NAWAFF COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

NAWAFF COMPLETE

NAWAFF COMPLETE

- - Post a Comment

 NAWAFF COMPLETE


Yau antashi da tsananin zafi, saka makon ranar data kwalle🌞, mutane kowa yana neman mafaka, a karkashin rumfa ko bishiya.
    Ga k'arar ababen hawa data cika birnin na kano, dukda katafaren gosulo d'in daya cinkushe titin, dayawa mutanen dake cikin moto cin sun gala baita, da tsananin zafin ranar.
     Amma wannan bai hana 'yan tallah daf dalaba suna yayata tallar ababen sana'ar su, musamman masu tallar ruwa, saboda yanayin zafin mutane suna buk'atar ruwa mai sanyi.
       Nakai dubana bisa wata farar mota mai k'yawun gsk, wadda daka mata kallo d'aya kasan mai ita yagama wada tuwa.
    Wata k'yak'yk'yawar yarinya nagani kwance a bayan motar, farace saidai farinta bamai haskeba sosai, tanada kala irinna 'yan itopia, tanada dogon hanci da manyan idanuwa, kwance take abayan motar tana nazarin littafi.
    Agaba kuma direbane, tad'ago kai tareda fad'in balarabe kaga abinda nake jiye mana ko?, shiyyasa nace kar mu biyo ta nan, gashi har ina neman makara, kuma inada lectures yanzu wlhy.
     Balarabe ya ce, "kiyi hak'uri hajiya, wlhy banyi zaton zamu sami wannan cinkoson ba.
     Ta d'anyi k'aramin tsaki tana fad'i ni wlhy saima karasa abinda yake haddasa irin wannan cinkoson a garin kano?, batareda ta saurari sharhin da balarabe yake mataba ta bud'e motar ta fice.
      Tafito dai2 sanda wata jar mota 'yar k'arama ta tsaya saitin ta, ahankali  aka zage gilashin motar zuwa k'asa, wani had'ad'd'en saurayi ya bayyana, saikuma wani danake tunanin abokinsane.
    K'yak'yk'yawan saurayinnan ne matuk'in motar, kallo d'aya zaka masa ka gano yana cikin farin ciki, dan sai kad'a kai yake da alama wak'a yakeji, kuma wak'ar tana masa dad'i.
     Ya d'akko kwalin hollanddia yana sha ahankali yana cigaba da kad'a kai, harda had'e yatsun hannunsa biyu yana bugawa.
      Karku d'auka wannan k'yak'yk'yawar yarinyar shitake kallo, A'a ko kad'an hankalinta baya kansa.
    Jitai wani abu yadaki k'irjinta, da sauri ta kalli jikinta.
   Hummm kunsan miye kuwa??.
Ba wani abu bane illa kwalin hollanddia da gay d'innan yake sha, takuma bin jikinta da kallo, dan ganin yanda yogot d'in yay mata kaca2 da bak'ar jallabiyar dake jikinta, ta maida kallonta ga motar dan ganin wane wawane yay mata wannan aikin??.
     Saitaga mutum yana kallonta yana tuntsirar dariya harda dukan sitiyari, d'ayan saurayin dake gefensa ya d'ago yana kallonsa, ya ce, "kai malam lafiyarka kuwa?, kanata dariya kai kad'ai kamar wani shafar aljanu.
    Cikin dariya ya nuna masa yasmeen dake tsaye tamkar gunki tana kallon ikon ALLAH, tana mamakin wannan wane irin shashashan mutum ne, yayi mata abu amma yana nunata yana dariya.
     Mas'ud ya ce, "amma kaidai d'an iskane NAWAFF, yazaka b'atama yarinya jiki, kakuma rink'a yimata dariya??.
     Kasan kuwa wacece wannan kalli nomber motar data fito fa.
    NAWAFF ya gallama Mas'ud harara yana fad'in aii bani nace tazo ta tsaya anan ba tana yima muta ne iyayi ko?, dazakace nawani kalli nomber mota, to saimi idan na kalla.

Duk abunda suke fad'i Yasmeen tana jinsu, dan haka sai zuciyarta tak'ara tunzura, cikin fasifa ta k'arasa gurin motarsu.
DOWNLOAD HERE👈

Post a Comment for "NAWAFF COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...