MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 3 Na Samira Harouna - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 3  Na Samira Harouna

MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 3 Na Samira Harouna

- - Post a Comment

 MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 3

Na Samira HarounaπŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.


Ina masoyan *Sajida*  da *Samira*  littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage*  da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da  kaunar da kuke musu inda suka zo  maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.


Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)πŸ‘Œ zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.


_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479*  Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar   *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._


_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_


Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.πŸ₯°πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *9*
Washe gari ta tafi makaranta kuma kamar kullum ana shiga hutun minti talatin duk suka had'e wuri d'aya dan ayi hirar duniya, saida ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya ta kalli Jamila dake kallon IPhone d'inta tana fad'in "Wai Mimi da gaske jiya ya baki wayar nan? Kai ina ma ni ce wallahi ta birgeni sosai."


Wani malalacin murmushi tayi tace "Kinga ban fad'a miki ba, jiya fa mutuminki na had'e dashi har mukayi magana baki da baki."


Da sauri ta kalleta tace "Shapi'u?" Harara ta dalla mata tace "Mayyar Shapi'u, to uban Shapi'u."


Dariya su Asma'u suka saka duk da dai basu gama shiryawa da ita ba, turo baki Jamila tayi tace "Mimi ban son cin zarafi, surukin nawa?"


Tab'e baki tayi tace "Kinga ni sheikh na had'u dashi nake son fad'a miki."


Da farin ciki tace "Lah! Sheikh Bala?"


Cikin jin haushi tace "Ke sheikh Balan wa? Sheikh Abdul Waheed nake fad'a miki, haba."


Ta k'arashe da d'auke kanta, duk zaro ido sukayi Jamila tace "Sheikh Abdul Waheed?"


Asma'u kuma kallonta tayi tace "Mimi ban sonki da k'arya ba fa, a ina kika ganshi ke kuma?"


Hararanta tayi tace "Tunda kinsan haka me yasa zanyi muku yanzu? Da wacce nake jin tsoro a nan?"


Jamila ce tayi saurin cewa "To ina kika ganshi?"


Gyara zama tayi tace "Jiya da dare ne na je siyowa Yaseen maganin zazzab'i, kawai na ganshi zai tsallaka titi har ya min magana..."


Yanda ta fad'a musu duk abinda ya faru yasa Jamila cewa "Tabb'! Mimi sheikh Abdul waheed ne fa aka ce mai bawa gwamna shawara akan harkar ilimi, sannan an ce shi kad'ai mahaifinshi ya haifa, kuma mahaukatan bilyoyi ya gada fa, uwa uba ga ilimin addini da Allah ya bashi, a hakane zaki ce kin ganshi a kan titi har ya shiga mota ya tuk'a? Mutumin da a wa'azi ma mutum biyu ne a bayanshi."


Cikin jin haushi ta kallesu su ukun tace "Yanzu mak'aryaci kuka d'aukeni ko me? Kun dai kunsan mutumin nan ba birgeni yake ba bare na yi k'aryar had'uwa da shi, tayiwu fa kawai sun san juna da Abbana ne."


Duk wani shek'ek'e suka kalleta alamar sam zancenta bai samu karb'uwa a wajensu ba, dan haka cike da alfahari tace "Ban wayata ke na nuna miki sanfiri."


Mik'o mata wayar Jamila tayi tana sake tab'e bakinta, karb'a tayi ta shiga jerin tΓ©lΓ©phone d'inta, lambar data gani mai jan rubutu data nuna an kira ba'a d'aga bΓ’ ta danna wacce ta mata kama sosai data Asas wacce ta sakawa sunan *d'an beauty*. Tana jin wayar ta fara k'ara tayi saurin sakawa a amsakuwa tana nuna musu su mayar da hankali kan wayar, duk zubawa wayar ido sukayi kamar zai fito daga ciki.


Ana d'agawa ta sake nutsuwa ta shiga caracterta ta jiya a gaban ustazu tayi shiru, daga b'angarenshi ne ya rangad'a sallama a sanyaye sosai, saida ta kalli Jamila kafin tace "Wa'alaikumus salam, barka."


Da sauri Asma'u ta k'yafaceta a kafad'a tana mata nuni da ido da hannu "Sheikh d'in zaki ce wa barka?"


Yatsina fuska tayi da sauri ta kalli wayar tana sauraren yana fad'in "Ryam antashi lafiya?"


A sanyaye ta amsa da "Lafiya lau sheikh."


A hankali yace "Ba sheikh ba, Abdul, ki kirani da Abdul Ryam hakan zai sa na ji nima bawa kuma ba kowa ba."


Da ido ta musu alamar ba kun ji ba? Ai na fad'a muku, jinjina kai sukayi suka sake kafe kunnuwansu, a nutse cikin murmushi tace "Wacece ni da zan sake maimaita wannan kuskuren, na jiya ma sub'utar baki ce."


D'an murmushi yayi har tana jin sautinshi kafin yace "Na so hakan, kuma akwai lokacin da zai zo na tursasaki fad'ar Abdul."


Da alamar tambaya duk suka kalli junansu, a nutse suka sake jin muryarshi yace "Ryam Abbanki ya dawo ne?"


Cikin rarraba ido tace "A'a bai dawo ba."


Rik'e hab'a Asma'u tayi alamar mamakin nan tana kallonta, cikin taushin murya yace "To me yasa kika kirani?"


Cikin murmushi tace "Tun jiya da kuke kira ne sai naji bana jin dad'in ganin lambarku a jan rubutun nan, shiyasa na karb'i wayar a hannun mama na kira."


Duk mamaki ne ya kusan kashe su Asma'u dake kallonta da saurarenta, ita kam ko a jikinta saima saurarenshi yana fad'in "Ba kina islamiyya ba?"


Da "Eh ina yi." Ta amsa, kallon agogo yayi a lokacin yace "Amma naga 10:14, kuna hutu ne ko?"


Jinjina kai tayi tace "Eh dake yau ban je islamiyya ba, saboda k'anina da baya da lafiya, jiya ma magani na siyo mishi muka had'u, shiyasa na zauna taya mamana aiyukan gida da kula dashi."


Cikin jin dad'i yace " Masha'Allah, Alhamdulillah, na ji dad'i sosai da kika kirani, na kuma gode."


A ladabce tace "Nima nagode, muna barar addu'a."


Lumshe ido yayi daga inda yake, to wai me yasa kowa ke fad'an hakane? Shin bakinshi yafi na kowa tsarki ne? Ko kuma waliyi ne shi da aka bugawa hatimin waliyantaka? D'an sauke ajiyar zuciya yayi yace "Insha'Allah, nima ina barar addu'arki."


Tana cikin k'yak'yabta ido yace "Zan sake kiranki anjima, ina wajen aiki ne."


A sanyaye ta amsa mishi sukayi sallama ta kashe kiran, cike da kuri da k'apapa ta shiga kallonsu a sama tana fad'in "Me na fad'a muku? Mak'aryaciya kuka d'aukeni ba."


K'wafa tayi ta mik'e tsaye cikin takon kuri da isa da k'asaita ta fita a ajin dan neman abinda za ta ci, kallon da Asma'u ta bita dashi ne yasa Jamila fad'in "Ke daina kallonta, Allah ne ya bata farin jinin nan sai hak'uri."


Harara ta galla mata tace "Na ce miki ina haushin hakane, ai baiwarta a jikinta take."


Sai lokacin kawai Aisha ta samu damar fad'in "Wallahi ni har birgeni take, farin jini ne da ita kamar k'asa mai tsarki, da babba da k'arami da tsoho da yaro mai kud'i da talaka kowa son ta yake."


Jinjina kai Asma'u tayi tace "Shiyasa ai take murza kambunta yanda take so."


Jamila ce tace "Kamar yanda idan ta shiga gidan sai labari ba."


Asma'u ce tace "Gaskiya ne kam, dan tana aure komai zai zama tarihi."                   *Asas*Kafeshi tayi da ido har ya gama d'aure takalminshi k'afa ciki ya mik'e yana sake nad'e hannun rigarshi, girgiza kai tayi tace "Yanzu Ashraf idan ka fita a haka waye zai kalleka yace d'an musulmi ne kai? Me yasa ba ka jin magana a kan saka k'ananan kayan nan."


Kallon kanshi yayi ya langab'e kai yace "Hajia basu min kyau bane?"


Hararanshi tayi tace "Wane maganar kyau ina maka maganar kimarka? Kasan da ko sheikh ya sha yi maka magana a kan saka irin kayan nan amma ka k'i ji."


Numfashi ya sauke ya had'e hannaye yace "Zan daina Hajiata."


"Yaushe?" Ta fad'a cike da katsalandan, murmushi yayi yace "Da zaran nayi aure, dan bana so 'ya'yana su tashi su ganni a haka."


Wata hararar ta masa tace "Oho! Kenan kai ma kasan ba abun kirki kake yi ba?"


Girgiza kai tayi ta dora da fad'in "Allah ya sawak'e."


Saida ya matsa kusanta ya sumbaci kuncinta kafin yace "Hajia zan tafi saina dawo."


Cike da gargad'i tace "Ashraf, bana so ka jima a wajen nan kamar yanda kayi jiya, ka dawo da wuri kaji."


Girgiza kai yayi yace "Hajia, me yasa kike damun kanki dani kamar wani k'aramin yaro? Na fad'a miki aΓ©roport kawai zan je saboda maganar tafiyarmu, daga nan kuma gida zan dawo."


Cikin rashin yarda ta nuna shi da yatsa tace "Da gaske zaka dawo yanzu?" Rik'e yatsarta yayi yace "Da gaske hajiata, wai me ye duk na damuwar nan? Naji sauk'i fa sosai Hajia, kuma ba gashi jiya har na samo miki wacce zata zama sarakuwarki ba."


Turo baki tayi irin shagwab'ar nan tace "Ba wani nan, har yanzu bata zama ba tunda sheikh yace sai ya gamsu da tarbiyarta."


Mik'ewa yayi tsaye daga rank'wafawar da yayi yana fad'in "Zai ma gamsu Hajia, na yarda da yarinyar sosai."


Jinjina kai tayi tace "Ashraf ina sake jadadda maka karka jima, idan ka wuce azahar zan fita nemanka da kaina."


Zaro ido yayi yace "Hajia nema na kuma? Anya kuwa zan iya yin aure nayi nesa dake?"


A marairaice kamar zatayi kuka tace "Nima abinda na fara tunani kenan, Ashraf larurar ciwon cikin nan naka ne yafi komai d'aga min hankali, shekara bakwai kenan ana fama babu likitar da bamu je ba, magani babu daga k'asar da ba'a aiko mana ba amma shiru, idan kayi aure kuma ba kowace mace ce zata iya jinyar ka ba, dan haka zan so ka zauna kusa dani, yanzu kaga fa wata biyu daya wuce daga waje abokanan ka suka kaika asibiti a some baka san inda kake ba."


Tallabo kumatunta yayi duka biyu yana fad'in "Hajiata, ki kwantar da hankalinki dan Allah, ina ji a jikina auren da zanyi shine silar warakar duk wani ciwo nawa insha'Allah."


Jinjina kai tayi tace "Da gaske haka kake ji?" Jinjina mata kai yayi alamar eh, ita ma jinjina kai tayi alamar shikenan tare da fad'in "Allah ya yarda."


Lumshe ido yayi yace "Ameen, saina dawo ko?"


D'aga kai tayi tana kallon fuskarshi, juyawa yayi zai fita ya d'aga mata hannu yace "Banda yawan kirana kuma karki fito nemana Hajiata." Dariya tayi ta gyara zamanta a kan kujerar tana girgiza kai.
                 *Maryam*Kwana biyun da bata lek'a ba yasa Maimuna aiko yaro kiranta, mik'ewa tayi duk da magriba ta kawo kai ta shiga gidan, da alama ta gama duk aikin gidanta zaune take ita kad'ai, dama bata tab'a haihuwa ba in kaga yara na mak'wabta ne.


Da sallama ta shigo hakan yasan Maimuna amsawa tana fad'in "Mimi ina aka shiga kwana biyu shiru ba'a lek'o ba?"


Dariya tayi tana zama kusa da ita tace "Wallahi aunty Maimuna karatu ne, kuma kinsan ni bana zuwa haka kawai in ba wani film ake mai kyau ba."


Ita ma dariyar tayi tace "Na sani, shiyasa ma da naga sun saka wannan nace su kiraki, nasan ke gwanar kallon film d'in india ce saboda soyayya."


Murmushi tayi tana kallon tvn data nuna mata, tabbas tana son film d'in sosai saboda soyayyarshi da kuma nishad'i da yake sakata a ciki, amma fa ita bata cika son mai-mai ba, bata son ta kalli abu yau ta kalla gobe, dan haka tayi shiru kawai ba tace komai ba, Maimuna ce ta mik'e tana fad'in "Bari nayi alwala an kusa kiran sallah."


Ita ma mik'ewa tayi tana fad'in "Aunty bari nima na tafi nayi sallah saina dawo anjima."


Kallonta tayi a maraice tace "Haba Mimi ki zauna mana kiyi sallahn a nan, wallahi gidan shiru ban da abokin hira duk ba dad'i."


Murmushin yak'e kawai ta mata ta jinjina kai, cire hijabinta tayi dan ita ba mutuniyar son zama da hijabi bace tana fad'in "Bari nayi alwala to."


Da kallo Maimuna ta bita, kai ita dai wallahi hallitar yarinyar na birgeta, kukkukup da ita digir-digir, kawai abinda ta fahimta Mimi irin mutanen nan ne da ko dusar dabbobi suka ci sai sunyi b'ul-b'ul, kumarinsu ba daga cin abinci bane hallita ce kawai. Dan yanzu ma riga da zane ne simple d'inki a jikinta, amma zanen sai ya mata hegen kyau k'ugunta na kad'awa sosai, ga rigar kamar dai sauran rigunanta ne masu tsayawa a iya kumkumi kawai. Farfajiyar ta fita tayi alwala a bakin panpo ta dawo ta d'auki hijab d'inta a lokacin an fara kiran sallah, sallaya ta d'ora suka kabbara sallah a tare har aka idar, suna gamawa Maimuna tare "Mimi zaki ci abinci?"


Girgiza kai tayi tace "A'a Alhamdulillah."


Mik'ewa tayi tace "Ina zuwa to." D'akinta ta shiga ita dai tana kallonta, jim kad'an ta dawo ta zauna tana aje wasu kaya a gaban Mimi tace "Mimi zab'a min wanda suka fi kyau a ciki? Ku ne yan zamani fa."


Dariya tayi tana k'arewa kayan baccin kallo, a hankali ta shiga dubawa saida ta cire guda uku ta mik'a mata tace "Aunty Maimuna kamar wannan sun fi ko? Kinga kalarsu ma ta dace da yanayin dare da kuma d'aukar hankali namiji, sannan sun fi sauk'i yakicewa a jiki."


Da mamaki Maimuna ta kalleta tace "Haka abun yake Mimi?"


Kunya ce ta kamata ta rufe ido tace "Haka dai nake tunani."


Jinjina kai tayi tace "To zab'a min wanda zan saka yau, kinsan fa Alhaji baya nan yayi tafiya amma zai shigo anjima."


Da tsantsar kunya ta nuna mata kalar fari tace "Ki saka wannan aunty, sannan ki shinfid'a zanin gadon da zai dace da kalar kayan, har labulenki ma idan zai yiwu komai ya zama kala d'aya."


Da farin ciki tace "Da gaske?" Jinjina mata kai tayi, cikin rarrashi tace "To mimi ko zamu je ki tayani saina canza d'in, na gyara komai wannan ne daai banyi tunani ba."


Murmushi ta mata tace "Ba komai aunty."


Mik'ewa sukayi inda Mimi ta sake cire hijab d'inta ta aje suka shiga d'akin, komai a gyare yake a kimtse, dan Maimuna kam ba k'azama bace ko wata wawuya, farin zanin gado mai kyau ta mik'owa Mimi ta karb'a ta d'auke waccen ta d'ora farin, ita kuma ta taka kujera ta cire labulayenta ta saka farare dan dama guda biyu ne a d'akin, bakin k'ofa da kuma tagar dake jikin bayan gado, suna gamawa Maimuna tace "Shikenan?"


Da d'an mamakinta ganin ko ba komai fa shekararsu shida da aure amma tana tambayarta ita da bata da auren, cikin rashin sakewa tace "Eh to ai har kun gama girki, zaku iya zuba abincinku a kwanukan da zasu dace da wannan kalar ma, sannan kuyi shigar da kuka san zata faranta mishi kuma yake so."


Fita sukayi daga d'akin da haka a sannu sannu har saida suka sha aiki ba kad'an ba, dan har jus saida Mimi tasa suka had'a, ita fa ba k'warewa tayi ba, kawai a harkar kalle kalle ne da karance karance duk ta iya wani salon kinibibi, da kuma wannan take tak'ama ko yau aka kaita gidan mai mace uku zata iya zama kuma ta birge.


Amir ne ya shigo da sallama suka amsa mishi, kafin yace komai Mimi tace "Kira na ake?"


Girgiza kai yayi yace "Mama ce ta ce na zo na duba idan kina nan, sannan na ji wai aiki kika ma aunty Maimuna."


Da fara'a Maimuna tace "Allah sarki, Amir ka fad'awa Mama aiki ne take kama min, amma har mun kusa kammalawa ma."


Juyawa yayi yana fad'in "To." Da kallo Mimi ta bishi yanda yake tafiya da k'arfinshi k'undul k'undul, mayar da hankalinta tayi kan lomar da take tace mata dafaffiyar mazark'waila da karanfani. Mik'ewa Maimuna tayi tana fad'in "Bari na shiga ko wanka nayi kafin ki tace na fito sai ki tafi gida Mimi tunda an fara nemanki."


Jinjina kai tayi alamar gamsuwa, shigewa tayi ita kuma ta ci gaba da tacewa, tana idawa ta d'auki madara peak d'in ta fasata ta juye mata a ciki haka ma maltina, d'auka tayi ta kai mata fridge ta aje, kankanar da suka yanyanka ta d'auki yanka d'aya ta juyo tana kai wa bakinta hannunta d'aya kuma tana gyara gashinta daya d'an sauko mata a kan goshi duk ya jik'e da gumin da take yi kasancewarta mai yawan gumi a kai musamman idan bata da kitso.


Cak ta tsaya tana neman sark'ewa saboda ido hud'u da sukayi da Alhaji Saminu, kallon tashin hankali daya wuce k'a'ida ne yake mata kamar zai afka mata, ya kasa ko motsawa bare ya had'a ko da yawu. A gaskiya dole ya samu yarinyar nan dan in ya rasata zai shiga matsala a yanda ya jima da soyayyarta, indai kud'i na samawa mutum alfarma to ba shakka zai kashe ko nawa ne ya sameta, ta mishi a yanda yanzu yake son ganin mace, komai na ta birgeshi yake, uwa uba wasu wadatattun mazaunai da Allah ya bata.


Da k'yar cikin k'osawa da tsaarguwa tace "Sannu da zuwa, ina wuni."


Da sauri ta dawo dashi hayyacinshi yana washe baki da fad'in "Sannu Mimi, aiki ake ne? Sannu ko? Kina lafiya?"


D'an murmushi kawai ta yak'o masa tace "Um."


Takowa ta fara yi dan ta d'auki hijabinta ta bar gidan, amma saiya gyara tsayuwa ya shiga k'ure gabanta da kallo zuwa wuyanta dake wani mul-mul dashi. Saida ta zo daf dashi zata wuce duk da kuwa kayan data gani a hannunshi nik'i-nik'i kawai ta ji ya rik'e hannunta ram a ciki na shi yana binta da wani kallo.


A tsorace kuma a gigice ta kalleshi tace "Subhanallah, kawu..."


Bai bari ta k'arasa ba ya aje ledojin hannunshi ya damk'a mata wata ledar yana sake murza hannunta yace "...
*Asma'u* 

*Aminatu*

*Rabi'atu* (Bintu Yusuf)

*Yagana ta*

*Rahamah* (Mom)

*Maryam* (Mom)

*Pretty Aeeshartyy*_Sannunku da k'ok'ari, Allah ya saka muku da alkairi, comment d'inku yafi na kowa._
*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *10*
Bai bari ta k'arasa ba ya aje ledojin hannunshi ya damk'a maya wata ledar yana sake murza hannunta yace " Wannan na ki ne Mimi, ki rik'e kinji karki ce a'a."


Da k'arfi ta ja hannunta ta raba da nashi tana binshi da wani fitanannen kallon mamaki, sake matsawa yayi daf da ita murya k'asa k'asa yace "Mimi lafiya? Kinga ki saurareni, indai zaki amince ki aureni wallahi zan miki komai a rayuwar nan, zan d'auki nauyin karatun k'annanki, zan canza muku gida na sabinta muku rayuwarku, Mimi amincewarki kawai nake buk'ata."


Da sauri ta ja baya saboda hannunta da yayi k'ok'arin kamowa, a razane cikin al'ajabi tace "Aure na fa? Ni d'in? Aunty Maimuna fa?"


Sake matsawa yayi ya samu kusanci da ita sosai yana fad'in "Mimi ai ba haramun bane, ina sonki wallahi kuma zan aureki, ki amince kin ji."


A kid'ime ta girgiza mishi kai tace "Gaskiya ba zan iya ba, kayi hak'uri kawu."


Da sauri ta k'arasa kan kujerar da hijabinta yake zata d'auka, tana juyowa suka had'e dan yana biye da ita ne, kamar jira yake dama a samu wannan tsautsayi sai kawai ya k'arasa rumgumeta jikinshi har rawa yake kar-kar-kar dan jaraba, dan shi fa irin mazan nan ne da kalami kawai zai iya tsumasu bare su ganki zahiri, ji yake kamar ya shige da ita d'akinshi ya samu sauk'i da sukuni, yana hawaltuwa sosai da azabtuwa akan yarinyar, siririyar ihu ta k'walla dan a rayuwarta haka bai tab'a faruwa ba sai yau, da sauri ya d'ora hannunshi ya rufe mata baki yana fad'in "Shiiiii! Haba mimi kamar ba wayayya ba."


Iya k'arfinta ta saka ta tureshi tare da fita a guje rik'e da hijabinta tana kukan takaici, duk da nauyin jikinshi bai hanashi shiga tashin hankalin da shi ma ya bi bayanta ba yana kiran "Tsaya, tsaya na ce."


Ganin bata saurarenshi yasa shi hangen mai gadi yace "Karka bari ta fita."


A gigice ta tsaya ta juyo ta kalleshi saboda mai gadin daya shiga kakkarwa rufe k'aramar k'ofar, kar ta fita yake nufi? Me zai mata? Tana ganin ya kusa k'arasowa ta durk'usa tana kuka tace "Dan Allah ka k'yaleni na tafiyata gidanmu, ni ba zan koma zuwa nan ba."


Yana zuwa sunkuyawa yayi ya kamo hannayenta ya mik'ar da ita tsaye, janye jikinta tayi daga na shi ta ja baya, cikin sigar rarrashi yace "Mimi ba zaki aureni bane? Ina sonki wallahi so na aure, ki fad'a min duk abinda kike so a duniyar nan zan miki shi da yardar Allah."


Girgiza kai tayi hankali a tashe tace "Ba zan iya ba, ba zan iya aurenka kawu, bamu dace ba ko kad'an."


Numfashi ya sauke yace "Kar ki ce haka mana Mimi, miye a cikin rashin dacewar mΓ» to? Ina sonki kuma ke ma zaki soni da mun yi aure, ina da kud'i zan iya baki komai kike so."


Cikin b'arin jiki ta kalli fuskarshi tace "Kud'i basu dameni ba, dacewata da mutum ita tafi komai mahimmanci a gareni, ba zan iya auren wanda bamu dace ba."


Juyawa yayi ya kalli k'ofar d'akin saboda tunanin kar Maimuna ta fito sannan ya kalleta yace "Yanzu dai ki tafi kinji, zamuyi magana dake a waya, bani lambarki?"


Ya fad'a yana mik'a mata wayarshi, a tsorace ta kalleshi tace "Ni bana da waya ai."


Wani sakaran murmushi yayi yace "Mimi ni ba kamar sauran mutanen bane da kike ninkesu ta baibai, nasan kina da waya wacce saurayinki ya baki, ki saka min lambar a nan kin ji."


Rarraba ido tayi cikin rashin gaskiya ta karb'i wayar tana fad'in "Dan Allah to karka fad'awa Abbana, wallahi hushi zaiyi dani."


Girgiza kai yayi yace "Karki damu, bana son abinda zai b'ata miki rai ai."


Saka mishi lambar tayi ta mik'a mishi wayar, karb'a yayi yana fad'in "Zan kiraki kinji sai mΓ» had'u."


Jinjina kai kawai tayi ta juya ta fita zuciyarta kamar zata fito tsabar b'acin rai da kuma shiga rud'u. Sai a k'ofar gida ta saka hijab d'inta ta k'arasa shiga cikin gidan,  Abbanta ta samu yana cin abinci akan tabarma, saida ta durk'usa tace "Abba sannu da zuwa."


Da sakin fuska ya amsa mata da "Yawwa sannu Mimi, har kin dawo ne?"


Jinjina kai kawai tayi dan shashek'ar kuka ce a lokacin ta zo mata, mik'ewa tayi ta k'arasa shiga d'aki ta cire hijabinta ta fito ta d'auki buta tayi alwala ta koma d'akin, ko da tayi sallah isha'i daga nan kan dardumar ta kwanta tana jin kamar ta daka ihu ta d'urawa Saminu ashar, dan ya sakata yanayin da babu mahalukin daya tab'a mata irin haka. Da wannan tunanin bacci ya d'auketa duk da tasan za'a ta kiran wayarta, amma bata damu ba tunda saida ta kasheta kafin ta saka a akwati, dan samarin na ta ba lissafuwa suke ba tsabar yawansu, kowa shi dai yana son ta kowa son yake yayi hira da ita, wani lokacin bata san d'aga waya ne dan tana magana da wani kiran wani ke shigowa, haushin wannan k'arar d'in-d'in-d'in kuma bata son ta.                 *Laraba* Ranar yau ta kasance ta musamman a wurinsu saboda farin cikin abinda zai riskesu, musamman da sukayi waya da rana ya sakΓ© tabbatar mata zai zo anjima, hakan yasa ta wuni cikin farin ciki da mantwaa da b'acin ran data kwana dashi, amma fa sam bata nuna mishi wannan haba-haban ba saboda ita ta tsani rawar kai ga namiji ma bare mace.


Tunda suka taso daga makaranta ta shiga sharar gidan tas, inda ta tura Amir a k'ofar gida tace ya share, dake lokaci lokaci ta kan yi haka sai Mama ba tayi mamaki ba, tana gamawa ta d'auki bokiti ta d'ibi ruwa a randa, d'aki ta koma ta cire kayan jikinta ta d'auro zani ta fito, duk'awa tayi zata fito daga d'akin a rashin kulawa yasa ta buga k'afarta a d'an dakalin dake bakin k'ofar, wata razanannar ihu ta saki tana kiran "Wayyo k'afata, mamana k'afata ta cire, wayyo Allah n..."


Tsawar da mama ta mata tana fad'in "Dallah yi wa mutane shiru uwar rakin tsiya."


Cikin hushi ta nufota dungui-dungui dan duba k'afar ta ta, d'an durk'usawa tayi tana kallon k'afar, wani dogon tsaki taja tana fad'in "Shirmen banza, ko gurjewa babu amma kike wa mutane wannan kukan."


Cikin kukan shagwab'a tace "Mama Allah da zafi, baki ji yanda na ji ba."


Juyawa tayi tace "Ai ke haka kike, da abunda ya kai na kuka da wanda bai kai na kuka ba haka kike, kina mace amma sai rakin sababi, dalilin da yasa kika yafe kitso kenan a rayuwarki, na ga yanda zaki rayu a haka."


Turo baki ta dinga yi tana mik'ewa ta nufi ban d'akin, dan gaskiya mama ta fad'a tana da jin zafi sosai fiye da kima, tana iya yin kwana tana kuka akan d'an abu da bai taka kara ya karya ba, uwa uba idan aka ce watanta yayi, har ta gama ba zaka daina ganin hawaye a idonta ba, shiyasa duk gidan basa fatan rashin lafiya daga gareta.                *Sheikh*


D'an murmushi ya saki dan lamarin na Asas kam ya fara bashi dariya, daga had'uwa da yarinya shekaran jiya duk ya damesu da zancenta, fatanshi d'aya a kan yarinyar nan ta zama ta k'warai, kamar yanda shi ma ya had'u da tashi a shekaran jiyar, a tare yasa a binciko masa komai a game da 'yan mata da sunansu ma ya zama d'aya, Allah yasa na gari ne da zasu zama abokan rayuwarsu, wannan shi ne burinshi.


Asas kam Hafsat yake kallo yana zuba mata zance da shirin tafiyarshi gidansu Mimi da zaiyi yanzu, hakan ne yasa *Abbakar* dake bi ma Eesha cikin ladabi yace "Amma dai tonton zan raka muje ko? Dan ina so na ga auntynmu."


A sanyaye sheikh ya kalleshi yana sakin murmushi, cikin fara'a Asas yace "Kana son ganinta kai ma? Ni kaina yaro a matse nake, amma kayi hak'uri idan na fara samun karb'uwa a wajen iyayenta yau, kaga jibi sai mu koma ka ganta."


Kallonshi sheikh yayi bai ce komai ba sai Hafsat da tace "Babu abinda zai sa ma su ce baka musu ba, zasu amince insha'Allahu."


Da zulud'i yace "Allah ya yarda aunty."


Wayar sheikh ce tayi k'ara babbar hakan yasa shi d'aukawa yana dubawa, mik'ewa yayi yana fad'in "Ina zuwa."


Fita yayi farfajiyar su kuma suka ci gaba da hirarsu cikin nishad'i, yana fita ya samu wani yaronshi da ake kira *Mudanseer*, hannu ya bashi sukayi musabiha kafin yace "Ya ake ciki? Ka kammala abin da na saka ka."


Kamar zai durk'usa ya sunkuya yana fad'in "An gama komai ranka shi dad'e, hak'ik'a a unguwar an bayar da shaida mai kyau a kan duka yaran, dan kusan kamar anguwarsu d'aya, wanda ya ban bayani a kan su ya fad'a min Maryam uku ke cikin layin, biyu 'yan mata sai d'aya k'arama, kuma duk kusan anguwar suna wannan islamiyyar ne dan ita tafi kusa dasu, a gaskiya dai babu wani b'atanci a kan duka biyun."


Lumshe ido yayi ya sauke ajiyar zuciya yace "Nagode."


Jinjina kai yayi yace "Sai dai kuma ranka shi dad'e d'ayar an fi kiranta da sunan Mimi, dan da k'yar aka samu wanda yasan asalin sunanta ma, an tabbatar iyayenta mutanen kirki ne, dan mahaifinta ma an ce yana zaune lafiya da kowa, d'aya Maryam d'in ce kuma a hannun kakarta tak ke wacce ta haifi babanta."


Wani murmushi ya kuma saki yana tunanin kenan wacce ke hannun kakarta ita ce Maryam d'in Asas, shi kuma ta shi ita ce ke gaban iyayenta, numfashi ya sauke ya sake bashi hannu yace "Nagode sosai."


Hannun ya bashi sukayi sallama ya fita shi kuma ya dawo falon kamar zaiyi tsalle dan murnan jin haka, dan shi yafi ma damuwa da Asas d'in saboda yanda ya ga ya zurma da yawa akan ta.


Shigowarshi shi kuma ya mik'e yana fad'in "Sheikh, ka bani wani wurdi nan na neman sa'a."


Yar dariya yayi ya girgiza kai yace "Bana da shi, ni ma nemanshi nake saboda abinda na saka a gabana."


Hannunshi Asas ya kama yana murmushi yace "Ya ustaz muje na ji to miye haka? Kar fa a zo kai ma yarinya ka samu zaka k'arawa yayata abokiyar zama kamar yanda kake fad'a."


Wata suka da Hafsat taji daga zuciyarta zuwa d'an cikin dake jikinta yasa ta saurin kallonsu tana mai tsaresu da ido, aje cokalinta tayi ba tare data d'auke idonta daga garesu ba, su kam juyawa sukayi suka fita sheikh na fad'in "Asas lafiyarka ita tafi damuna akan komai."


Suna fita farfajiyar ya kalleshi yana gyara tsayuwa yace "Sheikh nagode sosai da k'ok'arin da kake akan gaanin na samu lafiya, na tabbata Alhaji bai bar amanarmu a hannun da bai dace ba, Allah ya bamu ikon faranta maka kai ma."


Murmushi yayi yace "To miye a ciki? Mahaifinka namahaifina nono d'aya suka sha, mahaifina ne ya saki mahaifinku ya kama, duk abinda zan muku yan uwana na jini na yi ma."


Jinjina kai yayi yace "Hakane, Allah ya saka da alkairi."


Murmushi kawai ya masa yace "Saika dawo."


Jinjina kai yayi yace "Addu'arka fa sheikh."


Lumshe ido kawai yayi alamar to yana kallo har ya fita daga gidan a tsaleliyar hondarshi.Duk da ba had'uwa zasu yi ba amma haka ta shirya cikin ratsatsen leshen da Mas'ud ya siya mata a lokacin sallah, wani irin kyau tayi duk da bΓ’ kwalliya bΓ’ ce tayi mai yawa, turare ma yau na musamman ta bud'e a kwalinshi, d'an k'arami ne mai masifar sanyayyen dad'i mai sunan *mukhalat* ta shafa, mayafinta ta d'auka ta ce wa mama zata shiga gidansu Asma'u, bata hanata ba dan tasan mahaifinta ma yana k'ofar gida a lokacin dan ko sallah isha'i ba a yi ba.


Tana shiga a soron gidansu  Asma'u suka ci karo da yayanta da suke uba d'aya zai fita, tare gabanta yayi yana kallonta yana murmushi da fad'in "Mimi gari zaki tafi ne?"


Fuska a d'aure tamau tace "A'a, kauce min a hanya."


Wani murmushi ya kuma yi tare da gyara mata ta wuce ta barshi nan, tana shiga da sallama a bakinta, dayawa daga cikin mutanen gidan ne suka amsa har da Asma'u, idon kowa a gidan a kan ta yake yayin da suke shak'ar k'amshin tufafinta dana jikinta daya gauraye illahirin gidan, kowa zuciyarshi na girgiza tana jijjiga akan lamarin yarinyar. Mimi kam ko a jikinta sai ma hannun Asma'u data kama suka shiga d'aki tana fad'in "Wai ke miye haka? Dubi fa yanda kika yi wani gamin gambiza riga daban siket daban, a hakane zaki samu saurayi?"


Tsaki tayi sai Asma'u data fahimci yau kanta take neman juyewa kawai tace "Ina zaki je Mimi kikayi wannaan shirin haka?"


Murmushi ta saki tare da cire mayafinta ta aje akan gadonsu dake shirge da kaya tace "Ko ina, bana fad'a miki Asas zai zo wajen Abba ba, shiyasa na baro gidan."


Wani murmushi tayi ita ma tace "Allah dai ya nuna min Abba ya amince da Asas d'in nan ko hankalina ya kwanta."


Kallonta tayi tace "Idan Abba ya amince saina baki kyautar jaka goma."


Zaro ido tayi tace "Jaka goma fa? Ina ma laifin jaka guda."


Yatsina fuska tayi tana gyara zamanta da wayarta a hannu, bud'e tsaron wayar tayi ta shiga d'an daddanawa, hira suka dinga yi da Asma'u har aka kira sallah isha'i ta saka hijabin Asma'u ta kabbara sallarta dan da alwalarta dama, tana gama akan sallayar wayarta ta shiga vibration, d'auka tayi tare da sakin murmushi, Asma'u kanta murmushin tayi tace "Tunda na ke dake ban tab'a ganin an kiraki a waya kinyi murmushi ba sai yau, Asas kai d'an baiwa ne."


K'ala bata ce ba ta d'auki wayar ta d'ora a kunne, daga b'angarenshi yace "Maah, barka da dare."


 A sanyaye cikin b'oye farin cikinta ta k'irk'iro muryar gajiya da kasala ta saka tace "Barka, ya kake?"


Da fara'a yace "Komai ba daidai ba daga yanzu har sanda zan k'araso gidanku mu tattauna da Abba."


A hankali tace "Uhumm!" A shagwab'e cikin sangarta ta autanci yace "Maamah, dan Allah ki tayani addu'a Abba ya bani ke."


Da mamaki tace "To wai me ye idan ka rasani, ka daina jin tsoron zai hana maka ni mana, ka sameshi kan ka tsaye kawai."


Saida yayi kamar zaiyi kuka yace "Shikenan to, amma Mimi ni kad'ai nasan tashin hankalin da zan shiga idan na rasaki."

 

D'an murmishi tayi tace "Ba zaka rasani ba insha'Allah."


A tausashe yace "Allah ya amince." Shiru ne ya d'an biyo baya kafin sukayi sallama a lokacin ya kawo daidai da kwatancen data mishi tunda rana. 


Fitowa yayi daga motar yana gyara rigar shaddarshi gezna kalar ruwan k'asa mai duhu sosai wacce aka ma gajeren d'inki ya mishi kyau, saidai babu hula a kan shi sai gyaren kai irin na matasan zamani. Abba ne dasu Yaseen wanda yaji sauk'i suka jero sun dawo daga masallaci, ganin zasu shiga gidan yayi saurin matsawa yana musu sallama, Abba ne ya amsa tare da mik'a mishi hannu, lura d'Γ  yayi irin hallitar Allahn nan ce ta gajerun mutane yasa Asas cikin ladabi yace "Dan Allah Baba gidan malam Adam nake tambaya?"


D'an juyawa Abba yayi ya kalli Yaseen da Amir kafin ya k'arewa Asas kallo, duk da shigarshi ta yi kama data wayayyun yara ce kawai amma kuma ta fito mishi da haibarshi had'e da kamala ta cikakken bafulatani, dan haka ya d'an saki fuskarshi yace "Yaro ni ne malam Adam a dai layin nan, Allah yasa lafiya?"


Tarrr ya sake zaro ido a kan shi, daga k'asa ya sake d'aukowa ya kalleshi, daga shi har su Yaseen d'in duk tsayinsu bai wuce zuwa cinyarshi dan babu wanda ya kawo k'ugunshi, har gwara ma Amir ya d'an fisu tsayi da kad'an. 


Wani irin nauyi ne yaji tare da kunya sun kamashi, sai kawai ya tuna kalaman Mimi na safiyar shekaran jiya da take fad'in akwai baiwar da Allah ya ma iyayenta, shi ma idan ya gansu zai tabbatar da suna da baiwarsu. A take yayi saurin durk'usawa yana shafa sumarshi da fad'in "Ina wuni Baba."


Da murmushi Abba yace "Lafiya lau d'an saurayi, muna lafiya."


Gaisawa sukayi har saida Abba yace "Gashi kuma ban shaidaka ba? Daga ina haka?"


D'an d'ago kan shi yayi ya kalli su Yaseen, hakan yasa Abba cewa "Ku shiga ciki kunji."


Saida suka ga shigarsu kafin suka sake maido hankalinsu ga juna, a sanyaye cike da kunya yace "Abba dama mun had'u da Mimi..."


Tunda ya ji haka sai yace "Dakata samari, bari na kawo mana abun zama ko."


Cikin fara'a yace "A'a Abba da kun barshi, haka ma yayi nagode."


Gyara tsayuwa Abba yayi yana kallon sumar dake kan Asas yana fad'in "Dama mun had'u da ita ne, to na nemi na fara gabatar da kaina ne kafin na fara zuwa wajenta saboda a gaskiya aure ne ya kawoni ba wasa ba, shine na zo da kaina dan gabatar muku da kaina."


Numfashi Abba ya sauke yace "Yaro ya sunanka? D'an wane gida ne kai? Waye mahaifinka? Sannan me ce ce sana'arka?"


Ba tare da jin d'ar ba Asas yace "Sunana Ashraf Sabi'u, ni d'ana ga margayi Alhaji Sabi'u Aliyu Sharif Maina, ina zaune tare da mahaifiyata a unguwar Tchanga, sannan nayi karatu jarida ne amma ina kasuwa ne tare da d'an uwana sheikh wanda ya zama kamar uba gareni, dan gaba d'aya shi yake kula da harkar kasuwancinmu ni da 'yar uwata."


Jinjina kai Abba yayi yace "Masha'Allah, masha'Allah, yayi kyau haka, amma na ji ka ambaci Aliyu Sharif maina, kana nufin kai d'an uwan sheikh Abdul Waheed ne kenan?"


Da fara'a yace "Hakane Baba, mahaifinsa da mahaifina ciki d'aya suke fito."


Da farin ciki ba yace "Masha Allah, abu yayi kyau gaskiya."


D'an kallon Abba yayi yace "Saidai Baba akwai abu guda da ba zan b'oye muku ba."


Gaban Abba ne ya fad'i ya tsira masa ido, d'orawa yayi da "Baba shekara bakwai kenan da Allah ya jarabceni da wani azababben ciwon ciki mai tsanani, a duk shekarun nan mahaifiyata magani take nema min, amma insha'Allah komai ya kusa zuwa k'arshe dan yanzu haka muna ta shirin tafiya k'asar waje ne dan sama min magani."


Wata nauyayyen ajiyar zuciya Abba ya sauke tare da jinjinawa yaron sosai yace "Malam Ashraf wannan ai ba komai bane, ita larura tasan d'akin kowa kuma babu wanda Allah ya wuce ya jarabeshi da ita, Allah ya baka lafiya yasa a yi a sa'a."


Da murmushi yace "Nagode Baba."


Cikin murmushi da jin dad'i Abba yace "Masha'Allah, abu yayi kyau, Allah ya shi albarka."


Gyara tsayuwa yayi yace "Insha'Allah idan na shiga ciki yanzu zan tuntub'i yarinyar a kan maganarka, idan ta amince to fak'at, insha'Allah zan nemeka sai na maka bayani, bana da tamtama akan zuri'ar su sheikh, ina ji kai ma mutumin kirki ne kamar shi, ba zanyi bak'in cikin damk'a amanar 'yata ga wannan ahali ba."


Wuuuuu! Asas yaji kamar zaiyi kwasan karan mahaukaciya da Abba ya d'aukeshi ya goya, ko a haka aka tsaya yasan kam zai samu shiga da izinin Allah, dan haka bakinshi har kunne ya shiga godiya yana mishi addu'ar Allah k'ara girma da lafiya da d'aukaka da sauransu, Abba ma cikin farin cikin yau *uwar ta shi* bata yi masa jaye-jayen nan ba ya shiga shi mishi albarka, da haka suka rabu Asas ya d'auki hanyar gidan sheikh dan tsaigunta masa wannan labari mai armashi.


 Mimi ma da tun tsayawar motar ta lek'o tare da Asma'u tsaf ta k'are masa kallo ta kalli Asma'u tace "Gaskiya guyen nan ya had'u, kinga wani mahaukacin shiri kamar yau ne d'aurin aurenmu."


Kallon Asma'u tayi ta kama hannunta suka koma ciki tana fad'in "Ai dole ma Abba ya amince, inba haka ba kuka zanyi."


Dariya kawai Asma'u tayi har suka shige d'akin suna yar hirarsu.
             *Masha'Allah*Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.


Ina masoyan *Sajida*  da *Samira*  littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage*  da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da  kaunar da kuke musu inda suka zo  maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.


Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)πŸ‘Œ zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.


_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479*  Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar   *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._


_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_


Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.πŸ₯°*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *11*Ko da Abba ya shiga gida kam ya kalli mama yace "Ina Mimi ne?"


Kallon Amir tayi sannan ta kalleshi tace "Tana gidansu Asma'u har yanzu."


Shi ma kallon Amir yayi yace "Je kira min ita."


Gyad'a kai yayi ya mik'e ya fita, 'yar kujerar robar da Amir ya tashi ya zauna yana fad'in "Bak'o na yi yanzun nan, kai uwata da kwashe-kwashe ake, ni ko a ina ta kwaso farin jinin nan? Yarinya kamar wata 'yar sarauta."


Wani murmushi Mama tayi ta saci kallonshi tace "Farin jini ko shirme, hauka ke damunta yarinyar nan."


Girgiza kai yayi yace "Harda farin jini ga uwata, ki duba ki ga ba dan bud'e mata ido da nayi ba da yanzu gidan nan bai zama dandalin tara kowane jahili da sakarai ba?"


Yar dariya tayi tace "Allah dai ya shirya mana ita."


Da fara'a ya amsa da "Ameen." D'orawa yayi da "Yanzu fa kam indai har ba zata saka shirmen nan da ta saka game da lamarin yaron nan Mas'ud ba, to Mimi kam ta dace da miji na gari mai hankali."


Cike da tsantsar damuwa Mama tace "Ni wallahi a tsayar da ranar aurenta shi zai sama min kwanciyar hankali, dan lamarinzamanin nan da rayuwar da Mimi ta saka kanta tana kayar min da gaba."


Jinjina kai yayi yace "Ai dai kin shirya aurar da ita ko?"


Sunkuyar da kai tayi ba tace komai ba, murmushi yayi yace "Indai har komai zai zo mana da sauk'i, to insha'Allahu auren uwata ba zai wuce wata d'aya da rabi ba, dan ni kaina bana son ganinta a k'yal-k'yal d'in nan, tun muna sanin inda take samu wata rana zata rufemu ta bai-bai, duk da muna shaidar halayenta amma ai yaro ka haifesa ne baka haifi halinsa ba."


Cike da tabbaci tace "Tabbas hakane, Allah ya mana jagora."


"Ameen." Ya fad'a a dai-dai sallamar Mimi da Amir a tare, amsa musu sukayi har suka zuba mata ido tana sunkuyawa tun bata k'araso garesu ba ta durk'ushe, kusan a tare suka saki murmushin jin dad'in yanda Mimi take matuk'ar girmama su, tunda tayi wayo ta mallaki hankali ta daina tsayawa a sanda suke tsaye, dukansu hakan na musu dad'i fiye da kima kawai dai basu tab'a nunawa bane, saidai kullum suna mata addu'ar Allah ya bata yaran da zasu mata biyayya ita ma fiye da yanda ta musu.


Cikin nutsuwa Abba dake kallonta yanda kanta ke k'asa yace "Mimi, kinsan wani yaro mai sunan *Ashfar*?"


Da sauri ta d'ago kai sai kuma ta sunkuyar da kanta tana murmushi, Mama dasu Yaseen duk tintsirewa sukayi da dariya hakan yasa shi rarraba ido yana kallonsu, cikin had'e fuska yace "Wai lafiya dariyar ku kuma?"


Cike da kunya mama tace "Malam ai sunan ka fad'a ba daidai ba, ina kyautata zaton Ashraf ne ba Ashfar ba."


Sai lokacin shi ma ya ma kan shi dariya yace "To ni na sani ne, suna ne gashi nan dai idan uwaye suka saka ma yaransu."


Kallon Mimi yayi yace "Kin san shi ne?"


D'an sunkuyar da kai ta sake yi tace "E Abba."


Tsareta da ido yayi yace "Ya zo yanzu gidan nan, kuma izinin neman zuwa wajenki yake, shin kin amince da haka?"


Shiru tayi saida ya sake cewa "Kin amince?"


A hankali ta jinjina kai alamar eh, shi ma jinjina kai yayi yace "Shikenan tashi kije, zan d'anyi bincike a kan yaro na k'ara sanin halayenshi duk da dai d'an babban gida ne, gashi d'an manyan mutane kuma jinin malamai, amma ki sani uwata wannan karan ba zaki min iskancin nan ba, wallahi kika sa na shiga maganar nan kika sake kunyata ni Mimi sadakarki zan bayar."


A zabure ta d'ago tace "Sadaka Abba?"


Yatsina fuska yayi yace "K'warai kuwa, kina shakkar hakane? Ki jaraba ki gani."


Shiru tayi sai mama dake murmushi, tana so ta ce a bayar da sadakar ta ta ai zai fi, amma kunya da kuma girmama sunan sarakuwarta musamman da ya zamana a gabanshi take, Abba ne yace "Tashi ki shiga ciki."


Mik'ewa tayi zata shiga ya bita da kallo yana fad'in "Uwata ba dai zaki daina saka wannan sangen ba ko?"


Juyowa tayi ta durk'usa tace "Abba na daina fa, kawai idan zan shiga gidansu Asma'u ne ko aunty Maimuna nake sakawa fa."


Jinjina kai yayi yana kallonta ta mik'e ta shige d'akin kamar ta shiga taka rawa tsabar farin ciki.


*Yau* alhamis bbu karatu, hakan yasa tunda safe tayi shara da wanke wankenta ta kammala, tana idawa gaban mama ta durk'usa tace "Mama bani dala arba'in zan siyi k'osai da bredi nayi kari."


Wani murmushi Mama tayi tace "Ina ce jiya kinga tuwo aka dafa? Sannan kinga miyar da aka yi a matsayin mahad'in tuwon? Shi ne kike neman dala arba'in a hannu na?"


Girgiza kai tayi tace "Mimi idan ina da dala arba'in d'in da zan baki ai zan iya taimakawa mahaifinku ta hanyar yi mana cefanai me kyau muyi miya."


Wani huci ta sauke da tunanin mafita, ita fa tana da kud'in matsalar tambayar da zata sha yasa take b'oyewa, d'an kallon maman tayi tana karkare akaihunta dake jikin gajerun yatsunta tace "Mama to bari na ga ba zan rasa ba kam a jakata."


Mik'ewa tayi ta shiga ciro jakunkunanta masu kyau dake jikin hannun gado, zaune tayi ta shiga lalubarsu tana zazzagewa kamar gaske,  Abba ne ya shigo da sallama d'akin suka amsa, shigowa yayi yana kallonta yana fad'in "Ke kuma lafiya? Me kike nema?"


Cikin ladabi tace "Abba dala arba'in nake fatan samu a nan."


"Me za kiyi da ita?" Ya tambaya kai tsaye, amsa ta bashi tana ci gaba da lalabawa da fad'in "Abba abun kari zan siyo."


K'uri ya mata da ido, duk da yasan halin Mimi tana da saka kanta a uku a wasu lamura, amma maganar tuwo kam tunda yarintarta ne bata son cin shi, shiyasa basa matsa mata da sai ta ci d'in, saidai yana tsoron yanayin rayuwa, baisan ina rayuwa zata kai ta ba nan gaba, ya zatayi kenan? Idan fa su iyayenta sun d'auka wani ba zai d'auki haka ba, laluba aljihunshi yayi ya ciro talatin yana fad'in "Karb'i nan, je ki siyo abinda zaki ci."


Kallonshi mama tayi tace "Bata kayi wai?"


Shiru yayi yana kallon mimi data mik'e da sauri ya ta d'auki hijab ta saka ta fita, k'arasa shiga yayi ya zauna bakin gadon da kyau yana fad'in "To ya zamuyi in ba'a bata ba? Ta fita waje ta nemo muke so? Ai kinfi kowa sanin bata cin tuwo, hakan ba dan d'aukarwa kai bane ko kuma k'arya, hakane take tun fil'azal."


Numfashi Mama t sauke tace "To yanzu daka bata su kana da kud'in ne?"


Girgiza kai yayi yace "Allah zai dubemu ya bamu wasu insha'Allah."


Jinjina kai tayi tace "Allah ya bud'a mana."


"Ameen." Ya amsa dashi kafin ya mik'e yace "Zan fita yanzu, insha'Allah zuwa anjima zan dawo na kawo muku abinda ya samu."


Nan ma jinjina kai tayi tace "Allah ya bada sa'a, Allah yasa a dace."


Amsawa yayi da ameen ya fita a gidan, kwanar daya shiga anan ya samu Mimi tsaye bakin kaskon mai suyar k'osan, murmushi ya saki ganin ta wani d'aure fuska ta dafe k'ugu, yasan saboda su Maryam da su Na'ima na wurin ne dan basa shiri ko kad'an. Har saida ya kawo daf da ita zai wuce ya kalleta yace "Mamana da an baki ki wuce gida kinji."


Sai lokacin ta farga dashi hakan yasa ta saurin sunkuyawa tace "To Abba."


Wucewa yayi ita kuma ta mayar da kallonta ga mai k'osan, su Na'ima kam bushewa sukayi da dariya har da tab'awa inda Maryam ke fad'in "Wa ya ga d'an k'wak'ur, dunk'ul-dunk'ul kamar zai shige a k'asa, a haka kuma aka haifffffffff..."


Saukar marin daya zauna a kumatunta ne yasa ta jan harafin na k'arshe, bata gama fahimtar me ya sauka a kan ta ba Mimi ta kuma kifa mata wani marin, tuni ta canza yanayinta daga nutsatsiyar nan zuwa mahaukaciyar k'arfi da yaji, dan kuwa bakin wuta ta jawo a cikin murhu ta shiga tik'awa Maryam tare da cakumar hijabinta. Cikin tashin hankalin samarin dake gefe zaune da kuma mai k'osan duk sukayi kansu, dan Na'ima na ganin haka ta daka da gudu ta shige wani gida tana fad'in ta kashe Maryam, da k'arfi Bello ya karb'i iccen hannunta daya rage babu wuta a jikinshi yana fad'in "Haba Mimi da hankalinki, me ye haka? Me ya had'aku?"


Kafin ta bashi amsa muryar wani saurayin ta daki ku'nuwansu yana fad'in "Inna lillahi! Ta kashe yar mutane fa."


Duk kallon Maryam sukayi da zafin duka da iccen wutar nan yasa ta fad'uwa a sheme, dan hijabinta ma duk yayi shaidar ya ci wuta, kafin ka ce kwabo wurin har an taru daddazon jama'a, yanda ake ta cacar maganar ana tuhumar Mimi yasa mai k'osan ne cewa "A'a fa! Domin Allah yaran nan basu da gaskiya, ba dan basu da tarbiya ba ai iyaye sun wuce gaban wasa, kuma hallitar iyayen Mimi ai Allah ne ya hallicesu haka, shi ne suka tsaya suna mishi dariya harda shak'iyanci saboda ya wuce ta nan, ni fa ban ga laifinta ba wallahi 'yar halak kenan."


Ruwa aka shafawa Maryam ta farfad'o tana fashewa da kuka da zagin Mimi tana fad'in sai ta rama, Mimi kam uwar k'asaita da isa da fad'in rai, a lokacin da kakar Maryam ta iso lokacin ta matso kusan Maryam d'in tace "Wallahi ba dan anyi gaggawar k'watarki ba, da sai na miki wanka da ruwan man nan, na kasheki na kashe banza wallahi."


Juyawa tayi ta shiga takawa da k'arfi har k'irjinta na wata nutsatsiyar kad'awa a cikin hijabinta, tsuguno tayi gaban farantin k'osan da aka kwashe ta jawo farar leda, a nutse ta shiga k'idayawa kanta k'osan har ta zuba daidai kud'inta, mik'ewa tayi ta kalli mai k'osan ta aje kud'in akan kujerar katakon ta tace "Ga kud'in nan, na talatin na zuba, ko d'aya ban k'ara a kai ba."


Cikin takon izza kamar wacce ta ci kwalliya ta shiga takawa har ta k'arasa gida ta barsu nan ana cecekuce, tana shiga hannayenta ta wanke sosai ta d'auki ledar k'osanta ta shige d'aki, yanayinta sam bai nunawa mama wacce wani abu ya faru ba, dan haka bata tambayeta komai ba sai kallonta da take jefi jefi tana cin k'osan da d'a-d'aya, hayaniyar Zara ta ji da alama dai biyota sukayi a kawo shedarta gida, dan har kukan Maryam take ji wiwi, a sauk'ak'e tayi murmushi tace "Hummm!"


Mama da taji abun a tsakiyar gidansu fitowa tayi dan ta d'auki murya, abun kamar wasa sai kuwa tsohuwar nan Zara ta d'aga musu hankali, dan ta dage sai an bi mata hakk'int dan an ga ita marainiya ce, in ba haka ba kuma zata yi k'arar Mimi wajen yan sanda. Mama baiwar Allah wacce da k'yar ma take kallon ciwon Maryam d'in dan doguwa ce ita ma ta shiga bata hak'uri da jajantawa ganin duk inda jikinta ya samu bakin wutar nan ya fara d'urar ruwa ya mata bororo, saida makwabta suka shigo suka tayata bata hak'uri amma fa ta ce zata jiran uban Mimi ya dawo saita nuna mishi abinda ta ma Maryam.


Duk hargagin da ake tana d'aki zaune tana jin su, Mama kuma kawaici ne ya hanata shigowa ta mataa magana, saida aka ci aka sid'e mama ta shigo tana k'are mata kallo, bata yarda ta d'aga kai ta kalleta ba, sai ma mik'ewa da tayi ta fito ta jefar da ledar k'osan ta d'ibi ruwa ta shiga wanka.


Saida ta gama ta shigo d'akin ta gama shafa mai ta jawo akwatin k'arfenta tana duba kayan da zata saka ta ji mama tace "Mimi kin kyauta yanzu?"


Ba tare data juyo ba tace "Mama, karki shiga zancen nan dan Allah, ba Maryam ba wallahi ko waye a garin nan ya nemi raina min iyayena sai na illatashi, saidai a kasheni ni ma."


Tsuru ta mata da ido tana kallonta ta mik'e tana k'ok'arin saka pant tana kare jikinta da zanin data d'aure k'irji, tsaf ta gama shirinta cikin doguwar rigar atamfa mai kyau, hoda kawai ta shafa da d'an man leb'e kafin ta kashe d'aurin d'an kwalinta, hijabinta ta d'auka bleue wanda ya dace da kalar atamfar ta saka takalmi masu kyau ta kalli Mama tace "Mama ni zan wuce, baki da sak'o wajen Iya?"


Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi, bata hanata fita ba dan duk alhamis dama ta kan je gidan kakarta data haifi mamanta ta wuni a can, ranar juma'a kuma ta kan yi wanki ne sannan ta shiryawa kayanta zamansu a cikin akwati, hakan yasa take da tsari a kan komai. Girgiza kai tayi tace "Ki gaida Iya, nima zan shigo gidan watakila gobe insha'Allah."


Jinjina kai tayi tare da d'aukar jakarta mai kud'i da kuma wayarta ta fita, unguwar kam tayi shiru a lokacin dan yara duk sun tafi makaranta, a nutse ta shiga takawa a k'afa dan ba nisa ne da gidan ba gaban islamiyarsu ne kad'an.


Tana k'arasawa gidan da sallama ta shiga a k'ofar tana fad'in "Salam salam, ina tsofaffin gidan nan wai? Har yanzu suna nan da ransu?"


Iya Delu dake k'ofar d'akinta zaune ne ta tarbeta da fad'in "Uwarki ma sai ta mutu ta barni ni da mijina."


Dariya Mimi tayi tana k'arasawa gareta tace "Haba dai Iyeye, ina kika tab'a ganin haka? Ai mutuwa dole ce ko?"


Takalminta silipas ta d'auka zata jefa mata daidai fitowar malam daga d'aki yace "A'a! A'a karki fara."


Da shagwab'a Mimi ta k'arasa gareshi ta rik'e hannunshi kan ta a kafad'arshi tana fad'in "Ranka shi dad'e ka gani ko? Na fad'a maka matarka bata so na."


Kallon Iya yayi yace "Ba saΓ― kin fad'a ba na gani da idona, ke dama haka kike mata?"


Kallon Mimi yayi yace "Amaryas ya kike so nayi da ita?"


Murmushi ta saki ta Iya tace "Kin gani ko? Ki bani hak'uri saina yafe miki, inba haka ba kuma zan sa mijina ya yanka miki ticket."


Dak'uwa ta mata tace "Kin jima baki saka d'in ba, dama fa ina cike da haushinki yarinyar nan."


Dariya tayi ta kalli malam tace "Malam wai dan ban mata wanki ba a ranar, kuma fa sai da taga nayi lalle kawai zata ce na mata wankin tsofaffin kayanta, amma ynzu ba gashi na zo ba sai nayi."


Murmushi malam yayi yace "Ai idan ma ba zaki iya ba ki bari idan na dawo na fansheki."


Girgiza kai Iya tayi tace "Kana iya wankin dama kake barina na wanke maka na ka kayan?"


Dariya sukayi sai Mimi da tace "To ai saboda aikinki ne dama, kuma lada kike samu."


"Fad'a mata dai amayata." Ya fad'a harda bata hannu suka tapa, lokacin kawai suka nutsu suka gaisa sosai tare da tambayar iyayenya, saida suka gamsu kafin malam ya musu sallama ya fita suka bishi da addu'a, saida ta ga b'acewarshi ta d'auke kanta tana tunanin duk yanda akayi shi ne ta yi, shiyasa ta zama doguwa a cikin iyalinta, dan ita dai shi ne dogo a cikin kakaninta, wacce ta haifi mamanta ma wadarce yar duk'ul, wanda suka fi mahaifinta ma dukansu gajeru ne. Dan kakanin na ta ma sun bata labari dalilin dagiya da kakanta yayi ya auri Delu (wacce ta ke bin maza uku ko sama da haka a haihuwa) yasa duk danginshi suka juya mishi baya, dan a lokacin ana canfa komai ne ana ganin aurensu ba alkairi bane, hakan kuma zai jawo musu gauraya zuri'a da masu gajeruwar hallitar nan, amma gashi suna zamansu lafiya har suka haifi yayar mamanta wacce uta ma haka take gajera mai sunan *Sahura* sai kuma *Shapi'atu* sannan mamanta ita ce k'ara.


Cire hijabinta tayi tana zaman kan tabarmar da fad'in "Iya me kika aje na ci ne gidan?"


Hararanta tayi tace "Komai, uwar kwad'ayi."


Turo baki tayi amma ba tace komai ba dan a lokacin tana jin wayarta na vibrations wacce ta kunna a kan hanya, jin shiru yasa Iya cewa "Bari dai na d'auko miki d'umamen tuwo, tunda na ga yau alhamis zaki zo na tanadar miki shi."


Dariya tayi tace "In dai tuwo ne Iya ki ci abun ki kam."


Dariya kawai Iya tayi ba tace komai ba, jim kad'an ta fito daga d'akin ta mik'o mata langar (kwanon samira😭πŸ˜₯ a da fa sai yar gΓ’ta ake ma jere da su, ynzu kuma yar gatar ma k'walele suke mata saboda tsada😜), karb'a tayi tana bud'ewa, da sauri ta kalli Iya tace "Iyeee! Iya dad'i kuka ci ne jiya?"


Zaune tayi tana murmushi tace "Gashi kuma ke ma zaki ci ba."


Aje kwanon tayi gabanta tare da saka hannu ta d'auko tsokar naman ta jefa baki, duk da girkin tsofaffi ne amma dad'in ma na musamman ne, dan daga jin d'and'anon zaka san a nutse aka yi aikin, babu k'arni ko kad'an saboda yaji kayan k'amshi ga kuma uwar daddawar da aka saka hakan yasa shi zama kamar naman kai.


Tsaf ta cinye naman tana jin kamar kar ya k'are kafin ta mik'e ta shiga d'akin, saida ta saka wayar a silent sannan ta shiga aikin gyarawa Iya d'akinta kamar yanda take yi a kowane sati, saida ta gama ta had'o kayan wankin ta fito dasu waje, sabulu Iya ta bata inda ta zauna kan kujera 'yar tsuguno ta fara wankin suna hira da Iya cike da armashi.Haka ta wuni a gidan kakanin nata cikin farin ciki ba tare data amsa wayar kowa ba a wannan wunin, har bayan sallah magriba tana tunanin shiga d'akin Iya ta d'auki wayar ta duba sai kuma Iya ta zaunar da ita, wasu k'ullikan magani ta bata tana fad'in "Wannan mai duhun ki dinga wanka dashi, d'ayan kuma hayak'i zakiyi, sai d'ayan kisha a hura ko kunu."


Wani iska ta furzo tace "To fa Iya! Matsalata dake fa wallahi, da an had'u sai kin bΓ’ mutum wannan abubuwan."


Hannu ta kai kamar zata bigeta tace "Ke ni bana son iskanci, ke a yanda kike d'in nan kina ganin da ban jik'aki da wannan abubuwan ba da yanzu bakin duniya ya barki ne? Ko farin jininki kin d'auka haka kawai kika sameshi? To ni ce nan na shiga na fita tun kina k'arama na miki turaren farin jini."


Da mamaki tace "Yo Iye ina ga ma ke kika hallice ni haka ko?"


Duka ta kai mata hakan yasa ta tserewa a guje ta shige d'aki tana fad'in "To kaji Iya da rigima, Allah ya yi ni da farin jinina ki ce wai ke kika shiga kika fita, ta ina kika shiga to bare ba ki fita?"


Daga nan zaune Iya tace "Wallahi na sameki d'akin nan sai na ci uwaki Shapi'a, yar banza mai zubulin larabawan maroco, ba dan kina da d'an tsari a jikinki ba da yanzu ba kina nan a lalace ba."


Mimi kam ba tace komai ba dan a lokacin tana duba jerin sunayen wanda suka kirata, kama daga d'an beauty, bak'uwar lambar da take kyautata zaton ta Saminu ce, d'an wahala da kuma sauran 'yan wahalan suna take masa baya, har da d'an ajinsu na islamiyya da sauran lambobi barkatai. Sai lambar Salma data turo mata hotunan ta wanda aka had'a da suke nuna an kawo lefennta, taji dad'i sosai kuma saida tad'ora a status a take. Murmushi kawai tayi ta sake kashe wayar dan kar Iya ma ta gani ba tare data tuntub'i lambar kowa ba.       *Bayan kwana biyu*


A kwana biyun nan babu kiran wayar data d'aga musamman ma bak'uwar lambar data fi kyautata zaton ta Saminu, dan ko kallon k'ofar gidan bata sake yi ba tun daga ranar, dan jiya Maimuna har shigowa tayi da kan ta dan dubata, amma tana jin sai ta nuna bacci take a d'aki kawai har ta ban gidan tana jin tana wa mama k'orafin ta tafi ranar bata sani ba. Duk wani abu da zai b'ata mata rai ne yanzu bata k'aunarshi tunda daren jiya Abba ya bata izinin sauraren Asas idan ya zo, ba wannan ne yafi komai faranta mata rai ba kamar yanda ya ce ya turo magabatanshi, duk da tana jin d'ar a kan hakan dan bata san wane iri ne su d'in ba.


Da wuri suka gama shiryawa ita da Asma'u zasu je ganin kayan Salma da basu samu an kawo dasu ba, tun a kan hanya suke hirar Asas saidai ba wani sani ne da su ba sosai.


Suna karya kwanar gidansu dan isa bakin titi suka had'e da motar Muttak'a, saida ta feso wani iska a bakinta tare da furta "Iska na wahalat da mai kayan kara."


Tsayawa sukayi suna kallo har ya fito fuskarshi a had'e babu alamar wargi, yana tsayawa gabanta ya shiga kirta mata wani kallo irin na 'yan k'waya mai tsoratarwa, da yatsa ya nunata yace "...
*Alhamdulillah*πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *12*Yana tsayawa gabanta ya shiga kirta mata wani kallo irin na 'yan k'waya mai tsoratarwa, da yatsa ya nunata yace "Ke wannan wane irin rashin mutumci ne da ake kiranki baki d'aga? Akan me zaki tsaya kina min wasa da hankali ne wai? Dan kinga ana sonki ne zaki tsaya yi wa mutane iskanci? Mimi surarki da albarkatun da Allah ya hore miki a jiki ba zasu hana ni daddarza miki buru'uba fa, ki kiyayeni kinji na fad'a miki."


Tunda ya fara magana suke kallonshi kowace gabanta na fad'uwa sun yi sak'e, dan gaba d'aya yanayinshi da alamu sun nuna wani abun yasha dan idonshi ma a jajir suke, duk ta daga ciki kam a mugun bala'in tsorace take, amma a zahirinta sai ta k'i nunawa a fuskarta bare kuma jikinta, dakewa tayi kawai tana binshi da kallo da matsakaitan idonta, sai kakkauran leb'enta na sama data turo gaba amma fuskarta a had'e sosai. Ganin yanda take kallonshi sai kuma ya sassauta murya yace "Mimi, dan Allah ki d'auki wayata kin ji, damuwa nake shiga sosai idan ina kiranki ba kya d'aga min, kin gani ko Mimi?"


Ya fad'a yana nuna mata k'irjinshi yace "Wallahi a nan ne kawai nake jin zafi, bansan me yasa ba amma an jarabceni da sonki sosai, Mimi zaki aureni?"


Da sauri ta yatsina baki a ranta tana fad'in "Kana d'an k'wayar? Allah ya tsareni."


A zahiri kam ko alamar magana ma ba tayi ba sai binshi da ido, cikin wata irin murya yace "Mimi ki min magana mana, bana son shirun nan naki fa, ko dai yan jan ajin ne suka motsa?"


Da sauri Asma'u ta kalleshi sosai tace "Eh wallahi su ne, ni ma tunda muka fito har yanzu bata min magana ba, sai fa kana hak'uri da ita."


A rikice a kuma shagalce yayi ram da hannun Asma'u yana fad'in "K'awar matata, dan Allah ki fad'a min tana so na? Tana baki labari na wata rana?"


Mutsu-mutsu Asma'u ta fara na son ya sake mata hannu, ganin bai saketa ba yasa Mimi d'ora hannunta akan na shi hannun dake rik'e dana Asma'u, kallon hannayen nasu duka sukayi, hannun Asma'u dake da sirkin fari mai masara, sai na Muttak'a dake bak'i wulik, sai kuma na Mimi dake da kauri da tuwon hannu ga shi kuma jajir akan na su. Washe baki yayi tare da sakin hannun Asma'u ya kalli Mimi yana fad'in "Mimi na kinji lallausan hannunki kuwa? Shi yasa kullum nake k'ara son ki."


Wata uwar harara ta wurga masa tare da kama hannun Asma'u ta rik'e gam, cikin amon muryar gargad'i tace "Kar ka sake tab'a jikinta, bana so."


Fizgar Asma'u tayi suka barshi nan tsaye, juyawa yayi ya bisu da kallo da d'umbin mamaki, amma kuma sai yayi murmushi yace "Ai ce wa tayi bata so, kishina ne take wallahi, da bata jin so na ai ba zatayi kishi na ba, daga yau na daina Mimi ba zan kuma kula kowace mace ba ma, amma fa idan kin min alk'awarin aurenmu nan kusa."


Tunda suka barshi babu wacce tayi magana saida taxi ta d'aukesu sukayi nisa, da k'yar Asma'u ta sauke ajiyar zuciya tana fad'in "Kin gani ko? Abinda nake fad'a miki kenan Mimi, wallahi mutumin nan d'an k'waya ne na gaske."


Wani dogon tsaki taja tare da d'aga mata hannu alamar ya isa tace "Kinga dallah ba'a son yin magana akan waccen shashashan banzan."


D'auke kanta tayi ta juya tana k'ara had'e fuskarta sosai alamar hushi, babu wacce ta k'ara magana har suka isa gidansu Salma ana shirye shiryen magriba.


Saida suka fara gabatar da sallah kafin suka zauna kallon lefen, sosai kayan suka birge Mimi suna kallo kuma tana bata labarin Asas daga had'uwarsu har matsayar da ake kai yanzu.


Wayarta dake cikin jaka ta samu ta cire ta a silent ne ta shiga ruri, saidai sautin kiran ya tabbatar mata da layinta na Moov ne ake kira wanda ba sosai ta cika aiki da shi ba, d'aukar jakar tayi ta ciro wayar ta duba lambar, gabanta ne ya tsinke ya fad'i sakamakon ganin lambar sheikh ta fito, yanda tsoro da fargaba suka ziyarce ta ne yasa Salma lek'o screen d'in wayar tana fad'in "Besty halan wani jakin ne kika samu."


A rashin sanin me tayi da kuma jin zafin abinda Salma ta fad'a kawai ta kai mata bugu a baya tana fad'in "Ke ce jaka marar mutumci, wannan d'in?"


Salma da taji zafin bugun sosai ta dafe bayanta tana fad'in "Wai-wai-wai! Ni kika daka haka besty?"


Tsaki tayi tace "Dan Allah ni ku min shiru na amsa kiran ya sheikh, kinsan abun laifi ba kad'an yake a wurinsu ba, ni kuma ina so mu rabu lafiya da shi wallahi."


Shiru kam sukayi suka daina k'wak'waran motsi, danna ok tayi tare da saka amsakuwa ta aje wayar akan wani akwati mai kaya. Sheikh da tashin hankali ne ya d'ugunzuma shi har ya saka shi kiranta bai shirya ba shi ma yayi shiru, a kwana biyun nan yake jin sabon abu a game da yarinyar, matuk'ar son had'uwa da iyayenta yake sosai, amma har yanzu bata kirashi ba ta ce Abbanta ya dawo, sai kawai ya kasa hak'ura ya d'an dannawa lambar kira, dan so yake idan komai ya tabbata ayi aurenshi tare da Asas wanda yau yake sanar dashi an ce ya tura magabatanshi, kuma yayi alk'awarin tafiya anjima tare da kawun Ashraf d'in.


Kamar babu wanda zaiyi magana sai kuma ya rangad'a sallama a tausashe, d'an numfashi ta sauke ta amsa mishi kamar yanda ya mata, d'orawa tayi da fad'in "Barka da yammaci, anwuni lafiya?"


Murmushi ya saki daga inda yake yana mamakin me yasa ita bata iya kambama abu ba? Asma'u dai kallonta take tana kuma mamakin yanda take gaisawa da babban mutumin nan, haka, a tausashe ya amsa da "Lafiya lau, ya kike?"


Da fara'a da kuma ladabi tace "Lafiya lau, ya fama da mu?"


Murmushi yayi wannan karan ma mai sauti yace "Fama da ku? Ke zan tambaya Ryam ya aka ji da hak'uri da mu?"


Murmushi ita ma tayi tace "Alhamdulillah, amma ai mu ne iyayen k'iriniya."


Yar dariya yayi yana jin wani nishad'i na ratsashi, a hankali yace "Ryam kar ki ga na kiraki ki d'auka na haukace fa, a gaskiya ina son sanin idan Abba ya dawo ne, a matse nake sosai da son tattaunawa dasu."


A d'an ladabce da kuma sigar mamaki tace "Me yasa haka? Wani abu ya faru ne?"


Saida ya girgiza kai kamar yana gabanta kafin yace "Ba komai, kawai dai zamuyi magana ne a kan ki."


Tsam tayi ta kalli su Salma da Asma'u tana musu alama da ido a kan ta kuma? Saita nutsuwarta tayi tace "A kai na malam? Allah yasa dai ba laifi nayi ba."


Murmushi yayi bai ce komai ba na tsayin dak'ik'u kafin yace "Ryam, shekaruna sun fara ja gaskiya, saidai a shekarun nan nawa na ji ina son yin aure sosai, shin zaki *iya aure na*?"


Wani bahagon fad'uwa gabanta yayi har saida ta dafe k'irjinta da hannu ta waro ido tana kallon wayar, aurenta? Sheikh Abdul waheed? Da sauri ta zabura ta d'auki wayar ta cire amsakuwar ta d'ora a kunne, saidai bakinta ya gaza furta komai, d'an sautin murmushin shi ta ji yana fad'in "Na yi tunanin haka Ryam, nasan zaki ce na miki tsufa dama, ni kaina nasan wauta nayi dana bari zuciyata ta fara k'aunarki, ba komai zan hak'ura."


Jikinta yayi mugun sanyi duk sai take jin ba dad'i, da k'yar ta d'aga labb'anta tace "Ni ban ce fa."


Cikin fara'a yace "To me kike nufi da shirun kenan?"


Sai kuma ta kasa bashi amsa ta k'yale, wani murmushi ya sake yi yace "Ina jin ki mana, zaki iya aurena a haka?"


A zuciyarta tace "Ba zan iya ba gaskiya, ka min tsufa Abdul."


A zahiri kuma sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsar k'afarta cikin fitar da kalmomi da d'ad'aya tace " *Zan iya mana*, ai ba shekarun ne abun dubawa ba, nagartar da kuma dacewa."


Lumshe ido yayi daga inda yake tare da sakin murmushi, shiru kamar ba zaiyi magana ba sai kuma yace "Da gaske Ryam?"


Jinjina kai tayi tace "Eh, gafarta malam."


Cikin jin dad'i yace "Kenan kin amince yanzu na zo gidanku neman aurenki?"


Rarraba ido tayi tana tunanin abun yi, gaskiya har zuciyarta take jin bata son b'ata mishi rai, shiyasa ko kira yayi a na farko take d'agawa, amma shi kan shi Asas da take begen yin hira da shi bata damuwa dan ta share kiranshi, gashi tun had'uwarsu ta farko ta mishi k'arya da dama, bata so ya gano hakan zai zubar mata da kimarta, kawai ta fad'a mishi y'a zo ta tabbata idan ya zo za'a ce an bayar da ita, daga nan ita kuma saita cire layinta na Moov ta shiga sha'aninta, zai manta da ita ya kuma shiga rayuwarshi, idan kuma dole ne k'ara auren to zai nemi wata. Da wannan shawarar tayi ammana kawai ta sanyaya murya sosai tace "Eh, amma sai Abba ya dawo."


Da sakin fuska yace "Naji dad'i Ryam, yaushe Abban zai dawo?"


A hankali tace "Nan da kwana biyu ne inji Mama."


Jinjina kai yayi yace "Shikenan Allah ya nuna mana, zan kashe waya dan bana son kaucewa shari'a, magana da nayi da ke ma babu izinin mahaifinki saina nemi afuwarsa akan haka, saida safe."


Jinjina kai tayi ita ma tace "Saida safe." Aje wayar tayi ta sauke ajiyar zuciya, kallon Asma'u tayi ta mik'e tana fad'in "Tashi tashi malama mu koma, hankalina a tashe yake wallahi na yi wa malam k'arya."


Mik'ewa Asma'u tayi tana fad'in "Ke kuwa me yasa kikayi haka to?"


Saida ta saka hijab d'inta tace "Ba zaki gane ba Asma'u, muje kawai."


Salma ma mik'ewa tayi suka fita tana fad'in "Besty zan kiraki fa ki bani labarin wannan sabon kamun."


Dariya kawai tayi tace "In kika kira ban d'aga ba karkiyi hushi."


Dariya ita ma tayi tace "Wane hushi kuma? Ai har na saba, shiyasa na matsu iyayenki su san kina rik'e waya wallahi."


Da sauri ta shiga takawa tana fad'in "Bari kedai, zasu sani kinji." Da azama suka fita kamar wasu masu laifi suka samu taxi suka nufi gida, a taxin kam yaua saida sukayi baram baram dan Asma'u fad'a ta mata akan me zata mishi k'arya? Babban mutum ne fa ya zata mayar da shi wani shashasha haka? Ita kumaa ta ji zafi har sukayi fad'a, ana saukesu kowace ta shige gida babu mai yi ma wata magana.


Tunda suka dawo take d'aki kwance tana waya da Asas d'inta, da ta ji motsi za'a shigo take saurin b'oye wayar har sai ta ji shiru, a haka har Amir ya shigo yana fad'in "Mimi Alhaji ne ya aiko yaro yana kiranki ki kama ma aunty Maimuna aiki."


Zaune tayi cikin jin haushi tace "Kai je ka ce masa bana nan, jaraba kai."


Juyowa yayi yana turo baki ya fito, saukowa tayi ta durk'usa k'asan gadon ta jawo akwatinta ta saka wayar, ta mik'e kenan Mama ta shigo tana fad'in "Wace buru'ubar ce yau kika tashi da ita da zaki k'i zuwa kiran Alhajin, Maimuna ce bata jin dad'i ya ce ki je ki kama mata aiki."


Turo baki tayi ta rarumi hijabinta akan gado tace "To." Hanyar fita ta nufa Mama tace "Yanzu aikin da zaki masa ne kike wannan kumburar? Mimi anya kina tunawa da alkairi kuwa?"


Sake kumburo fuskar tayi tare da k'arasa fita a d'akin ta saka takalminta, a k'ofar gidan ta samu Abbanta zaune har da Alhaji Saminu akan tabarma suna hira, yatsina fuska tayi ta harareshi ta wuce, shigewa tayi cikin gidan kan ta tsaye ta shiga falon da sallama, ba wani abu daya nuna mata mai d'akin nan na faman da jinya, dan haka suka gaisa a sama sama tace "Mama ta fad'a min kin shiga gidan ai ina bacci."


Da fara'a tace "Eh wallahi, ranar na ga babu sallama sai fitowa na yi ban gan ki ba, sai Alhaji ne yace ya had'u dake a k'ofar gida kin fita ai."


Yak'e tayi tace "Hakane wallahi."


Jim ta d'an na wasu mintuna saΓ― kuma ta mik'e tace "Aunty Maimuna saida safe, dama dan mu gaisa ne."


Da fara'a tace "To Mimi saida safe."


Tana fitowa daga falon suka had'e ya shigo, had'e fuska tayi ta sunkuyar da kan ta tana jiran ya kauce, a yanda idonshi suka rufe sai yaji baya shakkar Maimuna tasan komai, kan shi tsaye kawai yace "Me yasa ina kiranki baki d'agawa?"


A dak'ile cikin b'acin rai tace "Haka kawai, ka kauce min na wuce ko na maka ihu yanzu."


Wani malalacin murmushi yayi ya d'an kauce mata yana fad'in "Malam ya ce mu tayashi karb'an bak'i, ina fata dai ba aurenki zasu zo nema ba?"


Saida ta saka takalminta tace "Eh, su ne, aurena zai basu insha'Allah."


Wata yar dariya yayi sanda take fita a k'ofar d'akin shi kuma cikin wayancewa saboda kallonshi da Maimuna tayi yace "Allah yasa alkairi Mimi, ai haka ake so."


Banza tayi da shi har ta fita a gidan gaba d'aya, sai dai shi kam haushi kamar zai kasheshi, ba wai rashin girmama shin da ba tayi ba, ba kuma yanda bata d'aga wauarshi ba kamar da ta tabbatar masa masu neman aurenta ne zasu zo, to kenan shi jiran banza yayi mata kenan? Tana fita gida ta sake shiga mama na tambayar ta "Har kin mata aikin ne? Ko kuma had'e mata fuskar kikayi ta gane tace ki tahowarki?"


Sakin fuska tayi tace "A'a mama, dama dan na juye mata abinci ne a kwanuka."


K'ala mama ba tace ba har ta shige d'aki, tana zaunen ne d'aki ta ji tsayawar mota a k'alla guda biyu, tana jin Abbanta ya shigo ya d'auki ruwa masu sanyi ya fita, gabanta fad'uwa kawai yake sai wani sabon fargaba da take ji yana ziyartarta, a k'alla minti talatin kafin ta ji bak'in sun bar k'ofar gidan.


Abinda bata yi tsammani bane kuma shi ma bai fad'a mata ba, saΓ― ga Abba da mahaifin Asma'u da suka tayashi karb'an bak'in sun shigo da akwatina har da goro da kuma kud'inta, akwati set biyu aka shigo da su masu kyau na zamani, goro d'auri biyu da kuma kud'in lefe million d'aya da rabi. A tsakar gidan kam tana jin hayanuyarsu har da kakanta ma suna tattaunawa su fa basu d'auka da kayan zasu zo ba, sai kakanta dake fad'in ai haka shine harkar girman, kawai a musu addu'ar fatan alkairi.                   *To fa*


Da safe tsaf ta shirya ta tafiyarta makaranta, saidai tana zuwa abun mamaki labarin har ya riga ta isa, dan kuwa Asma'u ce ta sanar wa su Jamila su ka suka yayata, saidai abun d'aure kan shi ne yanda Mimi bata cika bakin nan ko shan k'amshi da jin dad'i, murmushi kawai take musu sai tace "Hummm!"


A gida ma tana fita mama ta fara karb'an bak'i  daga makwabta har zuwa dangi suna taya murna na abun arzik'i. Har Mimi suka taso ta riski yan uwan mahaifiyarta su biyu aunty Shapi'a da aunty Sahura suna ta hira, d'aki ta shiga bayan ta durk'usa ta gaishesu, kayanta ta cire ta fito ta shiga ban d'aki ta dawo, har zata koma d'aki Shapi'a tace "Mimi zo."


Tahowa tayi tare da durk'ushewa dan suma kamar mamanta ne, cikin nutsuwa aunty Sahura tace "Mimi kin ji lokacin da mahaifinki ya tsayar da ranar aurenki?"


Girgiza kai tayi tana kallonta alamar a'a, jinjina kai tayi ta nuna mata kud'in hannunta masu yawa tace "Kinga wannan yanzu mahaifinki ya bayar da su, ya ce muje a rakaki kiyi siyayyar duk abun buk'atarki, dan gaba d'aya wata d'aya suka saka na auren."


Da sauri ta kalleta ta kalli mama tace "Wata d'aya mama? Bai yi kad'an ba kuwa?"


Kawar da kai mama ta yi saboda kunya ba ta tanka mata ba, aunty Shapi'a ce tace "Bai yi kad'an ba Mimi, me za'a tsaya jira tunda dai kin kai minzalin auren nan, sannan ba wani karatu kike ko wani abun ba na daban da za'a ce zai ja lokaci."


Sahura ce ta d'ora da "Ba komai kinji Mimi, kiyi addu'a Allah yasa haka shi yafi zama alkairi."


Ajiyar zuciya ta sauke ba tace komai ba, Shapi'a ce tace "Ranar alhamis baku karatu saiki shirya da wuri ki zo gidan Sahura ki same su, sai mu wuce kasuwa daga nan ki siyo duk abinda ya danganci sutura."


Jinjina kai tayi tace "To insha'Allah." Mik'ewa tayi zata koma d'aki Sahura tace "Sannan Mimi, dan Allah a cikin waccen akwatin da kike da na kaya har guda biyu, an fad'a min shak'are suke da kaya dan baki da aiki sai d'inki, kiyi k'ok'ari kafin alhamis ki zauna ki ware kayanki sabbi masu kyau, saiki ajiye su gefe ki je dasu d'akin mijinki, ko ba komai zasu anfaneki suma."


Jinjina kai tayi sai Shapi'a da tace "Ki godewa Allah miji kika samu d'an babban gida mai karamci, ya ce ke ya gani yana so kuma ke kad'ai yake da buk'ata, tsinke baya so a kai miki."


K'uri ta musu da ido tana kallo da tunanin anya kuwa! Hakan ba zai jawo mata abinda ta tsana ba? Wato *raini* a wurin danginshi, ta sani ne dole ta fuskanki k'alubale daga garesu, a yanda ta fahimta shi d'in d'an masu hannu da shuni ne, ita kuma yar talaka, sannan ita ce doguwa, amma dayawa ahalinta duk wadanni ne, ta sani ne ita kanta bata cire rai da haifar yara masu irin halintar iyayenta ba, saidai hakan sam ba zai zama abun k'yama a gareta ba, to amma dangin mijin da zata aura fa? Numfashi ta sauke mai nauyi tana tunanin idan mahaifinta ya zo zata mishi magana, gaskiya a mata kayan d'aki ko kad'an ne, dan ba zataa iya ji da wulak'anci da gori har biyu a lokaci d'aya ba, *yar talakawa*! *'yar wadanni*! Shigewa tayi d'aki tana lalubo wayarta a akwati ta kunna, duk da hankalinta na kan wayar amma tana jin yanda ake ta shiga da fice a gidan, daga yanda makwabta ke ta shigowa zaka san ana shigowa dan ganin gaske dai Mimi ce aka kawowa kaya jiya babu wanda aka fad'a ma? Sannan da aka ce million d'aya da rabi da gaske?
                *Masha'Allah*Assalamu Alaikum 

Masoyanmu da fatan kuna lafiya.


Muna mik'o maku godia da fatan alkhairi masu matuk'ar yawa a yadda kuka nuna mana kara da kauna wajen siyan littafinmu na kud'i.

Alal hak'ik'a munji dad'i kuma mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi ya k'ara bud'i.


Muna kuma k'ara kira ga masoyana wadanda basu siya ba dasu garzayo su siya domin muhimman darussa rayuwa, ilmantarwa da nishadantarwa dake cikin littafin. Dukkan wanda yaji taken littafin na *AURE YAKIN MATA* yasan littafi ne mai cike da ilmantarwa da bude ido akan irin rayuwar zaman auren da muke a zamanin yanzu don haka babu dana sani a siyan littafin.


Yadda kuke siyan littafin yana k'ara mana k'warin guiwa wajen yi maku typing din littafinmu na *KOMIN NISAN JIFA* da *Matar Mutum*, muna fatan zaku cigaba da siye don mu samu k'warin guiwar yi maku typing din littafin na kyauta akan kari ba tare da b'ata lokaci ba.


Mun yarda daku mun aminta da irin k'aunar da kuke mana,  nasan kuma zaku siya littafinmu mai take *AURE YAK'IN MATA.*


*MUNA SONKU SOSAI MUNA ALFAHARI DA KASANCEWA A CIKIN DUNIYARKU.*


Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)πŸ‘Œ zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.


_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479*  Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar   *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._


_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_


Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke mana don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna muna kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafinmuπŸ₯°
*Alhamdulillah*

Post a Comment for "MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 3 Na Samira Harouna"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...