RAGGON MIJI COMPLETE PART 1 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

RAGGON MIJI COMPLETE PART 1

RAGGON MIJI COMPLETE PART 1

- - Post a Comment

 RAGGON MIJI COMPLETE PART 1


faseelat yarinya ce and she's not above 21yrs tana da kyau sosai babban jiki ne daita fara ce sosai fuskarta is ready made ko ba tai kwalliya ba batada matsala abinda yafi daukar hankali ajikinta shine kugunta tanada babban kugu da big breast kusan ma sune suka sa ta kiban amma kibar ta me kyau ce saboda bata da tumbi bata da fadi, faseelat kyakkyawa ce de sosai, 

Gidansu matsakaita ne ba masu karfi bane kuma ba matalauta ba, mamansu ita kadaice awajen babansu su 5 ne mamansu ta haifa faseelat itace ta biyu kuma ita kadaice mace ta taso cikin gayu tun tana yarinya har girmanta mamanta cikin gyaranta take dayake ita kadai ce mace, yayanta sunanshi omer, se ita se abulkhair se ishak se auta Mubarak, 

Babansu meson karatu ne sam be wasa da ilimi ta sauke kur'ani kuma tagama secondry sede mamansu taki yarda tawuce makaranta, wai sanadin lalacewar yawancin yanmata kenan, babanta alhaji maaruf yayi iyakar yinshi amma ummi taki wai sede tabari setayi aure tayi, 

Yanzu haka faseelat bata zuwa koina se islamiya shima se weekend duk aikin gidansu itace keyi batada hutu ko kadan, ta kware wurin sanwa sannan kwararra ce wurin gyaran jiki saboda abinda mamanta ke koya mata ne, kullum ummi kamar yar 30yrs take saboda bata wasa da gyara kanta duk abinda ya shafi gyara ko abinci ko kwalliya wannan yasa abbansu yakasa yi mata kishiya dan ko kallon mace bayayi dan yasan inyaje gida tashi tafita. 

Har mazan gidan suma basa yawace yawace unlike other houses da namiji se ma ya kwana ba gida ba, su ko duk abunka karfe 10pm acikin gida takemasu.


Faseelat ba mummuna bace bare ace shiyasa batada saurayi kawai Allah ne be kawo ba har yau ba wanda ya taba tunkararta da kalmar so, wannan yana matukar damun umminta saboda ita burinta ta ganta adakin aurenta lami lpya kuma shine gurin kowace uwa akan yarta, shi ko abba be damu ba cewa yayi komi lokaci ne, 

itama faseelat abun baya damunta amma tanada buri a soyayya yadda take fara fari takeso, tanada kiba to mijinta ya zama siriri dogo, tana masifar son saje a fuskar namiji, yazama dole mijinta ya zama jarumi me karfin zuciya kuma sannan ya zama yana da rufun asiri da ilimi to shine mijin aurenta kuma shine burinta, 
So da dama takan zauna da mamanta su tattauna akan aurenta itade faseelat abun mamaki yake bata gani takeyi mamanta bata yarda da tarbiyyar da ta bata ba ,ko tagaji da ganinta kusa daita, 
DOWNLOAD HERE👈

Post a Comment for "RAGGON MIJI COMPLETE PART 1"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...