Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RIKITACCEN AL'AMARI COMPLETE

RIKITACCEN AL'AMARI COMPLETE

- - Post a Comment

 RIKITACCEN AL'AMARI COMPLETE


*RIKITACCEN AL'AMARI*
       ~A short story~
~Inspired by true life events~

*Na Billy Ladan*

♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

        bintladan.blogspot.com

_Wannan littafin gaba dayansa sadaukarwane ga kawata,aminiyata *Hauwa Suleiman Muhammad*_
_U understand me moredan any1 else,uv always bn there for me. In U I find my second self. I am blessed to have u  both as my Mirror  as well as my Shadow because Mirrors dont lie n Shadows neva leave._

_Hia is a quote for u swidy_
_"A friend is someone who reaches out for your hand, and touches your heart.Thanks for touching me in more ways than one.I cherish your friendship!"_

Bintalo! Bintalo! Yarinyar da ake kira da Bintalo ta juyo a kufule tana kallon mai kiran nata, tsaki ta ja tareda cigaba da tafia. Da sauri daya yarinyar ta kamota tace "Bintalo kina jina ina kiranki amma kika wani basar dani,dadina dake dama wulakanta mutum, hararta Bintalo tayi sannan tace "ai Zulai ko meh na miki keh kika siya da kanki dan sau nawa nake cewa banson sunan nan amma kiga yanda kike wani daga murya kalan samarin anguwannan su raina ni ko? Dariya Zulai tayi sannan tace "toh meh kike so in kiraki, ni dai da Bintalo ns sanki kuma hakan zan cigaba ds kiranki" cikin bacin rai Bintalo tace "in bazaki kirani da Binta ba toh lalle baza mu shirya ba, duk sanda ki kara kirana da Bintalo wlhy bani bake" cikeda mamaki Zulai ta dubeta sannan ta dan dafata "toh naji Binta zan kiyaye" sai sannan ta dan saki ranta, karasaw sukayi bakin rafin suna yar hirarsu. Wasu 'yan samarine su biyu suka zo suka musu sallama, Zulaice kawai ta amsa yayinda Bintalo ta ja wani uban tsaki tareda kawar da kanta, daya daga cikin saurayin ne yace "Bintalo ai ko ba komai kya amsa sallamar mu ko, harara ta watso mai tareda nuna shi da dan yatsa sannan tace "Iliya wlhy ka fita harkana kaji na gayama in ba haka ba sai na ma abunda bazaka taba mantawa dani ba, wai ana soyayyar dolene, kuma anki a amsa sallamar naka sai kayi abunda zakayi" tsaki daya saurayin yaja tareda cewa "kai ma Ilu sai kace maye ka rasa wanda zaka likewa sai wannan mara kunyar, ni ban ma ga abun so a jikinta ba,yarinya in banda fitsara ba abunda ta sani" katsesa Bintalo tayi ta nunosa da yatsa shima "kaga Shamawilu ban kasa da kai sabida haka ka ja tsamin bakinka kayi shiru kafun inma rashin mutumci "nunota yayi shima da yatsa yace "ke nifa ba Ilu bane da zai juri rashin kunyarki yanxu sai in baki jikinki a nan" murguda mai baki tayi tareda harararsa sannan tace "sai kuma in tsaya ka jibgeni,kana tabani wallahi zamu kwashi yan kallo da kai" da kyar Zulai da Iliya suka shiga tsakaninsu dan dagaske Bintalo ta ci serious, in an barta hada kafada zatayi da Shamawilu, da kuwa ta kwashi na jaki dan daga gani Shamawila ba karamin kashi zai bata.+
Sai da suka bar wajen Zulai ta dubeta tace "Binta kenan yanxu ke da an barki dukansa zakiyi, koh kin manta waye Shamawilun, kuma ni banga aibun Iliya ba, saurayine san kowa kin wanda ya rasa, gashi da kwazo da arziki, duk garinnan ba wanda ya kaisa noma kuma yana samu sosai, duk matan kauyen nan shi suke so amma ke da ya likewa ko kallo bai isheki ba" Tashi Bintalo tayi ta dubi Zulai tace "haba Zulai, kalleni da kyau, dubi kirar da Allah ya mun" ta fada tana jujjua jiki, "ke sai yaushe zaki gane cewa kalata sam ba na kauye bane, dirin da Allah ya mun na matan manya ne, irin Alhazawan birnin nan shi yasa kika ga ban kula kowa a kauyennan dan in kinga nayi aure toh dan birni na aura wanda zai kaini can in rayu cikin dadi, in an ganni a kauyan nan toh ziyara ta kawoni in so samu ma in tafi da su inna can mu zauna baki daya zama na har abada" cikeda mamaki Zulai ke kallonta sannan tace "lalle Binta kinyi nisa amma sai dai ki sani duk yanda kika kai da kin nan ne tushenki bakida inda ya fishi har karshen rayuwarki tarihinki a like yake da wannan rugar, kuma ma abunda kike fadi ko a mafarki bn jin zai faru, wani dan birni zai shigo wannan kauyen tamu har ya aureki,gskia da kamar wuya" duk da maganar ya batawa Bintalo rai, murmushi tayi sannan tace "Zan baki mamaki Zulai dan wlhy ko ta halin yaya sai na auri mai kudi kuma inje Birni, ni kinga tafiyata" tashi itama Zulai tayi sukayi sallama kowa ya wuce gida amma zuciyar Zulai cike yake da mamakin kawar tata.

STORY CONTINUES BELOW

Ko da Bintalo ta dawo gida dakinta ta wuce ta cire kayanta ta daura zanin wanka ta fito ta wuce bakin rijiyar gidansu ta debo ruwa ta wuce ban daki ta yi wanka, kwalliya ta cancada sannan ta bude akwatinta ta ciro wani English gown tana murmushi tace "yau ranarka ta zo" bayan tasa ta dauki gyale ta daure kanta da shi sannan ta dan fesa turare, ba ko mayafi ta fito cikin gidan
Bata bi ta kan Innarta da ke tsintar shinkafa a tsakar gidan ba ta sa kafa zata fice, ji tayi innar tace "Ke Bintalo" juyowa tayi tareda dan bata fuska sannan tace "Inna meh? Kada kai Inna tayi sannan tace "bari in taso in zo in sameki toh tunda ke kika haifeni" tana yatsina fuska ta karaso inda Innarta take ta tsaya a kanta, "wai ke yaushe zakiyi hankaline Bintalo, mutane na girma suna hankali amma ke sam dada lalacewa kike,maza dauki dakuwar can ki kai bakin tasha nasan baza rasa masu siya ba ko ma samu kudin mai da zamuci shinkafar da shi, dan turo baki tayi dan gaba daya Inna ta rusa mata budget, duk wankan nan ace a daura mata talla, gaskia ina bazai yu ba, ai talla ba ajinta bane yanzu Inna ya kamata ta fahimci cewar ta fi karfin hakan yanzu. Bakin dankwalinta ta kunce ta ciro naira hamsin ta ajewa Inna tace "Ga wannan Juwairah ta siyo ni da inda zani bazan iya zuwa miki talla ba" tana gama fadin hakan ta sa kai ta fice, binta Inna tayi da kallo yayinda hawaye ya fara bin kuncinta. Wata yar yarinya yar kimanin shekara 6 ce ta shigo gidan hannunta dauke da karamin allo, ganin Inna tana hawaye ya sata saurin karasa ta sa hannu tana share mata kwallarta tana "Inna meh ya sameki kike kuka? Murmushi tayi tareda shafa kanta tace "ba kuka nake ba Juwaira,abune ya shiga mun idanu, tashi kije ki cire kayanki kiyi wanka kizo ki ci abinci" tashi tayi tayi yanda Innar tace sannan tazo ta zauna tana taya Innar tsintar shinkafa, Abbantane yayi sallama ya shigo ta tashi da saurinta ta karbi fartanyar da ke hannunsa tareda mai sannu da zuwa, tabarma ta dauko ta shimfida mai sannan ta debo mai ruwa mai sanyi a yar karamin cup ta kawo mai, karba yayi tareda shafa kanta yana mai sa mata albarka, ganin ya shanye tas ya sa ta karban kopin ta sake cikasa da ruwa ta kawo mai sannan ta koma ta cigaba da taya inna aiki.
Bintalo kuwa tun kan ta karasa bakin hanyar ta ji ana mata horn, cigaba da tafia tayi tana yar rangwadanta, jin horn in yayi yawa ya sata juyowa, numfashinta ne ya kusa daukewa ganin wata dankareriyar mota a gabanta ga saurayin da yake ciki ba karamin haduwa yayi ba, saukowa dan saurayin yayi tareda karasowa inda take "haba yar kyakkyawa,ya inata miki horn amma ko ki tsaya? Wani dadine ya ziyarci zuciyar Bintalo jin ya kirata da kyakkyawa, cikin rausaya murya tace " ai ban san dani kake ba" "toh yanzu kin sani" ya mayar mata sannan ya tambayi sunanta "Sunana Binta" ta bashi amsa, "ni kuma sunana Bashir, wani gida na zo nema kuma an mun kwatance tun a bakin hanya amma ganinki ya sa na mnta da abunda ya kawoni" Bintalo ji tayi kamar kanta ya fashe, murmushi ta danyi sannan ta dubesa tace "wani gida kenan kake nema? "Gidan Malam Sabitu" ya bata amsa, kallonsa tayi sannan tace "in bazaka damu ba sai muje in nuna ma" motar ya bude mata ta shiga sannan shima ya zaga ya shiga tana mai kwatance har suka iso. Kashe motar yayi sannan ya dubeta yace "in bazaki damu ba ki dan jirani yanxu zan fito sai in mai daki gida" "ba damuwa zan jiraka" ta fada sannan ya sauka ya shige gidan. Duk da yawan mutanen da ke zauren gidan suna jiran ganin wannan malamin, Bashir kai tsaye ya shiga cikin falon, Malam Sabitu na ganinsa yayi saurin sallaman wanda ke gabansa sannan suka shige wani daki. Sun kai kusan awa daya sannan suka fito, har bakin kofa Mallam Sabitu ya rakaso,hannu ya bashi sannan yace "toh Bashari a sauka lafia,kuma ka tabbata kana samun abunnan inji dan in fara aiki" "godia nake malam,kuma zan kokarta inyi yanda kace" cewar Bashir kafun ya karasa gun motarsa. Bintalo kuwa anji AC har an fara bacci dan a kunne ya bar motar,karar bude motar ne ya sata tashi taga Bashir ne ya dawo. Tada motar yayi ta hau mai kwatancen gidansu. Har kofar gida ya kawota, Juwairah da ke zaune kofar gidan da tray na dakuwa ta taso da murnarta ganin yarta a cikin hadaddiyar mota, Bashir ne ya kafeta da ido,juyawa Bintalo tayi dan ganin wa yake kallo taga Juwairah tsaye sai faman taba motar take, "ka santa ne? ya ji ta tambayesa wanda hakan ya sa shi dawowa daga duniyar da yaje, kai ya kada sannan yace "kama naga kunyi nasan duk yanda akayi kanwarki ce", murmushi tayi kada mai kai alamar eh sannan tace "nagode ni zan shiga gida" dan riko hannunta yayi yace "tafia zakiyi ki barni bayan ban gaji da kallonki ba", gyara zamarta tayi sannan tace "kayi hakuri akwai abunda zanyi a gida ne, dan so ta ke ta ja mai aji kar ya dauka bata da class. Jakar motarsa ya balle ya ciro wani karamin tecno da kudi bandir biyu yan dari biyu da yan hamsin ya miko mata nan kam batayi jan aji ba ta sa hannu ta karba tana godia "ki tabbata wayan ya zamto da carji kullum dan zan na kira muna waya kuma in na samu lokaci zan zo" cike da murna tayi shigewarta gida. Kudin ta zube gaban Inna tana gaya mata abunda ya faru, kada kai inna tayi sannan tace "Bintalo ina rabaki, kada son abun dunia ya rudeki kije ki fada a abunda bazaki iya cire kanki ba, in ba rashin hankali irin taki ba daga haduwarki da mutum sau daya ya dauki irin wannan kudi ya baki kuma sai ki yadda,ni dai dauke mun su daga gefena bn bukatarsu" tashi tayi cikin bacin rai ta kwashi kudinta tana guna guni tayi dakinta. Akwatinta ta bude ta zubasu yayinda take tunanin abubuwan da zata siya da su. Wayan da ya bata ne ya hau kara, cikin rawar jiki ta dauka suka gaisa tareda kara gode mai. Tun daga wannan rana kullum sai sunyi waya da Bashir inda ya gama tabbatar mata sonta yake kuma da aure kuma duk sanda ya sake zuwa zai zo har gida gaida Abba kan ya turo manyansa, ba karamin dadi hakan ya ma Bintalo ba dan ji take burinta ya gama cika.

Bintalo 'yace ta fari gun Malam Ja'afar da Suwaiba wanda suke kira Inna, su biyu suka haifa daga ita sai Juwairah bayan su Allah bai sake basu haihuwa ba. Suna nan zaune ne a kauyen Yimir. Mahaifinsu manomi ne dan shine sana'ar da maxauna wannan kauyen suka fi yi.
Bintalo na zaune wayarta ya hau kara sanin ba mai kiranta sai bashar ya sa tayi saurin dauka, "ki fito ina waje" shine abunda taji ya fada, wani tsalle tayi ta diro daga kan gadon ta daura zanin wankanta ta fice cikin sauri tayi tsakar gida,ruwan da ta gani a bokiti ta dauka ta fada toilet. Tana fitowa Juwairah ta dubeta tace "Adda Bintalo ruwan wankan inna ne fa na tara mata" "toh mara kunya nayi amfani da shi sai kizo ki daken" tura baki tayi ta nufi bakin rijiyar ta fara kokarin janyo wani duk da ba wani iyawa tayi ba, Inna da ke jinsu ne ta fito ta karbi gugan a hannunta tareda sa mata albarka.
Suna cin abinci Bintalo ta fito sai kamshe ake ta wucesu ta fice,binta inna tayi da ido yayinda take nema mata shiriyar Allah a zuciyanta.
Ranar Bashir bai bar anguwar ba hat saida suka gaisa da Abba ya gabatar da kansa a matsayin wanda yake neman auren Bintalo. Bayan ya tafi Abba ya kirata yana mata tambayoyi game da shi, sai sannan ya ji basu jima da haduwa da shi ba kuma ba mazaunin kauyen bane, shiru yayi sannan ya dubeta yace "Bintalo kin tabbata sonsa kike dan kar azo ayi abunda za aji kunya,gashi mu ba wani saninsa mukayi ba ko wani dan uwa nasa balle musan koh ya cancanci mu bashi aurenki, dan bata rai tayi sannan tace " ai Abba tunda muna son junanmu ai shikenan kuma, yace zai turo yan uwan nasa kuyi magana" shiru yayi sannan yace "Bintalo bawai kinki nake ba son da nake miki da damuwar da nayi dake shiyasa kika ga na fadi hakan, aure dole sai da bincike baxai yu haka kawai ban san waye shi in dauki 'yata in bashi ba, amma zan jira zuwan 'yan uwan nasa daga nan sai in dada bincika inji ko ya cancanci in bashi aurenki,tashi ki je. Ta shi tayi ta wuce daki ta ciro wayarta ta kira Bashir ta gaya mai yanda sukayi da Abba inda ya kwantar mata da hankali tareda cewa zai turo manyansa a kwanan nan. Cike da Murna ta aje wayar.

Sati daya da wayarsu manyan Bashir suka zo harda sadakinsu, duk da Abba bai so hakan ba dole ya sa ya karba ganin Bintalo ta nace dan har da kukarta da cewa in ba a aura mata shi ba zata kashe kanta ko ta shiga dunia. Sosai ta bawa iyayen nata mamaki cikin bacin rai Abba ya tara jama'a a ranar aka daura auren, tana zaune a daki ya hau kiranta ta fito ta zauna a dan gefensa "Bintalo dukkan gata da iyaye ke wa yaransa nida innarku mun muku amma ke abunda zaki saka mana dashi kenan,yau kin nuna mana bamu isa da ke ba, tunda kin zabi bare damu iyayenki sabida san abin dunia naki sai kije, bazamu miki baki ba amma ki sani duk abunda ya biyo baya a auren nan kiyi kuka da kanki kuma koh a yau aurenki zai mutu kar ki yadda ki dawo gidannan, ga sadakinki nan ki dauka kije suna can suna jiranki. Tana hawaye ta koma daki ta dauki dan abunda ta tattara ta fito, durkushewa tayi gaban iyayen nata tace ku yafemun Abba,gaba dayansu ba wanda ya tanka hakan ya sa ta tashi ta fice suka dau hanya.

*RIKITACCEN AL'AMARI*
~A short story~
~Inspired by true life events~

*Na Billy Ladan*

♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*
bintladan.blogspot.com

Tunda Bintalo ta tafi Birni bata sake dawowa ba sai bayan shekara. Inna na zaune tsakar gida tana yi wa Juwairah kitso kawai taji Juwairah ta kwace kanta ta hau ihun "Adda Oyoyo" dago kanta tayi taga lalle kuwa Bintalon ce, rike da hannun Juwairah ta karaso ta zauna a gefen Innar tasu, hawaye ta fara, Inna kawar da kanta tayi tareda ajiyar zuci sannan tace "halan ya sako ki ko? Kai ta kada alamar a'a "nayi kewarku ne Inna,kuma dalilin da ya ban waiwayeku ba shine tun bayan auren aka mai transfer muka bar kasar sai shekaran jiya muka dawo shine nace bari inzo in dubaku" "toh ai kin kyauta Bintalo,ya shi mijin naki? "Yana nan kalau ya ma ce a gaidaku, aikine ya mai yawa da munzo tare,ga can ma sakonku daga wajensa" waya tayi sai ga driver da suka zo ya fara shigo da kaya niki niki, su dai bin kayan kawai suke da ido ganin yawarsa. Ana kan shigo da kayan Abba yayi sallama Juwairah ta tashi tayi saurin karban kayan da ke hannunsa, ba karamin mamaki yayi ba ganin Bintalo yace "wa nake gani kamar Bintalo" "nice Abba" ta bashi amsa sannan ta tashi ta karasa inda yake ta gaidasa cikin girmamawa, a zuciyansu sunace lalle aure ya gyara Bintalo. Ko da Inna ta nuna mai kayan baiyi wani murna ba, ya dai yi godia dan kar Bintalo taji wani iri dan sam shi bai yadda da Bashir ba, haka kawai zuciyansa bai daukesa ba.+
Juwairah ce ta shaida mata Zulai tayi aure kuma Iliya ta aura,duk da dai taji wani iri hakan bai hanata zuwa ba. Ba karamin mamaki ta sha ba da taje gidan Zulai kai kace a Birni take dan haduwarsa. Cikin jin kunyar juna suka amsa, hakuri Zulai ta bata ita kuwa ta nuna mata hakan ba komai bane sai gashi sun zage suna hirar bayan rabuwa.

Sati daya tayi ta fara shirin komawa. Suna zaune da Inna tayi gyaran murya tace "Inna dama wai ina cewa ko zan tafi da Juwairah ne can Maidugurin dan in sata a makaranta" wani tsalle Juwairah tayi dan ba abunda take so kamar tayi boko, Inna kuwa cewa tayi "Bintalo a bar wannan maganar dan bazata yiwu ba, ba inda Juwairah zata,ganinta na debemun kewa sannan in ta tafi wa zai na mun yan aikace aikace da talle da sauran aikan? "Inna zan nemo miki yar aiki amma dan Allah ki bari na tafi da ita, tunda itama tana da burin yin karatun sai kiga wataran anci amfanin karatun nata" cewar Bintalo
"Bintalo ni dai nace ba inda Juwairah zata kuma abbanku ma ba yadda zaiyi ba" jan bakinta tayi shiru yayinda Juwairah murna ya koma ciki. Tashi tayi ta shige dakinsu tareda tura kofarta, wayanta ta dauko ta kira bashir bugu daya ya dauka, ko gaisawa basu yi ba tace "Bashir su Inna fa inaga bazasu yadda in zo da Juwairah ba, dan ko maganar bata son ji" daga daya bangaren Bashir yace "ke dai ki cigaba da shiri kuma ki bani nan da gobe zan baki mamaki,Juwairah kaman ta zo Maiduguri" da murnanta ta aje wayar.

Ai kuwa ya bata mamakin dan ranar da zata tafi tareda Juwairah ta tafi, Juwairah na kuka su Inna nayi haka suka rabu, su dai sun rasa gane ta yanda akayi har suka yadda aka tafi da juwairah dan sam zuciyarsu bata son hakan amma bakinsu ya kasa furta hakan.

*BAYAN SHEKARU GOMA SHA BIYAR*

Yan mata ne biyu zaune suna nazarin wani littafi, daya daga cikinsu ta ce "Juwairah nikam kinga tafiyata da alama Nasir ba zuwa zaiyi ba" Juwairah ta tashi itama tareda dauka jakarta tace "Ai Meelat nima tafiya zanyi bn ji zan cigaba da jiransa ba, in yaso ya sameni a gida mu karasa dama supervisor nawa yayi tafia kinga kan ya dawo zan kokarta in gama" horn da suka jine ya tabbatar musu da zuwanshi, ko ta kanshi Juwairah bata bi ba ta ja hannun Meelat suka fara tafiya, da sauri ya sha gabansu tareda rike kunnuwansa yace "Hayati am sorry wlhy umma na kai anguwa kuma taki barina in dawo dole sai da na jirata" Meelat ce ta dubeta tace "A mai uxuri tunda ya bada excuse,amma Nasir a kiyaye dan a kan Bestyna muna iya batawa" dariya suka yi duka sannan suka koma gun motarsa ya jasu suka bar cikin University.
Sai da suka aje Meelat a gida sannan suka dau hanyar gidansu Juwairah da ke nan GRA, suna isa yayi horn mai gadi ya bude musu suka shigo, har kofan da zai sadata da cikin gidan ya kawota sannan suka tsaya suna hirarsu ta masoya, sai da suka shafi kusan awa sannan ya fito ya zagayo ya bude mata ta sauko suka hau daukan hoto, sai da sukayi kusan kala goma sannan ya taka mata har bakin kofar, suna sallamar karshe kofar palon ya budu amma sam basu lura ba sai da suka ji ance "ke Juwaira" gaba dayansu suka juyo taga Bashir tsaye rai bace, hanyar kofan ya nuna mata yace "maza ki shige" dan turo baki tayi sannan ta bi ta gefensa ta shige. Nasir kuwa gaishesa yayi, maimakon ya amsa sai ma harara da ya samu tareda jan wani uban tsaki ya yi banging kofar a kan fuskar Nasir. Cikin sanyin jiki ya koma ya shiga motarsa ya bar gidan.
STORY CONTINUES BELOW

Juwairah na shiga ta haye sama bata ko gaida Bintalo da ke zaune falo tana kallo ba, binta Bintalo tayi da ido bai jima ba sai ga Bashir shima ya shigo rai bace ya shige dakinsa, tabe baki tayi ta maida hankalinta gun film da take kallo dan inda sabo ta saba da wannan halin nasu.
Juwairah na shiga dakinta ta sa ma key sannan ta fada toilet tayi wanka ta shirya cikin kananan kaya masu kyau da tsada ta haye gado. Jakarta ta jawo ta ciro wayanta ta kira Nasir, bugu daya ya dauka tareda cewa "Hayati" wani sanyi taji dan ga dukkan alamu ransa bai baci ba, "na'am Habibi,ka isa gida lafia? "Lafia lau" ya bata amsa sai kuma sukayi shiru can tace "Habibi pls kana hakuri da uncle Bashir sam na kasa gane meh sa yake mun haka" murmushi yayi wanda har sai da taji sautinsa sannan taji yace "ai Hayati na saba, ni dai kawai na kasa gane mehsa ya tsaneni,sam baya son ganin mu tare, ni wlhy da ba dun yarki yake aure ba ko da sai ince ko wani cousin nakine dan yanda yake kamar sonki yake"
"Haba Habibi ya zaka fadi hakan, ai kasan hakan ba mai yuwa bane kuma bazai ma fara ba,its just dat he's ova protective dts ol" ta maida mishi, "ok,since u say so,yanxu yaushe zamu hadu mu karasa project in? "U can later at nyt if u ok with it" "anything for u Hayati,so u shld xpct me", sun dan taba hira irin ta masoya sannan suka aje wayar.

Da yamma bayan ta idar da sallar magrib ta wuce kitchen ta hada ma Nasir favorite drink nasa tasa a fridge sannan ta dawo daki tayi wanka ta shirya cikin wani English gown,tana gyara parking na gashinta kol nasa ya shigo tana dagawa ya shaida mata ya iso, karasa shirin tayi sannan ta yafa karamin gyale ta dauki system nata da wasu files ta fita. Ba karamin dadi taji ba ganin ba kowa a falon, juice in ta dauko sannan ta fice zuwa inda suka saba zama. Kai tsaye suka fara aikin project natan sunayi suna yar hirarsu, dayake Nasir ya kware a fanni abunda take so a mata bai dau lokaci ba ya gama, aje kanta tayi a kafadarsa tareda cewa "Habibi dnt knw wat i wl hv done wtout u,I luv u so very much" dago fuskarta yayi yana kallonta ido cikin ido yace "i luv u more Hayati,just promise me bazaki taba barina ba" murmushi ta mishi tareda gyada kai, zata budi baki tayi magana taji muryan Bashir yana "Su waye a cikin duhun nan" yar gajeriyar tsaki taja a ranta tana kara jin haushin wannan matsi da yake mata, har ya karaso cikin garden in bawanda ya tanka mai, Nasir ne ya dan russuna ya gaida shi ya amsa ba yabo babu fallasa sannan ya kai dubansa ga Juwairah da ta hade giran sama da na kasa yace "baki ji tambayar da na miki bane? "Assignment muke" ta bashi amsa a gajarce "toh maza ku karasa ki shigo dan zan rufe kofa" ganin bata tanka mai ba sai ma system nata da ta bude ya sa shi barin garden in cikin bacin rai. Yana fita Juwairah ta ja wani dogon tsaki, Nasir ya dubeta yace "D guy totally hates me, n if ta hannunsa zan nemi aurenki toh na tabbata baxai taba ban ba, ji fa yanda ya amsa gaisuwana, gaskia da wani abun a kasa imma ya na son hadaki da wani ko kuma sonki yake" Hannu Juwairah ta daga mai tace "Habibi in kai ma bata mun rai zakayi toh in shiga gida,wannan wace irin magana kake mara dadin ji,mijin yayata ne fa taya zakayi tunanin zai soni,gaskia kar ka sake mun irin wannan maganar, kuma da kake cewa he hates u n bazai baka aurena ba his opinion doesn't matter n he dsnt get to decide who i should or should not date bayida wannan right in dan shi ba ubana bane so ka ma daina tada hankalinka a kanshi" shidai Nasir shiru yayi dan tabbas jikinsa na gaya mai akwai wani abu a kasa dan irin wannan tsarewa da mijin yarta ke mata ba daga nan ba.

A haka har suka kare karatunsu da suke a nan jami'ar university of Maiduguri inda suka karanta masscomm. Ranar dinner/award nasu tun wajen karfe 4 ta shirya ta zauna jiran Nasir, kol nasa na shiga ta sake duba kanta a madubi sannan ta fito.
Tunda Bashir ya ji motsinta hankalinsa ya bar gun Bintalo da ke mai hira, jin ya daina tanka mata ya sa ta dago tareda bin inda yake kallo, ganin Juwairah tsaye ya sata tashi ta karasa inda take,rungumarta tayi tareda cewa "Masha Allah sis, kin ganki kuwa,ba karamin kyau kika yi ba,tsaya in dauko wayana in daukeki hoto" shigewa dakinta tayi yayinda Juwairah ta hau charting da Meelat,dagowar da zatayi taga Bashir ya kafeta da ido,wani haushi taji a ranta tayi saurin kawar da kanta "u luk stunning" taji ya fada,ba tareda ta juyo ba tace "tnxs", sai da Bintalo tayita daukanta hoto sannan ta rakota har waje inda ta hadasu da Nasir tayita daukarsu.
Kan su iso hall in already har an dan taru, suna shiga Meelat ta dago musu hannu suka karaso dan table daya suke.

Sunci sun sha sannan suka yi hotuna dan dukansu ba gwanayen rawa bane. Sun samu award kala kala a ciki harda best couple dan sosai suke burge mutane da salon soyayyarsu. Sai wajajen shida aka tashi sabida kar su shiga lokacin sallah.
Kasancewar date na Meelat ya tafi kan a tashi dole sai da suka biya suka ajeta sannan suka dau hanyar gida. Ta kofar gidansu Nasir suka wuce ya juyo ya kalleta yace "Hayati kinki zuwa ki gaida mum gashi kullum ke sai ta tambayeki" "Habibi ba wai kin zuwa nake ba wlhy ni kunyanta nakeji sosai,amma muje yanxu in gaidata" "ai basa gari sai dai in ni zaki taya hira" ya fada yana kinne mata ido harara ta watsa mai irin na wasan nan,hannu ya sa ya dan lakushi hancinta yace "u luk cute wen u do dat" suna hirarsu ta masoya har suka iso gidan. Kamar kullum har bakin kofar ya kaita sannan suka tsaya suna fuskantar juna dan yin sallama, wani zobe ya ciro a aljihunsa ya dan dago left hand nata ya sa mata a ring finger inta, dagowa tayi ta kallesa cike da tsantsar so tace "tnk u so much Habibi,its really beutiful" murmushi yayi sannan yace "i knw u"ll luv it dama" "i rilly do" ta bashi amsa cike da jindadin kyautar da ya mata, dago hannun yayi dan yayi kissing in ring in amma kafun ma bakinsa ya sauka akai yaji an daka mai tsawa da ya razanasu baki daya, juyowa sukayi sukaga Bashir tsaye idonsa yayi ja dan bacin rai,karasowa yayi ya dubi Juwairah cikin tsawa yace "maza wuce ki shiga" ganin yanda ransa ya baci yasa ta yi hanyar shiga amma bata karasa ciki ba ta tsaya jin abunda zai fadawa Nasir, nunosa yayi da yatsa yace "Nasir kowa kake da suna,in kana son kanka da lafiya toh ka nisanta kanka daga Juwairah in kuma ba haka ba i wil mk sure na batar da kai daga dunia" cike da mamaki Nasir ke kallonsa yayinda zuciyan Juwairah ya baci ainun taji kaman ta fito ta shake shi. Wani murmushi Nasir yayi sannan yace "kai baka isa ka rabani da ita ba kuma kasan irin kalamun da zaka na fada dan wlhy ko ciwon kai nayi sai ka ji ka gaban hukuma kan wannan furucin naka" yana gama fadin hakan ya shiga motarsa ya bar gidan.

Juwairah kuwa dakinta ta wuce tana kuka,tabbas zamanta gidan nan ya kare dan bazata zauna a rabata da masoyinta ba zata wuce gidansu Nasir ta kwana in yaso da sassafe su dauki hanyar kauyensu dan ya gana da iyayenta. Kayanta ta hau tattarawa tana zubasu a jaka,sai da ta tabbatar kowa yayi bacci sannan ta fito cikin sanda tayi hanyar waje.

~~~~
Kamar a mafarki taji ana tadata a mafarki cikin sauri, bude idonta tayi a hankali sannan ta dubi Bintalo da duk gaba daya a rude take, "tashi maxa Bintalo,zama bai samemu ba,yi maza ki dauki abunda zaki iya dauka barin kasar zamuyi" ganin bata tashi ba ya sata maimaita abunda ta fada sannan ta fice, binta Juwaira tayi ta ido yayinda take mamakin abunda ya firgita yayar tata har take cewa barin gidan zasuyi amma babban mamakinta na ga ganin kanta da tayi kwance a dakinta, koh dai mafarki tayi ne akan cewa ta kwashi kayanta ta gudu zuwa gidansu Nasir, kai ba mafarki bane ta bawa kanta amsa, juyowa tayi taga jakar da ta fita dashi nan ta gaskata hakan, tabbas ta dauki jakar ta fita amma bayan shi bata tuna komai ba. Ganin tunanin na neman haddasa mata ciwon kai ya sata tashi ta fada toilet tana fitowa taga Bintalo zaune akan gadonta tana ganinta ta taso tace "Juwairah baki shirya ba? Batareda ta kalleta ba tace "ni Adda nagaji da wannan tafiye tafiyen mara dalili,kuyi tafiyarku kawai ni zan koma kauye gun su Inna" juyawa Bintalo tayi cikin bacin rai ta bar dakin, bai jimaba sai ga bashir ya shigo. Da yake ta bawa kofar baya bata ma ji shigowarshi ba, ji tayi kamar an feso mata abu, kafun ma ta juya ta ga ko wayene jiri ya debeta ta fadi a gun.

*RIKITACCEN AL'AMARI*
       ~A short story~
~Inspired by true life events~

*Na Billy Ladan*

♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

*Dedicated to Hauwa Suleiman Muhammad*
     
bintladan.blogspot.com

A hankali ta bude idonta ta dubi inda take ta ga lalle cikin jirgine, runtse idonta tayi yayinda hawaye masu zafi suka fara gangarowa, Bintalo ce ta aje mujallar da ke hannunta tareda juyowa taga Juwairah na hawaye ,hannu ta sa ta dan tabata tareda fara mata magana a kasa kasa "Juwairah dan Allah ki bar kukan nan,kinga har mutane sun fara kallonmu, kiyi hakuri ki tsaida hawayenki har mu isa masaukinmu", hannu tasa ta share hawayenta yayinda take jin bakin cikin rabata da masoyinta da akayi dan taji a ranta sun rabu kenan. Jirginsu na sauka suka tari cab Bashir ya bashi address da zai kaisu, sai da suka shiga cikin gari taga posters sannan ta gane ashe Sudan suka zo. Har suka isa gidan bata tanka musu ba, akwatinta ta dauka ta wuce cikin gidan. Yanayin gidan exactly irin nasu na Nigeria ne hatta furnitures in iri daya. Sama Juwairah ta hau dan ko ba a gaya mata ba side nata kenan, tunda ta shiga ta kulle kanta a daki ta hau kuka sai da tayi mai isarta sannan ta jawo jakarta dan dauko wayarta, ganin wayan baya ciki ya sata sauka dan tambayar Bintalo, zaune ta samesu suna yar hiransu bata bi ta kan Bashir da ya kafeta da ido ba tace "Adda ina wayata? Kallon Bashir tayi ya dan kashe mata ido sannan ta maida kallonta ga Juwairah ta ce "ai garin sauri wlhy bn ma tuna na dauka miki ba", "bari yanxu in fita in nemo miki wani" cewar Bashir, "ban bukata" Juwairah ta mayar mai "kuma am not staying,am going back to Nigeria as soon as possible zan koma gun su Inna yafi mun da zaman da nake daku, u ppl r very selfish baku damu da kowa ba sai kanku kuka sani, me nayi muku da kuke son azabtar da zuciyata, kun rabani da mutanen da nakeso kun kawoni nan inda ban san kowa ba, toh wlhy ku sani bazan yi dare biyu a garinnan ba,ko kunki ko kun so am living" tana gama fadin haka ta juya ta hau sama, Bashir ne ya taso dan bin bayanta Bintalo ta rikosa tareda cewa "barta tukun, kai dai je ka nemo wayar na san meh zance mata. Tashi yayi ya fita bai jima ba sai gashi ya shigo da ledoji a hannunsa, aje mata yayi a gefenta sannan ya shige dakinsu. Bude ledan tayi taga takeaways ne da kuma waya da simcard. Takeaway daya ta dauka da drink ta haura sama da shi. Sai da tayi knocking dakin kusan sau uku sannan Juwairah ta zo ta bude mata tareda bata hanya ta shige sannan ta rufo kofar. Dan nesa da Bintalo ta zauna tareda kawar da kanta, "ga abinci da wayan na kawo miki Juwairah,nasan tabbas bamu kyauta ba but muna da dalili mai karfi na yin hakan, zamanmu a can ba karamin hatsari yake da ba dan ana farautar ran Bashir kuma hakan na nufin muma muna cikin hatsari dan kinga har gida an shigo, da ba dun Allah ya tsare ba da duk mun zama tarihi, kar ki manta halacci irin na Bashir, kiyi duba da sauyin rayuwa da kika samu a dalilinsa, da ba danshi ba da baki kai matsayin da kike a yau ba kuma yana kyautatawa iyayenki, ai ya cancanci ki sadaukar da rayuwanki na can saboda ceto rayuwarsa" ganin hawaye fuskar Juwairah ya sata murmushi dan tasan tayi nasara,tashi tayi ta dubeta tace "ki daure ki ci abincin sannan kiyi tunani akan abunda na fada, in kinga tafiyar shine yafi miki toh bazamu hanaki ba dan already ma har ya fara zancen karbo result naki ya nema miki aiki anan,so zabi na gareki" tana gama fadin hakan ta fita tareda rufo mata kofar. Tashi Juwairah tayi ta hada wayar ta sa chargi dan ta kagu taji daga Nasir da kuma Meelat. Abincin ta jawo ta fara ci,sai da tayi nak sannan ta rufe sauran ta sauko dan shan ruwa.
Bintalo na ganinta tama Bashir ido suka bar hirar da suke, wucewa tayi ta bude fridge dake gefen dining na palon ta sha ruwa sannan ta dawo parlor inda suke zaune itama ta nemi waje a kasa ta zauna.
Shiru duka sukayi sai can Juwairah ta dago tace "uncle pls kayi hakuri a bisa abunda ya faru, insha Allah bazai sake faruwa ba" murmushi yayi sannan yace "bakomai Juwairah,kuma insha Allah muddun komai yayi normal zamu koma gida but for d mean time zamu zauna nan, zanyi magana da H.O.D inku ya turo mun to whom it may concern naki sai in nema miki aiki anan" godia tayi sannan ta tashi ta shige ciki yayinda Bashir da Bintalo suka kalli juna suka sakewa juna murmushi, ko me murmushin ke nufi oho.+

STORY CONTINUES BELOW

Sati daya da zuwansu aka nema mata aiki a kampanin jaridar Sudan Times. Ranar da zata fara fita da wuri ta tashi tayi ayyukan gidan sannan tayi wanka ta shirya cikin Arabian gown tayi rolling ta fito sai kamshi take, a parlor ta taradda su Bashir suna breakfast itama ta karasa ta zauna tayi breakfast. Tareda Bashir suka fita, sai da ya tabbatar ta isa har cikin company in sannan ya wuce yin interview.
Bata sha wuya ba wajen samun office na managern, inda bayan ya mata wasu yan tambayoyi ya ce ta taso ta biyosa, wani office ya kaita wanda yake kunshe da kujeru biyu sai wata yar kofa, kujeran da ke kusa da kofan ya nuna mata sannan yace nan ne wajen zamanta and office da ke bayanta na oganta ne,she wil b working as his secretary,godia ta mai sannan ta zauna tareda bude computer da ke gabanta ta hau yar tabe tabe.
~~~
"Luk Juwi ma dream is about to come tru tunda ta samu aiki i wil get to chat more often" "Huh🙄 Riya,u r just like her u ppl r no fun,u r boring as hell" "wat eva" cewar Riya sannan tace "ya jima we didn't take over,so am gonna tk ova and have some fun" "Suit urself,nima zan samu time ina soon" cewar Juwi.
~~~

Kamar a mafarki taji ana dan bugata ta tashi a dan raxane,murza idonta tayi tareda mikewa tsaye tana kallon yarinyar da ke gabanta,miko mata hannu yarinyar tayi tace "am Laila,u must be Juwairah" kai ta gyada tareda mika mata hannu sukayi sallama "slipin on ur firstday,bad nyt i guess" laila ta fada tana kallonta, "believe me ban san lokacin da barci ya daukeni ba n i hardly do dat" Juwairah ta mayar mata kada kai Laila tayi sannan tace "am ur assistant, so i wil go sit while we wait for d boss,just let me knw if u nid anything, amma ga shawara "dnt get close to him cos he has eyes for beutiful women n u r undeniably beutiful" murmushi ta mata sannan tace "i wunt n tanx" sannan duk suka zauna
Idonta na kai kan screen na computer da ke gabanta taga chats birjik, duba tayi taga group ne, username in ta duba taga Riya, daga kafada tayi a zuciyanta tace maybe na old assistant in ne ta shiga mistakenly, fita tayi tareda jan wayanta ta hau kiran Nasir da Meelat amma kamar kullum duk a kashe suke,sake tura musu message tayi duka.

Sai wajen 8 Ogan nasu yazo suka tashi suka gaishesa, kallon Juwairah yayi tareda miko mata hannu yace "am Abdel" dagowa tayi ta gansa sannan ta kau da kanta,janye hannunsa yayi sannan yace "sorry i get it, i wil need coffee in d nxt 30 mins so see to it, ya fada sannan ya shige office. Tashi tayi ta karasa wajen Laila tace "wia do i get his coffee? Murmushi tayi sannan tace "ki zauna, d way it works is dat he orders u n u order me" murmushi tayi sannan ta mata godia ta koma ta zauna. Tana zama kol na Inna ya shigo,katsewa tayi sannan ta kirata, cike da murna suka gaisa take shaida mata aiki da ta samu inna ta tayata murna sosai, ganin Abdel da tayi tsaye kanta ya sa tayiwa Inna Sallama tareda tashi.
"Sit" yace da ita,zama tayi sannan ya miko mata wasu papers yace "type dem n send dem to d various mails", "Ok" sannan ta hau aiki. Ganin haryanxu yana tsaye a kanta ya sata dagowa taga ita yake kallo, suna hada ido ya mata murmushi itama ta mayar mai sannan ya juya ya shige office. Ajiyar zucia tayi sannan ta cigaba da aikin. Laila na dawowa ta karbi sakonsa ta shigar mai. Godia ya mata sannan ta juya ta fita batareda ta lura da mayataccen kallon da Abdel ke mata ba.

Sai wajen 11 ta gama,mika tayi tareda dan turo kirjinta waje tana dan jujjuyawa, tana bude idanunta ta saukesu akan na Abdel da ke kallonta har yana dan lashe baki, zumbur ta mike tareda dan kawar da kanta "am going out for breakfast,wanna come" "am ok" ta basa amsa, "anything i can bring for u? Ya sake tambaya "no tnx" ta amsa a gajarce dan his presence is mkn her uncomfortable gashi bata son kallon da yake mata. Yana fita tabi bayansa da harara sannan ta zauna tareda furzar da iskan gajia.

~~~
"See Riya i told u she's no fun,she's very boring, d guy is totally into her but she wunt even go out n hv breakfast with him"
"Juwi! D guy just wanna gets into her pants,dama abunda mazan yanxu suka fi kwarewa kenan, dey act like they care while jikinka kawai suke so,so let her be"
~~~

Sai four ta tashi suka fito itada Abdel har suka iso kofar da zata sadasu da waje, hannu yasa ya bude kofar tareda cewa "after u beautiful" murmushi ta mai sannan ta wuce shima ya bi bayanta. Ba karamin mamaki ba tayi ganin Bashir tsaye jikin motarsa fuskarsa a dan bace, karasowa tayi tareda gaishesa ya amsa "waye wancan" ya tambayeta tareda nuno Abdel dake kokarin tada motarsa, "my boss" ta mayar mishi "just b careful,i know guys like dem" ya fada cikeda damuwa a fuskarsa kai kawai ta gyada sannan suka bar wajen.

Suna isa gida ta ci abinci sannan ta wuce daki ta kwanta dan wani gajia da take ji, ba ita ta tashi ba sai wajen magrib tayi sauri ta fada toilet ta watsa ruwa tareda dauro alwala ta idar da magrib, sannan ta zauna ta dan yi kira'a har aka kira isha sannan ta gabatar ta tashi ta ciro kayan baccinta ta sa ta haura gado, addu'o'in kwanciya ta karanta sannan ta ja bargo ta kwanta.

~~~
Ptsss! Riya I dnt feel like sliping,i just wanna have sum fun n get drunk,am tired of bn stuck here,so lets go hv sum fun"
"Juwi it should be come with me n watch me have some fun, i wil rather read dan go with u"
"Arggh! U guys r no fun" nidai am going n d fun part is u have to come cos duk inda daya yaje d oda must come"
~~~

A hankali ta bude idonta ta bi inda take da kallo,zumbur ta mike ta zauna tana sake bin wurin da kallo,runtse idonta tayi sannan ta sake budesu taga tabbas ba mafarki take ba, bin jikinta tayi da kallo taga wasu shedanun kayane jikinta, tashi tayi ta fita daga wajen a hankali yayinda wasu maza suka hau binta, mamakine ya cikata ganin waje shiru ba alamun mota, tafia ta fara ko Allah zaisa ta samu mota, jin motsi a bayanta ya sata juyawa taga wasu maza biyu na binta, sauri ta fara yayinda suma suka kara daga kafa, gudu ta fara ganin suna shirin isota ai kuwa batayi nisa ba ta ji an rikota tareda toshe mata baki...........

*RIKITACCEN AL'AMARI*
       ~A short story~
~Inspired by true life events~

*Na Billy Ladan*

♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

*Dedicated to Hauwa Suleiman Muhammad*
        bintladan.blogspot.com

Ganin abunda suke shirin yi mata ya sata cizon hannun da ya rufe mata baki, a take kuwa ya saketa tareda yin baya, ihu ta saka na neman taimako, daya saurayin ya sake rufe mata baki, ji sukayi ance "ku saketa" ji tayi sun jefar da ita suka diba a guje, kankame jikinta tayi tana kuka mai cin rai, a hankali saurayin da ya ceceta ya karaso ya tsunkuya a gefenta tareda dan haska fuskanta, "kalli nan" taji ya fada, ba musu ta dago ta kallesa suka kwarawa juna idanu, dauke kansa yayi tareda cewa "tashi kizo" tashi tayi tana dan dar dar da shi ta bi bayansa har zuwa wajen motansa ya bude ya shiga, ganin tana tsaye ya sa shi cewa "in bazaki shiga ba zan ja motana in tafi, naga alama so kike su sake zuwa ko" jin haka ya sata zagayawa ta shiga, tada motar yayi sannan ya juyo yace "ina ne anguwarku" ba musu ta gaya mai ya ja motar suka bar wajen. A hankali yake tuki yayinda from tym to tym yake dan kallonta ganin sai sharar kwalla take, handki ya miko mata ta dago ta kallesa taga tukinsa kawai yake ta sa hannu ta karba, share hawayenta tayi sannan ta dubesa tace "pls in ka ga shagon da yake a bude inaso in siya kaya" wani kallo ya mata sannan ya maida hankalinsa ga tukinsa. Kaman bazai tanka ba kuma sai ya budi baki yace "dama wani iskancin ya sa kika fito haka" sabon hawayene ya fara bin kuncinta batareda ta dago ba tace "nasan bazaka taba yadda da abunda zan fada ma ba, no one wil even bliv me cos its crazy, wlhy wlhy ban san ya akayi naje wannan wurin ba,kuma kayan da ke jikina bn ma san ina na samo su ba, ni kasar nan ma duka duka sati na da zuwa i dnt even knw dis pls neither can i remember how i got here" ta karashe tana kuka, ji yayi jikinsa yayi sanyi yayinda wani sashin zuciyansa ya yarda da zancenta,amma toh wa ya kawota knan. Juyowa yayi yace "yanxu shaguna duk sun rufe but akwai coat ina a bayan motan ki sa hannu ki dauka its long enough to cover u up", hannu ta sa ta dauko ta sa a jikinta yayinda ta maida hankalinta kan titin. Jin ya tsaya ya sata dagowa taga suna kofar gidansu, juyowa tayi taga shima ita yake kallo " nagode sosai" ta furta mai har ta sa hannu zata bude ta juyo tace "can i have ur number so dat i can return ur coat" compliment card nashi ya miko mata tareda cewa "wen eva d nid arise u can kol me, but zancen coat na bar miki shi" godia ta sake mai sannan ta bude motar ta sauka ta nufi gate nasu ta bude sannan ta juyo taga har yanxu yana tsaye yana kallonta daga mai hannu tayi sannan ta shige, tana shiga shima ya tada motarsa ya bar wajen.+

Baiyi wani tafia sosai ba ya iso gida shima, knocking yayi wata budurwa ta zo ta bude tana ganinsa ta fada jikinsa tareda kankamesa "honey u scared me, ina ka shiga haka, n u wia not picking ma kols" kissing in lips nata yayi sannan ya riko hannunta yace "wlhy wani case ne na samu shine na zauna ina research bn san har lokaci yayi nisa ba, kuma na manta wayan a silent shi yasa kika ga ban dauka ba, ina Salim? "Yayi bacci ta basa amsa" kallonsa tayi tace "n ur coat? "Gv it to sum1 who nids it more dan me" ya bata amsa, baki bude ta kallesa sannan tace "oh no u didnt,u luv dat coat Honey" murmushi ya mata sannan yace "frgt abt d coat i miss u" ya fada tareda daukarta sukayi daki. Wanka yayi sannan ya fito ya shirya ya haye gado ya kwanta a gefenta, ganin harta fara bacci ya sashi ja musu bargo tareda rungumarta, yana rufe idonsa fuskar Juwairah ne ya zo mata, bude idonsa yayi tareda tashi ya zauna, yar tsaki yaja sannan ya koma ya kwanta.

Juwairah kuwa tana shiga ta wuce dakinta, compliment card in ta duba taga ansa Barrister Shureim Abdulkadir, murmushi tayi sannan ta bude purse nata dan sawa, zaro ido tayi ganin kudin da ke ciki basa nan,zazzage kayan ciki tayi amma ina ba kudi, wani receipt da bata san da shi ba ta daga taga receipt ne na kaya sunan jikin ta duba taga Juwi Azqi, baya tayi ta fada gado tareda rike kanta "wai meh ke faruwa da nine? Ta fada a ranta, tabbas dia is sumtn wrong, wayanta ta cire ta shiga net tayi searching sunan da ke jikin script in amma babu, a ranta tace " tabbas duk wanda ya fitar da ita daga gida shi ya mata wannan aikin, amma waye shi toh" ganin bata da amsar tambayar ya sa ta tashi ta dauro alwala tazo ta fara neman tsari a wajen Allah,akan sallayar bacci ya dauketa. Kiran salla ne ya tadata ta tashi ta shige toilet tayi alwala  ta tada sallah.

Ganin jiya ta danyi sammako ya sa ta danyi delay sai wajen 7:30 ta fito sanye da coat na Shureim dan ana dan sanyi, taxi ta tara ta gaya mai inda zata. Tana shiga office ta ga Laila har ta iso, karasawa wajenta tayi suka gaisa sannan ta nufi desk nata. Bata jima da zama ba Abdel ya shigo, hannu kawai ya daga musu ya shige office. Tashi Juwairah tayi ta bi bayansa ta tambayeshi ko akwai abunda yake bukata ya cemata babu sannan ta fito. Time na break nasa nayi ya fito ya dubi Juwairah yace "Juwairah" dagowa tayi tareda amsawa "dia is ds conference in Dubai dat i will b going in two days and i cant go wtout my secretary,so u in? Baki bude take kallonsa, it has always bn her dream to visit Dubai n its about to kom real,sai da ya sake magana tukunna ta gyada mai kai alamar eh, murmushi ya mata sannan yace "have laila book our flights den" sannan ya fice, tasowa Laila tayi ta rungumeta tace "am rily happy for u, av bn dia once u"ll really enjoy it n u"ll learn alot". Ranan da murnanta ta karasa gida dukda abun bai ma Bashir dadi ba dole ya barta ta tafi bayan kwana biyu kuwa suka daga zuwa Dubai.

Wani makeken hotel suka sauka kowa yayi dakinsa dan sai washe gari za fara, Juwairah na shiga dakinta ta yi tsalle ta fada kan gadon tana ta murnanta. Tashi tayi ta fada toilet tayi wanka sannan ta kira aka kawo mata abinci, ta ci ta kwanta
~~~~
" Riya remember dat day i went to the club, na hadu da wani balarabe AbdulRashid and guess wat he base in Dubai n inada compliment card nasa so am going out" "arrgh not again Juwi let d girl b,didn't u c her d last tym u tried sumtn stupid, ki tausaya mata mana,she has gone tru alot"
"We ol have gone tru hell so dnt lecture me cos am going anyways"
~~~~~

Da safe da ta tashi ta ji duk jikinta wani iri toilet ta fada tayi wanka sannan ta sa kaya, coat na Shureim ta dauko ta sa akan kayanta dan sosai take son coat in dan yana tuna mata da kyakkyawar fuskarshi da kamshin turarensa, fitowa tayi ta nufi cikin hotel in dan program in sai 10 zai fara, tana tafia a hankali tana kallon flowers da ke harabar hotel in ta hango Shureim tsaye shi kadai, murmushine ya bayyana a fuskarsa sannan ta karasa ta mai sallama, yana juyowa yayi sauri ganeta suka gaisa, "wat brings u here? Ya tambayeta "Conference" ta bashi amsa "N u? Kafun ya bata amsa taga wata tazo ta rungumesa tace "Honey sorry i kept u waiting" juyowa yayi ya kalli Juwairah da fuskarta ya dan canja yace "meet my wyf Khuraiba" sai sannan matarsa ta lura da ita ta miko mata hannu suka gaisa but she didn't miss to notice d coat Juwairah is wearing. Sallama ta musu ta juya ta tafi yayinda dukansu suka bita da kallo,Khuraiba ce ta juyo ta ga kallon da Shureim ke binta da shi ta ji zuciyanta ya buga, dan tabasa tayi ya juyo ya kalleta, "is dat ur coat?
"Yeah" ya bata amsa "we met in terrible situation had to giv it to her so dnt start forming tins in ur head" murmushi tayi tareda cewa "am not forming anything" "ok then,lets gt inside dnt want u catching cold" ya fada tareda mika mata hannu.

Juwairah kuwa tunda taji cewa Khuraiba matar Shureim ne ta rasa gane yanayin da ta shiga. Dakinta ta koma ta kwanta sai to 10 ta tashi ta sake shiri ta fito gun Abdel suka wuce gun conference in. Sai around 1 suka tashi suka fito yayinda Abdel ya tsaya yana gaisawa da mutane. Ji tayi an dafata tareda cewa "Juwairah" juyowa tayi dan ganin wanda ta tabatan, ido ta zaro ganin Meelat, rungumeta tayi sannan suka koma gefe suka zauna, sosai Meelat ta nuna bacin ranta gameda tafia da tayi ba sallama, nan ta labarta mata komai, ajiyar zucia tayi sannan tace "na fahimceki" "Nasir fa" ta tambayeta juyowa tayi ta mata kallon mamaki sannan tace "u min baki ji ba? " ji meh? Ta mayar mata riko hannunta tayi sannan tace "he was found dead d nyt u left,n duk binciken da akayi ba samu culprit in ba" tashi tayi tareda sa hannu ta rufe bakinta, hawayene ya fara bin kuncinta, da kyar Meelat ta kwantar mata da hankali sannan ta koma daki ta cigaba da kukañta, hankalinta ne ya koma gun Bashir,tabbas shi ya kasheshi dan yanxu it ol mks sense, ta san zaman da zatayi da su dan yanxu ta daina yarda dasu. A daddafe ta karasa sauran kwanakin dan duk labarin mutuwar saurayin nata ya canzata. Ranar da zasu koma tareda Meelat suka je airport, contact sukayi exchanging sannan suka rabu kowa da tunani daban daban a ransa.

*RIKITACCEN AL'AMARI*
       ~A short story~
~Inspired by true life events~

*Na Billy Ladan*

♻ *EXCLUSIVE WRITERS FORUM*

*Dedicated to Hauwa Suleiman Muhammad*

     
bintladan.blogspot.com

*For every year of my life, you've easily won the “Best Mother of the Year” Award. No one comes even within a mile of your winning ways. Wishing you a birthday as great as you r mum*

Suna isa suka tari cab kowa ya nufi gida, a parlor ta tadda su Bintalo, bayan sallamar da ta musu bata sake ce da su komai ba ta haura sama abunta. Kallon juna Bashir da Bintalo sukayi sannan duk suka tashi suka bi bayanta, rufe suka samu kofanta, duk buguwan da sukayi sam taki ta bude musu dan ji take zata iya shake Bashir in ta bude musu. Kukanta ta zauna ta sharba na rashin Nasir nata, a haka bacci ya dauketa. Ba ita ta farka ba sai wajen 9 na dare ta tashi da wani matsananci ciwon kai, da yake tana fashin sallah wanka tayi ta zo ta sha paracetamol ta kwanta.
Bugun kofarta da ake shi ya tayar da ita, take ciwon kan da ya addabeta ya dawo, tana dafa bango haka ta tashi ta bude kofar taga Bintalo da Bashir tsaye, kallonta suke da damuwa rubuce a fuskansu sannan Bintalo tace "Juwairah lafia kuwa, jiya kinzo ko magana baki mana ba kuma kika kulle kanki a daki, ko dai wani abu ya farune a can Dubai in? Murmushin karfin hali tayi sannan tace "kaina ne ke ciwo kaman zai fashe, har yanxu ma bai barni ba", " toh ai sai muje asibiti" cewar Bashir, Juwairah je tayi kaman ta shako shi taji dalilin da ya kashe mata Nasir amma ta dake tace "in na sha magani i wil b ok" , "toh za a kawo miki breakfast naki n i wil kol ur office to let them knw yau bazaki zo ba" murmushi kawai ta mai sannan ta rufo kofarta tana jin haushin rashin tambayarsa da batayi ba, amma ta san ya zatayi, dole sai ta hada mai trap da zai sa sa confessing, da wannan tunani ta fada toilet tayi wanka. Kafin ta fito har an kawo mata breakfast nata ta zauna taci sannan ta sake shan magani ta kwanta.+
Da yamma da ta shi ta nemi ciwon kan ta rasa hakan ya sa ta fito parlor, taya mamakin ganin Abdel zaune da Bintalo suna hira, karasawa tayi ta gaishesa shima ya mata sannu da jiki, fruits da ya kawo mata ya aje mata sannan ya musu sallama. Rakosa tayi har wajen motarsa sannan suka tsaya suna dan hira, Bashir ne ya kutso kai, da sauri yaje yayi parking ganin Juwairah tsaye da wani. Yana zuwa ko kallon Abdel be yi yace "Hiran meh kike keh da baki da lafia" kawar da kanta tayi sannan tace "He's ma boss, ya zo duba jikina ne" mika mai hannu Abdel yayi suka gaisa babu yabo babu fallasa sannan ya dubeta yace "ki maza ki shigo" ko sallama baiyi ma Abdel ba ya juya yayi cikin gida yayinda Juwairah taji kaman ta bisa ta shakesa har sai ya daina numfashi may be sannan zata huta da abunda take ji. Gyaran murya Abdel yayi yace "who is he? "Mijin yayatane" ta bashi amsa dan kada kai yayi sannan yace "y is he acting like a jealous boyfriend then? Murmushi tayi sannan tace " he's just over protective" "oh i gt it" ya fada sannan sukayi sallama ta koma ciki.

Sai da tayi hutun two days a gida sannan ta fara fita gun aikinta, sosai Laila tayi murnan ganinta dan tayi kewarta a yan kwanakin nan da bata zo ba. Yau da Abdel zai fita break dole ya jasu  suka fita duka.
Bata tashi da wuri ba kasancewar Abdel ya hadata da aiki, sai around five ta gama ta tashi ta kai mai papers in da ya bukata tareda mai sallama. Tashi shima yayi ya dauki coat da briefcase nasa tareda cewa "let me drop u" batayi musu ba dan tasan zata iya shan wahalan samun mota at dis tym.

Har cikin gida ya ajeta ta mai sallama tareda sauka a motar, taku biyu tayi taji ya kira sunanta ta tsaya tareda juyowa, kashe motarsa yayi ya sauko ya tako har inda take, yana dan sosa keya yace "am dia is ds birthday party am going by 7pm n i dnt have a date so i was hoping u wil b my date, i promise it wil just b for today, n dia wil b lots of journalist from dff org at d party so consider it as an opportunity to gt to meet new ppl" ya karashe yana kallonta, "i"ll b ready b4 seven then" ta bashi amsa, ba karamin dadi yaji ba jin ta fadi hakan, godia ya mata sannan yace zai zo by 7  dot ya dauketa.
STORY CONTINUES BELOW

Cikin wata hadaddiyar english gown ta fito tayi rolling da gyalen da ya shiga da kayan sai kamshi take, ganin ba kowa a parlor ya sata shiga dakin Bintalo ta tarar ba kowa. Wayanta ta ciro a purse nata ta tura mata text sannan ta fice. Tsaye ta ga Abdel yayi kyau cikin black suit shima sai kamshi yake, yana ganinta ya sake mata murmushi tareda bude mata motar "u luk stunning" ya fada "tnx, u luk handsome too" ta mayar mai kafun ya rufe mata kofar shima ya zagaya ya shiga ya jasu suka bar gidan
Wani hadadden gida suka shiga wanda harabarsa ke cike da motoci, parking Abdel yayi sannan suka sauko suka nufi ciki, suna shiga wani dan tsoho ya nufosa Abdel na ganinsa ya karasa suka rungumi juna, "Hapi Birthday Sir" ya fadawa tsohon nan tareda miko mai dan gift da ya kawo mai, juyowa yayi gun Juwairah yace "meet my mentor Sir Gabril" karasowa tayi tareda ma tsohon murmushi tace "hapi birthday Sir" murmushi ya mata sannan yace "just kol me Gabril dear, U r so beautiful" ya fada tareda kallon Abdel "Wia did u gt such a beauty queen? Dariya sukayi duka sannan ya jasu ya fara introducing insu wa mutanen da ke wajen. Juwairah da ta gaji da surutu ta danyi excusing kanta ta koma gefe ta dan tsaya tana kallon mutanen da ke rawa sam bata lura da Shureim da ya kafeta da idanu ba, Khuraiba kuwa jin tanata zuba baya tanka mata ya sata dagowa, bin inda yake kallo tayi da ido ta ga Juwairah yake kallo, gabantane yayi muguwar fadiwa yayinda taji wasu hawaye na kokarin zuba, juyawa tayi ta nufi restroom da ke parlorn.
Shureim kuwa da ya juyo bai ganta ba yayi tunanin ko tayi wani wajen ne,hakan yasa ya nufi inda Juwairah ke tsaye, sallama ya mata ta juyo ta amsa sannan suka sake wa juna murmushi, kan ma su fara wani hira taji muryar Abdel na cewa "dia u r,av bn lukin ol ova for u ashe ke kin buya a nan", murmushi  tayi sannan tace "Shureim dis ma boss Abdel" gaisawa sukayi sannan tayi excusing nasu ta wuce restroom itama. Tsaye ta ga Khuraiba gaban sink tana wanke fuskarta tayi saurin ganeta, karasawa inda take ta mata sallama ta amsa mata cikin sakin fuska sannan suka gaisa. Tare suka fito daga restroom in, Juwairah ce ta fara hango su Abdel ta ce "dia is ma date n ur husband" murmushi kawai Khuraiba ta mata sannan suka karasa wajensu suna yar hiransu. Basufi minti biyar da tsayuwa a wajen ba Juwairah ta fara hamma, cike da kulawa Abdel ya kalleta tareda cewa "Dear i nid to tk u home, kar gobe ince a rakani a ki zuwa cos i can c u r slipy" daria duk sukayi sannan suka musu sallama suka wuce.
Tunda suka karyo kwana suka hango Bashir tsaye ta san kuwa ita yake jira, kusa da shi Abdel yayi parking ya sauko ya bude mata motan, godia ta mai sannan ta wuce ta shiga tareda gaida Bashir, ganin Abdel ya nufo Bashir ya sata rakubewa a bayan gate dan taji meh zai gaya mai, mika mai hannu yayi, maimakon ya karba sai ya mai wani irin kallo tareda cewa "i knw guys like u so ka nesanta kanka da ita in ba haka ba wlhy sai na badda kai daga duniyan nan" murmushi Abdel yayi batareda ya kallesa ba ya juya ya shige motarsa ya bar wajen. Sauri Juwairah tayi ta shige ciki ta karasa dakinta ta hau safa da marwa, can dabara ya fado mata, ta san daren ranar da Bashir yayi threatening Nasir a daren ya mutu tabbas toh yau ma kashe Abdel zaiyi kaman yanda ya kashe Nasir, yau bata ga ta bacci ba, wani black hoody ta dauko da wando ta sa sannan ta sauka kasa ta rakube tana jira taga fitar Bashir dan ta samu ta bisa.
~~~~

Karar bugun kofarta ne ya tayar da ita, cike da mamaki ta dubi jikinta da kallo taga ba kayan da tasa bane jikinta, tunani tafara taya akayi ta dawo daki har ta canza kaya, jin sau buga kofar ake yasata tashi ta bude, Bintalo ta gani tsaye, gaisawa sukayi sannan tace "breakfast is ready" , kai ta kada sannan ta wuce tayi wanka tayi brush ta sauko suka karya yayinda hankalinta sam bai jikinta gashi ta kira numbar Abdel baya dauko kuma yau weekend ba aiki, da haka ta gama breakfast suka dawo parlor suka zauna, suna kallon film, Bashir ne ya fito daga dakinsu ta bisa da wani irin kallo har ya zo ya zauna. Remote ya dauka ya canza zuwa news inda a dai dai lokacin aka nuno hoton Abdel ana cewa an samu gawarsa a gidansa da safiyar Allahnan, ihu Juwairah ta saka tareda saka wani kuka, gaba daya kanta suka yo ganin yanda ta rude, ja da baya tayi tana nuno su da yatsa "kar ku yadda ku rabe ni,Cos i dnt trust u anymore ta na nuno Bashir, I knw u killed him, kai ka kasheshi kuma kai ka kashe masoyina Nasir, bazan taba yafe maka ba kuma sai ka fuskanci hukuma, i must c to it dt kaima ka fuskanci hukuncin rai da rai, kamar yanda ka kashesu haka kaima za kasheka" Bintalo ce ta rikota tana cewa "Juwairah ki nutsu, kin san meh kike fada kuwa, wani Nasir in ne na ya mutu, nan ta gaya mata abunda Meelat ta shaida mata, daga ita har Bashir ba karamin mamski sukayi ba, ganin mamakin da ke fuskar bashir ya sa Juwairah dariya tana nuno sa "wa zaka yaudara da wannan fuskar naka, ina sane da barazanar da ka samu akan cewa in basu daina rabata ba zaka kashesu shine ka bisu daya bayan daya ka kashe toh wlhy sai na kai kararka wa hukuma, tana gama fadin haka ta tashi tayi daki bai jima ba ta sauko sanye da hijabi tayi hanyar fita, bintalo ce ta taso dan tareta Bashir ya rikota tareda cewa "barta taje ni nasan ban taba kisa ba, kuma nasan yanda zan kare kaina.

Ta kwashi kusan awa biyu a station sannan ta dawo gida dan sun tabbatar mata zasuzo har gida suyi bincike, zaune ta samu Bintalo da Bashir, ko ta kansu bata bi ba ta haura sama

Da daddare tana dining taji ana buga kofa da sauri ta karasa ta bude dan tasan dole police inne, tana ganinsu ta saki wani murmushi sannan ta basu hanya suka shigo, waje ta nuna musu suka zauna, tashi tayi ta kira su bintalo sannan duk aka zauna, tambayoyi suka fara yiwa Bashir yana amsawa yayinda dayan ke jotting, suna gama mai mai tambayar ya juyo kan Juwairah yace "am madam kema akwai tambayar da zan miki" kirjinta ne ya buga kafun tace ok "according to d camera da ke gidan Abdel ya nunaki kin shiga gidan in a black hoody around 9 and baki bar gidan ba sai 4 na safe, ko zamu iya sanin meh kika je yi? Baki bude take kallon inspector in sannan tace "u must b mistaken, ban ma san gidansa ba taya za a yi inje" wayansa ya ciro yayi playing wani video ya miko mata, gabanta ne yayi muguwar fadiwa ganinta sanye da hoody da ta sa jiya tana shiga wani gida, dagowa tayi ta ma Bashir wani kallo dan tasan wannan aikinsa ne, hawayene ya fara bin kuncinta ta dubi inspector tace "wlhy ban san ya akayi naje ba, ku yarda dani" wani murmushi yayi tareda kallon abokin aikin nasa, juyowa yayi dan cigaba da mata tambayoyi wayat abokin aikinsa ya katsesa, alama ya mai yaje waje ya amsa sannan ya tashi ya fita, bai jima ba sai gashi ya shigo a gurguje, bakinsa ya kai kunnen Ogansa yana gaya mai wani abu, matsawa nayi nima dan jin meh yake fada "Sir yanxu aka kira daga hukumar bincike na Sudan da Nigeria, sunga case namu a kan news shine suka kira, dia has been similar killings in dis two places n investigation nasu yayi pointing at Juwairah dan Dubai harda hotonta suka turo, itace tayi kisan nan, dts y tayi saurin lakawa mijin yayarta dan kar a ganeta" dagowa yayi cikin tsananin bacin rai ya ciro bindigarsa ya sa a kan Juwairah tareda karanto mata Miranda Right "Juwairah, U r under arrest, u have d ryt to remain silent,anything u say can n will b used against u in d court of law, u hv d ryt to an attorney, if u can't afford an attorney, one will b provided for you............

_ayi hakuri da wannan zuwa bayan sallah,Allah ya sa muyi sallah lafia,love u ol😘_

*Billy Ladan*

*RIKITACCEN AL'AMARI*
       ~A short story~
~Inspired by true life events~

*Na Billy Ladan*

*Dedicated to Hauwa Suleiman Muhammad*
        bintladan.blogspot.com

_Hapi Sallah in arears to all readers of *RIKITACCEN AL'AMARI*,da fatan anyi sallah lafia,Allah ya maimaita mana,amin_

What? Juwaira ta fada cikin zare ido, "u must b mistaken,ni bn kashe kowa ba" police da ke rike da itane yace "ki adana kalamanki zaifi miki in kinyi shiru sabida duk abunda zai fito daga bakinki za a iya amfani da shi a kanki in anje kotu". Bashir ne ya matso yace "kiyi shiru juwaira, hakan zai fi miki, za muyi iya kokarinmu mu fitar da ke" hannunta ta daga ta wankesa da tagwayen mari sannan ta nunosa da yatsa "u wunt get away with dis" handcuff aka samata ganin tana kokarin yin fada da Bashir sannan sukayi waje da ita, Bintalo ce ta bi bayansu tana kuka, hannunta Juwairah ta rike tace "its k sis, ni nasan bnyi ba amma ki kula da kanki mijinki ba mutumin kirki bane a sannu zaki gane, sannan ki mun gata daya ki kira mun su inna, kar in mutu ban gansu ba" kafun ma Bintalo ta amsa mata polisawan sukayi waje da ita. Ba karamin mamaki tayi ba ganin mutane a bakin kofarsa wanda yawancinsu yan jaridane sai yan rahoton TV,da kyar aka tserar da ita daga tambayoyin da suke mata aka sata a mota
~~~
Shureim dawowarsa daga gun aiki knan ya shigo parlor, Salim na ganinsa ya yo wurinsa ya dagasa yana mai wasa, khuraiba ta taso ta mai sannu da zuwa sannan ta wuce ta dauko mai abinci tareda zuba mai, tashi yayi ya kunna TV tareda dauko remote sannan ya koma ya zauna, channel na news ya kai sannan ya debo chokalin abinci zai kai bakinsa,hoton Juwairah da ya gani sanye da ankwa ya hanasa kai  abincin bakinsa, kara volume yayi dan yaji abunda ake fada da kyau, ai bai karasa ji ba ya ture abincin tareda tashi ya dauki key, khuraiba da fitowarta daga daki ta ga yana niyyan fita ta tsaresa da ido tareda cewa "ina zaka tafi kuma bayan na sama abinci? "Ki dan rufe yanxu zan dawo bazan jima ba" ya mayar mata sannan ya sa kai ya fice. Komawa tayi ta rufe abincin sannan ta zauna ta dauki remote dan canza channel sai sannan hankalinta ya sauka kan TV taga abunda ya hana Shureim cin abincin,ko Shureim bai gaya mata ba ta san yana son Juwairah amma duk da haka in ya dawo sai ta tunkareshi.+

Shureim kuwa tun da yaga halin da Juwairah ke ciki kuma ya tuna da first haduwansu yaji sam bazai iya zamaba har sai yaji yanda take. Gudu yake sosai sai gashi har ya iso police station da ake tsare Juwairah. Tana zaune a cikin cell tana kuka taji an bude kofar, dago jajayen idanunta tayi ta kalli matar da ta shigo "ki taso kina da bako" shine abunda matar ta gaya mata, ba musu ta taso ta biyota har zuwa dakin da zai sadata da bakon nata. Ba karamin mamaki tayi ba ganin Shureim dan a halin da take ciki bata zaci akwai wanda zai so kusantarta ba, cikin sanyin jiki ta karasa ta zauna a kujerar da ke facing insa tareda maida kallonta zuwa ga table da ke tsakaninsu, a hankali taji ya kira sunanta ta dago jajayen idanunta ta saukesu a cikin nasa, sun jima suna kallon juna sannan tayi breaking eye contact in, a  nitse ya fara magana "Juwairah ki dago ki kalleni, ina so ki gayamun gaskiyar lamarin nan kinga yanxu daga ni sai ke bawanda zai ji,duk abunda zaki fada mun tsakaninmu ne sabida haka ki gayamun komai ni kuma na miki alkawarin tsayawa a matsayin lawyern da zai kareki" bayan hannunta tasa ta share kwallar da ya zubo mata sannan tace "wlh bnda masaniya akan abunda ake tuhumata akan na aikata, ban taba kisaba, dayan da ake zargin na kashesa fa is ma fiancé ta ya zan kashe wanda nakeso, dayan kuwa ko saninsa banyi ba ban ma taba ganinsa ba sai da aka nuna mun hotonsa" "Abdel fa? ya tambayeta yana kallonta "Abdel is a nyc person, bai taba mun abun da zanji in kashesa ba, wlh wlh wannan abu framing ina akayi dan bani na kashesu ba"

Shiru yayi sannan yace
"Toh ance anganki kin shiga gidansa in a hoody kuma baki fita ba sai around subh ko meh kika je yi? Kawar da kanta tayi dan bata san meh zata fada ba dan har ga Allah she can't rekol eva living home in dt hoody, sai da ya sake mata magana ta dago tace "ka tuna farkon haduwanmu da kai inda nacema bn san ya akayi na tsinci kaina a club incan wearing dat crazy dress ba? Kada mata kai yayi sannan ta cigaba "toh wannan ma hakane, ban san ya akayi na je gidansa ba actually bn ma san gidansa ba, blv me wen i tell u wani ne yayi kisan nan ya lakaya mun" shiru shureim yayi for some seconds sannan ya sake watso mata tambaya "ance kin ce Mijin yayarki kike suspecting ko mesa hakan? Shiru tayi sannan tace "ya sha threatening duk wanda ya rabeni ta hanyar cewa in bai nisanceni ba zai illatasa shiyasa nake ganin shi yayi"
STORY CONTINUES BELOW

"Toh in kika ce haka shi wannan balaraben Dubai infa, r u saying shima Bashir in ya san da shi?
Kai ta kada alamar a'a sannan tace "nima bn sanshi ba its ol confusing"
"dey have evidence against u Juwairah wanda yake nuna cewa ke kikayi duk kisan nan, an samu fingerprints naki akan 3 murder cases innan, so bn san ya zanyi da case inki ba dan nima inaga zai fi karfina i have to consult oda ppl, yanxu zan tafi but if akwai abunda kika tuna bayan tafiyana zaki iya sa a kirani", godia ta mai sannan ya mata sallama ya fice.

Yana fita bai jima ba su Bintalo suka zo, sam taki yarda ta gana da su har sai da aka fitar da Bashir sannan ta yadda ta zauna. "Juwairah nasan baki aikata ba kuma bashir na iya kokarinsa ganin ya fitar da ke" tashi tayi dan bata son jin kalaman yayar nata sannan tace "ni zan shige but ki tabbata su Inna sun iso kan a shigar da ni kotu" tana gama fadin haka ta juya ta fice

Ko da Shureim yaje gida kasa cin abincin yayi gashi kuma sai kirarsa ake tunda ya tsaya ya amsa tambayoyin da aka mai a bakin station karshe kashe wayan yayi gaba daya ya dan kishingide a kan 3seater dake parlon, a haka Quraiba ta fito ta samesa, zama tayi a gefensa tareda shafa gashin kansa, a hankali ya bude idonsa ya saukesu a kan kyakkyawar fuskanta, ganin damuwar da ke rubuce fuskanta ya sa ya tashi ya zauna tareda riko hannunta, "ya akayi habibti? Murmushi ta mishi sannan tace "meh ke faruwane Habibi, ka fita ko abincin da na sa maka baka ci ba, ka dawo kuma kayi zamanka a nan baka shiga ciki ba" murmushi ya sake mata sannan yace "sorry Habibti kaina ne yayi zafi, kin tuna Juwairah? Kai ta gyada sannan ya cigaba "toh she's bn charged with first degree murder bama daya ba har uku,kuma ta ce bata aikata ba kuma sunada evidence sosai a kanta but her luk says she's innocent kuma inason taimaka mata so am confused" hannunsa Quraiba ta dada damkewa sannan tace "u min zaka tsaya mata as her lawyer" kai ya kada alamar eh, sake hannunsa tayi tareda yin baya, take ya gane kishi ke damunta, riko hannunta yayi sannan yace "Habibti ki daina tada hankalinki kin san ni nakine ke kadai kinfi kowa sanin banda ra'ayin aje mata biyu a gidana so u hv ntn to worry"
Shureim na fa ga irin kallon da kake mata,in ka ganta sam hankalinka barin jikinka yake, jibifa ko abinci ka kasa ci da ka ga halinda take ciki, ko ni Shureim baka rawar jikin da kake akanta" murmushi yayi sannan yace "ai halin da take ciki Quraiba abun a tausaya mata ne, a halin da take ciki she nids all d support she cn gt, i blv she is innocent dts y kika ga na zabi in tsaya mata"
"Shureim knan, zaka iya duba kwayar idona kace mun ba sonta kake ba? Tashi yayi ransa a dan bace yace "luk Quraiba a bar maganan nan, yarinyar nan tausayinta kawai nake dts ol so ki daina fadin abunda babu shi" yana gama fadin haka ya shige daki. Binsa Quraiba tayi da ido har ya shige yayinda hawaye suka fara tsere a fuskarta, da kyar ta iya tashi ta shige dakinta, tasan tabbas Shureim na son Juwairah amma baxai taba bari ta sani ba dan yana mutukar sonta kuma baya son ganin bacin ranta shi yasa ma ta boye mai cutar da ke damunta amma yanxu tym yayi da ya kamata ya sani sai dai in ta gaya mai kuma zai iya sa ya kasa kare Juwairah a court kuma ita kadai take ji zata so Shureim da Salim tsakani da Allah bayan ita ta barsu, paper ta dauko ta fara rubuta wani yar wasika, tana yi hawaye na bin kuncinta kafun ta gama har yanayin fuskarta ya canja,folding papern tayi tareda stippling sannan ta jefa a jakarta ta dawo parlor.

Shureim kuwa tun da ya shiga daki yake tunanin abunda Quraiba ta gaya mai, da yaga tunanin zaiyi yawa ya ja wayarsa ya kunna nan messages da voicemails sukayi ta shigowa, deleting ya fara yi dan yasan duk bazai wuce yan son jin kwakwaff bane,har yaxo deleting na karshe hannunsa yayi playing mistakenly yaji bakon murya nace wa "Salam alaik, am Dr Abdulmajid from Nigeria, nazo wani conference a nan sudan naga case da ka dauka on TV n i tink zan iya taimakonka so kol me wen u get dis
Hannunsa na rawa ya kopi numbar ya kira, bugu daya yaji an daga, bayan sun gaisa ya shaida mai koshi wanene, sun tattauna sosai kafun suka aje wayar akan cewa gobe zasu hadu.
Washegari tun 7 ya gama shiri ya fito ya ga har Quraiba tayi breakfast, kitchen ya wuce inda ya tarar da ita tana wanke wanke, kansa ya daura a wuyanta tareda kissing nata a wajen sannan yace "shine baki tadani ba kike aikin ke kadai" hand towel ta dauko tayi drying hannunta sannan ta juyo ta sake mai murmushi sannan tace "naga kana jin dadin baccinka dts y bn tada kai ba,ynxu muje kayi breakfast" ta fada yayinda ta riko hannunsa sukayi parlor, zuba musu tayi sannan suka koma parlor suka ci abincinsu tare suna yar hirarrakinsu, suna gamawa ta kai plates in kitchen sannan ta zo ta dauki briefcase nashi ta rakasa,sai da ta ga ya bar gidan sannan itama ta shigo, cikin sauri ta shirya ta tada salim shima ta mai wanka suka fito,ajesa a makwabta tayi sannan ta wuce asibiti dan tana da appointment da Dr inta.

Wajen 7:50 Shureim ya isa office already Dr Abdulmajid na jiransa, bude musu office in yayi suka shiga sannan ya nuna mai wajen zama, yar rubuce rubucensa yayi sannan ya dago yace "Dr Abdulmajid bari inji da mai kaxo da shi" gyaran murya yayi sannan yace "baxan yi jumping into conclusion ba but i tink in an bani dama na ga client naka ko sau dayane zan gwada nawa bajintar, in case inmu ne i wil help u c to it dat she is cleared" kallonsa Shureim yayi yana dan nazari sannan yace "wani irin likita ne kai Dr Abdulmajeed? "Am a psychiatric Dr" ya bashi amsa,kada kai yayi sannan yace "mesa kake zaton psychiatric case ne? "Kaman yanda ka fada zato nake har sai na ganta tukun zan tabbatar" tashi Shureim yayi sannan yace "ok then sai muje ai".

Ko da sukaje tana zaune tana aikin da ta saba na kuka, har aka fito da ita bata bar kukan ba, da kyar Shureim ya lallabata tayi shiru sannan ya koma gun Dr Abdulmajeed ya shigo da shi, zama duk sukayi sannan Shureim ya dubeta yace "Juwairah ga Dr nan na kawo miki,yana yakinin cewa zai iya proving innocence naki so ina so ki basa hadin kai, kada kai tayi tareda dagowa ta kalli Abdulmajeed wanda shima ita yake kallo a zuciyansa yana yaba kyawu irin na Juwairah, ganin kallon yayi yawa yasa Shureim gyaran murya yace "Dr am a busy man kayi abunda ya kawo mu pls" dauke idonsa yayi a kanta sannan ya dubi Shureim yace "inaso kayi silencing phone naka ko ka kasheta baki daya cos abunda zanyi bai son hayaniya ko interruption" ba musu ya kashe wayarsa,
A hankali Dr Abdulmajeed ya fara magana "Juwairah kin san meh ake nufi da hypnosis? Kai ta kada alamar a'a, ajiyar zuciya yayi sannan yace "its a form of natural therapy da ake wa mutum dan fito da abunda yayi suppressing, ba mamaki akwai abunda ke damunki wanda ke bakisan da shi ba ko kin zabi ki binne shi but with my help zan iya taimaka miki har mu kai ga cimma burinmu,kin amince? Kai ta gyada alamar eh sannan yace "Juwairah inaso ki saki jikinki n drift into waking slip,ba bacci zan saki ba n ba dole zan miki ba amma idan kin fara jin bacci inaso ki rufe idonki n tk in ma words, yanxu inaso ki ja numfashi sosai, dia u go tk a deep breath n relax" ganin tayi yanda ya fada ya sashi cigabawa "yanxu inaso kiyi picturing kanki tsaye a can saman beni sai ki fara saukowa a hankali a hankali tkn one step at time,with each step u wil drift into a deeper slip" ganin idonta ya rufu kuruf kamar mai bacci ya sashi kiran sunanta. Jin bata amsa ba ya sake cewa "Juwairah kina jina" maimakon ta amsa sai suka ga fuskarta ya fara canzawa a hankali har ya dawo normal sai dai akwai dan changes, Shureim ne ya kalli Dr Abdulmajeed da ke rike da hannunsa dan tun da yaga fuskarta na canzawa ya nemi guduwa, mayar da shi yayi ya zauna tareda mai alamar yayi shiru sannan yace "Juwairah in kina jina ki amsa mun" mika tayi tareda bude idonta ta saukesu fes a kan Dr Abdulmajeed,murmushi ta mai sannan ta daura kafa daya kan daya tace "u"ll have to come ltr dan wannan ba Juwairah bace Juwi ce............
*Billy Ladan*

*RIKITACCEN AL'AMARI*
~A short story~
~Inspired by true life events~

*Na Billy Ladan*

*Dedicated to Hauwa Suleiman Muhammad*

bintladan.blogspot.com

_To any Psychiatric Medicine/Nursing Freak out there like me n my Kawa Hauwa Suleiman,dis page is urs_

Murmushi Dr Abdulmajeed yayi sannan yace "toh sannu malama Juwi, inaso ki gayamin......"
Kan ma ya karasa ta daga mai hannu tareda cewa "kaga Dr waye kake da suna" "Dr Abdulmajeed" ya tayata fada, tabe baki yayi sannan yace "wateva, ni ba wani dogon surutu nake so just get me out of this stinky place"
Ajiyar zucia Dr Abdulmajeed yayi sannan yace "eh zamu cireki amma meh kika sani gameda murder cases da ake tuhumar Juwairah? "Not much" ta fada tana wani cin magani, kallon juna Shureim da Dr Abdulmajeed sukayi sannan yace "toh munaso mu san abunda kika sani" kan ta sake basu amsa sai suka ga fuskarta ya sake canjawa ya dauki wani cooler form, a hankali Dr Abdulmajeed ya kira sunan Juwairah sai gashi a hankali ta bude ido ta saukesu cikin na Dr Abdulmajeed, murmushi ta sakar mai kafun ta fara magana cikin muryanta mai sanyi "haryanxu ba ita bace ni sunana Riya" Shureim ji yayi kaman ya fice ya bar dakin dan abun ya fara tsoratasa, gashi dai kana ganin Juwairah zaune saidai yanayin fuskarta da maganarta kadai zai nuna ma ba ita bace, abun ya zamto mishi tamkar shirin film, juyowa yayi ya kalli Dr Abdulmajeed murya can kasa yace "aljanu takeda ko? Murmushi ya mishi sannan yace "dey r called *Alters* zanma bayani anjima" sannan ya juyo gun Riya yace "Riya ku nawane? " Mu biyune kawai,daga ni sai Juwi" ta mayar masa
"Ok,inaso ki gaya mun abinda kika sani gameda kisan da ake tuhumar juwairah da cewar ta aikata" ta budi baki zata mayar suka ga fuskarta ya sake canzawa, yatsina fuska tayi ko bata fada ba sun san Juwi ce dan itace meh rashin kunyar "kuna bata lokacinku ne, Riya bata san komai akan kisar nan ba, ni zaku tambaya" dan murmushi Dr yayi sannan yace "toh muna jinki Juwi" dan mika tayi tana hamma sannan ta koma ta kwanta tayi luf da idonta, kiranta Dr Abdulmajeed ya shiga yi amma shiru,kallon Shureim yayi sannan yace "sun tafi kuman bn jin zasu sake dawowa,so zan tadata, matsowa yayi kusa da Juwairah yace "Juwairah yanxu zan tadaki,zan irga from one to five at d count of five zaki farka" nan ya shiga irge har ya zo 5 sai gashi ta bude ido a hankali, kallonsu tayi sannan tace "kun sami wani abu ne? Murmushi kawai Dr Abdulmajeed yayi mata sannan yace "ki dan huta for sum minutes sai in dawo muyi magana" kai kawai ta gyada sannan ya ma Shureim ido suka fita+

Suna fita suka dan nemi waje suka zauna sannan Dr Abdulmajeed ya fara magana "kamar yanda nayi suspecting case na Juwairah Psychiatric case ne, ka taba jin abunda ake kira multiple personality disorder ko split personality ko dissociative disorder? Kai Shureim ya kada alamar a'a, shiru Dr Abdulmajeed yayi dan bai san ta ina zai fara mai bayani ba, can ya dago yace "wato multiple personality disorder wani condition ne da several personalities suke taruwa a jikin mutum daya, in her case biyu take da shi but ana iya samu fiye da hakan har mai 200 personalities ma an taba samu a jikin mutum daya, yawanci yana faruwane dalilin wani trauma da ya sami mutum a kuruciyarsa, toh wannan mummunan abu da ya sami yaro a kuruciyarsa sai kaga hankali da zuciyarsa bazata iya dauka ba sabida yanada ciwo kuma yakan tada hankali, gudun haka sai yaro ya zabi ya binne wannan mummunar abu da ta samesa ta hanyar creating wani personality a jikinsa da zai tayasa mantawa da wannan event in, wannan personalities su psychiatrist ke kira *alters* ,in English in ance alter ana nufin ka canza ko ka sake, toh dts wat happen ta sake creating wani ita ajikinta dan ya tayata binne abunda ya sameta wannda ba mu san ko menene ba, but usually yana faruwa due to molestation ko kuma lost of a loved one duk kan iya jawo hakan, an ka gansu da kanka su biyune jikinta and ba lokaci daya aka haifansu ba, usually daya at a time, bayan anyi creating first one in similar trauma ya sake faruwa toh sai a sake creating wani n usually suna sanin junansu ita host ince baxata san da su ba har sai mu psychiatrist mun shigo ciki" ajiyar zuciya Shureim yayi dan jin abun yake kaman a mafarki dagowa yayi ya dubi Dr Abdulmajeed yace "Is it common? Kai ya gyada alamar eh sannan ya kara da cewa "recently an samu case na mai two personalities a Korea n i was privilege to c him" kallon dakinta Shureim yayi tareda cewa "but she seems normal" gyada kai Dr Abdulmajeed yayi sannan yace "Masu split personality seem normal har sai alter insu yayi taking ova Wanda zai iya lasting days ko sati ko wata ma sumtimes kuma host in bazai taba sani ba, shi dai zai na ji kaman ya manta wani part na rayuwarsa zai zamto kamar an mai wiping memory, bazai taba tuna abunda ya faru ba, n mostly alters suna samun sunansu ne daga sunan host in, kaga in her case Juwi/Riya= Juwairiya" tsorone ya bayyana fuskar Shureim sannan yace "kana nufin Juwairah ita tayi kisan? Shiru Dr yayi sannan yace "its inconclusive, but bazan ce ita tayi ba sai dai muce her alters did, its eida Juwi ce ta aikata ko Riya but dole mu sake ji daga garesu dan jin wa ya aikata tareda jin dalilin da yasa Juwi da Riya suka ginu a jikinta, sune kadai zasu san mummunan abunda ya sameta a kuruciyarta dan ita bazata tuna yanxu ba.
Hannu Shureim ya sa ya dafe kansa "yanxu ya zan kare wannan case a kotu, ai sai suce hauka nake kuma judge da zatayi case innan bata wasa gashi opponent ina ya san aikinsa, bai taba daukan case ya fadi ba, banji dey wil buy abunda zan fada ba" dafasa Dr Abdulmajeed yayi tareda cewa "sai kace ba Lawyer ba, kar ka karaya tun yanxu, d case is even simple, u just make an insanity plea"

Kallonsa Shureim yayi tareda sakin murmushi yace "kaga har ka fini sanin aikina, abunda zanyi kenan, zamuyi pleading not guilty sabida mental condition inta, baza mu amsa laifin ba sabida ba a cikin hayyacinta ta aikata ba" hannu ya mika mai yace "nagode Dr ds case will b in our favor insha Allah" Tashi Dr yayi yace "yanxu taso muje mu shaida mata abunda muka samu kan muje mu taro shaidu da zasu bada shaida kan wannan ciwo da ba kowa ya sanshi ba" Tashi Shureim yayi suka nufi dakin da ake tsare Juwairah, inda suka barta nan suka sameta, ko da Dr Abdulmajeed ya mata bayani kuka ta hau yi, da kyar suka samu tayi shiru ko da suka tashi tafiya cewa tayi ita su kasheta dan in basu kasheta ba ita zata kashe kanta dan gudun kar ta sake wani kisan, dole suka koma suna bata baki amma ina ita ta dage sai dai su nemo mata abunda za ta kashe kanta da shi. Ganin haka yasa Dr Abdulmajeed cewa shi zai zauna da ita, duk da Shureim bai ji dadin hakan ba dole ya koma gida tunda shi yanada family, haka ya musu sallama ya barsu akan cewa zai dawo da sassafe dan gobe za shigar da ita kotu.
Yana fita bai jimaba Bintalo suka zo dasu Inna, banda kuka ba abunda Inna da Abba keyi, cikin kuka Juwairah tace "Inna ban aikata ba" Inna na kuka tace "haba Juwairah har sai kin fada,nafi kowa sanin ba ke kikayi ba", ganin kukan yayi yawa yasa aka maidata daki su kuwa suka koma gida.

Washegari da sassafe Barrister Shureim ya fito cikin shiri,bakaken suit ne jikinsa hannunsa kuwa brief case ne sai gown na lawyers da hulansa, dakin Quraiba ya nufa yaga bata ciki, falo ya nufo ya ganta tana jera abinci a dining, ji tayi an rungumeta ta baya ta dan dago tareda juyo fuskarta, bakinsa ya kai kan nata ya danyi kissing sannan yace "mrn habibti,u r so early today kuma gashi hr kin gama brkfast" juyowa tayi tareda mai murmushi sannan tace "how do u xpct me not b up wen nasan zaka fita da wuri" jawota yayi ya rungumeta tsam a jikinsa tareda cewa "shi yasa nakesonki habibti, duk dunia bnjin akwai wanda yayi sa'an mata irina" "i luv u too habibi" ta mayar mai sannan ta zaunar da shi ta zuba mai, sai da yaci yayi nak sannan yace ta dan zuba mai a flask na mutane biyu in akwai, murmushi tayi tareda tashi tayi yanda yace, ko bai fada ba tasan wa Juwairah zai kai sai dai yanxu ta daina kishi dan tasan her time is limited kuma ko da yanason Juwairah ta san haryanxu mijinta na sonta kuma bazai taba canja mata ba. Har wajen motarsa ta rakosa tareda mai fatan samun sa'a sannan ta koma.

Yana isa station kai tsaye dakin da aka tsare Juwairah ya shiga, zaune ya sameta ita da Dr Abdulmajeed suna hirarsu Juwairah har da dariyanta, bara kace ita za a shigar kotu ba, ransa ne yaji ya sosu ganin kusancinsu gashi sai wani washe baki take, kawar da abun yayi a ransa tareda karasawa ciki, dagowa sukayi suka amsa sallamarsa a tare sannan ya aje musu containers biyu da ya zo dashi, tashi Dr Abdulmajeed yayi tareda cewa "bari inje in shirya sai mun hadu a court room" har ya kai kofa Juwairah ta kirasa cikin siririyar muryanta, juyowa yayi suka kalli juna "Kar ka jima pls,inaso ya zamto kana can time da za a shigar dani" murmushi ya mata sannan yace "u can count on me hun,i wil surely b dia" sannan ya fice. Shureim ji yayi kirjinsa ya hau bugawa da sauri sauri yayinda ya fara jin wani abu gameda Dr Abdulmajeed a ransa, kar dai zancen Quraiba ya zamto gaskia, kar dai ya fara son Juwairah, kawar da kansa yayi tareda cewa kai it cant b. Kallonta yayi tana cin abincinta cikin kwanciyar hankali ya karasa ya zauna a gefenta, gyaran murya yayi ta dago ta kallesa, sai yanxu ta tuna basu gaisa ba, cikin jin kunya ta gaishesa, tabe baki yayi yace "bazan amsa ba,sai da sabon saurayinki ya tafi zaki kulani" ya fada yana kallonta, murmushin takaici tayi sannan tace "Barrister Shureim knan, a halin da nake ciki har kana gani inada lokacin soyayyane, kawai i feel at ease when am around him,dts ol n ntn more" ajiyar zucia yayi wanda ya sa Juwairah dagowa suka hada ido, kawar da kansa yayi tareda tashi yace "bari in barki ki karasa,zamu hadu a waje, i want you to b very careful a court room innan, kar ki yadda idon mutane ko opponent ina ya baki tsoro, nasan Barrister Abbas is cunny dnt let him get to u, n bana so ki kara komai akan abunda kika gaya mun, exactly shi zaki fada a court in aka tambayek, in kinyi hakan insha Allah baza mu samu matsala a kotu ba" gyada kai yayi sannan ya sa kai zai fice "Thank You Shureim" yaji ta fada, runtse idonsa yayi jin yanda Sunansa yayi dadi a kan harshenta, sa kai yayi ya ida fita daga dakin batareda ya juyo ko ya ce mata wani abu ba.
*Billy Ladan*

*RIKITACCEN AL'AMARI*
~A short story~
~Inspired by true life events~

*Na Billy Ladan*

*Dedicated to Hauwa Suleiman Muhammad*

bintladan.blogspot.com

_Aunty *Aishat A Muh'd* wannan shafin na baki shi kyauta, u r such a nice,simple,kind and generous person, a gaskia samun irinki sai an tona, Allah ya biya miki bukatunki,ya saka miki da mafificin alkhairansa.Ina sonki har cikin raina_

Kotun cike yake makil da mutanen da suka zo jin ya case in Juwairah zata kaya, a dama Barrister Abbas ne zaune da mai tayasa defendn case insa, a hagu kuma Barrister Shureim ne zaune da Juwairah a gefensa sai kuma wani abokin aikinsa. A first row na audience na hango Inna,Abba,Bintalo da Bashir suna zaune duk damuwa rubuce a fuskarsu, sunfi minti biyar suna zaune ana jiran judge, umarni naji an basu duk aka tashi sai ga judge in ta shigo fuskan nan nata a murtuke kai kace bata taba daria ba. Sai da ta haura mazauninta ta zauna sannan kowa ya koma ya zauna. Medicated glass nata ta dauko ta maka a idonta sanna ta dan yi rubuce rubucenta, ba tareda ta dago ba tace "lawyern mai kara ur opening statement" cikin nuna isa da takama barrister Abbas ya bar mazauninsa ya zo gaba, wani kallo ya watsa wa Shureim da Juwairah sannan yace "ya mai girma mai shari'a da duk sauran mutane dake zaune a cikin kotun nan ina muku barka da warhaka, kamar yanda kuka sani ana shari'ane akan wannan gagarumar yar ta'addan da ta addabi ba nan kasarmu ba har ma da wasu kasashe" ya fada yana nuno Juwairah "she is a cold bloody murderer da ta dauki rayukan mutane uku aciki harda saurayin da zata aura, bayan ta kashesane ta gudo nan ta aikata wasu kisan kuma ta so lakaya wa mijin yayarta da ya bata dukkan wani gata amma dan butulci irin na dan Adam ta nemi lakaya masa, as we proceed zan fayyace muku daya bayan daya ta yanda zaku gamsu cewa ita tayi dukkan kisan nan" yana gama fadin haka ya danyi bowing wa Judge Sharifa tareda sake watsowa su Shureim harara sannan ya zauna. Yan rubuce rubuce Judge Sharifa tayi sannan ta ce "Lawyern wanda ake kara how do u plead?
" not guilty by reason of insanity" Shureim ya fada tareda tashi, "client ina na fama da wani condition da ake kira MPD" nan ya shiga kwararo musu bayani da Dr Abdulmajeed ya masa sannan ya kara da cewa "as d trial progress zan yi kokarin gamsar da ku akan cewa Juwairah bata yi kisan nan ba,alters nata ne sukayi kuma bata da masaniya akan hakan" yana gama fadin hakan shima ya koma ya zauna. Yan rubutu tayi sannan ta dago ta kalli barrister Abbas tace "r u ready to proceed? " yes ur honor" ya fada tareda tashi ya fito gaba ya tsaya yana kallonsu, yayi hakan na kusan minti daya sannan ya saki wani uban kara, kallonsa duk aka tsaya yayi can ya hau dariya ba kakkautawa sannan yayi shiru ya tsaya yana kallonsu, tafi yayi yace "ba dai kuna jira in baku hakuri ba, dan nima ba ni nayi ba,alter na ne yayi" "objection ur honor" Shureim ya fada "korafi bai karbu ba,barrister yusuf kana iya cigaba" yaji Judge Sharifa ta fada, wani murmushin mugunta Abbas ya watso mai, cikin sanyin jiki ya koma ya zauna sannan barrister Abbas ya karasa "ynxu zan kira mutum na farko da zai bada shaida wanda zai tabbatar muku cewa juwairah ita tayi wannan kisan, ido yayi aka shigo da wani, karasawa yayi gabansa yace "inaso ka gayawa kotu sunanka da kuma aikinka" gyaran murya wannan bawan Allahn yayi sannan yace "ni sunana agent Aaron kuma ina aiki ne a wajen tantance fingerprints" kada kai Abbas yayi sannan yace "shekaru nawa ka dauka kake aiki a can? "Kimanin shekara goma sha biyar knan yanxu" ya mayar mai, sake kada kai yayi sannan yace "na tabbata ka ci karo da finger prints da aka kawo muku na wannan murder cases in" kai ya gyada alamar eh, sake kada kai Abbas yayi alamar gamsuwa sannan yace "inaso ka fadawa ko kotu abunda ka samu akai" dan gyara zama agent Aron yayi sannan yace "eh toh bisa bincekenmu dai ya nuna wanda yayi kisan nan mutum dayane dan duk iri dayane kuma yayi pointing at Juwairah" godia yayi masa sannan ya juyo yace "ya mai girma mai shari'a wannan hujja kadai ya isa ya gamsar da kowa kan cewa Juwairah ita tayi kisan nan amma nan ba da jimawa ba zamu kawo wasu shaidun su sake gamsar daku" zama ya koma yayi sannan Judge Sharifa ta dubi Shureim tace "koh kana da tambaya? Tashi yayi tareda kada kai tareda cewa "banda tambaya ur honor, sai dai inason wannan kotu mai adalci tayi amfani da basirarta dan gano cewa bamu mutum mai hankalin da zai yi kisa sannan ya tafi batareda ya binne duk wani abu da zai sa a ganosa ba,dts ol ur honor" ya fada tareda zama, umarni aka bada aka fitar da agent Aron, bai jimaba aka shigo da wani tsohon balarabe, Barrister Abbas ya taso yace "Ur honor shaidata na biyu kenan, karasawa yayi yace "ko zaka iya gayawa kotu ko waye kai? Gyara tsayuwarsa tsohon nan yayi sannan yace " ni sunana Abdulrauf kuma mai gadine a gidan shahararran dan kasuwan nan na garin dubai wato Abdulkadir,
"Koh zaka iya gayawa kotu abunda ka sani gameda mutuwar uban gidan naka"
"Eh wata daya da ya wuce kenan wata daren lahadi uban gidan nawa ya shigo da wata yar budurwa,nidai naga shigansu tare amma fitarta ita daya nagani,toh da safe da na tashi ganin har lokacin fitansa yayi bai fito ba shine na bi bayansa inda na tarar da gawansa shine nayi wuri na kira jami'an tsaro" wani murmushi Abbas yayi sannan yace "na tabbata ka ga fuskar wannan yarinyar" "sosai naga fuskarta" ya bashi amsa "ai gidan alhaji Abdulkadir ko dare ma rana ne dan akwai wuta a ko ina wanda hakan ya bani daman ganin fuskarta" dan juyowa Barrister Abbas yayi sannan yace "mallam Abdulrauf inaso ka duba cikin kotun nan ko kaga wanda tayi kama da wannan budurwan" hannu ya daga ya nuno Juwairah wanda a take taji hawaye ya fara taruwa a idonta, "wani shu'umin murmushi barrister Abbas yayi sannan ya juyo yace " Ya mai girma mai shari'a a ranar da aka kashe wannan attajiri munada labarin cewa Juwairah taje conference dubai kuma an samu chat nasu da wannan bawan Allah sai dai ta dan canza suna dan kar a ganeta, amma bata fi karfin hukuma ba dan an gano sun jima suna tare kafun har ta samu damar kasheshi+

STORY CONTINUES BELOW

Komawa yayi ya zauna sannan Sharifa ta tambayi Shureim ko yanada tambaya, tashi yayi tareda kallon Juwaira sannan ya karasa gun Abdulrauf "mallam Abdulrauf, shin kana da matsalar gani, ma'ana kallonka na gushewa da dare ko makamancin haka? "A'a" ya bashi amsa sannan Shureim ya ce "ina so ka kalli wannan baiwar Allahn da kyau, ka tabbata ita ka gani? Sake kallo juwairah yayi da itama ta juyo dan bashi damar kare mata kallo, dan bata rai Abdulrauf yayi sannan yace "gaskia bazan iya ce ita bace amma dai suna dibi, hala ko yan biyuntane ko wata yar'uwartace" murmushi yayi sannan yace "ya mai girma mai shari'a, ko dan furucin wannan bawan Allah za a fahimci ba kage nake ba, alters suna kama da host nasu amma hakan bazai hana a banbantasu ba, ina mai tabbatar miki da cewa alter inta ita ta aikata wannan kisa, ina so nima a ban daman kiran first shaida nana
Dr Abdulmajeed ya kira inda ya fara mai tambaya akan multiple personality disorder inda ya shiga bashi amsoshi masu gamsarwa, hatta judge Sharifa aje biro hannunta tayi tana jinsa with keen interest, a haka har ya gama mai tambayar kafun aka bawa Dr Abbas damar tambayarsa wanda yawanci tambayar rainin hankali ya mai, yana komawa yana zama yace Sharifa ta bashi damar yima Juwairah tambaya, juwairah jin haka jikinta ya dau rawa, hannu Shureim ya kai ta kasan kujerar ya riko hannunta ya damke tareda juyowa, juyowa itama tayi suka hada ido ya sake mata murmushi tareda mouthing "its,ok" ji tayi jikinta ya bar rawa, cikin sanyin jiki ta tashi ta karasa inda za mata tambayar, dagowa tayi ta kalli inda su Inna ke zaune taga Inna ta mata murmushi, nan ta kara jin wani confidence ya zo mata, hango Abdulmajeed tayi yana mata murmushi,itama ta mayar mai, Shureim da ke lura da hakan, yaji ransa ya dan sosu, a xuciyansa yace "ba dai na janyo wa kaina alakakai ba da na yadda Abdulmajeed ya jona case innnan ba dai" jin Abbas ya fara tamvayarta ya sashi kawar da tunanin. Tambayoyi ya ringa mata akan Abdulkadir Abdel da kuma Nasir, wanda ta bada amsa akan iya abunda ta sani, a karshe videon tana fita daga gidan Abdel ya nuna mata, inda shima tace bata da masaniya akai, duk kokarinsa na yaga ya cusa mata ra'ayi ta yanda har sai ta ce ita tayi ya gagara dole ya hakura ya zauna sannan aka bawa Shureim damar tambayarta. Kan ya fara sai da ya basu labarin farkon haduwansu da Juwaira kan yace "Juwaira shin kina jin kaman kinada memory loss ko wani abu makamancin haka, kada kai tayi tareda cewa "sau dayawa nakan ji na mnta abu ko in ganni a wajen da bn san yaushe na kai kaina ba,kamar farkon haduwata da kai, bn san ya akayi na tsinci kaina a wancan wurin ba, kuma na kan ga strange messages a wayana wanda i dnt rekol sending, ko inga anyi amfani da credit card ina ko inga receipt na kayan da i dnt rekol buying" murmushi yayi sannan yace "dts ol,zaki iya komawa ki zauna sannan ya juyo gun Judge Sharifa yace " ya mai shari'a kaman yanda kika ji Dr Abdulmajeed yayi bayani ga signs innan ya nuna Juwairah na fama da wannan condition kuma in har zaki bamu dama zamu iya hypnotising inta a nan kigani kafun sauran shaidun mu karaso" dagowa judge sharifa tayi tareda cire glass da ke idonta ta mai wani kallo "Barrister Shureim, I wunt have u turn my court room into a cinema, i knw wat it is like to hypnotize sum1 i wunt have dat in my court room, and anan zanyi resting casr ina sai zuwa jibi, b4 den duk ku tanadi sauran shaidunku cos shine karshen zama da zanyi" tana gama fadin haka ta tashi tayi waje. Barrister Abbas ne ya karaso wajensa yana daria yace "in nine kai aje case innan zanyi, cos uv lost already but wait ai in kayi hakan it wunt b fun anymore n bazaka ga abunda na tanada ma a next zamanmu ba so gudluck" kafun ma Shureim ya mayar mai ya bar wajen. Dafasa yaji anyi yajuyo yaga Dr Abdulmajeed, murmushi ya mai tareda cewa "U did grt today so dnt let him gt to u, n nayi magana da Doctors in dey wil b here tomorrow so zasu ba da shaida akan wannan condition in, yanxu inaso in tafi da Juwairah in ta huta zuwa dare i will hyonotise her again dan inaso kan a kara zama inji wa yayi kisan a cikinsu tareda sanin wannan mummunan abu da ya sameta a kuruciyarta"
Murmushi ya mai tareda cewa bn san ya zanyi ba in ba kai, i wil try n b dia da daddaren amma yanxu i have to go home n get some rest, tare suka fito waje sannan ya musu sallama ya ja motarsa ya bar wajen
Da daddare ko da Dr Abdulmajeed ya sake hypnotizing inta Juwi ce ta fito, sai da ta gama musu rashin kunyar nata sannan ta fara basu amsar tambayarsu, "Juwi" taji Abdulmajeed ya kirata murkuda mai baki tayi sannan tace "wlhy ka fiye naci da shegen tambaya, gashi sai ina zaman zamana ka wani tasoni, kuma ji yanda kake wani kwala mun kira sai kace kai ka rada mun" murmushi duk sukayi sannan yace "Allah huci zuciyarki gimbiya Juwi" dan sake fuska tayi ganin haka ya sa ya cigaba yace "Juwi na tabbata kin san cewa in har aka yankewa Juwairah hukuncin kisa toh dts d end of u ol dan in ta mutu kuma kun mutu" idonta ne ya ga ta kawo kwalla ya gane cewa ya fara samun kanta dan haka ya gyara zama ya cigaba "Juwi kin san kashe rai ba kyau ko? Dan bata rai tayi tace "amma in ta kama dole kayi ai" kallon juna shida Shureim sukayi sannan Abdulmajeed yace "meh kike nufi da hakan"
"Dia r tyms dat u have to do it to protect urself, kaman in kaga mutum zai keta maka haddi kuma shine hanyar da zaka kare kanka" ta mayar mai "ok I get it so dat what happened kenan, u killed them to protect urslf"
Tashi tayi cikin bacin rai tace "baka isa ka sani in fada ba cos nasan u"ll jst use it against us" tasowa yayi ya nufota yace "Wlh bazan taba aikata hakan ba Juwi, ina sonku duka tunda Allah ya daura mun son Juwairah kinga kenan kuma kunada muhalli a zuciyata, bazan taba cutar da ku ba, i wil try n save you in har kin yadda ki fito a kotu" kada kai tayi alamar ta yadda sannan ya juyo gun Shureim ya ga baya wajen kallon Juwi yayi yace "bari in dawo da Juwairah ko" "wait" tace dashi "inaso Bashir da Bintalo su zamto suna wajen yayin zaman karshe, ka tabbatar suna wajen kuma ka sa a tsare kofofin fita ta yanda ba wanda zai iya fita har sai an kare shari'ar" kallonta yayi da mamaki yace "koh zaki gayamun dalilin hakan" komawa kan kujera tayi ta zauna sannan tace "patience Dr Abdulmajeed d forest wasn't made in a day, kai dai try and stay alive cos am sure bazaka so kayi missing abunda zai faru ba" ta fada tareda yin wani murmushi sannan ta rufe idonta murmushi yayi sannan yace "ashefa Juwi u r not dat bad" bude ido tayi tace "Dr dnt tell me u r falling for me already" daria yayi sannan yace "ofcos i am" dan ya fahimci mood in wasa take, dawo da Juwairah yayi ya mata bayanin abunda ya faru sannan ya fito dan duba Shureim. Jingine da motarsa ya gansa ya karasa ya dan dafasa tareda cewa "ya dai Barrister" dan kago murmushi yayi dan duk jinsa yake wani iri, tunda yaji yace yana son Juwairah yaji bazai iya zama wajen ba dan yanxu ya fahimci shima son Juwairah yake sai dai bazai taba karya alkawarin da ya ma Quraiba ba na cewa bazai mata kishiya ba, ajiyar zucia yayi sannan ya dubi Dr yace "kol na fito amsawa wlh,ya kuka kare? Nan ya kwashi komai ya fada mai, mamakin kalaman Juwi ne ya kamasa yace "Dr i have a feeling jibi akwai drama kaga tafiyata, today has bn a busy day, gobe ma haka likewise jibi so dnt xpct me early tmrw" ya fada yana shiga motarsa hannu ya daga mai sannan ya ja motarsa ya bar station in.

Abun tambaya shine, mesa Juwi tace a tabbatar Bintalo da Bashir suna wajen karshen zaman da a za yi na shari'ar nan🤔

Nidai Billy already na shirya yar karamar akwatina dan nima gobe jirgina zai daga zuwa sudan,baza ayi wannan shari'ar banda ni ba, waye zai bini?1

*RIKITACCEN AL'AMARI*
       ~A short story~
~Inspired by true life events~

*Na Billy Ladan*

*Dedicated to Hauwa Suleiman Muhammad*

     
bintladan.blogspot.com

Yau ma kotum cike yake makil da mutane dan har yafi na farkon zaman.
Can gefe na hango su Meenah,Pherty, Mummeetie,Maryam Chiroma,Hafsat Abuja,members in Billy ladan fans forum,Billy Ladan novels both na Facebook da whatsapp,ciwon ya mace group kai da ma sauran groups da bn ambata ba duk sun hallaru a wajen dan suma sunce baza kare shari'ar nan banda su baba

Kowa na zaune banda Shureim da Judge Sharifa wanda hakan ya tada hankalin Juwairah yayinda barrister Abbas ya ke ta murmushin nasara dan a zatonsa Shureim yayi dropping case inne. After abt 5mins Judge Sharifa ta shigo mutanen wajen duk suka tashi har sai da ta isa mazauninta ta zauna sannan suma suka zauna, kallon kujerar Shureim tayi for sum seconds sannan ta kawar da kanta ta danyi rubuce rubucenta, dagowar da zatayi ta hango Shureim ya shigo da dan sauri, da kai ya gaida Dr Abdulmajeed sannan ya karasa ya zauna gefen Juwairah tareda sake mata murmushi, wani ajiyar zucia tayi kafun ta mai murmushi itama. "Sorry am late hun,sumtin cm up at home" murmushi kawai ta mai tareda mouthing "its ok", muryar Sharifa suka ji tana cewa " barrister Shureim zamu iya sanin ko u r tru, after coming late kuma zaka bata mana lokaci" tashi yayi yana gyaran murya sannan yace "sorry ur honor,i apologize for coming late, yanxu zan fara gabatar da shaiduna wanda zasuyi backing up wannan condition da juwairah ke fama dashi, da fata wannan kotu mai adalci zata nutsu har ta gamsu da bayanansu dan yanke hukuncin da ya dace" nan ya sa aka shigo da first Dr wanda ba sai an fada ma daga korea yake ba, karasawa yayi ya tsaya a gabansa yace "inaso ka gayawa kotu sunanka da kuma aikinka" Shureim ya fada dagowa yayi yace "Ni Sunana Dr Hyung Jin Jung kuma psychiatric Dr ne a can Korea n i hv bn working for d past 30 years" kai Shureim ya gyada alamar gamsuwa sannan yace "shin ni na kiraka ko kuwa dan kanka kazo?
"ba kirana kayi ba, dan kaina nazo dan naga case in a news kuma recently nayi aiki a kan mai irin case in dts y naxo in taimaka" Dr ya amsa mai
Gyara tsayuwarsa Shureim yayi sannan yace"Toh ina so ka gayawa kotu abunda ka sani gameda wannan condition "
Gyaran murya yayi sannan yace "wato wannan disorder da ake kira multiple personality disorder ba kagenta akayi ba kuma bawai babu ita bane a dunia sai dai mutane dayawa ba su santa ba, yana samun mutum ne yayinda wani trauma ya samesa a yarintarsa, like d two recent cases da nayi treating a korea dayan yar yarinyace yar kimanin shekara 19  wanda take da alters biyu wanda suka samu asali dalilin sakaci da iyayenta sukayi wajen kula da ita, she was a survivor of emotional child abuse and neglect from both parents dan daya alter ta shaida mana akwai ranan da har aka barta a gida ita kadai for almost two days ba abinci, dayan kuma soldier ne dan shekara 20 wanda aka kawo mana shi daga barrack saboda hari da yake kai wa abokan aikinsa alhalin hakan ba halinsa bane, sannan kuma ana samunsa a wajen da bai kamata ba kuma daga baya in ya dawo normal bazai tuna kai kansa wannan wajen ba, a zamanmu da shi muka fahimci shi alters 7 garesa wanda acikinsu akwai mai sashi aikata mummunan abu wanda yayiwa kansa lakabi da "mr violence" akwai "mr rude,shit,timid" da dai sauransu,ur honor MPD is real u may not have seen it but it does exist" bayan shi wasu biyu sun sake zuwa sannan barrister Abbas ma ya kawo Doctors da suka ce sam su a rayuwarsu basu taba jin wannan condition ba, daya cewa ma yayi it doesnt exist kawai kirkira mutane keyi dan suyi ta'assa son ransu sai suce basu sukayi ba, sosai abun ya daurewa Judge Sharifa kai dan ta rasa abun cewa, shiru tayi for some minutes sannan tace za a tafi break in an dawo za a ji hukuncin da ta zartar.+

Tana fita Dr Abdulmajeed ya karaso wajen Shureim yace "barrister mai ya faru munyi akan zaka fitar da Juwi since ta yadda zatayi magana,murmushi yayi sannan yace " i saved d best for the last kai dai zo muje mu yi breakfast mu dawo".

STORY CONTINUES BELOW

Bayan kaman 30 minutes aka dawo, bayan kowa ya zauna Judge Sharifa ta shigo, sai da tayi kusan five minutes ta dago zata fara magana sai taga Shureim ya tashi yace "ur honor inaso a ban koda 3 minutes ne i want to show u ol" wani kallo Sharifa ta watso mai amma yi yayi kaman bai jita ba ya fita, bai jimaba sai gashi ya shigo da wasu dauke da projector da projector sheet, baki bude Judge Sharifa ke kallonsa har aka gama saita komai ta inda kowa zai iya kallon abunda ake projecting dan a can sama aka sa, sai da ta bari ya gama sannan ta danyi wani murmushi ta dubesa tace "barrister Shureim meh kakeyi ne i said no turning my court room into a cinema" batareda ya juyo ba ya ce "ur honor u said no hypnotising anyone in ur court room amma bakice bazan iya nunawa ba, ryt audience? "Ryt" suka amsa mai da murya mai karfi, ran Sharifa yayi mutukar baci dan barrister Shureim ya gama sa ta ji kunya, juyowa yayi wajenta yace "ur honor i promise ba hypnosis zanyi ba, batareda bata lokaci ba inason kiran juwairah" tasowa tayi a hankali ta zauna a inda aka tanadar mata, Qur'ani aka miko mata ta rantse da cewar duk abunda zai fito a bakinta gaskia ne, nan ya fara tambayarta a kan Nasir, ta kwashi komai ta gaya mai harda threat da Bashir ya mai, bayan ta gama ya tambayeta batun Abdel nan ma ta gaya mai komai har zuwa rabuwarsu, sai da ya gama tambayarta ya juyo gun Abbas ya ce "barrister Abbas any question? Cadak ya tashi kaman dama jira yake, da sauri ya karasa dan dama ya so asake bashi daman sake tambayarta, wani banzan kallo ya mata sannan yace " Juwairah bake nake son yiwa magana ba, da Juwi nakeson magana dan naji ance tafi taurin kai, so Juwi ina kike,comeout i want to talk to u,pls do come out Juwi cos am dying to talk to u Juwi" ya karashe in a teasing manner yana daria harda tafa hannu, ido Shureim yayi wa mai daukan Juwairah a video da ya matsa kusa da ita ya dauketa sabida sauran mutane su gani da kyau a kan projector cos yasan dole zata fito, gani nayi tayi luf da idonta yayinda fuskarta ya fara canzawa, barrister Abbas daskarewa yayi awajen dan tunda aka haifesa bai taba ganin irin wannan transformation inba ko a film, Sharifa ma har karkato da kujerarta tayi ta fara kallonta, a hankali ta bude idonta ta saukesu akan barrister Abbas ta basa wani deadly look, juyawa yayi zai koma kujerarsa yaji ta rikosa ta bayan wuya, dagasa tayi sama ta yanda har kafafunsa baya taba kasa sannan ta dan juyo da fuskarsa ta dan karkata kai tace "wia to huh? Ba kai kace kana son ganina ba, sai da na fito kuma zaka gudu, wato barrister Abbas i hate noise n ban so ina hutuna a tadani gashi kuma ka tadani, so let me c wat i wil do to you" ta fada tareda daura hannunta a baki alamar tunani🤔
Rufe ido kuma naga tayi a take fuskarta ya shiga canzawa for d second time, barrister Abbas da haryanxu take shake da wuyansa ba abunda yake sai hawaye dan yau ji yake mutuwarsa ce ta zo, gashi bawanda yayi yunkurin tserar da shi, bude idonta tayi tareda jefar da shi yayi baya ya fadi, in a cooler voice yaji tace "sorry r u hurt" wani kallon mamaki ya mata sannan yayi baya da gudu ya koma seat nasa yana huci, tashi Shureim yayi yana dariya kasa kasa yace "Riya i assume its you" kai ta gyada sannan ya mata umarni da ta zauna, ya juyo gun Judge da sauran mutane da duk mamakin abunda ke faruwa ya gama cikasu yace "toh kun dai ga da idanunku ba fada muku akayi ba, na farkon itace violent one in mai suna Juwi, na yanxu kuma Riya d cooler one, Riya inaso ki gaya mana ya akayi kuka samu kanku a jikin Juwairah? Dagowa tayi sai ga hawaye sharkaf a fuskarta, da kyar ta iya cewa " nice na biyu so zan bar Juwi ta gaya muku" tana gama fadin haka fuskarta ya sake canzawa sai ga Juwi ta dawo sai dai wannan karon a sanyinta ta dawo "Ina so in fara da yanda aka yi kisan nan" kai kawai Shureim ya gyada tareda komawa ya zauna sannan ta fara magana "zan fara da Nasir, ranar da sukayi dinner ranar Bashir yayi threatening nasa akan ya rabu da Juwairah ko ya illatasa, jin haka yasa Juwairah ta kwashi kayanta dan barin gidan amma ita a tunaninta bata bar gidan ba dan washegari ta ga kanta a gida, abunda bata sani ba shine i took over n went to him dan mu gudu to save us ol, but wen i went to him, he tried to force himself on me, yayi kokarin keta mun haddi nikuma wajen kare mu baki daya na kashesa na dawo gida, i took ova n killed him dts y Juwairah bata san da hakan ba" ta karashe tana kuka mai cin rai tashi Shureim yayi ya karaso gabanta yace "Abdel fa? Share hawayenta tayi sannan tace "shima bashir yayi threatening insa dts y ranan Juwairah ta kasa barci ta tsaya gadin Bashir, but i later took ova na kirasa ya mun kwatance naje na gaya mai abunda ke faruwa, ashe shima he is an asshole, shima kokarin mun fyade yayi duk kokarin hanasa sai da yayi galaba a karshe na samu karfi na ja wani glass na kwada mai a kai wanda a take jini ya fara zuba, ban ko juya na sake kallonsa ba na ja kayana na bar gidansa dan bai cancanci in tausaya masa ba" idanun Shureim a take yayi ja jin abunda a ka ma Juwairansa, da Abdel bai mutu ba a yanda yake ji yanxu shima zai iya kashesa, karfin hali yayi yace "shi kuma na sudan infa? " Abdulkadir mun hadu ne a chat room, wen i take over sai in hau inyi chating da wayanta, so tym da suka je conference da Abdel na yi taking over naje muka hadu yace inzo gidansa in gaida mum nasa, wtout thinking twice na bisa ashe shima kaman sauran ne, ol wat men tink of is sex like shine kadai abunda ya kawosu dunia, like d odas he forced him self on me sai shima na kawar da shi, so it was all in self defence, nayine dan kare kaina da mutuncina" kowa na court room in shiru yayi yana jinjina wa wannan al'amarin, banda Bintalo da Bashir da naga sai zufa suketa yi tashi Bashir yayi yayi hanyar fita amma akace mai ba mai fita sai an gama shari'a dole ya dawo ya zauna.

Sharifa ce tayiwa Shureim alama da hannu akan yazo ba musu ya karasa ta miko mai wani abu a paper, ko da ya karanta murmushi yayi sannan ya dawo ga Juwi yace "Juwi kin tuna alkawarinmu nacewa zaki gaya mana y kuka ginu jikin Juwairah? Kai kawai ta gyada mai tana murmushi sannan yace "toh judge Sharifa tace ta kagu ta ji so pls yanxu mukeso ki fada mana" barrister Abbas da tun da yaji shaka bai sake magana ba shima murya can kasa ya tashi yace "nima na kagu inji" wani harara ta watso mai da ya sashi zama da sauri, daria ta kwashe da shi sannan tace "jst kidding, Abbas u n i r now frnds i assume" dan murmushi shima yayi.

Yanayin fuskanta ne ya canza sannan ta dago ta kalli inda Bintalo da Bashir ke zaune, kallon da take musu kallone na tsantsar tsana, ta jima tana kallonsu sannan ta dauke kanta yayinda su kuwa suka sadda kai kasa dan sun tabbata yau asirinsu ya tonu, cikin murya mai cike da damuwa ta fara magana "Ni Juwi Juwairah tayi creating ina ne at d age of 7 time da ta dawo zama da su Bintalo da Bashir. Sun nuna mata so da gata ainun har suka sata makarantar boko. Satinta daya da fara zuw wata ranar asabar, tana kwance a dakinta har bacci ya fara daukanta taji ana shafa mata jikinta, bude ido tayi taga Bashir haihuwar uwarsa a kan gadonta" kukane ya ci karfin juwi ta kasa karasa zancen, tashi Shureim yayi ya zo ya durkusa gabanta yana bata baki, dagowa tayi ta cigaba da cewa "she was just seven then but ba ko tausayi ya shigeta a wannan daren ya rabata da budurcinta" Shureim runtse idonsa yayi yayinda wasu hawaye masu zafi suka fara bin kuncinsa, handki biyu ya ciro ya mikawa Juwi daya shima ya share idonsa da dayan sannan yace "meyasa toh bata gayawa yayarta ba? Wani daria Juwi tayi wanda ke kunshe da ciwo sannan tace "mesa zata fada alhalin tana wajen" kallon da Shureim ya mata ya sa ta cigaba "yes she was there, i rekol evry bit of it, itane ma ta tuna mishi harda cewa "Bashir baka sa maganin da malam ya bamu ba" ta fada tana kwaikwayar muryar Bintalo "kuma ita ta tayasa riketa dan kar tayi gardama har ya gama abunda zaiyi da ita sannan ta dauketa ta mata wanka aka kira doctor har gida ya mata dinki sannan Bintalo ta ja mata kunne a can cewa idan ta yadda ta fadawa wani mutuwa zatayi"
Ba Shureim kadai ba, duk wanda ke kotun nan in ka duba fuskarsa toh zakaga hawaye, hatta Sharifa ma kukan take, da kyar Shureim ya tsaida hawayensa yace "Riya fa, how was she made? Kafun ta basa amsa sai yaga fuskarta ya canja wanda ya  tabbatar mai Riyace ta fito
Cikin shesheka itama ta fara magana "ni Juwairah tayi creating ina ne tana yar shekara tara, dts tym da Bashir ya sake afka mata for the second time,and this time around ko da ta so tayi gardama hadewa sukayi suka daddaketa sannan suka daureta har bashir ya samu ya biya bukatarsa da ita" Juwi ce ta sake dawowa tace "since then duk wanda zai keta mata haddi ni ke protecting inta ta hanyar kawar da shi,she has gone tru alot tun tana yar karamatar an mata abunda hankalinta bazai dauka ba kuma aka hanata kuka balle ta fadawa wa wani, an zalunceta zalinci mafi muni ace wanda kuka fito ciki daya da ita ta zabi a cutar da kai dan wani son abin dunia, Judge Sharifa Bintalo da Bashir don't deserve to live, kashesu ya kamata ayi" tana gama fadin hakan ta rufe idonta, wani dogon numfashi taja sai gashi tayi gaba kaman zata fadi, da sauri Shureim ya tarota ta fada jikinsa, kuka yaji ta fara a hankali shima bai san sanda ya kankameta ya bar hawaye suka fara zuba a idonsa ba, sai da sukayi mai isarsu sannan ya dagata cak a hannunsa ya maidata kujerarta sannan shima ya zauna dan jiran jin mai Sharifa zata fada............

_Sorry guys i said dis story is gonna b a short one,but yaki karewa,will try n round it up soon insha Allah_
*Billy Ladan*

*RIKITACCEN AL'AMARI*
~A short story~
~Inspired by true life events~
*Na Billy Ladan*

*END*
*Dedicated to Hauwa Suleiman Muhammad*

bintladan.blogspot.com
Kusan Minti biyar kenan Judge Sharifa na dafe da kanta tana tunanin yanda zata bullowa wannan *Rikitaccen Al'amarin* can ta sauke wani ajiyar zucia tareda dagowa, gyaran murya tayi sannan tace "koh Bintalo da Bashir na cikin wannan kotu? Kai kawai Barrister Shureim ya gyada hakan yasa tace "toh kotu na bukatar su fito gaban kotu yanxun nan".
A take aka fito dasu suka tsaya wajen amsa tambaya, Qur'ani aka miko wa Bintalo amma ko kallonsa batayi ba, dagowa tayi ta dubi Sharifa tace "ba sai na rantse ba wlhy zan fadi gaskia ko dan samu amun sassaucin shari'a, murmushi kawai shari'a ta mata, kallon Bashir tayi da yake ta mata idanu alamar kar ta fada amma sai ma wani harara da ta watsa mai ta juyo ta fara bayani dan ita bata ji zata iya shiga prison ba "wato ya mai girma mai shari'a wannan abu ya fara ne tun bayan aurena da Bashir da yan watanni inda yake shaida mun ana son kara mai matsayi a gun aiki sai dai malaminsa yace zai iya rasa wannan matsayi da har ma aikinsa baki daya, jin haka ya tada hankalina dan na kasance mai son abin dunia dan yana daya daga cikin dalilan da yasa na auri Bashir dama bawai sonsa nake ba, nan na shiga tambayarsa koh akwai abinda zamu iya yi dan ganin bai rasa aikinsa ba inda yake shaida mun cewar malaminsa yace lallai sai ya sadu da yarinya karama wanda kuma ya tabbatar bayan ita ba mai kusantarta, nan na bazama neman yarinya karama wanda zan dauko a matsayin yar aiki daga nan mu aikata mugun nufin mu a kanta amma hakan ya gagara. Kwatsam watarana yace in shirya muje Kauyenmu dan yana so yaga malaminsa nikuma sai na duba gida,isarmu ko gida bnje ba na bisa wajen malamin nasa inda a gabana yace dole yarinyar da zai kusanta ta zamto jininace ita ko nasa, nan ya nuna cewa shi kaf danginsu ba yar yarinya mai shekarun da ake bukata, ko kadan bn kawo Juwairah a raina ba amma jin abunda Malamin ne ke ambata akan cewa zamu samu in har wannan aiki yayi kyau nan na yanke hukuncin dauko Juwairah in zan bar kauyen, ko da na tashi tafia gida bn yadda munje da Bashir ba gudun kar a zargi wani abun, ko da nayi wa inna maganar tafia da Juwairah sam bata yadda ba hakan yasa na kira Bashir na gaya masa wanda a take yasa malaminsa ya mana aiki da ya sa dole su Inna suka bamu ita, satinta daya da fara zamanta da mu na biyewa mijina ya raba kanwata da budurcinta saboda son abin dunia da yayi mun yawa, a farko abun ya so ya dameni amma ganin yanda kudade ke shigowa ya sa na manta da komai muka cigaba da aikatar da mugun nufinmu akanta,wannan shine gaskiyar al'amarin da fatan baza a yanke mun hukunci mai tsauri ba,wlhy na tuba, sharrin zucia ne da kuma munafurcin mijina shi ya zugani, a taimaka kar a kaini prison" ta karashe tana goge dan guntun hawayenta.+

Bashir kam duk jikinsa yayi sanyi dan ya kasa dago kansa,ko da Sharifa ta fara tambayarsa kansa a kasa yake amsa mata, ba musu ya amsa laifinsa. Suna tsaye awajen har Judge Sharifa ta gama yar rubuce rubucenta ta dago tace "bisa kwakwarran shaidu da dalilai wannan kotu mai adalci ta wanke Juwairah daga tuhumar kisa da ake mata dan ta yisu ne yayinda bata cikin hayyacinta a dalilin mental condition da ke damunta

And according to shari'a an insane person can't be held accountable for his actions, kuma na yadda da opinion in Dr Abdulmajeed and my final decision rest at Juwairah is not guilty by reason of insanity so Dr Abdulmajeed zai tafi da ita psychiatric facility dan aje a bata kulawan da ya kamata har zuwa time da zata warke. And you, ta fada tana kallon Bashir "kotu ta yanke ma hukunci dauri with hard labor har na tsawon shekaru ashirin ke kuma Bintalo bisa wasu dalilai kotu ta yanke miki shekaru 10 kema with hard labor, d court is now adjourned" ta karashe tare da tashi, kallon side na Shureim tayi ta dan yi bowing kanta tareda mouthing congratulations, murmushi shima ya mata sannan ya maida hankalinsa kan su Bintalo da aketa tsalle ana ihun an shiga uku, kwace kanta tayi ta nufi gunsu Inna ta durkusa tana neman yafiyarsu amma ba wanda ya dago ya kalleta, har aka zo aka dagata aka fice da ita. Tashi Inna sukayi suka karasa gun Juwairah, tana ganinta ta karasa ta fada jikinta tana kuka mai cin rai dan yanxu ta tuno komai she dnt hv to hold it in anymore, mutane sai tausaya mata suke yayinda ake Allah wadai da hali irin na Bintalo. Rike da hannun juna suka fito harabar kotun inda suka ga har yanxu ba a tafi da su Bintalo ba dan ta tsaya sai Allah ya isa taketa aikawa Bashir tareda cewan saiya saketa dan ko ta fito bazata jirasa ba aurenta zata yi, wani daria yayi sannan yace "wlh sai dai ki mutu dan ni da ke mutu ka raba takalmin kaza kuma jira dole kiyi in fito mu sha talaucinmu tare" yin kansa tayi kaman zata dokesa akayi saurin sa shi a mota, tana ganin su Juwairah sun fito ta yo kansu ta durkushe gabansu tareda riko kafar Inna "Inna ki dubeni da idon Rahama kar ki gujeni a halin da nake, wlh nayi nadamar abunda na aikata ku yafemun ko zanji sauki a raina" batareda ta kalleta ba tace "Bintalo kinga irin abunda muke guje miki kenan amma kika kasa gani son abun dunia ya rufe miki ido kika auri wanda baki gama sanin halinsa ba har ya kaiki ga hanyar halaka, ban taba sanin za a iya hada baki a cuci wani da ke ba sai gashi kin nuna mun akan yar uwarki wanda kuka fito ciki daya da ita, bazan taba Yafe miki ba Bintalo bisa wannan abu da kika aikata wa Juwairahta kin ha'inceta kin cutarta da ita tun bata mallaki hankalin kanta ba sabida son abun dunia naki, nida hukuncin kisa aka daura miki da yafi mun dan shine kadai nake ji zai yaye mun bakin cikinki a raina, amma duk da haka zaki gani dan rayuwar kurkuku kadai ya isa kiyi hankali sannan duk ranar da kika fito kar ki yadda ki dawo gida, ki nemi wasu iyayen daban amma bamu ba" Abba ma kara jaddada maganar Inna na karshe yayi sannan ya bi bayar Inna aka barta daga ita sai Juwairah, dagota tayi daga durkushen da take sannan ta dubeta tace "koh ba komai Adda kin cika mun burina na rayuwa amma hakan bazai hanani ganin illar da kikayi wa rayuwata ba, bazan ce na yafe ba kuma bazan iya cewa ban yafe ba sai dai ga shawara, a zamanki a kurkuku kiyi kokari ki gyara tsakaninki da ubangijinki, ki nemi yafiyarsa sannan ki yawaita istigfari hakan zai kawo miki saukin halin da kike ciki" tana gama fadin haka ta juya itama ta barta tsaye a wajen, sosai take son Bintalo kuma take tausayinta sai dai tayi abunda baxata iya yafe mata a yanxu ba ko ta nuna mata tausayinta da take ji, taji dadin tafiyar da zatayi da Dr Abdulmajeed dan ko ba komai zata manta wasu abubuwan.
STORY CONTINUES BELOW

Karasawa wajen su Barrister Shureim tayi,sallama ta musu suka amsa suna mata murmushi, shiru tayi tana kallon kasa can ta dago taga duk ita suke kallo, mayar da kallonta kasa tayi cikin siririyar muryarta tace "baki bazai iya furta irin godia da nake ba agareku, bani da abun gode muku dashi, kun mun abunda bako zai mun ba a hakan kuma batareda kun karbi ko da sisina ba, i wil always b indebted to u two" Inna ne suka karaso suma sukayi nasu godiyar sannan suka wuce gida dan tafiyarsu zai kai jibi. Sallama Abdulmajeed sukayi shida Shureim kowa ya nufi motarsa.

Koda Shureim ya isa gida yayi mamakin jin gidan shiru, nan ya shiga dubasu amma shiru basa nan, fitowa yayi ya nufi dakin maigadi ya kwankwasa ya fito sannan ya tambayesa ko su Quraiba sun fita, nan ya shaida mai ai an kaita asibiti, a kidime ya bar gidan ya shiga motar ya figeta, wayarta ya shiga kira sai da ta kusa tsinkewa aka dauka, muryar sistarta Siyamah yaji nan ta shaida mai asibitin da suke, baifi minti biyar ba ya iso asibitin, straight dakin da take ya nufa, salim na ganinsa ya taso ya rungumesa yana kuka, dagosa yayi yana shafa kansa har yayi shiru sannan ya karasa bakin gadon Quraiba inda take baccinta cikin kwanciyar hankali, sai yanxu ya lura da yar raman da tayi, zama yayi tareda gaida Siyamah sannan ya tambayeta abunda ya sameta, fashewa kawai tayi da kuka tareda ficewa daga dakin, binta yayi da ido sannan ya juyo ya kalli Quraiba, tashi yayi yabi bayanta inda sukayi karo da Dr yana kokarin shigowa dubuta, komawa ciki sukayi ya gama dubata sannan suka wuce office nasa, sai da ya ga Shureim ya dan nutsu sannan yace "wato Barrister Shureim matarka na fama da cancer kuma yana end stage" ido ya zaro tareda cewa "cancer fa kace Dr,kuma end stage" kai ya gyada mai sannan ya cigaba da cewa "she has been diagnosed month ago, dan tace tana jin wasu symptoms but she didn't tk dem serious har yayi progressing, tym da ta zo ko mun ce zamu mata aiki dia is 80% chance she wunt mk it shiyasa ta zabi boye maka ta kuma ki a mata aiki, she chuz to enjoy d few time she has with u Salim" hawayene ya fara zarya a fuskar Shureim, da kyar ya iya jan kafarsa ya koma dakin Quraiba, zama yayi a kujerar da ke gabanta ya riko hannunta ya daga yayi kissing sannan ya dafa goshinsa da shi ya cigaba da kuka, a hankali yaji an kira sunansa ya dago ya kalli Quraiba da itama shi take kallo, matsowa yayi tareda shafa kanta, murmushi ta mai tareda cewa "congratulations habibi, i saw your case on TV,u did grt dear" hannunta duka biyu ya rike ya fara wani sabon kukan, da kyar ya iya tsaida kukarsa yace "y did u hide ur sickness from me Habibti, y? Dago fuskarsa tayi tareda share mai hawayensa sannan tace "u wia busy with d case hun kuma bana son abunda zai raba attention inka, nasan in har kaji bazaka cigaba da case inba and i nid u to win it so dt Juwairah wil liv" kawar da kansa yayi tareda cewa "surgery infa y did u refuse to do it? Juyo da kansa tayi sannan tace "dia was 80% chance i wunt survive it, dts y i chuz to spend d rest of d few tym i hv wt u guys,pls ka daina damuwa akai n dnt b mad at me, haka Allah ya kaddara, iya tym da Allah ya debar mun knan a dunia, rufe bakinta yayi da nasa dan bazai juri jin kalamanta ba, sai da suka zama breathless sannan ya janye ya kalleta yace "ki daina kirawa kanki mutuwa Habibti,cuta ba mutuwa bace and ba lallai bane abunda Dr suka fada ya zamto gaskia,u"ll not die insha Allah har sai mun tsufa tare kinga yan jikokin" murmushi kawai ta mai dan ita kadai ta san yanda take ji ganin idonsa kawai ya sa take daurewa.Ganin ta fara rufe idonta ya sashi ja mata blanket tareda pecking inta ya fita ya barta dan tayi bacci.

Ranar da su Juwairah zasu daga zuwa Korea suka nufi gidan Shureim dan yi mai sallama,nan suka samu labarin rashin lafiyar Quraiba,waya Abdulmajeed ya cire ya kirasa ya gaya mai inda suke. Ko da suka zo ba karamin tausayawa Quraiba sukayi ba dan duk ta canza in just few days, Juwairah kam har sai da tayi kuka, da kyar aka samu tayi shiru, da suka tashi tafia kememe tace ba inda zata sai an sallami su Quraiba ganin ta dage ya sa Quraiba cewa a basu waje zasuyi magana, sun dau kusan 20 minutes suna magana sai can ta fito dauke da wani envelope tana hawaye koh meh ta gaya mata oho, dakin Shureim ya koma bayan sunyi sallama sannan suka nufi airport. Sai da suka ga tashin su Inna sannan suka wuce suma.
STORY CONTINUES BELOW

*Bayan shekaru biyar*

Dr Abdulmajeed ne zaune da Juwairah suna yar hirarsu kallonta yayi cike da so da kauna yace "Dear gaskia yanxu kin gama samun sauki,yanxu test daya ya rage mana and you r fit to go sai aurenmu insha Allah" ya fada yana kinne mata ido, daria tayi tareda rufe fuskarta, sallamar da suka jiyo shi yasa su juyowa gaba daya, ba karamin mamaki sukayi ba ganin Shureim dan tun da tazo bai taba zuwa ba sai dai suyi waya, bata san lokacin da ta karasa da gudu ta fada jikinsa tana kuka kamar ranta zai fita, Dr Abdulmajeed da kishi ya gama cikasa fita kawai yayi ya basu waje, banbareta Shureim yayi daga jikinsa tareda zaunar da ita, kasa dagowa tayi dan sai yanxu take jin kunyar abunda tayi, da kyar ta daure ta iya gaida shi sannan ta tambayesa Quraiba, gani tayi yanayin fuskarsa ya canja, a hankali taji yace "satinku uku da tafia Allah ya mata cikawa, ban fada miki ba dan ban son inyi abunda zai bata therapy inki" hannu ta sa a bakinta dan hana sautin kukanta fita,da kyar ta iya tsaida kukansa ta mai ta'aziya tareda rokarwa Quraiba gafara.

A yan kwanaki biyu da Shureim yayi ya fuskanci cewa Dr Abdulmajeed na matukar son Juwairah kuma itama tana sonsa, dole ya hakura ya bar wa zuciyansa abunda ya zo dashi dan haka ma ya fara shirin dawowa Sudan.

Daren ranar suna zaune suna cin abinci ya shaida musu cewa zai koma washegari kuma zai bar Sudan gaba daya dan yana so ya je ya kara karatu, wani tari ne ya kubcewa Juwairah wanda yasa ruwan da ta sha fitowa, bata san ta kafesa da idanu ba sai da taji Abdulmajeed na tabata yana mata sannu sannan ta dawo hayyacinta. Aje fork dake hannunsa Shureim yayi tareda tashi ya musu sai da safe ya wuce dakinsa. Juwairah ma a daddafe ta karasa cin abincin nata ta wuce daki, envelope da Juwairah ta bata da jimawa ta dauko ta shiga karantawa

_Juwairah nasan yayinda kike karanta wannan wasikar babu ni a dunia,ga amanar Salim da Shureim na bar miki dan bawanda nake tunanin zai kula da su fiye da ke, na tabbata ke Rahamace a rayuwarsu baki daya. Yau zan gaya miki abunda Shureim ya kasa gaya miki, Shureim na bala'in sonki son da koni Quraiba bai taba mun ba amma taurin kai da son da yake mun da kuma gudun bacin raina da yake bazai barshi ya furta miki hakan ba. Kema a yar haduwar mu dake na fahimci kin kamu da son mijin nawa amma kema naga taurin kan naku iri dayane,kar ki bari kiyi abunda zai dameki daga baya, kar ki hanawa zuciyarki abunda yakeso, kar kiyi kuskuren auren wanda bashi kike so ba dan u"ll both end up bn hurt and at long last regret ur actions wen its late,u md me a promise of mkn ma wish cm tru on our last encounter n my only wish is to c u happily married to Shureim n u bn a mother to my Salim, pls grant my small wish n tk kia of my luvlis for me._
_with love Quraiba_
Ko da ta gama hawaye ya gama wanke mata fuskarta, rungume da wasikar tayi bacci a haka har Abdulmajeed ya shigo ya sameta, a hankali ya ja wasikar hannunta ya karanta, cikin sanyin jiki ya mayar mata wasikar tareda rufeta ya fito. Ranar da kyar bacci ya iya daukarsa
Da safe koda ta tashi da sauri ta fito dan ganin ko Shureim ya tafi,ganinsu suna zaune suna breakfast ya sata sakin ajiyar zucia da ya sasu juyowa su kalleta, a kunyace ta karaso ta gaidasu sannan ta zauna itama aka kawo mata breakfast inta, bayan sun gama ta wuce daki tayi wanka ta danyi light mk up tayi zamanta a daki. Knocking kofarta da aka shiga yi shi ya tadata ta bude, Abdulmajeed ta gani tsaye kallonta yayi sannan ya juya yace "kizo kuyi sallama zai wuce" daki ta koma ta sa hijab nata ta fito, sam taki yarda su hada ido haka sukayi sallama ta wuce dakinta yayinda su Shureim sukayi waje.

Bayan kaman five minutes Abdulmajeed ya shigo ya nufi dakinta, batareda yayi sallama ba ya shige dakinta ya ganta zaune ta daura kanta akan knees inta tanata sharban kuka, bai bi ta kanta ba ya wuce ya hau shirya mata kayanta a akwatinta, jin motsin yayi yawa ya sata dagowa taga abunda yakeyi, share hawayenta tayi tareda tashi ta nufi inda yake tace "Dr meh kake yi haka? Maimakon ya amsa mata ya bi gefenta ya dauko hijabinta ya mika mata, ba musu ta sa dan a zatonta barin asibitin zasuyi, jan trolley in yayi har zuwa wajen motarsa yayinda take biye da shi. Gudu yaketa zubawa sosai wanda hakan ba karamin tsorata Juwairah tayi ba, sam bata ma lura da inda suke zuwa ba dan duk a tsorace take dan bata son rough driving. Jin ya tsaya ya sata bude idonta taga a airport suke, sauka yayi ya zagaya ya bude mata, dan bata rai tayi tareda turo bakinta " wai ni ina zamuje ne, ka daukoni sai gudu kake dani ka wani bata rai sai kace na ma wani abun toh ni ba inda zani har sai naji inda zaka kaini" yar gajeriyar tsaki yayi tareda cewa "ki fito kar ki bata mun lokaci dan wlh in flight innan ya tashi ranki sai ya baci" fitowa tayi tana guna guni ta tsaya ya rufe motar tareda ciro trolley in ya shiga ja, binsa tayi a baya har cikin airport in, cikin sauri ya shiga duba Shureim ya kuwa hangosa zaune ya rike kansa a hannunsa, har Abdulmajeed ya zauna a gefensa ma bai sani ba sai da ya dan tabasa,dago kansa yayi idanunsa ya sauka akan Juwairah da tayi kici kicin da fuska, suna hada ido ta dan saki ranta sai dai haryanxu fushi take dashi da ya tafi ya barta da kuma boye mai feelings inshi gameda ita da yayi. Tashi Abdulmajeed yayi ya ma Juwairah umarni akan ta zauna, nan ya hadasu ya gaya musu dalilin zuwansu dan yasan tabbas suna son juna kuma koda sunyi aure da Juwairah bazai taba jin dadinta ba dan ba shi take so ba, tunda ya fara magana Juwairah take hawaye, ta san tana son Abdulmajeed amma son da takewa Shureim daban ne. Har Abdulmajeed ya karashe maganarsa bata bar kuka ba, ajiyar zucia Shureim yayi tareda cewa "Nagode Sosai Dr da irin wannan karamci naka sai dai bazan iya rabaka da ita ba,kai ka cancanta da ita ba ni ba sabida haka bazan rabaku ba" tashi Abdulmajeed yayi tareda aje mai passport inta dan dama tun jiya ya shirya mata da daddare sannan yace "u two r meant for each other kuma kuna son junanku but ur ego wunt let u accept dat" karasawa yayi inda take zaune yayi pecking goshinta tareda runtse idonsa dan hana hawayensa fita, bai ko sake juyawa ba ya bar wajen. Sai da ya shiga motarsa ya bar hawayensa suka fara gangarowa. Yana zaune cikin motarsa har sai da ya ga jirgi ya tashi sannan ya fice.

❄❄❄❄❄❄❄

*Bayan wasu shekaru*

Barrister Shureim ne ya shigo wani gida cikin hadaddiyar motarsa,parking lot ya nufa yayi parking sannan ya fito ya nufi cikin gidan fuskarsa dauke da murmushi, yana shiga falo Juwairah da ke jera abinci a dining ta nufosa da gudu tareda dalewa jikinsa tana "wlcm my Luv n super super congratulations my luv bisa nasarar da ka samu akan wannan case nakan" dan bata rai yayi tareda sauketa a jikinsa yace "wato ke baki jin magana ko,so kike ki kashe mun yara ko" yana gama fadin haka ya wuce dakinsa, cikin sanyin jiki ta bi bayansa dan tasan ta tabosa, ita sam mantawa take da tanata ciki. Zaune ta samesa yana cire takalmansa tayi sauri ta karasa ta tayasa cire wa sai wani dauke kai yake har tazo ta fara tayasa cire kayansa, "ina yaran" taji yana fada "suna gidan inna" ta basa amsa, hade hannuwanta biyu tayi tace "sorry luv" yar hancinta ya ja yace "kin fiye rashin ji Nawa" kafun ya kara cewa wani abun ta hade bakinsa da nata ganin abun nasu yafi karfi na yasa ni fita har ina tuntube.

Bayan wasu shekaru Shureim da Juwairah sun sami sauyin rayuwa sosai, dan Shureim na daya daga cikin lawyers da ake ji da su a sudan yayinda Juwairah itama tayi suna saboda different programs da take gudanarwa a gidajen radio da television.

Labarin Bashir kuwa watarana fada ya kaurace a kurkuku akayi rashin sa'a dan daba ya coka mai wuka a ido duka biyu ya makance, Bintalo kuwa gobara ce ta kama a prison nasu kan a karaso kansu har wutar ta mata illa yanxu gaba daya baka iya ganeta gashi an yanke mata kafafu.
Ranar da za a cireta a prison Juwairah ta tasa su Inna a gaba suka zo, yanda suka ga Bintalo dole ya sa suka sauko dan abun a tausaya mata ne gashi yanxu bil haqqi tayi nadama. Gidansu Inna aka wuce da ita dan cigaba da kulawa da ita, kullum tana cikin kuka da neman yafiyarsu. Ana haka suka samu labarin mutuwar Bashir duk da dai ba dadi basu wani damu ba.
Kasar waje Juwairah tazo ta fitar da Bintalo inda aka mata plastic surgery tareda samata kafar roba. Ko da ta farka taga kanta ba abunda take sai kuka, sosai tayi nadamar abunda ta aikata. Da suka dawo Sudan islamia ta nema ta shiga a can ta hadu da wani malami ta aura. Inda itama cikin kankanin lokaci ta zama malamar dan har karatu take wa matan aure a gida,kullum in ta ga mutum na son abin dunia dayawa takan mai wa'azi tareda bada misali da kanta.

Dr Abdulmajeed ma yayi aurensa inda yake zaune da matarsa a korea har ma sun kawo ma su Juwairah Ziyara.

Alhamdulillah!
Duka duka anan na kawo karshen littafina *Rikitaccen Al'amari* kura kuren da ke ciki Allah ya yafemun, darasin da ke ciki Allah sa ya amfane mu.


Post a Comment for "RIKITACCEN AL'AMARI COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...