MUTUM CE KUWA COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MUTUM CE KUWA COMPLETE

MUTUM CE KUWA COMPLETE

- - Post a Comment

 MUTUM CE KUWA COMPLETE


Sai kai da komowa suke a bakin lebor room din dake cikin wata had'ad'd'iyar asibiti, babban asibiti ne na kud'i , dake cikin jahar sokoto   mai suna *city premiere* ,

Maza ne su hud'u kallo d'aya zakayimasu kasan sun jik'u da naira sai mahaifiyarsu hajjah wadda Sam bazace ta haifi wad'annan alhazawan ba, bafulatana ce usul jikinta irin na fulanin usuline wanda jindad'i da Hutu ya 'boye tsufanta, sai wasu mata su biyu suma kallo d'aya zaka gane suma fa ba baya ba,

Dukkansu acikin damuwa suke sanadiyar matar dake cikin d'akin tana nak'uda tun safe take abu d'aya gashi yanzu har la'asar amma shiru ,gashi an sanar musu yaron cikin ya wahala sosai wannan magana ta girgiza zukatansu don sun d'auki son duniya sun d'orama cikin nan bama kamar hajjah wadda jin wannan maganar yasa har tafara yimasu kuka, dakyar suka samu suka lalla'bata, A can d'akin haihuwar kuwa suna ganin ikon Allah, saboda fiye da awa d'aya kenan da kan jaririyar ya fito amma sunyi duk iya dabararsu don su ida janyo jinjirar abun ya faskara ko gezau yarinyar batayi ba,

Babban abinda yak'ara firgitasu shine yadda jinjirar ta bud'e idon ta tana kalle-kalle tun bata ida fitowa   duniya ba , hakadai sukayi tsaye suna kallon ikon Allah, sai can wata da akecema sister maryam tayi k'arfin halin yin addu@ - addu@ sosai tayi kamun takoma nufar jaririyar da nudin janyota aikuwa tana jawota sai gata ta fito gaba d'aya harda mabiyar, nanfa suka hau murna suka d'aga yarinyar sukad'an jijjigata ganin haryanzu batayi kuka ba, amma ina tun sunayi a hankali har suka fara jijjigata da k'arfi amma Sam wannan jaririyar batada alamar zatayi kuka harsuka gaji suka dubata ko ina suka tabbatar da lafiya qalau take sai suka shiryata cikin wasu kayan sanyi masu matuk'ar kyau da tsada kayan pink color ne Wanda bak'aramun k'ara fito da kyaun  jaririyar sukayi ba, su  Kansu masu k'ar'bar haihuwar sai tasbihi sukeyi ga ubangijin da ya hallici wannan yarinya, duk ji sukeyi ina ace 'yarsu ce , suna ciki haka sai d'aya daga cikinsu ta d'an kai hannunta saman kuncin yarinyar tana mata alamar wasa, ai basu Ankara ba sai gani sukayi jaririyar ta 'bingiremasu da dariya harda kyalkyatawa, ai dasauri duk sukaja baya cikin tsananin tsoro da firgita jikinsu sai rawa yakeyi tuni suka nemi hanyar fita daga d'akin, har suna garuwa da junasu amma basu damu ba burinsu kawai suga subar d'akiN.....
DOWNLOAD PART 1 HERE👈
DOWNLOAD PART 2 HERE👈

Post a Comment for "MUTUM CE KUWA COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...