Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

SANADIN BIKIN SALLAH COMPLETE

SANADIN BIKIN SALLAH COMPLETE

- - Post a Comment

 SANADIN BIKIN SALLAH COMPLETE‍     SANADEEN BIKIN SALLAH!!🤦‍♀


     Bilyn Abdull ce


NIKA'DAI WRITER ASSO......🤪


Gajeren labari......✍🏿


1⃣


Masallacin cike yake damk'am da mata, matasan 'yan mata dattijai, harma da zawarawa da tsoffi.

     Malam sai kwarara addu'oi yakeyi, kasancewar yaune za'a rufe tafsirin massalacin.

         Tsit masallacin yake, tamkar babu wani mahaluki, sai jefi jefi sukan amsa addu'ar Malam da ameen, saikuma yara dake wasa harma damasu k'aramin kuka (saboda takurasu da akayi akan zaman waje d'aya.


Zaune nake agefe kusada wani gungun matasan 'yammata, ak'alla sunkai su 8, tunda suka shigo atare suke, hakama wajen zama d'aya suka samu, sumadai sukan amsa addu'ar Malam d'in da amin.

    Tsawon mintuna 50 Malam na addu'oin har aka kammala, tareda sallamar kowa.

      Ananne aka fara k'ananun hayaniya, wasuna yunk'urin ficewa daga masallacin.

   Kasancewar muna kusan tsakkiya da 'yammatan nan yasa bamuko motsaba, munajiran nawaje sufara fita dana bakin k'ofa.

     Hankalina yanakan danna wayata, Dan ina k'ok'arin saving d'in tafseer d'in yaune danayi recording d'insa.

     Firar 'yammatance tad'an fara Jan hankalina garesu, saidai kafin naji misuke fad'a harsun fara mik'ewa, kasancewar anragu sosai acikin masallacin.

    Da sauri namik'e nima natake musu baya, Dan inasonji hirartasu.

   Aiko kusan atare muka fito harabar masallacin.1


Tafiya muka farayi.


d'aya acikinsu tarik'e k'ugunta tareda yin k'aramar mik'a tana fad'in wash ALLAHna! Yaukam mun zaunu wlhy, malamin nan kamar bazai sakemuba.

    Dariya mafi yawansu sukayi, wadda ke gefenta tad'an daki bayanta tana kiran ragguwar banza, ALLAH zee mijinki yashiga uku, koda yake jabeer ne.

     Wani wawan tsaki wadda aka kira zee taja tareda ballama mai maganar harara, cikin 6acin rai tace bar had'ani da wawannan mana, ai wlhy *_Sanadeen bikin sallar_* nan nidashi kowa zaikama gabansane.

     Ido suka kwalalo suduka, Hafeeza ta ce, zee anya kinada hankali kuwa? Asamiki biki damutum amma kice zaku rabu *_sanadin bikin sallah?!_*.

      Mtsooww yo ALLAH natuba Hafeeza saime idan mun rabu?, ace wai kana shirin auren mutum amma yagagara maka d'inkin sallah. Jiya yazauna saiwani tsarin banza da wofi yakemin.

       Hanci khadeejah tahuro, cikin 6acin rai ta ce, "wlhy zee ina bayanki, narantse da Al'kaseem yayi gigin k'in yimin d'inkin sallah dayaga jakar uba, Dan tun aranar zamuyi walle-walle, to amma ALLAH yataimakesa jiya yayarsa takawo kayan gidanmu. Amma dukda haka saimun yita, Dan kala 5 nayi dashi amma yakawo 3........

      Takusa da itace mai suna yagana takatseta da fad'in dak'yau khadeejarmu kina wuta wlhy, ai mazannan wutar karane Saida iji narantse.

    Maryam ta ce, hummm wlhy kudai kubi asannu, kada kuyi nadama a *_Sanadin bikin sallah_*.

       Wata uwar harara saudah ta watsa ma Maryam, to ustazu munji, kedama aii Ibraheem yasaba rainamiki hankali damaidaki baya cikin k'awaye, shekara biyu dakai kud'in aurenki amma ko sark'ar sallah baita6a siya mikiba.

        Baki Maryam ta ta6e tana fad'in aibadan wannan nakeson saba, inasonsane domin ALLAH, *_Sanadin bikin sallah_* bazan haddasa fitinar dazan dawo daga baya ina nadamaba.

     Wata shewa Bilkeesu tayi tanawani fari da idanu datafiyar k'asaita, mudai mun wuce wajan, Dan kowa yasan my Mahfouz akwati guda yamin na kayan sallah, har lallen kunshi Saida yasaka aciki.

      Wani uban tsaki Ameena tayi tareda fisgar hannun Taufeek'a tana fad'in kankudai akeji marasa aikinyi kawai.

     Gaba d'aya suka shek'e da dariya tareda tafawa suna fad'in jealousy ooooo!!!!!.

        Cikin hanzari Taufik'a takwace hannu ta daga na Ameena tana fad'in uban miye abin jealous agurinku? Banzaye kawai, aii maiyi baya fad'a, kowa yabari sai ranar sallar mana, aiza'a tantance *_WAYE WANE!!?._*

         HHHHHHH khadeeja  tasa dariya, takoma gabansu tana wani jijjiga kai, gskyarki Taufee, shiyyasa nake sonki, Dan kanki akwai kawo wuta wlhy, wannanma shawarace.

  *_sanadin bikin sallah_* za'asan kowa shi waye?.

       Dariya suka shek'e da ita suduka.

          Hafeeza tace kai dukma Ku tsaya, yaushene zamuje gidan mai k'unshin?.

         Bamunyi da'ita alhamis ba cewar Bilkeesu.

      Eh hakanefa zee tafad'a tana dafa kafad'ar Bilkeesu, tace to yau suwaye za'a farama kitson?.

      Da sauri Maryam tace kuma kunsan nice, daga nan sai yagana.

       Ameena tace wlhy yagana da maryam muna fukaine, kutunafa barama sune farkon kitso.

    ALLAH tsine uwar mai k'arya cewar yagana cikin masifarta.

       Saudah ta ce, ''kai yagana, nifa matsalata dake saurin fushi wlhy, daga fad'ar haka miye abin tada jijiyar wuya?.

     Bansaniba cewar yagana afusace.

           Zee Ce tashiga tsakani dantasan ayanzu saisuyi sama.


Kunga ya isa haka mana, yanzu kumuje rana na k'arayifa, kuma akwai meeting yau Dan bamu tsara da'ina da ina zamujeba.

       Hakanefa!!! Suka fad'a arazane kowa nak'ara saurinsa.


Nace hummmm🤔.

    Cakwakiya.2⃣


      Shara takeyi amma hankalinta nakan hirarsu tad'azu suda k'awayensu bayan sun taso tafseer.

     Itace mai zak'alk'alewa akan meyi baya fad'a, gashi kuma tunaninta yana hasko mata itace zataji kunya.

    Ta sauke ajiyar zuciya tareda Jan kujerar gefenta ta zauna, hannu biyu tasa ta tallafe kumatu domin samun damar yin dogon tunani, d'inkin sallarta kala biyune kawai, kuma duk atanfofi, mama tamata d'aya Anty zuhrah tamata d'aya, nawajen mamama yanaga tela Dan tarasa cikon 1000 dazata kaimasa ta kar6o.

    Sarai tasan waye garzali akan rashin M, koya kuke dashi bazai baka d'inkiba Saida kud'imsa ciff. Wata ajiyar zuciya takuma saukewa Dan tuna aii bama matsalar kenanba, akwai ta takalmi, harma da jaka, sark'a da 'yankunne. A6angaren mayafi tawuce wajen, dan shekaran jiya ta d'auki agwagwar🦆 babansu d'aya tasayar tabiya hajiya mai kayan koli tasayo mata, babu Wanda yasan tasaci agwagwar, kuma yawansu yahana mamanta ganewa bare baba dabaya zaman gidanma sosai.........

     Taufee...! Wani lafiyarki kuwa?.

    Muryar mamanta tadaki kunnenta, cikin hanzari tamik'e tana fad'in e...em...em mama mikikace?.

        Ajiyar zuciya mama tasauke, cikim sanyinta ta ce, "taufee mike damunkine? tunda kuka dawo tafseer d'in nan bakida sukuni.

       Bakomai mama. Wlhy azuminne yaked'an k'olani, saikuma wa'azin yau yaratsani sosai.

       To kiyi hanzarin kammala sharar, rana tayi, maganar tafseer kuwa aiki dashi zakiyi ba tunaniba.

     To mama ngd.

Mama batace komaiba takoma d'aki, itama cikin sanyin jiki tacigaba da shararta. Amma can k'asan zuciyarta tana kissima inda zata samu kud'i kafin gobe.+


Nace hummm sanadin bikin sallah🤦‍♀.

*_GIDAN KITSO_*


   Yagana zaune gaban mai k'itso anata yarfa mata twistin wanda ake k'ara gashin doki (attachment), Maryam nazaune kusada ita tana chart awayarta, sai faman murmushi takeyi.

    Zungurinta yagana tayi, k! Wai lfyarki kuwa?.


d'agowa Maryam tayi tana dariya, bakoma yagana, kawaidai muna fira da Anty salma ne, wai rigima sukeyi itada Abban Ahmad akan d'inkin sallarta.

   Nifa lamarinnan yana bani mamaki, shinwai miye d'inkin sallah ne?, nagafa bikin rana d'ayane tak.

     Dariya mai kitson tayi, ta ce, "aiko kayan sallah wani abine, kana gani anata gayu kai bandakai, wlhy danama baban Fatee alk'awarin nadaina kitson Attachment, amma tunda yak'imin kayan sallah sainayi, danyafi kawo kud'i.......

        Rabi'a dakecan gefe tana tazar kai (itama kitson tazo) ta ce, " amma haramunne, ALLAH yatsinema maiyi da Wanda akemawa.

     Dariya su yagana damai kitso suka saka. Yagana ta ce, ''yo ALLAH natuba aii wataran bazamuyiba, kuma kafin mu mutu zamu tuba, idan ba sallahba aibayi kakeyiba, dagafa shekara sai shekara. Wlhy nifa har farce zan k'ara,💅🏻 wasuma suna abinda yafi haka, kuma ALLAH ya yafe musu.

    (Wa'iyazubillah, kunjifa dak'ik'anci irinna d'an adam😕)


     Tab d'i Jan, lallai rayuwa ta lalace, 'yammata aii babu wani bawa dazaima ALLAH wayau. Ina mamakin masu sa6ama ALLAH da gangan sufake da *_SANADEEN bikin sallah_*.

   Bikin sallah yardajjen bikine a addinin mu, amma Bahaka akace mugudanar dashiba.......

    K! Malama munji, cewar Maryam tana yamutse fuska, kema kifarama kanki wa'azin mana kafin ki mana, nifa bancika son shishshigaba wlhy mtsowww taja tsaki.

     Yagana ta ta6e Baki tana fad'in karki 6ata ranki 'yar uwa, cusa Kaine kawai babu kwarjini, mudai mun wuce da ajin mutum.

    Hhhhhhh Rabi'a tayi dariyar rainin wayau tana mik'ewa tsaye, kallon raini tamusu tareda fad'in ina romon yake? Ballantana dad'insa, ina kuka kai balle ayi tunanin hangoku yara?.

     Gidan uwarki.. Cewar yagana tana fusge kanta daga mai kitso.

    Da sauri mai kitso tace kunga kada kumin fad'a anan dallah malamai, kubari saikun fita saiku kashe kanku babu ruwana.

    Komawa yagana tayi ta zauna tana huci, tace banza kawai zamu had'une.

     Dariya kawai Rabi'a tayi taja gefe tazauna abinta, hankalinta kwance, dantasan ko danbe sukayi da yagana babu abinda zata d'auka ajikinta.

  Dukda tasan wannan abun dabiyune, Dan k'awayen k'anwartane Bilkeesu dasuke uba d'aya.


Ranardai mai kitso Saida tama yagana, Maryam, Hafeeza, zee, da Ameena kitso.

      Saudah, Taufik'a, khadeejah, Bilkeesu sai gogobe za'a musu.


Washe gari tunda sassafe suka Isa kuwa, Saudah aka faramawa, sai Taufeeqa...

    Da yake tanada saurin kitson zuwa 2 duk an gama musu kuwa.

   Daganan sai gidan k'unshi, Wanda suka Tatar damk'am da jama'a, sauk'insuma sun kama layi tuni. Yanzu hakama zee akemawa, angamawa yagana da Ameena.

            Gefe sukaja suna hirarsu, saidai hankalin Taufee gabad'aya yanakan wata mata wadda kallo d'aya zaka mata kasan akwai rufin asirin ALLAH, tunda suka shigo idon Taufee yasauka kan kud'i 'yan dubu-dubu dasuka lek'i kad'an daga jakkar matar.

   Hummm Ashe ba ita kad'aiba, itama Hafeeza matsalarsu d'aya da Taufee, har garama Taufee tanada gyale, itakam Hafeeza daga d'inki kala d'aya batada komai, wannan yasa taje ta lodo bashi gidan wata mata tun azumi na 12, takai d'unkuna tuni kuma duk an d'inka. Sunyi Ajanda da tela akan bayan sallah zata bashi kanta yamora, Dan afad'arsa ya (tuba) cikin azumi, sai bayan sallah kuma.

   Baisan hafeeza akwali tasakashiba.

    Itakuma batasan tela yafita barikiba, Dan yashirya mata koda tayi k'ok'arin zillewa.

    To yanzudai matsalarta ta gyalene da takalma, sai kuma kud'in matar wajen dubu 28 dake kanta.


Nace Hummm sanadin bikin sallah🤦‍♀.


Can kunshi yazo kan Taufee. Tatashi taje tazauna aka fara da hannu har aka kammala, kan k'afarta aka koma, wannan yabata damar fara jan 'yar d'iyar matar da wasa, (to kunsan ance maid'a wawa), tuni mata tasaki jiki da Taufee.

    Ana k'unshi suna hira, can dabara tafad'oma tad'auki yarinyar tana ta6a siket d'inta, kai kai taufee tafad'a tana kallon matar.

   Matar tace yadai?.

Taufee tad'aga siket d'in yarinyar tana nunamata pampas d'in daya cika da fitsari, Anty kicire mata kada ya dameta.

     Gskyarki wlhy cewar matar tana amsar yarinyar, tamik'e tana cewa bara nacire mata kafin tafaramin k'ananun kuka.

    Hakane cewar Taufeeqa  tana baza hijjabinta kamar zata gyarashi, anan tazare kud'in duka, tasak'e cikin bra d'inta.

    Kafin matar tadawo angamawa taufeeqa, khadeejah tazauna aka fara mata.

       Sanin tsiyar datayi yasata cewa sauran 'yan uwanta zata gida, Dan bata kar6o d'inkintaba gidan Anty Zuhrah, itada Maryam da yagana da saudah suka tafi dansuma duk sunada uzuri, gudun kar a zargeta taje taima matar sallamar sannan suka fita.


( kai jama'a, kungafa sanadin bikin sallah🤦‍♀ )3⃣


   

     Har aka kammalama sauran suka baro gidan k'unshi matarnan batasan an yashetaba.

     Saida suka tafi dakusan 1h... Sannan akamata, tazo zaro kud'i sukace d'aukarni inda kika ajiye.

      Innalillhi take fad'a tana k'ara zazzage jakar. Mai k'unshi tace lfy?.

     Matar cikin rikuce ta ce, "kud'ina naira dubu 25 aka kwashe. Naga takaina ni wasila, dama daya nasamesu, wadda tafini so kuma takwashe, kuka sosai tafara dakiran shiga uku.

    Nanfa mai k'unshi ta kurma ashar tana fad'in ayi zazzage.

     Da sauri wata tace yo laure wane zazzage, bayan mutin yafi goma Wanda suka bar gidannan, ALLAH kad'ai kuma yasan 6arawon ciki.

      Wata dakecan gefe tanata danna wayarta tun d'azun bata shiga harkar kowaba agidan, tad'ago tana kallonsu, guntun murmushi tayi tareda fad'in ki binciki wadda takema 'yarki wasa d'azun.

    Da sauri matar tace wai mai Jan hijjabi?.

    Yes ita

Dan naga sanda tarufe jakkarki da hijjabinta.

    Kanjakar ubannan, aiko ko ubanwaye ubanta agarinnan saita biyani kud'ina. Fuuu taja jaka tafice tana fad'in laure zan aiko miki kud'in kunshinki.

       Fitar matar yajawo k'ananun maganganu.+


Wata tace aii ana ta6argaza *_sanadin bikin sallah_* wlhy wasu har jikinsu suke badawa Dan Asara, haba jama'a koma azumin ba'a kammalaba, amma munfara rusa ayyukanmu.

  

Watace, hummm ai duk Wanda yace burinsa birge wasu, tofa shi rayuwarsa rugurguzazzace.


Wata tace, nifa yau wata makwafciyarmu aurenta takashe saboda mijin yace bashida kud'in dazai bata tayi cin-cin d'in sallah.


Wata tace ai kad'anma kenan wlhy Wani aiki sai ranar sallah, zakiga tsagwaron iskanci wajen 'yanmata da samari.


Hakadai aikaita cecekuce, kowa nafad'in albarkacin bakinsa..

+++++++++

      Bayan fitar su taufee kuwa, suna fita taufee tamusu sallama akan gidan Anty zuhrah zataje.

    Suma kowa gabanta takama.

    Daganan babu inda Taufeeqa ta zarce sai kasuwa, duk abinda take buk'ata tasayoma kanta, tas takare 25k akasuwa.

     Sanda tadawo gida mamanta tana barci, wannan yabata damar 6oye kayanta danufin anjima idan salis saurayinta yazo tad'akko tace shiyya kawo mata.


Nace humm.


Ameena zaune gaban babansu sai zum6ura baki takeyi tana jujjuya k'aton hijjabai guda biyu da babansu yasaya mata itada k'anwarta Badariyya.

    Badariyya kam sai washe baki take tana kwarara godiya da nuna murnarta.

    Baban ya sallamesu kowa da ledan kayansa ahannu.

    Suna shiga d'aki Ameena tajefa tata agado tana k'unk'uni.

   Kallonta Badar tayi cikin mamaki, tace haba Yaya Ameena, kamar bakiyi farinciki da d'awauniyar da baba yayi damuba? Shida ummafa kala bibbiyu sukai mana, kala hudu kenan, gashi yaukuma yasayo mana takalma da sark'a harda hijjabai.......

    Harar data watsa mata tasata yin shiru, cikin Jan tsaki tace amma shine za'awani suyo mana wannan burma-burman hijjaban! Haba sallarma hijjabi zamusa? Yaza'ayi kwalliyarka taburge mutane?.. 

    Kallon mamaki sosai Badar take mata, tace yo Yaya Ameena *_Sanadin bikin sallah_* saimu kasa biyayya ga dokar ALLAH?.

      aganinki d'ame jiki da duk shigar damuka kadama shine nuna murnar bikin sallah?.

    Aiko aganina wannan bahagon tunanine, suttura aii mutuncin d'iya mace, shiyyasafa ake samun hauhawar matsalar zinace zinace da fyad'e *_sanadin bikin sallah_*, Dan mafi yawan 'yan mata kwalliyar burge wasu sukeyi, (agarin burge wasu kuma suke rusa Kansu ba) wlhy wani abunma mumuke *_jawoma kammushi_*, aita zuba shigar fitsara ana fakewa da bikin sallah........

    K! Dallah dakatamin, kinwani cikani da magana mtsoww.

    Yaya Ameena ba haka bane, inaso kifahimceni ne........

   Tobazan fahimtarba, dallah fitarmin anan, bak'auyar banza kawai, kedama aii kullum kanki a tukunya yake, mudai babu fashi kwalliya saimunyi ta kece raini.

    Hummmm ALLAH yarabaku da *girbar abinda kuka shuka kuwa*, cewar Badar tana fita, tareda bak'incikin k'in fahimtarta da yayartata yayi.

       Ameena kam tsaki tayi ta d'auki hijjabin ta tura cikin kayansu marasa amfani, daman tasan babu inda zasu samu Matsala sai akan gyale, tuni kuma tayima kanta magani tasaya a 6oye ta Adana sai ranar sallah....


Nace hummmmm.


6angaren Bilkeesu dai komai dai-dai, Dan ita Mahfouz yagama had'ata, rana kawai take jira.


To itamadai saudah haka, babarta tatanar musu komai Na sallah, Dan mamanta irin masu son komai afara gani ajikin 'ya'yansune, koda rigima tasakasu ayayi, acewarta *_(ranar biyan buk'ata! rai ba'abakin  komai yakeba)_*


Itama khadeeja komai dai-dai, yayansu yamusu komai, saidai batada sark'a, kuma tun ajiya taje gidan wata makwafciyarsu amarya ta aro sark'arta mai k'yau, irin masu kamar zinari d'innan, (Wanda akecema 6arayin goal) to itama rana kawai take jira.


Yagana kam sai a Slowly, amma saurayinta ya aiko mata da kayan sallah babanta yahana a kar6a, daga baya takirasa tace yakawo mata, zata 6oye, bazata bari baban yaganiba.

   To sunyi akan yau da daddare zai dawo mata dasu.


Maryam ma komanta dai-dai Dan babanta akwai k'ok'ari, kuma mamarta tasaya musu komai.


Zee dai hankalinta atashe yake, Dan haka ta tadama saurayinta hankali, akan inbabu kayan sallah tofa kowa Yakama gabansa.

      Hankalinsa yatashi, Dan bashida k'arfi sosai, ga d'inkin sallah k'annensa Na kansa, Dan babansu yadad'e da rasuwa, nauyin gidan duk akansa yake.

   Yarasa inda zaisa Kansa yaji dad'i, gashi yana masifar son zee, dole yasaida wayarsa ta hannu, yahad'a da satar kud'in ogansa yamata sayayya harda d'inkin daya rok'i abokinsa telane yaymasa aranar da daddare, washe gari aka kai mata, Daren sallah kenan.

   To itama rana kawai take tsumaye.


Hafeeza madai aganinta da sauk'i, Dan tahangoma kanta mafitar Inda zata samu kud'i a sauk'ake.

     To bara mucigaba dabinta Dan muju.


To yanzudai 'yan matannan komai agaresu yayi ready, rana kawai suke jira..   

    Saimu cigaba dabinsu domin muga ya bikin sallah zai gudana agaresu?.


Shin birgewar dasuka shirya yi zatayi tasiri?.


Mizai biyo baya garesu?, Dan dayawansu basu shirya bikin sallahr yanda shari'a tabasu damaba, ga rigima dasuka d'aurama Kansu *_sanadin bikin sallah_* rana d'aya tak.


To bara muga, wace riba zasu samo?.🤔🤪✋.


👇🏻


Matar da taufeeqa ta d'aukarma kud'i kam, tanafita daga gidan lalle tayi gamo da yaronta, mijinta ya aikoshi danya kirata.

      Cikin masifa ta ce, Abdul yaushe baban naku yadawo? banace daya dawo kakiraniba?.

      Mama yanzunnan yadawofa, kuma yana shigowa yashiga d'aki, saikuma yafito yace kina INA?, shine nace kinje gidan gwaggo. (Aihaka kikace nafad'a masa idan yatambaya ko).

    Kanta tagyad'a masa, Dan maganarma takasa, taja hannunsa suka tafi hankalinta amatuk'ar tashe.

    Suna shiga gidan ta iskeshi afalo zaune sai hura hanci yakeyi.

   A sanyaye tak'ara kusadashi tana fad'in abbansu Abdul sannu.

    Mik'ewa yayi batareda ya amsataba, yakalli Abdul ya ce, "jekayi wasa Abdurrahaman.

   To Abba, yaron yafad'a yana fita.

       Shikuma yakuma d'aure fuska, hajarah ina kud'ina?.

   Idanu tazaro tana fad'in Abban Abdul wane kud'i kuma?.

    Kinfini Sani aii, yayi maganar afusace.

    Dukda gabanta Na dukan uku uku hakan bai hanata fashemasa da kukaba tana fad'in nizaka d'orama sata Kameel?.

       Wata uwar harara yawatsa mata, yanunata da d'anyatsa, hajarah wlhy nabaki kwana uku duk abinda kikayi da kud'ina ki kawominsu, nakula ko kad'an bakida godiyar ALLAH, dagake har yarannan babu Wanda ban k'ok'arta nama d'inkin sallahba, nasaya muku takalma, amma saboda dak'ik'ancinki zakice abincin sallah saida drink's da Doughnut zakiyi?.

    Danna cemiki banida k'arfin hakan shine zaki biyo tabaya ki d'aukamin kud'i? Kinsan kud'ina miye? to wlhy kiyi gaggawar fiddomin kud'ina kafin kwana 3, inba hakaba narantse saikinyi nadama a *_Sanadin bikin sallah_* yanagama fad'aya yashuri takalminsa yafita.


Kuka tarushe dashi tana fad'in ta shiga uku ita hajarah, tad'auki kud'inne atunaninta bazai ganeba, saboda sunada yawa, itakuma gashi duktagama bazama makwafta zatayi Doughnut da cin-cin, harda gayyatar budurwar makwaftansu ta tayata aiki, wannan yasa tatafi dakud'in gidan k'unshi, anufinta da angama mata tashiga kasuwa.

    Idan yazo ya tambayeta tacemasa adashinta takwasa, Dan bazata yarda hafsa makwafciyarta tafitaba, Dan ita tun kwana hud'u daya wuce mijinta yahad'o mata komai Na buk'ata, yanzu hakama k'amshin soye-soyene keta fitowa daga gidanta.

    Tad'ora hannu aka tana kiran nashiga uku ni hajarah, asara goma da ashirin🤦‍♀.

     Wlhy yarinyarnan kowaye ubanta saita bani kud'ina.

    Gashi batasan gidansuba, dasauri tad'auki ummi tagoya danufin komawa ta tambayo Laure mai k'umshi.

    Saidai tana fitowa taga Abban Abdul a k'ofar gida, dole takoma Dan babu damar fita yanzu.

Nace Hummm, (akan birge wasu😒).Kukasance dani danjin yadda abubuwa zasu kaya.


Asoya kaji lafiya, kada kuma amanta dani dai🤪👌🏼4⃣

         Har k'arfe 8 na dare kunnuwansu Hafeeza abud'e yake, azuciyarsu kuma suna addu'a ALLAH yasa aga wata yau.

     Dayawansu suna taya iyayensu aikin sallah ne, Dan haka kowa ya kasance agida a wannan lokacin.

           Jiranne ya ishi zee Dan haka tad'auki wayarta ta bud'e data, sakwanni suka fara shigowa, tambaya tafarayi a group's ko anga wata?.

     Wata tace eh angansa, amma sarkin musulmai bai sanarba tukun, k'ila sai k'arfe 9.

    Godiya zee tayi tasauka gabad'a danjin kiranda ummanta ke kwala mata, dama aiki sukeyi tace mata tana zuwa, shine daganan tazauna charts.


09:pm.

      K'arfe tara sarkin musulmai yasanar da ganin wata, Ameena ce tafara kiran Maryam tasanar mata, sukad'au shewa awa tareda fad'in *_K'ureeeee wanka!!!!._* lol

    

🤣sunfa bani dariya.


Daganan sukaita kiran juna, har kowa yasani acikinsu.

*_Washe Gare_*


*YAU TAKE SALLAH*😂


         9:30am

Gaba d'ayan 'yan matan suka hallara gidansu Ameena, Dan nannane kan hanya, Badar takalli Ameena dake neman hijjabinta tayi 'yar dariya.

    Cikin sigar tsokana ta ce, "ya Ameena kekam mizakiyi da hijjab ranar sallah? Sakashifa zai hana wankanki ya burge mutane.

    Harara ameena ta watsa mata, tace nakulafa Badar kin mugun rainani, to dakike fad'ar haka an gaya miki sawazanyi?, zan sakane kawai naje idi, Dan hijjab amfaninsa kawai Edi aranar sallah.+


Murmushi Badar takumayi, tace ALLAH yabaki hak'uri, ni wasama nake miki.

     Tsaki Ameena tayi batareda tace mata uffanba.

      Duk abinda ke faruwa tsakanin Ameena da Badar su Bilkeesu Na jinsu, amma basu saka musu bakiba, Dan suna Shankar Badar, kokad'an bata wani sake musu fuska, kuma sunsan Badar d'in tafisu komai, k'yau iya kwalliya da jama'a.

     Badar sa'arsune, Dan bawani girmarta Ameenar tayi sosaiba, kwana 47 kawai Ameena tabata, badar d'iyar kishiyar Babar Ameenace, mamanta tarasu wajen haihuwarta, wannan yasa Maman Ameena ta shayar dasu itada Ameena, Dan sunyi zaman lfy sosai.

        duk da Ameena bawani Girman badar d'in tayiba, hakan bai hana Badar girmamataba tareda kiranta yaya.

        Wannan yasa Ameena kejin kanta wani on top.


Suna gama shiryawa sukatafi idi harda Badar, dukda dai nakula basuso had'a tafiyar da itaba, amma babu yanda suka iya dan Maman Ameena bazata baribama.


*Alhmdllh* ansakko idi lfy, saimuce ALLAH ya maimaita mana.

       Ana sakkowa idi duk gida suka dawo, agidan su Saudah suka yada zango yanzu.

    Bayan sun gaida Maman Saudah suka shige cikin wani d'aki dasu saudah ke kwana itada k'anneneta.

          Badar kam zamanta tayi awaje, wajen ummansu Saudah.


Meeting sukayi Na tsara duk inda zasuje ayau, dakuma abincin dasukasa wata makwafciyarsu amarya ta shirya musu Dan zuwa park, daganan saudah takawo musu abinci da cin-cin harda zo6o mai sanyi, sunci kowa yay d'if, k'in kiran Badar sukayi, itakam ko a jikinta tanata danna wayarta, (dama kosun mata tayima baci zatayiba).

    Sun shafe kusan 1hr... Sannan sukafito, daganan kowa hanyar gidansu yakama akan saisun had'u k'arfe biyu.5⃣


*_GIDAN matar da taufeeqa ta satarma kud'i._*


        Zaume take tarabga uban tagumi, abin duniya ya isheta, tunranar Abban Abdul yahanata fita balle ta binciko gidansu Taufeeqa.

    Babban tashin hankalintama shine ko naman sallah ba'a kawo gidanba.

   Yaukuma dawuri Abban Abdul yayma Abdul da ummi wanka da Kansa ya shiryasu cikin sababbin kayansu Na sallah, ya tattarasu suka tafi idi, har yanzu basu dawoba, gashi ya kulleta tabaya da k'aton kwad'o.

     Wasu hawayene masu zafi suka zubo mata, batadamu data shareba, saima wasu dake rige-rigen fitowa, itakam tarasa mafita, an6ata goma biyar bata gyaruba, tace nashiga uku ni hajarah, kardai Kameel yace bana bazamuyi abincin sallah ba? Aikam daya gama kasheni wlhy.............

         Jitai ance ai inbaki mutuba zaki dawwama a makarantar nadama, kuma inamai tuna miki maganar kud'ina Dan saura kawana biyu daga ukun dana Baki.

    Yanagama fad'a yashige d'aki, mintuna kad'an yafito d'aukeda madaidaiciyar jakka, wadda yazubo kayansu Abdul aciki.

     Ko kallon hajarah dake surutai da kuka baiyiba yafice abinsa, a yanzukam bai rufetaba.

   Yana fita yaro nayin sallama, baijira amsaba ya danno kai cikin gidan, k'aton tiren dake kansa yasauke ahankali, yana fad'in gashi inji Maman Ilham (hafsa makwafciyarta).

     Wani damm gabanta yafad'i, ta danne zuciyarta tace kace mata ngd.

    Yaro yace to, yafice abinsa.

     Yana fita tajawo tiren tafara bud'e kwanukan, kwanon farko Na babbar samira fankasune daya samu kyakykyawar suya, d'ayan kuma wainace tashinkafa shar da ita (masa) sai d'yar miyar alayyahu dataji isashshen naman rago, sai kamshin kori takeyi, saikuma wata babbar langa da'aka zuba farar shinkafa, d'ankwanon kusada ita kam miyace ta naman kaji, filet arufe mai cikeda coslow da akaima yankan nutsuwa, an zuba bama asamansa.

      Saikuma wani k'aramin kwano da'aka ciko da cin-cin doughnut & etc, ansaka gwangwanin maltina biyu na fanta biyu, dakuma babbar robar swan dake cikeda zo6o......

    Kawai jinai hajarah takwala k'arar kuka, tana fad'in kameel ka cuceni, duba kaga wadda bata kaini komaibama tahad'a wannan shagalin awajen *_bikin sallah_*, wlhy kameel baka isa *_Sanadin bikin sallah_* kasa 'yan anguwa su rainaniba, narantse baka isaba, yau koda sama da k'asa zasu had'e saika mana cefane gove nayi abincin sallah, (dolene Na nunama shegiyarnan bata isaba).

    Gyalenta tad'auka tafita tamkar wata mahaukaciya, bata dire ko inaba sai gidan k'awarta Aysha.

    Canma haka ta tadda Aysha baja-baja cikin hidimar bikin sallah, wannan yak'ara tada mata da hankali.

    Dak'yar Aysha ta'iya sakin aikinta tazo suka gaisa da hajarah, sukaima juna barka da sallah.

    Hajarah tace Aysha Dan ALLAH alfarma Nazo nema wajenki.

      To ALLAH yasa inada abinsa zan fiddaki kunya, Cewar Aysha.

    Hajarah tace ameen.

   Tad'anyi Jimm sannan tace Aysha kud'i Nazo nema rance Dan ALLAH.

     itama Aysha shiru tad'anyi, zuwacan kuma tace bar nawa?.

       Cikin zumud'i hajarah tace 40k..

     To, ke kam hajarah mizaki dak'ud'i masu yawa haka?.

       Wlhy Aysha kameel ne yakeso kafin aturo masa wasu kud'i.

      To shikenan, ainasan Abban Abdul babu wasa, ALLAHma yasa yanzu abokan Abban deeni dasukazo sukaci abinci sukaban 30k, bara naduba na hannuna idan sumkai 10.

      To, hajarah tafad'a cikeda farinciki.

    Babu dad'ewa Aysha tadawo da kud'i 40k cif, tabama hajarah, itakuma taimata godiya tareda sallama, Aysha ta tsayar da ita tana fad'in inazuwa.

    Bak'ar leda tabama hajarah sannan tarakota har gate .


STORY CONTINUES BELOW

Hajarah jitake kamar taita rawa Dan murna, kaitsaye kasuwa tatafi, siyayya tayo bata wasaba, (sai yanzu taji zuciyarta tayi wasai).


Nace hummm.


Tunda tadawo gidan tafara hidimar aiki, dandanan tagyara kajinta, tajik'a shinkafa, takwa6a fulawa dazatai abubuwa dashi.

     Ranar wuni tayi aiki, jefi-jefin yara 'yan yawan sallah kan shigo gidan, wasu tabasu barka da sallah, wasukam bata basu, har yamma lik'is Abban Abdul bai dawo gidanba bare su Abdul, wannan yabata damar gama aikinta tsaf, sauran kuma saida safe idan ALLAH ya kaimu.

      Koda Abban Abdul yadawo baiga wata alamar anyi aikiba, Dan hajarah komai da tsari tayishi tagyara gidan tsaf kamar ba'ayi komaiba, saidai tabasa mamaki, Dan cikin walwalarta ya isketa, amma baice da ita kanzilba, yay himarsa ya kwanta.

    Itama bata tambayesa yaranba, dantasan gidansu yakaisu.


*_02:30pm_*


Woooow!!.....😨nafad'a lokacin da idanuna suka sauka kan gungun matasan 'yan matan dasuka d'auki wanka Na kece raini, dolene ka kallesu ka kuma kallo, Dan babu k'arya sun d'au wanka iya wanka.

     Duk inda suka gitta sai an bisu da kallon birgewa.

    Tuni samari matasa suka fara fad'awa tarkonsu, sukam sai k'ara hura hanci suke da d'age kai sama suna basarwa. Lol🤣


Bawasu bane 'yanmatannan illah *_Taufeeqa, Khadeejah, zee, Hafeeza, Saudat, Maryam, yagana, Ameena, Bilkeesu._* sai Badar da kebinsu tamkar dole, Dan Maman Ameena ce tace dolene duk inda zasuje saida ita, inba hakaba Ameena bazata bisuba.

   Badan sun soba Badar tabisu, tana sanye cikin less irin Na Ameena da akaima d'inkin Riga da siket, amma dai ita da *_Hijjabinta_* iya gwuywa tasaka, tayi k'yau wlhy itama, Dan zan iya cemukuma ni wankanta yafi d'aukar hankalina.

    Mutananku kam aii kowacce da siririn gyale, wasuma akafad'a kawai suka d'ora, wasukam awuya, ga uban Google's🕶👓 duksun aza, dolekam duk wani gaye yagansu yayi Respecting nasu, Dan sund'au wanka iya wanka🤓.

    Ga wani taku dasukeyi d'ai-d'ai, kaikace bazasu taka k'asarba kosuna tsoron jimata ciwo.

     Abakin titi sukaja layi Dan duba abin hawa.

    Bilkisu taja gilas d'inta k'asan hanci tana kallonsu, cikin yauk'in magana tace guys mufa tare mota mai aji.

    yes, gskyarki billy, cewar Hafeeza tana yatsine baki.

   Daganan sukad'an fara firarsu k'asa-k'asa, itadai Badar tana gefe abinta, idanma baka saniba bazakace tare sukeba.

     Sund'anyi tsayuwar 24mnt suna jiran mota, dukda kuma titin akwai motoci sunata kara kaina, amma kosun tsaya saisu Maryam sufara yataine bakuna, wai motar bata musuba, suna nandai saiga wata taxi sabuwa dabatasha wahalaba.

    Wannankam da alama tamusu, dantana tsayawa Taufeeqa da Yagana suka k'arasa wajensa, yace 'yammata ina zuwa?.

    Cikin yatsine fuska yagana tace jabi park.

      Mai mota yad'anyi jimmm saican yace to nawa zaku biya?.

    Yagana tace kafara fad'a, yace Ku kawo 250² to.

      A'a Malam mubakadai 200².

       A'a idandai zakubada 250² d'in kushigo.

     Taufeeqa tace shikenan, sauran taima alamar sutaho.

     Mai mota yabud'e musu but suka saka kulolin hannunsu da k'ananun baskets da'aka ruling d'in bakinsu da Leda mai k'yalk'yali.

      Sannan duk suka shiga.


Kuyi hak'uri kunjini shiru *_Sanadin bikin sallah_* Na 6uya😍

[8/13, 6:44 AM] Aisha Galadima: 5⃣


*_GIDAN matar da taufeeqa ta satarma kud'i._*


        Zaume take tarabga uban tagumi, abin duniya ya isheta, tunranar Abban Abdul yahanata fita balle ta binciko gidansu Taufeeqa.

    Babban tashin hankalintama shine ko naman sallah ba'a kawo gidanba.

   Yaukuma dawuri Abban Abdul yayma Abdul da ummi wanka da Kansa ya shiryasu cikin sababbin kayansu Na sallah, ya tattarasu suka tafi idi, har yanzu basu dawoba, gashi ya kulleta tabaya da k'aton kwad'o.

     Wasu hawayene masu zafi suka zubo mata, batadamu data shareba, saima wasu dake rige-rigen fitowa, itakam tarasa mafita, an6ata goma biyar bata gyaruba, tace nashiga uku ni hajarah, kardai Kameel yace bana bazamuyi abincin sallah ba? Aikam daya gama kasheni wlhy.............

         Jitai ance ai inbaki mutuba zaki dawwama a makarantar nadama, kuma inamai tuna miki maganar kud'ina Dan saura kawana biyu daga ukun dana Baki.

    Yanagama fad'a yashige d'aki, mintuna kad'an yafito d'aukeda madaidaiciyar jakka, wadda yazubo kayansu Abdul aciki.

     Ko kallon hajarah dake surutai da kuka baiyiba yafice abinsa, a yanzukam bai rufetaba.

   Yana fita yaro nayin sallama, baijira amsaba ya danno kai cikin gidan, k'aton tiren dake kansa yasauke ahankali, yana fad'in gashi inji Maman Ilham (hafsa makwafciyarta).

     Wani damm gabanta yafad'i, ta danne zuciyarta tace kace mata ngd.

    Yaro yace to, yafice abinsa.

     Yana fita tajawo tiren tafara bud'e kwanukan, kwanon farko Na babbar samira fankasune daya samu kyakykyawar suya, d'ayan kuma wainace tashinkafa shar da ita (masa) sai d'yar miyar alayyahu dataji isashshen naman rago, sai kamshin kori takeyi, saikuma wata babbar langa da'aka zuba farar shinkafa, d'ankwanon kusada ita kam miyace ta naman kaji, filet arufe mai cikeda coslow da akaima yankan nutsuwa, an zuba bama asamansa.

      Saikuma wani k'aramin kwano da'aka ciko da cin-cin doughnut & etc, ansaka gwangwanin maltina biyu na fanta biyu, dakuma babbar robar swan dake cikeda zo6o......

    Kawai jinai hajarah takwala k'arar kuka, tana fad'in kameel ka cuceni, duba kaga wadda bata kaini komaibama tahad'a wannan shagalin awajen *_bikin sallah_*, wlhy kameel baka isa *_Sanadin bikin sallah_* kasa 'yan anguwa su rainaniba, narantse baka isaba, yau koda sama da k'asa zasu had'e saika mana cefane gove nayi abincin sallah, (dolene Na nunama shegiyarnan bata isaba).

    Gyalenta tad'auka tafita tamkar wata mahaukaciya, bata dire ko inaba sai gidan k'awarta Aysha.

    Canma haka ta tadda Aysha baja-baja cikin hidimar bikin sallah, wannan yak'ara tada mata da hankali.

    Dak'yar Aysha ta'iya sakin aikinta tazo suka gaisa da hajarah, sukaima juna barka da sallah.

    Hajarah tace Aysha Dan ALLAH alfarma Nazo nema wajenki.

      To ALLAH yasa inada abinsa zan fiddaki kunya, Cewar Aysha.

    Hajarah tace ameen.

   Tad'anyi Jimm sannan tace Aysha kud'i Nazo nema rance Dan ALLAH.

     itama Aysha shiru tad'anyi, zuwacan kuma tace bar nawa?.

       Cikin zumud'i hajarah tace 40k..

     To, ke kam hajarah mizaki dak'ud'i masu yawa haka?.

       Wlhy Aysha kameel ne yakeso kafin aturo masa wasu kud'i.

      To shikenan, ainasan Abban Abdul babu wasa, ALLAHma yasa yanzu abokan Abban deeni dasukazo sukaci abinci sukaban 30k, bara naduba na hannuna idan sumkai 10.

      To, hajarah tafad'a cikeda farinciki.

    Babu dad'ewa Aysha tadawo da kud'i 40k cif, tabama hajarah, itakuma taimata godiya tareda sallama, Aysha ta tsayar da ita tana fad'in inazuwa.

    Bak'ar leda tabama hajarah sannan tarakota har gate .


Hajarah jitake kamar taita rawa Dan murna, kaitsaye kasuwa tatafi, siyayya tayo bata wasaba, (sai yanzu taji zuciyarta tayi wasai).


Nace hummm.


Tunda tadawo gidan tafara hidimar aiki, dandanan tagyara kajinta, tajik'a shinkafa, takwa6a fulawa dazatai abubuwa dashi.

     Ranar wuni tayi aiki, jefi-jefin yara 'yan yawan sallah kan shigo gidan, wasu tabasu barka da sallah, wasukam bata basu, har yamma lik'is Abban Abdul bai dawo gidanba bare su Abdul, wannan yabata damar gama aikinta tsaf, sauran kuma saida safe idan ALLAH ya kaimu.

      Koda Abban Abdul yadawo baiga wata alamar anyi aikiba, Dan hajarah komai da tsari tayishi tagyara gidan tsaf kamar ba'ayi komaiba, saidai tabasa mamaki, Dan cikin walwalarta ya isketa, amma baice da ita kanzilba, yay himarsa ya kwanta.

    Itama bata tambayesa yaranba, dantasan gidansu yakaisu.


*_02:30pm_*


Woooow!!.....😨nafad'a lokacin da idanuna suka sauka kan gungun matasan 'yan matan dasuka d'auki wanka Na kece raini, dolene ka kallesu ka kuma kallo, Dan babu k'arya sun d'au wanka iya wanka.

     Duk inda suka gitta sai an bisu da kallon birgewa.

    Tuni samari matasa suka fara fad'awa tarkonsu, sukam sai k'ara hura hanci suke da d'age kai sama suna basarwa. Lol🤣


Bawasu bane 'yanmatannan illah *_Taufeeqa, Khadeejah, zee, Hafeeza, Saudat, Maryam, yagana, Ameena, Bilkeesu._* sai Badar da kebinsu tamkar dole, Dan Maman Ameena ce tace dolene duk inda zasuje saida ita, inba hakaba Ameena bazata bisuba.

   Badan sun soba Badar tabisu, tana sanye cikin less irin Na Ameena da akaima d'inkin Riga da siket, amma dai ita da *_Hijjabinta_* iya gwuywa tasaka, tayi k'yau wlhy itama, Dan zan iya cemukuma ni wankanta yafi d'aukar hankalina.

    Mutananku kam aii kowacce da siririn gyale, wasuma akafad'a kawai suka d'ora, wasukam awuya, ga uban Google's🕶👓 duksun aza, dolekam duk wani gaye yagansu yayi Respecting nasu, Dan sund'au wanka iya wanka🤓.

    Ga wani taku dasukeyi d'ai-d'ai, kaikace bazasu taka k'asarba kosuna tsoron jimata ciwo.

     Abakin titi sukaja layi Dan duba abin hawa.

    Bilkisu taja gilas d'inta k'asan hanci tana kallonsu, cikin yauk'in magana tace guys mufa tare mota mai aji.

    yes, gskyarki billy, cewar Hafeeza tana yatsine baki.

   Daganan sukad'an fara firarsu k'asa-k'asa, itadai Badar tana gefe abinta, idanma baka saniba bazakace tare sukeba.

     Sund'anyi tsayuwar 24mnt suna jiran mota, dukda kuma titin akwai motoci sunata kara kaina, amma kosun tsaya saisu Maryam sufara yataine bakuna, wai motar bata musuba, suna nandai saiga wata taxi sabuwa dabatasha wahalaba.

    Wannankam da alama tamusu, dantana tsayawa Taufeeqa da Yagana suka k'arasa wajensa, yace 'yammata ina zuwa?.

    Cikin yatsine fuska yagana tace jabi park.

      Mai mota yad'anyi jimmm saican yace to nawa zaku biya?.

    Yagana tace kafara fad'a, yace Ku kawo 250² to.

      A'a Malam mubakadai 200².

       A'a idandai zakubada 250² d'in kushigo.

     Taufeeqa tace shikenan, sauran taima alamar sutaho.

     Mai mota yabud'e musu but suka saka kulolin hannunsu da k'ananun baskets da'aka ruling d'in bakinsu da Leda mai k'yalk'yali.

      Sannan duk suka shiga.6⃣&7⃣


 

     Kasancewar motar tamusu kad'an aka kuma tare wata, yagana Maryam Ameena zee Hafeeza suka shiga d'aya.

     Taufeeqa Saudah Bilkeesu khadeejah Badar suka shiga d'aya.

     Haka motocin biyu suka jeru a kan babban titin Na Abuja.

    Tafiyar dabata wuce minti 40 ba takaisu jabipark.

    Bayan fitowarsu da biyan kud'i suka nufi cikin park d'in dake cikeda jama'a, maza da mata, yara da manya, mutanene dasuka kasu group group, wanigun kid'a akasa 'yanmata da samari nata cashewa, wanigun yara ne keta wasa, saikuma dokuna🏇🏼 daketa shawagi da mutane akansu, yawanci yara sunfi hawa, sai masu cacar nan da ake jera kwalaben drinks iri-iri harda giya, kajefa Abu idan yafad'a cikin kwalbar kaci kenan, so abubuwane dai kashi kashi nad'ebe kewar jama'a da tayasu murnar bikin sallah. (Duk Wanda yasan  Abuja, yasan irin wad'an nan wajenne mutane kanyi shagalin bikin sallarsu, musamman 'yan mata da yara, kasancewar babu wani hawan sallah da akeyi).

       Tundasu Hafeeza suka shigo sukebin mutane d'aya bayan d'aya da kallo, duk iya ganinsu basuga Wanda yako kama k'afar gayunsuba, wannan yasa Kansu yak'ara girma da fad'i. Lol😂.

    Yanzu ina zamu fara zuwa?. Cewar Saudah.

      Yagana tace inaga mud'an samu waje muhuta kafin anjima mu zagaya.

      Duk sun amince da zancenta.

    Ameena da Maryam sukaje wajen masu bada Ranching d'in carpets suka kar6o uku, d'ari 600, Dan d'aya d'ari biyu ne.

          Lokacin dasuka dawo har Bilkeesu ta kunna musu pm d'in dasuka taho da ita, aii anagama shinfid'a wasu suka zauna, wasukuma acikimsu suka fara cashewa.

         Hummm.

Hankalin mutane dayawa suka fara dawowa Kansu, saboda shewar dasukeyi yayinda wani yay wani abin burgewa acikinsu, yanda suka iya taka kowacce irin rawa saika d'auka daga gidan Drama aka yayosu, sosai suke cashewa abinsu tamkar filin babu kowa.

        Badar naganin masu waya sun fara video nasu tamik'e tabar wajen.

     Kan kace mi wajen yafara cika da 'yan kallo, sukam hakan yamusu dad'i, Dan haka suka k'ara himmatuwa wajen nuna fitsararsu.

       Haka sukaita shashancinsu har 04:30pm sannan suka fara hotuna, nanafa samari suka fara zuwa suma ayi hoton dasu, hardama 'yan mata masu rawarkai irin nasu.

     Suna gama hotuna sukaje suka biya kud'i suka hau dokuna, daganan sai jirgin ruwa, daga jirgin ruwa suka koma gaban DJ aka basu fili, zuwa sannan bak'aramar cika park d'in yayiba, sukam idanunsu yarufe sunata 6arar da rashin arzik'i, acewarsu murnar bikin sallah sukeyi.

     Duk abinnan dake faruwa badar nacan tana tsaron kayansu, Dan suna Barin gurin itakuma taje a zauna.+


5:30 dai-dai sukabar park, mota suka hau zuwa shoprite, dama duk saida suka k'ara gyara kwalliyarsu, taku sukeyi d'ai-d'ai, kaikace wata uwar sayayya sukazoyi wajen.

   Nanma cike yake da jama'a babu laifi, Dan nanma akanje ahuta *_Sanadin bikin sallah_*, itadai Badar binsu kawai takeyi, ammafa wajen yamata k'yau sosai, Dan bata ta6a zuwaba sai yau, mutanenku kuwa ansaba dama.

        d'an tsaki bilkisu taja, Yagana takalleta tana fad'in lfy kuwa?.

    Bilkeesu Tayatsine fuska takumajan tsaki, tace kigafa mutanen nan yau sai suka kashemana lifter.

      Khadeeja tace keko aii mutane sunyi yawa dolene sukashe aii.

        Bayan sunshiga sukayi hotuna ananma, daganan suka k'arisa ciki, kayan kwalam da mak'ulashe suka sayo, itadai Badar bata d'auki komaiba Dan tasan batada kud'i, hotoma itakad'ai tayi abinta, bata shiga cikin nasuba.

   Bayan sungama shahsncinsu sukazo wajen biya, akamusu bil dubu bakwai da d'ari shida.

        (Nazata bazasu iya biyaba)

   Amma amamakina sainaga zee tabud'e Jakarta tad'akko sun biya.


     Nace hummm🤦‍♀.


Daganan fita sukayi, can baya suka k'arisa inda ruwa yake, Wanda yatafi har jabi park.

     Anan suka sami guri suka zauna, nanma cike yake da 'yammata da samari, yarama kad'anne awajen, wasu daga samarin sai shaye-shaye sukeyi, (so wajendai dakagani yawanci marasa jine).


    Tunda su zee suka shigo naga wasu gungun samari sun dasa musu idanu.

    Saimagana sukeyi kus-kus, kuma duk motsinsu Hafeeza idon samarin nakansu.

    Badar ce tad'an tsargu, dan haka cikin hikima tace 'yan uwa yakamata mubar wajennan Dan tunda muka shigo idon mazancan akanmu yake.

         Wani kallon raini Hafeeza taima Badar, cikin gadara tace kodai akanmu, kekam mizasu kalla ajikinki? Bayan kin 6oye abin ganin.

    Zee tace yo badole su kallemuba, sunsandai munyi 100% wlhy, aiimu dole aganmu akallah.

    Saudat tace harma a k'yasa.

    Atare suka shek'e da dariyarsu, mutanen dake d'an kusadasu sukajuyo suna kallonsu.


STORY CONTINUES BELOW

Araina nace hummm🤔.


Tundaga nan Badar bata sake maganaba, saima tatashi daga kusadasu tabar wajen, amma tana kallonsu, dukda ita hankalintama yayi gida, tana tsoron kar abbansu yadawo gida basu komaba.


Basubar *_shoprite_* ba har yamma lis, saida suka gama zagaye ko ina da ina sannan suka fito. Aikam har bayan isha'i basu samu motaba, saida k'yar suka sami adai-daita guda d'aya, itakuma tamusu kad'an.

     Mai adaidaita yatsaya taimaka musu koza'a samu wata suk'ara, sunanan har 9 tayi, hankalin Badar yatashi ainun, Dan haka tafara kuka, sai safa da marwa take abakin titin, kasancewar ko'ina akwai haske.


----------------------------------

       Tun wajen k'arfe 5 Na yamma yake zaune awajen, can saman k'arshe Na gidansu, babu abinda yake kallo sai shigi da ficin da jama'a sukeyi cikin shoprite da titin.

              Wasu sukan bashi dariya da kwalliyar sallar tasu, wasukam haushi, yana nan zaune aka sauke wasu gungun 'yammata a kekenapep biyu, gayu sosai sukayi, saidai d'aya acikimsu tana sanye da hijjabi.

    Mamaki abin yabashi sosai, dama ranar sallah akwai 'yanmatan dakanyi wankan hijjabi?,  tabbas da labari aka bashi bazai yardaba.

   Baiga fuskartaba har suka shige gate d'in shoprite, har aka kira sallar magriba basu fitoba, wannan yasa yabaro sama yasakko k'asa, babu kowa agidan nasu, duk suntafi gidan abokin dadynsu yawon sallah, harda mamensu, shikad'aine agidan yake tunanima.

    Koda aka fito sallah saiya kasa komawa cikin gidan, haka kawai yaji yanason sake ganin matashiyar budurwa mai wankan hijjabi a ranar sallah.

    Kujera d'aya yakar6a wajen mai gadimsu yadawo k'ofar gate yazauna, zamansa babu dad'ewa saigasu sunfito.

    Ajiyar zuciya ya sauke dan ganin yarinyarma tafi sauran 'yanmatan dasuka tsuke k'yau da aji, gyara zamansa sosai yayi yana k'are musu kallo dafad'in masha ALLAH ahankali.

      Duk wahalar neman motar dasukeyi idonsa Na Kansu, har aka kira sallahr isha'i yatashi zuwa masallaci.

   Abin mamaki har yadawo sunanan, saidai ansamu napep d'aya.

     Kukan daya hango mai hijjabi nayi (kamar yanda yarad'a mata) saiyaji babu dad'i, cikin gida yashiga yad'akko mota yafito.....


Sukam su zee ganin dare nak'arayi, gashi mai napep na shirin guduwa shima sai suka yanke hukunci akan yakai wasu yadawo, idankuma sunsamu shikenan.

   Dayawansu basu yarda da shawararba, Dan haka kowa yafara rubibin hawa, itadai Badar tana tsaye tana share hawaye.

    Tsayuwar wata k'yak'yk'yawar farar mota yasa hankalin wasunsu dawowa wajen.

   Yasauke gilas d'in ahankali, idonsa akan Badar dake sharar kwallah.

      Tamkar mai ciwon baki yace miyasaki kuka?.

     Zabura Badar tayi Dan ita hankalinta baikai ga motarba ko kad'an.

   

Sukam su Bilkeesu duksun mutu atsaye suna kallon handsome da motarsa, tuni sunbar kokawar hawan napep.


Kuma maimaita tamabayar yayi ga Badar.

    Jikinta nad'an rawa tace inatsoron Abba yadawo gida bama nan, kuma wlhy ko sallahn magriba banyiba.

       Lumshe idonsa yayi yabud'e akanta, zuciyarsa Na tsikarinsa, yabud'e motar gabad'aya yafito.

      Atare su Taufee sukace wooow!!..

     Shikam hanky d'insa Fari tas yamik'ama Badar, cikin muryarsa mai taushi yace a INA kuke?.

     Kubwa tafad'a tana k'ara matso hawayen.

     Kansa ya jinjina yajuya ga motarsa yana fad'in kutaho mu tafi.

    Har rige-rigen bud'e motar sukeyi suna shiga, yagana tabud'e gaba zata shiga yawatsa mata harara, babu shiri tasaki murfin itama takoma baya, dukda sunyi masifar matsuwa haka suka zauna su biyar, Bilkeesu Ameena yagana zee Taufeeqa.

      Kallon Badar yayi yace kemuke kira, kokinason Abban yadawo.....

       Bairufe bakinsaba tak'araso wajen motar, gaban motar yanuna mata, babu musu tashiga, dukda gabanta nata fad'uwa, gatsoron kar'agansu amota afad'ama Abba. Ameena kam dasu zee ko'a jikinsu, saima kowaccensu da tafad'a tarkon son guy mai mota, Dan duk irin wannan mijin sukema Kansu fata.

     Khadeejah Maryam saudah Hafeeza sukashiga adaidaita badan ransu yasoba.

      Ahaka suka kama hanyar Kubwa.

       Tunda suka tafi su zee keta fafa abaya, da surutu waidansuja hankalin saurayi Kansu.

    Agaba kuwa shida Badar babu mai cewa k'ala, shi mamakima yakeyi da sakaci irinnan iyaye, yanda suke barin yaransu suna yawo mara dalili ana fakewa da shagalin bikin sallahne.

    Irin wannan sakacinne yakesaka yara dayawa fad'awa tarkon wahala a *_Sanadin bikin sallah_* amma yarasa mike damun iyayene?.

      haka suka k'araso kubwa, Badar dukda atsorace take haka tayimasa kwatacen gidansu kamar yanda yabuk'ata, Dan ita bata iya k'aryaba. Wannan yasa Ameena batason yawo da Badariyya, dan duk abinda sukayi aka tambayeta saita fad'a ta's.


Koda yasaukesu saiyayima Badar  sallama yatafi, saurankam duk sanabe da kwarkwasar dasuke masa basu isheshi ko kalloba.

    Badar taimasa godiya tashige gida abinta, saida yaga tashiga gida yaja moyarsa yatafi.*_Gidan hajarah._*


Washe gari tunda tayi sallahr asubahi tatashi tafara aikinta, kamar suyar sinasir dakuma dafa shinkafa.

   Abban Abdul kam tunda yadawo sallahr asuba yakoma barci, cikin barci yakejin k'amshi, tun yana d'aukar abin daga mak'otane hardai k'amshin yafara addabarsa.

    Tashi yayi yafito, cikin mamaki yake kallon hajarah daketa suyar sinasir hankalinta kwance.

      Hajarah!! Wakuma yabaki kud'in yin abincin sallah?.

    Kallonsa tayi fuska a washe, tace Abban Abdul kenan, yo daga ALLAH, kasanshi baya kunyata bayinsa, yakamatama kafara bugama abokanka waya kasanar dasu yau akwai liyafar cin abinci a gidanka. Kaga nakusa kammala komai, Dan har nagama rabama mak'ota, yanzu Altine ma tatafi kaina gidanku, basiru kuma Na gidanmu, kai namadai tak'aice maka nagama da kowa, Na abokankane anan kawai.......

    Wata gigitarciyar tsawa yadaka mata, cikin huci yace wlhy hajarah ki kiyayeni, kuma wlhy kin saka kanki a uku inhar dakud'ina kikayi wannan 6arnar, humm kikiyayi abinda zai biyo baya.

    Yana gama fad'a yashige ciki abinsa, zuciyarsa Na masa k'una da zugi.


Baki hajarah ta ta6e tace masifaffe kayi kagama, kud'ima idan kayi hak'uri aida abokanka sunbani barka da sallah zan biyaka abinka ko.


🤣jama'a kuji sarai gaci.

    Hajarah shike kawo jin yunwa😆.


Yana wanka tashiga d'akin, wayarsa ta lalla6a ta d'auka, falo tadawo tarubu gajeren message ta turama duk wani abokinsa sannan tadawo tacigaba da aikinta.

    Shikam baisan tsiyar data shiryaba, koda yagama shirinsa saiya fice batareda yabi takantaba.

     Zuwa 10am tagama komai, tagyara gida tayi kwalliyar sallarta wadda batasamu damar yiba a jiya.

      Sallamar abokansa tafaraji, aiko tayafo gyale yafito, wajensu 5 suka fara zuwa, kanta tsaye taimusu iso cikin falon, inda tahad'a gagarumar liyafar, ahaka sukaita zuwa d'ai-d'ai har suka taru wajen su 13, saidai haryanzu babu Abban Abdul.

      Auwal cikin abokansa yad'auki waya yakirasa.

   *_haba mutumin, yazaka taramu agidanka kaikuma haryanzu babu labarinka, yakamata ka k'araso inka gama jamana ajin?._*

         Sosai mamakine ya bayyana kan fuskar Abban Abdul, yayta maimaita maganar Auwal aransa, har yasamu damar fassarata.

     Wajen dealing d'in wayarsa yaduba ko hajarah takira wani amma baiga ankira kowaba, kafim tunaninsa yadawo massage yashigo wayarsa, Qaseem ne.

    Massage d'in yabud'e yaduba.

    *sorry kameel, nidai bazan samu damar shigowaba, Dan munje kd nida madam, amma amin afuwa, bansan da liyafarba.*

     Liyafa! Ya maimaita aransa.

    Duba sak'on dake saman Wanda Qaseem yaturo yayi,   cikin al'ajabi yace ni natura sak'on gayyatar wani cin abinci?.

    Zuciyarsa tace matarka dai.

   Da sauri yace Kai impossible, badai hajaraba.

    Sak'on yakuma dubawa da lokacin da'aka turashi, cikin d'imauta yadafe kansa, haka yanufi gida da k'udirin kartama hajarah rashin m.

    Amma ganin tarin abokansa sai jikinsa yay sanyi, baikamata yadakatar dasuba tunda basusan komaiba, dole yadanne zuciyarsa aka gaisa, daganan suka fara cin abinci, sunata zuba Santi da yabon hajarah, itakam sai dad'i takeji dak'ara daidaita ajinta, shikam ko ruwa k'insha yayi, yama k'agara sugama sutafi yad'au mataki akan shegiyarnan...........

Hummm tofa Sanadin bikin sallah kenan.🤦‍♀8⃣&9⃣


          Sosai suka ringa kod'a guy mai farar mota (kamar yanda suka rad'a masa suna) kowaccensu jitake inama yace yanasonta.

        Shikam tunda yatafi tunaninsa nakan *_hijjab girl_* (Badariyya) sosai ta burgeshi, Dan irinsu badar sune yara masu cikakkiyar tarbiyyar da babu yaudarar iyaye acikinta, Dan bak'aramin abin mamaki bane ranar sallah kaga had'ad'd'iyar budurwa datau wanka da hijjab.


Itakam badar harkokinta takeyi hankali kwance, saidai turarensa ya manne mata ahanci harma da jiki, dukda bata maida hankali wajen tunaninsaba time to time yakand'an fad'o mata arai.

    Saida sukazo kwanciya kuma Ameena ta addabeta da surutun kwarzanta guy d'in.

   Ganin Ameena ta zarma akan son wandama baisan tanayiba, saita bata tausayi, Dan aganintama k'ila har Abadan bazasu sake ganin junabama.


        *_Washe gari_*

  K'iri k'iri badar tad'orama kanta ciwonkan k'arya dankartabi su Ameena yawon sallah, sukam dama haka sukeso, Dan yau tareda samarinsu sukayi shirin fita, amma dayawansu ba'a saniba agida.

     Yauma haka suka d'auki *_wanka iya wanka_* suka fita suna basarwa, dolene kagansu kayaba komai kushenka, Wanda kuma sukasan kansu, sukan furta ALLAH ya shiryasu, Dan lamarin nasu babu tsari.

    Irinsu Ameena dama da hijjab suke fitowa gida, sai anbaro gidan acire asaka gyale, hijjab kuma yakoma bag.

    (Nace ALLAH dai ya shirya mana zuri'a)+


Aikam yanda suka shirya hakan ta kasance, sunfita da samarinsu, yawo sosai sukasha acikin garin Abuja, anshawo shagali, (harda abinda shari'a ta haramta) dan d'an Romancing d'innan saida aka ta6a dasu, dama samarin nasu yawanci irinsune.

   Kaf d'insu babu wadda taje da saurayinta dazata aura, duk guys d'in had'uwar sallah ce, garama Bilkeesu, tare suke da Mahfouz d'inta, Wanda shima bajin maganar yakeyiba dama.

        Sunsami yanda sukeso kuwa, dan sayayya hardata banza da wofi anyo musu, sai 9pm suka dawo gida.


*_gidan hajarah_*


     Masha ALLAH, anci ansha kamar yanda hajarah tayi fata, kuma taji dad'in yanda suka yaba mata, saidai yanda Abban Abdul ke balla mata wani mummunan kallo afakaice insun had'a ido yana sakata fad'uwar gaba.

      Wani 6angare Na zuciyarta kuma yana kwantar mata da hankali, idan tatuna zata sami kud'insa ta biyasa yanzu a wajen abokansa.

      Abokansa kam bayan sun gama kwasar gara saisuka shantake anata hira, basubar gidanba har aka kirayi sallahr zuhur, ananne wasu suka mik'e, hajarah tabasu butoci sukayi alwala suka tafi masallaci.

     

Hummmm🤣


Abu kamar wasa hajarah tagyara waje, ko sallar batayiba ta zauna jiran dawowar abokansa, dan azatonta sunje sallah su dawo sannan subata barka da sallah.

       Abu kamar tatsuniya har 2:30pm tayi babusu babu labarinsu, kuma tun 12:48pm sukabar gidan, hardai 3:pm yayi babu labarinsu.

      Saidai abinda hajarah bata saniba shine, abokan Abban Abdul suna fita sukaje masallaci, wasu kuma tun a k'ofar gida suka rabu, dan sallahr k'arfe biyu sukeyi su.

    Koda akafito masallaci wasu sukaima Abban Abdul godiya da d'awainiya sukamasa sallama suka wuce.

    Sauran kuma suka sami inuwa suka zauna zaman hira, ciki harda Abban Abdul, dukda hankalinsa nakan gidansa, dan bak'aramin tsanar hajarah yayiba ayau d'innan.

       Ganin baya fahimtar hirartasu yamik'e tareda musu sallama.

      Saifullah yafiddo 2k yabama Abban Abdul, kameel ga wannan abama Uwargida tasayi omon wanke-wanke, mungodefa sosai, ALLAH yabada ladan zuminci.

    Murmushi yayi yana fad'i wlhy dama kabarta.

    A'a dan ALLAH kakaimata dukda babu yawa, nida Fharuk ne, kasan abubuwa sai addu'a.

    Kar6a yayi yay godiya, shima Ahmad yabada d'ari Biyar, dama sukad'ai suka rage, sauran kowa ya ware abinsa.

      Gidansa yanufa kaitsaye.

     Afalo ya iske hajarah zaune tana cin kayan Snacks da fanta, hankalinta kwance sai basarwa takeyi.

    Shigowar Abban Abdul tad'an razana, danko sallama baiyiba (balle tayi tunanin da arzik'i yazo mata).

     Sannu tamasa, yaymata banza babu amsa.

      Kud'inda su Ahmad suka bata yajefa mata, gashi inji wad'anda kikama girki, sai nima kitashi ki fiddomin kud'ina ko.

        Wata irin zabira hajarah tayi tanamai k'urama kud'in manyan idanunta, cikin tsoro tace Abban Abdul 2500 fa nake ganin?.

          Shima kallon mamaki yamata tareda ta6e bakinsa yace oo! Dama kindafa musu abinci dansu biyaki, woow! Amma bansan ke tosanshiyar kwakwalwane dakeba sai yau, gsky nayi kuskuren d'aukarki matsayin uwar 'ya'yana.

    Nabaki nanda magriba kije gidanku sainazo, kuma kuma kafin nazo atanadarmin kud'ina 25k, inba hakaba wlhy saikinyi dana sani, danzan Baki mamaki irin Wanda baki ta6a tunaniba, mahaukaciya kawai.


STORY CONTINUES BELOW

Hannu tad'ora aka tafasa kuka, nashiga uku ni hajarah, *_sanadin bikin sallah_* najefa kaina a masifa, yazanyi da kud'in Aysha har 40k?.

         Abban Abdul dake fitowa daga d'aki yaymata kallon tsaf, baigamajin mita fad'aba, danhaka baifahimci zancen nataba, yafice yana fad'in karnadawo naganki agidannan, inba akaba jikinki zai fad'a mikine.


Nace hummm, bikin sallah yayi🤥🤙🏻


---------------------------------


Tun jiya haka ya kwana sukuku, tunanin yarinyar yagama addabarsa, hardai k'aninsa Shaheed yalura da halinda yayansa yashiga, danko barcin kirki baiyiba daren jiya.

    Suna dawowa masallaci yakoma barci, tuni kuwa barci mai nauyi yad'aukesa.

    Har 'yan gidan suka gama hallara danyin breakfast kamar yanda suka saba, amma baitashiba, mum ta kalli shaheed tace Shaheed wai lafiya kuwa? Ina *_Shureim_*!?.

      Wlhy mum barci yakeyi, nima narasa mike damunsa, dan tunda muka dawo daga gidan Abbeiy nagansa sukuku, kuma baiyi wani barcin kirkiba jiya da daddare, shiyyasa yaketa barci yanzun.

       Kowa shiru yayi yana mamakin maganar Shaheed, sunsan ya Shureim baya barcin safe, sukamsu fad'a yake musu akan hakan, kuma kaitsaye ba'a gane damuwarsa, kasancewarsa mutum mai hak'uri da shiru-shiru, bashida hayaniya ko kad'an, shiyyasa iyayensa da 'yan uwansa suke matuk'ar sonsa.

     Su shidda mum & dad suka Haifa, Haidar shine babba, yayi aure harda yara uku, babu wata tazara tsakaninsa da Muhammad Shureim, dan zamu iyacewa mum gwanne tayi alokacin, tahaifi Haidar da wata 7 tasamu cikin Shureim, wannan yasa Shureim da Haidar suka tashi tamkar tagwaye, saidai banbancin halayya, Shureim yanada hak'uri, Haidar kam yanada zafi, tun lokacin Auren Haidar dad yace shima Shureim dashi za'a had'a, saidai kuma Shureim bashida budurwa, dan baya kula d'iyar kowa, aganinsa 'yan matan yanzu basuda isashshiyar tarbiyya, musaman yanayin rayuwarsu ta 'ya'yan masu kud'i, yaga yanda 'yan matan cikinsu suke, dukda 'yanmata dayawa daga 'ya'yan abokan dad har k'awayen mum sunkawo masa caffa amma yazame, Shureim yanada kyansa masha ALLAH, kasancewarsa Bakatsinen asali, cikakken Barume, kyansa mai sanyine, shiyasa yake d'aukar hankalin 'yan mata.

     Babu yadda su dad suka iya akasha shagalin bikin Haidar, dan babu auren dole a tsarinsu.

       Abu kamar wasa har matar Haidar tayi haihuwar farki (twins) Shureim baya maganar aure, ananne dad & mum suka masa maganar, amma saiya basu hak'uri akan zai nemo.

     Haka suka saka masa idanu har matar Haidar takuma haihuwar mace, to daga nanne suka fara matsa masa, amma saidai yabasu hak'uri kamar yanda ya sabayi, har zuwa wannan lokacin baya maganar auren, har Shaheed yafidda mata shima, kuma shike bima Shureim d'in a haihuwa.

       Kwana biyu da d'aukar azumu  mum suka sake masa magana ne yace sutayashi da addu'ar samun tagari.

     ALLAH mai iko ranar sallahr farko saiga *_Hijjab girl_* tazo kamar amafarkinsa daya saba.

      Shureim nada k'anne 4, Shaheed, Afnan, Hanan, Ahkam, kuma duksun girma.

       Dad yakalli Ahkam yace auta jeka taso Ya Shureim.

    To dad, Ahkam yafad'a yana tashi.

     Yasan ya Shureim bayason atadashi da hayaniya, dan haka yak'arasa gaban gadon inda yake kwance k'udundune abargo, iska yafara hura masa a kunne.

    Tun Shureim najin iskar cikin barci, harya bud'e idonsa dakyar, ganin Ahkam yasashi tamke fuska, auta lafiya? Yay maganar cikin tsare gida.

     Ahkam yakama kunnensa biyu yana fad'in sorry yaya, dad ne yace natasoka.

        Bece komaiba yayunk'ura da k'yar yatashi zaune, dan jikinsa yamasa nauyi sakamakon rashin isashshen barci, sauka yayi zuwa toilet yayo brushing bakinsa, sannan yazura doguwar riga Ash color.

     Dama Ahkam yakoma tuni.

      Har sannan basu fara break d'inba suna jiransa, yarissina yana gaida mum & dad.

   K'annensa Suma suka gaidashi.

     Babu Wanda yaymasa maganar damuwarsa tsakanin mum & dad.

      Abinci kawai sukahauci cikin tsanaki.


Saidai suka gama tsaf, Hanan & Afnan suka gyara wajen, dad yamik'e tareda cema Shureim yabiyosa, falonsa sukaje, suna zama saiga mum itama, cikin hikima suka tambayi d'an nasu damuwarsa.

          Kansa ak'asa yace *_Hijjab girl_*!!.

    Mum & dad suka kalli juna tareda fad'in _Hijjab girl!_ kuma?, wacece haka?.

       Kuma k'asa yayi da kansa sannan yabasu labarin tun farkwan zamansa sama, dakaisu gida dayayi.

    Nanda nan fuskar dad & mum tawashe da farinciki, sukaita jera Alhmdllh.

   Dad yace ALLAH yayimaka albarka, aikam yau basai gobeba zan nemi Alhaji baseeru muje munema maka izinin zuwa wajenta, kaga daganan sumuji ko ba a mata mijiba ko? Dankarmu take shari'a.

    Mum tace gskyane, ALLAH ya albarkaci abin, lallai ina cikin farinciki, yau ALLAH ya amshi addu'ata akan Muhammad Shureim d'ina.

     Murmushi Shureim yayi yana susar k'eya. Lol🤪


STORY CONTINUES BELOW

Aikam kamar yanda dad yafad'a hakane tafaru, bayan sallar la'asar daga dad & Alhaji baseeru Shureim yakawosu har k'ofar gidan daya ajiye su Badar. Dukda baisan nanne gidansuba ko akasin haka.

          Tsayuwarsu babu dad'ewa saiga Badar tafito cikin hijjab har k'asa zatakaima kakarsu abinci.

      Ganin Shureim tsaye ajikin mota saida gabanta yafad'i, dukda da daddare tagansa hakan bai hanata ganeshiba, jiki a sanyaye tak'ara gareshi, rissanawa tayi ta gaidashi, kanta ak'asa tace lfy kuwa?.

         d'an murmushi yayi, cikin sanyin muryarsa yace k'alau, idonsa Na kanta, gani yakema yau tafi jiya k'yau, dukda yau ba'a ganin komai nata daga fuska sai tafin hannunta, kasancewar hijjab nata har k'asa yakeja.

        Duk abinda ke faruwa dad & Alhaji baseeru Na kallonsu, kuma suma duksun yaba tarbiyyar badar, inhar itace _Hijjab girl_ d'in dota In-law d'in tasu.

     Alhaji baseeru yace dole my son yasaka mata hijjab girl aii.

     Dariya dad yayi kawai baice komaiba.

      A can kuwa Shureim yace abbanmu yana gidane?.

          Badar dakanta ke k'asa tace wai Abbana kake magana?.

    Yace uhhm to hakane, amma nima aii hardani aciki, inba Rowa za'aminba.

     Ahankali tace amin Afuwa, yana nan, bara nasanar masa.

     Batajira amsarshiba tashige gida, babu dad'ewa suka fito tare.


Dukda Abba baisansuba hakan baihanashi karramasuba har sitroom nashi, bayan Shureim ya gaidashi cikin girmamawa yafita yabarsu, dan zancean manyane baikamata ya zaunaba.

    Badar takawo musu ruwa kamar yanda Abba ya umarceta.

    Bak'aramin dad'i su dad sukajiba, dan wannan yak'a nuna musu cewa gidan dattako d'ansu yasamo matar aure.

*_agurguje_*

            Dad & Alhaji baseeru sun tattauna da Abban badar, kuma anfahimci juna, Abban badar yabama Shureim badariyya, tareda alk'awarin aure, Wanda atake anan suka tsaida wata biyu, Wanda yay daidai Dana Shaheed, bayan Babar sallah da sati biyu.

    Su dad sunyi farinciki, dan basuyi zatom hakaba, suda sukazo Neman izinin zance sai akabasu d'ungurungum, batareda wani damuwaba, sunnuna farincikinsu sosai, musammamn ma urban gayya Shureim, jiyake kamar wani sabon mutum.

    Shikam Abba ganin mutanen sunada kamala yasashi yanke huncinnan, kuma yasan dad sosai, dan sunta6a had'a wajen aiki a shekarun baya, kafin dad d'in yazama wani Abu.

     Sannan sun matuk'ar Burgesa, dan azamaninnan bakowa yamasan darajar aurenba, bare yayi tunanin fara Neman izinin iyayen yarinya kafin yazo gurinta, amma saigashi iyayen Shureim sunyi, dukda kasancewarsa masu arzik'i, kuma basu k'yamacisuba dukda sun gansu k'asa dasu, talakawa.

    Wannan hujjojin suka sake Abba badar basu ita, dukada yayi k'udirin k'ara bincike akan yaron, tunda kowa da halinsa, kuma 'ya'yan yanzu basucika amfani da tarbiyyar iyayensuba dukda k'ok'arin iyaye naganin sun setasu a hanya.


Badar kam guduwa tayi kafin Shureim yafito, dukdama batayi tunanin wajemta yazoba ko kad'an.

    Harsuka tafi bai gantaba, baidamuba do farincikinsa yadanne masa hakan.


Haka Abba yashiga da labarin wasu Maman Ameena, tayi matuk'ar farinciki dan macece wadda tasan yakamata, kuma tana d'aukar badar kamar ita tahaifeta, ko kad'an bata nuna banbanci da sauran 'ya'yanta.

--------------------------------------    

Hankalin hajarah atashe da furucin Abban Abdul, tasanshi da bak'aramin zuciya idan ransa ya6aci.

      Kuma tabbas yadawo yaganta agidan zai akata duk abinda zuciyarsa tabasane.

    Tana kuka rurus tabar gidan, maimakon taje gidansu saita nufi gidan Laure mai k'unshi.

   Bayan sun gaisa ta tambayeta gidansu Taufeeqa, ras Laure tamata kwatance, aiko hajarah tace nasan gidan, koba gidan Maman zuhrah ba, mai saida gyad'a soyayya?.

    Nanfa 'yar gari cewar Laure.

    Babu 6ata lokaci hajarah tafito sai gidansu Taufeeqa.


Atsakar gida ta tadda yaran zuhrah sunata wasa, dan yau anan suka wuni har mamansu, ta tambayi Sa'eed maid'an wayon, yace sunje bayan layi itada ummana gaida wata batada lfy.

     Tsaki hajarah tayi, taja kujera ta zauna tana fad'in ALLAH yadawo dasu lfy, ina nan harsu dawo aii.


Aikam babu dad'ewa saigasu sundawo.

    Sama-sama hajarah ta amsa gaisuwarsu, duk yabasu mamaki hakan baihana zuhrah tambayarta ko lfy ba?.

     Cikin masifa hajarah tace inafa lfy, nazone abani kud'in da Taufeeqa tasatamin agidan k'unshi ana gobe sallah.

    Gaban umman Taufeeqa da zuhrah yafad'i ras.

     Har had'a baki suke wajen fad'in satafa kikace?.

    Kwaraima kuwa, idan kunason k'arin bayani zamu iya zuwa gidan Laure mai k'unshi.

     Zuhrah batada fad'a, hakama ummansu, ana haka saiga abbanta da Habubu Wanda Taufeeqa ke bimawa, suka tambayi abinda ke faruwa, nanma cikin tsiwa hajarah takori musu bayani.

     Zaginda habibu yafara, dafad'in wlhy kotabar gidan kokuma yalakad'a mata dukan tsiya.....

    Abbane yadakatar dashi, yacema hajarah tayi hak'uri suje gidan Laure mai k'unshi da zuhrah, dan suji yanda akayi.

     Hajarah bataji ko d'arba tace aje.


Aikam habibu yakasa hak'uri yabisu, tiryan-tiryan Laure mai k'unshi takira musu zance, suka dawo gida, hankalin Abba yatashi sosai, dan wani abokinsa yashaida masa yaga Taufeeqa a kasuwa ana gobe sallah tana siyan takalma a shagon makwafcinsa.

   Abba harya d'an musa masa da fad'in anya kuwa Alhaji ashiru?, nidai nasan ban aiketaba, hakama mamanta, inagadai maikama da ita kagani. (Sosai Alhaji Ashiru yayima ABBA rantsuwa).

   Badan Abba ya yardaba sukabar maganar, tokuma yanzu gawannan maganar ta 6ullo, kodai gskyne?.

     Hak'uri Yakuma bama hajarah, yace tadawo gobe idan ALLAH yakaimu da safe, sannan taufee tana gida, inma gskyane zai gane, kuma za'a bata kud'inta.

    Wannan dalilin yasaka hajarah yarda tatafi, bataje gidansu sai gidan yayarta Nafisa.


*_09:pm_*.

      Su Taufee suka dawo daga gantalin yawon sallarsu, kowa gidansu tatafi kasancewar dare yayi.


Saidai kuma taufee ta tarar yayarta nanan, dan anan zasu kwana itada yaranta, babu Wanda yaymata maganar hajarah har washe gari.

     Dasafe suna cikin dama koko itada yayarta zuhrah saisukaji sallamar Hajarah, gaba d'aya suka fito har abbanta da habibu & Umma.

     Taufee.... Nayin tozali da hajarah gabanta yafad'i, dandanan tarasa nutsuwarta, kunsan ance *_Mara gaskiya, ko'a ruwa ji6i yakeyi!_* to hakance tafaru da taufeeqa kuwa, dandanan tafara zufa, dukda sanyin hadarin daya mamaye garin.

     Kowa kuwa idonsa na kanta, kuma duksunga rud'anin data shiga, hajarah tamatso tashak'e wuyan rigarta tana fad'in to _6arau-6arau sasssatau_ munafukar ALLAH, harda yima Ummy wasa, Ashe 6arauniyace ke, wlhy ayau d'innan sainaga kud'ina zanbar gidannan, inkuwa bahakaba police zasu rabamu yau agarinnan.

         Taufee tarud'e, danta manata da iyayenta awajen, cikin kuka tafara bama hajarah hak'uri, kiyi hak'uri dan ALLAH, wlhy tsautsayine, amma ba halina baneba.

    Canta matse miki tsinanniya matsiyaciya, nidai inji dumus kawai, inko bahakaba wlhy saikinje Setetion yau.

     Umma & zuhrah kam kuka suka sake, yayinda Abba da habibu ransu yakai k'ololuwar tashi, Abba baisan sanda yajawo k'aton icce yafad'a jibgar banzaba.

     Dukda kururuwar datakeyi da ihu babu Wanda yakwaceta dan Habib gidan ya kullo, saida yayi mata lilis har bata ya motsin kirki sannan Yakoma gefe yana share hawayen bak'inciki.

     Hajarah kam ko'a kwalar rigarta, itadai kud'inta kawai, habibu yabata hak'uri akan yabasu lokaci zasu biyata, amma tace Sam, yaud'innan take buk'ata.

    Ganin bazata samuba tafita, saiko gata da mortar police, zuwa sannan gidan yacika taf dajama'a anata tambayar lfy, amma sunkasa bama kowa amsa, ga Taufeeqa kwance ak'asa shame-shame.

       Sai zuwan hajarah da police ne 'yan anguwa sukaji abinda Taufee tayi, dan hajarah tas takwashe zance tafad'a,.

    Nanfa kowa yafara tofa albarkacin bakinsa, masu ALLAH wadarai nayi, masu jaje da ALLAH yak'ara nayi, su Umma kam sai kuka sukeyi, suna ganin police suka kwashi Taufee zuwa mota aka wuce da ita..........

zee!1⃣0⃣🔚

            Zee Na zaune  a tsakar gida tana uban wanke-wanke Wanda yazame mata tilas, sai zum6ura baki takeyi da k'unk'uni, mamanta tana kallonta amma ta shareta.

    Da gudu k'aninta Sageer yashigo yana hakki, daga mama har zee kallonsa kawai sukeyi, cikin hakki yace yaya Zainab 'yan sanda sunkama k'awarki yanzu.

   Dafe k'irji zee tayi, tace sageer wace k'awar tawa?.

     Yaya Taufeeqa, wai naji mutane nacewa sata tayima wata mata ana gobe sallah.

    Sallallami Maman zee takeyi kawai.

   Zee kam jikinta sai rawa yakeyi.

       Basu gama tu'ajibin abinda yafaru da taufeeqa ba sukaji sallama.

        Jiki a sanyaye suka amsa, amma ganin yayar jabeer da k'anwar babansa sai gabansu yafad'i, mama cikin sanyi take musu maraba, Dan tabbas taji ajikinta ba alkairi bane ganin iya yalwa agidansu, kuma awannan farar safiyar.

     Bayan sunshiga d'aki sun zauna zee tashiga tana gaidasu, ganin Harar da iya yalwa kemata yasaka gabanta tsananta fad'uwa.

       Tashi tayi tafita, saidai kuma kafin ta ida fita iya yalwa ta tsaidata dafad'in dawo Zainab, aii zuwan nakine.

   Dawowa zee tayi ta zauna, mama dai batace komaiba, saida suka gaisa sannan iya yalwa tace baban Zainab fa? Dan tare muke da bak'i suna a waje.

      Bak'aramin fad'uwa gaban mama yayiba, murya a sanyaye tace yana d'akinsa bara natadosa, batareda tajira amsarsuba tafita kiransa.

   Zee dai tana zaune tsuru-tsuru, kareema sai banka mata harara takeyi dajan tsaki, itamadai iya yalwa kallonta tsana kawai take binta dashi.

      Bayan mama tayima baban Zainab bayani yamik'e cikin hanzari, k'ofar gida yanufa, manyan attijaine maza hud'u, cikin gidan yaymusu iso, bayan gaishe-gaishe. Wan baban jabeer yace Malam Usman dama dai wani abune yakawomu, amma munaso kayimana k'yak'yk'yawar fahimta dan ALLAH.

    jinjina kai kawai baban Zainab tayi danya kasa magana.

      Yacigaba da fad'in, dama jiya damisalin 10pm akazo har gida aka kama jabeeru, ahannun 'yansanda yakwana, to yaudai dak'yar muka samu ganinsa.

    Bayan munbi ba'asin kamashi da akayi police sukaimana bayani akan wai yad'ibarma ogansa kud'ine ashago.

    Hankalinmu yatashi, danba'a ta6a kama jabeeru da makamancin wannan halinba, wannan yasa mukace abamu damar mutanbayesa, sunyimana wannan alfarmakuwa, akafiddomana jabeeru muka tambayesa, bai 6oye mana komaiba yafad'a mana Zainab Ce ta takurasa akan yamata kayan sallah, idan bahakaba tafasa aurensa, wannan dalilinne yatada masa hankali yad'iba kud'in ogansa har 35k.

   Wlhy Malam Usman bakaga yanda suka canjama yaron kamanninsaba, sunmasa duka bana wasaba, to yanzudai ga kud'insu munhad'a musu dak'yar zamukai mu kar6osa.

    Asha-asha Abu baiyi dad'iba Cewar Malam Usman cikin tsananin 6acinrai.

    Yacigaba dafad'in, dalilin zuwanmu nankuwa shine gsky mun haramtama jabeeru auren Zainab, Dan kaitsayema mahaifiyarsa tace inhar ya yasake kallon Zainab batayafe masaba barema aurenta, kaga bikinsu sati uku kawai yarage, to gara tunda wuri kusan halin da'ake ciki.

    Dan aganinmu Barin Auren shiyyafi alkairi, tunkan ya aureta yafara saka Kansa cikin Matsala da halinda banasaba, yana mayaraya, inaga tazo gidansa? Ai ba'asan mizata sakashi aikatawaba kenan?.+


Wasu kwallah masu zafi suka cika idon baban Zainab, yagogesu tareda yimasu godiya,  hukuncin dasuka Yanke daidaine, kuma subar kud'insu zai biya afiddo jabeer.

    A'a suka fad'a at are.

   Baban Zainab yace inhar kun hanani kar6o jabeer da kaina to kunnunamin jabeer ba d'ana baneba kenan?.

   Hak'uri suka basa sannan suka mik'e sukatafi harda baban Zainab.

        Zee kam kuka takeyi rirus dakiran tabani ta lalace, su tausaya mata tanason jabeer wlhy, Dan ALLAH karsu rabasu,  wlhy kuskurene bazata sakeba, tanasonsa sosai.

   Wata maguza mamanta takai mata abaki saboda bak'incikin da zee ta haddasa mata, batasan kawai tafara jibgartaba, gashi babu kowa agidan, saida Tamata dukan tsiya sannan takoma gefe tana kuka dafad'in zee kin cuceni, ALLAH ya Isa ban yafe mikiba, kinzubar mana da kimarmu da tarbiyyar damuka baki zakijamana zagi agari, teer da halinki Zainab, tir dahali irinna k'awayenki, waccan tayi sata kekuma kinsaka mijin dazaki aura yayi,  ALLAH yawadaran halinku.


ALLAH saiya sakamana zagin da kukeja  mana agari.....

   Kuka sosai Maman zee keyi, itama zee d'in haka, bata ta6a tsanar kantaba irin yau, dalilin San zuciya tarasa abin sonta, anfasa aurenta ana saura kwana 21, *_Sanadin bikin sallah_* takafama kanta tarihin dabazai ta6a goguwaba, k'ilama yazama sanadin dazata rasa mijin aure anan gaba, wani irin kuma maiban tausayi tafashe dashi.😭


STORY CONTINUES BELOW

Nikaina tad'anban tausayi😢.


Tuni labarin zee ma yakarad'e anguwa, kuma komai ya Isa kunnen k'awayensu, wasu acikinsu hankalinsu yatashi sosai, Dan sunsan suma danasu tabon ajiki.


Bayan kwana uku dafaruwar wannan lamari akayi belin Taufeeqa bayan ancakema hajarah kud'inta cif, shidama jabeer tun aranar aka fiddoshi.

    Saikuma aka wayi gari da tashin hankalin sace Bilkeesu, wai da daddare yaro yazo kiranta akan Mahfouz yazo wajenta.

   Tashirya tafita, saidai har 12pm bata shigo gidaba, hankalin iyayenta yatashi, hardasu Rabi'a amasu nema, kaf anguwa an zagaye babu Bilkeesu babu labarinta har wayewar gari. Lamarin ya girgiza jama'a, musammamnma k'awayenta, duk kuma inda ake tunanin samunta babu ita.


A6angaren Saudat ma tana cikin matuk'ar damuwa, Dan maganar saka ranar Badar da Shureim tazagaya ko ina, kowa sai murna yake tayata, Dan abbansu yayi k'yak'yk'yawan bincike akan Muh'd Shureim, yasameshi mai kyakykyawan halaye nagartattu, yauma dasafe iyayen Shureim sukazo Neman alfarma akan adawo dabikin baya nanda 2weeks saboda wani cos da Shureim zaije k'asar Saudi-Arabia Na tsawon wata tara, Shureim ma'aikacine a (NNPC) kuma yanada kwazo sosai, cikakken Engineering ne afannin k'ere-k'ere, ALLAH yayi masa nasibi tanan wajen.

    Kowa ya amince dahakan kuwa.

   Badariyya kam abin nabata mamaki, tasan ko giyar wake tasha bazatace Shureim bai mataba, Dan irin namijin dakiwace mace take fatan samune, wannan yasa ta kwantar da hankalinta, taima iyayenta biyayya.

    Tun randa sukazo baikuma zuwaba, sai yau da abbanta yacemata tashirya zuwansa da yamma.

     Haka tawuni tanamai d'okin ganinsa ak'ark'ashin ranta, amma afuska baka Isa ganewaba.

    Ameena kam jitake tamkar ta dingure Badar Dan haushi, tayi kuka sosai dabak'inciki, harda dana sanin k'in yima mahaifinta biyayya akan saka hijjab, tabiyema k'awayen banza saboda kwalliyar birgewa da birge mutane, togashi agarin birge wasu, su sunshiga tarkon wahala da danasani, sunkasabin tsarin da musulinci yamana akan bikin sallah.

    Kukakam tacisa kamar babu gobe.


4:30pm Shureim ya iso gidansu Badar, sitroom aka kaisa, jikin Badar a sanyaye tad'auki tiren ruwa da zo6o da Maman amina tahad'a mata, sanye take cikin doguwar Riga ta atanfa, tasaka hijjabinta daya wuce guywa kad'an, tayi k'yau sosai, tana k'amshin humra mai sanyin dad'i.

    Cikin siririyar muryarta tayi sallama ak'ofar sitroom d'in, shima muryarsa mai tsaushi da nutsuwa ya amsa mata, kamar wadda kwai yafashema aciki haka tashigo falon, idonsa nakanta k'yam, jitake tamkar zata nutse awajen, hakadai tana k'afa dak'yar tak'arasa garesa, agabansa tadire tiren.

    Jiyake tamkar ya rungumeta saboda k'yan data masa, zama tayi ahankali ak'asan carpet can nesa dashi, ina yini....? Tak'atse masa tunanimsa.

    Firgigita yadawo hayyacinsa tareda sauke ajiyar zuciya, sakkowa yayi daga kujerar yakoma kusada ita yazauna, amma nesa k'ad'an, dan akwai tazarar tak'i biyu tsakaninsu.

       Yawani rabga tagumi yana binta da narkakken kallonsa.

   K'asa takumayi da kanta saboda kunya, k'ara gaisheshi tayi.

    Cikin sakin ajiyar zuciya ya amsa, tareda fad'in matana! kina lfy?.

    Bata iya amsa masaba saidai d'aga masa kai datayi kawai, yasaki murmushi mai sauti tareda fad'in babu magana? Nidai amin magana, ina sonjin Golden voice! d'innan nawa.

   Da sauri taja hijjabinta tarufe fuskarta, yajingina da kujera yana sassanyar dariyarsa, murya k'asa-k'asa yace nanda 2weeks iyanzu nacire kunyarnan insha ALLAH a birnin saudia fadar musulinci, fatana sanda zamu dawo k'asarmu munzama mu uku, nidake da babynmu da yardar ALLAH.

       bak'aramar kunya maganarshi tabata, tana mamakinsa, dama yana surutu haka? idan ka kallesa mai fuskar hak'uri, amma ji yanda yake d'akko manya-manyan zance.


(Nikaina bilynku zancensa yaso yafara fin k'arfin Alk'alamina😉).

       Aradu 'yammata da matan aure inayinku🙌🏻, irin sosai sosai d'innan🤩, wata soyayya sai a *_CIKI DA GASKIYA........._* (Sabon book d'ina maizuwa🤪🤙🏻).


Haka Shureim yayta zubama Badar kalamai masu kwantar da hankalin, zuwa 6pm yawuce gida, yabarta da kewarsa.


Washe garin kwana biyu da sace Bilkeesu aka tsinceta cikin mummunan hali, Ashe Mahfouz ne yasaceta, damacan badan ALLAH yake sontaba, Dan jikinta, kuma dama babu Wanda yasan Mahfouz d'an inane, kawaidai yazo yana zuwa wajentane, babu Neman izinin iyayenta, sukuma babu bincike suka barshi saboda kwad'ayi, koda aka kawo mata kayan sallah babu Wanda yabi ba'asi.

   To yanzukam sunga illar abinda suka aikata, kukakam anshashi, Bilkeesu tamkar zata shid'e saboda kukan bak'inciki da dana Sani, *_Sanadin bikin sallah_* yau tarasa MARTABARTA, Mahfouz ya cuceta, bakuma zata yafe masaba har Abadan.


STORY CONTINUES BELOW

Nace daga baya kenan takwara, aii anbaro shiri tun rani🧐.

   (Shiyyasa masu iya magana sukance *_Yaro tsaya matsayinka, kada zance 'yan duniya ya rud'eka_*😏)

  Wannan magana gskyce wlhy😎.


Abubuwan dasuka faru sunta6a zukatan mutane, *_"yan group d'in k'ureeeee wankaaaa!!!."_* sunga duniya da sharrin biyema kayan cikinta, saidai lamarin bai canjaba, Dan kuwa safiyar alhamis aka tashi da tashin hankalin yima Hafeeza fyad'e itama, kuma anrasa wanene ya aikata.


Niko nace dazasuzo guna dana fad'a musu, Dan kuwa *_"Telane"_* dasukayi ajanda da Hafeeza, bayan sallah yabi duk hanyar dazai sameta amma ta toshe masa, kwata-kwata tama 6oyema ganinsa.

    Ranar laraba da dare kuwa an aiketa ya *kwamisheta* sai wani kango, anan yaymata faca-faca.


Ba'agama tararrabiba hajiya mai kayan koli tazo kar6ar kud'inta Wanda Hafiza taciyo bashi, hankalin iyayenta yatashi sosai, mamanta tanufi inda take ajiye dashinsu Na anguwa dayake itace da d'auka, amma mizata gani wayam babu komai, tafito tana salati da sallalami ankwashe kud'i, cikin kuka Hafeeza tace ita tad'ebe tasayi takalmin sallah da jaka.


     *_(Humm iyayaye kuma kunada naku kuskure, sometimes zakiga 'ya'yanki da Abu amma bazaki tambayi inda yasamoba bare kid'auki mataki, yo aganina ko biskit kikaga d'anki/'yarki dashi aik'ya tambaya ballantana abinda ya haurama duku goma, duk wankan da Hafeeza takeyifa iyayenta Nagani, amma suka kasabin ba'asi balle binciken inda tasamu, to Dan ALLAH yanzu wa gari ya waya?, ai wlhy kowa rai yayima dad'i baran maishine, ALLAH yasa mugane)._*

    

Hafeeza dai gayanda takaya mata itada iyayenta, kuwa yana kukan nadama dana Sani.


Wanana abubuwa dake faruwa kuwa sunyi matuk'ar tada hankalin sauran k'awayensu irinsu Maryam yagana saudah khadeeja.


Dukda itama yagana ta d'and'ana kud'arta waken babanta, danshi mutumne mai zafi, tumda labari yadawo masa akan yagana tasaka saurayinta yadawo mata da kayan da akak'i kar6a, kuma tasaka ranar sallah, aikam yaymata shegen duka tareda badata sadaka ga wani yaronsa, kuma bak'aramar tsana yagana tamasaba, amma tasan tilas ta aureshi, aikam asafiyar juma'ar satin aka d'aura aurenta da Sabi'u, babu wani shagali da'akayi bare taro, haka aka kaita tamkar bazawara Mara galihu, tayi kuka sosai, gashi sabi'u Nada mata masifaffiya.

   

(Nace yagana, abinda kashukafa shizaka girba🤗)


Koba hakaba Fan's??!!🤷🏽‍♀.


Ana gobe d'aurin auren Badar 'yan fashi suka Shiga gidansu khadeeja, sunbiyo sahun sark'ar da khadeejah tasaka ranar sallah.

         Wadda ta'aro gidan amarya makwafciyarsu, sark'a mai amsa suna 6arayin gold, sukam 'yanfashi sunzata gold ne aikam sukayo sauda baya.

    'Yanfashi kam sune samari dasukaita kallonsu a Shoprite, Wanda Badar tafargar dasu amma suka dizgata dacewar wankansu suke kallo.

   To Ashe fataken darene, aikam dai Khadeejah dakowa Na gidansu yaci duka, dansunce saita rakasu gidan mata mai sark'a tunda tace batatabace, kuma ba gold bane.

   Amma Sam basu aminceba, ganin zata musu taurinki sukace taza6a, ko nuna musu gidan mata mai sark'a ko fyad'e, kuka da rok'onsu iyayenta suka shigayi, Dan basu amince da nuna gidan amarya mai sark'a ba, (aganinsu butulcine), aikam agabansu akaima kadeejah hawan sallah, Wanda yajazama mahaifinta fad'uwa sakamakon bugawar da zuciyarsa tayi yace ga garinkunan, (mutuwa rigar kowa, saidai takowa da sanadinta).

    Kadeejah dai tazama sanadin tababanta


To kadeejah, dama masu iya magana kance *kayan aro basa rufe katara.*🤐.

        Kinga abinda kika jama kanki, *_ga mari, gakuma tsinka jaka_*🤧

   Babu babanki, babu mutuncinki👌🏼.


Agurguje.🤭


Ranar Asbar 2:30pm aka d'aura auren Muhammad Shureim Umar katsina & Badariyya Jafar.

   d'aurin auren daya tara manya-mayan al'ummar musulmi, and'aurashi a k'ofar gidansu cikin anguwar Arabroad dake Kubwa.

   To ALLAH yasanya alkairi.

   Adaren ranar aka mik'ata family house na Shureim gidansu kenan, washe gari kuma suka d'age k'asa mai tsarki.


*to sainace ALLAH yabada zaman lfy Badar, in anje amana rok'o a d'akin ALLAH*🕋🤗

Wai kunjifa fan's saina fad'i daren farkon Badariyya & Muhammad Shureim😒, aradu nak'i fad'a d'in ehe😏, kowa tak'iyastama zuciyarta, hannuna yafara ciwo😫 saboda typing, bayanma babu Wanda yaban naman sallah, 😎

  Bara namuku gulma😶, harfa 'yan group d'ina *Taskar littatafan Hausa* basu baniba, su o e ma dankar Na tambaya daina hawa online akayi,🤧😫.

    Badan karna fad'a muku sunanta kumata boreba da yanzu zan bugata a shafin farko🤔, amma nayi shiru🤫 gudun had'a cakwakiyar sambad'ar kanta🤪😜.

          🙋🏻‍♀aradu inayinku fan's d'ina, irin tamau tamau d'innan😍, k'aunarku dabance a zuciyar *Bilyn Abdul* nasoku jiya,👈🏻.

ina sonku yau👈🏻,👉🏻 zankuma soku gobe, kai har k'arshen numfashina😘😍😍🤝🏻.


Agurguje.


Hajarah nagani zaune tsakkiyar iyayenta, sai uban kuka take darza, sakamakon takardar saki da Abban Abdul ya aiko mata da ita, gakuma Aysha tazo ta tirketa akan kud'inta 40k.

   Da da farko Abban Abdul yazone amata fad'a sukoma, dama kud'in data sata yatarasune akan zai bata tayi jari, amma ta kassarasu, anacikin sasancin saiga Aysha a haukace, tazayyane musu yanda sukayi da hajarah, abin ya6atama Abban Abdul rai, saboda k'aryar datayi dashi, aikam atake anan yabata redCart.

    Kuka take sosai da nadama,

sanafin bikin sallah takashe aurenta, tarabu da abin sonta, uban 'ya'yanta, mai sonta da iya gskyarsa, mai k'yautata mata da tausayinta, Abban Abdul akwai k'ok'arin sauke hak'in iyalinsa, gidanta babu rashinci babu rashin sha, sittira kodayaushe basai sallaba.

    Kuka sosai tayi, harda zazza6i, tanaji tana gani aka kwacesu Ummy da Abdul awajenta.


To hajarah, ai hassada ga mairabo takice, San zuciya kuma 6acinta, yaro tsaya matsayinka kada zancem 'yan duniya ya rud'eka, Wanda baiji bariba yaji hoho, hangen dala bashiga birniba, duk d'an daya hana uwarsa barci shima bazaiyiba wlhy, hak'uri maganin zaman duniya🤩


Alhamdulillahi ala kulli halin.


Anan nakawo k'arshen wannan d'an littafi nawa.

    ALLAH yasa sak'on dana isar yayi tasiri, kuma masu karatu su fahimta, suyi tankad'e da rairaya, su amfanu da abinda nafad'a daiadai, suyi watsi da kuskurena, dannima 'yar Adam Ce azija.


ALLAH ka gafartama mahaifina dadukkan 'yan uwa musulmai, marasa lafiyarmu ALLAH yabasu lafiya, muda muke da ita ALLAH yak'ara mana, ALLAH yak'arama shugaban k'asa lafiya dadukkan masu k'yak'yk'yawar zuciya irinsa a cikin shugabanninmu, masu mana k'afar angulu amulkinnan ALLAH kamana maganinsu, dankafimu sanin abinda ya cancanta agaresu, ALLAH kashirya mana zuri'a, kazaunar da k'asarmu lafiya, ya ALLAH ka kare musulinci da musulmai, ka d'aukakashi, ya ALLAH ka karya kafirci da kafurai kamana maganinsu.


ALLAH kasa ibadarmu kar6a66ace, ALLAH kad'auki ruhinmu muna masu imani da tsarkakakkiyar zuciya.👏🏻🤲🏻😭.Nagode da lokacinku dakuka bani cikin wannan d'an littafi nawa.

Post a Comment for "SANADIN BIKIN SALLAH COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...