maryam data kasa dangana tana qoqarin karb'arsa. Murmushi tasaki alokaci d'aya hawaye nasake suko mata saman fuska itama lokacin data karb'i yaron tana fad'in. "ALLAH mun gode maka daka dawo mana da Rashida lafiya daga hannun bayinka salihai masu kyakkyawar zuciya, ya ALLAH ka lullub'esu da tarin ni'imominka tare da yalwataccen farinciki marar yankewa acikin zukatansu da kuma fuskokinsu," Taqarsa maganar had'e da d'ago yaron tana sumbatarsa. "ALLAH ka isarwa mahaifiyarka Nuraddeen ita da iyayenka, yayi maka sakayya kaida mahaifinka ga muguwar kakarka data nemi salwantar maku da rayuwa kida mahaifiyarka, ALLAH..." Katseta mijin nata malan ubale yayi tahanyar cewa. "Haba Maryam, menene haka? Keda yakamta kigodewa ALLAH sai ki koma kinayiwa bayinsa mummunar addu'ah? Shin ashe hakan ya kamatan ceki kiyi bayan kinsan ALLAH maiyin sakayyane ga bayinsa wud'anda aka zalunta?." Shiru tayi had'e da miqawa aunty marwiyya little itama takarb'esa, shafa kansa ta shigayi cike da qaunarsa tana yaba kyawon da ALLAH yayi masa da yanayin jikinsa mai cike da ban sha'awa. Ganin gaba d'ayansu sun shagala yasa Fatima komawa cikin d'akin da Rashida ke kwance, tana zuwa ta isko tafarka daga allurar baccin da akayi mata lokacin kusan qarfe d'aya saura mintota nadare, da sauri Fatima ta matsa kusa gareta tana jero mata sannu, qoqarin tashi zaune tayi ta dakatar da ita tana fad'in "a'a komawarki ki kwanta maman boy." Tana dafa kafad'arta had'e da qoqarin maida ita kwance, "Aunty da gaske su ummata sun tafiyarsu?, Da gaske ba'asan inda suka tafi ba?, Shikenan bazan sake ganinsu ba?" Rashida tafad'a had'e da riqe hannuwanta tana kuka, cikin dakewa Fatima da tuni zuciyarta tayi rauni hawaye sun soma kaida kawo a fuskarta tace. "A'a maman boy, Zaki ga su ummanki komai daren dad'ewa, hakan bayana nufin kun rabu bane Rashida sai dai kawai ubangijinki na auna imaninkine ta hanyar yimaki jarabawa wata bayan wata Kuma dama haka rayuwar mumini take, idan anyi masa jarabawa ya canye ta sai asake yimasa wata jarabawar wacce tafi tafarkon da akayi masa don kawai a d'aukaka darajarsa da kuma imaninsa idan ya canyesu, kiyarda cewa zasu dawo agareki nan kusa bada jimawa ba in Sha ALLAH." Cikin kuka tace "Yaushe? Awane lokaci kuma aunty? Bayan zukatansu sunriga sunyi imanin cewa sun rasani kenan har abada." "Kisa aranki cewa kusa zasu dawo, haba maman boy karki manta ALLAH subhanahu wata'ala yana cewa." _"Laa taqnad'u min rahmatllah (kada mu kuskura muyanke qauna ga rahamar ALLAH)_" "Don haka kada kicire tsammanin cewa rahamar ALLAH zatasa iyayenki sudawo matuqar kika miqa dukanin al'amurranki agaresa kamar yanda kikayi abaya, haqiqa wawa, lusari, Wanda baisan kanshi kad'aine ke rabka hannuwa yana tsammanin cewa ALLAH bazai jarabcesa ba bayan kuma yace yayi Imani, walh Rashida ALLAH da kansa ke cewa matuqar kukace kunyi Imani to." _"wala nabluwannakum bi shai'in minal haufi wal ju'i wa naqsin min amfusi wassamarat, wabasshirisubirin, allazina iza asabathum musibatun qalu innalillahi wa Inna ilaihirrajiuun, ma'ana idan kunyi Imani dani to (zamu jarabceku da abubuwan tsoro, da yunwa da rashin rayuka daga kawunanku da kuma tsirrai, muna yima masu haquri bushara wud'anda idan musiba tasamesu sai suce ga ALLAH mukazo Kuma agareshi zamu koma)"_ "Saboda haka ki daure ki zamo cikin bayinsa masu haquri da yake yiwa bushara kinji ko!" Cikin kuka dake cike da sauti Rashida tafad'a jikinta tana fad'in. "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, allahummah thabbit aqadami wa haqqiq Imani,.." Qarar kukan nata yajanyo hankalin su baba balarabe dake waje da sauri suka shigo cikin d'akin har suna rige rigen qarasowa bakin gadonta, tana ganinsu taqara fashewa da wani kukan had'e da rungume aunty marwiyya tana fad'in. STORY CONTINUES BELOW "Wayyo ummana.." Babu yanda suka iya domin rasa iyaye tako wace irin fuska ce yanada matuqar rad'ad'i arai wanda dole ko ana so ko ba'aso awannan gab'ar dole abarta tayi kukan domin ko anhanata yinsa rad'ad'in da takeji azuciyarta bazai barta tahanu ba, sai da tayi mai isarta tayi shiru sannan tajaye daga riqon da tayiwa aunty marwiyya takwanta akan gado tana ajiyar zuciya har lokacin hawayen basu dena fita daga idanuwanta ba, sannu suka dinga yimata d'aya bayan d'aya tana amsawa had'e da binsu da kallo hawayen naci gaba da zubo mata. Rarrashinta suka taru sunayi had'e da ban magana da dad'ad'an kalamai Amma gaba d'aya ita ba abunda take gani sai hoton fuskokin iyayen nata da batasan ranar da zata koma had'uwa dasu ba. Gaba d'aya takasa tsaida zubar hawayenta wanda hakan yasa Dr nura yaje yakira Dr daya dubata yazo ya sake yimata allurar bacci bayan aunty marwiyya ta aza mata little daya fara qananun kuka tabashi nono yasha, Bacci mai nauyi sosai ya d'auketa sannan baba balarabe yace da aunty marwiyya taje gida tunda dare yayi sosai lokacin qarfe d'aya da rabi, Atafau tabuga kai ga qasa akan babu inda zataje anan zata kwana, don gani take za'a iya sake d'auketa idan taje gida kafin tadawo gobe da safe. Adole aka qyaleta tunda ta nace akan haka, Kiran mijinta tayi tasanar dashi anan zata kwana Kuma cikin sa'a ya amince mata don mutumne da baida matsala kuma ko bayan hka su biyu suke ga mijin nata shiyasa Bata damu da sai takoma gida ba. Yaya maryam ma daqyar baba balarabe ya samu tabi mijinta sannna yajuyo yana kallon Fatima dake riqe da little yace. "Fatima dake da Dr. Yakamata ku koma gida saboda akwai gajiyar tafiyar da kukayo kuna buqatar hutawa sosai, inyaso nida qanwar mahaifiyar ta zamu kwana anan idan Babu damuwa koda za'a buqaci sawo wani abu kunga ni Ina nan babu matsala." Ji Fatima tayi kamar ta k'walla ihu don har ga ALLAH bataso barin asibitin ba amma saboda dr.nura ya amsa yasa dole babu yanda zatayi ta haqura ta miqawa aunty marwiyya little kamar zatayi kuka ta karb'esa sannan sukayi saida safe suka tafi sai tunzurar baki takeyi, kallonta yayi yana tuqi yayi murmushi had'e da cewa. "Fatima meye abun b'acin rai naga kina turar baki haka?" Saida ta kallesa sannan ta maida kanta gefe tace. "Meyasa kaima bakace anan zamu kwana ba, ALLAH bana son rabuwa da maman boy ita da little hisby d'innan nawa, shine kai harda wani miqewa da sauri irin bakama damu ba." 'yar dariya yayi daidai lokacin suka iso inda 'yan sandan dake security akan titi suke yayi slow da motar had'e da ciro i.d card d'insa ya nuna masu suna yayyada bayan motar da wajen boot sannan suka basa izinin wucewa. Bayan sun wuce wajen ya juyo ya kalleta tare da aza hannunsa saman nata yace. "Kiyi haquri kinji matar?, Ba haka nake nufi ba amma yakamata kisn cewa yanzu bamuda wani sauran iko akanta, mu kawai masu taimako ne, munemi cikar ladar taimakon da mukayi, kada mu nemi shiga hurumin da iyayenta kad'ai suke da haqqi akansa, kada mutauye ladarmu tahanyar nuna ra'ayin zukatanmu bayan munsan ayanzu sunfimu tsananin buqatar kasantuwa da ita, koba haka bama ai dole murabu dasu ko bama so, don haka daga yanzu kifara koyawa zuciyarki yanda zata jurewa rashinsu akusa damu kinji ko?" Batare data amsa masa ba ta d'ora kanta kawai saman kafad'arsa tana shafa hannunsa har suka iso gida. Shima baba balarabe kiran iyalansa yayi yace surufe gida shi sai gobe zai dawo. ••• ••• ••• Su baffa nadawowa daga filin jirgi suka harhad'a kud'ad'en da zasuje kai yaya hawwa asibiti tare da wata 'yar qaramar jikka da kowanensu yasa kayansa kala d'aya da zasuyi amfani dasu don sai gobe zasu dawo kasancewar akwai nisa sosai tsakanin kano da kuma sokoto garin shehu, wanda koda sun isa dawuri bazasu kammala abunda ya kaisu ba har sai dare yayi, don haka dole suyi haqurin juyowa gobe idan ALLAH yakaimu bayan sun kammala abunda sukeyi.Bankwana sukayi da Inna Bilkisu bayan baffa Usman ya jadda mata da kada abar Yaya hawwa da yunwa kafin sudawo, suyi qoqari kota tagane su dinga ajiye mata abinci har ALLAH yadawo dasu lafiya sannan suka tafi, akan hanya sukaci karo da Inna ruqayya ita da baffa Ali tafe suna magana qasa qasa, kallo d'aya baffa Ali yayi masu ya d'auke kai Inna ruqayya kuwa harara ta zabaga masu had'e dayin tsuki tawuce tana fad'in.+ "Qarya dai fure take ba 'ya'ya, Kuma raminta qurarrene, sunyi abu yasha masu kai, gashinan garin neman gira anrasa ido, ba'a samu yabo ba ansamu wahala." Kanta baffa Usman yanufo ransa ab'ace baffa yariqe hannunsa had'e da cewa. "Haba Usman kada kataya mahaukaci hauka, ai kabarta tafad'i abunda ke ranta domin da kanta take, tafi muje ko nine a matsayinta zanfad'i abunda yafi hakan musamman idan akwai b'acewa atattare dani." Yaja hannunsa suka tafi. Yanajin sadda suka kwashe da dariya baffa Ali nafad'in. "ALLAH dai yaraka taki gona." Inna Bilkisu kuwa da kanta taje tabud'e d'akin Yaya hawwa ta ajiye mata abinci had'e dayin tsaye abakin qofar d'akin tana kallonta, ganin tayi ana buga Yaya hawwa ajikin bangon d'akin kafin a d'agata sama ayar qasa batasha mamaki ba sai da taga anjuyar da kanta gefe yana kallon sama sannan an mammal qwashe mata hannuwa sun koma baya, qafafuwanta kuma anbud'esu kowace anjata gefe, ahaka taga tana jan ciki tazo inda abincin yake tasa kanta ta turesa ya zube qasa sannan tafaraci da baki kamar yanda dabbobobi keyi, kuka ne ya qwacewa Inna Bilkisu ganin yanda aka maida ita kamar wata muguwar dabba da sauri taja qofar d'akin tarufe tabar wajen tana kuka, kobata tambaya ba tasan wannan aikin shed'anun aljanune don haka taje ta d'auko redionta tasa karatun qur'ani tanufi d'akin, da sauri Yusuf yariqota had'e da cewa. "Inna Bilkisu kada kiyi haka, bakisan wud'anne kala bane kada garin taimako kema su nemi cutar dake, kibari tunda su baffa sunje nemamata mafita anema mata." Wata qara sukajiyo daga d'akin da tasa yusuf jawo hannun Inna Bilkisu yana fad'in "kinji ko inna Bilkisu, ALLAH kimaida kada kitafi, ALLAH zai baki ladar niyar da kikayi." Inna ruqayya da baffa Ali nashigowa kuwa tsuki sukaja had'e da cewa. "Bisimillah, 'yar mahaukatannan tafara, wlh mukam dai anzaluncemu da aka ajiye manaita anan tana neman kashe mana kunne da baqar qara sai kace dujjal." Dariya baffa ya kwashe da ita had'e da zuwa ta tagar d'akin yana leqen Yaya hawwa yace. "Ikon ALLAH, ke ruqayya zo kiga yanda matarnan mai shegen cin zarafi da iya walaqanci ta koma, wlh kyace wata qwaguwa ce," leqawa tayi tafashe da dariya tace. "Ala gwai, wlh naji dad'i, dubi qafafuwan shegiya uwa na lala tacciyar mace, ke muneera.." Ta kwalawa muneera kira dake d'aki kwance tana bacci. Cikin magagin bacci tafito tana susar kai tace, "Matso nan kiga Yaya hawwa dake maki sherin gwalmammin qafafuwa kiga yanda ALLAH yamayar mata da nata." Leqawa muneera tayi had'e da murza idanuwanta don ta tabbatar da abunda suka gane mata da sauri ta jid'o had'e da cewa. "Tab.. ALLAH Inna hawwa takoma uwa banqararriyar kaza." Suka kece da dariya, shidai Yusuf da Inna Bilkisu nagefe suna mamakin yanda baffa Ali da Inna ruqayya kefitar da munanna kalamansu ga Yaya hawwa cike da isgilanci, sai kace ada ba itace wacce suka d'auka shugaba kuma aminiyar duk wasu shawarwarinsu da al'amurransu na duniya ba..... _"'yar uwa shin ko kinsan da wud'anne kalar mutane kike rayuwa dasu acikin duniya?, shin kina iya banbancewa wud'anda ke sonki da kuma maqiyanki acikin mutanen dake zagaye dake?,sanin hakan nabuqatar natsuwa da kuma nazari, tabbas ni nakoyi darasin sanin cewa mutum mugune kuma bayada tabbas awajensu baffa Ali haka kuma na d'auki darasin zaunawa nagano banbancin masoyin gaskiya da kuma naqarya awajen Inna Bilkisu, nayarda cewa mutum bayada alqibla wajen rashin gano ainahin kalarsa. Don haka kema yiqoqari ki tsinci naki darasin acikin wannan littafin mai suna SANNU SANNU Bata hana zuwa.._πŸ₯° STORY CONTINUES BELOW *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [8/21, 11:20 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___57πŸ’Ž ••• ••• ••• Sosai wan saheke Rashida tasamu sauqi zuwa azahar aka basu sallama, kai tsaye gidan Yaya maryam aka nufa da ita duk da baba balarabe yaso ace gidansa zata zauna, Amma ganin yanda Yaya Maryam d'in ta kafe kai da fata lalle wajenta zata zauna yasa ya haqura tunda itace yayarsa babu yanda zaiyi, Tunda Rashida ta bar gida yaune karo nafarko da taji tana son had'uwa da mijinta wato habibinta mahaifin d'anta Nuraddeen, suna kan hanyarsu ta zuwa gidan Yaya maryam da yake Dr nura ne ya d'aukosu a mota, Fatima na gefensa riqe da little sai Yaya Maryam da aunty marwiyya da ita Rashida abaya, shi kuma baffa mijin Yaya maryam ne ya d'aukosa saman mashin d'insa suka biyo bayansu, takalli aunty marwiyya tace. "Aunty ya nura fa?" Wata uwar harara ta zabga mata had'e da juyar da kanta gefe, ganin haka yasa ta kama bakinta har suka isa gida, Dr nura nayin parking su baba balarabe dake biye dasu na tsayawa da mashin d'insu, Yaya Maryam ce tafara fitowa sannan aunty marwiyya suka nufi cikin gidan, hakama Fatima itama tafito tare da riqo hannun Rashida dake qoqarin fitowa tayi mata jagora sukabi bayansu, A can cikin gida aunty marwiyya tafara fad'a tana fad'in. "Yaya wannan yarinyar batada hankali, kinji tambayar da takwyimun a mota wai ina ya nura? Wlh badon batada lafiya ba da saina d'auketa mari don ko sunan garinsu bana sonji balle sunansa." "Hmmm banni da ita marwiyya Ina jinta, bi izinillahi ko shikad'ai ya rage namiji aduniya bazata koma gidansa ba, ai tunda haka tafaru to ta tabbata komai mahaifiyarsa zata iya yimata saboda qiyayyar da take yimata kuma mu shedane akan haka, shikenan kuma don muna sakarkari sa mubarta takoma masa a kashe mana ita, narantse kozai mutu sai yasaketa tunda ba ita kad'ai bace macce aduniya ba." "Wannan shine daidai Yaya Maryam, in yaso yaje can uwarsa ta aura masa wacce take so." Aunty marwiyya tafad'a a qufule. Tana rufe baki suna shigowa, ta sakarwa Fatima murmushi had'e da cewa. "Wucikke matar Dr." Batare data kalli inda Rashida take ba. A falo suka shiga suka zazzauna kafin mijin Yaya maryam yashigo shima su Dr da baba balarabe nabiye dashi abaya. Bayan sun zauna Yaya Maryam tamiqe taje takawo masu ruwa da lemuna masu sanyi da 'yar sauran samosar data had'a da safe da take sayarwa ta ajiye masu, "Balarabe kutab'a wannan kafin kuwuce." Saida suka fara tab'a hira ana tayiwa little da Fatima ta ajiye tsakar falo yana faman yimasu qyaqya dariya sannan tamiqe taje ta d'ora masu dahuwar taliya da kifin gwangwani ga 'yar qaramar tukunyar gas cooker d'inta saboda tayi saurin nina, ai kuwa cikin mintotan da basu wuce goma ba ta nina ta zuzzubo a flate ta kawowa kowa, sake d'auko had'ad'd'en zob'onta na siyarwa da takeyi tayi ta kawo masu sannan itama ta zauna tana cin nata, "Kai amma zob'on nan yayi dad'i yaya maryam ya akeyinsa?" Fatima tafad'a tana sake kai cup d'in zob'on abaki. "Kai matar Dr Banda zolaya, zob'on na siyarwa?" STORY CONTINUES BELOW "Eh mana, gaskiya kina gyarasa sosai, ai wannan zob'on ko shugaban 'yan hasada yasha dole ya yabashi balle masu so da gaske." Dariya duk suka samata harda Rashida da tun d'azu takasa kai koda cokali d'aya abaki sai faman cakularsa takeyi, "Hmmm! Yakamata nabiya kud'in zobonnan tunda yasa madam Santi har na tsinkayo ana yimata waigi." Dr nura yafad'a yana dariya ganin aunty marwiyya na gyarawa Fatima hilon dake bayanta, juyowa tayi had'e da cewa. "Au..Ashe da gaske yakeyi, kai aunty marwiyya zakija yadinga tsokanata kuwa." Kallon Rashida baba balarabe yayi had'e da d'aure fuska yace. "Ke Rashida maza kici abinci kinji ko?" Ganin bada wasa yakeyi ba yasa tafaracin abincin tana b'ata fuska tamkar wacce keshan magani. Yanda su Dr suka saki jikinsu cikin 'yan uwan Rashida Kai ka rantse kace Abu d'aya suke ko kuma sun jima da sanin juna, hakan Kuma ba qaramar shaamquwa da yarda ta sake shiga tsakaninsu. Bayan kowa yaci yasha ya qoshi, baba balarabe yayi gyaran murya had'e dayin doguwar addu'a da nasihohi masu ratsa jiki bisa abunda ya faru sannan yarufe dayiwa su dr.nura shida matarsa godiya sosai shida su Yaya Maryam, irin godiyar da suke yimasu da kyawawan addu'o'i had'e da fatan alkhairi har seda suka fara jin kunya, daga qarshe aunty marwiyya tace. "Mungode sosai Fatima matar nura uwar nura, muna roqon Rabbissamawati wal ardi daya azurtaku da 'ya'yaye nagari masu albarka da zakuyi alfahari dasu duniya da lahira, ALLAH yakareku daga dukknin sharrin abinqi ya lullub'eku da rahamarsa da tausayinsa yayi maku arziqi mai yawa ya share maku dukkanin kukanku." "Amin ya ALLAH aunty." Suka amsa cike dajin wani dad'i da sanyi da farinciki azuciyarsu, Itama Rashida hawaye nazubar mata a idanuwa ta rungume fatima tana fad'in. "Dukkanin alqawurranku agareni wanzazzune hakama alkhairanku tabbataccine akaina, karamcinku da halacci masu girmane da mizaninsu yakai girman da bazan iya biyanku aduniya ba, amma har zuwa fitar lumfashina zuciyata da Kuma rouhina cike da qaunarku mai tsanani take, duk wani fitar lumfashi nawa cike yake da fatan alkhairan ALLAH agareku da kuma farinciki mai d'orewa, ina roqonku da kada kucireni acikin rayuwarku kada kumanta dani kubani damar da zan iyaci gaba da rayuwata tare daku matsayin 'yan uwa batare da zumunci ya yanke a tsakaninmu ba har izuwa ranar da zan kwatanta faranta maku zuciya kamar yanda kuka faranta tawa data ahalina koda sau d'aya ne." "Bazamu mantaki ba Rashida, bazamu rabu dake da little ba don kunzamo wani yankin daya sama mana farinciki na wani d'an lokaci arayuwarmu wanda muke fatan yatabbata atare damu har abada" Fatima tafad'a itama had'e da rungumeta tana kuka, kuka sukeyi sosai sai kace wud'anda suka rabu kenan har saida Dr nura ya cewa Fatima ta taso sutafi yana mai mamakin yanda shaquwa mai tsanani haka tashiga tsakaninsu a qanqanen lokaci, 'Daukar little tayi ta sumbacesa agoshi tare da wucewa gaba suka rakosu qin miqasa tayi har saida ta shiga mota Dr nura na Shirin tayarwa sannan ta badashi tana goge qwallan da suka zubo mata, shi kanshi Dr nura saida yaji ba dad'i Amma babu yanda suka iya dole yaja motarsa sukabar wajen. Su kuma yana tafiya rigima ta kaure tsakanin baba balarabe da yace a dole akira Nuraddeen da ahalinsa asaanar dasu yayinda sukuma su aunty marwiyya sukace atafau bazai yuyu ba, daga qarshema Yaya Maryam bugawa Rashida tsatsauran Jan kunne tayi akan karta sake koda mafarkine tayi tunanin zata koma gidan Nuraddeen tunda mahaifiyarsa bata sonta. Shikuwa baba balarabe duk da Yaya Maryam na sama dashi haka yatabbatar mata da cewa dole sai yasanar da Nuraddeen anga matarsa saboda haqqinsane kuma har lokacin tana aqarqashin igiyar aurensa, hakan yasa suka rabu baran baran, rayuwakan kowanensu a b'ace. STORY CONTINUES BELOW Yana komawa gida yashiga Kiran lambar baffa data baffa Usman Amma shiru kowace switch up, hakama ta Nuraddeen yakira yafi a qirga itama akashe saboda bai fara anfani da sabon layin daya siya acan. Hakan yasa hankalinsa tashi sosai marece nayi yanufi garin bebeji, yana isa yaci karo da baba Ali ya tsaya yana tambayarsa, sunjima suna magana kafin baba balarabe yabar wajen jikinsa a sanyaye, wata 'yar iskar dariya baffa Ali yayi sannan yawuce yana fad'in "da sannu duk sai kun gane kurenku har ita wacce sanadiyar b'atanta aka rufemu nida iyalina aka yimana dukan mutuwar da gangar jikinmu takasa d'auka" Kwana baba balarabe yayi yana juyi akan abunda baffa Ali ya sanar dashi duk da dai wani b'angaren na zuciyar tasa bai yarda da hakan ba. ••• ••• ••• Su Baffa kuwa a maimakon kwana d'aya da zasuyi agarin sokoto sai da sukayi kwana biyu saboda shawarar da wani likitan yabasu akan sukai marar lafiyarsu kware shine abunda zaifi masu sauqi, hakan yasa suka sake kwana d'aya acan har saida suka gama shirya duk abunda yakamata acan asibitin kware suka biya kud'in da za'a basu mota da jami'an lafiyar da zasu d'aukota sannan suka juyo zuwa gida bayan sun bada address d'in da za'a tura masu motar nan da kwana biyar, gaba d'aya wayoyinsu sun mutu saboda rashin charji da basuda wannan ne dalilin da yasa baba balarabe yayita kiransu bai samu ba. Saida suka iso zamfara don dama motar da zata ajiyesu acan sai daga nan su shiga wacce zata kaisu kano suka shigo kafin motar da suka samu ta kano ta cika suka shiga masallacin dake cikin tashar sukayi sallah sannan suka samu wani saurayi ya ara masu chargarsa sukasa wayar baffa charji, minti talatin sukayi sannan motarsu tacika lokacin baffa har yasamu d'igo biyu a 'yar wayar tasa qirar kamfanin itel mai madannai. Mintuna biyu yayi da kunnata kiran baba balarabe ya shigo. Cikin natsuwa baffa ya d'aga had'e da amsa sallamar da yayi masa sannan suka shiga gaisawa. "Am dama wata magana naji cewa Nuraddeen yabar qasar nan shine nace bari nakira naji shin ko gaskiya ne.?" Wani irin nauyi baffa yaji Amma bayada wata hanyar da zai iya basa amsar tambayar da yayi data wuce eh ko kuma a'a, tamkar baffa nagabansa ya duqar da kai had'e da cewa. "Eh malan balarabe hakane amma..." Kafin yaqarasa baba balarabe ya katsesa ta hanyar cewa. "To madallah, shikenan nagode." Had'e da kashe wayarsa, duk inda ransa yake in yayi dubu ya b'aci, Ashe akwai ranar da Nuraddeen zai nuna irin wannan halin ko inkula agaresu adaidai lokacin da suka rasa 'yarsu a hannunsa, Ashe har yanada qwarin guiwar da zaya iya barin gari acikin yanayin da yake kuma har yatafi batare daya yimasu sallama ba?, Me suka yimasa da suka cancanci haka daga wajensa? Ai koba komai ana bankwan saboda ba'asan halin rai ba, kuma ai yakamata ace ko don kaucewa zargi yazo yayi masu bayani, wud'annan tambayoyi sune suka dinga Kai da komo acikin zuciyarsa da kuma qwaqwalwarsa, rashin samun amsar sune yasake tunzurasa sosai, Ransa ab'ace yanufi gidan Yaya Maryam yakirata tare da zayyane mata duk abunda kefaruwa, dama tayi mamakin ganinsa shida jiya suka rabu baran baran da ita sai gashi har yana fad'in ko mijin Rashida naso ko baya so duk inda yaje dolene ya saketa, kuma dole duk wata alaqa dake tsakaninsu su datseta koda hakan na nufin zasu mayar masa da d'ansa a hannun sane. *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [8/23, 10:36 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž STORY CONTINUES BELOW *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___58πŸ’Ž Shiru Yaya Maryam tayi na tsawon daqiqu uku kafin tace. "Hakan shine daidai, dama abunda nayita qoqarin lurar dakai kenan ka kasa ganewa, to amma batun cewa za'a mayar masu da yaro don yanke duk wata alaqa dake tsakaninmu kabarta don ni gaba d'aya bana buqatar jinmu yakoma zama atare dasu tunda basa da zuciyar imani." Sun jima suna tattaunawa kafin yabar gidan har lokacin yanajin d'aci akan maganganun da baffa Ali yafad'a masa. ••• ••• ••• Baffa nagama waya da malan balarabe yakalli d'an uwan nasa ya sakar masa murmushi cikin qarfin hali sannan ya juyar da kansa gefe, yana maimaita innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun aransa. Dafa kafad'arsa baffa Usman yayi had'e da cewa. "Meke faruwa ne Yaya?" "Abunda Nuraddeen yayi gudun faruwarsa." Yabashi amsa had'e da juyowa suna fuskantar juna. "Kayi haquri Yaya, dama dole hakan zata faru, mu auna kanmu a matsayinsu mugani, don haka dole zamu lallab'asu har su fahimcemu, ayanayin yanda damuwowi sukayi masu yawa kamarmu, abune mai wahala su iya riqe fushinsu alokacin da sukaji labarin tafiyarsa musamman idan sun jine daga bakin daya kasa yimasu kyakkyawan bayanin da zayasa sufahimta, shi kuwa rashin bayani acikin kowane al'amari shike haifar da husuma da kuma aikin dana sani, don haka dole muyi haquri har zuwa lokacin da zasu fahimcemu." "Shikenan Usman, amma duk da haka mufara jaraba zuwa wajensa idan mun sauka." Awa hud'u ta d'aukesu kafin su isa kano, ana ajiyesu tasha suka sake shiga motar da zata kaisu qauyen na yarimawa, cikin qananan daqiqu suka isa sukaci sa'a kuwa yana zaune bakin gida yana arwala suka yimasa sallama, bai amsa ba har saida ya gama arwalarsa ya d'aga kansa sama yayi addu'ar da akeyi bayan gama arwala sannan ya kallesu fuskarsa a sake ba yabo ba fallasa ya amsa masu salamar. "A'a malan Idris, malan Usman sannunku da zuwa yanzu kuke tafe?." Yafad'a yana qoqarin ajiye butar da yayi arwala agefe, kallon baffa Usman baffa yayi kafin suji ya sake cewa. "Kai Hassan kushiga ciki ku kawo ruwa a butoci magrib taqaraso ana batun tada sallah." "Am sannunku da zuwa bari naqarasa masallaci kafin ku iso liman na batun tayarwa." "To shikenan!" Baffa yafad'a cike da mamaki a fuskarsa. Basu sake Shan mamaki ba sai da suka fito sallah suka tarar da tabarma an shimfid'a a qofar gida da kwanonin abinci, "A'a malan Usman ya akayi kukayi tsaitsaye? bisimillah kuzo kuzauna mana, Gaggaisawa suka shigayi kafinsu baffa sufara qoqarin canza maganar izuwa asalin wacce takawosu, Amma ga mamakinsu sai sukaga kawai yajawo kwanoni abinci yana fad'in bisimillah malan idris muci abinci ko." Babu yanda suka iya saboda yanada matuqar muhimmanci agaresu da bazasu iya yimasa musu ba, wanke hannayen su sukayi sukasa suka fara cin abincin tare har suka qare, Bayan sun kammala, baffa yace. "Don ALLAH malan balarabe kayi haquri ka sauremu, nasan an aikata maku ba daidai ba, amma kuskurene da babu wanda ya isa ya kauce masa, tabbas Nuraddeen yabar qasarnan saidai bada son ransa ba, nine natirsashi ganin yana shirin ruguza rayuwarsa, kuma dama ce wacce yasamu tun kafin wud'annan matsalolin su faru, ganin ba lallai bane ya sake samun wannan damar ba kuma ga yanayin da yake ciki yasa daya tirje akan babu inda zaije saboda yana tsammanin dawowar matarsa garesa wanda abune gaibi akan dawowarta yasa natilasta masa zuwa koya fita daga cikin halin damuwar da yake ciki." STORY CONTINUES BELOW "Hmmm malan Idris kenan!, Ai bance kunyi wani laifi ko kuskure ba, meye laifinku don kunyi qoqarin inganta rayuwar d'anku?, Meye laifinku don kunyi abunda zai sakaku cikin farinciki?, Ba kuda wani laifi don haka kumanta da komai, fatana d'aya muma ALLAH yabamu ikon d'aukar darasin da kuka koyamana muma mu inganta rayuwar 'ya'yanmu kamar yanda kukayi koma fiye da hakan.?" Duk iya qoqarin da sukayi wajen ganin sun lurar dashi ya fahimci gaskiya hakan ya cutara daga qarshema cewa yayi. "Don ALLAH da girmansa malan usman mubar wannan magana kada tajawo rugujewar sauran mutuncin dake tsakaninmu, d'anku dai ALLAH yabashi ilimi mai albarka mukuma ALLAH yatsare mana 'yarmu aduk inda take yabata juriyar shanye duk wani abu da zai nemi duqufar mata da farinciki." "Amin" suka amsa masa dashi bayan sun sake bashi haquri sannan suka wuce zukatansu a dagule. Bayan suntafi yakira Yaya Maryam lokacin tana zaune itada Rashida tana bawa little da sai qara wayau yakeyi nono, "Na'am balarabe ya akayi? Duk lafiya dai kuke ko?" "Lafiya klw Yaya, dama iyayen yaronnan mijin Rashida ne sukazo bada haquri...." "Kaga rufemun babinsu bana son ji, ai Ina mumuka haifi aburmu kuma muka bashi aurenta ko! don haka yanzu mun raba, ko suna so ko basa so yazama dole yabawa Rashida takardar ta, bazata koma gidansa ba ko mutuwa zaiyi, shashancin baza da wofi." Yaya Maryam ta katsesa tana masifa, Wata irin zabura Rashida tayi had'e da miqewa tsaye da kad'an little yafad'i, Yaya Maryam tayi saurin riqosa had'e da kashe wayar tana binta da wani mugun kallo mai cike da tarin tambayoyi, hankalinta atashe takalleta tana fad'in "Mekike fad'a haka gwaggo!," da yake da haka suke kiran sunanta sannan taci gaba da cewa. "Wai wa ake zancen zai sakeni?, Duk fa iya adadin kwanakinnan dana d'auka zuciyata cike take da mararinsa, idanuwa da kunnuwana cike suke da son ganinsa da kuma jinsa, kawai nayi shirune saboda kada kuga rashin kunyata tayi yawa amma Ina son na had'u da mijina, shine kuma kuke cewa sai ya sakeni?, Meye laifinsa?, Wne zunubin ya aikata da za'ayi yunqurin rabashi da ni?" "Ungo nan marar kunyar yarinya." Yaya Maryam tafad'a had'e dayi mata daqquwa tanaci gaba da cewa. "Ke wane zunubin kika aikata da uwarsa ta rabaki dashi, kin ganemun shashashar yarinya da batasan ciwon kanta ba, to bari infad'a maki wlh munfiso kimutu atare damu muyi maki sallah murufeki da mumaidaki gidansa uwarsa ta sake halakar mana dake, don haka tunwuri kiciresa aranki matuqar kina son muzauna lafiya dake kinji nafad'a maki." "Haba gwaggo! Haba gwaggo wannan wani irin tsattsauran hukuncine zakuyi mana, inada yaqini akan tunda wannan jarabawa tasameni shima t yake cikin irin tashi jarabawar, don ALLAH kada kura bamu kodon yaronnan." Taqarasa maganar tana kallon little dake hannun ita Yaya Maryam d'in had'e da fashewa da kuka, har ga ALLAH Yaya Maryam taji tausayinta, Amma Babu yanda ta iya, wannan ita kad'aice hanyar da zasubi su kub'utar da 'yarsu daga sharrin uwar mijinta, wacce itama tanacan cikin mummunan yanayin da basuda labari akai, cikin dakewa da qarfin hali tace. "Rashida kawai kuhaqura da juna, yaro kuma Allah shizai rayashi ko bakwa tare don haka kibi umurninmu kizauna lafiya." Wani kukan ta sake fashewa dashi had'e da durqushewa qasa tana fad'in. "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, astagfirullah ALLAH natuba kayafemun laifukana, ya ALLAH ka sauqaqamun wud'annan jarabawowin rayuwa kada sufi qarfin zuciyata susa na sab'a maka," kallon yya matram data kauda kai tana goge 'yan guntayen hawayen da suka zubo mata tayi. "Gwaggo baifa sakeni ba, taya zaku rabamu?, Karku manta dani harshi zamu iya sake ahiga wani hali idan kuka yimana haka, kunada iko akaina ammashi sam bai kamata kununa iko akansa tahanyar tirsasashi ya sakeni ba." STORY CONTINUES BELOW "Kedai zaki shiga wani halin keda kike ganin bamu isa mutirsasaki akan abunda muke ganin shine alkahiri arayuwarki ba, amma bandashi tunda har ya iya mance awane irin hali zaki shigaba keda abunda ke cikinki ba ya tsallake qasarnan ya tafiyarsa duk da yasan abunda yafaru dake Amma saboda ya gyara rayuwarsa kuma ya farantawa iyayensa yatafi yabarki acan duniyar da bai masan inda kike ba don ya inganta gobensa, ba kekad'ai da ba kyanan ba hatta mu iyayenki da yasan muna nan ya wofantar damu ta hanyar tafiyarsa batare da saninmu ba, wannan shi kike tunanin har zai shiga wani hali idan aka rabaku.? Tir da wannan banzan tunani irin naki" tana gama fad'ar haka tafice d'auke da little da yayi bacci a hannunta Tunda tafara magana Rashida ta dasqare a inda take tsaye, shin Anya maganganun da gwaggon tata ke fad'a gaskiya ne ko a'a?, Ko kwanto tashigayi akan cewa habibyn nata zai iya tafiya acikin yanayin da ake na b'atanta kuwa?, Inaaa hakan bazai yuyu ba , tabama kanta amsa had'e da miqewa tana goge hawayenta, dole yau sai tahad'u da mijinta koda hakan na nufin za'a rabata da lumfashinta ne, dole ta qaryata d'ayar zuciyarta dake neman gasgata kalaman da gwaggo tafad'a mata. 'Dakin da anan ne aka bata tashiga ta d'auko mayafinta da sauri tanufi qofar fita gidan, kota halin qaqa yau tanada buqatar zuwa ta had'u da masoyinta kuma mijinta, sand'a tafarayi gudun kada taganta ta hanata zuwa har ta isa bakin qofar gidan Tana fitowa taci karo da Fatima aqofar gida ita da Dr ya kawota. Cikin farinciki Fatima tarungumeta tana fad'in "'yar halak ina zakije ne ko kema kinyi kewar tamune kamar yanda mukayi?" Ganin yanda idanuwanta sukayi jajir saboda kukan da tayi yasa Fatima cewa. "Subhanallahi, maman boy meyake faruwa?" Hakan yasa Dr fitowa daga cikin motar yana kallonta had'e da qoqarin rufe marfin motar, qarasowa wajensu yayi kafin yace. "Maman boy lafiya?" Yanda sukaga ta sake fashewa da wani kukan yasa Fatima riqo hannunta zata shiga cikin gidan da ita da sauri taja baya tare da tirjewa. "Don ALLAH uncle ku kaini naga ya Nuraddeen, Ina son ganinsa Ina so nahad'u dashi Amma su baffa sunqi amincewa," "Kamar ya Rashida?" Dr.nura ya tambayeta cikin rashin sani. "So sukeyi su raba aurena dashi uncle kuma Ina son mijina, bayada laifi, akan abunda yafaru amma gaba d'aya sun kasa fahimtar hakan! don ALLAH ko sau d'ayane kataimaka akaro nabiyu ka had'ani da mijina kamar yanda kahad'ani da iyayena." Maganar takeyi tana kuka had'e da game hannayenta waje d'aya, Alama yayiwa Fatima dasu shiga motar sannan yajuya shima yashiga had'e da tayarwa, hannunta Fatima tariqa tabud'e gambun bayan motar tasata ciki sannan tarufe itama tashiga yaja motar sukabar qofar gidan, "Ina muka nufa?" Ya tambayeta adaidai lokacin da suka fito qauyen. "Bebeji." Tabashi amsa ataqaice tana goge hawayen da suka jiqa mata fuska sharkaf, Tafiya mai d'an nisa sukayi kafin su iso gaba d'ayansu Babu wanda kecewa wani uffan, tuqi yakeyi da hannu d'aya, hannun d'aya kuma ya azoshi saman tagar qofar yariqe hab'arsa dashi ita kuma Fatima sai faman jujjuya kwalin wayar dake hannunta takeyi wacce dama itace dalilin zuwan nasu saboda kewarta da tayi mata yawa kullum cikin zancenta ita da little yasa Dr yasiyowa Rashida wayar don suriqa gaisawa sai gashi sun tarar da ita cikin wannan halin.Bini bini take juyowa takalleta cike da tausayi kafin Dr yamiqo mata wayarsa. "Kamomin Yaya maryam" Scrolling contact d'insa ta farayi har takai ga lambar Yaya Maryam da yayi saving da Ya Maryam kano takirata. Bugu d'aya ta d'aga muryarta a hargitse. STORY CONTINUES BELOW "Dr." "Na'am, anwuni lafiya.?" "Lafiya klw, yanzu nake zancen kiranka na nemi Rashida sama ko qasa narasa saboda nayi mata fad'a." "Karki damu tana tare damu, dama shine kiran dana yimaki." "Tirqashi Amma wannan yarinyar anyi shashasha, shine zata fita fisabillahi bazata fad'amun ba, gaba d'aya duk tabi ta tayarmun da hankali?." "Kiyi haquri, Bata kyauta ba gaskiya amma yanzun nan zamu dawo tare in Sha ALLAH." Kasancewar akwai cikakkiyar yarda tsakaninsu yasa bata damu sosai ba duk da abun ya b'ata mata rai, asalima gaba d'aya ranta bai kawo mata cewa Rashida zatayi tunanin zuwa tahad'u da Nuraddeen ba balle har ta taka da kanta taje garin nasu, Koda suka iso angama sallar isha'i suka samu gefen wani shago sukayi parking, Fitowa tayi cikin motar suma suka biyo bayanta har suka iso inda za'a iya hango gidan, "Inane gidan Rashida?" "Wancanne uncle." Tafad'a tana nuna gidan da yatsa. "To muje ko." "A'a uncle bazan iya ba, kawai ni shi kad'ai nake son nahad'u dashi." "Bari to naje nasa ayo mani sallama dashi.," Yafad'a tare da tunkarar gidan. Tsaye kawai take duk qafafuwanta sunyi sanyi tanaji tamkar basu imata, kallon anguwar takeyi d'aya bayan d'aya, Kafin tahango Yusuf tafe yanufo inda suke gefen wani tsoho dake saida kalanzir saman d'an teburinsa, "Lado abani kalanzir na naira ashirin?" "Ahhh... yusufa d'an gidan yayansa nura, Wai ina yashige ne kwana biyu nadena ganinsa.?" "Laah...ashe lado bakasan yaje qasar waje ba?" "Kai yusufa!, Kace wlh." "Wlh lado da gaske nakeyi." "Kai ALLAH ban yarda da kaiba, shi nuran d'an mahaukaciya ne da zaibar qasar nan bayan matarsa da tsohon ciki tab'ata, sai kace wanda bedamu da ita ba," "To ni kabani kalanzir d'ina kada innar mu tabugeni, ai sai katambyi mutane kaji, yanacan yaje k'aro karatunsa." "Tirqashi! Amma gaskiya be kyauta ba." Kukan da Rashida ke qoqarin dannewa ne yaci qarfinta had'e da kucce mata. Da sauri Yusuf daya miqa hannu zai karb'i kalanzir d'in da lado kemiqo masa suka d'ago kai tare jin kukan da suka jiyo agefensu. "Yaa rasulu manzon ALLAH, ke baiwar ALLAH lafiya.?" Lado yafad'a had'e da sakin kalanzir d'in yana kallon Fatima da Rashida dake tsaye hasken k'wan shago na yadosu, da hannu Yusuf ya shiga nuna Rashida don fuskarta bazata tab'a b'oye masa ba aduk inda tashiga, kasa magana yayi sai faman ja da baya yana fad'in. "Aun..aunt..auntyyy.." Yaruga aguje yabar wajen had'e da nufar gida yana k'walawa su baffa.... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [8/24, 10:40 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ STORY CONTINUES BELOW Page___59πŸ’Ž Baffa, baffa, baffa ga aunty tadawo, abunda Yusuf kefad'a kenan har ya isa bakin qofar shiga gida, karo yaci da mahaifin nasa wato baffa Ali shida Dr. nura dake qoqarin barin wajen fuskarsa a cunkushe babu alamun walwala atattare da ita, kad'an yarage Yusuf yafad'i garin kallon Dr nura daya ga yanufi inda su Rashida suke, da sauri ya riqo hannun baffa Ali yana jansa had'e da nufar inda ya gasu Rashida yana nuna masa wajen da hannu, gaba d'aya Yusuf ya rud'e ya manta da cewa ba mahaifinsa yakamata yasan da dawowar taba sanin irin matsayin da take dashi awurinsa. Baffa Ali kuwa binsa yayi har suka isa wajen lado mai kalanzir, lokacin kuwa har su Rashida sunbar wajen saboda irin amsar da Dr nura nura yazo masu da ita, "Lado Ina aunty?" "Kai yusuf wace aunty kuma?." "Haba lado! Anan fa nabarta ita da wata mata, nan wajen!." Yaqare maganar yana nuna masa inda suka tsaya. "Aiho nan naga sunbi suda wani mutum." Lado yafad'a yana d'aure ledar daya zubawa wata yarinya kalanzir. Dagudu Yusuf yabi hanyar baffa Ali shima yabi bayansa don yatabbatar da da hakan, Suna kawowa su Rashida naqoqarin shiga mota ya shiga qwala mata kira. "Aunty, auntyyyy.." Juyowa tayi tana goge hawaye harya iso wajen, da sauri baffa Ali yab'oye bayan wani kango yana hangosu don kada taganshi. "Aunty ina zaki tafi kuma, kizo muje gida don ALLAH, ya nura nason ganinki shida su baffa da Inna bilki, kowama nason ganinki munyi kewarki sosai don ALLAH kizo muje kinji aunty." "Yusuf me zanje inyo agidanku Bayan wanda nazo don shi gaba d'aya yabar qasar, zantafi Kuma bazan sake dawowa acikin gidanku ba saboda bakwa sona." Tafad'a tana kuka tare da juyawa zata shiga motar, riqe hijab d'inta yayi shima yana kukan yace. "A'a aunty muna sonki don ALLAH kada kitafi." Hannunta tasa tacire hannunsa daga riqon daya yiwa hijabinta sannan tafad'a cikin motar Dr. Nura yaja sukabar wajen. Kuka Yusuf keyi kamar ransa zai fita had'e da nufar hanyar zuwa gidan baffa, da sauri baffa Ali yafito daga mab'uyar daya shige yatare gabansa had'e da kamo hannunsa, "Kai Yusuf ina zakaje ne acikin daren nan?" Ya tambayesa had'e da d'aure fuska yana kallonsa. Cikin sheshshekar kuka Yusuf yace. "Gidan baffa zanje." "Kaje kayo ubanmi acan?." "Zanje infad'a masa Aunty tadawo amma ta tafi kuma tace bazata sake dawowa ba." Saida ya sakar masa wani mugun ranqwashi akai sannan yace. "To uban waye ya aikeka? idan Auntyn tadawo qanwar uwarka ce kota ubanka da zakaje kasanar dasu tunda tace bazata koma dawowa to meye naka aciki.?" Qoqarin bud'e baki yayi don ya bashi amsa sai Kuma yayi saurin rufewa da hannunsa sanadiyar yanda ya murd'e masa kunne so had'e da cewa. "Karka sake inji kafidda wannan maganar waje kaji nagaya maka, inba haka ba yanda Yaya hawwa ta b'addata kaima haka zansa a b'adda kai, kaga shikenan baka ba ganin kowa naka wata qilama kamutu gaba d'aya ahuta, shashashan yaro kawai, har kamanta akanta akaje aka kullemu ni da mahaifiyarka, babu kalar azaba da kuma dukan da bamu sha ba ahannun 'yan sanda kuma duk ta dalilinta, to bari kaji duk kasake naji wannan maganar abakin wani sai nayi maka d'an banzan duka kuma wlh kadena cin abincin gidana kenan har kamatu, shegen yaro da bansan halin waye kad'auko ba, maza kawuce gida kafin in jijjimaka anan" STORY CONTINUES BELOW Sosai Yusuf ya tsorata dajin kalaman da baffansa ya fad'a masa don haka yanufi gida yana kuka kamar ransa zai fita, kasa shiga d'akin mahaifiyarsa yayi yakoma saman barandar part d'insu ya Nuraddeen dake rufe ya had'a kai d guiwa yanaci gaba da kukansa, tun qarfe takwas yake zune wajen yana kuka har wucewar goma da rabi nadare kan kace me tuni zazzab'i ya taso masa ya fara rawar sanyi, Inna Bilkisu ce tafito zata zagaya bayi tagansa wajen a kwance had'e da cewa. "Kai Yusuf lafiya kazo nan ka kwanta ko sanyin nan bakaji?, Maza tashi kawuce d'aki kar mura takama ka" Ba tare data tsaya sauraren amsar da zai bata ba tawuce bayi don yin lalurar data fiddota, koda tadawo ta tarar har lokacin yana a wajen kwance ko motsawa baiyi ba daga inda tabarshi "Ikon ALLAH, wai bakaji me nace maka bane Yusuf.?" Tafad'a tare da qarasawa wajen tana d'agosa, yanda taji jikinsa ya gashe da zafi sai faman rawar sanyi yakeyi yasa tayi saurin rungumosa ajiki tana daddafa kansa. "Subhanallahi, Yusuf dama baka lafiya shine kazo nan ka kwanta." 'Dago kansa yayi yana qoqarin yimata magana saiga baffa Ali ya shigo shida baffa Usman, ai yana ganin haka da sauri yaqarasa wajen yana fad'in. "Kai Yusuf mekakeyi wajen? Ko munafuccin ne kaima zaka koya." Ya zata maganarce yake fad'a mata, Inna Bilkisu najin haka tacire Yusuf daga jikinta had'e da zaunar dashi saman barandar tanufi inda mijinta yake tsaye yana jinjina irin kalaman da d'an uwansa ke alqanta iyalinsa dasu, shi kuwa baffa qiiiii...yaja hannun Yusuf har yana neman fad'uwa yana fad'in. "Wannan yaron anyi mai kunnen qashi, ina dai kasan abunda nace maka shine zakazo nan kasaki baki don rashin jin magana" hed'e da jefasa saman gadonsu d'an bono bayan sun shiga d'aki, ••• ••• ••• Dr kuwa banda tunanin kalaman da baffa yafad'a masa babu abunda yakeyi, wannan wace irin rayuwace muke ciki aduniya?, Wanda ma kayarda dashi alokaci d'aya sai ya sauya maka, ancuci yarinya kuma ankoma ana binta da sharri, a iya saninsa inzai tuna Rashida tafad'a masa cewa mahaifin mijinta na qaunarta Amma sai gashi maganganun daya fad'a masa akanta sunsha banban da irin kalaman daya dace afad'a ga wanda ake so, saita madubinsa yayi yana kallon yanda hawaye ke tsiyayowa daga cikin idanuwanta dake rufe ya saki wata irin ajiyar zuciya, tabbas ta cancanci tayi kuka ba kad'an ba, ko kad'an bazai hanata tayi shiba awannan karon saboda abubuwan sunyi mata yawa, a qaramcin shekarunta bai kamata ace tafuskanci irin wud'annan damuwowin ba donma Allah yataimaka ansamu jininta yakoma normal da tuni qila zuciyarta tabuga, duk da dai bai sanar da ita gaskiyar abunda yafaru tsakaninsa da baffa Ali ba daya nuna masa cewa shine mahaifin Nuraddeen, kawai dai ya fad'a mata cewa ance baya nan yabar qasar. Tare suka shiga gidan da ita lokacin da suka iso yaya Maryam na tsaye tsakar gida tana jijjiga little da sai faman kuka yakeyi tun d'azu. Miqa hannunta tayi ta karb'esa kanta naduqe aqasa batare data bari sun had'a ido da yaya Maryam ba data zuba mata ido tana kallo. 'Daki tawuce, su kuma suka tsaya suna gaisawa da ita, "Sannu Dr har kin dawo.?" "Eh ya gida yaya Maryam." "Gida Alhamdulillah Dr, kunbarni da yaro sai faman tsula Mani kuka yakeyi?" Murmushi yayi had'e da cewa. "Afuwan ai gamu mun dawo, dama kwana biyu Fatima tadameni da zancen ta shine nace bari muzo dubata sai gashi munci karo da ita, ganin babu alamun walwala atattare da fuskarta yasa nace bara muje da ita wani wurin taraka mu, I fatar za'ayi mana afuwa bisa wannan kuskuren?" Yafad'i hakanne saboda yasan ran Yaya Maryam b'aci zaiyi idan tasan gaskiyar inda sukaje. "Ba komai Dr, ai kaga Fatima gaisawa kawai mukayi tabi bayansu saboda sukad'ai tadamu dasu" Shiru yayi na tsawon wasu 'yan sakanni kafin yace. "Amm! Dama yaya maryam cewa nayi yakamata ariqa kwantarwa da Rashida hankali saboda yanayin damuwowin da suka tarar mata azuciya don kar takoma shiga wani halin, nasan kuna qoqari sosai tunda gashi naga cikin kwanakinnan tacanza ba kamar yanda muka zoba saboda yanayin natsuwar da tasamu, amma don ALLAH aqara bata kulawa, sha'aninta akwai bantausayi aciki sosai." "Ikon ALLAH!, Ai dama nasan dole qara tace zata kai wajenka Dr tunda muna ganin mutuncinka, yakamata ace rashida ta fahimci abunda muke guje mata faruwarsa saidai takasa gane hakan..." Nan takwashe komai tafad'a masa akan abunda yafaru ba qari balle ragi, sosai Dr yashiga rud'ani daya auna maganganun guda biyu, da wud'anda baffa yafad'a masa da kuma na yaya Maryam yagano akwai wani abun aqasa wanda ba daidai ba, ko meye kuma ALLAH kad'ai yasani." Haquri yabata tare da sake roqonta a lallab'ata in Sha ALLAH da sannu zata fahimcesu sannan ya koma bakin motarsa yana jiran fitowar Fatima. Rashida kuwa saida taba little nono yasha ya qoshi Fatima na gefenta tana dad'a bata haquri tare da rarrashinta sannan tamiqa mata shi ta kwanta saman qatuwar katifar dake cikin d'akin nata, anan maganganun da suka faru tsakaninta dashi a daren ranar suka shiga dawo mata a kwakwalwa, tabbas ita ta qarfafa masa yin wannan tafiyar kuma ko kad'an hakan da yayi ba laifi bane, Amma meyasa ya aikata hakan batare daya sanar da iyayenta ba.? Meyasa baiyi tunanin abunda zai iya faruwa ba akan wannan kuskuren da yayi, kamata yayi ace ya fahimci cewa komai na duniya kan iya sauyawa idan aka samu sauyin al'amurra, kama daga ra'ayi, buqata, lafiya, wajen zama da kuma yanayi na yau da kullum, gashi yanzu yaje yabar baya da qura, babbar damuwarta shine rashin sanin har tsawon wane adadin lokaci zai d'auka kafin yadawo. Jitayi Fatima nafad'in "maman boy zamu tafi, yana waje yana jirana, don ALLAH kimaida al-amurranki agaresa kidena kukannan bayada amfani, ga wannan wayace uncle d'inki ya siya maki zamu rinqa magana, akwai lambata da tashi aciki kuma na saka maki ta yaya maryam data aunty marwiyya saiki kirasu, kada kiyarda inkira injita akashe, ko yaushe ina son ki kasance tare da ita kinji ko?." 'Daga mata kai tayi sannan tajuya zata tafi tana d'auke da little. "Au! yau babu rakiya maman boy?" Ta juyo tana kallon rashida dake qoqarin tasowa alokacin. Har bakin mota ta rakata tare da yiwa Dr.nura godiya sosai tamiqa mata Little sannan suka wuce... _Darasi: 'yar uwa ki guji aikata laifi komai qanqantarsa domin bakisan iya adadin mutanen da Zaki iya cutarwa ba ta dalilinsa, wanda hakan kad'ai na iya zamowa dalinlin tsanantar hukuncinki awajen ALLAH, domin shi mai yafe haqqinsane amma banda haqqoqan rayukan da kika cutar, laifi d'aya yaya hawwa ta aikata akan rashida amma mutane da yawa sun cutu adalilinta, ciki kuwa harda qaramin yaro (yusuf) dake fuskantar damuwa da kuma barazana ta dalilin hakan._[8/21/2020, 8:13 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___56πŸ’Ž Saida suka gama shaqiyancin su day izgilanci tukuna suka baro wajen, A hankali Inna Bilkisu ta tako zuwa bakin rumfar d'akinsu suna qoqarin shiga d'aki jikinta a sanyaye tace. "Ruqayya, Ali kuji tsoron ALLAH, duniyar nan da kuke gani batada tabbas, shin ashe halin da Yaya hawwa take ciki bai isa yazame muna aya da kuma darasi ba?, Karku manta tare da muke zaune da ita acikin gidannan, itama mutumce kamarmu amma ALLAH yajarabci rayuwarta tahanyar komawa a cikin wannan yanayin da take ciki wanda muma bamufi qarfin ALLAH ya jarabcemu fiyema da yanda muke ganinta, I zuwa yanzu ya kamata ace mudukanmu munyi karatun ta natsu, mu zamo tsintsiya mad'aurinmu d'aya duk abunda yasamu d'ayanmu mu d'auka mu yasama kuma mu wa'aztu domin wannan halin da take ciki wlh iznane agaremu."+ "To jikanyar limamai, Ina ruwanki meya shafeki da al'amarinmu?, Dama akace maki ke muke tsoro da zakizo kice muji tsoron ALLAH?, Ke nifa bilki bana son sa ido kiyi sha'aninki kibarmu muma muyi namu, yo Ina ruwanmu da halin da take ciki ai haukane ba'agareta farau ba kuma ta cancancesa, wlh Banda ALLAH ya isa tsakaninmu da ita bisa abunda taja akayi mana Babu abunda zamuyi mata, aikin banza in wa'azi kike son yi to jeki kiyi mata ita dake d'auke da haqqoqan mutane akanta take damunmu da kuwace kuwace tana hanamu bacci." Inna ruqayya tafad'a tana harararta, tsaki baffa Ali yaja had'e da juyowa yana kallonta cike da takaici yace. "Ke Bilki, mufa yanzu babu ruwanmu da al-amarin kowa agidan nan don haka kifita harkarmu, baruwanki da duk abunda zamuyi koda kuwa kafirci ne, kabarinki daban namu daban kinajina ko!" Jinjina kai Inna Bilkisu tashigayi kafin tace "Wal'iya zubillah, Ali meyakawo wannan zancen, ai _inni laku minnannaasihin (ni kawai agareku mai nasiha ce)_ ubangiji ALLAH kashiryemu kuma yabaku haquri." Tana gama fad'an haka tajuyawarta tabar wajen tana maijin takaicin halin da suke ciki. Muneera kam tutse baki tayi tana susar kai tace. "Inna wai meyasa kuke yima Inna Bilkisu haka?, ALLAH tanada kirki kawai don baku gane bane, amma lokacin da kuke rufe wajen 'yan sanda ALLAH duk ita take kula damu tana bamu abinci." A hasale Inna ruqayya tayo kanta tana fad'in "Ke dallah rufemun baki, akace maki donku takeyi, duk wata maqarqashiyar rufemun da akayi ai da had'in bakinta ita da baffanninku, ai kinga kuwa dole su baku abinci ko don gudun duniya tazagesu." "Kai Inna, ALLAH ba haka bane, ai mukad'ai ke zaune dasu ina duniyar take balle ta zagesu, kawai kice keda baffana bakwa son gaskiya kuma wlh sai anyi maku irin na inna hawwa idan baku dena ba, ni Babu ruwana, abunda ma nece mata (banqararriyar kaza) wlh da gaske ni haka naga takoma." Kanta baffa Ali yayi da wani icce dake gefensa tafice da gudu daga gidan tana susar kai... ••• ••• ••• Baba da umma kuwa suna zamansu hankali kwance Babu wanda ke takurasu, gwargwado suna cin mai kyau kuma suna shan maikyau, hakama alhaji naqoqarin ganin ya kyautata masu saboda su samu kwanciyar hankali da natsuwa kuma Alhamdulillah ba laifi sun d'an fara ragewa kansu damuwa, wasu lokutanne kawai take bijiro masu idan suka tuna da 'yarsu sai 'yar matsalar hajia nafeesa dake musgunawa umma tahanyar yawan baqaqen maganganu da tsawar da take yimata duk kuwa da taka tsantsan da takeyi da ita, ga Rashin kunyar da yaranta keyi wanda shike sakesa hajia nafeesa fitina idan aka qiyi masu yanda suke so. STORY CONTINUES BELOW Yauma umma na kitchen tsaye tana jiran albasar data yanka acikin ruwan mai tasoyu sannan tazuba kayan miyan da zata dafa jallof dasu sai ga yaronta d'an shekara goma mai suna Shakur ya shigo, dube dube ya farayi cikin kitchen d'in kafin yace. "Ke umma zuba mun abinci." "Yi haquri Shakur abincin bai ida nuna ba." "Nidai kizuba mun haka zanci." "A'a bari dai nahad'a maka qanzon nan naturawa (cornflaks) kafin ka qarasa sha nagama kaji ko." Bubbuga qafa yafarayi zai b'are mata baki da kuka tayi saurin jawo plate ta zuba masa shinkafar data yiwa per boiling gudun kada kukan nasa ya jaxa mata walaqanci awajen mahaifiyarsa, "Ungo gashi" tafad'a tana miqo masa plate d'in farar shinkafar data zuba man da take soyawa da magi mai star akai yanda zaiji dad'inta ya karb'a yawuce abinsa. A daidai saman inda dining table ke ajiye yaje ya zauna qafafuwansa na reto a qasa ya fara cin abincinsa hankali kwance ko d'an sauran qarfin shinkafar daya rage tanuna baya ji tunda yunwa yakeji. Jim kad'an hajia nafeesa tafito cikin wani material mai shegen kyau yasha d'unkin riga bubu waya laqame akunnenta tana takawa d'ai d'ai, da alama wayace takeyi da wata, idanuwa ta qwalalo awaje hango d'an tsakiyar ranta wato Shakur yana cin shinkafar da kallo d'aya zakayi mata kasan Bata dahuba saboda yanda take tsaitsaye, wajensa taqaraso ta d'auke plate d'in dake gabansa tana fad'in. "Ina zuwa hajia hafsat, zankira daga baya." "Kai shakur a ina kasamu wannan?." "Momy a kitchen ne nasamu." "Waya baka?" "Umma mai aiki..." Tun kafin yarufe baki tashiga qwallawa umma kira da qarfi, umma najin haka tasan a fusace take. Tsoron qasqanci da walaqancinta yasa umma fitowa da sauri alokacin da tasake kiranta tana fad'in. "Na'am hajia, gani." Jeho mata plate d'in da sauran shinkafar tayi ya bugi goshinta sannan yafad'i qasa duk shinkafar ta wawwatse mata ajiki. "Har ke waye da zaki bawa yarona abinci gaya babu miya kuma d'anye wanda be nuna ba, ke wace nake tambayarki?" Hajiyar tafad'a a tsawace. Qasa umma tayi da kanta saboda batajin duk qasqancinta zata iya sa'insa da matar dako sa'ar qanwarta mawiyya batayi ba. Masifa tashigayi inda taka shiga ba nan take fita ba har tan fad'in umma tadena ganin tagirmeta zata iya zabga mata mari akan yaronta wai so takeyi takashe mata shi shiyasa tabashi d'anyen abinci salon cikinsa ya kumbure masa, cikin fushi tace. "To wlh maza ki tattarata ki kwashe kuma sai kin zauna anan gabana kincinyeta tas kamar yanda kikasa yarona yacita." Haka tayita masifa da ita har alhaji dake tsaye a harabar gate shida wani abokinsa suna magana yajiyo harshen nata, hakan yasa yayi cikin gidan ransa a d'an b'ace da zimmar yimata magana ya tadda umma durqushe a gabanta tana kakkab'e shinkafar dake jikinta had'e da qoqarin tattara wadda ta zube qasa ita kuma tana tsaye kanta tana faman jijjiga jiki, motsin da taji ya sata juyowa tana kallonsa had'e da cewa. "Yawwa qwanda daka shigo ka ganewa kanka abunda tayi, irin wannan iskancin da sukeyi kesa kake ganin kamar ina wulaqanta 'yan aiki, farar shinkafa na isko fa taba Shakur ko nina batayi ba salon taja masa wahalar da zata kashesa, musamman idan ta kumbura masa ciki." "Sai ke kuma kika yimata me?" yatambaya ransa a b'ace." "Shine da raina yab'aci nawatsa matashi kuma nace ta tattarar dashi ita tacinye." STORY CONTINUES BELOW "Ok. Ni ina wahalar samo abinci ke kina zubarwa qasa, shikenan umma ajiye ki tashi wajen." Yafad'a tare da matsowa wajen ita kuma umma takoma gefe ta makure, "Duqa ki tsincemun abina tas ki miqomun keda kika watsar dashi." Yace ma hajia nafeesa tare da nufar inda shakur yake zaune. Sanin halinsa yasa hajia nafeesa duqawa tsince abincin tana hararar umma tana kumbure fuska sai kace wacce aka hurawa mabusa. Riqo hannun shakur yayi had'e da cewa. "Shakur d'in baba ya akayi kake cin waccan shinkafar haka?" "Abba yunwa nakeji kuma umma bata gama abinci ba da nace tazubomun haka sai tace inbari ta had'amun cornflakes shine nace bana so da taga zanyi kuka sai ta zubomun a haka saboda nace zanci." "Bakasan cin shinkafa have done zata iya kumbura maka ciki ba." "Abba bazata yimani komai ba yunwa nakeji." Daidai lokacin hajia nafeesa tagama tsincikke shinkafar tazo tamiqo masa tana faman cika da batsewa, Murmushi yayi sannan ya karb'a ya ajiyewa Shakur agabansa yace "Ungo kayi bisimillah ka qarasa canye abinka kaji ko, Amma kada kasake yin haka Babu kyau." "Alhaji fa yayi qasa." Hajia nafeesa tafada kamar zatayi kuka. "Eh yaci babu abunda zai yimasa in sha ALLAH, Ina kinsan da haka amma kikace ita tacinye sa ko." Juyawa yayi yana kallon umma yace. "Umma kiyi haquri, kuma daga yau bazaki sake yin aiki agidannan ba." "A'a alhaji kada ayi haka, indai akan wannan ne babu komai zanci gaba dayi, bana son na zaunane waje d'aya, nafi son ind'an dinga mommotsa jikin." "A'a baza'ayi haka ba, aishi d'an adam daraja ne dashi yakamata ace angirmamashi musamman wanda ya girmeka, walaqanci bayada dad'i ko kad'an don haka kije zanyi magana da hajia fareeda sai ki koma acan b'angarenta inaga zaifi tunda kinfiso kina motsa jikin naki." "To shikenan alhaji ngd, bari na qarasa wannan girkin." "A'a umma kibarshi ita zata qarasa da kanta." Da qarfi hajia nafeesa ta d'ago kai tana kallonsa yayin da umma tafice daga part d'in tana godiya ga ALLAH daya kawo alhaji ya kub'utar da ita daga cin mutuncin da tayi niyar yimata kuma ya yaye mata damuwar zama da ita da kalolin walaqanci da cin kashin da takeyi mata. Jinjina mata kai yayi idanuwansa acikin nata alamun da gaske yakeyi sannan yace. "Kuma ba wannan girkin kad'ai zaki ida da kanki ba, daga yau nayi maki alqawarin babu wata macce da zata koma zama part d'inki da sunan yi maki aiki har sai lokacin da kika canza kuma kika san darajar mutane, don haka ya rage wajenki kidafawa kanki da yaranki abinci ko karki dafa duka ruwanki, wannan shine hukuncin dana yanke akai, idan kuma kikak'i ji to wlh kinji na rantse bakyaqi gani ba. Yana gama fad'ar haka ya juyawarsa ya fice, dama tuntuni yake son d'aukar mata mataki akan cin zarafin da take yiwa bayin ALLAHn dake qarqashinta ALLAH bai bashi iko ba sai yau. *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [8/21/2020, 11:20 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž STORY CONTINUES BELOW *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___57πŸ’Ž ••• ••• ••• Sosai wan saheke Rashida tasamu sauqi zuwa azahar aka basu sallama, kai tsaye gidan Yaya maryam aka nufa da ita duk da baba balarabe yaso ace gidansa zata zauna, Amma ganin yanda Yaya Maryam d'in ta kafe kai da fata lalle wajenta zata zauna yasa ya haqura tunda itace yayarsa babu yanda zaiyi, Tunda Rashida ta bar gida yaune karo nafarko da taji tana son had'uwa da mijinta wato habibinta mahaifin d'anta Nuraddeen, suna kan hanyarsu ta zuwa gidan Yaya maryam da yake Dr nura ne ya d'aukosu a mota, Fatima na gefensa riqe da little sai Yaya Maryam da aunty marwiyya da ita Rashida abaya, shi kuma baffa mijin Yaya maryam ne ya d'aukosa saman mashin d'insa suka biyo bayansu, takalli aunty marwiyya tace. "Aunty ya nura fa?" Wata uwar harara ta zabga mata had'e da juyar da kanta gefe, ganin haka yasa ta kama bakinta har suka isa gida, Dr nura nayin parking su baba balarabe dake biye dasu na tsayawa da mashin d'insu, Yaya Maryam ce tafara fitowa sannan aunty marwiyya suka nufi cikin gidan, hakama Fatima itama tafito tare da riqo hannun Rashida dake qoqarin fitowa tayi mata jagora sukabi bayansu, A can cikin gida aunty marwiyya tafara fad'a tana fad'in. "Yaya wannan yarinyar batada hankali, kinji tambayar da takwyimun a mota wai ina ya nura? Wlh badon batada lafiya ba da saina d'auketa mari don ko sunan garinsu bana sonji balle sunansa." "Hmmm banni da ita marwiyya Ina jinta, bi izinillahi ko shikad'ai ya rage namiji aduniya bazata koma gidansa ba, ai tunda haka tafaru to ta tabbata komai mahaifiyarsa zata iya yimata saboda qiyayyar da take yimata kuma mu shedane akan haka, shikenan kuma don muna sakarkari sa mubarta takoma masa a kashe mana ita, narantse kozai mutu sai yasaketa tunda ba ita kad'ai bace macce aduniya ba." "Wannan shine daidai Yaya Maryam, in yaso yaje can uwarsa ta aura masa wacce take so." Aunty marwiyya tafad'a a qufule. Tana rufe baki suna shigowa, ta sakarwa Fatima murmushi had'e da cewa. "Wucikke matar Dr." Batare data kalli inda Rashida take ba. A falo suka shiga suka zazzauna kafin mijin Yaya maryam yashigo shima su Dr da baba balarabe nabiye dashi abaya. Bayan sun zauna Yaya Maryam tamiqe taje takawo masu ruwa da lemuna masu sanyi da 'yar sauran samosar data had'a da safe da take sayarwa ta ajiye masu, "Balarabe kutab'a wannan kafin kuwuce." Saida suka fara tab'a hira ana tayiwa little da Fatima ta ajiye tsakar falo yana faman yimasu qyaqya dariya sannan tamiqe taje ta d'ora masu dahuwar taliya da kifin gwangwani ga 'yar qaramar tukunyar gas cooker d'inta saboda tayi saurin nina, ai kuwa cikin mintotan da basu wuce goma ba ta nina ta zuzzubo a flate ta kawowa kowa, sake d'auko had'ad'd'en zob'onta na siyarwa da takeyi tayi ta kawo masu sannan itama ta zauna tana cin nata, "Kai amma zob'on nan yayi dad'i yaya maryam ya akeyinsa?" Fatima tafad'a tana sake kai cup d'in zob'on abaki. "Kai matar Dr Banda zolaya, zob'on na siyarwa?" "Eh mana, gaskiya kina gyarasa sosai, ai wannan zob'on ko shugaban 'yan hasada yasha dole ya yabashi balle masu so da gaske." Dariya duk suka samata harda Rashida da tun d'azu takasa kai koda cokali d'aya abaki sai faman cakularsa takeyi, "Hmmm! Yakamata nabiya kud'in zobonnan tunda yasa madam Santi har na tsinkayo ana yimata waigi." Dr nura yafad'a yana dariya ganin aunty marwiyya na gyarawa Fatima hilon dake bayanta, juyowa tayi had'e da cewa. STORY CONTINUES BELOW "Au..Ashe da gaske yakeyi, kai aunty marwiyya zakija yadinga tsokanata kuwa." Kallon Rashida baba balarabe yayi had'e da d'aure fuska yace. "Ke Rashida maza kici abinci kinji ko?" Ganin bada wasa yakeyi ba yasa tafaracin abincin tana b'ata fuska tamkar wacce keshan magani. Yanda su Dr suka saki jikinsu cikin 'yan uwan Rashida Kai ka rantse kace Abu d'aya suke ko kuma sun jima da sanin juna, hakan Kuma ba qaramar shaamquwa da yarda ta sake shiga tsakaninsu. Bayan kowa yaci yasha ya qoshi, baba balarabe yayi gyaran murya had'e dayin doguwar addu'a da nasihohi masu ratsa jiki bisa abunda ya faru sannan yarufe dayiwa su dr.nura shida matarsa godiya sosai shida su Yaya Maryam, irin godiyar da suke yimasu da kyawawan addu'o'i had'e da fatan alkhairi har seda suka fara jin kunya, daga qarshe aunty marwiyya tace. "Mungode sosai Fatima matar nura uwar nura, muna roqon Rabbissamawati wal ardi daya azurtaku da 'ya'yaye nagari masu albarka da zakuyi alfahari dasu duniya da lahira, ALLAH yakareku daga dukknin sharrin abinqi ya lullub'eku da rahamarsa da tausayinsa yayi maku arziqi mai yawa ya share maku dukkanin kukanku." "Amin ya ALLAH aunty." Suka amsa cike dajin wani dad'i da sanyi da farinciki azuciyarsu, Itama Rashida hawaye nazubar mata a idanuwa ta rungume fatima tana fad'in. "Dukkanin alqawurranku agareni wanzazzune hakama alkhairanku tabbataccine akaina, karamcinku da halacci masu girmane da mizaninsu yakai girman da bazan iya biyanku aduniya ba, amma har zuwa fitar lumfashina zuciyata da Kuma rouhina cike da qaunarku mai tsanani take, duk wani fitar lumfashi nawa cike yake da fatan alkhairan ALLAH agareku da kuma farinciki mai d'orewa, ina roqonku da kada kucireni acikin rayuwarku kada kumanta dani kubani damar da zan iyaci gaba da rayuwata tare daku matsayin 'yan uwa batare da zumunci ya yanke a tsakaninmu ba har izuwa ranar da zan kwatanta faranta maku zuciya kamar yanda kuka faranta tawa data ahalina koda sau d'aya ne." "Bazamu mantaki ba Rashida, bazamu rabu dake da little ba don kunzamo wani yankin daya sama mana farinciki na wani d'an lokaci arayuwarmu wanda muke fatan yatabbata atare damu har abada" Fatima tafad'a itama had'e da rungumeta tana kuka, kuka sukeyi sosai sai kace wud'anda suka rabu kenan har saida Dr nura ya cewa Fatima ta taso sutafi yana mai mamakin yanda shaquwa mai tsanani haka tashiga tsakaninsu a qanqanen lokaci, 'Daukar little tayi ta sumbacesa agoshi tare da wucewa gaba suka rakosu qin miqasa tayi har saida ta shiga mota Dr nura na Shirin tayarwa sannan ta badashi tana goge qwallan da suka zubo mata, shi kanshi Dr nura saida yaji ba dad'i Amma babu yanda suka iya dole yaja motarsa sukabar wajen. Su kuma yana tafiya rigima ta kaure tsakanin baba balarabe da yace a dole akira Nuraddeen da ahalinsa asaanar dasu yayinda sukuma su aunty marwiyya sukace atafau bazai yuyu ba, daga qarshema Yaya Maryam bugawa Rashida tsatsauran Jan kunne tayi akan karta sake koda mafarkine tayi tunanin zata koma gidan Nuraddeen tunda mahaifiyarsa bata sonta. Shikuwa baba balarabe duk da Yaya Maryam na sama dashi haka yatabbatar mata da cewa dole sai yasanar da Nuraddeen anga matarsa saboda haqqinsane kuma har lokacin tana aqarqashin igiyar aurensa, hakan yasa suka rabu baran baran, rayuwakan kowanensu a b'ace. Yana komawa gida yashiga Kiran lambar baffa data baffa Usman Amma shiru kowace switch up, hakama ta Nuraddeen yakira yafi a qirga itama akashe saboda bai fara anfani da sabon layin daya siya acan. Hakan yasa hankalinsa tashi sosai marece nayi yanufi garin bebeji, yana isa yaci karo da baba Ali ya tsaya yana tambayarsa, sunjima suna magana kafin baba balarabe yabar wajen jikinsa a sanyaye, wata 'yar iskar dariya baffa Ali yayi sannan yawuce yana fad'in "da sannu duk sai kun gane kurenku har ita wacce sanadiyar b'atanta aka rufemu nida iyalina aka yimana dukan mutuwar da gangar jikinmu takasa d'auka" STORY CONTINUES BELOW Kwana baba balarabe yayi yana juyi akan abunda baffa Ali ya sanar dashi duk da dai wani b'angaren na zuciyar tasa bai yarda da hakan ba. ••• ••• ••• Su Baffa kuwa a maimakon kwana d'aya da zasuyi agarin sokoto sai da sukayi kwana biyu saboda shawarar da wani likitan yabasu akan sukai marar lafiyarsu kware shine abunda zaifi masu sauqi, hakan yasa suka sake kwana d'aya acan har saida suka gama shirya duk abunda yakamata acan asibitin kware suka biya kud'in da za'a basu mota da jami'an lafiyar da zasu d'aukota sannan suka juyo zuwa gida bayan sun bada address d'in da za'a tura masu motar nan da kwana biyar, gaba d'aya wayoyinsu sun mutu saboda rashin charji da basuda wannan ne dalilin da yasa baba balarabe yayita kiransu bai samu ba. Saida suka iso zamfara don dama motar da zata ajiyesu acan sai daga nan su shiga wacce zata kaisu kano suka shigo kafin motar da suka samu ta kano ta cika suka shiga masallacin dake cikin tashar sukayi sallah sannan suka samu wani saurayi ya ara masu chargarsa sukasa wayar baffa charji, minti talatin sukayi sannan motarsu tacika lokacin baffa har yasamu d'igo biyu a 'yar wayar tasa qirar kamfanin itel mai madannai. Mintuna biyu yayi da kunnata kiran baba balarabe ya shigo. Cikin natsuwa baffa ya d'aga had'e da amsa sallamar da yayi masa sannan suka shiga gaisawa. "Am dama wata magana naji cewa Nuraddeen yabar qasar nan shine nace bari nakira naji shin ko gaskiya ne.?" Wani irin nauyi baffa yaji Amma bayada wata hanyar da zai iya basa amsar tambayar da yayi data wuce eh ko kuma a'a, tamkar baffa nagabansa ya duqar da kai had'e da cewa. "Eh malan balarabe hakane amma..." Kafin yaqarasa baba balarabe ya katsesa ta hanyar cewa. "To madallah, shikenan nagode." Had'e da kashe wayarsa, duk inda ransa yake in yayi dubu ya b'aci, Ashe akwai ranar da Nuraddeen zai nuna irin wannan halin ko inkula agaresu adaidai lokacin da suka rasa 'yarsu a hannunsa, Ashe har yanada qwarin guiwar da zaya iya barin gari acikin yanayin da yake kuma har yatafi batare daya yimasu sallama ba?, Me suka yimasa da suka cancanci haka daga wajensa? Ai koba komai ana bankwan saboda ba'asan halin rai ba, kuma ai yakamata ace ko don kaucewa zargi yazo yayi masu bayani, wud'annan tambayoyi sune suka dinga Kai da komo acikin zuciyarsa da kuma qwaqwalwarsa, rashin samun amsar sune yasake tunzurasa sosai, Ransa ab'ace yanufi gidan Yaya Maryam yakirata tare da zayyane mata duk abunda kefaruwa, dama tayi mamakin ganinsa shida jiya suka rabu baran baran da ita sai gashi har yana fad'in ko mijin Rashida naso ko baya so duk inda yaje dolene ya saketa, kuma dole duk wata alaqa dake tsakaninsu su datseta koda hakan na nufin zasu mayar masa da d'ansa a hannun sane. *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [8/23/2020, 10:36 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___58πŸ’Ž Shiru Yaya Maryam tayi na tsawon daqiqu uku kafin tace. "Hakan shine daidai, dama abunda nayita qoqarin lurar dakai kenan ka kasa ganewa, to amma batun cewa za'a mayar masu da yaro don yanke duk wata alaqa dake tsakaninmu kabarta don ni gaba d'aya bana buqatar jinmu yakoma zama atare dasu tunda basa da zuciyar imani." STORY CONTINUES BELOW Sun jima suna tattaunawa kafin yabar gidan har lokacin yanajin d'aci akan maganganun da baffa Ali yafad'a masa. ••• ••• ••• Baffa nagama waya da malan balarabe yakalli d'an uwan nasa ya sakar masa murmushi cikin qarfin hali sannan ya juyar da kansa gefe, yana maimaita innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun aransa. Dafa kafad'arsa baffa Usman yayi had'e da cewa. "Meke faruwa ne Yaya?" "Abunda Nuraddeen yayi gudun faruwarsa." Yabashi amsa had'e da juyowa suna fuskantar juna. "Kayi haquri Yaya, dama dole hakan zata faru, mu auna kanmu a matsayinsu mugani, don haka dole zamu lallab'asu har su fahimcemu, ayanayin yanda damuwowi sukayi masu yawa kamarmu, abune mai wahala su iya riqe fushinsu alokacin da sukaji labarin tafiyarsa musamman idan sun jine daga bakin daya kasa yimasu kyakkyawan bayanin da zayasa sufahimta, shi kuwa rashin bayani acikin kowane al'amari shike haifar da husuma da kuma aikin dana sani, don haka dole muyi haquri har zuwa lokacin da zasu fahimcemu." "Shikenan Usman, amma duk da haka mufara jaraba zuwa wajensa idan mun sauka." Awa hud'u ta d'aukesu kafin su isa kano, ana ajiyesu tasha suka sake shiga motar da zata kaisu qauyen na yarimawa, cikin qananan daqiqu suka isa sukaci sa'a kuwa yana zaune bakin gida yana arwala suka yimasa sallama, bai amsa ba har saida ya gama arwalarsa ya d'aga kansa sama yayi addu'ar da akeyi bayan gama arwala sannan ya kallesu fuskarsa a sake ba yabo ba fallasa ya amsa masu salamar. "A'a malan Idris, malan Usman sannunku da zuwa yanzu kuke tafe?." Yafad'a yana qoqarin ajiye butar da yayi arwala agefe, kallon baffa Usman baffa yayi kafin suji ya sake cewa. "Kai Hassan kushiga ciki ku kawo ruwa a butoci magrib taqaraso ana batun tada sallah." "Am sannunku da zuwa bari naqarasa masallaci kafin ku iso liman na batun tayarwa." "To shikenan!" Baffa yafad'a cike da mamaki a fuskarsa. Basu sake Shan mamaki ba sai da suka fito sallah suka tarar da tabarma an shimfid'a a qofar gida da kwanonin abinci, "A'a malan Usman ya akayi kukayi tsaitsaye? bisimillah kuzo kuzauna mana, Gaggaisawa suka shigayi kafinsu baffa sufara qoqarin canza maganar izuwa asalin wacce takawosu, Amma ga mamakinsu sai sukaga kawai yajawo kwanoni abinci yana fad'in bisimillah malan idris muci abinci ko." Babu yanda suka iya saboda yanada matuqar muhimmanci agaresu da bazasu iya yimasa musu ba, wanke hannayen su sukayi sukasa suka fara cin abincin tare har suka qare, Bayan sun kammala, baffa yace. "Don ALLAH malan balarabe kayi haquri ka sauremu, nasan an aikata maku ba daidai ba, amma kuskurene da babu wanda ya isa ya kauce masa, tabbas Nuraddeen yabar qasarnan saidai bada son ransa ba, nine natirsashi ganin yana shirin ruguza rayuwarsa, kuma dama ce wacce yasamu tun kafin wud'annan matsalolin su faru, ganin ba lallai bane ya sake samun wannan damar ba kuma ga yanayin da yake ciki yasa daya tirje akan babu inda zaije saboda yana tsammanin dawowar matarsa garesa wanda abune gaibi akan dawowarta yasa natilasta masa zuwa koya fita daga cikin halin damuwar da yake ciki." "Hmmm malan Idris kenan!, Ai bance kunyi wani laifi ko kuskure ba, meye laifinku don kunyi qoqarin inganta rayuwar d'anku?, Meye laifinku don kunyi abunda zai sakaku cikin farinciki?, Ba kuda wani laifi don haka kumanta da komai, fatana d'aya muma ALLAH yabamu ikon d'aukar darasin da kuka koyamana muma mu inganta rayuwar 'ya'yanmu kamar yanda kukayi koma fiye da hakan.?" Duk iya qoqarin da sukayi wajen ganin sun lurar dashi ya fahimci gaskiya hakan ya cutara daga qarshema cewa yayi. "Don ALLAH da girmansa malan usman mubar wannan magana kada tajawo rugujewar sauran mutuncin dake tsakaninmu, d'anku dai ALLAH yabashi ilimi mai albarka mukuma ALLAH yatsare mana 'yarmu aduk inda take yabata juriyar shanye duk wani abu da zai nemi duqufar mata da farinciki." STORY CONTINUES BELOW "Amin" suka amsa masa dashi bayan sun sake bashi haquri sannan suka wuce zukatansu a dagule. Bayan suntafi yakira Yaya Maryam lokacin tana zaune itada Rashida tana bawa little da sai qara wayau yakeyi nono, "Na'am balarabe ya akayi? Duk lafiya dai kuke ko?" "Lafiya klw Yaya, dama iyayen yaronnan mijin Rashida ne sukazo bada haquri...." "Kaga rufemun babinsu bana son ji, ai Ina mumuka haifi aburmu kuma muka bashi aurenta ko! don haka yanzu mun raba, ko suna so ko basa so yazama dole yabawa Rashida takardar ta, bazata koma gidansa ba ko mutuwa zaiyi, shashancin baza da wofi." Yaya Maryam ta katsesa tana masifa, Wata irin zabura Rashida tayi had'e da miqewa tsaye da kad'an little yafad'i, Yaya Maryam tayi saurin riqosa had'e da kashe wayar tana binta da wani mugun kallo mai cike da tarin tambayoyi, hankalinta atashe takalleta tana fad'in "Mekike fad'a haka gwaggo!," da yake da haka suke kiran sunanta sannan taci gaba da cewa. "Wai wa ake zancen zai sakeni?, Duk fa iya adadin kwanakinnan dana d'auka zuciyata cike take da mararinsa, idanuwa da kunnuwana cike suke da son ganinsa da kuma jinsa, kawai nayi shirune saboda kada kuga rashin kunyata tayi yawa amma Ina son na had'u da mijina, shine kuma kuke cewa sai ya sakeni?, Meye laifinsa?, Wne zunubin ya aikata da za'ayi yunqurin rabashi da ni?" "Ungo nan marar kunyar yarinya." Yaya Maryam tafad'a had'e dayi mata daqquwa tanaci gaba da cewa. "Ke wane zunubin kika aikata da uwarsa ta rabaki dashi, kin ganemun shashashar yarinya da batasan ciwon kanta ba, to bari infad'a maki wlh munfiso kimutu atare damu muyi maki sallah murufeki da mumaidaki gidansa uwarsa ta sake halakar mana dake, don haka tunwuri kiciresa aranki matuqar kina son muzauna lafiya dake kinji nafad'a maki." "Haba gwaggo! Haba gwaggo wannan wani irin tsattsauran hukuncine zakuyi mana, inada yaqini akan tunda wannan jarabawa tasameni shima t yake cikin irin tashi jarabawar, don ALLAH kada kura bamu kodon yaronnan." Taqarasa maganar tana kallon little dake hannun ita Yaya Maryam d'in had'e da fashewa da kuka, har ga ALLAH Yaya Maryam taji tausayinta, Amma Babu yanda ta iya, wannan ita kad'aice hanyar da zasubi su kub'utar da 'yarsu daga sharrin uwar mijinta, wacce itama tanacan cikin mummunan yanayin da basuda labari akai, cikin dakewa da qarfin hali tace. "Rashida kawai kuhaqura da juna, yaro kuma Allah shizai rayashi ko bakwa tare don haka kibi umurninmu kizauna lafiya." Wani kukan ta sake fashewa dashi had'e da durqushewa qasa tana fad'in. "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, astagfirullah ALLAH natuba kayafemun laifukana, ya ALLAH ka sauqaqamun wud'annan jarabawowin rayuwa kada sufi qarfin zuciyata susa na sab'a maka," kallon yya matram data kauda kai tana goge 'yan guntayen hawayen da suka zubo mata tayi. "Gwaggo baifa sakeni ba, taya zaku rabamu?, Karku manta dani harshi zamu iya sake ahiga wani hali idan kuka yimana haka, kunada iko akaina ammashi sam bai kamata kununa iko akansa tahanyar tirsasashi ya sakeni ba." "Kedai zaki shiga wani halin keda kike ganin bamu isa mutirsasaki akan abunda muke ganin shine alkahiri arayuwarki ba, amma bandashi tunda har ya iya mance awane irin hali zaki shigaba keda abunda ke cikinki ba ya tsallake qasarnan ya tafiyarsa duk da yasan abunda yafaru dake Amma saboda ya gyara rayuwarsa kuma ya farantawa iyayensa yatafi yabarki acan duniyar da bai masan inda kike ba don ya inganta gobensa, ba kekad'ai da ba kyanan ba hatta mu iyayenki da yasan muna nan ya wofantar damu ta hanyar tafiyarsa batare da saninmu ba, wannan shi kike tunanin har zai shiga wani hali idan aka rabaku.? Tir da wannan banzan tunani irin naki" tana gama fad'ar haka tafice d'auke da little da yayi bacci a hannunta STORY CONTINUES BELOW Tunda tafara magana Rashida ta dasqare a inda take tsaye, shin Anya maganganun da gwaggon tata ke fad'a gaskiya ne ko a'a?, Ko kwanto tashigayi akan cewa habibyn nata zai iya tafiya acikin yanayin da ake na b'atanta kuwa?, Inaaa hakan bazai yuyu ba , tabama kanta amsa had'e da miqewa tana goge hawayenta, dole yau sai tahad'u da mijinta koda hakan na nufin za'a rabata da lumfashinta ne, dole ta qaryata d'ayar zuciyarta dake neman gasgata kalaman da gwaggo tafad'a mata. 'Dakin da anan ne aka bata tashiga ta d'auko mayafinta da sauri tanufi qofar fita gidan, kota halin qaqa yau tanada buqatar zuwa ta had'u da masoyinta kuma mijinta, sand'a tafarayi gudun kada taganta ta hanata zuwa har ta isa bakin qofar gidan Tana fitowa taci karo da Fatima aqofar gida ita da Dr ya kawota. Cikin farinciki Fatima tarungumeta tana fad'in "'yar halak ina zakije ne ko kema kinyi kewar tamune kamar yanda mukayi?" Ganin yanda idanuwanta sukayi jajir saboda kukan da tayi yasa Fatima cewa. "Subhanallahi, maman boy meyake faruwa?" Hakan yasa Dr fitowa daga cikin motar yana kallonta had'e da qoqarin rufe marfin motar, qarasowa wajensu yayi kafin yace. "Maman boy lafiya?" Yanda sukaga ta sake fashewa da wani kukan yasa Fatima riqo hannunta zata shiga cikin gidan da ita da sauri taja baya tare da tirjewa. "Don ALLAH uncle ku kaini naga ya Nuraddeen, Ina son ganinsa Ina so nahad'u dashi Amma su baffa sunqi amincewa," "Kamar ya Rashida?" Dr.nura ya tambayeta cikin rashin sani. "So sukeyi su raba aurena dashi uncle kuma Ina son mijina, bayada laifi, akan abunda yafaru amma gaba d'aya sun kasa fahimtar hakan! don ALLAH ko sau d'ayane kataimaka akaro nabiyu ka had'ani da mijina kamar yanda kahad'ani da iyayena." Maganar takeyi tana kuka had'e da game hannayenta waje d'aya, Alama yayiwa Fatima dasu shiga motar sannan yajuya shima yashiga had'e da tayarwa, hannunta Fatima tariqa tabud'e gambun bayan motar tasata ciki sannan tarufe itama tashiga yaja motar sukabar qofar gidan, "Ina muka nufa?" Ya tambayeta adaidai lokacin da suka fito qauyen. "Bebeji." Tabashi amsa ataqaice tana goge hawayen da suka jiqa mata fuska sharkaf, Tafiya mai d'an nisa sukayi kafin su iso gaba d'ayansu Babu wanda kecewa wani uffan, tuqi yakeyi da hannu d'aya, hannun d'aya kuma ya azoshi saman tagar qofar yariqe hab'arsa dashi ita kuma Fatima sai faman jujjuya kwalin wayar dake hannunta takeyi wacce dama itace dalilin zuwan nasu saboda kewarta da tayi mata yawa kullum cikin zancenta ita da little yasa Dr yasiyowa Rashida wayar don suriqa gaisawa sai gashi sun tarar da ita cikin wannan halin. Bini bini take juyowa takalleta cike da tausayi kafin Dr yamiqo mata wayarsa. "Kamomin Yaya maryam" Scrolling contact d'insa ta farayi har takai ga lambar Yaya Maryam da yayi saving da Ya Maryam kano takirata. Bugu d'aya ta d'aga muryarta a hargitse. "Dr." "Na'am, anwuni lafiya.?" "Lafiya klw, yanzu nake zancen kiranka na nemi Rashida sama ko qasa narasa saboda nayi mata fad'a." "Karki damu tana tare damu, dama shine kiran dana yimaki." "Tirqashi Amma wannan yarinyar anyi shashasha, shine zata fita fisabillahi bazata fad'amun ba, gaba d'aya duk tabi ta tayarmun da hankali?." "Kiyi haquri, Bata kyauta ba gaskiya amma yanzun nan zamu dawo tare in Sha ALLAH." Kasancewar akwai cikakkiyar yarda tsakaninsu yasa bata damu sosai ba duk da abun ya b'ata mata rai, asalima gaba d'aya ranta bai kawo mata cewa Rashida zatayi tunanin zuwa tahad'u da Nuraddeen ba balle har ta taka da kanta taje garin nasu, STORY CONTINUES BELOW Koda suka iso angama sallar isha'i suka samu gefen wani shago sukayi parking, Fitowa tayi cikin motar suma suka biyo bayanta har suka iso inda za'a iya hango gidan, "Inane gidan Rashida?" "Wancanne uncle." Tafad'a tana nuna gidan da yatsa. "To muje ko." "A'a uncle bazan iya ba, kawai ni shi kad'ai nake son nahad'u dashi." "Bari to naje nasa ayo mani sallama dashi.," Yafad'a tare da tunkarar gidan. Tsaye kawai take duk qafafuwanta sunyi sanyi tanaji tamkar basu imata, kallon anguwar takeyi d'aya bayan d'aya, Kafin tahango Yusuf tafe yanufo inda suke gefen wani tsoho dake saida kalanzir saman d'an teburinsa, "Lado abani kalanzir na naira ashirin?" "Ahhh... yusufa d'an gidan yayansa nura, Wai ina yashige ne kwana biyu nadena ganinsa.?" "Laah...ashe lado bakasan yaje qasar waje ba?" "Kai yusufa!, Kace wlh." "Wlh lado da gaske nakeyi." "Kai ALLAH ban yarda da kaiba, shi nuran d'an mahaukaciya ne da zaibar qasar nan bayan matarsa da tsohon ciki tab'ata, sai kace wanda bedamu da ita ba," "To ni kabani kalanzir d'ina kada innar mu tabugeni, ai sai katambyi mutane kaji, yanacan yaje k'aro karatunsa." "Tirqashi! Amma gaskiya be kyauta ba." Kukan da Rashida ke qoqarin dannewa ne yaci qarfinta had'e da kucce mata. Da sauri Yusuf daya miqa hannu zai karb'i kalanzir d'in da lado kemiqo masa suka d'ago kai tare jin kukan da suka jiyo agefensu. "Yaa rasulu manzon ALLAH, ke baiwar ALLAH lafiya.?" Lado yafad'a had'e da sakin kalanzir d'in yana kallon Fatima da Rashida dake tsaye hasken k'wan shago na yadosu, da hannu Yusuf ya shiga nuna Rashida don fuskarta bazata tab'a b'oye masa ba aduk inda tashiga, kasa magana yayi sai faman ja da baya yana fad'in. "Aun..aunt..auntyyy.." Yaruga aguje yabar wajen had'e da nufar gida yana k'walawa su baffa.... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [8/24/2020, 10:40 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___59πŸ’Ž Baffa, baffa, baffa ga aunty tadawo, abunda Yusuf kefad'a kenan har ya isa bakin qofar shiga gida, karo yaci da mahaifin nasa wato baffa Ali shida Dr. nura dake qoqarin barin wajen fuskarsa a cunkushe babu alamun walwala atattare da ita, kad'an yarage Yusuf yafad'i garin kallon Dr nura daya ga yanufi inda su Rashida suke, da sauri ya riqo hannun baffa Ali yana jansa had'e da nufar inda ya gasu Rashida yana nuna masa wajen da hannu, gaba d'aya Yusuf ya rud'e ya manta da cewa ba mahaifinsa yakamata yasan da dawowar taba sanin irin matsayin da take dashi awurinsa. Baffa Ali kuwa binsa yayi har suka isa wajen lado mai kalanzir, lokacin kuwa har su Rashida sunbar wajen saboda irin amsar da Dr nura nura yazo masu da ita, STORY CONTINUES BELOW "Lado Ina aunty?" "Kai yusuf wace aunty kuma?." "Haba lado! Anan fa nabarta ita da wata mata, nan wajen!." Yaqare maganar yana nuna masa inda suka tsaya. "Aiho nan naga sunbi suda wani mutum." Lado yafad'a yana d'aure ledar daya zubawa wata yarinya kalanzir. Dagudu Yusuf yabi hanyar baffa Ali shima yabi bayansa don yatabbatar da da hakan, Suna kawowa su Rashida naqoqarin shiga mota ya shiga qwala mata kira. "Aunty, auntyyyy.." Juyowa tayi tana goge hawaye harya iso wajen, da sauri baffa Ali yab'oye bayan wani kango yana hangosu don kada taganshi. "Aunty ina zaki tafi kuma, kizo muje gida don ALLAH, ya nura nason ganinki shida su baffa da Inna bilki, kowama nason ganinki munyi kewarki sosai don ALLAH kizo muje kinji aunty." "Yusuf me zanje inyo agidanku Bayan wanda nazo don shi gaba d'aya yabar qasar, zantafi Kuma bazan sake dawowa acikin gidanku ba saboda bakwa sona." Tafad'a tana kuka tare da juyawa zata shiga motar, riqe hijab d'inta yayi shima yana kukan yace. "A'a aunty muna sonki don ALLAH kada kitafi." Hannunta tasa tacire hannunsa daga riqon daya yiwa hijabinta sannan tafad'a cikin motar Dr. Nura yaja sukabar wajen. Kuka Yusuf keyi kamar ransa zai fita had'e da nufar hanyar zuwa gidan baffa, da sauri baffa Ali yafito daga mab'uyar daya shige yatare gabansa had'e da kamo hannunsa, "Kai Yusuf ina zakaje ne acikin daren nan?" Ya tambayesa had'e da d'aure fuska yana kallonsa. Cikin sheshshekar kuka Yusuf yace. "Gidan baffa zanje." "Kaje kayo ubanmi acan?." "Zanje infad'a masa Aunty tadawo amma ta tafi kuma tace bazata sake dawowa ba." Saida ya sakar masa wani mugun ranqwashi akai sannan yace. "To uban waye ya aikeka? idan Auntyn tadawo qanwar uwarka ce kota ubanka da zakaje kasanar dasu tunda tace bazata koma dawowa to meye naka aciki.?" Qoqarin bud'e baki yayi don ya bashi amsa sai Kuma yayi saurin rufewa da hannunsa sanadiyar yanda ya murd'e masa kunne so had'e da cewa. "Karka sake inji kafidda wannan maganar waje kaji nagaya maka, inba haka ba yanda Yaya hawwa ta b'addata kaima haka zansa a b'adda kai, kaga shikenan baka ba ganin kowa naka wata qilama kamutu gaba d'aya ahuta, shashashan yaro kawai, har kamanta akanta akaje aka kullemu ni da mahaifiyarka, babu kalar azaba da kuma dukan da bamu sha ba ahannun 'yan sanda kuma duk ta dalilinta, to bari kaji duk kasake naji wannan maganar abakin wani sai nayi maka d'an banzan duka kuma wlh kadena cin abincin gidana kenan har kamatu, shegen yaro da bansan halin waye kad'auko ba, maza kawuce gida kafin in jijjimaka anan" Sosai Yusuf ya tsorata dajin kalaman da baffansa ya fad'a masa don haka yanufi gida yana kuka kamar ransa zai fita, kasa shiga d'akin mahaifiyarsa yayi yakoma saman barandar part d'insu ya Nuraddeen dake rufe ya had'a kai d guiwa yanaci gaba da kukansa, tun qarfe takwas yake zune wajen yana kuka har wucewar goma da rabi nadare kan kace me tuni zazzab'i ya taso masa ya fara rawar sanyi, Inna Bilkisu ce tafito zata zagaya bayi tagansa wajen a kwance had'e da cewa. "Kai Yusuf lafiya kazo nan ka kwanta ko sanyin nan bakaji?, Maza tashi kawuce d'aki kar mura takama ka" Ba tare data tsaya sauraren amsar da zai bata ba tawuce bayi don yin lalurar data fiddota, koda tadawo ta tarar har lokacin yana a wajen kwance ko motsawa baiyi ba daga inda tabarshi STORY CONTINUES BELOW "Ikon ALLAH, wai bakaji me nace maka bane Yusuf.?" Tafad'a tare da qarasawa wajen tana d'agosa, yanda taji jikinsa ya gashe da zafi sai faman rawar sanyi yakeyi yasa tayi saurin rungumosa ajiki tana daddafa kansa. "Subhanallahi, Yusuf dama baka lafiya shine kazo nan ka kwanta." 'Dago kansa yayi yana qoqarin yimata magana saiga baffa Ali ya shigo shida baffa Usman, ai yana ganin haka da sauri yaqarasa wajen yana fad'in. "Kai Yusuf mekakeyi wajen? Ko munafuccin ne kaima zaka koya." Ya zata maganarce yake fad'a mata, Inna Bilkisu najin haka tacire Yusuf daga jikinta had'e da zaunar dashi saman barandar tanufi inda mijinta yake tsaye yana jinjina irin kalaman da d'an uwansa ke alqanta iyalinsa dasu, shi kuwa baffa qiiiii...yaja hannun Yusuf har yana neman fad'uwa yana fad'in. "Wannan yaron anyi mai kunnen qashi, ina dai kasan abunda nace maka shine zakazo nan kasaki baki don rashin jin magana" hed'e da jefasa saman gadonsu d'an bono bayan sun shiga d'aki, ••• ••• ••• Dr kuwa banda tunanin kalaman da baffa yafad'a masa babu abunda yakeyi, wannan wace irin rayuwace muke ciki aduniya?, Wanda ma kayarda dashi alokaci d'aya sai ya sauya maka, ancuci yarinya kuma ankoma ana binta da sharri, a iya saninsa inzai tuna Rashida tafad'a masa cewa mahaifin mijinta na qaunarta Amma sai gashi maganganun daya fad'a masa akanta sunsha banban da irin kalaman daya dace afad'a ga wanda ake so, saita madubinsa yayi yana kallon yanda hawaye ke tsiyayowa daga cikin idanuwanta dake rufe ya saki wata irin ajiyar zuciya, tabbas ta cancanci tayi kuka ba kad'an ba, ko kad'an bazai hanata tayi shiba awannan karon saboda abubuwan sunyi mata yawa, a qaramcin shekarunta bai kamata ace tafuskanci irin wud'annan damuwowin ba donma Allah yataimaka ansamu jininta yakoma normal da tuni qila zuciyarta tabuga, duk da dai bai sanar da ita gaskiyar abunda yafaru tsakaninsa da baffa Ali ba daya nuna masa cewa shine mahaifin Nuraddeen, kawai dai ya fad'a mata cewa ance baya nan yabar qasar. Tare suka shiga gidan da ita lokacin da suka iso yaya Maryam na tsaye tsakar gida tana jijjiga little da sai faman kuka yakeyi tun d'azu. Miqa hannunta tayi ta karb'esa kanta naduqe aqasa batare data bari sun had'a ido da yaya Maryam ba data zuba mata ido tana kallo. 'Daki tawuce, su kuma suka tsaya suna gaisawa da ita, "Sannu Dr har kin dawo.?" "Eh ya gida yaya Maryam." "Gida Alhamdulillah Dr, kunbarni da yaro sai faman tsula Mani kuka yakeyi?" Murmushi yayi had'e da cewa. "Afuwan ai gamu mun dawo, dama kwana biyu Fatima tadameni da zancen ta shine nace bari muzo dubata sai gashi munci karo da ita, ganin babu alamun walwala atattare da fuskarta yasa nace bara muje da ita wani wurin taraka mu, I fatar za'ayi mana afuwa bisa wannan kuskuren?" Yafad'i hakanne saboda yasan ran Yaya Maryam b'aci zaiyi idan tasan gaskiyar inda sukaje. "Ba komai Dr, ai kaga Fatima gaisawa kawai mukayi tabi bayansu saboda sukad'ai tadamu dasu" Shiru yayi na tsawon wasu 'yan sakanni kafin yace. "Amm! Dama yaya maryam cewa nayi yakamata ariqa kwantarwa da Rashida hankali saboda yanayin damuwowin da suka tarar mata azuciya don kar takoma shiga wani halin, nasan kuna qoqari sosai tunda gashi naga cikin kwanakinnan tacanza ba kamar yanda muka zoba saboda yanayin natsuwar da tasamu, amma don ALLAH aqara bata kulawa, sha'aninta akwai bantausayi aciki sosai." "Ikon ALLAH!, Ai dama nasan dole qara tace zata kai wajenka Dr tunda muna ganin mutuncinka, yakamata ace rashida ta fahimci abunda muke guje mata faruwarsa saidai takasa gane hakan..." STORY CONTINUES BELOW Nan takwashe komai tafad'a masa akan abunda yafaru ba qari balle ragi, sosai Dr yashiga rud'ani daya auna maganganun guda biyu, da wud'anda baffa yafad'a masa da kuma na yaya Maryam yagano akwai wani abun aqasa wanda ba daidai ba, ko meye kuma ALLAH kad'ai yasani." Haquri yabata tare da sake roqonta a lallab'ata in Sha ALLAH da sannu zata fahimcesu sannan ya koma bakin motarsa yana jiran fitowar Fatima. Rashida kuwa saida taba little nono yasha ya qoshi Fatima na gefenta tana dad'a bata haquri tare da rarrashinta sannan tamiqa mata shi ta kwanta saman qatuwar katifar dake cikin d'akin nata, anan maganganun da suka faru tsakaninta dashi a daren ranar suka shiga dawo mata a kwakwalwa, tabbas ita ta qarfafa masa yin wannan tafiyar kuma ko kad'an hakan da yayi ba laifi bane, Amma meyasa ya aikata hakan batare daya sanar da iyayenta ba.? Meyasa baiyi tunanin abunda zai iya faruwa ba akan wannan kuskuren da yayi, kamata yayi ace ya fahimci cewa komai na duniya kan iya sauyawa idan aka samu sauyin al'amurra, kama daga ra'ayi, buqata, lafiya, wajen zama da kuma yanayi na yau da kullum, gashi yanzu yaje yabar baya da qura, babbar damuwarta shine rashin sanin har tsawon wane adadin lokaci zai d'auka kafin yadawo. Jitayi Fatima nafad'in "maman boy zamu tafi, yana waje yana jirana, don ALLAH kimaida al-amurranki agaresa kidena kukannan bayada amfani, ga wannan wayace uncle d'inki ya siya maki zamu rinqa magana, akwai lambata da tashi aciki kuma na saka maki ta yaya maryam data aunty marwiyya saiki kirasu, kada kiyarda inkira injita akashe, ko yaushe ina son ki kasance tare da ita kinji ko?." 'Daga mata kai tayi sannan tajuya zata tafi tana d'auke da little. "Au! yau babu rakiya maman boy?" Ta juyo tana kallon rashida dake qoqarin tasowa alokacin. Har bakin mota ta rakata tare da yiwa Dr.nura godiya sosai tamiqa mata Little sannan suka wuce... _Darasi: 'yar uwa ki guji aikata laifi komai qanqantarsa domin bakisan iya adadin mutanen da Zaki iya cutarwa ba ta dalilinsa, wanda hakan kad'ai na iya zamowa dalinlin tsanantar hukuncinki awajen ALLAH, domin shi mai yafe haqqinsane amma banda haqqoqan rayukan da kika cutar, laifi d'aya yaya hawwa ta aikata akan rashida amma mutane da yawa sun cutu adalilinta, ciki kuwa harda qaramin yaro (yusuf) dake fuskantar damuwa da kuma barazana ta dalilin hakan._ *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [8/26/2020, 10:51 PM] FARI'S DOTAπŸ’ŽπŸ’ƒπŸΌ: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___60πŸ’Ž Tunda Rashida ta tabbatar da cewa Nuraddeen yabar qasar taji gaba d'aya komai na duniya ya tsaya mata, Babu abunda ke mata dad'i haka kuma babu abunda ke burgeta arayuwar duniya, kallo d'aya zakayi mata kafahimci tsantsar damuwar da take ciki saboda yanda duk tabi ta susuce, batada wani aike sai kuka, na safe daban na rana daban hakama na dare daban, duk tabi tarame tayi baqi, rashin iyayenta namatuqar damunta musamman yanzu da take cikin wani hali marar misaltuwa duk da kuwa Yaya maryam da baffa sunyi qoqarin nuna mata sun sauko daga dokin naqin da suka hau saboda yanda sukaga tana nemanfita hayyacinta sai dai aransu ba haka bane. Baffa Usman kuwa da baffa basu san abunda kefaruwa ba , gaba d'aya sun maida hankalinsu kocokom ga nemawa Yaya hawwa magani har zuwa lokacin da aka d'ibar masu nazuwa a d'auketa, ranar nayi misalin qarfe sha biyu na rana motar asibitin ta dira abakin qofar gidansu baffa, lokacin suna tsaitsaye da alamu dama suna jiran dakon isowarsune tun d'azu, wasu ma'aikatan lafiyane su biyar da kuma wani mutum yasha suit, da alama shine babbansu, Saida suka gaisa dasu sannan baffa Usman yayi masu jagora zuwa cikin gidan inda Yaya hawwa take ya bud'e masu d'akin, STORY CONTINUES BELOW Cikin qwarewar aikinsu suka shiga cikin d'akin yayainda Yaya hawwa tayi wani irin kukan kura tayo kansu. Ba qaramar wahala suka shaba kafin su samu damar rirriqeta tana keta wani irin ihu daya karad'e ko ina tana fizge fizge, sai da sukayi da gaske sannan suka sakata cikin mota suma suka shiga. Wajen motar baffa yatako yana hango ta glass d'in motar yanda jami'an lafiya ke qoqarin yimata allurar da zatasa tayi bacci kafin su isa yasa hannu ya goge k'wallan da suka zubo masa a idanuwansa yana mai addu'ar Allah yabata lafiya, gaban motar ya koma saiti gefen driver inda babbansu yake ya saukar da glass d'in motar yamiqa masa hannu suka sake gaisawa yayi masu godiya sannan motarsu tabar wajen, ahankali dandazon mutanen da suka taru qofar gidan suka fara watsewa cike da tausayin halin da sukaga anfito da Yaya hawwa aciki saboda yanda tayi baqi da rama sosai fiye da tunani, inba wanda yasanta sosai ba bazaka tab'a ganinta kace itace ba. Adai dai lokacin baffa Ali yadawo daga gona rataye da fartanyarsa a kafad'a yana rera 'yan waqoqinsa, yana hango su baffa Usman ya murtuqe fuska tunkafin ya iso har zai wuce abunsa sai kuma yadawo baya had'e da kallon gungun wasu yara dake tsaye abakin gidan. "Kai me kukeyi anan naga kun had'e kanu kamar d'iyan awaki?" "Wlh Yaya hawwa ce akafito da ita za'a kaita asibitin mahaukata abun gwanin tausayi." Wani yarone daga cikinsu yafad'a hannunsa na tallab'e da kuncinsa. Batare da baffa Ali yadamu da 'yan uwansa dake wajen ba yayi tsaki had'e da cewa. "ALLAH yaraka taki gona, ai mun huta da gayyar tsiya kullum ana hanamu bacci ana tsorata iyalinmu da yaranmu," Juyowa baffa yayi ransa amatuqar b'ace yace. "Karka damu Aliyu, SANNU SANNU ai bata hana zuwa...kamar dai yanda hawwa ke girbar abunda tayi haka kaima zaka girbi naka in alkhairi in kuma sharran." Guntun tsaki yaja batare daya damu da abunda baffa yace masa ba yashige cikin gida yana cigaba da rera 'yan waqoqinsa... ••• ••• ••• Kimanin satinsu Dr nura uku kenan da dawowa kano kawo Rashida, wanda sun jima hakanne sanadiyar Fatima data nace akan suyi zamansu sai qarshen wata saisu koma gaba d'aya tunda dama yakusa d'aukar hutu (annual leave), saidai hakan bazai yuyu ba saboda maganin little Nuraddeen da za'a karb'o masa gashi bayason idan yaje qarshen watan yasake dawowa har sai hutunsa yaqare, Hakan yasa cikin satin da zasu koma kafin ranar tazo yayi sakko yaje borno ya karb'owa little maganinsa wanda idan yasha shine naqarshe, Yana isa garin kai tsaye yawuce gidan iyayensa saboda akwai saqon da mahaifiyarsa tace yaje ya karb'owa Fatima na maganin da takesha, Yana isa yatarar da mahaifinsa shima yadawo lokacin yana zaune kan dining table yana cin abinci, qarasawa yayi bakinsa d'auke da sallama yaje ya d'an russuna gabansa had'e da gaishesa. Sake da fuska yamiqa masa hannu yana fad'in. "A'a bokan turawa saukar yaushe?" "Yanzunnan dady, mun sameku lafiya?" "Lafiya klw dady, ya kasuwar." "Kasuwa Alhamdulillah muna nan muna tattab'awa musanmman sabon shagon dana bud'e, abun Masha ALLAH gaskiya." "ALLAH yaqaro bud'emai albarka, dady ammie fa?" "Tana ciki, yanzu tabar nan inaga ankirata ne awaya." Yana rufe baki tana fitowa, babbar mace ce mai cikar zati da kamala, farar mace ce sosai mai yawan fara'a da son mutane, kallo d'aya zakayi mata kafahimci hutu na tattare da ita, da sauri yanufi wajenta had'e da gaishesa, rungumosa tayi ajiki kai kace bashine d'anta nafarin ba suka nufo wajen dadyn tana fad'in. STORY CONTINUES BELOW "Oyoyo mutanen kano ta dabo tumbin giwa yaro koda mekazo anfika, Amma inada tabbaci akan ba'afi yaron nawa ba saidai ayi gogayya dashi ko ba haka ba alhaji?" Taqarasa maganar had'e da jawo kujera ta zaunar da Dr nura. Dariya sukasa shida dady kafin yace. "Mezance hajia fareeda tunda kinriga kin fad'a, ai ko ba haka bane ta zauna, uwa da d'anta kome tace akansa ai babu wanda ya isa musa mata." Suka sake sa dariya. "Son ya hanya da 'yata Ina fatar kuna lafiya?" "Lafiya klw ammie, tace agaisheki sosai." "Muna amsawa, injin tana amfani da maganin yanda yakamata? Nasan halinku na 'yan boko baku fiye ba maganin nan namu na gargajiya muhimmanci ba.?" "Ahh ammie banda Fatima tana kulawa sosai da lokutan shansa yanda yakamata," "ALLAH sarki baiwar ALLAH, ALLAH yasa adace, yarinyar nabani tausayi sosai, tanada matauqar juriya da haquri wlh, badon haka ba idan irin 'yan matan nan namu na zamani ne da yanxu tabi ta tayar maka da hankali dama kanta ga abunda Babu mai iya baku sai ALLAH, kuci gaba da haquri, in Sha ALLAH lokaci nazuwa da ijaba zata sauka, muna nan muna yimaku addu'a," "Hakane nura! Kaci gaba da haquri kana kwantarwa da iyainka hankali, da SANNU ALLAH zai duba lamurranku ya share maku hawayenku, akoda yaushe addu'ar mu natare dake." "Dady, ammie nagode da kulawar da kuke bamu tare da addu'o'inku, koda ALLAH bai bamu aihuwa ba ku kad'ai kun isa farinciki agareni domin babu abunda yakai samun nagartaccin iyaye aduniya muhimmanci, sune kad'ai farincikin da idan katuna zaya dad'a sanyaya maka zuciya." Daidai lokacin umma tafito daga kitchen don tagama kammala komai zata koma part d'insu, "umma gafa d'anki da d'azu nake fad'a maki cewa yana kan hanya ya iso." Dama tuni umma tadawo wajen hajia fareeda da aiki kamar yanda dady ya umurta kuma tanajin dad'in aiki da ita sosai don kusan komai atare sukeyi cikin girmamawa, sab'anin hajia nafeesa da saidai ta nad'e qafafuwa tana bada umurni, murmushi tayi had'e da qarasowa wajen tace. "Sannu da zuwa.." Bata qarasa ba sakamakon juyowar da yayi suka had'a ido, cikin i'ina tace. "Kaine?" "A'a baba kece anan kuma.?" Yafad'a yana nuna baba da hannu, binsu da kallo su ammie sukayi cike da mamakin ganin sunsan juna, nan Dr nura yabasu labarin ynda yasanta har yana qarawa da tambayarta cewa. "Baba ina wanda naganku tare." "Yana can shagon da alhaji yabashi yariqa kulawa dashi, ai shi d'in mijinane" Tafad'a akunyace tare da komawa kitchen, Dariya su dady sukayi kafin sushiga bashi labarin zuwansu ataqaice amma basu fad'a masa cewa sanadiyar b'atan 'yarsu sukazo garin ba. Dawowa tayi d'auke da wani qaton try da suka shirya masa abincin da yafiso ita da ammie wato tuwon semolina da miyar kub'ewa d'anye, da sauri ammie taje tariqo mata tana fad'in. "Kai umma ai dabari kikayi nazo na d'auko masa." Sannan ta ajiye abincin agabansa, yana bud'awa yaga best food d'insa ba shiri yature jikkar gabansa yana qoqarin fara zubawa yaci, d'an mangararsa ammie tayi aqeyar kai tana fad'in. "Bazaka bari kafara watso ruwa ba.?" "Awshh....ammie bara nagama cin abinci tukuna, ALLAH yawuna har sun tsinke." Yafad'a yana shafa inda ta mangaresa, dariya umma dake tsaye tana kallonsu cike da burgewa tayi tana goge 'yan hawayen da suka zubo mata tunawa da tata 'yar sannan tabar wajen. STORY CONTINUES BELOW Bayan ya kammala cin abincinsa yaje ya watso ruwa sannan yaje wajen hajia nafeesa matar babansa ya gaisheta daga can kuma yawuce wajen malamin da yake karb'o maganin Little Nuraddeen awajensa ya karb'o sannan yadawo gida lokacin kusan qarfe biyu na rana yawuce kai tsaye d'akin ammie tana zaune tana tilawar alqur'ani, Saida takai aya sannan tarufe taje ta d'auko wata leda cikin drower d'in madubi tadawo inda yake zaune gefen bedside d'inta ita kuma ta zauna agefen gado. "Ungo wannan ka kaimata, don ALLAH kace takula da shansa tunda safe kafin taci komai, shi wannan ganyen koba don haihuwa ba yanada kyau adinga tafasashi ana sha da ruwan tea kafin aci komai da safe, yana wanke duk wata datti dake cikin jikin mutum har zuwa mara, hakama yana wanke dattin mahaifa sosai, hatta wannan tumbin da kake ganin kafara azawa idan kuna shansa tare zaya rage sosai, don haka kukula, shi magani da kuke gani dace ne bamusan ta ina ALLAH zaisa adace ba, ALLAH yabamu rayayyi masu albarka." "Amin ammie, amma shi wannan ganyen mene ammie?" "Ganyen guava ne." "Guava fa kikace ammie!, Wannan guava dai dana sani." "Eh mana, Ina tabbatar maki idan kuka gane shan tea da ita, bazaku tab'a bari ya tsinke maku va agida, da kanku zaku kirani kusanar dani amfanin da kukaji tayi maku ajiki." "To ammie shikenan mungode." "Yawwa ALLAH yayi albarka kuma yakiyaye hanya." "Amin ngd." Yafad'a had'e da miqewa ya kama hanyar komawa kano bayan yayi sallama da mahaifinsa. ••• ••• ••• Kimanin kwanaki uku Yusuf ya d'auka kwance yana fama da zazzab'i, baya fita ko ina daga d'aki sai d'aki har ALLAH yasa yasamu sauqi, baffansa nafita zuwa gona ya iske baba Usman a d'aki yana shiryawa zaije gidan baffa zasu koma wajen baba balarabe su sake bashi haquri akan abunda yafaru, dama Inna ruqayya tafita anguwa Inna Bilkisu kuwa tana waje tana share wajen dabbobinta da yayi datti, baffa Usman na gyara zaman hularsa akai yaji anriqo rigarsa, juyowa yayi had'e da cewa. "A'a Yusuf ka taso? Yajikin naka da sauqi ko?" "Eh baffa Usman naji sauqi sosai." "Masha ALLAH, ALLAH yaqara sauqi , to ya akayi ne." Duba gefe da gefe yayi sannan ya leqa ta qofar shigowa d'aki yaga ba kowa ya matso dab da inda baffa yake zaune a gefen gado a kunnensa yace. "Baffa aunty Rashida matar ya nura tadawo, naganta da idona Amma karka gayawa baffana." A razane baffa Usman yamiqe had'e da cewa. "Kai Yusuf bana son shashanci, a Ina kaganta ne?" Hannu Yusuf yasa had'e da rufe baki yana qwalalo idanuwa ya juya yana kallon qofa, Furzar da iska baffa Usman yayi had'e da kwantar da hankalinsa ya matso inda Yusuf ya dafa kafad'unsa. "Yusuf ka kwantar da hankalinka, Babu wanda zaiji kaji ko?, Yimun bayani a Ina kaganeta." "Bana son baffana yaji yace idan nafad'a nima zai b'addani kuma bazai sake bani abinci ba." "Bazaiji ba nayi maka alqawari kaji ko?" Nan Yusuf yayiwa bayanin baffa komai had'e da roqonsa don ALLAH kada yafad'awa baffansa shi yafad'a masa, jikinsa na rawa yabar d'akin shima baffa Usman jikinsa asanyaye yabar gidan yanufi wajen baffa yayi masa bayanin abunda Yusuf yafad'a masa, yayi matuqar shan mamakin cewa wai har yanzu baffa ali na adawa da Rashida, tsanar da yakeyi masu har takai girman da zai sake cillasu awata damuwar, tare suka fito suka nufi gidan lado mai kalanzir suka tambayesa abunda yafaru ranar tsakaninsa da Yusuf na zancen ganin matar da Yusuf ya tabbatar masu da cewa Rashida ce. Sun samu amsa daidai da zancen Yusuf don haka ba b'ata lokaci suka nufi gidan baba balarabe. Sai yanzu baffa yasake fahimtar dalilin fushin da baba balarabe yayi sosai, ya tabbata akwai maganganu da baffa Ali yafad'a masa marasa dad'i wud'anda sune suka tunzurasa, haqiqa ko shine malan balarabe zai d'au zafi fiyema da hakan domin d'a baifi d'a ba. Duk qoqarin da yakamata su baffa suyi wajen yiwa baba balarabe bayani yanda zai fahimci komai sunyi amma gaba d'aya Sam yaqi saurararsu balle yafahimce su, da suka d'auko masa zancen ganin Rashi da akace anyi kuwa buga kai yayi ga qasa yace shi baima san da zancen ba, Dole suka haqura suka koma gida, kusan ko yaushe cikin kiransa suke awaya da isko shi gida suna son tabbar da zancen amma ko kad'an yaqi barin hanya ko kad'ance da zasu iya gane hakan, musamman suka turo abokanansu da mutanen da suke da kima abashi haquri ko zai sauko yafad'a masu cewa Rashi tadawo. Amma baba balarabe yakafe akan bashida masaniyar hakan, ayanayin yanda yake sakin fuska da tarbar wud'anda suke turowa yasa bazasuqi amincewa da zancensa ba, gaba d'aya baffa yasake shiga damuwa har ya soma ramewa. A kullum bayada lokacin kansa saina bin hanyar zuwa gidan baba balarabe, baya can baya gidan Yaya Maryam, hakama aunty marwiyya, duk inda yake sa ran zai samu tabbacin labarin zuwan Rashida yana biye dashi Amma k sunqi bud'e baki sufad'a masa gaskiya. Duk zafin da aunty marwiyya ta d'auka akan maganar saida yasoma bata tausayi saboda irin yanda taga yana kaida komo gidanta shida d'an uwansa kawai saboda su sani ko Rashida ta dawo amma idan ta tuna cewa fada masu shine zai sake zamowa silar da Rashida zata koma acikin ahalinsu da Babu zuciyar tausayi ko Imani atattare da wasunsu sai taji zuciyarta ta karye, musamman idan ta tuna da rashin 'yar uwarta da tayi akusa da ita ta dalilin haka. Ganin irin kai da komowar da baffa keyi a tsakankanin gidajen nasu su uku yasa suka yanke shawarar had'a Rashida dasu Dr nura su koma da ita acan borno domin hakan shi zai fimasu kwanciyar hankali tunda sunsan inda take, koba komai itama zata d'an rage damuwar da take ciki tunda har yau taqi sakin jiki kullum cikin qunci take. Wata nakaiwa qarshe Dr nura sunzo yimasu bankwana yaya maryam takira baba balarabe da aunty marwiyya suka roqesa akan buqatarsu tasu koma da Rashi acan yafi masu kwanciyar hankali indai hakan bazai zamo takurawa agaresu ba har zuwa lokacin da ALLAH zai qaddari dawowar iyayenta, Sun matuqar jin dad'i yanda suka basu yarda haka tare da amice masu akan 'yar tasu duk da babu wata alaqa inbata musulunci ba a tsakaninsu musamman Fatima da tunkafin Dr nura ya amsa cewa sun amince tace. "Babu wata matsala sun amince ba komai." Har tana karb'ar little a hannun aunty marwiyya cike da farinciki. Rashida kuwa babu yanda ta iya domin ta dad'e da tabbatarwa kanta da cewa batada wani sauran iko akanta tunda tarasa iyayenta akusa da ita, komai yanzu sai yanda akayi da ita, sunjima agidan kafin Yaya maryam taje ta har had'o mata kayanta dana little, aranar ma Rashida tasha kukan rashin iyayenta sosai tare da fawwala dukanin al'amurranta ga ALLAH tana mai addu'ar ALLAH yasa wannan qaddarar da zata d'auketa ta maidata garin da tabaro tazame mata alkhairi, ahalin yanzu ko kad'an bata ganin laifin tafiyar Nuraddeen, saidai takanji wani irin zafi da qunci azuciyarta Idan ta tuna dashi wanda batasan dalilin faruwar hakan ba. Haka sukayita bata baki da rarrashinta sannan suka d'auki hanyar komawa borno ita dasu Dr. Gidan iyayenta kuwa tuni Yaya Maryam da baba balarabe suka yanke shawarar saka 'yan haya aciki kafin randa ALLAH zai dawo dasu sai suna jujjuya masu kud'in... Pls comment, vote and shareπŸ‘ *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­πŸšΆ‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___61πŸ’Ž Ba qaramar rawar gani Dr nura da Fatima ke takawa ba wajen kula da farinciki da kuma walwalar Rashida ba ita da d'anta, duk wani abu da take buqata basa bari har saita kai ga furta cewa tana so suke yimata, mutanene su day sukasan haqqin zaman takewa da kuma sanin kimar d'an Adam, ko kad'an abunsu baya rufe masu idanuwa balle ya had'a ka dasu, sosai suka nuna mata cewa dasu da ita duk abu d'aya ne babu wani banbanci don haka tanada 'yancin tayi rayuwarta yanda takeso acikin gidan ita da yaronta matuqar hakan bai sab'awa musulunci ba.+ Hakan yasa tafara sakewa kamar yanda suke buqata saboda taga tasasu farinciki yanda suke qoqarin sata itama. Sunada sati d'aya da dawowa Dr nura yaje ya sanar da iyayensa batun zaman Rashida agidansa da irin taimakon da yayi mata wanda daga qarshe har danginta suka roqesa akan tazauna wajensu nawani d'an lokaci kafin ALLAH yadawo da mijinta lafiya. Sun jinjina al-amarin sosai har ammie nayi masa fad'an meyasa tun farkon faruwar al'amarin bai sanar dasu ba sai yanzu, gashi sanadiyar banzar tunaninsa ya haifar mata da rasa iyayenta wanda da ansanar dasu dawuri da duk haka bata faru ba, haquri yabata tare da fad'a mata iya qoqarin yin hakan da yayi alokacin amma ALLAH beyarda ba sanadiyar wannan rubutacciyar qaddarar daya tsaro masu. Dady kuwa tunda Dr yafara bada labarin yake ganin kamancece niyarsa da nasu umma duk da dai bakomai yafad'a masu ba, jin dayayi Dr nura ya ambaci cewa ita mijin nata na qasar waje yaje karatu yasa ya janye hankalinsa daga wannan tunanin, a tsammaninsa ma yarinyar 'yar masu kud'ice don haka sai dai kawai ya nuna masa yanda yaji dad'in taimakon da yayi da kuma qara qarfafa masa wajen sanin kima da kuma darajar d'an Adam, ya sake horonsa akan ya taimaki duk wani mabuqaci shima ALLAH zai taimakesa domin shi alkhairi aduk inda kayishi to tabbas zai biyoka aduk inda kake. Haka ammie itama ta sake gargad'insa akan yariqa sanar dasu duk wani abu dayasan yinsa zai iya basa wata matsala ko akasin haka saboda suriqa bashi shawarwarin daya kamata harma da taimako idan akwai buqatar yin hakan, yadena yin gaban kansa akan wasu abubuwa matuqar suna raye dominsu har yanzu yaro yake agaresu, ya matuqar jin dad'in nasihohin da suka yimasa kafin yayi madu sallama yawuce gida suna masu sanya masa albarka da addu'ar ALLAH ya albarkacesa da zuri'a d'ayyaba. Zama mai cike da girmamawa da kuma mutunta juna ke tsakaninsu da Rashida, basuda matsala da ita haka itama batada wata matsala dasu, rayuwarsu sukeyi mai tsabta inganci da kuma nagarta har little Nuraddeen ya cika wata goma aduniya lokacin har yafara takawa Babu inda bai zuwa, yayi wayau sosai gwanin ban sha'awa dashi ga surutu, koda yafara iya magana da gwaggo yake kiran Rashida saboda sunan da yaji ana kiran mai aikin gidan dashi kenan sai yazata itama sunanta kenan yake kiranta dashi, Amma yanayin shaquwa da sabon da yayi da Fatima ita mama yake kiranta shi kuma Dr da Abba yake kiransa saboda tunda suka dawo kusan duka renonsa a hannunsa yakoma, iyakar Rashida dashi bashi nono sai wasu lokutta da idan uzuri ya gittowa Fatima sai tayi masa wanka da gyarashi, hatta bacci wani lokacin awajensu yakeyi ataqaice duk wata kulawa daya dace uwaye suyiwa 'ya'yansu su suke yimasa, kallo d'aya zakayi masa kasan d'an d'an 'yan gayune saboda irin gyaran da yake samu daga wajensu, wata irin mahaukaciyar soyayya sukeyi marar misaltuwa daga shi har mahaifiyarsa, idanko zasu fita sau goma ayini yadinga ihu kenan yana zallo har sai sun tafi dashi, ita abun har mamaki yake bata don ba qaramin shaquwa yayi dasu ba, Babu abunda ma yafi bata mamaki irin kud'in da suke kashikke masa aduk lokacin da suka fita dashi sai take tunanin kamar tad'ora masu hidima sosai akansa, lokacin data roqesu surage yimasu hidima kada abun yayi yawa nan take suka b'ata rai had'e da nuna mata rashin jin dad'insu akan haka, dole tabasu haquri taci gaba da yimasu addu'a suma ALLAH yakawo masu nasu 'ya'yan masu albarka kusa kusa kamar yanda tasaba akoda yaushe. STORY CONTINUES BELOW Hakama dady da ammie suna matuqar son yaron sosai don duk lokacin da Dr zasuje tare suke zuwa dashi, shi kuma baba randa yafara ganin yaron saida gabansa yafad'i saboda yanda ya hango tsantsar kamarsa da 'yarsa da kuma ummanta atare dashi, yadad'e yana tunanin anya wannan yaron ba jininsa bane kuwa?, Amma sanin cewa jikane ga alhaji tunda baisan alaqar dake tsakanin yaron da kuma Dr ba yasa yakama bakinsa yayi shiru daga bayama sai yashiga tambayar kansa taya hakan zai faru tunda yasan kosu waye iyayen yaron?.duk lokacin daya ga yaron sai yaji gabansa na tsananta fad'uwa, ji yake tamkar Rashidarsa ce hakan yasa yafara qoqarin jan yaron ajiki, Dady ma ranar daya ga little kai tsaye yacewa ammie yana kama da umma tayi dariya had'e da cewa. "Ikon ALLAH dama haka abun yake, qila idan anyo taliyo yanada alaqa da ita tunda dama mutane 'yan uwan junane idan an bincika." Basu wani d'auki maganar da muhimmanci ba shiyasa suka barta abakin nan batare da tayi tsayi ba. Yau da misalin qarfe biyar na marece Fatima tafito riqe da hannun little suna takawa ahankali kamar yanda take tafiya yasha manyan kayansa irin na cikakkun hausawa hadda babbar riga da hannuwa masu clips kai karantse kace babban mutumne, kansa saye da 'yar madaidaiciyar hula irin mai qube d'innan da takalma have cover yayi matuqar kyau sosai har yagaji, murmushi Rashida tayi had'e da cewa Masha ALLAH aranta kafin tace "Haba aunty, uncle fa nawaje yana jira kin tsaya biyewa tafiyar wannan yaron da sai magrib tawuce baku qaraso ba," "Eh munji dai, ai SANNU SANNU bata hana zuwa ko my boy." Taqarasa maganar had'e da d'aukeshi sannan taqaraso wajen tana d'agawa Rashida gira tana dariya had'e da kallon little tace. "To ya kikaga yarona?." "Ba kyau, kuma am jealous." Rashida tabata amsa had'e da wucewa gaba tana dariya. "Lallai ma maman boy, kawai kice dai jealous d'inne yahana kiga zallar kyan dake zuba anan.?" Saida suka iso suka shiga cikin motar sannan itama Rashida ta shiga sukabar qofar gidan, bayan sun hau titi sunfara tafiya Dr nura ya kalli Fatima yanda tayi kyau ita da little tamkar ace d'anta ne yace. "Wow..Masha ALLAH, matar yau kincini tukuici, wannan wankan na takwara dole yahau Instagram, yaro sai kace donsa aka halitto kayan nan na hausawa, gaskiya badon kar ace nayi sonkai da yawa ba da nace maman boy kinfi kowace uwa azamanin nan dacewa da kyakkyawan yaro kamar takwarana." "Kai uncle to ai wannan zancen naka ga mamansa nan azaune ita kad'ai zata iya fahimtarsa amma nikam yanzu haka nahango yaron daya fishi kyau da komai akan titin nan." "Jealousy jealousy.." Fatima tafad'a tana dariya. "Yawwa maman boy yaufa wajen su ammie zan kaiki kugaisa, tun satin can take cewa na kaiki wajensu kugaisa amma ko yaushe sai namanta saboda abubuwa da sukayi mani yawa, Yauma matar ce tatuna mani ganin Ina shirin tafiya can nida takwara shine nace tafad'a maki kigyara sai muje gaba d'aya, Ina fatan bamu takuraki ba ko?" "Laaa..uncle wace irin takurawa, ai nima matsayin iyaye suke agareni kuma kamata yayi ace tuntuni nayi wannan tunanin na zuwa nagaishesu lura da irin saqon gaisuwar da akoda yaushe suke aiko mana dashi amma rashin kammaluwar cikakken tunani irin nawa yasa nakasa yin hakan, babu komai kuma naji dad'i sosai koba komai naje naga mahaifiyar da tayi sa'ar samun nagartaccin 'ya'yaye kamarku, inada yaqini akan cewa tafi kowa sa'ar samun surukar qwarai irin aunty Fatima kuma nasan tana alfahari da ita sosai. "Hakane maman boy, mahaifiyata nason Fatima fiye da son da takeyimun, a kullum tana fad'a cewa itace cikar farincikin mu kuma hasken gidana." Yaqare maganar yana kallon Fatima data qura masa idanuwa had'e da d'aga mata gira. STORY CONTINUES BELOW Haka sukayita firarsu har suka isa qofar gidan wanda yayi daidai da shigowar baba yanufi sashen da aka basu. ••• ••• ••• Baffa kam tuni yagama haqura tare da fitar da rai akan komai, yanzu tunaninsa gaba d'aya yakoma akan d'ansa da tunda yatafi baya samunsa awaya kuma shi bai kiraba gashi yanzu kimanin watanni bakwai kenan da tafiyarsa, Ganin baffa na neman shiga wata damuwar yasa baffa Usman yakoma wajen iyayen matarsa Inna Bilkisu akan zancen auren 'yar yayarta da akayi da baffa mai suna nusaiba, nan take aka fara shire shiren biki nan da sati mai zuwa, fenti marar tsada baffa Usman ya siyo don yanzu bashida isashshin kud'ad'en a hannunsa saboda lalurorin da sukayita fuskanta yasa akaje akayowa baffa awancan gidan inda yake zaune lokacin yana kasuwa, koda yadawo yatarar da anyi fenti kuma anmaida komai yanda yake ya tambayi baffa Usman yafad'a masa cewa ai zancen auren sane yatashi, tabbas yasan yanada buqatar natsuwa ahalin yanzu saidai bayada tunanin ta inda natsuwar zata zo masa, dole yana buqatar taimako takowace irin fuska don haka dole yasawa d'an uwansa ido yayi abunda yakamata wataqil hakan shine zai sama masa natsuwa. Inna Bilkisu kuwa 'yan kud'in adashinta data karb'a tayiwa baffa magana yaqara mata wasu duk da kuwa basuda yawa tasa aka sawo mata akwati d'an madaidaici ta sayi atamfuna guda biyar masu sauqin kud'i da leshi d'aya mai d'an kyau da takalma kala d'aya da jikka d'aya sai hijab da mayafi shima qwaya d'ai d'aya, foda, turare, sabulu da 'yan sauran kwantsammai da basu taka kara suka kawo ba daidai gwargwado irin kayan auren da aka sani anayi aqauye takai amatsayin lefen da baffa yayiwa yarinyar. Duk da kayan basuda yawa an amshesu hannu biyu cike da farinciki anata saka albarka. Baffa Ali kuwa da Inna ruqayya yanda kukasan auren da baffa zaiyi abun kunyane haka sukabi gari duk inda suka zauna basuda tsogumin daya wuce wai baffa zai auri qaramar yarinya tsofai tsofai dashi don abun kunya bai isheshi ba, haka sukayita yad'a wannan maganar har ta zagaye garin, yayinda wasu ke kallon abun ba wani abune tunda ansaba yin hakan a qauyen wasu kuma suke kallon auren amatsayin abun kunyane agaresa. Wannan dalilin yasa ranar d'aurin auren d'aruruwan mutane na qauyen da kewayensa suka halarci taron d'aurin auren bisa sadaki naira dubu ashirin laqadan ba ajalan ba, Sosai innna Bilkisu da iyayenta sukayiwa yarinya kayan d'aki daidai arziqinsu kuma suka yima baffa hidima sosai don fitar da ita kunya. Bayan angama d'aurin auren aka wuce gidansu baffa usman inda yahad'a 'yar qwarya qwaryar walima, abincine jalop da sob'o yasa Inna Bilkisu da qawayenta na mutunci suka dafa 'yan d'aurin auren kowa yaci ya sha yaqoshi sannan suka kama gabansu suna masuyiwa baffa addu'a da fatar ALLAH yazaunar dasu lafiya yabasu zuri'a masu albarka... Acan cikin gida kuwa Inna ruqayya sai gud'a takeyi tana yadawa Inna Bilkisu magana wai anyi abun kunya an aurarwa da 'ya mijin kishin sauri, da dai sauran suruttan da no zasu iya tunzurata, amma taqyaleta ko cikanki bata cemata ba, dama dai munduwa biyu ka amo.. Bayan anyi sallar la'asar mutanen dake zoma Inna Bilkisu sun watse tajawo d'akinta tarufe sannan taje qofar rumfar Inna ruqayya yace. "To uwar muneera kizo mutafi yowa yayan mijinki bikon amaryarsa, duk da dai nasan zallar kishi bazai barku ba qaramar yarinya ta aure maki wan miji kuma ko ba'aso dole abata girmanta idan ansan girman manya sai akirata da matar Yaya ko kuma Yaya nusaiba. Tana gama fad'ar haka tafice tabar Inna ruqayya tana d'ura ashar tare da kumfar baki. Ana gama sallar magrib 'yan kai amarya suka raka nusaiba har gidan mijinta dake can farkon gari Inna Bilkisu nariqe da hannunta sai faman kuka takeyi, nasiha tasake yimata sosai sannan suka baro gidan yarage daga ita sai Aisha yarinyar baffa Usman da yusuf, suma Inna Bilkisu tace da zaran baffansu yadawo sudawo gida. Shikuwa baffa tunda aka gama sallar magrib yayi zaunensa masallaci yakasa motsawa ko nan da can, juya al'amarin kawai yakeyi a k'wakwalwarsa wai yau shine da sakeyin aure bayan tsawon shekaru kusan talatin da wani abu da aurensa na farko, abunda ko amafarki bi tab'a kawowa aransa ba. Baffa Usman na kalle dashi tun d'azu har akayi kiran sallar isha'i, tare sukabi jam'i har aka gama baffa yasake komawa inda yake zaune d'azu ya zauna yana tunani. "Ikon ALLAH, Yaya a Ina katab'a ganin ango ya zauna yana tunani haka?, Don ALLAH katashi katafi wajen matarka nasan yanzu haka tana can zaune ita kad'ai." "Usman wlh abunnan nauyinsa nakeji, sai naga kamar maganar dasu Aliyu kefad'a gaskiya ce, wlh abunne da kunya sosai." "ALLAH ne yahana?" "Ko kad'an." "To donme kake jin nauyi ga abunda ALLAH ya halasta maka?, Katashi katafi matuqar baso kakeyi tun yau kafara d'aukar haqqoqan amanar yarinyar mutane da aka baka ba." Shiru baffa yayi kafin yamiqe ya rungumesa yana fad'in. "Nagode d'an uwana, kayi Mani sutura kala kala arayuwa da bazan iya saka maka ba, a matsayinka na qane agareni kazamemani uba kuma aboki acikin rayuwa, ya ALLAH ka kula da dukkanin al'amurranka dana iyalanka ya shirya mana d'an uwanmu shima yayi maka fiye da abunda kayi mani." "Amin Yaya, ai wannan shi d'inne ake kira da zumunci, allah yabamu ikon cigaba da haquri da juna." Shi yarakasa har gida sannan ya juya batare daya shiga ba yana yimasa Saida safe, yana shiga suma su Aisha d Yusuf suka gaishesa tare da yimasa saida safe suka nufi gida.. *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­[8/29/2020, 4:20 PM] S WHITEπŸ’Ž: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ _Thank you guz for d warmest comment you did on a previous page, all jazakumullahu bikhair, fillah i feel so much appyπŸ’ƒπŸΌbless to be with you & always proudly to have youπŸ₯°_ Page___62πŸ’Ž Yajima tsaye abakin qofar d'akin kafin ya tattaro d'an sauran kuzarin dake jikinsa had'e da tira qofar d'akin sannan yashiga bakinsa d'auke da sallama. A tsakiyar gado ya hango yarinyar kwance ta lullub'e da alama bacci ya soma d'aukarta ya qarasa wajen yana qara rafka wata sallamar da d'an be qarfi tayanda zatajishi,+ Cikin yanayin baccin dake cinta ta tashi da sauri tana murtsuka idanuwa had'e da amsa sallamarsa, kasancewar akwai hasken wutar lantarki a d'akin yasa baffa qura mata idanuwa yana kallon irin kyawon da ALLAH yayi mata, kallo d'aya zaka yimata ka tsinkayo asalin kyawo 'ya'yan fulani dake tattare da ita, farace tas dake da dogon hanci da kuma manyan idanuwa farare tas da suka d'an zurma d'auke da zara zaran gashi a samansu sai kuma yalwataccen gashin girar daya kwanta luf asaman idanuwannata, bakinta kuwa d'an qaramine dake d'auke jajayen labb'a masu matuqar d'aukar hankali, tanada lotsawa a gefen bakinta(dimple) musamman idan tayi dariya wanda shike qara fitar da tsantsara kyannata, ataqaice dai tubarkallah masha ALLAH amaryar baffa sai sambarka, batada wani tsayi ko girman jiki daya d'ara qananun shekarunta don haka dole baffa yayi mamakin qanqancinta a kansa. Ganin yayi tsaye ya kasa qarasowa inda take yasa ta sauko daga saman gadon tare da takawa zuwa inda yake ta durqusa tana fad'in. "Ina wuni baffa?." Wani irin murmushine ya kuccema baffa da yasa haqoransa bayyana a lokaci d'aya yasa hannu ya d'agota daga duqen da take gabansa ya zaunar a bakin gadon sannan shima ya zaune gefenta had'e da cewa. "Lafiya klw nusaiba, bakiyi bcci ba." "Nafarayi sallamarka ta tasheni." Tafad'a tana murza d'ayar ijiyarta. Shiru yayi na tsawon wasu mintuna kafin can yajuyo qafarsa d'aya akan gadon itama yajuyo da ita suna fuskantar juna. "Nusaiba kinsan ya nake dake?" Yafad'a yana kallonta, saida tad'anyi jim sannan tace. "Yakumbo tace matsayin uba kake awajena ingirmamaka hakama kaka dasu baffa sunce kai shugabana ne inyi maka biyayya." 'yar dariya yayi don yafahimci metake nufi, anyimata nasihane data girmamasa saboda dattijantakarsa ta isa ya haifeta komanta zarta haka, sannan annuna mata shugaba take awajenta kasancewarsa mijinta wanda hakan zaisa dole tayi masa biyayya, wannan wata hikimace da nagartaccin iyaye keyi don d'ora 'ya'yayensu bisa turbar yin bautar gidan aure cikin ladabi da biyayya da koma girmama maigida, aransa yaji cewa tabbas yayi sa'ar nagartaccin ahalin mata awannan karon. Ajiyar zuciya yayi sannan yaciga da tambayarta cewa. "Me ake nufi da shugaba a gidan aure nusaiba?" "Mijin gidan." tabashi amsa hankalinta kwance. Yanda take amsa tambayoyin nasa cike da yarinta duk da dai tana fad'a daidai yasa yaqara gasgata qanqantarta don haka yaci gaba da tambayarta akan abunda yashafi karatun addini, kama daga tsarki da kashe kashensa, arwala, farillai, sunnoni da kuma mustahabbanta, yanda ake sallah da abubuwan data qunsa, wanka da kashe kashensa, banbancin Haram da halat acikin rayuwar auratayya duka saida ya tambayeta, yayinda kashi cas'in da twakwas bisa d'ari batasan komai ba sai 'yan qalilan daga ciki musamman ta b'angaren wanka, anan baffa ya fahimci cewa akwai aiki gabansa don dole tasan wud'annan abubuwan kafin komai yashiga tsakaninsa da ita, koba komai zuwa lokacin tasaba dashi kuma taqara sanin ko meye matsayinsa awajenta. STORY CONTINUES BELOW Yana wannan tunanin ne yaji anbubbugo qofar gida yamiqe had'e da ficewa yabar d'akin dama yanzu yake zancen zuwa yarufe don har qarfe goma tayi. Yana zuwa yatarar baffa Usman ne a qofar gidan riqe da ledoji a hannunsa ya miqo masa yana fad'in. "Yaya aini namanta da tsiren amarya har sai dana kwanta kuma nasan baka shiga da komai ba shiyasa nace Bari nafitu nan anguwarmu wajen habule mai nama inkarb'o maka tunda anan dai anguwar kusa banga tukubar mai nama ba, gashi ammafa aro nabaka kud'in." Yafad'a had'e da miqa masa ledojin yana dariya. Murmushi baffa yayi yakarb'a. "A gaida qanen nusaiba, ai gaba d'aya shaf ni namantan da wannan zancen, shine zaka fito awannan daren ai da kabarshi." "Inaa..ai ba'ayi hakan ba tunda sunna ce." "Hakane kuma, to nagode sosai ALLAH yabar zumunci, kud'inka kuwa har qari zanyi maka in Sha ALLAH." Saida Baffa Usman yayi dariya sannan yace. "Inaaa..kud'ina daidai zan karb'a bana son qari, salon kace ace nabada aron bashi na karb'i ruwa (bashi da ruwa).." haka sukayita raharsu kafin yawuce shi kuma baffa yarufe gida. A inda yabarta anan yasameta tana gyangyad'i ya ajiye ledojin gefe tare dad'an girgiza kafad'arta, zumbur tamiqe tsaye cikin gigin bacci tanufi qofar fita yariqo hannunta ya shiga toilet d'in dake cikin d'akin yace tayi arwala, Bayan sunfito yarufa mata mayafinta ya jasu sallah raka'a biyu sannan suka sallame, jawo ledojin yayi naman kazane qwaya d'aya da cire sai lemun Coca-cola na gora guda biyu ya tura mata agabanta yace taci, Citake tana rufe idanuwa had'e da sandare hannu cikin naman alamun har lokacin bacci nacinta don haka yasa hannunsa tare dayin bisimillah yana d'ebo naman yana tura mata abaki, haka yayita bata idanuwanta arufe tanaci har taqoshi don taci fiye da rabi saboda yunwar da takeji sannan yabud'e coke d'in ya azamata bakin gorarar abaki tafara sha, da sauri tabud'e idanuwa had'e da cire bakinta saboda yanda sanyi da gas d'inta suka shigar mata a hanci. "Bana shan wannan naqoshi." Tafad'a tana qoqarin zamewa takwanta anan inda take. Aje lemun yayi had'e da d'agata yaje ya wanko mata hannunta yabata ruwa tasha yakaita saman gadon takwanta ya lullub'eta sannan yadawo ya zauna ya canye ragowar naman yasha lemunsa sannan yafidda ledojin awaje. Yajima zaune yana tunanin abubuwa uku da suka yimasa kututu azuciya, nafarko rashin sanin halin da Nuraddeen ke ciki, na biyu zancen Rashida da aka tabbatar masa da cewa tadawo na uku rashin sanin inda amininsa yashiga wato mahaifin Rashida. ganin bayada tudun dafawar da zai samun mafita akansu yasa yamiqe yafara salloli yana kwararo addu'o'i akan ALLAH yakawo sassauci acikin jarabawowin rayuwarsu. ••• ••• ••• Baba na wucewa sashensu Rashida nafitowa cikin mota, jitayi gabanta ya tsananta fad'uwa da sauri tayi ta'awizi saboda korar shed'an, dama tunda taga annufo gate d'in gidan gabanta yasoma fad'uwa amma saita laqantashi da kyan gidanne da tsaruwarsa yasa tajin hakan, a hankali takebin ko Ina da kallo har zuwa lokacin da Fatima ta zagayo zuwa inda take tsaye tana d'an d'unguzarta da kafad'a. "Kai maman boy." Tafad'a tana d'an harararta. Dariya tayi had'e da cewa. "A'a aunty barni in kalli wannan aljannar duniya, tunda nake ban tab'a shiga cikin irin wud'annan gidajen ba koda kuwa a mafarki ne saidai in hangosu a tv." Hannunta Fatima taja tana d'auke da little sukabi bayan Dr nura daya wuce yana murmushi, "ALLAH kidena wannan qauyancin, idan ba haka ba kuwa nida yarona bazamu sake fita tare dake ba kada ki kofsa mana ko little?." Taqarasa maganar tana dariya had'e da kallonsa. STORY CONTINUES BELOW Dariya yayi tamkar wanda yafahimci metake fad'a yana qoqarin zillewa ya sauka qasa ganin annufo part d'in ammie, dama haka yakeyi duk sanda sukazo yafiso a ajiyesa yashiga da qafafuwansa, haka kuwa akayi ta ajiyesa da gudu yanufi cikin falo tana fad'in. "Little kadena gudufa?" Ita kuwa Rashida dariyar gudun nasa tashigayi tana fad'in "Wayyo ni ALLAH Rashida, wlh aunty yaronnan naki idan naganesa da daddare sai gudu, kingasa kuwa qurqur dashi sai kace d'an aljanu." 'Dago kai tayi tana kallonta had'e da harararta sannn tace. "Mungode, wato nida Dr mune aljanun ko?, Bari mushiga ai zanfad'awa uncle d'in naki abunda kikace." Hango ammie sukayi da tuni dr nura daya shiga yasanar da ita zuwan nasu tafito cikin shiga ta alfarma tad'auke little Nuraddeen da sai faman wangalar dariya yakeyi yana d'aga hannuwa. "Wowwww...Masha Allah, oyoyo maigida, wannan wanka haka gaskiya nasayeshi, iyyeeeee yaron Abba kasha kyau tubarkallah yau nikam auren dakai nakeyi." Shi kam banda dariya da gwarancin maganarsa da ba'a fahimta babu abunda yakeyi, d'ago kai ammie tayi lokacin da suka qaraso tana fad'in. "Maraba da 'yata takaina, kice yau tafe kuke da manyan baqi, bisimillah sannunku da zuwa" Tawuce gaba suna biye da ita har suka qaraso cikin falon, Bayan sun zazzauna suka shiga russunawa suna gaisheta cikin girmamawa yayinda shi kuma Dr nura kecan gefe zaune riqe da remote yad'ora qafa d'aya akan d'aya yana kallon wani shiri a tv. Gaba d'aya ammie ta manta dashi sai faman firarta takeyi dasu Fatima suna dariya kai kace ba surukarta ceba idan kaga yanda sukeyi, Rashida kawai ce bata wani saki jiki sosai ba, "Rashida kisaki jikinki mana, kemafa 'ya na d'aukeki tamkar su Fatima, don haka kid'auka nan gidanku ne har zuwa lokacin da zama zaiyi halinsa tsakanin mu dake kinji ko, koda inafatar ko hakan tafaru zumunci bazai tsinke a tsakaninmu ba ko?" "Insha ALLAH." Tabata amsa tana murmushi, Ganin sukayi Dr Nura yataso yana kumbura fuska ya d'auki little dake jikin Rashida yana faman jaye mata mayafi da alama nono yake son sha. "A'a son Ina zakaje kake qoqarin d'aukar Nuraddeen" don ita haka take kiran little, acewarta wai qara ariqa kiransa da cikakken sunansa yafi akan litte d'in. "To ammie fita zamuyi tunda yau gaba d'aya kin manta dani ta 'ya'yanki kawai kikeyi." "Ikon ALLAH, shine kake kumbura fuska haka?" "Eh mana, Nima ai da umma nan nasan zata kulani dani tunda kin shareni.?" "To da batanan fa?" "Nazama so lonely, waima Ina take ne? Yafad'a yana duba gefe gefen kitchen. "Aw sai yanzu kake tambayarta?, Ina tunda kashigo baka nemeta ba kuma kasan inhar dai tananan bazata barka haka ba idan kazo ko?" "Wlh shirincan ya d'aukemun hankali, ina tajene ammie?" "Babu inda taje, zazzab'i ke damunta yau shiyasa baka ganeta ba, Amma dai da sauqi don ban jima dabaro wajenta ba" "Ya Salam! ALLAH yasawaqe, Bari muje nida maigidanta mudubota." "To ai shikenan ka kyauta kuwa, kagaisheta idan kunje." 'Daukar little daketa faman rigimar shan nono Rashida tayi kamar bata fahimta ba yayi suka fice, Fatima tad'an harareta sannan tamaida kallonta ga ammie tace STORY CONTINUES BELOW "Kingata ko ammie?, Yaro nason yasha nono tahanasa shida kayansa, sai kace jiqawa zatayi tasha, ALLAH haka takeyi masa ko agida tayi kamar bata san rigimar me yakeyi ba." "A'a Rashida kidena yimasa haka, yaro fane sosai ina watansa goma akace ko?" "Eh." Tafad'a a kunyace. "Haba ai har yanzu yana buqatar ruwan nonon ajikinsa don sunada matuqar tasiri wajen basa garkuwa ga lafiyar jikinsa data qwaqwalwarsa, kidena ganin wannan girman d'an jikin da wayau da ALLAH yayi masa tunda bai shekara ba kina bashi nono isashshe yana sha kinji ko?." "Ai zakiga wasu yaran da wata tara har sun iya tafiya ga kuma d'an banzar wayo atattare dasu amma sukai har kusan shekaru biyu iyayensu na basu nono batare dasun damuba balle shi dake da wata goma da 'yan satukka akai." Dr nura kuwa d'auke da litte yanufi sashensu umma yayi sallama a bakin qofar shiga d'akin baba dake ciki ya amsa masa tare da bashi izinin shigowa, koda ya shiga kwance ya iskota lullub'e kanta na bud'e ya gaisheta tare da yimata ya jiki, shi kuwa little wajen baba yanufa ya d'aukesa yan dariya. "Kai babban mutum wannan gayun dai bazai burge amaryar kaba tunda kwance take tana fama da zazzab'i, abunda kawai za'ayi kabani kayannan naka sai in lallab'a maka ita ta tashi kugaisa." Baba yafad'a d'auke dashi yan gyara masa zaman hular kansa shi kuma sai hannuwa yake turawa cikin babbar rigar yana wasa da ita." Dariya yaba baba yace. "A gaisheka alhajin baka jeba, kodai alkhairi zakamun intaro hannu." Hatta umma dake kwance saida suka bata dariya, batasan meyasa yaron ke matuqar shiga ranta ba, ita dai har ga ALLAH jitake tana yimasa wani irin so nadaban, tana wannan tunanin taji ya hayikke jikinta yana qoqarin leqo fuskarta, shi kuma Dr nura suka fita tare da baba suna gaisawa yana tambyar mike damunta. Zaune umma ta tashi ta jawosa ajiki tana kallonsa, haka kurum taji tafashe da kuka wanda bako shakka kukan tunawa da 'yarta data hango kamarsa da itane, shin taya wannan yaron ya zamo jinin alhaji bayan jikinta da kamanninsa nafad'a mata akwai alaqa mai qarfi tsakaninsa da ita, wannan shine tmbayar da tashiga yiwa kanta tanaci gaba da kuka. Acan waje kuwa kud'd'i Dr yaba baba yace yaje yakai umma asibiti adubata saboda bai kamata ta zauna da zazzab'in ba tunda ba'asan meke damunta ba. Godiya yayi masa sosai sannan yakoma cikin d'akin ya d'auko little daya isko lafe ajikinta yana kallo yanda take kuka. Bayan Dr nura yawuce ya taimaka mata tashirya yana yimata fad'an tacire damuwa aranta kar azo ace itace keneman yimata barazana a lafiyar jiki sannan suka wuce asibitin. Basubar gidan ba sai bayan isha'i ammie tarakkosu har part d'in hajia nafeesa don su gaisheda dady tunda a part d'inta yake. Dr nura yafara shiga kafin su ammie da Fatima su shigo suma yana zaune shida hajia nafeesa da yaranta suna kallon wa'azin shaikh Ahmad tijjani Yusuf a tashar Sunnah tv, dama matuqar yana part d'inta to tashar ake kalla gaba d'aya saboda tarbiyar yaransa, idan kuwa baya part d'in basuda aiki sai kallon tashoshin waqe waqe da cartoon, Sallama d'auke abakunansu suka shiga aka amsa masu. Yaranta ko gaisuwa Babu suka mimmiqe zasu shiga d'akunansu dady ya katsa masu tsawa. "You stupid, bakuga mutane bane zaku shige baku gaishesu ba? Maza kudawo kugaisheshu." Yafad'a ransa a b'ace, kumbure fuska hajia nafeesa tashigayi tana binsu da harara har yaran suka duqa suka gaishesu suka tafi, Ita dai ammie naganin haka tagaida dady tare da d'aga wayarta da ake kira tafita don bazata juri walaqanci ba ko kad'an, Gaisheta dr. dasu Fatima sukayi ta amsa ciki ciki tana wani hurar hanta, Dr ya d'auke kansa daga kallon da yake yimata zuwa ga mahaifinsa yace. STORY CONTINUES BELOW "Am dama dady Rashida ce tazo gaisheku, kullum tana son tazo ALLAH bai yarda ba sai yau." "Af ikon ALLAH, maman little Nuraddeen kuke kiransa ko wa?" "Eh baffa." "ALLAH sarki, sannu kinji Rashida, ayita addu'a ana jurewa kowace irin jarabawa in sha ALLAH komi zai zama tarihi." "Hajia nafeesa kinga maman wannan yaron da kike tambaya kwanaki kina ganin Dr nashigowa tare dashi." "Au sannunki, ai nazata wlh agidan reno suka d'aukosa har ina cewa ALLAH dai yasa ba shege bane." Da sauri Dr suka d'ago kai su duka suna kallonta kafin dady ya girgiza kai cike da takaici yace. "Nafeesa kenan, to bahaka bane, da uwarsa..." Kafin yaqarasa yaji tace "Ai to baza'a gane hakan ba tunda ba'asan kowaye uban sa ba, Ina tsintar uwarsa akayi ko?." Bata qarasa ba ya katsa mata tsawa had'e da cewa ta tashi tabashi waje. Bayan tatafi dady yayita ba Rashida haquri kamar zaiyi kuka ita kuma tanuna ko ajikinta tunda tasan yanada ubansa, kawai dai dole zataji ba dad'ine ko kad'an, Fatima kuwa harda hawaye tana ganin da ace tana haihuwa baza'a tab'a jifarsu da zuwa gidan reno d'auko d'a, juyowa yayi gareta yaci gaba da cewa. "Fatima kada kibari kalaman auntynku suyi tasiri azuciyarki, ALLAH shi yake badawa bai manta daku ba in sha ALLAH jikina nafad'amun rabonku na kusa kusa domin akoda yaushe bamu cire qauna ga rahamar ALLAH ba, don haka kuyi haquri, kuyi haquri kunji ko?" K'wafa Dr yayi tare da miqewa yafita ransa ab'ace, dama shiyasa tun farko baya shiga sha'aninta ko kad'an saboda gujewa irin wud'annan matsalolin, dama albarkacin mahaifinsa takeci amma daga yau tagama. Sallamar Fatima yayi yarage daga shi sai ita da kuma little sannan yakira hajia nafeesar tafito daga d'aki, nuna mata kujera yayi ta zauna tana wani shashshan magani yace. "Nafeesa kinsan ALLAH." "Eh" ta amsa masa ciki ciki. "Wlh idan baki ba yarinyar nan haquri ba bisa abunda kika jefeta dashi narantse da ALLAH abakin aurenki kenan!" Da sauri Rashida tad'ago kai had'e da cewa. "A'a dady wlh babu komai nahaqura, ni batama yimun laifi ba idan ma tayi naya..." Bata qarasa ba sanadiyar juyowar da yayi fuskarsa a d'aure ya d'aga mata hannu da sauri tayi gum takama bakinta. "Zaki iya zab'an duk abunda yayi maki arai, amma hukuncin da nayanke yana nan babu ja da baya," Har zai miqewa yafita yaji muryar hajia nafeesa tace. "Kiyi haquri." Ciki ciki tana Mai jin wata iriyar tsanar Rashida da d'anta aranta. "Jeki Rashida, ALLAH yayi maki albarka." Yafad'a tare da ciro kud'i da batasan ko nawa bane yamiqawa little a hannu. Bayan tafita yakalli hajia nafeesa yace. "Kiguji duniya nafeesa da qyalqyalin dake cikinta, wannan rayuwar da kika d'auka bamai b'ullewa dake zuwa ga kyakkyawan qarshe bace shiyasa nake qoqarin aduk lokacin da kika tozarta wani agabana innuna maki kuskurenki saboda ko meye yazo maki da sauqi." "Amma alhaji.." "Rufemun baki." Yakatsa mata tsawa had'e da ficewarsa. Lokacin da Rashida kuwa tafito ta samesu tsaitsaye ammie nabasu haquri akan abunda yafaru don taji komai da kunnenta, haquri tasake ba Rashida sannan tace. "Son yakamata suje sugano umma kafin suwuce." "No... ammie tun d'azu suka wuce asibiti ita da baba saidai idan munqara dawowa." STORY CONTINUES BELOW "Ok son kuyi haquri don ALLAH kasaki fuskarnan taka, bana son inganeku cikin damuwa kinji ko 'yatah kuyi haquri." Murmushi sukayi kusan atare sannan sukayi mata sallama zukatan kowanensu ba dad'i kafin su shiga mota subar gidan, motarsu nafitowa daga cikin gate napep d'insu baba nawutowa sun dawo daga asibitin, kusan saida sukayi clashing da juna sannan napep d'in ta ajiyesu sukuma suka wuce. πŸ€ͺ *Target bend*πŸƒπŸ»‍♀️ *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [8/30/2020, 11:39 PM] S WHITEπŸ’Ž: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___63πŸ’Ž Tunda suka hau titi babu wanda yacewa wani uffan har suka isa gida, kowanensu ya lula duniyar tunani akan yanda rayuwa zataci gaba da tafiya dasu bisa linzamin qaddarar da suke akai, musamman Dr nura da yake ganin gaba d'aya cinmutuncin da matar mahaifinsa tayi akansa yaqare, don haka akwai buqatar ya d'auki matakin yiwa abun tufqa tunkafin yayi tsayi. Gaba d'aya sai sukajidaren ranar yazo masu abai baice, hatta 'yar firar da suka sabayi a kowane dare kasawa sukayi kowane ya shige part d'insa ya kwanta, haka ma da safe kusan yanda suka kwana haka kowane yatashi fuskarsa babu wata walwala har suka zauna wajen karyawa ba wanda yace wani abu bayan gaisuwa, miqewa Rashida tayi bayan tagama nata Karin zata wuce d'akinta taji muryar Dr yace. "Koma kizauna maman boy ina son zamuyi magana dake." Bamusu takoma ta zauna yayi gyaran murya had'e da cewa. "Ina mai baki haquri bisa abunda yafaru jiya, da nasan hakan zata kasance wallahi da ban d'aukeki nakaiki gidan muba, gashi hakan da nayi na neman sauya walwala da kuma farincikin gidannan gaba d'aya, naroqeki kimanta da abunda yafaru domin haka zaisa rayuwarki taci gaba da inganta kamar yanda tafaro, tabbas Bata kyauta ba data cutar dake ta hanyar munanan kalamanta batare da tasan koke waye ba! kuma ko kad'an batayi maki adalci ba a matsayinta na uwa da tasan irin zafin da akej idan aka aibatawa mutum d'a, Amma duk da haka Ina nema mata afuwa a matsayinta na matar mahaifina, ina tabbatar maki da hakan bazata sake faruwa ba in sha ALLAH kinji." "Uncle kenan! bazance banji komai araina ba akan abunda yafaru jiya kasancewar yazamo silar jefaku cikin halin da tunda nake zaune daku ban tab'a ganinku acikin koda makamancinsa ba, ba ina damuwa bane akan abunda tayi mani ba, kawai damuwata tabayyana ne adalilin yanayin da nake kallon fuskokinku aciki, kalamanta abune da babu tushe, asali ko kuma inganci aciki da har zan damar da kaina. amma shi b'acin ranku da kuma damuwarku tamkar wutace dake cin zuciyata idan Ina ganinku acikinsa wanda natabbata bazata dena ciba har sai lokacin da naga farinciki yabayyana fuskokinku, kuyi haquri domin nima nazamo sila wajen sa ajefeku da kalaman da suka cutar da zukatanku." Kallon Fatima Dr yayi had'e da cewa. "Kijifa abunda take fad'a!, taya za'ayi tazamo silar cutuwar zukatanmu bayan laifin ita akayiwa." "Hakan nafaruwa kuwa Dr, musamman ga zukatan da basu fiye son kansu ba kuma suke kallon damuwar wasu amatsayin tasu, don haka damu da ita mu manta da komai mu fuskanci gabanmmu." "Shikenan ALLAH yaqarawa zukatanmu haquri kuma yabasu girman d'auke duk wata jarabawa da kuma gwagwarmayar rayuwa." "Amin ya rabbi." STORY CONTINUES BELOW Suka fad'a tare suna murmushi, nan suka dasa rankon sabuwar firar da basuyi ba jiya, Bayan wata uku little yaqara wayau Rashida ta yanke shawarar yayesa saboda ganin irin girma daya taso masa kuma babu abunda bai iya ciba. Ana saura sati d'aya tayayeshi suna zaune ita da fatima tace. "Aunty nifa wani sati cire yaronki zanyi amama, ALLAH nagaji da tsutsannan da yakeyimun." "Kai maman boy, shekararsa d'aya da wata d'aya fa kenan?" "ALLAH nagaji aunty zalina yakeci sai yayita cizona da haqoransa masu kaifin tsiya sai kace reza." dariya Fatima tayi had'e da cewa. "Aikuwa baki isa ba, sai yayi 2years tukuna, haquri kawai zakiyi kema wayasan yanda ummanmu tayi fama dake." "ALLAH sarki umma, ai da zaku had'u kika tambayeta Allah zata fad'a maki bata wani sha wahalar renona ba saboda da kanta take fad'a cewa ni 'yar baiwa ce." "ALLAH!?" Fatima tafad'a tana dariya hadde da zaro idanu, gwaggo mai aiki dake goye dashi tana mopping tace. "Gaskiya hajia ta yaye yaron nan tunda ya iya cin komai, tubarkallah qato dashi gayanan yana neman karyamun baya," "Laaa...gwaggo har dake?, Zo kawomun yarona indai goyone daga yau yadena son naki." Qarar wayar rashidane data jiyo rurinta ad'aki ya katse firar tayi saurin miqewa don ta d'auko gwaggo tace "A'a Bari nad'auko maki, Amma cin hancin yaye d'an hajia ne zan baki." "Aikuwa angama gwaggo." Rashida tafad'a tana dariya "Ai sai kuyi bari abbansa yadawo zan fad'a masa ai." koda gwaggo takawo mata wayar har tayi missed call, murmushi tayai ganin lambar Yaya Maryam da kullum saita kira idan bataji takirata ba taji ya lafiyarau take ita da litte, saurin kiranta tayi don kada tasake kiranta bugu d'aya ta d'aga. "Rashida ya kike? kuna lafiya." "Lafiya klwa gwaggo ya wajensu baba balarabe?" "Kowa lafiya Rashida, Ina maigida." "Gashinan ya hayewa gwaggo mai aiki baya, dama yanzu nake zancen zan yayesa da aunty saboda mugun tsotsans." "Kul! Karki fara, kibari koda wata biyar ne nan gaba yad'an qara qwari kinji nafad'a maki ko?" 'bata fuska tyi kamar zatayi kuka had'e da cewa. "Kai gwaggo kinga yanda yazama wani tulele dashi, ALLAH bazan iya da tsutsar saba." "Cit d'inki, kenan ummanki sau uku tana zancen yayeki amma saboda qulafucin nono saita fasa har saida kika shekara biyu cif sannan ta yayeki, shima d'in haka kika dingayi kamar zaki mutu duk kikabi kika tada mana da hankali." "Nid'in gwaggo!?" Tafad'a tana kallon fatima dake jin duk abunda Yaya Maryam kefad'a tana gumtse dariyar dake neman kucce mata. "Ked'in fa, some some nawa kikayi?, Banda ALLAH yayi zakinfita ai da yanzu saidai labarinki, don haka kibari sai nan da wata hud'u idan ALLAH yasa munada rai." "Shikenan gwaggo, ya labarinsu ummana?" "Kiyi haquri Rashida har yanzu bawani labari akansu, amma munanan muna addu'a ALLAH ya karkato hankalinsu sudawo gida." Wata gauruwar ajiyar zuciya tayi kafin suyi sallama tana dubon inda Fatima ke zaune, kashe mata ido d'aya tayi had'e da d'aga mata gira tana dariya tace. "To 'yar baiwa ya akeyine?." "Ummaaa!.." tafad'a cikin sigar damuwa. "ALLAH sarki, ummanmu gaskiya baqaramin so da tausayinki take ba, amma ke shine kike so kicuci yaronmu, to ALLAH yakama ki duk naji abunda Yaya Maryam tafad'a, ashe haddasu some some akayi akan nono, oh ni Fatima! gaskiya umma taga jalala." taqare maganar had'e da tintsirewa da dariya tana tafa hannuwa, tayi hakanne saboda tadaqile tasirin damuwar dake shirin ziyartar Rashida akan zancen rashin dawowar iyayen nata da suka gama da Yaya Maryam. STORY CONTINUES BELOW Binta da kallo Rashida tayi tana murmushi, a zuciyarta tana mai addu'a, Allah ya dawwamar da irin wannan farinciki da Fatima ke ciki atattare da ita nahar abada. Dr kuwa tunda yaji zancen Rashida na Shirin yayen little shima yafara shire shiren nema mata takardun shedar kammala primary, dama sun tab'a maganar karatun da ita tafad'a masa primary ne kawai tayi har take basu labarin yanda tahad'u da abban little a sanadiyar rashin son karatunta sunata dariya, bai wani sha wahalar samun takardun ba saboda yanda komai ya lalace zaka iya samunsu matuqar akwai kud'i atare dakai, kafin kace me har yagama had'a takardun da cike mata form d'in shiga makarantar gaba da primary na wannan shekarar tare da taimakon Fatima batare da sanin Rashidar ba, akoda yaushe Rashida cikin farinciki take natakusa yaye little Nuraddeen tahuta da tsutsa ita kuma Fatima nayimata dariyar maida ita makaranta da suke shirinyi bada saninta ba, wanda ALLAH kad'ai yasan yanda za'a kwashe matuqar har yanzu tana nan akan bakanta na rashin son karatu. Satin yaye little nakamawa tahad'a gaba d'aya sauran kayansa dake hannunta takaiwa Fatima suna tayi mata dariya ita da Dr. "Ikon ALLAH, maman boy wannan wace irin korace haka akeyiwa takwara, anharhad'o komai nasa sai kace zai bar gari" "Uncle sunanta kora da hali, gaba d'aya nayi handing over dashi, gashi ga mamarsa kar akoma cewa ansanni, yabarni inhuta abuna ko d'akina kada yakoma leqawa har sai jinin jikina yadawo." "E'em kedai! karfa ayi haka bayan kwana biyu kice kinyi missing d'insa." "Cab! Uncle little d'in?, Ai yanda take addabar rayuwata da daddare babu wani missing d'insa da zanyi." "Kika ce?" Tayi dariya kawai had'e da juyawarta tabar falon fatima nafad'in. "Muna nan dake zakizo ganinsa muma muyi maki handing over." Randa akayi yayen little kuwa ba qaramar rigima suka shaba duk daya saba kwana wajensu amma sai kace wanda aka fad'awa yayesa za'ayi haka yadinga yimasu kuka cikin dare, sunyi lallashi har sungaji amma yaqiyin shiru, idan tayi tagaji taba Dr shima yayi nashi lallashin amma kamar ana sake sake turashi, ALLAH sarki Rashida tun tana iya sauraren kukan har takasa tasa pillow ta dad'e kunnuwanta amma bata dena jiba, tashi tayi tayi zaune tsakiyar gadon tanajin kukan nasa har cikin ranta batasan lokacin da itama tafashe da kuka ba, batasan meyasa ba ko kad'an bata iya jurar kukansa gashi bazata tab'a iya fita da sunan taje taduba saba, d'aga hannuwanta tayi sama ahankali tafara yimasa addu'a. "Ya ALLAH Kai kake karb'ar addu'ar mahaifiya ga d'anta, ALLAH kasa masa dangana, ya ALLAH kamar yanda yabar nono na ayau ALLAH karabashi da duk wani musibar rayuwa tun daga qanqantarsa har zuwa girmansa, ALLAH kasa yazamo mai juriya da haquri acikin rayuwarsa kuma ka albarkaceshi kasa amfani mai tarin yawa acikin wanda yasha na tsawon wannan lokacin." Tana gamawa takoma takwanta tana cigaba da saurarar kukan nasa, ahankali tafara jin sautin kukan nasa na ragewa har tadena ji gaba d'aya, ajiyar zuciya tayi sannan tagyara kwanciyarta har bacci b'arawo yazo ya saceta. Haka sukayi ta fama dashi har kwana biyu duk da qarfin hali kawai ne Fatima keyi itama kullum da zazzab'i take kwana, amma saboda shi take jurewa, arana ta uku ne safiya nawaye koda Dr nura yatashi yaganta a qudundune cikin bargo jikinta sai faman rawa yakeyi, "Subhanallahi, Fatima bakida lafiya ne?" Yafad'a yana yaye bargon, yanda yagata ba qaramin tayar masa da hankali yayi ba da sauri ya Ida cire bargon yatada ita had'e da rungumota ajiki yana tattab'a wuyanta da goshinta, "Fatima ko ciwon kanne?" Yafad'a arud'e da sauri ta d'aga masa kai had'e da cewa. "Inajin sanyi sosai." STORY CONTINUES BELOW Yatabbatar da haka don gaba d'aya jikinta yayi zafi sai rawar sanyi takeyi, First-aid d'insa yatashi ya d'auko yaciro maganinta na ciwon kai da take yawanyi ya b'alla mata yabata tasha ya had'a mata dana maleria sannan ya maida ita ta kwanta ya lullub'a mata bargo yana yimata addu'a. _As'alallahul azhim, rabbil arshil azhim, anyashfiki, laa ba'asa d'ahurun in sha ALLAH_ Ya tofa mata had'e dayi mata sannu sannan yayi kissing d'inta a goshi yabar d'akin, bayan mintuna biyu yadawo ya d'auki little dake sharkar baccinsa hankali kwance dama haka yakeyi, ya hanasu bacci da daddare da safe kuma yayita sharkar abunsa har rana, yanufi wajen Rashida dashi yace tagyarashi zai kaishi wajen ammie Fatima batada lafiya, nan take Rashida taji ba dad'i aranta sai take ganin kamar rigimarshi ta haifarwa da Fatima rashin lafiya. "Uncle baka ganin zai dami ammie sosai tunda baya bacci da daddare." "Nooo..Bakomai ki gyarashi, ai taso akaimata shi tun farko mu mukaqi ganin zaifi sauqi tunda yafi sabawa damu, amma yanzu tunda ga dalili sai akaimata shi, koba komai zata sama mashi maganin da ake ba yara na yaye tunda mu bamuyi dubarar haka ba?" "Shikenan uncle." tafad'a tare da karb'arshi agurguje tashiga shiryashi, koda yadawo d'auke da akwatinsa har tagama shiryashi yakarb'esa sannan yanufi wajen ammie dashi. Satinshi biyu a hannun ammie kuma yana samun kulawa sosai wajenta da kuma umma da kusanma yayen awajenta yake, don matuqar dady na part d'in ammie to awajenta yake kwana, little kam har zazzab'i yayi shima kusan sau biyu amma Rashida bata tab'a zuwa dubosa ba saidai Fatima da Dr suje duk da har yanzu itama tana fama da zazzab'in, babu yanda fatima batayi da Rashida ba akan taje taduboshi don har saida aka kwantar dashi asibiti na kwana d'aya amma taqi zuwa. Baba balarabe kuwa da aka sanar dashi safiya nawayewa yaje ya sanar da Yaya Maryam suka yanke shawarar zasuje ganinsa idan ALLAH yakai ranmu gobe,..... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [8/31/2020, 11:38 PM] S WHITEπŸ’Ž: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___64πŸ’Ž Cikin daren Yaya Maryam takira aunty marwiyya tasanar da ita zancen tafiyar zuwa borno tace. "Bazata samu dama ba saboda itama mai gidanta bayajin dad'i, Amma don ALLAH idan sunje su gaishesu sosai." Kasancewar son sukeyi suje ranar sudawo yasa tunda sassafe suka shirya, aron mota baba balarabe ya samo masu su hud'u, dashi da alhaji ubale mijin Yaya Maryam, sai ita da kuma matar baba balarabe guda wato uwar gidansa sukasa mai sannan suka d'auki hanyar zuwa borno... ••• ••• ••• *FEDERAL NEUROPSYCHIATRIC HOSPITAL (KWARE) SOKOTO.* canne asibitin da Yaya hawwa ke jinya, duk wani qoqari da yakamata ayi wajen bata kulawa anyi amma abun sai sake hab'b'aka yakeyi, allurori, magunguna da gwaje-gwaje don gano matsalarta da kuma yimata maganinta kullum cikin yimata ita ake, baffa yakashi kud'i da baisan iya adadinsu ba amma babu wani sauyi ko cigaba da aka samu, kullum al'amarinta jiya iyau, kimanin shekara d'aya da watanni kenan yanzu. Duk wanda yasan Yaya hawwa duniya ya kalleta ba lallene ya iya ganeta ba saboda yanda tabi talalace haukan dake saman kanta yafi hauka muni don hatta mahaukatan dake tare da ita sunfara tsoronta saboda tana cutar dasu, hakan yasa aka killace ta ita kad'ai batare da kowa ba, idan abun ya motsamata saidai jami'an lafiya suga tana lallaqe ailin da bango tamkar wata halintar daba mutum ba, sunaji suna gani zata dinga buga kanta ga jikin bango har sai yayi jini kuma duk wanda yaje cetonta in sunkai su goma suna fitowa da wata kamar tadaban daba tasu ba, kasancewar ma aikatan lafiya mutanene masu matuqar qoqari da kuma jajircewa wajen ganin sunyi yaqi da duk wata cuta dake damun marasa lafiyarsu batare da sun nuna gazawarsu ba yasa gaba d'aya likitocin suka zauna suka yanke shawarar had'a taron gaggawa na qarawa juna sani daga b'angaren mabanbanta likitoci kamarsu daga wasu asibitoci da sauran garuruwa akan wannan sabuwar cutar da Yaya hawwa ked'auke da ita wacce suke tunanin tana nema tafi qarfinsu don samun mafita mai d'auke da topic _HOW TO TREAT PATIENT WITH UNKNOWN NEUROSIS.._ STORY CONTINUES BELOW Cikin qanqnen lokaci taron ya wakana, manyan likitoci daban daban sun tashi sunyi bayani kala kala akan wannan matsala tare da samun solution d'aya da suke tsammanin shine qarshen matsalar, Haka kuma tundaga sokoto wani babban likitansu yaje kano don samun cikakken bayanai akan asalin yanda lalurar tasami yaya hawwa, da baffa Usman suka fara cinkaro kasancewar sun sanshi tunda sune suka kaita asibitin, duk wasu tambayoyi da suka yimasa qin amsa masu ko d'aya yayi har saida ya aika aka kira baffa, gefe suka keb'e dashi yayi masa bayanin abunda ya kawo likitan, d'ari bisa d'ari baffa yayi masu bayanin cewa cutace kawai da suka wayi gari suka ganta da ita, wacce bazasu iya cewa ga dalilin daya haifar mata da itaba, duk yanda likitan yakai qwarewa wajen ganin yasamu wani labari da zai iya basu haske aikai bisa tattaunawar da sukayi wajen taron qarawa juna sani cewa cutar nafaruwa ne tadalilin wasu kalolin halittu masu tsananin tsoratarwa dake bijirowa marar lafiya daga nan sai tasirin ya halbu ga qwaqwalwarsa tayanda zata riqa juyawa tana qara d'auko masa hoton abubuwan, daga nan kuma sai zuciya tafara aiki da sauri sauri saboda tsananin tsora sai kuma suriqa ganin duk wani abu da zai fuskantosu to cutar dasu zaiyi daga nan kuma sai tana tunzura jiki wajen baiwa kai kariya ko kuma neman kub'uta daga inda mutane suke zuwa wani wajen da suke ganin shine zai basu kariya idan sun kad'aita, duk hakan nafaruwane ta dalilin yawan mu'amalar da marar lafiya yayi da wajajen dake d'auke da abubuwan ban tsoro inda ba'afiya samun mutane awajen ba da kuma mu'amala da wani abun da kake tsoron zai iya cutar dakai alokaci d'aya ko rasa wani abun da kake so, amma baffa yaqi cewa komai akan haka, saboda yana kallon fallasa dalilin faruwar haka agareta amatsayin zubar da kimarsa da kuma ta d'ansa. Haka likitan yaqari masu tambayoyin yagama amma bai samu wani haske akan wancan bayaninba balle sutabbatar da hakan, har zai tafi saiga baffa Ali shida matarsa sun dawo daga wani wajen da ako yaushe suke zuwa tare, tsabar gulma shida bawani shiri yake da 'yan uwan nasa ba amma saboda yaga babban mutum d'an birni tare dasu yanufi wajen. "Assalamu alaikum, ahhh baqo akayi?" Yafad'a yana kallon baffa Usman, eh, yabashi amsa ataqaice yana qoqarin jan hankalin likitan subar wajen, d'an matsowa baffa Ali yayi yana kallon likitan had'e da goge hannunsa ga rigarsa sannan yamiqa masa yana fad'in. "Assalamu alaikum, sannu bawan ALLAH, yanzu ake tafe." Kallonsa likitan yayi kafin yamaido kallonsa gasu baffa yan tambayarsu shima tare yake dasu saboda ganin yanda sukayi kama su ukun sosai, baffa ya d'aga masa kai, cike da qyanqyamin yanayin da yaganshi na qazanta likita yamiqa masa hannu suka gaisa yana washe baki donshi yazata wani alkhairi ne zasu samu shima ya lakata. "Ok ko zan iya tambayarsa ko yanada wani bayani d'aya sani akai tunda tare kuke a gida d'aya?" "A'a Dr iya bayanin da muka yimaka shikenan daga shi babu wani abun, Aliyu zaka iya wucewa." Baffa Usman yafad'a yana tura baffa Ali cikin gidan, rigima suka soma yi baffa yariqe masa hannu. "Barshi Usman, Aliyu zo kafad'i abunda kasani. Cikin jin haushi baffa Ali yagyara rigarsa yana hararar baffa Usman, tambayarsa likita yashigayi akan matsalar Yaya hawwa ko akwai abunda yasani ai kuwa baffa yabud'e baki yanda kukasan indararo yanata zubawa likita bayani akan zuwan Yaya hawwa dajin qare kukanka har zuwa silar haukacewarta. Sosai likitan yaji dad'i kuma yasamu amsar da suke buqata yayi sallama dasu yawuce, ahasale baffa Usman yayi kan baffa Ali yakai masa naushi yafad'i qasa bakinsa yafashe da jini, cikin b'acin rai yashiga nunasa da hannu da hannu yana fad'in. "Anya wai kai mutun ne?, Wace irin zuciya gareka mai cike da son cutar da 'yan uwanka, wai kaima d'an uwane koko d'an wuta?..tir da halinka wlh kahi hasarar rayuwarka aliyu matuqar baka canza ba." STORY CONTINUES BELOW Wani naushin yasake kaimasa lokacin daya taso yana son fad'a masa magana yasake fad'uwa yabishi qasa zai dakai baffa yayi saurin riqe masa hannu, idanuwansa na zubar da qwalla yace. "Don ALLAH Usman ka qyalesa, kada kabiyeshi duniya ta zagemu a matsayin munfito ciki d'aya muna wannan hasuma, meye laifinsa ga abunda yafad'a Usman?, Wannan shine sakamakon abunda yakamata yamayarwa da hawwa bisa tonawa da binnewar da sukayi atare, wataqil inhar yad'a labarin suke sonyi akan cutar dake damunta don mutane su kiyaye sai yazame mata kaffara tahanyar rage mata zunubanta, kuma tazamo silar d'aukar darasi ga duk wani mutum mai hali irin nata ko son aikata abunda tayi don gujewa gobensa, ka qyalesa zo mutafi." Yafad'a tare da jan hannunsa sukabar wajen. Tofar da yawu cike da jini baffa Ali yayi yashiga d'ura masu zagi kala kala yana fad'in daga yau babushi babu su. haqiqa ba qananan kud'i asibitin suka kashe ba wajen ganin sun yaqi wannan lulura da suke ganin kamar wata sabuwar cutace kuma suke fatar asibitinsu tazamo tafarko wajen kauda ita kafin ta watsu ga duniya, Nan take manyan kafafen yad'a labarai a qasar nan da kuma gidajen jaridu sukayi dandazo a asibitin don samun tattaunawa da manya manya likitocin da suka jagoranci wannan shiri nakawo qarshen cutar da suka rad'awa suna _neurosis2020_ kan kace me tuni cikin qanqanen lokaci labarin lalurar haukar yaya hawwa yazaga ko ina ta kafafan yad'a labarai tahanyar fira da babban likitan asibitin yana wayarwa da mutane kai akan lalurar ana bayani ana nuno Yaya hawwa da irin yanayin da take ciki da wanda take shiga idan yamotsa, wasu idan sungani tabasu tausayi wasu kuma suyi ALLAH wadda da ita, wasu kuma subita da addu'a. Nan take suka maida kud'ad'en da suka kashe har riba tabiyo baya, kuma Alhamdulillah bisa sabuwar kulawar da aka koma bata tamusamman sun fara ganin canji akan gwaje-gwaje da suka sake yimata daga baya duknda dai har yanzun akwai sauran rina akaba. ••• ••• ••• Su baba balarabe basu isa garin borno ba sai kusan qarfe d'aya na rana, baba balarabe yakira Dr yasanar dashi zancen isowarsu lokacin yana zaune sungama shiryawa shida Fatima suna fama da ita akan taje ta sako mayafinta suje ganin little Nuraddeen agidansu ammie amma taqi, sai da taga Dr yad'aga wayarsa yana fad'in. "Na'am baba har kin iso, eh to kutsaya adaidai junction ganinan zuwa." Waro idanuwa waje tayi had'e da cewa "laaa uncle wane baban?" "Baba balarabe." Yafad'a in I don't care d'innan yana fad'in Fatima ta tashe suje don dama bai sanar da Rashida batun zuwansu ba su ammie kad'ai ya fad'awa. "Aunty dama zasu zo shine baku fad'an ba.?" "Eh to, aiba wajenki zasu zoba shiyasa ma ba'anan zasu sauka ba, gidansu ammie zamu saukesu tunda yarona sukazo dubawa kuma kinga ke kince baki zuwa shiyasa ban fad'a maki ba." "Amma dai zasu zo ko?" "Ina, Ina kibar wannan zancen kawai, idan kina son ganinsu kizo mutafi idan kuma bakya so to kizauna warki anan, mu muntafi" Dr yafad'a yana gumtse dariyar shi had'e da ficewa Fatima nabiye dashi abaya. Ganin hakan yasa taje ta d'auko mayafinta ta lullub'a tana turo baki itama tabi bayansu. Suna kawowa titi yayi parking da motar yace Fatima tajesu sutafi shi zai hau mashin yaje yazo dasu baba balarabe. Cike da kunya Rashida tashiga gidan tana wani nonnoce kai qasa Fatima sai dariya take yimata har suka isa, Kuda suka shiga part d'in ammie tana kitchen suna girki ita da umma, Kai tsaye Fatima taja hannunta suka wuce bedroom d'in ammie saboda warin girkin da taji yabugar mata hanci, "Kai aunty meye bazamu tsaya a falo ba har sai munzo d'aki." "Maman boy bana son qamshin abincin, mu zauna warmu anan bari nakirata awaya." tafad'a tana ciro wayarta cikin jikka. STORY CONTINUES BELOW "Hello ammie mun iso gamu a bedroom d'inki?" "Ok Ina zuwa." Tabata amsa, tana shigowa sukayi ido biyu da Rashida databi yanda d'akin yatsaru da kallo, da sauri ta jid'ar da kanta qasa tana wasa da 'yan yatsun hannunta. "A'a 'yata kice yau bikon maman Nuraddeen kika yomana, koda yake nasan badon mijina tazo ba don taga iyayenta ne ko Rashida." Ammie tafad'a tana dariya. Saukowa daga zaunen da suke kan doguwar kujerar dake cikin d'akin sukayi had'e da duqawa har qasa suka gaisheta tadafa kansu tana fad'in. "Lafiya qlw 'ya'yan albarka, kutashi ku zauna ALLAH yayi maku albarka." Itama ta zauna bakin gado. "Agaisheki Rashida sarkin fulanin duk duniya, wato haka kika yiwa maigidana sai yau don kinji su gwaggonki zasuzo ko?" Murmushi kawai Rashida tayi batare data tanka ba har lokacin kanta naduqe aqasa. "To ai shikenan kin kyauta, ALLAH yarabaki da wahala, 'yatah ya jikin naki da sauqi ko?" "Eh ammie, kawai yanxu baccine ke yawan damuna." "To may be rankon wanda bakiyi bane kwanakin baya, Ina son take?" "Yaje tahowa dasu Yaya maryam." "Au har sun iso? Bari make muqarasa aikin kafin su iso, Rashida kinemi kud'in da zakifa biyamu kafin mugwada maki maigida naga sai warar idanuwa kikeyi kina bid'ar inda zaki hangoshi." Cike da tsokana ammie tafad'ima rashida haka sannan tafice tana dariya. Koda su Dr suka iso su ammie na a harabar gida ita da dady suna jiran isowarsu ita kuma umma nacan tagama shishshirya abincin da sukayi tana gyarawa little daya qara wayau yayi kyau sosai, tawai tashiga yimasa tana fad'in. "Maigida mai raki, d'an Fatima mai kukan yaye, mijin hajiya mai babbar kyauta." Baba kuwa dake gefe zaune yana kallonsu sai faman dariya yakeyi, shima little d'in dariya yakeyi harda qyaqyatawa riqe da marfin mai yana wasa dashi. Cike da farinciki su ammie suka tarbesu had'e da yimasu iso zuwa part d'in nata, bin gidan su baba balarabe sukayi da kallo suna jinjina ki had'e da mamakin yanda suka fita daban acikin masu arziqi wajen girmama d'an Adam da kuma karrama shi har suka iso cikin falon, Yaya Maryam kam kusan lumfashinta d'aukewa yaso yayi saboda irin qamshi da sanyin a.c daya bugi fuskarta, ji tayi jiri na neman d'ibarta da sauri tariqe hajia Aisha matar baba balarabe, juyowa tyi takalleta had'e dayin murmushi cikin murya qasa qasa tace. "Yawwa Yaya riqeni, nima nan jiri d'ibata yakeyi ina neman fad'uwa" "Bari Aisha! wannan shi ake kira da aljannar duniya, anbasu duniya kuma ga dukkan alama lafira ma zasu samu" Bayan sun zazzauna ammie taje da kanta ta d'auko masu ruwan swan masu sanyi a tire tana jero masu sannu, bayan ta ajiye masu ruwan takoma ta d'auko wasu had'e da kofuna tanufi d'ayan parlon da dady yaja su baba balarabe, Saida ta ajiyema kowanensu agabansa sannan tanemi d'aya daga cikin kujerun tazauna tana gyara mayafinta dake qoqarin zamewa fuskarta asake. "Sannunku da zuwa, ya hanya?" Saida mijin Yaya Maryam ya ajiye cup d'in daya tsiyaya ruwan yasha sannan suka had'a baki shida baba balarabe suna fad'in. "Yawwa hajia, hanya Alhamdulillah, mun sameku lafiya?." "Lafiya klw wlh, ya kuka baro mutanen gida." "Kowa lafiya klw hajia, since agaisheki sosai da d'awainiya ALLAH yasaka da alkhairi." "ALLAH sarki ai Bakomai yiwa kaine, " "Hakane gaskiya angode sosai, yau ALLAH yanufa kun ganemu agarinku waccan rangon saurayinnan naku ya taddomu cikin wannan rana saboda rakinsa sai kace ba namiji ba." STORY CONTINUES BELOW "Aikuwa dai ya kyauta tunda gashi yasa anyi zumunci." "Hakane gaskiya, tofa angode da d'awainiya sosai Ubangiji ALLAH yabiya kuma yasaka maku da mafificin alkhairi." "Amin ya ALLAH." Ta amsa masu had'e da miqewa tanufi wajensu Yaya Maryam ta barsu nan tare dasu dady suna qara gaggaisawa. "Hajiya sannunku fa da hanya, don ALLAH kuyi haquri nabarku zaune ko?" tafad'a lokacin da take qoqarin shigowa inda suke. "Ai babu komai hajia, ya gida munsameku lafiya." "Lafiya klw Alhamdulillah." "Ya 'yan yaye sarakunan raki da jiki, muna zaunenmu yatado damu muda angwayenmu saboda rakinsa." "To ayi haquri hajia, ba raki bane kewarku ce tayi masa yawa shiyasa shi zazzab'i, gashi kuma tunda kuna son maigidan kun rugo ko kuwa?" "A'a indai mazan rakine mun barmiki namu sun ishemu, mukam dai albarkacin 'yarmu mukazo gani ba shiba." Yaya Maryam tafad'i hakan tana dariya. "A'a fa hajia, karfa yazo kugansa kuce baza kubi su alhaji ba ku kunga wurin zama inda maigidanku yake." Rashida kuwa tunda taji muryar su Yaya maryam take qoqarin fitowa Fatima tariqeta had'e da cewa tabari sugama gaisawa tukuna suma sufita gaishesu. Muryar ammie sukajiyo tana qwalawa Fatima kira da sauri tamiqe had'e da amsawa sannan tacewa Rashida tazo sutafi. Tare suka fito da gudu Rashida taruga qiris kad'an ta ture fatima tana fad'in "oyoyo gwaggona nayi kewarki sosai." Dariya duk suka aza mata Yaya Maryam nafad'in. "Oh ni maryama ko yaushe Rashida zakiyi hankali." "Kai gwaggo da hankalina fa, kawai dad'i nakeji naganku, ina su baba?" "Gasucan awancan d'ayan falon ammie tabata amsa tana mamakin irin sakewar da tayi, amma d'azu gaba d'aya tabi duk ta takura, sai alokacin Rashida ta tuna da ashe ammie nawajen cike dajin kunya tamiqe tanufi inda su baba balarabe suke cike da farinciki. Murmushi Fatima tayi lokacin da take qarasowa wajen tana girgiza kai tare da duqawa tagaishesu tana yimasu sannu da zuwa. Bayan sungama gaisawa ammie tace. "'yata jeki kikira umma tazo takawo masu Nuraddeen, naga matan nan nasa sai hararata sukeyi." Gaba d'aya sukasa dariya suna fad'in. "A'a hajia indai wannan maigidan nakine mai kukan yaye mun barmiki kiyita kaya basai yazo ba." Suna rufe baki umma nashigowa d'auke dashi yana wasarsa cike da gwalamniya, kasancewar taqofar baya tashigo yasa Rashida dake qoqarin fitowa daga wajen su baba balarabe tana dariyar labarin da suke bawa dady nata lokacin da aka yayeta tayi ido biyu dasu, kasancewar bataga fuskar umma daidai ba saboda tajuya tana yimasa wasa should kad'ai tahango gasu ammie a tsakiyarsu tasan bazata rasa ganinta ba yasa tayi saurin sadda kanta qasa, can kamar an tsinkaleta tayi saurin d'ago kanta tunawa da gefen fuskar wacce tagani, turo idanuwa tayi ganin wai ummanta ce agabanta d'auke da little, jitayi lumfashinta na neman d'aukewa da sauri tace. "Um..um..ummah.." tana nunata da hannu, Da qarfi umma ta d'ago kai jin muryar 'yarta tilo da bazata tab'a mantawa da ita ba, yayinda gaba d'aya su ammie suka miqe suna kallon abunda ke shirin faruwa, Ganin umma na neman sandarewa a inda take tasaki little yasa Fatima qarasawa da sauri takarb'esa tana kallon ikon ALLAH, Rashida da tuni hawayen farinciki suka jiqa mata fuska tafara takowa cikin rashin kuzari jikinta har wata tsima yakeyi cikin rawar murya tana fad'in. STORY CONTINUES BELOW "Um..mata ni..ni..ce Rashida, nice Rashida 'yarki data b'a..b'a.ta." Kafin taqaraso tuni qafafuwanta suka kasa imata tafad'i qasa tana kukan da babu shakka zata iya cewa na farinciki ne, haka umma gaba d'aya kasa motsawa tayi saboda qafafuwanta da suka yimata nauyi Saida taji su Yaya Maryam sunce. "Aisha.." atare sannan tasamu wani irin qwarin guiwar qarasawa wajen 'yar tata dake jan qafafuwa tana neman isowa inda take ta rungumeta tana wani irin kuka mai cike da ma'anoni kala kala, "Ina kika tafi Rashida kika barmu, munyi kuka mun shiga damuwa marar adadin duk ta dalilin rashinki, Ina kika tafi baki nememu ba kika sa gaba d'aya mukabar kowa namu Rashida saboda rad'ad'in rashinki akusa damu?." Kasa amsawa Rashida tayi sai sake naniqe mahaifiyarta takeyi cikin jiki tanajikamar lumfashinta zai fita saboda tsabar farinciki, daqyar tasamu cikin wata irin murya mai ban tausayi tace. "Kuyi haquri, kuyu haquri umma, son zuciya da biyan buqatar rayuwa tasa aka rabani daku, akanisantani da farinciki na aka nemi salwantar da rayuwata batare da andubi halin da nake ciki ba, saidai tsananin addu'arku agareni ya kubutar dani ga shiga duk wani irin gararin rayuwa, ya haskakamun dukkanin lamurrana, ya damqani a hannayen da babu son zuciya balle son kai acikin al'amurransu, d'ago kai umma tayi fuskarta jiqe da hawaye tariqe fuskarta tana goge mata hawaye da manyan 'yan yatsunta. "Kidena kuka 'yata, muyi godiya ga ALLAH daya sake had'a fuskokinmu ba tare da yad'au rayukanmu ba, haqiqa dukkanin bawan da yayi Imani kuma yayi haquri ubangiji bazai tab'a bari ya tozarta ba." "Hakane umma, nayarda da ALLAH shike jarabta rayuwar bawansa kuma yayi masa mafi qololuwar sakayya alokacin daya maida dukkanin al'amurransa agaresa, nayi kuka mai yawa lokacin dana koma agareku ban taradda kuba, saidai yau dukkanin kukana yaqare umma tunda gani gaku." Tare suka juya suna fuskantar alqiblah had'e dayin sujudush shukur sannan suka juyo Rashida ta sake rungumeta tana fad'in. "Ummahhh nayi kewarki" Murya suka jiyo a bakin qofa ana fad'in, "Ummanki kad'ai kikayi kewarta bada abbanki ba 'yata?." juyowa Rashida tayi daqarfi jin muryar mahaifin nata dake tsaye fuskarsa jiqe da k'walla yana takowa izuwa garesu yana bin 'yan uwansa daya gani a tsaitsaye da kuma 'yar tasa tilo da tuni yagama fidda ran cewa zasu sake had'uwa, "Babaaa..!" Rashida tafad'a tare da rugowa da gudu tayi tsalle ta hayesa had'e da rungumesa, wani irin sanyi taji aranta da yasa ta runtse idanuwa tsabar jin dad'i hawaye naci gaba da kwaranyo daga cikin idanuwanta. "Nayi kewarka baba.." "Kika ce?" "Nayi matuqar kewarka sosai babana." Murmushi yayi cike da farinciki yasa hannu ya goge hawayen dake zubowa daga cikin idanuwansa, sake rungumeta yayi sosai tamkar wanda za'a k'wacewa itama tashige jikinsa tanajin wani farinciki marar misaltuwa atattare da ita. Wannan al'amari da yafaru ba kad'an yasa dukkanin wud'anda ke cikin falon hawaye ba, musamman baba balarabe da Yaya Maryam da sukafi kowa jin dad'in faruwar haka idan aka cire Rashida aciki. Ganin taqi saukowa daga jikin baba yasa baba balarabe da tuni duk suka hallara afalon jin abunda kefaruwa ya qaraso wajen yad'an tulli bayanta kad'an had'e da cewa. "To cikamun d'an uwana haka kada kiqarasamun shi." Lokaci guda duk sukasa dariya kowane nagoge qwallan da suka zubo masa, rungumesa baba balarabe yayi yana fad'in. STORY CONTINUES BELOW "Meyasa d'an uwa?." Baba daya kasa tsaida hawayen farincikin dake yimasa zarya a fuska yace "Tsarin alqalamin qaddara d'an uwana." D'agowa baba balarabe yayi had'e da cewa "Baka kyauta ba ko kad'an kuma kada kasake yin hakan?, ko kamanta cewa mu muna buqatarku idan har ku bakwa buqatarmu da har zaku yanke hukuncin guduwa kubarmu batare dakun fad'a mana inda kuka jeba?" Duk da shine Yaya akansa hakan bai hanashi bashi haquri ba, Yaya Maryam kuwa koda yanufi wajenta d'an marin fuskarsa tayi hawaye nazubo mata had'e da cewa. "Zaka sake?" Kafin yabata amsa tasake kaimasa wani d'an marin agefe d'aya tana fad'in. "Zaka sake guduwa kabarmu.?" Cikin kukan farincikin irin son da suka nuna masa yace. "Kiyi haquri Yaya Maryam bazan sake ba." Yasa hannu yagoge mata hawayen farincikin dake kwance a fuskarsa. Nanfa dady yayi gyaran murya had'e da cewa. πŸ˜… *HOPE YOUR MISSION IS ARCHIVED?* *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [9/2/2020, 11:31 PM] S WHITEπŸ’Ž: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___65πŸ’Ž Nanfa dady yayi gyaran murya had'e da cewa. "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, inaga yakamata ace kowa yanemi waje ya zauna hakanan tunda ubangiji ya nuna ikonsa yanda yake so, alokacin da yake so kuma adaidai inda yake so, duk da dai azahirance wannan abun daya faru abun mamakine da kuma ban al-ajabi agaremu saidai bazai kuma hanamu fahimtar ko meye ke wakana awannan wajeba duba da kuma la'akarin yanda alokaci d'aya ALLAH ya dunqule ahalin da muke tunani biyu ne atare damu yakoma ahali d'aya, wannan abun farincikine da kuma murna agaremu, don haka ina mai neman alfarmar kowa yanemi waje yazauna ko don baqinmu da suka shawo hanya na tsawon awanni akwai buqatar ace sunci, sun sha kuma sun huta tukuna sai acigaba da jajantawa juna wannan al'amarin inaga hakan shiya kamata." Takowa baba yayi zuwa wajen alhaji ubale fuskarsa d'auke da farinciki marar misaltuwa yamiqa masa hannu suka gaisa, murmushi alhaji ubale yayi tare da riqe hannun har suka nemi waje suka zauna yana fad'in. "A gaisheka mai gayya mai aiki." Juye juye baba yafarayi yana neman Dr nura wanda shine yaje yakirawosa ganin abunda kefaruwa, cike da mamaki ya hangosa ajikin qofa yanad'e hannayensa aqirji yana tunano ranar daya fara ganinsu baba, sai yau yatuna da muryar umma dako yaushe idan yai yake tunanin inda yasanta ashe ta maman boy ce, lalle ALLAH gagara misali ne kuma huwarrahmanu yau yaqara imani akan cewa tabbas duk yanda bawa yakai maqura wajen son had'a abu aikin banza yayi matuqar ba ALLAH da kansa yaso hakan ba, yamatuqar sha wahala wajen neman iyayen rashida don ya had'asu amma ALLAH bai yarda da hakan ba sai yau da yaga dama, sai gashi cikin sakanni ya had'asu da kansa, haqiqa al'amarinsa abun girmamawa ne kuma duk wanda baiyi imanin cewa shi kad'ai keda iko wajen had'awa da kuma rabawa ba, ansa da hanawa, qaddartawa da kuma jarabtawa, iko akan komai aduk lokacin da yake so, ayanda yake so,a kuma inda yake so haqiqa yayi asara duniya da lahira. STORY CONTINUES BELOW Da hannu baba yayi masa alama da yaqaraso daga ciki sannan yabaro wajen yana murmushi, duqawa yajeyi agabansa da sauri ya rungumesa yana fad'in. "Nagode sosai dr." Rashida kuwa gaba d'aya ta naniqe ajikin umma takasa bari tamatsa konan da can, so take ta tashi tariqowa ammie abinci ashigo dashi amma itama shauqin soyayyar 'yar tata yahanta motsawa wajen, gani take kamar inta saketa zata sake dawo ta tadda bata nan, gashi bazata iya barin ammie taci gaba da kaida kawo ita kad'ai ba, don haka sai tamiqe riqe da hannunta kamar wacce za'a kwacewa tanufi kitchen d'in da ita, gaba d'aya falon sukabita da kallo musamman Dr. da yau yamatuqar qara gaskata kamar dake tsakaninta da umma da kuma little dake hannun fatima yana zallo ta d'aukesa da sukazo wucewa taqi. Suna kaiwa bakin qofar shiga kitchen sukaci karo da ammie ta d'auko kuloli da sauri umma tamiqa hannuwa zata karb'a tace. "A'a umma, ai kuma yanzu shikenan wannan aikin yadawo hannun maishi dama taimaka mani ne kikeyi, gashi da alama yau maman boy bazata bari ko lumfashi kiyi ba." Sai alokacin umma talura da yanda ta k'wak'wume hannun Rashida sosai da sauri tasaketa cike dajin kunya tana karb'ar kulolin hannun ammie sannan tabar kitchen d'in. Ganin ammie naqoqarin d'auko wasu kayan yasa Rashida itama ta taimaka aka jejjere abincin kowa yaci ya qoshi, Bayan sun kammala aka shiga maida maganganu inda Dr yashiga basu labarin adadin mayannun da yayi wajen nemansu da had'uwar da yayi dasu atasha da irin halin daya tsinci Rashida aciki tare da irin ciwon da little yayi tamkar bazai rayuba, duk dasu baffa da daddy sunsan da labarin tawani b'angaren yanzu su baba yake baiwa hakan bai hanasu jin tamkar yanzu suka fara jinsa ba, umma da baba sun zubar da hawayen cike da tausayawa 'yarsu sosai kafin baba yamiqa hannu yakarb'i little Nuraddeen dake hannun Dr. "ALLAHU akabar, duk wannan abun daya faru anyisa ne saboda kada kazo duniya karayu, amma da yake kai alqawarin ALLAH ne saida ya tsaro fitowarka tahanyar jarabta mahaifinka da mahaifiyarka, haqiqa rashin sani yafi dare duhu sannan alqawarin ALLAH tabbatacce ne ko ana so ko ba'a so, badon haka ba dabanyi kwad'ayin aurar da mahaifiyarka abagiren da ba'a buqatar taba duk da dai nasan cewa matsalar ba daga mahaifin kabane." 'Dago kansa yayi had'e da yima Dr godiya marar adadi kafin suma su dady yayi masu godiya sosai shida sauran 'yan uwansa san mazan suka tashi suka tafi wajen sallah su kuma matan suka tsaya nan part d'in ammie sukayi tasu, Rashida kam bin umma tayi sashenta sukayi sallarsu atare, addu'o'i sosai da washi da yabo umma tayi ga ALLAH tana mai godiya daya maido masu da 'yarsu agaresu cikin qoshin lafiya, haka shima baba har kowa yafito masallaci aka barosa shikad'ai yanata yiwa ALLAH godiya. Bayan sun dawo suna zazzaune falo ana sake maida firar yaushe gamo can sai ammie dake zaune tare dasu ummu taqara volume d'in makekeyir tv d'in dake laqe a bango tana fad'in. "Alhaji gafa maimaicin shirin da kake so nakiwon lafiya uwar jiki, da baka samu ka kalla jiya ba." "Af sun fara?" Dady yafad'a had'e da maido hankalinsa ga tv sannan yace. "Ai inaga saidai nahaqura wannan karon tunda banida lokaci, ki saurar inyaso anjima saiki maimai tamani tunda naga kema yanzu kina son shirin." "Eh gaskiya Ina so saboda akwai abubuwa masu muhimmanci da ake qaruwa dasu ciki ko umma?" Taqarasa maganar tana kallon umma dake zaune ita dasu Yaya Maryam suna fira, Rashida kuwa nacan d'aki ita da fatima da little. Sosai ammie tanatsu tana sauraren bayanin da likita keyi akan wata cuta da matar da ake nunowa wadda ke d'auke da ita su kuma sunaci gaba firarsu. "Yawwa 'yata zo kiga maimaicin labaran jiya da nakiraki na fad'a maki cewa yau ki kalla saboda it's very important to all the marry woman." STORY CONTINUES BELOW Ammie tafad'a tana kallonsu Fatima dake fitowa daga cikin d'aki, Wata irin qara sukaji Rashida dake bayanta tasaki had'e da cewa. "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, umma..uncle.baba." Gaba d'aya duk tabi duk ta rud'e ta kasa yin magana sai nuna tv takeyi da ake nuno irin yanayin da Yaya hawwa keshiga idan ciwonta ya tashi. Kafin kace me duk sun maido hankalinsu akanta Fatima na rirriqetatana tambayar ko lafiya, yanda sukaga hankalinta ya tashi yasa suka maido hankalinsu ga tv suma suna son fahimtar ko meye dalilin da yasata firgita hakan, iya kallon da zasuyiwa matar da ake nunowa a tv sunyi amma basu gano komai ba saboda da yawansu ma basu santa ba balle su iya ganeta cikin wannan lalurar da take ciki. Saida aka d'au d'an lokaci ammie dake riqe da hannun Rashida jikinta har tsima yakeyi tace. "Alhaji inaga bari akashe kallon nan, domin yarinyar nan jikinta har wani cira yakeyi." Har tamiqa hannu zata kashe Yaya Maryam tace. "A'a hajia dakata, kibarshi muga irin sakayyar da ALLAH keyiwa bayinsa wud'anda suka cutar da wasu bayin nasa, wannan matar da kuke gani ba kowa bace face surukar Rashida data nemi salwantar da rayuwarta data d'anta saboda son zuciya, ya ALLAH Ina godiya agareka da keke gaggauta yin wani hisabi tunduniya saboda sauran bayinka su wa'aztu." Wata irin zabura baba yayi had'e da miqewa tsaye yana sallallami yana kallon Rashida don tabbatar da abunda yayar tasu kefad'a, jinjina kai Rashida ta shigayi tana kallonsa itama had'e da cewa. "Baba innar mu ce, meye yasameta haka!?" Tana kuka. "Anya Rashida itace?, Innarku fa kikace mahaifiyar mijinki Nuraddeen? don ALLAH ki kalla da kyau kada kitayar mana da hankali." "Wlh baba itace, bazan tab'a mantawa d fuskarta ba, innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, nashiga uku umma Ina ya nura yatafi haka yabar Inna acikin wannan halin?, wayyo ni ALLAH baba, meye yasami Inna haka." Duk wanda ke falon binta yayi da kallo cike da mamakin lafuzzan dake fitowa daga bakinta, musamman Yaya Maryam data soma hasala ganin kukan da takeyi, cikin b'acin rai ta katsa mata tsawa had'e d cewa. "Kirufa mana baki ko inzo intakaki awurin, munji mungani itace, sai akayi me kuma da zaki azawa mutane kuka?" "Haba gwaggo! Haba gwaggo, uwar mijina face!, Surukata kakar d'an dana haifa, taya bazanyi kuka ba tana cikin wannan yanayi, gwaggo kidubi fa yanda takoma, dubi irin wahalar da take sha, don me baza'a tausaya mata tunda rayuwace itama." "Rashida fita d'akinnan kafin na sab'a maki, gwaggon taki ke fad'a kema kina fad'a?" Baffa yafad'a ransa a b'ace. "A'a bashar, ba dakai takeyi ba don haka kabarni da ita." Shiru baba yayi had'e da komawa yasamu waje ya zauna jikinsa a mace, haqiqa ubangiji Mai jujjuya al'amurransa ne aduk lokacin da yaso, yau gashi 'yarsu da akaso ajefa cikin wani hali a haukatar masu da ita ALLAH yakareta ita kuma wacce taso hakan agareta ALLAH yajuyar da al-amarin akanta dama haka rayuwa take _(aljaza'u min jinsil amala)_ sakayya nazuwa daidai da irin abunda ka aikata. Muryar matar baba balarabe hajia Aisha yajiyo tana fad'ar."Banda abunki Rashida meye na kuka awannan al-amarin? abunda ta aikatane ya koma mata, to tawane dalilin za'a tausaya mata, kiduba adadin mutanen data jefa cikin wani hali fiye da shekara d'aya, su kwana cikin qunci da baqincikin rayuwa duk ta dalilinta, ke kanki da mahaifanki harma damu duka sai yau ALLAH ya yaye mana d'inbin damuwar dake dasqare acikin zukatanmu, taya za'ayi ALLAH yabarta da wud'annan haqqoqa data d'aukarwa kanta batare da anbima bima masu sub?, Ai addu'armu d'aya itace ALLAH yakaremu da son zuciya irin nata."+ STORY CONTINUES BELOW "Kar kice hajia mama," da yake haka suke kiranta. "Dukkaninmu bayi muke ga ALLAH, kuma babu wanda yawuce ajarrabi rayuwarsa da khairan ko kuma akasin haka kuma bawai don namanta da abunda tayi manine ba nake tausayin wannan halin da take ciki, kawai ina tausaya matane saboda darajar haihuwa da tayiwa mijina koba komai ma ai baza'a tab'a canjawa tuwo suna ba, matsayinta na kakar jininku baza'a tab'a kankaresa ba, kuma idan kun duba itama rayuwace kamar mu, wlh hajia mama indai akan abunda ta aikata agareni ALLAH ke azabtar da ita haka nayafe mata duniya da lahira." Bud'e baki Yaya Maryam tayi da niyar yin magana maigidanta alhaji ubale yayi saurin dakatar da ita. "Haba Maryam, don me zakiyi qoqarin tirsasata bijirewa kyakkyawar zuciyarta, wlh bana tantama akan yarinyar nan bazata tab'a walaqantaba duniya da lahira saboda akowane irin yanayi dake samunta arayuwa takan kasance mai tsarkakakkiyar zuciya da kuma haquri, ni inaga ku k'yaleta, tanda ikon yafewa duk wanda taga dama, tazubar da hawayenta aduk lokacin da take so kuma ta tausayawa duk wanda taga yadace domin ita take da iko akan zuciyarta, kamata yayi kuyi alfaharin samunta a matsayin 'ya tagari ba kuyi qoqarin chanzata izuwa kangarariyar 'yaba." Saida Yaya Maryam tawatsa mata wata iwar harara tukuna sannan tace. "To ai shikenan saita shirya muwuce mukaita wajenta tazauna tayi jinyarta, inaga haka shiyafi kuma shi zatayi tanunawa duniya kyawon zuciyarta da kuma tausayinta." Murmushi dady da tund'azu ya mayar da hankalinsa ga tv yana mamakin irin yanayin da yaya hawwa take ciki kuma har ahalinta suka tsaya b'ata lokacinsu wajen zuwa asibiti, duk wanda yakalleta da abubuwan da takeyi yasan ba komai ke damunta ba illa matsalar jinnu ce, duk abubuwan da suke fad'a yana jinsu kawai yayi shirune saboda atunaninsa ba huruminsa bane, amma yanzu kalaman Yaya Maryam dake nuni da yanda ranta yab'aci su suka sakashi murmusawa har yake tunanin yakamata yace wani abu awannan gab'ar, musamman idan yayi la'akari da cewa akwai rashin cikakkiyar wayewa atattare dasu wanda yasa har suka iya irin wannan musayar bakin a inda bai kamata ba, kamata yayi ace sun ajiye wannan matsalar a tsakaninsu idan sun koma gida domin sirrin suce amma yanayin qaramcin wayewa dake tattare dasu yasa sun kasa fahimtar hakan. Saida yayi gyaran murya sannan yafara basu haquri akan su ajiye wannan matsalar daga baya saisu zauna su tattauna akanta domin hakan shine sirri agaresu sannan yayi masu nasiha sosai sannan ya sake tayasu farincikin had'uwa da junansu da sukayi. Sai alokacin baba balarabe da duk jikinsa yagama sanyi yayi ajiyar zuciya tare da sake miqa godiyarsu agaresu shida d'ansa bisa taimakon da sukayiwa 'yarsu da d'an uwansu da kuma matarsa. Saida akayi sallar la'asar sannan su baba balarabe suka kama hanyar komawa, sunso a haukarsu su koma dasu umma da baba amma sai Dr ya roqesu subari idan an kwana biyu sun shirya tsaf sai yawuce dasu tunda wurin aikin sane, Haka suka tafi cike d'inbin alkhairin da dady da ammie sukayi masu suna masu yabawa nagarta irin tasu, haka Dr nura shima ba'a barshi abaya ba don yayi masu alkhairi sosai harda suturu ya siya masu da sauran kayayyakin da zasuyi tsaraba dasu, saida yarakasu har suka fita gari sannan yajuyo ya koma can gida suka shiga tattaunawa da dady akan qudurinsa na mayar da Rashida makaranta da yayi gashi kuma yanzu da alama iyayenta bazasu barta anan ba idan suka tashi komawa. Murmushi dady yayi had'e da cewa. "Haba nura, ai kayi wauta, taya daga baka amanar yarinya zaka d'auko zance maida ita makaranta bayan kasan akowane lokaci zata iya komawa hannun iyayenta, bayan haka karka manta yarinyar nan tanada aure bai kamata ace kai tsaye kana zartar da abubuwa akanta ba, don haka ka ajiye maganar komawarta makaranta, iya taimakon daya kamata kayi kayi basai kashiga hurumin da ba naka ba kaji ko." "Eh dady." Yafad'a yana mai yaba hangen nesa irin na mahaifinsa, sai yanzu yafahimci gaba d'aya shirmene yaso tabkawa, nan suka cigaba da tattaunawa akan sauran alamurran dake gabansu kafin akira sallar magrib suwuce masallaci, bayan anyi sallar isha'i yashigo part d'in na ammie Fatima na kwance ta tattake da bargo ita kuma ammie na zaune tana karatun alqur'ani bayan tagama sallah, gaisheta yayi had'e da yimata seda safe sannan yace Fatima tafito suje gida. STORY CONTINUES BELOW Cikin qarfin hali tamiqe had'e da yima ammie saida safe itama sannan tabi bayansa, sashensu umma suka nufa tana biye dashi, "Sweety don ALLAH kabarni anan zan kwana, gaba d'aya banajin qarfin jikina." Juyowa yayi had'e da d'an dawowa baya yariqo hannunta. "Kiyi haquri Fatima bazan iya bacci acikin gidan canba idan har bakya nan kuma kinga ammie bazata barni na kwanar mata ad'aki ba da sai inyi kwanciyata anan nima. Cikin qarfin hali tayi murmushi had'e da cewa. "Haba dr! Ai kaima kasan kayi girma da kwanar mata d'aki." "Ok, to kinga sai kiyi haquri kawai muje gida gaba d'aya tunda nayi girma." Da haka suka iso sashen dasu umma suke sukayi sallama abakin qofa kafin umma tabasu izinin shigowa, kwance suka isko Rashida bisa qafafuwan umma shi kuma little nagefe yana bacci sai faman firarsu sukeyi hankali kwance, suna shiga ta tashi zaune tare da matsawa jikin umma ta d'ora kanta saman kafad'arta, sau d'aya Dr yakalleta ya d'auke kai had'e da gaisheda umma yana tab'o little dake bacci. "Takwara yau har anyi bacci dawuri ahaka!" "Aikuwa kaganshi nan inba ALLAH yatsare muba sai tsakar dare yatashi ya hanamu bacci da shegen kukannan nasa." I'm tafad'a tana qoqarin zame kafad'arta daga kan da Rashida ta aza mata, "Maman boy kitashi muje ko." Fatima tafad'a tana zolayar Rashi don tasan babu yanda za'ayi tabisu. Shiru tayi batare data amsa ba Dr. Yamiqe yana yima umma Saida safe, "Rashida tashi kuke ko?" Yanda Dr. Nura yaga ta shagwab'e fuska kamar zatayi kuka yasa yayi 'yar dariya had'e da cewa, "Kai maman boy saki fuskarki da wasa Fatima keyi, dama nazo muyi saida safe kuma muga yaronmu don nasan yau babu mai cewa ya rabaki da umman nan taki yasan ko waye ya aikesa." Dariya duk suka sannan suka wuce bayan itama tayi masu seda safe. Kusan ranar rashida da ummanta zaune suka kwana shikuwa baba masallacin dake cikin gidan yayi tafiyarsa ya kwanta bayan sun gama firar dashi kusan qarfe d'aya na dare. _kuyi haqnayi manage ne nayi maku typing, sai ahankali wlh yikawai nayi, don ALLAH Ina baran addu'arku kada kumanta daniπŸ˜°πŸ™πŸ»_ *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [9/5/2020, 10:02 PM] S WHITEπŸ’Ž: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___66πŸ’Ž Kasa bacci baba yayi, inbanda juye juye babu abunda yakeyi, da zaran yarufe idanuwansa babu wacce yake tsinkayowa sai Yaya hawwa da suka gani a cikin tv d'azu, tambayar kansa ya shigayi. Shin meke faruwa da matar aminin nasa kuma surukar 'yarsa?, shin gaskiyane ita d'ince idanuwansu suka gane masu acikin tv ko kuwa?, Idan har gaskiya ne itace meye silar fad'awarta a cikin wannan mummunan halin da gaba d'aya duniya ta shaida shi, Ganin yakasa samun amsoshin tambayoyinsa ya yanke shawarar isko aminin nashi da shikad'aine zai iya bashi amsarsu, miqewa yayi yafito daga cikin masallacin lokacin qarfe ukku saura kwata yanufi fanfunan dake jikin masallacin yayo arwala sannan yanufi sashensa saboda hasken wutar d'akin daya hango wanda shine ya tabbatar masa da cewa har yanzu su umma basu kwanta ba. STORY CONTINUES BELOW Knocking yayi abakin qofar d'akin Rashida tagwalo idanuwa waje tana kallon umma da gaba d'aya jikinta yayi sanyi akan labarinsu Dr da take bata na rashin haihuwarsu da soyayyar da suke nunawa little Nuraddeen, yanda tayi da idanuwa yaba umma dariya don kana gani kasan tsorone kwance fal a qasan zuciyarta, jin baba na sake bubbuga masu qofar ahankali muryarsa qasa qasa yana fad'in. "Maman Rashida wace irin firace haka kukeyi har qarfe uku takusa kuna zaune, da haka kutashi kufuskanci ubangiji mana kufad'a masa buqatocinku inaga yafi wannan b'ata daren da kukeyi a banza" Yasa umma saurin cewa. "To malan dama yanzu nake tunanin haka." "Yawwa to ai yafi, kutashi." Baba yafad'a tare da juyawarsa yakoma masallaci yana mai fuskantar ubangijinsa yana mai godiya tare da sake miqa d'imbin buqatunsa agaresa. Haka ta b'angaren aunty marwiyya tsabar farinciki hadda sadaka tayi lokacin dasu Yaya maryam suka isa gida suka sanar da ita zancen had'uwarsa dasu umma da sukayi acan garin, rawa tadinga kwasa tanayiwa ALLAH godiya, duk da bata san taya had'uwar tasu ta kasance ba itama harda k'walla tayi. A b'angaren baba balarabe ma bacci yayi yana tunanin ko meye gaskiyar abunda yafaru ga iyalin baffa?, Kenan maganar da d'an uwansa yafad'a masa ba gaskiya bace? Idanko haka ne yatabka babban kuskure abunda yayi masu, Tsaki ya dingayi naba adadi yana ALLAH waddai da zuciyar data tunzurasa yakasa banbance qarya da gaskiya tsakanin maganganun da su baffa suka fad'a masa da kuma wud'anda d'an uwansu yafad'a masa. Matsuwa baba yayi safiya tawaye don yad'au alwashin komawa garinsu saboda sanin halin da aminin nasa keciki, a iya saninsa yasan shi da kansa yace masu susa asako yaya hawwa da d'an uwan nasa da kuma matarsa, yana tsoron kada ace garin d'aukar matakine ya jefa iyalin tasa cikin wannan halin. Tunda akayi sallar asuba baba yagama karanta azkar d'insa ya hau shirye shiryen tafiya, kasancewar dady part d'in ammie yake yasa bayan ya kammala shirinsa yace umma taje ta sanar da ammie yana son magana da dady idan yatashi bacci, yanda yace haka umma tayi sannan tadawo tana goye da little Nuraddeen tace. "Wai malan lafiya naganeka kamar cikin damuwa? Ga alama ko bacci baka samu kayi ba jiya, Kuma yau tunda sassafe kahau shiri, meke faruwa da kaine kuma Ina zakaje?" Taqare maganar damuwa kwance a fuskarta, ganin haka yasashi d'an murmusawa had'e da cewa. "Babu komai maman Rashida, zancen bacci kuwa ai bani kad'aine banyi ba...." "To naji basai ka qarasa ba, amma ina zakaje? Ko yau zamu koma." "A'a bana tunanin haka domin idan nace zan koma banyiwa alhaji adalci ba don gaba d'aya amanar sabon shagonsa a hannuna ya damqata, zandai je kano ne Ina son in had'u da alhaji Idris akan abunda muka gani jiya dangane da iyalinsa? Kinga bai kamata ace nagani nayi shiru ba matuqar ita d'ince kamar yanda Rashida tafad'a." "ALLAH ya kiyaye." Umma tad'an fad'a kamar cikin jin haushi zatabar wajen. "Dakata mana, Ina Kuma zakije muna magana.?" "Ai mungama magana tunda kafad'a mani inda zakaje." "To meya b'ata maki rai aciki maman Rashida naga zakibar wajen rai a b'ace." "Bakya son natafi ne?" Shiru tayi batare data tanka saba tana d'an jijjiga little dake mutsu mutsu yana neman tashi, murmushi yayi don yasan dole hakan zata faru, mawuyacin abune ga uwa ta iya manta wanda ya cutar mata da d'a, musamman idan taga ana damuwa da al amarinsa alokacin da shima ya jarabtu sai taga kamar ita annuna rashin so akan nata ne da aka kasa nuna masa haka a lokacin da ake cutar dashi. STORY CONTINUES BELOW Lumfasawa baba yayi had'e da cewa, " kiyi haquri maman Rashida abunda zuciyarki ke tunani ba haka bane, iya sanina matuqar zamuyi koyi da mafificin halitta to bazamu rama cuta da cuta ba domin shi yakan rama cuta da alkhairi ne ga wanda yacutar dashi sannan karki manta da irin d'imbin alkhairin da d'an baiwar ALLAHn nan da mijinta suka yimani, koba komi tunda suka qaunaci 'yarmu sunngama mana komai arayuwa." "Amma kuma meya biyo baya malan?, Cutarwa da kuma neman salwantar mata da rayuwa, yakamata kafahimci hakan kabarsu suma da tasu jarabawar suji idan akwai dad'i, 'yarmu aka cutar amma rad'ad'in da zafin akanmu yaqare muda muka haifeta, don haka dole suma suji irin wannan zafin alokacin da take cutuwa duk da kuwa basu ke cutuwar ba." "Ashsha! Kada kibari 'yarki tafiki hankali da tunani, karki manta mu da muka shiga cikin tamu jarabawar ai ba qyalemu sukayi ba, qarfinsu, lokacinsu da kuma kud'insu harma da mutuncinsu duka sunyi amfani dasu wajen nuna mana damuwa akan halin da muke ciki, shine yanzu zakice mu muwofantar dasu saboda sun zamo silar cutuwarmu data 'yarmu?, Kiyi haquri mumanta da abunda yafaru tunda ALLAH ya maido mana da 'yarmu duk da nasan hakan abune mai wahala amma zamu iya matuqar mukaci gama da yawan tuna alkhairansu." Sosai jikinta yayi sanyi kuma b'acin ran da takeji akansu yad'an rage sosai, "Shikenan ALLAH yasawaqe yasa kaje lafiya kadawo lafiya." "Amin ya rabbi, bari naje inaga kiran alhaji ne qilan yafito." yafad'a yana ciro wayarsa dake ruri a gaban aljihu. Qarasa shiga cikin d'aki tayi shi kuma yanufi sashen ammie. Sida suka gaisa cikin girmamawa sannan yasanar dashi zancen tafiyar da yake so yayi yau, duk da ko kad'an dady baya son yayi nesa dashi haka yadaure yabashi goyon bayan yin tafiyar tare da ciro dubu goma yamiqa masa yace yayi na mota. "A'a alhaji da ka barsu wlh, akwai kud'i a hannuna sosai." "Ai nasani, ka karb'a ni nabaka kaqara, kud'i ai basa yawa ga matafiyi." Karb'a yayi had'e da yimasa godiya sannan yami zaifita, har yakusa kai bakin qofa alhaji ya kirasa had'e da cewa. "Am..malan bashar me zai hana kabari zuwa jibi sai mutafi tare don zanje sayo kaya, kasan duk kayan namu sunyi qasa.?" Sosa kai baba yayi had'e da cewa. "Ai da kabarshi alhaji, so nake yau ko gobe in juyo idan ALLAH ya yardar mana." "To shikenan ALLAH yakiyaye hanya, dama nafi samun natsuwa idan kana kusa lokacin da zan tafi, don ALLAH ka gaishe mana dasu." "In sha ALLAH zasuji mungode." Abakin qofa sukaci karo da Dr nura yana qwalawa ammie da dady kira, kallo d'aya zakayi masa kasan cikin farinciki yake saboda wani annuri dake fita a fuskarsa, d'an sunkuyawa yayi yana sosa k'eya ya gaida baba, fad'ad'a murmushinsa yayi had'e da amsa gaisuwar daya yimasa yana fad'in. "Agaida likita bokan turai kuna lafiya?.." Bai qarasa magana ba yaga Fatima na qoqarin shigowa itama tajawo hijab d'in jikinta yarufe mata fuska, ganin yayi tarugo da gudu hango ammie nafitowa tafad'a jikinta tana kuka. "Subhanallahi.. Dr lafiya?" Baba yafad'a yana kallon Dr nura da shikam sai faman washe haqora yakeyi, gaba d'aya 34 d'insa sun kasa rufuwa, Saida ya d'an sinne kai qasa had'e da kallon Fatima ta wutsiyar ido sannan yace. "Baba lafiya klw ku qyaleta kukan dad'i ne takeyi, addu'arku da kuka dad'e kunayi ne ALLAH yakarb'a mana shine fa tunda likita yafad'a take wannan kukan." "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah..." Gaba d'aya falon tundaga ammie dake faman rarrashinta har baba da dady suka fad'a atare, sai alokacin Dr yaji wata irin kunya tarufesa da sauri yajuya batare daya qaraso cikin falon ba. STORY CONTINUES BELOW Maida jiki gabas ammie tayi had'e dayin sujada hawayen farin ciki nazubo mata tace. "Lakal hamdu ala maqadait, walakash shukru ala man a dait, tabarakta ya zaljali wal ikram." Sannan ta tofa tashafe a fuska. Dady kuwa Banda murmushi Babu abunda yakeyi, nan take yaqudurta aransa zai yiwa baba dake tsaye wata kyauta a matsayin godiyarsa ga ALLAH bisa wannan ni'imar daya yimasu duk dako ba itace ta farko ba, Hajia fareeda wato ammie itace matar dady tafarko kuma uwar gidansa tanada yara uku dashi kuma sune manyan 'yayansa agidan, Dr nura shine babban d'ansa sai kuma qanensa faruq, saurayine Amma zaikai shekara ashirin da bakwai haka, sannan qanwarsu Khadija dake da shekaru ashirin da hud'u, tayi aure bayan shekaru uku da suka wuce bayan ta kammala karatunta a fannin lafiya wato (nursing), kuma ALLAH ya albarkaceta da samun yara biyu Shahid da Shahida idan kaganesu zaka d'auka tagwayene amma ba haka bane saboda haihuwar rurrutsa tayi, tana ilorin acan take aure saboda mijinta soja ne basu fiye zama waje d'aya ba, yau in suna wannan garin to gobe kuma suna waccan garin, wannan dalilin ne yasa dady cewa ba itace ni'ima tafarko da ALLAH yayi masu ba. Tun daga nan ammie bata sake haihuwa ba kuma hakan bai tab'a damun dady ba, acewarsa sukad'ai idan ALLAH ya raya masa sun isheshi, amma da yake ammie macece mai tsananin alkunya da kuma son mijinta ta tirsasa masa cewa dole sai yaqara aure saboda yasamu qarin zuri'a ita kanta tana sha'awar yara qanana gashi ga dukkan alamu haihuwar ta tsaya mata, don haka tayita rarrashinsa har tasamu ya amince ya auro hajia nafeesa, 'ya ga amaninsa da suka tashi tare ya rasu yabarsu su takwas ga mahaifiyarsu, rashin wadatar da suke ciki don shi sana'ar noma yakeyi, sai gashi ALLAH yamasa rasuwa yasa dady ke tsananin tausaya masu kuma yake taimakonsu sosai, daga nan ammie tabashi shawarar ya auri nafeesar saboda hakan zai qara bashi damar taimakon 'yan uwanta sai gashi tazamo butulu ta hanyar walaqanta duk wani dake tare dashi matuqar bayada arziqi, musamman hajia fareeda data d'auka wata maqiyiyarta aduniya. Dawowa cikin falon baba yayi fuskarsa d'auke da farinciki ya taya su hajia murna had'e da fatan ALLAH ya sauketa lafiya sannan yajuya yafita. Miqewa dady yayi shima had'e da cewa. "Dota congrat, ALLAH yakawo mana rayayyi masu albarka." Sannn shima yajuya yafice, ammie na dariya tasa hannu ta d'ago fuskar Fatima da tayi sharkaf da hawaye tana fad'in. "Kai 'yata wannan duk kukan farincikine ko kuma na shagwab'a ne akeyiwa ammie ankusa zama mama." Kasa tanka mata tayi saima faman share qwallar da takeyi tana wasa da gefen hijab d'inta had'e da sissinne kai qasa, karo nafarko kenan arayuwarta data fara jin kunyar ammie irin haka, arayuwa babu abunda take b'oyewa ammie, ta d'auketa tamkar uwar data haifeta da cikinta, hatta wani abun cikin rayuwr aure idan Bata sani ba ita take tambaya tafad'a mata, haka ab'angaren kayan jiki na gyaran mata duka ammie nahad'a mata tabata kuma tayi mata bayani batare da taji kunyarta ba, sai gashi yau gaba d'aya takasa d'aga kai takalli ammie su had'a ido. Murmushi irin na manya ammie tayi had'e da cewa, "ikon ALLAH, karmuyi haka dake 'yata, kisaki jikinki ni mahaifiyarkice don haka dena wani jin kunya akan wannan abun farinciki daya kamata muyi sharing happiness d'inmu atare, let celebrate together my dota bawani abubane, show me how much appy you feel about this, i will support you and make you enjoy it better kinji ko?." Ahankali tad'ago kai tana kallon ammie hawaye nazubo mata afuska. "I couldn't believe ammie, ammie ashe nima zan haihu ba juya bace ni kamar yanda ake fad'a, Ashe nima zan zama uwa am...?" Kasa qarasawa tayi sakamakon kukan farinciki da yaci qarfinta, Bata tab'a kawowa kusa cewa zata haihuba, Bata tab'a sama ranta tana da ciki ba duka da dai Bata tab'a cire tsammani da rahamar ALLAH ba, ako yaushe cikin sa rai take komai daren dad'ewa zata haihu itama in ALLAH ya yarda. STORY CONTINUES BELOW Cike da tausayinta ammie tajawota ajiki ta rungume tana fad'in. "Ya isa haka 'yatah, just blieve it, dama haka ALLAH yake, yakan lullub'e bayinsa da rahamarsa a lokacin da basu tab'a tsammani ba, kuma yakan dubi zukatan bayinsa da sukayi Imani dashi suka kyautata al'amurransu ya share masu hawayensu, wannan shine abunda nayita fad'a maki cewa idan lokaci yayi bazato ba tsammani zakiga abun kamar qyaftawar gira, Kuma nafad'a maki tunda dai har akece lafiyanki qalaw to kiyi haquri domin SANNU SANNU bata hana zuwa....gashi naki ALLAH yakawo ijaba har kin iso ko kuwa?" Tafad'a tana d'an turo idanuwanta kad'an tana dariya alamar tana jiran amsa. Jijjiga kai tashigayi alamar tabbatar mata da cewa hak ne ammie tace. "To mugodewa ALLAH ba kuka zakiyi ba kinji ko?, Yanzu fad'amun me kike son ci?" Rufe fuska tayi ammie nadariya tamiqe tana fad'in. "Ko zakici wainar fulawa nayi maki?" Ta girgiza kai had'e da cewa. "A'a ammie eba dai zanci." Turo idanuwa ammaie tayi had'e da cewa. "Tofah, kice maigidan nawa d'an yarbawa ne?" Duk sukasa dariya harda Dr nura da tun d'azu ke tsaye abakin qofa yace. "Ai kuwa ammie da yaci sunan qudusu" yafad'a kamar yanda yarbawa ke kiran sunan suka sake sa dariya atare, can batare daya ankareba ammie takamo kunnensa had'e da murd'ewa tana fad'in. "Son yanzu rashin kunyarka har yakai da kanka kake fad'an 'yata nada juna biyu kuma ka taso mani ita agaba, To Ida cikashe rashin kunyar taka ka fad'amun ko how many month ne?," Fatima na ganin haka ta tashi tashigewarta bedroom d'in mom tana murmushi, komai na surukar tata cike yake da burgewa da kuma ban sha'awa, ko kad'an batada wata matsala komai nata tanayinsa da cikakkiyar wayewar da babu qazanta acikinta. "Awwwshhh..ammie da zafi fa." "Nasani mana, bakai rashin kunya ba?" "Kai mom, albishir nefa nayi maku, ALLAH badon baba ba sai kun cike mani check tukuna zan fad'a, Ashe laifine nayi bansani ba, amma ita data azawa mutane kuka Ina gani sai wani lallashinta akeyi ana murmushi." Yafad'a yana turo baki sai kace wani qaramin yaro. Murmushi tayi had'e da sakinsa tace. "Srry kaji ko son, tsantsar farincikinne har yayi mani over shiyasa nanemi regesa akanka, congrat soon zaka shiga next level arayuwa, wato mtakin zama uba bayan magidanci, ubangiji ALLAH yayi maku albarka yabamu rayayye." "Amin ammien mu" yafad'a yana rungumeta. Baba kuwa koda yakoma sashensa acan ya tarar da Dr nura suna gaisaw da umma da Rashida yana basu labarin jiya a asibiti suka kwana saboda zazzab'in daya tasowa Fatima har saida aka qara mata ruwa, baikai ga fad'a masu zancen cikin ba baba yashigo yamiqe zai fita baba ya tsayar dashi yake sanar dashi batun tafiyar da zaiyi kano, nan take Dr yaji tafiyar bata kwanta masa ba, yayi iya qoqarinsa naganin ya hana baba tafiyar har zuwa banda gobe idan zaije wajen aiki suwuce tare amma yakafe kai da fata shidai ya barshi ya tafi ai yau zai dawo, hakan yasa babu yanda ya iya dole sukayi sallama akan idan zai tafi ya aika Rashida yakirawosa zai koma wajen ammie sai ya ajiyeshi tasha sannan yabar sashen yanajin wani irin. Baba kuwa zaunawa yayi suka sake d'an tab'a hira dasu umma yanata zolayarta wai yanzu idonta sun bud'e tadena kunyar Rashida amatsayinta na 'yarta tafari ashe b'oyewa takeyi tana sonta sosai sunata dariya. Daga nan kuma yajuya akalar firar tasu izuwa yimasu nasiha akan rayuwar duniya sai kace wanda akace idan yatafi bazai dawo ba, bayan yagama umma tayi ajiyar zuciya had'e da cewa. STORY CONTINUES BELOW "Malan nifa duk jikina yamutu wlh, nidai don ALLAH kabar zancen tafiyarnan har zuwa wani lokacin." Murmushi yayi had'e da cewa "Karki manta sau da yawa bama son abu sai kiga ALLAH yasanya alkhairi sosai acikinsa, kika San alkhairan da wannan tafiyar zata jawo mana, qilama 'yar qanwa zan samomaki shiyasa duk kikabi kika tada hankalinki akanta." Yaqarasa maganar cikin sigar zolaya yana dariya had'e da miqewa yana d'auke da litte, "Rana nayi bari na hanzarta yau nake son nadawo in sha ALLAH, Rashida jeki kikira Dr ni kam nad'au harma." Gaban Rashida ne taji yafad'i da sauri tace. "Baba kayi haquri kuwuce da uncle banda gobe." "Ikon ALLAH, har dake Rashida? Bakyason sanin halin da mijinki da surukarki suke ciki halan?" "A'a baba, ni kawai..." Saurin dakatar da ita yayi tahanyar cewa "maza jeki kice Ina jiransa." Har takusa fita yakira sunanta had'e da cewa. "Dawo nayi maku albishir ni namanta, maman Rashida matar Dr fa tasamu qaruwa." "Da gaske baba?" Rashida tafad'a cike da farinciki tare da ficewa da kad'an ma tafad'i garin sauri, umma kuwa Alhamdulillah tace tana fad'in "ALLAHU AKBAR, ALLAH maji roqon bayinsa, kai madalla bari naje nataya hajia murna." Kusan tare da ita suka fita yana maijin wani sanyi aransa saboda yanayin farincikin da yaga ya bayyana a fuskarsu wanda hakn baqaramin tasiri yayi ba wajen qara masa natsuwa azuciya..... _Godiya agareku masoya masu karamci da halacci bisa bibiyar lafiyata da kukayi, nagode sosai ALLAH yabar tare, maman ameera da ummu sauda ban manta daku ba, kunnuna kulawa agareni kuma jazakumullahu bikhair, fatan alkhairi aduk inda kukeπŸ‘πŸ»_ *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [9/7/2020, 1:07 AM] S WHITEπŸ’Ž: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___67πŸ’Ž Da gudu Rashida tashiga part d'in ammie tana kiran fatima. "Aunty, aunty.." da kad'an sunyi karo da ammie dake qoqarin shiga kitchen, d'an ja da baya tayi cike da farinciki kafin tasake matsowa kusa da ita tarungumeta tana fad'in, "Ammie kitayamu murna auntynah zata haihu." Murmushi ammie tayi cike da mamakin irin sakewar da Rashida tayi dasu tsakanin jiya da yau sab'anin yanayin da take ganinta abaya, tabbasa iyaye wani jigone da rashinsu kan kawowa 'ya'ya tawaya maigirma arayuwa, "Iyyeeeeee....to ina tayaku murana kice little yakusa zama big zai samu d'an qane.." Ko qarasa maganar ammie batayi ba Rashida ta saketa tanufi bedroom d'in ummie don tasan tana ciki tunda bata ganeta a falo ba, girgiza kai ammie tayi tana kallon Dr nura da yabi Rashida da kallo cike da mamakin tsantsar farincikin da yaga tashiga, juyowa yayi suka had'a ido da ammie yace. "Gaba d'aya ta canza tsakanin jiya da yau, kinga farincikin dake tattare da ita ammie sai kace wacce aa biyawa makka." "Haba son!, ai dole tayi farinciki, iyaye fa rahamana sosai ga kuma wannan batun data tsinta alokaci d'aya, matuqar ita d'in masoyiyar kuce dole kaga fiye da wannan farincikin atattare da ita, ni yarinyar na burgeni sosai saboda sanin yakamatar ta" STORY CONTINUES BELOW "Ehm..gaskiya hakane, Rashida kam akwai hankali." Da gudunta taqarasa shiga cikin d'akin tafad'a jikin fatima dake zaune bakin gado ta tallafe fuskarta da tafin hannuwanta guiwowinsu na akan cinainanta. "Yeeew...auntay na congrat, agaskiya Ina cikin farinciki marar misaltuwa ayau, bayan duk wasu fad'i tashi da suruttan mutane yau ALLAH zai bamu namu d'an, Ina farinciki sosai auntynah ALLAH ya inganta yaraba lafiya." Duk wannan surutun da Rashida keyi cikin farinciki Babu abunda Fatima keyi in banda kallonta, d'aga mata idanuwa Rashida tayi tana juya hannunta had'e da cewa. "Me akayi ne aunty?" Rungumeta tayi tajawo hannunta ta d'ora akan cikinta tana fad'in. "Maman boy I can't believe so soon zan haifa maki baby, thank you so much for supporting me, haqiqa babu abunda yakai qarfin addu'a tasiri arayuwa, nagode bisa addu'o'in da kika d'orani akai da kuma wud'anda kikeyi mani ba dare ba rana, tabbas anasamun warakar kowace irin matsala tahanyar jajir cewa dayin addu'a, ALLAH ne yace anemi maganin kowace irin matsala amma ana samun warakane bisa qarfin addu'o'inmu agaresa, maman boy kinzamo wani haske acikin rayuwarmu da bazamu tab'a iya mantawa dake ba, yanda kika faranta mana kema ina roqon ALLAH daya faranta maki acikin dukkanin lamurrank, Ina miki albishir da cewa idan ALLAH ya saukeni lafiya zamuyi maki takwara da yardar ALLAH idan aka samu macce, wannan shine tukuicin zamowarki sila wajen tsaida hawayen da muka dad'e suna yimana kwaranya a idanuwa." Taqarasa maganar had'e da riqo hannayen Rashida ta d'ora saman idanuwanta dake fitar da qwalla. "Kai aunty meye haka kikeyi?, Haba ya isa kidena wud'an maganganun don ALLAH, dukkaninmu ALLAH yakamata mumiqa godiyarmu agaresa, inada tabbin dama lokacin da zaki haihu yayi koda kuwa banbaki wud'an nan addu'o'inba, kawai sun zamo silane bisa wanzuwar qudurar ALLAH agareki, don haka kidena damuwa akan wannan, koda babuni acikin rayuwarku zaki haihu kamar yanda ALLAH ya tsaro, ita addu'a da kike gani ai makami ce babba da idan bawa yariqa duk nisan lokaci zai riskesa da yardar ALLAH." "Zancen yimani takwara kuwa ALLAH ban yarda ba, sunan yazama local, ni kaina dariyarsa nakeyi wani lokaci." "Commonnnn..." Fatima tafad'a tare dakai mata d'an duka agefen hannu tanaci gaba da cewa. "Waya fad'a maki sunanki local name ne, ai sunan Rashida da kike gani sunane mai girma, is drive from the one names of ALLAH dt's (AL-RASHID), Ma'ana mai shiryarwa, asalin sunan ubangijine sai akayi amfani dashi ta hanyar qara harafin (a) yazama (RASHIDA) sai ma'anarsa ta tashi daga Mai shiryarwa zuwa shiryayyiya, don haka kiyi alfahari da sunnki akoda yaushe, domin sunane da bazai kusuba ga wud'anda sukasan asalin ma'anar inda aka ciro sunan, hikimace kansa iyaye nasakawa 'ya'yayensu ire iren wud'annan sunayen saboda fatan ma'anar dake tattare dasu tad'ore akan 'ya'yan masu." "Laaa...kinsan ALLAH aunty! Hankalina bai tab'a kawomun wannan tunanin araina ba, atak'aice ma mantawa nakeyi da akwai sunan acikin jerin sunayen ALLAH da har zan iya tsinkayo ma'anar dake tattare da sunan nawa, kawai nidai tunda banji ana yayin sakawa jarirai sunan ba to sunan dane agurina, d'ai d'ai kune acikin yaran dake tasowa nake ji da irin wannan sunan, amma yanzu tunda kinfahimtar dani ma'anarsa da inda aka samo asalinsa Ina alfaharin kasantuwa ta da sunanan RASHIDA." Gyaran murya ammie tayi abkin qofa tana fad'in. "Agaida qanwar aunty, dama aikoki baban naki yayi shine kikazo kikayi zaunenki?" "Laaa.... ALLAH na manta ammie, bari naje nafad'a ma uncle." "Zauna abunki, ai ummanki data shigo tayamu murna tafad'a masa gashican har yafita." "ALLAH shaf ni namanta sai yanzu bari naje nabashi haquri daga nan nayi masa ALLAH yakiyaye." Tana gama fad'ar haka tamiqe tafita, ammie tace,"Kinga mutuniyarki tasaki jikinta sosai yanzu ko?" "Eh wlh ammie kuma naji dad'in hakan sosai, kinga kafin sutafi zata qara koyamun wasu addu'o'i sosai." "Wlh ammie tun watan da kika aikamun da wannan ganyen guava kikace mudinga sakawa cikin ruwan tea muna tafasawa muna sha kafin muci komai da safe tun alokacin nafara jin canji da kaina ajikina, ranar muna zaune nida ita sai take cemun akwai wasu addu'o'i acikin alqaur'ani da yakamata na dingayi wud'an annabawan ALLAH sukayi da bai basu haihuwa ba kuma daga baya yabasu, hakan zai taimaka wajen sanya maganin duk da nake amfani dashi yayi tasiri ajikina sosai saboda qarfin addu'a, ammie kamar da wasa ta nunnuna manisu acikin alqur'ani nafarayi, yanzu kimanin watanni biyar inyinsu kenan sai gashi cikin yardar ALLAH ijaba tasauka, tabbas ammie ilimi nada dad'i aduniya kuma yawane dashi da bazaya tab'a qarewa ba sai randa bawa yakoma ga mahaliccinsa, Kuma duk yanda kake taqama dashi sai kaga wanda yafika shi." "Dama hakane 'yata, koda kuwa wanda baikai darajarka bane ko kuma yafika zakaga yasan wani abun dakai baka sani ba, duk da nasan wasu daga cikin addu'o'in 'yata kifad'a mani sauran naji domin inada wata qawa yanzu kusan shekaru talatin kenan bta haihu ba, kuma tana matuqar son haihuwar kamar taqwato, babu gwaje gwajen da batayi ba, qasashen waje kuwa sunje ba iyaka amma har yau ba'a dace ba, kuma duk da hakan bata gaji ba har yanzu tana kan neman magani cike dasa ran wata rana zata dace, zanji matuqar dad'i idan tasamu irin wannan farincikin da ayau muke ciki kuma hakn zaisa nayi alfaharin tarayyata da ita nahar abada." "Ai kuwa ammie bari nafad'a maki don gab d'aya nahardace su akai, ba ita kad'ai ba, ina fatar duk wanda kecikin irin wannan matsalar ya amfana dasu domin samun waraka kusa kusa matuqar zai dage dayinsu cike da yaqinin ALLAH zai amsa masa." "To bara nad'auko biro da takarda narubuta 'yata, kinsan qwaqwalwar taku da tamu yanzu ba d'aiba." Takarda ammie ta d'auko Fatima tafara karanto mata addu'o'in daki daki kamar haka. ( _Rabbi laatazarni fardan wa'anta khairul warithiyn,_) ( _Rabbana hablana min azwajina, wazurriyaatina, qurrata a'ayunin, waja'alna lil muttaqina imama_) ( _Lillahi mulkussamawati wal'ardi, yakhluqu maa yasha'u, yahabu liman yashaa'u inasan, wayahabu liman yashaa'uzxukur.._) ( _Rabbi habliey minladunka zurriyatan d'ayyibatan, innaka sami'uddu'ah_) ( _Wa'inni khiftul mawaliya minw waraa'i wakanatimra'atiy aaqiran fahabliey minlladunka waliyya_.) ( _wayumdidkum bi amwalin wabanieyn.._) ( _wamaa tahmilu min unsaa wala tada'u illa bi ilmihi.._) ( _izhaa qada amraan fa'innama yaqulu lahu kun fayakuun.._) ( _qala kazalika qala rabbuka huwa alayya hayyinun waqad khalaqtuka min qablu walam taku shai'a_) ( _Yaa zakariyya Inna nubashshiruka bigulaminismuhu yahya lam naj'allahu min qablu samiyya_) ( _Rabbi habli minasswalihieyyn_). 'Dago kai ammie tayi had'e da cewa. "'yatah har yanzu addu'o'in basu qareba, naga har nacika takardar nan.?" Saida Fatima tayi dariya sannan tace. "Dayawa ko ammie?, Ai dama mai bid'a dole sai ya daure, balle ace d'an mutum kake so ai Dole sai an nace kuma anjajirce kafin akai ga gaci, ni ada nake ganin yawan addu'o'in amma daga baya da ALLAH yataimakeni na haddace wasu wasu kuma ina dubawa ga takardar dat rubuta mani wallahi sai nadena jin wahalarsu, kinsan ammie abun sa kaine, idan kad'auka da sauqi sai yazo maka cikin sauqi, duk yawannan nasu da kike gani idan natashi da daddare nayi raka'a biyu na sallame nakan maimaitasu fiye da sau goma wani lokacin kuma nakanyi ko sau d'ayane bayan nayi istigfari da washi zuwa ga ubangiji sannan nayiwa annabi salati tare dayiwa ALLAH godiya bisa wasu ni'imomin da yayi mana nadaban. Idan na kammala sai nakoma bacci, wani lokacin tare ma dashi mukeyi gaba d'aya idan anyi sallar asuba rana tafito sannan mukoma bacci, wani lokacin ammie ko sallarma bamayi, arwala kad'ai mukeyi muzauna muna bitar addu'o'in har bacci yana d'an fizgarmu wani lokaci." STORY CONTINUES BELOW "Tirqashi! Tabbas 'yata kunkoma ga Wanda kad'ai ya isa yabaku kuma yabaku, ubangiji ALLAH ya inganta yabaki rayayyi masu albarka, albarkacin miqa wuyan da kukayi agaresa." "Amin ammie nagode." 'Dan hararta ammie tayi akn godiyar data yimata, dariya tayi had'e da cewa. "Natuba ammienmu kiyi haquri." "Shikenan, ammafa kada kiqara." "Baran qara ba ammie.." "Shikenan addu'o'in nakirata taturo akarb'ar mata?" "Eh ammie, tun yanzu Zaki aika mata?." "Eh mana, ai qara abugi qarfe da zafinsa." "To ammie ALLAH yasa adace, Amma ammie kice tayi duka addu'o'in cike da yaqinin cewa ALLAH zai karb'a mata, kinsan yana d'aya daga cikin abubuwan da kesa ubangiji ya gaggauta amsar addu'ar bawa idan yayita da yaqini." "Ai zama tayi 'yata saboda akullum batada burin da yafi wannan, kinga kuwa dole zata dage, bari naje nadubo maki abinda kikace kina so." Ammie tafad'a tare da linke takardar ta ajiye akan madubi sannan tabar d'akin, miqewa tayi had'e da shafa cikin nata dako motsi bai fara ba tayi murmushi, gaba d'aya ganin ranar takeyi kamar mafarkine takeyi sannan itama tabi bayan ammien. Rashida kuwa koda ta isa baba na qoqarin shiga mota har lokacin little na ahannunsa, qarasawa tayi wajen baba yamiqo matashi, har tamiqa hannu zata karb'esa cike da zolaya yaja baya dashi yana fad'in. "Bazaki bari naje dashi ba nakaishi wajen kakansa, nasan zaiji dad'in ganinsa fiye da irin dad'in da mukaji." Murmushi Rashida tayi had'e da cewa. "Shikenan baba, kaga nida ummata dasu ammie mun huta da fitinarsa, sai yaje can yad'an tab'awasu baffa da inna Bilkisu suji yanda mukaji." "Wai hakane mai sunan babansa?." Baba yafad'a yana kallon little dake faman tafi da hannuwa yana kallonta, dama Dr nura naganin taqaraso wajen yad'an basu waje yana amsa waya, maida kallonsa baba yayi ga Dr da har lokacin wayar yakeyi ya basu baya sannan yace. "Rashida don ALLAH ku kula da bayin ALLAHn nan, mutanene masu karamci da halacci, duk abunda suke so kufisu sonshi wanda kuma basa so to kifisu qinsa, inaso kiriqesu tamkar mu da muka haifeki kuma ki kyautata masu iya qarfinki hakan zaisa kirage wata kunyar hidimar da suka yimana kinji ko.?" "In Sha ALLAH baba, ALLAH yasa kaje lafiya kadawo lafiya." "Amin ya rabbi, ALLAH yayi maki albarka dake da duka zuriar da zai baki." Yaqare maganar yana shafa kan little had'e da miqa mata shi yana murmushi. A daidai lokacin Dr yadawo fuskarsa cike da walwala ya shafa kan little had'e da cewa. "Takwara nazata dakai baba zaije?" "Yawwa uncle don ALLAH kuje dashi shima yarakashi." Karb'arsa yayi yayi sannan yashiga cikin motar yarufe gambun yana qoqarin tada motar tace. "Laaa...uncle congrat, little yakusa samun qane, ALLAH ya inganta uncle yabamu rayayye mai albarka nima narama abunda ake yimani akan d'an wasu." Batare daya kalleta ba yana key d'in motar yace. "Amin ya rabbi, Thank you so much maman baby, amma ko kunrama bazaku iya ramawa ba kamar yanda muka yimaku ba ko takwarana?" Da haka yatada motar had'e dayin ribas ya juya motar suka fara tafiya, binsu tayi tana d'agama baba hannu shima yana d'ago mata har suka fita, haka kurum saita tsinci kanta da fashewa da kukan da batasan dalilin yinsa ba, Saida ta tsaida kukan sannan tajuya tanufi sashen na ammie, umma tahango jikin qofa tsaye itama taqurawa gate d'in idanuwa tana mai addu'ar ALLAH ya saukeshi lafiya, STORY CONTINUES BELOW "Umma ya nagaki a nan tsaye?" Rashida tafad'a jikinta ba qwari. "Wlh Rashida nidai tafiyannan tashi bata kwantamun ba, daya bari har sai an kwan biyu tukuna tunda muma jiyan nan muka fita alhinin rashinki.?" "Kai umma, ki kwantar da hankalinki in Sha ALLAH zaije lafiya kuma yadawo lafiya." Rashida tafad'i hakan saboda takwantarwa da umma hankali don ita kanta tanajin ba dad'i akan tafiyar tasa. Dr nura bai baro tasha ba har saida yaga motarsu baba nashirin tashi sannan yanufi inda motarsa take, da sauri yajuyo ya tsaida motar had'e da leqawa tagefen tagar da baba yake yace. "Baba akwai waya a hannunka nasa maka lambata idan ka isa saika sanar damu don hankalinmu ya kwanta." "Likita kenan! ai inada lambarka tun satin can da alhaji yasaya mani wayar ya saka mani ita, in Sha ALLAH da zaran na isa zankiraku." "To shiken baba, amma ka kirani sai inga lambar taka nayi saving tunda banida ita." Nanfa fasinjoji suka fara suruttai suna qorafi akan suna b'ata masu lokaci amma kota kansu Dr baibi ba har saida baba yakirasa yaga lambar sannan yabar wajen, Saida yaga motar tasu tawuce sannan shima yaja tasa ya nufi gida. Ba'afi mintuna talatin da isar Dr gida ba saiga kira ya shigo ga wayarsa, lokacin duk suna zaune kan dining table suna lunch yana faman jinini wai ammie tabiyewa Fatima anyi masu eba kuma shi baya sonta, ita kuma ammie tace dole yacita don ita kad'ai tadafa kuma bazaibar gidan da yunwa ba, hakan yasashi tusa abincin yana wani b'ab'b'ata rai da kumbura fuska sunata yimasa dariya, ganin wayar tasa naruri yaqi d'agawa yasa dady tsaida dariyar tasa had'e da cewa. "Sorry son, qyale dota da ammienka, zamu rama kaji ko." "ALLAH dady babincinnan na garin kwaki bayada dad'i ko kad'an, ci kawai nakeyi badon Ina so ba." "Ajiye hakanan, kad'aga wayar da akeyi maka tun d'azu." Kallon wayar tasa dake famn ruri akaro na uku yayi had'e da qoqarin d'agawa yana fad'in. "Kai, Ashe baba ne ke kira tun d'azu, Assalamu alaikum, Eh nine, eh, yanzunnan fa ta tashi" "What?" Yafad'a da qarfi yana turo idanuwansa had'e da miqewa da qarfi. Hakan yasa su dady sakin cokullan dake hannunsu suna kallonsa. "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun." Shine abunda Dr keta nanatawa kafin yakalli dady dake tambayarsa ko lafiya yace "Dady wai motarsu babace tayi had'ari acan qauyen dake kan hanya idan anfita gari kad'an." Gaba d'aya sukasa sallami da sauri ammie tariqo hannun Fatima tayi d'aki da ita had'e da kwantar da ita kan gado tace. "'yata kinkwantar da hankalinki, kinsn yaron ciki kejikinki in sha ALLAH Babu abunda yafaru." Koda ammie tafito har dady da Dr sun fita. Sallallami tashigayi tana zagayar falo batare da tasan mezata aikata ba alokacin. Gaba d'aya su dady basuyi wta doguwar tafiya ba suka cimma inda akayi had'arin ashe suna fita daga cikin garinne sukayi karo da wata qaramar mota garin drivern ya kauce mata motarsu tayi cikin daji takife, kasancewar lambar Dr nura itace ta qarshe da baba yakira yasa lokacin da aka ciccirosu aka sami wayar ajikin baba da ko qwarzane baiyi ba amma rai yayi halinsa, kallo d'aya zaka yiwa gawarsa kasan mutumen kirkine saboda wani irin haske da qyalqyali da fuskarsa kefitarwa. Suna isa suka isko an jejjere gawarwakinsu agefen titi da sauri suka isa wajen, tsabar yanda hankalin dady ya tashi saida jiri yad'ebesa yayi baya baya zai fad'i Dr ya tarosa, gefe ya zaunar dashi sannan yanufi wajen 'yan sandan dake tsaitsaye suna korar mutane yayi masu bayani tare da nuna masu gawar baba dake kwance an lullub'a masa ganyen bedi akai ya nuna masu i.d card d'insa ta asibiti, suna tsaye motar asibiti ta iso aka kwashi gawawwakin kusan mutun uku wud'anda suka rasu biyar kuma sun samu raunuka, bayan motar su dady sukabi zuwa asibiti akayi 'yan bincike binciken da za'ayi ma gawawwakin da zai tabbatar da cewa mamatan sun rasu sukuma wud'anda suka jimu akayi masu treatment sannan akabasu dady gawar baba sukayo gida da ita, STORY CONTINUES BELOW Baqaramin tashin hankali su baba balarabe suka shiga ba lokacin da saqon rasuwar d'an uwan nasu ya isa garesuba, yayinda Yaya Maryam tadinga sabbatu tana fad'in. "Ba gaskiya bane, jiya mungansa, munhad'u dashi, munyi magana, mun yi fira da maganganu masu tsayi dashi, wara haka duk muna tare dashi taya za'ace yamutu, inaa banyarda ba, bashar bazi mutu yanzu ba bayan jiya jiya muna tare dashi, ya ALLAH kasa wannan zancen ba gaskiya bane, bashar mutumen kirkine, baikamata ace yamutu yanzu ba.." haka tayita sabbatu tana kuka har saida aka dinga rufe mata baki. Nan take baba balarabe da mijin yaya Maryam da wasu 'yan uwansa sukayi mota d'aya babba suka d'auki hanya cike da alhini. Duk da baba baifi shekara d'aya da watanni acikin garin borno ba babu inda mutuwarsa Bata kaiba, kuma duk wanda yab'ud'a baki fad'ar mutuncinsa da alkhairansa yakeyi, Umma kuwa da Rashida gaba d'aya sun fita hayyacinsu saboda sumar da sukayi, koda suka farfad'o itadai Rashida bata cewa komai si hawaye dake zubar mata tana kallon ammie da Fatima dake faman basu baki. Umma kuwa miqewa tayi tace akaita inda gawarsa take tana so taganesa, rirriqeta ammie da maqwabtanta da suka shigo sukayi suna fad'in don ALLAH tayi haquri kada take, ganin haka yasa Rashida tasowa tace. "Ammie don ALLAH kubarta taje." Matsowa tayi takama hannun umma tace "Umma zaki iya ganinsa." Kad'a mata kai tayi tariqe hannunta suka nufi wani d'aki dake gefen sashen ammie da alama d'aya daga cikin d'akunan dasu Dr sukayi zamane, suna kawowa zasu shiga faruq qanen dr yahanasu. "Don ALLAH kuyi haquri idan bazaku iya ba." yana qara tare bakin qofar idanuwansa cike da qwalla, duk da shi bai fiye shiga shirgin mutane ba saboda haka yake kamar yanajin warin mutane shiyasa baya mu'amala da kowa, amma duk da haka yana mauqar shiri da baba sosai don acewarsa shi mutumne nadaban ko acikin mutane, tasowa Dr yayi yasa hannu yajaye faruq gefe yana fad'in "Umma kushiga matuqar hakan zai rage maku rad'ad'i arai, saidai Ina so kutuna, ba'ayiwa mamaci kuka irin na jahiliya balle ga irin baba da mukeyiwa kyakkyawan zaton cewa ya dace." Yana gama fad'ar haka haka yad'an ja da baya yabasu hanya yana goge hawayensa, suna shiga sukaga baba kwance anlullub'esa, da sauri Rashida tarirriqe umma tana kuka tare da toshe bakinta. Duqawa umma tayi daidai fuskarsa tayaye lulub'in da aka rufa masa, ayanda taga fuskarsa tayi haske yaqara kyau tamkar yana dariya duk da tana cikin rad'ad'in mutuwarsa yasa tayi farinciki sosai. "Alhamdulillah malan, naji dad'in yanayin dana ganeka aciki, inafatar wannan qanwar dakace zaka samo mani tayimaka kyakkyawar tarba da kulawa kafin na iskoka, tsakanina dakai babu komai sai alkhairi idan ma kuma katab'a yimani wani abun nayafe maka duniya da lahira inafatar kaima baka tafi dani da komai acikin ranka ba kuma ina roqon ALLAH daya tsarowa rayuwarmu haka akan wannan bawa naka daka jiqansa da rahama, kagafarta masa ka amintar da rouhinsa." Rashida ta amsa da amin. Tana gama fad'ar haka tagoge hawayen idanuwanta sannan tamiqe suka fito, ayanayin da tafito kad'ai idan ka kalleta zaka tabbatar da cewa tagamsu da yanda taga mijin nata kuma tana yimasa kyakkyawan zato.. _karku manta mutuwa wajibice ga duk wanda keraye, azahiri ma idan munyi tunani soyayyarmu ko kuma qiyayarmu ga wata rayuwa bazata hana idan lokacinsa yayi ba ALLAH yakarb'i abunsa balle littafi, dayawan lokuta ALLAH yafi karb'e mana mutanen kirki aduniya fiye da na banza, da son samune nafiso baffa Ali yamutu fiye da baba amma ayanayin labarin mutuwar baba kad'aice zata haifar da rabuwar da Nuraddeen yayi da mahaifinsa har ya girma kamar yanda kuka gani a farkon littafi, Amma matuqar yana raye dattakonsa bazai bari hakan tafaru ba, don haka kuyi haquri da yanda labarin yake plzzz, ALLAH YAJIQAN BABA DA RAHAMA_πŸ‘ STORY CONTINUES BELOW *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [9/7/2020, 11:33 PM] S WHITEπŸ’Ž: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___68πŸ’Ž Saida 'yan uwan baba suka iso sannan akayimasa wanka aka sallaci gawarsa aka kaishi gidansa nagaskiya, a yanda mutane suka taru sukayi dandazo wajen sallar jana'izarsa kai ka dauka wani riqaqqen mai mulkine ko sarauta ko kuma wani hamshaqin malami, ALLAHU AKBAR, shiyasa akoda yaushe akeson mutum yazama mai sanyin hali da kyautata zamantakewa dtsakaninsa da mutane, duk da baba ba d'an asalin mazaunin cikin garin bane, kyakkyawan halayensa sun biyosa har zuwa qasarsa inda aka rufesa, bayada wani tarin arziqi kuma bai kasance wani sananne ba acikin garin da shekara d'aya kacal yayi acikinsa amma soyayyarsa ga ALLAH da kuma kyautata zaman takewarsa ga mutane yasa ubangijinsa ya soshi kuma yasa al'ummah ta soshi, babban abunda zaisa a kyautata masa zato shine yanda ruwa ke bulbulowa awajen haqar kabarinsa, har kusan sau biyu ana canza masa wani kabarin amma kowane aka haqo haka ake riskarsa, a dole aka d'aukesa akasashi hakanan acikinsu mutane namasu yabawa da ni'imarsa da ALLAH yayi masa tun akabari, duk inda kaduba cikin maqabartar cike yake da mutane ta ko ina da sukazo kawosa. Bayan andawo su baba balarabe sukaje sukaa yimasu umma nasiha akan sud'au haquri da tsarin qaddarar da ALLAH yayi masu akan d'an uwan nasu domin yanda yasamu jama'a suna kyautata masa zato had'e da yima junansu gaisuwa. Kwanan su baba balarabe uku sannan suka fara maganar komawarsu tunda anyi masa addu'ar uku, lokacin da sukaje wajen dady yimasa sallama akan zasu tafi kuma suna son suwuce da iyalan marigayin tunda dama shine jigonsu nazama garin kuma ALLAH yakarb'i abunsa sai dady yayi gyaran murya had'e da sake yimasu gaisuwar rashin d'an uwan nasu akaro na ba adadi sannan yace. "Malan balarabe Ina son in roqeki wata alfarma awajenku idan zaku iya" "Munaji alhaji ALLAH yasa batafi qarfinmu ba." "Eh to! Banace haka ba amma Ina son ne idan har kun amince kubar iyalan marigayi anan har zuwa lokacin da zata gama takaba, nayi maku alqawarin cewa zan kula maku dasu bisa amana har zuwa lokacin idan ALLAH yabamu aron rayuwa." Shiru baba balarabe yayi kafin yace to yabari sud'an shawarta tsakaninsa da sauran 'yan uwansa da suka zo tare, hakan yasa dady miqewa shida dr sukabar d'akin, bayan sun fita baba balarabe ya tambayi 'yan uwan nasa had'e da kirawo Yaya Maryam da aunty marwiyya dake can shiyar ammie da yake suma wan saheken rasuwar suka iso suda matan baba balarabe sannan yasa aka kirawo suma su umma sukayi shawara, nan take kowa ya amince da hakan don alkhairin da yayi masu bazasu iya hanasa wannan 'yar qanqanuwar alfarmar ba, umma kuwa dama cewa tayi duk shawarar da suka yanke akai tayi daidai batada ja, don haka koda suka nuna amincewar tazauna d'in batayi musu akaiba asalima yanzu tafijin garin aranta saboda mijinta dake ciki fiye da wancan garin da suka baro, gaba d'aya yafice mata arai batada sauran sha'awar komawa cikinsa. Sosai dady yaji dad'in amincewarsu da buqatarsa yayita yimasu godiya tare da fatan ALLAH ya saukesu lafiya, har bakin motocinsu gida biyu dake wajen gate yarakasu sannan suka wuce shi kuma yadawo gida yana mai jinjinawa qoqarinsu akan amincin da suka bashi. ••• ••• ••• Baffa da baffa Usman kuwa basusan abunda kefaruwa ba har akayi zaman ukkun baba basuda labari akan rasuwar tasa sai bayan kusan sati biyu sannan suka sani, baffa yayi kuka sosai akan mutuwar aminin nasa wanda d'an uwansa yakasa sanar dashi saboda wata 'yar rashin fahimta data shiga tsakaninsu, babu abunda yafi qona masa rai irin ace ALLAH yasa har ansan inda suka tafi amma akaqi sanar dashi har ta ALLAH ta faru akansa, yamatuqar jin zafi da Kuma rad'ad'i azuciyarsa fiye da abubuwan da suka faru abaya, hakan yasa yaqudurce aransa bazaya koma waiwayarsu baba balarabe ba akan maganar da tasa suka yanke ganawa tsakaninsa da aminin nasa idan har suna tunanin hakan tafarune da son ransa ko kuma da had'in bakinsa har sai lokacin da ubangiji yatashi bayyanar da gaskiyar al-amarin, duk da wannan matakin daya d'auka hakan bai hanashi had'a waau daga cikin 'yan uwansa mata ba da wasu abokanansa da 'yan uwansa maza kusan mota biyu sukaje har gida suka yowa baba balarabe gaisuwa, aranar baba balarabe yaji kunyar da bai tab'a jiba aduniya, so yake yakeb'ance da baffa suyi magana amma tsananin b'acin ran dake zuciyar baffa yasa ko bari bayayi su had'a ido dashi balle suyi wata magana, gaisuwa dai ce takawosa kuma yayi masa fatanshi d'aya ALLAH yajiqan aminin nasa kuma ya lullub'esa da rahama, haka sukabar gidan batare daya samu keb'ewa dashi ba ko kad'an, wannan abun yaqara saka baba balarabe cikin nadama da dana sanin abunda yayi don yatabbata shima baffa yayi fushi akan zancen rasuwar da ba'a sanar dasu ba, STORY CONTINUES BELOW Su baffa nafita nan suka nufi gidan Yaya Maryam da aunty marwiyya suka yomasu gaisuwa, nanma baffa bai nuna masu komaiba banda gaisuwar da sukaje yimasu ba sannan suka koma gida. Suna isa gida baffa yanemi waje yakwanta sboda wani irin zazzab'i daya rufesa, kallonsa matarsa nusaiba tayi had'e da cewa. "Baffa don ALLAH kafidda damuwar wannan abun aranka, karka manta duka mai rai mamacine, koda kasan da maganar ganinsu bazaka iya hana mutuwarsa ba tunda lokaci yayi, haka kuma koda ansanar dakai zancen rasuwarsa dawuri bazaka iya canza komai ba akan abunda yafaru, don haka kayi haquri muma nan duk ita muke jira, babu wanda kezuwa har sai lokacinsa yayi, su day suka tafi basuyi gaggawa ba mukuma da bamu tafi ba bamuyi jinkiri ba, ubangiji ALLAH kasa muyi kyakkyawan qarshe." "Amin." baffa yafad'a yana kallon d'an qaramin cikin dake jikinta yataso kad'an, murmushin da yafi kuka ciwo yayi yanajin wani irin zugi aransa, anan yaqudurta azuciyarsa idan ALLAH yasauketa lafiya matuqar namiji tahaifa zaiyiwa aminin nasa takwara, ganin yanda takafesa da idanuwa kamar zatayi kuka tana fad'in. "Baffa kayi haquri kaji." Don haka take kiransa har yanzu, yayi yayi da ita tadena amma taqi, hakan yasa yaqaqaro murmushin qarfin hali had'e da cewa. "Nusaiba to me akayi naga kina b'ata fuska, ai dole nahaqura tunda yariga ya tafiyarsa, amma inajin rad'ad'in rabuwata dashi sosai," "To kayi masa addu'a," "Zanyi masa nusaiba amma kema zakiyi masa takwara idan kika haifi namiji?" Cike da yarinta tasa hannuwa tarufe fuskarta, don har lokacin bata cika shekaru goma sha shida ba aduniya kuma ALLAH ya albarkaceta da samun ciki wata hud'u kenan ynzu da kwanaki, yana matuqar jin dad'in zama da ita duk da zamowarta yarinya da mafiya al-amurranta shirme sunfi yawa, amma takan nuna damuwarta aduk lokacin data ganesa cikin damuwa kuma tana bashi kulawa daidai iya qarfinta naqaramar yarinya dad'in dad'awa ma ladabi da biyayyar da take yimasa badon 'yan matsalolin dake tattare dashiba dake hanasa samun cikakkiyara natsuwa da yace gaba d'aya bai tab'ajin dad'in rayuwar aure ba sai yanzu, qaramar yarinyace mma tanada kiyayewa sosai wajen iya zama da miji bisa turbar da yake koyar da ita, hakan yasa duk yanda damuwa tayi masa yawa idan yaga hakan zai haifar da tasirinta wajen cutar da yarinyar yake dannewa, hakan yayiko yanzu yadanne duk abunda yakeji yashiga zolayarta tana dariya. Bayan kwana biyu baffa yaje can gidansu baffa Usman ya isko 'yan sanda sunyi cirko cirko aqofar gidan wai zasu kama muneera akan tafasama wani saurayi dutsi a ijiya har saida ta tsiyaye gaba d'aya. Inspector najida yagani a tsaye jikin motar fuskarta ba walwala tana jira ashiga akamo muneerar, wajenta yanufa tana ganinsa tasaki fuskarta had'e da qarasawa wajensa kafin ya iso, d'an russuna kai tayi tagaishesa had'e da cewa. "Baba ya gida ya kwana biyu?" "Alhamdulillah 'yata injin dai ko lafiya?." "Lafiya lau baba, yaron kune yafasawa wani ijiya shine aka kaimana qararsa." "Subhanallahi wakenan." "Muneera baba, yarinyar nan batajin magana sau biyu kenan ana kaimana case d'inta amma saboda kai sai nasa asulhunta abun, amma awannan karon dole mukai case d'in kotu." "Haba 'yatah, don ALLAH karkice haka ai shi taimako ba'a gajiya dayinsa." "A'a baba! Haka ya isa batajin magana da yawa, koda zamuyi wani abun dole sai munje kotu da ita." "Shikenan!, 'yatah ALLAH ya kyauta, zamu biyo bayanku in Sha ALLAH muji yanda za'ayi." Har inspector najida tajuya zata tafi sai kuma tasake juyowa ta tsaida baffa tana fad'in. STORY CONTINUES BELOW "Baba nikam nace wai yabatun tsohuwar matarnan taka Yaya hawwa, injin tasamu sauqi?." Saida Baffa ya sinne kai yana d'an sosa qeyarsa saboda nauyin maganar da yaji sannan yace. "Ehmm! Da sauqi zamuce, Amma har yanzu tana kware anaci gaba da bata kulawa aqarqashin jami'an lafiya." "ALLAH sarki, ALLAH yabata lafiya, kwanakima nayita neman lambarka awayata narasa lokacin da naga ana nuno yanayin da take ciki a tv, abun yabani tausayi sosai sai natuna da zancen bokan da take zuwa wajensa dake asibiti, shaf namanta nakiraka na sanar dakai cewa bayan angama bashi treatment yafarajin sauqi da sati d'aya ashe shima yasamu matsala aqwaqwalwarsa, abun mamaki koda akayi masa gwaje gwaje sai aka samu qwaqwalwarsa lafiya take Amma yanayin abubuwa irin na miyagun mahaukata dake iya illata kowa, asibitin na shirin sallamarsa sai aka samu ya gudu, yanzu haka zaka ganesa akan tituna tsirara haihuwar uwarsa ko akan juji yanacin lalataccen abinci marasa kyau kamar yanda mahaukata keyi a wani lokacin kuma sai kagansa da sutura ajiki yana bin mutane yana bara abashi abincin da zaici, rayuwa yakeyi gatanan dai, shi ba dabba ba kuma ba cikakken mutum ba, hakan yasa nayi tunanin cewa wataqila matsalarsu d'aya da tsohuwar matarka, Ina nufin qwaqwalwarsu lafiya klw take saidai suna azabtuwane ta dalilin miyagun aljanun da suka shiga jikinsu su sukesa sunayin wud'annan abubuwan dakesa anayi masu kallon mahaukata, shine nayi tunanin kiranka nafad'a maka ko zaku koma gwada maganin musuluncine tunda yanzu kusan shekara d'aya da watanni kenan ana fama dana asibitin ba'a dace ba." Shiru baffa yayi yana maimaita kalaman inspector najida a qwaqwalwarsa, tabbas maganarta akwai qamshin gaskiya aciki dole yayi nazari akanta sosai ko ALLAH zaisa adace. "Shikenan 'yata in Sha ALLAH zamuyi tunani akan haka nida 'yan uwana, dama qarfina yafara qarewa akan wannan matsalar tata, kullum cikin kashin kud'i ake, kuma duk da binciken da sukayi akanta suka yad'a aduniya ankasa samun tallafi daga ko ina." "ALLAH yasawaqe baba, har yanzu ita matar d'an naka ba'a ganta ba ko?" Saida Baffa yayi ajiyar zuciya sannan yace. "ALLAH kad'ai yasani 'yatah.." Ananma yake bata labarin rasuwar aminin nasa wato mahaifin matar d'ansa, tamatuqar tausayawa tare da yimasa addu'ar ALLAH yajiqansa da rahama, suna tsaye 'yan sanda suka fito da muneera duk anbubbuge mata fuska saboda taurin kan da tasa wajen kamota, su kansu 'yan sandan sai nishi sukeyi saboda wahalar dasu da tayi suna sake jibgarta da kulaken dake hannuwansu Inna ruqayya nabiye dasu tana d'ura masu zagi, juyowa inspector najida tayi da qarfi jin zagin da takeyi masu, Inna ruqayya naganin haka ta arta dana kare don bata manta irin azabar da tasha ahannun taba, ana qoqarin tura muneera mota tarugo da gudu ta lab'e bayan baffa da yayi tsaye yana kallon ikon ALLAH tana fad'in. "Wayyo baffa ka ceceni, wlh ba laifina bane, innace tace naje wajen salele na karb'o mata saqo ashe wai iskanci zaiyi dani ya bata kud'i, shine ni kuma na doka masa wani qarfe yafad'a akan wani abu nasamu nayi guduwata, shine akace wai nafasa masa ijiya, don Allah baffa kataimakeni bana son zuwa." "Yi haquri munneera jeki ku tafi yanzu nida Usman zamu biyo bayanku, Ina shi baffan naki yake?" "Ya gudu baffa, kuma wlh har dashi ke karb'ewa salele kud'i wai zaya aura mani shi ni kuma bana sonsa, kuma baffa ya..." "Ashsha muneera yishiru haka jeki kinji zamuzo yanzunnan?" 'Bare baki tayi tana kuka had'e da susar kai 'yan sandan sukazo suka cakumeta tanata tsalle tsalle da ihu suka sakata aciki, yaran anguwa da suka taru sai faman dariya sukeyi, girgiza kai baffa yayi sannan yabar wajen don ya tabbata Usman baya cikin gidan shi Kuma mahaifin nata sakaran wofi da rashin kunyarsa akansu kad'ai ta tsaya yayi guduwarsa... Daqyar baffa Usman da baffa suka samu sukayo belin muneera batare da anje kotu ba saboda ijiyar yaron batayi komai ba amma yace sai ambiyasa kud'insa. STORY CONTINUES BELOW Don haka sukaje suka kama d'aya daga cikin shanun baffa Ali suka sayar batare da yasani ba aka biya salele kud'insa sannan akayi masu tsakani da ita, sauran kud'in kuma baffa yakai masa, baffa Ali sai faman wasar baki yakeyi duk d'aukarsa a banza aka bashi kud'in, Saida yagama murnarsa sannan baffa Usman yafad'a masa yanda aka samu kud'in, wayyo ranar yini baffa Ali yayi yana d'ebe masu albarka tare da zunduma masu zagi, yaran gida duk Wanda ya matsosa saidai yaji ya falla masa mari yana d'ura masa ashar, daga qarshe da yaji rad'ad'in yaqi d'ebe masa yasa muneera d'aki yasata yayita jibgarta yana tsina yana fad'in sai yafidda kud'in naggensa ajikinta.Baffa Usman dake zaune yana shan fura yayi dariya had'e da cewa+ "Oho dai, inma kasheta zakayi ka kashe ai 'yarka ce, ayanda kake marar hankalin nan da tunani babu abunda yakamata ace kayi illa kanunawa duniya cewa nagge tafi 'yarka muneera awajenka, shasha kawai, mudai bazamu doku ba awajenka, ubangiji ALLAH kashiryar mana dakai kada baqincikinka yasa murasa rayukanmu *BAYAN SHEKARU ASHIRIN DA BIYAR* Abubuwa da dama sunfaru wud'anda duk wani mumuni ya ishesa d'aukar darasin duniya matuqar babu ta'bewa da 'bata acikin rayuwarsa.... *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [9/8/2020, 11:21 PM] S WHITEπŸ’Ž: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___69πŸ’Ž Musamman acikin rayuwar Rashida da mahaifiyarta da idan kazauna kayi nazari zaka fahimci dalilin daya hana Rashida yin karatu tace aure take so har ta auri Nuraddeen mahaifiyarsa ta turo mata aljanu suka d'auketa suka kawota garin borno, har hakan taja iyayenta suka baro garinsu cikin qaddarawar ALLAH kuma aka sake had'asu gari d'aya da inda 'yarsu take kuma ta ALLAH tazo ta afku akan mahaifinta da aka tsaro cewa nanne qasar da za'a rufesa, don bayan umma takammala takaba sai dady yasake bijirowa da buqatar d'ansa akan yana son Rashida ta tsaya anan taci gaba da karatu har lokacin da ALLAH zai dawo da mijinta, badon su baba balarabe naso ba suka sake amince masa akaro na biyu bisa sharad'in duk lokacin da mijin nata yadawo dole zata ajiye karatun takoma hannunsu don su mayar masa da ita, wannan dalilin yasa itama umma tace bazata komaba zata zauna da 'yarta don itama tabata tata gudun mawa wajen cikawa baba burinsa naganin tayi karatu mai zurfi kamar yanda yaso, kasancewar tanada 'yancin kanta yasa babu wanda ya tilasta mata akan sai takoma suka bisu da fatan alkhairi Cikin sati biyu Dr nura ya ida kammala shireshiren komawarta makarantar tare da sama mata Mai lesson na musamman da zai taimaka mata don j.s.s 3 yace akaita duk da kuwa qoqarinta bai kai can ba, nan take tafara karatu ka in da na'in cikin jajircewa da qaunar cikawa mahaifinta burinsa, Ammie kuwa tuni ta dakatar da umma batun aikin da takeyi mata tasa aka samo mata wata sai ya zamana umma bata aikin komai agidan inba kula da gyara shiyar da suke ba da kwanciya don ko girki ammie kesa ana kaimasu nasu daga sashenta idan andafa, dady kuwa akoda yaushe cikin kulawa dasu da yimasu hidima yake, kwatsam ranar yasami ammie da zancen yana son ya auri umma saboda shidai yana tsananin tausayinta aransa don tunda baba yarasu har yanzu takasa komawa daidai, kuma shi agani sa idan yayi hakan yiyi jahadi sosai tunda batawuce yin aure ba to baiga amfanin tazauna ahaka ba, asalima yana tunanin idan har tanada sha'awar yin aure Wanda zai iya damqawa amanarta kuma yariqeta hannnu biyu, hakan yasa azuciyarsa yaji ya amince d'ari bisa d'ari don tabbatar daya riqe amanarsu hannu biyu kamar yanda ya d'auka, zuciya batada qashi kuma shi kishi gaskiya ne don haka awannan lokacin ammie sai taji badad'i aranta amma saita danne zuciyarta tabashi goyon baya tare da qarfafa masa wajen aikata hakan, STORY CONTINUES BELOW Kwana biyu tayi tunda dady yayi maganar bata barin su had'u da umma saboda abunda takeji nataso mata aqasan zuciya saboda kada tayi abunda ba daidai ba, daga qarshe kuma tasaki taroqi ALLAH yasa hakan shiyafi zama alkhairi, Hajia nafeesa kuwa da taji Babu irin maseefar da batayi ba da habaice habaice tun umma batasan abunda kefaruwa ba don bai riga ya sanar da ita ba har tasani, ta matuqar girgiza had'e da nuna qin amincewarta amma ammie tayita lurar da ita da lallashinta har saida ta amince, ba'a wata samu matsala ta b'angaren 'yan uwanta dana baba ba sboda ganin dattako da cancantar dady suma suka amince, nan take dady yasa aka rushe sashen da take da wasu wurare cikin gidan itama aka fitar mata da part d'inta abunka ga mai arziqi cikin sati biyu aka kammala komai har d'aurin aure ta tare abinta, Duk wannan abun daya faru bisa amincewar Dr da taimakonsa dady yayis hakan kuma dashi har Fatima sunyi farinciki sosai ba tare da wata hiyana ba, Rashida ce kawai kullum take cikin jin kunya tana ganin kamar hakan da akayi ba'a kyautawa ammie ba, bayan duk taimako da halaccin da tayi masu ita da d'anta har saida ammie tazaunar da ita tanuna mata hakan ba illa bane tunda musulunci bai hana ba sannan tafara samun sakewa daidai, duk da ako yaushe idan hajia nafeesa tahad'u da ita har mahaifiyarta cikin jifarsu take da miyagun kalamai cewa wai Rashida tayi cikin shegene shiyasa tagudo suma da abun kunya ya ishesu sun kasa gano uban d'and'an dake cikinta sai suka biyo bayanta, hatta ma little da baisan komai ba kullum cikin kyararsa take tana aibantasa agaban 'ya'yanta tana kiransa da shege wanda ba'asan ubansa ba, hakan yasa har 'ya'yanta ma ke kiransa da haka amma da yake baisan komai ba baya damuwa. Haka rayuwa taci gaba Rashida nasamun kulawa da kuma gudun mawa sosai wajen karatunta da ita har d'anta ta b'angare biyu wato dady da kuma Dr, don tuni shima little Dr yasashi makaranta lokacin itama Fatima har tahaihu tasamu qaton d'and'anta suka rad'a masa suna basheer wato sukawa baba takwara, wannan ba qaramar kima da daraja yaqara jawo masuba a idanuwan umma da Rashida harma da 'yan uwansa, sunyi matuqar farinciki da jin dad'i sosai aransu harma suna ganin aduniya yanzu basuda masoya da suka fimasu su dady da Dr nura ba. Rashida kuwa tun tana dakon dawowar mijinta izuwa gareta ita da d'anta har tacire rai, gaba d'aya ta tattara wata rayuwar aure data tab'ayi abaya dama auren ta ajiyesu gefe taci gaba da karatunta ita da yaronta, saidai duk da hakan daidai da rana d'aya Bata tab'a yarda tayi wani abun da zaya keta mata marta da kuma darajar auren taba har ta kammala secondary lokacin little na primary 2 amma babu wani labarinsa, a lokacin fatima har tayaye basheer da suke kira (abbaty) tasake samun ciki ta haifi 'yan biyu duka mata saidai rurrutsa ce tayi a tsakaninsu, inda aka barsu da sunayensu na asali wato hassana da hussaina, murna kam awajen Dr da fatima bata misaltuwa, gashi dai SANNU SANNU cikin iyawar ALLAH suma sunfara tara nasu 'ya'yan da suke matuqar qauna a cikin shekaru uku kacal ALLAH ya arzuttasu da 'ya'ya uku, Babu wata wahalar reno da fatima kesha saboda Rashida nanan, duk wata kulawa da yaran zasu buqata tana basu tamkar ita tahaifesu. Shekarar Rashida d'aya tana jiran saka makon jarabawar tasu tafito kuma cikin taimakon ALLAH tayi nasarar lashe kowane darasin da kyakkyawan sakamako wato exelent gaba d'aya, ranar da ita har umma sunyi kuka sosai cike da son inama baba nada rai yaga yanda tafara taka mataki na biyu akaratu da kyakkyawan sakamako, godiya kuwa sunyiwa Dr da dady da ammie ba adadi har saida suka farajin kunya. Umma da ammie kuwa bazaka tab'a ganinsu kace kishiyoyi bane domin akwai tsantsar fahimta da mutunta juna atsakaninsu, hakan yaqarawa hajia nafeesa tsanar umma da rashida dama little gaba d'aya. ••• ••• ••• A b'angarensu baffama acikin shekarunne ALLAH ya sauki nusaiba matarsa lafiya saidai ba'a samu namiji ba kamar yanda yaso ALLAH ya arzuttasu dai da samun 'ya mace kyakkyawa kamarta sak da nusaiba baffa ya rad'a mata suna Rashida, yana matuqar son yarinyar fiye da tunani saboda sunan data zauna, sau da dama yakan tuna da baba da Kuma 'yarsa Rashida aduk sadda aka ambaci sunan 'yar tasa da taci sunan Rashida, wannan yasa ko kad'an baya son jin kukanta balle abunda zai b'ata mata rai, hakama gaba d'aya yakasa mantawa da gudan jininsa daya kasa samun labarinsa, lokacin daya tuntubi ma'aikatar da aka turasu qasar waje don qaro karatu akan labarinsa sai suka b'oye masa ainahin halin da d'an nasa ke ciki, domin koda Nuraddeen suka isa qasae waje bayan anbasu wajen zama sai yanemi wayarsa sama da qasa yarasa, gashi gaba d'aya wud'an da aka had'asa dasu zama 'yan jahohin kudu ne acan nageria babu wanda yasani acikinsu, asalima gaba d'ayansu babu ruwansu dashi saboda shikad'aine bahaushe sai suka nuna mashi halinsu qarara na qyamar jinsin da banasu ba musamman ma ga musulmi d'an arewa duk da kuwa qasarsu d'aya, hakan yasake jefasa acikin wata damuwar akan wacce yake ciki yana son yasan halin da ake ciki anan gida nageria amma bayada waya, kud'ad'ensa ma daya zo dasu gaba d'aya an sace balle yasamu ya sayi wata, wata irin wahalalliyar rayuwa yafarayi aqasar da kud'in ma da zai samu yayi amfani dasu babu, ana haka d'aya daga cikin qabilun da yake tare dasu yafara qoqarin jawosa jiki yana son taimaka masa da sunan tausaya masa, amma azuciyarsa bashine dalilin silar taimakon da yake yimasa ba kawai yana so ya d'orasa akan hanyar da zata hanasa karatune balle yasamu yayi abunda yakawosa har yakoma qasarsa ana alfahari dashi sai dai duk da haka Nuraddeen bai tab'a wasa da karatunsa da tuni suka fara yiba a fannin koyon likitanci na psychiatric musamman idan yatuna da halin daya baro mahaifiyarsa aciki sai yaji yaqara samun qwarin guiwar maida hankali sosai, hakan yasa yazamo kusan shine zakara kuma zaqwaqurin da yafi kowane d'alibi amakarantar, tun daga kan fararen fata har zuwa 'yan uwansa baqaqe, wannan abun yaqara baqantawa natare dashi rai ganin shi bakowa bane acikinsu amma ace ya zartasu qoqari acikin aji, don haka suka sake d'aukar d'amara wajen ganin sun durqushesa tahanyar jansa ga jiki, sunyi amfani da yawan damuwar da yake shiga wajen ganin sun jawo ra'ayinsa tahanyar zagayawa dashi wajaje masu ban sha'awa da d'aukar hankali aqasar wanda nan take suka fara zuwa club club dashi suna nuna masa hanyoyin shaye shayen qwayoyi da barasa da sunan zasu taimaka masa wajen rage damuwar da take ciki, yau da gobe babu abunda tabari, tun Nuraddeen najin bazai iyayin hakanba har yafara sha'awar aikatawa batare daya ankara ba, akoda yaushe yakan zauna yana qoqarin tunano gida da abunda yafaru sai yaji yakasa tuna komai, sab'anin da da kullum cikin tunaninsa da abunda yafaru tsakaninsa da matarsa yake, wani abu daya sake d'aure masa kai shine yanda bayason tuna qasarsa gaba d'aya balle ahalinsa shiyasa nan take suka samu nasarar juyar dashi yanda suke so, idanma yace zai zauna yatuna wani abu akansa sai yaji kansa na matuqar sara masa da yimasa ciwo, bazaiji yasamu sauqin hakan ba har sai ya d'auki barasar da tuni ya amince da takan rage masa damuwa yasha. STORY CONTINUES BELOW Gaba d'aya rayuwarsa tagurb'ace amma wani ikon ALLAH babu abunda ya sauya ta b'angaren karatunsa, zai iya sha yabugu sosai sannan yaje aji suyita yimasa dariya yana wartsakewa zaije yanemi topic d'in da akayi yayi reasarch akai kuma nan take yafahimta, idanma yakasa zaije yanemi malamin duk inda yake ya sake yimasa bayani, malamai da yawa na mamakin halin da yaron yajefa kansa aciki wanda shi da kansa idan an tambayesa bazai iya fad'ar daliliba, iya abunda zai iya fad'a akai shine baya son tuna komai akansa, ahalinsa da kuma qasarsa, idan kuma yayi yunqurin hakan to halin da zai tsinci kansa aciki shine zai haifar masa da shan barasa don yasamu magancesa.. *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [9/10/2020, 11:15 PM] S WHITEπŸ’Ž: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ _Masha ALLAH, a gaskiya zafafan comment d'inku akan yanayin da Nuraddeen keciki sun tafasa k'wak'walwata, da banyi niyar cewa komai ba but yazama dole nace wani abun wataqil hakan zaisa kud'an fahimceni, A iya sanina qarfin imanin mutum qarfin jarabawar da ALLAH zai yimasaπŸ˜…alkawarin ALLAH ne cewa duk wanda yace yayi imani to dole za'a jarabcesa tako ina arayuwarsa don atabbatar da ingancin imaninsa, don haka kuyi haquri da halin da Nuraddeen ya tsinci kansa aciki, ba burina ku karanta littafin ku nishad'antu dashi kawai neba, a'a ina son kutsinci darussan dake cikine tare da fahimtarsu, karku manta alqalamin marubuci bayana ta'allaqa kawai bane akan nishad'antarwa da burgewa, dole yazamo ansamu ilmantarwa, fad'akarwa da kuma luraswa aciki, hakan shi zai bashi damar isar da saqon da ake son isarwa ya yanda yakamata, da fatar nima kun fahimceni yanda yakamata_πŸ₯° Page___70πŸ’Ž Haka rayuwar Nuraddeen taci gaba da kasancewa acan batare da mahaifinsa sun san komaiba, sukuma jami'an dake kulawa da lamurran karatunsu babu abunda basu sani ba, duk iya matakan daya kamata su d'aukar masa suna iya qoqarinsu amma hakan tafaskara, ganin yana karatunsa yanda yakamata d'abiarsa ce kawai yagagara gyarawa daga yanda take yanzu zuwa yanda take ada yasa suka qyalesa, a qa'ida tsarin karatun nasu shekara shida zasuyo acan sannan su kammala, amma bayan shekara uku zasu dawo gida hutun wata d'aya sannan sukoma su ida qarasa sauran shekaru uku. Lokacin da suka shekara uku acan aka tashi dawowa hutu Nuraddeen kafewa yayi kai da fata shi babu inda zaije, Babu irin yanda ba'ayi dashi ba yace shi gaba d'aya baya buqatar hutun balle har yakoma qasarsa, kasancewar yanada matuqar qoqarin da tun daga d'aliban makarantar har zuwa malanta Babu wanda bai sanshi ba, don haka sai 'yan uwansa mazauna kano da sukazo tare sukaje suka sanar da wani malamin halin da ake ciki, koda yaje shima yayi masa magana irin amsar daya basu ya bashi, nan take malamin yaje ya sanar da shugabar makarantar da yake macece (Miss Florence Jackson) tasa aka kirawo matashi tayi masa magana, tayi iya juyin duniya akan yabi 'yan uwansa amma yaqi amincewa daga qarshe ma sai yafara riqe kai irin alamun maganar na neman saka mashi damuwa, don haka sai tace subarshi zatayi magana da jagororinsu na nan qasar zai zauna awajenta saboda su awajensu kowa nada 'yancin kansa yayi duk abunda yakeso, hakan kuwa akayi gaba d'aya d'alibban da sukaje tare dashi suka dawo gida cike da farinciki zasuga ahalinsu da iyalansu bayan tsawon shekaru uku da suka sharikke awaccan qasar. Baffa nasamun labarin dawowarsu cike da farinciki ya sanar da baffa Usman, Kwana da yini sukayi suna jiran isowarsa gida amma shiru wannan dalilin yasa baffa ya isko baffa Usman har gida cike da damuwa ya sanar dashi cewa tunda sukaga bai iso gida ba to tabbas ba lafiya yakamata suje su tuntub'i manyannasu suji meke faruwa?, STORY CONTINUES BELOW Ba qaramin tashin hankali baffa yashiga ba lokacin da akayi masa bayanin abunda yafaru na cewa Nuraddeen yaqi amincewa yadawo wai har sai sun kammala karatun gaba d'aya nan da wasu shekaru uku masu zuwa, kusan fad'uwa zaune yayi daga tsayen da yake saida Baffa Usman yayi saurin riqosa, ba abunda kefita bakinsa inba. "Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun, qadarallahu wama sha'a fa'ala." Tabbas jikinsa yanzu nabashi akwai abunda kefaruwa akan d'ansa wanda aka b'oye masa, Aikuwa daya matsa lallai sai ansanar dashi dalilin da yasa hakan zata faru sai suka sanar dashi gaskiyar halin da Nuraddeen keciki don bazasu iya cigaba da b'oye masa ba a matsayinsa na uba awurinsa kuma suka sanar dashi cewa yana cikin qoshin lafiya sannan kuma yana maida hankalinsa ga karatunsa sosai don haka yakwantar da hankalinsa. Awannan ranar gaba d'aya guiwowin baffa saida suka sare had'e dayin sanyi kuma ya yadda cewa tabbas rayuwar mumini kullum cikin jarabta ta akeyi, idan yafita wannan jarabawar sai kuma wata takunno kai, yashiga kwararo addu'a ALLAH yabashi qwarin guiwar da zai rinjayi zuciyarsa har zuwa lokacin da ALLAH zai canye dukkanin jarabawowinsa. Bayan sun dawo suna tsaye a qofar gida suna tattaunawa akan yanda zasu b'ullowa matsalar, baffa Usman nata rantsuwa cewa tabbas koma meye akwai abunda badaidai ba don yayi imanin bazai tab'a aikata abubuwan da akace ba, idanko har gaskiya ne to tabbas bayin kansa bane, Ashe duk abunda suka fad'a Inna ruqayya da zata fitowa tajisu don haka sai takoma cikin zaure ta lab'e tana saurarensu. Tsabar farinciki da jin dad'in abunda kunnuwanta suka jiyo mata nassa taji wani irin sanyi azuciyarta kuma ta gamsu cewa tabbas haqarsu ta cimma ruwa kuma abunda suka dad'e suna dakon jira amatsayin fansar da suke son d'auka ya tabbata, fasa fitar tayi takoma cikin gida fuskarnan tata tamkar ambiya mata makka tashige d'aki tana tiqar rawa had'e da cewa da SANNU SANNU zakuga aikina da ciwa, kad'an kuka gani ai indai ina raye saina qumsa maku baqincikin da kuka qumsa mani nida 'yata akan yaronku, tashi baffa Ali da bai jima da kwantawa ba yayi yana kallonta cike da mamaki, dama dawowarsa kenan daga d'aukar hatsinsu da suka girbe ta tambayesa kud'i ya hanata shine tafita tana kumburar fuska wai zataje ta aro wani wuri, sai gashi bata jima da fitar ba yaga kuma tadawo fuskarta d'auke da farinciki tana dabsar rawa, tun kafin ya tambayeta ta shiga zayyane masa abunda taji 'yan uwan nasa nafad'a akan halin da Nuraddeen keci acan qasar. Nan shima fa yatayata har yana fad'in wai anzo wajen!, sai su baffa sunyi dana sani da nadamar turasa qasar waje yaqaro katu, don bazaya tab'a dawo masu amatsayin wanda yayo karatu ba, sai dai yadawo masu a matsayin d'an iska lalatacce da baza'a iya tab'a banbance tsakaninsa da arna ba tunda suka zab'i turasa can akan aurar masa da 'yarsa, bayan duk walaqancin da akayi masu da wanda Yaya hawwa tayita masu alhalin ansamu damar da za'a iya aura masa ita, yazama dole yaje yabiya malan bakada imani don yanzu kam yatabbata yayi masu aikin daya dace, fatanshi kawai ALLAH yaqara duhu don girman d'ib. Ashe duk wannan abun daya samu Nuraddeen aikinsu ne, su suka kaishi wajen malamin tsibbu sukace ayi masa asarin da zai lalace kuma idan yabar qasar ya manta da kowa nasa, asamashi tsanar qasarsa gaba d'aya yadena sha'awarta balle ma yatuna da iyayensa ko matarsa, duk wata hanyar da zatasa yaci gaba a dwad'e masa ita hatta karatun da akace zaije yi ya kasa yinsa, aganinsu yin hakan shine kad'ai zaisa su d'aukar fansar abunda baffa yasa akayi masu, fansar da batada wani tushe balle asali. Ba'ayi wata da faruwar hakan ba su baffa sukaje sokoto asibiti wajen karb'owa Yaya hawwa sallama don ba laifi tafara samun sauqi, duk iya qoqarin su naganin ambasu sallama aranar hakan ta cutara daga qarshema sai ankace suje sai bayan sati biyu su dawo, ko kad'an basuso hakan ba amma babu yanda suka iya dole suka koma gida, sati biyu nacika suka sake komawa, awannan karonma saida sukayi da gaske sannan aka basu sallamar, itama d'in da sunan transfer ne akayi masu izuwa asibitin PSYCHIATRIC dake can kano sannan aka d'aukosu da motar asibitin. STORY CONTINUES BELOW Inna Bilkisu ita tagyarawa Yaya hawwa d'akinta kafin su iso, acan asibitin aka kaisu sukayiwa wani babban likita bayani akan suna son komawa da ita gida sugwada yimata maganin hausa idan ALLAH baisa aka dace ba sai sudawo, cikin sa'a da yake bahaushene kuma musulmi ya amince masu tare dasa hannu akan file d'in nata sannan aka aai aka ajiyesa inda yakamata, kuma ya fad'a masu aduk lokacin da buqatar kawota asibiti takama ba matsala sukawota in Sha ALLAH za'a dubata, data dai takowace irin hanyace ALLAH yabata lafiya, sunyi matuqar jin dad'i bisa karamcin daya yimasu kafin suyi masa godiya suwuce da ita gida. Qwararrin malamai masu ruqya suka samo akayi mata ruqya, inda nan take mugun aljanin dake jikinta ya bayya yana wata qara da kururuwar shi bazai fita ajikinta ba tunda tasa aka azabtar dashi, aka naqasa shi tare da illata masa rayuwa don haka shima bazai gusheba yana azabtar da ita acikin jiki ba har sai lokacin da ruhinta ya rabu da gangar jikinta, babu irin magiyar da ba'ayi masa ba amma yaqi don haka malaman sukaci gaba da yimata karatu ana watsa ma aljanin ruwan magani yana wata irin muguwar qara saboda zabar qonasa da akeyi har saida yaqone tas, nan take jikinta ya saki malaman suka yima ALLAH godiya daya basu nasarar qona aljanin batare daya naqasa taba, sannan suka bada maganukkan da za'a dinga bata tare da tabbatar masu da cewa in sha ALLAH tasamu lafiya musamman idan aka dage da kulawa wajen bata maganin. Cikin iyawar ALLAH da aka dage wajen kula da bata maganin sai gashi tafara samun sauqi sosai, duk wasu kuwace kuwace da wasu caccanza halittarta da akeyi tadenayi, tadena bugu balle maqura, haka kuma tana iya gane duk wanda yazo wajenta maganace kad'ai bata iyayi, yanayin yanda idan Inna Bilkisu tashiga kaimata abinci ko bata magani take kuka hawaye nazuba a idanuwanta shike qara tabbatar da cewa tasamu lafiya, don kallo d'aya zakayi mata kasan cewa ba kukan komai ne takeyi ba illa na tarin nadama, don gaba d'aya cinta, shanta, kula da tsaftaceta duka ita keyi ita da yaranta su Aisha, musamman idan basa komai d'akinta duk suke zuwa azauna ayita fira saboda kada subarta cikin kad'aici, wani lokacin saidai taqura masu idanuwa tayita kallo batare data tanka masu ba, duk da aranta babu wanda take tunani take son tambayar Ina yake kamar d'anta ya nura amma babu bakin magana saidai tazauna tayita kuka Inna Bilkisu na faman rarrashinta da bata magana. Haka baffa ma idan yazo ganinta, Babu abunda takeyi sai kuka wanda kukan ya tabbatar masa da cewa na nadamane takeyi don haka sai yanuna mata tadena damuwa, kamar yanda yafad'a mata ashekarun baya cewa yayafe mata duniya da lahira har yanzu hakanne aransa, Kuma yasa nusaiba ta shirya ranar sukaje tare ya gabatar mata da ita a matsayin matarsa tare da 'yarsa Rashida da har tafara tafiya, sannan yayi mata bayanin duk halin da d'anta Nuraddeen keciki saboda amatsayinta na mahaifiyarsa ta tayashi yimasa addu'a, ranar Yaya hawwa kwana tayi tana kuka azuciyarta tana roqon gafarar ALLAH da kuma yayewa d'anta halin da yake ciki, tana so ta tambayi Rashida matar d'anta amma ba halin haka domin bataga fuska ga kowa ba da zata iya tambaya, Babu mai d'auko mata zancenta ita kuma babu baki balle ta tambaya. Su baffa Ali kuwa tamkar babusu acikin gidan don sau d'aya sukaje dubata, qarama muneera takan d'anje tadubota wani lokacin shima idan basa nan. ••• ••• ••• Rashida kuwa tuni antaka matakin manyan mata don tuni an takammala karatunta na jami'a aqarqashin kulawar Dr da mahaifinsa, tasha karatu sosai fiye da tunanin mai karatu a fannin law wato shari'a, yanayin yanda tamaida hankali sosai ga karatun yasa tasamu nasara acikin kowane mataki data taka, tanada wata baiwa tamusamman da ALLAH yabata wajen jajircewa ga dukkanin abunda tasa agaba wannane yasa take nasara acikin dukkanin al'amurranta, bayan ta kammala Dr yayi sha'awar sama mata aiki Amma sai dady yahana, acewarsa hakan badacewa bane tunda tanada aure kuma dole amartaba igiyar aurenta sai kuma idan kotu za'aje araba auren tunda har yanzu mijinta bai waiwayeta ba, hakan yasa Rashida tace tahaqura duk da tanada sha'awar yin aikin, Amma har yanzu qauna da soyayyar mijinta na kwance azuciyarta da bata tunanin zata iya rayuwa da wani idan bashi ba, tasha alwashin bazata koma wani auren ba koda hakan na nufin tarabu da mijinta kenan har abada domin gaba d'aya tadena sha'awar auren, don haka sai dady yabata kud'ad'e masu tsoka sosai tafara gudanar da business, acewarsa zaifi kyau ta dogara da kanta domin ba'asan halin rayuwa ba, sosai Rashida tamurje tayi kyau tazama 'yar gayu, idan kaganta bazaka tab'a cewa wai Rashidar nance ta qauyen yarimawa matar malan nura ba. Ana haka ranar labari ya iso mata cewa ai su Nuraddeen sun dad'e da kammala karatunsu da sukaje yi tun shekarun baya amma shi yaqi amincewa yadawo, zamowarsa qwarare a fannin daya karanta namasu fama da matsalar neorology da gaba d'aya qasar basu tab'a samun d'aliba mai hazaqa kamar saba yasa qasar tariqesa har tabashi goyon baya d'ari bisa d'ari bisa muradinsa da kuma ra'ayinsa, nan take suka bashi aiki tare da yanka masa albashi mai tsoka, ayanayin da yake aciki lokacin koda bazasu bashi komai ba yafi son ya zauna acan qasar fiye da yadawo, da gwamnatin jahar tasu tanemi tsaurara al_amarin qasar ta d'auko maqudan kud'i tabasu, kasancewar yanda qasar tamu idonta yariga ya bud'e wajen ansan rashawa da cin hanci da Kuma rashin sanin ciwon Kai ya sukayi mui basu koma tada zancenba, baffa yayi kuka da baqincikin abun sosai amma daga baya ya haqura yaci gaba da addu'a tare da yaqini akan ko yaushene zai waiwayesu, Yaya hawwa ma duk da bata um balle u'um aranta tana yimasa addu'a tare da fatar ALLAH yadawo dashi kafin ta ALLAH takasance akanta, wannan labari ya matuqar girgiza Rashida duk da aqasan zuciyarta bata gamsu cewa zaiyi hakan ba sai indai akwai wani abu aqasa da bata sani ba, amma koma meye tayi alqawarin zata zauna zaman jiransa komai daren dad'ewa, kwatsam ranar tana kallon BBC news taga ana fira da wani likita mazaunin qasar malesia amma haifaffen d'an qasar Nigeria ne, qura masa idanuwa tayi saboda ganin yanda yake matuqar kama da habibynta amma azuciyarta sai tace shi wannan yafi habibynta qiba da kuma haske sosai asalima daka kallesa kaga d'an gayu wanda hutu ya zauna masa ajiki, badon ma yanayin haskensa dana mutanen can akwai banbanci ba da bazaka tab'a cewa shi ba d'an qasar bane, tana wannan tunanin ne taji ana tambayarsa sunansa... Qara volume d'in tv tayi had'e da juyowa tana kallon yaransu Dr dake zaune suna wasa wato (walida da sultan) wud'anda aka haifa bayansu shahid da Shahida, walida ita ke bimusu twins sunan ammie ne da taci shiyasa ake kiranta waleeda sai sultan shi kuma sunan dady ne aka saka masa ana kiransa da sultan, tace masu suyi shiru, gabanta ne yafad'i jin da tayi likitan yace Sunana...[2/13, 10:36 PM] Mmn Queen: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___71πŸ’Ž Sunana Nuraddeen Idris Aliyu wanda akafi sani da Dr N.I Aliyu wato qwararren likita a fannin lafiya daya shafi matsalolin qwaqwalwa... Waro idanuwa Rashida tayi had'e da qurawa masa idanuwa cike da farinciki, alokaci d'aya tashiga qwalawasu Fatima kira, aunty, aunty, aunty kufito kuzo kugani ga abban little a tv ana fira dashi, pls aunty kufito kugansa, habiby ne wlh, kufito don ALLAH kada agama firar dashi.+ Tadinga fad'a tana k'walamasu kira, ayanda take kiran nasu yasasu fitowa da sauri ba shiri, musamman Dr. Nura har yana shirin fad'uwa sanadiyar tuntub'en da yayi, ita kuma Fatima daqyar take takawa saboda nauyin da tayi, gashidai girma nadad'a tarar masu amma har lokacin haihuwa bata tsaya masu ba tasamu daqyar ta qaraso ciki, Saida takai jikin tv tasa yatsa adaidai gefen da aka nuno hotonsa tana fad'in uncle wannan shine mijina, shine abban little aunty, Dawowa tayi tariqa Fatima tana cewa, kuzauna aunty kusaurari firar da za'ayi dashi, gaba d'aya ya canza saida nakallesa da kyau da sunan sa daya fad'a sannan zuciyata ta gamsu da cewa shid'inne, taqare maganar had'e da zaunar ita saman kujera, kaima uncle kazauna tafad'a lokacin da take qoqarin zaunawa itama had'e da qura masa ido, wani irin farinciki take jin kanta aciki marar misaltuwa, addu'a tadingayi azuciyarta akan ALLAH yasa yafad'i cewa zai dawo garesu nan kusa bada jimawa ba, Wayarta tajawo ta lalubo lambar umma lokacin tarako dady zai fita riqe da hularsa tana yimasa addu'a, kasancewar wayar na nan falo saman kujera yasa umma tad'auko tare da d'agawa, Saida tayi murmushi sannan tace Rashida kuna lafiya, cikin zumud'i ta amsa mata tana cewa umma ku kunna tv a tashar BBC ana fira da mijina, gaba d'aya tamanta da umma take magana saboda hankalinta gaba d'aya na wajen firar da akeyi da Nuraddeen yana bada amsa, jin da tayi umma tayi tsaki had'e da cewa marar kunya yasa takashe wayar tana girgiza kai yasa tayi saurin toshe baki tana dariyar da da zaran ka kalleta zaka fahimci tsantsar farincikin dake tattare da ita taci gaba da kallonta Dady ne yatambayi umma ko lafiya yaga tayi tsaki, tace kabarni da yarinyarnan marar kunya wai ni take fad'awa na kunna tv tashar BBC ana fira da mijinta inba tsabar rashin ta ido ba sai kace mijin nata yadamu da itane, dariya yayi tare da matsawa ya d'auki remote d'in tv dake kunne yana fad'in, to meye abun kunya aciki, idan bata fad'a maki ba wa kikeso tafad'awa?, ko Qaryane tafad'a shid'in ba mijinta bane? yaqare maganar daidai lokacin da yakamo tashar BBC, juyawa tayi zatabar wajen don batasonma ganinsa gaba d'aya dady yariqo hannunta had'e da cewa don ALLAH tsaya suji ko zasu samu wata hujja acikin firar da akeyi dashi wacce tahanasa dawowa, dama tuni ita umma tafara jin haushinsa tun lokacin da suka tsinci labarin cewa yace bazai dawo qasar ba yafiso yayi zamansa acan, shene abun yaqona mata rai har take ganin kamar yayine don yacutar mata da yarinya data kafe kai da qafa saishi duk da yashafe shekaru masu yawa acan batare daya tab'a tunanin waiwayo taba. Babu yanda ta iya dole suka zauna suna kallon fira. Gaba d'aya b'angaroran biyu sun shagala da irin firar da akeyi dashi har zuwa lokacin da ake tambayarsa dalilin daya hanasa komawa qasarsa yabada gudun mawarsa duk da zamowar gwamnatin qasarce ta d'auki nauyin karatunsa da komai nasa har zuwa lokacin daya kammala, yajima shiru yana tunanin amsar da zai bayar amma daga qarshe yace bayada wani dalili, kawai yafi sha'awar yayi zaunensa acan ne, da aka sake tambayarsa cewa ko yayi hakanne saboda kud'in da can qasar za'a bashi anan qasar baza'a tab'a iya bashi koda makamancinsu bane amma bud'ar bakinsa sai cewa yayi koda qasar bazata biyashi ko sisi ba yafiso ya zauna acan, shi kawai baisan abunda yasa hakanba amma yafi son zama acan har iya qarshen rayuwarsa fiye da yakoma qasarsa. STORY CONTINUES BELOW Tirqashi! Nan take Rashida taji wani dimmmm! akanta tanajin gaba d'aya duniyar tayi mata nauyi saboda maganganun da taji suna fitowa daga bakin wanda zuciyarta tagama bashi aminci da yarda, d'ago kai tayi tana kallon irin yanda yake b'ata rai da nuna damuwarsa qarara afuska adaidai wannan gab'ar wanda farkon fara firar dashi ba haka yake ba duk da akwai sauyesuyen da tagani atattare dashi alokacin na rashin walwala da sakin fuska da ada Bata sanshi daau ba, amma da akazo daidai wannan gab'ar sai taga sauyin yasake lunkuwa atattare dashi, nan take jikinta yayi sanyi tashiga jerowa kanta tambayoyi akan me hakan kalamansa ke nufi?, shin ko yamanta da ita ne?, meye ma'anar zai zauna acan har abada?, Shin a Ina ya ajiye auren nasu?, Idan kuma zancensa ya tabbata meye makomarta?, Meye makomar rayuwarta?, wane hali zata kasance aciki?. Kafin ta lalubo amsar wud'annan tambayoyin sai taji ansake jefo mata wata tambayar da tayi daidai da d'ai daga cikin tambayoyin da tayiwa kanta, shin kamar yanda kafad'a kafi son kazauna acan qasar nahar abada to ya zancen iyalinka da kuma sauran ahalinka?, Sai daya murza goshinsa da yatsun hannuwansa na tsawon daqiqu biyu sannan ya d'ago kansa idanuwansa sunyi jawur yana kallon wanda keyi masa tambayoyin yace iyali? Ahali?, Kamar ya?, Abokin firar nasa yayi d'an murmushi yana jujjuyawa akan kujerar da yake zaune akai sannan yace Ina nufin matarka da 'ya'yanka, iyaye harma da 'yan uwa, bud'ar bakinsa ba abunda yace sai iyaye, 'yan uwa? bansani ba, yaqare maganar cikin yanayin ko inkula. Wata irin razana Rashida tayi had'e da miqewa tana girgiza kai tana ja da baya, tsaye tayi cak lokacin da taji yana cewa mata da 'ya'ya shi bayada ko d'aya bayan ansake jefa masa wata tambayar akansu, durqushewa tayi wajen tare da fashewa da kuka tana fad'in, Kada kayi hakan malamina, iyaye, mata, 'ya'ya, ahali duka kana dasu, idan har zaka manta dani baici kamanta da iyaye da kuma d'anka da muka rabu ina d'auke dashi, safe, rana, dare soyayyarka bata tab'a fita azuciyata ba, idan kuwa zakayimun halacci ban cancanci kamanta dani ba balle har kafurta babuni acikin rayuwarka gaba d'aya, duk iya shekarunnan narayune da igiyoyin aurenka akaina batare da nadamu da qananan shekaruna ba ina dakon jiran dawowarka agaremu, na b'ata duka lokacina wajen baka yardata da kuma soyayyata amma acikin qananan mintuna gaba d'aya ka rosamunsu. Wani irin kuka tasaki tare da rugawa tashige d'akinta tasa makulli, adaidai lokacin little Nuraddeen yadawo daga makaranta, ya isko su Dr da gaba d'aya sun kasa motsawa daga inda suke zaune yayi sallama, ganin hawaye daga idanuwan Fatima da tausayin mamansa yasata kuka yasa ya jefar da jikkarsa abakin qofar shigowa falon yazo ya duqa agabanta yana goge mata hawayen tare da tambayarta meyasata kuka, riqo hannunsa tayi tana shafa kansa had'e da kallon tv tana hango kamarsa acikin fuskar Nuraddeen da ake concluding firar da akeyi dashi, tabbas jini jini ne duk da kamannin little gaba d'aya na mahaifiyarsa ne amma akwai na mahaifinsa kad'an atare dashi, ganin tana kallon tv yasa shima yamaida hankalinsa ga tv, qurawa Nuraddeen idanuwa da ake nuno qaton hotonsa had'e dayin d'an taqaitaccen sharhi akan bayanin da yayi cikin firar da akayi dashi, maido kallonsa yayi ga fatima had'e da cewa, wayeshi mama?, Meya samesa naga ana nunosa kina kuka?, Kasa amsa masa tayi saidai Dr nura yace yamaza yaje yacire uniform d'insa yayi wanka sai yazo yaci abinci. A lokacin little nada shekaru goma sha biyar aduniya kuma yana matakin aji na hud'u a makarantar secondary. Umma kuwa murmushin da yafi kuka ciwo tayi had'e da kallon dady tace kagani, kawai ita kad'aice ke hauka akansa, gaba d'aya ya manta da ita balle abunda ke cikinta, dafari na d'auka yanda suka nuna damuwa akanta koda tabbaci suka samu akan tamutu bazasu manta da itaba, nayi tunanin son da suka nuna mata zaisa susamu tawayar farinciki atatattare dasu don nuna damuwarsu akai, amma sai gashi cikin wannan yanayin da ake ciki yasamu qwarin guiwar barin qasar, naji ba dad'i lokacin da aka sanar damu amma marigayi yalurar dani na fahimci hakan ba laifi bane, sai gashi akaro nabiyu da ranta bata mutuba sun wofantar da ita kuma nasan cewa dole zasusan cewa anganeta daga wajensu balarabe da sauran mutanen gari, hakan da sukayi shima babu kyautawa aciki, sai kuma gashi anxo mana da labarin yace bazai dawo qasar saba alokacin da tagama sa burin cewa zai dawo zuwa wajensa, shima d'in banji dad'i ba araina don Babu uwar dake burin ta zauna tana kallon 'yarta agabanta kuma da sunan tanada aure musamman yanda ake sheganta mata yaro, amma kazauna ka lurar dani cewa ba lallene abunda aka fad'a yatabbata ba, ka hana zuciyata ta gasgata zancen sai gashi yau agabanka, da kunnuwanka ka gani kuma kaji abunda yafad'a da bakinsa, Wai bayada mata da 'ya'ya gaba d'aya saboda rud'in duniya da abun duniya daya d'ebesa, alhaji shin shima wannan ba gaskiya bane?, shima suruttaine it na mutane kada I gasgata?, STORY CONTINUES BELOW Sau d'aya kabani gamsashiyar amsa amatsayina na uwa kuma macce dake d'auke da zuciya irin ta d'an adam da batada qashi shin yakamata raina yab'aci kuma naji zafi akan wud'annan abubuwan ko kuwa?, *ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*πŸ‘πŸ˜­ [2/13, 10:36 PM] Mmn Queen: 🚢‍♀️🚢🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚢🏻‍♂️🚢‍♀️ πŸ’Ž _Bata hana zuwa..._πŸ’Ž _WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπŸ’Ž* _DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*πŸ’‹ _BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*πŸ’ž *DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*πŸ’– *FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️ Page___72πŸ’Ž Shiru Dady yayi gaba d'aya yakasa yin magana saboda yanda jikinsa yayi sanyi akan kalaman da Dr Nuraddeen yayi, yajima zaune yana nazarin maganganunsa dana umma yanaso yagano dalilin da zaisa Dr Nuraddeen yayi hakan, amma duk iya nazarinsa da zurfin tunaninsa kasa samun dalili d'aya yayi da yasa ya aikata hakan, abu d'aya zai iya cewa shine kodai k'wakwalwarsa tasamu matsalane ko kuma rud'in duniya, Amma wane irin abune zaisamu aduniya da sukafi iyayensa da iyalansa da sauran 'yan uwansa aduniya, yatabbata dole dai akwai abunda ba daidai ba acikin wannan al-amarin, wanda qoqarin gyarashi izuwa daidai d'in baqaramar wahala zaiyiba, dole koma meye yazamo d'aya daga cikin wud'anda zasu fahimci rad'ad'in da umma keji aranta fiye da yace zaiyi qoqarin fahimtar da ita kuma awannan karon, domin hakan zai saka mata wani shakku arai tayi tunanin kondon bashi yahaifi Rashida ba tunda ranta yariga da yagama b'aci, Saida ya sauke wata irin gwauruwar ajiyar zuciya sannan ya kashe tv had'e da kallon umma dake sharar qwalla da gefen hannunta yafara qoqarin bata maganada kuma kwantar mata da hankali, A matsayinki na mahaifiya tabbas nasani dole zakiji badad'i bisa abubuwan dake faruwa domin UWA DA 'DA sai ALLAH, ayanayin daya fitar da lafuzzansa babu kyautawa aciki ko kad'an kuma beyi adalci ba, mussamman ga iyayen da suka haifesa, anan yakamata kiyi tunani,abubuwane marasa dad'i kefaruwa akan Rashida kikaji ba dad'i aranki to mekike tunani ga iyayensa da suka haifesa daya nunama duniya baisan komai akansu ba alokacin da akayi masa zancensu, wannan abu mai girmane da akwai buqatar ace anbinciki qwaqwalwarsa da zuciyarsa kafin a amince da kalaman da yayi, anawa tsammanin indai wud'annan maganganu da yayi dagaskenke yakeyi to tabbas yarasa hankalinsa ne, idan kuma da hankalinsa yayisu to rud'in duniya ne kuma zaiyi nadama akai ko yaushene, don haka Ina so kiyima Allah kicire komai aranki uma ki kwantar da hankalinki muje can garin iyayen nasa muji ko meye kefaruwa don asamu maslaha aciki. Maslaha! Maslaha dadynsu? Wace irin maslaha za'aje nema awurin iyayen da suka cutar da 'yar wasu kuma suka nemi gyara rayuwar nasu d'an don ALLAH yamayar masu da aniyarsu?, ai shi ALLAH baya zalinci kuma abunda duk kayi sai anyi maka, saboda haka babu inda zamuje tunda hatta su kansu yanuna baya buqatarsu balle suyi darajar da zasu iyayin wani abu akansa, umma tafad'a cikin b'acin rai da nuna tsantsar baqincikin daya tarar mata azuciya, ganin haka yasa dady ya d'auki hularsa dake gefenta had'e da cewa ALLAH yasawaqe yabar gidan don yasan duk bayanin da zaiyi mata alokacin bazata fahimceshi ba, asalima zai dad'a qaramata wani rad'ad'ine azuciya idan ya matsa mata, duk da shima wani sashe nazuciyarsa nafad'a masa Nuraddeen yayi kuskure mai girma amma acan qasan zuciyarsa yahanasa gasgata hakan domin shi mutumne mai yawan yiwa mutane uzuri. ALLAH sarki rayuwa kenan, shi rashin sani yafi dare duhu, kuma sanin gaibi sai ALLAH duk jarumtar umma da alkunyarta dole zata ajiyesu agefe tayi duk abunda take ganin ya dace akan 'yar tata tilo da take kallo amatsayin sauran farincikin da yarage mata aduniya, saboda rashin sanin ainahin abunda kefaruwa ga Nuraddeen da batayi ba , ba itaba hatta iyayen nasa dake tare da wud'anda suka aikata son ransu akansa basu san abunda kefaruwa ba, Basu san abunda akayi masa ba har yakoma haka balle ita, abune gaibi dabai bayyana agaresu ba, amma komai nisan dare gari zai waye kuma SANNU SANNU bata Hana zuwa...in Sha ALLAH da sannu ALLAH zai bayyana komai kuma yawarware dukkanin wani qullin da basuda masaniya akansa, ya haskake duhun dake gabansu suka kasa ganosa kuma ya yaye masu duk wani shamakin daya zamo silar wanzuwar wannan qaddararriyar matsalar data cutar masu da d'a. STORY CONTINUES BELOW A b'angarensu Rashida kuwa little nawucewa Fatima tanufi d'akinta tana bubbuga mata qofa tana kiran sunanta, tanajin yanda sautin kukanta ke tashi alamun tana jinta amma taqi zuwa tabud'e qofar, tasowa Dr nura yayi yadafa kafad'arta ta juyo ya girgiza mata kai alamun ta qyaleta tace amma Dr tana buqatar wani akusa gareta dazai rarrasheta kuma kasan tana fama da matsalar bp nan kada yazo ya tasar mata, jawota Dr yayi yana fad'in, ki k'yaleta babu abunda zai sameta, ahalin yanzu tafi buqatar kad'aici fiye da komai, mubarta tazubar da hawayen shine zai sama mata sassauci azuciya fiye da ace anhanata fitar dasu, wallahi matar Ina tausayin rayuwar yarinyar nan, tun daga lokacin datayi qoqarin sauya ra'ayin mahaifinta akanta yayi mata abunda takeso ALLAH ke jarabtarta har zuwa wannan lokacin, idan tafita wannan saita shiga waccan kuma duka adalilin rayuwar auren da tayi iqirarin cewa tana so, ubangiji nayi mata hakanne saboda yagwada qarfin imaninta agaresa, kinga kuwa tanada dalilin zubar da hawayenta ko don tasamu qarfin canye jarabawarta, sau da dama kukan da mukeyi akan damuwarmu yana taimaka mana wajen yaqi da ita sab'anin shirunmu dake mummukar zuciya har yasanya mana raunin da zamu iya yaqi da damuwar tamu balle mucanye jarabawowin mu. Suna nan zaune afalo har little yayo wanka yadawo fatima tasa shahida da alokacin tanada shekaru goma sha biyu ta zibo masa abinci, Saida yaci yaqoshi sannan yafara dube dube yana tambayar Fatima ina gwoggonsa wato Rashida, don yasan idan tana nan to tabbas bazataji dawowarsa daga makaranta ba kuma taqi fitowa, kasancewar har lokacin bata fitoba balle taci abincin rana yasa Dr yace yaje ya had'a mata abincin ranarta yakai mata tana d'aki, yayi hakanne don yasan ahalin yanzu shikad'aine zata iya saurara kuma ya kusanceta taji sanyi aranta. Shahida ce tayi saurin riqa masa tray d'in daya d'auko da abinci tabi bayansa dashi, sau kusan uku yana qwanqwasa mata bata bud'e ba kafin can yasoma kiranta, gwaggo, gwaggo kibud'e qofa yaci gaba da fad'a yana dukan qofar, tanajin murayarsa da sauri ta taso tabud'e qofar, qura mata idanuwa yayi ganin yanda sukayi ja had'e da kumburewa kafin yajuyo yakarb'i tray d'in ahannun shahida yana fad'in sannu sister, sannan yashiga daga ciki had'e da sake tura qofar da qafa tarufe, Saida ya ajiye tray d'in a saman gado daga gefe sannan yadawo ta gabanta ya zauna, yanaci gaba da kallonta cikin natsuwa yanason karanto damuwarta, little yarone Mai matuqar natsuwa da sanyin hali, koda yatashi baiyi irin qiriniyar nan ta yara ba saboda rashin son hayaniyarsa, yanada matuqar tsinkaya da kuma fahimtar abubuwa da sauri, musamman ga mahaifiyarsa da akoda yaushe yake jinta har tsakiyar ransa, duk da bawata shaquwa bace sosai tsakaninsa da ita saboda gaba d'aya kulawarsa ta ta'allaqane akansu Dr da kuma su umma da ammie, amma yana jinta aransa tun daga lokacin da yasan cewa itace mahaifiyarsa wacce tahaifesa da cikinta, saboda kulawar da yake samu awajensu Dr baisan cewa basune suka haifesa ba sai lokacin da hajia nafeesa taci masa mutunci tare da zazzagesa shida umma, anan ne yagano cewa yanda yake d'aukar ammie amatsayin kakarsa dady kuma kakansa ashe ba hakan neba, umma daya d'auka amatsayin matar dady kawai ashe itace kakarsa, gwaggo kuma itace 'yarta wato mahaifiyarsa basu Fatima da Dr ba, Cikin natsuwa yace waya b'atawa gwaggona rai haka har ta zubar da hawayen da suka kumbura mani idanuwanta?, d'ago kai tayi ta kallesa sai taji wasu sababbin hawaye sun zubo mata tasake fashewa da wani kukan tare da jawosa tarungumesa, sunjima ahaka kafin tatsaida kukan nata had'e dasa hannu tana share hawayen da suka jiqa mata fuska tana fad'in, kana so kasan wanda yab'atama gwaggonka rai? Da sauri ya d'aga mata kai yana gogen 'yan hawayen da suka zubo masa sanadiyar kukan da yaga tanayi, wani irin nishi mai sanyi tayi sannan tace dashi, abbanka ne little, abbanka shi yasani wannan kukan da naga kanayi. Cikin farinciki yamiqe yana dudduba ko ina cikin d'akin had'e da cewa, abbana yadawo ne gwaggo? A ina abban nawa yake?, yaushe yadawo ne gwaggo amma kikak'i kirana?, Abba, abba.., ya shiga kiransa yana qoqarin fita. Saurin dakatar dashi tayi tana kallonsa had'e da cewa, kadena kiran sunansa don bazai amsa ba, kadena nemansa don bazaka tab'a ganinsa ba kuma kadena tunanin zaka had'u dashi nan kusa kamar yanda nake fad'a maka don bazai dawo ba, STORY CONTINUES BELOW Dawowa yayi ya zauna kusa gareta yana fad'in, Amma gwaggo ke kike bani labarinsa akullum tayanda zuciyata tacika da qaunarsa da kuma son ganinsa da jin muryarsa, ke kika sanya mani tunanin cewa zanga mahaifina nan kusa alokacin da ake shegantani, gaba d'aya mafarkina da kuma muradaina sun ta'allaqane alokacin da zan had'uwa da mahaifina kamar yanda ako yaushe kike fad'amun cewa nan kusane bada jimawa ba amma meyasa yau zaki rusa mani su tahanyar cewa nadena tunanin abubuwan da nake fatan zuwansu gareni akoda yaushe?, duk wanna