RUWAN SAMA COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RUWAN SAMA COMPLETE

RUWAN SAMA COMPLETE

- - Post a Comment

 RUWAN SAMA COMPLETE🍇💦RUWAN SAMA....💦🍇

*•Baya Chanza d'and'anon teku•*


**Fatima Muhammad Gurin**

*Gureenjo6763 on wattpad*


'Yar Mutan Adamawa

               

           *Taa-daaa!!!! Happy Eid el fitr, Allah ubangiji yasa ibadunmu kar'ba'bbu ne yasa muna daga cikin en tattun bayi na wannan wata, rabbi ya gafarta mana dukkannin zunnubanmu  ya sa muna daga cikin masu tsawon kwanan ganin wani azumin*


*innal hamda lillah, Alhamdulillah, bismillah tawakkaltu Alallah wala haula wala quwwata illah billah*

*P1*


Kallon fuskar wayar dake ta kara tayi tare da fad'ad'a fara'arta ganin me kiran, leka fuskata kan wayan nayi naga an saka "ruhool na'im❤️🔐" d'auka tayi cike da murmushi tace.

"hello this is Mrs Saif shamsuddeen Suraj how can I help you?" Dariya yayi daga d'aya bangaren yace "hooo oo my heart ke baki gajiya da zolaya but that name suits you and kin wanke laifinki".

Murmushi tayi tace "am sorry Abban Neeha ban kira ba I was so busy with your kids ne su suka d'auken hankali".

Yace "I'm badly missing them up here" cikin shagwa'ba tace "ni kuma fah?" Dariya yayi yana cewa "mene?" Turo baki gaba tayi tace "nayi fushi" tana shirin kashe wayan kenan taji muryanshi cikin kitchen d'in.

"Surprise"

Wani irin ihu tayi tana juyowa tare da fad'awa jikinshi sossai farin cikin ganinshi ya bayyana a fuskanta.+


"What a surprise!!!" She exclaimed

Yace "I so much miss you sweetheart d'azu da ban fad'a ba har anyi fushi dani right?" d'agowa tayi daga jikinshi ta kalli kanta sanye take da doguwar rigar simple material se hulan dake kanta ko ear rings babu kunneta ta kalleshi yaci wanka cikin sky blue yadi me shara shara ya kafo zanna bukar d'innan yadda take son shi se kamshi yake zubawa.


Baki ta tura tace "I'm jealous" lakace mata hanci yayi yace "anty jealousy am hungry of you muje d'aki daga baya kya d'aura daga inda kika tsaya" sossai ta shagwa'be fuska tace "wato kai ko a jikinka?" Kafad'a ya d'aga yana ta'be baki, da sauri yaja baya ganin ta d'aga hannu da niyyan dukanshi gwalo ya mata ya juya da sauri aiko da gudu ta biyoshi be tsaya ba se d'akinshi tana kawo hannu ya chabke ya murd'e.

Ba ta yadda zata ji zafi ba ya mannata da jikinshi ta baya tare da sanya kanshi cikin wuyanta yana shakan daddad'ar kamshinta nan take ya kashe mata jiki da salonshi kan kece me zance ya sauya.


Bayan sun samu natsuwa ya kara rungumeta cikin jikinshi yana son matarshi sossai har abada be tunanin za'ayi mace da ta kai mishi ita a komai har kwanciyar aure, ya zurma cikin tunaninta bayan gata a kan jikinshi se ji yayi tana shafa cikinshi tace "na tabbatar bakayi breakfast ba love gashi har to 12, lemme get you something to eat".

Tana kokarin mikewa ya dawo da ita da hannu d'aya d'ayan hannun yasa ya kama fingers d'inta yana wasa dasu yace "In Ina tare dake heart bana jin komai bare wannan abincin da kika ban yafi min ko wani irin abinci" murmushi tayi tace "I have to cook oo bcs kids sun kusa tasowa".

Yace "you don't have to yau gabad'aya ba shiga kitchen hutawa zakiyi".

Tace "then what are we going to eat?" Kissing lips d'inta yayi yace "you" waro ido tayi zata kuma magana yace "Allah d'agani" ya yunkura ya mike da ita zuwa toilet wanketa yayi kan ta tayashi yayi nashi sukayo na tsarki suna fitowa taji ana sallama daga parlor, kallon ta yayi itama shi take kallo sbd ta san In yana gari baya son baki na zuwar mishi gida, cewa yayi "are you expecting someone?" Kai ta girgiza, yace "Ohk lemme check".


Jallabiya ya sanya kan towel d'in jikinshi gashin kanshi jike yake da ruwan wankan da sukayi yanzu, seda ya bi corridor d'in d'akunan nasu kan ya fito babban parlorn gidan daga bakin corridorn ya tsaya yana kallonta, ta ci wani irin ado na tashin hankali fuskan nan yasha penti ko ta ina ta saka wata arniyar straight gown na atampha da ya kamata har numfashi da kyar take.

Tsiririyar gyalenta na rike a hannunta da tsinanniyar hill d'inta ta shigo har tsakiyar parlorn ta samu wuri ta zauna, kallon kanta yayi d'aurin da tayi me bayyana rabin kai ne attachment d'in dake sanye a kanta ya bazo har tsakiyar bayanta, murmushi ta sake mishi tace "yaushe a gari?".

Kwa'be fuska yayi yace "mene?" Waskewa tayi tace "Ina yini?" Ba yabo ba fallasa yace "lafiya" ba tare da ya kuma tankawa ba ya juya don komawa tace "erhhmm nace ba, matar gidan fah pls?" Juyowa yayi ya mata kallo d'aya ya juya ya koma room d'inshi.

Tana gyara doguwar rigar atamphar jikinta da aka mishi d'inkin A shape ya tsuke daga sama har kan cikinta daga kasa kuma ya baje, tace "wayene roohul na'im?".

Tsiririyar tsaki ya ja yace "a duniya ban ta'ba ganin abinda na haneki dashi kika cigaba dayi ba se kawance da wannan 'yar iskar yarinyar, I hate her for that me yasa ne ni kam?" Shagwa'bewa tayi tace "haba love ban fa sanka da haka ba, Ina kawance da ita ne sbd watakila In iya zama sanadiyar shiryuwanta kaga dagani har kai zamu samu lada, I'm sorry please".

Hararinta yayi yana zama stool d'in mirror yace "karki yaudareni da wannan puppy face naki" murmushi ta saki sanin ya bar maganan kenan, d'ankwalinta ta d'auka ta kafa d'auri tare da matsawa jikinshi ta d'an kwanto tare da mika hannu kan mirror ta d'auki turarenshi ta feffesa tana ajiyewa tayi pecking cheeks d'inshi tace "am coming" ta fice daga room d'in.

Da kallo ya bita he loves her, he always do be ta'ba ganin simple and caring mutum irinta ba she's always smiling baka ta'ba ganin fushi kan fuskanta ko da kuwa en uwanshi sun bakanta mata yadda suka saba, ajiyar zuciya ya sauke yana huro iskan bakinshi waje yace within his throat "three kids, ko se yaushe zasu dena tsanarki su gane kyawawan halayenki?".

"Oyoyo zuby" murmushi zuby ta sake tace "oyoyo shaaty" bata zauna ba tace "Ina zuwa" kitchen d'inta dake manne da parlorn ta wuce ta d'auki bottle water da maltina ta d'aura kan karamin tray tare da sanya cup ta fito fuskanta cikin murmushi tace "yau kuma kece a gidana zuby yaushe rabon da In ganki?".

Cikin rigima kaman wata er bariki tace "hmmm Ai kun kusa dena ganina shaaty tunda duk randa na sanyo kafata gidanki se mijinki ya min wulakanci". Shaati tace "Eyyah kiyi hakuri ba wulakanci bane kawai dae In yana gari be cika son baki bane ba ke kuma kaman had'in baki se yana gari kike zuwa".

'Daukan malt d'in tayi ta fara sha ba tare da ta damu da cup ba tace "hmmm kede kawai kare mijinki kike son yi, love birds" dariya sukayi a tare shaati na cewa "haka dae kika ce, Ina su malam da inna?" Iyayen zuby kenan.

Cewa tayi "suna gaidake" hira suka ci gaba dayi sama sama, da gudu wata kyakyawar baby ta shigo sanye da uniform yarinyar bazata wuce 3yrs ba lunchbox ne kawai a hannunta se hijab da shima yana rike a hannunta kitson kalabanta ya sauko har kafad'anta "oyoyo maami" bata ma kula da bakuwar ba ta fad'a jikin uwarta cikin shagwa'ba tace "Maami I miss you".

Murmushi shaati ta sake na farin cikin ganin yarinyar tace "miss you too my baby, where are your siblings?" Tana shirin magana wani yaro da ze yi 4yrs ya shigo kyakyawa kaman wannan babyn wadda duk kammannin na mahaifinsu ne goye da karamin school bag d'inshi hannunshi rike da lunchbox daga bayanshi wata yarinyar ce itama sak su a kamanni bazata wuce 6 ba.

Duk da gudu suka rungumeta itama ta amshesu cikin farin ciki, "Assalamu alaikum" wata ta fad'a tana shigowa sanye da uniform irin nasu sede ita she's dark in complexion ita kuma she's 9yrs old nayi mamakin ganin ta daban ko ba abinda ta d'auko na mahaifiyar ko na mahaifin nasu, "wa'alaikissalam warahmatullah an dawo?".

A gajiye tace "eh maami, barka da gida" dukawa tayi tace "Anty zubaidah Ina yini?" Tana murmushi tace "ohhh Lafiya kalau Arwa ya school?" Tace "Lafiya" shaati ne ta kalli sauran yaran tace "Yasmin, Sameer, Neeha baku gaida Anty zubaidah ba" kallonta sukayi a tare sukace "good afternoon Anty zubaidah".

Murmushi tayi tace "how are you guys doing?" Sukace "fine" kallon Arwa Tayi cikin murmushi tace "oya Adda Arwa aje a cire uniform" ta gane da yaran take yi kama hannun sameer da neeha tayi yayinda Yasmin ta bisu a baya suka shige corridor d'in d'akunansu.

Hira suka ci gaba dayi hankalinta na kan saif sede ba daad'i ta bar zuby haka ga kuma tana tunanin yaran sun dawo da yunwa yace kar tayi abinci she knows he mean it ko me zasu ci? Bata gama tunanin ba taji kamshin turarenshi ya bule parlorn lumshe ido tayi ta bud'e su fess kanshi sanye yake da kananan kaya blue jeans da sky blue shirt ya gyara gashin kanshi zuwa sajen nan sun kwanta lublub idanunshi sanye da farin medicated glass d'inshi.

Ba tare da ya kalli inda suke ba ya bud'e kofa ya fita, tana mamakin irin kallon da taga zuby ke mishi, sede bata kawo komai a ranta ba kawai taji ya bud'e kofa ya shigo hannunshi rike da manyan ledoji da sauri ta tashi ta kar'ba.

"Where are my kids?" Ya furta kasa kasa daidai kunnenta bayan ya had'a hannunta da ledan ya rike.

"Suna changing just go back to your room pls I want to surprise them" cikin wani salo yace "really?" Yana wani kashe mata ido murmushi kawai tayi, taune lips d'inshi yayi cikin command sound yace "ki sallami wanchan abar I want to be alone with my family".


Fuskan tausayi tayi ya had'e rai ya wuce d'akinshi ajiyar zuciya ta sauke ta juyowa zuby fahimtar abinda yake faruwa yasa ta ta'be baki tace "bari inje zamuyi waya" kan shaati tayi magana ta fice cikin sauri rannan a had'e alamun fushi tayi ajiyar zuciya shaati ta sauke kan tayi kitchen ta ajiye ledojin ta fito zuwa d'akin yaran tana tura kofa taga Sameer da neeha na guje guje sanye da kananan kaya dukkansu girgiza kai tayi tana amsan neeha da ta fad'o jikinta tace "kid's I have a surprise for you".


Duk kanta sukayo har arwa dake sanye da English wear amma riga da skirt, Yasmin dake sanye da riga da wando tace "wow maami what surprise? I know your surprise is very special" Arwa tace cikin sanyinta irin na mahaifiyar tace "maami fad'a da sauri am eager to hear" murmushi tayi tana cewa "ku biyoni" Da sauri suka bita suna dariya.


Direct d'akin babansun tayi dasu tana tura kofan tace "surprise...." ihu sukayi gabad'aya sukayi kanshi suna "oyoyo paapa" mikewa yayi suka rungumeshi gabad'aya cikin farin cikin ya d'aga neeha ya rungume yana jin son yaran nashi har ranshi. Murmushi tayi kawai ta juya kitchen ledan da ya shigo dashi ta duba order ne daga wani elegant restaurant, fried rice with chicken plates da spoons ta d'ibo na mijinta daban daga ka gani zaka san na me gidan ne don kyaunsu a dining ta shirya ta zubawa kowa nashi package d'in a plate ta kawo musu ruwa da drinks.


Seda ta tabbatar komai intact kan ta koma room d'inshi ta samu sun baje suna ta zuba mishi labari tana shiga ta kama kwankwasonta tace "guys food is ready" duk mikewa sukayi suka biyota suna me cigaba da mishi hira yana amsa musu cikin sakin fuska, kowa ya san sit d'inshi a dining so zama duk sukayi suka fara ci Bayan sunyi bismillah a fili.


Tunda suka fara ci ba wadda ya kara magana har suka gama arwa ce ta tattare kwanonin ta kai kitchen tana dawowa paapa yace "oya kuje ku sanyo hijab zamu fita" Da gudu duk sukaje suka d'auko kananun half sunnah d'insu suka sanyo kan su dawo suka samu paapan da maami na hiransu tana tambayar shi Ina tsarabansu, yace "yana car kin san ko akwatin ban fiddo ba".


Tace "Ina kukayi ni ba'a gayyata ta?" Murmushi yayi yace "yi zamanki ki mana gadi gidan yakumbo zamu je Daga nan zamu je gidan Anty tala se ya sukaina duk wai suna son ganina" dammm haka gabanta ya fad'i kallon Arwa tayi se tayi saurin kawar da kanta tausayin yarinyar na kamata ta san bazata dawo cikin farin ciki haka ba, ita karan kanta Arwan seda gabanta ya fad'i Jin sunan mutanen nan amma bazata iya cewa paapa d'insu bazata ba, cikin kawar da damuwanta tace "a gaidamin su sossai" shi karan kanshi ya san bazata ji daad'in hakan ba amma basu da wani option baze watsar da mahaifiyarshi da yayyunshi sbd ita ba.


Sallama ta musu suka fice ita kuma ta zube kujera tana sauke ajiyar zuciya me nauyi a fili tace "Arwa ba laifina bane Ki yafemin" ta jima nan kan ta tashi ta koma d'akinta ta kwanta bayan ta gabatar da sallar azahar ba jimawa bacci ya kwasheta.  *tou fah my readers  ganinan Tafe da wata salon ban ce yafi na kowa ba amma believe me salon na daban ne, a sha karatu lafiya*2

                   🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA...💦🍇

*•Baya chanza d'and'anon teku•*


**Fatima Muhammad Gurin**

*Gureenjo6763 on wattpad*


'Yar Mutan Adamawa


*P2*


Tunda suka fara tafiya ta dukar da kanta kasa gabanta na tsananta fad'uwa yarinya karama er shekaru 9 har ta san wani fad'uwar gaba ganin shirunta yayi yawa ne yasa shi kallon ta ta mirror ya kuma kalli yasmin da itama gabad'aya bata son zuwan nasu gidan en uwansun sbd abinda suke yiwa arwa, cikin sanyi yace "Arwa, Yasmin hope we are safe?" Kallon mamaki suka mishi yace "yes nah.. yadda ake hararanmun nan se kace ba lafiya ba ko Neeha?".

Kai ta gyad'a Arwa ta waro ido yasmin na dariya tace "paapa ni kam dae ban harareka ba sede In Adda arwa" Da sauri arwa tace "Allah nima paapa ban harareka ba" nan fah yace firr sun harareshi suma suka tsaya a sam basu harare shi ba, wannan hirar ce ta ja har suka manta inda zasu sunayi suna dariya yana taka birki neeha ta fita da gudu ta fad'a gidan tana kiran "yakumbooo".

"Eyehh d'iyar arzikice gidana? Kishiya me ban haushi, uwar masu gida da alamu da malam kike ko? Don in ba shi wannan ballagazazziyar uwarkun ba kawo ku zatayi ba".

Itade neeha tayi lub jikinta bata ma san zancen me takeyi ba shigowar Saif da sallamane hannunshi rike da hannun sameer yasa tace "ahappp Ai na fad'a Sannu malam maraba lale sannu da zuwa..."

Kanshi ya dukar yana me tsugunawa kasa yace "Ina yini hajiyata?" Tace "Lafiya klau malam ya wajen aikin?"..

Yace "Lafiya klau mun sameku lafiya?" Zatayi magana kenan ta d'aura idanunta kan Arwa da Yasmin yafito yasmin tayi tana cewa "ke zo nan rabu da wannan 'bara gurbin ki zo nan munafuka me halin uwarta ke kam na kusa yafewa wanchan shegiyar ke daga cikin jikokina".

Yasmin ta matso a hankali idanunta na zub da hawayen tausayin yayarta tazo kusa da yakumbon ta zauna, kwafa taja ta kalli sameer tace "me gida na karfen ina shefane na ne?".

Murmushi ya saki kawai yana kallon Adda arwa da ta duka bakin kofa, cikin sanyin murya saif yace "Arwa karaso mana" cikin karaji yakumbo tace "ta karaso inaa? Bade gidana ba sede naka da ta fi wayau, ke fice min daga gida kar In tashi In karya kafanki da wani fuska kaman na shed'an".

Da sauri Arwa ta fita jikinta na rawa, Yasmin ma ta mike zata fita yakumbo ta jawota "ke wai yaushe nayi sa'a da ubanki ma bare ke da zaki nunamin wai zuciya, daga ke har ita kunci munafukar uwaku fitsararru kin kusa dawowa gabana In har haka zaki ci gaba dayi inga ta karyar soyayya, wawiya kawai".

Saif yace "yakumbo dan Allah ki dena haka ba Don ni ba a dinga abu ana duba gaba ba'a san me ze haifar ba, ba wadda yafi karfin kaddara ba fata ba kina da jikoki k...." katseshi tayi da "Kai dallah rufemin baki mijin tace wato an wanke maka ka shanye kai gaka me zuciyar imani da tausayi, ba laifinka bane, aikin asiri ne tashi ka tafi ka ban wuri" jiki a sanyaye ya mike In har ze zo gidan yakumbo da yaran nan se ranshi yayi mugun 'baci a koyaushe.

Hannu yasa a aljihu ya zaro kud'ad'e masu yawa ya ajiye mata kan ya wuce shiyar kishiyarta innani mata me fara'a da hakuri ta shanye duk wani wulakancin yakumbo tun Alhajinsu na raye tana kuma sha har yanzu da yake kushewa "lale maraba da manyan gari saifullah kaine", yana zama yace "nine innani mun sameku lafiya?" Tace "Lafiya kalau Alhamdulillah ya wurin su shaati? Ina Sauran yaran?".

Yace "suna wurin yakumboo" mikewa tayi tana kwalawa er autanta kira "Sumayyah! Sumayyah" yarinyace ta fito da bazata wuce shekaru goma ba kusan sa'an arwa da gudu ta rungume Saif "Yaya oyoyo" yace "oyoyo sumayyata ya school?" Tace "fine" innani tace "Sumayyah je maza kira Arwa" Da sauri ta fice don Arwa kawartace sossai class d'insu d'aya, ita kuma innani sanin halin yakumboo yasa ta aika a kirata kila tana chan tsugune kofar gida.

Aiko chan ta sameta hannunta ta kama suka shige shiyar yakumbo zuwa na innani a lokacin har innani ta kawowa Saif ruwa da drinks ya kuwa sha yana kallon Arwa da ta zauna Shiru cike da damuwa, mikewa yayi yana ajiyewa innani kud'i daidai yadda ya ajiyewa yakumbo yace "zamu wuce innani, ga wannan ban samu riko muku komai ba" cikin kula tace "Ai da baka wahalar da kanka ba saifullahi me ka ragemu dashi? Tun kan malam ya rasu ka d'auke mana nauyin komai, har bayan rasuwarshi baka fasa ba, Ba abinda muka nema muka rasa da ka ajiye kud'inka kila ya maka wani anfani" cikin ladabi yace "innani munyi waya da Sulaiman yake cemin ya kusa gama service ya rabu da kasar arnan nan" ya karashe yana dariya tuna yadda Sulaiman ke mitar kabilancin arna.+


Ta gane so yake ya kau da maganan hakan yasa tace "eh saura sati biyu yace min, anya ma ze sameka gari?" Yace "a'a Don sati guda kawai zanyi in koma" Tace "Toh Allah ya taimaka ya bada sa'a" yace "Ameen Adda Arwa mu tafi ko?" Mikewa tayi tana kirkiro murmushi tacewa innani "se anjima" innani ta bita da kallon tausayi.

Bata shiga shiyar yakumbo ba se mota da ta wuce mintuna kad'an se gasu sun fito duk suka shiga, yaja se gidan Anty tala dake unguwan hayin banki wacce Arwa tafi tsoro duk duniya itace first born d'in yakumbo se Ya sukaina se paapa yayinda innani ke da ya sulaiman me bin paapa se Anty Aisha se auta sumayya, hawaye ta fara wadda hakan ya sa Saif fara dana sanin tahowa dasu har ga Allah yana son en uwanshi su d'auki arwa yadda suka d'auki su yasmin amma sun kasa tun tana karama suke mata mugunta har kawo yanzu da ta fara banbance tsakanin me kyau da marar kyau.

"Arwa kuka kuma?" Ya furta yana kallonta da sauri ta share hawayenta tace "a'a Paapa abune ya fad'i a idona" ta juya wurin yasmin tace "Yasmin hure min" murmushi kawai yayi na takaici wai Arwa ke mishi wayau, hannunta ya kama suka bi bayan su neeha da sameer da tuni sun shige, da sallama ya shiga matar ta fara taranshi da dariya ganin arwa yasa ta had'e fuska kaman an mata albishir da shiga wuta, Arwa ta d'aga kafa kenan da niyyan taka Australian carpet dake parlorn matar ta saki salati.


"Ke! Ke!! Ke!! Karki kuskura ki takamin carpet ban shirya bada wankinshi ba tsaya nan kan tiles shi be da wahalan gogewa" babban d'anta da yake da 16yrs ne yace "haba mommy wallahi kin tsoratani, dan Allah menene In ta taka se kace mu ba takawa muke ba?" Tace "dallah rufemin baki har had'a mu kake da wannan najasar? Ka kuwa sa..." Saif ne yace "Anty...." yadda yayi maganan zaka tabbatar ranshi na 'bace da action d'inta inda Arwa ke tsaye nan shima yake ko motsi ya kasa.

A kausashe ya nuna mata yaranta 'yan mata uku bayan babban yace "Aisha, hajara da zuwaira duk basu wuce Allah ya jarabcesu kaman yadda ya jarabci karfin imanin Aisha ba, In har haka zaki ci gaba dayi wallahi Anty zan dena taka kafana gidanki kenan In har zaki ki Arwa Toh zaki ki Yasmin, neeha da sameer har ni kaina ma.."

Arham babban d'anta ne yace "uncle kayi hakuri please" hawaye Anty tala ta fara tana cewa "Lallai Saif ka riqa ni zaka zo gidana kana gayamin munannan kalamai kana had'a 'ya'yana da zuriyar matarka sbd an wanke an baka ka shanye.... to yayi kyau shikenan, maganan yakumbo ya tabbata Allah sarki da baba na nan na tabbatar se yayi nadamar abinda ya aikata..."

"Anty kina tunanin akwai ranar da zata zo nayi nadamar auren Aisha? Never in shaa Allah, Ina sonta so na tsakani da Allah Sannan Ina kara sanar muku ku guji hakkinta ya juyo muku, Sameer, Neeha ku wuce mu tafi" dama yasmin na bayanshi juyawa kawai tayi shima ya juya suka fice Arham se kiransu yake, a zuciye ya bugi siteri yana sauke numfashi yaushe wannan pentin ze goge ne a idanun en gidansu? Yaushe matarshi zata zama kamar kowacce surka?.

Sbd yadda ranshi ya 'baci fasa zuwa gidan ya Sukainan yayi ya d'auki hanyar gida, cikin sanyin murya yasmin tace "paapa mu biya gidan Anty Aisha kan muje gida please" kallon Arwa yayi yace "Arwa muje?" Cikin sanyin murya tace "A'a paapa please muje gida kaina na ciwo" yasmin da sauri tace "sorry Adda" Kai ta gyad'a mata sameer da neeha ma sukace "sorry Adda" suma kai kawai ta d'aga musu.

Suna parking a gidansu dake unguwan sarki Arwa ta fice da sauri ta nufi room d'in Maaminsu tana shiga ta ganta kwance da alamu tashinta kenan daga bacci don ga idanunta nan sun nuna, fad'awa jikinta tayi kawai se ta fashe da kuka me tsanani har jikinta na rawa cikin kuka tace "maami please ki fad'amin me nayiwa su yakumbo ne basa sona kaman su yasmin? Me nayi?" Ta maimaita tana kuka, hawaye ne ya gangarowa shaati ta runtse idanunta da karfi tana furta "ya Allah na tuba, ka saukakawa 'yata rayuwarta ka bata daman rayuwa irin na kowanni yaro ya rabbi bata da laifi" tare da fashewa da kuka itama rungume da Arwa.

Suna cikin kukan ya shigo da sallama tare da tura kofan ya rufe a natse ya tako yazo gaban gadon ya zauna tare da sa hannunshi bayan shaati yana shafawa, Shiru tayi tana me share hawayenta a hankali ta d'ago Arwa tace "ba abinda kikayi kinji? Kuma su yakumbo suna sonki kaman yadda suke Son su yasmin suna 'boyewa ne sbd ke d'iyar fari ce kinji?" Kai ta gyad'a ba don ta yarda ba yanzu ta fara wayau ta san wad'annan kalaman har ta haddace sbd kullum In ta tambayi maaminsun amsanta kenan.

Mikewa tayi ta fice tana share hawaye, share fuskanta tayi da murmushi ta kalleshi tace "har kun dawo kenan, ni kam ma bacci nayi bari in wanko fuskana inzo Musha  labarin Abuja da en matan da kayi" ta mike ta shige toilet murmushi ya saki ya jima da sanin Shaati bata ta'ba yadda ya fuskanci damuwanta ko yanzu ze kamata tana kuka zata wayance ta shigo da wasa cikin lamarin.

Tana fitowa yayi saurin kara waya a kunne yace "babyy na gayamiki Ina gida kar matata ta kamani" Da sauri ta karaso ta fisge wayan tare da juyowa se taga ko haske babu alamun wasa yake mata, bubbuga kafa ta fara tana d'an dukanshi kama hannunta yayi yana dariya yace "Anty kishi ke fa kikace zakiyi kizo In baki labarin 'yan matana" Tace "na fasa bana son ji" ta mike ya kama hannunta nan fa ta fisge ita a dole tana fushi, da hanzari ya janyota jikinshi yace "ke d'aya ce tal a zuciyar saifullah Aisha daga ke ba Kari In shaa Allah".

Ta'be baki tayi tace "na ji amma fah ban amince ba" shi kuma yace se fa ta amince nan suka fara wasansu irin ta masoya waennda sukeyiwa junansu son da be da misali be da tamka.


HAYIN BANKI


"Wai mommy fisabilillahi me Arwa tayi muku ne? Dan Allah ina son ji me yasa baku sonta daga ke har Anty Sukaina da yakumbo?" Cikin fad'a tace "zo ka matseni se in fad'a maka, kaga ka kiyayeni fah Arham ka kiyayeni da shiga abinda ba'a saka ba, In baka tayani kin abinda nake ki ba kar ka kuskura ka fara tunanin kayi girman titsiyeni".

Ajiyar zuciya ya sauke tausayin Arwa na ratsashi ya jima yana tausayawa yarinyar makarantansu d'aya a da yana kula da ita sossai ba kamar kannenshi da suke taya mahaifiyarsu tsanarta ba, be bari kowa ya ta'ba ta duk randa su Aisha suka kuskura suka fad'a mata bakar magana cikin irin wadda uwarsu ke fad'a mata kuwa se ya tabbatar yarinya ta fidda jini, sbd hakan ne yasa Anty tala tayi duk yadda zatayi tasa Abbansu fitar dashi daga makarantar future leaders aka maidashi Dembo.

         A zuciye ya mike ya fita driver d'insu ya kira yace "malam Musa zo ka kaini gidan uncle" mikewa malam Musa yayi ya nufi mota seda ya janyo zuwa tsakiyar gidan kan Arham ya shige suka fice se unguwan sarki seda ya cewa malam musa ya tafi abinshi In ya gama ko drivern gidan ze maidashi, da sallama ya shiga mai gadi ya amsa mishi seda suka gaisa kan ya shige cikin gidan.

     "Ya Arham" cewar neeha da sameer murmushi yayi musu yace "Ina Adda Arwa?" Neeha tace "suna d'akinsu da Adda yasmin" yace "oya go and call her for me" Da gudu ta mike tana ihun Adda Arwa Ya Arham is calling you, wadda hakan ya sa Shaati da Saif ji kallon juna sukayi kan suka mike a tare suka fito bayan ta d'aura d'ankwalinta yana ganinsu ya duka har kasa yace "Anty shaati Ina yini?" Tace "Lafiya kalau Arham ya makaranta? Ina su Hajar?" Yace "suna gida Anty, uncle Saif Ina yini?".


Yace "Lafiya kalau Amma mamanka bata san ka zo nan ba ko?" Yace "eh uncle but don na zo gidanka Ai ba wani abu bane" a zuciyarshi yace haka dae kake gani, Arwa ce ta fito tana murmushi tace "ya Arham" yace "kanwata" sukayi dariya a tare da alamu sun saba da juna sossai, ficewa Saif yayi yayin da shaati ta shige kitchen tana kiran yasmin, snacks ta had'a a plate da drinks tace ta kaiwa Arham dake ta hira da arwa yana bata hakurin abinda mom d'inshi tayi mata itade ta sake kuma taji daadin zuwanshi Don har ta mance da 'bacin ran da take ciki.


BADARAWA


Yakumboce rike da waya a kunne tana aikin gyad'a kai tana Jin bayanin da Anty tala ke mata da abinda ya faru gidanta da Saif ya zo, daga karshe ta d'aura da "Yakumbo wallahi In bamu d'auki mataki ba yarinyar nan na gab da rabamu da Saif haka na lura".

    Yakumbo da mamaki Tace "wato nine baze iya yiwa rashin mutunci ba se ku akan wannan bakar yarinyar me bakar fuska toh tunda ya fara muku kenan nima watarana ze gangaro kaina, ba matsala na san matakin da zan d'auka aure kawai zan nema mishi ya kara inga karyar soyayya"

      Sossai suka tattauna akan batun auren kuma da gaggawa suke so ayi daga karshe sukayi sallama ba tare da sun tsayar da yarinyar da ze auran ba akan se sun had'u.
                    🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA....💦🍇

      *•Baya chanza d'and'anon teku•*


    **Fatima Muhammad Gurin**

       *Gureenjo6763 on wattpad*


   'Yar Mutan Adamawa           *P3*


Weekend me daad'i suka gudanar kaman yadda suka saba In har ya zo weekends be cika zuwa ba shiyasa idan ya zo haka yaran suke matukar jin daad'i, sun ziyarci wurare daban daban a kaduna cikin so da kaunar junansu yau Monday, Bayan ta gama shirya yaran sun wuce makaranta suna me jin kewar baban Don sun san baza su dawo su sameshi ba neeha kam har da kukanta da kyar suka lalla'bata ta tafi.


Suna shiga parlorn ta rungumeshi tace "ni ma kaman in taya neeha kuka zamuyi kewarka" murmushi ya sake yana kissing forehead d'inta yace "yi hakuri kar kiyi In ba so kike in kasa tafiyar ba" tura baki tayi tace "Toh In ka tafi sai yaushe zaka samu shigowa?" Yace "ba rana" trolley d'inshi ta nufa ba tare da tace komai ba ta fara gyarawa duk abinda ta san ze bukata ta had'a mishi tsab ga kayanshi a shirye a goge gwanin ban sha'awa.


Wanka ya shige bayan ya fito ta taimaka mishi ya shirya ganin taki mishi magana alamun fushi take yasa tana gama gyara mishi zaman necktie ta juya kenan ya janyota jikinshi a kunne ya rad'a mata "tuba nake sarauniyata nan ba da jimawa ba zan zo In aiki ya min sauki ma next week se ki ganni kiyi hakuri kinji?" Murmushi ta saki tace "Yauwa hoorul Na'im ko kaifa da fa cemin kayi ba rana" yace "to yanzu akwai shikenan?" Kai ta gyad'a tana me mika mishi dark blue suit d'inshi kar'ba yayi ta sako gyale akan doguwar rigar atamphar jikinta tare da d'ago trolley d'in suka nufi waje.


Har jikin mota seda ya bud'e boot ya saka trolley d'in ya juyo da nufin shiga mota ta fad'a jikinshi ta kankameshi tare da cewa "zanyi kewarka rabin raina ka kula min da kanka please, karka manta da adu'ar matafiya Allah ya tsare min kai da tsarewarshi ya kare min kai daga dukkan wani abin cutarwa" yace "Ameen my dear, take good care of yourself and the kids I love you" ya saketa tare da fad'awa motar ya kunna ja baya tayi tana d'aga mishi hannu cikin kasa da murya tace "love you too".

Hannu shima ya d'aga mata kan ya ja motar kirar GLK 350 ya fice daga gidan ajiyar zuciya ta sauke kan ta koma cikin gidan zuciyarta na cike da kewar mijinta abin alfaharinta.

       Seda ya biya gidan yakumbo yayi mata sallama daga ita har innani kan ya wuce ya kama hanyar Abuja yana juya maganganun yakumbo akan karin aure, shi gaskiya baze iya ba, ba abinda shaati ta rage shi dashi ba ta inda ta Gaza ga kulawar ta gareshi da kuma yaranshi toh me laifinta a abinda Allah ya riga ya rubutashi tun daga randa aka halliceta? Yana sonta ba abinda ze iya ruguza wannan soyayyar da yake mata ba irin ruwan da Za'a kara akan kogin son da yake mata da ze iya chanza d'and'anon sonta a cikin ranshi, gaskiya baze iya yi mata Kishiya ba dama cewa yakumbo yayi ze yi tunani a kai toh da haka ze waske mata.3


Tana shiga d'aki taga wayanta na ta aikin haske alamun ana kiranta da sauri ta karasa tana dubawa taga "Ya Meenah" seda gabanta ya fad'i dukda zuwa yanzu komai ya wuce amma fah alakarsu da en uwan nata be koma daidai ba kaman da, receiving tayi tare da sallama ta d'aura da "ya meena ina kwana?" Daga d'aya 'bangaren tace "lafiya kalau ya yaran?" Tana d'an murmushi tace "suna lafiya sun tafi school" ya meena tace "yayi kyau amm wai kinji matar ya hameed ta haihu?" Ido ta d'an waro "ta haihu??? Wallahi banji ba yaushe?".

    Ya meena tace "har jibi suna ban san ai bakiji ba, an samu d'a namiji" jikintane taji yayi sanyi idanunta suka cika da hawaye wai se yaushe en uwanta zasu mance da abinda ya riga ya faru? Ta san bata da laifi tunda duk abinda ya faru ba da son ranta bane ba itama ba yadda ta iya ne sbd bata da wani wayau da dabara, ya meena ce ta katseta da cewa "hello" jin shirun yayi yawa cewa tayi "arhmm inaji Masha Allahu, Allah ubangiji ya raya bisa sunnah bazan samu zuwa barka ba tunda se yanzu nakeji gashi yau babansu neeha ya koma wurin aiki, zan tambayeshi zuwa sunan In shaa Allah" ya meena ta d'anyi jimm kan ta ta'be baki tace "Toh Allah ya kaimu a unguwan rimi za'ayi bukin sunan, Se anjima" bata jira cewarta ba ta katse kiran.

Rike wayan tayi a hannunta hawaye na gangaro mata bata san sadda kuka ya kwace mata ba sossai take kuka tana tsinewa wanzuwarshi a duniya adu'a take yi kullum ba dare ba rana akan Allah ubangiji ya saka mata ya bi mata hakkinta na tarwatsa rayuwarta da yayi, vibration d'in da phone d'inta ya d'auka ne yasa ta goge fuskanta tana kallon fuskan wayan "Maamah" ta gani rubuce fuskan wayan da sauri ta d'aga da sallama.

      Amsata mama tayi daga d'ayan 'bangaren kan ta d'aura "Lafiya naji muryanki haka?" Tana gyaran murya tace "Lafiya kalau Mama Mura nake, Mama ya gidan?" Mama tace "Lafiya kalau, Aisha me ya faru baki kira yayanku hameed kin mishi murnan haihuwa ba ya zo nan ya isheni da mita? Sannan har cikin gida naji ana cewa kinki zuwa barka?" Wasu hawayen ne suka gangaro mata kowa laifinta yake jira a gidan cikin muryan kuka tace "ban sani bane Mama yanzu Ya meena ta kirani take fad'amin wallahi ban sani ba" Shiru Mama tayi na d'an mintuna kan cikin sanyin murya tace "Toh me na kukan kuma?" Shesheka ta fara cikin rawar murya tace "wai se yaushe zasu gane bani da laifi a duk abinda ya faru da rayuwa na?" Ta karasa da kuka sossai tana d'aurawa "kowa fah Mama jira yake nayi wani abu da za'a samu na jifana dashi a cikin family yau na godewa Allah ba don ya turomin saif a rayuwana ba da ban san halin da zan shiga ba, na sani Mama kema har yanzu baki d'aukeni shaatinki na da ba...." katseta Mama tayi "kayya Aisha komai ya riga da ya wuce, yanzu ki dena kukan nan ki kira hameed ki mishi murnan samun karuwan da yayi in da hali kije musu barka ko gobe ne inde mijinki ya barki kenan In kuwa be bari ba ku had'u anan suna jibi kinji?" Kai ta gyad'a sukayi sallama.1


Seda taci kukanta kan ta fara neman numbern yayan nata tayi dialing seda ya kusa tsinkewa kan ya d'aga sallama tayi ya amsa mata ta gaidashi ya amsa a dakile tace "ashe kuma mun samu karuwa?" Yace "eh" Tace "Toh Allah ya raya bisa sunnah yasa me taimakon addini ne" yace "Ameen" daga haka ya kashe wayanshi wayan tabi da kallo wasu hawayen suka kuma zubo mata tabi wayan da kallo kaman ba favorite yayanta ba, kaman ba sune sukayi wani shakuwar da zaka d'auka bazasu ta'ba samun sa'bani ba har duniya ta nad'e tana kewarshi tana kewar dukkanin shakuwarsu da en uwanta da yanzu babushi.


Bata san iya adadin lokutan da ta d'auka zaune a wurin ba seda taji wayanta na kara dubawa tayi se taga video call daga habeebinta mikewa tayi da sauri ta shiga toilet ta wanke fuskanta sossai ta fito ta sa kwalli tare da shafa powder kad'an yadda ze 'boye kukan da taci kan ta d'auki wayan lokacin har ya mata two missed calls.

Kiranshi tayi itama video call ringing biyu ya d'aga tar yake kallonta itama haka yana zaune cikin mota juya idanunta tayi tace "yalla'bai barka da hanya" yace "Yauwa yalla'biya" dariya tayi idanu ya kura mata a zuciyarshi yace tayi kuka, katseshi tayi da cewa "sorry kayi two missed calls bana kusa" yace "naga baki kira lokacin da kika saba kira kiji ya hanya ba In har na bar gida shiyasa na kira inji ko Lafiya?" Murmushi ta sake tana cewa.

"I'm so sorry wani d'an aiki ne ya rikeni" ta'be baki yayi yana d'age bakin girarshi me cika yace "aikin har ya Fini ko?" Tace "a'a ya ma isa? Yanzu de ayi hakuri please Sannan a maida hankali kan hanya Allah ya tsare bye" bata jira cewarshi ba ta kashe ta san In ta biye mishi Haka zasuyi ta waya ita kuma tana tsoron kar wani abu ya sameshi tunda ba parking yayi ba yana tafiya ne kuma yake wayan da ita.


Ajiyar zuciya ta sauke tana jinta wasai sbd ganinshi kawai da tayi yasa duk damuwarta sun yaye mikewa tayi ta nufi kitchen da shirin sama musu abinda zasu ci na rana don en school sun kusa dawowa. Jollof rice ta musu na manja da wake Don ta san duk suna so yaji kifi ta juye a food flask babba ta kai dining tana ajiyewa suna shigowa da murnanta ta tarbesu itama kaman yarinya a cikinsu da kanta ta kaisu d'aki ta chanzawa neeha da sameer kaya neeha na ta damunta da surutun abinda ya faru a makaranta tana amsawa bata gajiya da magana da yaran nata Don In har mijinta baya nan Toh fah sune abokanta bata zuwa ko Ina koyaushe suna tare shiyasa sukayi muguwar shakuwa.


Suna fitowa Arwa da yasmin na fitowa suma sun chanza zuwa kananan kaya dining suka wuce arwa tayi serving d'in kowa suka fara cin abinci Bayan sun gama yasmin ta tattare kwanukan ta kai kitchen da gudu neeha ta koma d'aki ta d'auko tab d'inta ta kira paapa d'insu video call aiko ya d'auka gashi zaune a parlornsu na Abuja har yayi wanka ya sauya kaya da murna suka fara mishi surutu wannan ta fad'a wanchan ta fad'a wannan ya fad'a.

      Murmushi kawai shaati ke yi tana kallonsu dukansu basa gajiya da juna basa ta'ba gundurar juna In har ba abinda yakeyi zama yake ya ta zuba surutu da su kaman ba mahaifinsu ba dukda idan ya juya duk tsoronshi suke amma sun shaku matuka dukda ba kasafai suke zama gabad'aya ba idan ba anyi hutu sunje Abuja gabad'aya ba ko ya samu saukin aiki ya taho gida ba, hannu ya d'aga mata yace "wato baza'a min magana ba ko?".

         Murmushi tayi tace "ruhool na'im fah magana kake da sarakan surutun nan Ina naga sararin maka magana?" Kallon yaran yayi yace "Toh fah kunji malamai ku kyale mata zatayi waya da mijinta" dariya sukayi duka har neeha kaman ta san wani me mata da mijin ke nufi Arwa kaucewa tayi ta kama hannun neeha tace "baby zo muje kiga abinda na sayo miki a section d'inmu" da sauri ta mike ta bita sameer da yasmin ma suka mike suka bisu da sauri yasmin na cewa "Ai yau Allah Adda baku isa ba kullum neeha kawai kike sayowa abu In har baki sayo mana ba nata zamu kwace ko sameer?" Yace "yes Adda yasmin" suka shige.


Kallon da yake jefanta dashi ta kawar da "ka isa Lafiya?" Yace "Alhamdulillah me akayi ne?" Ta san abinda yake nufi da hakan, ba wadda ya fishi saninta nan duniya a yanzu ko maamah kuwa so yake yaji dalilin kukan nata da sauyin yanayinta Don har lokacin bata dawo daidai ba duk ta sawa kanta damuwa sbd tunanin abinda zata fuskanta In taje suna amma ya ta iya? Dole taje In ba haka ba ta shiga bakin duniya.


"Babu" ta amsa tana murmushi yace "ban yarda ba" Tace "Yauwa matar ya hameed ta haihu ya samu d'a namiji jibi suna" a zuciyarshi yace so that is it, cewa yayi "Allah ya raya da dare se kuje da yaran kiyi mata barka habu ya kaiku kin san ban son driving d'inki da dare" Tace "Ameen" tana murmushi ta d'aura da "roohul na'im ka kuwa ci abinci?" Shafa cikinshi yayi tare da karkata kai yace "inafa na ci ni da banda wadda ze bani" murmushi tayi tace "please ka fita ka ci kar a bar min ciki da yunwa" jiyo ihun neeha da kukanta yasa tace "uhm toh an ta'ba min d'iya bari naje naji ita da waye, please ka fita kaci kaji love?" Kai ya gyad'a yace "se munyi magana" ya kashe wayan da sauri ta mike tayi d'akinsu Arwa da ipad d'in neehan hannunta.

                     🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA...💦🍇

    *•Baya Chanza d'and'anon teku•*


**Fatima Muhammad Gureen**

    *Gureenjo6763 on wattpad*


                'yar Mutan Adamawa


     *P4*


Juyi kawai take akan yaloluwar katifarta idanunta na kallon azaran d'akin da ko arzikin silin be samu ba tsaki taja tare da kallon wayan hannunta da ya bani asalin mamaki wadda ya kasance iPhone 11 pro max, ta kuma jan tsaki tare da mikewa daga ita se zani d'aurin kirji yayinda kanta ba d'ankwali kitson attachment d'intan nan har kan d'uwawu fitowa tayi tana fad'a da kofar yaloluwar katako na d'akin tana cewa "ni Wallahi na gaji haba talauci har yayiwa mutum katutu In ba samarina suka bani kud'i ba da se ni ma inci wannan bakar tuwon da inna ke ci, shi baba ba ruwanshi kullum yana yawon cin abinci a waje".

               Tsaki ta kuma ja tana cewa "Allah yau se an yi ta ta kare baba se ka san yadda kayi da ni akan wadda nake so" tareta mamanta tayi a kofar zaure ita innan na shigowa yayinda ita kuma take fita "a'a Lafiya zubaida Ina zuwa a haka?" Cewar inna, juya keya tayi tace "wurin baba zani in nima se na biyashi ne kan ya min aiki zan ji haba tun yaushe nake binshi akan wadda nake so na gaji da zaman akwalan gidan nan wallahi".

      Ta'be baki inna tayi tace "ku kuka jiyo" tana wucewa taji zubaida na cewa "idan ai na auri me kud'in ku zaku dinga min tururuwa a kofar gida" ta shige zauren, baban na zaune wata mata durkushe gabanshi tana ajiye mishi makudan kud'i tare da mikewa tace "to me yankan wuka dan Allah inga aiki da cikawa na sanka sarai bazaka watsan kasa a ido ba" dariya baba yayi yace "karki damu mune fah zakiga aiki jeki kawai".

     Ficewa tayi yayinda baban yayi saurin kwashe kud'ad'en ya turasu cikin babban riganshi ta'be baki zuby tayi tana zama tace "baba ya batun aiki na? Ni fah na gaji wallahi na gaji da rayuwar bakar gidan nan kayi min aiki a kan wadda nake so ko In san matakin da zan d'auka wadda baze muku dad'i ba ehe".+


Hararanta yayi yana cewa "Toh fitsararriya marar kunya kin san bana aikin banza In har kina son aiki ajiye kud'i" itama rama hararinta tayi kan tace "idan fah kayi aikin nan kune da riba amma ba komai zan biya amma ka tabbatar na shiga gidan nan karku saka ran samun ko biyar" a zuciye ta mike ta koma d'akinta ta d'auki tsadaddiyar handbag d'inta ta bud'e ta d'auko rafar 500 ta juya ta koma zauren ta dangwarar mishi washe baki yayi yana cewa "yanzu kike zance d'iyar nan ya ma kika ce sunanshi?".

"Saif shamsuddeen suraj".1


*******


"maamah! Mamaah!! Maamah!!" Farar dattijuwar dake zaune saman sofa idanunta sanye da medicated glass tace "oh ni fad'imatu zasu karar da sunan In shigesu" dariya dattijon da shima ya kasance fari sol yayi yace "ah gwara ai ko zasu samu shiga a wurin mijin nasu da kika kwace" ya karasa yana dariya itama dariya tayi a daidai lokacin da Arwa, Yasmin da neeha suka shigo parlorn suka fad'a jikinta suna dariya.

"Kai me haka? Maza ku sauka tunda kuma ba wadda ya karya muku kafata" Shaati da ta shigo hannunta rike dana sameer ta fad'i, sauka sukayi suna turo baki kallon Abba da sukayi yasa suka washe baki Arwa tace "laa Abba yaushe ka dawo?" Yace "d'azunan khadijatul kubra" tana son sunan hakan yasa ta kuma washe baki tace "toh Abba sannu da hanya ina yini?" Yace "Lafiya kalau ya makaranta?" Tace "lafiya Abba" yasmin tace "ni ba'a ganni ba ai" tana turo baki.

Yace "ah na isa? Me sunan uwar muminai, uwata kuma uwar gidata?" Mamah tace "Lallai Alhaji ni kuma fah?" Dariya sukayi a sanda neeha ta koma wurin shaati dake zaune kasa tace "maami Abbanki wai baya so na" ta kare da turo baki, Abba yace "na shigesu fad'imatu sharri zaki min?" Suka kuma yin dariya shaati tace "Abba kyale yaran nan ka biye musu se su saka surutu Ina yini?" Yace "Lafiya kalau uwata ya gidan naki? Tace "Lafiya kalau ashe kuma mun samu karuwa" yace "eh" Tace "Toh Allah ubangiji ya raya" ya amsa da "Ameen thumma Ameen" juyawa tayi ga maamah tace "maamah mun yini Lafiya?" Tace "Alhamdulillah, kai miskili kafi mahaukaci ban haushi baka iya gaisuwa bane?".

Abba yace "ke kuwa wai miskili kina ganin yaro kyakyawa fari sol son kowa kin wadda ya rasa zo nan sameeru" ta'be baki maamah tayi tace "ku kuka jiyo".

Mikewa shaati tayi tace "bari In je wurin me jegon" maamah tace "Toh se kin juyo akwai maganan da nake so muyi kuwa" Tace "Toh" tana fita dayake gidansun katoton family house ne kannen babanta da yayyunsu da matansu da 'ya'yansu Sannan a cikin 'ya'yansun ma akwai wadda sukayi aure aka ware musu part part duk nan cikin gidan sede gini ne irin na zamani ko wanni part da irin colour d'insu ginin wajen gidan ne kawai aka zagaye da color guda wato milk haka gate d'in ma katoton iron get ne milk color.

'Dakinsu ne kawai babu wadda yayi aure a cikin gidan gari suka shiga abinsu, sbd matsalolin gidan yawa ne dashi ga shegen kishi irin na balbali da suka d'aurawa kansu.


Direct part d'in da ta san zata samu uwar jego ta nufa wato part d'in hajja kakarsu don duk wacce ta haihu inde 'bangaren namiji ne a gidan to a part d'in hajja zata zauna har bayan suna kan a dankata da danginta In tayi arba'in ta koma gidanta, gabanta na fad'uwa ta bud'e kofan parlorn hajjan da sallama hajja dake zaune ta amsa kan ta d'aga Kai ta kalleta tare da ta'be baki tace "au ashe 'bara gur'bin jikata ce, Sannu me suna uwar kazafi".

Had'e rai tayi tace "kinga wallahi In ba  kya so In shigo shiyarki ne se in koma, Haka kawai kuyi tayiwa mutum kallon makaryaci Alhalin kun san ni Aisha karya ba d'abi'ata bace... ba damuwa komin daren dad'ewa gaskiya zatayi halinta kuma karki ce zaki nemi yafiyata na gayamiki Don bazan yafe ba ehe".

Ta san In ba hakan tayiwa tsohuwar ba ba kyaleta zatayi ba, turo d'ankwali hajja tayi gaban goshi tana ta'be baki tace "hmm mutum de ya ringa jin tsoron me duka, ba Don bawan Allahn nan saifullahi ya taimaka ya aura min ke ba da ban san yadda zanyi ba ga Alhajijo baya nan bare in ce ya had'amu ya aure".

Ko kallonta shaati bata karayi ba ta shige d'akin da ta san zata samu me jego d'akin cike yake da mutanen gidan kusan duk sa'anninsu Don itama me jegon mujeebatu kawartace a da kut da kut sede yanzu halin rayuwa ya rabasu.

Sadiya d'iyar baba sale ta amsa tana d'aurawa da "ashe kina nan tafe na sha bazaki zo ba ai ganin har jibi suna".

Murmushi kawai tayi tace "se gani ko? Ya kuke?". A yatsine duk suka amsa girgiza kai tayi ta karasa bakin gadon me jegon Tace "mujeebatu kin sauka lafiya? Toh Allah ubangiji ya raya ya dayyaba" ta sa hannu zata d'auki yaron da sauri mujeebatu ta kawar tana cewa "Ameen In ya kai zuci" hafsah diyar baba haladu tace "aiko dae ku da ake gaba daku Ina za'a muku fata na gari daga zuciya" Zainab d'iyar baba habu tace "ko kuma ayi muku sharrin zina ba ta d'auka kowa irinta ne 'bara gur'bi marar tsoron Allah".

Shaati zatayi magana kenan hajja ta katseta da ta jima tsaye bakin kofan tana jin abinda suke cewa tace "mujeebatu maza bata d'an nan, hafsah, sadiya, Zainab ku kiyayeni na gayamuku kun isa hanata d'aukan d'an da ma ta fi ku hakki a kanshi? Bana son haka kuji da kyau ba a gidana ba, ke kuma ki zauna sakara dake kina biye musu kina musgunawa kawarki da da baki da kamanta".

Dangwarar da yaron tayi tana gunguni su sadiya suka mike gabad'aya suka fice suna kananan maganganu kasa d'aukan yaron shaati tayi se juyawa da tayi ta fice da sauri hajja na magana amma taki tsayawa bata yada zango ko Ina ba se part d'insu direct d'akin Mama ta wuce Bayan ta wucesu a parlor.


Mikewa mama tayi ta bi bayanta a bakin gado ta ganta zaune tana haki idanunta a runtse alamu nema take tayi controlling kukan da yake shirin kubce mata cikin sanyin murya mamah tace "duk me hakuri yana tare da riba watan watarana gaskiya zatayi halinta ki ci gaba da daurewa komai me wucewa ne" bata san sadda kuka ya kwace mata ba cikin shesheka tace "maamah tsoro nake ji, Ina tsoron randa Khadija zata san gaskiya a wurin en uwana ko en uwan saif In ta tambayeni ban san irin amsan da zan bata ba maamah ya Isma'il ya cuceni ya ha'inceni Sannan ya sa an maidani makaryaciya ya rainawa kowa hankali....."

Maamah tace "kiyi ta hakuri Allah Ai baya d'aurawa bawa abunda yafi karfinshi ki ci gaba da adu'a tunda iyayenshi sunki DNA test har suna gaaba da mu da mahaifinki sbd hakan Tabbas duk damuwarki na shekaru 10 Aisha baki kaimu ba mu iyayenki kuma muna adu'a muna sadaka Allah ya cigaba da baki kwanciyar hankali yasa iya kaddararki kenan, tashi ku koma se kun zo sunan dare yayi".


Mikewa tayi tana share fuskanta tana fita parlorn ta had'a idanu da mahaifinta murmushi ya sakar mata me narkar da zuciya tana iya hango kararar damuwanshi da iyakar kaddararta da wannan fuskan take ganinshi har yau be ta'ba farin ciki har kasan zuciyanshi ba, hakan yasa wasu hawayen suka kara sulalowa, kasa ta duka ta mishi sallama cikin sakin fuska ya amsa mata da "Allah ubangiji ya kaiku lafiya, yayi albarka" ta amsa da Ameen kan ta mike ta sa su Arwa gaba suka fice.


*******


Rungume da wani bakin saurayi a jikin motanshi ba kunya ba tsoron Allah se shafata yake, basu hankara ba se ji sukayi an dalleta da fitila tsaki taja tana d'agowa a masifance ganin baba ne yasa taja wata tsakin cikin fad'a tace "haba baba ya za'ayi mutum na soyayyarshi zaka wani dalleni da touch light ko bashi kake bina?" Shima tsakin yaja yace "er iska kawai wawiya aikinki zan baki In kuwa baki so inyi komawata".


Da sauri ta saki saurayin da dama bata sakeshi don idon uban ba tace "ka ma isa? Bayan ka cinyemin kud'i? Muje ka bani" ta juya ga saurayin tace "jeebson mun had'e anjima zan zo gidanka" a gaban baban ba kunya yayi kissing lips d'inta yace "will be waiting for yhu honey" ya juya ya shige motanshi ya wuce, se mugun kallo baban ke jefanta dashi ta murgud'a baki tace "me??" Tsaki yaja yayi shigewarshi ta bishi.

            Kwalli ya bata da wani turare "Ai kin san gidan uwarshi, inde don shine bazaki ta'ba aurenshi ba, ki zizara kwallin nan ki fesa turaren nan kije kiyi mata ladabin karya shikenan kin shiga gidan kin gama".

     Tsalle tayi ta dire tace "ubana na kaina me yankan wuka aikinka na kyau se ma burina ya cika zan cikaka da goron wannan aikin".

   Yana wani bubbud'awa ya shige gidan tabi bayanshi, direct ruwa ta d'iba taje tayi wanka tazo ta shirya kaman wata arniya da wata shegiyar wando da shirt kai ko arzikin d'ankwali se wani hill da tasa kaman me shiga wuta, ta d'auki handbag d'inta zata fita innansu tace "ke zubaida kan ki fita ki bani er d'ari biyar mana da zan samu na karyawa, na tabbatar In kin fita mu da ganinki se gobe gashi wannan ta'babben yayan naki ko malam ba bani zasuyi ba".

      Cikin kunkuni tace "kede innan nan bade aukin maula ba nine mijinki ko baba" jakanta ta zuge ta d'auko d'ari uku ta jefa mata tace "ga abinda zan iya badawa nan, kinga tafiya ta" Da Harara innan ta bi bayanta kan ta d'uka ta kwashe kud'in tana mita.


**********


Washegari

Bayan ta sallami en makaranta sun tafi ta dawo da niyyan kwanciya kenan taji ana danna doorbell, seda ta yafa gyale kan taje ta bud'e cikin minti kalilan ta sake fuskanta cike da fara'a tace "oyoyo namesake" wacce aka kira da nameske d'in ta shigo tace "Ai nayi fushi namesake yaushe rabon inga kafanki gidana?" Girgiza kai tayi tace "afuwan 'yar uwa na san nayi laifi ayi hakuri ban samu dama bane".

    Namesake tace "haka kullum kike cewa" saukar da goyon bayanta tayi tace "rike d'iyarki ta isheni wallahi ga shegen nauyi"

  Kar'ban babyn tayi tana lekan fuskanta tace "ismatt en mata" kallon Aisha dake shirin zama tayi tace "namesake mu karasa room d'ina se yafi daad'in hira" karasawa sukayi tana ci gaba da cewa "kin kuwa san duk kwanakin nan tunaninki nake yi Allah ne kawai be yi ba da kin ganni"

       Aisha ta ta'be baki a daidai lokacin suka karasa ciki suka baje kan gado, nan fah hira ya 'barke Aisha kanwar Saif ce d'iyar innani kenan, tunda ta shigo familyn itace ta kar'beta kaman er uwa gashi akayi katari sunansu yazo d'aya, sun saba sossai Aisha na da aure d'iyoyinta uku, hira sukeyi sossai har Aisha ta gangaro kan abinda ya jima yake damunta "ni kam namesake duk zamana dake kin kasa bani labarin rayuwarki dukda yawancin lokuta Ina riskanki cikin damuwa".

Dib fara'arta ya d'auke idanunta suka cika da Hawaye cikin sanyin murya tace "namesake ba wani labari na daad'i cikin rayuwata se d'aci da damuwa, In na tuna ya Isma'il da abinda ya min ko ince yake kan min se inji kaman In nemi wuka in da'bawa kaina In mutu In huta, namesake labarina akwai sarkakiya da har yanzu be gama warwarewa ba, kowa kallon makaryaciya yake min abinda ni banayi...." kuka ne ya kwace mata cikin kuka tace "namesake kiyi hakuri bazan iya baki labarina yau ba sede In Shaa Allahu wata rana zaki ji mummunan kaddarana".

              🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA...💦🍇

     *Baya chanza d'and'anon teku*


    *Fatima Muhammad Gurin*

**Gureenjo6763 on wattpad**


           'Yar Mutan Adamawa

     *P5*


Gabad'aya se bata ji daad'in taa da maganan da tayi ba ganin duk mood d'in shaatin ya chanza hakan ya sa ta chanza maganan da "kin kuwa san sulaiman ranar saturday ze dawo? Yace in gayamiki In ya dawo ke zaki samar mishi da mata irinki".

    "Ai uncle sule da fitina yake, ko menene halin nawa da ya addabeni da mata irina?" Tayi maganan tana dariya, kukan da ruqayyah ta fara yasa shaati ajiyewa uwar ita tace "ji da innani bari in samo miki abin ta'bawa".

      "A'a wallahi a koshe nake seda nayi nak kan na fito dasu waleed na ajiyesu school yanzu ma chan gida nayi badarawa".

      "Haba dae namesake yaushe kika zo da har kike batun tafiya ba tare da kinci komai ba?" Cewar shaati.

"Ai gwara ni nazo d'in kefa? Yaushe rabon da inga kafanki?" Girgiza kai shaati tayi tace "na shiga uku da wannan mitan, zan tambayi yayanki In ya amince gobe kan In je Unguwan rimi se in biya in huta da fitina".

Dariya Aisha tayi tana cewa "Yauwa yanzu naji zance" ta mike tana goya erta, har waje inda ta ajiye motanta shaati ta raka ta sukayi sallama kan ta dawo cikin gida.

Seda ta d'an kakka'be gidan ta kunna burner tare da sa turaren wuta, jin wayanta na kara yasa taje gareshi da sauri ganin roohul na'im d'inta ne me kiran yasa ta kwanta tare da d'agawa fuskanta cike da farin cikin jinshi da kuma soyayyarshi "rabin raina" yace "na'am rayuwata ya kk?".

"Lafiya kalau ya office?" Yace "gashinan so boring duk kewanki ta isheni".

"Nima gani kwance cikin tsananin kewarka abokin rayuwa, me ake ci ne?" Cikin yanayin sanyi yace "breakfast nakeyi a office" "na tabbatar ba wani abin kirki bane pls a dinga bani abinci Ina koshi" cikin sanyin dae yace "ai In ni na koshi baki da matsala" "kenan ba'a damu da nawa cikin ba? Gaskiya ni ban yarda ba ni ai nafi muhimmaci tunda se na nema naka ze ci, tukuna ma me ke damunka ne roohul na'im?".

         "Me kika gani?" Tace "kaima ka san in kana cikin matsala ba se wani ya fad'amin ba rabin raina, muryanka kad'ai ta isa" yace "ba abinda ke damuna kuwa" kukan shagwa'ba ta fara wadda shi gabad'aya zatonshi na gaske ne tuni ya mike tsaye har yana had'a harshe wurin cewa "no! No pls ya isa naji Ina cikin damuwa na amince, kukan ya isa dan Allah".

         Cike da damuwa da ya bayyana kan fuskanta tace "me ya faru? Meke damunka?" Iska ya fesar kan ya zagaya ya samu sofa ya zauna, "Hayati maganan nan ki bari se na taho se muyishi" katseshi tayi da "se kuma ka zauna cikin damuwa har se ka dawo? Inaaa fad'amin yhu promised we will share our happiness and sadness no matter what".

     Cikin sanyi yace "promise me bazaki sa damuwa a ranki ba" Tace "I promise in shaa Allah".

"Yakumbo ke shirin sani a matsala Aisha" Jin ya kirata da sunanta hakan yasa ta san matsalan babbace da sauri ta mike tana cewa "subhanallah, Astagfirullah haba roohul na'im Ina ka ta'ba jin uwa ta saka d'anta matsala uhmm? Me akayi?" Lumshe ido yayi a zuciyarshi wace mace ta isa kamo darajarki a idona? Seda yayi Shiru na mintuna kan yace "aure take so nayi".+


Dib ta d'auke numfashinta ya tsaya chak na mintuna adu'a ta fara a zuciyarta nan taji numfashinta ya fisgo da karfi bata ta'ba jin irin abinda taji yanzu ba a rayuwarta ashe haka matan da akeyiwa Kishiya suke ji? Ashe haka suke fama da kunar zuciya? Wannan inaga mijin yana nuna zalamar karo auren ya kenan? Se kuma ta tuna gwara saura watakila a mutunce mijin ya samesu ba kamar ita ba da Isma'il ya lalata mata rayuwa harda tsaraba, kenan yanzu saif ze aure buduruwa ya 'bare kayan shi daga leda, kenan daga nan ze fara ganin bata da kima da daraja?.

     Bata san sadda ta kashe wayan ba cikin tashin hankali kuka kawai ta fashe dashi hankalinta yayi mugun tashi fiye da tunanin me tunani, a rud'e ta danna kiran wayan Mama nashi na shigowa tana katsewa har mama ta d'aga itama a firgice ta fara cewa "Aisha natsu natsu, Innalillahi wainna ilaihi rajiun" tayi ta maimaita mata, chan ta amsa ta fara yi, tukun ta d'an samu natsuwa.


"Maamah aure, aure Saif ze yi shikenan buduruwa ze aura, Ismail ya cuceni mamah shikenan nikam banda kwanciyan hankali banda ranan samu..." tayi maganan cikin kuka, shiru mamah tayi na mintuna kan tace "Aisha ki dena tada hankalinki pls bikhair In shaa Allah, kiyi ta istigfari in na baro office zanzo muyi magana kinji? Sannan ki dena kukan nan ki natsu ki fahimci mijinki".

         Tana share hawayenta tace "toh mamah na gode" ta kashe wayan ta d'anji natsuwa kad'an a maganan da tayi da mahaifiyarta, dukda tana ganin call d'inshi haka ta kasa d'agawa se toilet da ta shiga tayo alwala ta hau kan sallaya tayi nafila raka'a biyu ta fara karatun qur'ani.


*******


Zirga zirga kawai yake hankalinshi tashe ya san hankalinta gabad'aya na chan a tashe kila ma kuka take ya kira numbernta yafi sau hamsin bata d'aga ba, har tunanin tafiya kaduna ya fara, tunawa yayi da kiranta da yayi tayi da farko tana waya ya tabbatar da mamah take waya Don yanzu Itace best friend d'inta In aka wareshi.

           Numbern mamah ya nema ya danna kira tana d'agawa ya samu wuri ya zauna cikin rawar murya yayi sallama ta amsa mishi da fara'a, tausayin shi na kamata tasan yana son erta Allah kad'ai ya san dalilin da yasa ze kara aure tunda d'iyartata bata fad'a mata ba.

"Mamah kunyi waya da Aisha?" Mamah tace "Eh saifullah munyi magana hankalinta duk a tashe but na san zuwa yanzu ta samu natsuwa karka tada hankalinka, In ta gama natsuwa zata kiraka da kanta kaji?"

       Cikin damuwa yace "Mamah wallahi ba da niya zanyi auren nan ba yakumboce ta Matsa harda barazanar tsinuwa sbd ban san yadda zanyi ba hakan yasa na amince na bata za'bin wacce taga ta mata, mamah bazan ta'ba iya wulakanta Aisha ko tozartata da Sanina ba, mamah Wallahi Ina sonta fiye da raina ban son wannan er abun yasa ta fara wasu tunane tunanen da bashine ba".

     "Karka damu kayiwa mahaifiyarka biyayya shine daidai saifullah In Shaa Allahu zan fahimtar da ita anjima zanje gidan, Allah yayi muku albarka" ya amsa da "Ameen Ameen na gode mamah, Allah ya kara tsawon rai".


********


Tsab ta fito a shirye cikin riga da zani da wata doguwar hijab har kasa da ta d'inka da safen ta feshe jikinta da wannan turaren da baba ya bata ta saka kwalli mad'au ta fito, da sakakken baki inna ta bita da kallo kan ta ta'be baki taci gaba da abinda takeyi.

  Mutanen unguwansu Karan kansu sunyi matukar mamaki da ganinta haka kowa se kallonta yake da masu gulma se masu Allah ya shirya don an san ba abin arziki zata aikata ba, direct badarawa ta wuce da sallama ta shiga gidan.

Yakumbo dake zaune tana kallon tv ta amsa tana cewa "wayene karaso nan" parlorn ta shiga kaman an tsikari yakumbo ta mike "a'a sannu da zuwa Sannu, bakuwa ashe mukayi maraba lale" Da wuya kaga yakumbo tayiwa bako irin wannan taryan amma abin mamaki har ruwa ta kawo mata.

           Seda tasha kan suka gaisa yakumbo tace "sede fah ban gane daga Ina ba amma d'iyar albarka kin burge ni abin sha'awa d'as dake" murmushi zuby tayi a kunyace tace "eh daga nan bayan kabala road nake zan wuce ne d'an uxuri ya kamani shine nace bari In shigo in roki alfarmar a barni nayi" yakumbo tace "ah haba tashi shiga ga d'aki je kiyi d'iyar albarka".

      Murmushi tayi ta tashi ta shiga d'akin tana shiga ta daka tsalle tace "yes" shiga toilet d'in tayi ta d'an wanke kafanta ta fito.

      Ganin yakumbo tayi zaune ta kafa tagumi cewa tayi "na gode Kwarai Allah ya saka se anjima mamah" yakumbo tayi saurin cewa "tsaya er nan, nace kina da aure ne?" Kai ta girgiza yakumbo tace "Alhamdulillah zaki auri d'ana? Don na yaba da hankalinki kwarai" kai ta dukar cikin kunyar karya, yakumbo tayi murmushi tace "Alhamdulillah na gode da wannan amsan karki damu ze rikeki da amana ko don natsuwarki".

        Nan fah yakumbo ta ajiyeta da hira har abinci tasa me aikinta kawo mata ta kuma kar'bi numbernta da na baba, don gulma se ga zuby da matse ma yakumbo kafa ai kuwa tayi ta ci mata albarka da kyar suka rabu hmmmm.


********


Bata tashi daga kan sallaya ba seda taji yaran sun dawo daga school nan ma dakatarwa kawai tayi seda suka shigo rungumeta sukayi ta d'an shafa kansu kan ta kalli arwa da tace "Maami me ke damunki?" Murmushi ta d'anyi kan tace "ba komai arwa kaina ke d'an ciwo, d'auki 5k kan cushion d'in chan ki kaiwa driver yayo muku takeaway, fita da kannenki ki chanzasu".

     Kamasu tayi suka fice Bayan sun mata Sannu tagumi ta buga dukda zuciyarta ba daad'i amma zuwa yanzu taji sauki sossai, tana nan zaune taji yaran sunayiwa mamah oyoyo bata motsa ba har mamahn ta shigo ita kad'ai da alamu yaran sun kyaleta, da sauri ta mike taje ta rungumeta se wani kukan.

  Dagata mama tayi ta kama hannunta zuwa kan cushion dake d'akin suka zauna cikin lallashi Tace "meyasane kike son sawa kanki damuwa Aisha? Uhm wai kin mance Allah ne yake kaddara auren? Sannan in an kawo matan kanki zata zauna ne? Ki dena haka In irin kishin nan kikace zakiyi wallahi kece zaki kwana ciki, damuwarki baki kawo budurcinki gidanshi ba ko? Tsaya ki saurara kiji".

       Wayanta ta d'auko ta shiga recording tayi mata playing d'in wayansu na d'azu jin yadda duk yake a rud'e da damuwa yasa jikinta yayi sanyi rud'ewa ne yasa tayi judging d'inshi haka.


Nasiha sossai Mama tayi mata akan hakuri da zama da Kishiya ta bata wasu adu'o'i da zata dingayi, sossai ta mata godiya kan suka fito har Arwa ta zuzzuba musu abincin suna ci seda sukayiwa Mama tayi tace "kuci kayanku ina da tanadadden tuwona shiyasa ko yaushe na fi ku kumari"

Dariya sukayi gabad'aya ta fice itama har waje da tayi parking car d'inta Aisha ta rakata kan ta dawo, akan se sun had'u gobe.

            Ciki ta dawo har zata wuce arwa tace "maami ga naki abincin" se lokacin ta tuna da ko breakfast batayi ba, girgiza kai tayi tace "se anjima arwa" ta wuce d'akinta wayanta ta kunna seda ta tsorata ganin fifty missed calls nashi zama bakin gadon tayi ta danna kiranshi ai ko ringing be yi ba ya d'aga "haba rayuwata ya zaki hukuntani da irin wannan hukunci me tsauri haka, kin kuwa san irin tashin hankalin da na shiga? Wallahi har leave na tambaya aka hanani da kin ganni kaduna".


"Kayi hakuri" ta fad'a cikin sanyi yace "kiyi hakuri, ki rufamin asiri Aisha karki rikeni a zuciya da abinda banyi niyyan aikatawa da son raina ba se don farin cikin mahaifiyata" katseshi tayi da "mahaifiyarka Mahaifiyatace hakanan umarninta kaman na mahaifiyatane Allah ya bamu zaman lafiya ya baka ikon yin adalci" duk yadda yaso ta sake kaman da kasawa tayi magana take kaman ba ita ba a haka ta nemi alfarmar biyawa gidan Aisha kanwanshi kan taje gidan suna a take ya amince.


Ya kuwa tabbatar mata ze mata transfern 100k ta sayi abin sunan godiya tayi kan tace "zanyi sallah se anjima" ta kashe tare da mikewa, ranar gabad'aya haka ta yini ko waya basu kara yi ba tana jinsu da yaran suna fad'amishi kanta na ciwo and bata ci abinci ba breakfast d'inta ma bata ta'ba ba da sauri ta kashe wayanta don kar ya kirata ta kuma rufe room d'inta tana ji suna knocking taki bud'ewa.


WASHEGARI

Har safiya bata bud'e wayanta ba yaran ma bayan sunyi bacci ta tattare iPads d'insu ta rufe ta kai d'aki da sassafe ta shiryasu suka fice ta tabbatarwa driver in ya d'aukosu unguwan rimi ze kai mata su, seda ta had'a kayan da zasu saka In sun taso a wata jaka kan ta shirya cikin wata arniyar lace da kud'in zasu haura 100k sanin kallon kurillahn da za'a mata yasa ta kuma d'auko sarka, d'an kunne, da zobe na dakakken gwal ta saka ta yafa gyale tare da d'aura black Iwatch a tsintsiyar hannunta ta zura half cover me sheki da ake yayi tare da d'aukan handbag d'inta tayo waje d'ayan hannun rike da karamar trolley da ta zuba kayan su Arwa.


Motanta kirar Mercedes benz golden colour ta shige taja gateman ya bud'e mata gate ta wuce seda ta tsaya super market ta sayawa jaririn kaya masu tsada da kyau kusan na 50k kan ta d'aukarwa uwar jegon super wax, tana fitowa tayi tudun wada inda nan gidan Aisha yake.

Aikuwa taji daad'in ganinta ta cika mata gaba da kayan ciye ciye suka sha hira shaati ko a fuska bata nuna mata tana cikin damuwa ba har sukayi sallama ta wuce gidan suna.
                    🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA....💦🍇

      *Baya chanza d'and'anon teku*


          *Fatima Muhammad Gurin*

       **Gureenjo6763 on Wattpad**


     'Yar Mutan Adamawa


*This first dedication goes to Gurinjo Novels Group Ina jin daad'in comments d'inku sossai su ke karan karfin gwiwan yin wani page, love you guys lodi lodi🥰*

     *P6*


Part d'in mamah ta fara nufa tana sa kai da sallama suka had'a ido da ya fadeelah a tare suka kawar da kai, mamah da ya ameena ne suka amsa mata sallaman mamah tace "kin samu karasowa?" Tace "eh mamah Ina kwana?" Tace "Lafiya kalau ya gd?" Tace "Alhamdulillah, ya meena, ya fadeelah Barkanmu da safiya" suka had'a baki wurin cewa "Yauwa" kallonsu Mama tayi ta kawar da kai, tana nan tana kan adu'a Allah ya nuna mata randa yaran nata zasu koma da rayuwarsu kaman da, ita kanta ta San Ismail ya tarwatsa mata gida In har abinda Aisha ta fad'a gaskiyane.

          Ya meena tace "Shaati ashe kuma aure Saif ze kara?" Bummm haka taji gabanta ya fad'i ta san mama ce ta gayamusu Don su tayata jaje haka kuma ta kwana da sanin maganan nan tunda ya shiga kunnen ya fadeela to kowa ma se yaji a gidan nan hakan kuma ze zama kaman abun gori ko habaici a gareta.

     Cikin sanyin murya tace "Eh ya meena" ya fadeela tayi charab tace "kema meena da magana kike wai se kin tambaya? Wani namijin ne ze auri mace ba'a buduruwa ba Sannan kiyi tunanin daga baya baze karo zankaded'iyar buduruwa gal a leda ba".

   Murmushi me ciwo shaati tayi tace "Allah sarki naga waenda aka baresu a ledan ma basu tsira ba, harma gwarani tunda seda na shekara 8 kan aka karo ba watanni ba".

    Ya fadeela a harzuke tace "ke Aisha ni sa'arkice?" Shaati zatayi magana mamah tace "ya isheku hakanan bana son shashanci ke fadeela ki kiyayeni da baki fara magana ba zata amsaki ne? Ke kenan bazaki ta'ba kama girmanki ba a matsayinki na babba da ita toh kuci gaba shashashu kawai na waje su mata ku ma en uwanta ku mata"

      A zuciye ta mike da d'iyarta mimi a hannunta ta shige d'akin mamahn, tsaki Shaati taja tana mitan "mutum baze yi abinda ya shafeshi ba se abinda be shafeshi ba, daad'in abin kun sanni sarai ba'a min ban mayar ba Aisha nake" Mamah tace "bance maganan ya isa ba? Ku...." "Assalamu alaikum" ya majeed ya shigo da sallama amsashi sukayi gabad'aya yace "Lafiya kuwa mamah? Naji kina ta fad'a".

Tace "ni da yaran nan ne" hararin shaati yayi yace "ke wato In baki kashe mana su ba hankalinki baze ta'ba kwanciya ba ko? Se yaushe kike so su huta da damuwanki? Da aurenki da yaranki amma se an tasa ki a gaba an ta miki fad'a kan zaki san abinda yake me kyau?" Cikin sanyin murya tace "ya majeed....." ya daka mata tsawa "shut up!!" Mama tayi saurin cewa "Abdulmajeed ba itace ba ni da fadeela ne, kaga kyaleta ya yaran?".

        Yace "sun tafi school se an tashi zasu zo" Mamah tace "uwar tasu fah?" Yace "sharifah ta kaiwa mujeebatu wani sako daga chan zatayo nan ta gaidaki" Aisha da kanta ke kasa zuciyarta na kunan yadda duk en uwanta ke hantararta ta d'aga kai tace "Ina kwana" be amsa ba se na Meena da ta jefo bayan na shaati ya amsa ya samu wuri ya zauna.

     Nan suka fara hira su uku ita dae Aisha tana nan zaune shiru Don In ta sa baki ta san se ya jefeta da bakar magana koshi ko meena, jingina tayi da cushion tare da lumshe idanu nan take ta fad'a duniyar tunanin abinda ke damunta na karin auren Saif Allah ya sani tana cikin damuwa sossai da sossai sede tana iya kokarinta wurin ganin ta kawar da damuwan da ambaton ubangiji.

     In har zata tuna auren Saif se gabanta ya fad'i a take sau uku ko fin haka, wani irin fargaba da tsoro ke shiganta, ji tayi an ta'ba mata hannu a hankali ta 'bud'e idanunta da suka rine sbd rashin bacci da kuma tsabar tunani ta d'aura kanshi inda yake cewa "bacci kike a haka?" Murmushi ta saki tana gyara zamanta tace "a'a ya mujeeb yaushe ka shigo?" Mamah tace "Ina zaki san ya shigo kina chan kin fad'a duniyar tunani Ina guje miki fah Aisha!!!".

Ya mujeeb wadda shine babban yayansu yace "tunanin me kuma ze dameta haka mama?" Mama Tace "aure mijinta ze kara" wani irin dariya hameed dake shigowa ya saki cikin nishad'i shi fah duk abinda ze bakantawa wannan yarinyar rai sonshi yake har kahon zuciyarshi ganin hararan da mama ta sakar mishi yasa shi sa hannu yayi zipping bakinshi alamun yayi Shiru.

       Ya majeed yace "Angon karni baban boy dariyar nan fah?" Ya karasa kusa dashi ya zauna yace "wallahi wani abu ne ya bani nishad'i" ya karasa yana nuna mujeeb da ya kama hannun shaati sukayi compound da baki, girgiza kai kawai majeed yayi meena kam murmushi ta saki tana kwalawa fadeela kira.+


Suna fita suka zagaya wurin garden d'insu kan kujerun dake wurin suka zauna yace "kanwata na san ke jarumace me ze d'aga miki hankali har haka a kan Kishiya?" Tace "yayana ka san irin halin da na fad'a ka san irin bakar kaddarata taya kake tunani hankalina baze tashi ba akan auro buduruwa da Saif ze yi?".

     Murmushi yayi yace "kanwata har yanzu baki san maza ba, namiji fah ba ruwanshi da wannan In har yana sonki to yana sonki bare Saif da na tabbatar baze iya rayuwa ba tare dake ba" Shiru tayi ya kuwa ci gaba da kwantar mata da hankali har da karawa da "kinga yanzu kaman ni In nace zanyiwa murjanatu kishiya wallahi wallahi kinji rantsuwar musulmi ko? Ta kuskura tamin hauka ko ta nuna min 'bacin rai harda kashe min waya da dai sauran abinda mata sukeyi toh fah se na bakanta mata itama ta hanyar Amaryar one way or the other Sannan kimanta ze ragu ne a idanuna".

      Gaban shaati ne ya fad'i dukda bata fad'a mishi tayiwa Saif hakan ba se take tunanin kawai duk maza haka suke yanzu kenan kimanta ya dad'a raguwa a idanun Saif Don maganganun ya mujeeb kaman da ita yakeyi, se hankalinta ya koma kan mijinta, tana ji ya mujeeb na ta bata shawarwari da lalla'bata take ta nuna mishi ta sake don duk cikin yayyunta ba wadda ya rage da ragowar sonta a zuciyarshi se mujeeb, ita a zuciyarta bata ajiye kowa matsayin yayanta ba In ba mujeeb ba duk bassa sonta.

        Kan kace me ta sake sossai sun fara hira da dariya "Toh soyayyar en uwantakace ta motsa?" Anty murja tayi magana daga bayansu, duk juyowa sukayi suna dariya shaati tace "to ya son ranki ko kishi kike?" Tana dariya tace "ah ni a su wa in ba so kike yayanki ya sallameni ba" nan ma dariya sukayi Anty murja tace "kinga biyowa nayi In d'aukeki muyi site d'in hajja en suna na chan a cike mu muna nan"

   Mikewa sukayi yayi gaba ya barsu da matar tashi suna hira tana tambayarta yaranta inda tace duk suna school se an taso zasu biyo nan, seda ta shiga parlor ta yafa gyale ta d'auki tukuicinta kan suka fito tana tambayan mama "su ya fadeela fah?" Mama ta amsata da "suna site d'in hajja" Da toh kawai ta amsa suka fice, a hanya ta bud'e jaka ta d'auko wayanta tare da switching d'inshi on yana gama booting ta danna kiran layinshi.

     To her biggest surprise wayanshi switch off abinda bayayi ko da kuwa kwanciya bacci ze yi kuma dae baza'a ce ba charge ba tunda ko da ba wuta a gida dole akwai a office bare in babu a gidan ma akwai inverter, da tunanin me ya faru suka karasa part d'in hajja a cike da en mata da matan aure duk yara suna school se waenda basu kai sawa ba akallah matan aurensu sunyi 15 banda en mata da bazasu wuce 6 ba waenda suke jami'a kenan, matan gidan su 7, ta 'bangaren maza kenan wato ubbanninsu goggoninsu hud'u kuma suma da yaransu a ciki har da waenda sukayi aure sede duk cikin goggonin nasu ba wacce tayi aure nan kaduna shiyasa had'uwa se sa'i da lokaci.


Barka ta kuma yiwa mujeebatu dake mata wani irin kallo haka sauran sa'annin nata ma sannunku kawai ta ce musu tana karewa sharifah kallo yadda ita a dole taci ado da lace me tsada da taga na jikinta kuwa se ta d'auke wuta har hassadanta na nunawa saman fuskanta, murmushi kawai tayi ta Mikawa hajja dake aikin had'a kayan baby da na uwar wuri d'aya nata kayan.

Tana bud'ewa ta fiddo super wax d'in se da ta d'ago ta kalli shaatin dake tsaye gefenta tace "ke me suna wannan atamphar Ai itace na tambaya a wani shago yacemin dubu saba'in don shine sarkin 'barayin duniya yanzu a haka kika saya?" Murmushi shaati tayi tace "Ai kuwa dae me suna haka kud'inshi yake duk inda zaki ke sarauniyar son kud'in duniya ko me zakiyi da kud'i da iyayenmu ke taramiki??".

              Dariya wasu daga cikin matan d'akin sukayi murjanatu tace "ka ji min shaati da wata magana ina ruwanki tunda ba ke ke bata ba" hajja tace "ah toh gayamata dae murjanatu In ba almubazzaranci ba zanin da zaka d'aura a kugunka ka zauna kasa kayi tusa ciki shine zan saya dubu saba'in to wallahi gwara In sayi er dubu dubu ehe, su waenda iyayen naki ke kawowa Ina d'inkawa ne kawai don ba yadda na iya da kasuwa zanna kaiwa Ina sayarwa Ina chake kud'ina".

           Zama shaati tayi gefen hajja tare da fuskantan me jego ta mika hannu ta d'auki babyn seda gabanta ya fad'i ganin kamannin yaron da Arwanta tana jaririya daga baya kuma kamannin ya 'bace, adu'a ta mishi tana satan kallon su ya fadeela da suka cika fam jin yadda hajja ke ta kuranta gudumawan shaati yafi na kowa In ka cire na iyaye da mijinta se na shaati Don kayan jaririn ma abin kallo ne.

      Sharifah matar ya majeed uwar hasada kaman ta mutu, don dirkawa shaati haushi fadeela tace "ni kam Aisha yaushene aka saka auren mijin naki?" Tsit d'akin ya d'au Shiru na mintuna kan hajja tace "Me suna aure saifullahi ze yi?" Murmushi Aisha tayi wadda kowa seda yayi mamaki Don har had'awa tayi da dariya tana kallon ya fadeela tace "Eh wallahi hajja ya naga kowa yayi dib kaman sakon mutuwa aka fad'i, aurene fah ba wani abu ba ai abokiyar zama daad'i gareta ko ya fadeela?".


Had'e gabas da yamma fadeela tayi don ta san da ita shaati keyi watanta takwas da aure mijinta yayi wani auren kuma taci kwakwa hannun kishiyan kan iyayensu suka tsaya tsayin daka akanta yanzu ta samu sauki, maganganu ne ya fara tashi a d'akin "Lallai Aisha yanzu ke ko a jikinki?" Cewar hajja, "Amma shaati naga jarumtarki" cewar hafsa d'iyar baba haladu, "Amma dae munafurci ba kyau gwara ai mutum ya nuna maka ainihin color d'inshi akan yaga fuska faran faran zuciya kuwa baki kirin" cewar Zainab d'in baba habu, sharifah da meena suka had'a bakin wurin cewa "ah to".

      Murmushi tayi tana kallon hajja tace "hajja me ze sa In d'agawa kaina hankali In Allah ya kaddaro auren nan yau ko tumbur zanyi yawo se yayi so gwara na kar'ba da mutunci da na kar'ba ta tsiya" hajja tace "shiyasa nake sonki me suna akwai ki da hangen nesa tambarin masu sunan mu kenan, karki damu na tabbatar ba abinda zata nuna miki ko fiki dashi zan kuwa gyaraki irin gyaran da hmmm sha kuruminki er kirki".

        Dariya Aisha tayi tana rungume hajja tana cewa "shiyasa nake sonki me suna Allah ya barmu tare yaja tsawon kwana" kallon en d'akin tayi da kowa yaji haushin gyaran da hajja tace zatayi mata tunda cikinsu akwai masu Kishiya amma hajja bayan amare bata ta'ba yiwa wani gyara hakan nan ba sbd kishiya se kan Aisha, (dayake hajja er maiduguri ce kuma ita ke yiwa duk jikokinta gyaran amare) d'age gira shaati tayi tana kallon ya fadeela tace "ya dae? Buhari ya shigo lamarin ne?" (Tana nufin sunji haushi).

      Dibbb ta nemi fara'anta ta rasa jin muryan da yayi sallama kofan d'akin hajja, wani irin malolon abu ne ya taso tun daga kasan cikin ta yazo daidai zuciyarta ya kafe chak, har tafasa taji zuciyarta nayi kanta ya d'auki sara lokaci guda, bayyananshi da kamshin turarenshi da ada tayi haukan so suka taso mata da amai tsabar tsanan da ta mishi yanzu.

          Sama sama take jin en d'akin na mishi sannu da zuwa, wasu na tambayar saukan yaushe, bata hankara ba ganinshi tayi ranwkafe gefenta ya sa hannu da niyyar d'aukar jaririn hannunta bakinshi na furta "namesake oya come to your papa and namesake" garin d'aukan babyn hannunshi ya gogi nata, bata san sadda ta wani irin mikewa a zabure ba tare da sa hannunta biyu ta hankad'a shi daga shi har babyn tare da tsirtar da nyau ta juya a fusace zata wuce, carab taji an rike tsintsiyar hannunta wani irin juyowa tayi se taga ya hameed yana shirin wanka mata mari cikin zafi nama ya rike hannunshi.

               A zafafe shima ya kalleshi yace "ya Ismail da ka kyaleni na tsinka mata mari ko zata dawo hankalinta da bakayi tsayuwan kirki ba ba abinda ze hanaku fad'uwa da kai da Lil Isma'il" wadda aka kira da Ismail na kalla tabbas yana satan kama da Arwa amma sak yake da yasmin kaman shine mahaifinta, sede fah kyakyawane na ajin karshe haske kawai saif ze nuna mishi sede su kara a gasar kyau don bazan iya tantance wadda yafi wani ba.

     "A'a hameed....." be karasa abinda yake son fad'a ba shaati ta pincike hannunta dake cikin na hameed ta kalleshi cikin ido tace "wallahi wallahi da ka mareni kan wannan, da ba abinda ze hanani nima tsinka maka mari, sede duk abinda ze faru ya faru, I hate you all" ta juya a zuciye ta fice sun santa tana da bala'in zuciya haka In ka mata abu tana da wuyan mantuwa tana da shegen riko.

     Dukda fara'a da sanyin halinta bata barin bashi, ita karan kanta ta san waenda take d'an ragawa su yakumbo ne kawai, Tana fita wayanta ya d'auki ringing ganin Roohul na'im d'inta yasa ta tsaya ta sauke numfashi tare da picking shiru tayi na mintuna kan ta zazzaro idanunta waje a firgice tace "whatttt!!!".


                     🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA💦🍇

      *Baya chanza d'and'anon teku*


   *Fatima Muhammad Gurin*

**Gureenjo6763 on wattpad**

          'Yar Mutan Adamawa

     *P7*


"Innalillahi wainna ilaihi rajiun* ta fad'a idanunta na cika da hawaye da sauri ta karasa part d'insu, Mama na zaune a parlor se ganinta kawai tayi tsulum kaman an jefo ta, jakanta kawai ta bud'e ta ba Mama key d'in gidanta da kallo Mama ta bita na mamaki kan tayi magana taga ta 'bace kaman walkiya.

      Kallon keyn tayi ta kuma kalli kofa a fili tace "ikon Allah" se kuma ta mike ta fito har gate d'insu bata ga komai ba se kuran motanta me gadi na kokarin rufe babban gate d'in, a fili ta kuma furta "ko me ya faru? Toh Allah ubangiji ya tsare" ta koma parlor cike da tarraddadi, hanyan Abuja ta d'auka tana tafiya tana share hawaye zuciyarta a matukar chunkushe a fili take furta "ko me ya faru ni ce sanadi, pls kar wani abu ya sameka in hakan ta faru bazan ta'ba yafewa kaina ba".

          Gudu ta dinga shatatawa kaman ba mace ba duk wadda ta gilma se ya bi motan da kallo yana "Allah shi kyauta ko shi kuma saurin me yake?" Dayake tinted glass gareta.

  Awa biyu chip ya kawota Abuja direct FMC da aka ce mata yake ta wuce har yanzu hawaye be bar zuba mata ba idanunta sunyi ja har bata ganin hanya da kyau, a haka ta karasa private word na asibitin zuwa room numbern da aka gayamata.

      Wani irin wawan ajiyar zuciya ta sauke da ta bud'e d'akin sbd ganinshi zaune yana kallonta, bata san sadda ta karasa da gudu ta rungumeshi ba tare da sa wani kukan, se kuma ta d'ago ta shafa kumatunshi tace "kana Lafiya? Ba abinda ya sameka?" Kallon jikinshi ta fara ganin bandage nannad'e a kafanshi da gwiwan hannunshi se a goshinshi yasa ta kuma sa kuka.

       "Sannu yana ciwo ko?" Kama hannunta yayi se ya jata jikinshi ya rungume tare da lumshe idanu seda suka kwashe mintuna a haka yace "laifina ne da nayi ta miki alkawarin bazan kara aure ba kika sa a ranki" Da sauri tace "a'a laifina ne kayi hakuri ka yafemin, In kuma baza ka iya ba ka mareni ko ka dakeni duk ni naja da wawanci na kayi hakuri dan Allah".+


Kuma rungumeta yayi yana shafa bayanta a hankali da hannunshi me ciwo yace "kul na karaji kin kira kanki da wawiya se mun 'bata, Sannan kin fi karfin duka ko mari a gareni Rayuwata kiyi hakuri da auren da yakumbo tasani yi, ba yadda na iya ne shiyasa na amince" d'agowa tayi ta kalleshi da murmushi tace "karka damu hai Allah ya bamu zaman lafiya yasa ba fitinanniya za'a kawo mana ba, wacece kanwartawa?".

       Ta'be baki yayi cikin sanyi yace "oho nima ban sani ba ce mata kawai nayi ta za'bi duk wacce take so zan tura musu kud'i suyi komai" murmushi kawai tayi a zuciyarta tana mamakin irin tsanan da su yakumbo suka mata, kumatunta taji ya kama ya d'an ja ba yadda ze mata zafi ba yace "karki karamin hukunci irin haka rayuwata ki min ko wani irin hukunci zan jura amma banda na hana kanki abinci da hanamin muryarki ba zan iya Jura ba".


Rungumeshi tayi tace "ba zan kara ba kayi hakuri" yayi kissing forehead d'inta yace "I love yhu" cikin murmushi tace "love you more".

   "Toh love birds zan duba patient d'ina" da sauri ta d'agashi tana sunne kai shi kam ko a jikinshi yace "dr ni a sallameni In koma gida zataji da ni yadda zan warke cikin lokaci kankani" dr yace "da alamu saurin zuwa gareta ne ya jawo wannan accident d'in" Saif yace "ba zaka gane bane" dariya dr yayi yayinda ita kuma ta saki murmushi, "taya zan gane tunda ni ai ba mata gareni ba" dariya sukayi.


Ya dubashi tare da mishi allura yace "se gobe za'a baka sallama sbd jikinkan be gama kwari ba dukda dai ba sossai ne raunikan ba" godiya suka mishi ya fice, zama tayi kan farin plastic chair dake d'akin tace "wai ya akayi kayi hatsarin nan ne?" Yace "kaman yadda dr yayi guessing na kasa handling halin da kika sani ciki hakan yasa na bar office ba tare da na sanar ba, a nan kusa da Abuja nayi hatsari garin kaucewa wata akuya da ta hau kan titi from no where".

        Tace "Allah ya kiyaye na gaba, ai dr d'inne ya kirani" yace "Ameen, na san yayi guessing hakan ne sbd ganin yadda kiran da na miki ya cika call logs d'ina, shiyasa ya kiraki kuma Alhamdulillah ya samu number d'inki kunne".


Shiru sukayi na seconds kan yace "wa ya kawoki" kallonshi tayi tare da yin narai narai da ido ta san tayi laifi tunda ba barinta driving me irin nisa haka yake ba, itama bata ta'ba irin driving haka ba se yau, ganin yadda tayi yasa ya gane be ce komai ba se kwanciya da yayi a hankali tare da lumshe idanu, zatayi magana kenan wayanta ya fara ringing d'aukowa tayi se yanzu ta tuna yadda wayanta yayi ta ringing a hanya ko kallon inda yake batayi ba, ganin mamah yasa tayi saurin picking.


"Ina kika jefar da wayanki haka ne? Lafiya kuwa naga kin fice a rud'e me ya faru?" Cikin muryar tausayi kaman zatayi kuka don gudun fad'a tace "babansu ne yayi accident a hanyarshi ta zuwa kaduna" Mamah tace "subhanallah ya jikin nashi? Be de yi tsanani ba ko?" Tace "eh da sauki sossai" nan fah mamah ta bud'e babin fad'a na kama hanyarta haka ba sanarwa Sannan ita kad'ai ba driver bayan ta san yadda hanayar kaduna to Abuja yake.

Se hakuri take bayarwa dama ita ta kware a fannin bada hakuri, bayan maman ta sauko tace "Mamah se a d'aukowa su neeha kaya su zauna nan kan In dawo" cikin fad'a mamahn tace "bazasu zaunan ba" kit ta kashe wayanta, dariya shaati ta sake a fili tace "uwata ta kaina Allah ya bar mini ke".


Take kuma fara'arta ya d'auke tunawa da In har yaranta na gidan mamah to fa se sun had'u da isma'il wani irin haushi ne ya kamata da yakumbo watace da se su koma hannunta dukda itama tana sonsu amma fah tarbiyar yara a gareta se a hankali don duk abinda d'a yake so shi za'ayi sanna d'a yayiwa babba rashin kunya a gabanta ba abinda zata ce, haka ba'a kwa'bar d'a gabanta, ta tabbatar ba don su Saif sun tashi da uba tsayayye ba kan rasuwarshi da dukkansu se a hankali zasu tashi.

       Kallonshi tayi a hankali tace "kayi bacci?" Shiru yayi mata ganin yana motsa yatsanshi na hannune yasa ta san be yi bacci ba kenan fushi da ita yake, ita kam taga ta kanta cikin sanyin murya tace "I'm so sorry roohul na'im hankalina ne ya tashi nayi tunanin maybe you are badly hurt shiyasa na kamo hanya ba tare da wani tunani ba, I was crying all the way here bcs i know it was all my fault if something bad happens to yhu I will never forgive myself, pls don't be mad at me".


Ba ze iya kuma shareta ba sbd yadda take maganan ma kad'ai ya sanyaya mishi jiki wani irin feelings a kanta yake ji marar missaltuwa In tana magana haka ji yake wani abu na yawo a jikinshi, tayi mugun sanin lagwanshi shi kam anya ze iya rayuwa ba tare da ita ba? Itace komai nashi shi ya sanya yake kiranta da rayuwanshi.

   Lumsassun idanunshi ya bud'e cikin nata ta kuwa yi raurau tana jiran yace kit ta rushe da kuka, be san sadda murmushi ya kamashi ba ya kuwa sake har fararen hakwaranshi na bayyana lumshe ido tayi ta bud'e tare da sa hannunta ta shafi kumatunshi tace "you are so handsome" shima ya shafi nata kumatun yace "you so cute and hot my baby" dariya ta saki shima ya tayata.


*********


BAYAN KWANA BIYU


Zuwa yanzu ya warke sossai ya koma gida ba inda yake lekawa suna like da juna yafi kowa farin cikin zuwanta don kulawa ba irin wadda baya sha kaman ta kamashi ta goya, holewarsu suke su biyunsu ba gida suke ba bare suyi tunanin ganin wani bako Sannan ba yara wai soyayya har na bugawa a jarida.

       Yakumbo ta kirashi ta fad'a mishi ta sama mishi matar sunanta zubaidah, da yayi kyau kawai ya amsata sbd Shaati dake kwance jikinshi, ta kuwa tabbatar mishi ta tura mishi numbernta ya kira ya kira fah nan ma toh kawai ya amsata, yana kashe wayan ya manta da baabin wata wai zubaida.


A 'bangaren su Arwa kuwa da suka dawo suka samu mamansu batanan aiko neeha ta tsaya da rigima suma jikinsu a Sanyaye sbd basu saba rabuwa da uwar tasu ba In ma Abujan zasu zata jira se anyi hutu su wuce tare nan ma maamah bata fad'amusu babansu ne yayi accident ba, da lallami da rarrashi suka hakura kwana biyu suka sake.

     Mamah ta fad'awa su meena hatsarin da Saif yayi da tafiyar shaati but to her biggest surprise ba wadda yayi adu'ar Allah tsare na gaba se ta'be baki, mujeeb ne kawai da matarshi suka nuna alhini take kuwa suka kirata sukayi mata jaaje suka kuma gaisa da saif d'in.

       Ran mamah yayi mugun 'baci inda ta kira Abba ta fad'amai nan fah ya sasu gaba yayi musu wankin babban burgo ya sheda musu tunda ba su suka haifeta ba, ba kuma su tayiwa laifi ba Ina ruwansu? Toh ya karaji wani ya mata ko kallon banza ne se ransu duk ya 'baci, ya d'aura da fad'an abinda sukayi wurin suna ya kuwa tabbatarwa hameed daa ya mareta babu abinda ze hanashi ajiyeshi itama ta rama kuma shima ya rama mata.

       Fad'a yayi musu kaman ze ari baki maamah ma ta d'aura da nata, majeed ne ya katseta da cewa "haba maamah kune ke d'aurewa yarinyar nan gindi take abinda taga dama, bayan ta gama yawon karuwancinta tazo ta d'aurawa wadda be ji ba be gani ba mutumin da ba ruwanshi ko magana wahala take mishi, kun kuma biye mata bayan aure tanawa kowa abinda taga dama bayan mune sama da ita, ni kuwa da nine hameed da se na mareta in g....".


Wani irin wawan mari yaji a fuskanshi da sauri ya dafe kunci ya kalli mamah da ta zabga mishi mari, kallon Abba yayi yace "Abba kana ganin Mama ta mareni" Abba yace "Au haba ashe marinka tayi" tassss shima ya sauke mishi mari a d'ayan side d'in yace "to nima na mareka zo ka rama" mujeeb yace "haba majeed wai me yasa kake abu kaman yaro da aurenka da 'ya'yanka me yasa bazaku rungume kanwarmu ba da duk wani kaddarar da ya fad'o mata? Duk a tunaninku da son ranta hakan ya faru ne?

Ko kowa be yarda da ita ba ya kamata ku ku yarda da ita sbd kun kwana da sanin aisha tun tashiwanta bata karya, don wawanci kuna gani dai iyayenshi suka ki DNA test sbd sun san abinda d'ansu yake aikatawa a 'boye amma shine kai hameed harda sakawa d'anka sunanshi don bakantawa Aisha".

      Shiru yayi na mintuna kan yace "In zaku gyara tun wuri ku gyara na gayamuku bakin cikin Aisha be kashe su Abba ba amma na tabbatar naku ze iya kaisu lahira" kallon mamah dake kuka yayi yace "Mamah kiyi hakuri ki dena zubar musu da hawaye na san kina jin zafi a ranki sbd ba uwar da zata haifi yara ta so ganinsu suna kin junansu akwai zafi, adu'a zaki ci gaba da yi mana Allah ubangiji ya shirya mu gabad'aya".


Abba yace "Allah yayi maka Albarka Abdulmujeeb, hakika baka zama yayan kwabo ba se waennan" ya nuna majeed da hameed yaci gaba "abinda bakuyi tun kuna kananan yara ba shi kukeyi yanzu" Mamah tace "a da Ina farin ciki na d'auka yadda kuka tashi da tausayin juna haka zaku d'aure amma se shed'an yayi nashi rawan duk wani soyayyar dake tsakaninku ya wargaje har zan iya fad'amuku er uwarku na cikin tashin hankali mijinta yayi hatsari ba wadda ze iya bud'an baki yace Allah ya tsare, toh bari kuji In fad'a muku duk wadda ya kara fad'awa Aisha maganar da ya 'bata mata rai ban yafe ba, ba ruwanku tunda ba ku kuka haifar min ita ba Sannan Abdulmajeed Ina so ka sani ban haifi karuwa ba, ku tashi ku bani waje".


Mikewa sukayi suka fice duk ransu a had'e girgiza kai mujeeb yayi Don ya san ba abinda ya shigesu d'an gwara ma da mamah tace wadda ya kara fad'amata magana marar daad'i bata yafe ba yaga duk sun tsorata kuma ya san baza su fad'a matan ba amma ba abinda ze hanasu In sun fita yanzu su had'u suyi mata wankin babban burgo sede aikin 'bur inji tusa tunda ba a kunneta sukayi ba, seda ya tabbatar ya kwantarwa da iyayen nashi hankali kan ya kira su Arwa yace su taya mijinsu hira ya mike ya fice aiko nan take suka sa farin ciki a ran kakannin nasu da irin ba'a da suke musu.


********


Sanye take da tshirt d'inshi wadda iyakarshi cinyarta ba wani wando kasa banda pant d'in dake jikinta gashinta ta sake shi ko ribbon bata saka mishi ba goge parlorn take tana er wakanta cikin nishad'i Don kwana biyun da sukayi tare ji take she is the happiest person in the world sbd irin soyayar da ya gwada mata tsantsa ta gama yarda da gaske bada son ranshi bane ze kara aure, ta tabbatar duk duniya bayan mahaifiyarshi babu wata mace da yake ji ze iya bada ranshi dominta se ita, ta amince yana mata so marar misali.


Tana goge center table ya shigo hannu yasa a kwankwaso yace "rayuwata wai T-shirt's d'ina su suka koma kayan sawanki ne?" Juyowa tayi ta mishi gwalo tace "Eh mana" ya waro ido yace "mene?" Ta kama kwankwaso cikin rausaya tace "yess bari ma kaji duk T-shirt's d'inka zan tattara In koma dasu kaduna sbd suna min daad'in sakawa moreover akwai kamshin turarenka da nake mugun so".

   Nufo ta yayi yana cewa "Ai ko baki isa ba zo ciremin kayana" Da gudu ta fara zagayen kujera ganin ze chabke ta yasa ta nufi d'aki a d'ari tana dariya tana shiga taga wayanshi dake kan gado na kara d'agawa tayi ba tare da wani tunani ba da nufin in ya shigo se ta kara mishi a kunne "hello takwabin Allah, my husband to be in not more than two months!!!!".


Ras ras haka take jin gabanta na fad'uwa In ba karya tayi ba ta san muryan nan a fili Tace "zubaidah!!!!" Kit taji an kashe wayan a zabure ta kalleshi murya na rawa tace "me sunan wacce zaka aura??" Cikin mamakin yanayinta ko wa ya kirashi? Don be ji sadda tace zubaidah ba, cewa yayi "yakumbo tace zubaid...." be karasa ba ta yanke jiki ta fad'i, da azama ya tareta a rud'e yake kwala kiran sunanta sede inaaa ta sume..........


Tou fah my readers ya take nee?


                  🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA....💦🍇

     *Baya chanza d'and'anon teku*


     *Fatima Muhammad Gurin*

  **Gureenjo6763 on wattpad**


         'Yar Mutan Adamawa

     *P8*


A hankali ta fara bud'e idanunta da taji sun mata nauyi tar ta bud'e shi a saman pop dake d'akin juya idanunta tayi zuwa ga hannunta se taga karin ruwa d'akin ta karewa kallo kan ta fahimci a inda take wato asibiti, da sauri ta lumshe idanunta jin alamun za'a shigo zuciyarta ne yake bugawa da karfi wani irin d'aci na ziyartar kan harshenta a yayinda abinda ya faru ke dawo mata a hankali.

    "In not less than two months ze zama mijinsu itada zubaidah, amma me tayiwa zubaidah haka da ta rasa wadda zata aura se mijinta? Allah kad'ai ya san irin abinda take ji a zuciyarta bata fata wata mace er uwarta taji irin wannan abin" duk a cikin zuciyarta take wannan tunanin.+


        Da karfi ta kuma runtse idanunta tare da taune harshenta jin abunda likita ke fad'awa Saif wai tana da ciki!!! She's pregnant of about five weeks ba tare da ta sani ba, tana ji likitan ya ci gaba da mishi bayani a kauracewa duk wani abunda ze tada mata hankali har ya sata suma haka sbd zasu iya rasa cikin In hakan ya cigaba da faruwa tunda ba wani kwari yayi ba, tana ji Saif ya mishi godiya cike da farin ciki kaman wannan ne cikinta na fari dashi seda Doctor d'in ya fita kan ta d'aura hannunta kan cikin hawaye na gangarowa ta gefen idanunta.


Da sauri ya karaso gareta tare da d'aura hannunshi kan hannunta dake kan cikin d'ayan hannun kuma yasa kan fuskanta yana share mata hawaye a hankali cikin damuwa yace "Rayuwata wai me ya same kine all of a sudden? Waye ya kirani? Me ya faru?" Shiru tayi se kuka da ta cigaba dayi ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idanunshi.

     "Aisha!!!" Yadda ya kira sunan nata ne ya tsoratata don be ta'ba mata magana haka ba ya had'e fuska kaman be san dariya ba "na tabbatar kinji abinda dr yace kenan so kike ki zubar da cikin? Bakya son haihuwa da ni kuma ne?" Da sauri ta girgiza kai cikin d'an d'aga murya yace "then what???? Who the hell called my phone??" Tsabar hankalinshi ya tashi be bi ta kan wayan ba sadda ta fad'i kaya kawai ya iya sauya mata ya taho da ita asibiti.

              "Ashe zubaida zaka Aura?"

Maganan ya zo mishi bazata don ko rantsuwa ze yi ba ze yi kaffara ba seda yaji wasu rugugi a kwakwalwanshi cikin wani irin yanayi yace "wace zubaida?" Hawayenta tayi kokarin had'iyewa a hankali tace "zuby kawata" "whattt!!!" He exclaimed yana mikewa kaman an tsikareshi cikin disbelieve yace "am not fool karki gayamin abinda hankalina baze d'auka ba".


"Hello!! Takwabin Allah, my husband to be in not less than two months, shine abinda aka ce bayan an kira ka kuma ko da a bacci na farka ba zan mance kalar muryar zubaida ba musamman in da saurayi take magana" majina taja kan ta kalleshi tace "saifullah!!!" Da sauri ya d'ago ya zuba mata lumsassun idanunshi cikin sauke murya tace "dan Allah kayi hakuri ka chanza zubaidah da wata, ga mata nan dayawa a duniya ka za'bi ko ma uku ne ka aura amma banda zubaida, nafi kowa sanin halinta, na san waye mahaifinta, Dan Allah kada ka kawo min ita ta tarwatsamin gida".

           Kuka take sossai zuwa yanzu kan ta sauka ta fisge karin ruwan tare da durkusawa kan guiwowinta "wannan shine first alfarmar da na ta'ba roka a gareka In Shaa Allahu kuma shine na karshe kada ka auri zubaida" gabanta ya karasa ya d'agata tare da rungumeta ya lumshe idanu, cikin sanyin murya yace "na tsane ta bazan ta'ba iya rayuwar aure da ita ba ko da kuwa baki roki alfarma ta ba bazan ta'ba aurenta ba".


Cikin kuka tace "na gode" ya mayar da ita kan gadon yace "maman unborn me kike sha'awar ci na samo miki tun safe bakici komai ba" rausaya kai tayi tace "nide muje gida tshirt d'inka nake son sawa" murmushi yayi yace "na baki su duka, yanzu ki jira ruwan nan ya kare se mu tafi but you must tell me what do you want to eat?".


"Pizza na dominos and cock wadda ya fara kankara se samosa" yace "done your highness" murmushi tayi shima yayi yace "bari In kira dr ya maida miki ruwan just kwanta ki huta before I come back Ohk?" Tace "Alright se ka dawo" fita yayi ba jimawa doctor yazo ya mayar mata da ruwan.


Ta 'bangaren saif yana fita gida ya wuce ya d'auki phone d'inshi seda ya samu bakin gado ya zauna kan ya danna kiran yakumbo, bayan ta d'aga sun gaisa yace "yakumbo wacece kika za'bamin ma kikace?" Murmushi tayi a tunaninta ya fara son zubaidah tace "au ahto sunan ta zubaidah" da gaskiyar Shaati ya ayyana a ranshi cikin rashin yarda yace "yakumbo kin santa ne ko er uwa ce?" Aiko yakumbo ta zage ta fara bashi labarin zubaida rana d'aya kawai ta ganta amma In kukaji yadda take yabawa hankalinta da natsuwarta se kunyi mamaki.


"Ahhh yakumbo ya isa haka please yarinyar nan na santa tana zuwa gidana kawar Aisha ce wallahi bata da kamun kai na Sha hana Aisha abota da ita don mugayen halayenta amma Aisha ke tausata da hujjan tana abota da itane ko zata zama silar shiryuwarta ni de bazan iya au...."


"Kaiiii ashe baka da hankali ka kalli tsabar idona kace wannan kamilar baiwar Allah bata da kamun kai?" Yace "nide bana sonta kuma banzan ta'ba sonta ba ki nema min wata amma banda zubaidah" nan fah yakumbo ta hau bala'i kamar zata ari baki "Toh wallahi wallahi se ka aureta In har dae ni na tsuguna na haifeka ana nuna maka annabi ya faku kana kaucewa In umarnin Aishace karka aureta ni kuma nawa umarnin ka aureta muga na uban wadda zaka bi, karewarta ma na tura kawunanka sun nemo aurenta yau yau d'innan, nan da wata biyu ta zama matarka In ka rainani ka dinga gutsurar namanta kana ci In an kawota wawa kawai" kitt ta katse wayan.


Dafe kai yayi da hannu bibbiyu idanunshi na rinewa ba wacce ya ta'ba tsana nan duniya irin zubaida tun kan ya auri Aisha ma kuma yanzu ace ita ze aura? Impossible, layin kawunshi umaru ya nema ya kira Bayan sun gaisa ya roki alfarmar su koma su janye neman auren zubaida baya sonta abin mamaki kawu umaru ya zage ya mishi tas harda ana nema mishi gata yana kaucewa wani namiji ne ze ki yarinya kyakyawa haka ko Don yana ganin matarshi tafita kyau? To 'yar mutunci ake nema mishi ba zuciyar mahaifinshi dasu ba da ya yarda ya aura mishi wacce ta gama wastewa a titi.


Daga nan ko ya kara sauraranshi ya kashe waya, "innalillahi wainna ilaihi rajiun" ya furta yana mikewa "meke shirin faruwa dani ni saifullahi" Da sauri ya kuma duba numbern kanin babanshi muntari ya danna kira abin mamaki kaman had'in baki shima tatas ya mishi ya kashe wayan, rigib ya fad'a kan gado da shima macene ba abunda ze hanashi rusa kuka tsabar bakin ciki.


Tunawa da Aisha na chan na jiranshi yasa ya mike ya nufi dominos ya samo mata pizza d'in ya kuma nemar mata samosa da cock ya nufi asibitin zuwa lokacin ruwan ya kare tana zaune tana kallon kofa murmushi ta sake mishi shima ya mata yake daga ganinshi ta san baya cikin natsuwarshi ranshi a 'bace haka idanunshi a rine saukowa tayi tace "likita ya sallameni muje gida".


Fitowa sukayi zuwa mota har suka isa gida bece mata komai ba ledojin ya mika mata yace "gashi shiga gida ki tabbatar kinci kan In dawo Ohk?" Kai ta d'aga tana kar'ba ta rufe kofar gyaran zaman ledojin da zatayi a hannunta se wayanshi ya fad'i da alamu ya makale jiki be lura ba, d'agowa tayi da niyyar mishi magana amma Ina ya ja motar baya ya fice.


Rike wayar tayi kawai ta shige gidan abinda ta farayi shine cire kayan jikinta ta saka tshirt d'inshi kan ta fito ta bud'e ledan ta fara ci seda taci tayi nak kan ta kalli inda wayanshi yake tunanin abinda zubaida tace a ciki ne ya fad'o mata se kuma ta tuna yanayinshi ko sun sake waya ne? Dayake wayanshi automatic record yake yasa ta d'auko ta bud'e ta riga ta San password d'in komanshi Aisha ne.


Inda ta san zata samu records d'in ta shiga kira uku taga yayi bayan wadda sukayi da zuby, ajiyar zuciya ta sauke kan tayi playing na yakumbo wayar ya fara magana ta lumshe idanunta Allah kad'ai ya san halin da take ciki bata bud'e idanun ba seda na yakumbo ya kare tayi playing na Kawu umuru nan kan seda tayi kuka Allah sarki kowa kallon da yake mata kenan na karuwa "Allah ya isa! Allah ya isa Isma'il" ta furta cikin kuka, kan tayi playing na bappa muntari bata gama ji ba ta kashe tare da ajiye wayan ta mike ta koma d'aki.


Kwanciya tayi tare da lumshe ido hawaye na gangarawa gefe da gefe zuwa cikin kunnenta a haka bacci ya kwasheta.


********


Had'e rai tayi tamau In ka ganta kaman ba karamar yarinya ba yasmin ce ta dafa kafadunta tace "ya Arwa me aka miki?" Tsaki tayi tace "I hate that man behind you" juyawa yasmin tayi ta ganshi da sauri ta juyo tace "I hate him too yaya".


Se kuma tace "but why did you hate him" Arwa tace "I don't know but I don't like him he stares like monster" dariya yasmin tayi se ji sukayi yace "are you referring to me?" A razane suka juyo yasmin ce tayi karfin halin cewa "Ina ruwan mutum da maganan mu" dalle mata baki yayi tare da daka mata tsawa "hey watch out I bet uwarku bata fad'amuku waye ni ba..... I..." be karasaba Arwa ta ja hannun yasmin sukayi cikin gate d'in Abba, dama school suka dawo su neeha tuni sun ruga ciki.


Cikin kuka Yasmin ta shiga gidan Arwa na rike da hannunta itama kaman ta fashe da sauri mama tace "yasmin wa ya ta'baki?" Arwa tace "it's one wicked man outside the compound he even insult us wai uwarmu" Mamah ta waro ido tace "eyye who is he? Karami ne?" Yasmin ta wuce room d'in da maamah ta ware musu cikin kuka, arwa tace "ba yaro bane bafa Mama kaman uncle majeed" Shiru Mama tayi in haka ne Isma'il kenan.


Shine kad'ai yaran basu sani ba a cikin uncles d'insu tunda yafi shekara 9 da barin nigeria, Tayi zurfi cikin tunani har bata san Arwa ta wuce ba, a d'aki ta samu yasmin tana kiran maami d'insu video call.


********


Cikin bacci taji wayanta na ringing zaune ta mike dayake ita ba me nauyin bacci bace ba kuma ta d'an jima a baccin janyowa tayi se taga yasmin d'auka tayi tana wara idon ganin yaran nata, ganin tana kuka ne yasa hankalinta tashi "yasmin me ya sameki? Wa ya bugeki?".


Labarin abinda ya faru ta bata cikin kuka "what ya bugeki? Lallai Isma'il" jin muryar Saif tayi yana cewa "hmmm kar ya kuskura ya tarowa kanshi abinda ba ze iya ba wallahi kar ya sa na maida hannun agogo baya" hannunshi ta dafe tare da girgiza mishi kai ta nuna yaran da ido, kwafa yayi ya mike ya wuce duk ka ganshi zaka san yana cikin 'bacin rai.


         Kwantar musu da hankali tayi Sannan ta musu fad'an ko wayene In ya girmesu be kamata su ce sun tsaneshi ba kaman rashin kunya ne and she don't like it, kar su damu zata dawo nan kusa ta d'aukesu daga gidan, nan suka sake sossai suna ta hira da yaran nata kan ta tambayi er autanta bata rufe baki ba neeha ta shigo da gudu ganin maami ya sa ta fara tsalle tana kiran sunanta.

     Haka dae suka ta hira har ta sallamesu, sauka tayi ta shiga toilet ta wanke face d'inta ta fito zuwa parlor, girgiza kai tayi ganinshi zaune ya buga tagumi be san yadda ze yi ba wallahi har kasan ranshi baya son maganan zubaida amma In har yayiwa yakumbo maganan d'auka zatayi umarnin Aisha ne, shi da yaje wurin yassar ma (friend d'inshi) be samu wani kwakwaran shawaran da yake so ba bcs if he use his advice dole yayi hurting Aisha In one way or the Other.


Da karfi ta zauna gefenshi har ya d'an firgita ya kalleta ta turo baki alamun en rigiman ne kusa, ajiyar zuciya ya sauke kan yace "my life menene?" Kallon shi tayi tace "ba kai bane" cikin shagwa'ba karkata kai yayi yana murmushi don gani yake duk duniya ba wadda shagwa'ba ke kar'ba irin Aisha, "Toh ni d'an mutum biyu me nayi?".


Gyara zamanta tayi ganin dae yayi murmushi da yaje kasan ranshi Tace "ka daina sa damuwa a ranka roohul na'im maganan da mukayi d'azu a hospital na janye i will pretend bamuyi irin magana haka ba, mahaifiya ta wuce gaban komai you should just follow what she wants, beside ka manta komai kaddara ne? In Allah yayi zaka auri zubaida se ka aureta kuma se kun yi rayuwar aure mu barwa Allah komai mu kai mishi kukan mu, dukda I will never ever forget what zuby did to me but destiny yafi gaban komai".


Hannayenshi dake cikin nata ya kara damkewa exactly what yassar told him ta sake maimaitawa, cikin sanyin murya yace "will you be fine?" Tayi murmushi me fad'i har fararan hakwaranta na bayyana ta gyad'a mishi kai fisgo hannunta yayi zuwa jikinshi ya rungume, sun jima a haka kan ta d'aga tace "Ina so na koma kd tunda ka warke" kwa'be fuska yayi yace "tun yanzu?" Tace "I can't trust my children with Isma'il tunda ya fara shiga harkarsu harda duka komai ze iya faruwa so the earlier the best"


Lips d'inshi ya taune yace "hmm he dares to touch my child, after touching the love of my life, my woman, please my life ki janye alkawarin da kika sa na d'aukar miki" girgiza kai tayi tace "ka barshi da Allah I can't let you get back to him ka kyaleshi ai Allah baya bacci ko kamanta yace In an zaluncemu mu kai kara adu'ar wadda aka zalunta kar'babbiya ce? I want him to confess with his mouth".

         Shiru yayi kan yace "as you wish, gobe driver ze biyo motar haya yazo se ya maidaki".


**********


"Baba kayi aiki iya aiki kayiwa na waje ma bare ni? In kud'i ne zan sakar maka but Ina so In shiga gidan chan da karfi na, matarshi er renin hankalice kayi min maganinta" bubbuga kasa baba ya cigaba da yi a hasale cikin rashin tarbiya tace "Da kai fah nakeyi ka kyaleni".


"Ke dallah chan aikinki nakeyi kin dakatar dani tukuna ma biyani kan In fad'amiki taimakon da na miki yau" jakanta ta bud'e ta dibo kud'in ta watsa mishi baki a hangale ya kwashesu tsab kan yace "Ina waenda sukazo neman aurenki?" Tace "Ina ji" yace "ai da suka fita magana sukayi akan gaskiya bazasu amince da wannan auren ba gidan nan ba wani tarbiya" waro ido tayi tace "mene? Yanzu me ka musu?".


Dariya ya kwashe dashi yace "kwantar da hankalinki mukayiwa wasu ma bare na cikinmu hahahahahhaha, rufe musu baki nayi kaman na sani Ina gama aiki kuwa mutumin ki ya kirasu akan su zo su janye baya so zageshi sukayi tas anan na san sun kamu bakinsu ya rufe ruff" ajiyar zuciya ta sauke tare da kara kwaso kud'i ta bashi tace "aikinka na kyau" dariya ya kyakyace dashi tare da yiwa kanshi kirari.

          "Shi Saif d'in ba abinda za'a mishi bana son tsanan nan Ina so ya soni kaman gwal" wani dariyan yayi yace "aikinshi baze yiwu kina waje ba se kin shiga ciki a jikinki za'ayi aikin da ya kusanceki an gama hahahaha" had'e rai tayi kan tace "ita munafukar uwarshi ni kad'ai na isa maganinta, wanchan shegiyar karuwar matar tashi fah?" Bubbuga kasa yayi kan ya kwashe da wata irin dariya na shed'anu.....                         🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA....💦🍇

    *Baya chanza d'and'anon teku*

     *Fatima Muhammad Gurin*

**Gureenjo6763 on wattpad**


           'Yar Mutan Adamawa


    *P9*


"Hahahahaha ita tsari ne a jikinta sossai amma ki bani lokaci zan san yadda na ra'beta me kike so a mata?" Cikin had'e rai tace "duk abinda kaga yafi dacewa, a sata warin ja'ba, ko a sa mishi mugun tsanarta a zuciyarshi, ko a haukatata ko ma a kasheta gabad'aya".

      "An gama ki sa ido kiyi kallo" mikewa tayi cikin farin ciki ta shige gidan ranan tsabar farin ciki haka ta hana innarsu girki se sayowa kowa takeaway tayi yayanta har kud'in shaye shayenshi ta bashi.


******


"Yakumbo kin tabbatar da hankalin yarinyar karfa muje garin neman kiba mu samo rama" cewar ya sukaina, "kayya ke kam sukaina tunda yakumbo tace miki tana da hankali Ai baza ta miki karya ba ko kin fita son samun natsuwar Saif d'inne" zata hayyayyako mata kenan yakumbo tace "bance ku fara sana'ar ba, yarinya dae da hankalinta ga natsuwa ga kuma kyau Allah ya bata tabarakallah, yanzu ke tala tunda sana'anki ne had'a lefe se ki had'a mishi zan tabbatar ya baki kud'in da ze isa har ya rage".

       Kallon sukaina tayi tace "se ki d'an had'a mana shagali na gidan maza don de ba za'a yi bukin er kirki mu dangin maza bamuyi rausaya ba zan sashi baki kud'in kun san halin kanin naku" nan suka ci gaba da tsara abinda za'ayi ba tare da ko innani ta sani ba.+


***********


Washegari da wuri driver yaje ya taho da ita kaman karsu rabu da mijin nata ko a fuska bata sake nuna mishi alamun damuwa akan aurenshin ba hakan ne ya kwantar mishi da hankali har ya sake ya dena damuwa sossai dukda har lokacin bawai son auren ko son zama da zuby yake ba, ba yadda ya iya ne kawai.


Da kanshi ya had'a mata T-shirt's d'inshi kusan goma a wata karamar jaka tunda dama bata zo da akwati ba dayake tana da wasu kaya nan, da kyar suka rabu suna masu kewan juna.


Suna isowa kaduna unguwan rimi suka nufa daidai gidansu yayi parking cewa tayi "ka bani key d'in ga wannan ka hau adaidaita ka tafi don zan jima anan" amsa yayi cikin ladabi yace "Toh hajiya an gode" ya bata key d'in ya fita itama ta fito ta rufe motar ta shige babban gate d'insu na gidan karo suka kusa yi da juna ba don tayi azamar kaucewa ba da ba abinda ze hanata fad'a mishi.


"Auzubillahi minnashaid'anir rajeem" waro ido yayi yana had'e rai yace "ke nine shaid'anin?" Harara ta banka mishi tace "wallahi ka fi karfin shaid'an kai kam, munafuki kawai, azzalumi me fuska biyu wallahi karshenka baze yi kyau ba" lip d'inshi ya taune a da farko farko da yayi mata wannan mummunan aika aikan tsoronshi take kaman ranta ko ganinshi tayi se tayi kaman zata suma amma yanzu tana da bakin mishi rashin kunya.


Murmushi ya saki tare da d'aga kafad'a yace "banga laifinki ba babe, baki gayawa marasa tarbiyar yaran nan naki matsayina bane?" Dariyar takaici tayi kan Tace "rashin tarbiyya!! Kai ashe akwai wadda yafika rashin tarbiyya?" Gyara tsayuwarta tayi ta cigaba da cewa "bari kaji ingayama ba shaatin da ka sani bace na da yanzu a gabanka, In na so da kalma d'aya tak wallahi se in 'batar da kai a duniya Ina so In ja maka kunne ka fitar harkar yarana sbd ba abinda ya had'asu da kai In kuwa kaki ji kayi kuka da kanka, d'an akuya kawai".


Ta juya ta wuce ta barshi nan sake da baki ranshi na tafasa Lallai yarinyar nan ta mugun rainashi ya kamata ya karasa lalata mata rayuwa kan ya kuma barin garin se yaga bakin rashin kunya daga ita har banzayen yaranta kwafa yayi ya juya ya fice.


"Assalamu alaikum" "yeeeyyyyyyy oyoyo maami" Da gudu yaran nata suka taso suka rungumeta suna me farin cikin ganinta, itama cikin farin ciki ta tarbesu, seda suka gama murnansu kan suka kyaleta ta zauna ta gaisa da mamah da Abba da suke ta murmushin ganinta, Abba yace "Maraba uwata ya jikin mahaifinsun?" Tace "Abba ya ji sauki dama ba sossai bane hatsarin Allah ya takaita" yace "Toh Allah yaci gaba da tsarewa" ta amsa da "Ameen, Arwa kama kannenki kuje d'aki ganinan zuwa" kama neeha da sameer tayi yasmin ta bi ta a baya suka shige.


Kanta a kasa tace "Abba babansu neeha ze kara aure saura ma wata biyu In shaa Allah" murmushi yayi yace "shiyasa nake sonki uwata akwai jarumta, Allah ya baki hakuri da juriya kinji?" Hawaye ta fara mamah tace "a'a shaati yanzu ake yaba miki kuma shine zaki fara kuka?" Share hawayenta tayi tace "ku tayani da adu'a Sannan dan Allah Abba, maamah ku yafemini ko bayan raina ku min adu'a".


Abba yace "mun riga mun yafe miki tuntuni uwata Sannan rai da rayuwa duk na Allah ne kika sani ko mu rigaki mutuwa?" Girgiza kai tayi cikin kuka ita kam ta san bazata iya rayuwa a haka ba inde har zuby ta shigo gidanta ta kwana da sanin se ta rabata da Saif ko ta wani hali, In kuwa babu Saif a rayuwarta to babu ita, mamah ce tace "me takamammen abinda ke damunki Aisha?" Shiru tayi seda baba yace "mamana menene?" "Zubaida kawata mahaifiyarshi ta sashi aure".


"Innalillahi wainna ilaihi rajiun" Mama ta furta idanunta na kawo ruwa itakam Aisha haka Allah ya kaddaro mata daga wannan se wannan, "Aisha!!" Yaune rana na biyu da Abba ya kira sunanta haka, "Adu'a yafi karfin komai kinji? Karki sa damuwa a ranki zamu tayaki da adu'a kema ki cigaba dayi In baki da hakkin kowa Allah baze bari ta cutar dake ba kinji?".


Abba ya riga ya san zubaida kuma ya jima da hana Aishan harka da ita sbd ya san mahaifinta malamin tsubbu ne, nasiha suka cigaba da mata har ta sake hankalinta ya kwanta taji wani natsuwa iyaye kenan, se dare kan ta kwashe yaranta suka tafi suka ci gaba da rayuwa yadda suka saba cikin soyayya da kulawa da tsantar shakuwa .


********


A KWANA A TASHI


Yau saura sati d'aya chip bukin zubaida da saif, ba ta hanyar da Saif be bi ba Don dakatar da auren nan amma abin yaci tura yakumbo tayi baje baje baba kuwa ya tare duk wani hanya, abinda yafi d'aga mishi hankali yadda bukin na matsowa Aisha na ramewa Don abin ya kasa barin ranta dukda tana iya kokarinta na kawar da tunanin.


Innani da Aisha har gida suka zo suka kwantar mata da hankali sossai, hajja kuwa har gida take zuwa ta bata abubuwa itade tana anfani dasu ne kawai amma ta san ba ta nan zuby zata zo ba, gwara kowacce irin Kishiya akan zubaida a gareta duk yadda zata misalta halinta ba ganewa za'ayi ba inba zama ne ya had'aka da ita ba.


Tun last week yazo kaduna yassar ya kar'bar mishi three weeks leave ba tare da ya ma sani ba, ta wani fannin ya so hutun ta wani fannin kuma be so ba, ya so hutun ne sbd yana son kasancewa da Aisha yana so ya nuna mata babu d'igon sonta da ya ragu a zuciyarshi se ma karuwa dayayi, kuma yayi nasara a sati d'ayan nan wani irin holewa suke yazo kuma yaran na hutu kullum se sun fita yawo wurare daban daban.


Be so hutun ba sbd baya fata yaje d'aurin auren nashi kuma bazashi ba, kaman yau suna zaune gabad'aya a parlor suna cin popcorn dukkansu kananan kaya ne jikinsu har shaati wando Jeans ne da wani vest brown jikinta cikinta ya d'an fara fitowa, kanta ba d'ankwali se kitson calaba da aka mata kanana ya zubo suma yaran duk calaba kansu harda beats.


"Please please please paapa" neeha ke ta aikin wannan roko akan ya tashi su fita Wani children park sabo da aka bud'e, kallon shaati yayi yace "yarinyar nan bazata kasheni ba, Ai duk ke ta biyo mutum in ya so abu kaman d'a ya so fita daga cikin mahaifiyarshi" waro ido tayi tace "ni fah kace? Nide ba ruwana Allah, Neeha ana shan ice cream a wurin?" Da sauri yasmin tace "har samosa" Arwa tace "and cock" da sauri Aisha ta mike tace "oya please papa tashi muje" dafe goshi yayi yace "shikenan kuma" had'a baki sukayi sukace "please" mikewa yayi yace "ohk ku tashi mu tafi".


Ihun murna sukayi kan suka mike kowa yaje ya shiryo duk After dress suka d'aura har ita suka yafa gyale suka fito ya d'aukesu ana tafiya ana hira da wasa da dariya har suka isa yace kowa yayi ordering abinda yake so nan fah suka wuce suka bar iyayen nasu, samosa da cock ta fara ci kan tayo ordern ice cream, suna soyayyarsu tana sha ze iya rantsewa ba flavourn da bata sha ba a wurin.


Sun jima sossai Don seda suka taya yara wasa harda hide and seek gwanin sha'awa sun ajiye tarihi sossai a lokacin, sun baje akan grass carpet suna hutawa se ji sukayi ance "hi fam" da sauri duk suka juyo d'an murmushi Aisha tayi kan ta kawar da kanta tana mikewa tace "guys ku tashi mu tafi" mikewa sukayi taja yaran suka wuce tana jin lokacin da tace "magana zamuyi" juyawa tayi se taga ya tsaya da sauri ta juyo suka karasa jikin mota suna jiranshi.


"Mene?" Wani irin kallo ta mishi kan tace "tambaya ma kake? Ka fa san zuwa yanzu bukinmu saura sati guda baka ta'ba kirana ba In na kira baka d'agawa nayi text baka min reply" yace "wai ke kam mayya ce? Nace bana sonki bana sonki na tsaneki amma kin nace min bari kiji zan aureki kawai sbd umarnin mahaifiyata amma ki sani bazan ta'ba sonki ba" a hasale tace "kana nufin duk events d'in da na shirya bakka zuwa?" Yace "yes bazani ba and ba wadda ya isa sani zuwa dole an tirsasani aurenki amma ki sani baza a ta'ba tursasani zama dake dole ba, kinga tafiyata" ya juya ya wuce.


A cikin mota ya samesu shiga kawai yayi yaja suka wuce ba tare da yayiwa kowa magana ba, har suka isa gida yaran ne kawai masu hira direct d'akinshi ya wuce ta bishi a baya "lokuta dayawa muna bari fushi ya rinjayemu har hakan yasa a illatar damu ta wannan hanyar, baka san yawaita fushi ba kyau ba? Uhmm" ta furta a hankali.


Kwafa yayi yace "bazaki gane bane" Tace "ba kuwa abunda zan gane roohul na'im, it's high time da zaka ajiye duk wani fushi da tsana na zubaida ka rungumeta hannu bibbiyu sbd bazan so ka tashi gaban ubangijinmu da shanyayyen 'barin jiki ba, dole mu rungumeta a duk yadda tazo mana" mikewa yyi kawai ya fad'a toilet ba tare da ya ce mata komai ba.


Bayan ya fito ya kama sameer suka wuce masallaci Domin mika sallar magrib, bayan sun Idar ya tura sameer gida yayinda shi kuwa ya d'auki mota ya fice se gidan yakumbo tun safe tace in ya samu time ya zo tana son magana dashi ranshi a had'e ya shiga gidan ya tabbatar maganan da ya shafi zubaida ne don ita yanzu bata da magana In ba na zubaida ba.


Ai ko kaman ya sani bayan sun gaisa tace "ni kam a ina kayi shirin ajiye zubaida ne?" Gyara zama yayi yace "irin gidan da ta fito a ciki nake nema amma har yanzu ban samu ba kila ko se mun dangana da kauye" dakuwa ta mishi tace "kaci gidanku saifullahi wai ni kam na zama sa'ar wasanke ne? Ko raina ni zakayi Don kaga ba idon mahaifinka?" Se ta sa kuka.


Kara had'e fuskanshi yayi yace "to wai ni yakumbo ya kike so nayi ne? Sani auren dolen da kikayi duk be isa ba se kin ci gaba da takurani akan wannan yarinyar ni fah abinda kikeyi Allah shi ke kara sani tsanarta" kuka taci gaba da yi ba tare da tace komai ba ganin da gaske kukan take yasa cikin sanyi yace "kiyi hakuri ki dena mini kuka, a ina kikeso a ajiyeta?".


Tace "ka nema mata gida kato irin na Aisha ko ka ajiyesu gida d'aya" yayi saurin cewa "inaaa bazan iya ajiyeta gida d'aya da iyalina ba hakannan ita kad'ai bazan iya nema mata gida irin na Aisha ba, zan de sama mata gida ba irin nasu ba shikenan?" Ta gyad'a kai ya mike ya fice da sulaiman sukayi sallah a massallacin kofar gidan bayan sun fito suka wuce gidanshi tare.


Shakuwa sossai ke tsakaninshi da Aisha da sauran yaran tunda ya dawo kullum se yaje sun sha hira kan yake dawowa gida, a mota yake bashi labarin halin da yake ciki, kwantar mishi da hankali yayi tayi inda ya d'aura da "yaya In ka sa damuwa a ranka Aisha kuma tayi yaya? Na tabbatar tana iya kokarin ta wurin kau da kai amma kai In baka bata kwarin gwiwa ba zata karaya, na san duk su yakumbo ba sonta sukeyi ba kuma sbd tsananta ne yasa suka kara aure amma ya zaka yi? Ba'a chanzawa tuwo suna kaman yadda ba'a chanza uwa da kuma en uwa so adu'a, hakuri abu biyun nan shine mafita".


Da wannan hirar suka isa gida yaran kuwa sunyi farin cikin ganin uncle Sulaiman, nan da nan hira ta 'barke anan yaci abinci ana raha da wasa se kusan 9 ya tafi, Arwa ta kama su neeha zuwa makwancinsu Don basa wuce 9 ba suyi bacci ba, ta sauya musu kaya nan da nan bacci ya kwashesu su, ita da yasmin suka wuce d'akinsu kowacce ta kwanta akan gadonta.


Aisha ce ta karasa tattare sauran abubuwan parlorn ganin iPad d'in yasmin yasa ta d'auka ta nufi d'akin Don ajiye mata ta kuma tabbatar sun kwanta Don ta san halinsu, "Adda kin san aure paapa ze yi saura sati d'aya?" Ajiyar zuciya Arwa ta sauke tace "na sani yasmin kuma Anty zuby kawar maami ze aura" yasmin tace "ni kam Ina tsoro Adda haka fah Zainab d'in class d'inmu babansu ya auro kawar mamansu daga baya ya dena sonsu har mamansu bakiga ba kullum se tayi kuka? Kenan muma haka zatayi mana?".


Arwa tace "hmm ni de tun da chan wallahi bana sonta gashi zata zo ta aure mana baba in kin lura kullum maami se tayi kuka" yasmin tace "kuma In munyi magana se tace abu ne ya fad'a idanunta" arwa tace "ko wannan shine ake cewa auren cin am..." tura kofar da shaati tayi yasa sukayi shiru.


Ta shiga ta samu wuri ta zauna Bayan ta ajiyewa yasmin iPad d'in a bedside tace "ku tashi muyi magana" mikewa sukayi suka zauna had'e rai tayi tace "kuna so In 'bata daku?" Kai suka girgiza tace "to kar na karaji kuna irin wannan maganan tsakaninku Arwa babanku kike shirin cewa ze yi auren cin amana? A ina kika san auren cin amana? Me ma cin amana yake nufi?".


Kanta kasa tace "kiyi hakuri" gwa'be mata baki tayi tace "Sannan yaushe kika fara rashin jin magana bance kar a kara cewa babba Kin tsaneshi ba? Wato har kin fara koyawa kanwarki rashin ji" kuka ta fara tana cewa "sorry" juyawa tayi ga yasmin tace "yasmin yaddikon zainab daban haka Anty zubaidah daban ita bazata rabaku da Paapa d'inku ba kinji? Sannan In ma hakan ya faru ke bazaki zama kaman ita kullum kuka ba adu'a zaki ma paapa kinji?".


Kai ta gyad'a tace "we are sorry Maami" murmushi tayi tace "apologies accepted" murmushi sukayi Arwa ta share hawayenta, shaati tace "ayi adu'ar bacci maza a kwanta" adua sukayi suka shafa suka kwanta ta jima anan a zaune har seda ya leko kan ta mike ta kashe musu wuta ta fita.


RANAR DAURIN AURE


Duk cikin en uwanta ba wadda yaje sbd ta hanasu, ta tabbatar In sun zo d'inma banda bakin ciki ba abunda zasu kara mata, a jiya da dare innani da Aisha suka kawo mata kayan fad'ar Kishiya akwati bakwai a shake da kaya wadda shi ya bawa Aisha kud'i ta had'o mata.


Tarba sossai ta musu a d'akin saukan baki tasa aka ajiye mata kayan nasiha innani ta kara mata kan suka tafi, bayan tafiyansu yassar ya zo kayan Saif ya kawo mata wadda ze sa gobe, shima ya mata nasiha da ban hakuri tana jin daad'in yadda kowa ke tausarta auren nan ya kara mata shakuwa da iyayenta kullum se sun kirata sun kwantar mata da hankali.


Ganin 7 yayi yasa ta fara bubbugashi "tashi roohul na'im mana tun fah d'azu nake tashinka but kaki tashi na san kana jina please tashi" mikewa yayi ya zauna yace "na tashi me zanyi?" Tace "wanka, shiryawa ka tafi d'aurin aurenka" komawa yayi ya kwanta yana cewa "bazani ba...." be gama rufe baki ba tace "wallahi se ka je" wani irin kallon mamaki ya mata.


A mamakance yace "musu zaki farayi dani?" Tace "a'a amma tunda na rantse se kaje, me kake so ka gayama mutane? Baka san rashin zuwanka ni ze janyowa magana ba?" A sanyaye tace "yanzu ma ba tsira nayi ba duk wasu events da akayi na dangin amarya da dangin ango kin zuwa kayi, ni kuma ya shafa bayan ba yadda banyi ba kaki zuwa, so please ka tashi ka shirya ka tafi" ba tare da yace komai ba ya mike ya shige toilet wanka yayi ya fito.


Kayan da yassar ya kawo ta fitar mai farar gezna er ciki da babbar riga da taji zubi da blue zare, ta fitar mishi da kanta ta taimaka mai ya shirya ta kafa mishi zannarshi a kai ta kawo half cover dark blue ta ajiye mai ya saka ta d'auko perfumes d'inshi ta fesa mishi yayi kyau sossai gwanin a sace wadda hakan ya dakar mata zuciya.


Car keys da wayoyinshi ta mika mai ya kar'ba yana kallonta, tace "se ka dawo Allah ya tsare ya sanya alkhairi" ta juya mishi baya tana jiran ya fita se jinshi tayi a jikinta cikin rarrashi yace "na San it's not easy for you but ki kara hakuri na san ke me hakuri ce Allah yayi miki albarka, Allah yasa kece uwargidata mafi soyuwa a raina har a aljannah, Ina sonki Aisha ki sa wannan a ranki" ya juya ya fice yayinda ta fashe da kuka tana zubewa bakin gado.                    🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA....💦🍇

     *Baya chanza d'and'anon teku*


      *Fatima Muhammad Gurin*

  **Gureenjo6763 on wattpad**


     'Yar Mutan Adamawa


*dedicated to Gureenjo Novels group kuna sani nishad'i wollah team shaati and team zuby duk Ina yinku inajin daad'in comments d'inku Allah ya barmu tare much love🥰🥰*


     *P10*


Ta jima zaune a wurin tana kuka kan ta mike ta share fuskanta ta fito a babban parlor ta samu yaran duk suna zaune cikinsu ta shiga ta zauna shiruu minti minti ta kalli agogo tana kiyasta saura mintuna nawa suka rage a d'aura auren, sallaman da taji ne yasa ta kakalo murmushi tana kallon yaran da suka tashi da gudu suna "oyoyo Anty Aisha".


Rungumesu tayi tace "oyoyo yaran Anty Aisha" Da azama Arwa tasa hannu a kunce mata baby nan Aisha ta kunce mata tayi d'aki da sauri yayinda sauran yaran suka bi bayanta da gudu, murmushi Aisha tayi tace "In kun kwantar da hankalinku kwanan nan zaku ga baby a gidanku sarakan son baby's".+


Dariya shaati tayi tana cewa "a wurin Amarya ko?" Tsaki Aisha tayi tace "ko ba Amarya ba" murmushi kawai shaati tayi tana mikewa tace "kin kuwa zo a daidai dama tunanin mikewa In fara aikin abincin da za'a kai amarya dashi nake se muje ki chanza ki tayani" Aisha tace "Abinci zakiyi musu?" Shaati tace "Eh mana mamah tace ya kamata inyi abinci Don In sun kawota nan kan su wuce gidanta su tafi dashi haka akeyi".


Aisha tace "na san su yakumbo zasuyi da baki wahalar da kanki ba shaati" hannunta ta kama ta jaa suka wuce d'akinta tshirt da zani ta bata, ta chanza tana mitan da ma bata zo ba dariya kawai shaati ke mata nan suka wuce kitchen suka fara aikin, suna yi suna hira a gaskiya shaati tayi matukar jin daad'in zuwan Aisha ba wai Don aiki ba se Don ta d'ebe mata rabi daga cikin damuwanta bata barta ta shiga tunani ko na minti d'aya ba.


Karfe 11 ya shigo gidan a gajiye ya zube parlor sam ya hana duk wasu abokanshi da yassar ya gayyata zuwar mishi gida sbd ya tabbatar taron Jama'a ze dinga tuna mata buki fah ake bukin kuma na mijinta, bata san shigowarshi ba se fitowa da tayi don saka zobo a fridge d'in parlor ta ganshi kishingid'e idanunshi a lumshe babbar riga da hula ajiye gefenshi.


"Ango Ango" bud'e idanunshi yayi ya watsa mata harara dariya tayi tana cewa "Toh ni kuma me nayi? Uhm na san yunwa ya gama ci min kai mu karasa d'aki ka watsa ruwa kan In had'oma abinci kaji?" Ba tare da yace komai ba ya ci gaba da kallonta har ta gama sa zobon a fridge ta karaso ta d'auki hula da babban rigan ya mike suka jera zuwa d'akinshi suna shiga ya fisgo hannunta tare da mannata da kofa cikin wani yanayi yace "wato na lura rayuwata ko kishi na bakiyi ko?".


Waro ido tayi tana murmushi tace "haka kace dae roohul na'im amma ni ko nake kishinka, kana bukatar kwarin gwiwa daga gareni bana maka son da zan kasance me son zuciya, Ina tayaka murnan kara aure Allah ya bamu zaman lafiya" ta bi ta gefenshi ta wuce tana kokarin mai da hawayen idanunta, toilet ta shiga ta had'a mishi ruwan wanka ta fito inda ta barshi anan ta sameshi.


"Kaje kayi wanka bara na zubo abinci" ajiyar zuciya ya sauke yadda take yin nan yana sa shi feeling guilty kaman be mata adalci ba, wani iri yake jinshi gabad'aya a gabanta kamar marar gaskiya toilet d'in ya shiga Bayan ya cire kaya ita kuma ta fice, a kitchen ta samu Aisha na kokarin rufe coolern da ta zuba pepper chicken murmushi ta saki tana cewa "sannu da aiki" Aisha tace "sannun mu, naji kaman yaya ya dawo?" Tace "eh ya kwaso yunwa bari In zuba mishi abinci" fried rice d'in ta d'iba mishi a plate ta d'iba yankakkun cabbage dasu carrots a wani bowl kan ta had'a da mayonnaise basu had'a bane sbd kar yayi ruwa.


Akan tray ta shirya kan ta d'auki wani saucer ta sa mishi pepper chicken ta sa mishi zobo ta kai mai be fito ba hakan yasa ta ajiye ta fiddo mishi kayan sawa kan ta fice, karasa ayyukan sukayi ta gyara kitchen d'in ba ita ta fito ba se da ana kiran sallahn azahar Aisha dake ba babynta nono ta d'ago ta kalleta tace "amma Namesake kin yi matukar kokari ina ganin kokarinki wallahi" murmushi kawai tayi ita kad'ai ta san abinda take ji a zuciyarta, "namesake kenan, mu karasa d'akina ki samu ki watsa ruwa ki huta kin sha aiki".


Aisha tace "haba dae se kace wacce bata saba aiki ba, je ki fara shiga In kin fito se in je Inyi" wucewa tayi zuwa d'akinta ta tube tayo wanka tare da alwala bayan ta fito ta shafa mai ta feshe jikinta da body's pray kan ta sa doguwar hijab har kasa da zani ta tada sallah, bayan ta idar ta koma gaban mirror ta chanchad'a ado na ji da gani tayi wani irin kyau sossai ta d'auko wata atampha riga da skirt 16pieces ta saka yadda d'inkin ya amsheta ko bazakace tana da d'a ko d'aya ba.


'Daurinta ta kafa kan ta kara feshe turaruka daidai lokacin taji an shigo ba tare da ta juya ba tace "namesake wai se yanzu kika gama shayar da ita? Tuntuni nake ta jiranki ban gama shiryawa bane da kin ganni na janyoki" jin shiru ba'a amsa ba yasa ta juyo se ta ganshi tsaye rike da handle d'in kofa yana kallonta.


Misalta irin kyaun da ta mishi 'bata baki ne, musamman da ta sakar mishi murmushi tace "sorry na barka kai kad'ai ko? Wanka nazo nayi shiyasa baka ganni ba" cigaba da kallonta yayi tayi mugun tafiya da imaninshi a ko yaushe ya ganta se yaga kaman kara sabunta mishi ita akeyi matsota ya fara wadda ita hakan ya bata dariya, ya iya tafiya wata duniyar In yana kallonta ta sheda wannan, mikewa tayi fuskanta d'auke da murmushi tace "roohul na'im" Shiru tayi jinshi a jikinta ya rungumeta kam tare da lumshe idanu.


A hankali yace "hope ba fushi kike dani ba?" Murmushi ta saki tana mikewa daga jikinshi "na isa fushi da tsarkakken ruhi? Me ka gani?" Kumatunta ya shafa yace "you will always be the love of my life forever and ever babu wata mace nan duniya da zan mata ko da rabin son da nake miki ne, Just like wine gets sweeter as it gets older, you keep getting so beautiful with age. I fall a little more in love with you with every passing day".


Ta kasa dena blushing what's more joyful than kaji mijinka na fad'amaka matsayinka a zuciyarshi, a hankali ta furta "I soo much love you and I promise to be with you in shaa Allah throughout your life ko ta wani irin hali" murmushi me narkar da zuciya ya sakar mata "you look so beautiful" janyewa tayi tace "muje parlor in ba yaran nan abinci I know sun fara jin yunwa yanzu".


Yace "mamansu ta basu" Tace "to muje dae zata shigo tayi wanka" yace "nide mu dawwama a haka" yadda yayi maganan cikin wani yanayi ya sanyata saka dariya tace "nop lets stay for a while se mu tafi yayi maka?" Yace "yes" sun d'an jima a haka tana kwance kan jikinshi kan ta mike ta kama hannunshi be Musa ba suka fito parlorn yaran sun gama cin abinci abin mamaki sadiya, Zainab, ya meena, ya fadeela, Anty sharifah matar ya majeed da Anty Murja matar ya mujeeb se hafsa duk da yaransu sun cika parlorn ana ta hira.


Murmushi ta saki taji daad'in ganinsu dukda ta san bazasu tafi basu kunsa mata wani bakin cikin ba amma ko yaya da daad'i en uwanka su zo maka haka rabon da su had'u haka a gidanta tun sunan neeha, "maraba sannunku da zuwa ashe kun zo?" Anty murja tace "Eh wallahi ance kina wanka, Masha Allah irin wannan kyau Shaati Ai se ayi mistaken d'inki da amarya" dariya kawai tayi tana sauraran su ya meena na ta jan saif da wasa "ango kasha kamshi" "Ango mijin Amarya" "Angon zuby bada kanka a sare kaje gida kace ya fad'i" irin haka dae.


Ko ta nuna musu taji, se murmushi take tana wasa da yaran en uwan nata shi kuwa da kyar yayi murmushi guda ya juya ya koma d'aki yana tsaki, Aisha ta wuce room d'in shaati don yin wanka da sallah yayinda shaati ta zubowa su ya fadeela abinci ta zubawa yaransu Allah ya sa abincin sun yishi dayawa.


Bayan la'asar ya mujeeb yazo dashi da Sulaiman suka dinga janta da wasa ta kuwa kara sakewa sossai su fadeela da zainab se kallonta sukeyi ko zasuga tana bakin ciki amma tunda sukazo fuskanta be rabu da dariya da murmushi ba wadda hakan ya 'bula su, Har Bayan Isha suna nan sbd se sunga Amarya kan su wuce, Mama ta taimaketa da se ta sake d'aura wani abincin tunda na Amarya da en uwanta kawai ta rage, Mama ta turo en aikinta da abinci shi en uwan nata suka ci bayan isha.


Bayan tayi sallah ta sauya kaya zuwa wata lace orange me shegiyar tsada tayi ado da gwalagwalanta ta kara gyare fuskanta cikinta ya d'an d'ago gwanin sha'awa se ta kara wani kyau da sheki flat shoe ta sanya ta fito suka ci gaba da hira da Aisha da kuma Anty murja, bata jima da fitowa ba aka fara shigowa en kawo Amarya sunzo dib dib dib haka gabanta ke fad'uwa amma ta daure tayi ta maza.


Se murmushi takeyi nan kuwa en uwan zuby da kawayenta suka cika mata gida da gud'a da habaice habaice, ko a fuska bata nuna alamun tana gane abinda sukeyi ba se mikewa tayi ta tari zuby da "lale maraba Amaryarmu sannu da shigowa" zaunar da zuby tayi kan ta zauna gefenta ta cewa dattijan da suka sakankance suna kallonta "bismillahnmu ku zauna Mama" zama sukayi suka gaisa a mutunce kan suka damka mata amanar amarya ta amsa kuwa a sake.


Ta mike ta kira Aisha sukayi kitchen zobo da ruwa suka zuzzuba a tray suka kawo musu aiko suka sha suna kallonta tana jeka ka dawo da coololi masu tsada da ta zuzzuba musu abinci, se jikinsu yayi sanyi banda en barikin kawayenta da suke taunan cingam kaman karuwai suna wani tas tas tas dashi kowacce taji attach da bleaching abinda ya d'an rufa musu asiri ma arzikin atamphar da sukayi anko ba wacce ke da gyale cikinsu.


Ita kam har ga Allah banda warin Attachment ba abinda take ji a jikinsu har amaryar ta tsani abin kyankyaminshi take sossai, haka ta daure iya dauriya har suka tattari abincin suka d'auki amaryarsu suka wuce, suna fita ta saki wata ajiyar zuciya tana kallon Anty murja dake waya cikin murmushi tana cewa "Ai autanki jarumace  Mama komai ya tafi daidai har sun wuce" kau da kai tayi tana murmushin takaici.


Sallamanta su zainab sukayi suka fara watsewa Anty murja da Aisha ne suka tattare mata gidan suka saka mata turarukan wuta nan taji parlorn nata ya dawo daidai kishingid'a da kujera tayi ta lumshe ido kanta da bayanta kaman zasu cire, haka ta lalla'ba ta raka Anty murja mota se lokacin Saif ya fito daga d'aki yayi rakiyar ya mujeeb godiya sossai ta musu kan suka wuce Aisha ma ta fito ta wuce bayan tasha dunbin godiya daga garesu nuna musu tayi ba komai Ai Saif ya musu abinda bazasu ta'ba mantawa ba da ba Don shi ba Allah kad'ai ya san irin halin da suke ciki yanzu.


Ya tsayawa dukkanninsu bayan ubansu be raye en uwan mahaifiyarsu kuma sun 'bace sakamakunsu na fulanin tashi, bayan ta wuce suna shigowa parlor kawai jiri ya kwasheta Allah ya taimaka yana hankalce da ita da sede yaji fad'uwanta "subhanallah Hayati dama baki da lafiya shine baki gayamin ba?" Murmushi kawai tayi ya kwantar da ita kan kujera tare da dukawa gabanta yasa hannu a goshinta tare da lumshe ido "d'an gajiyace kawai ya sa min stress na sani ba wa.." Shiru tayi jin yana cewa "pls mamah kizo yanzu bata da lafiya" girgiza kai kawai tayi.


Ta lumshe idanunta a haka suka zauna yana ta aikin jera mata Sannu har suka ji sallaman mama da kyar Shaati ta bud'e idanunta tare da kokarin mikewa zaune ya taimaka mata ta jingina da kujeran yana amsa sallaman mama, Abba da Aisha ta gani bayan mama ne yasa hawaye ya fara zuba mata.


"Uwata na fita hakkinki dukda ke bakiyi kokarin sauke mana namu hakkin a matsayin iyayenki ba na shayar dake, tufatar dake, ciyar dake, baki ilimi na boko da arabi, amma ba abinda kika saka mana dashi se bakin ciki da dana sani, Uwata kinyi matukar sa'a kin samu Saif a matsayin wadda yake sonki so na gaskiya, In kin ga dama ki zauna In kin ga dama ki fita amma ki sani duk randa kika kuskura kika fita daga gidannan da sunan yaji ko saki ba gidana ba kuma ba na en uwana ba, bakin cikin da kika kunsa mana a baya kad'ai ya ishemu, na barki lafiya"


Wannan rana shine rana na farko kuma na karshe da Abba ya ta'ba zuwa gidan ta se kuma yau, waennan sune maganganun da Abba ya fad'a mata bayan ya kawota har tsakiyar parlorn nan, Ina zata manta, Ina zata iya manta lokacin Rayuwanta na tsaka da gur'bacewa.


"Uwata jikin ne" firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da ta fad'a da sauri ta sa hannu ta goge hawayen a sanyaye tace "a'a Abba sannu da zuwa" kokarin mikewa ta kawo mishi abin sha take wadda ta kasa, da sauri Mama ta dafata "yi zaman ki ba se kin kawo mana wani abu ba" dubata ta fara dayake Mama ta kasance babbar Doctor duk haihuwan yaranta a hannunta sukeyi hakanan duk wani ciwo nasu itace likitarsu.


Paper da biro ta fiddo ta fara rubutu yayinda Saif ya duka kasa yana gaida Abba Bayan ta gama sun gaisa ta mika mishi "samo mana wannan stress d'inne ya mata yawa ga karamin ciki Sannan ga damuwa da ta sawa kanta" su Arwa ne suka fito cikin murna suka fara gaida Abba amma ganin mahaifiyarsu kwance se suka shiga damuwa, kar'ba yayi ya fice, nan su Arwa sukayi cirko cirko yayinda Abba ya fara bawa Aisha labarin wani kissa akan kishi da maganinshi wadda adu'o'i ne da mayarwa Allah lamarinshi, suna nan har saif ya dawo Mama ta taimaka mata suka shiga d'aki bayan Tayi sallama da Abba cikin fara'a Don ita zuwanshi kad'ai ya wanke mata zuciya.


Ruwa mama tasa mata bayan tayi wasu allurai ciki ta taimaka mata ta cire lace d'in ta saka rigan bacci nan da nan bacci ya kwasheta Mama ta fito ta shiga d'akin su Arwa ta had'a musu kayansu a wata jaka suka fito ta cewa Saif "zan tafi dasu samun ta d'an huta zan turo baaba Larai ta kwana da ita" kanshi kasa yace "Mama ba se kin turo ta ba ni zan kula da ita" Mamah tace "a'a kabar Amarya da wa?" Shiru yayi kanshi kasa Abba yayi murmushi yace "kada ka damu baaba larai itace tayi renonta zata iya kulawa da ita" godiya yayi suka wuce da yaran.


Ya koma d'akinta ya zauna shi ba inda zashi, yana nan zaune har baaba larai tazo a parlor ta zauna ganinshi a d'akin, yana ta kallon kiran su yassar na shigo mishi tun 9 har ya gaji ya kashe wayanshi karfe 11 na dare yaji ana bubbuga gidan "wayene da wannan daren" ya furta yana mikewa kan ma yayi tsakiyar d'akin yakumbo ta shigo kaman an jefo ta.


Yadda ta banko kofan ne ya tashi Aisha ta bud'e ido tana kallon ikon Allah "ubanka saifullahi nace ubanka, Don ka rainamin hankali ka renani a matsayi na na mahaifiyarka In kai maka Amarya ka kyaleta kayi zamanka nan ta kirani tana kuka a tsorace? Toh wallahi ka wuce ka wuce tun ban sa'bamaka ba" kallon shaati yayi yace "yakumbo kina ga shaati ba lafi......." katseshi tayi "ba shaati ba uban shaati Ina ruwana da rashin Lafiyanta, au oho rashin lafiyar be tashi tun kan ayi aure ba se da taga kayi aure?"

"Kan bala'i" shaati ta furta a kasan makokoronta, lokacin da taji yakumbo ke cewa "daga yau har kwana bakwai da zaka gama da amarya In kazo gidannan ka wuce awa d'aya wallahi ban yafe ba Allah ya isa nono na da ka sha, Anya kuwa kana son gamawa da duniya lafiya?" Da sauri Aisha ta mike zaune ganin yadda har jikinshi ke rawa tsabar takaici da 'bacin rai a hankali tace "roohul na'im calm down, you can go don't mind me ok? Please obey her" zeyi magana tace "pleassss" ajiyar zuciya ya sauke kan ya wuce ya fita yana ji yakumbo na cewa "dayake uwarka ta baka umarni to In har an fad'i abinda be min ba da yaren da bana ji Allah ya isa".


Abinda ze bukata ya had'a a trolley ya janyo haka yakumbo ta sashi a gaba ko komawa d'akin shaati ta hanashi suka fice, ya tabbatar Aisha na chan tana kuka haka ba yadda ya iya seda ya ajiyeta gida ta kuma ja mishi kunne da gargad'i kan ta shige ya wuce gidan zubaida yana jin wani tururin 'bacin rai da tsanarta gashi ya kira Aisha wayanta a kashe ya san kashewa tayi.


Ta 'bangarenta kuwa yana fita ta had'a kai da gwiwa se kuka, bayan sun wuce baaba larai ta shigo ta dafata tace "d'iyata kiyi hakuri bala'in uwar miji ba daad'i hakuri zakiyi watarana se labari kinga ba lafiyace ta isheki ba" d'agowa tayi tana share hawayenta tace "Toh baaba" wayanta ta janyo ta kashe kan ta kalli karin ruwan saura kad'an tace "baaba ki hawo ki kwanta dare yayi In ruwan ya kare zan cire" baaba taki da farko sede sanin nacin Aisha yasa kawai ta hau ta kwanta tun tana kallonta har bacci ya kwasheta seda Aisha ta tabbatar baaban tayi bacci kan ta bud'e baabin wani kukan, ita ba kwana gidan zubaidan ne ya dameta ba, nan da kwana bakwai awa d'aya kawai ze yi da ita kuma yana cikin garin kaduna a gidan wata ba ita ba.


In ta tuna hakan se taji wani kukan ya kwace mata da kyar tayi controlling kanta ta cire ruwan taje tayo fitsari da alawala ta fara nafila.
                    🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA.....💦🍇

    *Baya chanza d'and'anon teku*


   *Fatima Muhammad Gurin*

**Gureenjo6763 on Wattpad**


         'Yar Mutan Adamawa


      *P11*


Yana shiga gidan direct d'akin da ya tanadarwa kanshi ya wuce tare da datsewa da makulli ya tube kayanshi yaje ya watsa ruwa yazo ya saka kayan bacci tare da fad'awa gado ranshi na kunan wannan aure na dole da aka mishi shi ba mace ba.

     Layin shaati yacigaba da gwadawa but har yanzu switch off jefar da wayan yayi tare da juyawa rub da ciki sake sake kawai yake akan irin rayuwar da ze yi da zuby yadda ya tsani komai nata, gashi daga zuwanta har ta fara kaishi kara wurin yakumbo abinda be ta'ba had'asu da shaati ba kai kara, yaja tsaki yafi kala d'ari kan bacci yayi awon gaba da shi.


Ta 'bangaren zuby taji shigowanshi hakan ya sata saurin d'aukan gyalenta ta yafa kan wata pigaggiyar kayan bacci da ta saka an sake attachment na yawo, tayi gaggawar komawa tsakiyar gadon ta zauna, ta jima nan zaune tun tana kirga seconds har ta shiga mintuna har ya kai awa ba shi ba labari yaye gyalen tayi ta mike "me wannan yake nufi?" Ta fad'a a fili.+


Fita tayi ta nufi room d'inshi hannu tasa ta bubbuga shiru ta murd'a nan ma Shiru, kuma bubbugawa tayi cikin bacci yaji ana mishi bugun hauka zaune ya mike yana dafe kai yace "waye?" Cikin wani siga tace "ni ce" bata gama rufe baki ba yace "ubanme zan miki?" Shiru tayi kan ta kama wani kukan kissa "dan Allah ka bud'e tsoro nakeji, Ina tajin motsi" tsaki yaja kan yace "ki wuce ki barmin kofan d'aki kan In sa'ba miki wallahi wawiya kawai marar aji".


Baki ta wangale itace ma marar aji? Hmm Allah ya kawoka hannuna ta fad'i a zuciya, "please ka taimakeni wallahi bazan iya kwana ni kad'ai ba ban saba ba" juyawa yayi yayi kwanciyarshi ba tare da yace komai ba yana jinta tayi ta magiya har ta gaji ta tafi tsaki yaja ya gyara kwanciyarshi yaci gaba da baccinshi hankali kwance.


Kiran sallahn Asuba ne ya farkar dashi dayake akwai massallaci nan kusa da su, mikewa yayi ya fad'a toilet ya watsa ruwa tare da d'auro alwala ya fito sanye da jallabiya kan ya fice massallacin bayan yayi sallah ya jima ciki Don har seda gari ya fara haske kan ya mike ya fito duk yadda ze zauna da ita ya gama tsarawa tunda yanzu ta riga ta zama matarshi ba yadda ya iya amma dole ne ta shiga taitayinta ta san wa take aure.


Ranshi a had'e ya nufi d'akinta to his biggest surprise tana nan kwance tana sharar bacci fita yayi zuwa fridge ya kuwa samu ruwan sanyi karau ya d'auko se d'akin cikin bacci taji wani irin sanyi a jikinta a firgice ta farka tana ihu yace "shut up!!! Nan ba gidan kafirai bane da zaki tashimin bacci da ihu, wuce kije ki warware wannan abin na kanki tass wallahi kar inga ko zarenshi d'aya gidana, kuma ki cire abin farcen nan naki kiyo alwala kizo kiyi sallah, awa guda na baki".


Kallon jikinta tayi rigan baccin da ya jika ya manne a fatar jikinta da ba komai kasa, kukan kirsa ta fara tana wani babbankaro mishi kirji, wani tsawa da ya daka mata bata san sadda ta hantsila tayi toilet ba, tsaki yaja "karyar iskanci kawai" ya juya ya fice a parlor ya samu wuri ya zauna yana kirga mintuna yana nan zaune yaji ana sallama mikewa yayi ya fito abin mamaki yakumboce rike da basket.


Abin dariya abin takaici kana ganinta zaka san ba karamin wuya taci kan ta iso gidan ba ko bata gane bane ko bata samu abin hawa bane Allah masani "yakumbo kece da safen nan?" Tace "eh dannan wai abinci na kawowa er kirki na san baza ta iya girki yau ba" kar'ban basket d'in yayi yace "mun gode, ki karaso mana" ganin yadda ya sake mata fuska sossai se ta zata komai ya faru daga yanzu kuma shikenan ba se ya dinga 'bata mata rai kan zancen zuby ba.


A zuciyarta tace "shege namiji hmm" a fili tace "a'a tafiya zanyi me abin hawa na jirana, tana Ina?" Murmushi yayi kan yace "tana wanka ne yakumbo" Tace "Au au too ka gaisheta In ta fito" ta juya yace "a'a bari to In kawo miki kud'in abin hawan" dakatawa tayi yaje mota ya d'auko kud'i yazo ya bata ta juya ta fice, girgiza kai yayi ya d'auki basket d'in zuwa ciki, d'iba yayi ya fara ci se Shaati ta fad'o mishi ko ta karya? Kuma gwada layinta yayi har yanzu switch off.


Ya tabbatar baaba larai bazata barta da yunwa ba, abincin yaci gaba da ci seda ya koshi tukun ya d'auki basket d'in ya kai d'akinshi ya ajiye ya fito ya nufi d'akinta, bata ciki hakan yasashi tura kofan toilet tana baje a kasan bayin ga scissors gabanta ta gugguntule attach d'in tana ta faman kuncewa tana ji'bi, murmushin mugunta yayi yana karewa tsawon asalin gashin nata kallo dariyane ya kamashi ya tabbatar wannan gashin nata se assemblyn gwai gwai don ko parking bazeyi ba.


"Awa nawa nace na baki?" Ya fad'i a kausashe tace "awa d'aya please kayi hakuri kitson ne dayawa" gira ya d'age yana cewa "Au ashe kin iya bada hakuri na kara miki minti talatin kai karki kuskura nazo na sameki nan" ya juya ya fice, kan minti talatin d'in kuwa taci sa'a ta gama ta watsa ruwa tare da yo alwala abinda ze baka mamaki alwalan karan kanshi bata iya ba.


Ta fito da naga sallahn kuwa se nace toh alwalar ma ashe ta d'an iya hmm (Allah ka rabamu da jahilci da jahilai ya rabbi ka bamu daman bawa 'ya'yanmu tarbiyya me kyau me anfani) tana iddarwa ta mike ta shafa mayukanta ta fesa turare har yana hawa Kai ta d'auko wata Jeans da crop top ta saka kan nan ba d'ankwalin gashin gasunan tsaitsaye kaman ciyawa ta fito.


Kallo d'aya ya mata ya kau da kai kusa dashi tazo tace "baby na gama" a fili ya furta "baby!!! Waye babyn naki? Feeding bottle kika gani bakina?" Wara idanu tayi a zuciyarta tace "Da gani kaman wayayye ashe dunkum ne" shi kuwa sarai ya sani iskanci ne kawai irin nashi, "ki wuce kije ki girka abinda zamu ci don ni matata ba haka take ba bata barina da yunwa haka har 8 ban karya ba".


Kwafa tayi ta nufi kitchen ranta na suya tabbas duk abubuwan da yake matan nan se ta rama yana shigowa hannunta hmmm, kwai guda hud'u ta soya hh In kunga yadda kwain nan sukayi baki kirin se ka d'auka cikin garwashi aka zuba su direct, ta had'o tea me kauri cup biyu ta fito tana zufa ta ajiye a gabanshi kallon kwain kawai da yayi seda yaji zuciyarshi na tashi kau da kai yayi.


"Ka sauko muci to" magana ne take yinshi ba respect a voice d'inta, "had'a da nawa ki cinye" Tace "ban gane ba?" Yace "abinda kikaji na ce" Shiru tayi ta gutsiri kwan da fork ta kai baki ai bata san sadda ta furzar ba, ga kuna ga gishiri da ta labta, kallon mamaki ya mata "karki kara furzar min da abinda kika riga kika sa a kazantaccen bakinki, maza ki cinye kwan nan tas don ba'a min almubazzaranci a gida na gayamiki".


Hawayen gaske ta fara gaskiya bazata iya ci ba ganin tana kuka ne yasa shi sake wani murmushi kad'an kenan daga cikin takaicin da kika kunsa min, ya fad'i a ranshi ta gefe ido yake kallon yadda take had'iye kwan kaman me had'iyar magani In ta mulmula ta jefa se ta kur'bi tea ta runtse idanu baki ya ta'be ya maida kanshi tv, tana gama ci wani irin amai ya taso mata da gudu tayi cikin d'aki zuwa toilet ta fara kwararawa tana hawaye.(nace kad'an kenan ba kince tushe a inda ba'a bukatarki ba?).


Tsaki yaja ya mike ya shiga d'aki yayi wanka tare da shiryawa cikin kananan kaya ya fito seda ya tabbatar ya rufe d'akinshi da makulli ya zare key ya saka a aljihunshi kan ya fice ko kallon d'akinta be yi ba se jin fitar motanshi tayi, gidan shaati ya nufa direct.


tana kwance kan doguwar kujera sanye take da tshirt d'inshi Ash color se kasan ta saka wando iyakarshi cinya, kanta sanye da hula bigbom sweet ne a hannunta tana sha, se jin sallamarshi tayi kaman ya san tunaninshi ne fall ranta, da sauri ta mike zaune tana murmushi shima murmushin yayi kan ya had'e rai yace "was planning not to laugh or smile idan nayi ido hud'u dake se gashi nayi ba tare da na sani ba".


Dariya tayi tana cewa "I know you can't, me nayi dama da baza'amin murmushi ba?" Zama yayi dab da ita ta kuwa kwanta kan jikinshi zuciya da banzan sake sake se take hangen zuby kwance yadda take, kenan fah da zuby ya kwana a jikinshi jiya, kenan duk abinda yake mata shi yayiwa zuby kishi kumallon mata shine ya motsa, har bataji yana magana ba se da ya girgiza hannunta tace "na'am me kace".


Yace "tunanin me kike?" Murmushin takaici tayi kan tace "na ka" yace "bayan gani kusa dake? Uhmm me yasa kika kashe min waya my life? Ban hanaki min irin wannan hukunci ba?" Kanta ta dukar tace "I'm so sorry na mance na kashe wayan wallahi" yace "is ohk" "ya kwanan Amarya?" Harara ya banka mata kan ya tusa hannunshi cikin rigarta cikin rad'a yace "ya kwanan babynah? Be yi kewana ba kam?".


Tace tana murmushi "Lafiya kalau yayi kewanka amma kad'an sanin wani kanin aka je sama mishi" had'e fuska yayi yace "me yasa kike neman se kin 'bata min rai ne Hayati?" A zuciyarta tace "namiji hmm" kallon time tayi tace "ka tashi ka koma please" yace "ban gane ba? Korata zakiyi ni da gidana?" Tace "amma ai kana sane da abinda yakumbo tace jiya?" Runtse idanunshi yayi ya lura Shaati na cike da bori ba kishi ga kaman cikin nata na da d'an masifa, mikewa yayi ya nufi kofa kasa kasa tace "dama abinda ake so kenan" sarai ya ji ta sede baze iya sa'insa da ita ba macece tana bukatar uzuri kuma tayi hakuri iya hakuri tayi jarumta.


A bakin kofa ya tsaya ya juyo gareta yace "ki kunna wayanki please" kan ya juya ya fice ajiyar zuciya ta sauke se kuma haushin kanta ya kamata.


BAYAN KWANA BIYU


Yau kwanan zuby uku a gidanshi banda wahala ba abinda yake bata kuma ko a gyalenta fata kawai take ya kusance ta amma har yanzu yaki duk wani hanya da zatabi ta tayar mishi da sha'awa ya riga ya toshe, babban abinda ke damunshi sauyawar Shaati duk yadda take so tayi controlling kanta In yaje yin awa d'ayan nan se ta 'bata mishi rai.


Iya kokari yanayi Don ganin bai 'bata mata nata ran ba ze kira sau biyar kan ta d'auki d'aya shi dinma basa jimawa take kashewa ita karan kanta ta rasa abinda yake damunta kullum dare haka take kashewa da rabi kuka rabi nafila yanzu yakumbo hankalinta kwance bacci take harda minshari.


Saura mishi sati guda ya koma aiki Allah Allah yake ya koma d'in ko wani abin ze ragu mishi ya tabbatar In shaati bata kwana da masaniyar gidan zuby yake ba wani abin ze ragu, yau tun safe ya fice be jima da fita ba zuby tasa kafa ta fice abinta itama.


Direct gidan jibson ta nufa suka sheke ayarsu tana mitan tayi mugun kokari kusan satinta biyu rabonta da namiji da sunan wani gyaran banza gyaran wofi tunda wadda akayi Don shi d'in kallon arziki baya had'asu amma fah tana Son ko ta tsiya ta kusanceshi sbd wannan magani na mallaka kankat yadda baba ya fad'i mata sunan, jeebson de yayi takaicin auren nata sede dayake d'an duniya ne be nuna mata ba tade bashi tabbacin duk sadda yaji yana son ganawa da ita ya kirata zata amsa mishi.


Bayan sun gama holewarsu suka had'u parlorn shi da sauran kawayenta nan fah ta bud'e baki "ke Nancy wallahi so nake na d'and'ani guy dinnan kuma na d'ana mishi tarko a lokaci d'aya, mufee tace "shegiyar gari kice tsuntsu biyu zaki jefa da dutse guda amma fa daga gani guy d'in ze yi zuma" tsaki jeebson yaja kB saurayin Nancy yace "ina wayonki zuby? Ga wannan jikawa wawan guda biyu a ruwa kiga yadda ze baki mamaki".


Kar'ba tayi ta kalli mufee tace "toh ni da baya cin duk abinda ya fito a hannuna ya kenan zanyi?" Aboy saurayin mufee yace "amma kin rako matan bariki wallahi Zuby baya shan ruwa ne?" Wani irin dariya suka kwashe dashi banda ita da ta kulu a zuciye ta mike ta fice se gidanta Allah ya taimaketa be dawo ba kwashe bottle waters d'in fridge tayi ta bar biyu kawai ta bud'e ta zuba abinda akace mata biyu ta kuwa zuba hud'u hud'u ta jijjiiga ta mayar ta ajiye ta koma d'akinta.


Wanka tayi ta sa figaggiyar riga tare da bankawa kanta maganin da baba ya bata ta d'aura da wasu na mata ta kuma shafa na shafawa ta kwanta ba azahar ba la'asar ba magriba ba ish'a kan kaga tayi sallah to yana gida ya sata a gaba, se bayan isha ya dawo room d'inshi ya fad'a ya watsa ruwa ya sa kayan bacci kan ya kwanta ba tare da ya neme ta ba.


Har bacci ya fara d'aukanshi se yaji yana jin kishirwa mikewa yayi ya fito parlor tana tsaye jikin labule kuwa tana ta Allah Allah ya fito tuntuni ganinshi yasa ta washe hakora, girar faro d'in ya d'uko ya bud'e Allah be nufa ze ga bakin a bud'e ba ya kafa kai be sauke ba seda ya shanye tass ai yana gama sha yaji kaman an sokeshi a baya da mara dafa kujera yayi da kyar ya zauna tare da lumshe ido sede me?.


Wani bala'een feelings yake ji har kaman ze mutu cikinshi ya hau bala'in ciwo yau be je gidan shaati ba throughout da ze iya driving da yaje, zubyce ta fad'o mishi in ba mutuwa yake sonyi ba gwara ya rufawa kanshi asiri abinda yakeji yafi karfinshi, a daddafe ya mike ya nufi d'akinta layi na kwasarshi.
                      🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA....💦🍇

    *Baya Chanza d'and'anon teku*

      *Fatima Muhammad Gurin*

   **Gureenjo6763 on wattpad**


         'Yar Mutan Adamawa

  

*Wannan page d'inma naku ne en Gureenjo novels group kuna kasheni da comments d'inku🤣 en team Shaati da team zuby I really appreciate🥰🥰*


     *P12*


Kwance yake rigingine a tsakiyar gadon nata tunani yakeyi amma har zuciyarshi ya rasa tunanin menene yakeyi d'aya, ji yake kaman an sabuntashi nan duniya, ajiyar zuciya ya sauke jin hannunta kan kirjinshi cikin kashe murya tace "baby me kake tunanine haka" kallonta yayi ya rasa me yake ji kanta, tsintar kanshi yayi da cewa "tunaninki nakeyi honey" ajiyar zuciya ta sauke da har tana tunanin aikinsu be ci ba but jin yadda ya mata magana harda honey ta tabbatar komai ya tafi daidai murmushin mugunta ta saki kan ta langwa'be mishi "baby washh zafi muje kamin wanka".+


Da sauri ya mike tare da d'agata chak suka nufi toilet se Sannu yake mata alhali chan kasan zuciyarshi ya san ba buduruwa ya sameta ba, haka dae ya mata wankan yace tayi na tsarki nan tace bata iya ba, nuna mata yayi ba tare da damuwan komai ba, tayi yadda yace shima yayi suka fito tana makale dashi.


Alwala yayo yana son yin nafila amma yadda ta narke mai tana kukan shagwa'ba ya hanashi sallahn tare da komawa suka kwanta, ba shi ya farka ba se asuba mikewa yayi yaje yayo alwala ya fito, "honey, honey tashi asuba tayi" cikin bacci tace "kyaleni zanyi anjima" "Toh" shine abinda ya furta kan ya fita zuwa d'akinshi ya chanza zuwa jallabiya kan ya fice masallaci bayan an idar da sallah ya mike ya fito zuwa gida.


Yadda ya barta haka ya dawo ya sameta gefenta ya ra'ba ya kwanta don haka kawai bai son tashinta sbd kar ranta ya 'baci makaleshi ta sake abinda shi bayayi baccin safe haka ya biye mata suka koma bacci se around 10 suka tashi a tare sukayi wanka suka shirya "muje restaurants muci abinci ko? Don gaskiya bazan iya girki ba" Kai ya gyad'a kan yace "Toh muje" suka fice zuwa wani elegant restaurant suka ci abinci sukayi kat kan ta sashi zaga gari kaman yau ta fara fita a garin kaduna.


Se around 12 suka dawo da kaya niki niki Don har shopping seda sukayo, wanka suka sake yi kan suka fito parlor ta kwanta a kan kafanshi tare da kunna kallo shide kallon yake amma hankalinshi na chan wani wurin da baze iya cewa inane ba, ba wai ya manta yana da iyali bane sede baya jinsu a cikin zuciyarshi sam kaman panko Haka yaji ya koma.


*******


Kwance take tunanin abin duniya sun dameta, wai me yake nufi da ita kuma ne? Jiya throughout be je ba ya kira bata kusa da dare ta kira be d'aga ba, ta tabbatar zuwa yanzu kam ya kamata ace yaga miscall d'inta, ko ma be gani ba ai basu ta'ba yini su kwana su kuma wayi gari ba suyi waya da juna ba, wayanta ta janyo tare da danna kiran layinshi.


Seda ya kusa tsinkewa kan aka d'aga to her biggest surprise Zubyce "hello ya akayi" shine abunda ta furta, wani irin fad'uwar gaba taji wadda har kasan mararta tajishi cikin sanyi tace "Assalamu alaiki, me wayan fah?" Murmushi zuby tayi tace "baby kaji abinda take cewa dani da kai ba d'aya bane?" Wani irin mikewa tsaye shaati tayi jin muryan shi yana cewa "d'aya ne mana honey duk abunda za'a fad'amin In ya shiga kunnenki shikenan".


Rasa abin fad'a shaati tayi she is more than shock da abinda take ji, a zuciyarta tace "me ke faruwa?" Daurewa tayi tace "dan Allah bashi ko kice mishi shaati ce" cikin iyayi tace "baby wai shaati ce" tsaki yayi yace "In shaatin ce so what? In bazata fad'amiki abinda take so ba just kashe wayan kizo mu ci gaba da kallonmu" Innalillahi wainna ilaihi rajiun shaati ta furta tana zubewa kan kujera.


"Allahumma ajirni fi musibatin wa aklifnee khairan minha, lahaula wala quwwata illa billah" sune abinda tayi ta maimaitawa bayan tayi disconnecting wayan, ta rasa ma me zatayi anya kuwa ba mafarki takeyi ba? Anya kuwa Roohul na'im ne? Ko de me irin muryan shi ne? Ta rasa me zata kama iyakar rud'ewa ta rud'e duk yadda taso kuka yazo mata yaki ashe hawaye ma rahama ne.


Ita Roohul na'im ke cewa In itace so what?? Ko de be gane wace shaatin bace, sake kiran layin tayi yayi ta ringing ba'a d'aga ba ta kuma kira, seda ta jera 10 miscall kan aka d'aga muryanshi ne wadda bata ta'ba ji zuwa gareta ba yana cewa "wai me haka ne Aisha baki da hankali ne? In kin kira sau d'aya ko sau biyu ba'a d'auka ba ai kin san wani uzurin mutum yake" muryan ta na rawa tace "Roohul na....." "wai meye????" Ya fad'a cikin fad'a.


Wani irin marayan kuka ta fashe dashi tana kuma mikewa tsaye, d'an Shiru taji yayi kaman kukan ya shigeshi kan kuma yaja tsaki ya kashe wayan, bata da hankali fa yace? Kuka takeyi wadda yake fita daga kasan zuciyarta ita kam taga ta kanta shikenan bazata ta'ba farin ciki ba a rayuwa? Wani laifi tayi mishi haka da ya za'bi mata irin wannan tozarcin? Seda ya bari bazata iya rayuwa in bashi ba se ya nemi juya mata baya?.


"A'a lafiya d'iyata? Ko wani abu ya faru a gida ne?" Jikinta ta fad'a Don tana bukatan shoulder to cry kuka take sossai bazata iya d'auka ba banda wannan, rarrashinta baaba larai tayi tayi da kyar ta samu ta d'an sarara kan tace "me aka miki ne haka d'iyata?" Bazata iya fad'awa Mama wannan abinba Don ta tabbatar se ta fita shiga damuwa Sannan bata da kawa ko d'an uwa da zata iya fad'awa taji sauki sauki bata option Se na fad'awa baaba larai.


"Ikon Allah, ko de wani laifin kika mishi ne d'iyata?" Hawayenta ta share tace "baaba ban mishi wani laifi ba, na de san bayan aurenshi bana sake mishi kaman da sbd zuciya da kishi amma wallahi ba d'igon sonshi da ya chanza a zuciyata, baaba ko na mishi wani abin baze iya fad'amin ba se kawai ya d'auki fushi dani irin wannan me muni?".


Baaba tace "abinda zan gayamiki shine ki cigaba da adu'a Sannan ki yi hakuri ki dena kukan nan ko don sbd abinda ke cikinki, ki barwa Allah komai In ya shigo se kuyi maganan cikin salama ba da fad'a ba kinji?" Kai ta gyad'a tare da share fuskanta da yayi jaajir sbd farar mace, "Toh baaba pls ki tayani da adu'a kuma karki fad'awa mamah dan Allah" baaba tace "Toh d'iyata" nasiha ta kara mata kan ta koma bakin aikinta na girki da take.


Mamah ta kira sounding normal tayi suka gaisa kan ta nemi a dawo mata dasu Arwa taji sauki, Mama ta amsata ta kuma tabbatar mata da In driver ya zo ya dawo da baaba larai godiya tayi kan sukayi sallama, ba'a jima ba kuwa driver ya kawosu tasa baaba shiryawa ya wuce da ita bayan ta kara mata nasiha tabi komai a sannu karta d'aga hankalinta ko Don sbd cikin jikinta godiya ta mata kan sukayi sallama.


Dalilin da yasa ta sa yaran suka dawo kuwa ta san ko ba komai zasu d'ebe mata kewa bazasu bari tayi kewanshi sossai ba.


**********


WASA FARIN GIRKI


Zaton abu takeyi kaman wasa amma yau kwanansu hud'u da yin wannan abin be kirata ba kuma be neme ta ba In ta kira baya d'agawa hankalinta fah yayi bala'in tashi, abu tun ba'aje ko'ina ba? Jiya ya kamata ya dawo mata daga gidanta kuma ze wuce Abuja amma bata ganshi ba wayanshi ma kwata kwata switch off, Lallai zama be ganta ba.


Mikewa tayi ta shirya cikin atampha riga da zani ta sa hijab ta fice Bayan ta tabbatarwa su Arwa karsu fita ko nan da chan ta kuwa kara tabbatar me gadi kada ya barsu su fita, motanta ta d'auka ta nufi unguwan da ya fad'a mata gidan Amaryan yake tana son tabbatar da ko yana lafiya ne, da kyar ta gane gidan da tambaya da komai ta karasa.


Zuciyarta na aikin bugawa cikin tarraddadi ta kwankwasa get d'in gidan me gadinsu ya leko yana tambayar "waye?" Tace "uwargidan me gidan ce" yace "au toh hajiya barka da zuwa" Tace "Yauwa, suna ciki kuwa?" Yace "Eh Eh suna nan ai rabon da su leka waje ma ya kwana biyu ko abinci kullum kawo musu ake" yana nufin order.


Wuceshi tayi ta nufi main door d'in gidan kwankwasawa tayi da sallama ta d'an jima kan taji an bud'e yana tambayar "wayene?" Wani kullutun abu taji ya taso ya tsaya mata a kahon zuciya cikin takaici da baqin ciki take kallonshi daga shi se karamar boxer, "Ni ce roohul na'im" had'e fuska yayi yace "wa ya baki izinin fita?" Tace "baka bani ba Amma hakkinane In tabbatar da lafiyanka, tunda kana Lafiya hakkina ne ka kasa saukarwa yayi kyau na bar...." bata karasa ba taji zuby na cewa "baby wayene?" Kallonshi tayi tana jiran Jin amsan da ze bata se ji tayi yace "Aishace".1


Da sauri zuby ta karaso kofan tace "au shaati ashe kece" muguwar harara ta banka mata, ta'be baki tayi kan ta kwanta jikinshi tace "baby me take so ne?" Yace "wa ya san mata" ganin In ta tsaya za'a iya samun matsala yasa ta juya a sanyaye ta fara tafiya se ji tayi zuby na cewa "Da ka bi ta ai baby kasan ko wani abu me muhimmanci ke tafe da ita?" Abinda ya sa ta bursting into tears ji tayi yace "kyaleta kawai jarabace kawai irin nata, kinga kar muyi late d'in tafiya muje mu karasa had'a kayan nan".


Kenan da ita ze koma Abuja, driving take tana kuka iyakar iyawanta har dishi dishi taje ganin hanya neman wuri tayi tayi parking kan tayi kuka me isanta ta share hawaye ta nufi gidanta, da gudu yaran sukayi mata oyoyo wadda hakan ya sata karajin wani kukan ya taso mata, da kyar ta lalla'ba ta shige room d'inta ta kwanta hannunta dafe da cikin jikinta tunani fal ranta ba irin tunanin da batayi ba sede akace zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya hakan yasa ta kawar da komai ta d'auko qur'ani ta fara karantawa.


*********


Yakumboce zaune parlornta tana tunani a fili ta fara magana "ko yaron nan na lafiya? Kwana biyar kenan be zo ba be kuma kirani ba, be saba hakan ba Anya yana lafiya?" Mikewa tayi taje ta d'auko hijab d'inta ta saka ta nufi sashen innani cikin tsananin mamaki innani tace "yaya kece sannu da shigowa" Tace "Yauwa nace ko yaron nan kuwa yana kiranki yadda ya saba?" Innani tace "Ai rabona dashi tun ranar aurenshi sede ya kirani bayan nan da kwana biyu daga nan kuma be sake ba".


Yakumbo tace "kuma be mana sallama akan ya tafi habuja ba" innani tace "to ko Sulaiman yaje gidan nashi ya gano ko lafiya" yakumbo tace "yanzu haka kila wanchan mayyan Aishan ne ta makaleshi bari kiga inje da kaina sbd In yi maganinta" innani na mata magana sede inaa ta wuce fir fir fir, gidan Aisha ta nufa a bala'e ta bankad'a kofan se taga yaran ne kawai zaune a parlor suna karyawa.


Oyoyo suka mata banda arwa da ta makale jikin kujera kanta kasa, "Ina munafukar uwar taku" yasmin tace "tana d'akinta yakumbo amma me tayi na munaf....." "rufemin baki fitsararriya wuce kije ki kiramin ita" kallon sameer tayi tana komawa kan kujera tace "sameer call maami" da gudu yaje ya kirata se kuwa gata ta fito sanye da hijab har kasa ta duka tace "yakumbo sannu da zuwa mun tashi Lafiya?" Cikin hargowa tace "ban sani ba, nace ban sani ba Ina shi lusarin?".


Murmushin takaici tayi a zuciyarta tace ashe ba ni kad'ai aka raba da kai ba har mahaifiyarka da 'ya'yanka, "yana gidan Zubaidah" washe baki yakumbo tayi kan tace "au au to bari inje inji dalilin kin kiranmu ai se ya gayamin kila d'iyar kirkice bata jin daad'i" ba tare da ta kara bi ta kan shaati ba ta wuce fiiiiii, girgiza kai shaati tayi cike da tausayinta kan ta mike ta koma d'aki.   *Kuyi hakuri da wannan d'an uzuri ne ya kamani ya hanani yi dayawa*

                    🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇

   *Baya chanza d'and'anon teku*


     *Fatima Muhammad Gurin*

  **Gureenjo6763 on Wattpad**


           'Yar Mutan Adamawa


      *P13*


Zaune tayi a parlorn Bayan ta gama kwad'a sallamanta taji shiru, ta kai kusan mintuna ashirin zaune kan zuby ta fito sanye da wasu kananun kaya earpiece manne a kunnenta duka biyun tana tafiya tana taka rawa irin na wadda ya Samu duniya d'innan.

       "Zubaida" yakumbo ta ambata sede bataji ba kila kuma taji iskanci ne kawai irin nata, seda yakumbo tayi motsi da karfi kan ta d'ago ta kalleta a banzance ta cire earpiece d'in kunne d'aya tace "au ashe kece" yakumbo tace "Eh d'iyannan nice nazo ya gidan?" A shekeke tace "klau" ta samu wuri ta zauna ta d'aura d'aya kan d'aya tare da cigaba da bin wakanta, sakaka yakumbo tayi tana kallonta a hankali tace "to kode diyarga bata ganeni bane" gyaran murya tayi tace.


"Nace ba!!!" Ko sake dubanta zuby batayi ba bare ta san tana magana seda ta d'aga murya tace "zubaida" kallonta tayi tana d'aga gira tace "ya Ina hutawata zaki zo kina min ihu aka Malama me kike bukata ne?" Da mamaki yakumbo tace "yanzu en nan ki dubi tsabar idona kice Ina miki ihu a ka?" Tace "to meye kike min in ba ihu ba mutum na hutawarshi In wurina kikazo na gode se anjima, In kuwa wurin me gidan kikazo wato d'anki to bacci yake In kuma ya tashi Abuja zamu wuce bashi da lokacinki".

           Tsabar mamaki yakumbo ta kasa magana se kallo da take binta dashi Anya wannan zubaidace ba chanza ta akayi ba out of words tace "dama haka kike?" Wani irin dariya tayi kan tace "mene? Ai kad'an ma kennan zuby tafi haka yarinya, kinga tashi ki bar min gida ko zaki kwana gidan nan in ban ga dama ba ba ganin babynah zakiyi ba kin gane?".+


    Sallallami yakumbo ta fara "me zan gani ni Hansatu?" Mikewa zuby tayi ta nuna mata kofa "fita kuma karki kara zuwar min gida ba gayyata" sakaka haka yakumbo tayi gwanin tausayi kan ta mike harara zuby ta kuma danna mata tace "Ai In bakayi sharar massallaci ba kya yi na kasuwa fita nace!!!" A sa'bule yakumbo ta fito tana kuka haka ta samu wuri kofan gidan ta zauna taci gaba da kuka kaman karamar yarinya, seda ta fi awa biyu nan kan taji motsin bud'e gate da sauri ta mike.


Aiko zubyce hakimce gefen Saif sanye da rantsatsiyar arab gown shi kuwa kananan kaya ce jikinshi hankalinshi na ga hanya be kula sam da yakumbonba yayinda zuby kuwa sarai ta ganta sede kashe mata ido da tayi suka wuce a guje, hannu biyu yakumbo ta d'aura a kai a fili ta furta "na kashe kaina".


*********


Tayi ma kanta Alkawari In Shaa Allahu ta dena sawa kanta damuwar Saif abinda ta sani shine bazata kashe kanta a banza ba tabbas In ta mutu a yanzu shi bashi da asara dukda dole ya dameta amma ya ta iya? Allah ya riga ya kaddaro mata hakan zata ci gaba da zama a gidanta cikin rufin asiri In har ba sakinta yayi ba.


Zata ci gaba da mishi adu'a har Allah ya ganar dashi In me ganewa ne dukda ta san haka kawai ruwa baya tsami banza, sede dayake ance zato zunubi ko ta fara tunanin wani abin daban zatayi auziyya taci gaba da abinda take, yanzu yaranta sune top priority d'inta, babban matsalanta rashin aikin yi tabbas itama tayi ganganci da ta yarda in sunyi aure ba aiki.


Dole ne ta nemi aikinyi sbd bata ga alamun ze cigaba da yi musu hidiman kud'i kaman da ba and more over ATM card d'inshi da take rikewa ba wani abun kirki a yadda de suka saba rayuwarsu na yau da kullum cikin wadata, Sannan babban damuwanta yaran sun fara damuwa da rashin magana da mahaifin nasu ita kanta dauriya da karfin hali kawai take.


*******


Yakumbo kuwa ganin abunda ya faru yasa ta fara dana sanin abubuwan da tayiwa Aisha sede aka ce dana sani keyace gashi bazata iya fad'in ma kowa ba sbd tsoron kar ayi mata dariya, sede ta tabbatar ko ba jima ko ba dad'e se kowa ya sani tunda shine karfinsu a gidan sulaiman ba aiki ya samu ba bare ya ci gaba da kula dasu Sannan a yadda take kuntatawa mahaifiyarshi tun Suna yara ta san ba lallai ya had'a da ita wurin taimakon ba.


Ita kam taga ta kanta ba abin ta fad'awa su Tala ba itace da kunya tunda ita ta tabbatar musu da nagartar tarbiyar zubaidah, to me mafita? Ko itama zata nemi wani malamin ne a kwato mata d'anta? Haka ta kwana ido biyu cikin wasu wasi.


*********


Ta 'bangaren zuby ah duniya sabuwa an koma rayuwar Abuja babban birni gidanshi na chan dake Asokoro ma yafi mata na kaduna da taci burin shiga kyau nesa ba kusa ba amma na kadunan ma se ta dawo rayuwa ciki gaba gaba dai...


Kwance tayi abinta komai shi keyi kan ya tafi aiki ta tabbatar mishi In yana Son hutu ya samo masu aikin komai da komai a gidan, dukda tana samu daidai gwargwado sede fah ba yadda take so ba, tana so taga irin kallon da yake yiwa Aisha daga kasan zuciyarshi gareta, tana so taga yana fara'a da dariya kaman yana tare da Aisha amma yanzu sede ya mata yake, tana so ya zama kaman baby yana mata shagwa'ba irin na Aisha amma ko hira me tsawo chan baya iya yi da ita, a hakan ma ta gode.


**********


WASA WASA


Abu kaman wasa ya koma gaske yau watan Saif biyu rabonshi da kaduna In kunga Aisha se kun tausaya mata duk ta kare a tsaye cikinta ya shiga wata na hud'u, duk kowa a familynsu Saif ya san Saif na cikin jarrabawar ubangiji Don duk alkhairinshi garesu ya dakata, yanzu sossai yakumbo tayi hankali sede fah har yanzu ba wai ta fara son shaati bane.


Mazajen d'iyoyinsu ke kawo musu kayan abinci duk wata, sulaiman na iya kokarin wurin ganin ya Samu aiki ya d'aura daga inda yayanshi ya tsaya, duk yadda suka so su samu Saif zuby ta tosheshi kud'i take zubewa baba yana mata duk abunda take so, Abinda zai matukar baku mamaki gidansu Aisha ba wadda ya sani har rana e tayau.


Kaman yau tana zaune parlor tana ninke kayan su Arwa da ta duka ta wanke da kanta sbd yanzu ba halin kai wanki da guga, sallaman Aisha ta jiyo da sauri ta d'ago cikin sake fuska ta amsa ta "barka da zuwa namesake" Aisha cikin tausayawa yanayin da shaatin ta tsinci kanta Tace "Yauwa namesake, ya gidan?" Shaati tace "Alhamdulillah zauna mana kinyi tsaye kina kallona" dariya sukayi a tare kan Aisha ta zauna.


Mikewa shaati tayi Aisha ta bi ta da ido har ta shige kitchen ruwan pure water guda biyu ta Sanyo a plate ta fito dashi ta ajiye a gabanta, hawaye ne ya cikowa Aisha ido baza ta tuna ranar da taga pure water a gidan yaya Saif ba se yau, In kuwa be dawo hankalinshi ba watarana pure water d'inma se sun rasa.


'Dauka tayi ta sha tana goge Hawayenta a fakaice sarai shaati ta gani sede ta yi murmushin yake kawai gefen zuciyarta chunkushe da damuwa hira suka fara sama sama, Aisha tace "namesake haka wai zakici gaba da zama fisabilillahi? Kinga yadda kika koma kuwa? Bazaki fad'a a gida ba meyasa?" Murmushi tayi kana gani zaka san na yake ne tace cikin sanyin da yanzu ya zama yanayinta tace.


"Namesake na yarda da Allah, Sannan na yarda babu wata halitta da ta isa cutar dani ba tare da umarnin mahallicina ba, zuciyata a wanke take na tabbatar kaddarata ce ta zo haka, daga wannan se wanchan sede na tabbatar komai d'an lokacine watarana se labari Namesake so me yasa zan tada hankalina da na iyayena? Hmm baki san tashin hankalin da suka shiga sanadiyata bane a da yanzu bazan so bakin cikin da nake ciki ya zama ajalinsu ba".


Shiru Aisha tayi tana kallonta cikin tausayawa, sallamar yaran ne ya katse abinda take son fad'a sanye suke da kayan islamiya yadi blue colour sede fah har ya kod'e abinda kullum se an wanke kala biyu kawai ke garesu kuma kullum se sunje islamiya In ka ware juma'a da alhamis, har wando sameer ya yage daga gwiwa abinda bai ta'ba faruwa dasu ba, su karan kansu sun faad'a.


Da murmushi ta tari yaran "yaran maami an dawo?" Suka had'a baki wurin cewa "Eh maami" Tace "sannunku da dawowa" gaida Anty Aisha sukayi da murnan ganinta kan shaati tace "to aje a sauya kaya azo maza ayi home work" da gudu sukayi d'akinsu banda Arwa da ta tafi a natse, bayan sun sauya kowa ya d'auko Assignment d'inshi suka baje a corridor aka fara.


Aisha ta kusa magrib kan ta wuce bayan ta bawa Shaati kud'i firr taki kar'ba se makale mata tayi jikin kujera ba tare da ta sani ba, har wajen gate ta rakata kan ta dawo ta kulle gidan da jam lock ta shigo ciki dayake yanzu ta sallami duk mai gadi da driver d'in yaran sbd bata da kud'in biyansu.


Tana shigowa ba'a jima ba aka kira magrib sallah sukayi kan ta saka musu abinci shinkafa da wake da mai da yaji Don bata da wasu kud'in kayan Miya ko nama sbd duk naman fridge d'inta sun kwana biyu da karewa, haka kayan Miya d'an kad'an ya saura lalla'bashi take sunfi chin abu me mai da yaji, Bayan sun gama sukayi sallahn isha kan suka fito kallo se aka d'auke nepa.


Wayanta ta kunna musu fitilar suka cigaba da hira neeha ce ta dubeta cikin rikici da kuka "maami a kunna generator please, I don't like this darkness maami call paapa ya kunna In baki iya ba, maami please please maami" tsawa ta daka mata "will you shut up and sit down!! Haba" zama neeha tayi tana cigaba da kuka, yarinyar bata son duhu sam rayuwarta gashi ita bata da wasu kud'in man petroleum na mota ma tana d'an sakawa ne sbd kaisu school da d'aukosu.


Arwa ce tace "neeeha zo kiji wani tatsuniya" mikewa tayi tana kuka ta nufi wurinta a cinyarta ta d'aurata tana kallon mahaifiyarsu da ta jinginu da kujera ta lumshe idanu, yasmin ta kalla da itama mahaifiyar tasu take kallo hawaye cike da idanunta Don yasmin akwai fahimta sossai tana da kaifin basira, hannu da take ta cuccusawa jikin kujera taji ta ta'ba wani abu da sauri ta kalla se taga kud'i.


Zarowa tayi tace "maami look" kallo tayi se taga kud'i mika hannu tayi ta kar'ba, Kenan Aisha seda ta ajiye kud'ad'en nan ta fad'a a ranta tana kirgawa 10 thousand ne adu'a ta mata kan ta Adana kud'in tana kallon Arwa da ta zage tana ba neeha da sameer tatsuniya murmushi tayi, zuwa 9 gabad'aya suka tashi suka shige yanzu en matan gadon mamansu suke kwana sbd ita ta nemi hakan suna d'an d'ebe mata kewa da hanata wani abin kaman In tayi niyyan kuka.


Duk kwanciya sukayi Bayan ta tabbatar ta rufe ko Ina, cikin dare kaman yadda ya zama sabonta ta mike ta d'auro alwala tare da fara mika godiyanta ga ubangiji cikin kuka ta nemi gafara kan ta fara rokarshi akan mijinta da ya 'bata hankalinshi ya mance dasu, har asuba bata runtsa ba seda ta shiryasu ta sa long hijab ta kaisu school, da d'an kud'in da Aisha ta basu ta kara mai ta biya kasuwa ta saya musu kayan Miya da nama, murmushi takeyi Hawaye na gangaro mata ta san zasuyi farin ciki sossai In tayi rice and stew.


Bayan ta isa gida ta karasa kikkimsa abubuwan da suka 'bata, bayan ta gama ta gyara kayan miyan tayi blending tana cikin wanke nama taji knocking da kokonton waye ta isa gate d'in tana bud'ewa ta zaro ido ganin yaran nata da ta ajiye school da sauri ta matsa suka shigo zata kulle gidan Arwa tace "maami me napep da ya kawo mu bamu biyashi ba".


Da sauri ta koma ta d'auko kud'in ya kar'ba ya bata chanji yana karewa wannan tabkeken gidan kallo kuma ace labarin da yaran ke yi a napep gaskiyace? Hmmm Allah ya kyauta ya fad'a yana jan napep d'inshi yayi gaba, dawowa tayi tana kallon arwa tace "Arwa lafiya kuka dawo? Me ya faru?" Shiru sukayi dukkansu yasmin kam hawaye takeyi seda ta daka mata tsawa "ba magana nake miki ba?" Cikin sanyin murya tace "maami an koremu kud'in school fees".


"Innalillahi wainna ilaihi rajiun, Allahumma la sahlan illa ma ja'altahu sahl wa anta taj'alul hazna iza shi'ita sahl, la haula wala quwwata illa billah" ta jerosu a tare, tabbas mutane ba'a iya musu ashe akwai ranar da ze zo da za'a kori yaranta kud'in school fees daga feature leaders? Na shekara mahaifinsu ke biya Don wannan an kara wata be biya ba shine baza'a iya musu uzuri ba?.


Yau dole ta kira Saif Ina taga kud'in biya musu ko na term guda ne? Ta dubi Arwa "kama kannenki ku shiga ki chanza musu kaya zuwa na gida, yasmin kukan nan ya isa haka zaku koma school gobe in Shaa Allahu paapa d'inku ze biya" Kai ta gyad'a ba Don ta yarda ba suka shige wayanta Dake hannunta ta shiga lalu'be akan number d'inshi ta tsaya cikin tashin hankali da taraddadin yadda ze amsata ta danna kira.


Seda ya kusa tsinkewa kan taji an d'aga ajiyar zuciya ta sauke jin muryanshi kuka na shirin kwace mata sede ta fuske jin yace "ya akayi?" Cikin magana d'aid'ai tace "dama yaran ne aka koresu kud'in makaranta shine nace bari In fad'ama ko zaka turo In biya" jin muryar zuby tayi tana cewa "ce baka da wannan uban kud'ad'en na biyan feature leaders, ta ciresu ta mayarsu government inda ake biyan 100 naira kud'in PTA".


Sak yadda zuby ta fad'a haka ya maimaita kan ya karasa Shaati ta katse wayan, a zuciye bata fata randa zata gaggasawa Saif magana da aurenshi kanta ya zo tana iya kokarinta wurin danne 'bacin ranta sede baya gani, d'akinta ta wuce ta fara bincika duk wasu gwala gwalanta ta had'a wuri guda ta sanya hijab ta fito tana kallon Arwa tace "kula da kannenki Ina zuwa" fita tayi da kanta ta bud'e Gate ta fitar da car d'inta ta dawo ta rufe kan ta fice zuwa kasuwa.
1

   *kuyi hakurin rashin jina jiya ulcer ce ta d'an dameni*
1

                    🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA.....💦🍇

   *Baya chanza d'and'anon teku*

     *Fatima Muhammad Gurin*

   **Gureenjo6763 on Wattpad**


             'Yar Mutan Adamawa


*Gureenjo novels group bani da kamarku ina matukar kaunanku har raina🥰 kuyi hakuri kwana biyu bana samun yi ma kowa reply d'in comment d'inshi sbd halin da nake ciki ku cigaba da tayani da adu'a kaman yadda kukeyi yanzu Ina ganin each and every comments d'inku and wallahi I really appreciate shi kuma ke sa min kwarin gwiwan yi muku ko da kad'an ne na gode❤️❤️ Son so🥰🥰*


   *P14*


Ta samu ta sayar da golds d'in cikin sa'a sbd gold da suka hau, kayan abinci ta kara musu sossai kan ta wuce direct bank taje ta biya kud'in makarantar su na term d'in da suke cikin tana fata Allah ubangiji ya mata hanya ta biya sauran kan next term a kuma koransu, bayan ta biya ta wuto gida tana jin daad'i har cikin ranta.


Tana parking taji wayanta na ringing da sauri ta duba a zatonta Saif ne se taga mamah, d'agawa tayi da murnanta ta d'aga tabbas ajiye kadara daad'ine da shi, "Assalamu Alaikum mamah" Tace "Wa'alaikissalam warahmatullah sannu madam kila gida zan biyoki Awo ko?" Wara idanunta tayi tace "laaa wallahi shap na mance da wani awo, gobe in Allah ya kaimu in yaran sun wuce school zan zo" Mamah tace "Toh shikenan ki gaidasu" Tace "zasuji bye".+


Da murna suka tare ta ganin ta shigo tana dariya rungumesu tayi gabad'aya tace "gobe se school na biya ga taller d'inku" murna suka fara yasmin tace "maami paapa ne ya turo?" Fara'arta ne ya d'an disashe se kuma ta saki murmushi tana gyad'a kai, tace "guess what are we going to eat today?" Neeha tace "spaghetti" sameer yace "rice and beans" Yasmin Tace "as usual" wato rice and beans d'in, Arwa tace "jollof rice" duk girgiza kai tayi suka had'a baki wurin cewa "what then!!!" Cikin tunani, tace "rice and stew" waro idanu sukayi neeha tace "with meat?" Ta gyad'a kai se gasu suna murna har seda hawaye ya gangaro mata da ubanku da arzikinshi amma ace rabon da su ci abinci me ma'ana me suna abinci yadda suka saba ci daa ta manta.


A 'boye ta goge hawayen nata tana cire hijab d'inta ta nufi kitchen yasmin da Arwa suka bi ta yayinda sameer da neeha suka ci gaba da kallonsu da ta samesu sunayi, 'bare maggi, daka garlic, miko mai miko kaza da haka suka taimaka mata wurin girkin nata nan da nan suka gama, sunayi suna hira daga kitchen mota suka koma suka tattaro sayayyan da tayo suka shirya a store Arwa ta share kitchen da store d'in.


Wanka duk sukayi suka sa kayan shan iska kan Arwa ta zubo musu abincin dukkansu a tray guda da spoons a parlor suka baje sukaci a natse yasmin ta tattara sun d'an huta kan aka kira sallah suka gabatar ta kwanta abinta ta barsu suna kallo, bata tashi ba se la'asar ta kuma watsa ruwa sbd wutan da aka d'auke gashi ana zuba zafi bayan tayi sallah ta fito basa nan alamu sun nuna sun wuce islamiya da 2 yayi dama ta sabarwa Arwa yi musu shirin islamiya da sa su a gaba su tafi tunda ba wani nisa ne da shi ba, ammafa da ubansu na nan a mota ake kaisu a d'auko su.


***********


"Wallahi gaskiyace dae bazan dena fad'a maka ba Saif wai kana cikin hankalinka kuwa? Shaatin kake cewa baka da lokacinta?" Cikin masifa yassar ke wannan masifan zaune a office d'in Saif, kuma had'a rai Saif yayi yace "wai Ina ruwanka da rayuwata ne? Matarkace ko matata? Me naka a ciki? bani da lokacin zuwa kaduna Sannan bani da time d'insu se me? Me ka isa yi Min?" Shima ya mayar cikin masifa.3


Yassar yace "ko don su yakumbo bazaka iya zuwa kaduna ba? Wai anya kuwa Saif? su neeha yaushe rabon da ka kira kaji lafiyansu? Anya kuwa kana son gamawa da duniya lafiya? Ina zaka kai hakkin yakumbo da na Yaran nan In ka cigaba da musu haka? Sannan Aisha....." katseshi Saif yayi cikin d'aga murya "Ba ruwanka it's my life I have the right to live yadda na so,  me naka? Uhmm I hate hearing everything about kaduna so please spare my life and get the hell outta my office and life".


Yassar ya mike yana cewa "ni kake cewa In fita daga rayuwanka?" Waro idanu yayi yace "yes leave me alone and please get out" fita yayi a zuciya tabbas In Shaa Allahu ya bar Saif kenan har Abada yayi yadda yaso da rayuwarshi.


Komawa yayi ya zube kan kujera bayan fitan Yassar hawaye yaji yana cika mishi idanu shi karan kanshi ya san ba daidai yake ba, wani irin maraici yakeji na abinda yafi komai sabo dashi, kasan zuciyarshi a chunkushe take sede a duk sadda aka ambaci Aisha se yaji gabanshi na dukan tara tara, baze iya d'aga waya ya kirata ko ya amsa kiran yaran ba sbd ji yake baya bukatar su cikin rayuwarshi baya sonsu har gwara ma su da yakumbo, gani Yake zubaida ce gatanshi nan duniya duk abinda yake so ze iya yi mata ko mai girmanshi kuwa.


Gashi yanzu yassar da ya rage mishi nan duniya yayi sanadiyyar rabuwarsu a yadda ya sanshi da zuciya, kaman ya kurma ihu yake ji duniyar gabad'aya tana cikin mishi kunci, karan wayanshi ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya fad'a, shafa gashin kanshi yayi shi kanshi yayi duhu ya rame, wayan ya janyo da sauri ya mike ya gyara zamanshi ganin honey kan screen d'in.


'Dagawa yayi a natse yace "hello!!" Tace "kana Ina ne?" Yace "office" tace "meke faruwa naji muryanka haka?" A dakile yace "nothing" Tace "Ohk in kana dawowa ka biya ka sayomin grilled fish" yace "Ohk" ta kashe wayanta, chan kasan zuciyarshi Aisha ce ta fad'o mishi, wai wani irin pleasure yake samu ne daga wurin zubaida? Ba ladabi, ba tausasa murya, ba kulawa he really miss something special da ya kasa sanin menene.


Yanzu har aikinshi rawa yake sbd rashin natsuwa da yawan tunani, to menene bayayi a rayuwanshi da da yakeyi? Idanunshi a sama yana tunani chan kasan zuciyarshi yace "Adu'a" yes yanzu ya manta when last ya zauna yayi azkar na safe bare na yamma, a da kullum se shaati ta tuna mishi har adu'an fita, kau da tunaninta yayi yana lura da yanzu ko sallah ne yana sallama mikewa yake ya manta when last ya zauna yayi adu'a, ze gyara In shaa Allah.


*********


"Mene??? Haba baba ya za'ayi kacemin aikina yana rawa? Me na tara? Burina gaskiya be gama cika ba banyi wulakancin da nake so ba tukuna" hahahaha ya fashe da dariya yace "In har Ina raye bazan ta'ba bari aikinki ya karye ba, me nayi kenan? Karki damu ita shegiyar matar tashi ce itama ta mike tsaye" a zafafe tace "haba shiyasa mana har yanzu be bar tunaninta ba, harfa mafarki yake da ita yana kiran sunanta".


Baba yace "zanyi me kankat zanyi aiki kanta itama zan kara d'aureshi shima" ranta ba daad'i tace "nide har yanzu ban samu yadda nake so ba da kyar fah yake min magana me tsayi" (kujimin matarnan da buri, duk yadda ta samu be isheta ba) baba yace "karki Samu damuwa zanyi me yiwuwa" Tace "ita uwar tashi fah?" Yace "karki damu da ita har yanzu batayi hankali ba wawiya ce" dariya sukayi a tare tace "shikenan baba zakaji alert please aikina yayiwu, Ina ga muna nan d'innan bana turawa shaati bakin ciki kaduna zan sa mu koma ko na satittika ne kuma In sauka gidanta In karta mata rashin mutunci" a tare sukayi dariya yace "yanzu na san na haifi magajiya karki damu Ina jin kara zakiga aiki da cikawa".


Sallama sukayi ta gyara kwanciyarta ta kunna data tare da fara chatting tana taunan chewing gum.


***********


Yakumboce zaune an rabka uban tagumi tunanin duniya ya isheta ta rasa madafa sallaman innani ne ya dawo da ita daga duniyar da ta tafi ta d'ago tana amsawa, zama innani tayi cikin damuwa tace "yanzu Haka zamu cigaba da zama mu zubawa yaron nan ido a irin halin da yake cikin nan?" Yakumbo tace "nima kullum da wannan tunani nake kwana nake tashi ban san mafita ba su tala sun turani ciki sun barni tunda ba d'an su bane ba kuma abinda ya ragesu da rashin kulawarshi garemu, nayi magana da wata sabuwar kawar da nayi a kasuwan ladi tace ta san wani malami da ze taimaka ya kwatominshi in da kud'i".


Innani tace "subhanallah, wa'iyazubillah haba yaya, kina abu kaman bakiyi zama da malam ba? Da yana raye da se yafi kowa jin zafin abin da kika fad'an nan, gidan malamin duba ko boka? Gaskiya ban goyi baya ba kin kuwa san duk randa kaje wurin wani malamin duba ko boka shirka kayi? Kuma Allah ubangiji ya tsani masu shirka baze kar'bi sallollinku na kwana arba'in ba kenan kinga kika mutu a wannan 'bigiren se wuta, Sannan babu tabbacin Allah ze baki ikon samun abunda kikaje nema a wurin wani ba shi ba".


Ajiyar zuciya yakumbo ta sauke tace "Toh me Zan yi?" Se kuka cikin kuka tace "duk ni na jawa kaina na ja wa yarona yana zaman zamanshi na sashi auren dole ga irinta nan" ta karashe da kuka sossai, innani tace "a gaskiya yaya kina bukatar gyara a rayuwarki, ki dena d'aurawa kanki abunda Allah ya riga ya kaddara ze faru da Saif, gyararrakinki kuwa na farko ki rungumi Aisha wallahi wallahi itace mace tagari matar arziki da ta dace da rayuwan saif, na biyu yanzu ba Don Allah kike son jikokinki ba se don saif? Yanzu tunda Saif ya barnan zaki iya fad'amin sau nawa kikaje kika dubo halin da baiwar Allahn nan ke ciki da yadda take ci dasu?".


Yakumbo dae ba baka se kuka, tabbas da gaskiyan innani ta takurawa yarinyar dayawa sannan jikokin da take ikirarin tana so tun bayan tafiyan mahaifinsu bata ta'ba zuwa taga ya suka kwana suka tashi ba bare abinda suka ci ko suka sha, sede fah ita har ga Allah bataji tana son Aisha ba sbd ta sawa zuciyarta er iska karuwa ce seda ta gama yawon karuwancinta kan tazo ta aure mata d'a.


Kau da tunanin tayi tace "ni de damuwa na ya za'ayi saifullahi ya dawo cikin hankalinshi?" Innani tace "Adu'a ya kamata mu dukufa mishi In ya kama har sadaka" a nan suka tsayar da shawara sede fa yakumbo bata wani gamsu har chan ba (😡🤧 mata kaman ita ta haife baban zubaida)


**********


"Bye bye yaran maami se na zo d'aukan ku" a tare sukace "bye maami Allah ya tsare" murmushi ta sake seda taga shigansu makarantar kan ta nufi asibitin da mamah ke aiki, riga da zani ta saka se ta d'aura katon hijab har kasa bata so Mama ta fahimci wani abu da zaman gidanta In har lokacin jin yayi zasuji amma ba yanzu ba gaskiya.


Direct office d'in mama tayi ta tura da sallama amsawa tayi tare da d'ago ido ta zubawa er autanta da kallo guda kawai ta mata ta san bata cikin natsuwa ta gashi ta hango ramar dukda murmushin da Aishan ke ta zabgawa zama tayi tana cewa "Mamah Ina kwana?" Tace "Lafiya kalau ya kwnan yaran?" Tace "Alhamdulillah ya Abba? Kwana biyu bamu gaisa dashi ba" Mama tace "yana Lafiya, shaati wani abin na damunki ne?".


Cikin murmushi tace "a'a Mama me kika gani?" Ta girgiza kai tace "babu" mikewa tayi sukayi abinda ya kawo Aishan, da kallo kawai Mama take binta wadda yake matukar sata tsarguwa ta san mama da saurin fahimta da sunsunan abu tana da sa ido akan abinda ya shafi yaranta ba Tun yau ba, "Aisha kikace kina lafiya? Kinga yadda kika rame kuwa?" Kanta kasa tana murmushi tace "kawai salon wannan cikin ne I think but lafiyata kalau" hira suka d'anyi kan Mama ta korata suka rabu faran faran amma har zuciyar Mama bata yarda lafiyan Aisha kalau ba abinda yake damunta ba.


Gida ta nufa motanta na tashin sautin qira'ar alqurani cikin suratul Anbiya, tana bi da bakinta har ta isa, bata shigar da motan gida ba sbd d'auko yaran, bayan ta shiga ma qur'anin ta kara kunnawa a Home theater sbd bata son abinda ze disashe mata d'an farin cikin da ta samu, sakayau take jinta in tana ambaton Allah kaman bata da matsala a rayuwa, tana karatunta har ta gama girki inda tayi musu jollof rice with salad had'add'e wadda yaji kwai.


Wanka ta sake ta d'an huta kan ta d'auki wayanta ta kunna data family group d'insu ta shiga wadda se da tayi da na sani don auren Isma'il taga an saka wadda ya dakar mata zuciya ba wai har yanzu tana son Ismail bane a'a sede tana so a lokacin Da Allah ze tashi rama mata abunda ya mata ya zamana bata tausayawa kowa nashi ba amma yanzu In yayi aure ya haihu matanshi da yaranshi da basu da laifi fah? Anya zata iya yafe mishi sbd su kuwa?.


"Hahahha yaro man kaza kina tunanin akwai rannan da na ta'ba sonki na d'igon miskala zarratin a zuciyata ne? In kuwa kina tunanin hakan kin yaudari kanki, ni Isma'il ban ta'ba sonki ba sede yes ina sha'awarki kuma zan kashe kishirwana kuma In kwana lafiya but kefa? Hahahhahahahhaaha kin san kuwa abinda nake kulla miki? Mistakenly babe kikayi kokarin tonamin asiri se na lahira ya fi ki jin daad'i" ya saka takalman kafanshi da suka kasance timberlands ya gurd'e mata yatsun kafa da kasa, wani irin kara ta sake cikin azaba........


Runtse idanunta tayi tuno kad'an daga cikin abinda isma'il yayi mata wallahi ko 'ya'ya dubu yayi bazata iya yafe mishi ba, da sauri ta kauda tunanin ganin yana shirin sakata kuka ta mike ta koma d'aki don ta d'an runtsa kad'an kan lokacin tashin yaran.
                    🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇

*Baya chanza d'and'anon teku*


    *Fatima Muhammad Gurin*

  **Gureenjo6763 on Wattpad**


           'Yar Mutan Adamawa


    *P15*


YAU NE GOBE NE


Abu de gashinan ga kamanshi zuwa yanzu cikin Aisha ya shiga wata na bakwai kuma har yau bata ga kyallin idanun Saif ba basu kuma waya ba, kud'ad'en gwala gwalanta sun taimaka sossai sede zuwa yanzu komai yayi kasa, har wasu kayayyakin sawanta sabbin supers d'inta ta sayar akan sayan abinda zasu ci a cikinsu da 'ya'yanta.


Har rana yi ta yau bata sanar a gidansu ba se adu'a da take Ta san ko ba jima ko ba d'ad'e Allah ze amsa mata, karan wayanta ne ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi, kallon neeha dake mika mata tayi kan ta kar'ba ganin Abbanta ne yasa ta yi saurin d'agawa da fara'arta "Abba barka da dare" yace "Yauwa Auta ya yaran? Ya kuma karfin jiki?" Tace "Alhamdulillah Abbana, Ina Mama?" Yace "tana nan lafiya, nace Saifullah na lafiya kuwa? Kwana dayawa ya rabu da kiranmu gaisauwan jum'a d'azu nake maganan mamanki ma tace haka itama ta jima rabon da suyi waya".+


Gabanta ne ya fad'i ta kirkiri murmushi me sauti tace "Abba yana nan lafiya I guess don muma kwana biyu bamuyi magana ba sbd baya kasan" Shiru Abba yayi yana juya magananta Haka kawai ya kasa yadda da magananta don mutum baya kasa se akace baze kira iyalanshi ba? Gyaran murya yayi yace "Amma kina dae lafiya ko? Mahaifiyarki ta kawo min karanki" da saurin tace "ayi min aikin gafara Abba na dukda ban san laifina ba".


Murmushi Abba yayi yana son diyar nan nashi dukda yana cikin waenda suka kasa yarda da ita a baya sede ya tabbatar bazata fad'a musu abinda ba shine ba, "Tace wani Abu na damunki wadda kika ki fad'a mata Sannan jininki ya hau yadda ba'a so ga me juna biyu" ajiyar zuciya ta sauke tabbas ba abinda ya sauya soyayyar dake tsakaninta da iyayenta da ta zata a baya ya wargaje sbd abinda Isma'il ya aikata ga rayuwarta.


"Abba ba komai" yace "tsakaninki da Allah Uwata In baki fad'a mana matsalanki ba wa zaki gayawa uhmm? Ko de ba Uwata bace da na sani a da wacce bata 'boyemun komai?" Shiru tayi ya kamata ta fitar da abinda ke damunta kar iyayenta suma su shiga tashin hankali In wani abin ya sameta, ta san bata da ya su Sannan binne damuwanta kaman tarama kanta bomb ne wadda ta tabbatar randa ya fashe bazeyi kyau ba sbd tana shanye abubuwa dayawa.


Tuna saura sati guda su Arwa su gama exams in sun gama kuma bata da kadaran sayarwa ta biya musu kud'in wani term d'in tayi, a hankali tace "Abba......." se kuka, da sauri ya mike zaune fuskanshi cike da damuwa tausayin d'iyar tashi itakam daga wannan se wanchan, ta tashi da farin ciki da son en uwanta da faran faran a gidan amma lokaci kalilan ta nemi duk wani farin cikinta ta rasa.


Be katseta ba seda ta fitar da nauyin da ke cikin zuciyarta, kan tayi Shiru tana kallon su Arwa da suka kura mata ido ta kasa controlling ne amma ganin neeha da sameer da yasmin duk suma sun fara kuka yasa ta mike ta koma room d'inta a sanyaye yace "komai ya faru da bawa maganinshi Allah uwata, kiyi hakuri shine ze sa kici ribar kaddararki" share fuskanta tayi tace "Abba rabona da Saif yau wata biyar Abba, be san cinmu ba be san shan mu ba, be san rashin lafiyanmu ba, Abba duk na sayar da komai na har kayan sawana sbd In ciyar damu In kuma biya musu kud'in makaranta" hawaye ya gangaro mata, Shiru Abba yayi cikin mamaki tsantsa mamah ma da ya sa a speaker tana ji seda ta girgiza wani irin juriya ne ga Aisha haka?.


Abba yace "kuma ke kin gwada nemanshi?" Tace "eh Abba In na kira baya d'agawa in ya d'aga kuma fad'a kawai yake hawana dashi, lokacin suna nan kaduna kan su koma Abuja kusan korata yayi" Mamah tace "shi saifullahn? Anya yana cikin hankalinshi kuwa?" Cikin damuwa tace "Mamah banyi zargin kowa ba Adu'a kawai nakeyi Allah ya karkato mana da hankalinshi".


Abba yace "Amma mamana kinyi kuskure duk duniya baki da kaman mu irin haka na faruwa dake tun farko mu ya kamata ki sanarwa" Tace "Abba kayi hakuri ina tsoron kar In sa ku cikin damuwa kaman baya....." se tayi Shiru Abba yace "is Ohk ki zauna d'akinki zan yi magana da malam sulaiman, In Shaa Allahu na tabbatar ze yi iya kokarin shi" godiya tayi sukayi sallama.


***********


"Amma Abbansu baka gani ta dawo gida shine solution?" Murmushi yayi yana girgiza kai yace "mata dae, mata dae ko yaushe tunaninku iri d'aya, In ta dawo gida ya zata cigaba da fuskantan en uwanta na nan da suma ba sonta suke ba? Sannan da aurenta ba sakinta miji yayi ba ya za'ayi mu d'aukota mu dawo da ita gabanmu? Kinga barta d'akinta komai ze daidaita In shaa Allah" wayanshi ya fara dannawa chan ya samo numbern abokinshi malam sulaiman me almajirai.


Kira ya danna mishi ringing biyu ya d'aga suka gaisa kan ya koro mishi abinda ke faruwa gyad'a kai kawai yake yana mamakin duniya, seda Abba ya kai aya kan yace "Toh Alhamdulillah In Shaa Allahu zanyi iya kokarina, ka dinga yawaita sadaka ni kuma zan saka yaran nan su dinga mata sauka akai akai Allah ya taimaketa ya karkato da hankalin mijinta kanta da 'ya'yansu".


Godiya sossai Abba yayi mishi kan sukayi sallama ya kuma fad'awa Mama yadda sukayi, itade duk ta shiga yanayi Allah ya gani tana tausayin Aisha fiye da duk yaranta haka kuma tafi sonta ko Don sbd ita tafisu shan wahalan rayuwa? Se da Abba ya kara kwantar mata da hankali kan ta mike ta nufi kitchen don ci gaba da abinda take.


********


"Assalamu Alaikum" sallaman yakumbo ya karad'e parlorn ta rame gabad'aya itama juya hankalin d'a kan uwa fah ba wasa ba, bare Saif da ya kasance garkuwansu, amsawa Arwa dake parlor tayi tana cewa "sannu da zu...." ganin yakumbo yasa maganan ya makale da gudu tayi d'akin maman nasu a firgice Don matan na matukar bata tsoro.


Da sauri Shaati ta rike ta tana cewa "Lafiya Arwa me ya faru?" Cikin sauke numfashi tace "yakumboce ta zo" mikewa shaati tayi ta d'auki hijab d'inta tana kallon su yasmin da suke tare dama a d'akin tace "kuje maza ku gaida kakarku" fita sukayi yasmin na tura baki, itama bayansu ta bi tsaye ta samu yakumbo da Sauri ta zube kasa tace "yakumbo sannu da zuwa Ina yini?".


Se kawai yakumbo ta fashe da kuka da sauri Aisha ta mike tana cewa "yakumbo lafiya kuwa? Wani abin ne ya faru da saif?" Ta fad'a cikin razani yakumbo ta girgiza kanta tana zubewa kasa tace "ki gafarceni d'iyar nan, na musguna miki a rashin sanin addini da kaddara gashi abinda nake gudunki kanshi ya faru da jikata" a firgice tace "subhanallah yakumbo me ya faru?".


"Hajar d'in talatu wani la'anannen Allah yayiwa fyad'e bayan 'batanta da yini guda yanzu haka tana asibiti" salati Aisha ta d'auka tana me kama ha'ba khaih duniya ina zaki damu? Kan ta kuma magana taga yakumbo na shirin fad'uwa da sauri ta kamata tana kiran sunanta idanunta taga sun fara kakkafewa da azama ta kwalawa Arwa kira da gudu ta fito tace "tayani kamata zuwa mota" Da sauri Arwa ta kamata sukayi waje zuwa mota da gudu Yasmin da Arwa suka bud'e mata kofa ta fice Bayan ta tabbatarwa Arwa karsu je ko Ina kuma ta tabbatar ta rufe gidan.


Giwa hospital ta wuce da ita inda NHIS d'insu yake, da azama doctors suka kar'beta aka rufu kanta, Aisha de na waje tana aikin safa da marwa hannunta dafe da goshinta Allah Allah take kar yakumbo ta rasu Saif be nemi yafiyarta ba, d'aya 'bangare na zuciyarta kuma cike da tausayin hajar, Allah ya tona asirin duk marar imanin da ya mata haka, ta kai awa biyu tana zirga zirga anan kan doctor ya fito yace ta biyoshi office.


"A gaskiya mahaifiyarku na bukatan hutu da kulawa, Sannan tana bukatan cin abu masu kyau, hawan jini ya had'u da sugar be da daad'i" waro ido tayi tace "kana nufin yakumbo ta kamu da diabetes" yace "kwarai kuwa, yanzu munyi mata karin ruwa ta samu bacci, ku kiyaye please matsalanta babba ne don sugan sauka yake ba hawa ba" godiya ta mishi a sanyaye kan ta mike ta fito.


Layin Anty sukaina ta nema ta kira Bayan ta d'aga a dakile ta amsa sallamanta kan tace "ya akayi?" Aisha tace "yakumboce ba lafiya anyi admitting d'inta shine nace ko zaki zo ni na bar yara a gida ba kowa" bud'an bakin matan nan se cewa tayi "Allah sarki Allah ya bata lafiya gashi kuma bana nan munyi tafiya da mijina muna lagos" kashe wayan kawai Aisha tayi kenan bazata iya zuwa ba, ace maka mahaifiyarka na asibiti.


Tsaki tayi ba abin ta kira ya tala ba tunda itama ga halin da take ciki, Sannan innani In ta bar gidan waze kula da sulaiman da kuma sumayya ba'a ma maganan Aisha tunda basa had'a inuwa d'aya da yakumbo, ajiyar zuciya ta sauke tare da duba time, Mama ta tashi office kiran number d'inta tayi tare da nufan kofa Bayan ta d'aga suka gaisa kan Tace "am Mama kina gida please".


Mama tace "Eh ya akayi?" Tace "am yaran nan nake son kawowa wurinki su d'an kwana biyu zan zauna asibiti da yakumbo" Mama Tace "yakumbo ba lafiya?" Tana tada motanta tace "Eh wallahi hawan jini da kuma low diabetes" Mama Tace "subhanallah Allah ya bata lafiya, se kuma ke zaki zauna da ita shaati?" Tace "Mama In na zo zamuyi magana bani da wani option ne" kashe wayan Mama tayi tana cewa "Ohk".


Tana isa gida ta had'a musu uniforms d'insu da wasu kayansu trolley guda ta sa suka shirya ta rufe gidan da kwad'o bayan itama ta d'ibi duk wani abinda ta san zata bukata suka fice, da murna Mama ta taresu se yau take ganin ramar yaran suma da ta kwana biyu bata gansu ba, hawaye ya cika idanunta Bayan sun rungumeta, ta goge tana dariya tace "karku karyani please" Shaati ta sa baki "hey get off her now ku kai kayan nan room" da sauri suka saketa yaran suka kwasa da gudu yayinda Arwa taja trollyn suka wuce.


Fad'awa mama fyad'en da akayiwa hajar tayi ta kuma sanar da ita yadda sukayi da sukaina, Mama Ta amsa da "Lallai Shaati kin amsa sunanki Allah ya biyaki, ya saka miki da alkhairi wannan zamani da wuya a samu kamanki yanzu duk bayan wulakanci da cin mutuncin da yakumbo ta miki finally kece zaki rufa mata asiri, to be sincere ko ni bazan iya wannan jarumtar ba".


Murmushi kawai shaati tayi tace "hope za'a dinga aiko mana abinci Daga nan please" murmushi mama tayi tace "sure, I transferred some little amount to your account use it well" godiya shaati tayi mata kan ta fice, da kud'in da Mama ta turo mata ta biya bills d'in yakumbo, a gajiye ta zube kan plastic chair dake d'akin tana kallon kafanta da ya fara suntuma.


Chan baya ta tuna lokacin sauran cikinta da In cikinta ya shiga wata bakwai kullum se Saif yayi massaging kafafunta da dare kan suyi bacci ka'ida ne wannan har se ta haihu, kau da tunaninshi tayi ganin tana shirin fara kuka.


**********


"Kaga dakata mene? Ni gaskiya haihuwa ba yanzu ba tun ban gama cin karena babu babbaka ba? Don't you dare spoiled my mood this Afternoon" kanshi kasa yace "sorry but...." katseshi tayi tana waro ido "au musu kuma zamu fara?" Ya girgiza kai tace "Ohk fine zan haihu but se nan da one year" tuna gargad'in babanta da yace kar ta dinga kaishi bango bursting d'inshi bazeyi kyau ba.


Kanta ta dukar tare da kirkiro hawayen karya da sauri ya taso ya manna ta da jikinshi tare da fara bata hakuri ta langwa'be kuwa chan yace mata "na fara neman d'aukan hutun da kika bukata sunce nan da month zasu ban two weeks break" ihun murna tayi zata kuntsawa shaati bakin ciki son ranta.1

    Tou fah😭🤧
                   🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇

  *Baya chanza d'and'anon teku*


      *Fatima Muhammad Gurin*

   **Gureenjo6763 on Wattpad**


          'Yar mutan Adamawa


      *P16*


Numbern innani ta kira Bayan sun gaisa take gayamata yakumbo na asibiti ba lafiya, salati ta d'auka kan ta tambayi asibitin, gayamata tayi a sanyaye tace yanzu sulaiman ze kawoni, ta kashe wayan anan tayi zaune tana tunanin ta kira Saif ko kar ta kira har akayi kiran magrib ta mike taje tayo alwala sallayar da ta taho dashi ta shimfid'a ta tada sallah Bayan ta idar tana zaune nan tana azkar taji wayanta na kara "uncle lesu" shi ta gani d'auka tayi tace "uncle sule kun iso?" Yace mata "eh gamu a reception" Tace "Ohk ku taho amenity room 16" ta kashe wayan.+


Mintuna kad'an se gasu da sallama, mikewa take kokarin yi innani tace "a kul Aisha yi zamanki Sannu" murmushi tayi tana zaman kuwa dama taji daad'in zaman "sannu da zuwa innani" Tace "Yauwa Aisha me ya faru haka?" Tace "wallahi taje chan gida muna magana kawai naga alamun tana shirin fita hayyacinta shine muka rugo asibiti" kallonta kawai Uncle sulaiman yakeyi cike da tausayawa rashin d'a babban abu ne amma ya suka iya ya rasa sau nawa yake kiran yayan nashi baya d'agawa In kuwa ya d'aga sede yaji muryan zuby ta kuma karta mishi rashin mutunci.


Da kyar ya samu aiki a wani private school na teaching ana biyanshi 33k duk wata sbd kasancewarshi me degree da kud'in makarantar sumayya ya kare ma mijin Aisha ne ya biya er dubu talatin da ukun nan akan kananan bukatun gida yake karewa baya saving ko biyar, maganan Shaati ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi "uncle sulaiman lafiya kuwa Ina ta magana shiru" yace "sorry Inlaw wallahi na tafi wata duniyar ne daban ya nauyin jiki?".


Ta amsa da "Alhamdulillah wurin hajar kuka fito ne?" Cikin damuwa yace "Eh baki gani ba abin tausayi itama har yanzu bata farka ba kuma mahaifinta na kan bincike" cikin tausayawa da sanin hali makamancin haka da ta shiga tace "Allah ya tona asirinshi ya bi mata hakkinta" suka amsa gabad'aya da Ameen kan sule yace "me sukace yake damunta ne?" Tace "wallahi bp ne se low sugar" yace "Allah ya bata lafiya bills d'infah? Nawa sukace?" Murmushi tayi tace "na riga na bada karka damu" Albarka innani tayi ta saka mata tana fata Allah ya ba sulaiman mata irinta.


Yanzu In ba macen arziki ba waye yakumbo Zata yiwa wannan cin kashi ta dawo kuma tana jinyarta a yanayi na ciki? Ai se me karfin imani, innani tace "Toh Allah ya saka miki da gidan aljannah Aisha, ya karkato miki da hankalin mijinki gareki, yanzu kije gida sbd yara ni se in kwana nan" a zuciyarta ta amsa da Ameen thumma Ameen, kan ta d'aura da "innani kema kina bukatar hutu kije kawai zan kwana nan da ita yara kuma suna chan gida unguwan rimi" innani ta matsa Aisha ma ta nace hakan ya sa ta kyaleta sun d'an jima nan kan aka kira wayan Aisha tana dubawa taga driver d'in gidan su ne d'auka tayi suka gaisa kan yace yana waje ya kawo abinci.


Sulaiman ta tura ya kar'bo, bismillahn abincin tayi musu sede sunki su ci ba jimawa sukayi mata sallama suka tafi kuma har lokacin yakumbo bata farka ba, bayan tafiyansu ta d'an d'ibi abincin tuwon shinkafa da miyar zogale se er pepper soup na naman kai, zama tayi taci sossai Don ta manta rabonta da tuwo yaran ba so suke ba se in tayi sha'awa tayi d'an daidai cikinta taci.


Se chan cikin dare yakumbo ta farka zuwa lokacin Aisha ta d'an sa pillow ta kishingid'a kan sallayar abinka da mai tsohon ciki motsi kad'an ya farkar da ita mikewa tayi ta karasa jikin gadon tace "sannu yakumbo" kallonta tayi kan ta kalli d'akin a sanyaye tace "sannu d'iyarnan, wai asibiti nake?" Aisha tace "Eh bari In kira likita" fita tayi ta gayawa nurses ta farka wata nurse ta mike ta biyota zuwa d'akin ruwan ta cire mata tare da duba file d'inta za'a kuma kara mata wani ruwan.


"Mama kiyi abinda zakiyi ki d'an huta zan kuma sa miki wani ruwan" 'bata fuska yakumbo tayi tace "kayya diyarnan baza'a barshi ba kawai" murmushi nurse d'in tayi tace "a'a Mama bakiga halin da kike ciki ba har yanzu? Kiyi hakuri a karasa ku tafi gida gabad'aya" gyad'a kai yakumbo tayi, nurse d'in ta fice Aisha ce tazo Don taimaka mata da sauri tace "a'a Aisha kina fama da nauyin jiki kuma In kara miki wannan bari zan lalla'ba" murmushi Aisha tayi Lallai yanzu yakumbo ta gane gaskiya wai har ita takeyiwa magana cikin sanyi da kulawa? Lallai za'ayi ruwa yau harda kankara.


Lalla'bawan kuwa tayi ta shiga toilet yayinda Aisha ta samu wuri kan plastic chair ta zauna, chan ta fito da alamu alwala tayo kan sallaya ta nufa ta zauna a zaune ta fara sallolin da aka biyota tana raka'an karshe na isha Aisha ta zuba mata abinci tana gama adu'o'inta ta jere matasu gabanta godiya ta shiga mata ita dae nata murmushi.


Seda tayi nisa a cin abincin kan ta d'ago ta dubi Aisha "ke kinci abincin kuwa?" Aisha tace "Eh yakumbo" ta sake cewa "Ina kuma kika baro yaran?" Tace "suna unguwan rimi" godiya yakumbo ta mata yayinda ta sake murmushi tace "Ba wani matsala yakumbo" Bayan ta gama cin abincin ta huta kan Aisha ta kira nurse d'in aka maida mata ruwan suka kwanta.


Washegari da misalin karfe takwas innani ta zo a lokacin har an kawo musu breakfast daga gidan Mama sun karya, yakumbo tayo wanka innani na shigowa da kayan ta ta kar'ba ta sanya yayinda Aisha ta nemi taje gida ta chanza kaya Daga nan zata wuce asibiti ta dubo hajar kan ta dawo nan.


Duk Allah ya tsare suka mata cike da kulawa, ta wuce ta fita motanta taja ta wuce, bayan fitanta yakumbo ta dubi innani tace "kinga d'iyar arziki wallahi yanzu duk kunyanta nake ji" innani tace "haka duniya ta gada Ai baka san me maka ba shiyasa ba'a so ka wulakanta mutum" Shiru tayi kan tace "yaron nan kuwa ya sani?" Innani Tace "be sani ba amma bari In fad'amishi" Airtel line d'inta da be dashi ta kira.


Seda ya kusa tsinkewa kan ya d'aga da sallama ta amsa kan ta d'aura da "Anya saifullahi ka san darajar uwa da hakkokinta a kan d'a? Na tabbatar ka sani sede In zaka take saninka kayi abinda kake so, In ka manta bari In tuna maka ba se da kalma ba fushinta kawai gareka daga yanayin chanzawar fuskanta kawai se Allah ya kamaka da laifi bare kullum se ta zubar da hawayenta kanka, ya kamata ka duba kan komai ka sa hannu kai ya tarwatse, kaji tsoron Allah ka tuna da fifita uwa da yayi akan komai na duniya".


Shiru yayi idanunshi a lumshe ya san har kasan zuciyarshi abinda yakeyi baya kyautawa sede ya ya iya tunanin yakumbo kad'ai yayi se yaji kaman ana hura mishi wuta a kofofin jikinshi zuwa sassan jikinshi har cikin kwakwalwanshi bare yayi tunanin kiranta ko zuwa kaduna, a sanyaye yace "zanzo In sha Allah" tace "yaushe se ta mutu? To tana asibiti Giwa hospital amenity d'aki na sha shidda rai a hannun Allah ka yarda ta mutu baka nemi yafiyarta ba ka gama duniya da lahira" kit ta katse wayanta.


Ta tabbatar In ba haka ta mishi ba da matukar wuya tankwarashi yadda asiri ke kan ganiyar cinshi, suna adu'a ba wai basayi ba, Allah ya sani suna kanyi Allah ya warware wannan matsalar, sun tabbatar duk lokacin da Allah ya tsara ze karye me karyewa ne, kusa ko nesa.


******


Hankalinshi yaji ya d'ugunzuma ya tashi jikinshi har rawa yakeyi sarai duk wani iliminshi na addini na nan ba inda yaje ya kwana da sanin cewa ya kad'e har ganyenshi In ya yarda sanadiyarshi wani abin ya samu yakumbo, da sauri ya mike ya tattari abunda ya san ze bukata ya bada excuse akan be da lafiya ze tafi asibiti aka bashi umarnin tafiya yana fita se filling station ya cika tankinshi kan ya nufi kaduna cikin tsananin gudu.2


**********


A hankali take takawa sbd kafafunta da suka kara kumbura agogon hannunta ta kalla daga wanka ta shirya bacci ya kwasheta ba ita ta tashi ba se bayan awa guda hakan ya sa shirin ya mata nawa cikin lace doguwar riga bubu ta shirya tare da yafa katon mayafi Bayan ta d'aura d'ankwalin irin na zamani Chas ta fito kaman bata da wani damuwa nan duniya yatsun hannunta sanye da jan lallen da bata rabuwa dashi wadda tun last week arwa ta sanya mata.


Direct asibitin da su Hajar suke ta nufa, maganan da taji an mata ne yasa tayi saurin waigawa "Maami" murmushi me yalwa ta sake tace "Arham ya kk?" Yace "Ina kwana" Tace "Lafiya kuwa bakaje school ba? Ya jikin hajar?" Yace "jiki da sauki ta farka ma, Sannan school mun dena zuwa lesson muke sbd waec da zan fara" Tace "masha Allah, Allah ya bada sa'a bari na karasa" yace "maami In kin fito zan biki In gaida yakumbo" tace "to shikenan karka damu bari naje".


Da sallama ta tura d'akin Yaya tala na zaune gaban gadon tana bawa hajar d'in kakkauran tea da teaspoon, dakatawa sukayi suna kallonta murmushi ta saki tana karasa shigowa dukda basu amsa sallamanta ba, yaya tala ta d'auke ido tace "murmushin makiyi, Allah ya isa da wannan azzalumin da ya 'bata mini rayuwaki hajar wa ya sani ma....." katseta Aisha tayi da cewa "Ina kwana yaya? Ya kuma me jiki?".


Shiru tayi mata se kananan magana da take jefanta dashi, tace "Toh Allah ya tsare na gaba, Allah ya toni asirin koma waye" a masifance tace "Dallah malama yi min Shiru tsohuwar munafuka kaman yaje zuci, na tabbatar aka tona zuciyarki farin ciki da murna kike to Allah ya mayar kanki inde da hannunki cikin wannan bala'in abinda ya samu d'iyata kuma ki fice ki barmin nan bana son banzar gaisuwarki".


Murmushi kawai shaati tayi dukda maganan ya mata zafi harda zargi haka, cewa tayi "Allah ya kara sauki" ta juya ta fice, Hajar ta girmi Arwa bazata so abunda ya faru da hajar ya faru da d'an kowa ba sbd itama tana da 'ya'ya mata amma shine nan har ita aka d'aurawa zargin sakawa ama er 13 years fyad'e.


Duddubawa tayi ko zataga Arham chan ta hangoshi tsaye jikin motanta kan ta karasa ta bud'e mishi ya shiga tana karasawa ta kunna suka nufi asibitin da yakumbo take dukda holdup ya d'an rikesu da tayi parking kuwa kafafunta suka dameta da ciwo dukda ta saba ita haka kafafunta suke mata In har cikinta ya fara nauyi amma wannan ya had'u da bp da take kan fama dashi.


Da kyar ta sauka tana cije baki se sannu Arham ke mata, murmushi kawai ta mishi itace gaba yana binta a baya hannunta na hawa kan handle kofan na bud'uwa carab idanunsu ya fad'a cikin na juna a tare gabansu yayi mugun fad'uwa kallon kallo sukayiwa junansu ido cikin ido ganin baze juri kallonta ba yasa yayi saurin saukar da idanunshi kan cikin jikinta.


Yadda gabanshi ya fad'i yafi kallonta da yayi Shiru ya d'anyi kan yaji tace "malam d'an bani hanya" kallonta yayi tare da watsa mata bazan kallo ya d'an ra'beta ya wuce sede seda hannunsu ya gogi juna yayinda a tare wani shock ya ziyarcesu kaman basu ta'ba ta'ba jikin juna ba, wani tsuka me sauti yaja yana ficewa ko maganan Arham be amsa ba, ajiyar zuciya ta sauke tare da karasawa cikin d'akin "a'a har kin dawo? Da kin kwanta kin huta sossai ai" murmushi tayi tace "zan koma kan azahar In shaa Allah" sukace a tare "to Allah ya kaimu" kallon damin kud'in dake bakin gadon yakumbo tayi ta kauda kanta.


Ta samu kan sallaya ta baje, tana kallon Arham dake ta zuba musu surutu suna dariya ba ruwanshi yaron natsatse ga faram faram, tana jinshi ne sbd bata son tunanin Saif ya zo mata cikin kwakwalwa amma duk yadda ta so kau da tunanin nashi seda zuciyarta tacigaba da wassafa yadda ta ganshi yau bayan kusan six months bata ganshi ba, ba wannan hasken annurin yayi duhu kad'an kuma ya rame wata zuciyar tace kode rashin lafiya yayi?


Jin an turo kofa ne yasa ta d'aga Kai ta kalli kofan se suka kuma had'a idanu duk suka kawar da kai cikin basarwa ta fara mammatsa kafafunta shi kuwa karasa shigowa yayi babban doctor na binshi baya kuma duba yakumbo yayi ya tabbatar mishi sugan ya dawo normal sede hawan jinin gashinan de tana bukatar kulawa, godiya Saif ya mishi kan ya fice, kallon yakumbon yayi yace "yakumbo ba wani abinda kike bukata?" Ta kalleshi duk ya lalace sede ya ta iya bazata ci gaba da fushi dashi ba sbd kaddaranshi kenan.


Cikin sanyi tace "hakkin iyalanka fah?" Shiru yayi kan yace "zan saya kayan abinci In ajiye musu kan In wuce" yakumbo tace "abincine kawai damuwansu? Ka san yadda suka zauna wata biyar da bakazo ba bakayi sako ba? Duba kaga yarinyar nan cikine jikinta wata d'aid'ai har bakwai amma ka ta'ba kira kaji lafiyarta? Da kazo ka ganta nan ka mata ko sannu?" Shiru yayi tare da 'bata fuska satan kallonta yayi ta kurawa yatsun kafanta ido tana kallo kaman yau ta fara gani.


A ranshi yace wannan Ai iskancine dama haka take so shiyasa tayi kus tana ji ana mishi fad'a, shi ita ta san inda ta samo cikinta kila da gaskiyan zuby da tace mace da ta saba da rayuwa bazata iya zama ba namiji na tsawon wata biyar bata nemi maza ba toh gashi ya gani harda tsarabar bariki da aka makalamishi, kara had'e rai yayi ze yi magana wayanshi ya d'auki kara da sauri ya d'auko sbd ringing tone d'in na daban ne zuby ce jikinshi har rawa yake wurin d'auka.5


"Honey" Tace "yes baby ya kk?" Yace "fyn ya gdn?" Tace "fine, kana Ina?" Kan yayi magana yakumbo tayi magana da d'an d'aga murya Tace "Aisha kina kuwa ganin likita kumburan kafafunkin nan na yawa" Da sauri ya isa bakin kofa sede ya makara ta rigada ta ji wani uban ashar da ta lailayo ta zuba seda yaji duniyar ta juya mishi "ni zaka munafunta saifullahi? Ni zubaida?? Ashe dama kullum ka fita da sunan ka tafi office nan kake zuwa? Allah ya isa tsakanina dakai kuma wallahi zaka zo ka sameni Ina daidai da zamaninka" cikin rawan murya yace "I'm sorry ba haka bane, karki kashe pls tsaya ki saurareni".


Kit ta kashe wayanta da sauri ya juyo ga yakumbo ya fiddo wasu kud'ad'en ya kara kan wadda ya ajiye yace "I'm sorry ana nemana a office ban nemi izinin Tahowa ba Allah bada lafiya se munyi waya" jiki na rawa ya fice, duk kasa magana sukayi yayinda wani takaici yazowa Shaati wuya sede batace komai ba sannan tayi matukar kokari da ko hawaye be taru idanunta ba bare ya zubo, "ki kara hakuri Aisha" shine abinda yakumbo ta fad'a murmushi kawai shaati tayi kan ta kishingid'a kad'an tana me lumshe idanu.

                   🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇

    *Baya Chanza d'and'anon teku*


    *Fatima Muhammad Gurin*

  **Gureenjo6763 on Wattpad**


         'Yar Mutan Adamawa

     *P17*


Yana isa Abuja be zarce ko Ina ba se gidanshi cikin tsinkewar zuciya ya kutsa kanshi cikin kintsatsen parlorn nashi da ba wani kamshi me daad'i dake tashi dukda a tsabtace yake sbd masu aiki da suka sanshi da tsabta be son kazanta, straight d'akinta ya zarce, ita kuwa jin motsin parking d'inshi yasa ta fad'a gado tare da fashewa da kukan karya.


Da hanzari ya karasa yana d'agota yace "subhanallah honey me akayi miki?" Cikin kuka tace "ba kaine ba wato yanzu zaka iya abu ba tare da ka nemi izini na ba? Wato kullum cin amanata kake kana zuwa wurin karuwar matarka ban sani ba?" Yace "wallahi wallahi ban ta'ba zuwa ba se yau, yau d'inma sbd yakumbo ba lafiya ne naje".+


Tsaki tayi a zuciyarta tace munafurci dae, a fili kuwa tace "shine ka karasa wurin wanchan matar taka ko?" Yace "ni ban je ba" ganin yayi Shiru tace "wallahi karya kake, kaima ka zama munafuki Toh wallahi Ina daidai da zamaninku dukkanku" har kasan ranshi be ji daad'in zagin da ta mishi ba sede ya ya iya? Sulhu yake nema dukda ya kwana da sanin cewa haka zata kwana tana wannan bala'in.


"Shikenan banje ba amma mun had'u sede na kula kinyi gaskiya cikin jikinta ba wani babba bane alamu dae be fi five months ba" gira ta d'age cikin murmushi tace "ahab ba na gayama ba kila kaman yadda Arwa take ba erka ba, er kan titi kila haka sauran yaranka" kaman an buga mishi guduma a kai haka yaji maganan sede ya yake baki yace "ze iya yiwuwa ko?" A masifance Tace "Toh dama a buduruwa ka aureta? Ba da tsarabar titi ka sameta ba?" Yace "haka ne zan tsaurara bincike a kanta muddin na kamata da cin amana ta se ta yabawa aya zakinta" washe baki zubaida tayi tace "ko kaifa yanzu kake magana kaman namiji, yanzu je kayi wanka akwai abinci dining".


Mikewa yayi ya fice cike da tunanuka kala kala, sam kwakwalwanshi yaki ya amshi wannan maganan sede ya lura duk ta yadda zubaida take dagewa ta chusa Mashi In ya natsu ya lura se yaga kaman da gaskiyan zubaida a takaice dae zargi ya shiga tsakaninshi da Shaati.


**********


BAYAN KWANA BIYU


Yau ake sa ran sallaman yakumbo daga asibiti sbd Alhamdulillah jiki yayi sauki Sannan Saif ya d'an kokarta a kullum ze kira sau uku shi d'inma biyu se ya 'buya kira d'aya kawai zubaida ta yarda yayi shima a gabanta daga yakumbo ko innani In tana asibitin bata yarda su gaisa, bare kuma ayi maganan shaati da ita ke wahala da mahaifiyar tashi.


Kud'in da ya ajiye musu yakumbo ta raba uku ta bawa innani kashi d'aya sauran biyun ta raba d'aya ta kara a kan d'aya kan ta d'auki rabi ta baiwa shaati d'aya da rabi seda ta nuna 'bacin ranta kan shaati ta kar'ba tayi godiya, aiko da yammacin ranan aka sallameta a mota shaati ta d'aukesu zuwa gida da kanta ta kakka'bewa yakumbo gidan dukda hanata da takeyi shaara ne kawai ta bari yakumbo tayi sbd bazata iya ba.


Se da suka d'an jima nan suna er hira da yakumbon har suke tattauna matsalar hajar anan yakumbo ta kara bata hakuri akan maganganun da ya tala ta jejjefeta dashi zuwanta asibiti wurin yakumbo ko a lokacin nunawa tayi ba komai bare yanzu da ya wuce, "ba komai yakumbo Ina fatan Allah ya toni asirin wadda ya aikata mata haka ko da za'a dace, hajar abin tausayice bana fata tayi rayuwa makamanciyar wadda nayi, ina mata adu'ar Allah ya kawar mata da duk wani fitinan rayuwa da ze biyo bayan hakan".


Ta karashe hawaye na cika mata idanu tuna irin rayuwar da tayi, mikewa tayi tace "yakumbo bari na tafi zan biya na d'auki yaran nan bani so dare ya mana waje" yakumbo tace "Toh Allah ya tsare ya kiyaye, ba daad'i kam yin magrib a waje, Sannan Ina rokon alfarma watarana ki bani labarin rayuwarki da ban natsu naji ba na d'aura miki karan tsana".


Murmushi ta sake tace "In shaa Allahu yakumbo zan baki duk sadda na samu lokaci, Allah ya kara sauki se munyi waya" sallama sukayi seda ta shiga tayo sallama da innani kan ta wuce direct gidansu ta wuce hankalinta kwance yanzu fah ita bazata iya kashe kanta ba akan Saif wallahi ta dena sa damuwanshi har chan kasan ranta sbd lafiyarta yanzu so take hankalinta ya kwanta ta sauka lafiya ko ma me za'ayi se ayi.


Bayan ta isa sun mata oyoyo se ta ke'be da iyayenta Abba ya kuma mata nasiha akan hakuri kila taci ribar hakurin lahira ya kuma bata teller d'in su Arwa da ya biya musu na shekara, godiya tayi tayi ya kuma ce washegari za'a kawo mata kayan abinci enough da nama da komai, har hawaye tayi tabbas iyaye rahama ne wadda bashi dasu Allah ubangiji yaji kansu ya gafarta musu yasa aljanna ya zama makomarsu, iyaye sune komai nan duniya a wannan marrar da muke ciki.


Cike da tausayinta sukayi mata sallama suka fice, suna isa gida suka samu ba wuta aiko ta kira wani almajirin makocinsu ta bashi kud'i ya samo musu petroleum gallon guda, da kud'in abin hawa ba'a wani jima chan ba ya dawo dashi da kanta ta kar'ba tayi godiya, nan da nan ta saka ta kunna musu aiko suka dinga farin ciki bayan sunyi magrib suka zuba abincin da baaba larai ta zubo musu suka ci sun jima suna hira kan aka dawo da wuta suka kashe gen sukayi kwanciyarsu gwanin daad'i hankalinta kwance.


Ranar Friday akayi hutun makaranta aiko daga nan suka samu abokin hira kullum dare se uncle sulaiman ya zo sun sha hira se kusan 11 yake tafiya, watarana da sumayya yake zuwa ta kwana musu biyu kan ta koma, a haka har aka shafe hutu aka koma school amma dukda haka be bar zuwa ba yayinda kullum Abba se ya kirata ya tausasheta sossai abubuwan suka zo mata da sauki, akai akai yanzu yakumbo ke zuwa ta duba su.


Yammacin yau Su Arwa suna baje tsakar gidan suna wasa yayinda maamin tasu ke zaune kan wani Lallausan carpet tana karatun littafi a wayanta sossai take jin daad'in karatun na littafin ZUCIYA Na Ayusher mohd, tsayuwar mota sukaji se kuma knocking da karfi kaman za'a 'balla iron get d'in nasu, dakatawa duk sukayi da abunda sukeyi, a gaskiya bata so ta tura arwa sbd bata san wani mahaukacin bane tunda dae wannan ba bugun hankali bane.


Gashi taji daad'in zaman sossai da kyar ta lalla'ba ta mike ta nufi gate d'in a hankali kuma cikin sauri sbd har yanzu ba'a dena bugawa ba, 'budewa tayi tana cewa "wanene haka?" Idanu ta had'a da Saif a tare duk gabansu ya buga kallon harara yake mata yayin da ita kuma take mishi kallon tsananin mamaki "megidan ne, Ko kina da magana?" Da sauri tace "a'a bismillah" tana kaucewa kau da kanshi yayi yace "Da matar gidan nake bud'emin gate" a zafafe ta d'aga ido ta kalleshi "tsabar rashin tausayi Saif a wannan yanayin da nake ciki zaka ce In bud'e maka gate?".


Wani kallon banza ya watsa mata kan yace "In ke bazaki iya ba turo shegiyar da kika shigo da ita ta bud'e tunda bazata ci a banza ba" a matukar razane cikin matukar firgita ta waro idanunta tana kallonshi In a more than shock shi karan kanshi yaga firgicinta har kan cikin jikinta, da kyar ta had'iyi wani mugun miyau ta koma da baya da kyar ta tura get d'in a hankali har karshe kan ta jinginu da jikin gini kanta na tsananin sarawa kokari take kar hawayen idanunta su zubo.


Mota ya koma ya janyo ya karaso dashi ciki ihu yaran suka sanya tare da nufan motan suna ihun paapa wani irin tsawa ya buga musu yana bud'e motan yace "ban son iskanci wani irin rashin tarbiyya ne wannan?" Chakk suka ja suka tsaya, a hankali ta sa hannu ta kirasu su duka da sauri suka karasa wurinta a hankali tace "Arwa tura get nan" Arwa tace "Toh" kan ta tura, itade Shaati idanunta na kan Saif da zuby har suka sauka ya ciro musu trolleys d'insu suka wuce cike, cikinta ta dafa jin har yanzu yana juyawa.


Tun daga randa ta had'u da Saif har sukayi shekara kusan 12 be ta'ba yi mata gori ko habaici akan abinda ya faru da ita a rayuwarta ba se yau, abin yayi mugun firgitata wadda seda neeha ta jijjigata kan ta dawo hankalinta tana kallonta kuka take tana kawo karan Paapa ya mata tsawa, hakuri ta basu tace "kuyi hakuri abinda kenan zan iya cewa muje ciki" ciki suka nufa a parlor duk suka zauna jiki a sanyaye, daga nan suna jin dariyar zuby.


Ganin shirun ze musu yawa yasa ta saka musu MBC3 tace "maza muyi kallo" kallo suka cigaba dayi yayinda ita idanunta suna kan TV amma hankalinta na wani wurin ambaton Allah kawai take cikin zuciyarta ya kawo mata sauki zamansu gidan, suna nan zaune har aka kira magrib Mikewa sukayi suka gabatar da sallansu yadda suka saba abinci ta zuba musu yana shigowa daga masallaci ya gansu zaune suna cin abinci.


Tsaki yaja yana kyankyamin yadda suka had'u dukkansu plate guda suna cin tuwon shinkafa da miyar kuka da yaji nama da man shanu, tsaki yaja yana wucewa d'akinshi, chan kuma se gasu sun fito sanye take da wani sleeves gown me shegen transparent ga tsagu daga kugu har kasa, ba bra jikinta se pant, a manne dashi suka zube kan kujerun parlorn da sauri Shaati tace "kuje ku wanke hannayenku ku tafi d'akina maza ganinan zuwa".


Mikewa sukayi suka wuce a tsorace Da mahaifinsun dake zabga musu harara, cike da takaicin dawowarsu gidanta kar su 'bata mata tarbiyar yara ta lalla'ba ta mike ranta na suya bafa ze sa'bu ba bazasu sa mata hawan jini ta mutu wurin haihuwa ba, seda ta daidai ta tsayuwanta kan tace "Saif" daga idanunshi yayi ya kalleta be ta'ba ji ta kira sunanshi ranta a 'bace cikin zafi haka ba, zuby ma ita ta zubawa idanu cewa tayi.


"Be kamata ba sam wallahi, inace tana da gida? Ya dace ka kawota nan gidana ta tare kuna kokarin 'batamin tarbiyar yara?" Waro idanu zuby tayi tace "ashe har wani tarbiya ce dake ban sa...." cikin tsawa tace "ke dallah rufemin kazantaccen bakinki ba da ke nake ba da wadda ya auroki nake, kai kuma kana jina ko 'ya'yannan ko ba naka bane bazakaso tarbiyarsu ya lalace sbd kai ba, ya kamata ka koma hankalinka ka san abinda kakeyi".


Bata jira abinda zasu ce ba ta shige d'akinta kan ta isa tana jin yadda zuby ta rikice mishi akan ta zageta yana ji yaki cewa komai, tsaki taja tana karasa shiga d'akinta, duk wani abinda suka saba yi sukayi suka kwanta da wuri ranar yaran dukkansu d'akin suka kwana sbd tana tsoron su fita su dinga ganin haukan zubaida da Saif Don ita a wurinta hauka ne ba soyayya ba.


Da kyar ya samu ya lalla'bata kan ta turashi sayo musu abinci, bayan fitanshi ta wuce d'akinta tana dialing numbern babanta, kira uku ya d'auka "baba na zo kaduna fad'amin abinda kace zaka fad'amin se na zo ze yiwu akan wannan wawiyar yarinyar" Shiru ya d'anyi kan yace "ki samu lokaci ki zo zan baki wani laya da zaki kai makabartar yamma ki ba me gadin ze binne cikin sabon kabari da aka kai ranan yayi sheda bayan kwana uku ya d'ibo miki kasar daidai wurin, hahahhaaha".


Murmushi tayi kan tace "me d'aya ze faru? Me ma zanyi da kasan?" Yace "zakiji se aiki ya kankama d'iyar arziki kede inji kud'i duk wani hanya da za'a rabaki dashi se na toshe miki shi" dariya sukayi a tare kan suka kashe wayan, bayan Saif ya dawo daga sayo abincin suka ci suka kwanta.


Washegari bayan tayi sallahn asuba ta shige kitchen ta fara fere Doya yayinda Arwa ta fara yiwa kannenta wanka Yasmin na shiryasu tana cikin fere doyan taji alamun tsayuwar mutum d'ago kai tayi se suka had'a idanu ta kawar da kanta tana cewa "mun tashi lafiya?" Be amsa ba se cewa da yayi "hope da mu duka kike wannan girkin?" Kai tsaye tace "nop" Wara idanu yayi "kina da hankali kuwa? Wa kike aure? Ni zan sauka gidana in kwana jiya baki bani abinci ba Sannan yanzu kice..." katseshi tayi "dakata malam kayan abincin da suke gidan nan ba kobonka bare sisinka ciki, ka bari duk sadda ka sayo ka ajiye  se In dafa dakai ba se ka min ihu ba"


Waro idanu yayi yace "ni kike cewa nake ihu?" Tace "me maraban wannan da ihu? In d'aga murya kake don er gwal d'inka taji ta san ka zo 'batamin rai ka sani a ban...." d'aga hannu yayi a Zafafe ya kai mata..........

                    🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇

   *Baya Chanza d'and'anon teku*


       *Fatima Muhammad Gurin*

    **Gureenjo6763 on Wattpad**


              'Yar Mutan Adamawa

        *P18*


Cikin azama ta kauce ya mari iska, a mamakance tace "mariii?" Kallonta yayi se ya ja tsaki ya fice, wani irin banzar murmushi ta sake tana cewa "Da kuwa ka mari igiyar aurenka" ta ci gaba da girkinta kan ta gama soya doya da sous d'in har sun shirya tsab ta zuba musu suka zauna a dining suka ci suka koshi, kowacce ta d'auki lunchbox d'inta zuwa mota yayinda Shaati ta watsa ruwa sharp sharp mai kawai ta shafa se turare ta zura doguwar riga tare da zumbula hijab ta fito.


Suna ganinta Arwa taje ta bud'e gate seda ta fidda mota kan Arwa ta rufe gate d'in ta taho da gudu ta shige motan, ba 'bata lokaci ta ja suka wuce zuwa school d'insu suna hira da dariya da yaran taji daad'i sossai da basu damu sossai har chan da chanzawar uban ba neeha ce ma take d'an rigimanta kad'an kad'an tana kiran sunanshi, amma shaati na bata sweet dake cikin motan ta mance dashi suka fara rikici da sameer, bayan ta saukesu ta sauke ajiyar zuciya tare da kwantar da kanta kan staring d'in motan.+


Me Saif ke nufi ne da ita? Ba fa zata lamunci zaman zubaida gidanta ba Allah ya gani tana tsoron tarbiyar yaranta yadda zubaida take marar kunya yara kuma gasu duk da kaifin basira da saurin fahimtar abu, Sannan bafa zata amince a dinga banzar Iko da ita sbd wata Kishiya ba Sannan bazata dinga kulewa d'aki ita da gidanta ba.


Nazari ta dingayi yadda zatayi zaman dasu sede duk yadda take ganin abin ze yi sauki ta tabbatar bazasu jima cikin zaman lafiya da zuby ba har gwara saif zata iya taka mishi birki Don ta lura kallon cikin kwayar idanunta chan kasa baya barinshi yin duk abinda yayi niyya, Sannan adu'a ma na taimakonta yawan ambaton Allahn da takeyi yasa take iya fuskantarsu har kuma taji duk wani 'bacin ran da suka kunsa mata ya gushe cikin kankanin lokaci.


Murmushi tayi a fili tace "Allah sarki Roohul Na'im, I'm ready to forgive you duk sadda ka dawo" jan motan tayi zuwa gida, da kanta ta sauka ta bud'e gate ta shigar ta dawo ta rufe kan ta nufi parlor, turus tayi ganinsu baje suna karyawa da alamu fita yayi ya saya, "Assalamu Alaikum" shine kawai abunda ta furta kan ta nufi corridor don zuwa d'akinta.


"Ke!!" Taji muryanshi ya fad'a bata tsaya ba kaman yadda bata nuna ta San da ita yake ba saura be wuce taku biyu ta shige ba yace "Aisha" chakk ta tsaya tare da waigowa tace "na'am" kallon ta yayi daga sama har kasa kan yace "zaman aure kikeyi ko zaman kanki?" A mamakance tace "zaman aure" yace "then why zaki fita ba tare da izinina ba? Kenan dama rashin zamana garin nan ya baki lasisin yin yawo duk sadda kika ga dama" katseshi tayi "ka ajiyemin kud'i? Ka ajiyemin abinda ze sa bazan fita nema ba? Naga dai yaran nan nakai makaranta na sallami driver d'insu sbd ba kud'in da zan biyashi to shine laifi?"


Kallonta kawai yakeyi wadda hakan ya ba zubaida haushi gani take wani kallo na daban yake mata cikin kashe murya tace "baby to ga shawara mana" kallonta yayi yayinda shaati ma ta zuba mata idanu murmushin mugunta tayi tace "naga akwai wani government school nan kusa damu ka maida su mana kawai yadda zasu dinga tafiya da kafa ba se an fita kaisu ba".


Murmushi yayi yace "tabbas hakan za'ayi yau ba se gobe ba zanje In fiddasu" kan ya gama ajiye maganan Shaati tace "impossible wallahi, 'ya'yan nawa za'a cire a makaranta me kyau irin feature leaders a kawosu wannan government school d'in? To baze yiwu ba tunda dae ba kai ka biya musu kud'in makaranta na shekaran da suke ciki ba".


Mikewa tsaye yayi yace "aw ashe 'ya'yan ki ne ke kad'ai ban sani ba? 'Ya'ya nawa ne Sannan ni nafi iko kansu ciresu a school se na cire sede zan bar miki taki In kin yi ra'ayi ki kaita waje karatu karshen private school" kallonshi kawai take ba tare da ta amsa ba, ta harari zubaida ta wuce d'aki tana shiga ta d'auki wayanta ta kira yakumbo cikin kuka ta bata labarin abinda ya faru.


Ai kuwa nan da nan tace gata nan zuwa, tana shigowa yana kokarin shiga mota "tsaya tsaya dakata malam!!" Fitowa yayi tare da tsuguna yace "Ina kwana yakumbo?" Tace "kalau, saifullahi ashe har asirin da matar taka ta maka ya cika haka ban sani ba da zaka nemi taggayara rayuwar 'ya'yanka?" Mikewa tsaye yayi yace "hajiya yaran nan fa sauki nake nema musu daga ita har su taya za'ayi ace kullum se ta fita sau biyu kaisu da d'aukosu ba tare da izini na ba? Sanna makarantar gomnatin ma fa ana ka..." katseshi tayi "dakata au haka matar taka ta gumtsa maka ka fad'a?".


Kanshi kasa tace "tambayarka nake? To saifullahi In har na isa dakai ka kyale yaran nan yadda ka dawo ka samesu In kuwa ban isa da kai ba kaje ka ciresu ba ruwana da asirin dake cinka tsine maka zanyi kabi duniya kowa ma ya huta" kanshi kasa be bata hakuri ba be ce komai ba chan de ya juya ya shige cikin gida, a baya yakumbo ta bishi daidai lokacin Shaati ta fito rike da plate d'in abincinta zata ci ganin ya shigo a fusace yasa ta ta'be baki se kuma taga yakumbo ta shigo.


Murmushi ta saki tana cewa "ah yakumbo sannu da zuwa" murmushi tayi itama tana zama, kasa take kokarin zama da sauri yakumbo tace "a'a a'a zauna sama Ai kasan ze mike wahalan tashi" ta zauna tana gaidata amsawa tayi tana kallon plate d'in shaatin kan tace "yanzu wannan zakici?" Murmushi tayi tace "Eh yakumbo bari In zubo miki" Da sauri tace "aaaaa ni rabani da kika kirani d'umamen tuwo na nake ci, naci nayi nak shiyasa fa muka fiku kumari yanzu a doyan ma d'an wannan ne zaki ci?"


Dariya sukayi a tare daidai lokacin zubaida ta fito tana er wakanta "kowakki sharan masallaci dolen dole yayi na kasuwa.... ayyiririr nanaye" kallonta yakumbo tayi zatayi magana Shaati tayi saurin cewa "yakumbo batun makarantar yaran nan ya yarda kuwa?" Murmushi tayi tace "Ai dole ma ya yarda, Yauwa kinga wannan annamimiyar munafukar yarinyar wallahi karki raga mata tana cewa ass ki amsa mata da chasss karki d'auki reninta kiyi ta yawan hakurin nan naki".


Murmushi shaati tayi a gaskiya yakumbo bata san wace ita ba In aka zo 'bangaren masifa, tana kallo zubyn ta shige kitchen d'inta kau da kai tayi tana ji yakumbo na cewa "wani bala'in ne ma ya kawosu gidanki? Me ya samu gidanta?" Cewa tayi "yakumbo kyalesu nan ma Ai gidanshi ne kuma yana da iko damu" hira suka ci gaba da yi har zuby ta kuma fitowa hannunta rike da kofi tana wakanta ta shige.


Ba'a jima ba yakumbo ta wuce bata ko kara neman Saif ba, bayan fitanta shaati ta koma d'aki ta kara gyare jikinta ta sanya paper lace dinkin doguwar riga da yayi matukar amsarta ta kafa d'auri Bayan ta gyare gashinta tayi parking a tsakiya powder ta shafa da kwalli se jambaki nan ta fita d'as kaman ba me tsohon ciki ba, wayanta ta d'auka ta koma parlorn a ranta tana cewa 'tunda ba na uban kowa bane'.


Ba kowa ciki hakan ya sa tayi zamanta nan tare da janyo remote ta maida sunna tv tana kallo, chan ta jiyo tafiya bata d'aga Kai ta kalli me zuwan ba bare wani abu ya dameta, seda taji wurinta akayo yasa ta d'aga Kai zuby ce ta nufota sanye da kayan baccinta dae ko wanka har yanzu batayi ba, kallon ikon Allah take mata har ta karaso ganganta ta sa hannu ta d'auki remote ta maida shi boom tv.


Mikewa Shaati tayi tana ajiye wayanta a hankali tace "ke zubaida kike ko wa? Kin san girman ubangiji karki kaini bango a gidan nan? Bana fad'a bare cacan baki sede zan miki duka, kin gane duka, so maida abin nan inda kika sameshi kan ran kowa ya 'baci a gidan nan" Aisha akwai tsare gida In ta tsare tana masifa ko namiji se yayi shakkanta, Bare mace irin zubaida da ta mata farin sani ta san tana da karfin dukantan ba cika baki ba.


Tsaki tayi tana cewa "mtsewww kayan banza ayi dae mu gani in mijin ya kula bare ya yaba" wani irin dariya Shaati tayi tace "har ke Ina kike lokacin da ake yabawan daga kasan zuciya ba na dole ba? Karki kara sa inyi magana ki mayar min da abina inda kika ganshi tunda ba tsohonki ya sai min ba".


Mayarwa tayi kan ta saki ihu tana fad'uwa da sauri Saif da ya gama sa hula da turare ze fita ya fito da gudu yana nufanta d'agota yayi yace "honey lafiya? Me ya faru?" Kuka ta saka cikin makirci tace "tunda ka d'aurewa tsohuwar karuwar matar kan nan gindi ba dole ta raina ni ba marina fa tayi ta turani seda na fad'i" waro ido yayi kan ya d'ago ga shaati "kina da hankali kuwa? In ban da salon neman fad'a da munafurci taya zaki turata tayi wannan fad'uwan ki tsaya kina min innocent face?".


Cikin kuka zuby tace "wallahi bazan yarda ba se ka ramamin" gyara tsayuwa shaati tayi tana kare musu kallo yayinda take yiwa Saif wani kallon Allah ya baka sa'an tasowa rama mata se kuwa taga ya kamata ya mikar yace "Ina gargad'inki kada ki kuma dukarmin mata don se ranki yayi mummunan 'baci, tara miki nakeyi kin hanani abinci a gidana, kin kai karana wajen uwata Sannan yanzu ki daki matata? Randa duk kikayi na hud'un wallahi wallahi baki bina bashin rantsuwa se nayi mummunan sa'ba miki".


Ganin ya hau kuma ya d'auka da matukar zafi yasa ta kau da idanunta tana cewa "Allah ya baka hakuri" tare da zama ta maida hankalinta kan wa'azin da sheik tijjani yusuf guruntum yakeyi, kama matarshi yayi suka shige chan se gashi ya fito ya fice ba'a jima ba itama ta fito cikin shiganta dae irin na da kan tayi aure attach me shegen tsada two colors har kan duwawunta ta fice tana taunan cingum, girgiza kai shaati tayi tana mata fatan shiriya.


**********


"Wai kece haka diyar nan?" Tace "ni ce mana inna me kika ga nayi?" Tace "kina cikin jin daad'i da morewar rayuwa haka shine zakice me kikayi? Kinga yadda fatanki ya koma? Amma shine baki ta'ba turomin ko naira ba" ta karasa abun tausayi kaman gaske, Wara idanu zuby tayi tana ta kallon gidan wai ita kyankyami se 'bata fuska take tace "wai inna baba be ta'ba baki kud'i ba?" Tace "a'a nide be bani ba" had'e fuska tayi tana cewa "lallai baban nan kin san Ina turomishi akan ya baki?" Nan fah inna ta hau sababi da masifa akan baba maganganu zagi kaman basu ta'ba had'a shimfid'a ba.


Batayi Shiru ba seda Zuby ta ajiye mata 50k kan kafa nan ta washe baki tana sanya mata albarka suna nan yayanta ya shigo a buge da wata shar'bebiyar tsirarar wuka a hannunshi a tare duk suka mike inna tayi saurin 'boye kud'inta matso zuby yayi yana mata wani kallo "ke dan ubanki kina chan kina jin daad'in rayuwa mu kin barmu da neman na apawa haka akeyi er kaza kaza kaza" ashar dae kala kala, da sauri ta bud'e jakanta ta d'auko dubu ashirin ta bashi nan ya fara yabonta kaman itace oganniyanshi kan ya wuce d'akinshi yana ball da kwanonin inna dake tsakar gidan.


Komawa sukayi suka zauna ba jimawa baba ya dawo nan fa suka kule a kuryarshi bata bari ma sun fara zancen shaati ba ta fara mishi maganan kud'i seda ya damka mata wata laya kan tayi tsit yace "itace zaki kai makabartar yamma ki bawa me gadin zan mishi waya mutumina ne" yayi shiru yana tsubbace tsubbacenshi kan yace "dangin ita kishiyar taki sun matukar tashi tsaye idan baki hanzarta aiki ba komai ka iya lalacewa" wata ashariya ta lailayo ta zuba cikin tashin hankali tace "bamuyi haka da kai ba, ba munce aikina baze ta'ba 'baci ba har abada me yasa kake kawomin zancen yanzu?" A zuciyarshi yace "akwai wani me gaskiya ne in ba Allah ba? Akwai wani dawwamammen aiki da baya lalacewa ne In ba na ubangiji ba?" A fili kuwa yace.


"Karki damu sake hannu kawai zan kula da komai" wasu kud'ad'en ta ajiye mishi tana mikewa bata kara minti d'aya a gidan ba ta fice tana tofar da nyau itafa gidan yanzu ba tsaran zamanta bane, direct napep ta tara tana ayyanawa a ranta dole ne kawai ya saya mata mota baze yiwu wanchan matar tashi na yawo a mota ita tana yawo a napep ba.


Tana isa ta bashi tare da bashi kud'i ba tare da sunyi magana ba ta juya ta fice, gida ta dawo ta shige d'akin Saif dukda ba kowa parlorn sede bazata iya zama ba.


Yau da dare sulaiman ya zo sbd be samu zuwa Jiya ba hirar da suka saba suka kafa cikin raha da wasa da dariya, suna d'aki suka jiyo dariyarshi murmushi zuby tayi tace "Da alamu maganata na son tabbata In ba iskanci takeyi ba me ze kawo namiji da dare gidanka me ya samu rana da be zo ba se dare?" Kallonta yakeyi a hankali yana yarda da abinda take fad'a ta kara da "yanzu haka In ka bincika kullum se ya zo to me yakeyi In ba d'ebe mata kewa ba? Kayi tunani da kwakwalwanka".


Shiru yayi cikin nazari kan ya mike ya nufi parlorn cikin kausasa murya yace "me kakeyi a gidan nan?" Da sauri sulaiman ya juyo yaji ance yayan nashi na gari sede fa shi be so su dinga had'uwa kar zuciya ya d'ebeshi ya jibgi wawiyar matarshi da yake samun labarinta a gari, "yaya barka da dare?" Cikin fad'a yace "ba abinda na tambayeka ba kenan" Saif da ba mafad'aci ba se sam fad'a baya mishi kyau yasmin tace "papa yana zuwa kullum yana mana hira da tayamu d'e...." cikin tsawa yace "will you shut up bastard, dake nake magana? Wato an koya muku tarbiyar sawa manya baki In suna magana".


A tsorace yasmin ta 'buya bayan sulaiman tana hawaye neeha ta mike tace "papa papa plsss stop act....." mari ya kifeta dashi da seda ta hantsila ta sake wani kara cikin firgita da sauri Shaati ta mike ta d'agata tana mannata da jikinta, cikin tausayawa yarinyar kuka take bilhakki da gaskiya, mikewa sulaiman yayi yana cewa "In Don na zo gidanka shine zaka tasani gaba kana fad'a harda dukan yaran da basuji ba basu gani ba kayi hakuri zan tafi bazan sake zuwa ba" ya juya ze fita.


Shaati tace "sulaiman kayi hakuri karka d'auka da zafi kaji?" Cikin yarda da maganan zuby yace "Eh haka zakice Ai dama an kora miki me d'ebe miki kewa, ashe honey tayi gaskiya" kallo sulaiman da ya razana da jin maganan yayanshi yayi yace "ka sake zuwa min gida wallahi court ce zata rabamu banza maci amana" ya juya ya shige, da hanzari sulaiman ya fice cikin tashin hankali yayinda shaati ta saki salati tana karawa cikin mika dukkanin lamuranta ga Allah. Zarginta kuma ya fara?.

                    🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇

   *Baya Chanza d'and'anon teku*


       *Fatima Muhammad Gurin*

   **Gureenjo6763 on wattpad**


              'Yar Mutan Adamawa


       *P19*


Da kyar taja kafafunta zuwa d'akinta hannunta rike da na neeha dake kuka, da kyar ta zauna ta kwantar da ita kan cinyanta tayi ta shafa kanta, tun tana yi da karfi har ta dawo a hankali daga karshe shesheka se kuma bacci ya d'auketa cikin sauke ajiyar zuciya, idanunta na kan hannunshi da ya kwanta kan fuskan yarinyar gwanin tausayi, ta rasa tunanin da zata kama sam komanta ya tsaya chak.


Mikewa tayi ta shige toilet ta zauna kan ta fara kuka cikin kunan rai, ta jima sossai tana kukan kan ta mike ta wanke fuskanta Don ta san su Arwa na chan maybe kukan suma sukeyi she have to be strong ko don sbd su, fitowa tayi zuwa parlorn she guessed right sun kuwa had'e wuri d'aya kaman wasu marayu Allah ya taimaketa ma Arwa bata da magana da kila ita ze dinga jibga Sannan she is glad da be ta'ba kawo zancenta a gabanta ba.+


"Yaran maami me kukeyi nan ku taso muje muyi shirin kwanciya" Mikewa sukayi seda suka wuce kan ta bi su a baya, tana zaune idanunta zube a kansu har suka gama chanzawa zuwa kayan bacci sukayo alwala suka zo suka kwanta, kasa ta sauka bayan tayo alwalan itama ta kashe musu wuta, tana jinsu sukayi adu'an bacci suka kwanta. Ita kam sam bacci ya kauracewa idanunta Allah kad'ai ya san kaddaranta nan gama sbd ta lura bazasu zauna da Saif ba, zargi a cikin aure shine babban abu dake saurin kashe aure.


Ba'a ta'ba zaman aure ba yarda, amma In ta bar gidan saif yaranta fah? Bazata iya barinsu hannun azzaluman nan ba, sbd ta san ba kyautatamusu zatayi ba, da sake saken da ta san bacci ba d'aukanta zeyi ba yasa ta fara karatun qur'ani cikin wadda ta haddace kanta har bacci ya kwasheta.


BAYAN THREE DAYS


Har zuwa yau da zata je kar'bo kasan da baba ya mata umarni kullum se sun samu matsala da shaati, yayinda hakan ke kara bakantata wuri Saif, ko gaisuwanta ba amsashi yakeyi ba sbd zarginta da ya tsananta gareshi bare yaran da kallon arziki be had'a su Allah ya taimakesu suna zuwa islamiya da boko se dare nan ma ba wani jimawa suke a parlorn ba suke kwanciya.


Shaati dae ta tabbatar aka kuma duba jininta se an sameshi ya hau yadda ba'a so sbd duk ta yadda ta so nuna bata damu da damuwansu ba hakan na damunta kwarai da gaske, rashin kunyar zubaida kuwa tana fata ta sauka lafiya ta setata ba ruwanta da Saif dukan mutuwa se ta mata shi ko ba jima ko ba dad'e, yakumbo

Bata kara zuwa gidan ba hakama sulaiman, ta de kira Mama ta fad'amata dawowansu sede ta 'boye abubuwan da suke mata, tana mamaki idan akace tana da en uwa da suke ciki d'aya amma basu nemanta ko ta kirasu ba lallai su d'aga ba ya majeed ne kawai suke waya da yaji labarin halin da take ciki wurin Abba kuwa har zuwa gidan yayi bayan ya turamata kud'ad'e masu yawa account.


A shirye tsab ta fito tana karairaya kaman zata karye ta karewa shaati dake yankan farcen hannunta kallo wani irin dariya ta kwashe dashi ta kuma kalleta sama da kasa "yarinya duk abinda kika san zakiyi kiyishi don gobe ba labarinki nan duniya" wani kallo ta watsa mata tace "dayake kece ubangiji ko? Bari kiji baki isa yi min Abinda Allah be kaddara ba In kinga kin samu galaba to Allah ne ya so daga ke har mahaifinki nafi karfinku sbd Allah na rike".


Baki ta ta'be tana wucewa, direct makabartar tayi aiko wannan marar imanin me gadin ya bata kasan a wata leda ta juya ta wuce, seda ta sauka kofan gate d'in gidansu kan ta fiddo waya ta kira baba, bayan ya d'aga ba gaisuwa ba komai tace "na kar'bo ya za'ayi dashi?" Yace "ki bari se cikin dare kiyi yadda zakiyi ta 'bata mai makura har ya saketa, toh kan ya saketa ki zuba kasan nan bakin kofan fita daga parlorn In har ta bi ta tsallaka shikenan magana ta Kare sede wata ba ita ba".


Cikin tsananin murna ta kashe, ta shige gidan tana tunanin abinda zatayi bata karasa ba ta kuma juyawa ta fito sbd idea da ya fad'o mata, jeebson ta fara nema seda ta kira sau kusan hud'u kan ya d'auka da alamu harka yake cikin wani yanayi yace "ya ne? na tabbatar bukatanki ce tasa kika neme ni, sbd yanzu kinyi kud'i shine kike d'ad'age min kai".


Tace "ni de ba wannan ba jini nake so ka samo min leda guda ko nawa kake so zan baka" yace "koh? Toh 200k nake so yanzu kiga aiki da cikawa" tsaki tayi tace "wannan ba komai bane ka samomin zan maka transfer in ka samu ka kirani zan maka kwatancen inda zan kar'ba" kashewa yayi ba tare da ya amsa ba ta shige gida tana wakanta cikin farin ciki bata kula Shaati dake zaune parlorn ba ta san karshenta ya riga ya zo.


Chan kuwa ba jimawa sossai ya kirata yace ya samu ina ze sameta ta mishi kwatancen gidan ya kuwa kawo ta fita ta kar'ba tare da damka mishi kud'in ya so ya nemi wani abin bayan kud'in ta harareshi ta wuce, a 'boye ta shige da jinin ta adana.


TASHIN HANKALI WADDA BA'A SANYA MATA RANA.


Wuraren karfe 11 a lokacin gidan Shiru duk sun shige yayinda Saif ke zaune yana operating system d'inshi da alamu wani aiki me muhimmanci yakeyi Mikewa tayi ta je jikin socket ta saka wayanta dama d'azu ta 'bata charger d'inta da gangan, d'agowa tayi tana kallonshi tace "kashh charger na ya lalace gashi Ina da wani important call wallahi" d'agowa yayi ya kalleta yace "dauki wayata mana in yaso gobe se in sai miki wata chargern".


Shagwa'bewa tayi tace "ban haddace numbern ba gashi wayanka ba Iphone bace, yanzu ya zanyi?" Tayi maganan gwanin tausayi yace "Ai wayan Aisha iPhone ce je kar'bo charger d'inta kiyi anfani dashi" murmushin samun nasara tayi kan ta shiga closet ta sanyo hijab ta kunzuga jinin tare da soka allura jikin hijab d'inta ta kuma d'auki ledan kasan ta fito ta fice.


Seda taje ta barbad'a a kofan parlorn kan ta dawo zuwa d'akin Aisha bubbugawa tayi tayi har seda Aishan ta taso ta bud'e idanunta da alamun bacci, ciki ta nufa wadda yasa Aisha bata hanya taga gudun ruwanta, seda ta kalleta sama da kasa ta karewa d'akin kallo kan tayi wani murmushi se kawai ta tsala mugun kara ta kuma tsalawa da azama ta sa alluran nan ta 'bu'bula jinin nan nan take ya fara bin kafanta ihun ta ci gaba dayi hannunta dafe da cikin Aisha da Ta zama speechless sbd wannan abin al'ajabin ta karaso tana ta'ba ta tace "ke kina lafiya kuwa?".


Kan ta rufe baki Saif ya shigo hannu zuby ta mikamishi cikin kuka ta d'aga hijab d'inta salati suka d'auka a tare da Aisha da Saif cikin tashin hankali yace "me ya faru? Me ta miki?" Cikin wani irin yanayi tace "tun a Abuja da nayi wani rashin lafiya naje asibiti akace Ina da ciki na 'boye maka ne sbd Ina son ma surprise......."


Numfashi ta ja tana taune lips tace "shine yanzu daga zuwana aran charger wannan marar imanin ta nausheni a ciki" kuka ta saka harda shesheka kaman gaske ta d'aura da "dama sunce ba kwari yayi ba tunda na satuttukane Sannan mahaifana ba karfi abu kad'an na iya zubar dashi, gashi ta min asarar d'ana na fara shikenan na shiga uku..." ta kuma rushewa da kuka tana kallon yadda Saif ke 'bari tsabar 'bacin rai ta san ta yadda yake son yara ne kawai zata iya cin galaba akan hakurinshi.


Murmushin cin nasara ta sake cikin kukan da takeyi na karya ta cigaba da sambatu, a hankali ya sauketa ta kwanta kasa ya mike, Aisha da ta zama kaman kankara wani sanyi take ji yana shiganta har cikin 'bargonta tsabar shock da ya shigeta, wannan irin sharri ne da yake hana ko iya motsa en yatsu, ganin irin kallon da yake mata yasa ta fara girgiza kai tana kallon gadon da 'ya'yanta suke cikin zafi yace "shikenan burinki ya cika? Kullum baki da abin so sede kiga kin bakantamin rai kin bakantawa matata, Aisha wallahi na tsaneki tsana mafi muni da ban ta'ba yiwa wani halitta ba, dama kin dad'e kina haintata zama kawai nake dake sbd abinda ke cikinki amma yanzu zan d'au mataki".


Girgiza Kai ta ci gaba dayi ta kasa furta ko A, cikin karaji yace "wuce ki fitarmin daga gida Aisha na sakeki saki d'aya wallahi kika kara mintuna biyu se na illataki daga ke har banzan abinda ke cikinki da ban tabbatar nawa bane ko ba nawa ba" bata iya magana ba se juyawa da tayi ta duka kan sallayanta ta d'auki hijabin sallanta ta saka, wani irin kallo ta mishi na ka tabka babban kuskure ta kuma kalli zuby dake kasa har yanzu idanunta kaman zasu fad'o tsabar firgita da be saketa ba tayi wani murmushi na takaici ta juya ta fice a hankali.


Yau 'bacin ranta ya tsananta hakanan zuciyarta ya dake ba abinda take iya tunawa se kalmomin Saif na na tsaneki tsana mafi muni, mutumin da ta d'auki son duniya da kulawa ta d'aura mishi inda tayi kuskure kenan bata iya ambaton sunan Allah ba se kwakwalwanta da taji ya birkice hannu ta kai ta bud'e kofan parlorn tare da d'aga kafa ta tsallaka ta kara d'aga d'ayar ta tsallaka.


Wani irin abu da bata san menene ba taji yana bi mata jiki shaaaa daga kai har kafa yayinda take jin wani irin kara a cikin kunnuwanta harshenta taji yayi nauyi ya cika mata baki tabb yayinda abin cikinta ke wani irin juyawa, kafanta dake rawa taci gaba da ja dukda azabar da takeji bata fata ta kara minti guda cikin wannan gida.


Tun tana sanin inda take sa kafanta har ta fice hayyacinta, ta fara tafiya kawai ba tare da ta san inda take jefa kafanta ba har ta bar layin unguwan ta fara kutsawa har ta 'bace.


Ta 'bangaren Saif kuwa d'aga zubaida yayi zuwa d'aki a rikice yake cewa "ko mu tafi asibiti?" Kai ta girgiza tace "kad'an kad'an kawai marana ke ciwo barni In huta anjima kad'an In watsa ruwa se gobe inje asibitin da inna" cikin damuwa yace "to Dan Allah ki 'boye musu karki fad'a musu, In kun dawo se mu d'auki yaran nan mu wuce abuja sbd na san yakumbo se ta kusa tsinemin ko ta saka In mayar da Aisha a tsanar da na mata kuwa zan iya kasheta ta dawo gidana".


Wara ido tayi tace "mu tafi da wasu yaran?" Yace "su Yasmin mana, karki tada hankalinki In munje zanyi DNA dasu in 'ya'ya nane to sun koma Abuja kenan da rayuwa ba wadda zan ba d'ana" Shiru tayi a zuciyarta tace 'kan ubanchan, na kashe maciji kenan ban sare kanta ba' kwanciya kawai tayi cikin sake saken yadda zata wulakanta yaran se sun zama abin tausayi.


Ta 'bangaren Arwa kuwa tunda zuby tayi ihun nan ta farka komai akayi a gabanta suna fita ta d'auko wayan mamyn nasu ta danna kiran Mamah cikin wannan dare, seda ya kusa tsinkewa kan mamah ta d'aga tace "Aisha lafiya kuwa?" Kuka Arwa ta saka tana cewa "Mama ba lafiya ba maami ta tafi Yanzu Paapa yace wai ya saketa" a rud'e tace "Innalillahi wainna ilaihi rajiun Arwa fahimtar dani yadda zan fahimta ban gane ba me kikace? Cikin daren nan? Da tsohon ciki jikinta?".


Kuka kawai Arwa keyi Mama tace "dena kukan nan yi Shiru bari muga zuwan Maamin naki" ajiye wayan tayi tana ci gaba da kukan ta, ta bangaren Mama cikin tashin hankali take fad'awa Abba da yake tambayanta abinda ke faruwa, shima Mikewa yayi tsaye ya fara zirga zirga cikin kirga mintuna ko zasu ga shigowarta sede Shiru bata ba alamunta.


Kuka Mama ta fara "Innalillahi wainna ilaihi rajiun kar dai sun salwanta min rayuwar 'ya ya rabbi ka kawota gida cikin tsarewarka" khaih tun fa ana maganan minti har aka koma awa Ai da hanzari Abba ya fita ya d'auki mota da gudu Mama ta biyoshi ba yadda ya iya se jiranta ta shiga yaja motan suka fice zuwa gidan Shaatin sede tunda suka kama hanya har suka isa kofan gidan suke dubawa basuga me kaman ta ba bare ita.


Yawon nemanta sukayi tayi tunda har Arwa tace ta fita, a yanzu Abba baze iya fuskantan Saif ba shiyasa be buga gidan ba don idan har sukayi ido hud'u to fah me rabasu se Allah, a daren nan suka kai police station tunda ba waya hannunta, chan gidan kuwa hajja taji fitan mota wadda hakan ya sa ta tado duk ka en gidan sukayi cirko cirko jin maigadi yace Abba da mamah ne suka fita a rud'e.


Tsayuwar jiransu suka kafa, kusan awa biyu se ga horn d'insu a sanyaye ya sanya kai cikin gidan yana parking Mama ta fito cikin kuka take tambayarsu "Aisha bata zo ba?" Suka had'a baki wurin cewa "Aisha kuma wani abin ne ya faru?" Hajja tace "Mamman me ya samu Aishan?" A karye yace "mijinta ya saketa ta fita cikin daren nan da tsohon ciki tun kusan awwani uku har yanzu bata zo nan ba kuma bata gidan" salati hajja ta sake yayinda Mama ke kara kukanta cikin tashin hankali.


Bud'an bakin baba habu se cewa yayi "wa ya sani ko yawon da ta saba irin na baya ta fita? Kun wani d'aga hankalinku" baba sale yace "Kai ma dae ka fad'a" wani banzan kallo hajja ta watsa musu kan ta juyo ma Abba ya kama Mama sun wuce part d'insu ba tare da sun kulasu ba, hajja tabi bayansu tana girgiza kai da Allah wadai da halinsu.


*In Allah ya kaimu gobe zaku jini Shiru sbd lectures da nake dashi a jere from 9-6*                    🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇

   *Baya chanza d'and'anon teku*


     *Fatima Muhammad Gurin*

   **Gureenjo6763 on Wattpad**


            'Yar Mutan Adamawa


   *P20*


Tafe yake cikin tsananin gudu kaman ze tashi sama kasancewar hanyar ba wasu ababen hawa sbd dare da ya raba har asuba na neman shiga, gudu kawai yake yana duba time ana bukatarshi maiduguri kan karfe 8 na washegarin ranar meeting d'in is so important to him gashi se bayan magrib ya baro Abuja, ko kad'an be tsoron irin hanya haka ya riga ya saba tafiyan dare MAJ Shareef kenan, ko Ina yana iya zuwa cikin dare sbd ya saba kuma bashi da tsoro.+


Duba time da yakeyi kuwa sbd matarshine jiddah ya san In har ya hau hanya hk kuma ta sani bata iya bacci sbd rashin tsaron da kasar ke dashi sede shi fa ba ruwanshi In yayi niyyan abu to fah se yayi, tun daga nesa yake hangan kaman mutum ne kan tsakiyar titin kuma kaman mace da ciki, slow down ya fara zuciyarshi cike da zargin anya ba tarko bane aka kafa? Sede Ai bazece daga wasu colleges d'inshi bane tunda ba wadda ya san tahowarshi, kila 'barayi ne kara speed yayi sossai ya nufi kanta kaman ze bugeta da karfi ya taka birki gab da ita har motan na ta'bata ganin ko kallonshi batayi ba hannunta dafe da cikin idanunta na kallon gabanta.


Bindiganshi ya d'auka kan ya bud'e kofan ya fito "baiwar Allah" ya ambata ba tare da ya matsa kusa da ita ba, kallon kafafunta da suka wani irin suntuma yayi Allah kad'ai ya san iya tafiyar da ta sha da wannan kafan, a galabaice ta d'ago manyan idanunta ta kura mishi se ta juya ta fara tafiya kuma a hankali ta nufi kasurgumin dajin dake gabanta hankalinta kwance.


Har ya koma kaman yaja ya tafi yaga inaa baze iya ba kasancewar shi me tsananin tausayi, fitowa ya kuma yi ya nufeta zuciyarshi d'aya ya sa hannu ya rike hannunta, da sauri ta d'ago ta kalleshi tana zare ido tare da kokarin fisge hannunta sede rikon da ya mata ba da wasa ba, motanshi ya nufa da ita ya bud'e ya sanyata tare da zagayawa ya shiga, gangarawa yayi yayi parking dukda ya san hatsarin irin wannan tsayuwa Allah ya taimaka ma ba dajin tsakanin Abuja da kaduna bane sede na kaduna da Abujan ma ba wani tazaran banbanci, "baiwar Allah me ya fito dake cikin wannan tsohon daren da ciki haka?" Ba amsa se kallonshi da takeyi.


Jikinta ya kalla batayi kama da mahaukaciya ko almajira ba ya kuma cewa "bakya magana ne?" Nan ma Shiru dafe kanshi yayi yana kuma duban time, ganin call d'in matarshi masoyiyarshi yasa ya d'auka yana huro iskan da ya cika mishi baki, "Assalamu alaikum ya reef ya hanyan?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "lil hanya Alhamdulillah sede an d'an samu er matsala" rud'ewa tayi ta fara tambayar ko wani abin ne ya sameshi.


Yace "calm down lafiyata kalau, wata baiwar Allah na gamuda cikin dajin Allah ba gida gaba babu baya gata da tsohon ciki duk kafanta ya kumbura ga kayoyi ciki" salati ta d'auka cikin tausayawa tace "daga Ina ta ce maka take ya reef? I pity her" sanin halin matar tashi da tausayi yasa ya murmusa kad'an yace "taki magana lil da alamu bata magana, ban san yadda zanyi ba Lil gashi Ina running out of time, me shawararki?" Cikin kulawa tace "ka taho da ita kawai ya reef, In tayi magana daga baya ta fad'i inda take se a mayar da ita" cikin son tabbatarwa yace "do you really think this is right?" Tace "yes sure bcs we don't have any other option sbd we can't say from where she is kaduna or kano, am quit sure ka baro kaduna yanzu zaka fara shiga wuraren kano ba inda za'a kaita ba tare da tayi magana ba more over ga ciki, did she looks like Muslim?" Yace "eh, she's wearing a long hijab" Tace "Ohk just ka zo da ita I really pity her" yace "Ohk dr jiddah" dariya sukayi kan suka kashe wayan.


Jan motan yayi suka hau hanya karatun dake tashi kasa kasa ya karawa volume nan da nan bacci yayi awon gaba da ita gudunshi ya cigaba da shatatawa gab asuba suka kawo maiduguri, a gate aka dakatar dasu sede ganin wadda ke motan yasa suka daskare hannu kawai ya d'aga musu, aka bud'e mai ya shige ya barsu da gulman yadda yake rayuwarshi shi kad'ai dukda yana da yara escorts kenan dariya wani sojan yayi yace "dama ni aka sa kasanshi kun san wani lokacin gudu yakeyi ya 'bata musu shikenan sede su jishi wani garin?" Dariya duka sukayi imagining yadda ze gudu ya 'bacewa yaran nashi.


Suna isa GRA ana kiran assalatu har lokacin bata farka ba, horn ya danna a kofan tamfatsetsen gidan nashi da sauri me gadin ya leko ganin me gidan ya sa yayi saurin komawa ya wangale gate d'in kutsa motan yayi zuwa parking space yayi parking tare da kallonta a ranshi ya furta "tana da kyau" saurin kau da tunanin yayi ganin Jiddah sanye da kayan bacci ta d'aura hijab a kai idanunta sanye da farin medicated glass d'inta.


Side d'in shaati ta bud'e tana kallonta cikin tausayawa tace "welcome ya reef" yace "thank yhu, tasheta ku shiga ciki" hannunta ta d'an bubbuga a kasalance ta bud'e idanunta da suka rine ta kalleta murmushi ta sakar mata tace "sis you are home, muje ciki kiyi wanka ki huta se muje asibiti a duba mana lafiyan babynmu" ta karasa da murmushi da idanu kawai shaati ke kallonta kan ta sauka cikin natsuwanta kaman wacce take Lafiya garau hannunta jidda ta kama suka nufi ciki tana cewa "ya reef ruwan wanka na toilet d'inka" murmushi ya saki yana fitowa tare da rufe motan ya nufi cikin gidan yana d'agawa mai gadi hannu.


Kan ma ya shiga main parlorn sun haura site d'in jiddah stairs by his left ya nufa ya haura babban parlorn da ya ji kayan alatu komai royals yaci karo dashi d'akuna biyu ne a saman, na farko ya shige tare da fara cire kayan jikinshi sauri sauri ya fad'a wanka.


Ta 'bangaren Jidda kuwa direct d'akin bakinta ta kai ta duk gidan tsab tsab kaman ba asuba ba kaman anyi sharan Safe a hakan kuma gari baze gama wayewa ba za'a sake shara da mopping, toilet ta shiga ta had'a mata ruwan wanka ta fito da towel hannunta ta bata tace "ki cire kayan kije kiyi wanka na had'a miki ruwa" kallo kawai take binta dashi, tunani tayi ko de kurma ce? Da hannu ta mata alamun ta tu'be taje tayi wanka.


Kar'ban towel d'in tayi ta rike ganin tana ta miko mata, seda Jidda ta kama hannunta ta mike suka shiga toilet d'in tare bayanin yadda zatayi anfani da abubuwan toilet d'in tayi dukda batayi kama da bakauyiya ba, tun tuni Jidda ke nazarinta ga jan lalle hannunta gwanin kyau fatanta kuwa me yalki da sheki ne ba wani alamun tana cikin wahala, da ta cire mata hijab kuwa seda ta ja baya ganin abubuwa biyu, gashinta dake wanke baki sidik se kyalli yakeyi da kuma tsadadden kayan baccin da ta gani jikinta ta ta'ba gani a spain ance be shigo Nigeria ba ko lokacin ta so saya sede kud'ad'enta basu kai ba tsada ne dasu.


Fita tayi ta kyaleta tayi wankan, d'akinta ta koma cikin Abayoyinta ta za'ba mata wani italian gown kud'inshi ze yi 35k ta dawo d'akin zuwa lokacin ta fito wankan dae gashi ga kamanshi mai ta tayata shafawa kan ta tayata sanya kayan ta bata hijab "tashi kiyi sallah ga sallaya chan bari nima nayi Inzo" Mikewa tayi ta sa hijab d'in a mamakance Jidda ta bi ta da kallo ganin ta tada sallah cikin tsananin natsuwa.


***********


Da kyar mama tayi sallahn asuba jikinta zazza'bi rijib hajja na tare da ita, bayan Abba ya dawo daga sallahn asuba ya kira yaranshi gabad'aya har matan duk ya tambayesu ko shaati ta je duk kaman had'in baki amsan shine batazo ba se da suka kuma tambayanshi ko lafiya ake nemanta? Kai tsaye yake basu amsa ba 'boye 'boye duk kuma se hankulansu suka tashi.


Kan karfe 8 gidan cike da en uwanta duk sun zo sun saka maman a gaba gwanin tausayi an mata karin drip tana bacci yayinda Abba da ya mujeeb suka kuma fita yawon nemanta, duk sauran kuwa da suke ciki d'aya se jikinsu yayi sanyi yayinda sauran bappaninta biyu suke sha'aninsu hankali kwance yayinda karaminsu da matarshi ke sashen Abban.


Bayan sun gama yawon sun dawo lokacin Mama ta farka a galabaice tace "Abbansu yaran fah? Ka d'auko Ko da Arwa ne" mujeeb ne ya mike yace "bari inje In d'aukota zan gwada dukkansu In uban yaki kawai a kyale masa su" fita yayi Meenat ta mike ta bishi a tare suka nufi gidan Shaatin.


********


Yarinya kaman Arwa amma haka ta kusa kwana bata runtsa ba se bacci 'barawo da ya saceta, ana kiran asuba bayan saif ya fita Zuby ta mike ta nufi d'akin Shaati, da karfi ta bankad'a kofan ta shige toilet ta d'ibo ruwa tazo ta kwarawa Arwa da yasmin a firgice suka farka cikin razana abinda ba'a ta'ba musu ba, tsawa ta daka musu "ku dena kallon da kulu kulun idanunkun nan kaman na uwarku, maza gashi zuwa d'akina akwai kaya a laundry basket d'ina ki d'auka ki koma baya ki wanke min su tas ke kuma d'auki tsintsiya ki share gidan nan gabad'ayanshi".


Kwalalo idanu sukayi a rud'e jin uban aikin da ta saka su wadda basayi Arwa tayi karfin halin cewa "Anty makaranta fa zamu...." bata karasa ba zuby ta gwa'be bakinta "shegen ubanki kun tashi ko se nayi kasa kasa daku" Mikewa sukayi yasmin na mamakin Ina Maaminsu yayinda Arwa ta fara hawayen tausayin kansu, Arwa ta tattaro kayan wankin tayi baya yayinda Yasmin ta d'auki tsintsiya ta fara daga baya, tana kallon yayarta tace "Adda Ina maami?" Arwa tace a sanyaye "Paapa ya koreta jiya" kuka yasmin ta saka cikin kuka tace "Adda mu tafi muma dan Allah wallahi ko bazaki gane gidansu ba ni zan gane mu bi ta, nide bazan zauna Anty ta kasheni ba".


Aikin suka fara duk a galabaici ita Arwa kayan sun mata nauyi so ba wani iya yadda Zata yi tayi ba haka kayan ta kwaso manyan zannuwanta ta banka musu omo sossai ruwa kuma be haura ba sede ya jika omon Sannan ta zuba hypo ciki kusan rabin goran ta tuttula ciki, da kyar da kyar yayinda Yasmin sharanta yake fita rabi yayi kyau rabi be yi ba duk ta jiku da zufa da hawaye da majina.


Chan kuwa bayan gari yayi haske rana ya fito kar yasmin ta gama sharan wajen ta koma ciki tanayin na cikin, lokacin zuby ta fito ta nufi bayan Don ganin abinda Arwa ke yi waro idanu tayi ganin har yanzu ba'a shanya ko guda ba ko ta Ina hannunta ze kai se Allah, gaban baf d'in ta isa tana ci gaba da zaro idanu, hannunta ta saka ta d'aga wani holland d'inta da ta sayeshi kusan 80k sawanshi guda se gani tayi colour na gangara yayi wani fari fat ya 'bubbule wani kara ta saki tana d'auka Arwa da Mari ihu itama tayi batayi wata wata ba ta fara jibganta.


Ihu take amma Saif na d'aki a kwance ko a jikinshi, yayinda sameer da neeha suka farka suka fito yasmin tabiyo bayansu duk sukayi cirko cirko suna kuka suna kallon yadda take dukan Arwan daidai lokacin Ya meena da ya mujeeb suka shigo, zare idanu ya meena tayi ganin wani irin duka da Zuby ke yiwa Arwa dukda ba son yarinyar take ba, da wani irin gudu ta karasa ta fisgota tare da tsinka mata Mari hagu da dama da azama mujeeb ya rike meena yayinda zuby ta fara ihun se ta rama yayinda yaran suka koma bayan kawunsun.


Se fa lokacin Saif ya fito yana karewa su mujeeb kallo da gudu zuby tazo ta fad'a mishi tana kuka ya d'au mataki kan meena, kallon mujeeb yayi yace "me ya kawoku gidana ba na tura muku 'yarku ba? Me kuma?" Ya mujeeb da bashi da fad'a cewa yayi "yaran muka zo d'auka Sannan ba tura mana 'yarmu kayi ba Don ba haka addini ya tsara ko zakayi sakin kayi ba yanzu zancen da nake maka har yanzu Aisha ba'a san inda ta shiga ba duk inda muke tunanin taje bata nan polisawa suna aikin nema, ka gode Allah In aka sameta In kuwa ba'a ganta ba kayi kuka da kanka shariace zata rabamu".


Kallon yaran yayi yace "ku wuce mu tafi" tsalle zuby tayi ta dire tana kallon Saif "yarda zakayi a tafin maka da 'ya'yanka? Da su ta zo gidan?" Saif yace "ba inda zasuje In zaku tafi da ita 'yar gaba da fatihar ku tafi da ita Don bani da had'i da ita amma daga kan yasmin har neeha ba wadda zan baku" nan su kuma sukace se sun tafi dasu ganin rikici na shirin 'barkewa yasa mujeeb jan Arwa da meena suka nufi gate yayinda Arwa ta tirje bazata tafi ta bar kannenta a kashe mata su ba da kuka da ihu aka rabasu kaman zata shid'e har suka isa main house Arwa na kuka da ihu.


Haka a chan ma neeha se kuka take yayinda zuby ta korasu d'aki ta kuma tabbatar musu ta kara jin fyat d'in yaro se ta ci kaniyansu haka suka shige suna kuka zat tausayi.


Mujeeb na ajiyesu yace "meena ku shiga zanje court" dayake shi barrister ne me ji da tashe da zamani, nan da nan ya shigar da kara a take aka turawa Saif sammaci.

Hmmmm yanzu fah aka fara.                    🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇

   *Baya chanza d'and'anon teku*


      *Fatima Muhammad Gurin*

    **Gureenjo6763 on Wattpad**


            'Yar Mutan Adamawa


*Ga page d'inku na jiya idan naga gamssasun comments ku samu na yau anjima idan kuwa ban gani ba to fa se gobe in Allah ya kaimu.*

     *P21*


Da sassarfa yake gangarowa idanunshi na kan wristwatch d'in hannunshi he's almost late hakan ya sa ko ta kan dining area be kalla ba ya nufi waje se jin maganan jiddah yayi "ya reef har zaka tafi baka karya ba?" Juyowa yayi yana kallon stairs d'inta rike take da first aid box, ta chanza kaya zuwa doguwar riga ja ta nad'e gyalen kanta, ajiyar zuciya ya sauke yace "I'm almost late lil meeting d'in ba wani dogon time ze ci ba In na dawo se in yi breakfast d'in".


Murmushi tayi tace "Ohk Allah ya bada sa'a baka tambayi patient ba" dafe goshi yayi yace "oh lil kina kara wasting min time Allah, toh how's she?" Ganin ta kwa'be fuska, tace "nayi treating kafafunta she's sleeping, b....." katseta yayi "karki kawo maganan ganin zaheeda, bye se na dawo" tana dariya tace "Allah ya tsare ya kiyayemin kai hubby a dawo lafiya" ya juya ya fice yana amsawa.+


Aiko yana fita se ga zaheedan da yake wa gudu "Ammy where's Abbiey? Ammy Ina kince yau ze dawo? Oh is he really back be neme ni ba? I most be mad at him, Ammy are you not going to office today?" Dafe kai Jidda tayi a zuciyarta tace shiyasa Abbiey yaki nemanki ai mutum se surutun tsiya, kallonta tayi tace "zaheeda pls run downstairs driver is waiting for you, you don't have to be late Ohk?" Gyad'a kai tayi tana gangarawa Da gudu murmushi jidda tayi kan ta wuce d'akinta ta ajiye first Aid d'in ta dawo d'akin da ta sauke shaati ta fara gadi don kar ta farka tana jin yunwa ita kuma bata kusa.


**********


"Mene?" Abba ya tambaya yana mikewa tsaye "meyasa zaka kaishi kara uhm? Ka bari a bi komai a hankali mana, maza koma ka janye karan nan zanyi magana da wakilinshi idan abin ya gagara se a kai court d'in, ku yaran yanzu kunfi so ayi rabuwar rashin mutunci bayan kuma 'ya'ya sun had'a" fad'a yayi tayi kan ya kashe wayan ya kira bappanshi wadda shi ya wakilci auren.


Seda ya kusa tsinkewa kan ya d'aga suka gaisa a mutunce ya mishi bayanin abinda ke faruwa, salati ya d'auka cikin jimami yace "Alhaji kayi hakuri dan Allah, bari inyi magana da mahaifiyarshi I will get back to you" Abba yace "Toh ba damuwa" ya kashe wayan yana kallon Arwa da har yanzu take kuka lallashin duniyan nan taki hakura itade kannenta ko Maaminta seda ta zo nan ta fahimci Maamin ma 'bata tayi ana kan nemanta.


**********


Yakumbo zaune suna shan hiransu da innani Don matsalan Saif d'innan ya had'e kansu yanzu duk wani tijara da take mata da yanzu babu, wayanta taji yana neman agaji da sauri ta janyo tana d'agawa, gaisawa sukayi da bappa kan cikin tarradaddi ya bata labarin abinda Abba ya fad'a mishi yanzu, salati ta d'auka tana mikewa tsaye, se kuka "me zanji haka? Me yaron nan yake son zama ne? Yanzu ta Ina zamu fara neman er mutane ga tsohon ciki jikinta fi sabilillahi?", bappa yace "su cewa ma sukayi ita kam zasu cigaba da nemanta amma yaran ki kar'besu sbd......" nan ya bata labarin abinda su meena suka je suka samu ake ma yaran suka d'auki arwa saif ya hana su d'aukan saura har babban yayanta ma ya kaishi court amma uban ya sa ya janye se idan mu bamu d'auki wani mataki ba.


Yakumbo tace "bari inje nima ai bazan barwa wanchar mayyar jikokina ta kashe min su ba, amma wallahi babu ni babu saifullahi" tayi maganan cikin kuka sossai tausayin Shaati na rufeta, baiwar Allah ko wani hali take ciki? Allah masani, bappa yace "karkije ki jirani gani nan zuwa idan yaso se muje tare" Ta amsa mishi tana kashe wayan, sulaiman da ya shigo tana wayan ne ya fara tambayar Abinda yake faruwa da shaati, nan yakumbo ta musu bayani.


Cikin jimami innani ta fara hawayen tausayin shaati, sulaiman kuwa har jikinshi 'bari yake tsabar yadda ranshi ke kuna, me shaati tayiwa ya Saif da ta chanchanci wannan irin hukunci haka? Ya Allah ya jefaki hannu na gari shaati, Allah ubangiji ya kareki dake da abinda ke cikinki, Allah ya bayyana mana ke cikin lokaci kankani, suna nan zaune har bappa ya karaso duk Mikewa sukayi suka shige motanshi har sulaiman direct sukayi gidan Saif.


Inna da zuby sun fito kenan su yakumbo na isowa, ko kallon inda suke batayi ba bare ta nuna ta sansu iyayen mijinta ne, suka tari napep suka wuce ta san ba yadda suka iya da Saif don mayar da shaati ko ana ha maza ha mata bazata dawo wannan gida ba Don ya fi karfinta har Abada, sede fa bata san takamamman outcome na asirin da ta barbad'a bakin kofa ba, ta'be baki tayi a zuciyarta tace "ko ma menene chan ta matse musu".


Su yakumbo na shiga yasmin dake mopping parlor tazo ta gudu ta rungume uncle sulaiman tana kuka, a safiyar yau kad'ai har yarinyar ta fad'a, yakumbo ta dafa kanta itama tana hawaye innani ne tace "Ina kannenki?" Cikin kuka tace "Anty ta rufesu da key a d'akin maami Bayan ta doki neeha wai ta isheta da kuka, yakumbo ku bud'eta tun Ina jin kukanta yanzu banaji ban san me ya sameta ba".


Hawaye yakumbo ta share tana zama bappa ma ya zauna yacewa yasmin "je ki kiramin Babanku" girgiza kai tayi tana kuma 'buya bayan sulaiman tace "dukana ze yi bappa yace kar mu kuma zuwa inda yake" girgiza kai bappa yayi yana danna kiran saif d'in a wayanshi, seda ya kusa tsinkewa kan ya d'aga bappa yace "sameni parlorn gidanka" kan ya kashe wayan.


Chan se ga Saif ya fito sanye da kananun kaya, kaman ba Saif d'in da d'an wanka da gayu ba yanzu iyakaci yayi wanka ya saka kaya yayi duhu sossai Sannan ya rame ya kuma tara kasumba, kaman ba shine me 'batawa kanshi kud'i da lokaci akan gashin kanshi da kyakyawar kasumbarshi zuwa gemunshi ba, zama yayi yana kallonsu, cikin jam'i yace "Ina kwananmu" ba wadda ya amsa se yakumbo da tace "Saifullahi ka kyauta, kayi abun arziki sede ka jira sakamakonka tabbas hakkin wannan baiwar Allahn Aisha da abinda ke cikinta baze barka ba se Allah ya saka mata".


Cikin hasala yace "meyasa ne kowa laifina kawai yake gani? Ya zata kama yarinyar mutane ta daketa har tayi 'bari don na d'auki mataki ayi ta cewa hakkinta se ya kamani? Ni kuma hakkin d'ana da ta zubar fah? Hakkin cin amanata da kanina fah?" Duk zaro ido sukayi yayinda sulaiman ya runtse idanunshi ji yake kaman ya tashi ya rufe yayanshin da dukan mutuwa tsabar takaici, bappa yace "ban gane cin amananka da kaninka ba?" Nan ya musu bayanin zargin da yakeyi da shedodin da zuby ta nuna mai, har da hoton Shaati da sulaiman kwance jikin juna ya d'auko ya watsa musu.


Innani girgiza kai kawai takeyi a fili tace "wannan ba Aisha bace wallahi, ko na yarda sulaiman ze aikata zina wallahi wallahi bazan ta'ba yarda Aisha zata aikata ba, Saifullah gwara ka dawo cikin hankalinka ka natsu kasan me kakeyi tun kan lokaci ya kuremaka" bappa yace "sulaiman me nake ji haka?" Yace "wallahi wallahi bappa zan iya rantsuwa da Alqur'ani me girma ban ta'ba ta'ba ko da hannun Aisha ba bare har ya kai ga wannan mummunan aikin, duk sharri ne irin na kafirar matarshi marar tsoron Allah".


A harzuke Saif yace "karka kuma zagarmin mata sulaiman" shima a harzuke yace "an zagetan ya Saif kuma ko yanzu zan kuma......." da sauri innani ta kama hannunshi wadda hakan ya sakashi Shiru se hawaye yanzu zuwa don taimaka mata debe kewa ma abinda ya ja mishi kenan, yakumbo tace "mu ba takkwalaye bane irinka saifullah kaje ka d'auko min neeha da sameer ka kuma kwaso min kayansu zan tafi dasu In ka ga dama ku tafi har bangon duniya da kai da matar son taka, amma tabbas babu ni babu kai in kuwa Aisha ta salwanta sanadinka wallahi Allah se na tsine maka albarka duk abinda ya sameka daidai da kai ne".


Mikewa yayi zuciyarshi na tafasa yaje ya bud'e d'akin Shaatin, kwance ya gansu a manne da juna tsawa ya daka musu wadda ya sa sameer mikewa yana kare neeha da tayi kuka har ta galabaita zazza'bi rigib a jikinta, cikin ko In kula yace "kamata ku wuce ku barmin gida kuma munafukai masu kama da uwarsu" Mikewa sameer yayi ya kama neeha gwanin tausayi suka fito ciki ya shiga ya kwaso kayansu a trolley ya fito ya ajiye ma su yakumbo yana kallonsu yadda innani ta d'auki neeha a jikinta tana hawaye gwanin tausayi.


Mikewa sukayi sulaiman da bappa suka d'auki kayansu zuwa mota yakumbo ta rike sameer suka fice daga gidan, suna shiga mota bappa ya kira Abba, "kayi hakuri Alhaji Saifullahi yayi nisan da bai jin kira Allah ne kawai yanzu muka barwa al'amuranshi sede mun d'auki yaran zasu zauna hannun mahaifiyarshi" Ajiyar zuciya Abba ya sauke da farko ya zata yaran ma Saif ya hana a d'aukesu ne, yace "ba matsala hakan ma Ai Alhamdulillah tunda ba'a kai ruwa rana kan ya yarda a kwashe Yaran ba, muna kan neman Aisha In Allah yayi mun ganta to In kuma bamu ganta ba zamu ci gaba da mata adu'a Allah yasa tana hannu na gari" bappa yace "Ameen ya rabbi" sukayi sallama.


Nan ya tada mota suka koma gidan yakumbo bayan sun biya chemist an duba neeha an mata allura an kuma bata magani, girki yakumbo tayi musu yayinda innani ta musu wanka suka tasa su a gaba suka ci abinci suka koshi kan ta kaisu d'akinta suka kwanta nan da nan bacci ya kwashesu cikin sauke ajiyar zuciya a kwana guda kenan da babu mahaifiyarku wannan da kun zauna da ita kam kan wata ya zagayo da sede In tattaro gawarwakinku Cewar yakumbo tana kallon yaran.


***********


Shaati bata farka ba se wuraren 1 a lokacin har Shareef ya dawo ya ci abinci ya d'an kwanta Don ya huta ya kuma yi d'an baccin da be samu jiya ba bayan yayi azahar, yayinda jidda ta janyo zaheeda da ta isheshi da surutu suka dawo d'akin shaatin tana d'an wani aiki a system yayinda zaheeda ta addabeta da surutun waye wannan? Laaa babyne a cikinta, Ammy a kasuwa ta sayo? Ammy kema ki sayo mana plss, Ammy kaza Ammy kaza.


Chan tace "Ammy Anty ta bud'e ido" jidda ta d'auka karya zaheeda keyi seda taji motsin shaati kan ta juyo da gaske ne kuwa ta bud'e ido ta kurawa zaheeda da bata wuce sa'ar neeha ba ido, In ta girmeta ma to da wattani ne don neeha har tayi 4, jidda tace "kin farka?" Kallonta kawai shaati tayi to her biggest surprise se taga ta gyad'a mata kai, da Sauri jidda tace "dama kina magana?" Nan ma kai kawai shaati ta gyad'a mata, jidda ta kuma cewa "zaki iya yi?" Ta girgiza kai.


Zaheeda tace "Anty pls talk I want to hear your voice" d'an karamin murmushi tayi jidda ta daka tsalle cikin murna tace "Alhamdulillah sunana jidda, sunan 'yata zaheeda mijina da ya samoki kuwa sunanshi shareef, ke fa ya sunanki?" Mamakin surutun jidda shaati keyi, se kuma ta fara tunanin ya ma sunanta? Chan se ta tuna abinda kwakwalwanta ke tuna mata abu biyu ne kachal duk yadda ta matsa don tuna ko da sunan mahaifinta ko mahaifiyarta ne ta manta, daga sunanta se yaranta da sunayensu abubuwan dake kwakwalwanta kenan bazat iya tuna sunan mijinta ko garin da ta fito ba, Sannan duk yadda tayi don bakinta ya bud'e tayi magana ta gagara harshenta yaki motsawa sam jinshi take a cike tab a bakinta.


Jidda tace "ko bazaki iya fad'a ba?" Kai shaati ta gyad'a jidda tace "to zan dinga kiran sunaye In kinji naki ki dakatar dani kinji? Bari muga da wani suna kika dace" murmushi kad'an shaati tayi tana jin son jidda a ranta matar sam bata da damuwa faram faram da ita, girgiza kai shaati tayi don kila ta sha wahala se kawai tayi mata alamar ta kawo mata biro da takarda, jidda tace "yess kinga na manta, tunanin hakan be zo min ba dama bakiyi kama da jahilai ba" inda take aiki yanzu ta koma ta samo pen da memo ta kawo mata.


Kar'ba tayi ta fara rubutu kusan mintuna kan ta mikama jiddah zaheeda se leke take kaman ta iya karatu, "sunana Aisha ina da 'ya'ya hud'u Arwa(khadija), yasmin (Aisha) sameer and Neeha (fatima) bayan su bazan iya tuna komai akan rayuwata ba" kallonta jidda tayi cikin tausayawa kan tace "bari In kawo miki abinci kici na tabbatar kina jin yunwa, ki kwantar da hankalinki a sannu zaki tuna komai na rayuwarki kuma bakinki ze bud'e" kai shaati ta gyad'a cikin gamsuwa, zaheeda tace "Anty what did you wrote to Ammi?" Jidda ta kama hannunta suka nufi waje tana cewa "she said she has a beautiful neeha just exactly like you" zaheeda tace "laaaa Ammi I want her to be my friend where is she? Beautiful Neeha come to your friend Beautiful zaheeda" dariya Jidda ta saki yayinda shaati ma daga d'aki take murmushi yarinyar akwai shiga rai da surutun tsiya.


**********


"Baba hauka fa kace?" Yace "shine kad'ai ze d'anyi tasiri a jikinta shi d'inma ban tabbatar ba tana tare da Allah ko yaushe adu'o'inta ba masu fad'uwa bane, yanzu d'inma bata haukace ba sede kwakwalwanta ya shafe abu kad'an take tunawa, zanyi iya kokarina inga bata tuna komai ba tacigaba da zama a haka don karyewar asirin nan shine randa aka tone wanchan layan kabarin".


Ajiyar zuciya zuby ta sauke tace "Allah ya sa ta fad'a hannun waenda zasu azabtar da ita da azaba mafi muni, na tsaneta wallahi mutum kaman maye komai akayi se ta tsallake?" Baba yace "hmmm ai da wadda baya tare da Allah ne aka yiwa wannan aiki yadda muka ci nasaran nan da sede a tsinceshi tsirara tsakiyar bola yana hauka tuburan, itama zamu san abunda muka kara mata...."
                    🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇

  *Baya Chanza d'and'anon teku*


     *Fatima Muhammad Gurin*

   **Gureenjo6763 on Wattpad**


           'Yar Mutan Adamawa


     *P22*


Abinci ta kawo mata pepper soup na kan sa da bread se kayan tea, da ruwan zafi da kanta ta jere mata su ta had'a mata tea ta mika mata a zaune haka ta ci abincin akan gado, tana yaba mutuncin jidda yanzu duk girman gidan nan bata da girman kan neman me aiki tazo tayi ta mata komai da komai, minti minti take sake murmushi In taga yadda jidda da zaheedan suka zuba tagumi suna kallonta ko er tari tayi za'ayi saurin tambayarta, a haka ta gama breakfast d'in.


"In baki koshi ba an kusa gama abincin rana se a zubo miki" Kai ta girgiza tana shafa cikinta alamun ta koshi, Tray d'in ta d'auka ta fice, yayinda zaheeda ta bud'e babin surutu dukda ba amsa mata shaati ke yi ba se murmushi, a bangaren jidda kuwa Bayan ta mayar da trays d'in kitchen ta nufi d'akinshi ta duba har yanzu be tashi ba kila se asr, komawa d'akin ta tayi ta za'bowa shaati wasu kayan bubu atampha da gyale Don jikinsu ze yi d'aya da shaatin In ma Shaatin zata nuna mata wani abu se hips, d'akin shaati tayi ta ajiye mata kayan tana cewa "Aunty Aisha kiyi wanka ki sanya se muje asibiti In duba lafiyan babynmu kar a shiga hakkinshi".+


Memo da biro da jidda ta ajiye gefen gadonta ta d'auko tayi rubutu ta mikawa jidda "ki taimaka pls dama duk banji motsinshi ba" waro ido jidda tayi tace "shine kikayi shiru? Maza tashi kiyi wanka mu tafi Allah dae ya sa lafiya har kika ci abinci be motsa ba?" Gyad'a kai shaati tayi tana Mikewa da dabara don kafanta dake tsananin ciwo wanka tayi ta sanya kayan ya kuwa zauna mata gwanin kyau ta yafa gyalen Bayan ta d'aura d'an kwali.


Ta samu wuri ta zauna tana jiran jidda chan se gata sanye da Italian gown coffee color tayi wrapping gyalen ta makala pin hannunta rike da wata moshiano toy brown bag, kafanta sanye da snickers black, farin glass sanye a idanunta "muje ko na gama" Mikewa shaati tayi suka fito zuwa kasa inda anan taga zaheeda na kallon cartoon a Nickledion neeha ce ta fad'o mata rai tuna yadda suke fad'a da sauran yayyunta akan tashan.


To Ina ta baro 'ya'yan nata tunda bata manta Sunansu ba? Tambayar da tayiwa kanta kenan wadda ta rasa amsa, "taso muje In saukeki gidan yaaya don na barki nan kya iya hana Abieynki bacci" Mikewa tayi da tsallenta suka fito wata Elantra blue ta janyo suka shige, fitansu kan kwaltan da ya kasance shiruu se polisawa da sojoji da zaka dinga hange gida na d'aya na biyu na uku by there left tayi parking tace "oya bye bye" sauka zaheeda tayi tana d'aga musu hannu da gudu ta karasa tayi knocking seda suka ga shiganta kan jidda taja tana cewa shaati "gidan iyayena kenan mahaifinshi wa ne ga mahaifiyata".


Kinga nan ta nuna mata gida na hud'u by right "nan ne gidanmu" murmushi shaati tayi tana gyad'a kai, nuna garin tayi ta juya hannunta jidda tace "wai nan wani gari ne?" Gyad'a kai shaati tayi jidda Tace "borno kenan" murmushi shaati tayi haka jidda taci gaba da mata bayani duk inda zasu wuce ita dae sede ta murmusa ba laifi bane don zaheeda na surutu ga inda ta gado ko shi Shareef d'in na da wannan surutun? Ta tambayi kanta a haka suka karasa asibiti.


Duk inda zasu wuce se anyiwa jidda magana tsabar yawan mutanenta kuma ko yaya se tayi surutu harda masu jinyar patients, nurses da colleagues d'inta doctors kowa dr jiddah, a haka suka karasa office d'inta kwanciya tasa shaati tayi ta mata scanning cikin taka tsantsan anan ta gano yaron be da lafiya, da kyar yake motsi kad'an wadda ba lallai har uwar taji ba, paper ta samu tayi rubuce rubucenta kan suka fito.


Daga asibitin chemist babba sukaje ta shiga ta sayo magunguna daga nan suka wuce wani katon mall, gowns tayi ta jidarwa shaati masu tsada, ta sayi atamphopi kala biyar laces biyar shadda uku kampala biyu, ta sayin gyalulluka, ta saya mata takalma da jaka kaya kam kaman ba gobe garda en kunnaye da sarkoki, man shafawa da gel na wanka su shampoo da turaruka, itade shaati binta kawai take a baya tana kallon ikon Allah.


Bayan sun gama ta bada card d'inta aka cire kud'in aka tattara musu kayan zuwa mota kan suka nufi gida, basu d'auki zaheeda ba se gidan major da suka shige, masu aikinta ta kira tace su kai mata kayan nan d'akin bakin side d'inta pls, tattara sukayi suka shige dashi, suna kokarin shiga shareef na fitowa yana saka bottons na hannun riganshi da alamun alwala yayi.


Dukda baki ne amma kyakyawane, daga ka ganshi zaka san babarbarene sede fah bashi da irin zanensu sanna fatanshi chocolate color ne a murje alamun kud'i da hutu yayinda jidda take fara sossai kuma ta fishi kyau a xuciyar shaati cewa tayi "kila ita ta had'a jini da shuwa Arab tunda duk wadda ya san borno ya san yawancin barebare suna auren shuwa" jidda tace "ya reef ba de wani wurin zaka ba" yace "nop massallaci zanje madam" Tace "Ohk se ka dawo" kallon shaati yayi ya d'aga mata hannu yayi wucewarshi.


Ciki suka shiga seda sukayi sallah kan masu aiki suka shigo suka fara shirya mata kayan cikin wardrobe d'in d'akin, shaati a zuciyarta take mamakin alkhairin jidda tabbas macece ita me karamci wacce ta tashi gidan karamci yanzu a wannan marrar wace macece zata ganki da mijinta bata san ko cikin jikinta na waye ne ba, ta iya bata wannan kulan? Harda kashe mata wannan uban kud'in kuma ba mijinta bane ya bayar?.


A parlorn Shareef kuwa jidda ce rike da papern shaati ta mika mishi "kaga abinda rubuta" kar'ba yayi ya karanta yayi Shiru cikin nazari nan ta bashi labarin rashin lafiyan babyn cikinta amma ta dubata ta sayo magunguna, cikin nazari yace "lil me kike ganin ze rabata da 'ya'yanta da gidanta tunda dai baza'ace karuwa bace tunda har ta haifi 'ya'ya hud'u?" Jidda tace "kuma ba hatsari ba ba komai ba, ni Ina ganin asiri ne" kallonta yayi da sauri tace "to in ba shi ba me ze gogewa mutum kwakwalwa haka farat d'aya ka manta komai kuma ka dena magana ba accident ba ba komai ba" ajiyar zuciya ya sauke yace "zanyiwa baba bayaninta da abinda kike gani shi watakila ya gane menene" dayake babanshi Muhammad babagana babban malami ne sossai sananne.


Mikewa yayi yace "bari In shiga mu gaisa mun had'u masallaci amma gaisuwan chan be yi ba" Tace "to baka jin yunwa?" Yace "nop inci abinci 12 yanzu inji yunwa? Se dare pls ki min abu me ruwa ruwa da kanki" Tace "yes sir!!" Tana kamewa dariya yayi yana kallonta, chan yace "nayi kewarki sossai lil d'ina" murmushi ta saki tace "ko de kace kayi kewan surutunmu da zaheeda" yace "kusan haka sarakan surutu ba na rasa ya akayi soja kamana na auri aku kuturu" bubbuga kafa ta fara a shagwa'be dariya ya saki yana shirin fita yace "Yauwa pls zan tura miki kud'i se ki saya mata duk abunda zata bukata".


Tace "kajimin wayau se ka cinye ladan kai kad'ai? To na saya mata komai" yace "toh nawa kika kashe?" Tace "bana bukata fah Don Allah nayi" ya kafe se ya sani ganin taki fad'a yasa ya nufi wayanta da gudu ta karasa ta d'auka tana 'Boyewa nan ya bi ta ya danne seda ya kwace wayan ya duba kud'in kan ya fice yana mata gwalo, murmushi ta saki tana Mikewa ta biyo Bayan shi.


D'akin shaati taje ta samu tana sallah se kawai ta sauko zuwa kitchen ta fara aikin abincin dare don ta san in 8 yayi baze ci abincin ba kuma se gobe.


Zaune a gaban babanshi dottijon arziki muhammadu baba gana Bayan sun gama gaisuwa yake bashi labarin shaati tas ya kwashe komai ya fad'amishi, baban yace "subhanallah Allah ya bata lafiya shine baka kawo ta nan ba ka d'aurawa hauwa wahalan?" Yace "baba na shigo cikin dare ne yasa kuma ita jiddance ta so ta zauna da ita" yace "Toh shikenan ko zuwa dare se jiddan ta rakota se na ganta zan iya tantancewa".


Godiya yayi kan ya mike yana cewa bari ya karasa ciki, side d'in Mamanshi da ta kasance uwargida ya fara shiga kamansu sak kaman an tsaga kara a kasa ya zauna tare da d'aura kanshi kan kafanta yace "hajja barka da gida" Tace "Yauwa babana an dawo lafiya?" Yace "Alhamdulillah ya muka sameku" ta amsa nan itama ya bata labarin shaati don baya 'boyewa iyayenshi komai itama mitan rashin kawota wurinta tayi har ta d'aura da "da bata d'ebe min kewa ba Ina zaune ni kad'ai se masu aiki" murmushi ya saki yana fad'a mata sak abinda ya fad'awa baba, sun d'an jima suna tattauna matsalanta kan sukayi na wurin aikinshi daga nan ya mike ya nufi side d'in kishiyarta Ya kyallu, gaisawa sukayi ta tambayeshi aiki yace alhamdulillah daga nan ya tambayi kannenshi mata biyu ta 'bangarenta tace suna makaranta dayake shi shi kad'ai ne wurin mamanshi kuma shi kad'ai ne d'a namiji gidan.


Bayan ya fito ya shiga gidan goggonshi kuma aminin mahaifinshi iyayen jidda kenan, yara ne cike da gidan dayake su gidan yara ne duk jikokin nan ake turosu murmushi yayi ganin zaheeda dama seda Hajja ta fad'a kila ta gudu gidan YaYa wato mahaifiyar jidda don sunfi yara chan, da gudu suka taho suka rungumeshi d'aya bayan d'aya ya d'agasu ya rungume kan ya karasa suka gaisa da iyayen jidda a tare ya samesu se kawai ya basu labarin shaati suma kuwa sun mata jimami kan sukace suma ta shigo musu In ta zo wurin baba.


Daga nan masallaci sukayi sbd magrib da aka kira Bayan an idar ya koma gidanshi, a parlorn yaga jidda sanye da Jean da tshirt tana saka turaren wuta dukda gidan ya d'auki kamshi matuka amma bata dena ba, rungumeshi tayi tana mishi sannu da zuwa Daga nan tayi dining dashi tare da serving d'inshi zama yayi sukaci abincin take tambayarshi zaheeda yace tana gidan Abba wato babanta, bayan sun gama ci yake fad'a mata abinda baba yace tace se sunyi isha zasu shiga in shaa Allah.


Itama shaati abincin take ci a lokacin bayan sunyi sallahn isha Jidda ta d'auki After dress ta d'aura kan riga da wandon tare da wrapping gyale, yayinda shaati ta d'aura hijab da tayi sallah kan cotton doguwar riganta me karamin hannu suka fito suna isa daidai parlon baba zasu shiga kenan se shaati ta tsaya chak taki motsi, ba yadda jidda batayi da ita ba su shiga taki shiga se rawa da jikinta keyi gashi tana tsoron ta shiga kiranshi shaati ta fice Don fita kawai take so tayi daga gidan yayinda ba hali ta kwala mishi kira tunda ba tarbiyarsu ba kenan.


Haka ta biyewa shaati suka fito se Sannan ta fara sauke wasu ajiyar zuciya a jere a jere, gidansu jidda suka shiga yaran wasu har sun kwanta sbd gajiyan wasa yayinda zaheeda tazo da gudu "Anty kema kinzo muyi wasa?" Yake tambayar shaati girgiza kai tayi zaheeda tace "kin zo gaisheda Abba da YaYa?" Kai ta gyad'a ciki suka shiga dayake mahaifiyar su jidda ita kad'aice nan parlorn Abba suka sameta suka zauna kasa jidda ta gaishesu yayinda shaati ta dukar da kanta kasa kawai tana bawa kanta amsar tambayar d'azu tabbas jidda mahafinta ta d'auko kana ganin shi kaga ruwa biyu, su suka mata sannu ta gyad'a kai cikin natsuwa da ya kasance jininta, sun d'an ta'ba hira kan suka fito jidda bata fad'amusu abinda ya faru ba dukda tayi niyya sede kaman an rufe mata baki ruff.


Da zaheeda suka koma gida, bayan shaati ta koma d'akin da ta sauka zaheeda ta matsa da ita zata kwana haka jidda ta sa mata kayan bacci ta turata suka kwanta seda ta tabbatar sun kwanta ta kashe musu wuta ta kashe na side d'in kan ta nufi d'akin mijinta seda ta shiga ta tu'be hijabinta wasu fitinannun kayan baccine jikinta yana zaune sanye da cotton kayan bacci yana aiki a system se matsar da system d'in yayi ba tare da ya kashe ba yana me mika mata hannu a yangance ta karasa tana me zama jikinshi ya jefo mata tambayar "ya kukayi da baba Habibty?" Nan ta fad'a mishi abinda ya faru Shiru yayi tare da shiga tsantsan mamaki.


In zama da baba ya mishi wani anfani kenan bakin aljani aka mata asiri dashi wadda ya hanata magana ya kuma goge mata kwakwalwa sannan ya hanata shiga wurin baba, kenan se baba ya zo gidan da kanshi a bazata ba tare da saninta ba? Shiru yayi cikin nazari chan dae ya murmusa komai a sannu ake bi zata samu Lafiya ciwo ne ke shiga farat d'aya lafiya se a hankali.                    🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇

   *Baya Chanza d'and'anon teku*


       *Fatima Muhammad Gurin*

    **Gureenjo6763 on wattpad**


          'Yar Mutan Adamawa


    *P23*


"Mama dan Allah ki kwantar da hankalinki ki dena d'aga hankalinki tunda Shaati ta 'bace yau sati guda kenan kinki kwantar da hankalinki bare lafiya ta samu, ita kanta Shaatin bazata so ta dawo ta ganki a wannan hali ba" fadila ke wannan maganan a yayinda yaran suka zagayeta kwance a gadon asibiti Don ciwon yafi karfin gida.


A wahale Mama tace "taya 'yata zata 'bata da ciki ni uwa in kwanta inyi bacci hankali kwance a wannan zamanin na san wani irin hannu take? Sannan me laifinta? Hakuri? Juriya? Ko kuma karfin kaddara da ta fi ku? Ciwon nan ya jima yana damuna sbd hankalina be ta'ba kwanciya ba tun bayan abinda ya sameta, sbd kun d'auki karan tsana kun d'aura mata bayan kokarin da takeyi wurin gani ta koma normal rayuwanta amma hakan ya gagara gareku, kwarai da gaske nayi mamaki sbd ba haka na tashe ku ba, ban gina gidana kaman gidan kafurai ba akwai so, shakuwa da tausayin juna tsakaninku me yasa kuka mata haka? Me yasa kuka banzartar da rayuwanta? Ku tayiwa laifi ko mahaliccinta? Kun ta'ba zama kunce Aisha bamu labarin abunda ya faru tunda tace Isma'il ne kuka karyatata kuka watse......" kuka ne ya ci karfin mama dama damuwan na nan dankare a zuciyarta yanzu ne yake fitowa a hankali.+


Duk Shiru sukayi cikin damuwa tabbas In Aisha bata kashe mahaifiyarsu ba abinda suka jima sunayi ba tare da sun san yana damunta sossai ba ze kasheta hameed da yafi kowa d'aukan zafi shide har yanzu be ga aibin abinda yayi ma shaati ba tunda ita ta ja komai, yayinda fadila da meena duk jikinsu yayi sanyi suka fara da na sani majeed kam runtse idanu yayi cikin wasi wasi har ranshi yana kewar kanwartashi dukda sun fi shakuwa da hameed amma ita me sonsu ce tsakani da Allah.


Mujeeb da dama shi be ta'ba tsanan kanwar tashi ba yace "Mama menene takamanmman labarin ne da baku fad'awa kowa ba daga ke har Abba?" Shiru Mama tayi kan tiryan tiryan ta fara basu labarin abinda ya faru da shedar shaati kan ta gama fadila da meena kuka sha'be sha'be yayinda mujeeb da majeed idanunsu suka kad'a suka jajir hameed kam ya rasa me ze d'auka karyace ko gaskiyace shaati ta fad'awa iyayensu dukda shine best friend d'inta kan lalacewan komai.


Sun jima cikin jimami kan Fadeelah Tace "Aisha pls ki yafeni, ban kasance sister da zata yi supporting d'inki a komai da komai ba, hakan nan ban zame miki kafad'a da zaki yi kukan duk wani damuwanki ba se na zama ni ce me saki kukan ni ce nafi kowa uzzura miki a mafi munin lokutan rayuwarki ina ma ina ma, khaih kaicona Allah ubangiji ya bayyanaki karki mutu baki yafemana ba Aisha" ta karasa da kuka sossai, meena ma Hawayenta ta share tace "Mama dan Allah kiyi hakuri zamu gyara In Shaa Allahu kiyi fighting situation d'innan mama sbd ki sake ganin had'in kanmu a rayuwa".


Majeed yace "sorry mamah we are really sorry for letting you all alone in this situation me makon mu tausaya muku se mukayi adding salt into it pls find a place in your heart to forgive us" hameed da har yanzu zuciyarshi be gama aminta ba yace "we are sorry" mujeeb yace "Mama I promise you in har Ismail makes Aisha suffer and go through this hardness all alone court ce zata rabamu I will definitely act as eldest son of this family ki yafe musu ki sa Mana albarka".


Ajiyar zuciya ta sauke tana share fuskan ta tace "Allah yayi muku albarka ya bayyanamin er uwarku, Allah ubangiji ya yafe mana gabad'aya" suka amsa da Ameen. Abba da ya d'an jima jikin kofan ya karaso yana amsawa da "Ameen" shima, Mama ta dubeshi ta tabbatar shima kokari yakeyi amma yana jinya a tsaye cikin sanyi tace "akwai wani labarine?" Yace "babu, sede commissioner of police yace he will put all his effort wurin ganin an bincikota da yardar Allah" wayan Abba ne ya fara kara dubawa yayi se yaga abokinshi malam sulaiman d'agawa yayi suka gaisa inda yake tambayanshi situation na Aisha yanzu.


Murmushin takaici yayi kan yace "ta 'bace malam" "subhanallah garin yaya?" Malam sulaiman ya tambaya nan Abba ya bashi labari da irin wahalan da ta sha kan 'bacewar tan, malam sulaiman yace "tabbas Aikin asiri ne, zamu dage mata Daga nan ku kwantar da hankalinku Allah muka rike kuma shi ze kawo mana d'auki" magana sossai sukayi kan sukayi sallama.


**********


Ta 'bangaren Arwa zuwa yanzu ta gama fahimtar duk wani abinda ke faruwa kasancewarta me hazaka da wayau, ta san ita ba d'iyar saif bace papa d'insu sede ta rasa ita waye mahaifinta, sanna ta san mahaifiyarsu 'bacewa tayi a ranar haka ta kwana kuka wadda ba wadda ya san tayi abin ya fara affecting brain d'inta as yarinya karama ta gamu da abinda yafi karfin tunaninta she's totally confused ga kewar en uwanta dake addabar ta tunda take basu ta'ba kwana wurare mabanbanta ba da juna se a washegarin 'batar mahaifiyarsu zuwa yanzu.


Ranar kuwa da suka had'u a makaranta se sun baka matukar tausayi sbd yadda suka rungume juna suna kuka yayinda neeha taki sam ta koma class d'insu duk yadda akayi da ita se kyaleta da akayi class d'in su arwa breakfast ma tare sukayi dukkansu taji daad'i sossai har ranta da taji yakumboce ta d'aukesu ta san aka wareta to fah yakumbo na son kannen nata bazata ta'ba cutar mata da su ba, da aka tashi da kyar suka rabu bayan Arwa ta rungume uncle sulaiman da yazo d'aukansu ta sha kukanta.


Kad'an kad'an abinda ke faruwa yake affecting Arwa ba tare da kowa ya sani ba har aka kai Mama asibiti, washegarin ranar da aka kaita bayan driver ya d'aukota daga school baaba larai ta sata tayi wanka ta kawo mata abinci chakula abincin tayi ba tare da taci na kirki ba ta mike ta fice daga cikin gidan zuwa katon garden d'in gidan, wuri ta samu ta zauna tare da kafa tagumi tana tunanin to in ba paapa bane babanta waye ne? Ko rasuwa yayi? Amma In har rasuwa yayi me yasa maami bata ta'ba fad'a mata ba.


Yarinya da tunanin abinda yafi karfinta se ta fara kawo lokuta da dama da zata zo yakumbo ta hantareta maami ta rungumeta tayi ta kuka tana neman yafiyarta to ko de...... da sauri ta d'aga kai jin an jefeta da dutse kallon wadda ya jefetan tayi, Isma'il ne yana tsaye nesa da ita yace "ke rasa kunya tunanin me kike ne da yarintarki?" Wani irin kallon tsana ta jefeshi dashi tare da dukar da kanta.


Matsowa ya fara yace "lemme guess, tunanin mamanki? Ko na babanki? Au ashe fah baki san waye maman naki ba, karki damu inde don itace dama chan ta saba yawonta tace 'bacewa tayi" wani irin kallo take mishi kuka na shirin kwace mata yace "ko de tunanin waye mahaifinki kike don a yadda kike da idanunki tsaitsayen nan na tabbatar kin gama fahimtar komai" bata tanka shi ba sede tabbas maganganunshi na matukar tasiri gareta.


Dukowa yayi daidai kunnenta yace "bari In baki Satan amsa, ke de shegiyace baki da uba sbd a yawon banza uwarki ta sameki" yana kai nan yayi gaba yana waka wadda be gama fita daga garden d'in ba yaji ihun Arwa, ko a jikinshi yayi shigewarshi ihu ta dingayi hannunta rufe da kunnuwanta wadda ihun tan ya ja hankalin me bawa flowers d'insu ruwa da gudu ya shiga garden d'in a tunaninshi ko maciji ne ya sareta sede inaaa duk yadda ya so ta mishi magana ki tayi se ihu da kuka.


Da sauri ya kira baaba larai tazo nan ma taki motsi se ihun da take ta kurmawa Daga nan kuma ta fad'i sumammiya hankalinsu yayi mugun tashin inda baaba ta Tura a kira hajja a d'ari hajja tazo ta d'agota jikinta tana kuka "me ke Faruwa da iyalaina ne?" Tayiwa kanta tambayar cikin kuka duk zatonta aljannu ne suka buge Arwa d'aukanta sukayi zuwa parlorn Abba duk wani adu'a sun mata sede bata motsa ba da hanzari hajja ta kira Abba a rude yasa a kawota asibitin da mama take nan da nan suka wuce aka shige da ita emergency.


************


Ta bangaren su Saif tun a ranar ya tarkata duk wani abinda ze bukata suka wuce Abuja da niyyan shi da kaduna kuma se baba ya gani, duniya sabuwa wa zuby ita kad'ai se yadda tayi da Saif tana Jin daad'i sossai a zamanta dashi se abinda take so gashi yana kaffa kaffa da ita sbd blackmailing d'inshi da tayi akan 'barin cikinta kullum se ta mishi kukan munafurci yayi ta bata hakuri yana d'aurawa kanshi laifi da be ce taje d'akin shaati ba da bata je ba, duk mutanen Saif na da sbd mutuncinshi da son mutanenshi yanzu babu, ya zama komai fad'a da masifa, Allah ya taimakeshi be samu matsala a aikinshi ba har yanzu sbd kwazonshi da tsoron Allahn shi, Abinda zuby bata sani ba duk waenda suke tare dashi a da da yanzu basa tare sbd rashin mutuncin da take karta musu sun dukufa mishi adu'a da neman sauki a wurin ubangiji tunda suma ya musu a lokacin da suke da bukata, a takaice dae zuby na tsaka adu'a ko ta Ina.


**********


Ta 'bangaren shaati kuwa har yanzu basu gana da baba ba sbd rashin lafiyan da take ciki lafiya yaki isanta, kullum da ciwo take yini cikinta a kulle, tun jidda na yin jinyar a gida har suka dangana da zaman asibiti wadda hajja da yaya suke zarya kansu, tsantsar soyayya mutanen na mata dukda basu santa ba basu san daga Ina ta fito ba sede Allah ya sa masu tausayinta cikin ransu matuka dukda su asalinsu masu karamci ne da mutunci.


Tayi sabo sossai da iyayen marikan nata sede daga baba har Abba ba wadda ya ta'ba zuwa sede su gaisa a waya in matansu sunzo, har sauran yayyun jidda mata na zuwa haka kannen Shareef sun zo sun koma dayake AUN suke karatu yola, shi kanshi Shareef duk abinda me ciki zata bukata marar lafiya kan a fad'a mishi ya riga yayi mata tausayinta ya matukar samun gur'bi a zuciyarshi dukda basu ta'ba zama daga ita se shi ya mata tambayoyin da yake so ba dukda ya san amsan ta wurin jidda.


Har yanzu papern da ta rubuta sunan 'ya'yanta na wurinshi In ya kalla se yaji kaman ya musu hawaye Allah kad'ai ya san irin halin da suke ciki, iyayenta ma kad'ai ya san suna cikin tarraddadi yayinda a chan kasan ranshi tunanin mijinta ke d'arsuwa, a jiki tayi kyau ta murje Asalin kyaunta da kyaun fatanta sun fito ta cika ta ko Ina, cikinta a yadda yakeyi yaron na cikin tsaka me wuya dake barazana da ranshi suna tunanin kan ta isa EDD d'inta zasu saka mata ruwan labour ta haihu kawai shine abinda yafi sauki In ba haka ba ze iya rasa ranshi a yanzu saura two weeks ta shiga watan haihuwanta.


************


Tunda likitan ya fito, majeed, mujeeb, hameed da Abba suka tasa shi gaba suna jiran jin me ya faru da Arwan hajja da ta buga tagumi cikin tunani bata ma san likitan ya fito ba, gumi ya share cikin tausayawa Arwa yace "am sorry to say khadija na cikin wani hali wadda ya ta'ba mata kwakwalwa tabbas akwai wani abu da ya faru da ita wadda yafi karfin tunaninta ya had'u kuma da ta jima cikin damuwa da matsawa kwakwalwanta da tunani, yanzu haka ta farka sede mun mata alluran bacci shi zamu ci gaba da mata sbd firgita da takeyi da ihu zamu ci gaba da bincike Allah ya bata lafiya"

Yana kai nan ya wuce tashin hankali dae wannan familyn suna kan gani duk sun shiga damuwa da kyar hajja ta karasa wurinta yayinda mujeeb yabi bayan likitan Don kar'ban prescription, Abba da Hameed suka koma wurin mama, majeed yabi bayan hajja d'akin, a rud'e Mama ta tambayi Abba ya jikin Arwan? A sanyaye ya fad'a mata abinda likitan ya fad'a, anan ta sa kuka kenan kwakwalwan Arwa yayi sensing duk wani abinda ke faruwa amma definitely akwai abinda taji da ze kara birkitata kwakwalwanta na son believing zuciyarta na rejecting.


Anan mama ta tabbatarwa da kanta dole ta samu lafiya da izinin Allah sbd bazata iya zuba ido familynta na ci gaba da ta'bar'barewa ba kaman yadda mujeeb ya fad'a dole in Isma'il na da hannu kan wannan abinda ke faruwa da sun don shine mabud'i to fah bazata yarda ba ko sama zata had'e da kasa they must bring him into Justice, wahalan shaati will not be in vain.


A ranar kuwa ta nemi aka sallameta duk yadda taso hajja ta hakura ta koma gida ita zatayi jinyar Arwa hajja taki haka ta kyaleta suka koma gida, bayan sun isa ta d'aga waya ta kira yakumbo Don su kuma tattaunawa taji lafiyan yaran ta kuma fad'a mata arwa ba Lafiya dukda ta san ba sonta take ba, ringing na karshe yakumbo ta amsa cikin kuka da tashin hankali wadda ya tsorata Mama a rud'e take tambayar yakumbo me ke faruwa sede inaa alamu ya nuna bata ma san ta d'auki wayan ba kashewa tayi tana neman izinin Abba na zuwa gidan yakumbon take ya bata izini yace taje sede taje da driver nan suka fice.

                    🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇

   *Baya Chanza d'and'anon teku*


      *Fatima Muhammad Gurin*

    **Gureenjo6763 on Wattpad**


          'Yar Mutan Adamawa


   *P24*


"Assalamu Alaikum" ta kutsa kanta cikin gidan bakinta d'auke da sallama zugum zugum ta gansu Anty tala, yakumbo, innani, sulaiman, bappa, Kawu da hajar zaune duk matan sunyi kuka sun gaji, sun buga tagumi har mazan sun rasa abin fad'a, da kyar innani tayi mata bismillah gefen taburman da suke zaune zama tayi tana gaida su, a tare duk suka amsa tace "ko lafiya?" Yakumbo cikin jimami tace "Ina fa lafiya, ni kam ban san wani irin ibtila'i bane ke fad'owa yaran nan abin yayi yawa yanzu wannan tashin hankalin da muka rasa ta Ina zamu fara kamamishi shi yafi komai ciwo da zafi".+


Mama tace "subhanallah Allah shine ze mana maganin komai, shi zamu mikawa duk ragamar rayuwarmu sannan bawan da ba'a jarabceshi ba ai be cika me imani ba, kun manta kar'ban kaddara me kyau ko marar kyau yana daga cikin shika shikan imani? Wani abun ne kuma ya kuma faruwa da saifullahi ko yaran?" Innani tace "talatuce....." se kuma tayi shiru, sulaiman ya karasa da "baban su hajar ne aka gano ashe shi ya sace ta ya mata fyad'e sbd bokanshi yace muddin ya sadu da ershi mace to fah se yaci wannan takarar na gomna da ya tsaya".


"Innalillahi wainna ilaihi rajiun, la haula wala quwwata illa billah, hasbunallahu wani'imal wakeel" Mama ta jerosu a tare hawaye na gangaro mata ganin hajar d'in duk ta firgice tayi wani iri bata magana kwata kwata, wannan duniya ina zaki damu? Ashe Don kawai mulki na duniya mutum ze iya salwantar da rayuwar ershi ta hanyar sa'bawa mahallicinshi ta mummunan hanya? Me yarinya hajar d'innan ta sani da ya za'bi tozartata da rayuwarta, kuka sossai Mama ta saka cikin jimami da tarradaddin abinda duniya ta zama yanzu, ya tala da dama kukan nata be tsaya ba taci gaba da yinshi daga kaji kukan zaka san na tsantsar bakin ciki ne da zallar damuwa da ta rasa yadda zatayi dashi.


Seda Mama tayi kuka sossai kan ta share fuskanta tare da d'agowa tace "to yanzu me aka mishi?" Bappa yace "hmm da matasan unguwan suka so banka mishi wuta amma se hukuma sukayi saurin isowa suka kamashi kan su kamashin ma ya haukace tuburan se fad'e fad'en duk wasu abubuwan da yayi yake tayi" hakuri mama ta ba Anty tala, girgiza kai Anty tala tayi cikin tashin hankali tace "babban abinda yafi damuna shine cikin da yarinyar nan da bata wuce shekara 14 ba ta samu ya zanyi dashi? Me zan ce mata? Me zan cewa mijin da en uwan da zata aura? Ashe duk ka ganka cikin wani rahama na ubangiji ya kamata ka gode mishi ba ka butulce mishi ba? Kenan duk abubuwan da muka yiwa Aisha (shaati) se anyiwa hajar ba tare da anyi la'akari da irin tata kaddarar ba?"


Kuka sossai yaci karfinta danasanin abubuwan da suka dinga yiwa shaati na kamata Lallai duniya kenan, (ashe kenan babu kyau duk wani kaddara da ya fad'arwa mutum ka dinga hantararshi da hakan kana yamad'id'i dashi ba, baka san ta inda naka kaddaran ze zo ba, Allah ya sa kaddararmu ta kasance me kyau) duk jikinsu yayi matukar sanyi musamman yakumbo da ta dinga tayasu Allah ya taimaketa ta nemi yafiyar shaati kan 'bacewarta amma tabbas sun san sunyi matukar kuntatawa rayuwarta.


Mama ne ta yanke shirun da "Ina sauran yaran suke?" Innani tace "suna shiyata da Aisha itace me karfin halin d'auke musu hankali amma Arham kam ya rufe kanshi tuntuni yaki bud'ewa se kuka yakeyi" Mama tace "yana Ina?" Innani tace "yana d'akin sulaiman" Mikewa mama tayi ta karasa inda innani ta nuna mata da hannu a matsayin d'akin sulaiman a kofan ta tsaya ta fara kiran sunanshi shiru tayi ta d'aura da "na san kana jina Arham ka saurara kaji abinda zan fad'a maka.


(Ga masu cewa be kamata komai ya faru ga Aisha ba sbd adu'o'in da takeyi ku saurara kuji da kyau Adu'a baya hana kaddararka afkuwa gareka sede yana iya sassautawa ko ya saukaka maka)


Ka san babu wani hutu da kwanciyar hankali ga bawa a wannan rayuwa ta duniya sai yayi imani da kaddarar Allah, wato ya sakankance cewa duk abinda Allah ya qaddara mai aukuwace, kuma abinda be so faruwarsa ba to hakika baze faru ba, haka kuma lallai da alumma zata taru gabad'aya ta cutar da bawa da wani abu to ba zasu iya ba saidai da Abunda Allah ya rubuta ze sameshi, hakanan da zasu had'u domin su anfanar dashi bazasu iya ba face da abinda Allah ya rubuta.


Allah yana cewa a cikin suratul qamar Aya ta 49.

"أنا كل شيء خلقناه بقدر"

"Lallai mun halicci komai da qaddara".

Sannan ya kuma cewa cikin suratul A'ala.

"الذى خلق فسوى ٢  والذي قدر فهـدى"

"Shine wadda yayi halitta kuma ya daidaita. Kuma shine wanda ya qaddara abubuwa kuma ya shiryar dasu".

   Sannan ya kuma cewa cikin suratul furqan aya ta biyu.

"وخلق كل شيء فقدره تقديرا"

"Kuma ya halicci kowane abu, kuma ya qaddarashi kaddarawa"

        Ayoyi da hadisai da sukayi magana ko kuma nuni da qaddara da kuma kar'barshi suna da matukar yawa Arham na san ka sansu tunda kayi islamiyya tuni kawai nake maka, ka ta'ba sanin kaddarata a matsayin uwa da kaddarar d'iyata Aisha? To yau zan baka labari tiryan tiryan ta fara bashi labarin rayuwar Aisha tun daga farko har kawo yau, ta karasa cikin kuka seda tayi d'an Shiru kan ta d'aura da.


Ka san me nake fad'awa Aisha da zuciyata? Ta ja numfashi ba tare da ta jira amsanshi ba tace waenchan ayoyin da na gayama da kuma tunawa da duk wadda bashi da cikakken imani baze shiga aljanna ba, wadda kuma be kar'bi kaddararshi me kyau ko marar kyau ba bashi da cikakken imani, dole ce in muna son samun rabauta mu kasance masu kar'bar kaddara" ta karasa tana kallon ya tala da duk suka gama jin labarin da ta gama bayarwa, duk sunyi lakwas jikinsu yayi matukar sanyi, kunyar Aisha da mahaifiyarta na rufesu.


Sbd abubuwan da suka dinga mata, wannan duniyan ba bakin komai bace tabbas Aisha ta kasance mace mai dauriya da d'auke kai akan abubuwa, ga mamakinsu se ga Arham ya bud'e kofan ya fito ya kama hannun Mama yana me sakin kuka me ciwo, In ya tuna yadda abokanshi suke watsewa da ya durfafi cikinsu, In ya tuna yadda ake zund'enshi In yana tafiya cikin unguwa, In ya tuna kuka me ciwo da kanwarshi take kwana yi a lokacin da aka mata fyad'en rashin imani, se yaji khaih baze iya da wannan qaddarar ba Ina ma ya kashe kanshi ya huta? Amma kuma jin wannan kalamai daga Mama se yace Alhamdulillah, be san kaddarar wani ba gashi Anty Aisha da wannan irin rayuwar wahalan da tayi ko ma yace take kai tana ci gaba da rayuwarta cikin fara'a da sakewa cike da dauriya kaman ba abinda yake damunta nan duniya.


Mikewa Mama tayi ta ja hannunshi suka zauna tana sake murmushi tace "ku daure ku mai da komai ba komai ba zakuji daad'in hakan ku maida lamuranku ga Allah" godiya suka mata suna guntun murmushi tabbas sunji dama dama, innani tace "ko zaki iya bamu shawara akan yadda zamuyi da cikin yarinyar nan?" Ajiyar zuciya mama ta sauke tace "zubar dashi babban hatsari ne ga rayuwarta kasancewarta yarinya komai ze iya faruwa da ita kenan, zaku iya d'aukan alhakin ranta In ta mutu lokacin zubarwa? Ni a shawarata ku kyaleta dashi Allahn da ya bata shi kad'ai ya san dalilin hakan" duk na'am sukayi da shawaranta kasancewarta likita tabbas abinda ta fad'an hakane.


Fad'a musu tayi Arwa na asibiti tana fama da birkitan kwakwalwa da farko sun d'auka hauka ne duk sun rud'e se daga baya da ta musu bayani suka fahimta sede duk da haka sun matukar shiga damuwa inda suka tabbatar mata zuwa gobe zasu shigo dubata sallama ta musu tana me wucewa, Arham ya lumshe idanunshi cike da tausayin Arwa da tun da chan tausayinta yayi matukar tasiri a zuciyarshi, da kyar ya iya bud'e baki ya cewa mahaifiyarshi "mommy waec result na na fita kasan nan zan bari bazan iya karatu a nan ba" Kai kawai ta iya gyad'a mishi suka ci gaba da zaman Shiru.


************


BAYAN WATA GUDA


Rayuwa juyi juyi me cike da abin al'ajabi da mamaki a tare da taraddadi, zuwa yanzu Mama da iyalanta sun kar'bi kaddararsu sun rungumi adu'a sbd sun sha neman Aisha har sun gaji ba labarinta, yayinda jikin Arwa har yanzu yaki sauki tana nan kwance asibiti har yau cikin alluran bacci suke mata don in har ta farka to cikin ihu da kuka take tashi da buge buge wadda akalar familyn suka karkata gareta kaman ba ita bace lokacin cikin aka so a zubar da duka.


Har yau hajja ke kula da ita yayinda lokuta da dama fadila da meena ke yawan tayata haka mama da In har tazo aiki zuwa d'akin sau kusan ba adadi ya kasance kaman dae In ta shiga ta koma zata samu ta farka Lafiya kalau, su yakumbo duk suna zuwa akai akai haka ya tala da yanzu duniya ta koya mata hankali, mijinta ya mutu gidan yari bayan haukan da yayi daga karshe da duka da azabtarwa wurin en gidan yarin ya sa ya kashe kanshi da kanshi.


Dukda ga kud'i dukiyarshi duk an mallaka mata kasancewar bai da wasu en uwa ko mata, waec d'in Arham ya fito wadda yayi kyau sossai nan da nan sulaiman ya mishi processing ya samu admission a LA ya wuce abinshi, bayan yayi kukan rabuwa da Arwa Don kullum se yaje wurinta asibiti bayan ya tafin ma kuwa kullum se ya kira Mama sau akalla hud'u a rana yaji ya jikinta.


Har suggesting ya tala tayi zata kai Arwa waje sede mama taki ta tabbatar mata abinda nan da waje zasuyi duk d'aya ne in akayi rashin sa'a ma kila likitan da take wurinshi anan asibitinsu shi zata gani outside d'in tunda babban asibitine masu manyan likitoti, hajar na nan ta koma Shiru Shiru bata fita ko Ina sbd mutane hakanan a gidan bata iya ko da dariya ne ga en uwanta ba.


Yasmin itama tana yawan zuwa ganin yayar tata musamman In suna gidan Mama dayake kaman jeka ka dawo sukeyi In sun kwana biyu wurin yakumbo se suje gidan Mama su kwana biyu, adu'a kuwa basu daina shi ba har kawo yanzu shi sukeyi, malam sulaiman ma be dena ba yayinda akayi auren Isma'il last two weeks ko a jikin su mama basu bada hankalinsu kan shagulgulan bukin ba yayinda iyayensu suke jefa musu magana a kaikaice.


Hmmm Allah sarki mama baiwar Allah ko ta nuna musu ta san suna jefa mata magana akan diyarta ta tafi yawon karuwanci da aure suna nan suna wani adu'a sadaka da yanka sbd Allah ya bayyana musu ita.


Ta 'bangaren Shaati har zuwa yanzu tana kan bed rest sbd d'an yaki lafiya yayinda take samun duk wani kulan da ya kamata daga iyayen Shareef da jidda har yau Allah be yi sun gamu da baba ba sede suji ya jikin nata wurin matansu, Shareef ya jima da komawa Abuja sede yana yawan waya da jidda sbd jin lafiyanta da abinda ke cikinta har yau Allah be yi tayi magana ba sede rubutu biro da memo kullum yana tare da ita, har yau bata iya tuna komai a kan rayuwarta ba se 'ya'yanta da a kullum suke ranta.


Ta 'bangaren Saif da zuby rayuwansu suke cikin kwanciyar hankali dukda cutar dashi da zuby keyi haka yake zaune da ita inda Allah ya taimakeshi yanzu ya natsu hankali ya shigeshi ya koma bin Allah sossai yake Adu'a yanzu yana d'an samu peace of mind don in be yi ba se yaji kaman an d'auki duniya ne gabad'aya an d'aura mishi a kai wani irin nauyi da uneasiness yakeji muddin ya tsallake azkar d'inshi a yanzu wadda hakan ke matukar bawa zuby haushi, har yau be san abubuwan dake faruwa kaduna ba tunda ba zuwa yake ba sede suyi waya da yakumbo sa'i da lokaci shima tana d'auka ne sbd fad'an da mama ta mata akan ta bishi a haka taci gaba da mishi adu'a har ya koma kanshi.


*********


A yau ake shirin sawa Shaati ruwan da ze taso mata da labour sbd ciwon babyn karuwa yake, Shareef tun cikin daren ya iso yayinda washegari ya d'auki Su hajja da yaya suka wuce asibitin bayan da baba ya bawa hajja wani ruwan tofi ya tabbatar mata ta bata ta sha, jidda tun safe take asibitin sbd ba ita ta kwana ba me aikin hajjace ta kwana wacce take ta yasu kwana wani lokacin.


Suna isa asibitin suka karasa d'akin da take murmushi ta saki ganinsu tana d'aga musu hannu suma cikin fara'a suka d'aga mata suna tambayar jidda ya jikinta ta amsa musu da da sauki su kad'ai ake jira suzo a shiga da ita labour room, ruwan hajja ta bata tace "kar'bi kisha Aisha Allah ubangiji ya saukeki Lafiya" kar'ba tayi ta sha sukayi ta mata adu'a tana kar'ba a zuciyarta nurses ne suka zo suka turata har sun isa kofa kan taji muryanshi cikin sanyi yana cewa "Allah ya raba lafiya" murmushi kad'an ta mishi kan suka fice aka shige labour room aka sanya mata drips d'in hannu biyu.


Kan kace me azabar nakuda ya fara nukurkusanta tun tana ji a hankali har ya fara fin karfinta cikin matukar azaba takeyiwa mahaifiyarta adu'a a zuciyarta dukda ta manta sunanta bare kamanninta, hmm tashin hankali tana cikin wannan hali Bakin aljanin jikinta ya tashi nan fah labour room ya rud'e karanta kakeji har inda su hajja suke asibitin gabad'aya ya d'auka, salati hajja da yaya suka sake a sanyaye hajja tace "dama tana da iska ne?" Duk kasa amsa mata sukayi sbd ba sani sukayi ba abu fa ya rincha'be kara take har wasu aljannun na tashi a cikin asibitin gashi haihuwan yaki yiwuwa, wani bala'e'en karan da ta saki seda duk doctors suka kame wuri guda abinda aka d'auke hannayenta da kafafunta dashi da kansu suke neman warwarewa sossai likitotin suka tsorata da gudu jidda ta fito ta kama hannun Shareef ta ja shi ciki cikin karfi ya fara rera wasu adu'o'i hawaye na gangaro mishi tsabar tausayin shaati..

                    

                🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA....💦🍇

*Baya Chanza d'and'anon teku*


*Fatima Muhammad Gurin*

**Gureenjo6763 on Wattpad**


'Yar Mutan Adamawa


*P25*


Idanunshi a runtse haka ya cigaba da rera ayoyin ruqya daga cikin qur'ani duk da yadda ya runtse idanunshi kunnuwanshi suna jiye mishi tsananin wahala da gurnanin da take ciki a hankali ajanin ya gudu nan kuma labourn ya taso gadan gadan be dena ba se da yaji jidda ta furta "Alhamdulillah" juyawa kawai yayi ya fita zuciyarshi cike da tausayin mata waenda a ko yaushe sune jigon rayuwan 'ya'ya.+


Be ta'ba experiencing yadda ake labour ba se yau, son hajja seda ya ninku a zuciyarshi yayinda tausayin mata ya kara samun gurbi a zuciyarshi, yana fita hajja ta tareshi tace "ta haihu?" Kai ya gyad'a suka amsa da "Alhamdulillah" chan se ga jidda ta fito tana kallon su hajja cikin murmushi tace "baby boy muka samu sede be da lafiya be yi kukan kirki ba" yaya tace "Allah sarki Allah ya bashi lafiya uwar fah?" Tace "ana gyarata Lafiya kalau take" duk ajiyar zuciya suka sauke suna zama.


Bayan an gama kimtsa ta aka turata d'akin hutu yayinda yaron aka kaishi children unit, su yaya suka shige d'akin yayinda Shareef ya wuce wurin baba don yi mishi bayani ya kamata zuwa yanzu a san abinyi, hajja na shiga ta had'a mata wani kunu da ni karan kaina ban san na menene ba turirin zafi kawai ke fita daga cikinshi kar'ba tayi Don wani bala'e'en yunwa da take ji seda ta shanye katon cup d'in gabad'aya kan ta kwanta se bacci.


Ta jima cikin baccin gajiya kan ta farka hajja kawai ta gani d'akin murmushi ta mata yayinda hajja ta mayar mata, tace "sannu Aishatu tashi muje kiyi wanka kan ki gama shiri na san yaya zata karaso da abincin ki se kici ki koshi kan a kawo baby ya sha" Mikewa tayi zaune hajja ta taimaka mata suka shige toilet, da kanta ta had'a mata ta tsaya tana kallonta ganin shaati ta sa hannu a ruwan tayi saurin cirewa tana yarfawa yasa hajja sakin dariya a zuciyarta tace "Lallai ma yarinyar nan".


Me makon ta fita se ta d'auko towel madaidaici ta jefa ruwan katon baff dake toilet d'in ta nuna mata alamun ta shiga zazzare ido take tana shirin shagwa'be fuska Don ta san haihuwan Arwa da baaba larai ta mata bataji da daad'i ba shiyasa sauran haihuwan nata take nacewa zatayi da kanta In ta shiga kuwa se ta kara surke ruwan, da lallama hajja ta sa ta shiga baff d'in ta fara mata anan ta san na baaba larai rahama ne da na hajja.


Da zizzilewa da komai akayi wankan aka fito sede taji daad'in jikin nata sossai, sun kuwa samu yaya ta karaso abincin ta zuba mata tuwo ne na dawa da miyan kuka yaji daddawa se turiri yake a wani plate d'in kuma kakkauran pepper soup na kan sa ne wadda yaji kayan had'i yayi kauri kitip duk wadda ya san kanuri ya san yadda suke p soup d'insu, seda ta shimfid'a mata darduma me taushi kan taburman dake d'akin kan ta jefa pillow kan nan shaati ta zauna ba tare da ta saka kaya ba, bud'e cikinta tayi ta ci abincin sossai jefi jefi take sauraran hirarrakin hajja da yaya, seda tayi nak duk zufa na karyo mata kan ta mike hajja ta bata kaya riga da zani na atampha ta saka tare da d'aura d'ankwali ta hau kan gadon ta zauna tana kallon yaya dake hura coal cikin kasko Lallai wannan jego nata na gata zatayi wadda bata ta'ba irinshi ba ko daga wanka da abincin da taci ta gane banbanci kwarai da gaske da nasu Don yanzu jinta take garau kaman ba ita ta haihu ba.


Hajja ta kira wata cleaner ta gyare d'akin tsab yayinda yaya ta saka turaren wuta me sanyin kamshi, nan da nan d'akin ya d'au kamshi wani sabon bacci ne ke shirin fisgan ta daga zaune se taji an turo kofan, kallon kofan tayi jidda ce rike da babyn cikin showel murmushi suka sakar wa juna, ta karaso ta d'aura mata babyn kan kafa yayinda ta rikeshi da kyau tana kallon fuskanshi gabanta ne yayi wani mugun fad'uwa ta san fuskan nan sak sede ta rasa na waye duka gabanta ya ci gaba dayi yayinda ta fara ambaton Allah a zuciyarta.


Seda jidda ta ta'bata kan ta dawo hayyacinta tana kallonta cikin murmushi jidda tace "so you are carried away kinga handsome baby wadda yafi mamanshi kyau" murmushi ta saki hajja tace "jidda yaron ne yafi mamanshi kyau?" Tace "wallahi kuwa kinga kyaun yaron be d'auko komai nata ba, bari ya sha in baku ku gani dukda an hana" murmushi sukayi Aisha ta ciro Mama ta fara bashi ganin yadda yake jejjefa hannu alamun yunwa yakeji.


Kar'ba kuwa yayi sede in ya zuka d'aya se ya sake wadda duk ya zuka d'in kaman numfashinshi ze bar jikinshi, tausayinshine ya rufe shaati Allah sarki Allah ya baka lafiya ta furta a kasan ranta, a haka ya sha kad'an yaki kar'ba jidda dake ta zuba wa hajja da yaya surutu ta mikawa, aiko ta mikawa hajja shi kallonshi take tana "tabarakallah Masha Allah, ashe da gaskiyanki jiddatu" dariya jidda tayi yayinda yaya da ta leko fuskanshi tace "for the first time jidda ta fad'i abu aka tabbatar gaskiyace" bubbuga kafa ta fara a shagwa'be yayinda hajja da yaya suka sake dariya shaati kam se murmushi tayi, ji take kaman kar a tafi da babyn.


Bayan fitan jidda ta kwanta ta lumshe idanunta tana forcing kwakwalwanta ya tuna wani abu akan rayuwarta, sallamanshi ta jiyo wadda hakan ya kuma sa ta matse idanunta, gadon ya fara kallo ganin tana bacci yasa ya d'an kura ma fuskanta idanu kan ya kawar yana duban hajja yace "hajja baba ze mana kwace" hajja tace "tooh kwacen me kuma?" Yana zama kan kujera dayake duk kan taburma suke yace "kwacen Aisha mana" yadda ya furta sunan seda gabanta ya fad'i.


Yaya tace "me ya faru ze kwacetan?" Yace "wai daga asibiti kar mu kuskura mu wuce da ita gidanmu mu ci gaba da yaranta mu had'a ta da hajja tayi chan gida" dariya hajja tayi ganin kaman har zuciyarshi be so ba tace "Ai ko be fad'a ba dama chan ni ban yi niyyan barin muku ita ba, na riga na sa a raina tana haihuwa gidana zata koma bare yanzu da ba lafiya ne da ita da babyn sossai ba matarka kuma ba abinda ta sani kan wannan".


Yace yana duban yaya "yaya zamu iya kula da ita mana, hajja inace jidda Doctor ce Ai In ba lafiya ne da itaba zata fi saurin ganewa" girgiza kai hajja tayi tace "me ka fad'awa baban naka?" Bayani ya mata akan lokacin da jidda suka je gaida baba da Aisha ta kasa shiga ya d'aura da "na so yiwa baba bayani se kuma rashin lafiyanta ya sha kaina" girgiza kai hajja tayi tace "ba dole yace ta koma ba, yanzu da ya san hakan da bata haihu Lafiya kalau ba wani damuwa ba? Yanzu dai yadda ya fad'a kaima ka san hakan za'ayi kuma madallah ma".


Shi ya koma jidda yadda ya shagwa'be fuska kaman ze yi kuka se kawai ya mike ya fice ya barsu suna mai dariya murmushi shaati tayi a zuciyarta tana musu adu'ar dacewa da gidan Aljannah karamcinsu har so yake yayi yawa, yana fita children unit yaje yaga babyn da har yanzu jidda na zaune kanshi tana kallonshi, tana ganin shi tace "Yauwa ya reef zo kalli kyaun babyn nan pls na kasa dena kallonshi" kallon yaron yayi tabbas kyakyawa ne kuma be d'auko komai na Aisha ba basu san farin fata ba ko babanshi fari ne ko na Aishan ya d'auko sede sun san yaron fari ne sol har jaja jaja yake yi.


Yace "tabarakallah Masha Allah, kyakyawa dashi" Tace "ya reef kana tunanin babanshi ya d'auka?" seda yaji wani iri a ranshi sbd wannan tambaya na jidda yace "lil Ina zan sani? Maybe" yayi maganan yana Mikewa yace "In kin tashi aiki lets go for there shopping" Tace "Ohk toh" fad'amata abinda baba yace yayi itama ta ringa bone fuska bata so ba sam, seda ya lallasheta yace karta damu tana kwana biyu zasu kwato kayansu kan ta d'an sake shi kuma ya fice.


BAYAN KWANA BIYU


Yau aka sallamesu yayinda ya kasance saura kwana biyu suna, duk wani kulawa shaati na samu wurin hajja da yaya da suke jinyantan bibbiyu lafiya take ji a cikin jikinta garau sbd cimar da ake bata ba irin waadda ta saba ba ga wani kunu me d'aad'i da gard'i da bata san na menene ba, hakanan tayi wani fresh tayi bulbul tumbin da ta d'anyi na haihuwan har ya koma dama ita nature d'inta ne tumbi bayan haihuwa baya zama mata, yaron zuwa yanzu yaji sauki sossai kukan shi yake yararai yararai kaman ba shi ba haka yana shan Nono sossai the more yake kara kwana duniya the more kamanninshi suke fitowa da Saif.


Bayan sun tattara duk komai an kai mota ta mike tana gyara zaman hijab d'in jikinta da ta d'aurashi kan wata doguwar riga ta saudi me d'an fad'i hajja ce rike da yaron yayinda yaya ke rike da last flask d'insu suka shige motan kirar Highlander, suka wuce jidda yau bata zo ba haka ma Shareef, a chan gidan Hajja suka samesu d'akin da aka gyare mata nan kusa da hajja aka kai kayanta da jidda ta kwaso daga gidanta da sabbin shoppings da suka mata da na yaron.


A parlor suka yada zango ya kyallu da bata ta'ba zuwa asibitin ba ta shigo tayi musu sannu da zuwa tayi ficewarta, nan fa matan unguwa suka fara shigowa barka sede jidda taki a ga yaron d'akin hajja ta kaishi sede su cewa mutane an hana d'aukanshi sbd lafiya bata isheshi ba, shaati jinta take kaman er gida yadda ake nuna mata kulawa da kaffa kaffa bayan mutane sun ragu hajja da kanta kaman yadda ta saba ta mata wanka, bayan ta fito hajja ta fice Don barinta ta shirya, cikin doguwar rigar atampha ta shirya tare da sanya hijab ta fito parlor.


Zama sukayi suka kafa sabon hira basu kula ba se jin sallaman Baba sukayi zuwa cikin parlorn hajjan, da mugun azama shaati ta mike zata gudu d'aki ya daka mata tsawa "dawo!!!!! Dawo ki zauna" chak ta tsaya jikinta na tsananta rawa yace "ba magana nake ba!!!" Karkarwa take har kafanta na kin d'aukanta Shareef, jidda, hajja da yaya duk kallon ikon Allah sukeyi da sauri ya mike ganin tayi baya kaman zata zube se ta zauna kanta a kasa.


Zama baba yayi a kujeran dake fuskantanta yace "juyo kalleni" Shiru tayi ba tare da ta juyo ba yace "bana maimaitawa Aljanni magana bare irinka bakin kafiri na kara maka magana sau biyu ba abinda ze hanani kona ka har lahira, juyo nace!!!" Ya buga mata tsawa, da sauri ta juyo kanta kasa har yanzu baba yace "don rashin imani da kafirci ka samu wuri jikin baiwar Allah kayi zamanka ka hanata magana ka hanata tuna komai? Akan me? Me ta maka?".


Cikin wani kakkausan murya tace "Ba ruwana nima aiko ni akayi" baba yace "aikoka? A Ina aka d'auko ka?" Yace "a makabarta" baba yace "subhanallah, wani marar imanin ne ya aikoka?" Cikin muryanshin nan dai marar dad'in ji yace "uban kishiyanta" zaro ido en parlon sukayi mahaifin kishiyanta ne ashe da wannan aikin? Kenan malamin tsubbu ne? Baba yace "to kazo inda baka dace ba, sbd wannan baiwar Allahn tafi karfinka ka kama hanya ka fice tun ban maka lahani ba kaje ku karata da wadda ya aikoka".


Shiru yayi baba yace "magana nake" da sauri yace "ayi min aikin gafara bazan iya fita ba, yanzu haka ma ban cika aikina yadda ya kamata ba sbd karfin adu'ar ita yarinyar na shiga jikinta ne da nufin zata zama mahaukaciya tuburan me yawo akan bola, zata wulakanta ta haihu a wulakance amma se na kasa yanzu In koma in cewa wadda ya aikoni me Bayan d'an hana magana da goge kwakwalwa da na mata a hakan ma na kasa?".


Baba yace "kenan ce min kake bazaka fita ba? In baka fita ta daad'i ba zaka fita ta wuya, jidda d'ibo min ruwa a cup kad'an" Mikewa jidda tayi ta d'ibo ta kawo mishi, ya jima yana tofi cikin ruwan nan yayinda shaati ke zaune jikinta se wani irin mugun rawa yake seda baba ya gama tofinshi kan yayi gyaran murya ya fara bismillah tare da fara karanto ayoyin ruqya.


Tun shaati na zaune shiru har ta fara buge kanta da hannu nan ta fara Toshe kunne kan kace kobo ta fara soshe soshe se ihu, ganin da gaske baba ze masa lahani yasa ya daka tsawa "dakata dakata!!!" Cikin tsawa baba yace "kul iye bakinka aljanni be isa yi mini tsawa ba, ka fice daga jikinta ka kuma dawowa ko ta hanyar da take ne na maka alkawarin se na lahira ya fika jin daad'i"


"Kalleni" baba ya fad'a shaati na d'ago kai domin kallonshi kawai baba ya watsa mata ruwan tofin nan a fuska wani irin ihun da ta kurma se da kusan rabin unguwan nan suka ji a jiggace yace "zan fita na shiga uku!!! Zan tafi, na rantse da sarkin dake busan numfashi se na rama abinda wannan munafukin bokan ya mini, ya d'aukoni Ina zaman zamana gashi yayi min sanadiyyar konuwar fuskata na har Abada se na rama, se na d'au fansa" ya kuma kurma wani ihun kan hayaki ya gauraye parlorn a hankali bakin hayakin yabi kofa ya fice.


Ajiyar zuciya duk suka sauke baba ya mikawa jidda sauran ruwan yace "shafa mata a fuskanta" kar'ba jidda tayi ta nufeta a tsorace yayinda ya dubi hajja yace "zan had'a mata wasu magunguna se a dinga sa ta amfani dasu zuwa wani lokaci, Ina jikanan?" Yayi tambayar yana baza idanu ko ze ganshi yaya ce ta mike taje ta d'aukoshi ta kawo mishi, kar'banshi yayi yana furta "barakallah Masha Allah" adu'o'i ya fara zuba mishi ya jima sossai yana mishi adu'o'i kunnuwanshi yaron kuwa yayi tsit yana ji kaman me saurare se kyakyafta idanu yake.


A hankali ta bud'e kwayar idanunta ta d'aura a kan pop d'in parlorn "sannu" taji jidda ta ambata kallonta tayi na seconds kan ta gyad'a kai abubuwan da suka faru daga farko har kawo yau Suna dawo mata, gabanta ne ya mugun fad'uwa Allah kad'ai ya san wani hali Mama ke ciki don itace ta fara zuwa mata rai kan su Arwa, "sannu Aisha" taji yaya da hajja sun fad'a gyad'a kai tayi tana kallon baba da yake ta ma babyn adu'a.


Bayan ya gama ya kalleta yayi murmushi a kunyace ta dukar da kanta ya kalli Shareef yace "an mishi hud'uba?" Girgiza kai shareef yayi yace "bamu san sunan da take son saka mishi ba so ban yi mishi ba" kallonta baba yayi yace "Aisha" d'ago kai tayi ta kalleshi yace "wani suna ne kika zabarwa jikana?" Kallon en d'akin tayi idanunta suka tsaya chak kan Shareef na seconds kan ta kalli baba cikin muryanta na asali me sanyi da daad'in saurare tace "Shareefuddeen" da sauri duk suka kalleta ta gyad'a kai tana murmushi.


Da karfi ya lumshe idanunshi wani bakon yanayi na ziyartarshi, har baba yayiwa yaron hud'uba ya gama shareef be iya bud'e idanunshi ba, seda baba yace "Allah ya raya shareefuddeen nayiwa d'ana hud'uba da sunan da na fi so duniya gashi kuma na sake yiwa jikana hud'uba dashi sauran kuma ka girma ka kwacemin mata" dariya duk sukayi baba ya kuma cewa "Aisha ko zaki iya bamu labarin rayuwarki da inda kika fito sbd muyi contacting iyayenki na tabbatar duk inda suke har yau hankalinsu ba kwance yake ba".


Ajiyar zuciya Aishata sauke for the second time zata kuma bada labarin rayuwarta me cike da abin tausayi, a hankali ta fara da "Sunana Aisha kaman yadda kuka sani sunan mahaifina Muhammad, mu en asalin garin kaduna ne mun kasance Fulanin nan sede mu bamu tashi da fulatanci da jinshi ba kaman kakkaninmu, mahaifina su su shidda ne wurin babansu "baba megari" da "hajja(Aisha)" wacce na ci sunanta.


Tun farkon aurensu suka baro asalin kauyensu suka dawo cikin kaduna da zama nan unguwan rimi, baba sale suka fara haifa kan baba habu se mahaifina wadda suke cewa mamman se baba haladu me bi mishi ta kasance mace tana aure katsina wacce muke cewa "maman katsina, Sadiya" se autansu "Mama rakiya" tana aure jigawa, mahaifinsu asalinshi manomi ne sannan In ya noma zuwa yake yi ya sayar kusan ya had'a duk wasu sana'o'i na samun kud'i a da, wato noma da kasuwanci tun yanayi da kanshi har ya kai ya kawo sede ya samu yara en gida masu mishi.


Shi mutum ne me son mutane da faram faram da wuya ya zauna wuri ko na kwana guda ne ya zo tashi se anyi kukan rabuwa dashi kwarai ya san hakkin mutanen da suke zagaye dashi, yaranshi dukkansu ya sanya karatun boko a lokacin har matan dukda ba kowa ke zuwa ba su ya saka musu sha'awan zuwan yayinda mahaifina yafi mai da hankali akan sauran en uwanshi sossai yake son karatun boko tunda ya sauke tun yana shekaru 11, wadda ya riga kaf en uwanshi mazan sauka, halinshi yazo d'aya sossai da mahaifinshi tun yana karami wadda sanadiyar hakan yasa mahaifinsu da mahaifiyarsu d'aukan son duniya su d'aura mai dukda suna iya kokarinsu wurin ganin en uwan basu fita daban ba.


A kwana a tashi har mahaifina ya gama secondary school inda sauran en uwan nashi basu gama ba, tun kan ya gama ma ya fantsama cikin Yaran mahaifinshi suke kasuwaci har ya kai a cikin kud'in sallaman da ake basu shima ana cire mishi nashi wadda In an cire se ya bawa mahaifiyarsu ajiya baya ta'ba komai tunda mahaifinsu be ragesu da komai ba, bayan ya gama a lokacin ya tara kud'ad'e dayawa inda yayi investing a kan sana'ar mahaifinshi suka had'a hannu da hannu kenan.


Baba sale da baba haladu a hankali hankali suka d'auki hassada da kyashi suka d'aura mai dukda babu wadda baba ya hana yin kasuwanci ko shiga cikin kasuwacinshi basu gama secondary ba a lokacin sukace su aure suke so baba megari be ki ba suka samo matansu yara kanana irin dae rayuwar da, ya aurar dasu bayan ya yanka musu side side a cikin gidan nashi ya gine musu auren gata ya musu.


Inda mahaifina shi ya nuna be shirya aure ba fa, haka babansu ya kyaleshi ya fita waje karo karatunshi akan harkar kasuwanci, inda yana shekaran karshe ya gamu da mahaifiyarmu dake karantar likitanci aji d'aya a jami'arsu, ya nuna yana sonta dama iyayen shi sun matsa mishi da maganan aure tunda har kaninshi haladu ma yayi sede duk cikinsu har ya gama ba wadda ya haihu se sale inda ya samu naseer.


Baba habu matarshi na haihuwa se yaro ya koma ko kuma tana samun ciki se 'bari, a lokacin da babanmu ya nuna mahaifiyarmu yake so wacce ita kuma sunanta fatima, se baba sale da baba habu sukace Ina Ai baze auri er boko su suna fama da kauyawan matansu da a lokacin duk sun tsofe, inda babansu ya dage yace shi kuma tunda ya aura musu wadda suke so baze ki aurawa mahaifinmu wadda yake so ba, inda ba 'bata lokaci aka d'aura musu aure dukda ita er kano ce nan cikin gidan baba ya yanka mishi fili shima sede yaki baba ya mishi gini a lokacin da kud'inshi ya Gina mata side dinta na zamani wadda ake yayi a lokacin.


Inda hakan ya kara tunzura bakin ciki da hassadar mahaifinmu sbd tunani suke ko baba ne shima ya mishi ginin, Mahaifiyarmu ta tare basu wani jima ba suka koma outside inda anan suka ci gaba da rayuwa kan su gama, farkon shekaransu ta haifi babban yayanmu Abdulmujeeb, shekaranshi biyu ta kuma haifan Abdulmajeed, a lokacin babanmu ya jima da gamawa yana de jiranta itama lokacin ta gama suka tarkato suka dawo Nigeria inda ta fara aiki asibiti shi kuma ya d'aura kan business d'in mahaifinsu wadda zuwa lokacin rabi kud'inshi ne 50 50 suke tafiya.


Bayan dawowansu da shekara guda mahaifiyarmu ta kuma samun ciki inda a lokaci d'aya suka samu da baba habu ba 'bata lokaci ya fara shige da fice wurin bokaye da malamai akan a tsayar mishi da cikin kar wani abu ya sameshi bakin ciki yake In yaga ya mujeeb da ya majeed, cikin sa'a cikin ya zauna har lokacin haihuwa kwana d'aya tsakanin haihuwansu mahaifiyarmu ta samu Abdulhameed su kuma suka samu Isma'il.


Hmmm a lokacin baba sale ya kara haihuwa inda baba haladu ma ya samu mace familyn se kara girma yake yayinda kullum ake turawa hajja abinci daga kowane side inda In har Mama ta tura Nata har tururwan ci ake sbd yadda ta iya sossai, Sannan kyautan da take yiwa hajja duk cikin matan ba me mata, da gayya baba yake tura Isma'il wurin su ya hameed tun basu sakin jiki sbd yadda yake hantararsu har suka sake hameed ya shaku da Isma'il duk wani abinda Abba ze yiwa su yaya hameed to haka ze yiwa sauran yaran gidan sede idan mamace ta ga dama ta sayawa yaranta abu da kud'inta.


Wadda nan ma in sun gani se su d'auka Abba ne yake banbanta yaran, bayan ya hameed Mama na da cikin ya fadila Allah ya kar'bi ran baba megari mutuwar da ya girgiza ahalin, sede ba yadda suka iya dole sukayi tawakalli suka fawallawa Allah a lokacin an kusa auren Mama sadiya wato maman katsina, hajja ce ta nemi a raba gado aba kowa nashi sbd sanin halin yaran nata da aka zo rabon gadon kuwa seda aka Samu matsala gani sukayi an raba arziki biyu an bawa Abba d'aya kan aka fara maganan rabon rabin kuma har da Abban.


Nan suka dire sukace ba'a isa ba seda hajja ta tsaya alkali ya nuna musu shedu tabbas halalin mahaifinmu ne dukda haka gani suke hajja ma son kai tayi ta yarda aka bawa mahaifinmu rabin dukiyan, aka raba musu rabi, nan sukayi shawaran komawa karatu tsakaninsu su uku inda suka koma kuwa baba habu diploma yayinda baba sale da baba haladu NCE.


Bayan rasuwar baba da wata hud'u Mama ta haifi yaya fadila a lokacin bukin Mama sadiya ya taso inda Abba ya buge zana da ya zagaye gidan yayi ginin bulo ya zagaye yayi penti ya saka musu katon gate, aka sha buki aka kaita katsina shi yayi mata kayan d'aki gabadaya, inda hajja ta kara ganin kiman Abban mu sbd ya nuna ko bayan rasuwar mahaifinsu ze iya kula da en uwanshi a matsayin uba.


Yaran duka makaranta d'aya suke zuwa kuma Abba ne ke biya musu kud'in makarantar dukda haka basu gani ba, bayan ya fadila Mama ta kuma haifan ya meena, da shekara d'aya ta haifeni inda ta sha matukar wahala daga nan ta juya mahaifanta, suka d'auki son duniya suka d'auramin gashi naci sunan hajja, itama minti minti zatazo neman takwaranta.


Wadda ni kuma ban sani ba ashe sunfi tsanata kan duk en gidanmu wadda na rasa dalili tun fara wayau na na san basa sona sede kuma munyi matukar shakuwa asalin shakuwa da Ismail da ya hameed sbd shakuwarmu dashi yasa yaya hameed ke cemin bestynah, shi kuma Ismail ke kirana baby, duk abinda Isma'il yaci to fa nima se na ci shi haka duk abinda naci se ya ci.


A makaranta duk wadda ya ta'bani se ya ramamin ba ajin da baya fad'a da mazan har seniors akaina, duk wani taurin kai irin na maza ni kuwa na iya shi yayinda shakuwa tsakanina da en Uwana mata daban yake, a haka muka tashi wata rana yaya majeed ya bugeni sbd na 'bata mishi zanenshi da colors da ba su yayi niyyan sawa ba.


Da gudu na nufi side d'in baba habu don in fad'awa ya Ismail d'ina ya ramamin kan na shiga naji baba habu na ce mishi "shiyasa nake sonka d'ana kayi yadda na sakaka karka kuskure kan komai sena koya musu hankali dani ake zancen" ban maida hankali ba na shige da Sauri ya mike yace "baby wa ya bugeki?" Cikin kuka nace "ya majeed" da sauri ya kama hannuna muka fice zuwa side d'inmu ya kuwa samu majeed suka fara fad'a, har jimishi ciwo yayi a goshi Abba ne yazo ya raba fad'an ya kuwa zaneni akan ni na jawo fad'an inda sbd dukanan da yayi min Isma'il ya dena zuwa side d'inmu seda mama tayi bikonshi.


Duk gidajen akwai sa'annina mata sadiya kanwar ya Ismail, Hafsat, Zainab sede duk ba'a nuna musu irin son da ake min sanan na fi su wayau da son mutane da farin jini dukda class d'inmu d'aya amma ko a school ba wadda ake son kawance dashi kaman ni wadda hakan ke basu haushi suke zuwa suke cewa iyayensu Ai anfi so nane sbd ana cewa babanmu yafi kud'i a gidan.


Da wayau mu akayi auren Mama rakiya aka kaita jigawa, a haka na tashi ban san babu ba ga dariya da wasa en uwana da iyayena suna matukar sona kawata mace d'aya mujeebatu makwabciyarmu kuma class mate d'inmu babansu sossai yafi namu kud'i kowa na son kawance da ita yayinda ita kuwa take matukar sona tun bana kula kawancemu har nake kulata inda mukayi makaranta tare har secondary a lokacin su yaya mujeeb duk sun gama inda ya mujeeb ya tafi waje ya fara law, ya majeed ya kasance architecture ya hameed ya d'auki business yayinda Isma'il ya tafi islamic sbd ya kasance ustaz ustaz a hankali soyayya ta fara shiga tsakaninmu sbd irin shakuwarmu har a waje da ya tafi kullum se munyi waya komai nawa ya sani na san nashi har fara period d'ina shi ya fara sani.


Ashe ashe duk wannan abinda ya Ismail ke min ba tsakani da Allah bane don wani manufa ne nashi ashe kaddarana na jone da rayuwarshi, ashe shine sanadiyar duk wani bakin cikina na rayuwa wadda a da ban san menene bakin ciki ba.


*two pages ne nan ayi ta hakuri dani🙏*
                     🖤Gureenjoh🖤


      🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇

*Baya Chanza d'and'anon teku*


  *Fatima Muhammad Gurin*

  **Gureenjo6763 on Wattpad**


     'Yar Mutan Adamawa


   *P26*


A hankali soyayya me karfi ta shiga tsakaninmu da ya Isma'il wani irin so da bazan iya misaltashi ba, ya min sabo da kanshi ko wani lokaci muna tare a chat, WhatsApp call ko video call, komai d'inmu ya zama d'aya har su ya fadila Suna jin haushin irin wannan soyayyar da mukeyi, Mama bata ta'ba nuna min tana so ko bata so ba tunda a lokacin nayi nisa ko ta fad'a ba ji zanyi ba mutumin da muka tashi tare dashi nayi wayau.


Wata hutu da suka ta'ba dawowa wadda bazan ta'ba mantawa dashi ba, randa akace yau suna hanya ban samu kaina ba abinci nayi musu ko ince sbd shi nayi abinci kusan kala biyar da drinks homemade da na kampani, duk a side d'in Hajja na zage na sha wannan uban aiki tana kara min karfin gwiwa don tafi kowa jin daad'in tarrayarmu, bayan na gama na shiga toilet d'inta na tsala wanka da na kusan awa, na fito Shiri ma zama na musamman na mishi na tsala kwalliya ta da sabuwar material da mama ta mana, duk abinda yasa nake hakan sbd wannan ne had'uwanmu na farko tunda muka fara soyayya.


Na kasa zaune na kasa tsaye tsabagen zumud'i ban huta ba seda naji karan shigowan motocin da suka je tarbarsu, zama kawai nayi kan kujeran hajja hannuna dafe da kirji sbd tsananin bugu,  chan bayan kusan mintuna 15 da isowarsu naji sakon shigowar massage wayata dubawa nayi se naga shine, murmushi na saki ganin ya rubuto "where are yhu?" Ba 'bata lokaci na tura mishi "side d'in hajja" beyi reply ba, kaman 5mins naji an turo kofa da sauri na mike Ina kallonshi bakina ya Gaza Rufuwa dukda kunyanshi da ya kusa nitsar dani.+


Ban hankara ba se ji nayi ya rungumeni, cike da zullumi na zame Ina dukar da kaina yace "come on babe, menene haka? Shekara nawa rabon da na ganki shine zaki hanani pleasuren rungumarki?" Murmushi na saki nace "welcome home, ba wai na zame bane sbd wani abu na zame ne sbd be dace ka rungumeni ba a musulunce if you wanna have me all for yourself then marry me" na karasa Ina sakar mishi murmushi, 'bata fuska ya d'anyi kan yace "not now yanzu me kika tanadarmin?" Kallon dining nayi nace "abinci gasu chan all your favorites" ido d'aya ya kashe yace "only food?" Kau da kaina nayi ina nufan dining nace "lemme call su ya hameed suzo kar su ce ma zasu ci abincin Mama".


Kiransu nayi ina kallon Isma'il da ko kuma glancing inda nake be yi ba, he was busy taping his phone, har su ya hameed suka shigo be kara cemin komai ba dukda son ya fara min magana da nake ji amma aji irin na mace irina a lokacin da nake ji da kyau samari goma se sunyi sallama dani biyu basuyi da ya fadila ba bare ya meena, da kaina nayi serving kowa muka fara ci ba muyi nisa ba su sadiya da su ya fadila suka shigo sukayi joining nan hira ya 'barke sede ni na kasa maida hankali kan hirar sbd ganin gabad'aya hankalin Isma'il be kaina kaman da se kan waya.


Da gayya na fara tari kaman na kware duk yayyuna suka fara min sannu ya meena na zuba min ruwa a cup kurba nayi ina kallonshi sau d'aya ya kalleni ya d'auke kai ajiyar xuciya na sauke a raina na furta 'to kode fushi yakeyi dani don ban rungumeshi bane?' A sanyaye ta karasa cin abincin, bayan mun kammalla muka dawo parlorn hajja aka bud'e wani sabon hirar su ya fadila se tambayansu yadda kasan waje yake suke su kuma suna basu amsa cike da kewa yayinda ni kuma nayi Shiru na shiga duniyar tunani.


Tunani nake ko ya Isma'il yayi wata budurwarne yasa yake shareni gabad'aya ya addabeni, ko ya dena sona ne? Ko laifi na mishi ne? Duk ni kad'ai baby" naji ya ambata da sauri na kalleshi yace "zo ki kar'bi tsarabarki" ya mike ya hameed yace "ba wani tsaraba kace kana bukatar space da masoyiyarka mu kuma munzo mun takura maka" duk dariya aka d'auka banda Ismail da tuni ya fice da sauri na bishi cike sa kunya.


Tafiya muke side to side sede ba abinda ya ce min gajiya nayi da shirun nace "bae me nayi maka ne?" Yace "me kika gani?" Nace "naga tunda naki ka rungumeni kake fushi baka sake kulani ba after all ba haka muke da ba, ko kayi wata buduruwa ne ka dena sona?" Wani irin murmushi ya saki muna shiga room d'inshi dake side d'insu ya riko hannuna duk yadda nake so in kwace tunanin kar ya kuma fushi dani ya hana, yana kallon tsakiyar idona yace.


"Me kike tunani ne baby? Zan dinga binki duk inda kikayi ne kaman da? Yanzu fa ba da bane sannan kai ya waye moreover waje nake karatu ina ganin en mata masu kyau da class da suka dameki wayewa ban rungumesu ba sbd ke na tako na zo gareki kuma kina neman watsa min kasa a ido?" Raurau nayi da idanu nace "to Ai naga be dace bane wannan ba shine tarbiyarmu da al'adarmu ba" yace "enough baby in bazaki iya soyayya dani irin na zamani ba ba dole I have dozens of girls da suke bina a kullum, ga tsarabarki chan I need some space" d'auka nayi nace "na gode" a sanyaye na fice Don bazan iya abinda yake so ba har ga Allah bazan ci amanan iyayena ba.


'Dakinmu nayi a nan na samu ya fadila da ya meena har sun shigo, ya meena na kar'bar trolleyn da na shigo dashi a sunan tsarabata tace "har kun gama zancen?" Ya fadila na zama gefen ya meena dake bud'e trolleyn tace "eye masoya ba duk wannan tsarabarce?" Dogayen rigunane masu kyau da tsada guda hud'u se sneakers na mata biyu se turaruka da chocolates jibgi duk irin waenda nake so ne.


Dukda hankalina be kan tsarabar sede sunyi matukar burgeni se naji kaman Ina jin tausayin shi me laifinshi don yace yana so muyi soyayya irin na zamani? Cire kokonto nayi nace "guys Ina da damuwa" duk kallona sukayi ya meena Tace "me ya faru lil?" Dayake haka suke cemin, nace "ni da ya Isma'il ne" na sauke ajiyar zuciya ya Fadeelah ta dafa ni tace "what happened?" Nace "so yake muyi soyayya irin na zamani soyayyar shan minti" ya meena ta zaro ido tace "what??? Lil Anya kuwa kinji da kyau? Ya Isma'il fah? Bawan Allah da magana ma bata dame shi ba" zanyi magana ya Fadeelah tace "ah gaskiya lil inaga bakiji da kyau ba ko jikina duk kunnuwane bazan yarda ba Anya bayan su mama akwai me miki son Isma'il? Karkiyi wasa da damanki".


Shiru nayi bazasu gane ba sbd ko zan kwana fad'a kowa ya san ba haka halinshi yake ba, turo kofanmu da akayi yasa duk muka d'aga kai Mama ce ta shigo tana mikawa ya fadila kud'i Tace "ku tashi ku sayomin atampopi uku a suraj plaza yanzu pls akwai abinda zanyi dashi" har zata juya taga trolleyn tace "Ina kuka samu wannan kuma?" Nayi saurin cewa "dama yanzu zan kai miki ki gani ya Isma'il ne ya kawomin tsarabar" girgiza kai tayi tace "an gode" tana ficewa a sanyaye nacewa su ya meena "ku d'auki rigunan d'ai d'ai da chocolates d'in" ihun murna sukayi suna godiya sbd rigunan sun had'u nan aka shashantar da maganan da na kawo musun.


Suka shirya suka fito driver ya d'aukesu se suraj plaza, suna shiga inda idanuna suka fara sauka shine ice cream spot d'insu da sauri nace "ya fadeela" tsayawa sukayi suna kallona ganin yadda nayi puppy face yasa ya meena tace "eherrmm ya fadeela kinga ta kanki" dariya mukayi gabad'aya nace "ba wani taga ta kanta please mu saya ice cream kan mu je wurin atamphar please please".


Ta kalli wurin ice cream d'in ta kuma kallon kofan store d'in tace "amma kin san mama ta hanaki shaye shayen zakin nan kam ko?" Ya meena da itama taji kwadayin ice cream d'in tace "kin san yanzu In ba muje ba mun shiga uku da mita" Tace "to shikenan muje" zuwa mukayi kowacce ta za'bi flavourn da take so kusan five scoops aka saka mini waje guda se lashe baki nake sbd Ina son abun zaki sossai.


Naki sam a had'amin Leda d'aya da nasu nawa kad'ai na rike sbd sanin halina, rike da abata muka shiga cikin store d'in mukayi wurin atampopi suna tsaye suna aikin za'ba ni kuwa na zaga wajajen turaruka mutanena ina duba wani turare being together, ganin ban samu ba yasa na bud'e ice cream d'ita a wurin a hankali nace "bari In sha kad'an don miyau na se tsinkewa yake" diba nayi na sha Ina lumshe ido.


Na kuma diba na sha idanuna lumshe na juya da nufin komawa wurin su ya meena se ji nayi nayi bumping into mutum mun buge sossai yadda ice cream d'ina dake bud'e yayi splitting up gabad'aya se jikinshi ni a nawa wautan ba ta jikinshi ko bugeshi nake ba se ta ice cream d'ina ganin ba wani abinda ya saura yasa na fara hawaye, kallon mamaki yake min kan ya furta "seriously!!" Cikin mamaki.


"Baiwar Allah ki bugeni ki min staining kayana kuma kece me kuka?? Unbelievable!!" Ya furta yana smirking, Harara na banka mishi nace "Allah se ka biyani ice cream d'ina ka san da yadda ya fadeela ta sayamin?" Na karasa a shagwa'be dariya ya fara har yanzu cikin mamaki, girgiza kai yayi ya bi ta gefena ze wuce ban san sadda na riko hannunshi ba chak ya tsaya a hankali ya kalli hannun nawa da ya rike nashi ya d'ago ya kalleni da sauri na sake shi Ina cewa "Allah in ban sha ice cream d'innan ba ka d'auki alhakina kuma se Allah ya sakamin" girgiza kai yayi yace "muje in saya miki but with one condition" nace "what?" Ina mishi kallon renin sense.


Murmushi yayi yana zaro phone d'inshi yace "ur digits" ni a ganina ba komai bane so na sakamishi ya cire handkerchief fara sol yana share inda na 'bata mishi muka jera zuwa wajen shagon muka shige ice cream spot d'in ba tare da ya kalli me sakawan ba yace "saka mata all the flavors you have here" da sauri na kalleshi ba tare da ya maida hankali ya kalleni ba yace "shikenan? Then bye" da sauri nace "tsaya tsaya ni fa ba wawiya bace in da gaske kake ka jira a damkamin a hannu na kan ka tafi" murmushi yayi yau ya ga abin mamaki.


Tsayawa yayi seda aka gama zuba mani aka sa min a leda aka mika min na kar'ba kan na saki murmushi ina kallonshi zare manyan idanunshi yayi yace "zan iya tafiya yanzu?" Be jira amsana ba ya juya ya fice da sauri na bishi Don mishi godiya se naji su ya meena suna min magana "shaati Ina kika shiga tun d'azu muke nemanki?" Dayake be yi wani nisa ba Sarai ya ji se ya murmusa ya furta shaati 'Aisha' yana karasawa wurin motanshi ya bud'e ya shige yana ja.


Ya meena tace "lil me ya had'aku da wannan handsome d'in? Kinga kyaun shi?" Dariya nayi nace "ice cream na ya zubar shine ya biyani" na karasa Ina d'aga musu ledan da mamaki suke kallona suka kuma kalli motanshi gaba nayi abina zuwa motanmu na shige suka zo suka shiga a takaice har muka isa gida magananshi be bar bakinsu ba se kurantashi suke ni kuwa ko a jikina haka muka karasa gida.


Bayan kwana biyu


Har kawo yau ya Isma'il be sakemin ba sbd naki bashi had'in kai yayinda ni kuwa nake makale mishi duk da yadda yake dizgani har fad'a seda mama tamin wani ranar da ya kusa dukana tsabar fad'a wai Don garin saurin kawo mishi zobo na 'barar mishi a jiki, sossai Mama ta min fad'a har take cewa a haka bana kama kaina nake son in ya aureni ya mutuntani namiji ne fah!! Kuka nayi tayi ta kyaleni tayi tafiyanta, Ina kwance Ina aikin kukana naji wayana na ringing d'auka nayi ganin number na makala a kunne ba tare da na bar kukana ba se ji nayi ance "cry cry ke baki gajiya da kuka?".


Baki na tura nace "and who are yhu? Yaushe da yaushe kaga nayi kuka fi sabilillahi?" Murmushi yayi har ina jin sautinshi yace "and again wannan bakin Baya gajiya da tsiwa?" Cewa nayi "a Ina ka samu digits d'ina?" Yace "ke kika ban in exchange of ice cream" Wara idanu nayi nace "ohh ice cream man" dariya yayi yana cewa shima "ohh ice cream girl" dariya mukayi a tare yace "Aisha am saifullah shamsuddeen suraj" nace "sunana kuma a Ina ka samu in exchange of what?" Dariya kawai yayi yace ya gaisheni tunda kuka ya kare when ever I feel like crying in kirashi ze min magani, mukayi sallama nayi saving number d'inshi.


Kan na mike na nufi d'akin ya Isma'il na ta bashi hakuri cemin yayi "In har Ina so ya hakura i should write apology latter with my handwriting in kawo mishi, da sauri na koma na rubuto kuwa da kyakyawan handwriting d'ina harda style a rubutun na kawo mishi ya kar'ba yana pecking forehead d'ina da sauri na fice, hmmm ban sani ba ashe wannan lattern shine makami na farko a gareshi Don yakan farin cikin rayuwata da ban san dalilinshi na yin hakan har yanzu ba.                    🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA.....💦🍇

*Baya chanza d'and'anon teku*


     *Fatima Muhammad Gurin*

   *Gureenjo6763 on Wattpad*


         'Yar Mutan Adamawa


   *P27*


Washegari muna zaune muna hira da su ya fadeela parlon mama se ga Abba ya shigo cikin fara'a yace "uwata Albishir" cikin zumud'i nace "Goro Abbana fara kal" yace "result d'inki na nursing school ya fito kinci saura interview" cikin murna na rungume mama Ina tsalle dariya duk suke min suna min congrats don nawa ne ya fara fitowa ya meena na neman kasu yayinda ya fadeela ke neman ABU.


Ranar haka bakina yaki Rufuwa duk wadda muka gamu dashi se na fad'amishi masu taya ni murna nayi, tattaki nayi har d'akin ya Isma'il da fara'a nace "bae result na ya fito kuma naci" cikin tayani murna ya rungumeni sossai a sunan tayani murna da karfi na fisge raina ya fara 'baci da wannan halin nashi, raina a had'e nace "a gaskiya ya Isma'il In haka kake so mu cigaba da rayuwa ni fa bazan iya ba, akan wani daliline zakayi ta ta'ba min jiki? Haka ake soyayyar? Nide gaskiya bazan cigaba da d'aukan wannan hali ba" na juya na fice yana kirana ko waigowa banyi ba.+


Raina 'bace na fad'a kan gadona Ina lumshe ido vibration na wayana yasa na maida hankali kai ganin "Ice cream man" yasa na saki murmushi Ina d'agawa da sallama, Amsawa yayi yana cewa "Da alamu yau ba kuka" cikin dariya nace "yau ba kuka se farin ciki" yace "to a d'an bani nima kad'an nasha" nace "nací exams d'in nursing school saura interview" har ya so fina farin ciki sossai ya min adu'ar samun nasaran interview d'in wadda naji daad'i sossai.


Daga ranar ya maida yamma lokacin kirana kuma In har ya kirani bana kin d'auka wani lokacin ma rike wayan nake a hannu Ina jiran call d'inshi, wasa wasa muka fara shakuwa, bayan kwana biyu da fitowar result d'ina mukayi interview sati tsakani shima ya fito naci, a ranar da kaina na kira Saif ya d'auka yana mamakin yau kuma nice na kirashi sbd ban ta'ba ba, na fad'amishi fitowan result d'in interview kuma naci.


A ranar ya sani kwatan ta mishi gidanmu ze zo haka na kwatantamishi bayan munyi yarjejeniya se na ce yazo kan yazo kar ya zo min bazata, ta 'bangaren ya Isma'il kuwa ganin da gaske nake na shareshi yasa ya kirani garden ya bani hakuri inda muka koma kaman da sede da gaske Ina jan Baya dashi sossai, kuma ya fahimta amma sede ko a fuska yaki nuna min ya sani.


WATA RANAR LARABA


Shiri nake cikin sauri sbd makara da na so yi zan je makaranta yin registration da hanzari na fito Ina cewa Mama se na dawo na fice, driver ne ya d'aukoni yana ajiyeni nace ya tafi In na gama zan kirashi sbd ban san adadin lokutan da Zan d'auka ba so i can't keep him waiting, wata na gani na tambayeta office d'in provost sbd shi Abba yace in samu sunyi magana.


Ta kuwa nunamin naje bayan mun gama duk wani abinda ya kamata na fito Ina duba time 12 yayi ajiyar zuciya na sauke ina kiran layin driver sede be shiga ba, na kuma kira be shiga ba har na fito wajen gate d'in makarantar horn naji anamin kallon wurin nayi se na saki murmushi ganin motan ya Isma'il ne karasawa nayi ina bud'ewa nace "ka taimaka bae ganinka yafi ganin gomna" dariya yayi yana gyara zama rabon da naga dariyarshi haka gareni na manta ban kawo komai ba na shiga.


Ya ja ya fara tafiya ganin bamu d'auki hanyar gida ba yasa na dubeshi nace "se ina kuma?" Yace "wani wuri gininmu da na fara zan nuna miki kin san ina business ko a Uk ban zauna Haka nan ba" murmushi nayi sede ban gamsu ba nace "yaya tun yanzu? Ba'ayi tambaya ba ba'ayi komai ba zaka kaini ganin gida? Ina In za'aje d'inma ya kamata muje da wani ko wata sbd ka san haramcin ke'bantuwan namiji da mace" wani irin kallo yamin da zan iya cewa na hango tsantar tsanata a cikin idanunshi be tanka ba ganin mun fara barin garin kaduna muna shiga wasu wuraren da ma ban ta'ba zuwa ba yasa na fiddo wayana Don kiran Abba ban hankara ba naji ya fisge wayan yana parking wasu maza da zasuyi hud'u suka zo suka bud'e side d'in da nake yunkurin ihu nayi d'aya daga cikinsu yayi saurin sa min wani handkerchief a fuska yana dannawa.


Daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba se bud'e idanuna da nayi na ganni cikin wani gida karami me two bedrooms da parlor se kitchen kwance na ganni kwance kan gadon d'aya daga cikin d'akin da karfi na farka Ina furta "innalillahi wainna ilaihi rajiun, Laila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzaleemin" da sauri na dira daga kan gadon cikin tashin hankali na nufi kofan Ina jijjigawa sede a rufe yake kirib kiran sunan Ismail na fara da karfi.


Be amsani ba yasa na fara ihun a taimakeni ko Allah ze sa wani yaji ya taimakamin sede inaaa ba motsin kowa jakata na duba ban gani ba bare wayana cikin tsananin damuwa nake kuka na rasa yadda zanyi gashi ban san time ba a yanzu, sadakarwa nayi na fad'a toilet dake d'akin nayi alwala nazo na fuskanci inda raina ke rayamin gabas ne na tada sallah, bayan nayi wrapping gyalen doguwar rigana cikin sallahn nayi ta kuka Ina neman taimakon ubangiji ban san me zasu min ba hakan shi yafi komai d'agamin hankali.


Bayan na idar ma kukan naci gaba dayi har naji hawayen idanuna sun kafe, Ina nan zaune naji an murd'a kofa da karfi na mike Ina komawa Baya, Isma'il ne ya shigo cikin kuka nace "na Rokeka da Allah Isma'il ka maida ni gida me na maka? Me yake shirin faruwa? Wani irin laifi na maka da ka za'bi saceni? In ma wasa kakeyi kayi hakuri na tuba duk abinda kake so zan maka In shaa Allah".


Wani irin dariya yayi yana cewa "yaro man kaza wai ke dama kin ta'ba sawa a ranki sonki nake? Ban ta'ba sonki ba a da dana fara baba ya dakatar dani ya bud'emin ido naga masu sona naga marasa sona, yau zan sauke duk wani bakin cikin iyayena wadda mahaifinki ya kunsa musu tun suna kanana har kawo yanzu a kanki, se na lalata miki rayuwa inga kuma waze cigaba da sonki kaman yanzu" a rikice nace "na tuba Isma'il kayi hakuri karka min haka na rokeka ka aureni kan faruwar komai pls ba don ni ba" yana dariya yace "bazan ta'ba aurenki ba In kin sa a ranki ma yarinya ki maza ki cire shi, ban ta'ba sonki ba sede fah Ina son jikin nan" ya karasa yana lashe baki tare da nufo ni.


Ban ta'ba sanin ina da karfi ba se ranan na sa a raina shi shi kad'ai kam karya yake ya keta min haddi ganin Ina ta bashi wahala yasa yayi wata inkiya nan take mazan d'azun suka bayyana shikenan na sa a raina shi kenan kwanana yau ya kare Don na tabbatar In har nufinshi ya cika a kaina ba abinda ze hanani mutuwa, me zanje in cewa Abba da mamah? Da wani idanu zan kuma kallonsu na shiga uku.


Na raya ina fashewa da kuka cikin rashin imani suka d'auremin hannayena da kafafuna a gabansu a gaban maza da sukafi mutum uku marar imanin nan ya keta min haddi ta karfin tuwo cike da mugunta, tunda uwata ta haifeni ban ta'ba riskar azaba irin wannan ba har ranayi ta yau, ashe wannan me d'an sauki ne ban san irin munafurcin da ya had'amin a gida ba da na sani kuwa a daidai lokacin dayake ketamin haddi da nayi yadda nayi na d'auke numfashina gabad'aya a wannan duniya.


Yau ko da duniya gabad'aya zasu taru a kaina da sunan yafewa Isma'il yafiyata ne kad'ai ze yi sanadiyar shiga aljannarshi na rantse bazan iya ba bazan yafemishi ba se Allah ya mana hisabi.


Ta share hawayen fuskanta ba tare da ta iya kallon kowa a parlorn ba ta d'aura da.


A chan gida kuwa zaune ya fadeela take tana kallon film akan gadonta tun tuni take hangan paper kan gadona sede ta d'auka duk cikin credentials d'ina ne na zubar na tafi tana nan zaune mama ta shigo tana cewa "ikon Allah yarinyar nan tuntuni bata dawo ba gashi har an fara kiraye Kirayen magrib ko lafiya?" Ya fadila tace "Mama ki kirata mana" Tace "na kirata wayanta kashe, na kira Abbanku yace Bari ya karaso tukuna Allah dae ya sa lafiya" ya fadila ta amsa da Ameen.


Gadona ta zauna se taji hannunta ya ta'ba paper d'auka tayi ta bud'e se taga handwriting d'ina da farko har zata rufe se taga "Ku Yafemin iyayena" da sauri ta kai kanta farkon sakon "Allah ubangiji yasa bazaku yi fushi dani ba zaku fahimceni yadda ya kamata banyi hakan Don wani abu ba se don ra'ayin kaina, ni Aisha Muhammad a yau na bar gabanku na bar muku rayuwarku na takura na nemawa kaina freedom.


Ba nisa nayi ba Ina cikin kadunan nan sede fah dole inyi chilling na kwana biyu inji ya rayuwar enci yake tunda ku baku kasance masu bani ba, ku yafemin iyayena zan dawo nan kusa kila da tsarabar bariki. Taku har kullum Aish...." Mama bata karasa ba ta yanke jiki ta fad'i ihu fadila ta saka tana kwala kiran Abba, shigowansu kenan da yaran mazan gabad'aya da azama suka shiga d'akin jin yadda fadila ta rikice.


Ya hameed ne yayi saurin fad'awa toilet d'inmu ya d'ibo ruwa ya yayyafa mata se gashi ta ja numfashi se kuka har tana shid'ewa, cikin damuwa duka suke tambayarta lafiya? Papern ta d'auka ta mikawa Abba kar'ba yayi se kuma ya mikawa ya hameed "karanta da karfi" ya furta yana runtse idanu sbd ya san ko menene ba alkhairi bane, tiryan tiryan ya fara karantawa kan ya gama duk sun rikice, tashin hankali karara ya bayyana akan fuskokinsu, tun farawanshi ya mujeeb ke girgiza kai wannan ba Aisha bace ta rubuta baze ta'ba yarda ba.


Be gama tunanin ba yaji Abba na cewa cikin rawar murya "Fadeelah Ashe akwai wani tauye hakki da nake muku ban sani ba? Shine baku ta'ba fad'amin ba? Ashe Ina takura muku?" Da sauri ita da yaya meena suka girgiza kai har suna had'a baki wurin cewa "ko d'aya Abba, Wallahi duk wani abinda 'ya mace zatayi tutiya tana samu daga iyayenta bayanmu ne".


Yace "Ashe Aisha na kawo muku complain shine baku ta'ba fad'amin ba?" Ya meena tace "wallahi Abba bata ta'ba fuskantanmu da irin wannan matsalar ba" ya mujeeb yayi saurin cewa "Abba wannan ba gaskiya bane Aisha bazata iya aikata hakan ba inaga kafin a yank....." "shut up" Abba ya buga mishi tsawa yana fisgo papern daga hannun ya hameed ya mika mishi "wannan rubutun uban waye Abdulmujeeb??" Yayi maganan kaman muryanshi ze d'aga d'akin se kuma ya sassauta "Aisha bazata kashe ni ba, tace zata dawo ko? To Ina me baku umarni ku dinga zama kuna kulamin da gidana matukar kuka ganta cikin gidana ku tabbatar mata kar ta kuskura ta had'a idanu dani ta bar min gida bari na har abada In taki kuwa ku daketa dukan mutuwa ku fitar da gawanta ku jefar bola umarni ne ba shawara ba".


Be kara magana ba ya kama hannun Mama suka fice, cike da damuwa ya mujeeb yace "me hakan kenan? Me ke faruwa?" Ya majeed yace "Lallai Aisha baki kyautawa rayuwarki ba tabbas baza muki bin umarnin Abba ba" ya hameed yace "ni Isma'il nafi tausayawa akan kowa" su ya meena kam se kuka sukeyi sun rasa abinda zasuyi believing.


Se bayan Awanni hud'u na farka a galabaice duk jikina ba inda baya ciwo ji nake kaman ana kwankwantsa duk wani kashi na jikina kuka na fashe dashi rasa makaman dafawa motsi bana iya yi ga salloli da suke kaina la'asar, magrib da isha da na tabbatar yanzu ya wuce jin garin yayi Shiru, hawaye kawai ke gangarawa daga idanuna zuwa cikin kunnena, a lokacin da wadda ya sanni ze ganni baze iya ganeni ba tsabar kumbura.


Ina nan kwance marar imanin ya shigo direct daidai kaina yazo ganin hawaye na fita daga idanuna yace "au ashe kin farka, baby haka kike da sugar ban sani ba? Ai da tun da na Aiwatar da wannan Shiri nawa naci karena ba babbaka ba yanzu ba" shafa fuskata yayi yana kara cewa "kawai ki yarda muyi ta zama a haka kina lasa min zumanki..." be karasa ba na tara miyau na watsa mishi a fuska cikin kuka nace "Azzalumi macuci wallahi se Allah ya sakamin mugu la'ananne" ba sossai muryana ke fita ba sede Sarai ya ji kafanshi ya d'auka sanye da takalmi timberland be saukeshi ko Ina ba se kan kirjina cikin mugunta yasa iya karfinshi ya............


Kuka ne me tsanani ya kwace mata yayinda jidda ta fad'a jikinta tana kuka sossai wani irin muguntane wannan? Hajja da yaya duk kuka suke yayinda baba ya runtse idanunshi yana ji ma iyayenta wannan irin rayuwa da aka jefasu, Shareef kam dama tun da ta kawo inda aka saceta ya saka handkerchief d'insu na sojoji ya rufe fuskanshi har yanzu be bud'e ba.


Seda tayi kuka sossai ta d'aura, "Haka ya cigaba da gana min azaba mugunta iri iri a daren ranar haka na kwana kuka da bakin ciki wallahi wallahi na kasa motsi, se da gari ya waye sanyin Safiya ya busa kan na iya lalla'bawa na mike zaune idanuna sun Bushe sun kankance haka na fad'i kasa da ja da komai na isa toilet d'innan daga zaune na sakewa kaina ruwa na jima nan kan na iya Mikewa nayi wanka Ina had'awa dana sallah da kyar na fito naga an ajiyemin wata doguwar rigar Don na jiya ya gama yagewa an yaye bedsheets d'in sede ba'a shimfid'a wata ba.


Sakawa nayi na tada sallah, Ina idarwa naji an turo kofa Ina d'aga kai naga shine cikin karfin hali irin nawa na mike cikin d'aga murya nace "Isma'il kai la'ananne ne, ya Allah ka nisanci wannan bawa naka daga rahamarka ya Allah, ka hanashi jin daad'i duniya ka munana lahirarsa ya rabbi ka nuna isarka akan wannan bawa naka, Allah ya had'aka da bala'i da masifa, duk abinda yake alkhairi Allah ya hanaka duk abinda yake sharri Allah ya had'aka dashi ya ubangiji ka amsamin wannan adu'a tawa ya rabbi"


Na karasa da tsananin kuka, wani irin dariya ya saki yana girgiza kai yace "dakata bari In yi second round Sannan mazan da kika ganin nan jira suke In gama nawa su kar'ba, a lokacin se kiyi adu'arki da tushe" dukda rashin kwarin jikin da nake fama dashi dukda yunwa da ya kusa hallakani sbd rabona da abinci tun safiyar jiya a haka na wawuri bedside lamb dake d'akin banyi wata wata ba na kwala mishi ban jira ba na kuma kwala mishi ihu yayi yana dafe goshi take jini ya fara fita, da gudu na fito ban tsaya kallon ko akwai mutane parlorn ko babu ba na fito tsakar gidan na bud'e Gate na fice Ina kuka sossai ban tsaya bin titi ba na tabbatar lokaci guda ze kamani se na yanki lunguna da bansan inda nake jefa kafafuna ba na jima ina gudu kan numfashina ya nemi fita Ina kokawa dashi ji nayi ance "baiwar Allah lafiya?" Jinine ke bin kafata se a lokacin naji rad'ad'in da kasata ke min, ban san ya akayi kafafuna suka kasa tsayuwa ba se zubewa da nayi sumammiya.
                    🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇

  *Baya Chanza d'and'anon teku*


     *Fatima Muhammad Gurin*

    *Gureenjo6763 on Wattpad*


          'Yar Mutan Adamawa


*Wannan page d'in naku ne masoyana musamman Gureenjoh Novels group, godiya ba adadi da kulawarku gareni Son so❤️*2


     *28*


Ban san iya adadin lokutan da na d'auka a sume ba na de farka na ganni kan wata taburma a kwance wata tsohuwa na zaune gefena tana min fifita, a razane na mike zaune ina kiran sunan Allah sbd duk a tunanina zan farka na ganni hanun Isma'il, "sannu baiwar Allah, Sannu Allah ya sakamiki" kuka na fashe dashi Ina jin duniyan na min baki Kirin seda nayi kuka me isata kan ta fara bani baki da kyar nayi shiru tace "ga chan ruwan zafi muje In gasaki ko zaki iya?" A lokacin jikina yayi tsananin tsami ko tsayuwa seda ta dafani nayi mukaje toilet d'inta dukda de gidan kam akwai kazanta haka na daure ta min wankan ta gasani ba laifi naji dama dama sede ko ni na san ina bukatan ganin Doctor.+


Wani d'aki ta buge yankwanannen kofar katakon ta shige tana cewa "biyoni nan d'akin 'yatace Bari In nema miki kaya cikin nata" haka ta bincika duk kayan banzan da suke wurin da kyar ta samu jallabiya guda ta bani na saka, tace "na san kina jin yunwa amma wallahi baiwar Allah banda kwandala......" shigowa d'akin da akayi ne ya sasu duk mai da hankali bakin kofan d'akin wata buduruwace ta shigo cikin shigar banza ko arzikin d'ankwali babu da farko nayi tunanin kafurace sbd ba abinda ya banbantata dasu se kuma naji mahaifiyarta tace "zubaidah" suna na biyu da ya gama tarwatsamin rayuwa.


"Inna wace kuma wannan da har zaki bata kayana ta saka ba tare da an tambayeni ba?" Inna cikin lallami tace "wallahi taimakonta nayi fyad'e aka mata inaga ta samu ta tsira daga garesu ne muka gamu kan tayi magana ta fad'i sumammiya kinga yanzu farkawarta wanka kawai tayi shine na nemamata nan kin san bazata iya saka kayana ba".


Shiru zuby tayi tana kallona se kuma ta saki murmushi ban sani ba ko Don taji tausayina ko kuma kyauna ne ya ringayeta don se kallona takeyi tace "sannu" nace "Yauwa" inna tace "zubaidah nace don Allah in da wani abin hannunki ki d'an bamu In sarrafa mata abinci, kin san wanchan bokan uban naki ba bayarwa ze yi ba seda muka kwashi bala'i ma kan farkawar baiwar Allah".


Cikin tsananin mamaki nake kallon wannan family me kenan? Haka wai suke ko kuwa yau ne kad'ai? Haka zubaidah ta bud'e jakanta ta bawa inna kudad'e nan ta fita Don aike, ba zan ta'ba manta karamcin inna a gareni ba dukda abinda 'yarta tayi min wadda har In mutu bazan manta ba, dukda su sun kasancene masu rayuwa kaman dabbobi sbd rashin ilimi da jahilci da ya musu yawa, rayuwa sukeyi kaman tun kan shigowar musulunci.


Kwana na biyu a gidan nan na fahimci mahaifin ma malamin tsubbu ne Sannan tana da yaya wadda be da aiki se shaye shaye ya shigo su d'ibewa juna albarka da mahaifin da mahaifiyar, ganin nan ba gidan zama bane yasa na cewa innar zan tafi sbd na san duk inda iyayena suke hankalinsu a tashe yake, taso rakani sede naki sam don Mama kusan yankani zatayi ta ganni da waennan familyn da jahilci ya musu yawa dukda sun taimaki rayuwata a lokacin da nake cikin halin mutuwa ko rayuwa.


Zuby da take shishigemin lura da ilimi da kuma natsuwa irin ta masu ilimi ga kyau da wayewa da suke tare dani yasa ta kasa barin kusa dani har seda na bata lambar wayana nace In na isa gida zamuyi magana, sallama mukayi ta ban kud'in napep, har bakin titi suka rakoni na Sami abin hawa kan suka koma gida suna me jaddada min In dawo fah, kar In manta dasu.


Ta 'bangaren Saif kuwa ashe tun daga yammacin ranar da ya kira yaji wayana kashe hankalinshi ya d'an fara tashi be shiga damuwa ba se ganin har washegari da safe kuma har yammaci, cikin rashin kuzari da karfin jiki ya nufi kwatancen gidanmu da na mishi, yana isa da Isma'il ya fara had'uwa sukayi musabaha daga bakin gate se yace "pls Aisha nake nema" ya fad'a yana kallon isama'il d'in kai tsaye sbd be saba wata kwana kwana ba.


"Kai bakaji labarin ba kenan? Kana cikin samarin da suke zuwa wurinta?" Kallonshi yayi yana jin kaman ya fara 'bata mishi rai tambaya d'aya ya mishi amma ya kuma mayar mishi da tambayoyi har biyu cikin kuluwa da jin haushin Isma'il da ya rasa dalili yace "pls In tana ciki you should let her know" yace "ta tafi yawon karuwanci yanzu haka ma mahaifiyarta na asibiti a kwance rai hannun Allah" be ida ba Saif ya sauke mishi wani wawan naushi a baki dukda bandage da ya gani zagaye da kanshi take Isma'il yayi niyyan ramawa tuni aka fara taruwa take aka rabasu inda anan Isma'il ya fad'i wurin wadda yazo nan aka fara zancenta wadda daman mutanen unguwan sun kwana sunayi nan take ya fara jin maganganu masu muni a kaina wadda ya nemi juya mishi kwakwalwa sede sam be yarda da zancensu ba taya Aisha zata fara wannan rayuwa kwatsam rana d'aya?.


Ya tambayi kanshi yafi sau nawa driving yake sede har dishi dishi yake gani tsabar yadda kanshi ya d'au zafi, da kyar ya kwana lafiya a ranar number na kuwa ya kira yafi sau abinda yafi sede amsa d'ayace switch off, washegari ya sake komawa nan ma dae ba wani nasara me gadi yace mishi ban dawo ba har yau, ya jima nan kan ya koma gida cikin rasa abin yi ba wani sanina yayi irin chan ciki cikin nan ba sede ya tabbatar a yanayina da tarbiyata bazan ta'ba aikata hakan ba be ma kawo yarda da hakan kusan ranshi ba.


Washegari da safe ya sake komawa anan yaga dawowar su umma daga asibiti ya mujeeb ya nemi gani sbd ganin shine wadda damuwa ke shimfid'e fuskanshi kuma yafi kama dani a waje suka tsaya ya tambayeshi ni nan ya bashi labarin abinda ke faruwa ganin tsantsan damuwa a fuskan Saif d'in, "ko wuka za'a d'auramin a wuyana bazan yarda cewa Aisha zata aikata hakan ba, kuma kuka yarda?"  Ya mujeeb yace "ko kusa ban yarda ba sede ba yadda na iya tunda ga sako da handwriting d'inta" Saif yace "ba wani abin da zamu iya yi Don ganin mun sameta?" Ya mujeeb yace "tabbas da saceta akayi se muyi tunanin nemanta ko ta halin yaya amma tafiya tayi da kafafunta nemanta ze yi wuya, sede mu bar wa Allah komai".


Ajiyar zuciya Saif ya sauke be san ta inda ze fara nema na ba godiya yayiwa ya mujeeb ya tabbatar mishi ze dinga zuwa kullum ko zai samu ta dawo, girgiza kai mujeeb yayi don be yi tsammanin ko ta dawo Abba ze iya hakura ya kyaleta gidan ba, sbd yadda ya d'auki zafi ga mama da taki cewa komai akan hakan se kuka da damuwa, exchanging number sukayi ya fice.


Tunda na sauka a napep wasu makwabtanmu suka fara kallona ban kula su ba na nufi gate d'in mu se naga har nunani da yatsa akeyi gabana na tsananta fad'uwa, tura gate d'in nayi a zabure baba mai gadi ya mike tsaye "uwar masu gida kece?" Gyad'a mishi kai kawai nayi na nufi side d'inmu ina tura gate d'in ganin motoci dayawa daga part d'inmu na tabbatar yayyuna duk suna nan.


Hawaye ne ya gangaromin tuna yanzu fah shikenan rayuwata ta lalace kaman yau na fita da budurcina daga gidan nan gashi yanzu babu shi, me zan cewa mijin da zan aura nan gaba In Ina da rabon auren? Kuka ne ya kwacemin jiki a sanyaye na sa hannu na tura kofar parlorn mu, duk Mikewa sukayi suna kallona har Abba na nan zaune, kallon su hameed yayi yace "me nace muku?" Hameed da majeed suka zare belt a tare cikin tsananin 'bacin rai sbd yadda a cikin gidan ma ba'a barsu ba bare waje ba irin habaici da zage zage da basu ji ba don ma na cikin gidan hajja ta taka musu birki.


Ganin sun nufoni yasa ban iya cewa komai ba se sulalewa da nayi na zauna kasa, me suke nufi? Bazasu tsaya suji daga bakina ba? Shikenan duk abinda zasuyi suyi tunda haka suka za'ba ni kuma bazance komai ba, abu d'aya dani Ina da matukar zuciya da kowa ya sanni da shi har gudunshi en gidanmu suke, tunda na zauna na runtse idanuna cikin tsananin karayar zuciya, Ina jin saukar bulala ko ta Ina na jikina sede na kasa bud'e idanuna bare nayi yunkurin kare kaina.


Dukana sukeyi har na rashin imani wallahi wallahi a lokacin zafin da nakeji cikin zuciyata yafi karfin bulalinsu shiyasa ko motsi na Gaza yi, bakin cikina shikenan Isma'il ya rabani da iyayena ya huta, Mama dake kuka sossai ganin dukan ba na kare bane yasa ta mike tazo ta rungumeni take suka tsaya da dukan, ji na a cikin jikinta yasa na fashe da wata iriyar kuka me ta'ba zuciyar me saurare.


Kuka ne da nakeyinshi daga kasan zuciyata kukan bakin ciki da dana sanin sanin Isma'il a rayuwata, itama kukan takeyi haka ya meena da ya fadeela, Abba ne ya daka mata tsawa cikin 'bacin rai yace "Fatima sake yarinyar nan ki tashi a wurin nan, ki bar yaran nan su cika aikin da na basu Don wallahi yarinyar nan baza ta zauna min gida ba ta tafi chan ta karasa yawon duniyan da ta fara" sakeni Mama tayi ni kuwa naki sakinta, ba wai tsoron bulala ba sede na san tunda Abba ne ya fad'a kuma shikenan.


Da kyar ta kwace hannunta tana kuka ta wuce d'akinta, dukana su ya hameed suka ci gaba dayi yayinda har lokacin ban dena kuka ba, da rarrafe na karasa gaban Abba na rike kafafunshi cikin kuka nace "Abba wallahi wallahi ba yawon karuwanci na tafi yi ba wadda ya fad'a muku hakan karya yakeyi Abba saceni akayi....." cikin fusata ya tsinka min mari daya d'auke ji da ganina na mintuna "shut up!!! Bazan miki baki ba sede fa wallahi se kin bar min gidana bazaki zauna min a gida ba, saceki akayi zaki iya rantsuwar da mutuncinki kika dawo gidan nan?" Kuka ne ya kuma kwacemin Ina girgiza kai bazasu saurari abinda zan fad'a ba? Paper naji an wullo min d'auka nayi na bud'e sak handwriting d'ina wadda ya sa na karance papern daga farko har karshe.


Idanuna na zaro kaman zasu fito waje tsabar kaduwa Ina girgiza kai nace "wallahi wallahi Abba ba ni na rubut......" wani Marin ya saukemin yana nuna min kofa "fita min daga gida" cikin kunan rai nace "Abba bazan iya fita ba sede su kasheni su yarda gawata kaman yadda ka basu umarni" waro ido su ya meena sukayi a da suna jin tausayina sede kaman a ganinsu rashin kunya nayiwa Abba yasa suka fara jin haushina.


Ni kuwa har zuciyata ba da niyyan rashin kunya na fad'i hakan ba se de hakan shine gaskiyata In na fita Ina zanje? Ba wadda na sani se su so duk abinda sukayi min zan d'auka In kashenin sukayi fine kowa ya huta, wani Marin da ya hameed ya d'auke

Ni dashi again se ga bakina na zub da jini dama na Abba ya sa idona ya tara wani jinin, majeed ma d'agawa yayi se muka ji ance "dakata kana saukewa wallahi kai zaka bar min gida, Lallai mamman Ina maka ganin me hankali ashe kaima sha ka tafi ne? Yanzu ba murna zakayi ba yarinyar nan ta tuba ta dawo?".


Na katseta da "wallahi dama chan ba tafiyar nayi da ra'ayin kaina ba kaman yadda kuka gani anan ba ni na rubuta ba" Tace "rufemin baki kan nima na kwad'a miki nawa marin anan, kin ban kunya takwara Ina ganin hankalinki da natsuwarki ashe ba haka bane, kai mamman ka barta" farkon ranan da na ta'ba sani Abba yayiwa hajja musu "hajja kiyi hakuri sede na riga nayi rantsuwa wannan bazata sani kaffara ba, na tsaneta na tsani ganinta Allah se ta barmin gida tunda ba da kud'in karuwancinta na saya ba" salati hajja ta kama ta sauke tana kallonshi da tsananin mamaki Lallai mamman ya d'auka da zafi In tace zata tirsasashi komai ze iya faruwa sbd banzan zuciya irin nashi na d'auko.


Kallon su meena tayi tace "ku je ku d'ibomin duk kayanta zuwa side d'ina, ke tashi mu tafi, ku kuma In kara ganin ko kallon banza kun mata a gidan nan" Mikewa nayi har lokacin kuka me cin rai nakeyi musamman In na tuna Abba ma ya yarda karuwanci na tafi yi har yake dangantani da kalman hakan, a haka nabi bayanta sbd da ita yasa duk wadda muka gamu dashi be ya'bamin magana son ranshi ba har muka isa.


A parlorn ta na zube ina me kuka sossai wace iriyar kaddarace wannan me tsananin muni ba abinda yafi breaking trust d'in iyaye ciwo, sbd baze ta'ba dawowa ba sede nima ba da son raina hakan ya faru ba, kaddarace wadda ba'a sa mata rana, su ya meena ne suka shigo da akwatunana ko kallon inda nake basuyi ba zan musu magana ya fadeela tace "kika min magana wallahi se na kwad'a miki mari, shikenan kin rusa farin ciki da burukanmu kin huta, iyayenmu basu ta'ba fuskantan bakin ciki ba se a akanki, ban ta'ba ji sunyi fad'a ko chachan baki ba se a kanki haka nan duk yadda Abba ke da buri wurin ganin munyi karatu yanzu ya tarwatse yace ya bamu wata biyar mu fidda mazaje sbd tsoron kar mu mishi abinda ke kikayi mishi wallahi se Allah ya saka mnaa wawiya butulu".


Suka fice abinsu kuka naci gaba da yi naga ta kaina, shikenan rayuwata karshenta yazo tabbas, da sauri na mike na shige d'akin hajja tana zaune taga shigowata a fujajan da sauri ta mike zata min magana na fad'a toilet d'inta ganin kaman ba a hayyacina nake ba yasa ta biyoni zare ido tayi tana kurma ihu ganina da kwalban fiya-fiya, dama ita bata yarda da wani maganin sauro ba se shi kuma a nan toilet d'inta take ajiyewa, da karfi ta fisge kwalban tana dubawa tabbas na sha kusan kwata mari ta tsinkamin se gashi na zube kasa a sume bakina na fidda kumfa.
1

                   🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇

*Baya Chanza d'and'anon teku*

  *Fatima Muhammad Gurin*

  **Gureenjo6763 In wattpad**


        'Yar Mutan Adamawa

*P29*


A hankali na fara Wara idanuna da suka min matukar nauyi na kurawa pop d'in inda nake idanu chan na juya a hankali se nayi tozali da fuskan Mama akan tebur d'inta sanye da lab-coat idanunta sanye da farin glass na jima sossai Ina kallonta yadda a lokaci kankani ta rame damuwa tsantsa ya bayyana a kan fuskanta tausayinta ne ya ratsa zuciyata ban san sadda na fara yiwa Isma'il Adu'o'i marasa daad'i ba a raina, kaman ance ta juyo se taga idanuna bud'e suna kallonta da sauri ta mike ta nufoni.


Hannuna ta kama tana zubar da hawaye tace "ashe baki da hankali Aisha? Irin tarbiyar da na miki kenan?" Girgiza kai nayi cikin kuka nace "Mama ya kukeso nayi? An saceni an lalatamin rayuwa na samu na tsira da taimakon Allah na dawo gareku sede kunki yarda dani, mama ashe zaki iya yarda yawon karuwanci na tafi?" Na karasa da kuka sharemin hawaye tayi tace "wa yace miki ban yarda dake ba Aisha? Uhmm ko kowa ze ki ki duniya ki cireni ciki, babu uwar da bata san me ta haifa ba da kuma irin tarbiyar da ta bashi na sani sede shedu sun nuna tafiya kikayi hakan ya sa mahaifinki d'aukan zafi har hakan ta shafeni, na yarda kaddararki kenan Aisha sede a yanzu ba yadda na iya dole in taya mahaifinki nufinshi sbd abubuwan dake kuma faruwa tsakaninmu na saka en uwanki tsananki Aisha ban da yadda zanyi dole ke zaki hakura".+


Mikewa nayi zaune tace "ko mai tsanani Aisha kika sake yunkurin cutar da kanki bazan ta'ba yafe miki ba" nace "kiyi hakuri bazan sake ba" kaina ta shafa tana me Mikewa se ga hajja ta shigo masifa ta hau ni dashi ta inda take shiga ba ta nan take fita ba ban tankata ba haka kuma banyi kuka ba sbd ni yanzu kuma zuciyata ai ta riga ta bushe, babu d'igon hawaye cikinta.


Bayan mama ta sallameni muka wuce gida da hajja d'akinta ta kaini ta kwantar don har lokacin bani da wani kuzari, chan yamma se ga sallaman yaya mujeeb Saif na biye dashi a Baya, hajja tayi musu maraba ganin shi da bako, zama sukayi ya nuna mata Saif yace "hajja wurin Aisha yazo tun tafiyarta kullum se ya zo Toh shine yau da yazo naga kuma ta dawo be kamata in hanashi ganinta ba" hajja tace "sannu bawan Allah ko lafiya kake zuwa kullum nemanta bayan bamu sanka a matsayin maneminta ba?" Murmushi ya saki yace "hajja sonta nake so na tsakani da Allah kuma auren ta zanyi".


Wara idanu sukayi daga hajja har ya mujeeb sukace "so??" Murmushi yayi ganin yadda suka razana yace "ban sani ba ko an mata miji amma wallahi har kasan zuciyata nake son Aisha zan iya zama da ita ko cikin wani irin hali" hajja tace "amma d'annan ka san abinda ke faruwa kuwa?" Yace "na sani a hakan nake sonta na tabbatar bata da laifi a abinda yake faruwa In har zaku tsaya kuji ta bakinta In har kun yarda da ita kenan, ni na yarda da ita duk abinda ta fad'a hakan ne ko da kuwa karyace bare ma na san bazatayi karya ba".


Ha'ba hajja ta dafe tana furta "ikon Allah, ikon gaske" Mikewa tayi tace "bari In turo maka ita dukda bata da lafiya" tayi maganan tana shiga d'akinta Mikewa ya mujeeb yayi ya fice yana cewa "In kun gama Ina waje" murmushi kawai yayi dukda ya mujeeb ze girme mishi amma shi ya d'auke shi kaman aboki, a hankali nake tafiya kaina kasa tun kan na karaso na san ana kallona jin kaifin idanunshi kaina zama nayi ina me kin kallonshi.


"Wannan yanayi be kamaci kyakyawar fuskan nan ba haba sarauniyar mata ke da na sanki da wasa da dariya da kuma tsokana" d'agowa nayi na kalleshi se kawai na fashe da kuka, Mikewa yayi yazo ya tsuguna gabana nasiha ya fara min akan kaddara da kar'barshi Sannan ya min fad'a kan fiya-fiyan da na sha sossai kan ya bi da lallashin fushin da Abba ke yi.


Nan take naji natsuwa ta saukarmin Saif shine mutum na farko da sam yaki yarda zan aikata duk abinda aka ce nayi, nan ya cigaba da kwantar min da hankali be tafi ba seda yaga murmushi kan fuskata wadda ni karan kaina se da nayi mamaki a tunanina bazan kara murmushi ko dariya ba har Abada, a haka hajja ta ci gaba da kula dani yayinda kullum se Saif yazo su ya mujeeb sun koma school da sati biyu na tashi da zazza'bi.


Duk fa zamana wurin hajja har tafiyarsu Allah be yi mun had'u da Isma'il ba dukda ya san na dawo gidan, kullum da safe zanje na gaida Abba da mama sede be ta'ba amsamin ba tsananin fushin da yakeyi dani yasa ko kallon inda nake bayayi kullum se nayi kuka Abba da ya yarda dani sossai ya bani dukkan yarda gashi nayi breaking trust d'inshi dukda ba laifina bane, na tabbatar shima ba daad'i yake ji ba tunda se rama yakeyi a tsaye.


Ganin zazza'bin safen yaki ci yaki cinyewa yasa hajja yiwa Mama magana, nan tace In shirya mu wuce office d'inta tare muna zuwa ta hau dubani a razane naga ta dafa kujera tana zama ganin zata iya fad'uwa taci gaba da tsayuwa idanunta kad'ai sun nuna tsananin razanar da take ciki kallona kawai takeyi ta kasa cewa uffan, Mikewa tayi tace "biyoni" ta fice na bita a baya ganin mun nufi hanyar gida yasa gabana fara fad'uwa meke faruwa? Na tambayi kaina ban gama tsurewa ba se ji nayi ta Kira Abba tace "ka dawo gida akwai matsala".


Muna sauka bata ce min komai ba se kawai na wuce side d'in hajja ashe nan taci gaba da zama seda Abba ya shigo shi ya bud'e mata kofan kafafunta da sukayi matukar sanyi suka kasa d'aukarta se dafe Abba da tayi zasu nufi side d'inmu tace "a'a muje side d'in hajja" side d'in hajja suka nufa suna shiga parlorn ta samu wuri ta zauna tana sauke ajiyar zuciya cikin damuwa yace "Fatima menene wai?" Ajiyar zuciya ta sauke kan tace "ciki ne da ita" cikin rud'ani yace "wa kenan?" Tace "Aisha" a zabure ya mike yana kwala kiran sunanta.


Rana na farko kenan da naji yana kiran sunana haka da sauri na mike na fito ban kai ga magana ba naji Abba ya rufe ni da duka banda ranar da ya mareni yau ne rana na farko da na san Abba na dukan d'iyarshi ko mace ko namji ihu nake Ina neman agaji Don alamu sun nuna bashi da hankali da natsuwa a tare dashi dukan cikina kawai yake yana harbi da kafa yana fad'in In fad'amishi uban waye ya min ciki.


Hajja bata gidan tana makwabta tsinko zogala Don shi nace mata nake son ci In na dawo gashi na gidanmu yayi tsutsa shine taje makota nema, a dukan da yake min ne da maganganun da yake furtawa yasa na gane ciki ne da ni nan na fara kare cikin kar wani abu ya sameshi sbd bazan ta'ba yafewa kaina ba In har na bari Abba ya cutar da abunda be ji ba be gani ba.


Duk sauran mutan gidan sun taru a makeken parlorn hajja ana kallon ikon Allah ba wadda yayi yunkurin cetona, Mama kam ta toshe baki tare da runtse idanu se kuka takeyi, wani wawan naushi da Abba ya kawowa cikina, cikin zafin nama naji an kareni ya sauka a jikin wadda ya karenin duk en parlorn kallonshi sukeyi Suna mamakin shi kuma daga ina.


Kanshi ya dukar kasa cikin raunin murya yace "Abba kayi hakuri ka dena dukanta Haka" ashe tunda Abba ya fara dukana ya shigo dayake ya saba ko ince hajja ta sabar mishi In har yazo ba wani bakunta side dinta yake wucewa direct yayi zaman shi parlor su sha hira In na fito In tayasu In ban fito ba ta gaji ta shiga ta koroni waje, "waye kai? Waya baka Damar shigomin gida har zuwa nan cikin parlorn mahaifiyata?" Saif ze yi magana hajja ta amsa da "nice nan na bashi wannan dama In kuma ban isa bane se ka fad'amin, wai kai Mamman meke damu ka ne? Se akace kaddara baze fad'a kan erka ba? Toh duk ku munafakan nan ku samu wuri ku zauna zanyi gargad'in karshe.


Kowa zama yayi tayi fad'a sossai akan suna gani Abba na kokarin illati bazasu kwaceni ba, ta juyo kan mama itama ta sulle ta tas akan ta zauna biyayya tana ji tana gani ta san erta ta bari ana cutar da ita ta kuwa koma kan Abba ta tabbatar mishi wallahi ya kara dukana bare barazanar zubar da cikin jikina tsinuwace zata had'asu, har a lokacin Saif be tashi daga durkushen da yake gabana ba ji yake Ina ma ni matarshi ce a lokacin, Don kuka nakeyi cikin tashin hankali.


Magana ya fara "Abba ka min alfarma d'aya ka taimaka ka bar min ita gidanka har zuwa haihuwanta da akwai dama da na aureta a yanzu sede ba yadda za'ayi In aureta a haka, amma wallahi wallahi Ina kaunarta har abinda ke cikinta zan rike a matsayin nawa na har Abada" kuka Mama ta fashe dashi Lallai Allah kenan wato Allah shi ke yadda yaso a lokacin da ya so wa ze ki Saif yaro kyakyawa ajin karshe ga alamun kud'i da ilimi ita bata ta'ba kawowa Aisha zata samu miji ba har Abada.


Abba karan kanshi mamakin Saif yake yayinda ni kuwa a Sannan wani masifaffen soyayyarshi ta shiga zuciyata, ya ma Abba alkawari Ina haihuwa ze aureni da yardar Allah en gidan suka fara tayar da maganganu kowa na mamakin Saif wasu na jin haushinshi, yayinda en matan gidan dama suka mutu a kanshi, Abba ya dubeni "ke ki fad'amin waye uban d'annan?" Duk ido suka zuba min kowa na son ji.


Cikin disashewar murya nace "Isma'il....." Ai ban ajiye ba uwarshi da baba habu suka hau masifa da bala'i shi karan kanshi Abba be yarda ba, yayinda mama ta san tabbas tunda na fad'a hakan ne, a nan kam hajja bata goyamin baya ba sbd sanin waye Isma'il a zahiri basu san bad'inin shi ba kowa Mikewa yayi ya fita suna ta sakin maganganu, Saif ma ya mike ya sallamesu yana me neman izinin turo iyayenshi Abba yace ya dakata tukuna ze nemeshi Sannan be hanashi zuwa wurina ba.


Bayan fitansu hajja ta mike ta shige kitchen don kwad'anta min zogalen, nan Abba ya dubeni yace "Ina saurarenki, kin san zaki mutu ki kwanta kabarinki daga ke se halinki, karki mana karya gani ni da mahaifiyarki ki bamu labarin abinda bamu sani ba tsakaninki da Allah, Allah na kallon ki" har raina naji daad'i da Abba ya yi niyyar saurarata a hankali na fara basu labarin abinda ya faru ina kai aya se ga Abba na share hawaye sossai jikinmu duka yayi sanyi nasiha ya min dukda har lokacin be sake ba sbd ba wani hujja da ze nuna hakan gaskiyatace na fad'a.


Kama Mama yayi suka fice, na mike na koma d'akin hajja, anan naci gaba da rayuwa ina rainon cikin da taimakon Saif kaman shine uban cikin soyayyar da yake nunamin yasa kwata kwata In ka ganni se ka d'auka cikin na sunnah ne, kullum ze zo da Leda kayan makulashe ba de ince Ina bukatar abu kaza ba ko a wasa se ya kawo dozen d'inshi, soyayya mukeyi ban sa damuwar kowa a zuciyata ba su ya meena ma sun fitar da mazajensu har an saka buki kan haihuwata sbd Abba yayi ranstuwar ficika baze kashe a aure na ba bayan kayan d'aki daga an d'aura aure za'a mika ni.


Kwata kwata ban damu ba karatu na ne kawai yake min zafi In na tuna na gama kenan har Abada Don Saif ma be bani wani goyon bayan karatu ba, cikina na wata bakwai aka sha bukin en matan gidanmu shidda, yayinda na sha habaici har na zube jinina ya hau Mama da Saif ne suka dage min se hajja har ya koma normal daidai de na masu ciki, Ina shiga watan haihuwana mahaifin Saif yazo malam mutum me karamci da dattako.


Saif be 'boye mishi komai game dani ba se ga malam har side din hajja ya min nasiha sossai ya kuma tabbatar min inda ranshi da yardar Allah se na auri Saif, Abba da hajja da mama sunji daad'in wannan al'amari sossai, randa na fara labour Saif ya fara sani dayake muna waya abun ya taso min kashewa yayi ya kira Mama ya sanar mata se gata hajja na bacci kawai taji mama na tambayar Ina ina wai Ina labour se gasu cikin d'akin nan mukayi asibiti muna isa Saif na isa.


A hannun Mama na haihu inda na haihu lafiya kalau, Abba da kanshi ya zo asibitin ya kar'bi yarinyar sonta da tausayinta na shiga ranshi nan ya mikama Saif akan ya mata hud'uba kar'barta yayi yayi mata hud'uba da khadija inda ya mikawa hajja yana cewa "Allah ya raya khadija(Arwa)" awata 24 aka sallamemu se gida cikin yayyuna ba wacce tazo sbd a lokacin tsanata yayi kamari a ransu, ranan suna saif, malam da Abba duk suka kawo raguna masu lafiya aka yanka mata duk wani abu da hajja ta san me jego zata bukata na kulawa ta bani.


Saif ya min hidima har na ba gobe ya kaunaceni da Arwa kaman ba gobe, ashe ban sani ba ta wurin mahaifiyarshi da en uwarshi ba auren suke so ba, yakumbo ta tada bala'i sossai seda malam ya mata jan ido dukda haka ta d'auki zafi da Saif sossai a takaice har gida tazo taci mana mutunci ba wadda ya tankata, fitana daga jinin haihuwa da kwana goma aka d'aura aurena da Saif.


Na sha kukan rabuwa da gidanmu da iyayena da har lokacin basu sakemin kaman da ba, bama kaman Abba randa za'a kaini Abba ya hana kowa zuwa da kanshi ya tukani hajja na baya rike da arwa Ina gaba ya kaini har tsakiyar parlor na kan ya fara magana "Uwata na fita hakkinki dukda ke bakiyi kokarin sauke mana namu hakkin a matsayin iyayenki ba na shayar dake, tufatar dake, ciyar dake, baki ilimi na boko da arabi, amma ba abinda kika saka mana dashi se bakin ciki da dana sani, Uwata kinyi matukar sa'a kin samu Saif a matsayin wadda yake sonki so na gaskiya, In kin ga dama ki zauna In kin ga dama ki fita amma ki sani duk randa kika kuskura kika fita daga gidannan da sunan yaji ko saki ba gidana ba kuma ba na en uwana ba, bakin cikin da kika kunsa mana a baya kad'ai ya ishemu, na barki lafiya".


Tunda suka fice nake zaman jiran Saif chan kuwa se gashi ya shigo da farin cikinshi na samuna yayinda ni kuwa bakin ciki ne fal raina na rashin kawo mishi abinda kowacce amarya buduruwa ke kaiwa gidan mijinta, wadda shine ze kankaro mata mutunci da kima a idon mijin, daga ranar duk wata kulawa muna samunshi daga wurin Saif har na haifi yasmin wacce taci sunan mahaifiyarshi Aisha.


Kullum se yakumbo ta zo taci mutuncina cikin ikon Allah ban ta'ba d'aga ido na kalleta ba, bayan na haifi sameer malam ya rasu mun shiga tashin hankali sossai sbd malam mutum ne wadda ba iyalanshi kad'ai ba duniya gabad'aya suka ji mutuwanshi, fitinan yakumbo se gaba yayi ba baya ba ta takuramin fiye da tunani sede bazan iya ko da mata kallon banza bane sbd ta haifi Saif, Saif kuwa shine farin cikin rayuwata da komai na.


Daga nan ta d'aura da rayuwarta har haihuwar neeha da samun cikinta, auren Saif da zubaidah rabasu da Saif se had'uwarsu da Shareef, tana ajiye numfashi duk suka ajiye suma shareef be ce komai ba ya mike ya fita, Baba ne ya kara mata nasihan rayuwa cike da tausayawa ya tabbatar mata tana kara samun sauki ze mata wani kafi a jikinta ba na asiri ba da adu'o'i yadda asiri kuma yayi karyar kuma kamata. Godiya ta mishi ya mike ya fice su jidda da Yaya suma suka kuma bata baki da hakuri.

                   🖤Gureenjoh🖤

🍇💦RUWAN SAMA......💦🍇
  *Baya Chanza d'and'anon teku*

     *Fatima Muhammad Gurin*
   **Gureenjo6763 on Wattpad**

          'Yar Mutan Adamawa

*wannan page d'in naku ne masoya wannan littafi na Ruwan sama.... Ina ganin comments d'inku da adu'o'inku na gode kwarai Allah ya saka da alkhairi, Yauwa Ina so kowa ya fito ya fad'i ra'ayinshi a kan Baba da d'iyarshi Zuby? Me kuke tunani makomarsu ze zama nan duniya?🤔 In Allah ya kaimu gobe zaku samu update sbd ido yayi sauki sossai na gode🥰*
7
    *P30*

Kwance yake idanunshi a lumshe chan kasan zuciyarshi wani bala'in kewa yake ji yana addabarshi ya rame gabad'aya kaman ba Saif me ji da gayu da kud'i ba, me kud'i ne na karan kanshi Don tun kan ya fara aiki da NNPC yake business d'inshi yazo kuma shekarunshi kusan 10 yana aiki dasu, kasancewar shi graduate of 1st class B.Sc Human Resources gashi da gaskiya da amana yasa a ko da yaushe cikin kuma Kara mishi matsayi ake.+

Ga kud'in amma yanzu be da abinda ze yi dashi sede zubaidah tayi ta facakanta, en uwanshi ya manta dasu haka mahaifiyarshi, talakawan da a kullum damuwarsu shine nashi yanzu duk babu, yayi duhu sossai se kuma zuby ta fara ganin ya mata local sbd rabon da ya chanza mota irin wacce ake yayi ma tun suna zaman lafiya da matar sonshi, dukda GLK gareshi C350, amma bayan shi an fitar da dayawa sabbin designs da models, amma yaki saya gani take kaman ayi ta ganin shi da mota d'aya ma raini ne, dukda ta san yana da wasu biyu a kd banda na shaati da kuma na kai yara makaranta.

haka tayi tayi dashi su bar kasar yaki se zamansu ya koma kawai kowa zaman shi yake baya nemanta se itace in tana da bukatarshi ta nemeshi, zaman su ba armashi sam d'an soyayyar da take hange yake zubawa shaati ko d'igo bata gani, ita de zama take amma ba wai jin daad'i takeyi ba In aka cire 'bangaren kud'i.

*******

Ta 'bangaren Arwa yanzu ta samu sauki sossai ta dena ife ifen da takeyi sede magana kuma ya mata wuya kayi ta mata baza ta amsa ba In ta gaji se kuka, dukda su mama suna iya kokarin su wurin ganin sun kula da ita  sun kuma sa ta farin ciki ganin taki sakewa yasa yakumbo tattaro su Yasmin gabad'aya ta dawo dasu gidan Abba sun kuwa ci nasara sbd kannenta tana d'an sakewa dukda ba kaman da ba, Har kuwa zuwa lokacin Abba be dena neman shaati ba kullum se ya kira police stations daban daban ko an samu labarinta amma babu.

********

Kula sossai take samu daga wurin hajja, yaya da jidda duk abinda take so shi ake mata ci wannan ci wanchan kan ran suna ta wani murje ta kara kyau, dinkuna jidda ta kar'bo mata masu kyau da tsari ranar suna kuwa baba ya yanka Sa, Shareef ya ajiye raguna biyu duk en uwansu na cikin gari seda suka gayyata aka cika sossai kaman sunan er gida.

Inda jidda ta so a yiwa Shareef d'in inkiya amma se shi yaki, bayan suna da sati baba ya kira shaati a parlornshi suka zauna ya mika mata wayanshi yace "Aisha ko kin haddace numbern iyayenki ki samin In kirasu sbd a samu hankalinsu ya kwanta" kar'ba tayi ta saka numbern Abba ta mika mishi dama itama duk kwanankin nan da tunanin halin da suke ciki take.

Ringing na karshe Abba ya d'auka gaisawa sukayi cikin mutunci seda baba ya mishi bayanin waye shi da garin da yake kan ya d'aura da "erka Aisha ce Allah ya jefota hannunmu" Abba na rigingine kan gadonshi ne be san sadda ya mike ba har kana jin rawar muryarshi yace "Aisha? Aisha nawa? Alhamdulillah! Alhamdulillah na gode, na gode" murmushi baba yayi yace "karka damu ai musulmi duk inda yake d'an uwan musulmi ne tana cikin koshi lafiya da ita da abinda ta haifa, wai jira nake ta d'an kara warwarewa se mu kawo ta" Abba yayi saurin cewa "a'a Alhaji ba za'a yi haka ba zamu zo gobe in Allah ya kaimu zamu taho ba se ka zo da kanka ba Ai hakan da ka mana ma mun gode".

Baba be hana ba sbd ya san ko yaya bazasu so su kara kwana ba tare da ita ba, ya tabbatar mishi ze turo mishi address d'inshi yanzu ba tare da jimawa ba godiya Abba ya dingayi kaman ze yi kuka, Baba ya mika mata wayan tana kar'ba ta kuwa fashe da kuka, murmushi Abba yayi yana girgiza kai yace "Mamana kenan" Tace  "Abbana kuna lafiya? Ina Mama? Abba ya su Yasmin kuna ji daga garesu?".

Yace "duk kowa lafiya uwata su Yasmin duk suna nan gida" Tace "Alhamdulillah" tana sauke ajiyar zuciya, yace "kina de lafiya ko?" Tace "Ina nan kalau Alhamdulillah Abba zaku taho gobe d'in?" Yace "In Allah ya kaimu yanzu ma zanyi booking flight" cikin jin daad'i ta tambayi Mama yace ta tafi office, Bayan sun gama wayan baba ya dubeta yace "wato har an gaji damu" dariya tayi tana cewa "ba haka bane baba na san mama bata cika jin daad'i ba ban san ko sanadin nan wani abin ya sameta ba shiyasa nake so na gansu na tabbatar komai lafiya".

Murmushi yayi yana cewa "haka ne kam" wasu adu'o'i ya bata yace "ki dinga karantawa da safe da yamma" kar'ba tayi tana godiya kan ta mike ta fice.

A kd kuwa Abba na sauke wayan riga kawai ya sa, ya fito parlor ba kowa se su neeha dake wasa direct sashen hajja yaje tana rigingine tana aikin cin goro ya kuwa ya duka ya mata Barka da yamma, cikin farin ciki ya fad'a mata bayyanar Aisha kuwa a hannun mutanen kirki Don babban malami ne ya riga ya sanshi, ita ma kuwa daad'i ya kamata murna har kaman ta taka rawa nan tace itama Zata je taga mutanen arziki en albarka se adu'o'i take zuba musu.

Mama na dawowa bayan tayi wanka ta huta ta nufi d'akin shi yana zaune yana aiki a system yana ganinta ya saki murmushi itama ta mayar mishi tana zama yace "Albishir" Tace "goro fari sal" yace "Aisha...." kan ta karasa ta mike tana dafe kirji "An sameta???" Dariya yayi yana gyad'a kai da sauri ta nufi fita yayi saurin capke hannunta yana dariya yace "Ina zaki?" Tace "tana Ina? Sashen hajja ko d'akinsu? Ko tana wurin su Yasmin don ban ji su ba" yace "ina kunyan fulanin Fati?" Dukar da kai tayi yace "tana maiduguri na mana booking flight gobe zamu je" waro ido tayi "a hannun waye? Ya akayi ta isa maidugurin?" Yace "duk Adana tambayoyin gobe in Allah ya kaimu in munje duk zamu ji amma hannun mutumin kirki ne".

Ai Mama bata ta'ba ganin daren da ya mata nisa irin wannan ba Allah Allah take gari ya waye, bayan jirginsun ma 11 ce washegari kuwa tun 9 suka gama komai ta Kira su meena duk ta fad'amusu adu'o'i suka musu ta tafiya lafiya suka tabbatar mata suna sauka zasu kira suji, 11 jirginsu ya d'aga se maiduguri aiko driver suka samu baba ya turo musu don kan su taso seda sukayi waya da baban.

Tun safiyar shaati ta kasa zaune ta kasa tsaye ita da jidda suka shiga kitchen suka musu girki sossai na karshe, suka chanchad'a wanka suka zauna parlor da su hajja suna hira da yaya da ta shigo mahaifin jidda ma daddy na wurin baba suna tattauna maganan shaatin Shareef be shigo ba kuwa, tana jin karan shigowar motar sukayi saurin Mikewa suka fito jidda rungume da Shareef.

Tana ganin sune kuwa taje da gudu ta had'a Abba da maman ta rungume se kuka sossai take kuka sbd chan kasan ranta Saif ne dankare mama ma se ta hau tayata, da kyar ta tsagaita ta rike hannun hajja tana hawaye hajja tace "ke ni ba ta ke nake ba nima Ina kishiyar tawa ko mijina?" Tayi maganan tana leke leke dariya sukayi jidda tace "gashinan kuwa Hajja mai gida ne zankad'e'd'e" kar'banshi tayi tana Masha Allah, baba da fitowarsu kenan yace "Assalamu alaikum" da sauri Abba ya juyo sukayi musabaha.

Yace "mu karasa sun Barku nan" dayake jidda da shaati ne kawai dama suka fito baba yace "Kira iyayenku matan ku samemu parlorna" parlonshi ya nufa suka bi shi a baya, jidda kuwa ta kirawo su hajja suka sanyo hijab zuwa parlorn kan su shiga ma suka samu ana ta gaisuwa suma gaisuwa suka mika, bayan sun natsu maids suka shigo da drinks da ruwa suka jejjera.

Bayan sun d'an sha baba ya kalli jidda da ta koma gefen Mama ta zauna kaman mamanta yace "Ina mai gidan naki ne?" Jidda tace "ya tafi wani meeting yobe state baba amma a yau ze dawo" Kai ya gyad'a kan ya dubi Abba ya musu bayanin duk abinda ya faru godiya suka hau yi Mama kam seda ta sha kuka ita da hajja nan kuwa ta sa a ranta idan har zubaida na tare da Saif to ba shaati ba Saif.

Bayan nasihar da baba ya kara yi ya basu hakuri akan abinda Isma'il ya aikatawa rayuwarsu, matan suka mike zuwa ciki hajja rungume da lil Shareef a sashen hajja suka yada zango yayinda suka bar Abba da su baba, aka kai musu abinci suma abinci jidda ta gabatar musu duk kuwa suka ci suka shiga sukayi sallah suka kuma fitowa suka kafa hira dayake dukkansu basu da wani bakunta nan da nan suka sake  shaati kam kwanciya ma tayi kan cinyar mama dukda tsiyar da su yaya ke mata.

**********

Gudu yake tsugawa a cikin wata kasungurmin daji bayanshi wasu munanan halittu ne ke binshi rike da wasu irin sarkoki da gudumomi manya da kwara d'aya ma se yayi tsawon mutum biyu da kibar mutane akallah biyar, ihu yake yana neman agaji sbd daga ganin mutanen basu san alamun imani ba katti ne fuskokinsu ba kyaun gani.

Cikin gudun ceton rannan wani iriyar muguwar guguwa ta taso ta daukeshi ihu kawai yake cikin neman agaji be tsinci kanshi ko Ina ba se cikin wata katuwar rami da manya manyan macijai da kunamai abin tsoro, suma yayi be farka ba se cikin wata macijiya wacce wutace ke cin cikinta, a firgice ya mike yana ihu da sauri inna ta mike tana kallonshi "lafiya?" Ta furta ganin yadda yake had'a shegiyar gumi tsuru tsuru yayi yana zazzare idanu.

Abin Mamaki a cikin d'akin ya fara ganin wasu munanan kadangaru masu wasu irin manyan hakwara sun nufoshi da azababben gudu ya mike ya nufi fita inna ta chabkoshi zatayi magana ya banketa ya fita yana ihu, yana fitowa kuwa ya ganshi bakin rijiya cikinta wata irin muguwar wuta ke ci juyawa yayi yaga kadangarun nan sun kuso shi kawai se ya fad'i ya suma.

Salati kawai inna ke yi a firgice meke faruwa?.

*********

Kwance take cikin tsananin zazza'bi dafe da kai sbd yadda kanta ke Sarawa ta rasa wannan ciwon kan da ya addabeta tun kwana biyu da suka shige take fama dashi ta sha magani ba sauki ta je asibiti sun rasa me ke damunta, suka had'o ta da wasu magunguna, kallon Saif dake bacci hankali kwance tayi ta ja tsaki ta mike ta fito parlor a'a ba se taga parlorn ya kaure da wata muguwar bakar hayaki ba yana ta shawagi.

Juyawa tayi zata koma se taga ba kofan kwata kwata zaro ido tayi ta nufi makunnin wuta tana kunnawa wata muguwar halitta ta gani gabanta me ido kwaya d'aya jajazir kaman mace kaman namiji gashin kanshi ko kanta tsaitsaye yayinda harshen ke zazzagowa yana dilalar da jini da miyau faratun hannun kuwa sunyi tsawon mutum.

Baya baya ta fara yi tsabar tsorata ta kasa ihu se 'barin jiki wutar d'akin ya fara d'aukewa yana kawowa take akayi wani tsawa da ya nuna mata wannan halitta na shirin had'iyeta Ai da ta saki wani mahaukacin ihu se gata zube kasa ta kume kai da steps take jini ya fara zuba, cikin bacci yaji ihun da sauri ya mike ya fito aiko ya ganta kwance kasa jini na fita kanta da sauri ya karasa ya d'agota yana kiran sunanta inaa ta sume ne ko ta mutu Allah masani.

Da gudu yaje ya d'auko car key ya d'auke ta ya fito yana kiran me gadi se gashi yaso bud'e mishi kofa yayi ya ja se hospital nan suka ki kar'barta wai se ya kawo police, Kira kawai yayi cikin mintuna se ga wasu polisawa biyu sun zo nan aka shiga da ita emergency, baze iya zama ba Don haka sallaman polisawan yayi ya koma gida yayi kwanciyarshi barci bayan ya shedawa nurses d'in a mata duk abinda ya kamata kar a kirashi se da safe kud'i ba matsala.

                   🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA........💦🍇

  *Baya Chanza d'and'anon teku*


      *Fatima Muhammad Gurin*

   **Gureenjo6763 on Wattpad**


      'Yar Mutan Adamawa


    *P31*


Kwanan su Mama biyu maiduguri kan suka juya da shaati da kusan akwatunanta set bayan bata zo da ko kaya d'aya ba, ta tafi ta bar su jidda da kewa haka suma sun tafi da kewansu sossai suna masu yabon karamci da mutunci irin na su baba, bayan haka baba ya basu duk wasu adu'o'i ya kuma tabbatar kar shaati ta dena anfani da magungunan da ya bata.


Hajja da yaya suka had'a su da turaruka na d'aki, na jiki, na tsugunu, humras masu bala'in kamshi, da lafayas, shaati seda tayi kukan rabuwa dasu sbd bazata ta'ba mantawa da su ba adu'arta baze ta'ba katsewa daga kansu ba se ta dena numfashi mamaki take yadda tun ranar suna har yau bata kuma ganin Shareef ba sede taji suna waya da jidda, ta so su ke'be ko yaya  ne ta mishi godiya sede hakan be samu ba tunda be dawo ba kuma bata da waya.+


Ko su Abba da suka so ganin shi hakan be yiwu ba sbd daga yobe gaba yayi yace kuma it was urgent ba yadda za'ayi ya juyo sede sukayi waya da Abban ya kuma kar'bi contact d'inshi, suna sauka Airport ta bud'e baki cike da tsantsar mamaki take kallon wai waenda suka zo tarbansu Ya hameed, ya mujeeb, ya majeed, ya meena da ya fadeela se Anty tala da namesake d'inta, se ma ta rasa wa za ta fara runguma ganin dukkansu fuskokinsu kwance da murmushin farin cikin ganinta.


Kawai se ta tsaya chak ta fara hawaye ya majeed da ya mujeeb ne suka nufota tare da rike hannayenta suna kallon irin kyau da yalkin da jikinta ke zubawa dukda ta d'anyi duhun jego amma tayi matukar kyau, kawai se ta rungumesu su biyun tana kara sautin kukanta ya majeed yace cikin sanyin murya "is Ohk sis" ya mujeeb yace "welcome home dear" kai kawai take gyad'amusu tana murmushi da hawaye har suka saketa ya meena da ya fadeela da suka karaso suka rungumeta.


Se suma suka saka kuka sossai suke kuka seda mama ta ce "a Airport fa kuke hankalin mutane na dawowa kanku" saketa sukayi suka had'a bakin cewa "we are sorry lil, we are so sorry" murmushi ta musu tace "thank you for being your real self's I missed you two so badly, I missed everything about us da har na fara mantawa almost 9yrs" girgiza mata kai sukayi ta saki hannunsu tana murmushi ta kalli ya tala da namesake cikin fara'a da Hawaye suka rungumeta se taji Saif a zuciyarta ji take kewarshi na taso mata, da sauri ta kawar da wannan tunanin ta d'ago tana murmushi ta kalli hameed tace "hey bro" murmushi kawai yayi.


Kallon ya fadeela da ta kar'bi Shareef daga hannun hajja da ta kumbura fuska tana jiran ace mata kyat ta fashe tace "masha Allah lil wannan kyakyawar babyn" meena tace "photocopy d'in Saif wallahi" namesake ta leka fuskanshi tana cewa "ya sunanshi?" Mama tace "Shareef her life savior" ras haka gabanta ya fad'i jin abinda mama tace, se tayi saurin sakan murmushi ta kalli hajja da bata motsa ba Bayan sun fara tafiya tace "hajja kalau kuwa naga ki......" bata karasa ba hajja ta cha'be "an tsaya d'in nace an tsaya d'in, dukkanku zaku lalla'bo ku sameni lullu'be kan gadona ne wallahi se nayi maganinku d'aid'ai ni zaku mayar saniyar Ware?".


Abba da tuni yana jikin motan mujeeb yana waya da baba, ya juya yana kallonsu jin da karfi hajja tayi maganan murmushi yayi yayinda su kuwa suka saki dariya majeed yace "kajimin tsohuwa yanzu fisabilillahi waya mai dake saniyar Ware?" Dakuwa ta mishi tana nuna Abba tace "ka ga chan tsohon ba de ni ba, ko wannan ta gabanka a gabana kuka nuna kunfi son er uwarku a kaina na hau wannan karfen ta bature na sauka lafiya ba wadda ya iya ce min barka, Ai wandon roba nake daidai nake da kugun kowa" (@hauwa Ibrahim bahaushiya manya to an gode da wannan hausan) ta fad'a tana kwafa.


Dafe baki sukayi shaati tana dariya tace "to kuwa in har Abba tsoho ne kenan ke kuwa tsohuwar tsohuwa za'a ce miki" binta tayi da sauri ta zagaya ta fad'a motar ya mujeeb tana locking duk dariya suka fashe dashi har Mama murmushi take yayinda Abba ya d'an sha kunu dukda dariyar dake son kwace mishi shima ganin ta zage tana ta masifa don an ce mata tsohuwa da kyar Abba ya lalla'bata ta shiga motar hameed kan shaati ta bud'ewa mujeeb motan tana kan dariya har lokacin.


Allah sarki her family her everything ta jima rabon da tayi dariya haka ko Don zuwan hajjan maiduguri tana marmarinta yasa basu raba hali yadda suka saba ba, yadda take jinta cikin farin cikin sakewarta da en uwanta Ina kuma In ta ganta cikin 'ya'yanta she can't even imagine, Allah kawai ya kaisu gida lafiya.


***********


Kwananta biyu bata san inda kanta yake ba ita ba bacci ba ita ba ido biyu ba a yanda taken ita kad'ai ta san yadda take ji, ba irin tsoratarwar da ba'a mata cikin duniyar bacci duk azabar kuwa tana jinshi jikinta abin takaici da bakin cikin ba bakin kuka ba kafan gudu, ta rasa me ke faruwa da ita, wani lokacin tana jin maganan Saif kanta se taji kaman tayi ta zunduma ihun sunanshi ko Allah ze sa ya ji ta sede inaaa.


Likitoti sunce buguwar da tayi a kai ne yaja mata wannan fitinennen baccin yayinda basu san bakin aljanni ke azabtar da ita a hakan ba, abinda take ji ta san wallahi baze fad'u ba kaman yadda baze rubutu ba ita Allah gani take kaman gwara mutum ya mutu gabad'aya da azabar da take ji ga yunwa da kishi dake azabtar da ita a kwance, cikin kuka ta furta "me yasa ba wadda ze ji ni ne? Meke faruwa? Baba Ina kake?" Dariya me kuwwa kawai taji a kanta anata 'ba'bakawa a tsorace take jujjuya kai sede ba abinda take gani se azababben duhu da karar dariya.


********


A 'bangaren baba kuwa gwara karamin mahaukaci dashi a halin da yake ciki yanzu yanzu ze yi shiru yanzu ze birkice yayi ta zunduma ihu dukda da hankalinshi sarai ya san abinda ke faruwa amma gane ganen da yake na neman hallaka hankalin kwakwalwan kanshi, inna gabad'aya ta rasa natsuwa ita karan kanta gashi yayan zuby yau kwana biyu kenan bata ganshi ba ta rufe baba gida ta fara yawon nemanshi.


Duk inda ta san yake zuwa wuraren shaye shayenshi baya nan ganin kar ta bar baba shi kad'ai ya jima be ganta ba abin nashi ya tashi yasa ta nufi komawa gida sede tana shiga ta nemeshi sama da kasa ta rasa neman duniya kaman ance ta leka rijiya aiko se gashi shame shame cikin rijiyar yana bulayi ihu ta kurma tana fita neman temako sede kuma akayi rashin sa'a sanin halin baban yasa ba wadda ya kula innan se chan wasu matasa suka taimaka suka zo suka fiddashi Allah ya takaita rijiyar ba irin masu zurfin nan bane sbd suna da yawaitar ruwa unguwar.


Baba ya sha ruwa sossai wadda da kyar suka samu ya farfad'o sukayi tafiyarsu suna me tabbatar mata ta kaishi asibiti sbd kanshi da kafafunshi da suka bugu har kafar ta suntuma suntum yayinda kan ke jini, dukda ya farka idanunshi biyu sede a wahale yake numfashi, cikin masifa da gundura take tambayarshi inda yake ajiye kud'i ta d'auka ta kaishi asibiti sede fir yaki magana kuma tana sane da gangan yake cikin fad'a tace "shikenan Ai tunda baka so a ta'ba kud'in se kayi ta zama a haka har kafar ta rube a guntule Ina anfanin wannan rayuwa, lafiyarka ma ace kana bakin cikin kashe masa kud'i mutum se shegen lukudi ban san wace kaddara bace ta jaji'boni auranka wallahi".

Tana ta sababi ta jashi zuwa d'akin shi ta yasar tayi fitowarta.


***********


Hmmm Ina en Gureenjo novels group kuzo ku tayani kallon ikon Allah, zaune wata shirgegiyar mata da gani ka san wata tsohuwar kilaki ce da bleaching ya mai da fatar jikinta kaman na Guza, wata shegiyar ingozinta tsaitsaye a tsakiyar kanta shar'be'biyar bulala ce kwance gefenta yayinda na leka da kyar ta gefen ta wa zan hango Isma'il zaune ta tara mishi wankinta da na kwartayenta yana ta aikin wankewa daga shi se vest da boxers yayi wani irin rama ya lalace kuma kallonshi da kyau nayi Don tabbatarwa ba makawa Isma'il d'inne kuwa.


Bayan ta zuki tabar hannunta ta d'auki bulalan ta shar'ba mishi tana feso mishi hayakin sigarin ta ce "banza rago kawai lusari ajiye wankin nan maza kaje ka kai min nika kazo yanzu ka dafa min Abinci Don yunwa nake ji na tabbatar Darious yanzu Haka in ya tashi yace yunwa yake ji tunda ka kasa aikin da yake naka shi yayi ma" ta sa kafa ta naushe gabanshi tana furta "lusarin banza kawai ragon namiji".


Hawaye ne ya gangaro mishi yana Mikewa ya nufi kitchen kayan miyan ya gyara yana mamakin shi kuwa me ya kaishi auren wannan mata, ya de san gani d'aya yaji yana sonta kuma be yarda a cikin familynshi kowa ya santa ba har aka d'aura wadda duk events d'inta na tsakar dare ne da ya had'a partyn maza da mata da shaye shaye, a lokacin ya tabbatar da za'a hanashi auren ta da anga tashin hankali sede tunda ta taro gidan daren farko ya tabbatar a tsarinta ya mata kankanta dukda yadda ya sameta kofar taxi ma albarka haka ta wankalar dashi ta danna kiran samarinta daga lokacin yake cin azaba kala kala a gabanshi kuwa se tayi sex da maza akalla biyu uku.


Kud'ad'enshi kuwa ya tabbatar yanzu aka duba account d'inshi baza'a samu ko ficika ba motar hawanshi ma yanzu ko kallo be isa yi mishi kwakwara ba, bayan ya d'auki kayan miyan da ga blander amma ta gwammace yaje yabi layin nika ya fito, ta chilla mishi ashirin ya d'auka ya fito yana tafiya cikin sanyi wata bakar mota doguwa ta faka wasu gardawan maza da bakaken kaya sanye da mask suka sungumeshi zuwa cikin motan nan suka ja a matukar guje suka wuce suka bar kayan miyan yashe nan kasa.


**********


Suna parking part d'in Abbanta taga garden d'in gidansu cike da mutane ana ta ciye ciye yayinda hayaniyar yara ya kaure gidan gabad'aya da mamaki take kallon wurin to me akeyi? Dama taga motoci a cikin gidan ta d'auka duk samari da en matan gidan ne kowa na nan kila da wasu abokansu bata ida mamaki ba seda taga namesake ta ja ta zuwa tsakiyar filin da akayi decoration me shegiyar kyau da d'aukar hankali.


"Maaaaamiiiiii" da sauri ta juya inda taji ana kiran sunanta se taga neeha sanye da kayan Barbie Princess tana mata dariya kan tayi magana taji sauran yaran sun d'auka "happy birthday too youuu! Happy birthday tooo youu!! Happy birthday dear mamyy happy birthday too youuu" murmushi take bakinta yaki rufuwa da sauri ta juya jin an ta'bata se taga sameer da yasmin sanye da wasu kyawawan kaya sun sha kyau da sauri ta bud'e musu daidai lokacin da neeha ta karaso da gudu ta had'asu ta rungume Allah ya gani ta mance kwata kwata yau birthday d'inta.


Tafi manyan wurin suka fara se taji karan trolley juyawa tayi se taga Arwa sanye da kananun kaya tana turowa manyan cakes ne masu kyau da tsada guda biyu a kai anyi rubutu d'aya an saka "happy birthday maami" d'ayar kuwa an saka "welcome home our dear sister" hawaye ne ya gangaro mata dukda murnan da take ciki da farin cikin wannan surprises da taro duk sbd da ita hakan be hanata fahimtar wani abin na damun Arwa ba.


Sake su neeha tayi tana bud'ewa Arwa hannu da gudu tazo ta rungumeta tana furta "thank God you are home Maami" se kuka, kowa tafi ya kuma d'auka ta d'ago tana ta murmushi take sharewa Arwa fuskanta dukda tana bukatan hutu haka ta shantake nan ta yanka cake ta ciyar da en uwanta banda hameed, Mama da Abba da basu zo nan d'in ba amma har hajja na wurin da yakumbo.


Kawayen su ya fadeela da Anty murja matar ya mujeeb da Anty Sharifah matar ya majeed da wasu kawayensu da abokanan yayyinta dayawa da matansu da yaransu aka baje abinci akayi ta ciye ciye cikin murnan dawowanta gida cikin koshin lafiya, duk abinda akeyi hankalinta na kan arwa da ta lura tayi wani mugun rama kuma bata da sukuni da fara'a, haka ta danne se sun ke'be ta tambayeta damuwarta da wayan Mama tayi ta hotuna tana turawa jidda daga karshe ma video call sukayi aikuwa sarauniyar surutu ta had'u da neeeha da yasmin nan aka hau surutu a take suka saba.


Se dab magrib taro ya watse kowa ya tafi banda ya tala, yakumbo, namesake da uncle sulaiman se sumayya cikin Abba sukayi suka zauna parlor, nan mama ta basu labarin yadda akayi Shaatin ta fad'a hannun mutanen kirki, sun jajanta abun sossai kan yakumbo suka kuma neman gafararta ita da Anty tala take tace ita dama bata rike ba ta jima da yafe musu.


Sulaiman ya d'aura da tayiwa Abba godiya ya samar mishi aiki yanzu har mota yake dashi loan d'in company da za'a dinga cirewa kad'an kad'an a albashi godiya tayiwa Abban kaman yadda ya roka murmushi sukayi kan suka mike suna musu sallama da fatan su ganta gidansu ziyara yakumbo kan harda kukanta bazata ta'ba so Saif yayi asarar mata irin shaati ba sede yanzu ba yadda ta iya shaati bazawarace da ta gama idda she have full right da zata za'bi wadda take so a sadda take so.


Bayan sun tafi ya meena da ya fadeela ma suka nemi yafiyarta harda kuka, cikin jin daad'i ta yafe musu suma tace wallahi bata ta'ba sawa ta tsanesu ko bazata ta'ba yafe musu ba sbd komai ya faru a sanadiyarta ne zasu fara zagin Isma'il Abba ya dakatar dasu tare da korasu kowacce ta nufi gida mijinta da yaranta, bayan tafiyansu Shaati ta dubi mama tana shafa kan Arwa da tayi bacci kan kafanta tace "Mama wani abu na damunta ne?" Kallon Arwan tayi tana sauke ajiyar zuciya Abba ne ya bata labarin irin jinyar da Tasha wadda ya sa shaati shan kuka sossai seda iyayen suka mata fad'a.


Tashinta tayi suka nufi d'akin Mama dayake chan aka kai mata kayanta, a kan gado ta kwantar da ita tana shafa kanta da nufin ta lallasheta ta koma bacci se Arwa ta bud'e idanu cikin sanyi murya tace "Maami da gaske ne wai bani da baba? Ni shegiyace? Na tambayi senior friend d'ita Tace shegiya na nufin wadda aka haifa ta iskanci ba tare da aure ba kenan ni....." kasa karasawa tayi ganin yadda shaati ta zaro idanu kaman zasu fad'o tana girgiza kai In a shock na yadda taji maganan kawai............
                   🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇

*Baya Chanza d'and'anon teku*


*Fatima Muhammad Gurin*

**Gureenjo6763 on Wattpad**


'Yar Mutan Adamawa


*032*


Shiru ya ratsa tsakaninsu se kukan shaati dake tashi ajiyar zuciya ta sauke tana runtse ido tace "tunda kin zabi sani gwara in fad'a miki khadija" zama tayi bakin gadon ta kama hannun Arwan da ta mike zaune tiryan tiryan ta bata labarin komai bata 'boye mata ba kan ta karasa Arwa ta fad'a jikinta suka sha kukansu tare seda suka natsu Arwa tace "I don't like him maami he made me sick" waro ido shaati tayi tace "he was the reason behind your sickness? What the hell did he told you?" Bayani ta mata abinda ya faru sossai ran shaati ya 'baci ta kwantar da Arwa tana cewa "sleep daughter don't think of anything kinji? Papa d'inku is your father always and forever in shaa Allah".


Murmushi ta saki cikin cire komai ranta yarinyar ta kwanta zuciyarta fall tsanan Isma'il sede ko kad'an bata zargi mahaifiyarta ba se ma tausayinta da ya rufeta a haka bacci ya kwashe ta abinka da yarinya se bata tsawallawa kanta ba tunda de ba laifin maaminta bane, shaati na fita ta samu har yanzu Mama da Abba na zaune suna hira a harzuke tace "Abba abin Isma'il fah ya isheni gaskiya Abba zan d'auki mataki da duk abinda na mallaka duniya ko da kuwa zan rasa komai ne".+


Abba ya murmusa yace "natsu uwata natsu, me kuma ya faru?" Cewa tayi "Abba fah cewa Arwa yayi ita shegiyace a yawon karuwanci na haifeta sanadiyar ciwon da tayi ta kusa rasa hankalinta fah kenan!! Abba me yake kuma so dani bayan duk bakin cikin da ya ja min a duniya??" Shiru Abba yayi Mama ce tace "dankari Amma Isma'il anyi marar mutunci gaskiya Abbansu kayi wani abu akan hakan abin nashi ya fara wuce gona da iri" murmushi kawai Abba yayi dukda shima har ranshi yaji zafin hakan sede ya danne yace "uwata kenan ki barshi da Allah, Ai Allah ba azzulumin bawanshi bane taya kuke tunani zan iya barin ku ku kai d'an d'an uwana kotu? Ku barshi da halinshi ba Arwan ta samu sauki ba? Kuma bata rike ki a ranta ba so pls a bar maganan nan anan watarana gaskiya zatayi halinta".


Kuka shaati ta saka ta juya ta nufi d'akinta dukda tana jin shareef na tsala kuka ko ta kanshi bata bi ba In ranta yayi dubu to ya 'baci, seda baaba larai ta kawo mata Shareef kan ta mike tana share fuska nasiha tayi ta mata kan ta fice ta barta tana shayar dashi idanunta tsab kan fuskanshi mahaifinshi kawai take kallo a wannan d'an karamin fuskan tsabar kammaninsu amma shine Saif yake cewa maybe ba cikinshi bane ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe idanu.


Ta jima kwance har seda Shareef yayi bacci kan ta kwantar dashi ta mike ta fad'a toilet wanka tayi ta fito cikin kayanta na maiduguri ta d'auki riga da Wando na bacci ta sanya tare da saka hula ta haye gado ta kwanta kusa da Shareef ta kura mishi idanu tana me tunanin Shareef a ranta to ko wani abin ta mishi ne? Tunda ta gama basu labarinta daga ranar be sake mata magana ba sede ya shigo ya duba Shareef karami ya duba Lafiyarshi ya fita ajiyar zuciya ta sauke tana kauda tunanin irin tsare gidanshi.


Da tunaninshi bacci ya kwasheta, washegari ma en uwanta gidan suka yini suna masu kuma rokarta gafara, bata d'aukesu da zafi ba sam ita daad'in rayuwarsu a haka take sun koman da ba fad'a ba wani abu da yamma suka tarkata suka koma site d'in hajja a nan suka baje suna cin kwad'on zogalen da tayi dukda shaati ta san sarai se ya 'bata mata ciki, kaman ance ta d'aga kai taga wata mata na shigowa ko sallama babu ba wadda ya lura da ita se shaati cikin mamaki tace "Mama lafiya kuwa? Ko 'Batan hanya kikayi? Shigowa ba sallama" had'e rai matar tayi ganin kowa kuma se ya tsaya yana kallonta hararar shaati tayi ikon Allah shaati ta furta kan lips d'inta.


Hajja tace "ke wace mama kuma? Matarfa Isma'il ce" Ai shaati bata iya rike wata shegiyar dariyar da tazo mata ba ta fashe dashi yi take har da hawaye wai wannan matar Isma'il tsohuwar da zatayi sa'ar mahaifiyarshi se kuma su meena ma suka fara tayata ganin shegiyar dariyar da take, gabas da yamma matar ta had'e tace "ke dariyar me kikeyi?" Matse lips d'inta tayi tace "ni kuma? A'a ba dariya nake ba" ganin bazata iya controlling dariyar ba yasa ta mike ta shige d'akin hajja tana me cigaba da dariyarta don sossai abin nan ya sata nishad'i.


Kwafa matar tayi wacce sunanta ya kasance Saratu tana zama tace "hajja Isma'il ne ya 'bace" wara idanu hajja tayi en parlorn a tare sukace "what!!" Hajja tace "wani irin 'bacewa ana zaune kalau da girmanshi kaman wani yaro karami" ajiyar zuciya ta sauke tace "na aikeshi markad'en kayan Miya tun rana har yamma be dawo ba da na fita nemanshi se wasu suke ce min sunga wata bakar mota ta zo a guje ta d'aukeshi ga kayan miyan watse to shine na kai kara police station har yanzu Shiru shine na ga ya dace in zo In fad'a muk...."


Bata gama ajiye numfashi ba shaati da ta kasa hakuri ta kuma fitowa tace "kika aikeshi markad'en kayan miya?" Se dariya hajja tace "wani irin iskanci ne wannan Aisha? Ce miki akayi fah an saceshi shine kike wannan shegiyar dariyar? Ke kuma saratu kike wani irin hali ne hakan wani irin tarbiyya ce na aikan miji ba kasuwa bama ko shopping markad'en kayan miya?" Shiru hajiya saratu tayi yayinda hajja ta dinga zuba masifa wallahi har lokacin dariya shaati ke yi abinta kasa kasa yayinda hajiya saratu ke ta hararata kaman idanunta zasu tsiyayo kasa.


Kiran yaran mazan hajja tayi gabad'aya da matansu aka zauna magana akan 'batan Isma'il mama kam kasa hakuri tayi tace "ikon Allah to ko shima yawon ya tafi yace ya 'bata" duk Shiru sukayi suna kallonta 'bata fuska tayi don ita tayi shiru ma bata kara da yawon iskanci ya tafi ba kaman yadda ya fad'a kuma iyayenshi Suka fad'a sau biyu akan erta!!


Ba wadda ya tanka se Abba da ya yi mata magana da idanu kan yayi gyaran murya yace "to kuma dukkanku baku kar'bi kira ba ko kidnappers ne tunda ance d'aukanshi akayi" sun tsayar akan a jira kiran kidnappers d'in inda 'bangaren d'aya suka roki Abba ya kira commissioner of police, ba 'bata lokaci ya kirashi sukayi magana sossai kan suka katse, kowa watsewa yayi harda saratun wucewa tayi abinta cikin halin ko In kula.


**********


Yau Allah yayi aljannin nan ya kyale zuby ta tashi shi Saif kam ma Baya nan ya tafi office trip Lagos, a hannun nurses ya barta ana kula da ita amma dayake abunku na Nigeria samun kud'i suke daga gareshi amma ba kular da ya kamata su bata, randa ta farka yunwa kaman ze kasheta da kishir ruwa Ai da sauri ta sauko ta fito tunda ba Karin ruwa bane a jikinta ba komai ba.


Sede fah ba kud'i hannunta d'akin kuwa babu komai fitowa tayi bata had'u da kowa ba haka ta nufi gate ji take kaman zatayi hauka In bata ci abinci ba da sauri ta fito ta tsaya taran taxi ta fi mintuna ashirin bata samu ba, hannu kawai ta dafe a kai tana safa da marwa hawaye na cika mata ido, wani restaurant ta gani a tsallaken titi daga gani me tsada ce kallon gefe da gefe tayi kan ta tsallaka wallahi bazata kashe kanta ba.


Shiga tayi yadda suka ganta daga ita se doguwar riga da wata gyale d'an karami dake d'aure a kanta zama tayi tare da ordern abinci cikin tunanin yadda zata biyasu kud'insu sede bazata iya hakura ba, abincin kusan 5k tayi order ta zauna ta hau ci har kallonta ake yadda take ci hannu baka hannu kwarya har tana kwarewa, seda tayi nak aka kawo mata bill ta fara zazzare idanu "madam ATM ne ko cash?" Kallon waitern tayi tace "sede ka bini gida ka amsa gaskiya don ba ATM ba kuma cash hannuna" seda ya kalleta sama da kasa yace "what kaji min rainin hankali" nan take ya fara bala'i me makon tayi shiru ai itama se ta hau masifa nan fah bala'i ya kaure su kuma sukace bazata ci abinci a banza ba nan take suka kira police kuwa akan se ta biyasu kan a saketa tunda abin nata rashin arziki ne bakinta be mutu da bala'i ba seda ta ganta cikin kazantaccen wurin nan kira take "wallahi mijina me kud'i ne karku rufe ni anan muje gidana zan baku duk abinda kuke so" ko saurararta basuyi ba suka rufeta sukayi gaba suna zaginta.


********


Baba fah duniya ta mishi zafi fiye da tunanin me tunani ba me zuwa da sunan bashi aiki tunda yanzu aljannun ma ba aiki suke mishi ba, kafanshi yaki samun lafiya duk irin dabarunshi na gida gashi har yanzu be dena abubuwan mahaukata ba wadda mutane suka d'auka da gaske ya haukace se zagi yake had'ashi da en unguwa har matar tashi ba abinda yafi mishi ciwo kaman kana ji kana gani lafiya garau rau ana yi maka kallon mahaukaci.


Zaune yake kan taburmanshi na gado a yanzu da kullum yana kai yana birgima cikin azabar ciwo, gangara yayi kan kasar gidan ya fara chachakka da yatsun hannayenshi goma ya rasa me yake tonewa dukda yadda yake jin hannayenshi na ciwo tun yana jin ciwo har ya fara ganin jini sede fa be dena ba seda inna ta fito taga yadda ya dage yana tone kasa hannayenshi duk na zubar da jini tayi saurin rikewa "lafiyarka kuwa malam?" 'Dagowa yayi ya kalleta aiko se yaga kaman wata bakar aljanna me abubuwan tsoro ya gani ihu ya kwala ya fara kokarin tashi ya gudu kafa yaki kan ya gama tashi ya kuma fad'awa kan kafan ihu ya tsala yana sumewa.


Da sauri inna ta fad'a d'akin shi ta fara bincike da neme neme da kyar ta samu inda yake ajiyar kud'i akwai kud'i kuwa dayawa a wurin bata tsaya kirgawa ba ta d'iba ta fito taje ta nemo taxi da kyar aka zo aka d'auke shi se asibiti private kuwa ta kaishi ganin yana da kud'i duk kan kace kobo kud'ad'en da ta debon ma sun kare seda likitoti suka jima kanshi kan suka fito inna suka samu suka mata bayanin gaskiya kafanshi bazata gyaru ba ciwon da yaji da ba'ayi treating da wuri ba parasites suka ta shiga jikinshi har wurin ya koma wani iri kaman ru'ba'bbe yanzu baze gyaru ba sede a yanke a yanzu In ba haka ba aka barshi hakanan ze iya kamuwa da cancer at any moment.


A take ta yarda a yanke ta kuma komawa ta d'auko kud'i tazo ta biya na operation da za'a mishin bayan ta biya ta wuce kasuwa ta musu sayayyar kayan abinci ta nufo gida abinta hankali kwance, zuwa dare baba ya koma ba kafa guda har washegari be tashi ba, se yamma ya farka ganin shi gado yasashi fara kokarin Mikewa zaune yana zama me ze gani ba kafa d'aya an guntule ihu ya tsala se kuma yayi saurin yin Shiru jin ihun na kara mishi azabar kafan kawai se ya hau kuka.


*********


Iska ake me matukar karfi da se ya tsorata duk wadda yake cikinshi ya fara ambaton Allah don iskan kaman ze d'auke mutum haka ya taso gadan gadan duk wani musulmi adu'o'i yake jerawa hakan ya kasance a 'bangaren mai gadin makabarta a er d'akin shi zaune yana ambaton Allah, kaman ya sanshi.


Sossai ya rud'e jin iskan har kaman ze zubar mishi da d'akin Mikewa yayi ya fito yana leken makabarta da mamakinshi duk kaburburan da ya binne wani abu na malam daidai wurin guguwa me karfi ya zagayesu yana juyawa da kasar wurin, kuma Wara idanunshi yayi Ai be hankara ba yaga duk wasu binne binne sun fito yayinda wannan iskar ta nufoshi gadan gadan Bayan ta chure waje d'aya.
                  🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇

   *Baya Chanza d'and'anon teku*


    *Fatima Muhammad Gurin*

  **Gureenjo6763 on Wattpad**


          'Yar Mutan Adamawa


   *P33*


Salati ya fara Ai guguwar nan na isa kanshi ya tsala ihu anan take a wurin ya haukace tuburan ya fita da gudu cikin wannan muguwar iskar.


A daidai lokacin da shaati ke kwance tana danna wayar da d'azu ya mujeeb ya sayo Mata shi hira sukeyi da jidda ta chat, a firgice ta mike zaune gabanta na tsananta fad'uwa sunan Allah ta fara ambata tana janyo Shareef jikinta rungumeshi tayi kam tana jin yadda zuciyarta ke luguden bugawa akan lips d'inta ta furta 'Saif'+


**********


Zaune yake yana wani aiki a system a yayinda labulayen d'akin da yake yake d'an kad'awa sbd iskar da akeyi gabad'aya duniyar ce, kanshi yaji yayi mugun sarawa a take ya dafe yana ambaton Allah gabanshi ya ci gaba da luguden bugu yayinda hankalinshi gabad'aya ya nemi barin jikinshi, wani bala'e'en sanyi ya fara ji da sauri ya janyo remote d'in Ac ya kashe yana me dukunkunewa a bargo tare da runtse idanu wata zazzafar zazza'bi na saukar mai da kyar yake iya jan numfashi.


******


A daidai lokacin Zuby dake zaune cikin cell ta mike a firgice harshenta taji yana cika bakinta yana neman fitowa waje bata hankara ba tajishi kaman an tsinkashi se lilo yake a waje yana dilalar da miyau, kallon bakin take kokarin yi aiko se taji idanun sun fara ganin duhu bata iya kallon komai alhalin a bud'e suke ihu take kokarin yi se taji maganan ma baya fita a fili ta furta "na shiga uku me nake shirin gani" aiko se taji magan tata ma ba fitowa yake ba magana taci gaba dayi sede baya fita kwatakwata.


Haukacewa tayi ta rasa me zatayi wadda za'a ji a kawo mata d'auki se ta hau jijjiga karafunan cell d'in da iyakar karfinta tana wasu irin abubuwa dukda da hankalinta jikinta ba wai hauka tayi ba sede fa yadda takoma tana wasu irin abubuwa cikin tashin hankali.


*******


A daidai lokacin baba dake cikin tarradaddin kafanshi ya hantsilo ya fad'a kan kafan ba tare da ya sani ba yana shirin tsala ihu yaji ya kasa kaman a wasan koikoyo se ji yai yayi paralyzing a nan ya sheme ya kasa tashi.


A daidai lokacin aka tsuge da Ruwan sama me karfin bala'i wadda shine first Ruwan sama da ya sauko a farkon daminar shekarar, lumshe idanu shaati tayi tana jin ni'imar Allah na ratsata sbd bata rufe windows d'in d'akin ba, karan wayanta ne ya sata bud'e idanun ta zuba mishi gabanta ne ya fad'i welcome back tayi bata da number d'inshi saved one sede daga ganin numbern ta gane shine hawaye ne ya cika mata idanu, yau Saif ne ya d'aga waya ya kirata? Tayiwa kanta tambayar tana kallo har ya katse bata d'aga ba aka sake kira turo kofar da akayi yasa tayi saurin kifa wayar tana share hawayen fuskanta.


Tare da kirkiro murmushi tace "Mama  In zo ne?" Mama da ta tsaya kallonta tace "hmm babanki ke kira" ta karasa tana fita, dukda ta tabbatar Mama taga hawayenta ta za'bi ta shareta tunda bata so ta gani ba, kawai se ta mike ta d'auki hijab ta sa ta fito parlor Abba na zaune yana kallon news sbd 9 da tayi ta kalla tace "sannu da gida Abba" yace "Yauwa uwata".


Zama tayi tana wasa da fingers d'inta seda ya gama karanta headline kan yace "Yauwa uwata dama na kiraki ne inji me kike sha'awar yi sbd zama hakan ba wani anfani ze miki ba ya kamata kiyi wani abin na anfanan kai kan ki samu wani mijin" dukar da kanta tayi tare da d'an nazari nan take ta d'ago "Abba makaranta nake so in koma" Shiru yayi cikin nazari shima kan yace "degree ko school of nursing d'in?" Cikin d'an jin daad'i sbd ta san ze barta yasa tace "Abba Ina so a nema min ABU se in karanci BSc Nursing d'in inaga ze fi tunda dama takadduna sunyi kyau" murmushi yayi yace "kin ci sa'a kuwa nan da 2weeks za'ayi jamb se kiyi registration samun admission ba wani abu bane In har kinci jamb a dage da research".


Godiya sossai tayi cikin farin ciki Alhamdulillah ta furta kan lips d'inta, ta san ba abinda ze d'auke mata hankali irin karatu shiyasa ta za'beshi kuma dama chan ta so nursing Isma'il ya ja mata, gwara su ya fadeela mazajensu sun yarda sunyi karatu amma ita Saif ya ki karatun dama, yanzu kuma dama ta samu kuma se ta dama, d'akin ta koma ta d'auki wayanta tayi blocking numbern Saif d'in kan ta gyara tayi kwanciyarta bacci hankalinta kwance.


*********


Be san ya akayi hannunshi sukayi dialing number d'inta ba sede ya san cikin zafin zazza'bi yayi kiran kuma idanunshi rufe yayi dialing numbers d'in ganin bata d'auka ba yasa ya yasar da wayan yana jin yadda kanshi ke tsananin sarawa hakwaranshi suna had'uwa idanunshi na lumshewa da kansu, cikin zafin zazza'bi yake ji ana knocking ya tabbatar abincin da yayi order ne aka kawo mishi sede motsi ma ya kasa bare ya mike ya kar'ba.


Tafiya akayi bayan five minutes nan ma aka dawo akayi knocking yana ji amma ya kasa tashi again, tafiya aka sukeyi aka sake dawowa se yaji ana bud'e kofan daga nan kuma be sake sanin inda kanshi yake ba, hotel attendants d'in da suka shigo da manager da gudu sukayi kanshi suna bud'e blanket d'in da yake lullu'be dashi ganin halin da yake ciki yasa sukayi rushing d'inshi asibiti dake nan kusa da hotel d'in tare da informing office d'inshi.


Su kuma sukayi azamar kiran zuby bata d'aga ba se suka nemi next of kin d'inshi wadda ya kasance sulaiman ne da Shaati so na sulaiman suka fara kira tunda shine namiji yana zaune yana cin abinci a parlorn yakumbo yayin da su kuma suna zaune gefe suna hirar daminar da ya sauko a yau wayanshi ya hau kara kallon sumayya dake zaune gefe suna cin abinci da sadiyar Anty tala yayinda Antyn talan ke gefe tana danna waya, "sumayya ban wayata" Mikewa tayi ta d'auko mishi ya kar'ba da sauri yana amsawa.


"Hello good afternoon am I talking to sulaiman shamsuddeen suraj? The next of kin to SSS haka yawanci suke ce mishi daga shi har sulaiman abokansu haka suke ce musu wadda hakan ya sa ya gane Saif ake magana kuma a da ya san shine next of kin dinshi kan ya auri Shaati, amsawa yayi da "yes sure hope all is well?" Daga d'aya 'bangaren akace "uhmm he fainted just recently at Lagos yanzu haka he was admitted shine mukace bari mu sanar da gidansu".


Salati yayi yana tambayar me ya sameshi, yace be sani ba but suna bukatar d'an uwanshi kusa don da yamman nan lafiya kalau yanzu yayi hakan shiyasa suka tsorata inda suka tabbatar musu zasu turo musu da tickets biyu na any available flight daze tashi daga kaduna to Lagos se su zo, godiya ya musu yana fad'an sunanshi da na yakumbo don su ya kamatan su je d'in.


Bayan sunyi sallama yake fad'a musu duk se hankalinsu ya tashi suna nan suna jimami har de yaji sako a WhatsApp yana dubawa yaga tickets d'in kuwa aka turo na su biyun, yakumbo ya fad'awa time d'in tashinsu da misalin 11 kan ya mike ya nufi d'akin shi yana tunanin dole ya nemi kud'i kan su fita.


Ta 'bangaren Saif kuwa da kyar suka samu ya dawo cikin hankalinshi aka kara mishi ruwa da alluran bacci Don harda stress a take bacci ya d'aukeshi, ba shi ya farka ba se washegari da misalin sha biyu, a daidai lokacin da su yakumbo suka sauka sede basu karaso ba seda suka kusa share wata awar yana nan kwance cikin azabar ciwon jiki da ciwon da yake fama dashi, sallan asuba dake kanshi yake tunanin tashi ya gabatar sede ya kasa hakan.


Kasala ne sossai ya rufeshi anan kuma take kwakwalwanshi ta fara aiki sbd kwanciyar banza ba abinda yake, tunanin shaati ya fara tun daga farkon rayuwarsu har kawo yanzu gabanshi ne yayi mugun fad'uwa hankalinshi yayi kololuwar tashi "Innalillahi wainna ilaihi rajiun" kawai yake ambata a yayinda tunanin abubuwan da suka faru tun daga aurenshi da zuby har kawo yanzu ba abinda ya manta ko guda.


Dafe kanshi yayi kawai se ga hawaye da azama ya mike yana fisge karin ruwan hannunshi wadda a daidai lokacin likotoci suka shigo da sulaiman da kuma yakumbo da sauri suka rikeshi ana tambayar lafiya ina zashi sede ya kasa  amsawa se waje yake nuna alamu wadda haka ya sa sukayi tunanin kwakwalwarshi ta samu matsala dukda ba wani abinda ze jawo hakan a yanayin Jinyanshi da suka duba sede yadda yake kokarin fusgewa hawaye na gangaromishi yana nuna waje yasa sukayi saurin dankara mishi alluran bacci har biyu a take ya sulale se bacci ajiyar zuciya suka sauke suna juyawa ga yakumbo dake kuka tana tambayar me ya sameshi.


Sulaiman ma tambayar abinda ke faruwa yayi inda d'aya ya mishi bayani da turanci a jiya de zazza'bine sossai kuma me zafi ya saukar mishi amma yanzu basu da tabbaci sede ganin irin halin da ya shiga zasu ta mishi allurar bacci har zuwa suyi scanning kwakwalwanshi kuma de tests na kwakwalwa yana iya kwasar sati biyu kan fitowar result sbd ana bukatar taka tsantsan.


Godiya suka musu kan suka fice yakumbo taja kujera ta zauna tana hawaye tana mishi adu'ar samun Lafiya, haka sulaiman ma daga office d'insu aka kama musu d'akuna biyu na hotel da kud'in asibitin inda nauyin sulaiman kan abinda zasu ci ne kawai.


********


Ko da inna ta shigo ta samu baba a haka da gudu taje ta Kira doctors aka zo aka d'aukeshi aka d'aura gado suka hau bincike cikin bakin ciki suka sanar da inna abinda ya faru magana ma da kyar yake yinta bayan ya farfad'o nan ta fara neman zuby Don sanar mata halin da mahaifinta ke ciki sede taji ana mata yaren da ba ganewa take ba wadda yana nufin wayan a kashe, ta ajiye wayan cikin jimami gashi ta rasa yayan zuby.


Ta 'bangaren zuby kuwa polisawan na ganin halin da ta fad'a suka ja ta suka yasar bakin titi ba bakin roka bare magiya bare kuma tsiwa Sannan bata gani cikin haka ga harshenta da yake zazzare ya cika bakin har ya fito waje yana dilalar da miyau tana ta'ba hannayenta taji sun koma na kutare fad'uwa tayi nan ta fara birgima cikin tashin hankali.


Tana bukatar idanun da zata kalli hanya har taje gida ta nemi Saif ko babanta.


Tana bukatar magana sbd ko zata iya neman taimako a taimaka mata.


The worst part tana tsananin bukatar kafa da hannayenta sbd ta tabbatar In ta zama kuturuwa to fah sede ta rabu da Saif Don baze iya zama da kuturuwa ba bare ita da ta aureshi ta karfi da yaji, Hawaye kawai take zubarwa kaman kogi bata fara nadamar rayuwarta ba kuwa har yanzu.


*********


BAYAN SATI BIYU


A yau shaati tayi jamb d'inta bayan ta Shaa uban karatu kuma ta tabbatar da ikon Allah zata ci, bata kara bi ta kan Saif ba sbd bata damu ba da ya Kirata da kar ya kira duk d'aya abinda ta sani de kawai bazata ta'ba koma mishi ba bayan duk wasu wulakancin da ya mata, karatu zatayi ba maganan aure yanzu a budget d'inta, yaranta suna samun kular da ya dace daga wurin mahaifinta harma da mahaifiyarta karatunsu makaranta me tsada ci da sha da kula da tarbiya duk suna cikinta hakan yasa bata ta'ba d'aga hankalinta ba.


Kwance take tana chatting da jidda se kuma kawai ta kirata vídeo call wai tana son ganin zaheeda sbd isarta da voice note da tayi hira suka hau yi da uwar da 'yar inda zaheeda ta damu a kira mata beautiful friend d'inta neeha, shaati tace karta damu zasuyi magana anjima sbd ita yanzu bazata iya tashi ba, da kyar jidda ta korata suka fara hirarsu ta kawayen da suka shaku da juna, suna cikin hirar kawai aka fisge wayar daga hannun jidda bata hankara ba se ganin Shareef tayi yana kallonta.


A zabure ta mike sbd kanta da ba d'an Kwali kalabar da ya meena ta mata last week sun sauko har kafadunta daga ita se T-shirt da ya Kama ta da jean da sauri ta sa mayafi ta rufe kanta zuwa kirjinta kan tace "Ina yini?" Tunda suka bar maiduguri basu sake kallo ko jin muryar juna ba, sede time to time ta san yana gaisawa da Abba da kuma mama, ita dayake be ta'ba nemanta yasa ta tattarashi ta watsa kwandon shara kaman yadda tayi da Saif.


Amsawa yayi da "lafiya ina lil Shareef" haska mishi fuskanshi tayi na minti d'aya kan ta dawo kanta yace "masha Allah a shafa min kanshi, naji kinyi

Jamb Allah ya bada sa'a, bye yanzu lokaci na ne" ya karasa yana kashe wayan ba tare da ya jira jin me zata ce ba murmushi ta saki tana girgiza kai wato lokacinshi ne, Mikewa tayi ta fita parlor tana mamakin halinshi na ko In kula.

                  🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇

   *Baya Chanza d'and'anon teku*


    *Fatima Muhammad Gurin*

  **Gureenjo6763 on Wattpad**


           'Yar Mutan Adamawa


*Wannan page d'in naku ne En Gureenjo novels group comments d'inku na sani nishadi godiya nake🥰*


     *P34*


A yau result d'inshi ya fito, Anty tala da bata jima da sauka ba ta zuba tagumi tana nazarin, yakumbo ta katse mata tunani "tala muje muji me zasu ce tunda naga lokacin da suka ce ze fito d'in yayi ko Ina sulaiman ya tsaya?" Tana rufe baki sulaiman na shigowa se kawai suka mike suka fice a tare zuwa office d'in doctorn da Saif ke hannunshi, zaune suka sameshi yana dubawa suka shiga ya sauke ajiyar zuciya yace "Alhamdulillah lafiyar shi kalau In Shaa Allahu zamu mishi wata allura yanzu anjima da yamma ze farka da yardar Allah".+


Godiya suka mishi kan suka fito yakumbo tace "ko me ya saka shi acting haka?" Sulaiman yace "maybe, maybe fah ya dawo hankalinshi haka nake tunani" Anty tala tace "tabbas ze iya yiwuwa amma na matukar tausaya mishi yadda yake son shaatin nan yanzu ya san ya saketa Ina ze saka rayuwarshi" yakumbo karan kanta damuwar hakan ne dankare a zuciyarta.


Basu jima da komawa ba doctorn ya shigo ya mishi ya fice ya tabbatar musu nan da four hours in shaa Allah ze farka lafiya, aiko dab magrib ya farka a kasalance ya bud'e idanunshi da suka mishi nauyi yana kallon saman d'akin, ya kai 2mins kwance idanunshi a kafe a saman POP d'in d'akin Abubuwan da yayi mata su ke sukar ranshi har gwara mahaifiyarshi ita a kullum Suna tare kuma me yafiya ce a gareshi a ko wani hali amma Aisha!! Sunanta da ya furta cikin zuciyarshi ma seda yaji gabanshi ya fad'i yafi kowa sanin irin zuciyarta.


Runtse idanu yayi se kuwa hawaye suka gangaro mishi tuna randa ya sakata bud'e gate ga tsohon ciki, gorin rashin kawo budurcinta gareshi da yayi alkawari har Abada baze ta'ba nuna mata ko alamun a fuska ba, sakinta cikin dare ga ciki ba imani ya kuma korarta a lokacin, mari... abinda ya san tafi tsana a rayuwarta namiji me duka anya ze iya yafewa kanshi bare har ya iya rokar gafararta? Yaranshi.


Kawai gani sukayi ya mike zaune ya cusa kanshi tsakanin cinyoyinshi abinda ya manta rabon da yayi se gashi yana kuka da hawayenshi kuka me cin rai bakin ciki ya mishi yawa, tsanan kanshi yake ji har kasan ranshi, kau da kai sulaiman yayi hawaye na cika mishi ido yayinda Anty tala kam kukan take tayashi yakumboce ta mike ta dafa bayanshi tana bubbugawa aiko se ya d'ago ya jinginu da ita tare da runtse idanu cikin rawr murya yace "Hajiya taya zata iya yafemin? Ta yaya yarana zasu iya yafemin? Me ya hau kaina har idanu na suka rufe na aikata abinda na aikata ga shaati? Nayi zarginta, I slapped her and then accused her akan abinda batayi ba and divorced her a tsakiyar dare da tsohon ciki hasbunallahu wani'imal wakeel......"


Duk seda suka mishi kuka ba abinda yafi ciwo shine kayi abu ba tare da sanin kayin ba, yayi hurting mace mafi soyuwa a ranshi bayan mahaifiyarshi cikin rashin sani da sharrin mace irin zubaida, sunanta da ya ambata yasa ya tuna ya baro ta asibiti baze ta'ba yafe mata ba sede ba abinda ze mata sede ya saketa ya dankawa mahaifinta taje ita da Allah.


Share fuskanshi yayi yana tunanin wani irin hakuri ze iya ba shaati har ta hakura, yakumbo ta share hawayenta tace "ka yafemin nice sanadiyar duk wani halin da kuka shiga na kasa hakura In yarda kaddarar shaatince haka na ja maka abinda har ka mutu bazaka manta ba" cikin dashewar murya yace "baki da laifi hajiya haka Allah ya kaddara hakan rubutaccene daga rabbissamawati" ajiyar zuciya ya sauke yana mikewa daga jikinta ya furta cikin sanyi "Ina wayata?" Sulaiman ya fiddo daga aljihunshi yace "gashinan" kar'ba yayi ya duba number d'in hospital da zuby take kira yayi cikin sanyin murya suka gaisa ya tambaya Ina patient d'inshi nan sukace sunyi discharging d'inta sun kira wayanshi Baya shiga, suka mishi karya sbd ya kamata yayi suing d'insu taya patient zata bar asibiti ba tare da hospital sunyi noticing ba? Abinda suka sani tunda tana cikin hankalinta zata iya kai kanta gida.


Godiya ya musu ya kashe ya kira layinta Baya shiga, gateman d'inshi ya kira yana tambayan ko ta koma? Ya tabbatar mishi bata dawo gidan ba, tsaki yayi yana jefar da wayan, sulaiman ya taimaka mishi zuwa toilet yayi wanka tare da alwala ko mai be shafa ba ya saka wasu kananun kaya da sulaiman ya d'auko mishi daga d'akinshi na hotel cikin kayanshi, sallah ya fara gabatarwa cikin natsuwa dukda chan kasan ranshi damuwane dankare hankalinshi tashi yake ko da wasa In ya tuna Aisha taya ze fara shawo kanta sanin shegiyar kafiya da zuciyarta? Allah ya mikawa komai ya tabbatar In Allah yayi zata dawo mishi ko min fushin da tayi dashi zata sauko.


***********


Sati biyun nan ya zamewa zuby kaman shekaru biyu cikin azabar rana da ruwa, ga yunwa da kishi a ranar da abin ya faru da ita da kyar ta lalu'ba da lalu'be ta isa jikin wani gida ta zauna nan Ai batayi seconds ba guards d'in gidan suka fito suka ci mata mutunci suka fatattaketa tana kuka tana tafiya gashi ba bakin neman alfarma a kira mata numbern Saif, ba hannun rubutawa a paper ta mika ba ma idon, da kyar da makyarkyata ta samu wani unguwa da ba mutane cikin wani sabon gini da akeyi ta lalu'ba ta zauna.


Yunwa kaman ze kasheta hakan ya sa ta fara jujjuya hannunta ga duk wadda yazo wucewa se ta nuna bakinta abin tausayi, da kyar wani yaro yazo wucewa rike da takeaway d'in chips ganin yadda takeyi yasa ya tausaya mata ya bata abincin da sauri ta fisga tana ci hannu baka hannu kwarya har tana kwarewa bayan ta gama ta had'a hannunta alamun godiya ya juya ya fice, anan taci gaba da zama yaron nan da ta lura tausayinta ne ya kamashi yasa kullum ze kawo mata abinci sau d'aya da ruwa anan uncompleted building d'in take rayuwa ba wanka bare wanki bare kuma sallah sede zuwa yanzu ta fara tunanin abinda tayi ne yake dawo mata.


*************


Bayan kwana biyu result d'in jamb d'inta ya fito kuwa taci sossai ba laifi nan take Abba ya kira wani friend d'inshi dake registerer na NAS gabad'aya wato sciences ya roki alfarmar sama mata admission nan da nan kuwa ya tabbatar mishi ta samu ta gama Tunda dama result d'in waec d'inta yayi kyau sossai ga jamb taci ya tabbatar mishi cikin first batch kuwa sunanta ze fito In shaa Allahu.


Godiya ya mishi sukayi sallama murna kaman me shaati ke yi dayake tana nan suke wayan kuma a handsfree Abba ya saka shi, godiya tayiwa Abba tana mikewa, d'akin yaran taje suna baje sameer na game a iPad d'inshi yayinda yasmin da Arwa ke homework sunayi suna hira abinsu neeha kuwa na had'a word puzzles, suna ganinta suka sakar mata murmushi itama murmushi tayi tana zama gefen neeha a tare suka ci gaba da had'a word d'in suna hira cikin sakewa kaman ba wani abu cikin zukatansu da rayuwarsu.


Shareef ne ya fara tsala kuka daga wurin baba larai inda Arwa ta mike don kar'boshi cikin umarnin mahaifiyar tasu, se gata da shareef a kafad'a hannunta rike da waya da sauri ta mika mata "maami ana Kiranki" kar'ba tayi tana picking ta makala kafad'a tana kar'ban shareef da be bar kuka ba, "Kai kam shareef baka da hakuri in kaji yunwa wallahi".


Muryarshi taji yana cewa "ko kece kika ji yunwa ba hakuri zakiyi ba bare lil shareef kar a matsa mana da fad'a ehe" dariya ta saki tana cewa "laaa ya reef barka da yamma" kaman yadda Jiddah ke Kiranshi, yace "Yauwa Aisha, yayanki ya nemeki tunda ke bazaki iya kar'bar number d'inshi ki kirashi ba" Tace "am so sorry wal..." katseta yayi "no is Ohk karki damu, wannan tsohon saurayin naki ya isheni da ragwantaka Allah namiji ne amma wata macen ta fishi abin arziki banza rago".


Dama yana zagi? Tayi maganan a zuciyarta bata ma san a fili tayi ba se ji tayi yace "in ta kama ba" se kuma maganan tsohon saurayinta yayi clicking mind d'inta waro ido tayi tace "Mijin mama? Bade kai ka saceshi ba yaya shareef?" Kwafa yayi yace "yaci sa'a ma ban kasheshi har lahira ba sbd a musulmi nazo" Tace "pls kayi hakuri ka sakeshi hakanan na tabbatar zuwa yanzu yayi hankali" had'e rai yayi yace "bade har yanzu kina sonshi ba?" Da sauri tace "Auzubillah Allah ya tsareni" for the first time taji dariyarshi haka a sanadiyarta sossai yayi dariya kan yace "hmmm zan sakeshi amma har yanzu banji na rama miki kwatar abinda ya miki ba, bansan abinda zan mishi In gamsu ba Allah kila nakastashi zanyi".


"Ayyah kayi hakuri da ma ka barshi zamanshi da matarshi mama ma kawai ishara ne ga masu irin halinshi na tabbatar yanzun ma be ji da daad'i ba 'barawo hannun mata" murmushi yayi yace "to zagemu da wayau" dariya tayi tana kallon neeha datake cewa "pls maami I want to greet uncle" jin abinda tace ne yasa yayi murmushi yace "give her the phone" bata tayi yace "hi beautiful neeha" washe baki tayi tace "hello handsome uncle" dariya sossai yarinyar ta bashi bakinta kaman zaheeda ya furta a ranshi.


Yace "how are yhu?" Tace "am fine uncle" yace "don't call me uncle ur friend zaheeda used to call me Appah kema haka zakina cewa, where are your siblings?" Tace "Ohk Appah, yaushe zaka kawo beautiful zaheeda In ganta maami refused to take me to her" yace "karki damu hai on Monday in shaa Allah we are coming" ihun daad'i tayi tana mikawa yasmin da itama take son waya dashi gaisawa sukayi itama ta bawa sameer shima suka gaisa se jin daad'i yake Appah ya kirashi lil soldier, Arwa ce karshe itama suka gaisa kan ya kashe wayanshi nan fah yaran suka kafa hiranshi.


Itade shaati tayi shiru tana tunanin da gaske ne ze zo Monday d'in ko wasa yake yiwa yaran? Ta jima tana nazari kan tayi murmushi Lallai mijin hajiya Mama saratu yaci ubanshi hannun sojoji ta tabbatar, shareef dake tsaye jikin guard room d'in ya kalli Isma'il da ya chanza kammani ya koma wani hallita daban, fuskan nan ta kumbura suntum tsabar duka har Baya gani sossai In idonshin ma be samu matsala ba.


Azabar yunwa na addabarshi don se ya kwana d'aya ake bashi abinci sau d'aya sede yana d'an ta'ba ruwa ana bashi dukda shima ba akai akai ba, ba kalar d'aurin muguntan sojoji da be sha ba waenda suke gana mishi azabar ma karan kansu in tsiya da muguntarsu irin ta Soja ta tashi haka zasu mishi d'aurin kidnappers suci ubanshi ko da Shareef be ce ba, ya rame gwanin tausayi.


Harara shareef ya watsa mishi wadda ya sashi saurin kauda kanshi cewa yayi "na so da daga kan Aisha baka kara sanin wata mace ba a rayuwarka har Abada kai komai na Maka wallahi ban jin zan rama mata abinda ka mata, amma yanzun ma bata 'baci ba ka gama sanin mace a rayuwarka kai ku dandakeshi" ihu ya tsala yana rokan gafara amma shareef ko a jikinshi ya juya ya fice kurtayen sojoji kuwa mugunta ta tashi mana nan take suka nemo wata guduma tapkekiya suka ware kafafunshi.


*********


Ya kira layinta bila adadin sede baya shiga wadda ya tabbatar mishi blocking d'inshi tayi tun daga ranar da be san ya akayi ya kirata sau biyu ba, dole ne a gobe lahadi ya bar lagos ya tafi Abuja ya d'auki wannan shegiyar da ta tarwatsa mishi gida da takkadarta ran Monday ya bayyana kaduna dole ze fuskanci Aisha koma me zata mishi tayi mishi.


Sallaman da ya nema aka kawo mishi da dare jirginsu yakumbo ze d'aga ya Ware so da kanshi ma ya kaisu Airport ya tabbatar musu shima In shaa Allah Monday ze shigo kadunan seda yakumbo ta mishi fad'ar kar ya kuskura ya sawa kanshi damuwar komai ya barwa Allah shi ya san yadda ze yi shi ze iya mishi, godiya ya musu sossai dukkansu sbd sun tsaya mishi a ko wani hali basu yasar dashi ba In ya tuna abinda ya ma sulaiman ko kunyar kallonshi yake har seda sulaiman ya gane ya mishi maganan hakan.


Ya tausayawa Anty tala ma jin abubuwan da suka faru nan ya nuna mata abinda ya jima yake son nuna musu daman, baka san abinda Allah ze yi ba, tambayarsu Ya sukaina yayi sukace tana lagos dinnan da jimawa sede ko wayansu ta dena d'agawa ta dena kiransu tun da jimawa inda ya tabbatarwa yakumbo In ya natsu ze nemeta karta d'aga hankalinta.


Bayan tafiyarsu shima yayi booking flight na Abuja kan ya koma office nan ya roki su bashi hutu sbd stress ne ya mishi yawa har hakan ke faruwa ya jima be d'auki wani leave ba haka suna ji suna gani aka cire shi a aikin da ya kawoshi lagos, hotel room d'inshi ya koma ya had'a kayanshi, ya nufi Airport ba 'bata lokaci jirginsu ya d'aga se Abuja, yana sauka ba wadda ya fara nema se...........                  🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA........💦🍇

  *Baya Chanza d'and'anon teku*


     *Fatima Muhammad Gurin*

   **Gureenjo6763 on Wattpad**


           'Yar Mutan Adamawa


   *P35*


"Yassar please listen to me duk abinda na maka I wasn't my self se kace baka san halina ba? Tun shigowa na nan almost 20 mins ka kasa tsayuwa ka

Saurareni? Idan kai baka saurareni ba Aisha kuma da nake hoping fah..." ya karasa a raunane yana zama idanunshi na cika da kwallah ya zama wani iri yanzu kaman ba namiji ba hawaye na saurin zuwar mishi muddin ya tuna irin abubuwan da ya aikatawa shaati duk cikin sharrin zubaida.


"Shikenan ya wuce Saif na san ba yinka bane sede ko kaki ko kaso harda sakacinka wurin duk abinda ya faru azkar dinnan In kayi na safe da kyar kake na yamma, Allah ya tsare gaba ya raba duk wani namiji da sharrin mace irin zubaida" Da Ameen kawai ya amsa idanunshi na kafe wuri guda yayinda lip d'inshi na kasa ke cikin bakinshi yana ciza a hankali.+


"Ina take?" Ya san wa yake nufi so ajiyar zuciya ya sauke tare da feso iska daga cikin bakinshi yace "I don't know" yassar yace "to me zaka mata?" Idanunshi ya zubawa yassar na mintuna yace "nothing I will just divorce her and take her to her parents kaman yadda shari'a ya tanadar Hakkin shaati kad'ai ya isheta bare kuma na su Yasmin, because in nace zan mata wani abin I might end up killing her".


Mikewa yassar yayi daga kujeran office d'inshi yace "let's go together" fitowa sukayi zuwa gidan daga bakin gate ya tambayi gateman ko tana nan yace bata nan tun randa ya fita da ita a hannu basu kuma ganinta ba, fita sukayi cikin motar yassar din bayan ya ajiye luggage d'inshi, asibitin suka koma nan suka tabbatar musu sun sallameta bincike yazo har gate securities d'in suka tabbatar musu bayan fitanta wanchan restaurant na tsallake ta shiga.


Tsallakawa sukayi suka tambaya nan aka basu labarin abinda ya faru ranan har police station d'in sukaje suma suka fad'a musu abinda suka sani tabbas a lokacin ran Saif ya kai kololuwar 'baci da wacce yake so ne ko kuma wacce ya sani me mutunci a idonshi ba abinda ze hanashi suing police station, asibiti da restaurant d'innan sede sun ci sa'a, neman ta da yake ma so kawai yake ya damka mata takardarta ya damkata hannun iyayenta kaman yadda suka bayar sbd In magana taje tazo harda mahaifiyarshi da uncle's d'inshi tsundum ciki.


Da polisawan suka fara bincike sbd ganin mijin nata ba karamin mutum bane ba, da arzikinshi iya gwargwado, tun safe suke abu d'aya se yamma lis suka iso unguwar da take, dandazon mutane ne daya taru a gefe an chabke wata mata ana bugu ya ja hankalinsu polisawan nan suka dakata Don duba abunda ke faruwa da kyar suka kwaceta matasan nan na ikirarin se sun kasheta wallahi.


Kallo d'aya Saif ya mata ya d'auke kai tare da tsirtar da miyau a zuciyarshi ya furta Allah ya isa sani had'a jiki da kikayi dake, In ka ganta a lokacin kaman sabuwar mahaukaciya datti har naso yake a jikinta kayan jikinta sun had'u da jini da daud'a sun bada wani banzan kazantaccen colour, wara ido yayi jin abinda wani saurayi ke fad'awa polisawan.


"Kisa fah tayi yalla'bai" police d'aya yace "ta yaya a wannan yanayi irin nata?" Matar dake kuka cikin tashin hankali tace "wannan munafukar matar tun satuttuka biyu zuwa uku da suka wuce ta zo Anguwan nan from no where ta tare cikin wanchan kangon, tunda d'ana ya kyalla ido ya ganta ya hau kai mata abincin shi a kullum tun ban lura ba har na fara lura ba yadda banyi don hanashi ba yaki In har ban saka mishi ya kai mata ba ya dinga kuka kenan da birgima, ashe itace ajalinshi yau ya kawo mata abinci tun wurin sha d'aya har kusan awa biyu be dawo ba shine na biyoshi kawai na samu gawanshi a yashe gabanta tana cin abinci hankali kwance kuma wallahi ba makauniya bace tsab tana kallo don har had'a idanu mukayi ta kawar".


Matar ta karashe da tsananin kuka nan matasan sukayi Chaaa "a bamu ita mu karta kawai" ankwa polisawan suka saka mata d'aya yace "kiyi hakuri ki bamu yaron za muyi bincike ita kuwa zamu tura ta court" juya kai kawai Saif yayi abin kunya abin takaici motanshi ya koma ya rubuto mata takardar sakinta guda uku ze fito yassar ya rikeshi yace "me kakeyi? Kana son lalata image d'inka ne a gaban mutane?" Yace cikin takaici "wani image d'in kuma nake dashi bayan wadda ta tarwatsa? Me ma kake nufi? Kana nufin kar In saketa?".


Girgiza kai yassar yayi yana furta "ban ce ba baka ganin masu viewing da recording har da locals stations in suka d'auka suka kai gaba suka fassaraka da wata manufar fa?" Ajiyar zuciya ya sauke yana gyara zama se kuma ya d'aura kanshi kan laps d'inshi takaici da bakin ciki sun mishi yawa Allah ya gani, bayan police sun d'auketa sun tafi da ita se yassar ya ja motar ya bi su a baya har police station kasa motsi Saif yayi se shi ya sauka ya kai musu takardar ya bada numbern iyayenta akan su nemesu suyi magana mijin ya riga da ya saketa.


50k da yayi dropping kan desk d'insu ne ya hanasu magana ya juya ya fice yadda ya barshi haka ya dawo ya sameshi Jan motan kawai yayi yana girgiza kai tausayin aminin nashi na kara hauhawa a ranshi, har gida ya kaishi a take ya sallami masu aikin da ta tara ta barsu gidan suna abinda suka ga dama da komai, yassar ne ya rikeshi ganin yadda yake layi "Saif yaushe rabonka da abinci?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "yesterday's lunch" wara idanu yassar yayi "are you crazy? Taya za'ayi ka hana kanka abinci tun jiya fisabilillahi?" Fisge hannunshi yayi yana furta "whatever" ya shige parlorn girgiza kai yayi ya juya yaje ya yo mishi takeaway ya dawo


A parlor ya sameshi kuwa yana kishingide ji yake kaman ya wuce kaduna yanzu but he have to report kan ya Tafi gobe in shaa Allah, yassar ya jima dashi yana kwantar mai da hankali don yadda ya damu se ya baka tausayi shi abinda ke bashi tsoro fushin shaati be da kyau, Sannan In ya tuna abubuwan da ya mata a lokacin wani irin kunci ke ziyartarshi mara misaltuwa, har dare kan yassar ya tafi.


**********


"Ku maidashi inda kuka d'aukeshi ku yasar" yana kai nan ya katse wayan tashi Bayan sun tabbatar mishi aikinsu ya cika, jidda dake serving d'inshi tace "me yake faruwa haka ne ya reef?" Kallonta kawai yayi ya d'auke kai kenan baya son maganan hakan ya sa ta kyaleshi ta karasa saka mishi abincin ta tafi shiryawa zaheeeda kaya sbd ya fad'a mata tun jiya gobe ze wuce kaduna ze gaisa da su Abba da basu ta'ba had'uwa ba Sannan ze barta wurin shaati nan da two days in ya gama abinda ya kaishi abuja ze dawo ya d'auketa se su taho gida tare.


Bata sa komai ranta ba se ma shirya abubuwan da za'a kaiwa shaati take, a cikin kayan zaheeda ta shiryasu tsab don sarai ta san halin shi In hannunshi ta bada bama ze kar'ba In ko ya kar'ba tabbas a car d'in da ya kaishi Airport ze bar mata ko a Airport d'in, shima zuwa tayi ta shirya mishi nashi kayan a jakanshi irin na sojoji da ya saba yawo dashi a baya daga wanchn gari zuwa wanchan gari, wurinshi ta koma tana tambayar karfe nawa ne flight d'in.


Kaman baze amsa ba se kuma yace "10:30" zama tayi ta zuba mishi idanu wasu halayen da yake mata kwanan nan sam bata sonsu ba haka suke da ba yana yawan shareta yanzu yana yawan had'a mata rai ta rasa dalili, dayake ita bata iya boye abinda ke ranta ba tace "Ya reef ko wani laifin na maka ban sani ba?" 'Dagowa yayi ya kalleta yadda tayin kuma se shima be ji daad'in abinda ya aikatan ba wadda shi karan kanshi ya rasa dalilin hakan kawai zuciyarshi ke saka mishi kawai zama yake da ita ba wai Don yana sonta ba.


Aurensun dama had'i ne akayi katari kuma tana mugun sonshi sbd sun saba tun tana karama da aka mishi suggesting aurenta kuwa be musa ba ya kar'ba so tunanin hakan yasa zuciyarshi ke bashi har yanzu be san menene so ba, murmushi kawai ya mata yana me mikewa ya fice ajiyar zuciya ta sauke tana furta "Toh Allah sa dae kalau" tattara kwanukan ta fara a tsanake.


************


Kwance take tana game a wayanta yayinda shareef ke gefenta yana chichilla kafa da hannu Mama ce ta turo kofan ta shigo da sallama, Mikewa zaune shaati tayi tana furta "Mama akwai wani abinda zan miki ne?" Murmushi mama tayi tace "Ina fa bayan kin cika mana ciki da beta" dariya tayi tana gyara zamanta Tace "Kai Mama ai training d'inki ne" maman ma murmushi tayi tace "Yauwa kinga d'azu Abbanku ke fad'amin gobe shareef ze zo da zaheeda so ya kamata ki shiga kasuwa kiyo sayayyar duk abinda zaki bukata da babu a gida kin san tarbar da ya kamata su samu Ai" murmushi tayi tace "kwarai kuwa bara nayi wanka se nazo muje sede fah nan gida zan bar wannan sarkin rikici da naushin" dariya mama ta saki tana fita tace "ba dole yayi naushi ba anyiwa soja takwara" tana dariya itama tace "Ai da na san ana gadon halin masu sunan da ma ban fara ba" Mama de ficewa tayi tana murmushi ita kuwa shaati seda ta d'an dangwalar mishi kai ta mike ta fad'a toilet haka kawai take jin nishad'i har fata take gobe yazo.


************


An sallamo baba yau sbd yaki zaman asibitin dukda jikin be warke ba sam yayinda inna kuwa ta fara gajiyawa da jinyar tashi, suna isowa ba da wani jimawa ba wasu masu bakaken kaya sukayi sallama Bayan sun parker wata bakar picnic doguwa innan ce ta amsa tana fitowa ganinsu yasa ta gyara tsayuwa tana gyara murya tace "sannunku bayin Allah, lafiya kuwa?" D'aya baki da fuskanshi ba d'igon fara'a yace "yaron gidanki ne aka kama suna kokarin kidnapping yaron ministern wutan lantarki so garin ceto shi yaron mu SS muka harbesu kidnappers d'in Bayan sun kashe mana mutum biyu mukayi nasarar kamasu yanzu haka shi ya rasa ranshi ya ma ci sa'a sauran kam an kamasu" a tsorace inna tace "mene? Na shiga uku me yake faruwa da mu ne?" Se kuka.


Ba abinda suka ce mata ganin ma zata 'bata musu lokaci se kawai sukace "a zo a fiddashi muna da abinyi" ba Don tsoron ganin yadda fuskansu yake ba da ta d'ud'uramusu zagi nan ma bata barsu a zuciyarta ba se tsine musu take, gidan me unguwa dake makwantaka dasu ta shiga ta sanar mai tana kuka ta san ko ta fad'awa uban yanzu ba abinda ze iya, ba Don albarkacin musulunci ba babu abinda ze sa ya tara mutane en kalilan ayi mishi wanka a kaishi makwancinshi sbd ba mutunci ne da su ba bare ma kar shi yaron yaji labari ya addabi kowa unguwan wasu har murnar mutuwar tashi suke.


*********


Tafe take tana waya da meena tattaunawa suke akan karatunta suna dariya sbd yadda take bata labarin uwar wahalan da Tasha da haihuwa, goyo da karatu, kaman daga sama taji wata motar da taho a guje kaman ba kasuwa ba dayake inda take irin bud'ad'an space ne da parking space kato na kasuwan parker motanta kenan ta fito, dukda ba bugeta motar tayi ba sede ta goge ta sossai har wayarta ta fad'i screen guard d'in ya fashe.


"Kan bala'i" ta furta tana juyawa ai kuwa taci sa'a wai parking ze yi yake tsula wannan gudun cikin kasuwa aiko ko da ba parking ze yi ba se ta d'auki plate number d'inshi ta kaishi police station, wayanta ta duka ta d'auka ta juya ta nufi motan har yanzu na ciki be fito ba, tana isa ta sa hannu ta kwankwasa glass d'in ganin ze 'bata mata lokaci ta kama handle d'in ta fisgo aiko se gashi ya bud'u cikin bala'i tace.


"Wani irin rashin mutunci ne wannan? Taya za'ayi kana driving kaman wani makaho fisabilillahi? Kaci sa'a wayata ka fasa da kuwa ka kuskure bugeni I promise you se kayi dana sani, mtseww" ta ja tsaki ta juya tana banbaminta kaman zata ari baki, "ji mana" taji ance daga cikin motan dakatawa tayi tana cewa "kutumelesi ni yake wani cewa ji mana?" Ta kuma jan tsaki ta cigaba da tafiyan ta batayi taku biyu ba aka sha gabanta.


Had'add'en saurayine kuwa sede da gani babba ne ba irin chan ba kaman de su ya majeed haka yana da kyau Don kyau sede hakan be d'ad'a ta da kasa ba Don ko itama baze nuna mata kyau ba, harara ta zagba mishi tace "malam kaucemin a hanya In wuce ka wani tsatsareni da idanu" murmushi me kyau ya saki yace "I'm so sorry kiyi hakuri ban lura bane" yadda yake hausa yasa ta tabbatar shi ba bahaushe bañe don hausa bata isheshi ba, zagayeshi tayi zata wuce ya kuma shan gabanta.


"Sorry" tace "ya wuce sede ka dinga lura In kana driving, se kace wadda ya koyi tuki a kan titi ba driving school yaje ba" "In shaa Allah ma" ya furta ta kuwa watsa mishi harara ya saki murmushi yace "to tunda kin hakura a ban phone number mu dinga gaisawa kinga se ki ci gaba da min nasihar taki kullum" zatayi magana yace "pleasesss" ya karashe yana jaa, bata da option ganin yadda ya tsatsareta da idanun roko kaman wata neeha In tana pleading, mika mishi wayan tayi yana kallon fuskan ya wara idanu "aikin da nayi kenan subhanallah" se kuma ya d'aga yana wawwara idanunshi a kasuwan se kuma ya kalleta "ga wani shop chan muje In canza miki" zatayi magana ya sa hannu a lips d'inshi yace "shiiiii" Shiru tayi ta bi shi don har yayi gaba.


Bayan an chanza mata screen guard d'in har wata sabuwar had'addiyar pouch ya saya mata yadda bata tanka ba haka shima be ce mata komai ba bayan an gama sakawa an bashi yayi dialing number d'inshi ciki seda ya shiga kan ya mika mata "am suhail" Tace "Aisha" tana kar'aban wayan nata tace "thank yhu" tayi gaba abinta murmushi kawai ya saki sossai ta burgeshi iyakar burgewa taune lower lip d'inshi yayi kan ya wuce yana wani irin tafiya da daga gani zaka san akwai sarauta nan.


         *Masoyana en Gurinjo Novels group Ina yinku over irin over d'innan, thanks for your prayers son so. And Ameeratuh a dena kishi da en gureenjo novels much love🥰🥰*1

                 🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA........💦🍇

  *Baya Chanza d'and'anon teku*


     *Fatima Muhammad Gurin*

  **Gureenjo6763 on wattpad**


          'Yar Mutan Adamawa


     *P36*


MONDAY


Tun da ta Idar da sallan asuba bata koma ta kwanta ba, se ma EarPods da ta makalawa kunnenta ta saka karatun qur'ani tana bi tare da dukufa musu breakfast seda ta gama breakfast na gidan ta zuba a food-flasks ta kai dining ta jere su kan ta dawo ta fara had'a nashi zobo ta fara d'aurawa se tuwo da ta tuke shi na semo ya tuku sossai ta saka a ledojin tuwo tare da rufesu a wani had'ad'un flask.+


Bayan ta juye zobon kan ya huce ta fito yin breakfast sbd tana jiyo sautin yaran da iyayenta akan dining d'in kan ta zauna ma sun had'a baki wurin cewa "good morning maami" ta amsa da murmushi saman fuskanta kan ta gaida Abba da mama cikin ladabi suma suka amsa fuskansu washe, Mama ta gama serving kowa so kanta kawai ta sawa ta had'a tea suka fara ci a natse.


Bayan sun gama ta koma kitchen d'in ta d'aura miyar egusi da Tasha crayfish da naman karamar dabba ga ganda, kan kace me gidan nan ya bule da kamshi bayan ta gama, ta d'aura mishi chicken biryani da taji jidda tace yana matukar so sbd zaman india da yayi, bayan ta gama ta zuba shi shima a had'ad'en warmer, se lokacin ta had'a zobonta dake tashin kamshin abarba, citta da flavour ta saka a jug ta sa a fridge, sauran kayan kuwa ta jeresu saman kanta, bazata iya gyara kitchen d'inba sbd gajiyar da tayi so se ta kira me aikinsu lantana ta zo ta hau gyarawa ita kuwa ta wuce d'aki.


Seda ta shayar da shareef dake kwance kan gado shi kad'ai abinshi yana wuwulla kafa kan ta fad'a toilet tayi wanka da ruwan d'umi ta zo ta bi lafiyar gado kan ta fara bacci arwa ta shigo ta d'auki Shareef suka fice nan take bacci ya kwasheta, ba ita ta farka ba se 10mins past 12, nan ma sbd kukan da take ji na shareef toilet ya fad'a Don wanke fuskanta se ta fito ta amsheshi se kawai ta tsinci kanta da wanka bayan ta fito kuma se ta dena jin kukanshi se kawai ta zauna gaban dressing mirror ta fara shafa body mist, kan ta d'aura manta kai ta feshe jikinta da body spray kan ta je wardrobe ta fara neman kaya bazata iya saka atampha yanzu ba se kawai ta samu blue jean and pink top ta saka ta d'auko black abaya da yaji adon peach na manyan flowers da stones ta d'aura kai ta d'aura igiyar rigar ya zauna mata cas.


Bata saka hula ba se gyalen da ta yafa bayan ta gyara parking d'in gashinta ta koma ta kuma fesa perform nan kamshinta ya bule d'akin seda ta gyara gadon da ta kwanta kan ta nufi parlor hayaniyar su Neeha duk ya cika mata kunne, Tana gama bayyana parlorn a kanshi idanunta suka fara sauka aka ci sa'a shima tun kan ta iso kamshinta ya isar mishi da sakon tana kusa seda suka kalli juna na kusan minti d'aya kan tayi saurin d'auke kai daidai lokacin zaheeda ta fad'a jikinta cikin ihun murnan ganinta.


Da murna itama ta tareta ta rungume "oyoyo lil Angel" dariya en parlorn ke yi sbd zaheeda duk ta damesu da surutu dama duk yadda suke korafin surutun neeha se suka ga zaheeda ta dameta ta shanye, se lokacin ta lura yayyunta gabad'aya suna parlorn gaidasu tayi d'aya bayan d'aya suka amsa banda hameed da har yanzu tana lure dashi kallon kallo yake mata, shine karshe ta gaida "ya reef Barka da zuwa ya hanya?" Yace "Alhamdulillah mun sameku lafiya?" Tace "Lafiya kalau Alhamdulillah" tana kallon Shareef karami dake hannunshi yayi d'ib yana shan yatsa.


Murmushi tayi tana mikewa zaheeda Tace "maami Ammi tace ki duba cikin kayana ta saka sako In kin gani ki kirata a waya, and then tace In gaisheki sossai In gaida granny, kar inyi fad'a da beautiful neeha, banda taurin kai banda 'barna, wai da gaske ne in nayi 'barna kina duka?" Se ta turo baki ta kuma cewa "Ai da kike gida baki ta'ba dukana ba right?" Zata kuma yin wani maganan yace "zaheedah quit pls wai ke bakinki Baya ciwo?" Turo bakin tayi sauran en parlorn se dariya sukeyi shaati na murmushi tace "Ohk dear duk naji and bana duka sede fah kikayi ma granny 'barna tana duka" waro ido tayi daidai lokacin Mama ta fito daga d'aki tace "granny da gaske kina duka?" Tayi maganan a shagwa'be kan mama ta amsa neeha ta kama hannunta tace "beautiful zaheeda muje muyi wasa a garden" da gudu suka fice suka bar shaati da ajiyar zuciya.


Ko bata kalleshi ba ta san idanunshi kanta suke Don tana jin kaifinsu a jikinta, se ta rasa me zatayi zama zatayi ko juyawa d'aki zatayi, har ta juya da nufin shigewa d'aki se shareef ya tsala kuka yana wuwwula kafafu da hannaye, ya majeed yace "to Shaati sojanki na neman agaji gwara ki kar'beshi kisha naushi kad'an" dariya duk sukayi har shareef don sun bashi labarin yadda take mita da masifan naushin da yake isanta da shi.


Nufansu tayi tana tafiya ne sede takunta karuwan bugun zuciyarta da ta rasa dalili kaman ta juya da gudu take ji, satan kallonshi tayi aiko se suka had'a ido sbd shima kallonta yake yadda take tafiya kaman kwai ya fashe mata a ciki shi har ga Allah mamakin wai ita ta haifi Arwa, yasmin, sameer, neeha da Shareef yake don da a hanya ya ganta ko wuka aka saka mishi a wuya baze yarda ba.


Yadda suka samu kusanci se kamshinsu ya had'e wuri d'aya ya gauraya ya bada wani kamshi na mussaman wadda take jin sanyin har ranta, lumshe idanunshi yayi yana fighting abinda yake ji yana taso mishi ji yake kaman ya fisgota ya rungume ko zai ji sauki, kokarin kar'bar shareef take wadda garin haka hannayesu suka had'e tare da gogan juna, wani irin shock da taji bata san sadda ta sake yaron ba, ba Don ya rikeshi da kyau ba ba abunda ze hanashi fad'uwa, se fasa kar'bar yaron tayi ta juya da sassarfa ta shige corridor d'in d'akunan gidan.


Ajiyar zuciya ya sauke Allah ya taimaka yayyun nata hiransu suke tsakaninsu ba wadda ya kula, lantana da baba larai ne suke safa da marwan shirya dining d'in yayinda Mama take tsaye wurin tana duba yadda suke yi d'in dukda ta san ba wani matsala za'a samu ba, suna gamawa ana kiran azahar Mikewa gabad'aya sukayi suka fice masallaci a chan suka had'u da Abba da dawowarshi kenan daga wani meeting da ya tafi.


Bayan sun idar suka nufo gida suna hira tsakaninsu sossai shareef ya sake dasu kaman tun da chan ya sansu har ji yake inama yana da en uwa maza haka suke zuwa sallah su dawo da mahaifinsu a tsakiya abin burgeshi yake, basu zauna ba se a dining Allah ya taimaka da d'an yawa shaati tayi abincin dukda haka mazan ne kawai ze ishesu su yaran wani abin lantana zata dafa musu.


Yadda mama tayi umarni kenan, shaati Abba ya kira ta fito tana gyara mayafin kanta ta nufi dining d'in barka da zuwa ta mishi kan ta karasa ta fara serving don ta san dalilin kiran kenan, seda ta sakawa Abba kan ta sakawa sauran yayyunta shi kuwa dole se ta zagaya ta gabanshi kan zata iya sakamishi In ba haka ba zata iya zubarwa ko ta 'bata plate d'in.


Kaman wacce take tausayin kasa haka ta zagaya ta isa gabanshi kowa seda ta tambayeshi abunda zata saka mishi amma shi kuma se ta kasa, hannunta dake rike da serving spoon har rawa yake wani irin uneasiness take ji, lura da yadda take a rikice yasa yace "Chicken biryani" d'auko plate d'in tayi ta zuba mishi, tare da zuba mishi zobo a cup ta saka spoon and fork ta turo mishi In a whisper yace "thanks" ta juya ta fice.


***********


Ta 'bangaren Saif kuwa Bayan ya je office be gama binda ze yi ba se wuraren 11 hakan yasa be fito da wuri ba, bashi ya shigo cikin kaduna ba se 1 massallaci ya samu yayi sallah tare da rokon Allah akan ya dafa mishi al'amarin shaati In Alkhairinshi ce Allah ya dawo mishi da ita, Allah ya sassauta mata fushinta, har ya d'auki hanyar gidansu se kuma ya fasa don har ga Allah tsoro yake, yana matukar tsoron fuskantanta me ze ce mata?.


Gidansu ya nufa aiko dama innani da yakumbo sun shiryawa zuwanshi abinci kala kala haka suka shirya mishi sede abin takaici rasa sukunin ci yayi kwata kwata se tsatsakura da yayi, tausayin hajar duk ya cika mishi kwakwalwa da zuciya Allah sarki duk tayi wani iri, sauran en uwantan ma ba wani sukuni suke dashi ba har gwara ya tala yanzu tayi tawakkali ta barwa Allah lamuranshi.


Bayan ya gama d'akin sulaiman da aka shigar mishi da kayanshi ya shiga don baze iya komawa gidan chan ba sbd tabbas ya shiga gidan chan se yayi kuka duk wani memory's d'in abinda yayiwa Shaati a gidanchan yake ko komawa d'akinta zatayi ba de a gidan chan ba kuma, wanka yayi ya sauya kaya zuwa wani brown cargo pants and milk Allen solly shirt ya feshe jikinshi da turarukanshi da ya san take matukar so bayan ya gyara gashin kanshi.


Wuri ya samu ya zauna tare da fad'awa duniyar tunani abinda baya so  sede ba yadda ya iya da kwakwalwanshi da yake dawo mishi da hannun agogo Baya, ba abinda yake kallo se kwayar idanunta a duk lokacin da yake mata wasu abubuwan how broken she was, har sulaiman ya shigo be sani ba se da ya dafa shi kan ya dawo duniyar mu na mutane tare da kafa mishi idanu, "ya Saif be dace kana zurfafa tunani haka ba In Shaa Allahu zata yafe maka komai ze wuce mussaman da ta san ba laifinka bane".


Murmushin takaici yayi yace "har da zarginka da nayi da ita?" Lumshe idanunshi yayi yace "Kai kaman mahaifi kake a gareni ka d'auki nauyin karatuna da tarbiyata tun bayan rasuwar mahaifinmu har kawo shigowar zubaidah rayuwarka a gaskiya zan fad'a maka abubuwan nan ba na mantawa bane sbd she trusted you with all her heart se kazo kayi turning d'inta down.


Aisha ta sha kwana kuka, ta sha zama da yunwa, ta ci damuwanta ita kad'ai har seda abin yazo yafi karfinta kan iyayenta suka sani ya Saif ga ciki ga kuma yara gabanta dole abun yayi mata zafi kwarai da gaske musamman a lokacin da In naje nake d'an d'ebe mata wani kewan tunda Ina saka yaran da ita kanshi dariya da nishad'i se kuma kazo ka wargaza mata komai ta koma ita kad'ai cikin damuwa In Gaya maka gaskiya? Aisha matar zama ce na kwarai sbd har kawo yanzu akwai abinda ka mata da ta binne shi ranta har yau ba wadda ta iya fad'awa, bazan iya shiga maka gaba wurin neman yafiyarta ba kai zakayi fighting da kanka hakan baze yiwu ba se ka zama jarumi ka kuma mikawa Allah lamuranka".


Kai ya gyad'a tare da lumshe ido cikin karyewar murya yace "thank you sulaiman" Mikewa yayi suka fito tare sbd sallahn la'asar da aka kira, seda sukayi sallah kan ya fice a motarshi ya nufi gidansu Aisha.


**********


Ta 'bangarensu kuwa Bayan sun gama cin abincin tafiya su ya hameed sukayi yayinda shi kuwa ya zauna jiran su neeha su gama cin abinci sbd alkawarin fita da yayi dasu wai be kawo musu tsaraba ba so suje se su sayi abinda suke so, bayan sun gama shaati ta fita musu da kananun hijabs d'insu suka saka har zata juya yace "ji mana" yayi maganan yana kallon side din su mama da Abba, kallonshi tayi yace "ke fah baki son tsarabar?" yayi maganan yana d'age girarshi tare da mata wani kallo.


Da sauri ta kawar da kai gabanta na fad'uwa zatayi magana muryarta ya fara rawa murmushi ya saki se yaji neeha tana cewa "tana so mana papa tace zata sayi perfumes" harara ta bankawa neeha tana cewa "ban hanaki manya na magana kina sa baki ba?" Hannunta ya kama ya maida gefenshi yana cewa "kyale min 'ya gaskiya ta fad'a oya je d'auko lil Shareef mu tafi" bata da option don bazata iya mishi musu ba, d'akin Mama taje tayi sallama mama ta amsata tare da yi mata izinin shiga, shiga tayi suna zaune da Abba suna magana kanta kasa tace fita zasuyi da yaran da ya reef Abba yace "Allah ya kiyaye ku dawo da wuri" Tace Toh tana me ficewa yayinda Mama ta bi ta da kallo.


Shareef ta d'auko ta kara fesa turare ta fito suka wuce, motan da ya d'auko su daga Airport wata shegiyar land cruiser ce baka wulik se sheki takeyi, kar'bar key d'in yayi daga hannun driver d'in cikin turancinsu na sojoji ba wai Don be iya na asali ba yace mishi yaje ze yi driving da kanshi, kame mishi yayi kan ya juya ya fice seda ya zagaya ya bud'e mata gaba ta shiga kan ya bud'ewa yaran baya suka shige ya shiga gaba ya ja motar bayan yayi bismillah.


Wata katuwar store ya kaisu suka sauko yaran sukayi gaba yayinda ita kuwa suka jera a tare suka nufi ciki se kallo ake binsu dashi dayawa sun zata irin mata da miji da yaransu ne suka zo shopping yayinda sauran matan wurin shi kanshi ne yafi d'auke musu imaninsu, wandon khaki ne jikinshi me zips dayawa se takalmansu na sojoji da wata bakar bodyhug da ya kamashi ya fitar da duk wani murd'ad'un muscles d'inshi hannunshi rike da jacket na sojoji yayinda gashin kanshi yayi mishi aski irin na sojoji.


Fuskanshi a sake yana tambayarta ya batun admission ita de a d'arare take amsawa sbd duk wani iri take ji in tana kusa dashi, kallon yadda yaran suke kwasan abubuwa take tana kokarin hanasu shi kuwa ya tsatsareta da idanu, Ko a jikinshi se cewa ma da yayi "kids stick together kar wadda ya je ko Ina Ohk?" Sukace "Ohk papa" kallonta yayi yace "oya muje ki d'auki turarukan" gaba yayi ta bi shi a baya tana kare mishi kallo kasa d'auka tayi se shi ne yake d'auka mata wadda yaga dama har wurin bags and shoes yaje ya d'auka mata masu d'an yawa yaje wurin abayoyi ya d'auka mata wasu had'addu.


Bata san sadda tace "pls ya reef kayan sun isa haka thank yhu" yadda tayi maganan ya sa ya juyo yana binta da wani irin kallo, ajiyar zuciya ta sauke tana juya kanta gefe murmushi yayi sukaje suka biya suka fito ya tsaya wurin ice cream ya saya musu a motan suka fara sha sun cika motar da surutu, a hanya ya tsaya yayi sallahn la'asar kan suka nufo gida yana janta da hira d'add'aya yayinda take amsawa kaman bata so wadda hakan ke kara mishi wani irin abu a jikinshi a kanta.


Suna parking wayanta ya d'auki kara dubawa tayi se taga suhail murmushi tayi tuna irin masifar da ta mishi Jiya, d'auka tayi a daidai lokacin da Shareef ya bud'e mata motan fuskanta d'auke da murmushi a kuma daidai sadda idanunta suka sauka kan saif tsaye jingine da motanshi..........

                   🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇

   *Baya Chanza d'and'anon teku*


      *Fatima Muhammad Gurin*

   **Gureenjo6763 on wattpad**


         'Yar Mutan Adamawa


   *P37*


Wani kasalallen murmushi ta saki tare da kallon ya reef kaman bata ga wani Saif ba tace "ya reef gyalena gyalena ze fad'i" shi kuwa da azama ya sa hannu a kan gyalen yana gyaramata daidai lokacin ta cewa suhail "sorry suhail Ina zuwa I will get back to you" ganin tana kokarin fitowa ga waya a kunne ga kuma Shareef a hannu yasa ya saka hannunshi ya kar'bi lil Shareef d'in dake bacci ya makalashi kafad'a yana cewa "ke ma dai da rigima kike taya ga baby a hannu kina kokarin saukowa kuma kina amsa call. Yanzu In shareef ne ya fad'i ba gyale ba fa?" Shagwa'bewa tayi tana murmushi tace "sorry baza'a sake ba" shagala yayi da kallonta.+


Aiko a kasan zuciyarta kuwa tunani take me ya kawo Saif kuma kofar gidansu? In har yana cikin hankalinshi ta tabbatar yanzu ya gama kuluwa sbd ya tsani wani namijin yaga shagwa'barta bayan shi, aiko kaman ta sani a lokacin da takeyiwa Shareef dramar ta Saif ji yayi kaman zuciyarshi zata fad'o kasa a take idanunshi suka kad'a sukayi jajir jijiyon kanshi suka mimmike, tabbas In tace zata auri wani bayan shi ya san wallahi mutuwa ze yi baze iya d'auka ba bare kuma irin Shareef da shima namijin gaske ne wadda In yace a yanzu ze baje mata kolin soyayyarshi wallahi se ta manta da wani Saif rayuwarta.


Da idanu ya bi su har suka shige shi Shareef be lura ba yayinda ita kuwa sarai ta san kallonsu yake se kara sakewa shareef murmushi take, Yasmin ce karshen fita sbd neman murfin ice cream d'inta da take kan ta fito kowa ya shige, a hankali ya tako zuwa jikin motan cikin sanyin murya yace "Yasmin" da sauri ta d'ago ta kalleshi ganin yadda idanunshi suka kad'a sukayi ja ba abinda ya fad'o mata se ranar da ya mari neeha har ta kusa suma cikin razana kar itama ya maretan sbd ranar ma haka idanunshi sukayi tayi saurin jan baya ze yi magana ina ta kwasa da gudu ta nufi gate.


Daidai lokacin Shareef ya kuma fitowa da sauri ya riketa yana cewa "lafiya yasmin?" Kuka ta fara tana nuna mishi Saif "papi ze d'auke ni ya kaini wurin Anty zubaidah and she's evil" kallon Saif yayi tabbas shine mahaifinsu sbd kammani a ranshi yace "ashe shima namiji ne" murmushi ya saki yace "karki damu ina nan ba inda ze kaiki kinji? Oya shiga gida" Da gudu ta shige gida shi kuwa Saif In aka ce a wurin hawaye ya fara to baze musa ba sbd reaction d'in yarinyar ya mugun firgitashi banda ma maganan shaati da ya gani da wani saurayi.1


"Assalamu alaikum" Shareef ya furta yana mika mishi hannu a kasalance ya d'aga nashi sukayi musabaha, kan ya bud'e motanshi ya d'au abinda ze d'auka ya koma ciki ya bar Saif tsaye nan kaman an dasa shi har ga Allah yayi matukar bashi tausayi sede yanzu shaati ta zama allura cikin ruwa se me rabo ze iya d'auka, ko ma ta ganshi? Ya tambayi kanshi se kuma ya ta'be baki tare da d'aga kafad'a yana furta Ina ma ruwana.


Tana shiga gidan d'akinta ta wuce rike da shareef da shareef babba ya mika mata a kofar parlorn, a gado kawai ta ajiye yaron tana me fisge gyalen kanta safa da marwa ta fara tare da dunkule hannunta d'aya tana dukan tafin d'ayar, abubuwan da suka faru ne suke dawo mata bata san sadda kuka ya kwace mata ba tare da zamewa ta saka kanta tsakanin cinyoyinta tare da kara sautin kukanta.


Mama da taga wucewarta kuma taga kaman tana cikin tashin hankali se ta biyo bayanta dukda bata san me ya faru ba bata son katsalandan cikin al'amuran yarinyar tunda yanzu tayi girman da ta san fari da baki, ajiyar zuciya ta sauke ta fita tare da jan kofan a hankali.


Seda tayi kukanta ma'ishi kan ta mike ta shiga toilet ta wanke fuskanta, zuciyarta tunani daban daban, wanka kawai tayi ta fito ta shafa mai tare da zura material ta saka turban kanta, ba ita Zata yiwa Shareef abincin dare ba mama da lantanace so sai kawai ta kwanta ta d'auki wayanta ta danna kiran suhail gaisawa sukayi nan ya fara janta da hira cikin son sanin wacece ita, bata 'boye mishi ba ita bazawara ce me 'ya'ya har biyar, yayi matukar mamaki sbd jikinta be nuna hakan ba sam.


Be bud'e mata zuciyarshi ba sbd kwarai daga yadda take magana ya fahimci tana da wadda take so so kuma na hakika, se kawai ya roki alfarmar zama yaya a gareta wadda zata iya neman shawara ko taimakonshi haka itama zata iya taimaka mishi a ko wani hali, cikin jin daad'in yadda ya fahimceta suka hau hira nan yace se ya gaisa da 'ya'yanshi take kuwa ta hau kwalawa Arwa kira aiko se ga ta mika mata tayi tana cewa "uncle suhail" gaisawa sukayi ya tambayeta sauran kannenta ta fita da wayan a kunnenta.


Ajiyar zuciya ta sauke tana bukatar zama ta natsu ta san abinda ya kamaceta sede fah yanzu ita karatu zatayi shiyasa bata son sauraran kowa kar Abba ya kawo zancen aure a katse mata karatunta wannan tunanin ne ya kautar da na ganin Saif da tayi ta mike tayi fitowarta, ganin basa parlor yasa ta nufi kitchen tayiwa mama sannu da aiki amsawa tayi tana kallonta, ganin bata nuna ko wani irin damuwa ba yasa ta amsa suka ci gaba da ayyukansu, fita tayi ta nufi garden chan ta jiyo hayaniyarsu aiko ya zage suna ta wasa da dariya da yaran kaman ba soja ba wallahi In yana wani abun yana nan kaman me juju yanzu yanzu ze iya tsimewa ya fito asalinshi anjima ka jiyo hayaniyarshi da yara.


Kan ta zauna ta fara jiyo ihu a tsakiyar gidan nasu da sauri ta saurara kaman kuwa umma ce mahaifiyar isma'il da sauri ta nufi waje Mama ma dake kitchen seda ta jiyo, ganin yadda ta fitan ya sa ya dubi yaran yace suyi wasansu bari yazo, bin bayanta yayi suna fita gate d'in site d'insu suka ga gabad'aya zuriyar gidan a harabar gidan sunyiwa isma'il dake zaune cikin fitan hayyaci zobe.


Gefe Shareef ya koma ya tsaya yana kallonshi yayinda mahaifiyarshi da Hajja suka rikeshi "lafiya isma'il? Wani marar imanin ne ya aikata maka haka?" Se kuka shima kuka kawai yake Abba ne suka shigo da yayanshi haladu se su ya hameed suma se da suka tsorata ganin wannan aikin rashin imanin Abba cikin 'bacin rai yace "Amma duk wadda yake da sa hannu a wannan halin da ka shiga in shaa Allahu se mun yi Shari'ah dashi wani irin rashin imani ne haka?".


Katse Abba yayi "babu marar imani se ni kaina Abba, ni ne nayiwa kaina duk wani illan da ya sameni yau" d'agowa yayi yana neman shaati chan ya ganta tana kallon Shareef kallon tuhuma yayinda shi kuwa ya juya kanshi gefe kaman be san wainar da ake toyawa ba, da rarrafe ya isa gabanta tare da fashewa da kuka ya sa hannu ze ta'bata cikin azama ta fisge kafafunta tana watsa mishi wani kallo.


Cikin kuka yake cewa "ki yi hakuri Aisha ki yafemin, wallahi sharrin shaidan ne da kuma tsanarki da aka sa min a rai tun ban san kaina ba, na san na cuceki cuta mafi muni wadda har hakan ya ja miki tsananin fushin Iyaye but trust me wallahi Ina jin fiye da ciwon da kikej......" cikin tsawa tace "shut up!!! Just shut up wai kai har ka san kwatan abinda na ji? Isma'il ba zan ta'ba yafe maka ba wallahi ka cuceni" se kuka, hajja tace "wai me ke faruwa ne?".


Cikin kuka isma'il yace "kuyi hakuri na sakaku tsana da zargin Aisha na shekara da shekaru cikin sakaya halina na fuska biyu da nake dashi.........." tiryan tiryan ya fara basu labarin abinda ya faru da yadda yake nemanta take ki da yadda ya saceta ya azabatar da ita, se ga hajja na kuka, Abba karan kanshi dukda yaji labarin sede ji daga bakin isma'il d'in yafi karya mishi zuciya Allah sarki, hameed karan kanshi kuka yake.


Babanshi da ya cika yayi pim yace "to an maka hakan kenan sbd ita?" Kallon Shareef yayi da ya tsatsareshi da idanu a take hanjin cikinshi ya kad'a cikin rawar murya yace "na d'auki hakan a matsayin hukuncin abinda na aikata dukda banji rabin takaicin da taji ba, an rabani da mazantaka ta bani da wani hope na samun haihuwa Arwa dai ita kad'aice jini.....".


"Kulll.... wallahi kar naji ka had'a kanka da Arwa baka da had'i da ita kwata kwata, a matsayin evil ta sanka kaje chan ka nemi inda kake da jini ba nan ba" kuka sossai yakeyi gwanin tausayi ta juya ta shige gida, Mama ma bata tofa komai ba tayi komawanta yayinda hameed ya gayyaya mishi magana hajja kam har kusan tsinewa mahaifinshi tayi sbd shine ya d'aurashi kan komai har seda Abba ya bata hakuri, isma'il kam da kyar ya lalla'ba bayan kowa ya watse ana ta Allah wadai da irin halinshi.


D'akin shi na gidan ya nufa ya zube yana me ci gaba da kuka da dana sani, shareef wurinta ya je dayake chan bayan garden d'in taje ta zauna tana kukan, a gefenta ya zauna seda ya barta tayi kukan sossai kan yace "menene abin kuka haka kuma Aishaaa" yadda ya kira sunanta seda tsikar jikinta ya tashi, "ke ba murnanki bane ya gane kurenshi ya wanke ki gaban iyayenki da en uwanki da suke miki wani kallon da ba shine ba? Pls ki dena kukan nan haka ya isa ko duk ya had'u da na ganin Saif da baki karasa d'azu ba?".


Da sauri ta kalleshi se ya kawar da kai kenan ya san d'azu taga Saif? Ya kuma san tayi kuka? Kau da kanshi yayi sbd yadda idanunta suka d'anyi ja wani abin daban yake ji da ganin hakan, cikin murmushi yace "ba kuka bañe solution natsuwa zakiyi kiyi anfani da kwakwalwanki me kike so ne? Me ya kamata kiyi ne? Abinda ya dace kiyi nazari kenan yaranki da wasu daga cikin masu sonki bazasu so su dinga ganinki cikin wannan hali ba".


Fuskanta ta share cikin sanyin murya tace "Ya shareef ya zanyi?" Murmushi ya saki yace "ki barwa Allah komai kiyi ta Adu'a, Sannan kaman yadda na fad'a miki use your brain and think, ni zan wuce na so in kai gobe but yanzu nayi receiving order ana bukatata a Abuja so I will take my leave, se na dawo d'aukan zaheeda shaa we will talk ehen" Kai ta gyad'a.


Har ya mike ya fara tafiya kan ya tsaya ya juyo ya kalleta "ba adu'a bare rakiya" yadda yayi maganan ya sata jin wani abu har kasan ranta lumshe idanu tayi tace cikin sanyi "Allah ubangiji ya kiyaye hanya ya tsare ya bada sa'a" yace "Ameen" yana murmushi kan ya juya ya fice seda sukayi sallama da yaran kan ya shiga sukayi sallama da Abba da mama su ya majeed suka rakoshi waje ya wuce.1


Kaman an zabureta ta mike jin yadda tunaninshi ke shirin fin karfinta abinda ke bata mamaki ko tunanin ganin da tayiwa saif batayi, buga goshinta ta fara da tafin hannunta "na Shiga uku ni Aisha, me nake yi? Me nake shirin aikatawa. mijin jidda? Inaaa baze yiwu ba, wai me ya hau kaina ne tun farko?" Daga bayanta taji ance "shaid'an" Da sauri ta juya Mama ce tsaye tana kallonta ta d'aura da "na barki ne kiyiwa kanki fad'a sede na lura baki da niya ashe haka hallaci yace Aisha? Ai In da amana to fah ruwa bazata ci kifi ba, ba haramun bane don kin so ko kin auri shareef sede ana barin halal don kunya" tana kainan ta juya ta fice.1


Zama shaati tayi cikin damuwa ashe Mama na hankalce dasu? Ta lura shi karan kanshi Shareef yana da interest kanta sede bazata iya cin amanan jidda ba se yanzu abubuwan da takeyi suke dawo mata zatayi karya In tace deep down bata fara jin wani abin a kanshi ba sede ya mata nisa, nisan da bazata iya kamoshi ba ko kyauta aka d'aura mata shi kafa zata kwance ta yasar sbd hallice irin na matarshi a gareta.


**********


A ta 'bangarenshi kuwa yana jan motan Abuja ya nausa awa biyu ya shigar dashi cikin Abuja sede dayake yamma tayi cunkoson Ababen hawa yayi yawa a kan hanyoyin seda ya share wani awan kan ya isa base d'insu yana shiga yayi reporting, be fito ba wayanshi ta fara kira d'agawa yayi se yaga baba cikin mamaki ya amsa yana d'agawa cikin sanyin murya baba yace "Shareef ka nemi flight ka dawo" yace "baba meke faruwa?" 'Dan Shiru baba yayi kan ya furta "gidanka yayi gobara ba'a fidda ko tsinke ba gashi jidd......." baba be rufe baki ba yaji d'ib.


Wato a duniyarshi be ta'ba sanin yana son jidda so na hauka ba se yau, dena ji da gani yayi lokaci d'aya be san sadda wayan ta zame ta fad'i daga hannunshi ba se kokarin bin wayan yake inaaa se de ganin shi sukayi kasa Don ya gama sadakarwa rasuwar jidda  baba ze fad'a mai tunda bata tambayeshi izinin zuwa ko Ina ba kenan In ba'a fitar da tsinke daga gidan ba har ita kenan, cikin zafin nama akayi kanshi se d'aukanshi akayi zuwa clinic d'in base d'in a take aka hau bashi taimakon gaggawa yayinda oganshi ya d'auki wayan ya kira baba.

1

                   🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA........💦🍇

    *Baya Chanza d'and'anon teku*


       *Fatima Muhammad Gurin*

    **Gureenjo6763 on Wattpad**


            'Yar Mutan Adamawa

    *P38*


Be san iya adadin lokutan da ya d'auka tsaye a wurin ba zuciyarshi na racing up and down kaman Zata fito waje, In akace yayi awa guda a tsaye a haka baze musa ba don har seda wani da ya zo wucewa ya ta'bashi yana tambayar "malam lafiya?" Ajiyar zuciya ya sauke yana lumshe idanun shi kan ya amsa da "Alhamdulillah thank yhu" Da kyar muryarshi ke iya fita, a hankali ya ja kafafunshi zuwa motanshi nan ma ya jima a zaune kan ya tayar ya bar wurin Allah ya gani yana da mahaukacin kishi da be san me ze iya aikatawa ba In ya motsa.+


Sede ya san yanzu shaati na da right d'in za'ban wadda take so be yi tunanin zata amince dashi ba after all what he did to her, staring motar ya duka da hannunshi da karfi kan ya mayar da hannun gashin kanshi ya chakud'a hawaye ne ke shirin escaping idanunshi yana cijewa lip d'inshi na kasa ya sa hakwara ya danne da karfi he wish ze ga zuby wallahi da ba abinda ze hanashi crushing d'inta kan titin nan, ganin ya fara ganin dishi dishi yasa ya samu wuri ya parker tare da d'aura kanshi kan sitiyari hawayen idanunshi na gangara, Allah ya gani he really loves her, he can't live without her.


Karan wayanshi ne ya dawo dashi hankalinshi dubawa yayi se yaga yassar d'auka yayi tare da lumshe jajayen idanunshi yassar yace "ya ake ciki?" Cikin karyayyen muryanshi yace "she's into someone yassar I really don't know what to do, ya zanyi?" Yayi tambayar In a bit harsh dukda muryarshin ba fita take ba tsabar takaicin da ya cikashi.


**********


"Ba fa ta mutu ba I don't really know what kind of soldier yaron nan yake ikon Allah!!" Dariya oganshi yayi yace "when it comes to love ba maganar waye waye Alhaji" dariya baba yayi yace "pls tell him she's fine when he regain conscious, tana asibiti ne bcs of the smokes amma bata kone ko kad'an ba" sallama sukayi da ogan kan ya nufi clinic d'insu.


Ya jima tsaye kanshi kan ya fara motsi kaman yadda military doctor d'insu yace, a lips d'inshi yake furta "no! No!! No way Jiddah you can't just go like that, you can't leave me alone, pls don't go for the sake of love you have for me, I promise you I will love you to death habeebty" dariya dae commander ke yi yana jinjina girman so, In ba so ba what can take namiji irin shareef down one time? Be gani ba.


A shoulder d'inshi ya sa hannu ya furta "hey! Hey!! Bata mutu ba, she's not going to leave you not now in shaa Allah" a hankali yake bud'e idanunshi ya zubawa ogan nashi kan ya kuma lumshesu he hoped gaskiyane abunda yaji kunnuwanshi ke fad'a mishi da be san irin farin cikin da ze yi ba, In kuwa daga bakin oganshi maganan ya fito to kuwa ya san gaskiyace Don baze mishi karya ba ya sani.


"Hakan da kaji na fad'a hakan yake, man up she's still alive Ohk?" Da sauri ya bud'e idanun yana mikewa zaune se kuma ya sa hannu a goshi ya sara mishi kan ya furta "salute" saluting d'inshi ogan ma yayi kan yayi murmushi ya mika mishi wayar "zaka iya tafiya, I already booked you a flight to maiduguri but se after magrib ze tashi" godiya ya mishi kan ya fice.


Wani wawan ajiyar zuciya ya sauke yana dafa daidai saitin zuciyarshi ashe yana son jidda haka be sani ba? Ashe bazaka ta'ba sanin value d'in abinda kake dashi ba se kaji ka rasashi ko ka kusa? He's really blessed da ya samu second chance na showing d'inta with endless love, dama chan ba wai ya tsane ta bane sede d'aukanta yake as his shoulder and abokiyar shawara tunda ya riga ya aureta har da haihuwa ashe abin ba haka yake ba, dafe goshinshi yayi a fili ya furta.


"If what I had for jidda is what is really called love then me nake ji akan Aisha?" Yayiwa kanshi tambayar In very confused way se kuma ya ba kanshi amsan within his lips deep down his throat "pity" grinning teeth d'inshi yayi ya furta "WTF!!! What was I doing?" Ajiyar zuciya ya sauke ya shiga lalu'ban numbern hajjanshi tana d'agawa yace "Hajja ya jidda? Hope ba abinda ya sameta? How comes ma wuta ya tashi a gidan hasbunallahu wani'imal wakeel I am about going crazy right now" murmushi hajja tayi tana girgiza kai tace "babana ba sallama?" Yace "oh Assalamu alaikum".


Amsawa tayi kan ta d'aura da "ba abinda ya sameta shareef babanka ya fad'amin halin da ka shiga ka kwantar da hankalinka ko yatsar ta Allah ya tsare wutan be ta'ba ba, babu wadda ya san ya akayi wutar ta tashi from no where kawai aka ganta" da sauri yace "can it be sakawa akayi?" Da sauri tace "Allah ma sani ka kyautata zato, ko set up d'inne ma ba gashi Allah ya kareta ba?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "in Shaa Allahu hajja, I will be at home around 8:00pm In shaa Allah" Adu'ar kariya ta mishi kan sukayi sallama.


***********


Ta jima tsaye nan bayan tafiyar Mama kan taji sawon kafa na tahowa inda take hanyar ta zubawa ido, kawai se ganin ya hameed tayi ya bayyana kau da kanta tayi sbd ta san ko ta mishi magana ba mata ze yi ba, to her greatest surprise se ji tayi yace "besty" da sauri ta kalleshi irin kallon tuhuma ya kuma furta "yes am talking to you" kallonshi ta cigaba dayi rabon da taji ya kirata hakan shekaru kusan goma kenan hawaye ne ya cika mata idanu dama kukan na kusa kawai se ta saka kuka.


Sossai fah take kukan da sauri ya matso ya kama hannunta se ta jinginu dashi ta cigaba da kukanta, a hankali yace "am so sorry fav. Bani da bakin baki hakuri I know you despise me, ban da abin cewa se kiyi hakuri ki yafewa wannan yayan naki" cikin kuka tace "bestie ban ta'ba rikeka ba dama chan ko ka manta you was my favorite? And you will always be, I knew that abubuwan da kake tunani nayi yasa ka tsaneni sbd kasa believing da kayi, please let bygones be bygones I really need some advice now".


Da murmushi yake kallonta yana mamakin me yasa duk zuciyarta ta kasa fushi da en uwanta na jiki tayi saurin yafe musu? Be da wannan amsan sbd damuwar er uwarshi tashi ce, yace "thank you!! Me nene ya faru?" Tace "Shareef shine damuwana" zare hannunta tayi daga nashi ta fara bashi labarin komai in details wadda be sani ba, Shiru yayi yana sauraranta har seda ta ajiye numfashi.


Yace "dukda ni namiji ne a ganina don kin auri Shareef ba wani abu bane amma kaman yadda Mama ta fad'a hallaci be ce haka ba Sannan kina a matsayin bazawara zaki d'auki 'ya'ya har biyar ne ki tare gidan me guda d'aya? Yau ko min kud'inshi watarana se yaji ya gaji da wannan rikon na 'ya'yan wani ba nashi ba, Sannan shi Saif baki kyautata zaton ze dawo daidai Tunda kema kin san yana miki mahaukacin so sharrin mace ne ya....." katseshi tayi "hmmm bestie mu bar maganan roo.... saifullah pls, In Shaa Allahu daga yanzu na rufe babin shareef a rayuwata har Abada na sani, na fi kowa sanin irin ciwon da mace ke ji in namiji ya auri friend d'inta, na sani" tayi maganan tana murmushin takaici hawaye na gangaro mata.


Sharewa tayi tace da jan hanci yana kallonta yace "sorry I wasn't there for you" Tace "is ok" cikin gida suka nufa tana rayawa a ranta zata dakatar da duk wani feelings da take ji kan shareef da ma ko wani namijin, karatunta yanzu shine up priority d'inta she hoped admission d'inta ya fito soon ta wuce school, a parlor ta zauna tana duba phone d'inta, nan ta lalu'bo numbernshi don jin ya ya isa sbd yanzu a yaya ta d'aukeshi kaman su mujeeb.


Kusan ringing na karshe ya d'aga gaisheshi tayi ya amsa d'add'aya yana tunanin yadda ze zullewa wannan banzan abinda ya fara ji a kanta se yanzu ya duba ya san tabbas In shi namijin kwarai ne ya aureta ko ya sake ya nunawa jidda wani feelings na shaati to kuwa be kyauta ba, wace macece a wannan marrar miji ze kawo mace da tsohuwar ciki ba tare da ta san inda ta fito ba ta kar'beta hannu bibbiyu? Ba wani cuta se ma kyautatawa? jidda didn't deserve this from him gaskiya.


Ganin yadda yake amsata itama se ta takaita maganan tayi mishi sallama har zata kashe yace "wait!! Something terrible happened but Alhamdulillah, gidana yayi gobara fire outbreak from no where....." bata jira ya karasa ba a rud'e take tambayar "jidda!! Jidda hope ba abinda ya sameta?" Yace "babu Allah ya tsareta but sbd hayakin da ya mata yawa ta suma har yanzu tana hospital ni ma yanzu zan wuce Airport sbd after magrib jirgi na ze tashi pls inform Abba and mama".


Ajiyar zuciya ta sauke tana furta "Alhamdulillah Allah ubangiji ya tsare na gaba ya kare" yace "Ameen bye" kashe wayan yayi yana godewa Allah da be furta mata yana sonta ba da be san ta yadda ze wanke kanshi ba, ita kuwa Mikewa tayi ta nufi d'akin Mama tana kwala mata kira nan ta sanar mata abinda ya faru itama tayi jimami kam amma tunda ba wani ciwo Ai se a gode Allah, hajja ta kira suka hau maganan abinda ya farun.


Ita kuwa shaati fitowa tayi ta kamo yaran tazo tayi musu wanka baaba larai already tayiwa shareef, ana kiran magrib ta sasu sukayi sallah ta basu abinci zuciyarta kal ba damuwan kowa, wani sakayau takejinta sometimes you have to let something be, ba wai Don baka so ba se don duba wanda hakan ze cutar, kaima kuma In aka maka hakan to fa Lallai bazaka ji daad'i ba so she freed off her mind from wani Shareef she's now having peace of mind.


Bayan sun gama ta jerasu sukayi karatun qur'ani ta musu kari sukayi isha kan ta rakasu har wurin bacci suka kwanta ta tofesu da adu'o'i, bayan ta fito ta biya ta kar'bo shareef tayiwa mama da Abba se da safe suma suna nan suna jimantawa Shareef wannan tabkeken gida da motoci duk yayi asara yanzu fa be da wani mota ko guda tunda ba wai ajiyewa yake wani wurin ba.


Amma sun tabbatar baze wani damu ba shi karan kanshi mahaukatan kud'i ne dashi bare aka had'a da mahaifinshi ba magana, bayan ta kwantar da shareef kawai se tayi changing to kayan bacci don kuma bazata iya wani wankan ba kaman wata agwagwa yau tayi wanka sau uku, tana kwanciya wayanta ya hau ringing.


***********


"Wai kai Saif me ke damunka ne? In kana wani abun se kace wadda be san mace ba wallahi, Aisha dai kafi kowa sanin halinta kai ka zauna da ita na almost 10 years so akwai wadda ze fi ka sanin yadda zakayi da ita ta sauka? Haba think mana, use all the tactics you know will work on her Ohk?" Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ohk thank yhu" ya kashe wayan ya ja motan wurin sai da registered SIM card yaje ya saya daga nan ya wuce gida.


Da su yakumbo ya zauna ya sake sossai yana me danne damuwanshi sbd ganin damuwar da suka shiga sanadiyar nashi damuwar suka sha hira da dariya har se da aka kira magrib suka wuce masallaci da sulaiman, wani d'akin yakumbo ta gyara mishi da kanta suka shigar mishi da katuwar katifa suka shimfid'e da babbar darduma sbd kasan d'akin tiles ne.


Manyan pillows guda biyu suka jefa mai nan Anty tala ta shiga ta wanke mishi toilet d'in d'akin sumayya ta janyo trolleynshi ta dawo mishi dashi nan d'akin, tsab ya gyaru se kamshin turarukan wuta da Sanyin Acn dake tashi, ba su suka dawo ba se after isha don karatu suka zauna sukayi na qur'an suna me tuna memory d'insu da mahaifinsu, se Bayan sun idar da isha suka dawo abinci suka ci a parlorn yakumbo dukkansu.


Abinda suka jima suna burin gani shine yau yake gani yakumbo da innani na cin abinci kwano d'aya abinda har mahaifinsu ya rasu da burin wata rana yaga had'in kansu ya kwanta dama, sossai zamanshi cikin en uwanshi ya rage mishi damuwa sede fah a fuska kawai zuciyarshi will not be at ease in ba ganin shaati yayi yau a matsayin matarshi a karo na biyu ba, har yanzu image d'inta da shareef ke dawo mishi tiryan tiryan a kwakwalwa.


Suna gama cin abinci ya shige d'aki ya saka number d'inta bayan ya loda kud'i cikin simcard d'in ya kirata.


************


Salatin da inna ke ta faman kwararawa ya ja hankalin makwantanta na kusa se la'ana take tana tsinewa wanna rayuwa da yake son kasheta da ranta, tashin hankalinta na yau daban na gobe daban, shigowa aka fara yi Don jin ba'asi abinka da unguwar da gidajen manne suke da juna kuma basu da wani tsawon gini ko zurfin gidan da ze hana na waje jin hayaniyar ciki.


Kowa ya shigo se ya wara idanu ya sa hannu a kai yana salati, wasu kam se suce Khaih duniya abinda ka shuka shi zaka girba, baba ne ya rataye kanshi da kanshi har lahira bayan dirka dirkan zunubai da yayi a doron kasa bayan chance da Allah ya bashi ya gyara kura kuranshi dayake Allah be nufeshi da shiriya ba se ya kashe kanshi ya mutu kafiri Allah ubangiji ka tsaremu ka bamu daman gyara kura kuranmu.


Ba se ga mata sun fara jerin gwano ba duk wacce yayiwa aiki abu ya lalace ya dawo kanta ga malam shima yanzu ta kanshi yake a gaban ubangiji, tashin hankali nan en unguwa suka ce fir se inna ta bar unguwan ko su konata da gidan ba wadda ya damu da ratayayyen malam bare a sauke shi nan ta d'auki kaya da en sauran kud'ad'en da ya saura da kuma wayanta, itama ta fice ta barshi nan kan ta fito matasan unguwan kowa rike da galón d'in petur da kyar ta gudu su kuwa suka bankawa gidan wuta kan ma mai unguwa yazo ya hanasu take gidan ya kone kurmus suna tsaye suga ubanda ze ce ze kashe Bayan sun kone iya gidan suka kashe sukayi gaba.

                  🖤Gureenjoh🖤🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇

   *Baya Chanza d'and'anon teku*


       *Fatima Muhammad Gurin*

    **Gureenjo6763 on Wattpad**


           'Yar Mutan Adamawa


    *P39*


"Assalamu alaikum" ta furta tana me lumshe idanu, wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke da har seda taji, muryanta yake ji yana ratsa mishi zuciya he missed her like crazy, kuma sallaman tayi tana me sauraren jiran amsa a hankali ya amsa mata "wa'alaikissalam warahmatullah" jin muryanshi ne yasa cikin azama ta cire wayan zata kashe yayi saurin cewa "In kina yiwa Allah da manzonsa karki kashe wayan nan" mayarwa kunnenta tayi, cikin karyayyiyar murya yace "how have you been?" Shiru ta mishi.


Yace "Aisha na san bani da bakin da zan iya baki hakuri sede ki sani wallahil azeem cikin hankalina dae bazan ta'ba iya aikata rabin abinda na aikata ba, I didn't know what came over me, ban ta'ba yarda asiri ana iya samunshi na gaskiya yanzu a wannan zamanin ba se gashi ya hau kaina har na wulakanta mace mafi soyuwa a raina, duk abinda nayi miki na san ke a wurinki ya riga ya wuce but ni har yanzu zafinsu nake ji har cikin raina kaman ni akayiwa, Aisha I loved you, I love you and I will keep loving you to eternity, Ina so ki san RUWAN SAMA Baya Chanza wa ruwan kogi d'and'ano, kaman yadda babu abinda ya isa ya Chanza d'and'anon sonki a cikin zuciyata, za'ayi RUWAN SAMA da na tabbatar se ya wanke duk wani ta'bon bakina a zuciyarki In Shaa Allahu" ajiyar zuciya ta sauke kan tace "excuse me!!" Ta kashe wayanta.+


Lumshe idanunshi da sukayi ja yayi yana tunani wani wahalan kuma ta sha a randa ya saketa sbd tsanan nata gareshi yayi yawa ya dae san ta 'bata tunda har gidanshi aka zo nemanta, be san yadda ta haihu ba, be san me ta samu ba d'anshi guda be san ko da sunanshi ba, da karfi ya runtse idanunshi yana me d'aura hannayenshi saman kanshi abin da ciwo sede hakuri shine magani se adu'a mikewa yayi ya d'auro alwala ya fara nafilfili yana rokon Allah ya sassauta mata.


Ta 'bangarenta kuwa sossai maganganunshi suka tsaya mata a rai sede a lokacin tayi iya yinta ta ciresu ta watsar ta gyara kwanciyarta se bacci hankalinta kwance.


Ta 'bangaren Shareef yana isa jidda na farkawa a matukar tsorace take kallon jikinta ganin ba inda ta kone yasa ta sauke wani wawan ajiyar zuciya tana furta "Alhamdulillah" yaya dake zaune ta kalleta tana murmushi tace "Allah shine abin godiya kin tashi?" Kai kawai ta gyad'a tana tuna yadda wutan nan ya tashi, a daidai lokacin ya turo kofar wadda yana shigowa yaya ta mike ta fice, tana bada baya ya karaso cikin sassarfa ya rungumeta cikin jikinshi kaman wani ze kwaceta har seda ta d'anyi kara kan ya sassauta ajiyar zuciya kuwa ya sauke sunfi goma idanunshi a lumshe ya samu kunnenta "thanks for being Alive lil".


Murmushi ta saki tana d'agowa tace "Da na mutu fah?" Yace "I would have regretted not showing you how much I love you, I would have regretted duk wasu laifi da na miki duniya, oh Allah I can't even imagine you dying now" kissing lips d'inshi tayi tace "Alhamdulillah" Ai kallon kinyi kad'an ya mata kan ya chabke Lips d'in nata ya fara mata wata kalar mahaukaciyar kiss🚶‍♀️🚶‍♀️🚶‍♀️


***********


Washegari da safe Shaati na tashi kawai taga an turo mata sako, bata duba ba sbd ta bada saif ne, ta cigaba da abinda take bayan ta gama musu breakfast kaman yadda ta saba tayi wanka ta shirya kan ta d'auki wayan, miss calls hud'u ta gani na wannan numbern da Saif ya kirata jiya bata bi ta kai ba don ba kira zatayi ba ya ci sa'a ma da batayi blocking contact d'in ba.


Abinda taga an turo mata yasa ta mikewa tsaye fuskanta na cika da farin ciki ba kaman a da da ta cunne ba, da gudu ta fita kaman yarinya tana kiran "Abba! Abba!! Abba!!" Fitowanshi kenan ze zauna dining yace "uwata are we safe irin wannan kira?" Tace "Abba admission na samu" shi da mama sukace "Alhamdulillah congratulations dear" cikin farin ciki tace "thank you" Abba yace "to zo zauna ki ci abinci kar farin ciki ya sa cikin naki cika" Tace "Ai ma ya sa Abba Ina zuwa" ta ruga d'aki mama tana girgiza kai Tace "Allah ya shirya mutum da 'ya'ya amma har yanzu ya gaza hankali?" Abba na dariya yace "ke kyaleta ko ke aka ajiyeki gaban umma haka zakiyi ehe" dariya tayi kawai tana cigaba da serving d'insu.


Tana shiga hajja ta kira cikin shagwa'ba tace "hajja ina so in yi magana da jidda hajja har yanzu baki isa hospital d'in ba?" Hajja tace "ni kam yau wayar nan zan barwa jidda ko zan huta ahh" dariya duk en d'akin sukayi har shareef jidda ta kar'bi wayan tace "Ina jinki dear kyale hajja yau d'innan ana sallamana se na biya na sayi wata wayar kan in koma gida kuma ke zan fara kira" dariya sukayi a tare shaati tace "Alhamdulillah kina lafiya?" Tace "garau ma kuwa Ina beautiful neeha" shaati tace "ahh ba wata beautiful neeha kice zaheeda kike so ki tambaya kike wani kame kame" jidda tace "dallah chan kema kin san ba wadda zanji kunya nan don na tambayi zaheeda ehe" shaati tace "chan de ta matse miki, mutum ya sa kafa d'aya lahira ya samu ya dawo da kyar amma baki be mutu ba" jidda ta bud'e baki zata amsa shaati tayi saurin cewa "hey na samu admission" ihun murna jidda tayi wadda ya sa Shareef zare wayan ya makala kunne yace "oya bye bye time na ganin Doctor" ya kashe dariya duk su hajja suka saka yayinda jidda ta turo baki ita kuwa shaati murmushi kawai takeyi.


Lallai zuciya muguwar aba ce in kace zaka biye mata Allah sarki da yanzu ta biyewa zuciyarta da ta wargaza farin cikin wannan baiwar Allahn da ta d'auketa aminiya farat d'aya, Allah ya taimaka ya kubto ta da bata san inda zata kai kunyar duniya ba, ta d'and'ani irin bakin cikin miji ya auri kawa bazata yiwa kowacce mace fatan hakan ba ko da kuwa makiyanta ne abin ba daad'i ajiyar zuciya ta sauke ta mike ta fito.


Yaran ta samu baaba larai na musu wanka suna haukatata musamman neeha da zaheeda, seda ta tsawatar suka natsu Arwa ta shiryasu tace "a gama shiri a ci abinci mu fita yawo" ihu sukayi cikin murna suka kwasa waje, Shareef ta d'auka ta fito ta koma d'akinta ta shiryashi itama ta shirya cikin shigan Abaya ta d'aukoshi suka fito Bayan taci abinci tayiwa mama sallama bayan ta kar'bi car key ta d'aukesu gidan ya meena suka fara zuwa.


Aiko tayi murnan ganinsu abubuwan ci kala kala ta sauke musu inda suka bar yaran suka shige kuryan d'aki suka bud'e chaptern hira, nan ta bata labarin abunda ke faruwa, ita ma sossai ta mata fad'a na son bin rud'in zuciyarta da tayi kan suka gangaro maganan saif inda meena ke nuna mata ta yafe mishi kawai a wuce wurin murmushi kawai tayi ta mike tace "zamu gudu ya meena muna da wuraren zuwa jibgi" abubuwa ta had'awa yaran tare da rakosu mota kaman kar su tafi suka wuce se gidan ya fadeela ita dae hiran duniya kawai sukayi basu kawo abinda ya shafi rayuwarta ba.


Itama basu jima ba suka wuce gidan ya mujeeb nan ma sun samu tarba tunda dama tun da chan suna shiri da Antyn nata, sossai suka taya ta murnan samun admission d'inta daga nan se gidan yaya hameed da shi suka kebe suka sha hira kan ta fito zata wuce, jin muryar mujeebatu tayi tana cewa "ki yafemin shaati na san ban kyauta ba, ba kuma haka aminci yace ba mun tashi tare islamiyar mu d'aya ajinmu d'aya bencin mu d'aya karewanta ma da yayanki ya nemi ki za'bar mishi mata ni kika ce kanki tsaye amma duk wannan hallacin daga abu kad'an ya sameki na zama cikin masu zaginki da hantararki ki yafemin pls".


Murmushi kawai tayi tace "Allah ya yafemana" a zuciyarta kuwa cewa take Ai yanzu na dawo daga rakiyar kawaye kuma jidda kad'ai ta isheni, ko godiyar da take mata bata saurara ba ta fice dama ya hameed na jiranta wurin yaran a mota, kud'i ya basu yace ta biya ta sayan musu ice cream, gidan namesake d'inta suka wuce suka sha hira itama, daga nan ice hub suka wuce kowa ya za'bi flavor d'inshi anan suka zauna dayake had'e yake da wurin wasa haka na yara tana zaune tana karanta yadda abubuwan ABU suke su kuma yaran suna wasan su.


Kaman ance ta d'aga ido se had'a ido sukayi dashi tsaye yana kallonta, kau da kanta tayi ta mayar kan wayan kaman bata san Anyi halittanci wurin ba, a yaran sameer ne ya fara ganin shi da gudu ya isa gareshi ya rungume yana cewa "paapi" yasmin dakatawa tayi haka ma arwa, neeha kam da gudu ta je ta zata fad'a jikin shaati da sauri ta tareta sbd shareef dake kan kafanta.


Kallonshi tayi yadda yake rungume da sameer kaman ze yi kuka tabbas yayi missing yaran nashi over yadda ta sanshi da son yaran nashi, kallon neeha tayi tace "neeha tafi wurin paapi d'inku baki da kamarshi nan duniya" make kafad'a tayi Ai bata san sadda ta bugawa yarinyar tsawa ba "wuce ki bar kusa dani In bazakije ba, bani wuri" a tsorace ta matsa tana kuka kama hannun sameer yayi ya nufo su a natse yake tafiya idanunshi akanta da babyn shi da be san sunanshi ba kuma be iya ya tambayi yakumbo ba.


Dukawa yayi gaban neeha yace "neeha paapi d'inki kike tsoro?" Kallonshi takeyi tana hawaye zaheeda ma ta rike mata hannu tana hawaye "bar kukan babu abunda zan miki kinji? Kin sha ice cream yadda kike so ko In kara miki?" Kallon son tabbatar da ba abinda ze matan take mishi yana murmushin karfin hali yace "menene sunan beautiful kawarki?" Ta kalli zaheeda tace "beautiful zaheeda" dariya yayi yana sharewa zaheedar hawaye yace "beautiful basa kuka duk kuka sake kuka I won't call you beautiful zaheeda or beautiful neeha sede ugly neeha and ugly zaheeda" dariya sukayi ya shafa kansu ya rungumesu yana lumshe ido ya furta "paapi miss you baby" tace "I miss you too paapi, when are you coming back paapi?" Yace "I'm already back dear sede ki tambayeni when are we reuniting again a sabon gidanmu?" Ta wara ido "really?? Ka mana sabon gida?" Yace "yes Ai shiyasa kuka koma gidan Abba, ginawa nake" tsallan murna ta fara yana murmushi ya yafiyo yasmin zuwa tayi ta tsaya yace "bakiga paapi ba lil angel?" Tace "paapi I missed you" se ta rungumeshi se kuka.


Murmushi yayi ya rungumeta back ya kuma d'agota yana share mata hawaye yace "miss you too dear, bani son wannan kuka Ohk?" Kai ta gyad'a Arwa ya kalla ze yi magana Shaati tace "kama su ku yi mota gani nan zuwa" Arwa taje ta kama hannun zaheeda da neeha sauran suka bi ta suna waiwayen mahaifin nasu, tunda be hanasu bin umarnin mahaifiyar ba yadda yasmin ta so ba yadda suka iya sbd sanin halinta.


Mikewa tayi ta sa'bi shareef tana kara rufe mishi fuska zata bi bayansu ya sha gabanta "bazaki yafemin ba hayatee?" Tace "don't call me that, had it been ni ce rayuwarka da baka wulakantani ba, da baka zargeni da aikata zina da aurenka a kaina ba, da baka tu...." katseta yayi "keep quiet pls" idanunta na cika da hawaye tace "I won't da baka sakeni cikin tsakiyar dare akan laifin da ban aikata ba, da a bayanta baka azabtar da yaran da kake ikirari kana s......" kaman shima ze zubda hawayen da ta fara zubarwa yace "please......" kallonshi ta tsaya yi hawaye na zuba a idanunta har ga Allah yanzu da take tuna mishi da bakinta se yake jin kaman ze yi hauka kwata kwata baya son ji ya tabbatar ze fi karyewa idan har daga bakinta abubuwan da ya matan ya fito.


"Me kike so in yi miki da ze wanke ni daga waen nan laifukan da ba da sanina na aikata ba? Baza ki min uxuri ba? So kike inyi yawo duniya ina fad'an laifi na? Ko so kike in duka kan gwiwowina In roki yafiyarki kan ki yafemin? Aisha wani irin uba nake da Ina da d'a da har ya kusa rufa wata hud'u ban san fuskanshi ba bare sunanshi, nayi kuka na shiga damuwa jinya kawai kike so In fara kanki yafemin?" Dukda hawayenta basu tsaya ba sede harararshi take cikin masifa tace "bana bukatar ko d'aya cikin abinda ka lissafa just leave me alone yara ne naka ne in kaga dama kazo ka yanzu ka tattarasu ka tafi dasu but banda wannan na hannuna da kace Kai ba ubanshi bane hakan yake yana da uba da ya kula dashi tun kan ya zo duniya ya bashi gatan da kai baka isa ka bashi ba kuma shi zan aura" tana kaiwa nan tayi gaba se kuma ta d'an dakata ta juyo tace "and banda wacce kace ka gaji da ciyarwa da kulawa da ita bayan ba kai kayi zinar kawota duniya ba, Sannan banda ni karan kaina karuwa" ta juya tana share hawayen dake zuba daga idanunta babu control.4


Shima kuwa seda hawayen ya zuba mishi hannu yasa ya share ya gaji da kuka akanta menene laifinshi bayan ba a hayyacinshi ya mata hakan ba? Though ya san da ciwo amma she should have forgive him su koma rayuwarsu kaman da tunda ya dawo mata, sannan ba shi yaga zubaida yace yana so ba ya aureta, ajiyar zuciya ya sauke ya fice shima daga wurin dama shigowarsu wurin ya gani yana wucewa ya jima sossai zaune a mota yana contemplating ya shiga ko ya tafi shine daga karshe ya samu ya shigo d'in.


Tana shiga mota ta cewa yaran "kar naji maganan ganin paapi a gida I want to surprise mama about it sede kawai ta ganmu sabon gida ohk?" Suka amsata jan motar tayi ta fice zuciyarta ba daad'i sam, suna isa Mama ta so fahimtar wani abu sede ita shaati ta zame ta wuce d'aki washegari Abba ya kirata ya kamata ta tafi makarantar tunda admission ya fito, zasuje da mama su zauna gidan friend d'inshi na kwana biyu kan ya samar mata gida cikin samaru Sannan ya bata kyautar sabuwar mota hyundai had'add'e golden color murna kaman me.


Sun ajiye akan zasu tafi friday yaran baaba larai zata kula dasu sannan zata tafi dama da Shareef da lantana sbd ta samu me mata girki da taya ta kula da shareef, Abba ya sha adu'a har da hawayenta se dariya suke mata, kan satin ya zagayo Abba ya cika mata boot d'in motanta da provisions, ta shirya akwatunanta uku na shareef biyu biyar kenan se kayan lantana, mota biyu dama zasuyi harda wadda ze dawo da mama in Zata dawo shima boot d'inshi cike da kaya driver d'in mama da na Abba ne suka ja motan se garin zariya.


Kan su bar cikin garin kaduna kuwa ta ga number d'in Saif na kira dama tun randa suka rabu dashi a ice hub ranarce kawai be kira ba shima ta zata zuciya yayi se gashi washegari da call d'in ta tashi haka taki d'agawa kuma shi baya gajiya da kiran kaman maye a rana se ya mata 20missed calls bata d'aga ba, to yanzu ma tana ganin ya fara kira ta sa wayan silent ta gyara jinginuwarta lantana na rike da shareef.


Ta 'bangaren su shareef ma jidda ta samu lafiya an sallameta se suka dawo gidan hajja part d'inshi na da kan yayi aure yayinda Baba ya d'auki nauyin gyara mishi gidan Abban jidda kuwa ya saya musu cars guda uku, take aka rushe wurin aka fara tada wani ginin fin wanchan, soyayyar da yake nuna mata kuwa wani sa'in har hawayen daad'i take ita kam wannan gobara alheri ce shi yayi mata akwatunan kaya guda 7 had'add'u kaman na amarya.

Shaati taso in zaheeda ta tashi komawa wani satin ta bita taga jikin jidda se kuma maganan makarantarta ya sha kanta sede ta had'a sha tara na arziki da take so a had'awa zaheedan In ta tashi tafiya ta barwa Mama, yaran har kukan tafiyarta sukayi, sun iso zaria ba wani jimawa inda suka sauka gidan aminin Abban tarba kuwa me kyau suka samu.


Kwanansu biyu aka sama mata gidanta nan Samaru, d'an daidai ciki biyu da parlor se kitchen da store har da wurin parking na mota biyu, nan suka shiga kasuwa suka sayo duk wani abinda zata bukata na kayan gida ba irin masu tsada chan ba tunda makaranta ne akazo aka shirya mata yayyunta kowanne seda ya turo mata 100k su uku, se ya meena ta bata 50 akan tayi hakuri ya fadeela kam atmphopi da gowns ta bata ita dae cikin farin ciki take tun daga randa isma'il ya dawo bata kara ganin shi ba kuma bata neme ganinshi ba ta de san yau ya kuskura ya shiga harkar Arwa anan ze ga true color d'inta.


Tana dae ji Abba na magananshi akan jinya yake amma ko Mama bata maida hankali kai ba hakan yasa basu san halin da yake ciki ba, bayan an gama gyara mata komai da komai an shirya mama ta juya da driver d'inta da kuma driver d'in da ya kawo tata motar bayan ya damka mata key, lantana ce tayi musu girki suka ci, washegari kuwa ta shiga school dama uncle Rabi'u abokin Abban ya riga ya mata registration dept d'insu kawai ta nema ta fara sanin wasu abubuwan.


Saif be tashi sanin ta tafi school ba se a ranar bayan ta dawo makaranta ta kira yakumbo Don su gaisa sun kwana biyu basu gaisa ba anan take fad'a mata ta taho zaria makaranta Dayake a handsfree wayar take tsab yake jin komai a take yaji ranshi na suya wato bama ta da niyyar koma mishi, sbd da tana da niyya da bata nemi makaranta ba sanin baya so har yau maganan wadda ya zama mahaifi wa shareef kuma shi zata aura kaman yadda ta fad'a dawo mishi yake a kai, kar dai da gaske shi sojan da ya gansu tare zata aura, wayanshi ya d'auka yayi mata transfern 500k, daga nan ya mike ya fita yana tunanin mafitar da ya samu kuma In shaa Allahu hakanshi zata cimma ruwa.........         *comments pls samun In karasa muku In huta exams zan fara ranar Thursday*


3

                    🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇

    *Baya Chanza d'and'anon teku*


     *Fatima Muhammad Gurin*

   **Gureenjoh6763 on Wattpad**


         'Yar Mutan Adamawa


*Kuyi hakurin akasin da aka samu na fara exams d'ina, Ina muku fatan alkhairi*

  *P40*


Direct gidansu shaati ya nufa Allah ya taimakeshi daga Abba har mama suna gida, iso ya nema me gadi yace sunce ya isa, har main parlorn gidan yaje ya samu wuri a kasa ya zauna dukda yadda Abba ya matsa ya zauna kan kujera amma ya kiya, kanshi a kasa ya gaidasu cikin sanyin murya sbd kunyarsu da ya gama cikashi dukda abinda yayi wa 'yarsu gashi again durkushe a gabansu cikin neman alfarmar sake kar'bar amanar d'iyar tasu a karo na biyu.


Kasa magana yayi dukda yadda yake jin idanun iyayen nata a kanshi ya san abinda ze yi be dace ba sede wannan ne kad'ai hanyar da ze iya bi a yanzu ya samu shaati sauran abubuwan ze zauna tsakaninsu, hawaye ya fara a hankali Abba yace "subhanallah Saifullah menene haka me ya faru?" Tun yanayi a wasa sede abubuwan da ya matan suna dawo mishi da gaske tunda be ta'ba bud'e baki yayi maganan ba, daga ya bud'e bakin da niyyan magana se kuka ya hanashi.+


Tausayinshi ne ya cika Abba da mama hakan na nuna cewa Saif ya dawo cikin hankalinshi sossai sukayi murna don bazasu so rasa suruki irin Saif ba ya rike d'iyarsu da amana a lokacin da su suka so wanchakalar da rayuwarta, tabbas ba don aiki irin na asiri ba sun tabbatar ko wuka aka sawa Saif a wuya da nufin ya saki shaati baze iya ba, Abba ne yayi gyaran murya yace "Alhamdulillah! Alhamdulillah Lallai Allah shine abin godiya da ya kwato mana kai daga sharri irin na asirin da akayi maka, wato saifullah a kullum kaman yadda bana manta mahaifiyata a adu'ata haka kaima bana ta'ba manceka, tabbas kai namijin kwarai ne da ko wani suruki ze yi alfaharin samu ban ta'ba maka godiyar rike min uwata da amana ba, ba wai na manta bane a'a Ina jiran lokacin da ya dace ne, na gode kwarai saifullah".


Murmushi yayi yana kuma share fuskanshi yace "Abba gafararku nake nema, pls ku yafemin bani da niyyar zaluntar Aisha da gayya" Mama tace "Saif mun sani wallahi karka damu, Allah ya yafe mana gabad'aya" Abba na murmushi yace "na san ba wadda ze kai Uwata farin cikin samun lafiyarka" kanshi kasa yace "Ai Abba ta sani" Abba na kara sakin murmushi yace "ah to Masha Allah" mama tace "er kaniya shine ko ta fad'a mana wannan abin farin cikin?" Kanshi kasa yace "wai kunya take ji bata san ta inda zata fara ba, Abba aurenmu nake so a mayar sbd tayi karatunta cikin kwanciyar hankalinku na tabbatar ba wai hankalinku ya kwanta bane barinta chan wani gari a matsayin wacce ta ta'ba aure, In da hali Ina neman alfarmar a mayar min da aurenta juma'a me zuwan nan" Abba yace "but ka san yanzu a matsayin bazawara take tana da ikon za'ban duk wani mijin da take so ko? Bazan mata dole ba In har tace bata son komawa gidanka Saif dukda ina sonta da kai".


Kuma kasa yayi da kai yace "ita ta turoni bayan mun had'u sau biyu Ina bata hakurin laifin da na mata" ya san iyayenta sun san halinta sarai bata cika sauka da wuri ba amma Tunda ya furta sun had'u sau biyu zasuyi tunanin kila ta sauka ta yafemai don dole, Abba ze yi magana neeha ta shigo da gudu tana kawo karar yasmin ganin Paapinta yasa ta tafi da gudu ta fad'a jikinshi tana ihun murnan ganinshi murmushi yayi yana d'ago ta yace.


"Hey angel" Tace "paapi ka gama mana sabon gidan da kace?" Yace "no saura kiris but I promise nan ba da jimawa ba zan gama" daidai lokacin Yasmin da Arwa suka shigo, yasmin ma karasawa tayi ta rungumeshi tace "paapi oyoyo" sameer da y shigo yanzu shi da zaheeda yace "paapi ka jima baka zo ba tun randa muka had'u a ice hub" zaheeda tace "paapi" ya shafa kanta Mama tace "oya ku wuce ciki magana muke in mun gama kwa fito ku mishi mitan nan".


Ciki suka shige suna jaddadda mishi kar ya tafi, Abba yayi gyaran murya yace "Saif ba matsala kaje zuwa gobe zamuyi magana duk yadda ake ciki" godiya yayi ya mike mama ta kira su Yasmin tace su sameshi garden, aiko ya jima dasu suna hira har arwa seda ya sa ta sake dashi dama chan shi ta sani matsayin mahaifi dukda yadda yake farin ciki cikin yaran nashi zuciyarshi na adu'ar Allah ya sa kar Abba ya kira ta ya tambayeta ya san daga ya kirata shikenan kuma.


Ta bangarensu kuwa Abba ya kalli mama yace "kina tunanin Uwata har tayi saukowan da ze sa tace a mayar mata da aurenta juma'an nan?" Tace "ka bani zuwa anjima da dare zan d'an bincika maka ita" Kai ya gyad'a yana mikewa ya shige ciki, Shiru tayi tana tunani kan tayi murmushi ba wadda ya fi ta sanin halin shaati ta san bata sauka ba sede ba ko yaushe ya kamata a biyewa fushinta ta cutar da kanta ba Bayan ga abinda ze anfaneta, Mikewa tayi zuwa jikin window ta ci gaba da kallon yadda yaran suke farin ciki tare da mahaifinsu, ita uwace tana da right d'in za'barwa erta abinda yafi dacewa da rayuwarta bare tayi imani har ga Allah shaati na tsananin son Saif har yanzu, ajiyar zuciya ta sauke tana ayyanawa a ranta 'ze iya da ita kenan tunda har ya nemi a mayar ba tare da saninta ba' .


Bayan ya tafi ta kira yasmin take tambayarta dama sun had'u da mahaifinsu ne randa suka fita? Ta tabbatar mata sun had'u har taki zuwa maaminsu ta kusa dukanta sbd hakan, kai ta gyada nan Neeha ma ta gayamata yace yana Gina musu sabon gida kuma ya ma kusa gamawa, murmushi kawai tayi.


Da dare da Abba ya dawo take gaya mishi itama sunyi magana da Shaati ta amince zata koma gidan mijinta, ta san halinshi ko da Saif alkhairin shaati ne, farin cikinta da rayuwarta In har bata amince da koma mishi ba baze ta'ba mata dole ba kuma bata so ya ga kaman karya Saif ya mishi sbd ze rikeshi da hakan, yayi farin ciki sossai take ya kira Saif yace ran juma'a za'a mayar musu da auren a babban masallacin almannar, murna a wurin Saif kaman ya zuba ruwa a kasa ya sha kenan basu tsaurara bincike ta 'bangarenta ba.


Ta 'bangaren shaati kuwa tunda taga kud'in nan take neman layin shi yaki shiga da gangan ya sata black list sbd be Shiryawa bala'inta ba, aiko ita kad'ai ta karashi cin ranta tanayi tana saukewa kan Shareef kaman shine Saif d'in, daga Baya taso mayar mishi da kud'in se kuma taga gwara taci taci banza kuma ko me ze yi bazata koma gidanshi ba. Rayuwar zariar daad'i ya mata hankalinta kwance bata san wainar da ake toyawa ba har ana gobe juma'ah.


Ta 'bangaren Saif kuwa dama tun washegarin ranar da ya shigo kaduna ya sa aka tada mishi gini a wani filinshi dake malali, kuma express ne ginin had'add'en duplex ake ajiyewa wurin, gabad'aya rayuwarshi ji yake ba wadda ya kaishi farin ciki, kowa a familynshi seda ya san yana cikin farin ciki tsabar irin alkhairan da yayi tayi, kullum se ya je gidan Abba wurin yaranshi da zaheeda da taki komawa sbd yadda suka shaku da yaran.


A takaice har jidda ta San da maganar komen amma banda uwar gayyar, duk sukayi waya da mama tana so a bata zaheeda se sunyi maganar auren hajja ma ta turowa mama wasu ingantattun had'e had'e daga maiduguri ta mota da wani had'add'en humra da ya amsa sunanshi dayawa, banda wadda hajja na nan ta har had'a ta ajiye tana jiran Amaryar, har ya meena jidda ta matsawa ta tura mata numbern saif ta ba Shareef a lallai wai su zama abokai suma.


Dayake Saif d'inma yaji labarin shareef da irin taimakon da yayiwa shaati wurin ya mujeeb so mutuncinshi sossai Saif ke gani hakan ya sa yana kiranshi suka jone inda yayiwa shareef d'in godiya sossai, nuna mishi yayi ba komai Ai takwaran da ya mishi ma kawai ya isheshi, dariya sukayi a tare, wasa wasa cikin sati suka wani mugun jonewa kaman waenda sukayi shekara tare Toh hali yazo d'aya, barkwanci, son hira, zolaya duk haka suke idan shareef ya sashi a gaba da zolayar zuby se Saif ya had'ashi har da yakumbo don takaici yayinda shareef ke kwasan dariya idan Saif ya kulu.


Tun Alhamis shareef ya shigo kaduna a hotel ya sauka abinshi in an d'aura aure ze juya da zaheeda sbd school, jidda tace bazata zo ba se in shaatin zata taare suma har yanzu suna gidan baba don ba'a karasa ginin nasu ba, kaman had'in baki yassar ma ya diro kuma hotel d'in da shareef yake ya sauka shima nan suka jone a masaukin shareef suka sha hira, se anan Saif ke gayamusu yadda ya linke shaati dariya da zolaya kam ya shashi seda suka ga ya koma abin tausayi kan shareef ya dafa shi yace.


"Karka damu baza ka sha wahala ba sbd trust me har gobe Aisha me sonka ce na gaskiya, za de ka gwaro Don fa mata hmmm" se suka kuma sa dariya murmushi kawai yayi babban damuwan dama a d'aura aure ne daga igiyoyinta sun shiga hannunshi komai me sauki ne duk bala'inta zata sauka.


Itama a 'bangarenta yanzu ta shaka sbd kiran da yake damunta dashi yanzu bayayi haka baya Tura mata ko sako ne ya shareta fah wadda hakan ya sa ta kuma tunzura tana ganin dama chan ba wai son ta koman yake ba, dukda tana waya da yayyunta da en gidansu wasu da kuma su yakumbo da namesake d'inta ba wadda ya kuskura ya fad'a mata sbd mama ta hana ta tabbatar ko a ranar juma'an ta kira Abbanta tace bata san da zancen ba se ya wargaza auren.


***********


JUMA'A


Da misalin karfe biyu daidai aka maida auren Saifullah da Aisha ranshi kal kaman an sashi aljannah har kuka yayi ya roki Allah ya bashi ikon riketa da amana kar ya kuma failing d'inta a rayuwa, tana zaune a parlor rike da shareef tana koya mishi zama, A daidai lokacin da aka shafa fatiha a daidai lokacin gabanta yayi wani mummunan fad'uwar da har ta sake shareef ya kwad'u da kasa bata sani ba, seda ya tsala ihu kan ta dawo hankalinta da sauri ta d'agashi tana jijjigashi.


Sede yaro yaki shiru juyin duniyan nan tayi amma shareef wani irin kukan da ba sabonshi ba yakeyi Ai itama bata san sadda ta fara kuka ba, dama haka take in tana goyo In yaro ya rikice itama rikicewar take a irin wannan lokacin ne uban ke da anfani tuna hakan ya kara tunzura kukanta, da sauri lantana ta fito ta kar'beshi tana tambayar me ya sameshi sede shaati ta kasa magana, wasa wasa zazza'bi ya saukar mishi sbd ya bugu sossai kasancewar kasan tiles ne ba carpet ba.


"Uwar d'akina ko asibiti za'a kaishi jikin nashi yayi raurau alamun zazza'bi" se a lokacin wani tunanin asibiti ya fad'o mata da sauri ta zari gyalenta dama doguwar rigace jikinta d'aki ta shiga ta d'auki pos d'inta da car key ta fito ta kar'beshi tace "ki kula da gidan" har ta nufi kofa se kuma ta tsaya tace "zo ki bud'emin gate" da sauri lantana ta wuce ta bud'e mata gate d'in ta ja motar ta fice.


Dama abokin abbanta ya nuna mata asibitin da ya kamata ta dinga zuwa nan ta nufa da sauri kuma a rud'e ta shiga a take nurses suka kira doctor ganin yadda take zaka d'auka an ce mata ya mutu ne, cikin wannan rud'anin Saif ya kirata ba tare da ta duba ba kawai tayi picking, jin yadda tayi sallama tana jan hanci ne ya sashi Mikewa tsaye daga zaunen da yake a hankali ya fara takawa yana barin inda su shareef suke shi duk a tunaninshi taji aurensu da aka mayar ne ta tada hankalinta a sanyaye yace.


"Kuka kikeyi?" Ai kuwa se ta sake sakin kukan tana dafa kirjinta "Shareef ba lafiya gashi se fad'uwa gabana yake" idanunshi ya lumshe yace "kiyi ta ambaton Allah halan kuka yayi sossai kema kika fara tayashi" sanin hali, ya karasa a ranshi shiru tayi se lokacin ma ta san da wa take waya, kawai ji yayi ta kashe lumshe idanu yayi ya kuma bud'ewa, sabuwar dalleliyar prado d'inshi da ya saya jiya ya nufa yana cewa su shareef da suke tsaye tare "Amarya tayi kira se munyi wayanku" a d'ari shareef ya rikeshi yana jefa mishi harara "kayi kad'an wallahi ba inda zakaje se kaga tafiyar kowannenmu".


Kallon yassar yayi yace "ko ba haka ba?" Yassar yace "Ai wannan yaci uwar rainin wayo In gayama ba matsalarshi bane in munga dama mu mutu a hanya tunda shi Ai burinshi ya cika" dafe goshinshi yayi kan yace "Ohk to muje kowannenku ya kama gabanshi se in tafi pls ku hanzarta shareef ne ba lafiya kuma Hayatee ta iya in yaro ba lafiya tayi ta kuka" Shareef yace "Allah ya ceceka, sbd lil soldier tafi Allah ya tsare" seda ya shiga motar ya tayar kan yace "da ma baka sakeni ba da duk se kunci bugu" be karasa ba ya ja motar da gudu yana dariya.


Shareef gidan Abba yaje bayan sunyi sallama da yassar ya kama hanya, zaheeda ya d'auka su neeha harda kuka zaheeda karan kanta da kuka da komai ya lalla'bata suka wuce bayan mama ta had'a mata goma na arziki.


Kan ya isa seda ya Kira Ya meena Bayan sun gaisa yake tambayanta address d'in shaati a zariyar, nan ta ce ya bata five minutes ta kira mama, bayan mintuna ta turo mishi text d'in address d'in kuwa karawa motarshi gudu yayi dayake ba wani nisa bane nan da nan ya isa seda ya tsaya gidan yayi knocking lantana ta bud'e suka gaisa kasancewar ta sanshi ya tambayeta inda shaati take tace mishi suna asibiti sede bata san sunan asibitin ba.


Da wayanshi yayi tracking location d'inta nan yaga sunan asibitin motanshi ya koma ya ja, tunanin mahaifiyar zuby na fad'o mishi, five days back ta kirashi bayan sun gaisa take tambayarshi zubaida nan ya bata labarin abinda ya faru, gafararshi ta dinga roka akan ya yafewa zuby shi kuwa yace baze yafe mata ba sbd ta mishi wani rauni da har abada baze goge ba Don baze ta'ba manta irin wulakancin da yayiwa shaati ba.


Labarin abubuwan da ya faru ta bashi ko d'igon tausayin su be ji ba, tace mishi ta koma kauyensu abinda zataci ma gagararta yake ya taimaketa ya fiddo mata zubaida In yaso ya tura mata ita kauyensu ba Don halinta ba, sbd yadda take magiya da kuka ya sa ya amsa mata, nan ya kashe ya kira police station d'in Abujan a take suka ce mishi an ajiyeta ba wani wadda ya neme ta Sannan kisan nan dae da hannunta dumu dumu an turata prison dukda tayi hauka tuburan kan shigarta.


Ba tare da yace komai ba ya kashe ya Kira uwar ya fad'amata yana gama fad'a ya kashe wayanshi yayi blocking d'inta tare da goge numbern, murmushin takaici yayi a fili ya furta "yanzu Ina anfanin duk abubuwan da kikayi? Duk wani fad'i tashi na ganin kin rabamu kin mayar da farin cikinmu bakin ciki at long last muna tare zamu ci gaba da farin ciki ke kuma kina Ina?".


Kwafa yayi yana cewa a zuciyarshi tabbas ya kamata mata masu irin wannan hali naki su tuba su komawa Allah don ba abinda ke karshensu irin tarin bakin ciki da nadama, a daidai lokacin ya isa asibitin yayi parking ya fito, dakakkiyar farar gezna ce a jikinshi ya cire babbar riga da hulan ya zubasu mota kafafunshi sanye da black half cover me bala'e'en kyau gashin kanshi har sheki yake tsabar gyaran da ya sha na d'aurin aure.


Yana wulwula car key hannun shi d'aya a aljihu ya nufi cikin asibitin, direct ward d'in yara ya nufa yana jan kananun tsaki na yadda en mata ke binshi da kallon burgewa, tun daga nesa ta hangeshi seda gabanta ya fad'i runtse idanunta tayi 'me ya kawoshi' dukda bata wani kalli fuskanshi ba but daga yanayin tafiyan ta san na waye ne ko da kuwa cikin mafarki ne.


Shima kuwa ya ganta hakan ya sa ya kura mata ido se kuma ya kalli gefe da gefenta wani irin kishi ne ya taso mishi yadda ta saka gyalen nata ya bayyana rabin baki sid'ik d'in gashin kanta Sannan abayar me shape ce wadda ya zauna mata zakayi tunanin buduruwace sbd yadda take da jiki me kyau ainun, yadda yake tako kafanshi zuwa gareta haka zuciyarta ke bugawa kaman a kai yake tafiya kan ya karaso turarenshi ya bule inda take seda ya matso kaman ze shige jikinta bata hankara ba se hannayenshi taji a saman kanta ya ja gyalen ya gyara mata a zabure ta matsa baya.


Tana watsa mishi harara da colored eyes d'inta, wata munafukar murmushi ya saki cikin husky voice d'inshi yace "hello love".....
  "Last page na nan zuwa kuyi hakuri"

1

                  🖤Gureenjo🖤🍇💦RUWAN SAMA.......💦🍇

*Baya Chanza d'and'anon teku*


*Fatima Muhammad Gurin*

**Gureenjoh6763 on Wattpad**


'Yar Mutan Adamawa


**FINALÉ**


Idan dutse ya motsa to shaati ta motsa daga banzan hararar da ta sake mishi, be kuma tankawa ba se idanunshi da ya zuba mata wadda yake sata jin bata kyauta ba, da karan kanta kuma ta d'ago ido tace "Ina yini" wani murmushi ya saki da ya ja mata fad'uwar gaba, da sauri ta kauda kanta yace "Lafiya kalau Amarya" Shiru ta mishi tana juya zancen amarya da ya kirata dashi maganan doctor ne ya dawo da ita hankalinta yace "kune iyayen shareef Saifullah?" A tare sukace "eh mune" se ta kalleshi, ita fa har yau bata manta zargin da ya mata ba sede ta yafe mishi da jimawa ta sani.+


Bayani ya musu akan ba wani matsala er zazza'bi ce ta saukar mishi sbd kukan da yayi tayi wadda ba sabonshi ba and ya had'u kuma da buga kanshi da yayi yanzu ya musu prescribing drugs su saya se su wuce, kar'ban shareef d'in tayi daga hannun nurse da ta fito rungume dashi, bata gama balancing d'inshi a jikinta ba taji an zameshi har tsorata tayi ta d'ago se kashe mata ido yayi, bata san sadda tayi tsaki ba Ai kuwa ya wara idanunshi kanta.


Kar'ban papern tayi tayi gaba ba tare da ta jirashi ba, a baya ya bita har pharmacyn asibitin ta sayi magananin cikin tsare gida kar ma yace ze gwada bada kud'in, bayan an bata ta fito ya kuma biyota har wurin motanta mika mishi hannu tayi "bani shi" yace "bazan baki ba" bata kuma magana ba ta bud'e motan ta shiga ta ja shima nashi ya nufa ya shiga ya kwantar da shareef kan sit ya ja motan yabi bayanta tana parking yana yi, rannan had'e ta nufoshi "wai kai me damuwanka da nine da zaka sani gaba kayi ta bi? Ka kyaleni inyi rayuwata banzo garin nan don ka takuramin ba".


Zagayeta yayi ya nufi cikin gidan a baya ta bishi tana zuba masifa sede ko ya kulata seda ya mikawa lantana shareef dake bacci ya tabbatar ta shige d'akin da take kan ya fusgo hannun ta se cikin d'ayar d'akin da ya tabbatar nata ne, cike da bala'i ta fisge hannunta "wai me yake damunka ne? Aurenka ne kaina da zaka dinga ta'ba min jiki duk sadda ka so? Ko kuma mahaukaciya ka maida ni da tun d'azu nake magana kayi min banza" abinda yayi mugun bata mamaki bata karasa ba ya danneta da kofa tare da had'e bakinsu sossai ta firgita wani irin iskanci ne wannan? Me ya hau kanshi? Gabad'aya karfinta tasa ta tureshi tare da d'aga hannu zata tsinka mishi mari sede kuma ta kasa sauke hannun kawai tayi ta fashe da kuka sossai.


A take ya rud'e ze kuma ta'bata ta buge hannun, yace "kiyi hakuri ban yi dan 'bata miki rai ko don saki aikata zunubi ba, sema lada da nayi imanin zaki samu" katseshi tayi "lada? Wani irin lada? Aurenka ne kaina da zan samu ladan sumbatata da kayi?" Shiru yayi yana kallonta seda ta maimaita abinda tace cikin ihu kan yace "aurena ne kanki a yau aka d'aura da misalin karfe biyu na rana" tsabar shock bata san sadda komai ya d'auke mata ba, ganin yadda ta shiga rud'ani yasa a hankali ya duka kan gwiwowinshi "na rokeki da girman Allah Aisha ki yafemin wallahi kece rayuwata bazan iya rayuwa ba tare da ke ba, bani da wani option da ya wuce bin hakan na sameki sbd kinki saurarata na san ban kyauta ba kwarai da gaske da na cewa iyayenki da amincewarki zan mayar dake sede ko wanene in my shoes baze so rasa mace irin ki ba, I'm begging you kome zakiyi kiyi la'akari da ba yadda na iya ne...."

Waje ta nuna mishi cikin wata iriyar murya tace "get out!! Just get out from my side Saifullah ashe na zama banza kayan wanki ban sani ba? Ko yaushe kayi niyyar samuna se ka sameni ba da yardata ba ba komai ba? Na gode but please leave me alone ko Ina me maka rantsuwa da Allah in fita In bar maka gidan da garin baki d'aya" Mikewa yayi ya fita a sanyaye jikin kofa ya tsaya yana jin yadda take tapping kafafunta alamun abu take jira be gama tunanin menene ba kawai yaji tace "ya meena da gaske an maida aurena da babansu neeha?" Ai be ji me aka ce mata ba ya de ji ta fashe da wani irin kuka, zama tayi kasa tana ta kuka kaman wacce akayiwa mutuwa.


A daidai lokacin shareef ma ya farka da wani kukan lantana ta fito dashi ta bawa mahaifin ta koma sede juyin duniyan nan ya mata ta bud'e kofan nan ta bashi Nono ta ki, haka ya hakura yaje ya had'a mishi madara da ya gani parlorn wadda ya san shi take ba yaranta, ya bashi ya sha ya d'auki magananin da ta ajiye nan kan kujera ya bashi yadda akayi prescribing, bayan ya gama bashi ya yi ta jijjigashi har seda ya koma bacci duk abinda yakeyi hankalinshi na ga kofan sbd har lokacin bata dena kuka ba.


Ya rasa tsanar da ta mishi ne ya sata kukan nan ko kuwa auren da aka mayar without her consent ne ya sata wannan kukan? Kofan ya koma yayi ta had'ata da Allah, Ai bata yi niyyar bud'ewa ba seda taji yadda shima ya fara tayata kukan a daidai lokacin wayanta ya fara ringing bata duba ba se kawai ta d'auka Mama ce nan ta hauta da fad'a ba wani lallashi seda ta mata tatas kan ta yanke call d'in dukda yadda take jin kukan er tata.


Ai se kawai Saif yaji ya tsani kanshi jin bayan call d'inta da maman wani kukan da ta sake saki ji take ta tsani kanta sbd ba me sonta a nata tunanin kenan, da kanta ta bud'e mishi kofan seda ta bari ya shiga ta rufe kan ta ja baya ta fara cire kayan jikinta tana kuka take cewa "ba abinda kake so kenan ba? Abinda ya sa ka takurawa rayuwata ka hanani yin abinda raina ke so ba? Gani saifullah kayi duk yadda kake so ka fice min da gani wallahi na tsan......" wani irin wawan runguma ya mata da seda yasa ta shiru bugun kirjinshi ta fara tana me cigaba da mishi hauka.


Rungume da ita a jikinshi har ta gaji da kokarin kwacewar tayi shiru, nan kuma zazza'bi ya saukar mata da ciwon kai take ta fara rawar sanyi, hakuri ya ringa bata yana mata wasu irin kalamai a cikin kunnenta sede kaman bataji haka ta koma, haka ya lalla'bata ya kwantar ya fita ya nemo mata magunguna da nama gasashe me ruwa ruwa.


Se yoghourt don ya san bazata ci wani abin kirki ba, bayan ya dawo ya shigo da motanshi da nata ciki, ya karasa yayiwa lantana knocking bayan ta fito yace "ki kula da shareef plz in yayi kuka ki bashi madaranshi mahaifiyarshi ba lafiya" amsawa tayi da "to in Shaa Allahu" dama yana wurinta kuma fitanshi ta d'auko kayan wankanshi a d'akin shaatin ta mishi wanka ta sa mishi kaya.


Leda d'aya ya mika mata ta kar'ba da godiya ta juya ta rufe kofanta, d'akin shaati ya shiga, a natse ya cire kayan jikinshi yana zubawa bayanta idanu seda ya saura daga shi se boxers da vest, hawa gadon yayi ya ta'ba jikinta zafi jau sauka yayi zuwa toilet ya d'ibo ruwa tare da d'auko karamin towel ya dawo a hankali ya d'agota ya fara goge mata jikin idanunta biyu sede a lumshe suke samansu ya kumbura alamun taci kuka a hankali yake bin jikin nata seda ya goge lungu da sako bayan ya gama ya samo wata er doguwar vest ya sa mata.


Abincin ya d'agota taci sede sam taki da kyar da lallashi da komai ya samu ta d'an ci sede ya sha harara, sam be damu ba ya bata maganin ta sha sede jikin yaki yayi sanyi se karuwa zazza'bin yake ai ba shire ya shige bargon ya zame kayan jikinsu tare da had'eta da bared skin d'inshi dukkansu seda suka sauke ajiyar zuciya.


Kuma rungumeta yayi yana furta "I miss you like crazy" jikinshi ta shige tana binni fuskanta a kirjinshi anan ya shantake yayi ta bata hakuri tun bata sauraranshi har ta fara anan ta dinga tuna mishi abinda ya mata kowanne se ya bata hakurinshi daban yana murmushi a hakan ma seda ta dinga dukan kirjinshi dukda bata da karfi har seda ta gaji kan ta kyaleshi tana d'aura lips d'inta da ta gama jikashi da miyaun bakinta a kan kirjinshi razana yayi wadda ya sanyata sakin murmushi me sauti cikin sanyin murya tace "nima nayi kewarka roohul na'im, kwakwalwata bata ta'ba hutawa da tunaninka ba a yayin da nayi kukan bakin ciki da takaici a ranar da wannan lips d'in naka suka furta min kalman saki, sune kalmomi mafi muni da baki a rayuwata gabad'aya, bana tausayin shareef ko kad'an kaman yadda nake tausayin kaina because nothing is more painful than been unable to forget what you wish to forget".


Kuma cuddling d'inta yayi yana pecking gashin kanta yace "you are so strong that's why you managed to survive like that, i respect you for that pls keep staying alive and strong for me, I love you hayatee" bata amsa ba se lub da ta kuma yi, to ya ta iya duk abinda mama ta fad'a mata gaskiyace ba karya ciki har Abada bata ga wadda zata so irin Saif ba kuma ya mata hallacin da bata ta'ba rufe idanu bata tuna da hakan ba.


Sannan me laifinshi take wahalar dashi akan abinda yayishi baya cikin hankalinshi dukda akwai ciwo? Babu so ta za'bi ta rungumeshi su zauna kan 'ya'yansu tare ba fah wai zama zatayi Don darajar 'ya'yanta ba zama zatayi Don tana sonshi, ita bata daga cikin matan da suke kashe kansu su zauna a inda basa samun farin ciki ko na miskala zarratin wai sbd 'ya'yansu, kiran sallahn magrib ya dawo da ita tunanin ta mikewa yayi yana zameta daga jikinshi se kuma taji kunyanshi ta juya da sauri murmushi ya saki ya shige toilet ya san bata sallah so wanka yayi ya fito sharp sharp ya fito ya maida kayanshi ya karasa bakin gadon yayi pecking lips d'inta yace "take care bari naje na dawo" ya juya ya fice yana murmushin wannan sabuwar kunyar.


Wasa wasa nan ya kwana kan ya dawo tayi wanka ta sanya kayan shan iska ta bula turare jikinta ta kuma gyaran d'akin fita tayi zuwa wurin su lantana ta samu tana sallah shi kuwa shareef se baccinshi yake ta'ba jikinshi tayi taji normal se kawai ta kyaleshi nan ta shiga kitchen tana tunanin me zata bashi yaci ne, karan wayanta ya sa ta koma d'akin ta d'aga jidda ce nan ta sa ta a gaba da tsokana dariya kawai take baata bata amsa seda ta gama kan suka koma serious topic, wai jidda ke gayamata yadda zata kula da Saif dariya take harda rike ciki da ta gaji taga jiddan bata da niyyan denawa se ta katseta da cewa "Ohk Anty jidda naji komai da komai kuma zanyi aiki dashi" jin yadda tayi maganan ta san gatse ne yasa tace "sannu wato ina gayamiki abinda ze ficeki kina min iskanci?" Wani dariyar shaati ta sa tace "sorry ma'am shekaruna 9 a system d'in shi yasa ban son lesson d'in me 6years oya go and take care of your oga ni ma bari inji da nawa bye" bata tsaya jin masifan jidda ba ta kashe wayan tana dariya ta san ta kulu iya wuya.


Daga bayanta taji ance "what's up da wannan dariya haka hayatee?" Tana juyowa tace "welcome, ni da jidda ne wallahi" yana rungumeta yace "hala halinsu d'aya da mijinta" tace "sossai ma harda zaheeda" dariya yayi yana cewa "waennan gidansu akwai ciwon ciki" zame jikinta tayi tana cewa "hmmm se a hankali, me zaka ci In dafama?" Yace "zanso cin girkinki sbd nayi missing d'inshi but yanzu kaduna zan wuce akwai wani aikin da ya kamata In karasa yau d'innan"


Fuskan kuka tayi kaman neeha but batayi magana ba pecking goshinta yayi yace "I'm sorry habeebty ko kin fasa karatun mu koma ki tare yau?" Da sauri ta d'ago ta zuba mishi wani kallo dama ya san za'a rina wasa kawai ya maida maganan daga nan ya mata sallama ta rakashi har motanshi ya ja ya fice, dawowa ciki tayi Ai tunda har ta fara karatun nan kuma be isa ya hanata ba abinda ma baze yiwu ba kenan, ta san da gaske yake tunda tun da chan a sharud'anshi ba karatu sbd ya tsani chakud'uwar matarshi da maza dayawa.


Tunda ya kama hanya suke waya har ya isa abin dai zam nan da nan soyayyarsu da sukayi kokarin binnewa ya fito waje ya dawo sabo dal.


BAYAN WATA UKU


E zuwa yanzu shaati har tayi hutun first semester kuma a komawantan nan ne zata tare gidanta da yaranta, soyayyarsu da Saif ko ba'a magana dukda ya jima da komawa Abuja sede waya da suke yawan yi zata iya Kirga sau nawa yazo zariah sossai yake darajata da maganarta yanzu, itama kuma tana ganin kimarshi sbd ko nemanta be ta'ba yi ba iyakaci runguma da pecks har yanzu, komawansu kaduna da kwana biyu hajja, yaya da jidda suka zo tarba na garari suka samu inda aka hau gyara shaati, Mama ta samu akan ita kam a san yadda za'ayi bata son haihuwa se ta gama school, shawarar yadda zatayi planning marar cutarwa sukayi, ana gobe zata tare sun fita da jidda

Saloon sun dawo kenan suka nufi part d'in hajja don kar'ban d'inkinta da telanta ya kawo aka kai part d'in hajja instead of part d'insu.


Kawai se ganin mutum tayi gabanta, da sauri ta ja baya tana rike hannun jidda kallonshi take tana ta'be baki dukda yadda ya rame ya lalace be sa taji ko d'igon tausayinshi ba, kwanaki taji wai mamanshi ta jibgeshi ta sakeshi ta tattare duk arzikinshi ta gudu, Sannan taji wai mahaifinshi ya nemi gafarar Abbanta akan duk abinda suka mata da shi kanshi kuma ya yafe bata damu ba jin wai be da wani maraba da mace yanzu gani take ya samu duk abinda ya kamata ya samu a ha'intarta da yayi.


Kasa ya zube gabanta cikin zubda hawaye yace "na tuba Aisha ki dubi girman Allah ki yafemin abinda na miki ko zan ga haske a rayuwata, na tuba ki gafarceni kamar yadda Allah yaji kanki ya taimakeki a lokacin da na so wargaza miki rayuwa, ki bari Khadija ta san ni mahaifinta ne ko zan samu me min adu'a In na koma ga ubangijina kila sanadiyarta Allah ya ji kaina, na yarda na amince da duk wadda aka zalunta Allah se ya bi mishi hakkinshi nan duniya ba se kaje lahira ba na tuba!!" Se kuka kaman mace, shaati zata zagayeshi ta wuce taji an ce daga bayanta "ashe baki san girman Allah ba?" Da sauri ta juya.


Abba ta gani tsaye yana kallonta "Ina miki kallon me hankali uwata? Mutum babba kaman isma'il, d'an uwanki jininki kai ko ba jininki ba ko ke kafura ce mutum ya had'aki da Allah ki kasa yafe mishi? Ko ubangiji muna yiwa laifi ya yafe mana, bance dole se kin bashi Arwa ba sbd nima bazan yarda da wannan ba but at least ki yafemishi" hawayen da ya gangaro mata ta share tace "Allah ubangiji ya yafemana gabad'aya" ta zagayeshi ta wuce, jidda tabi bayanta Arwa dake tsaye daga chan bayan Abba tana jinsu tana kallonsu kawai se ta juya ta koma garden ta zauna.


Allah ya gani a da ta tsani mahaifin nata sede yawan samunshi kullum yana zubda hawaye cikin nadama a nan garden d'in yasa ta tausayinshi bata da burin komawa hannunshi sede zata dinga gaisheshi, aiko tana nan zaune se gashi a gefenta ya zauna kanshi kasa kunyan duniya ya rufeshi ko kallonta be iya yi ba, se jin muryanta yayi tana cewa "maami ce ko? Kayi hakuri zata sauka bata da wuyan sauka in dae har ka gane laifinka ka bata hakuri".


Hannunta ya kama ya kai fuskanshi share mishi hawayen tayi, se kawai ya rungumeta, sun jima nan zaune da kad'an da kad'an suke magana har suka fara d'an sakewa, kaman daga sama taji muryan shaati "ke khadija" yadda tayi maganan da mamaki saman fuskanta mikewa Arwa tayi ta nufeta tace "maami kuka yake tayi shine nake bashi hakuri Antynmu tace In babba kuma namiji na kuka Haka ba karamin abu bane" nuna mata hanya tayi tace "wuce ciki" wucewa tayi shaatin tabi bayanta bayan ta harari isma'il da yake kallonsu.


Washegari da dare aka kaita bayan jidda ta chanchad'a mata lallen sole-tape da suka jima sunayi tun safe yayinda yaya mahaifiyar jiddar tayi mata wani kitson da ya bata mamaki kaman da allura ake tsagasu tsabar kankanta ta fita amaryarta sak, da daren suka shiryata cikin lafaya daga nesa in ta wuce se kaji kamshinta ya bule ka har yana neman zauta ka, anyi na jiki akayi na tsuguno, ga na kaya da suka jima a kabbasa, Sannan ga humras kala kala bata fesa turaren bature ko guda ba banda roll on da ta shafawa hammatanta.


Sbd Er karamar walimar dare da Saif ya had'a a compound d'in gidan yasa ta d'anyi light makeup tayi kyau sossai, motoci kusan goma suka yi convoy zuwa malali, duk en gidansu seda sukaje Sannan ga su ya meena da matan yayyunsu yawanci ma da motocinsu ne, har yaran ba'a bari ba amma zasu koma da su jidda, gidanta ba karya ya had'u dukda Saif yaki Abba yayi mata kaya but seda yayin Turkish sets na had'add'un cushions da kayan gado kala biyu, red and milk da kuma Ash and milk shi ma Saif ba'a barshi a baya ba seda ya mata royals kala biyu.


Gidan ya had'u ba karya kowa se santin gidan yake, parlornta biyu sama da kasa banda na part d'inshi Sannan a parlorn kasan site d'in su Arwa yake, fasalta gidan ma 'bata lokacine, kowa ya kiyasta had'uwarshi a ranshi, anyi walima anci an sha aka watse inda Amarya da ango suka kare a d'akin shi, sossai ya nuna mata yadda yayi kewanta inda suka kashe daré cikin so da kaunar juna.


Bayan sati da tarewarta da safe suna breakfast aka kirashi ganin yakumbo yasa ya d'aga da sauri sede kukan da yaji tanayi ne ya sashi mikewa yana tambayar Abinda ya faru rasuwar hajar ta fad'a mishi inda ya fara salati nan yace gashinan zuwa, sharp sharp suka Shirya suka fice, Allah sarki sossai Anty tala ta d'aga hankalinta sede daga baya tayi tawakalli ta barwa Allah, a ranar ya sukaina ta diro da ita da almajira ba maraba tayi wani irin yunkonewa ta rame ashe bin mijinta da tayi ba arziki ya kaishi ba tara karuwai yake na yau daban na gobe daban kuma ita cin kaniyarta yake duk wani wahalansu itace ga ba abincin kirki, da ga karshe ta saci kud'inshi ta gudo.


Sossai shaati tayi musu kokari a gidan rasuwan nan itace kan komai har aka watse, bayan sati ta koma makaranta shima ya koma wajen aikinshi inda sukayi da mama yaran zasu zauna wurinta kan aga abinda lokaci ze yi, yanzu arwa ta sakewa Isma'il sossai har baba take ce mishi yanzu, ya maida hankali sossai yanzu akan aikinshi sede karma da ake cewa ya hanashi sakat da sukuni.


10years later


Alhamdulillah Alhamdulillah, e zuwa yanzu shaati ta gama makaranta har ta sake haihuwa inda ta samu 'ya mace wacce taci suna saudah suna kiranta nasreen, tana aiki a hospital d'in da mama tayi aiki a daa wadda yanzu tayi retiree, arwa an zama en mata tana karatu nan kasu 200lvl inda take karantar Business Admin, yayinda yanzu su Yasmin ke waec, rayuwa juyi juyi yanzu isma'il ya maida kud'inshi sossai sede be da wani amfani tunda ba aure ze yi ba, kud'inshi kan 'ya'yanshi su arwa yake karewa wadda yanzu ze iya zuwa gidan shaati ya yini suna hiransu.


Se kuma taimakon marasa shi da marayu, massallatai da ya sa a gaba wadda har shareef da shima yanzu ya samu karin matsayi ke matukar jin kunyarshi, shima yara har hud'u ya kara a shekarun bayan zaheeda.


Kwance take tana waya cikin kashe murya da karairaya irin ta en mata masu ji da kyau da arziki, shigowar shaati yasa tayi saurin mikewa zaune tana kashe wayan tace "maami wani abin zanyi?" Harararta tayi tace "ban sani ba, ni kam wannan waya wannan waya Allah ya gani yana 'batan rai ya isheni haba? Shi Arham d'in ko gundura dake bayayi? To me ma kuke cewa haka In banda karya da abinda ba shine ba? Ni tashi maza kije ki ki gyaramin part d'in mahaifinku bani ma wayan nan".


Mikewa tayi tana tura baki ta bata wayan ta nufi side d'in Saif a natse ta gyareshi tas ta kunna bunner ta saka turaren wuta me bala'in kamshi ta fito, hawa saman maamin tayi Don amsan wayanta nan ta samu maamin na waya da paapinsu dake hanya, "ni Allah kazo ayi ayi auren nan ko na huta da baby kaza, baby kaza, baby kaza a gidan nan yanzu har fa su Yasmin babyn baby suke ce mata" dariya sossai Saif yake, ita karan kanta Arwa seda ta dara jin yadda maamin ke magana wai tana koikoyon muryanta bata san me paapi yace ba ta de ga maamin ta kashe wayan ta mike tana harararta ta shige d'aki.


Wayanta ta d'auka ta gangara da sauri seda ta tsaya kitchen taga abubuwan da aka had'awa Paapi ta d'ibi masa da miyan ganda ta wuce d'akinta nan ta baje taci ta koshi, dama tana da class 2 so direct shiryawa tayi ta fito hawa sama tayi ta samu maami ta fito wanka tana chanchad'a kwalliya a ranta Tace ita matan nan bata girma da tarairayar miji in ni nayi kuma a ga laifina.


Murmushi ta saki tana cewa "maami na tafi school" Tace "se kin dawo" Tace "maami motana fuel d'inshi saura kad'an" kallonta shaati tayi ta girgiza kai tana cewa "duba bedside d'ina ki d'au 5k" d'auka tayi tayi godiya ta fice ba wai bata da kud'in da ya ci uban 5k d'in a account d'inta bane kawai dae kud'in maamin nan dae shi take so, fita tayi ta ja wata jar camrynta XLE ta fice daga gidan.


Bata jima da fita ba motan Saif yayi horn aka bud'e mai ya zama wani babban mutum ya d'an tara gemu wadda ya had'e da kasumbarshi irin babban mutum nan, a natse ya nufi cikin gidan Ai daga parlorn kasa yaji qurratul ayn d'in nashi ta rungumeshi kar'banta yayi yana cewa "ashhhh se ki karyani hayatee" Tace "Barka da zuwa roohul na'eem ka san yadda nayi kewanka kuwa? Muje In tayaka wanka kazo ka ci abinci kan yaran nan naka fitinannu su dawo" dariya yayi yana binta a baya yace "Yauwa d'azu munyi magana da Arham yace a baki hakuri kan ya diro kasan wani project ne ya ajiyeshi but yana dirowa ze d'auke miki d'iyar taki ki huta tunda kin gaji da ita" tana ta'be baki tace "kullum project kullum project yaron nan tunda ya sa kafa ya tafi degree, masters ya gama ya ci gaba da musu aiki nan ba yadda ba'ayi ba yaki dawowa In na gaji ze dawo ya iske babyn tashi tayi aure tunda feeder yake bata".


Saif na dariyan magananta suka shige d'akin shi, Allahu akbar hajja ta tafi a lokacin da burinta ya cika na ganin had'in kan 'ya'yanta yanzu zumunci ba ya su, cutar hassada ta mutu murus.


Inna tun tana saka ran dawowar zuby har ta hakura ta samu wani mijin tayi aure a nan cikin kauyen ta maida hankalinta gurin kuma neman yardar Allah da tuba a gareshi sbd wadda ta aura malamin musulunci ne kuma ya bata kaso mafi yawa cikin abinda ya samu yaranta shi yasa kullum take tubarwa Allah, yanzu har ta kuma haihuwa 'ya mace ta sa mata Aisha.
Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!


Anan na kawo karshen wannan littafin nawa na RUWAN SAMA..... Ina fatan abinda na rubuta daidai Allah ubangiji ya bani ladanshi abinda nayi kuskure kuma Allah ubangiji ya yafemin, Allah ya sa duk wadda ya karanta littafin nan ya karu da abu ko min kankantanshi.

Post a Comment for "RUWAN SAMA COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...