MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 1 Na Samira Harouna - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 1  Na Samira Harouna

MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 1 Na Samira Harouna

- - Post a Comment

 MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 1

Na Samira HarounaπŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *1*


A nutse suke taka k'asar kowace da jakarta a hannu da dogayen hijab d'insu har k'asa, yanayin kamalarsu da fuskokinsu zai nuna maka sun samu tarbiya a zahirance dai, girgiza kai d'ayar tayi tace "Gaskiya yau ba zan je ba, dama ina shiga kallo ne a gidan idan ans sΓ©rie d'in da nake so, yau kuma ba'a yi dan haka ina gida."


Wacce tafi tsayi da haske sosai ga kuma 'yar k'ibarta tace "Ni kam zan je, dan jiya mbc Bollywood sun yi tallar khabi kushi khabi gham, dan haka zan je nayi kallo."


Tab'e baki tayi tace "Amma *Mimi* da dare ne fa, kinsan Abbanki ba zai barki fita ba."


Kallonta tayi ita ma tace "Kinsan yau asabar yana tafiya babban masallaci wajen sauraren karatu, yana tafiya ni ma zan tafi, awa d'aya suke yi kafin su gama na dawo."


Sake tab'e baki tayi tace "To yau *Mas'ud* ba zai zo bane?"


Wani dogon tsaki tayi tace "Ina farin ciki zaki lalata min shi ta hanyar kiran sunanshi."


Da mamaki ta kalleta tace "Mimi, Mas'ud fa shi ne iyayensa suka kawo kud'in gaisuwarki gidanku kuma iyayenki suka karb'a, sannan sun tsayar da magana cewa ana fara azumi zai kawo lefenki da sadaki, amma shi ne ba ki son maganarshi."


Yatsina fuska tayi tare da cunno leb'enta na k'asa mai kalar pink sosai tace "Wa ya fad'a miki zan yarda ya kawo? Wallahi bana son shi."


Da mamaki sosai tace "Ba kya son shi kuma kika bari manya suka shiga maganar?"


Cikin rashin bawa abun mahianci tace "Eh, saboda kawai ya takura min ba yanda zanyi, sannan bani da wani tsayayye har yanzu da zai dinga d'aukar d'awainiyata, sannan kuma yana da wani abu da nake son namiji ya kasance da shi."


Girgiza kai ta shiga yi da mamaki kafin tace "Mimi me yake damunki? Me yake da shi da kike so? Dama ba dan Allah kike kulashi ba?"


Wani murmushi tayi da yasa kumatunta masu tudun gaske sake fitowa tace "Sam bai min ba ne *Asma'u*, sa'arshi d'aya ya iya d'aukar wanka."


Jinjina kai tayi tace "Kenan kamar bankinki kike mayar dashi?"


Dariya tayi da tasa hak'oranta fitowa farare tas tace "Kusan haka?"


Cikin jimami tace "Allah ya shiryaki." Da dariyar mugunta tace "Ameen."


Suna k'arasowa gidajen na su Mimi tace "To nasan dai saida safe, dan ke ko 'yar wayar nan baki da za'a dinga yin jira ta WhatsAp."


Murmushi Asma'u tayi tace "Ke ma da kike da babbar wayar karki manta ba da sanin mahaifinki kike yi ba, kuma duk ranar daya sani zaki kad'e." 


Dariya tayi tace "Ba ma zai sani ba, kafin lokacin na yi aurena na tafi na barsu."


Dariya Asma'u tayi tana girgiza kai tace "Mimi haka kika zama yanzu?"


Fari ta mata da ido tace "Ah to! Zamu zauna rayuwa babu ci gaba ne, ke ma kina son kiyi auren ai rashin matsayi ne."


Girgiza kai tayi tare da shigewa gidansu, ita ma shiga tayi tare da yakice hijabinta ta cire tana siririyar sallama, babu kowa a tsakar gidan sai mahaifiyarta dake zaune bakin murhu tana kad'a miya, yatsina fuska tayi tace "Mama yau ma dai na gadon ne?"


Juyowa tayi ta kalleta, girgiza kai tayi ta yi banza da ita ta ci gaba dΓ  abinda take, da sauri ta shige d'akinsu bayan ta duk'a kafin ta iya shigewa ciki, aje kayan makarantar tayi sai siket d'in data ja sama tayi d'aurin k'irji da shi ta fito, bokiti ta d'auka ta je gaban randa zata d'ibi ruwa uwar ta kalleta cikin muryarta kamar ta yara tace "Karki fara *uwa*, kar ki d'ibar min ruwa kinji na fad'a miki."


D'agowa tayi ta kalleta da mamaki tace "Mama wanka zanyi fa."


Cikin fad'a tace "Ruwan alwala kawai zaki iya d'iba, shi ma idan za kiyi sallah."


Da mamaki tace "To me yasa? Babu ruwan ne?"


Kai tsaye tace "Babu, kuma kinsan ai ke kinfi k'arfin d'ebo ruwan, k'annanki ne ke d'ebowa da k'yar suna kawo mana, amma ke kika fi kowa anfani dasu."


Turo baki tayi tace "To yanzu dai bari na yi wankan, zan d'ebo miki gidansu madame *Maimuna*."


Hararanta tayi tace "Ke d'in? Ke ce zaki d'auko bokitin ruwa?"


Da sauri tace "Wallahi zan d'ebo."


D'ibar ruwan tayi rabin bokiti ta shiga d'aki ta d'auko kwandon wankanta mai d'auke da rantsatsen sabulu mai tsadar gaske da samarinta suka siya mata tare da maclean da brush ta shiga ban d'akin. Ta jima a ciki tana gyara jikinta kafin ta fito rik'e da kwandon, bokitin kuma ta baroshi a can,da kallo uwar ta bita dan ita har ta gaji da mata maganar d'auko bokiti ma, idan ta tashi ta d'auko kawai.


Buta ta d'auka tana sake zubawa k'afafunta ruwa tana fad'in "Gaskiya Abba ya daure a shafe mana ban d'akin nan da simitin, haba ban d'aki kamar wani filin dambe."


Tana saurarenta ita dai har tayi alwala ta shige d'akin, mai ta fara shafawa tare da d'auko k'atuwar jakar kayan kwalliyanta, sanyayya kwalliya ta yi wa kanta mai birgewa kafin ta mik'e ta nufi wajen kayanta. Tabbas kayan dake cikin akwatinta kana kallonsu zaka san sun fi k'arfin 'yar wannan gida, k'arya da d'aukarwa kai ne kawai zai bata wannan suturu, dan duk girman akwatin nan na k'arfe shak'e yake da kaya, daga kallonsu a ido kawai zai tabbatar maka sababbi sun fi yawa kuma duk d'inkunan zamani ne masu tsada.


Wani mahaukacin leshe ta d'auka ta saka riga da siket wanda aka cika gaban rigar da duwatsu masu k'yalli, dake tana da kumari sosai sai suka zauna mata d'ass a jiki musamman siket d'in daya fito da mazaunanta sosai, hijab ta saka ta fara gabatar da sallah magrib kafin ta gama ta d'aura d'an kwalin kayan, wani mayafi ta d'auka shara shara ta feshe da turare ta fito tsakar gidan.


Kallon mahaifiyarta tayi dake tsaye tana sallah, hallitar Allah kenan, domin kuwa duk kyan *Maryam* da tsayinta da wannan baiwa da Allah ya mata, mahaifiyarta 'yar wada ce, ma'ana irin gajerun nan k'anana, dan da zata tsaya kusa da ita ba zata kawo mata a k'ugunta ba. Matsawa tayi kusan kwanukan data gani ta shiga bud'ewa, d'an tsaki tayi tace "Yunwa nake ji amma wallahi ba zan iya cin tuwo ba."


Mik'ewa tayi ta koma d'akin ta d'auko 'yan canji a jakarta ta fito daidai da gama sallarta, kallonta tayi tace "Ina zaki je kika yi shiri haka?"


Cikin turo baki tace "Babu inda zan je Mama, nan gidansu madame ne zan shiga."


Girgiza kai tayi tace "Uwa bana son kowane lokaci kina zuwa musu gida, me yasa ba zakiyi hak'uri da kallon ba wai? Tunda Allah bai hore mana ba."


Kamar za tayi kuka tace "Mama zan daina, yanzu ma wani film ne za'a saka mai kyau da ban tausayi, yanzu na dawo fa."


Jinjina kai tayi ta d'auke kanta daga gareta tace "Idan ma baki dawo ba ke da mahaifinki ne babu ruwana."


Cikin rad'a tace "Mama har sun tafi karatun ne?"


D'aga mata kai tayi tace "Sun tafi tun kafin ki shigo."


Murmushi tayi ta nufi hanyar fita tace "Yanzu zan dawo Mama."


Da kallo ta bi k'ugunta dake bala'in juyawa sosai, tafiyar kuma a nutse take yinta amma dake Allah ya horesu, girgiza kai tayi tana fad'in "Allah ya shiryaki Mimi."


Gidan yana kallon nasu ne babban gida ne mai d'auke da babbar k'ofa, kai tsaye ta shiga bayan sun gaisa da mai gadin, saida ta tsaya a farfajiyar ta ciro wayarta daga k'ark'ashin siket d'inta kusa da cibiya kafin ta shiga d'aukar kanta selfie, saida ta d'auki masu kyau kafin ta shiga WhatsAp ta d'ora wanda suka mata a statu tana wa jama'a barka da da dare, da sallama ta shiga babban falon yaran da matar gidan suna amsa ma ta, gaisawa sukayi a mutumce kafin ta nemi kujera ta zauna tana fad'in "Tanti mbc basu saka film d'in nan ba?"


Lalaba kujerar da take kai tayi ta d'auki remonte ta mik'o mata tana fad'in "Gashi duba ki gani."


Karb'a tayi inda Maimuna ke fad'in "Ni fa kallon ba damuwata yayi ba, idan ta ni ne ma saina wuni ban kunna tvn ba."


Dariya kawai tayi sanda take nemo tashar, ganin ana tsaka da film d'in yasa ta gyara zama tace "Yawwa an fara."


Tattara hankalinta tayi gaba d'aya ta mayar kan tvn, kallonta Maimuna tayi, yarinyar na birgeta sosai saboda iya d'aukar wankanta da saka kaya, kamar ba 'yar talakawa ba, dan ko ita dake auren mai kud'i bata kai ta saka kaya masu tsada da kyau ba, uwa uba jikinta dake d'aukar ido kamar na wata babbar yarinya. Mik'ewa tayi ta bar ta nan ta shiga k'arasa kimtsa gidan, tana kammalawa ta saka turaren tsintsiya kafin ta d'ebo abinci a plate, k'asa ta aje ta kalleta tace "Mimi sauko mu ci abinci."


Kallonta tayi ta kalli plate d'in, kai har ga Allah ba zata ce a'a ba, macca ce fa da jar miya da naman kazi, ai duk rashin had'amarta tafi k'arfin cewa a'a tunda dama yunwa take ji, tasowa tayi a hankali ta zauna cike da kunya, ita kan ta Maimuna tayi mamaki dan gaske duk sakewar Mimi a gidan nan bata cika cin abinci ba, yanzu ma dan taga akwai yaran makwabta ne yasa ta zubo mai yawa idan ita bata ci ba su sun ci.


Cikin nutsuwa suke ci suna kallon tvn saidai babu mai magana, basu ji tsayawar motarshi a k'ofar gidan ba sallamarshi kawai suka ji a tsakiyar falon tare da amsa gaisuwar da yaran mak'wabtan ke mi shi.


Bayanta yake kallo dan tana fuskantar tv ne, saidai daga yanayin shigar yasan ita ce, ga k'amshin turarenta *pure love* daya gauraue d'akin duk da turaren wutar da aka yi, musamman data aje gyalenta a kan kujera saiya samu kan shi da k'urawa bayanta ido, d'inki ne kamar na yanzu bayan ya sauka sosai fiye da kafad'unta, rigar kuma a kan k'ugun take zaune har yana ganin zip d'inta da kuma zariyar da akayi a baya na salon d'inki. D'an lashe leb'enshi yayi tare da kallon gashinta data dunk'ule ta rufeshi da ribom, dan yanayin d'aurin d'an kwalin yasa tsakiyar data tara gashinta a bud'e yake. Murmushi ya saki yana k'arasowa yana fad'in "Sannunku, abinci ake ci?"


Tunda ta ji sallamarshi ta tsaya cak saboda kunya, sunkuyar da kan ta tayi saida taji ya baro bayansu kafin tace "Ina wuni."


Da sakin fuska ya amsa da "Lafiya lau Mimi, an wuni lafiya?"


Sunkuyar da kan ta kawai tayi ba tace komai ba, mik'ewa Maimuna tayi tana fad'in "Sannu da zuwa? Yau ka shigo da wuri."


Murmushi ya mata yace "Hakane, zan d'an fita ne shiyasa."


Tsaye tayi gabanshi tace "Muje kayi wanka ko?"


Jinjina kai yayi tare da mik'ewa, hakan yasa ita ma mik'ewa tana kallon Maimuna tace "Aunty ni zan tafi, saida safe."


A tare suka kalleta da sauri yace "A'a Mimi zauna, ba jimawa zan yi ba kinji, zauna ki ci abincinki."


Murmushi tayi sai lokacin ta kalleshi, a k'alla ba zai gaza shekara arba'in da bakwai zuwa da shida ba, yana da kwalliya saidai matsalar mutum ne mai k'iba. Girgiza kai tayi tace "A'a zan tafi, saida safe."


D'aukar mayafinta tayi da wayarta duk da hannu d'aya hannu d'aya kuma a sagale saboda abincin daya tab'a ta juya, duk da yana gaban matarshi saida ya sake bin bayanta da kallo, lumshe ido yayi ya sake lashe leb'e yana ayyana a ran shi "Insha'Allah zaki zama matata ke ma, ina son ki Mimi, wannan surar taki zata zama tawa ni kad'ai, gidan hutu ne ya dace dake."


Saida ya ga fitarta kafin ya kalli Maimuna data wuce gaba ya bi ta baya. Tana fita a farfajiyar ta wanke hannu ta sha ruwa a bakin panpon, yafa gyalenta tayi ta shiga latsa wayarta, tana kaiwa k'ofar gida kira na shigowa wayar, dubawa tayi ta ga an ruba *d'an wahala*.


Tsaki tayi tare da d'auka dan bata tsallake kiranshi kasancewar mutum ne mai sakin hannu, a yanda ta wuni ba wadataccin kud'i zata so samun na kashewa.


Cikin sanyayyar murya tace "...

*Alhamdulillah*

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *2*Cikin sanyayyar murya tace "Hello."


Amsawa yayi da "Gimbiyata, ya kike?"


A dak'ile ta amsa d'Γ  "Lafiya lau."


D'orawa yayi da cewa "Na ga statu d'inki na yi magana na ga ba kya en ligne (online)."


Cikin yatsina fuska tace "Hakane." 


Cikin murmushi yace "To ki hau za muyi magana."


A k'asan mak'oshi tace "Um um!" Da sauri yace "Me yasa?"


Shiru tayi hakan yasa shi cewa "Ko babu mega (data) ne?"


Yanzu ma a mak'oshin tace "Um." Wani murmushi yayi yace "Haba gimbiya Mimi, kuma shine baki kira kin fad'a min ba? To kinga bari na turo miki da kati yanzu saiki hau zamuyi magana."


A dak'ile tace "Uhm! Nagode." Da fara'a yace "Haba ba komai, matar da zan aura ace babu kati a wayarta, ai abun kunyata ne."


Yana kashe kiran taja tsaki tace "Aikin banza, ko me zanyi da shi? Wani k'azami dashi ko turare bai iya sakawa ba."


Mayar da wayar tayi ta soke a siket d'inta kafin ta fita a gidan, canjin hannunta ta nufi bakin titi dan samun wani abu da za ta ci, dan da tana da kud'i isashi kayan shayi zata siyo, dan a rayuwarta tana son shayi sosai musamman da bred da soyayyen k'wai, a hankali ta taka har ta k'arasa bakin titin, babban birni kenan ba'a cika samun irin kayan soye soyen nan ba, a hakan ma wai dan suna unguwar marasa k'arfi, wani shago ta k'arasa kawai ta siyo sardine da bred ta juyo dan komawa gida.


Tana ganin motar ta sunkuyar da kai dan ta gane shi ne, duk da haka saida ya tsayar da ita ya fito daga motar yana fad'in "Mimi daga ina kuma? Na d'auka ai gida kika shiga."


Da ladabi tace "Na je nan ne bakin titi siyo abu."


Murmushi yayi yace "Mama ce ta aikeki?" Da sauri ta kalleshi jin yace wai mama, bayan kuma tana da tabbacin ya girmema mahaifiyarta ma, d'an tab'e baki kawai tayi ba tace komai ba, hannu yasa aljihu ya ciro yan jaka biyar biyar gida biyu ya bata yace "Ga wannan kya siyawa su *Amir* abun kari da safe."


D'an d'aga idonta tayi, a gaskiya ita kallon uba take masa da kuma mai taimakaonsu, ba kuma su kad'ai ba duka unguwar yana tallafawa gajiyayyu, haka yasa ta karb'a ba tare da tunanin komai ba tana fad'in "Angode, Allah saka da alkairi."


Murmushi ya mata yace "Ki shiga gida kinji, bana son ganinki a haka ana kallonki."


Da sauri ta d'aga kai ta kalleshi amma kuma saita sunkuyar dan idonshi a kanta suke, jinjina kai tayi alamar to tare da takawa tana maimaita kalamanshi, saida tayi nisa kafin ta ji ya tayar da motar yayi gaba, da sauri ta sake kallon kud'in tana murmushin jin dad'i su ma ta sokasu a poshet d'in wayarta kafin ta saka wayar ta b'oye ta k'arasa gida.


Daf da shiga gida wayarta tayi vibrations, tana dubawa tsabar kati ne ya turo mata har na jaka biyar, ko a jikinta dan ya turo mata fiye da na haka ma, shigewa tayi gidan da sallama tare da nufa wajen kwanuka dake cikin kwando a killace, k'aramin faranti ta d'auka na silba ta dawo ta aje kan tabarmar tare da ledar hannunta, d'aki ta shiga ta b'oye wayarta da kud'in kafin ta dawo ta zauna kan tabarmar ta mik'e k'afafu, uwar na kallonta ita dai har ta bud'e kifin ta juyeshi a ciki ta d'auki bredin, turawa uwar tayi tace "Mama ci."


Girgiza kai tayi tace "Um um, a ci lafiya."


Jawowa tayi ta ci gaba da cin abin ta tana fad'in "Mama har yanzu su Abba basu dawowa ba?"


A sanyaye tace "Basu dawo ba, kinsan tafiya tare da su *Yaseen*."


Cikin had'e fuska tace "To mama shi ma Abba ya dinga zaman shi a masallacin nan unguwar mana, yana wahala doguwar tafiyar nan fa."


Da mamaki ta kalleta tace "Mimi d'aukar karatun da yake zuwa? Kuma kin fi kowa sanin shi d'in yana matuk'ar k'aunar karatun *Sheik Abdul Waheed Salman Aliyu Sharif*, ba zai daina ba tunda yana so."


Shiru tayi ba tace komai ba hakan yasa mahaifiyar ta sakΓ© kallonta da kyau tace "Mimi, ni ko ki mayarwa da Mas'ud wayar daya baki?"


Turo baki tayi tace "Na mayar Mama."


Nunata da yatsa tace "Tsakaninki da Allah kin mayar?"


Shiru tayi sai kuma ta kalleta kamar zatayi kuka tace "Wallahi mama gobe da ya zo zan mayar masa, ni dama wayar bata min ba."


Jinjina kai tayi tace "Idan baki maida masa ba wallahi mahaifinki zan fad'a ma, ya fad'a miki baya son ki da waya yanzu Mimi, shiyasa ko da Mas'ud ya baki wayar nan nace ki mayar masa."


Cikin turo baki tace "To naji zan mayar." Tuttura bredin ta dinga yi har ta mik'e ta wanke hannayenta da sabulu ta koma d'aki, kayan jikinta ta cire ta saka doguwar riga mai taushi ta yadi, tana fitowa tayi zaune mamarta tace "D'ebo ruwan fa sai yaushe?"


Da sauri ta kalleta kamar zata fashe da kuka, saida ta turmuza k'afafunta alamar an takurata kafin ta mik'e bazar bazar ta d'auki bokiti tana gyara kallabin rigarta ta fita.


Har zai wuce akan babur cikin sanyayyar murya tace "Ina wuni *Bello*."


Tsayawa yayi tare da juyowa yace "Mimi, kina lafiya?"


K'asa tayi da kanta tana murmushi kamar ba da hushi ta fito ba tace "Lafiya lau."


Kallon bokitin hannunta yayi yace "Ya na ganki da bokiti? Wani wuri zaki tafi?"


Cikin muryar shagwab'a da take da tabbacin tana kayar da mazan yanzu tace "Wallahi Mama ce ta aikeni d'iban ruwa, kuma kaga dare yayi yanzu babu kowa a wuri, shine nake tunanin shiga gidanku na d'ebo."


Wani murmushi ya saki yace "Haba Mimi, kamar ki ace zaki d'ebo ruwa ki d'auko a kan ki bayan gamu a garin nan? Kinga koma gida ki zauna, dama gidan zan shiga yanzu idan na shiga zan saka yara su kai muku ruwan."


Da farin ciki tace "Kai amma naji dad'i, nagode sosai."


Murmushi ya mata yace "Ba komai." Juyawa tayi shi ma ya tayar da bΓ’bur d'in ya wuce gidansu da gida hud'u ne tsakaninsu, tana shigowa ta aje bokitin mamanta tace "Ina ruwan? Mimi ban san iskanci fa, yanzu cewa za kiyi babu ko kuma sun rufe gida."


Dariya tayi tace "Mama ki zuba ido ki gani za'a kawo miki ruwa adadin da kike buk'ata."
   *Ahalin Aliyu Sharif*


 


Babban masallaci ne da a k'alla yake d'aukar dubbanin jama'a, ana sallahr juma'a da sallah eid a ciki, ginin ya tsaru sosai ya k'awatu, a duk ranar asabar masallacin kan cika tantsam da mutane saboda babba kuma shahararren malamin dake tafsirin Alqur'ani a wannan ranar, mutane daban daban kan zuwa dan sauraren wa'azi daga gareshi, a ciki har da manyan yan siyasa dan dama masallacin a unguwarsu yake a cikin gidan *Gaddafi*, da kuma manyan attajirai manyan k'usoshi a gwamnati da saurensu. Ac dake wuri da panka ya hana mutanen gurin yin gumi duk da ba yanayin zafi a ke ciki ba.


Teburin dake gabanshi tare da mai ja bak'i dake gefenshi a ciki yake da wayoyi manya da k'anana ana d'aukar recoding, sai d'an agaji guda a bayanshi da kuma wani mai tsaron lafiyarshi guda cikin bak'ak'en kaya da bak'in gilashi. A zahirance kyakyawa ne ajin da ba zai gaza hawa matakin farko ba, saidai kasancewarsa bafulatani yasa kana ganin zaka gane haka, a k'alla shekarunsa *arba'in da bakwai*,  dan gemunshi ma har fari ke akwai wanda ya k'ara k'awatashi. Yanzu ma cikin raha da hankali da nutsuwa yake musu sharhin suratul *Noor*.


Kiran wayarshi aka yi dake hannun mai tsaron lafiyarsa ya kuma d'auka saboda ganin lambar daga babban gida ce, yana d'aukar muryar Hajia cikin kuka tace "Sheikh, kana ina ne? Jikin *Ashraf* ya tashi fa, ga mu nan clinique de *gazobi*."


Da sauri jami'in yace "Hajia muna tare da sheikh yana darasi, amma zan fad'a masa yanzu."


Cikin tashin hankali tace "To dan Allah kayi sauri."


Kashe kiran tayi hakan yasa jami'in matsowa ya sunkuyo kusan kunnenshi ya fad'a masa, da sauri ya kalleshi sai kuma ya sunkuyar da kan shi, ya jima haka kafin ya d'ago yayi gyaran murya, cikin nutsuwa da muryarshi mai taushi da sanyi da harshenshi mai gurgiri yace "A bisa wani babban uzuri daya taso min yanzu, zamu dakatar da darasinmu a nan saboda hali na ujila, da fatan zaku gafarceni, kira ne daga gida kan d'an uwana da baya da lafiya, muna barar addu'arku."


K'ok'arin mik'ewa yayi yana jin yanda masallacin aka d'auki hayaniya ana jefo mishi addu'a ta fatan samun lafiya ga d'an uwanshi, ta hanyar baya suka nufa tare da d'an agajin da kuma mai tsaronshi, suna fita ta k'ofar wasu daga cikin mutanen har sun zagaye k'ofar, kowa hannu yake mik'o masa yana son sai ya jajanta masa baki da baki, wasu kuma lambarshi suke son amsa saboda a dinga kiranshi. Dake hakan ba sabon abu bane saiya shiga k'ok'arin zillewa amma ina dole saida ya gaisa da wasu, da k'yar ya samu ya shiga mota dreban ya ja shi zuwa asibiti.


Suna zuwa asibitin kud'in clinique de gazobi suka fita a motar suna take mishi baya, saida aka fara fad'a musu d'akin da aka kwantar da shi kafin suka rankaya can, daf da zasu shiga ciki ya juyo tare da d'aga musu hannu alamar su jira shi, tsayawa sukayi suka hard'e a bakin k'ofar shi kuma ya shiga ciki.


Su hud'u ne a d'akin, mahaifiyar Asharf da shi Ashraf d'in, sai kuma yayar Asharf d'in wacce mata ce ga Sheikh d'in sai kuma k'annan Hajia, amsa sallamarshi sukayi inda idonshi ke kan Ashraf dake bacci hannunshi d'auke da k'arin ruwa, cikin nutsatsiyar murya yace "Ya jikin na shi?"


Cikin kuka Hajia tace "Jikinshi da sauk'i, sheikh wai yaushe ne za'a fitar da shi? Jikin Asharf ya fara bani tsoro fa, yanzu ciwon yana yawan taso mishi ba kamar da ba."


A hankali ya matsa kusa da ita ya rik'o hannun yace "Kiyi hak'uri Hajia, insha'Allah zai samu lafiya, har yanzu a kan shirye shiryen tafiyarsa nake."


Jinjina kai tayi tace "Allah ya sa." Da murmushi yace "Ameen, insha'Allah muna fatan haka."


D'an juyawa yayi ya kalli uwar d'akinshi, sanyin idaniyarshi abar k'aunarshi, murmushi suka sakarwa junansu kafin tace "Sheikh mun d'aga ma ka hankali ko?"


Girgiza kai yayi yace "Ba matsala, Allah ya bashi lafiya."


Ita ma a sanyaye tace "Ameen." Saida ya saci kallon Hajia kafin ya kalleta da kyau, da hannu da kuma ido da girarshi ya mata alamar "Ya ajiyata?"


Murmushi tayi tare da masa alama da motsa bakinta tace "Lafiya lau yake."


Lumshe ido yayi alamar jin dad'i, sunkuyar da kan ta tayi ita kam dan kunya,  shiru d'akin ya d'auka na wani lokacin kafin Hajia ta kalleta tace "Ki tashi ku tafi gida tunda jikin nasa da sauk'i ko?"


D'an kallon sheikh tayi kafin ta jinjina kai alamar to, a hankali ya taka ya k'arasa daf da Asharf ya zauna bakin gadon, rik'o hannunshi yayi yana kallon kyakyawar fuskar Ashraf, duk da ba ciki d'aya suka fito ba amma yana bala'in son d'an uwanshi, sun shak'u sosai tun yana yaro, ladabinshi gareshi da kuma k'iriniyarshi suna birgeshi, kusan baya da aboki bayan yaron duk da kuwa ba tsaranshi bane, amma yanzu haka da zai samu sab'ani tsakaninshi da yayarshi na zaman tare, to shi yake ajiyewa tsakaninsu ya ja musu kunne.


Lumshe ido yayi kafin ya sake bud'ewa, addu'a ya shiga karantawa yana tofa masa kusan minti talatin, su kuma kallonshi suke dan bai d'aga murya ba bare su ji su amsa da ameen, dan haka suna ganin ya sakin hannun Ashraf suka amsa da "Ameen."


Mik'ewa yayi ya kalleta yace "Mu tafi." Kallonsu Hajia yayi yace "Saida safenku."


A nutse suke takawa masu tsaron na gaba shi kuma suna baya tare da ita, suna fita mai tsaron ya kama murfin mota zai bud'e mishi, d'aga mishi hannu yayi alamar a'a, dakatawa yayi ya koma mazauninshi, da kanshi ya bud'e mata ta shiga ta zauna kafin ya rufe ya zagaya d'aya b'aren suka bar asibitin. 
*Alhamdulillah*

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *3*Kasancewarshi malami zai sa kayi mamaki idan kaga tabkeken gidan da mai gadi ya bud'e musu suka shiga, amma idan kasan margayi Alhaji Aliyu Sharif zaka tabbatar wannan ba komai bane, dan tsohon shahararren d'an kasuwa ne daya tara mahaukatan kud'i kuma ya mutu ya barwa magadansu, haka na su iyayen suma suka musu suka bar musu suka gaji nasu kason, haka kuma sheikh Abdul Waheed ba malamin ci da ceto bane, d'an kasuwa ne haka kuma a cikin gwamnati ma shi d'in mai bawa gwamna shawara ne akan harkar data shafi ilimi. Shigarsu k'ayataccen falon yasa yara tasowa da gudu suna musu oyoyo, da murna shi ma ya d'auki k'ananan yana rumgumesu a jikinshi, babbar cikinsu kam a hankalce ta k'arasa kusa da mahaifiyarta tana fad'in "Momy sannu da dawowa, ya jikin tonton?"


Da murmushi ta amsa mata da "Jikinshi da sauk'i, dan mun baroshi ma yana bacci."


Da nutsuwa yarinyar tace "Allah ya bashi lafiya." Da fara'a tace "Ameen."


Sauke yaran yayi yana kallon yarinyar yace "Uhm! *mamana* shi ne ko a kulani? Sai mamanki ko? To na yi hushi ma."


Dariya tayi ta matsa kusa da shi ta kama hannunshi tace "Abu, kayi hak'uri, ina tambayar jikin tonton d'ina ne."


Dafa kanta yayi yace "Ku masa addu'a kun ji, zai samu lafiya insha'Allah."


Da kai ta amsa masa tare da fad'in "Insha'Allah Abu." Murmushi ya mata shi ma yace "Masha Allah."


Kallon *Hafsat* yayi yace "Zan shiga ciki."


Da ido ta masa alamar "Ina zuwa." Wucewa yayi yana murmushi tare da cire babbar rigarshi irin ta malamai da bata da wuya sai hannaye kawai, kallon *Aisha* tayi tace "Eesha, ku je d'akinku ki taimakawa k'annanki su watsa ruwa su saka kayan baccinsu, dare yayi kin ji."


Da ladabi tace "To Momy." Kallon k'annanta tayi su uku tace "Muje."


Mai bi mata ne ya kalli uwar yace "Momy, amma ai ban da ni ko?"


Dariya tayi tace "Kai ai yanzu saurayi ne."


Murmushi jin dad'i yayi tare da wuce suka haye sama inda d'akunansu suke, mik'ewa tayi da k'yar saboda k'afafunta da suka kumbura sakamakon cikin dake jikinta na wata biyar ta nufi d'akin sheikh, falo ne mai zaman kan shi dake zagaye da litattafai na ilimi daban daban da littafi mai tsarki kala kala anyi jere dasu, kai tsaye d'akin baccin ta wuce ta samu har ya shiga wanka, zaune tayi bakin gadon ta d'aga muryarta tana fad'in "Shi ne ka shiga ka barni ko? Ai zaka koma ne dan da kan ka zaka min wankan yau."


Yana jin ta sai murmushi da yayi bai amsa mata ba, bai wani jima ba ya fito da rigar wanka a jikinshi, yana dariya, kama hannunta yayi yana fad'in "Muje na miki to, shikenan?"


Turo baki tayi tace "To me yasa zaka tafi ka barni?"


Murmushi ya sakΓ© yi yace "A gafarceni to."


Murmushi tayi ita ma tace "To na gafarceka sheikh nawa."


Zip d'in rigarta ya ja zai cire tayi saurin cewa "A'a nagode, zan yi da kaina ai."


Lumshe ido yayi ya girgiza mata kai alamar a'a yace "Ki barni, ina so na samu ladar, zanyi koyi da annabina ne manzon rahama, yayi wanka tare da matanshi yayi raha da dariya dasu."


Jinjina kai tayi tace "To ai ni yanzu kunya nake ji, wannan abun fitowa yake sai nayi muni."


Dariya yayi sanda ya kalli cikin data nuna mishi, shafa kumatunta yayi yace "A rayuwar aure babu kunya tsakanin ma'aurata, karki manta addininmu shine addunin da yafi kowane kunya hasalima ya koyar da mu jin kunya, amma a bisa haka ya fayyace mana komai game da rayuwar aure da yanda zamu tafiyar da addininmu, manzon Allah (S.A.W) yafi budurwar data fara k'irgen dangin kunya, yanda take jin kunya ta kasa sakewa da mahaifiyarta ma, a cikin gidansu ta kan zama kamar marar gata ko bak'uwa, amma a haka ya warware mana addininmu, kama daga yanda zaka samu najasa a jikinka har zuwa yanda zaka tsaftaceta, saida ya fad'a mana, dan haka wannan cikin kar ya sa ki cuceni ko ki cuci kan ki, kin ji Hafsat."


Da kai ta msa alamar to, tana kallo ya cire mata kayan duk ya d'aure mata jiyoyin jikinta da k'aramin tambihinshi, hannunta ya ja zuwa ban d'akin ya shiga wankaceta soso da sabulu, saida ya gama mata suka fito, duk da d'akinshi ne amma a nan ya samu rigar baccinta ya saka mata, kwantar da ita yayi ya kalli fuskarta yace "Kiyi bacci kin ji, kin wuni ba kya jin dad'i yau hakan yasa na kai ki wajen Hajia, gashi alamu sun nuna a can ma baki samu hutu ba."


Murmushi tayi tace "To, kai fa?" Murmushi yayi shi ma yace "Zan kwanta, amma zan fara dubo yaran nan na gani."


Jinjina masa kai tayi ta bishi da kallo cikin doguwar farar rigarshi har ya fice a d'akin.
               *Maryam*Dake jiya saida Bello yasa yaran gidan suka cika musu kaf mazubin ruwa dake gidan yasa yau bata tsaya jiran ruwa ba, wanka kawai tayi ta shirya dan tafiya makaranta, fitowa tayi cikin hijabinta fari k'ar har k'asa rumgume da Alqur'aninta a k'irji, zaune tayi a kan tarmi tana kallon k'annanta dake cin d'umamen tuwo, yatsina fuska tayi tana ayyana ba zata iya cin shi ba, ta d'auko kud'in da mijin Maimuna ya bata Alhaji *Saminu*, idan ta je makaranta ta samu ko alala ta ci, fitowar mahaifinsu daga d'akin yasa ta saurin sauka daga turmin ta durk'usa kan ta a k'asa, saida ya tsaya gabanta cikin ladabi tace "Abba ina kwana."


Da fuska a washe ya amsa da "Lafiya lau Maryam, har an shirya?"


Jinjina kai tayi tace "Eh Abba." Kallon su Amir yayi dake cin abinci yace "Ku hanzarta to karku tsayar da ita."


D'an satar kallonshi Maryam ta yi a ran ta tana fad'in "Su ba yara ba ace sai na jera tare da su mun tafi?"


"Maryam." Mahaifinta ya kira sunanta, da sauri ta d'ago tana zuba mishi idonta, masha Allah, daga mahaifiyarya zuwa mahaifinta har k'annanta duk hallitarsu iri d'aya ce, dan kuwa mahaifiyarta ma har tafi mahaifin tsayi, dan shi ba zai wuce gwiwar Maryam d'in ba, k'annanta ma haka suke can cikin k'asa a haka kuma mai bi mata shekararshi goma sha hud'u, hakan yasa take matuk'ar kunyar tsayawa a tsaye idan iyayenta na tsaye, tana jin nauyinsu sosai da girmama halittarsu, shi ya sa bata iya tsayawa idan ba a hali na tafiya take ba. Cikin dattako *malam Adam* yace "Ku kula kinji, Allah ya tsare."


Jinjina kai tayi tace "To Abba, ameen." Kallon mahaifiyarsu yayi yace " *Rabi'a* zan fita, da wani abu ne?"


Shiru tayi kan ta a k'asa tana mai jin kunyar fad'a masa ba su da abinda zasu sarrafa da rana su ci, kunyar yaran yasa ta kasa yin maganar, lura da yayi yasa shi komawa d'akinsu, mik'ewa tayi ta bi bayanshi hakan yasa Maryam bin su da ido, saida suka b'acewa ganinta ta kalli k'annan nata, harara ta zabga musu tace "Wai sai yaushe zaku gama cin tuwon ne ku kuma? Sam ba kwa gajiya da had'iyar tuwo."


Tsaki tayi ta mik'e tsaye tana ci gaba da kallonsu, cikin sauri suka shiga turawa dan kar ta fara d'imarsu da k'ulli, suna kammalawa suka mik'e suka wanke hannayensu suka sha ruwa, daidai nan suka fito daga d'akin y'a nufi k'ofa uwar da duka yaran suka bishi da addu'a, yana fita suma suka bi bayanshi suka fita, suna gaba tana baya tana takonta a hankali a haka har suka k'arasa makarantar dake bayan gidansu.                  *Asibiti*Saida suka gama gaisawa ya samu kujera ya zauna yana kallon Ashraf dake zaune yana kurb'an shayi, murmushi suka sakarwa juna inda sheikh yace "Ya jikin na ka?"


Lumshe ido yayi yace "Jiki da sauk'i, ina so ma su sallami idan zai yiwu."


D'an hararenshi yayi yace "Gaggawar me kake? Wani abu kake shiryawa ne?"


Dariya Hajia tayi tace "Tambayeshi dai, ya manta jiya a some muka kawoshi nan."


Yanda ya tsareshi da k'ananan idonshi yasa Ashraf cewa "Shekh ka fahimta mana, zaman a nan babu abin da zai k'ara min ko ya rage min, na ji sauk'i kawai su sallame ni."


Rantsatsen rigarshi mai kama da alkyabba irin ta sarakuna ya d'an jawo daga gaba yana ci gaba da kallonshi, sanin ba zaiyi magana yasa Ashraf cewa "Wato kafi son nayi ta zama a nan ko? Saboda baka so na dinga zuwa gidanka ina damunka."


Murmushi yayi cikin taushin murya yace "Da zasu rik'e min kai d'in ai da naji dad'i, dan na gaji da zaryar da kake min a gida kullum."


Dariya Hajia da Ashraf suka yi inda ya kalleshi yace "To ba ga irinta ba, ni kam da zaka saka baki a sallameni, na rantse maka sai nayi budurwa gobe goben nan."


D'aga girarshi d'aya yayi kamar wani gogaggen d'an duniya tare da murmushin gefen labb'a yace "Da gaske?"


Saida ya had'e fuska yace "Ka sa a sallameni ka gani."


Cikin dariya Hajia tace "Sheikh kasa baki to, idan haka ta faru ai zan fi kowa farin ciki, watak'ila Allah ya dubeshi ya bashi lafiya sanadiyar auren."


Wata tattausar ajiyar zuciya ya sauke yana ci gaba da kallon Ashraf, d'an murmusawa yayi yace "Shikenan, amma idan sun ce da wata matsala ba zan takurasu ba."


Babu wanda yace wani abu har ya mik'e yana gyara babbar rigarshi ya fita, ya d'an jima kafin ya dawo musu da takardar sallama, Ashraf na murnar zai tafi gida sheikh na mishi dariya da fad'in "Kamar wanda ya aje mata hud'u."


Shi ma dariya yayi yace "Mata hud'u fa? Ai ni ra'ayina na yin mace d'aya ne, kuma ma me ya aikeni karambanin yinace hud'u? Bayan kai ma da ke ustazu d'aya gareka."


Wani k'ayataccen murmushi yayi yace "Ni ma ina nan ina nema, zan k'ara ne ai dan samun wannan tagomashin na masu mata sama da d'aya."


Da zolaya Ashraf yace "Kenan tare za muyi auren?"


Sake d'aga masa gira yayi wanda hakan ya zama jikinshi yace "Watak'ila."


Turo baki yayi yana hararenshi yace "Lallai ma sheikh d'in nan, wato zaka wa 'yar uwata kishiya kuma shi ne kake fad'a ma a gabana."


Wani murmushi yayi ya juya ya kalli Hajia dake ta had'a kayansu dan tafiya bata kula da su ba yace "Na fad'a a gaban Hajia ma bare kuma kai."


Hajia ce tace "Ni ai murna zanyi da faruwar haka, tunda arzik'i ne zai ci uban na da."


Dariya sukayi sai sheikh daya sake sunkuyar da kai dan bai d'auka tana jin su ba, suna had'a kayan suka fito da sauri masu tsaronshi su biyu suka karb'i kayan hannunshi wanda ya karb'a a hannun Hajia, dake a mota biyu suka fito yau dan wajen aikinshi zai tafi yasa d'aya motar masu tsaronshi ne d'ayar kuma shi da su Ashraf da Hajia har suka isa gida, sai dai bai shiga ciki ba saboda lokaci ya tafi sosai.                 *Maryam*Hutun minti talatin aka fito dan mai buk'ata yayi buk'atarsa, a cikin ajin suke zaune tare da k'awayenta suna ta hira inda wasu ke cin abinci, ita ma robar alala ce gabanta inda Asma'u ke kallonta da mamaki dan bata d'auka zata iya cinye wanda ta siyo ba, saida ta ga ta ida ta d'auki ledar pure water ta tsotse ta jefar Asma'u tace "Masha'Allah, lallai yau na tabbatar Mimi ba matar k'aramin mutum bace ke."


Harara ta wurga mata tace "Ban gane ba, me ya faru?"


Saida ta kalli robar ta kalleta tace "Alalar dala arba'in fa kika cinye ke kad'ai."


Tsaki tayi ta sake hararenta tace "Miye a ciki? Kud'inki ne ko nawa?"


Girgiza kai tayi tace "A'a naki ne, Allah baki hak'uri."


Tab'e baki tayi ta kalli wacce ke kusanta tare da zura mata hannu tace "In ga wayarki Jamila na tura vidΓ©os."


Wayar ta mik'o mata tana fad'in "Ban da sababin vidΓ©os fa har yanzu, na wa'azi ne kawai aka turo min jiya."


Saida ta fara dubawa kafin ta kalleta tace "Wai duk wa'azin shi ne kika turo?"


Da murmushi tace "Eh, yana birgeni wallahi saboda ya iya wa'azi."


Tab'e baki tayi tace "Shi ne ke birgeki? Ko kuma wa'azinshi? Ko kuma ilimin da Allah ya bashi?"


Cikin rashin damuwa tace "Duka ma wallahi." Dariya 'yan matan suka saka inda Asma'u tace "Da alama dai Jamila da sheikh Abdul Waheed zai ce yana sonki da gudu zaki auresa."


Da sauri ta kalleta tana dariya tace "Wallahi tsaf kuwa, ai ko bai fad'a ba da zan ganshi ido da ido ma ni saina rok'eshi ya aureni."


Da mamaki Maryam ta kalleta tana nuna wayar tace " *Tsohon*? A hakan ma ke zaki rok'esa?"


D'auke kanta tayi tace "Tabb'! Lallai da kin wulak'antamu."


Jamila ce ta turo baki tace "Wallahi bΓ’ tsoho bane, dubeshi da kyau fa."


Tab'e baki tayi tace "Na gani, amma akwai wa'azin da yayi yake bayanin wani abu daya faru, a lokacin ya ce yana da shekara ashirin da shida, ni kuma Abba na ya fad'a min yana neman auren mamana aka yi wannan al'amarin, a lokacin shi yana ashirin da shida shi ma, hakan na nufin shekarunsa *arba'in da bakwai* fa, kinga kenan tsoho ne tunda sa'an babana ne."


Dariya sukayi sai wata dake kusa da Asma'u tace "Gaskiya indai hakane tsoho, fuskarshi ce dai bata cika nunawa ba."


Asma'u kam cewa tayi "To ko ni dai da zai aureni wallahi zan amince, tunda yana da ilimi."


Maryam kam tab'e baki ta sake yi tace "Allah ya rabani na rasa wa zan aura sai sa'an babana."


Jefawa Jamila wayarta tayi ta mik'e zata fita dan wanke hannu tana fad'in "Wannan ai lalata k'uruciyarku kuke son yi."


K'arar da wayarta tayi yasa Asma'u d'auka tana dubawa tace "Mimi Mas'ud ne ke kiranki."


Shiru ta mata saida ta wanke hannayen ta dawo ta zauna ta karb'i wayar, datse kiran tayi tare da kashe wayar gaba d'aya, Asma'u dake kallonta tace "Me yasa kika kashe?"


Kallonta tayi tace "Shi mahaukacin ina ne da zai kirani yanzu bayan yasan ina makaranta."


Jamila ce tace "Watak'ila dan yaga lokacin hutu ne, wallahi ya damu dake mutumin nan Mimi."


Banza tayi da su hakan yasa Asma'u cewa "An tab'o mata hirar data tsana a duniya, kuyi harkar gabanku kawai."


Tab'e baki Maryam tayi tace "Da dai yafi kam."


Wata hirar aka shiga saidai Asma'u kam ta damu sosai da abinda Maryam d'in ta fad'a mata cewa Alhaji Saminu ya bata kud'i, dan haka hankalin kowa na tafiya wani wurin ta sake gyara zamanta tace "Mimi, me yasa da Alhaji Saminu ya baki kud'in nan kika karb'a? Ba kya jin tsoro ke?"


Kallonta tayi tace "Tsoro kuma? Na me?"


D'an numfashi ta sauke sai kuma tace "Idan fa yace yana son ki?"


Wata dariya ta kece da ita har da d'an bubbuga table d'in kafin ta tsagaita ta kalleta tace "Ya ce yana so na? To sai me? A gaban idonsa zan fad'a masa ba zan iya aurensa."


Ba tare data d'auke idonta daga kanta ba tace "Me yasa? Amma naga mutumin kirki ne."


Wawan tsaki taja tace "Ke yanzu dan ina mahaukaciya sai na yi soyayya da Saminu? Bayan kasancewarshi tsoho fa kin ganshi k'ato da shi, me zanyi da shi ni kam."


Murya k'asa k'asa tace "To indai hakane ki daina karb'ar komai daga hannunshi dan Allah, ni wallahi tun rannan da muka je gidan naga ya cika kallonki da yawan kiranki na ji ina zargin akwai abinda yake nufi a kan ki."


Yatsina fuska tayi tace "Wannan shi ya shafa wallahi, ni ko a jikina."


Jin an busa usur d'in dake nuna lokaci ya k'are kowa ya shiga aji yasa Mimi sassauta murya tace "Malam yace da yamma wajen walimar sabka zamu tafi, da uniforme zamu je ko kayan gida?"


Ita saida ta sassauta murya tace "Bari a tashi sai mu tambaya mu ji."


Shigowar malamin yasa akayi shiru babu mai magana sai mayar da hankali a kan shi da kowa yayi, inda duk wani mai waya tuni ya kasheta dan an hana zuwa da ita, masu taurin kai ne ke tahowar da ita.

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨

        *MATAR MUTUM*

            _(K'abarinsa)_

πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨πŸ‘©‍❤️‍πŸ‘¨


                   *NA*_SAMIRA HAROUNA_       *SADAUKARWA*


                   

               _GA DUKA_


     *'YAN AMANA TA*πŸ’«✨ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*🌟

_(Tsintsiya mad'aurinki d'aya)_🀝


  ☆ *[ T.M.N.A]* ☆ πŸ“–πŸ–Š️ 


https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/


_Bismillahir rahamanir rahim_                    *4*A marairaice ya kalli Hajia yace "Dan Allah Hajia ki barni na fita, wallahi na fi jin dad'i idan ina waje."


Ita ma a marairaice tace "Ashraf ba wai na hanaka fita bane, ka jira jikinka ya k'ara sauk'i mana."


Kamar zaiyi kuka yace "Hajia na ji sauk'i fa, ba abinda nake ji a jikina yanzu."


Da alamar tuhuma tace "Ka tabbatar?"


Cike da tabbaci yace "Na tabbata Hajia, insha'Allah babu abinda zai faru ki kwantar da hankalinki."


Jinjina kai tayi tace "Ashraf burina d'aya ne a duniyar nan naga ka samu lafiya, ciwon cikin nan naka yana d'aga min hankali fiye da tunaninka."


Murmushi ya mata yace "Kenan Hajia baki da burin ganin nayi aure?"


Turo baki tayi tana dukanshi a kafad'a tace "Dan na ga kayi auren har 'yan mata na dinga lissafa maka dake cikin ahalin nan, amma ka rufe ido ka nuna baka so basu ma ka ba."


Jujjuyar da kan shi yayi yace "Hajia ai duk cikinsu ne babu wacce ta dace da kalar tsarina."


Baki sake da mamaki tace "Iyeh! Wato har wata kalar tsarinka kake fad'a? To fad'i na ji ko zan iya samo maka."


Dariya yayi ya gyara zamanshi yace "Hajia ni wayayya nake so mai ilimi, 'yar zamani da kuma tsafta wacce ta iya kwalliya, sannan wacce zata dinga kwantar min da hankali."


Rik'e hab'a tayi tace "Ashraf matar sakawa a gaban mota kake nema?"


Tintsirewa yayi da dariya ya mik'e ya fita har da d'an gudunshi har ya bar gidan a galleliyar motarshi.                    *Sheikh*


A hankali yake juya kujerar kanshi na kallon sama amma idonshi rufe, hannunshi rik'e da katin gayyatar da aka kawo masa daga wata islamiyya da zasuyi sabkar Alqur'ani mai girma, jefi jefi ya kan sauke ajiyar zuciya saboda tunanin da zuciyarshi ke bijiro masa, dan gaskiya yana matuk'ar son ganin ya k'ara aure, ba dan Hafsat ta gaza ba ko baya jin dad'in zama da ita, kwad'ayin ladar da zai samu yake, yana son ganin shi ma kimarshi ta k'aru fiye da ta mai mace d'aya. Saidai abinda ke hanashi bai wuce tunanin 'yan matan yanzu ba, yaran da ko iyayen da suka haifesu basa iya tank'warasu, yaran da idonsu a tsaye a kai saman kai suke nuna maka baka waye ba, yaran da basa da hak'uri da juriya, yaran da waya da k'awaye suka fi komai mahimmanci a garesu, hakan yasa yake d'an dakatawa wasu lokutan, saidai kamar yanda yanzun zuciyarshi ke raya masa kawai zai rufe ido ne ya je ya nemi alfarmar malamin kan ya duba masa yarinyar daya yarda da tarbiyarta da nagartar iyayenta, idan ya masa haka shi da kan shi zaiyi yak'in neman k'uri'ar aurenta. A hankali ya bud'e idonshi tare da d'ora yatsanshi a kan kybord d'in na'urar ya turawa sakataranshi sak'on ya amince da gayyatar kuma zai je da kan shi da misalin 04:30 na yamma.                    *Maryam*


12:00 cif na rana suka taso, a hanya ma dai hirarsu bata fahimtar juna bace tsakaninta da Asma'u, dan akwai banbanci ra'ayi sosai a tattare dasu, tana cikin b'acin ran da Asma'un ta k'unsa mata a kan maganar wani saurayi da ita har ta manta da lamarinshi ma wai ta ci kud'inshi dayawa, bata tsoron ya k'i yafe mata? Shi ne fa ta hau take ta masifa take fad'in "Ai bani na ce ya so ni ba, kuma ni ban tab'a bud'a baki nace a bani ba saidai kai ne ka d'auka ka min."


Mas'ud suka tsinkaya a kan dallelen mashin d'inshi yana danna wayarshi, wani uban tsaki ta kuma ja tace "Shi kuma me yake mana a k'ofar gida?"


K'wafa tayi hakan yasa Asma'u cewa "Sai ma kin tambaya? Wurinki ya zo mana."


Tab'e baki tayi tace "Duk da dama ina son ganinshi, amma ba zan ganshi yanzun ba, dan ni ba'a min haka wallahi."


Rab'a Asma'u tayi zata giftata ta wuce tayi saurin rik'e hannunta tace "Ina zaki tafi Mimi? Karki masa haka mana."


Tsaki ta kuma yi tace "Ke sake ni, shigewa zanyi na barsa mana."


Da mamaki tace "Amma kinsan wurinki ya zo ko?"


Fizge hannunta tayi tare da wucewa da sauri ta barta tsaye tana mamakinta, ai kam ko kallon kusurwar da yake ba tayi ba ta shige cikin gidan tana mitar ita zai wa dirar mikiya kamar wani ubanta? Shigewarta kawai ya gani hakan yasa shi tsayawa sagale da baki yana kallonta, saida ya tabbatar ita ce dai kafin ya d'an d'auke kan shi yana basarwa, kad'an daga aikin Mimi kenan, ya rasa gane wane irin so yake mata da har yake iya shanye komai daga gareta haka, ta masa wulak'anci ta ja masa aji ta yarfa shi fiye da kima, amma ya jure ya nace saboda tunanin ta kusa zama tashi, lokaci kad'an ya rage shi ma ya fara nashi salon mulkin, duk da dai ya tabbatar ba zai iya muzguna mata ba, amma saiya rama ko da na kwana d'aya ne dan taji idan da dad'i.


Shi yasa baya nuna bai ji dad'i ba idan ta b'ata masa, ko ba komai Mimi ta yi, ta had'u iya haduwa da kowane namiji zai so samunta a matsayin ta shi, ga ta da wani siddabarun saurin dukan k'irjin namiji, indai kana da rai da lafiya sannan tsufanka bai kai k'adamin da baka sha'awar mace ba, to idan kaga Mimi zuciyarka zata amsa ma ka saidai kayi shiru da bakinka kawai, ba wai tsananin kyan da take d'auke dashi bane a'a, wata irin halitta ce da ita da kuma yanayin dake saurin d'ad'a namiji a k'asa warwas. Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke tare da sakin murmushi yana mai jinjina lamarin ubangiji, wai yarinyar data fito daga gidan nan na k'asa, sannan ta fito daga tsatson wadanni har take yagawa mutane rigar mutumcinsu? Lambarta ya shiga kira amma sam ta k'i d'agawa dan a lokacin ma wanka ta shiga yi.


Tana fitowa ta saka riga da siket na atamfa ta feso turare kafin ta d'auki gyale ta yafa ta d'auko wayar ta cire layinta da card ta fito, a farfajiyar gida ta samu mamanta zaune ta zuba tagumi, tana kallonta tace "Mama lafiya?"


D'agowa tayi ta girgiza kai tace "Ba komai, ina kuma zaki je?"


Yatsina fuska tayi tace "K'ofar gida, Mas'ud ne a waje."


Jinjina kai kawai ta yi ita kuma ta fita, cikin takonta mai birgewa ta k'araso ta tsaya tare da d'ora hannunta akan hannun mashin d'in ta juya mishi baya, kakkauran hannunta ya kalla wanda ya tabbatar zai yi matuk'ar kyau da awarwaron zinare kafin ya kalli k'eyarta yace "Ko dan sarauniyata tafi kowa sanin hushinta shi ne silar shiga damuwa shi ya sa take son tsokano damuwata?"


Ba tare data juyo ba tace "Idan gaske ne me yasa kai ma za kayi abinda kasan baya daga cikin tsarina?"


Murmushi yayi mai sauti yace "Na d'auki laifina da hannu biyu, a gafarceni ba zan k'ara ba, dama na zo ne saboda tun jiya nake kiranki, amma Mimi kin k'i d'aga min waya ban san me yasa ba? Shi ya sa na zo saboda ina da muhimmiyar magana da ke."


A hankali ta juyo ba tare data d'auke hannunta ba tace "Wace irin magana kuma?"


Leb'enta ya bi da kallo wanda bata shafawa komai ba, hakan yasa na k'asa tsayawa a kalar pink d'inshi sosai na sama kuma bak'i dashi, saidai na k'asa ya fi na sama girma da d'an tsayi daidai da fuskarta, numfasawa yayi yace "Dama akan maganar aurenmu ne..."


Da sauri ta katseshi tace "Aurenmu? Aka ce me?"


D'an zaro ido yayi yana mata murmushi yace "Mimi ko dai kema kin matsu?"


Yatsina fuska tayi tace "Ina jinka."


D'orawa yayi da cewa "Dama jiya malam sun had'u da Alhaji a wajen karatu, shi ne suka tsayar da ranar da za'a kawo kaya a saka mana rana, nasan malam ba zai fad'a miki ba sabida ke 'yar fari ce shi yasa na zo na sanar dake."


Wani galala tayi ta bud'e idonta da kyau tace "Na ji dad'i daka fad'a min, dan kaga da sunyi kuskure."


Da mamaki yace "Kuskure kuma? Na me?"


Ba tare da damuwa ko d'aya ba tace "Kuskuren aurar dani mana ban shirya ba."


Da wani sabon mamakin yace "Baki shirya ba kuma? Mimi sai yaushe zaki shirya?"


Gyara tsayuwarta tayi ta mik'o masa wayar hannunta tace "Ga wayarka, kayi hak'uri Mas'ud a gaskiya ban tashi aure ba yanzu, idan ma na tashi ba zanyi da kai ba saboda wasu dalilai."


Girgiza masa kai ta sake yi tace "Kayi hak'uri, Allah ya baka wacce ta fini."


Da sauri ya shiga kakkarwa zai sauko daga mashin d'in kamar zai kifa ya fad'i, idonshi da suka rine sukayi ja ya shiga lumshewa yana fad'in "A'a Mimi! Mimi dan Allah tsaya kiji, Mimi..."


Da sauri ya sha gabanta tare da durk'ushewa yana kallonta hawaye na sauka a idonshi yace "Mimi me na miki? Fad'a min wallahi zan gyara, bana so na rasaki Mimi ke ce rayuwata, dan Allah kiyi hak'uri kinji, wallahi idan ma auren ne ba kya so na janye, zan jiraki Mimi har sanda kike so sai ayi."


Girgiza kai tayi tace "Mas'ud ka gane wani abu, idan muka ci gaba a haka zan yaudareka ne, shi fa aure ana ginashi ne da soyayya, ni kuma har yanzu bana jin sonka a cikin zuciyata."


Tsam yayi tare da mik'ewa tsaye yana kallonta yace "Ba kya so na? To Mimi watannin da muka share muna soyayya fa? Duk murmushi da kalaman da kika min fa? Dan Allah Mimi ki ce wasa kike min."


Idonshi ta kalla tace "Kayi hak'uri, dama gudun kar na wulak'anta ka yasa tun farko ban fad'a maka ba, yanzu ma nasan zaka d'auka yaudararka nayi, amma ba haka bane gaskiya ce na fad'a maka."


Da mamaki ya girgiza kai ya juya ya kalli yanda idon mutanen dake kai kawo duk idonsu a kan su, sake kallonta yayi yana ci gaba da girgiza ai yace "Wulak'anci? Ai kin riga da kin gama wulak'antani, Mimi ki fad'a min wani dalilin da yasa kika guje ni, idan ba haka ba zan zargeki da cin amanata."


Ajiyar zuciya ta sauke ta sake kallon fuskarshi tace "A gaskiya bana sonka ne." Rab'ashi tayi ta wuce tana fad'in "Kayi hak'uri."


Juyawa yayi ya bita da kallo harta shige, ji yayi wasu hawayen sun sake taho mishi, d'an tsaki yayi na jin haushin kan sa, ji yayi kamar ya d'auki takalminshi ya jefa cikin gidansu, amma zuciyarshi sai b'ari take ga zazzab'in da yake jin zai rufe shi, haka ya juya yana saka wayar a aljihu ya hau mashin d'inshi y'a bar unguwar.


Tana shiga ta kusa da mamanta ta zauna tana fad'in "...
Alhamdulillah, munsan Allah ya azurtamu da masoya masu d'umbin yawa a k'asarmu Niger da d'ayar K'asarmu Nigeria harda ma sauran kasashe na nahiyar Africa.


Ina masoyan *Sajida*  da *Samira*  littatafansu??? Marubutan nan masu rubuta littafin *Bak'a ce, Mage*  da *Badak'ala, Allura ta tono Galma* wanda kuke kauna har cikin ranku. Ku matso kusa don nuna musu d'umbin soyayya da  kaunar da kuke musu inda suka zo  maku da sabon littafinsu mai taken *AURE YAK'IN MATA* daga jin sunan kunsan cewa littafin kunshe yake da darussan rayuwa wadanda suka shafi rayuwarmu ta aure,kalubalen da mata ke fuskanta a gidan aure da kuma yanayin zamantakewar aure na zamanin yanzu, duk da ba sabon abu bane, amma namu ba irin nasu bane, sai an gwada akan san na kwarai.


Ga mai bukatar wannan littafi *Farashin mai sauki ne* naira dari uku (300) kacal ga yan Nigeria, yan Niger kuma dala dari ne (500)πŸ‘Œ zaka samu wannan littafi mai dubbin darussa a cikinsa.


_Domin tura kudin siyan littafin ga yan Nigeria sai a tura ta wannan account number din *2377403479*  Khadija Umar Abubakar. Zenith Bank. Kuma akwai damar tura kati ta wannan lambar   *081-686-594-14* IDAN KA YI TRANSFERT SAI KA TURA SHAIDA TA WANNAN NUMBER +227 93 81 16 18._


_'Yan Niger kuma sai ku tura katin MOOV ko Airtel ta dala dari watau 500 francs ta wannan lambar *+277- 94-98-56-52*_


Mun yadda daku, mun aminta da irin kaunar da kuke muna don hakan muna da yakinin cewa zaku siya don nuna mana kalar soyayya da kaunar da kuke mana da littafanmu.πŸ₯°
*Alhamdulillah*


Post a Comment for "MATAR MUTUM (kabarinsa) CHAPTER 1 Na Samira Harouna"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...