MATAR KULLE COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

MATAR KULLE COMPLETE

MATAR KULLE COMPLETE

- - Post a Comment

 MATAR KULLE COMPLETE


Hankaɗe ta yayi da ƙarfi tayi baya hade da buga kunkumin ta jikin gadon barcin su, ta sake yunƙurawa a karo na biyu zata tashi ya cukumo wuyan ta hade da manna ta da jikin bango yana binta da kallon mugunta sai huci yake yana zazzare idanu saboda tsananin masifa jijiyoyin kanshi da na jikin sa sun tashi rada_rada,

Qara ta sake cike da azaba saboda riqon da yayi mata numfashin ta har neman daukewa yake yi, kuka mara sauti take dan ta galabaita sosai har bata iya magana sai faman girgiza kai take yi,

"Wato Ni zaki mayar mutumin banza ko? Saboda gaki tunkiya ko wani namiji naki ne duk iya ƙoƙarin da nakeyi don kare miki mutuncin ki sai kin saka Ni na gaza, kinyi tunanin zakiyi min wayo dake da ɗan iskan saurayin ki ku yaudare Ni a gaban ido na kuma ban gane ba?"

Da qyar ta iya bude bakin ta cikin ginin kuka tace "khamis wallahi ba saurayi na bane kawai diban jini na yayi, Ni babu komai tsakani na dashi ka yarda dani"

"Babu komai tsakanin ki dashi shine bayan na nemo nurse mace ta dibi jinin kin kika kirashi yana tattaba hannun ki Kuna jin dadi sannan zaki fake da ɗiban jinin ki yake ko? Bari kiga abinda zanyi miki gobe ba zaki sake gangancin raina min hankali ba" ya fita a fusace fuuu,

Daga murya tayi cikin kuka tana qwala mishi kira "khamis! Khamis dan Allah kayi haquri na tuba wallahi" saboda tasan irin abinda zai iya aikatawa,

Bai bata lokaci ba ya dawo hannun shi dauke da vacuum plask Wanda ta zuba tafasasshen ruwa dazu da safe kafin su tafi asibiti, ya qaraso wurin da take zaune yana bude marfin plask din,

Zaro Ido tayi cike da tsoro ta fara ja da baya_baya tana "dan  Allah kayi haquri" Amman  Bai saurare ta ba ya sunkuya ya riqo hannun ta na dama "ina wannan hannun ya taba? Wannan hannun da nake matuqar so kika bashi dama ya taba qazamin jikin shi?"

Kwarara mata ruwan yayi a wrist dinta a zabure ta miqe tana sakin ihu cikin radadi da azaba ta fettu gefe tana diddirje wurin da hannun ta na hagu ko zata samu zafin da take ji ya ragu aikuwa saiga fatan wurin ya tattare garin sosawa ta kwaile shi,

"Wannan shine hukuncin ki na yau, bazan taɓa lamuntan iskanci ba kina da aure Amman Baki san mutuncin kanki ba, to bari kiji Ni ba sakarai bane kuma Ni kadai na biya sadakin ki na aure ki dan haka ke tawa ce Ni kadai duk wanda yayi ƙoƙarin shiga tsakani na dake sai na kawar dashi, kuma shi wannan ɗan iskan zaisan ya tabo matar khamis wallahi! Billahi!! Daga yau ba zai sake kwana a duniyar nan ba sai na kashe shi dan uban shi"

Ya ja qofar dakin da qarfi ya rufe da key ta waje tana jin fitan shi yanda ya kulle qofar parlor da qaran fitar motar shi ta kulle gate din waje,

Kuka ta sake sakawa tana nadaman auren khamis a karo na babu adadi, tayi danasanin yarda dashi tayi danasanin amincewa da soyayyar shi khamis ya lalata mata rayuwa data sani da ta ɗauki shawaran A'isha da duk hakan bai faru ba,

Ya saka ta rayuwa cikin qunci da wahala, tunda ya auro ta dauko ta daga Adamawa ya kawota Birnin Kebbi ya bude mata babin azaba saboda baqin kishi, ya hana ta riqe waya wai dan kada ta kira namiji ya hana ta kallon TV saboda kada ta ga namiji, tunda sukayi aure sai ɗaya taje gida shima wuni ɗaya tayi ya dawo da ita saboda yayun ta da qannen ta duka maza ne ita da qanwar ta guda daya ne kawai mata, babu ziyara, babu ta'aziyya, babu gaisuwan mara lafiya, babu Barka, babu suna rabon ta da fita gate kafin yau da suka je asibiti da safe har ta manta, khamis ya gama lalata mata rayuwa ta *tsane shi!!!*2

🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ Yanzu muka fara tafiyar🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ zamu garin nisa😂
Insha Allah zan dinga ƙoƙorin update akai_akai Amman posting kullum sai na gama *kama da wane* insha Allah

Kuci gaba da bin alqalamin Ummu Najma, masoya na ina alfahari daku matuqa🤩💝

Don't forget to follow me and vote for my stories on Wattpad @ayeeshatmuhd ✔️

Aci gaba da gashi💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

*Yesterday and today's morning I was like woww🤩 plenty of comments on matar kulle made me extremely happy that I just can't wait to continue posting it😅💖*

*The book is not long but I will make sure it will be interesting insha Allah 👏🏼 so please don't get tired on the way and reduce the rate of comments😏 I'm very proud of you my fans, ummu Najma loves you so much ❤️❤😘️*+

02🧛🏽‍♂️
1 year ago

Da qarfi nake jawo hannunta tana tirjewa Amman Saida nasan Yanda nayi Mata dole ta shigo cikin gidan mu, ta Yaya ma za'ayi ta wuce Bata gaida mama na ba?

Hango mama da tayi a tsakar gida tana tankaden garin tuwo yasa ta daina qoqarin komawa ta shigo ciki tun daga qofa mama take Mata sannu da zuwa, qarasawa wurin ta tayi ta tsunguna ta gaidata kanta a qasa ni Kuma Ina tsaye a kansu Ina dariya qasa_qasa,

Dagowa mama tayi tace "hajiya Kun dawo?" Gyada Kai nayi nace "eh mama"

Na manta ban gabatar da kaina ba, sunana Yusrah Ado Hisham shekaru na 19, mu fulani ne dake zaune a garin adamawa Amman mahaifiyata bahaushiya ce kuma ita na dauko a siffa da kamanni saboda chocolate color nake ba kamar mahaifina da yake da haske ba dukda shima ba sosai bane,

Ina da kyau irin nawa dai_dai gwargwado Yanda Babu Wanda zai ganni dai ya diba da gudu....lol^_^
Ina da yayu uku duka maza, sai qanne biyu mace da namiji macen itace autar mu Nasreen shekarun ta 12,
Yanzu haka na Gama secondary School Dina tun shekara daya da ya wuce Amman kasancewar jamb Dina beyi kyau ba yasa na jira sai wannan shekaran last month na sake rubutawa Kuma alhamdulillah na samu abinda ake so sauran admission muke zaman jira nida qawata Aisha Amman ita maths ne Bata dashi a waec da neco yasa take sake rubuta wani,

A hadda Kuma Ina ajin qarshe har Mun fara riqe ma malamai aji Dan ya zama kamar wajibi idan ka Gama karatu ka koyar Koda na shekara daya ne matuqar ba wani Abu bane ya Hana ka hakan,

Dawowar mu daga hadda Kenan nida aminiyata Aisha duk da gidan mu da Dan nisa saboda ba unguwa Daya muke ba Amman amintar mu ta zamo abin kwatance ma duk Wanda ya sanmu, Aisha sun fimu wadata dukda Suma ba za'a Kira su wasu masu fitinannen arziqi ba Amman ita mutum ce da Bata da girman Kai Bata da wuyan sha'ani shiyasa tamu tazo Daya dan Nima Haka nake🙊 ba yabon Kai ba fa,

Bayan Aisha sun Gama gaisawa da mamana na nemi Izininka raka ta bakin hanya ta Shiga napep gidan mu bayi da Nisa daga makarantar haddan mu shiyasa kullum sai na raka ta bakin hanya kafin na komo gida,

"Besty" Aisha ta kirani da sunan da muka Sanya wa juna, kallon ta nayi nace "na'am Yaya akayi?"

"Maganar ku da malam Naseer wallahi ni yabi ya matsamin Yana sonki in Miki magana ke Kuma saboda wulaqanci kullum nayi Miki magana sai kiyi min banza, Dan Allah ki fada min kina son shi ne ko Baki son shi na fada mishi ya sake min wuya"

Kai tsaye nace "kije kice Masa bani son shi"

"Amman meyasa please? Aisha ta tambaya da Dan damuwa a fuskar ta "kince Baki son malam Abdulqadir yanzu Kuma malam Naseer din da nake ganin ya fishi komai harda nutsuwa ma kince Baki son shi"

Tsaki naja nace " Ina kuwa yake da wata nutsuwa mutum sai shegen kallon matan tsiya Wai shi a dole malami, duk sun shiga rigan malanta malum_malum dasu suna 'bata yaran jama'a bakiga Yanda 'yammata ke liqe mishi bane? Kuma a hakan yake cewa Yana so na inyi me dashi?"

" Kina da matsala Yusrah to menene a ciki dan 'yammata suna binshi? kefa kikace su suke son shi ba shi yace Yana son su ba, ki auri abinki Dan Ina da tabbacin da gaske yake in yaso daga baya sai kiyi fighting halayen shi duk zai daina hankalin shi ya dawo kanki dan wallahi kafin ki samu irin shi a samarin yanzu ma said kinsha baqar wahala saboda dukan su kina kallon su kaman mutanen kirki ba qananun 'yan iska bane Basu da aure Amman sun San 'yammata da yawa"

"ba dukan aka taru aka zama Daya ba miss besty, Yanda kamannin mu yake daban_daban Haka halayen mu suke da banbanci ni nasan akwai Mai halin qwarai Wanda ba ruwan shi da matan banza, Wanda zai Soni kaman zai mutu sannan Yana tsananin kishi na Yanda bazai so kowa ya ganni ba ma ballantana a kwace Masa ni"

" Aikuwa da kin Shiga uku wallahi, bature fa yace everything too much is bad, Kuma Yanda kike wannan bayanin Allah Mai hankali ba zaiyi irin wannan abun ba, har wani kotsewa Kika kina harde hannayen ki wai 'mai tsananin kishi na'" ta fada a yangance tana wani kashe Ido,

"Wallahi Kika samu Mai irin wannan halin sai kin Shiga uku Dan said ya maidaki *MATAR KULLE* ganin ki sai mun yanki ticket"

Murguda Baki nayi nace " da'alla matsa, ke Baki San bature babban maqaryaci bane har Zaki wani kafa hujja dashi? Bari ki gani Allah ya bani irin shi haka zai maida ni kamar sarauniya saboda tsananin so da kiyayewa, yanzu dai tafi gida kada momyn ki ta Zane ki"

Na fada Ina Tara Mata a daidaita sahu, ban barta ta sake min magana ba nayi Mata ciniki na tura ta ciki ina daga Mata hannu har suka tafi sannan na koma gida na cire uniform dina na Shiga kitchen Taya mama tuwon dare,

Na Gama rude (talge) Kenan Zan hada sanwan miya mama tace babi Maggi da ajino tun kafin na dawo Kuma ta aiki Nasreen har yanzu Bata dawo ba, Raina a bace na Shiga dakin mu na dauko hijab na Zan fita Nemo ta na saka ma Raina idan har na same ta sai na make ta Raina ya baci sosai Babu abinda na tsana kaman na fara aiki wani Abu ya katse min shi ina Allah_Allah na gama naje nayi chatting,

Har na Kai bakin qofa mama tace "hajiya" Juyowa nayi Ina kallonta ta gwada ni da yatsa tace "wallahi sauran ki taba min yarinya ki gani nasan ki da saurin hannu kullum sai kiyi ta narkan ta kamar ke Kika Haifa min ita to wallahi kada ki kuskura"

Zumbura Baki nayi na fita ai kuwa a lungun gefen gidan mu na hango Nasreen sun baje da ita da qawayen ta suna carafke ga laidan Maggi can ta yada shi a qasa, saidana shashshafa Mata Mari kafin na dauko laidan nayo gida Ina sauri_sauri Jin tana Bina a baya tana kuka zata Kai qara،

Daya Shiga ta nayi hanyar dakin mu Zan boye har sai ta Gama kukan ta na fito lokacin nasan mama ta huce, ban Ankara ba sai ji nayi an gwabje ni na zube a qasa...........🤦🏻‍♀️
Follow, vote and share as you read

*Ummu Najma ce*😘

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

03🧛🏽‍♂️
Ban qarasa gane inda nake ba Nasreen tazo kaina tana kwarkwasa lokaci Daya ta daina kukan munafurcin da takeyi
"Wa ya fada Miki and taba auta a zauna lafiya?"

" Babu Wanda ya Isa ya taba auta na ransa Bai baci ba Amman kema na sake aikan ki Kika je kikayi zamanki ranki sai ya baci"+

Tashi nayi Ina qunquni na wuce dakin mu, "ai gwara ma mutum yayi aure ya fita daga gidan Nan ya huta, Kuma wallahi idan na riqe Nasreen sai ta Gane Bata da wayo"

Bansan maganar da nayi ya fito ba sai Jin mama nayi tana fadin "idan Kika riqeta Dan Allah kada ki barta da Rai, shashasha kawai"

Zumbura Baki nayi na Dale Kan katifar mu tare da jawo wayata na kunna data Nan messages Dina suka fara zuwa Allah_allah nakeyi su shigo gaba daya Naga zancan me akeyi a group, idan Kuma tuwo ne Nasreen din da suka find so sai tayi musu tunda koyaushe sai an nuna Mata fifiko a kaina,

Saqon Aisha na fara Shiga na duba har yanzu tana online kaman ko wani lokaci Dan basu aikin fari balle na baqi a gidan su maids keyi musu komai,

"Besty an kawo ashoben mu fa Ina gobe da wuri Zaki zo?"
Ashoben da take magana a Kai Na bikin autyn ta ne Wanda za'a fara gobe alhamis zasuyi family and friends shine mamanta ta hada dani da ita tayi Mana ashobe,
Na tura Mata "insha Allah Ina Gama abincin rana zan fito, kin karbo harda gyalallukan ne?"
" Eh sai kinzo kawai ki gani idanma akwai gyara sai mu mayar ma telan kafin lokacin sakawa yayi"

Daga maganar ashobe muka zarce hiran duniya Nan ma Saida ta sake kawo min maganar malam Naseer Amman na gwada Mata ba tashi nake ba yanzu, Saida aka fara kiraye_kirayen sallahn magrib sannan na fito na zuba ma yayu na ruwan alwala a buta na jera musu nasan Nan bada jimawa ba zasu zo su dauka sannan Nima nayi alwala na koma dakin mu nayi Sallah ko addu'a banyi ba na sake runguman waya ta naci gaba da chatting,

Mama da kanta ta tuqa tuwo ta zuba Mana nida Nasreen Bayan mun gama ci na nannarke ta na turn ta waje na rufe qofata kada mama ta sake Tara min gajiya, na Dan qara taba chat kadan sannan nayi sallan Isha nabi lafiyan gado saboda inaso gobe na Gama ayyuka na da wuri na ware gidan su Aisha,

Yau tun qarfe 11:30am na Gama abincin rana, ban damu da fadan da mama takeyi ba na tattara abubuwan da nake buqata su takalmi da jewelries dina na fita zuwa Raya bidi'a, da lokacin zuwa family and friends yayi Aisha da kanta tayi min kwalliya nayi kyau sosai kaman Yanda wasu ke cewa kwalliya tanayi ma baqaqe kyau, muka fito cikin ashoben mu na qannen amarya motocin da angwaye suka turo suka dibe mu zuwa hall din event,

Tun daga sauqa ta daga cikin mota Naga Yana Bina da Ido Yana jingine jikin motan shi Civic tare da sauran abokan ango, da ya lura kaman na Gane sai ya dauke kanshi Bai sake kallo na ba har aka kusan tashi lokacin da babban yayan mu usman yazo dauka ta,
Saboda nasan gaba Daya yayuna Basu da matsala yasa nayi ta marairaicewa ya tsaya zuwa wani lokaci kafin mu tafi, Yanda nake riqe da hannun ya Usman ko Ina janshi nakeyi ya Samar mishi da tsananin bacin Rai a tunanin shi saurayi na ne, nifa banma San dashi ba Dan sha'anin gaba na kawai nake yi kaman wata 'yar dangi,

Bamu koma gida ba a ranar sai Bayan sallar magriba, kafin mu tafi Ina tsaye jikin mashin din ya Usman Ina jiran shi ya fito daga masallaci hannu na riqe da waya ta Ina abinda ya zamo min sana'a wato chatting,

Har yazo kusa Dani Yana Shirin min magana ya Usman ya fito daga masallaci sai yayi saurin canza hanya nikuwa ban sani ba, na hau Bayan mashin din Yaya na muka tafi gida,

Bansan Yaya akayi ya Sami numbern Aisha ba Amman taga takuri da Bata taba ganin irin Shi ba ita Kuma Bata so ta bawa mutumin da bata sani ba number na kada ace Mai cutar wa ne, Amman saboda naci irin na khamis Saida yasan Yanda ya tursasa ta a ranar ta tura mishi number na,

Bai Kira ni ba sai washer gari har naje gidan su Aisha Mun fara Shirin kamu Wanda dress code dinmu lufaya ne zamu saka gaba dayan mu, Ina cikin shiryawa Naga waya na tayi haske, abinku da habibiyar phone nayi saurin dubawa, saqo ne aka turo daga baqon number,

A hankali na fara karanta shi cikin zuciya ta

" '''you are beautiful and special I've never seen any woman that captured my heart in a glimpse of an eye except you'''

'''dan Allah yau kada ki saka kayan da suka Kama ki Sannan kada ki tsananta kwalliya saboda ke ta musamman ce Kuma kyanki belongs to someone special, have a nice day my dear'''

_your beloved *Khamis*_

Da mamaki na nuna ma Aisha saqon, tsaki taja tace "wannan Dan anacin ne jiya haka ya Hana ni barci saboda fitina sai da na bashi number ki na samu kwanciyar hankali, tashin farko ya fara jero Miki wasu dokokin iskanci sai kace wani uban ki, ki jefa shi a kwandon shara kawai"

Qanqameshi hannun ta nayi cikin nawa Ina tsallen murna " wallahi besty yayi Mun, duk qualities da nake buqata Yana dashi Dan Allah muna zuwa ki gwadamin shi"

Baki bude Aisha take kallo na " Amman girl dinnan Baki da sense wallahi Ina jiye Miki tsoro ki daina buri ki roqi Allah alkhairin tarayya kada ki jawo ma kanki zama *MATAR KULLE* dan wannan khamis din tun Kuna saurayi da budurwa Kenan Ina ga kin zama matar shi?"

" Ai suna na ma kenan"
" MATAR KULLEN ko?"

Farrr nayi da Ido a yangance nace " qwarai kuwa, MATAR SO Kuma MATAR KULLE"

" Shikkenan Yusrah Allah ya Baki sa'a, qarasa shiryawa mu fita kada mu rasa mota"

Skin tight na saka da baqin Riga Wanda tsayin sa Bai rufe ciki na ba saboda lufayan mu Yana da duhu kuma yadin da kauri sosai nasan ba zai gwada jiki na ba,

ma Aisha aka fara nadawa ta fito sakk kaman kanuri har an fara nada min aka shigo sanar Mana motoci zasu tafi su barmu, Nan Mai nadawan ta hanzarta nada min bai wani zauna da kyau ba Kuma Nima ban damu ba Dan buri na yanzu kawai na ganni a cikin mota,

Muna Isa wurin kamu na matsa ma Aisha sai da ta nuna min Khamis, and I was like "hasbunallah khamis is all I need!!" Gayen ya hadu, ba zai wuce 28 ba tall and handsome ga arziqin shi moderate Dan har ga Allah bani son mutum Mai tsananin kudi saboda yawancin su Basu daraja matan su musamman idan suka San ba don Allah Kika aure shi ba,

Bawan Allan tunda mukaje hankalin shi na kan wayanshi fuskar Nan a daure tamau, Yana cikin masu jigila da dangin ango ne shiyasa yake zuwa da wuri, ko Shiga wurin bamuyi ba ya fada cikin motan shi yaja yabar wurin,

Biki yayi biki kada kuso kuga hajiya Yusrah na zage ana ta hidindimu Dani kaman ba karere ba, just then babban qaddara ta gifto Wanda har gobe bazan manta dashi ba, muna cikin rabon soveniers bansan Yaya akayi ba wata ta take min qasan lufaya na, motsawan da zanyi sai ga shi ya zamo daga jiki na Ina tsaye cikin jama'a daga ni sai skin tight da guntun Riga.............🤦🏻‍♀️

Don't forget to Follow, vore, share and comment as you read💖

*Ummu Najma ce😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

04🧛🏽‍♂️
Sandarewa nayi a wurin na kasa Koda motsa 'dan yatsa na I can't believe nayi tsirara a gaban dumbin mutane, kamar qiftawa da bismillah sai ga Khamis a gaba na, baisan Yanda ake nada lufaya ba Amman haka ya tattaro ya daura min Yanda zai rufe wurin da ya bayyana a jikin na Sannan yaja hannu na muka bar wurin event din,

Passenger seat ya bude ya saka ni Sannan ya zaga ya Shiga driver seat ya tada motar muka bar unguwar, tunda muka fara tafiya baice min komai ma Nima banyi magana ba saboda tsananin kunya ko kallon idon shi na gagara yi Amman ta gefen idona nake kallon Yanda jikin shi yake 'bari Wanda Nima bansan dalilin hakan ba,+

A qofar gidan mu Khamis yayi parking Yana zaune cikin motar ya runtse idanuwan shi Yana qoqarin daidaita nutsuwar shi ko zai samu ya iya min magana, ni Kuma da Naga yayi shiru kawai na bude qofar motar na fita tare da lalubo kalmar "Nagode" nayi cikin gida zuciya ta fall da mamakin Yanda akayi Khamis yasan gidan mu daga haduwar mu jiya, kuma ba tare da na gwada Masa ba,

Ina Shiga na hangi mama zaune a Kan tabarma da Nasreen kwance a Kan cinyar ta tanayi Mata tsifa, Nasreen na gani na ta kwashe da dariya ta fara tsokana ta saboda ta maida ni kamar sa'an ta, yarinyar ne Bata Jin duka kaman jaka ita idan ban masgeta ba ma Bata Jin dadi, tasan idan nayi niyyan dukanta ba'a Kan cinyar mama take ba ko Bayan baba ta dale wallahi sai na dirke ta Amman ganin ban kula ta ba duk sai taji Babu dadi,

Ina kwance ta shigo taga waya ta a ajiye Kuma ba barci nayi ba, tsungunawa tayi a bakin katifar mu tana tambaya ta abinda ya same ni, bansan nima me yake damu na ba, Zan fada Mata ne tsaraici na ya bayyana a bainar jama'a? Ko zan fada Mata sakaci na ne da ban maida hankali na suturta jikina da kyau ba?

Muryar Nasreen ne ya sake dawo dani cikin hayyaci na, tana Dan jijjiga hannu na tace "Aunty Yusrah ki fada min abinda ke damun ki dan Allah"

Tashi nayi zaune na rungume ta a jikina Ina sakin wani marayan kuka ko zanji sanyin radadin zuciya ta, yau badan Khamis ba da bansan Yaya zanyi ba haka na qarasa wunin ranar babu walwala a tattare dani tun mama tana magana har ta gaji ta Bari qarshe baba da yayu na ne suke ta aikin lallashi, sun Kira Aisha sunyi Mata tambayar duniyar Nan tace Bata San abinda ya same ni ba saboda tasan bazan so a fada ba wannan sirri ce tsakanin mu,

Har 12 na dare Ido na biyu Ina jiran Kiran Khamis saboda na samu damar gode Masa, Saidai abinda ban sani ba tunda Khamis ya koma gida zazzabi Mai tsananin zafi ya rufe shi ko magana bayi iya yi saboda tsananin zafin kishi,

Satin shi guda Yana fama kafin ranar da ya warke yaje ya dauko abokin shi angon dadan Aisha suka zo gidan mu, Ina kitchen Ina rabon abincin rana 'dan aike ya shigo yace Wai Khamis yana sallama da baba, Saida gaba na ya Fadi da naji an ambaci Khamis Dan tsawon lokacin da banji daga gare shi ba na dauka Ina tsumayen ganin shi,

Kalmar Baki bai taba Shiga tsakani na dashi ba Amman tunda ya taimake ni ranar son shi ya Gama mamaye zuciya ta, ban taba son wani 'da namiji kaman Yanda nake son Khamis ba kullum idan na dauki ways ta sai naji kaman na Kira shi naji me yasa Bai neme no ba Amman sai wani bangare na zuciya ta ya Hana ni, Amman yau gashi Allah ya kawo min shi har gida, bansan da me yazo ba Amman Ina fatan Allah yasa auren mu yake so ayi Nan da wata 1😁

Ban qarasa rabon ba nabar wa mama sauran taliyar ta a cikin tukunya da gudu na ruga na qule cikin dakin mu suka bini da Ido, hularshi baba ya dauko ya fita waje ya samu Khamis da yaji dalilin zuwan su ne yayi musu iso cikin gida Nasreen ta shimfida musu tabarma suka zauna,
Rimi_rimi Khamis yayi ma baba bayanin cewa izini yake so ayi mishi ya fara nema na kafin ya turo iyayen sa ayi magana, baba ya yaba da hankalin Khamis saboda a zamanin yanzu Koda ace saurayi Yana da niyyan auren yarinya sai sun Gama daidaita a kafin ya nemi iyayenta, hakan yasa yayi mishi izini sannan ya fara bincike sosai a kanshi,

Ranar da Khamis ya fara zuwa wuri na da sunan Hira I almost jumped over with excitement, nayi kwalliya ba da yawa ba na shirya cikin atamfa ta na qasan akwati na murza dauri sannan na tarbe shi a parlon baba da hadadden abinci da drinks,
Khamis is indeed a great talker he really knows how to impress any girl with his sweet words Yana sani inji kaina kamar wata sarauniya Mai daraja , na Gama mutuwa a Kan Khamis yanzu bani da burin da ya wuce ni da shi mu zama Mata da miji,

Soyayya da shaquwa ya ginu tsakani na dashi, Hala qaunata da way ya qaru sabida akwai Khamis a cikin ta, ko girki nakeyi ko wanki ko shara Kai kome nakeyi muna way da Khamis a hankali a hankali yasan abubuwan da nakeyi da abubuwan da nake so da mutanen da nake tare dasu, ko fita baniyi sai da Izinin Khamis, gyalelluka na gaba Daya sun koma na Nasreen saboda Khamis bayi so, Ina fita da gyale zai kirani yayi ta surutu sai naje na saka hijab Kuma bansan Yaya akeyi yake sani ba Dan ko mantawa nayi na fita ba tare da sanin shi ba sai ya nuna bacin ranshi sosai,

Ni Kuma saboda irin son da nake mishi yasa bani son ganin bacin ranshi ko qanqani har gidan su Aisha sai da na rage zuwa saboda Khamis Bayan hadda bani fita ko Ina sai ya zamo Dole,
Da ya lura da irin son da nake mishi ne yayi amfani da wannan damar ya saka na fara saka niqab da socks idan Zan fita Wanda shi da kanshi ya siya Mun, to be honest I was very uncomfortable in it saboda mahaifin mu bayi da wannan tsananin, gyalalluka na manya ne sosai Kuma mama Bata yarda na yafa shi anyhow idan zam fita sai ta tabbatar na suturta jikina na da kyau,
Amman saboda irin son da nakeyi wa Khamis yasa na jure, a ranar da aka kawo goron tambaya aka hado da sadaki sannan aka saka Rana watanni 4 lokacin iyaye na sun Gama shiryawa tunda ba wani qarfi sosai ne dasu ba,

Kafin a karbi sadakin Khamis baba yazo min da result din binciken da sukayi, an duba anga Khamis bayi da matsala wurin addini sannan hanyar da take samu ta halal ne Amman Kuna yanayin mu'amalan shi da jama'a akwai naqasu, saboda shi mutum ne Mai tsananin zuciya Kuma idan ya qullace ka HAR ABADA ba Zaku sake samun jituwa ba, sannan akwai wani Abu daya Kuma bayi son competition ko kadan, ko Kaya ne ya siya ya saka idan wani ya siya irinta to haka zai kunna ma nashi wuta ko ya jefar a bola duk irin son da yake yi ma abun kuwa,

Abun Bai ko dameni ba nacewa baba naji na amince Babu matsala saboda Daman nasan dole za'a Sami matsala ta wani wurin because no body is perfect,
Kwanci tashi Babu wuya a wurin Allah yau aure na da Khamis sauran sati biyu, ni da Aisha Mun Gama raba ashobe ma sauran qawayen mu yanzu haka ta fara rabon Kati, ni Kuma an kulle ni a gida ana min gyaran jiki ko Khamis dinma ya daina gani na saboda anyi mishi transfer zuwa  birnin kebbi shiyasa a can dinma ya nema Mana gidan hayan da zamu zauna,

Da daddare Ina kwance Ina sana'ar chatting Aisha ta shigo a birkice, nasha mamakin ganin ta a irin wannan lokacin na tashi na zauna Ina tambayar ta abinda ya faru,
"Yusrah kinsan cewa Khamis daga babban gida ya fito Bai fada Miki ba? Kuma Yana da qanne da yayu maza da Mata, babban abinda yafi daga min hankali shine Wanda nasa ya bincika Mana ya fada min Yana da zafin rai sosai Kuma bayi da hali don akwai wani abokin aikin shi da mummunan sabani ya taba Shiga tsakanin su har yau ba'a sake ganin shi ba, Kuma ana kyautata zaton akwai saka hannun Khamis a batan shi...........🤦🏻‍♀️
_Don't forget to follow, vote, share, and comment as you read_ 💖
*Ummu Najma ce* 😘

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

*Masu complaint din a qara yawan typing kuyi min haquri, typing novels biyu a lokaci daya is not an easy task, Ina Gama rubuta KAMA DA WANE komai zai daidaita insha Allah saboda yanzu shi na saka a gaba,*

*Thanks for the love and support💝 love you so much 💞*

05🧛🏽‍♂️
Kallo kawai nake bin Aisha dashi har ta gama kwararo baya Nan ta Sannan na ja dogon tsaki "wallahi kinban kunya ban taba tunanin hassadan ki har kaina zai hau ba, kina baqin cikin Zan Riga ki aure shine kike so ki 'bata Khamis a Ido na daga baya ki lallaba ki aure min shi ko? Allah ya Isa tsakani na dake Aisha Kuma ni ba irin mutanen dake daukan jita_jita bane ballantana kiyi tunanin qarairayin ki zasuyi tasiri a kaina"+

Tsananin mamaki da firgici sun Hana Aisha magana, tayi sakare tana qare min kallo Bata taba tsammanin haka daga gareni ba, ban ankara ba sai naga hawaye zirrr a fiskar ta na sake Jan wani tsakin qasa_qasa Yanda nasan zata jini nace "munafurci kawai"

Muryar ta har sarqewa yake yi saboda takaici da qyar ta iya furta "Yusrah haka Zaki ce? Yanzu idan ma zanyi hassadan sai nayi Miki? Me kike dashi me akayi akayi Khamis da zanyi Miki hassadan auren shi??, I just care about you saboda ke aminiyata ce idan na Bari wani abu ya sameki Bayan inada halin karewa Allah bazai barni ba that's it"

" You are lying maqaryaciyar banza kawai, wallahi tun ranar da na hadu da Khamis na lura da take taken ki, I regret calling myself your best friend tunda amintakar ki batai min Rana ba inda ace bansan me wacece bane Kuma bansan sirrikan ki ba to shine, nasan you are desperate to get married saboda buqata da kike dashi Amman ba hakan na nufin sai kinyi min qwacen Khamis bane Zaki samu kiyi aure, go and find a guy for yourself babe, qeace Bai dace dake ba kwata_kwata"

" Sanin kanki ne cewa ba rasa mijin aure nayi ba, yeah! Na yarda nayi babban kuskure da na bude Miki ciki na Amman kinsan da ace da gaske auren nake son yi ba Zan nemi Khamis ba, ban rasa samaruka ba ban rasa mijin aure ba ke kanki shaida ne a kan haka, Kuma Koda ace na rasa kalma daya Zan fada wa mahaifi na zai kowa min mazaje har gida sai Wanda na zaba, Wanda suka find Khamis asali, dukiya, haduwa da Kuma cancanta ni wallahi ko a qafa aka daura min Khamis Zan since na Yar"

Shewa nayi hade da tafa hannuwa Dan babu qarya Aisha ta bani dariya, tana kuka Amman ita Wai dole sai ta cakka min maganar da zai saka na rabu da Khamis Bata San kuwa ta makaro ba domin ni da shi Mun Riga Mun zama hanta da jini rabamu sai mutuwa,

"Aishatu kenan da Baki samu irin khamis din bane kike cewa idan aka daura miki shi a qafa Zaki Yar Amman wallahi tallahi ba zanyi kaffara ba da Khamis zai Budi Baki yace Kee yake so Babu abinda zai saka kiqi amincewa Kuma ki aure shi a lokacin ba tare da sani na ba"

"Shikkenan Yusrah bazan zauna Bata yawun Baki na Ina musu da ke ba, Ko zamu samu sabani banyi tunanin namiji bane zai Shiga tsakanin mu Yusrah saboda irin son da nake Miki yasa na tilasta mahaifiyata tayi amfani da kudin da za'a canza min system harda qarin nata a kai tayi hiring detective ya bincika Mana Khamis ciki da waje Amman gashi kin watsa min qasa a Ido thank you so much, Babu komai kin nuna min matsayi na da iyaka ta Kuma nayi kuskure da na tsallake shi Kinga tafiya ta" ta dauki jakarta tayi hanyar fita,

STORY CONTINUES BELOW

Ganin ta gasa min Mai zafi zata tafi ban mayar Mata da raddi ba yasa na dan daga murya kadan saboda dare nace "idan Kinga dama HAR ABADA kada ki sake dawowa cikin rayuwa ta Babu Yanda za'ayi na cigaba da Hulda da munafuka inba tsoro ba kije kiyi auren sai na tabbatar da abinda kike fada, aikin banza kawai"

Kuka ne yaci qarfin Aisha ta rufe bakinta kada 'yan gidan mu suji sannan ta fita da sauri dukda tana Jin Kiran da Nasreen take mata, kafin ta qarasa motan yayanta Saida ta Sha kukan ta a qofar gida ta daidaita nutsuwar ta saboda Bata son kowa ya gane abinda ya faru tsakanin mu, tana Shiga mota yayanta safwan ya fara azalzaleta wai take ta zauna, tana jinshi ta share abinda nayi Mata kadai ya isha ta,

A ranar kasa barci nayi, Saida Aisha ta tafi Naga rashin kyautawar da nayi Mata, ita mutum ce Mai nagarta ni shaida ce Akan hakan Amman yarda na ita Yana nufin rashin gaskata nagartan Khamis Kenan,
Allah ya gani inason Aisha sosai Dan Yanda nake jinta yafi qawancen inajinta kamar 'yar uwata matsayin da take dashi a zuciya ta Daya da na Nasreen (ohh do you mean Koda ace Nasreen ce taso aibanta Khamis Zaki iya rabuwa da ita Kenan?)

Well I don't know, nidai abinda na sani shine son da nakeyi wa Khamis ya ninka Wanda nakeyi wa Aisha saboda ita Ina sonta ne kaman Yanda nake son rayuwata shi Kuma Ina son shi fiye da Yanda nake son rayuwata, enough with the questions please ummu Najma,

(Tsuke Baki na nayi kada Nima ayi min irin Koran Aisha) lol😂

Washe gari da safe haka na tashi jikina Babu kuzari gaba Daya zuciyata ta Shiga damuwan rashin Aisha kusa dani, ana ta shirye_shirye baqi na ta zuwa gida na qara cika Amman Babu besty nah a tare dani har aka fara events din biki Aisha Bata leqo ko Daya ba Nan ne na Shiga tashin hankali,

Gaba daya sai Naga kaman abubuwa Basu tafiya daidai kwata kwata Babu Wanda yake min abinda ya dace, Aisha ce kawai tasan abubuwan da nake so Kuma bata nan,

A komai sai samun matsala akeyi saboda Babu Aisha, sauran qawaye na Basu kula da abubuwa Yanda ya Kamata kowa kawai burin ta tayi saurayi a wurin Amman Babu Mai bautuwa min ta kula da buqatun baqi na tayi duk wasu wahalhalu Dan ganin biki na ya tafi perfect, Nasreen kadai nake dashi yanzu Kuma itama ta Gaza,

A komai sai anyi latti, kayan sawa na ma Basu kammalu ba Wanda suke a matsayin qawaye na Banda barci da Hira a ways sai ci Babu abinda suka iya, kayayyaki na suna wurin tela, head dina Yana kasuwa, size din takalmin da Zan saka yayi girma infact everything is a mess saboda Babu Aisha,

Damuwa na yanzu ya fara fitowa a fili inason na Kira ta naji Yaya take Amman girman Kai da Kuma qaunar Khamis ya Hana ni, saidai Kuma tunda aka fara hidiman biki damuwa na suka fara raguwa saboda Yanda Khamis ke tarairaya ta Yana shagwabani Yana nuna min zallar so abin ba'a cewa komai,

Na yarda Khamis yasan Kan mace dan idan Yana tare dani ji nake nafi ko wace mace sa'a a duniya kaman sauran ma ba aure sukayi ba, idan naga Mata da mijin ta a wurin bikin mu sai na tausaya Mata da ba Khamis ta aura ba nasan ma Bata San menene dadin aure ba,

Har aka gama bikin mu aka kaini gida na a birnin kebbi Aisha tana kwance tayi qaryan rashin lafiya Bata so mamanta ta Gane wani Abu ya Shiga tsakanin mu, ta daure sai dirkan magani da allurori takeyi har daga qarshe ya jawo Mata ciwon gaske ta rame lokaci daya tayi baqi ko iya tashi Bata iya yi sai an daga an kwantar saboda illar magungunan a cikin jinin ta ni kuwa Ina can Ina cin amarci,

Farkon rayuwar mu da Khamis abin burgewa abin sha'awa da burin samu wurin ko wace 'ya mace, sai da na Shiga gidan shi ne na dada tabbatar wa son da take min sahihi ne so ne Mai tsabta Babu algus a ciki, Daman normally kunsan amarya Bata fita sai ta dauki tsawon lokaci to hakan Nima nake kullum Ina cikin gida manne da mini na muna zabga soyayya,

A ranar auren mu Khamis ya saka na karya sim card Dina ya saya min wani Amman already inada numbern admins din groups din da nake ciki rubuce a takarda shiyasa Ina sakawa na bude WhatsApp aka maida no cikin groups Wanda gaba Daya su ma zallan Mata ne aka ci gaba da hiran duniya,

Ban sani ba Ashe hakan da nayi ba qaramin Bata was Khamis Rai yayi ba saidai bayi son na fahimci hakan, cikin dabara muna zaune Ina faman latse_latsen waya ya karba ya buga shi da gini a take ya tawarwatse sai ya fake da Bai sani bane gobe_gobe ze Kai a gyara harda bani haqurin qarya, ni Kuma ban kawo komai a Raina ba na bashi wayar,

Washe gari Bayan ya dawo daga aiki inata murna an gyaro min waya ta sai ganin shi nayi da injin wanki niqi_niqi ya kawo ya ajiye min yace nayi haquri sai qarshen wata zai siya min wani wayar yanzu kudin hannun shi ya qare kuma bayi so in dinga wanki da hannu na bayi son na wahala,

To kunji Yanda na rabu da wayata gaba daya Kenan............🤦🏻‍♀️

Don't forget to follow, vote, and share as you read,💖

*ummu Najma ce😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

06🧛🏽‍♂️
Bayan kwana biyu da yin haka, Khamis na wurin aiki nazo girki na samu bani da ashanar da Zan kunna gas dashi, bani da 'dan aikan da zai siyo min Kuma Babu waya a hannu na ballantana na tambayi Izinin shi kafin na fita, shiyasa banyi wani tunani ba na saka hijab dina na fita waje ko Zan Sami shago na siya,+

Tsayawa nayi Ina qarewa unguwar kallo banma San Yaya tsarin shi yake ba don tun ranar da aka kawo ni cikin gidan kaina a lullube ban sake takowa waje ba, wani 'dan almajiri na samu ya nuna min Yanda shaguna suke naje na siya ashana ban tsaya wani Abu ba na dau hanyar komawa gidan dukda na lura kaman Mai shagon Yana min kallon sani Amman ban kula shi ba don ni ban sanshi ba,

Har na bude qofar jikin gate Zan Shiga gida naji muryan mace tana min sallama, Ina juyawa Naga Mata ne da mijinta da alama kaman daga unguwa suke ko Kuma unguwa zasu je,

"Ina wuni amarya, sunana maman auwal nice maqwafciyar ku dake wannan gidan" ta fada tana nuna gate din gidan dake gefen nawa ta hannun hagu,

Da murmushi a fiska ta muka gaisa sannan na gaisa da mijinta
"Kiyi haquri fa, kin Sami maqwabciyar da kirkin ta yayi yawa har yau ban samu na shigo ba Amman insha Allah cikin satinnan Zaki ganni"

"ayyah Babu komai maman auwal ai komai sai Allah yaso, yanzu dai Ina jira tunda kin saka rana zanyi ta baza Ido"

Dariya tayi tace " bama sai kin baza Ido ba amarya umm...."

" Yusrah"
" Yauwa amarya Yusrah gobe ko jibi Zaki ganni da ikon Allah, mu zamu wuce unguwa a gaida Mai gidan idan ya dawo"

"insha Allah zaiji na gode" haka na tsaya har Saida suka Shiga mota suka bar wurin matar sai daga min hannu takeyi tare da 'danta Wanda nake tsammanin shine auwal din kafin na Shiga gida,

Ina Jin Dadi a raina nima mutane zasu fara Shiga gida na Kuma Zan Saba da mutanen unguwar da nake domin tunda nazo Babu Wanda ya taba zuwa gida na ko daga dangi na ko daga dangin Khamis Wanda ban ma San ko mutum 'daya a cikin su ba Bayan mahaifiyar shi da mahaifin shi da na ganshi a photo,

Cikin gaggawa na samu na daura abinci, qarfe 1 har ya kusan wucewa nasan yanzu haka Khamis Ya kusa dawowa shiyasa nayi jallop rice na hada da salad Wanda bani rabuwa dashi saboda Khamis Yana so sannan na jere shi a qaramin dining dinmu Mai wurin zaman mutane 4 na Shiga wanka,

Qaran bude gate da naji yasa na Gane shine ya dawo, cikin hanzari na fito daure da towel ko Kaya ban saka ba na daura hijab Dan ban sani ba ko ba shi kadai ya dawo ba, ganin shi nayi hakince a Kan hannun kujera ya daura qafar shi daya a Kan kujeran daya Kuma ya sauqe shi qasa ko takalmin qafarshi Bai cire ba ga fuskar shi a murtuqe kaman anyi mishi alqawarin jahannama,

Da fara'a ta na qarasa wurin shi Ina Masa oyoyo Amman Yanda Naga ya fuske yasa nasha jinin jiki na sai Kuma na fara tambayar shi me ya faru,
"Wa ya Baki izini ki fita daga cikin gidan nan Yusrah? Me yasa Kika fita?"

" Laa shago fa naje baby, ashanar mu ya qare ne Kuma bani da waya balle na Kira ka na tambaye ka"

" Me yasa ba Zaki nemi 'dan aika ba ma ko Kuma ki jira ni idan na dawo naje na siyo Miki da kaina?"

Dan marairaice murya nayi ganin lokaci daya kaman ya dauki abun da zafi nace " baby Babu Wanda na sani fa a unguwar Nan yanzu idan na bawa yaro 500 kuma ya gudu min da canji na fa? Bani so na Bata lokaci ne kuma bani son ka dawo da yunwa ban tanadar maka da abinci ba Amman kayi haquri hakan ba zata sake faruwa ba"

Wani tsawan da ya daka min Saida ya saka hanjin ciki na kadawa ya tashi a zuciye ya qarasa wurin dining ya dauki food plask din da na saka abincin Yana nuna ni dashi,

"A Kan wannan abin ne kika fita Kika zaga unguwar Nan ko wani banza da jaki ya qare Miki kallo? Yusrah kin cutar dani sai me idan na dawo gida da yunwa? To yunwar ta kashe ni mana! To hell with your filthy food" ya fada a tsawace tare da jifa da food plask din Bai Fadi ko Ina ba sai jikin show glass dina ji kakeyi ta..tsa..tsau komai yayi rugu_rugu a wurin,

Numfashi naja da qarfi har Ina neman shidewa na koma gefe Ina kyarma gashi Allah yayi ni da bala'in tsoro, lokaci daya Khamis ya canza min sai ina ganin wannan kaman wani ne bashi Khamis Dina ba,

Bai damu da yanayin da nake ciki ba ya tako inda nake tsaye sannan ya ja wuyan hijab din dake jikina tun daga sama har qasa ya dare ya zamo daga ni sa towel, cukumo suman kaina yayi da qarfi Saida na saki qara saboda azaba Yana qare min kallo cikin Ido,

Cikin izza da qunci ya fara magana "yanzu wani ya kalli cinin idanun ki ya saqa wani Abu a ranshi, wani ya kalli lips dinki shima yaji wani Abu a ranshi, wani kina wucewa Yana kwatanta yanayin surar ki, wani Kuma Yana Jin kaman Yana tare dake, Kuma ke din nawa ne ni kadai Dole tare Dani Zaki rayu Kuma tare Dani Zaki mutu babu Wanda zai mallake ki duk duniyar Nan bayan ni Amman yau kin cutar dani,

irin cutarwa da bazan iya yafe Miki ba dole nayi Miki hukunci saboda Nan gaba kada ki sake maimaita makamancin wannan kuskuren" ya qarasa fada hade da sakin gashin kaina ya tura ni gefe ya zare belt din jikin wandon shi ya nannada a hannun shi sannan ya nufi ni, ban Ankara ba naji ya sauqe min tsumagiya a cinya gashi Babu Kaya a jikin na..............🤦🏻‍♀️
2
_don't forget to follow, vote, share and comment as you read_

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

07🧛🏽‍♂️
Kada kuyi tsammanin dukan wasa Khamis yayi min, Saida ya tabbatar bani iya motsi kafin ya rabu dani Ina kwance shame_shame a qasa ya fita daga gidan gaba daya, ranan Naga tashin hankali don ko iya sallan la'asar banyi ba ko Ina na jiki na ciwo yakeyi duk da ni ba fara bace Amman shatin dukan da yayi min ya fito rada_rada a saman fata na,
Nafi awanni biyu Ina kwance naci kuka har na gode ma Allah dan tunda nake iyaye ne ko malamai na Basu taba min irin wannan dukan ba da qyar na daddafa na tashi da Jan qafa na Shiga daki, Ina ganin fuska na a mirror bansan lokacin da na saki kuka ba gaba daya kamanni na ya canza Khamis ya kumbura min fuska da duka,+
Sake komawa cikin toilet nayi na hada ruwa Mai Dan zafi na saka qaramin towel Ina gasa jiki na sai bayannan ne na danji sauqi kadan nayii alwala na fito na samu wata 'yar guntun Riga Mara nauyi Wanda tsayin sa iya cinya na saka sai na daura babban hijab har qasa a Kai Na tada Sallah inayi Ina kuka don ko wani gaba na jiki na ciwo yakeyi,

A cikin sujjada na fara Kai kuka na ma Allah Amman Kuma sai na rasa roqon Allah zanyi ya saka min zaluncin da Khamis yayi Mun ko Kuma Zan roqi Allah yasa ya sauqo ya daina fushi ne? He punish me out of love, son da yake min da kishi na ne ya jawo haka idan na roqi Allah yayi Mana sakayya ban kyauta mishi ba,

Ina cikin sallar Khamis ya shigo ya zauna a bakin gado Yana jiran in idar, ajiyar zuciyar da yaji inayi ba qaqqautawa yasa yaji zuciyar shi tayi nauyi Yana Jin baqin cikin dukan da yayi min da Kuma tausayi na, Bai san Yaya akayi har zuciyar shi da qwaqwalwar shi sukayi tasiri wurin ingiza shi ya aikata abinda zai cutar dani ba,

Ina sallamewa ko addu'a banyi ba naji ya rungumo ni ta baya Yana maimaita kalmar "I'm very sorry baby" harda 'dan qollan munafurci, qara nayi kadan saboda fama min ciwuka na da yayi,
yayi saurin sake ni ya dawo ta gaba Yana fiskanta ta still Yana fadan "sorry" ya zare hijab din jikina na Yana qarewa raunukan da yayi Mun kallo ya runtse idanuwan shi tare da kawar da kanshi gefe kwata_kwata baiji dadin gani ba,

Kaman Mai iskokai ya sake zaran key din motar shi ya fice, Bai dawo ba sai Bayan 45 minutes ya shigo da laidoji a hannun shi lokacin Ina parlo Ina tattare broken glasses da ya fasa, ajiye laidan yayi cikin sassarfa ya qaraso ya daga ni daga wurin ya zaunar dani a Kan kujera sannan ya bude daya daga ciki laidojin ya Ciro wani healing ointment ya fara shafa min, sai binshi da Ido nakeyi Yanda take shafa min maganin a darare Yana runtse Ido da ciza baki kaman a jikin shi ciwon yake,

Saida yabi duk wani wuri da ya shata min bulala da magani sannan ya tashi da kanshi ya dauko plate da spoon a kitchen ya zuba abincin da ya siyo ya fara feeding dina ba tare da yace min komai ba,
Nima bance Masa qala ba kuma banqi karban abincin ba Saida ya tabbatar ciki na ya cika sannan ya ajiye plate din a gefe ya dauko bottle water a fridge shima ya bani a Baki, durqusawa yayi a Kan guiwowin sa ya riqo tafukan hannaye na cikin nashi sannan ya sauqe wata nannauyan ajiyar zuciya ya fara fadin

"Kiyi haquri dan Allah Yusrah ba'a son Raina na aikata Miki haka ba, shaidan ne ya yayi min qawa a zuciya shiyasa na hau dokin zuciya da Kuma tsananin son da nakeyi miki, ba Zaki fahimta bane Amman da za'a bude Miki zuciyata ba Zaki juri ganin irin tarin son da nakeyi miki a ciki ba, sonki ya jawo nake tsananin kishin ki saboda a kullum buri na bai wuce ki kasance tawa ni kadai ba Zan iya mutuwa idan na rasa ki Yusrah"

Lokaci daya naji duk wani 'dan guntun haushin Khamis da nake ji ya gushe son da nake mishi ya dawo sabo qall harda burbudi a Kai domin Khamis ya riga ya Gama dani shi e ya zamo cikar burikan rayuwata duk wasu mafarkayyan da nakeyi Khamis ya maida su gaskiya,

"Yusrah!!" Ya Kira suna na cikin nutsuwa, Juyowa nayi Ina kallon shi yace
"Kiyi min alqawarin duk wuya duk rintsi ba Zaki guje ni ba, idan hakan ta faru Kuma Yana nufin qarshen rayuwata tazo, Kuma ki sani idan har da sauran rabon tarayya a tsakanin mu duk inda Zaki tafi sai naje na nimo ki ko cikin qasa Kika shige Nima sai nasan Yanda nayi na biki saboda ba Zan juri rashin ki ba, I love you alot darling"

Wayyo Allah dadi, a take naji zuciya ta tana sukuwan farin ciki Wai nice mini na yake min irin wannan son to me Kuna Zan Nima a rayuwar duniya? Khamis ya riga ya bani komai bani buqatar wani Abu Kuma

Tallafo fuskar shi nayi da hannu na cike da kissa nake shafa sajen shi fuskata dauke da faffadan murmushi nace
"Don't worry my dear husband, Yusrah taka ce Kai kadai kake da ikon yin Yanda kaga dama da ita, Allah ya riga ya mallaka maka ita, ba zata guje ka ba HAR ABADA Yusrah tana qaunar ka sosai da sosai Kuma tana neman yafiyar ka akan laifin da ta aikata,

Dariya Mai sauti yayi ya miqe yayi min peck a goshi Yana faman zunduma min ruwan albarka, da kanshi ya tattara broken glasses din show glass Dina da ya fasa, tun daga lokacin Kuma muka dawo normal kaman Babu abinda ya taba Shiga tsakanin mu don ni tuni nama manta da yayi min laifi,
washe gari yana dawowa daga office ya shigo cikin salo da dabara ya stura ni bedroom dina ba tare da na Ankara ba ya saka ma qofar key har sanda suka gama abinda zasuyi cikin parlorn ya sallami ma'aikatan sannan yazo ya bude ni Ina fitowa nayi arangama da sabon show glass babba Kuma sabon design, (wait!! ba Khamis bane yace kudin hannun shi ya qare bayi da Wanda zai siya waya ba?)

Haka dai ban zurfafa bincike ba na nuna mishi nayi farin ciki da hakan Kuna shima yaji dadi sosai da na gwada hakan amman Kuma shakku ya fara d.'darsuwa cikin zuciya ta game da magananun Khamis yawancin abinda ya fada ba shi yake aikatawa ba'

Friday
4:07pm

Naji ana knocking gate din gida na, da murna naje Zan bude yau Nima nayi baqi Amman naji gate din a rufe daga murya nayi nace "ana zuwa sannan na koma ciki da gudu na duba cikin drawers da Khamis yake ajiya na dauko spare key naje na bude,

Aisha ce da yayanta Safwan kafin na dawo daga duniyar tunani naji ta rungume ni tana "oyoyo besty"............🤦🏻‍♀️
*Post din Kama da wane sai gobe idan Allah ya yarda, bani da charge yanzu Haka ma manage nayi na samu yin wannan"

_Don't forget to follow, vote, share and comment as you read_ 💖

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

08🧛🏽‍♂️
Cike da farin ciki na dago Ina kallon fiskar ta ita dinne da gaske, iso nayi musu cikin gidan Ina mamakin zuwan su, nasan duk daren dadewa wasu zasu zo daga garinmu Amman banyi tunanin Aisha bace zata zo saboda Yanda mukayi rabuwan rashin mutunci,

A parlo suka yada zango na kawo musu drinks da snacks sannan na koma gefen Aisha na zauna muna gaisawa da ya Safwan, dukan wasa takai min a cinya ta hade rai tace+

"Haba bestie, meye a cikin duniyar Nan da Zaki guje mu dan kinyi aure?? Ko sau daya baki Kira ko a way kinji lafiyar mu ba gashi kema idan an Kira wayan ki bayi shiga gaba daya kin tada hankalin mama kinsa ta dago mu Babu shiri"

Murmushi nayi Ina murza zoben hannun na cike da kunya da Jin nauyin Aisha dan har yanzu ban manta zagi da tozarcin da nayi Mata ba Amman gashi yau tazo gareni kaman ma Babu abinda ya raba faruwa,

"Sorry bestie waya ta ne ya samu matsala Amman next week yace zai gyaro min insha Allah, Yaya gida Yaya momy Yaya kowa da kowa?"

" Hmmm abubuwa da yawa sun faru Bayan Baki Nan ai da masu dadi da marasa dadi, kwanaki irin ciwon da Nasreen tayi bamuyi tsammanin zata rayu ba wallahi yanzu Haka kwana biyar Kenan da Mata operation din appendix"

Dafe qirji nayi hade da zaro Ido Ina maimaita "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Yaya akayi hakan ta faru ban samu labari ba?"

" Bake 'yar aure dadi ba? Har aunty suhaila ta rasu da 'dan cikin ta anyi 40 shima Baki sani ba"

Cike da jimami nake girgiza Kai Ina " hasbunallahu wa ni'imal wakeel, Allah sarki ya Safwan Yaya haquri"

Murmushin Yaqe yayi yace " haquri alhamdulillah"

"Allah ya jiqansu ta yasa ta huta, Allah yasa aljannah ce makomar ta"

Da "ameen" ya amsa lokacin da wayarshi ya fara ringing, yayi excusing kanshi sannan ya fita waje don amsa Kiran, Yana fita Aisha ta matso kusa Dani tare da daka min duka a cinya wannan karon zafin shi ya shige ni na fara sosawa Ina binta da harara,

"Ke an kawo sadaki na fa? Za'ayi Aure na in 3 months time, Ina ta so in disa Miki gurmi Amman na kasa samun ki Nima na kusa Shiga layin ku"

Ta qarasa tana wani rangwadi tare da rausaya Kai kaman wata qadangaren gobara, hannu na miqa Mata muka tafa da bayyanannen Jin Dadi saman fiska na nace "Masha Allah gaskiya nayi Miki murna best inama ace Ina Nan a adamawa za'ayi komai tare Dani!"

" Ai kin riga kinyi missing, sai fa haquri Dan Allah ya gani ko sahun qawaye na ba Zaki Shiga ba kije kiyi ta saka Burma burman hijab Wai gaki matan aure"

Muna cikin zantawa ya Safwan ya shigo ko zama baiyi ba yace ma Aisha "mu tafi ko? Kinga dare nayi Kuma da tafiya sosai a gaban mu", marairaice fuska nayi nace "Allah sarki Yaya ka Dan Bari zuwa anjima Mana ko minti 30 fa bakuyi ba Kuna nasan idan kuka tafi sai na dade ban sake ganin ku ba",

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi yayi yace " qanwata tuqin dare Babu dadi Kuma Kinga hanya akwai nisa mama ne ma tace muzo yau mu kawo Miki sauran kayayyakin ki da aka kawo daga baya ko zakiyi amfani dasu Amman da sai kin shekara guda kafin muzo"

Ana cikin haka Khamis ya bude qofa ya shigo, ganin Yanda yake a firgice yasa gabana faduwa! Inada tabbacin motar ya Safwan da ya gani a waje ne ya daga Mishi hankali fata na Allah yasa kada yayi wani Abu da Bai dace ba a samu shaidan da za'a Kai ma iyaye na dan already nasan Aisha qiris take jira har yanzu yanayin ta bai nuna ta gamsu da Khamis ba,

Fuska a sake Safwan ya miqa mishi hannu suyi musabaha, Khamis ya tsaya Yana qare wa hannun kallo Wai gardin da ya shigo mishi gida ne saboda tsabar rashin kunya zai miqa mishi hannu su gaisa?,

Baice musu komai ba ya juya a fusace yayi ciki, Safwan na ganin haka Yaja hannun 'yar qanwar shi sukayi min sallama suka fita, sauqe ajiyan zuciya nayi ganin har sun tafi Khamis Bai fito ba da sauri na bi Bayan shi dan ganin me yake yi a ciki,

Shigana ke da wuya Naga Khamis ya nufo qofa zai fita da zuqeqiyar screw driver, a tsorace na rufe qofa na qaraso inda yake murya qasa nake tambayar shi me yake Shirin aikatawa,

Shaquro wuya ta yayi ya buga ni da garu Yana zazzare idanun shi da suka kada sukayi jaa ruwan bala'i kwance a cikin su,
"Kashe shi zanyi, wallahi sai na kashe shi kema na kashe ki Kuma nazo na kashe kaina, ba Zan boye Miki ba Yusrah tunda Naga rashin sani ne yake saka ki aikata ganganci, I'm evil when it comes to you, bani da Imani ko kadan akan abunda nake so abinda ya raba ni da family na da brothers dina Kenan"

Sake ni yayi ganin na fara qaqarin mutuwa a hannun shi, zubewa nayi a Kan guiwowi na Ina tari ji nakeyi kaman ya daure ni da kaca a wuya na, shima tsugunawa yayi ya matso kusa Dani har yana Jin sauqar numfashi na, sannan ya fara gwada ni da screw drivern hannun shi
"Dole nasa mahaifiyata ta rabu da sauran qanne na da yayu na ta dawo zama tare Dani kadai kinsan dalili? Because I love her so much, ita kadai nake so Dan haka itama dole ta Soni ni kadai I never share what I love I hate to share my loved ones,

Yusrah na gaji da boye Miki asalin dabi'u na da Kuma ni wanene, idan inaso dole a So ni Kuma ba'a so tare dani, Ina sonki kina Sona yanzu ya zamo Miki dole ki bar son kowa sai ni kadai Zaki bawa dukkan soyayya da kulawar ki kinji ko?" Ya qarasa a tsawace,

Amman bashi ya firgita ni ba, Jin wani zafi da azaba a gefen ciki na ne ya rikida ni, a hankali na sauqar da idanu na wurin don naga wani Abu ne haka, sai arangama nayi da screw drivern dake hannun Khamis ya bula ruwan ciki na, na saka hannu na na shafo jinin da ke malala daga jiki na Ina qare Masa kallo, lokaci daya naji wani jiri idanu na suka daina ganin komai sai duhu, rigib na zube a qasa tun daga lokacin ban sake gane inda kaina yake ba,
A hankali na bude idanu na inajin sunyi min nauyi, jujjuya kaina nake yi dan na samu gane inda nake, asibiti ne aka kwantar dani harda oxygen ana saka min ga Khamis zaune Yana riqe da hannu na daya ya kwantar da kanshi a jikin gado na,

Fara tunano abinda ya faru baya har dalilin da ya kawo ni asibitin nayi, Babu wacce ta Fado min a rai sai Aisha ,Ina tuna ranar da Aisha tazo gidan mu da daddare ta fada min gaskiyar Khamis Amman nayi Mata Koran Kare, Aisha is right Khamis is an evil person yanzu Kam na fara yarda da maganar ta,

Har yanzu Ina son Khamis Kuma har gaba Zan ci gaba da son shi, Amman tsananin tsoron shi ya Kama ni kuma zanyi takaicin kasancewar shi haka da bakin shi ya fada shi ba mutumin kirki bane Yaya yaranmu zasu ji idan suka taso suka ga uban su haka? Shin zasu dinga min addu'a saboda na sama musu uba na gari ko Kuma zasuyi Allah wadai dani da nayi zaben tumun dare?

Zare hannu na nayi daga cikin nashi a hankali Ina qoqarin tashi na zauna, firgigit ya farka da azama yayo kaina Yana dudduba ko Ina don ganin ko lafiya nake, runtse idanu na nayi gamm Ina tsoron Khamis ya sake qoqarin min wani abun bayan wanda yayi min a baya,

"Baby please open your eyes, I'm very sorry please ki taimaka ki kalle ni, kwanan ki biyu kina kwance a nan idanun ki a rufe look into my eyes please"

Takaici ne ya turnuqe ni duk abinda ya farun nan kalmar da Khamis zai fada min Kenan in yi haquri? Hawayen da bansan na meye bane suka fara bin kunci na Ina tausayin kaina a hannun Khamis wallahi I'm not sure ko yana da cikakken hankali,

Ganin hawayen fiska ta yasa ya sake rikicewa ya fara shafa fiskana Yana girgiza ni kaman want mahaukaci ya fara sumbatun da ni bani Gane komai a ciki bayan open your eyes da ya fada yafi qafa 50,
Qara zage qarfin shi yayi Yana girgiza ne harta hantan ciki na Saida suka jijjiga ga gefen ciki na da yayi min rauni inajin kaman Yana sake stabbing dina a Kan ciwon wurin sai qara fitar da jini yake yi, dukda oxygen din da aka saka min Amman Ina Jin numfashi na yana qoqarin daukewa,

nikam ta kaina da wannan bawan Allan, anya Khamis ba burin kashe ni bane a ranshi ya fake da wani soyayya? Ana cikin haka doctor ta shigo ganin abinda Khamis yake min yasa tayi saurin qarasowa wurin shi tare da ture shi gefe tana masifa,

Saidai da Khamis ya fara nashi sai ta saka ma nata bakin sakata banbami yakeyi kaman zai tashi dakin da muke ciki Wai dole tasa na bude Ido na kalleshi Kuma nasamu lafiya mu tafi gida,

Jin tana magana a Kira security yasa na bude Ido na tare da cire oxygen mask din fiska na da qyar nake iya magana a haka dai na lallabi doctorn ta haqura Bata saka an fitar da Khamis ba Amman Saida ta Kore shi kafin ta dudduba ni tana fita ya sake dawowa..........🤦🏻‍♀️
Don't forget to follow, vote, share and comment as you read💖

And also don't forget that this novel is fiction Naga fans are getting emotional😂 kowa sai masifa take tana qarewa Khamis tanadi🤣 just chill an enjoy the story, I agree that it happens sometimes but a case like this is rare and happens on contrary,

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

_*I REPEAT* don't forget that this novel is fiction Naga fans are getting too emotional😂 kowa sai masifa take tana qarewa Khamis tanadi🤣 zagi kuwa jiya yasha fiye da qafa 150👻 uwar shi ma ta kwashi rabon ta🥵 just chill an enjoy the story, I agree that it happens sometimes but a case like this is rare and happens on contrary_+

09🧛🏽‍♂️
Qarasawa kusa dani yayi Yana taba ni dan ya tabbatar da lafiya ta Amman hakan da yayi tsoro ya bani Ina gani kaman so yakeyi ya sake stabbing dina na mutu ya huta, a tsorace nake dan jajjanye jiki na daga gare shi kwata_kwata naqi yarda mu hada Ido bansan hakan da nayi ya qara tunzura shi ba, ya riqo fuska ta a dole yasa nake kallon cikin idon shi,

"Baby Wai me kike so ne? Ba nace kiyi haquri ba? Ko kina tunanin Zan fitar Miki da jini a son Raina ne?"

Har ga Allah bani da qarfin magana, jiki na da kaina Yana min mahaukacin ciwo numfashi na bayi fita da kyau uwa uba azaban da ciwon na yake min, Amman a haka na daddage Saboda Yanda take masife ni nace
"Na haqura fa Khamis"

"To a Kan me yasa ba Zaki kalli fuska ta ba? Fuskar wa kike son kallah iye? Yusrah haka Zaki Mun tun ba'aje ko Ina ba kin fara nuna min akwai gurbin wani a cikin zuciyar ki bayan ni?"

" Ka rabu dani dan Allah Khamis, ka barni naji da Abu daya ple...."

Magana ta ne ya katse saboda numfashi na da yake Nima daukewa gaba daya na fara gasping for air Amman Khamis ko lura da hakan Bai yi ba gaba Daya idanun shi sun rufe sai tashin hankali yakeyi shi kadai,
Hayaniyan shi ne ya shigo da doctorn da ta duba ni dazu tare da wata nurse a bayan ta, ta nemi nurse din da taje tayi magana da security suzo su fita da Khamis Amman duk da halin da nake ciki firr naqi, ba Zan juri ganin ana wulaqanta miji na ba,

Khamis na dakin ta sake dubani sannan tayi min alluran barci saboda na samu hutu daga fitinar shi dukda yunwar fitan hankali da nake ji kuwa, tana fita ya sake dawowa gefen gado na Amman wannan karon a hankali yake magana don a tunanin shi na riga nayi barci,

"A Kan me Zaki ce na rabu da ke Yusrah? Kinsan kuwa me kalmar rabuwa dake take nufi? Rabuwa da rayuwata fa Kenan! Wallahi indai Ina raye Yusrah bazan rabu da ke ba, ke ko mutuwa nayi ma Allah bazan rabu da ke ba sai nasan Yanda zanyi mu kasance tare"

Yana surkullen shi mai kama da na mahaukata nayi barci na barshi, zuciyata ta ta fara saka min kokwanto a kan lafiyar Khamis, ko shi kalan tashi soyayyar Kenan Mai wuya da azaba?

Sake farkawa nayi a Karo na biyu Amman na kasa bude idona saboda tsoro, nasan fiska Daya Zan fara cin Karo dashi itace na khamis Amman 'dan hayaniyan da naji yasa nayi saurin wangale idanuna na zuba su a Kan mutanen dakin,

Mahaifiyar Khamis ce zaune tana yanka fruits da wata qanwar shi, numfashin da naji ta gefen fuska ta yasa na maido da duban na wurin aikuwa sai idona a cikin nashi,
"Good morning baby" ya fada fuskar shi dauke da murmushi"

Nima 'dan guntun murmushin na mayar mishi da qyar na iya amsawa da "morning" sannan na fara qoqarin tashi ga ciwon da ciki na yakeyi, sauri yayi ya tallafa min na zauna yayi magana ma mahaifiyar sa da barin jiki ta matso min da abinci da fruits din da ta zauna ta gyara min qanwar shi kuwa har qasa ta tsunguna ta gaida ni,

Bani da kuzarin amsawa da qarfi sai kawai na gyada Mata Kai sannan na fara sauqa da nufin Shiga toilet, Khamis da kanshi ya taimaka min ya kaini har ciki Bai damu da idon mahaifiyar shi ba yaja qofa ya rufe Saida na Gama abinda zanyi ya taimaka min na kintsa jiki na nayi alwala muka fito ya saka min kujera a saitin gabar saboda bazan iya Sallah a tsaye ba,

Ina idar da sallah ya dauko abinci ya fara feeding dina, kadan naci nace na qoshi haka kuwa ya rufe Ido Yana zubar ruwan bala'i Wai saboda a hannun shi ne yasa naqi cin abinci, uwar shi kuwa tana kallon mu bata ce Masa komai ba, ni na lura ma kaman tsoron shi take ji,
duk abinda ya zartar tofa babu mai jayayya dashi harda mahaifin sa, sai da ciki na ya cika damm na fara qaqarin amai tukunna ya rabu dani, ya bani ruwa shima Saida na Sha glass biyu inajin kaman ciki na zai fashe wani qarin rashin lafiya sabo ya taso min Amman na matse,

Shiru ne ya ratsa dakin na wasu lokaci Ina zaune Ina rarraba idanu, Khamis kuwa ya saka ni a gaba kaman TV motsi daya zanyi ya ishe ni da sannu da tambayoyi kaman sabon 'dan jarida, yarinyar da suka zo tare kuwa tunda ta gaida ni har yanzu Bata sake cewa uffan ba Kuma Ina kyauta zaton a dalilin Khamis ne,

Baki na nakai dai_dai kunnen shi nace
"Baby har yanzu 'yan gidan mu basu zo ba?"

"Me Kuma zasu zo suyi Miki?"

" ban gane me zasu zo suyi min ba? Baka fada musu bani da lafiya Ina kwance a gadon asibiti bane da bazasu zo su duba ni ba"

Hade fuska yayi Yana binta da mugun kallo yace "Wai me kike nufi ne Yusrah? Kina so na Kira iyayen ki ne nace musu by mistake nayi stabbing dinki har an kwantar dake a asibiti na kwana 3 suyi tunanin na aure ki ne don in cutar dake? Ba ga mahaifiyata ba, zatayi miki duk wani abun da kike buqata kawai fada Mata abinda kike so zakiyi tai miki"

For the first time naji takaici da baqin cikin Khamis ya turnuqe ni, ya fiye son kansa Khamis kanshi kadai ya sani Bai damu da kowa ba Kuma,
"Yanzu da ace ban tashi ba na mutu shima ba zaka fada musu ba sai mahaifiyar ka kadai"

Zare min idanun shi yayi tare da daka min tsawan da yasa dole na firgita Daman da burbudin tsoron shi cikin raina, bani kadai ba harda yarinyar da suka zo tare da mahaifiyar shi, ita kuwa kaman ma ba a dakin take ba she didn't show any reaction as a mother,

"Kada ki kuskura ki sake min irin wannan Maganar, bamu samu zuri'a ba kike maganar mutuwa? Babu Wanda zai sanar ma iyayen ki ballantana a daga musu hankali, Zaki warke garas in dauke ki mu tafi gida muci gaba da rayuwa shikkenan",

Daga Jin wannan Maganar na gyara kwanciya na just ma Khamis baya hawayen takaici na sintiri a fiska na, gwanda nayi kukan ko Zan samu naji sauqin abun dake zuciyata Dan nasan ko fada ma mahaifiyar shi nayi aikin banza ne dan Bata nuna zata iya wani abu a Kai ba,

A haka na cika sati na 3 a asibiti kafin aka sallame ni muka koma gida ba tare da iyaye na sun Sami labarin abinda ya faru dani ba, to be honest I've never seen a crazy family like khamis's, mahaifiyar shi wani lokaci kaman tana tsoron shi,
wani lokaci ta dawo bashi umarni kawai Yana bi ko magana in a commanding manner take mishi wani lokaci Kuma sai ta koma kamar wata gunki, ko magana mukeyi ko fada da tashin hankali sai ta rufe kunnen ta kaman Bata ji ba idan Kuma na matsa Mata da complain sai tace wai mace ta gari da haquri aka santa da Kuma biyayya was mijin ta, haka dai na haqura naci gaba da zama tare da Khamis saboda har yanzu Ina son shi, wataran da dadi watarana akasin haka,

Tuesday
7:08pm

Da qarfi nake qwala ma Khamis Kira Ina dariya, ya fito a firgice daga toilet Yana wanke singlets dinshi, hannun rigan shi a nannade ,yayi tunanin wani abin ne Kuma ya same ni, tsayawa yayi daga nesa yana qare min kallo, na nuna TV da yatsa na Ina fadin,

"Kaga a film din da muke kallo ranan ishq mein marjawan 2, Vansh ya bankado asirin kishiyar uwar shi da Kuma tsohon saurayin matar shi, baka ga kalan wulaqancin da yayi musu ba shiyasa nake SON SHI wallahi he is very intelligent,

_Faty amadulle ke kadai Zan gaisar saboda ke kadai ce kike team din Khamis 😅 kin riga kin fada musu duk abinda yake yi ba laifin shi bane SANYI NE Amman sun kasa ganewa🤣🤣🤣_
_Alhamdulillah yau na Gama rubuta KAMA DA WANE daga gobe Zaku fara samun long chapters idan Allah ya yarda_

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

10🧛🏽‍♂️
Wani mugun kallo Khamis ya bini dashi Sannan ya qarasa jikin TV ya Ciro shi daga jikin bango ya rada shi da qasa, taqarqarewa yayi ya tuma tsalle a Kan screen din TVn Nan a take ya 'burma, sai sauqe numfashi yake Yana huci ya fara takowa wurin da nake, sai a lokacin qwaqwalwata ya fara hasko min barnan da na aikata,+

Tsoro da fargaban abinda Khamis  zai iya aikata min ya Kama ni Kan kace me na zura a guje na Shiga bedroom dinshi na rufe qofa dake shi yafi kusa Kuma nasan idan na Shiga daki na zai iya dauko spare key ya bude,

Dukan qofar yakeyi da iya qarfin sa kaman zai ballata Yana qwala min Kira, jiki na sai tsuma yake Ina karkarwa na kasa bude Masa qofa kaman Yanda yake umarta na, da qyar na daga murya Baki na ya it's furta
"Dan Allah kayi haquri wallahi ba da wani nufi na fadi hakan ba"

Ci gaba da dukan qofar yayi Yana "ki bude qofar Nan Yusrah kafin ranki ya baci"

Cikin gunjin kuka nake roqon Khamis Allah da Annabi yayi haquri Amman ko saurara ta baya yi sai bugun qofa yake yi har tsoro ya Kama ni kada yaji ma kanshi rauni, Bayan kaman mintuna 10 muna cikin wannan yanayin sai Kuma naji diff kaman daukewar ruwan sama, hargowan da yakeyi ya tsaya,

Har zuwa wani lokaci banji komai ba, sadaqarwa nayi na qarasa jikin qofar na murda key na bude Ina hadiyan yawu, abinda na gani shi yayi matuqar firgita ni, Khamis ne kwance a qasa warwas kaman gawa nayi kansa da gudu Ina taba shi ya tashi Amman shiru, hannu na Kai Kan hancin sa naji bayi numfashi, rasa abinda zanyi nayi dan kaina ya kulle Ina kuka nake Kiran sunan shi Ina bubbuga shi da sauran qarfi na,

Wani dabara ne ya Fado min na saka hannu na cikin aljihun wandon shi na zaro wayar shi da nufin ko iyayen shi ko abokin shi Zan Kira na fada musu halin da yake ciki su kawo min dauki, saidai wayan a gargame take Kuna password ne ba pattern ko finger print ba ballantana na samu budewa cikin sauqi, gwada saka sunana nayi Naga ko zai bude amman baiyi ba, na saka na mahaifiyar shi shima haka, haka nayi ta trying kusan 6 attempts Babu sunan Wanda ban saka ba harda nashi Amman wayar Bai budu ba sai kawai na Shiga kitchen na dauko ruwan sanyi daga fridge na dinga shafa mishi a fuska cikin ikon Allah kuwa yaja wani dogon numfashi ya furzar sai ya bude idanun shi,

Tashi yayi ya zauna Yana Bina da sharp look ga idan shi sunyi jawur saboda bala'i Amman Bai ce mini uffan ba, sunkuyar da kaina qasa nayi Ina bashi haquri Bai kula no ba saima tashi da yayi ya shige dakin da na fito yayi zaman shi lokacin sallan Isha nayi ya fita ba tare da ya furta min ko kalma daya ba,

Zuciya ta baiyi min dadi da abin da nayi Masa ba, ai ance idan kasan halin mutum sai kasha maganin zama dashi, tunda nasan miji na Mai tsananin kishi ne da ban yabi wani har na furta kalmar so a kanshi ba,
Babu Yara a gida na ko Kuma baqi masu shigowa ballanta ya dauki datti shiyasa kawai na kunna charcoal Yana kamawa na zuba turaren wuta na bude ko Ina dashi Sannan nayi Sallah na qara powder da lip gloss sannan na feshe jikin na da turare na fito hada mishi dinner zuciyata na taraddadin dawowar shi cikin gidan bansan da me zai shigo ba,

STORY CONTINUES BELOW

Baiyi sallama ba kaman Yanda ya Saba ko yashe idan zai shigo gida, kaitsaye ya wuce ya ja kujera ya zauna nayi serving dinshi yaci yayi damm ya tashi yayi tafiyar shi ciki, haka muka qarasa Daren Ranar Khamis kaman kurma ko qwqqwaran tari yaqi yi duk abinda zance Masa saidai ya bini da ido Kuma da alama har yanzu ranshi a bace yake,
Da wuri nayi Shirin kwanciya na canza Kaya na zuwa na barci sannan nazo gefen shi na kwanta, Ina jiran Khamis yaune gobe ne har bacci ya dauke ni Yana zaune ya tasa laptop a gaba, 2:06 na farka na miqa hannu na Kan bedside drawer na dauko waya na, kunna flashlight nayi Ina haska Khamis dan naji shi manne da jiki na,

He is sleeping peacefully kaman bashi bane ya Gama rikita ni dazu ba, gyara zama nayi na fara jero addu'oi Ina tofa mishi dan bazanyi qarya ba tunani na Yana bani akwai wani matsa a tare dashi, ban Ankara ba Ina Kan mishi tofi Ashe bawan Allan ya bude Ido,

Sunkuyowa da zanyi da nufin tottofe shi idanu na suka sauqa cikin nashi a take ciki na yayi wani kuka qulululu, na fara rarraba Ido Ina kame_kame tun ma Bai tambaye ni ba, finciko ni jikin shi yayi sai Kuma ya juya ya dawo shine a sama na ya sauqe min nauyin shi gaba daya cike da mugunta,

Da kaman ba zaiyi magana ba dukda roqo da magiyar da nakeyi mishi sai Kuma ya saka bakin shi daidai kunne na in a wisper yace
"Kada ki taba tunanin rabuwa dani Yusrah, bazan iya jurewa ba ko kadan bazan yarda kiyi nesa dani ba, idan kikayi gangancin rabuwa dani Zan azabtar dake, I will surely make you suffer bansan irin abinda zanyi ba idan Baki tare dani Zan iya illata duka mutanen gidan Nan idan sukayi qoqarin raba ni dake dan haka ki tsayar da idon ki a kaina kawai, ni kadai, Allah ya riga ya bani ke duk duniyar Nan Banga Wanda ya Isa ya raba ni dake ba wallahi"

Nidai qoqarin ture shi kawai nakeyi Dan ji nayi numfashi na Yana neman daukewa, kaman Wanda ya tuna da wani Abu yayi saurin sauqa daga gadon ya fita daga dakin gaba daya, kafin ya dawo na rufe Idona na samu barci ya dauke ni kafin ya dawo ya ci gaba daga inda ya tsaya,

12:44
Tsaye nake a kitchen Ina bare maggin da Zan saka a Miya naji qaran buga gate, ajiyewa nayi na fita a darare na qarasa bakin gate din na tambaya waye ne? Ina tuna abinda ya faru dani lokacin zuwan su ya Safwan da Aisha,
"Maman auwal ne" ta bani amsa

Da sauri na Shiga dakin Khamis na dauko spare key na bude Mata ta shigo tare da qaramar 'yarta da take goyo, karban yarinyar nayi zamu Shiga ciki tun a qofa ta fara min gorin zuwan ta gida na sau uku kenan Amman ni na kasa leqa gidan ta har tana cewa daga yau ba Zata sake shigowa ba idan banje ba but little did she knows ko gida Khamis ya hana ni zuwa Naga qanwata da aka ce bata da lafiya,

Bayan an sallame ni daga asibiti da na sanar dashi anyi ma Nasreen aiki zanje na duba ta haka ya rufe Ido ya dinga masifa Wai ai Bai Kamata ba ko wata 5 banyi ba na fara sintiri n zuwa gida, Ina ji Ina gani ya hana ni Amman ya bani wayar shi munyi magana dasu sau 'daya shi kuma yaje har gidan ya gaida su har ya zaga dangi,

"Allah kuwa da gaske nake wannan shine zuwa na qarshe idan har Baki Shiga min ba ga gida Baki da hanci Amman ko leqe ya gagare ki"

"Dan Allah auntynah ayi haquri insha Allah kwanan Nan Zan shigo, har yanzu ban fara fita bane shiyasa Amman a list daga gidan mu sai gidan ki"

"ohk Allah yasa da gaske Dan alqawarin ki kaman ruwa ne a cikin kwando, to Yaya gida Yaya maigidan"

"lfy qlau Yaya su auwal"

Da "lafiya qlau" ta amsa min lokacin ne abin da ya faru da Khamis a Jiya ya Fado min, na Dan matsa kusa da ita sannan nace "yauwa maman auwal dan Allah kinsan babban malamin Nan da yake bada magani? Ana yawan sa wa'azin shi a TV ni meye ma sunan shi? Yauwa malam aminu(not real)"

" Eh ai duk Wanda ke zaune a birnin kebbi yasan shi, Amman maganin me Zaki je karba a wurin shi? Ko Baki da lafiya ne?"

Inda_inda na fara nace "Aa...bani bace qani na ne"

"Ayyah, me yake damun shi? Kinsan ba ko wani irin magani take bayarwa ba yafi bada Wanda suka shafi aljanu ko mayu ko Kuma na karya sihiri, shima irin matsalar ne yake damun shi?"

" I can't say, har yanzu bamu tabbatar ba Amman inaga idan muka fada mishi signs din zai iya ganewa tunda ba zai yiwu muje tare dashi ba"

" To shikkenan idan kin shirya sai mu tafi Amman Kinga gobe zamu fi samun shi available"

Sanin Khamis ba zai barni na fita ko Ina ba yasa kawai nace Mata bazan samu zuwa ba Amman na zayyane Mata duk alamomin da Khamis yake nunawa Wanda nake tunanin rashin lafiyar aljanu ne, tace zata karbo maganin ta kawo min,

Kaman Yanda mukayi da maman auwal bayan kwana biyu ta kawo min maganin tamin bayanin Yanda za'ayi amfani dashi, yanzu matsalar guda 'daya ce takk Yanda Zan saka Khamis ya amince yayi amfani da wannan maganin,

Qarfe 2 ya shigo gidan, na tarbe shi cikin so da kulawa yau Kam a fili ya fito yace min na Shiga daki za'a shigo ayi gyara, banyi musu ba na Shiga ya saka key ta waje kusan 30 minutes suka dauka suna aikin kafin ya sallame su suka tafi ya zo ya bude ni,

Yaja hannu na zuwa kitchen, da Shiga na nayi arba da qaton gas cooker Mai dauke da oven a jiki, dake da table gas aka kawo ni daga gidan mu, juyawa nayi Ina kallon khamis sai faman zabga murmushi yake yi yace "I hope you like it, zai sauqaqa Miki aiki"

" To baby waya na fa?............🤦🏻‍♀️
*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

*To the tons and tons of readers, fans, commenters, A VERY BIG THANK YOU💖 haqiqa naji dadi sosai Yanda kuka bani goyon baya kuka amshi MATAR KULLE hannu hudu_hudu 🤭 wallahi abin so Masha Allah 🤩 I will like to dedicate some pages to some of you Amman yawan ku yasa hakan ba zai yiwu a short book ba Amman duk Wanda take yi ta sani, a duk inda kuke ummu Najma tana son ku tana alfahari daku💞*+

11🧛🏽‍♂️
"Sai next month yanzu kudin hannu na sun qare"
Bata Rai nayi nace " haba baby this is the 4th time da kake fadan haka ni Banga amfanin gas dinnan ba daman wayan ka siya min da kudin, abincin namu nawa ne da zamu buqaci gas me Kai 4 da oven? Bani baking komai, deserts siyowa kake yi kaga Babu amfanin da zaiyi Mana"

" Naji to, shi wayan amfanin me zaiyi Miki?"

"Ko fa Kiran iyaye na bani samun yi saboda bani da waya, inaso ko wani lokaci Ina gaisawa da 'yan uwa da abokan arziqi" na fada hade da Turo Baki

" 'yan uwa da abokan arziqi sun fini daraja Kenan da Zan so Abu kiyi min musu ko?"

" Aa Basu fika daraja ba Amman kaima kayi min alqawari baka cika ba, gidan Nan idan ka fita haka nake zama shiru Babu 'dan abinda zai dauke min kewa"

" Allah sarki iyayen mu, a lokacin su Babu wani waya ko TV, radio ma sai gidan wane da wane Kuma haka matayen su suke zaune cikin gidan mazajen su without any complain, kema idan Kika qara haquri kwanan Nan Allah zai bamu yaran da zasu dinga debe mana kewa, idan kuma gaisawa kike son yi da iyayen ki sai na Baki nawa ki Kira su Kuna gamawa ki maido min da abuna Amman a yanzu na fada Miki bani da kudin waya indai ba sata kike so nayi ba"

" Aa Allah ya baka haquri, ka je ka canza kayan ka kazo muyi lunch" na fada sannan na fita daga kitchen din,

Tun kafin yazo nayi serving abinci na barbada garin maganin da maman auwal ta karbo min, ban zuba tun a cikin girki bane saboda bani so na munafunce shi Ina mishi magani ba tare da sanin shi ba idan har ya gane hakan ba zaiji dadi ba, yanzun sauran damuwan shine Yanda zanyi convincing dinshi yayi amfani da na shafawa Bayan anyi wanka da Kuma na hayaqi, hakan ba Abu Mai sauqi bane,

Fitowa yayi da T-shirt da three quarter ya zauna, har yakai spoon daya Yana Shirin Kai na biyu ya lura da Abu kaman qasa a saman abincin,

Saurin ajiye spoon din hannun shi yayi Yana gwada abincin da yatsa yace "menene wannan Yusrah?"

Shagwabe murya nayi nace "Haba baby Zan baka abin da zai cutar da Kai ne? Na riga da na mallake ka ballantana ace maganin mallaka na saka maka" na qarasa cikin sigar zolaya,

" No ba abinda ya Dame ni ba Kenan, ni idan Kika saka min maganin da zai saka na qara son ki saidai nayi Miki godiya Amman matsalar shine daga Ina wannan abun ya fito? Waye ya kawo shi? Ko fita kikayi daga gidan Nan ba tare da sani na ba?"

Da sauri nace " Haramun!! Wallahi ko waje ban sake leqawa ba tun daga wancan ranar, maman auwal maqwafciyar Mun Nan ne na aika ta kawo min, magani ne"

STORY CONTINUES BELOW

"Maganin mene?"

Sunkuyar da kaina qasa nayi Ina wasa da yatsu na, zuciya ta fall da taraddadin Yanda Khamis zai dauki maganar, bansan me zaiyi tunani a Kai ba Amman Allah ya gani da tsarkakakkiyan niyya na aikata haka,

"Uhm...mm...maganin...." Sai Kuma nayi shiru na dago Ina kallon shi,

"Uhm hmm Ina jinki ai, nace maganin menene?"

"M...maganin matsalar shafan aljanu ne, Yana calming mutane idan sukayi amfani dashi Kuma naga Yanda kake da saurin mm... You usually get angry or furious easily, sudden mood swings, and about yesterday's incident shiyasa kawai nayi tunanin ko zamu jarraba ko za'a dace maganin ya...."

"A taqaice dai kina nufin bani da hankali Kenan"

kafin na bude Baki nayi wani magana ya daga plate din abincin da yake ci ya watsamin shi a jiki na ban Ankara ba naji ya dauke ni da Mari ya qara min daya a kuncin hagu har Saida na ga wani green light ya gifta ta Ido na,
Miqewa yayi ya danqo ni riqon gaske har Saida naji qashin kafadu na sunyi qara, bansan lokacin da na saki kuka ba nasan ko bashi haquri nayi sai ya Ida nufin sa, so yin hakan ma aikin banza ne,

" I don't want to hurt you yusrah but you keep repeating your mistakes, ban ma yarda da wannan maganin ba wa ya sani ko so kike ki fitar Dani daga hayyaci na ki tsere Mun tunda nasan lafiya ta lau saidai idan kece mai aljanu,
Ita Kuma wannan munafukar matan ta samu na barta tana shigowa cikin gidan Nan shine zata hure Miki kunne ta saka ki cutar dani ko?"

Sake ni yayi, yayi hanyar waje Yana fadin, "Bari naje na same ta sai ta fada min uban da ya Sanya ta kawo Miki wannan 'dan iskan abun da sunan magani, shegiya munafuka irin su ne matan mutane suna zaman zaman su zasu fara hure musu kunne su kawo musu matsala a zaman aure kwana biyu kiji anyi saki saboda maqwaftan, wannan karon kam batayi sa'a ba because she messed with a wrong guy"

Saurin bin Bayan shi nayi na riqo hannun shi Ina Girgiza Kai, kuka nakeyi kaman Raina zai fita nace "Aa wallahi Babu ruwan maman auwal a ciki Khamis, ni na roqeta ta nemo min maganin Bata ma san maganin ma kai bane,"

"koma menene ita ta sani, Amman Ina son tabbatar miki duk ranar da Kika rabu dani itama tayi bankwana da mijinta har abada kuwa,

"Aa Khamis Dan Allah kayi haquri wallahi bazan sake ba dan Allah kada kaje ka cutar da ita Babu ruwanta a cikin duk abinda ke faruwa"

Bai saurare ni ba ya ci gaba da tafiya, ni Kuma na daddage iya qarfina Ina janshi baya har Saida yaje jikin qofar dake gate Amman ban haqura ba Ina janyo shi Ina kuka, na kanainaye shi na qi bashi daman bude qofar saboda bani so ya jawo Mana abun kunya a unguwa Dan nasan nayi kuskuren barin shi ya Shiga gidan maman auwal yau mutanen garin Kebbi gaba Daya sai sun San abinda muke ciki,

Ganin ba rabuwa dashi zanyi ba yasa ya dauko ni cak sannan ya Shiga Dani parlor ya wurga ni a saman kujera, tashi nayi na zauna shima ya durqusa a gaba na Yana qare wa fiska ta kallo,

"Naji bazan cutar da maman auwal yanzu ba Amman ki sani duk lokacin da ta sake Shiga gona ta zanyi Mata abinda idon Mai Imani ba zasu iya gani ba,

And for you dokokin zan shimfida Miki wanda zai qara Mana danqon so da qauna I just hope you will love it" ya qarasa Yana shafa gefen lips dina dake fitar da jini saboda Marin da na diba dazu,

"Kayi wa Allah kada ka cutar da matar nan Khamis, na fada maka bazan rabu da kai ba kada kayi including dinta a cikin matsalolin mu please"

"ai kin riga kin saka ta, amman idan kika kiyaye dokoki na maybe Zan fasa Mata abinda nayi niyya, daga yanzu dai ba ita kadai ba Babu Wanda zai sake shigowa cikin gidan nan Koda kuwa 'dan jinjiri ne idan ba namu ba,

STORY CONTINUES BELOW

Ba Zaki fita ko Nan da bakin qofa ba ballantana ki qarasa gate, bazan siya Miki waya ba I don't trust you with it, ba za'a sake kallon TV ba kema kinsan dalili, ki manta da dangantakar ki da kowa daga yanzu na gutsure ta, Ina so zuciyar ki da qwaqwalwar su zamo blank ki Saba da rayuwa ke kadai tare dani, ki daina musu Dani sannan ki daina abubuwa ba tare da sani na ba, idan hakan ya faru ni kuma nayi Miki alqawarin I would be the best husband you could ever have,
duk wani abun da kike so a duniyar Nan ko menene shi nayi Miki alqawarin ko yafi qarfi na sai nasan Yanda nayi na samo Miki shi, I promise to treat you like a queen, nayi Miki alqawarin Babu matar da zata fiki Jin dadi da more rayuwa, infact idan kina so na zamo Mai arziqi just say it ni Kuma ko ta wani hanya ne zanbi sai na Tara dukiya just for you to be happy Kuma ki zamo nawa ni kadai"

Da alqawarurrukan da Khamis ya dauka a wannan ranar muka ci gaba da rayuwa, dukda dokokin da ya shimfida min sunyi mini tsauri Amman Ina ita bakin qoqarina wajen kiyaye su, na sabar ma kaina da zama shiru, I over eat, over sleep, over think,. I became sad, dull, and depressed kadaici ya riga da ya Saba da zuciya ta, just nakeyi kaman ina rayuwa a cikin wata duniya da Babu kowa a cikin ta Bayan NI da Khamis,

Amman fa kada kuyi tunanin matsalolin mu sun qare no, no, no,

Na cigaba da azabtuwa a hannun Khamis fiye da Wanda nayi a baya, abin nashi kullum qaruwa yake yi he is always furious sai ya Gama illata ni daga baya Kuma ya saka ni a gaba Yana bani haquri Yana neman gafara na ba zai barni na motsa daga wurin ba har sai na yafe mishi Kuma hakan ba shi zai Hana gobe ya sake maimaita kuskuren shi ba,

Abun Bai tsaya a Nan ba, Khamis Yana harassing dina Yanda baku tsammani saboda firgici da tsananin tsoro da nake rayuwa a cikin su yasa cikina na fari Bai zauna ba tun bansan dashi ba ya zube sai daga baya bayan munje asibiti muka gane miscarriage nayi, hmm haukacewa ne kawai Khamis baiyi ba a lokacin Amman no ya haukata ni tabbas saboda a ganin shi duk laifi na ne da bani kula da kaina Yanda ya Kamata yasa cikin jiki na zubewa Kuma Bayan haka ya hana in sanar da iyaye na,

I've suffered both mentally and physically, Khamis ya maida ni na zamo kaman wata sakarya Mara amfani bani iya aikata komai, idan naji qaran shigowar motar shi cikin gida haka gaba na zaiyi ta faduwa qirji na Yana bugawa da qarfi, Haka jiki na zaiyi ta tsuma Yana karkarwa idan yayi magana kuwa jinta nakeyi kaman tsawan mala'ika, Ina mazari zanje na aikata abin da ya umarce ni,
Amman small mistake.... slightest mistake zaisa yayi min abinda wani hankalin ba zai dauka ba, ba sau ɗayaba ba sau biyu ba Khamis ya fitar min da jini yafi sau a qirga, jiki na har Babu kyan gani saboda tabo kuma da kanshi ya siyo min maganin da Zan shafa su bace, saidai fa duk abinda yake yi Ina mishi uzuri kunsan meyasa???

A lokacin da abun Yana tsakiya baiyi tsanani ba ya barni naje wunin bikin Aisha a sanadin gaisuwan gida da naje, cikin Shiga ta suturar da ba'a ganin komai a jiki na Bayan idanuwa na khamis ya dauke ya kaini wurin Aisha Bayan dogon roqo da magiya a lokacin ta sanar dani abinda ya hargitsa dukkan tunani na , she told me that Khamis is a PSYCHO har ya taba jinya a asibitin mahaukatan dake garin yola Amman a sirrince Babu Wanda ya sani saboda qarya iyayen shi sukayi Wai ya tafi karatu, itama detective din da suka dauka kwanaki ne ya bankado Mata wannan sirrin harda file dinshi Saida yayi photocopy ya Bata ita Kuma ta nuna min na gani da Ido na,

Haba! Biri yayi Kama da mutum, ban taba Jin labarin ko ganin mutum irin Khamis ba a rayuwa ta, a lokacin naso sanar ma Aisha ko mahaifiyata halin da nake ciki a gidan Khamis Amman ta wani fuskan sai nake gani kaman yin hakan bude sirrin aure na ne,

Nasan ba zasu yarda su barni naci gaba da zama tare dashi ba ko na minti daya Amman nayi qarama ma zamowa bazawara sannan Khamis yanzu abun tausayawa ne tunda yanzu son da nake mishi ya goge a zuciya ta Amman ban tsane shi ba, instead tausayin shi ne ya Kama ni,

Haka muka koma gida Dani da Khamis inaji kaman kada na bishi Ina ji kaman na zauna a gida wurin iyaye na Nima naji dadin rayuwa, ni abun tausayi Khamis abun tausayi haka muka ci gaba da rayuwa cikin gida daya, ban tsani Khamis ba sai ranar da ya shigo min da jini a jikin shi tsakar dare lokacin Kam haukan nashi tuburan ya fito, da bakin shi ya fada min ya kashe Mai shagon unguwar nan Wanda ranar na siya ashana a wurin shi saboda duk lokacin da suka hadu sai ya tambaye shi Yaya amarya? Ko kuma yace mishi yayi sa'ar Mata and some things like that,

Tun daga lokacin na tsani Khamis tsana Mai tsanani nayi qoqarin gujewa daga gare shi Amman Abu ya faskara yanzu ko qofar parlo bayi Bari a bude kada na fita saboda yasan Babu sauran son shi a zuciya ta tsere mishi Abu ne Mai sauqi,
to a Kan hakan muke rayuwa har Izuwa yanzu,
______________________

Fita nayi daga dakin na Shiga kitchen, a jikin famfon sink na saka hannun na kunna mishi ruwan sanyi Ina Jin zafin ruwan har cikin zuciya ta, Saida na Bari ruwan ya zuba na wurin 5 minutes kafin na dauko first aid box na saka gv a ciwon don yayi covering Naman jiki na da ya fito baro_baro na nannade da bandage,
Ina fita parlo na samu ya shigo da laida a hannun shi Mai dauke da maganin quna................🤦🏻‍♀️

Las las... Groups din da Basu comment Zan daina Muku posting cos abin ya danyi min yawa Kuma ana Koko Dan riba ne, I won't be wasting my time post, you read and you can't write even 2 lines 2 show appreciation, ba sai kin biya sisi ba Zaki samu novel dina only comments matters,

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

12🧛🏽‍♂️
Baice dani koman ba ya zaunar dani a kujera, sannan ya warware bandage din da na Nade qunan dashi ya dauko maganin da ya siyo ya fara shafa min, rintse idanu na nayi saboda radadin Yanda Khamis yake murtsuke min ciwo da sunan shafa magani Amman a hakan sai maimaita "I'm very sorry baby" yake yi,+

I hate him! Na tsani Khamis to the core, that maganar da yake min yanzu jinta nakeyi kaman fitar wuta daga kogo, haka ya Gama jagwalgwala min hannu sannan ya kwantar dani a Kan kujeran,

"Yusrah har yanzu baki haqura bane?" Ya tambaya cikin muryan shi ta nutsuwa Mai tsananin firgita ni, Baki na Yana rawa nace
"Aa Na haqura"

"To bude idonki ki kalle ni"

Ko rufe bakin shi baiyi ba na ware idanu na a kan fuskar shi that I hate so much, murmushi ya saki Yana shafa gefen fuska ta a hankali yace
"That's my lovely wife, Ina sonki Yusrah"

Shru nayi bance komai ba, wurge ni da wani mummunan kallo tare da hade fuska yace "ba Zaki bani amsa b...."

"I love you too baby"

Dariya yayi ya Kai min peck a cheeks dina Ya cire dankwali na Yana shafa gashin kaina da rabon shi da yaga kitso har ya manta, saidai na wanke na tace Dan bani da nutsuwan yin ko kalaba ballantana stretching,

"Na sani baby, and kada ki damu ciwon Nan Yana warkewa Zan Kira doctor har gida gazo ta duba min ke kinji?"

Da sauri na gyada Kai tare da miqewa, bansan meyasa ko yaushe idan Ina tare da Khamis jiki na yake rawa ba Amman yanzun ma haka ne, bari nakeyi kaman Wanda tayi wanka da qanqara, shima miqewa yayi yana tambayan "Ina Zaki je?"

"Fitsari nake ji zanje toilet ne"

" To muje na raka ki Kinga ma Baki da lafiya"

Gaba nayi ya bini a baya muka Shiga toilet Ina gamawa ya dauko ni cakk ya dire ni kan gado saboda Babu wuta ya dauki mafifici Yana fifita ni har barci ya dauke ni Sannan ya fita ya rufe qofar da key ta waje, kofar parlor ma ya Danna Mata key, gate ma Saida ya rufe shi gamm sannan ya tafi,

2:08 na farka cikin hukuncin Allah ciwon hannu na bai cabe ba, har Baki bakin yayi duhu kaman Yana Shirin fara bushewa, amman zazzabin da na tashi dashi da safe ya dawo sabo jiki na yayi zafi rau, ga baqin kasala ji nake yi kaman bazan iya taka qasa ba saboda Yanda jiki na yayi min nauyi,

A haka na daddafa jikin bango nabi na Shiga toilet na dauro alwala sannan na fito na shimfida sallaya na tada Sallah, Ina cikin addu'a Khamis ya shigo ya zauna gefe na yayi shiruu Yana qare min kallo har Saida na kammala, tashi nayi na koma gado Ina rawan sanyi cike da tausayawa ya dauki blanket ya lullube ni sai jero min sannu yake yi sannan ya fita,

Shigowa yayi dauka da takeaways na abinci a cikin laida sai Kuma plate da cokali, ya ajiye a qasa ya fita ya dauko ruwa da cups, sannan yazo ya daga ni ya zaunar Yana feeding dina, spoon biyar nayi nace na qoshi lokaci daya yanayin Khamis ya canza 'dan lallabi da tarairayan Nan duk ya watsar dashi ya danqo ni Yana dura min abincin Nan da mugunta har Saida na cinye takeaway guda Ina Jin kaman ciki na zai fashe tukunna ya sake ni,

STORY CONTINUES BELOW

Aikuwa ko motsawa daga wurin banyi ba amai ya biyo baya, Saida na amaye abun da ke ciki na Tass kafin na koma na jingina da jikin gado Ina maida numfashi, Bai damu ba ya dauko tsintsiya da faka ya share Aman Tass ya goge wurin sannan ya dauko nashi abincin ya nufo ni,

Wani irin matsan da Khamis yayi min ko iska bani iya shaqa da kyau ya dinga tura min abincin Nan ko iya taunawa bani yi haka nake hadiyewa, Bai rabu dani ba Saida yaga Ina kuka da hawaye sannan ya sake ni Yana min warning kada na sake na fito da abincin Nan idan ba haka ba nasan sauran,

Ina Jin amai Amman haka na dinga dannewa Ina tsayar da numfashi na Dan kawai kada ya samu nasaran fitowa, inajin Yana taso min Yana Hawa kaina har ta hanci na ji nakeyi kaman sai fito idona ya kada yayi jaa Khamis kuwa na zaune ya qura min eyes fuskar Nan a murtuqe Yana jiran qiris ya dauki mataki,

Bayan mintuna kaman hudu da yaga banyi aman ba ya sake tashi ya fita, can sai gashi da likitan da take kula dani lokacin da Khamis yayi stabbing Dina na kwanta a asibiti,

INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN 😢
I was tested pregnancy positive

Ina dauke da cikin Khamis a jiki na har na wata 1 da sati 2 wannan shine baqar labarin da na taba samu a rayuwa ta, lokaci daya naji duniyar ta qara min zafi a Kan na baya, ni da nake Shirin guje ma Khamis Kuma ni dince nake dauke da cikin shi Nan gaba Zan aifa mishi yaro ko yarinya?
Yanzu Yaya za'ayi na koma gaban iyaye na da ciki? Idan na aihu bazan iya miqa abinda na aifa wa mahaukaci ba Kuma ko Yaya zanyi Khamis bazai barmin shi ko ita a wuri na ba, Yaya zanyi? Ina zansa kaina? Idan na haife abun ciki na  wanini dalili zance ya raba ni da mahaifin shi, Shine tambayoyin da suke yawo a kaina, ban Ankara ba naji Khamis ya rungume ni so tight har Saida na saki qara hawayen fuska na Yana dada qaruwa saboda takaicin Jin jikin shi a cikin nawa,

"Thank you baby, thank you so much kin riga da kin Gama biya na Babu abinda zance Miki sai Allah ya saka Miki da alkhairi ya biya ki da gidan aljannah, yanzu Kam Ina da guarantee din ba Zaki rabu Dani ba, we will have children Nima Zan samu Wanda zasu fara Kira na baba or dady, oh my God"

Sai ya sake ni ya riqe haba Yana tunanin menene? Allah masani, ya juyo zaiyi magana yaga idanu na da hawaye, murumushi yayi ya sake runguma ta sannan ya dago Ya saka yatsan shi biyu ya share mun hawayen Yana
"No tears baby, nasan kina murna Amman ba sai kinyi kuka ba godiya ma Allah zakiyi, ni nasan Daman muna da rabo Kuma zamu aifi Yara da yawa in dauke ki mu tafi can wani wuri Mai nisa muyi rayuwar mu ba tare da wani matsala ba, so this is just the beginning"

Duk abinda yake dinnan ban tanka shi ba, dukda na tsani Khamis Amman Ina tausayin shi sosai Yana da burika da yawa Wanda Ina da tabbacin ba zai cika su ba, idan ma ya samu daman hakan to ba tare dani ba don har yanzu da nake da cikin sa qiris nake jira na guje mishi, shiko ya tsaya riqe da qugu Yana gwada dakin da muke ciki Yana ta bayani

"Yanzu za'a canza abubuwa da yawa a bedroom dinnan, kinga za'a fitar da shoe rack dinnan ya koma daki na don bazaki dinga shaqan warin takalmi Kuma kina da ciki na, noo impossible,
za'a canza curtains a saka masu haske Yanda Rana zai dinga Shiga dakin Nan sosai dan yanzu kina buqata sosai, za'a fitar da hanger shima ya koma daki na kina buqatar space, Zan siyo rechergerble standing fan Naga Baki shiri da zafi so I know baby na ma bazai so ba"

Ci gaba yayi da lissafe_lissafe da Naga abin nashi nayi ne sai kawai na nemi wuri na zauna damuwan dake zuciyata kadai ya Hana ni sauraron shi, peck naji yayi min a cheeks na dago Ina kallon cikin idon shi, murya can qasa yace

"Kina buqatar hutu ko? Ki kwanta ki huta abinki daga yanzu Babu abinda Zaki dinga yi a gidan Nan bayan hutu, ki fada min abinda kike son ci yanzun Nan naje na kawo miki"

Girgiza Kaina nayi da qyar na iya furta "Babu komai" saboda tsananin takamci dake cin zuciya ta,

Lakatan hanci na yayi Yana dariya yace "qarya kikeyi nasan bakin Nan na son abin kwadayi Bari naje na kawo muku abun dadi ke da baby na"
Yana fita na sauqa daga Kan gadon na kwanta flat a qasa Ina kuka Mai gunji Mai tsuma zuciya, ni ba haka naso ba banso wasu su Shiga cikin matsala ta da Khamis ba ballantana 'ya'yan mu na cikin mu nasan definitely sai abun yayi affecting dinsu dan babu Yanda za'ayi na haqura na zauna Khamis ko ta halin qaqa sai na gudu,

Saida nasha kuka na na qoshi na tashi na Shiga toilet na wanke fuskata na fito, Ina Danna handle din qofar cikin daki naji shi a rufe, tun daga wannan lokacin salon zaman cikin gidan Khamis ya canza,

Nasan mutane zasuyi tunanin ya canza zuwa Mai kyau ko? But no!! It changed to the worst!! Sabon babin azaba Khamis ya bude min duk a cikin salon kula da babyn shi dake ciki na, sai yanzu ne na amsa sunana MATAR KULLE na gaskiya dan ko bakin qofa bayi bari na in fita,

Ya dauko mahaifiyar shi ya ajiye ta cikin gidan mu, ita take min komai harta daga cup da hannu na khamis ya haramta min shi, Wai Yana son in samu complete bed rest saboda babyn shi yayi qato yayi lafiya, anyi mishi bayani sau da yawa cewa ina buqatar motsa jiki na Amman yace fyattt shi ciwon haukanshi ba haka ya fada mishi ba,

I suffered! Nasha wahala Yanda Baku tsammani, ga damuwa, over thinking, anxiety, depression and the biggest of all shine laulayi da nake yi Ina kwance and Khamis was making it harder for me da magungunan da yake dirka min na bacci da Wanda zai saka jiki na mutuwa duk da sunan Ina buqatar hutu,

Wannan mahaukacin ya maida rayuwata miserable Yanda duk wani Mai Imani idan ya kalle ni sai ya zubar da qolla, na zama kaman wata gawa, Baki na ya bushe badon bani samun ruwan Sha ko Kuma lotion Bai ishi jiki na ba saidai side effect din magungunan ne suke wahalar dani, idanu na sunyi kwarmi ga dark circles, Banda numfashi da ci da Sha bani iya komai da kaina dai idan shi ko mahaifiyar shi sun taimaka min 24/7 Ina kwance a gado,

Na koka nabi na sake kokawa ma mahaifiyar shi Amman ko sau daya Bata you komai a Kai ba, ko sau daya Bata yi qoqarin kwato min hakki na a matsayin ta na uwa ba Amman tana qoqarin bani kulawa sosai, bani zuwa awu bansan Yaya lafiyan abun ciki na yake ba, yanzu Kam jiran mutuwa ta kawai nakeyi Amman Ina roqon Allah yasa kada na mutu sai na aife abun ciki na dan nasan da wuya na aihu lafiya a halin da nake ciki yanzu,

Yau cikk na ya Shiga watan shi na 7 yayi qato sosai Amman Yana tsaye qeqam banma San ko lafiya ko ba lafiya ba, tashi na daga barci naga mahaifiyar Khamis Bata dakin, nasan Bai wuce tana kitchen ba Kuma bani da kuzarin tashi na biya buqata na shiyasa kawai na mayar da Ido na Zan rufe na koma barci Amman kafin Nan na hango wayar ta a Kan hannun kujera dake dakin,

Bansan daga I wani qarfi yazo min ba na sauqa da sauri dukda sai tangadi nakeyi kaman Wanda Tasha giya na dauki wayan na saka number mahaifiyata sannan na turn mata saqo kamar Haka

'''mama Yusrah ce ku taimake ni Dan Allah kuzo ku fitar dani a gidan Nan kafin Khamis ya kashe ni, shi criminal ne mama dan Allah kuzo da hukuma su Kama shi'''..........🤦🏻‍♀️
Don't forget to follow
Vote
Share
And comment as u read💖

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*
*The writer of*
     *HAR ABADA* and
     *KAMA DA WANE*

13🧛🏽‍♂️
Takun da naji alamun ana zuwa wurin qofar yasa nayi saurin sending ba tare da na gama rubuta bayanin komai ba nasan tunda Aisha da sauran 'yan uwana sunsan gidana ba zaiyi wa mama wahalar zuwa ba, har Bari nakeyi cike da tsoro message din yaqi tafiya, zufa Yana yanko min ta ko ina nasan idan har Khamis ya Kama ni to yau saidai wata ba ni ba a gidan nan,+
Finally message din ya tafi, bansan lokacin da na sauqe wani gauron ajiyar zuciya ba nayi deleting record na message din tare da ajiye Mata wayan a inda na dauke shi, da sassarfa na koma gado na ina Shirin kwanciya sai gashi ta bude qofar idon ta doll a cikin nawa, hadiye wani mugun yawu nayi nayi saurin kawar da kaina inayi kaman Ina son sauqa be daga gadon Amman na gagara saboda kada ta gane ni,

Luckily, Bata Gane ba ta qaraso fuskar ta da murmushi kaman ko yaushe, tasan bani iya magana shiyasa Bata ce dani komai ba ta riqo ni ta tallafa min muka Shiga toilet, fitowar mu muka samu Khamis ya shigo Yana zaune da niqi niqin shopping bags a gaban shi, kwantar dani maman shi tayi ta rufa ni da blanket saboda wurin ya 'dan saka sanyi kafin ta fita ta bamu wuri,

Jaka daya ya dauko ya qaraso wurina Saida yayi min peck a goshi sannan ya dago da faffadan murmushi a fiskan shi ya fara Ciro hadaddun kayan babies daga ciki na maza da na Mata,
"Baby see these cute tops nasan sunyi kyau sosai zasu karbi babyn mu"

Nidai kawai Ido nake binshi dashi don Babu bakin magana, yaci gaba da cewa
"Kinga ma ban fada Miki sunayen da na yanke za'a saka ma abin da Zaki Haifa ba, idan namiji ne zamu saka mishi sunan dad dinki Adam Amman zamu dinga Kiran shi Abulkhair idan kuma mace ce sunan mahaifiyata nake so a saka Mata Firdaus sai a dinga Kiran ta Jannat, idan Kuma 'yan biyun ne sai kawai a hada sunayen idan ma  jinsin su 'daya zamu San abin yi, ko Yaya Kika gani?"

Wani tausayin Khamis ne naji ya Kama ni, he have so many hopes in me Amman gashi ni din da yake so da yawa ni nake shirin destroying dinshi, Khamis ya soni da yawa Kuma har yanzu Yana tsananin so na Amman wannan soyayyar shi zai zama Masa guba Wanda zai tarwatsa tsarin rayuwar shi gaba daya, zan tura Khamis gidan yari saboda kisan Kai da ya aikata sannan Zan dauke Abulkhair ko Jannat daga gare shi,

Zan zame ma 'dana ko 'yata uwa Kuma uba, Zan zamo mishi garkuwa ga duk wani cutarwa da zai iya samun shi, daga yanzu ba Zan sake yarda da wani 'da namiji ba zanyi gwagwarmaya Zan jure duk wani wahala dan na sama ma 'ya'ya na ingantaccen rayuwa,

Yatsan shi yasa ya share min hawayen Kan fuska ta, Cikin rada yace
"Dan Allah ki daina kuka, bani so Ina ganin hawayen ki suna qona min zuciya, raina bayi min Dadi duk lokacin da na ganki cikin damuwa Yusrah I'm sorry!!"

Wannan karon Kuma Mai sauti na fashe dashi da mirgina na rungume Khamis qyam a jiki na Ina kuka kaman Raina zai fita, Ji nake kaman yanzu ne za'a raba ni dashi, I hate Khamis but I also love him,
inama ace bai aikata abun da ya aikata ba? Inama ace yafi qarfin zuciyar shi? Inama ace ya rage zafin rai da kishi? Bazance meyasa bayi tunani kafin ya aikata Abu ba saboda ba laifin shi bane wannan cutar tabin hankali da take dashi jarrabawa ce daga ubangijin sa, Amman da ace Babu wa'innan matsalolin da Zan kasance tare da shi har qarshen numfashi na,

STORY CONTINUES BELOW

Dagowan da zanyi Naga shima kukan yake yi, kaman yasan abinda ke Shirin faruwa yace
"Dan Allah Yusrah kada ki Bari a raba ni dake, wallahi bazan iya rayuwa ba tare da ke ba, kece cikon ruhina numfashi na da sunan ki yake fita Yusrah, rayuwata ya ta'allaka a kanki ke da baby na, I don't even love my parents as much as I love yo...."

Saurin saka tafin hannu na nayi na rufe bakin shi Ina kuka Ina girgiza mishi Kai, da qyar baki na ya iya furta "No, no please"

Gyada Kanshi yayi yace "it's ok, ki daina kukan kinga kun gaji kina buqatar hutu" ya gyara min kwanciya sannan ya bude drawer ya ballo magungunan da yake dirka min kullum ya bani sannan ya fita hade da rufe min qofa,

For sometimes Jin zuciyata nakeyi kaman ana Cinna Mata wuta, bani da tabbacin saqo na ya Isa wurin da ya Kamata Amman idan ya Isa zanyi Rashi babba, bazan taba son wani 'da namiji kaman Yanda naso Khamis ba, zuwa wani lokaci Kuma barci ya dauke ni ban farka ba sai Bayan la'asar,

Ina tashi nagan shi zaune tare da mamanshi da qanwarshi Wanda ta zauna tare damu lokacin muna asibiti, taimaka min sukayi nayi alwala nayi Sallah sannan Khamis yayi zaman bani abinci, Saida muka gama yake fada min wai mamamshi zata je gida sai gobe da yamma zata dawo,
godiya ma Allah nayi da uwa ba zata shaida Yanda za'a qwamushe 'danta ba nasan da wuya sukai har gobe da yamma basu qaraso ba, gyada musu Kai kawai nayi tayi min sallama ta fita ni Kuma na koma barci dan har yanzu Bai Gama sake ni ba,

3:00am

"Yusrah! Yusrah!" Naji muryan da na kusa rabin shekara ban saurare shi ba Yana kirana cikin sautin kuka, a hankali na bude idona na ware su Kan mahaifiyata tana zaune idanun ta sunyi jaa ta riqe ni a jikin ta,
Shikkenan!! An Kama Khamis! Runtse idanuwa na nayi kawai sai ga hawaye sharr Yana zubo min, na rasa na miye daya? Na farinciki ne that I'm free again? Ko Kuma na baqin cikin rabuwa da Khamis cikin wannan yanayin?"

Aisha da Nasreen ne suka qaraso wurin da nake kwance suna kuka, har Basu iya daga Ido su kalle ni saboda Yanda na koma, a Haka dai suka saka min hijabi suka kakkama ni aka fitar Dani daga dakin ba tare da sun tsaya daukan komai nawa ba suka saka ni a motan ya Safwan mama ma ta Shiga Nasreen da Aisha da Ya Usman kuma suka Shiga na mijin Aishan,

Motar police har yanzu Bai tafi ba suna ta faman kokawa da Khamis an saka Masa ankwa a hannu Amman ba shi ya Hana shi qoqarin qwacewa ba, musamman da yaga motocin mu sun fito yasan tabbas Ina cikin daya Kuna gashi zasu tafi dani right before his eyes, haka muka bar wurin Yana ji Yana gani Bai iya aikata komai ba sai ihu yakeyi Yana buge_buge,

Already sun dauko Takardu na sabida halin da nake ciki yasa ba'a Sha wahalar yimin passport ba don an cika komai da sunan tafiya jinya shiyasa tun kafin asuba aka gama muka wuce airport, gaba daya matan muka Shiga jirgi maza Kuma suka bi mota,

Tafiyar minti 30 ya kaimu garin adamawa, muna sauqa a airport wani yayan Aisha Mas'ud yazo ya dauke mu, bamu tsaya ko Ina ba sai babban asibiti a fujajan sukayi admitting dina a emergency room suka fara bani taimakon gaggawa,

Sun so tun a lokacin su cire cikin jiki na Amman wannan dai maganin da Khamis yake bani shi ya qpara rikita komai, ya saka min rashin lafiya ya saka abun ciki na a tsaka mai wuya, idan har suka ce zasu taba ta tofa za'a iya rasa daya daga cikin mu shiyasa kawai sukayi iya abun da zasu iya wajen ganin sun ceto rayuwan dukan mu biyun,

Har 12:00 likitoci suna kaina da qyar da tsammanin nasara aka fito dani aka tura ni ICU Dan har yanzu fa Babu kanta, walau na tashi walau bazan tashi ba aka Debi jinin babanmu aka saka min don blood group dinmu daya ne,
Aisha, mama, Nasreen duk sun Shiga tashin hankali da rudani, barin ma mama da ta dauki laifin abin da ya faru dani ta daura da kanta, Allah ya Basu amana ta sunyi min aure Amman Basu bi baya suna binciken halin da nake ciki ba,

Duk lokacin da ta Kira Khamis tace zata turo Nasreen tayi min sati sai yace munyi tafiya ko Kuma ya nimo wani qaryan shi daban ya maka, Bata taba kawo komai a ranta ba, hasalima ita Bata San Ina da ciki ba tana dai jiran tsammani ko wataran Zan Kirata Amman shiru,

Sati na 2 a asibiti Ina ta fama, a hankali a hankali maganin yake fita daga jiki na Amman Yana rikita ni sosai, wani lokaci ni kadai haka zanyi ta shaking Ina fitar da wani weird sound ina gurnani kaman Mai aljanu, na koma kaman qaramar mahaukaciya har sai nurse tayi min allura kafin abin ya lafa,

Haka Zan kwanta nayi ta bin mutane da Ido, bani cikin hayyaci na shiyasa banmasan suwaye a kaina ba, tunda aka kawo ni asibiti ban furta ko kalma daya ba Nasreen kullum idonta bayi rabuwa da hawaye qarshe ma su mama Saida suka saka ta a gaba da fada Kan tayi ta min addu'a kawai kukanta ba zai amfane ta ba Amman a maimakon hakan sai ta hada duka biyu tana addu'an tana kukan,

Ko Kuma tazo gefe na ta zauna tana min sumbatu
"Aunty Yusrah kiyi haquri, wallahi sai Allah ya saka miki, ba zamu taba yafe ma Khamis din Nan ba sai yaga musiba da tashin hankali a rayuwar shi kaman Yanda ya saka mu muka gani,
Aunty Yusrah dan Allah kiyi min magana no ko zagi na ne kiyi zanji dadi Amman bazan iya jure shirun ki ba Kuma wallahi tallahi kinji na rantse Miki ba Zan sake fada da keba, zanyi Miki biyayya sosai Kuma zanji maganar ki tunda kece gaba dani, please say something aunty Yusrah dan Allahhh"

Sati na 5 a asibiti aka sallame ni lokacin kuzari na ya 'dan dawo har nakan iya Shiga toilet da kaina kina iya sallan asuba da magriba a tsaye Dan yanzu cikin bayi wani damu na sosai, Ina iya magana Amman baniyi ma kowa bani ma son zama cikin mutane, idan Nasreen ta shigo dakin mu ta saka ni a gaba da surutu haka Zan tashi salum alum na fita na koma 'dakin mama naci gaba da zama na abuna ko yaushe Ina tunanin Khamis,

Yanzu Yana Ina? Cikin wani Hali yake? Me yake tunani a kaina, na yaudare shi ko Kuma me? Ina Jin kunyar haduwa dashi Amman ya zamo min dole don Nan da kwana 4 zamu Shiga kotu a raba auren mu, Kuma mutanen unguwar da muka zaune da police sunyi qoqarin samo shaidan cewa shi ya kashe Mai shago,

Kada kuso kuga hauka a lokacin da aka tursasa shi ya sake ni Khamis alqali ne inajin kawai Bai buga ba Amman haka ya dinga duka Yana ihu yace shi ko yanka shi da wuqa zasuyi su Ciro zuciyan shi ba zai sake ni ba, cikin qasa da wata biyu ya Gama lalacewa ya muzare yayi baqi, that handsome gentleman is no where to be seen,

Ina tuna lokacin da na fara ganin Khamis a wurin bikin auntyn su Aisha, so calm and gentle, duk Wanda yace bayi da cikakken hankali a lokacin ba za'a yarda dashi ba, Amman yanzu idan ka kalli Khamis din dake tsaye a gaban mu Yana hauka ba zaka ce shi bane wancan,

Qarshe rabuwa dashi akayi alqali ya raba auren, kisan Mai shago Kuma yasha bulus kaman Yanda kuka sani the law says ba'a shari'a da mahaukaci saidai family shi zasu biya diyya shi Kuma a maimakon prison za'a kaishi asibitin mahaukata,

Ana Gama yanke hukunci Khamis yayi wani qara tare da daka wani mahaukacin tsalle ya fito ta saman deck, bamu Ankara ba sai ganin shi mukayi yayi wani sufa ya cafko ni..........🤦🏻‍♀️

Don't forget to follow
Vote
Share
And comment as you read

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*
*The writer of*
*HAR ABADA* and
*KAMA DA WANE*

14🧛🏽‍♂️
Qanqameni yayi a jikin shi Yana kuka kaman qaramin yaron da za'a raba shi da uwan shi Yama kasa magana sai ihu yakeyi irin na bebaye Yana da'da cukuikuye ni, burin shi bai wuce kada a raba ni dashi ba, ni kuwa Ina tsaye qyamm kaman gunki na kasa tabuka komai Khamis is now my biggest weakness,+

da qyar aka zo aka banbare shi daga jiki na wasu qattin maza majiya qarfi su uku suka tattara shi suka nufi hanyar waje dashi Amman Saida yasan Yanda yayi ya qwace ya sake kwasowa da 'dan iskan gudu zai riqe ni baba na ya Shiga tsakanin mu ya taqarqare ya zabga ma Khamis Mari,

Shi kuwa ko a jikin shi kaman bashi aka daka ba, ya saka dukkan qarfin shi ya hankada tsoho na gefe ya sake riqo ni abinda yayi ma baba yayi min zafi shiyasa Nima nayi amfani da sauran qarfina na ture shi sannan na juya da sauri zanbar court room din yasha gaba na tare da hade hannayen shi biyu,

"Please, please, please kada ki rabu dani wallahi na fada Miki bazan rabuwa dake ba duk inda Kika je Zan biki faaa wallahi sai na biki, Babu inda Zan tafi na barki, eh wallahi Babu Wanda ya Isa ya raba mu tamm zanyi kisa wallahi zanyi kisa a kanku kizo mu tafi gida kinji na fada miki" Da sauri_sauri yake maganar, kana ji kasan zautacce ne ba'a cikin hankalin shi yake ba,

Hannu na ya riqo zai jani mu tafi Amman sai ya tsaya cakat na 'yan sakwanni sai Kuma ya zube a qasa ragwab sakamakon alluran da suka danna mishi a wuya, muna kallo aka tattare shi aka saka shi a mota sai a lokacin kuka yazo min na fita da sauri sukabi baya na, ban tsaya sauraran Kiran da suke min ba don bani son gwada ragonta na a bainar jama'a na qarasa bakin titi na tsari napep ba tare da munyi ciniki ba na fada mishi wurin da ze kaini na fada ciki mukayi gaba,

Duk iya Yanda naso nayi controlling kaina Saida kuka yaci qarfi na har Jin kaina nakeyi Yana mugun Sara min kaman ana daba min adda, I cried my eyes out kafin mu Isa gida tausayi na sosai ya Kama me Keke Yanda na birkice na fita hayyaci na ga tsohon ciki shiyasa Yana ajiye ni ya juya ya tafi ba tare da ya tsaya karban kudin shi ba,

Da Kama garu na Shiga gida har wani zazzabi naji Yana Shirin rufe ni, ga ciwon ciki da na baya na Shiga dakin mu na Danna kwado ta ciki Dan a irin wannan lokacin bani buqatar kowa a tare Dani, zama nayi daram a qasa akwai sanyin floor inajin Yana ratsa ni amman ban damu ba na hade Kai da guiwa Ina risgan kuka harda majina,
Inajin dama ace duk wa'innan abubuwan da suka faru mafarki ne, da kuwa idan na farka bazan sake komawa cikin sauqi ba, cikin wannan yanayin su mama suka shigo suka same ni harda mahaifiyar Khamis da Aisha da ya Safwan, tun daga waje suke jiyo sautin kuka na sunyi bugun duniyar Nan naqi na bude musu qofa bani ma Jin Zan iya dan qabobi na gaba daya sun mutu,

"Yusrah dan Allah kiyi haquri haka Nan ki bude qofar kada ki cutar da abinda ke cikin ki bai Kamata laifin Khamis ya shafi 'danshi ba kin riga kin dauki fansar abinda Khamis yayi Miki burin ki ya cika kin lalata mishi rayuwa yanzu abinda ke cikin ki shi kadai ne abinda nake dashi Wanda ya dangance shi dan Allah kada ki cutar da kanki" cewar mahaifiyar shi Kenan,

STORY CONTINUES BELOW

Bansan lokacin da kuka na ya tsaya cakk ba, naja wani dogon tsaki ba sannan na bangaje qofar na fito hade da riqe qugu Ina Mata kallon hadarin kaji, for that moment mantawa nayi da ita uwar miji na ce,

"Ke har kin Isa? Kin Isa ki daura min laifin abinda ya faru da Khamis? Kuma ki bude Baki kice na lalata mishi rayuwa? Kina tunanin duk abinda ya wakana cikin babin rayuwan shi ban sani bane? To tun da dadewa Khamis ya sanar komai da komai, tun a lokacin na fara kokwanto ke wata irin uwa ce?
Duk abinda ya faru da Khamis tun daga yarintan shi har zuwa yanzu laifin ki ne, kinsan 'danki Yana da matsala Amman Kika biye Kuma Baki dauki mataki a Kai ba saboda kina gudun tsangwaman kishiyoyi, ko wace rana kina bude idanu ki ganshi a cikin wannan yanayin Yana azabtuwa wajen ganin ya daidaita kanshi ya dawo kamar ko wani yaro amman ya kasa because he was too naive, ko tausayin shi Baki ji ne?

Kaman Yanda kullum nake koka Miki ki kubutar dani daga qangin Khamis haka Khamis yake koka Miki ki kubutar dashi daga qangin rayuwar da zai iya Shiga Nan gaba saboda matsalar qwaqwalwa but you never care saboda kin cika son kanki" na qarasa a tsawace Nima bansan nayi hakan ba,

Rai a bace mama ta fisgo ni jikinta sai huci nakeyi bacin Rai ya rufe idanu na bani iya ganin komai a yanzu Kuma ba Zan samu nutsuwa ba idan ba na fitar da abinda ke cin zuciyata bane,

"Yusrah Baki da hankali ne? Surkuwar ki ce fa!"

"so what? Sai me Dan ita surkuwata ce sai ba Zan fada Mata laifin ta ba? 'dan cikinta fa ta cutar uban 'ya'ya na, itace dalilin da yasa suke kiran shi da sunan da ya tsana fiye da komai a duniyar Nan, saboda ke suke Kiran shi SHAIDANI, be it DEVIL or SHAITAN kin saka duk ya rikice a ko Ina bayiso aji ana ambatan sunan Koda ba dashi ake ba it really drives him crazy,
shiyasa duk Khamis ya fiku riqo da addini ba don kin daura shi a kanta ba sai dan Yana tsoron a danganta shi da shaidan Kuma sunan ya Sami asali ne lokacin da ya kashe seat mate dinshi saboda bacin rai, Khamis ba yanzu ya fara aikata kuskure ba saboda Babu ishashen hankali a tare dashi, Kuma wallahi Allah ba zai Kama shi da laifin komai ba duk hakkin mutanen da ya dauka ku zaku biya shi ke da mahaifin shi,

He is your son after all, ya Kamata ace matsalar shi ya zama matsalar ki mama, da ace tun Yana yaro Kika kaishi aka Masa jinya cikin ikon Allah da ya warke da yanzu muna zaune dashi lafiya qalau zamu Gina kyakkyawar zuri'a Wanda idan Allah yaso zasu zamo abun alfahari ma al'umma Amman inaa saboda ke duk mafarkayyan Mun sun rushe we no longer have dreams,

Da ace kin kaishi asibiti Bayan tsautsayin kisan farko ya faru da ba'ayi mishi laqani da SHAIDANI ba a maimakon haka saboda 'yan uwanshi da 'yan uwanki da sauran mutane sun guje shi kasancewar shi criminal at a very young age sai Kika dauke shi kuka koma wani gida daban daga Ke sai shi sai kuma mahaifin shi idan ya kawo muku ziyara kowa a familyn ku tsoron Khamis yake ji,

Kika daura shi a Kan turban kinfi qaunar shi ne shiyasa Kika raba mishi gida da 'yan uwanki shi Kuma Kike zaune dashi shi kadai, tun daga lokacin Kika fara dasa qiyayya a zuciyar Khamis, kike nuna mishi shi ba irin sauran mutane bane komi nashi daban ne Dan haka kada yayi iri daya da kowa idan Kuma Kika ga abun shi yayi shigen na wasu yaran sai kinsan Yanda kikayi Kika haramta mishi shi saboda burinki ki nuna mishi shi super natural ne ba abnormal ba,

Kayan Khamis daban da na sauran 'yan uwana shi, kayan wasan shi Dana, makarantar shi daban, dinkin uniform dinshi ma daban yaje da na sauran students, harta abincin da Khamis yake ci daban yake ta Hala har Kika tusa masa aqidar ya zauna a cikin zuciyar shi Amman abinda Baki sani ba shine, hakan da kike yi yana cutar dashi it's hurt him deep down inside Yana Ji kaman ya rasa Daman da sauran Yara suke dashi ne, Yana hi kaman shi yanzu ma 'dan Adam bane, Yana son yayi rayuwa normally Amman Babu dama,

STORY CONTINUES BELOW

A dalilin haka ya zamo Mai tsananin so da kishin abinda yake dashi, bayi so yaga kowa ya rabe ki saboda a tunanin shi ke kadai yake dashi Yana tsoron a Haka kema zai iya rasa ki, shine Nima qaddarar ta hawo kaina tunda ya samu ya mallake ni sai ya zamo Mai tsananin zafin kishi da kiyayewa, Babu shakka son da Khamis yake min so ne na gaskiya so Mai tsabta,

Amman kin riga da kin cutar da qwaqwalwar shi baisan Yanda zaiyi soyayya ba, garin neman gira ya rasa Ido yanzu na haramta mishi Kuma duk saboda ke kin haukata 'danki da gangan tirr da uwa irinki"

Ina dasa Aya naji an dauke ni da Mari har Saida nayi gefe kadan na dago Ina kallon fiskar ta
"Not agajin Aisha, a wancan lokacin kinyi dai_dai da Kika gargade ni Gane da auren Khamis, Amman wannan karom kada kiyi qoqarin dakatar dani dan ya zamo dole na fada mata kuskuren ta sannan na karba ma khamis 'yamcin shi da ta tauye tsawon shekara da shekaru,
Baki San irin wahalan da nasha a hannun shi bane, na azabtu it azabtuwa Khamis ya gasa kin aya hannu abinda kuka game ma ba komai bane ni kadai nasan halin da na Shiga lokacin da nake tare dashi, I convulse, I trembled out of fear, Khamis ya zamo min kaman mala'ikan daukan Rai da zaran na ganshi kwanciyar hankali na ya qare duk Kuma saboda ita ne, ki fadamin meye amfanin yin shiru na?

A lokacin da abin yaje faruwa na dauka laifin shi ne Amman tunda ya fito ya warware min zare da abawa sai na gane he is not the villain in my story, sashi akayi ya zamo haka"

" Duk wani musulmi Kuma mumini ya yarda da qaddara ke meyasa ba Zaki rungumi Taki qaddaran fa saboda tsantsan fetsara da rashin ta Ido kin saka Mata sa'an uwar ki koma ta girme ta a gaba kina disgracing dinta wannan wani irin Hali ne? Da ace wata ce takeyi ma taki mahaifiyar haka zakiji Dadi? Ko kina tunanin shi Khamis din zaiji dadin hakan da kikayi Mata ne?"

Tabbas akwai qanshin gaskiya cikin maganar Aisha ko bataci darajan kowa ba zata ci darajan kasancewar ta mahaifiyar miji na itama uwa ce, daga idanu nayi Ina kallon su kowa yayi jingum_jingum Ina hango tsananin bacin Rai shimfide a Kan fiskar mamana,

Juyawa nayi na koma cikin dakin mu dan nasan bani da gaskiya, banyi abinda ya dace ba, inajin qaran takun su sun watse na cigaba da kuka na daga inda na tsaya, shigowa Nasreen tayi da cup din tea a hannunta ta ajiye a qasa ta gefe sannan ta qaraso wurin da nake qudundune a qasa tana patting dina a baya gata da saurin kuka har fiskan ta yayi shaqaf da hawaye,

"Aunty Yusrah Dan Allah kiyi haquri, ance ba'a son masu ciki suna yawan Shiga damuwa gashi sai kuka kikeyi tun dazu, dan Allah kiyi haquri kisa wani Abu a cikin ki kodan babyn ki" ta fada tana miqo min cup din tea din,

Karba nayi na ajiye a gefe sannan na riqo hannun ta duka biyu na dunqule cikin nawa dan Ina buqatar fitar da irin radadin da nake ji cikin zuciya ta I need to share my feelings with someone,

"Nasreen ni mutuniyar banza ce ko? Bani da da'a right?"

" Waye yace haka aunty Yusrah? Ke jaruma ce sosai kinyi abinda yawancin mu ba iyawa zamuyi ba idan ma Akan maganar da aunty Aisha ta fada ne kada ki saka shi a ranki duk abinda Kika fada ma maman Yaya Khamis daidai ne duk Wanda yayi ba daidai ba dole ayi scolding dinshi a nuna mishi laifin shi ko kin manta haka mama take fada Mana?? Dan Allah kada ki daga hankalin ki a Kai kinji?"

" You are just 14 har yanzu bakiyi wayon da Zaki iya banbance girman laifi ba Amman nasan kinsan cewa Babu kyau rashin kunya ma babba sannan abinda nayi was mama ba daidai bane tana da matuqar kima da daraja a idon Khamis Bai Kamata na 'daga murya a kanta ba"

" Haka ne yanzu dai aikin Gama ta Gama ba zamu iya juya hannun agogo baya ba saidai muyi fatan Allah yasa hakan ya zamo izina a gareta ta gyara kuskuren ta, Kinga Yaya Khamis yayi nisa damu Dan Allah Kada kiyi sanadin da babyn ki zaiyi nisa damu gashi Kisha zanje na kawo Miki abinci" ta qarasa hade da dakko cup din ta danqa min Saida taga nasha fiye da Rabin cup din kafin ta fita,

Maganganun da na fada ma mahaifiyar Khamis ya Sosa ranta ba kadan ba Haka ta koma gida ta dinga kuka cike da nadama, tabbas tasan abinda na fada Mata duka gaskiya ne Babu qarya Kuma ita dince silar lalacewar rayuwan danta ba wani ba, tasan ba zata samu ganin Khamis a yanzu ba Amman ta shirya neman gafaran shi a duk lokacin da sukayi Ido hudu da ita ta zalince shi ba Kadan ba,

Nasreen tafi kowa qoqarin ganin ta saka ni farin ciki a cikin gidan mu dukda mama itama tana nata qoqarin da Aisha da sauran 'yan gidan gaba daya na zamo kaman wata qwai sai tarairaya ni akeyi ana wani shagwaba ni Amman hakan bashi ya rage yawan tunanin Khamis da soyayyar shi a cikin zuciya ta ba ko kadan!!

Hmm babban su uban su Kuma shine ya Safwan, duk want Abu da ya Kamata ace da Khamis ne zaiyi Mana shi duk ya dauke sai hidima yake Mana ni da baby na bayi ko nuna gajiyawa nidai Allah yasa ba Sona yake yi ba =_=

Yau tunda na tashi nakejin ciwon Yana 'dan taso min kadan_kadan I'm not even sure about na menene Amman kafin 9:00am naji abin ya fara wuce lissafi naquda ya taso min gadan_gadan, kasancewar yau Saturday Babu makaranta Nasreen tana gida tana wanki, Nishi na da taji ya jawo hankalin ta cikin dakin mu tana ganin halin da nake ciki Bata Bata lokaci ba ta Kira ya Safwan yazo suka tattare ni sai asibiti.............🤦🏻‍♀️
Don't forget to follow
Vote
Share
And comment as you read 💖

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

*Yarda da QADDARA Yana cikin shikashikan IMANI Wanda idan mutum bayi dashi ya tabe duniya da lahira, Allah shi yake tsara ma ko wani 'dan adam kalan nashi qaddaran Amman shi addu'a tabbas Yana sauya qaddara*

Rabbana hablana min azwajina wa zurriyati na qurrata aynin wa ja'alna lil muttaqina imama,2

(Ya Allah ka bamu mataye da zuri'a Wanda zasu zamo mana sanyin idaniya Kuma mu zamo shuwagabannin masu imani)

_'yammata da matan aure, maza da Mata, babba da yaro duk mu lazimci wannan addu'a mu koya ma qannen mu da  yaran mu, kada mu gajiya wurin yawaita addu'a da ikon Allah qaddarar mu zata zo da sauqi Kuma Allah zai hada mu da abokan zama na gari ya shiryar Mana da Wanda muke tare dasu_

15🧛🏽‍♂️
Allah bayi taba daura ma bawa abinda yafi qarfin sa, nasha wahalan rayuwa da Khamis cikin hukuncin Allah sai bansha wahalar dogon naquda ba, cikin abinda baifi awa 2 ba na aihu Allah ya sauqe ni lafiya na samu 'ya mace qatuwa sosai dan Saida tayi weighing 3.5kg a scale,

Bayan na samu kaina aka daura min ita saman qirji na Ina qare Mata kallo idanun ta da gashin girar ta harda Suman kanta irin na khamis ne sakk saidai ni ta dauko a yanayin fata, soft brown skin, qura mata Ido nayi Ina tunanin mahaifin ta cikin raina da ace Yana Nan da yafi kowa farin ciki, murnan da Khamis zaiyi a irin wannan lokacin bazai boyu ba, nayi burin Khamis ya kasance tare dani lokacin da Zan aifa mishi 'ya, naso naga irin qaunar da zai nuna ma yarinyar a kallo na farko Amman Allah Bai bani wannan damar ba,

Dago yarinyar nayi a hannuna na kaita saitin Baki na Sannan na manna Mata peck a goshi hawaye Mai zafi na sauqa daga idona, ganin Ina Shirin canza masu yanayi yasa Aisha tayi saurin karban yarinyar tana harara na,

"Ke bamu son wulaqanci daga zuwan mu duniya sai ki tarbe mu da kuka?"

"I can't help it besty, kaman mafarki nake ganin abun and her father is not here"

" Sai mene? At least ai zakiyi farin ciki koda kadan ne kiyi dariya Dan ki gwada ma Allah godiyar ki, ya Baki irin wannan zankadeden budurwa Amman kina zubar da hawaye? Gaskiya Bai Kamata ba"

Miqa hannu nayi na karbe ta Ina murmushi still hawaye na zuba daga idona nace su bani dabino da zamzam, dabinon na fara taunawa na saka Mata a bakin ta sannan nayi addu'a a cikin zamzam din shima na Bata kadan tasha,

Mama dai ta zuba idanu tana kallon ikon Allah cikin ranta tana jimami 'Yusrah Bata kunyar 'yar fari' Yanda taga nake tarairayan yarinya Ina Mata abinda ya Kamata ace mahaifin ta ne yake mata su,

Niko bansan ma tana yi ba, muna 'dan zantawa da Aisha qasa_qasa Yanda Babu Mai jinmu sai ta fada min wani Abu da tsananin farin ciki yasa na 'dago yarinyar Ina binta da kisses ta ko Ina, yanzu Kam fa abun yafi qarfin mama tayi kawaicin har ta gaji, sai ji mukayi taja wani dogon tsaki dago idon da zanyi na kalleta Naga har ta kusa kaiwa bakin qofa tana qunquni,
"Yaran yanzu kaff Basu da kunya kana taba su suce maka wani zamani"

STORY CONTINUES BELOW

Tana fita na saka dariya nace " kiji mama fa besty, tun last week take min huduba Wai kada nayi rashin kunyan iyayen zamani Wanda Basu Jin kunyan 'ya'yayen su na fari, Dan Allah ki Gane min hanya akan me Zan aifi yarinya Kuma daga baya nazo Ina Jin kunyar ta?"3

"qyale mama haka ma wata goggo na take a fadan da suka min lokacin da zanyi aure harda cewa Wai idan Allah ya bani rabo na farko na zamo Mai kawaici kada na yarda in sake jiki dasu,

Ai kuwa suna gamawa mahaifiyata ta Jani gefe tasa na watsar da duk wanna bayanin ta qara da akwai cutarwa Mai yawa a cikin wannan al'adar saboda yaran suna experiencing loneliness Kuma yakan zamo Basu da kaifin basiran da zasu iya tare wani cutarwa idan yazo musu saboda Basu samu training daga makaranta ta farko ba Wanda itace mahaifiya, idan suka Shiga wani hali na damuwa Basu da Wanda zasu zo wurinta su fada Mata damuwan su saidai qawaye ko abokai Wanda a Nan ne tarbiyyan Yara yake fara baci saboda ba lallai bane abokan nasu su zamo masu isasshen tarbiyya ba, Kuma dole su dauki ko wace irin shawara ne zasu Basu saboda Basu iya banbance daidai da ba daidai ba sai kiga kina ta Shan wahala kina tufka ana warware Miki"

"Tabbas haka ne ballantana yarinya ta da ni kadai take dashi a halin yanzu, Koda duniya zata zage ni sai nayi iya bakin qoqari na nashiga jikin ta da rayuwar ta gaba daya Yanda Zan tafiyar da al'amuran rayuwan ta gaba daya, bazan bari ta raina ni ba Amman zamu zamo kaman aminan juna insha Allah zanyi iya qoqarina wurin ganin Jannat  ta samu irin rayuwar da ko wace yarinya take buri a duniya, ba rayuwa Mai cike da qawa da qyale_qyale ba, saidai rayuwa Mai cike da soyayya da nasarori idan Allah ya yarda, Zan zamo ma Jannat uwa da uba bazan taba Bari ta tozarta ba da ikon Allah,

Riqe baki Aisha tayi cike da mamaki tace "iyeee, shi Kuma Jannat din a Ina Kika samo shi? Ko tun tana ciki kukayi Mata suna ne?"

"Aa ba'a rada Mata suna ba tukunna, sunan da mahaifin ta yake burin saka Mata ne idan tazo duniya"

" To yanzu Mai kike jira?"
A kaikaice na kalle ta nace " ban gane Mai nake jira ba"

"Ki rada Mata sunan Mana tunda ya riga ya fada miki, aike mahaifiyar ta ce kina da damar Sanya ma 'yarki suna a musulunce"

A lokacin na rada Mata sunan da Khamis yake buri sunan mahaifiyar shi, I can't help but to cry again tunda yanzu kuka ya zamo kaman sana'a a gare ni idan banyi ta ba kwata_kwata bani Jin Dadi, na runqume Jannat a qirji na Amman Ina kaffa_kaffa kada na karya qashin baiwar Allah😅

About 3hours later

Jina nakeyi kaman zanyi amai Amman mama sai dada dura min sirki takeyi saboda a sama ma Jannat  abinda za'a saka Mata a cikin ta sai tsangwala ihu takeyi nono yaqi zuwa,

Muna cikin wannan yanayin sai passing_passing akeyi da yarinyar aka bude qofar dakin qanwar Khamis ta shigo bayanta maman shi sai laqo mu takeyi tana baya baya kaman taga dodo, Kuma nasan duk saboda ni ne, tana son ganin jikanta Amman tana Jin kunyar hada Ido dani saboda abinda ya faru a tsakanin mu kwanakin baya,

Cike da Jin nauyin ta na 'dan gyara zama nace mata "mama bismillah shigo"

Dariyan yaqe tayi ta sake sallama sannan ta shigo ciki har gaban gado na ta karbi yarinyar a hannun Nasreen ta nemi wuri ta zauna tana tambaya ta Yanda na samu kaina, da fara'a na amsa haka da ta gani yasa ta dan sake aka dan fara hira tana jefo min tambayoyi akan abinda ya shafi jego da raino cikin dabara sabida idan akwai abinda ban sani ba ta sanar dani, a nan ne Nasreen take shaida Mata an riga da an saka ma yarinyar suna,

"Allah ko autar Ummi, menene sunan kishiyar tawa?"

"Ga aunty Yusrah Nan ki tambayeta ta fada Miki da bakin ta Amman nasan idan Kika ji sai kinyi min kyauta tunda ni na sanar dake wannan albishir din"

STORY CONTINUES BELOW

" Ko? To shikkenan indai sunan Mai dadi ne ba irin na tsoffi ba zanyi miki babban kyauta" ta juyo tana fiskanta na tace " menene sunan yarinyan Yusrah?"

Qasa da Kai nayi Ina murmushi nasan tabbas zata ji dadin sunan nace "sunan ki ne mama Daman ya fada min idan mace ce Yana so a saka Mata sunan ki sai mu dinga Kiran ta da Jannat"

"Masha Allah, Allah ya raya jannatul Firdaus" kaina a qasa na amsa da ameen ta sake yin addu'a ma Jannat tana gamawa Yaya Safwan ya shigo da doctor aka qara duba lafiyan mu sannan aka rubuta Mana takardan sallama,

Nifa rawan qafan da ya Safwan yake yi har ya fara bani haushi, idan kunga Yanda yake hidima har kayan mu ya Hana yayu na diba haka ya kwashe su ya saka a mota yayi settling bills na asibiti sannan kaimu har gida tare da maman Khamis da qanwar shi ita ta wanke Jannat tass suka dan taya mama sauran ayyuka kafin suka tafi,

3:40
"Waiyo Allah mama ni bazan iya ba zafi wallahi"

"Ai kowa da haka ya fara ko Kuma zaki bar 'yar Taki da yunwa ne?  Tunda kince bakijin kunyar ta sai ki kalle ta cikin Ido kina shayar da ita hala idan tana ganin fuskar ki ba zata dinga tsotsa da qarfi ba"

Runtse Ido nayi Ina ciza lebbe dan wani zafi naji yake ratsani har cikin qwaqwalwa saboda wannan ne breast feeding dina na farko, 'daga labulen qofa Nasreen tayi ta shigo da laida babba Mai zanen yellow da baqi ta ajiye a gaba na, kallon ta mama tayi tace "auta wannan fa, Menene a ciki?"

"Kaji ne mama" ta fada tana bude laidan don mama ta gani,

Aikuwa mama ta hango su daqwale guda uku an yanka an gyare shi Tass "Ok har yayan naku ya dawo ne? Amman gaskiya sunyi arha sosai indai da kudin da na bashi ne ya siyo duka wannan saidai ban sani ba ko yayi ciki, Kije kice yazo Ina niman shi"

"Mama ya Safwan ne fa ya kawo" Da sauri na bude Idona na sauqe a Kan laidan da Nasreen ta shigo dashi, tsaki naja na kwantar da Jannat a saman gadon mama Ina Shirin miqewa nace "ina ya Safwan din yake?"

"Ya tafi, ammaj yace da dare zai shigo yaga baby"

" Mama dan Allah ki gani fa tunda na dawo gidan Nan mutumin Nan yake ta kashe min kudi ni wallahi bani so, ace mishi ya Bari haka nan kada gaba abubuwa su juya"

" Wani abubuwa ne zasu juyan? Mutumin Nan ba roqon shi kikayi ba fa shi yayi niyya yake Miki hidima, tayuyu ma tausayin ki kawai yake ji"

" To idan ba tausayin bane ba fa? Mana 'dan Adam fa da wuyar Gane Hali ni kada ya Gama wahala ya qarar da kudin shi a kaina Kuma yazo Bai samu abinda yake Nima daga gare ni ba fa?"

"to Allah yasa ma abinda kike tunanin ne, Mun Riga munsan Safwanu ciki da Bai Kuma mutumi ne mai nagarta me dattaku ga halaye na gari qanwar shi Aishatu Bata bar mishi komai ba, zanyi matuqar farinciki hada zuri'a dashi, Allah yasa yazo ya tattare ki ko zamu samu chanji dan ni har na qosa da ganin ki a gaba na"

" A'a'a haba mama meyasa zakiyi jumping to conclusion? Yace Miki Yana son aure na ne da zakiyi wannan Maganar?"

"Ih, idan Bai fada ba ai ya nuna, haquri zakiyi fa ki yayyafa ma zucian ki ruwan sanyi idan mini yazo Miki ki rufe Ido kiyi auren ki abun ki"

Tura baki nayi na gyara ma Jannat kwanciya don da ta samu wani Abu ya Shiga bakin ta har ta samu nutsuwar bacci,
"Haba mama saikace Wanda kuka gaji dani? Kwana na nawa ne a gidan Nan gaba daya da zaki fara kawo min zancen wani auren?"

" Dan Allah aunty Yusrah ki yarda ki aure shi Kinga zamu sake wani biki Kenan a gidan nan"

Hade fuska nayi Ina gwada Nasreen da yatsa cikin fada_fada nace "auta, auta wallahi ki kiyaye ni idan muna magana na sake Jin bakin ki Allah sai nayi Miki brush da yashi, ke me Kika sani a Kan aure? Biki ne kadai a cikin ranki Baki San me yake qunshe a cikin zaman auren ba dan haka ko da wasa kada na sake Jin kince na auri ya Safwan, idan auren Dadi gareshi ke kiyi Mana 'yar rainin hankali kawai"

"yayyafa ma zuciyar ki ruwan sanyi ni ba baquwar tsanani bane, idan Kinga dama HAR ABADA kada ki sake aure ko a jiki na, nidai idan ya Safwan ya tambaye ni abinda kike ji a kanshi ce mishi zanyi kina tsananin sonshi har idan kina bacci Baki sanin lokacin da kike cewa I love you ya Safwan, ki gani wallahi washe garin ranar ya turo da sadaki Kuma Dole a daura mu girgije a biki ehe!"

Shiru nayi Ina tunani, nasan Nasreen ba hankali take dashi dashi ba tsaff zata iya aikata abinda ta fada harda qari gwanda na lallabe ta kada yanzu taje ta dauko min dala ba gammo,

"Umm umm Allah sarki 'yar qanwa ta, har zamu fara fada dake? Kin manta lokacin da bani da lafiya kinyi min alqawarin ba Zaki sake fada Dani ba?"

" Ai lokacin da Baki da lafiya Kika ce Kuma yanzu ya wuce, kina maganan past while we are living in present, Kuma fa tunda Kika dawo gidan Nan wallahi bani da kwanciyar hankali, da lokacin da baki Nan Ina zuba shagwaba ta Yanda Naga dama abinci wannan sai mama ta roqe ni nake ci,
Amman tunda Kika zo attention din kowa ya koma Kan ki Kuma Kika qara da wannan Mai qatoton Kan yarinyar wallahi ko wanka ne idan banyi ba a gidan Nan Banda baba Babu Mai ganewa haba duk kinzo kin cika Mana space!"

"To Yaya kike so inyi da Raina Nasreen? Kinsan dai da son zuciya ta bazan dawo gida na zau...."

" Dan Allah tsaya aunty Yusrah"
" A zaune nake"

"To Ina nufin ki dakata, idan dai da gaske kikeyi ba son ranki bane sai ki sake wani auren, dazu ma malam Naseer yazo lokacin kina barci............🤦🏻‍♀️
Don't forget to follow
Vote
Share
And comment as you read💝

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

*She is wonderful, simple, and she have a very big heart,💓 she is MAI DAMBU😎🤭 writer of MATAR SO and other wonderful novels, a very responsible woman, I heart you and respect you alot auntynah💃🏻💃🏻 Allah ya dafa miki,🤩 muna qaunar ki matuqa* 💝

16🧛🏽‍♂️
"Wallahi kuwa na dauki Jannat na Kai mishi ya dinga rangada Mata addu'oi Yana shafe qatoton kantan Nan dashi, shima yace zai dawo wataran ku gaisa idan zuwa lokcin Baki tsayar da ya Safwan a matsayin mijin da Zaki aura ba na rantse da Allah shima ce mishi zanyi idan Yana sonki kince kin amince Zaki aure shi"+

Kafin nayi wani magana mama ta jawo Nasreen ta zuba Mata dundu a baya Saida ta boqare ta hada mata da ranqwashi
"Ja'ira mara kunya ita sa'ar ki ne da Zaki tsaya Mata a ka kina titsiye ta kaman uwar da ta aife ta? Wuce ki bamu wuri Kuma kiyi wani rashin hankali kiga Yanda zamu qare dake a gidan Nan auta"

Miqewa tayi tana matsar qolla muna hada Ido nayi Mata gwalo abin sai ya qara qular da ita, Saida takai bakin qofa yanda tasan mama ba zata iya kamo ta ba tace

"Kuma wallahi har wurin maman su aunty Aisha zanje nace mata kince ta taimaka Miki ta barki ki auri ya Safwan idan Baki same shi ba mutuwa zakiyi, gobe zanga da bakin da zaki min gwalo, dukan da aka min Kuma Akan 'yarki Zan rama nasan Zaki fi jin zafi" bumm ta daga labule ta fita mama ta bita da Ido ita dai idan muna zaune a wuri daya to bata da kwanciyar hankali fada Kam kullum a cikin ta muke,

Juyowa tayi ta dube in a serious tone tace "wani wurin auta tana da gaskiya hajiya ta, tunda Allah ya hore Miki Baki rasa manema ba kiyi amfani da damarki ki bawa namiji dama ta biyu, kiyi aure ki nema ma 'yar ki uba zama single mother da wahala musamman a cikin qabilar hausawa, ba ke kadai abin zai shafa ba harda Firdausi, za'a dinga kyaran ta ana tsangwamar ta dukda kuwa ansan tana da uba ba shegiya bace Amman sai an samu masu goranta Mata Kan abinda ya faru da ke Wanda ita bata da laifi a cikin sa"

" To mama dan Allah da kuke ta magana yaushe yaushe ne auren nawa ya qare ne? Sai kace Wanda na shekara goma Babu miji"

" Ai Nima bance Miki yanzu bane, na dai fada ne saboda ki saka ma ranki duk ranar da Kika shirya bude sabon babi a cikin rayuwar ki sai kice ma Safwanu ya shirya"

Again!! Sudai Safwan dinnan dai suke so, bansan me suka gani na musamman a tattare dashi da suka matsa min da maganar na aure shi ba harda yayu na maza Suma ba'a barsu a baya ba,

"Mama yanzu shi Safwan din yace Muku Yana so na ne? Baifa fada ma kowa a cikin ku Yana son aure na ba, tausayi ne kawai da hallaci irin na zuriyan su Aisha ba komai ba"

"to shknn naji Safwanu baice Yana son ki ba, shi Kuma Nasiru fa? Kowa ya sani tun kina 'yammata yake son ki Kuma har yanzu Bai fasa ba"

Saida na hade Rai na juyar da kaina gefe dan ko sunan malam Naseer bani son ji na rasa Mai yasa na washe shi da yawa
"Ni wallahi bazan auri malam Naseer ba koda na rasa mijin aure"

" A dalilin?"
" Bani son shi"

" Baki son Safwanu Baki son Nasiru to wa kike so?"

"Khamis!! Khamis nake so!!!" Shine abinda zuciyata take maimaitawa, ba abune Mai sauqi na cire son shi a cikin zuciyata lokaci daya ba, dukda zama na dashi baiyi Dadi ba kwata_kwata Amman Khamis is my first love, bawai ban taba yin saurayi ba ko Kuma ban taba kula wani namiji ba Amman bansan menene soyayya ta gaskiya ba sai a Kan Khamis,

STORY CONTINUES BELOW

"Yusrah!! Yusrah!"
Firgigit nayi na dago Ina kallon mama hade da fadin na'am,

"Tun da yarintar ki kin fara saka damuwa a zuciyar ki? Kibi komai a hankali ba zamu taba Miki dole ba Dan takurawa Bata da amfani, Amman dan allah ki saki ranki ki daina yawan tunani Firdausi tana buqatar lokacin ki da kulawar ki, kiyi qoqarin tsaida zuciyar ki wuri Daya ko dan ita kinji?"

Gyada Kai nayi Ina qoqarin placing fake smile a saman fuskata nace "to mama zanyi bakin qoqari na insha Allah, kidan ban Aron wayan ki idan Zaki fita"

Miqo min wayar tayi ta dauki laidan kajin da ya Safwan ya kawo ta fita dashi, Ina ganin ta fita na Haye gado na kwanta gefen jannat sannan nayi displaying pic din auren mu a wayan mama said kawai na fara kuka Wanda bansan dalili ba Ina shafa saitin fuskar Khamis,

"Abban Jannat" toshe Baki na nayi da tafin hannu na lokacin da naji kuka Mai sauti da zafi yazo min saboda sunan da na Kira Khamis da shi, sunan da yake da burin ji gashi yana raye Amman har yanzu Allah Bai bashi daman ji ba,

"Abban Jannat cikin wani hali kake yanzu? Kana cikin qoshin lafiya ko akasin haka? Kaga Basu ma damu da halin da kake ciki ba har sun manta da Kai suna son shigo da wani daban a cikin rayuwa na amman abinda Basu sani ba shine memories dinka da soyayyar ka ba zasu gogu daga zuciyata cikin sauqi ba, nasan kaima baka manta dani ba Kuma Yanda kake tunani na Koda yaushe Nima haka kana maqale a cikin zuciyata dukda cewa yanzu Kai ba nawa bane Nima ba taka bace, a Karo na farko Zan roqe ka dan Allah ka fita daga zuciyata ko dan saboda rayuwar Jannat ta inganta wallahi ba Zan iya tabuka komai ba idan Ina tunanin ka"

**********

" Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, na Shiga uku bansan Yaya zanyi da rayuwata ba, komai qara lalacewa yake yi a maimakon Khamis Yana qara Sami sauqi ciwo sai gaba_gaba yake yi yanzu 'dana ya zama cikakken mahaukaci, Yaya zanyi ne dan Allah Yaya zanyi da raina" cikin gunjin kuka mahaifiyar Khamis take wannan Maganar,

Takowa inda take dabashe a qasa baban shi yayi da dago ta sannan ya saka yatsun shi biyu Yana share Mata Hawayen fuskar ta sannan ya dago fuskar ta Yanda zai Bata damar kallon cikin idon shi, yace

"Ki kwantar da hankalin ki Firdausi, insha Allah daga wannan tsananin zai samu sauqi gaba daya ai kinji abinda likita ya fada Mana ko?"

Gyada Kai tayi, yace " to Banga abin tashin hankali a Nan ba tunda an tabbatar Mana zai warke kedai kawai ki ci gaba da mishi addu'a Kuma ki dauke idon ki a kanshi ki daina yawan bibiyar shi zakiga kaman gobe ne ya Gama jinya ya dawo garemu"

" To Amma baka gani bane Yanda yaji ma kanshi ciwo, duk jikin shi raunuka ne sai ihu yakeyi Yana hargowa ya Hana ni samun Daman zantawa dashi ballantana na sanar dashi matar shi ta aihu k...."

" Aa kull, kada ki kuskura ki qara sanar dashi wani Abu da ya danganci Yusrah ko 'yarshi, hakan zai qara rikitar dashi ya kasa samun nutsuwa zaiyi ta burin zuwa ya ganta Kuma Kinga hakan ba samuwa gareshi zaiyi ba, ki rabu dashi kawai ai 'ya tashi ce dole idan ya fito zai samu damar zuwa ya ganta idan yaso ma ya daukota ta dawo wurin shi"

" To shikkenan, yanzu Bari na tafi mu qarasa Shirin suna Dan ni siyayyan da auntyn su tayi no baiyi min ba gaba daya, inaso sunan 'yar Khamis dina yafi na kowa Rabin kudin adashe na Zan kashe a kanta na nuna ma mutane ko Bata da uba a kusa tana da gata"

"**********
Da sauri Nasreen ta miqo ma Aisha ruwa sai Jan Baki takeyi tana yarfa hannuwa saboda zaban yaji,

Sauqe wani gauron ajiyar zuciya tayi yayin da sanyi ruwan ya ratsa har cikin maqogwaron ta, Bata daddara ba taci gaba da zambada ma kifin dake gabanta yaji tana ci, nikam na zabga tagumi Ina kallon ikon Allah Saida tayi haja kusan sau uku har numfashin ta wani sama_sama yakeyi saboda jaraba,

Can ta dago ta kalle ni tana dariyan dole
"Shhh yahh Yaya ne Mai jego, shhh shin wani qura min shhshido?"

" Wallahi Allah sai ya Kama ki idan kikayi kisa Kuma ki sani duk son da mijin ki yake miki a kan danshi Zaku iya yin hannun riga"

Tsaki taja tana sake Buda ma piece din dake jikin fork dinta borkono, takai Baki ta Kora da ruwa sannan ta sake dago idanun ta da ruwan hawaye ke kwance a cikin su tace
"Meye abun shhh kisa a Nan? I'm craving for spicy food idan banci ba ji nakeyi kaman Zan mutu ki barni naci Kaya na Babu Wanda yasan irin naki fitinar lokacin da kike da cikin Jannat"

Wani matsiyacin dariya nayi da na tuna lokacin, Ina kwance Ina Shan baqar azaba a hannun Khamis magana ma ba iya shi nake ba ballantana a Kai Kan zaben abinci,

"Hmm Kedai ci kifi kawai tunda abincin suna yayi Miki kadan Saida Kika daga bawan Allah Yana zaman_zaman shi kin dago shi Wai ya siyo Miki kifi zaiyi tunanin ma horo muke Miki da yunwa ko Kuma Mun Miki Rowan abinci"

Tabe baki tayi tace "idan ma yayi tunanin hakan can mishi dan nikam buqata na ya biya, ta daga wayanta ta danna Kiran Safwan Saida ya kusan tsinkewa kafin ya dauka,

"Haba Yaya na? Telan ya riqe ka ne kowa ya Gama shiryawa Kaya Basu iso ba?"

"me yasa Baki da haquri ne? Bai Gama hada dayan na Yusrah bane yace Yana gamawa zai Kira ni na hado gaba daya na kawo muku"

" Ohoo yanzu Yusrah tafi ni Kenan kou? Tunda an Gama nawa ka karbo ka kawo min Mana ai ita tana da Wanda zatayi fitan suna dashi anjima"

" Ai Dole na tunda na zamo bawan ki da Zaki saka ni jigila sau biyu, idan ba Zaki iya jira a Gama na Yusrah na hada na kawo muku ba sai ki Kira mijin ki ai shima Yana da mota zanyi Masa kwatancen shagon yaje ya karbo miki" diff ya katse wayan,

Qwafa Aisha tayi tana kallo na sai dariyan mugunta nake Mata Dan naji conversation din nasu gaba daya,
"Ke kiyi lokacin ki ne kinga nazo wurin da kike ne dole duk rashin mutuncin da Kika min na dauka, Amman Yaya Safwan zai Gane Kuran sa dan auren ku Saida izini na za'ayi idan nace ban yarda ba Babu Yanda za'ayi kice kin amince"

4:22pm
Yana tsaye jikin maotar shi da waya kunnen shi Nasreen ta fito karba musu kayan a wurin shi,

"Eh gata nan ta fito sai ki daina damu na yanzu fitinanniya kawai" ya fada tare da katse wayan, sake fuska yayi suka gaisa da Nasreen sannan ya bude marfin motan ya Ciro laidan kayan su Aisha ya miqa Mata,

"Gashi ki bayar a hannun Yusrah ta fara dauka tukunna ki bawa Aisha"

Da "To" Nasreen ta amsa sai Kuma taja ta tsaya,
"Yaya dai qanwa ta, kina buqatar wani Abu ne?"

Girgiza Kai tayi tace "inaso na tambaye ka ne"

"Uhmm hmm Ina jinki"

"ya Safwan kana son aunty Yusrah ne?"

Wani banbaraqwai yaji tambayar, "mai yasa Kika tamabaya? Ko wani Abu ne ya faru?"

" Aa itace kawai tace na fada maka indai kana sonta zaka aure ta itama tana son ka.............🤦🏻‍♀️

*Idan na samu dama Zaku samu qarin post kafin gobe*
Don't forget to follow
Vote
Share
And comment as you read 💖

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

17🧛🏽‍♂️
"Ita Yusran ne ta fada Miki haka Nasreen??"

Gyada Kai tayi tana wani lanqwasa wuya kamar kamilan gaskiya tace
"Wallahi kuwa ya Safwan, tace tana Jin kunyar ka ne shiyasa ba zata iya fada maka da kanta ba"

" Shine ta rasa ma Wanda zata bada saqo ya fada min sai ke?"

" Eh Mana, ai tasan idan ta fada ni bazan ji kunyar fada maka bane shiyasa ma suka turo ni"

" Qarya kikeyi, Yusrah ba zata taba yin haka ba ko wanene ya fada bazan yarda ba saboda nasan halinta nasan abinda zata iya aikatawa da Wanda ba zata iya ba, dan so kam Ina son Yusrah sosai Kuma Ina da niyyan auren ta Amman kada ki sake irin haka ko ba Mani ba kinji?"+

Turo Baki tayi cikin shagwaba da yabi jinin jikin ta ya zamo Mata dabi'a tace " to ai daman Bayan ma Kai Babu ma Wanda Zan fada Amman tunda bakaji dadin abinda nayi maka ba akwai wani malamin su da ya dade yana sonta zance mishi injita ta shirya ya fito nasan shi bazai qaryata ba"

Ta juya bujim_bujim zata wuce da sauri ya jawo gefen gyalenta ta dawo, "yi haquri dan Allah auta kada kimin haka, na gane qaunata kikeyi da Kika fada min wannan zancen Amman yanzu bansan ma ta Yaya Zan fara neman auren Yusrah ba Kinga Bata dade da aihuwa ba yanzu yayi wuri"

" To shikkenan tunda haka kace, sai ka Bari wani yazo yayi maka over taking, nidai Allah ya gani na fita hakkin ka tunda na sanar da Kai halin da ake ciki, kaga tafiya ta sai anjima"

Ta juya zata koma ciki ya sake jawo gyalen ta
"Matsala ta dake Kenan auta, har yanzu Baki da wayo yanzu idan Kika tafi Kika barni da Wannan da baqin labarin Yaya kike so nayi? Ai tunda Kika tunkare ni Kika fada min matsala ai dole tare zamu Nemo mafita"

" Eh to, ni inada mafita Amman sai kayi min wani alqawari"

" Ko menene kike so ko meye kawai ki fada Zan Baki shi Nasreen indai Zaki Mun hanyar Yanda Zan mallaki Yusrah"

"Ni bani buqatar wani Abu, ni kawai burina ka dauke aunty Yusrah daga gidan Nan da wuri duk tabi ta cika Mun space Ina buqatar ganin ta fita daga gidan mu da ita da yarinyar ta, so idan zaka aure ta da wuri kawai ka wuce direct wurin baban mu ka fada mishi qudurin ka indai shi yayi Mata maganar ka ba zata taba musu ba zata amince ta aure ka"

Washe fararen haqwaran sa safwan yayi yace " Allah ko auta"

"Ka gwada ka gani Mana nidai kawai ka cika min alqawarina na auren ta cikin gaggawa idan ba Haka ba Kuma, hmm mmm Wanda yasan Yanda yayi ya hada yafi kowa sanin Yanda zaiyi ya wargaza"

" Baza ma ayi haka ba auta, kin Gama taimako na yanzu kwanan Nan Zan daga Miki Yusrah ki samu space, na gode qwarai qanwar mu ga tukuicin ki"

Ya fada tare da Ciro 3k daga aljihun shi ya miqa Mata, Saida ta harari kudin kaman ba zata karba ba sai kuma wani tunani yazo mata ta karba,
"Na gode ya Safwan Bari na Kai musu kayan kada suyi ta jira"

STORY CONTINUES BELOW

Gyada Mata Kai yayi fuskar ta dauke da murmushi zuciyar shi fari Tass ta juya ta Shiga gida, finally shima zai sake samun family, zai maybe gurbin matar shi da Dan cikin ta da suka rasu da Yusrah da Jannat,
**********
"Ga kayan aunty Yusrah, yace ki fara dauka kafin ki miqa wa aunty Aisha nata"

Karban laidan nayi Ina duba kayan ciki nace "yanzu Mai ya zaunar dake Nasreen, ko hira kikayi da ya Safwan din?"

"Allah ya sawwaqe ni Mai zanyi da bazawari?" Ta fada hade da yamutsa fuska,

Riqe Baki ni da Aisha mukayi a tare muka ce " iyee??! To me ya saka Kika dade a wurin shi idan ba hira ba?"

Ranqwafowa daidai kunne na tayi saboda da mutane da yawa a dakin ta rada min
"Auren ki naje hadawa, Kuma wallahi yace very soon zai turo a Baki shi ya aura ki tafi ki bar Mana gida"

Wani bacin Rai naji a zuciye na yunqura Zan Kai ma Nasreen duka tayi saurin ja da baya tana dariya,

"Wallahi Kika sake Kika dake ni sauran Abu biyu da na fada ranan zanje na cika su Kuma kinsan tsaff Zan iya, yanzu Nan na hada Miki ciwon Kai na kwanta saman cinyan mama nasha barci" tana dariyan shaqiyyanci ta fita daga dakin ta barni da tuquqin baqin ciki,
"Tofa yanzu dai Abu ya kankama, daga anbi qafan manya sai abiyo ta qafa na dan daga Jin bayanin Nasreen nasan akwai haske cikin wannan lamarin"

Tsaki kawai naja na dauki Jannat na fita daga dakin, naso na wuce dakin mama ne na zauna ni kadai dan abinda Nasreen tayi ba qaramin Bata min rai yayi ba su Basu da wani burin da ya wuce su raba ni da Khamis ne? Meyasa Nasreen tayi saurin manta matsayin shi cikin rayuwata ne? Dukda ita yarinya ne ai tana da hankali takai munzalin da ya Kamata ace ta fara banbance daidai da ba daidai ba,

Da fita na mutanen dake wajen suka tsare ni Wai za'a dauki pictures, badan naso ba na tsaya na Shiga Ina ta murmushin Yaqe photographer Kuma kashe hasken yake ta ko Ina,
Basu barni na huta ba sai Bayan magriba, Aisha ta tsokane ni son ranta musamman da taga kaman ba son Safwan nake ba gashi Nasreen ta Gama hada min bomb Amman Saida ta Taya su mama kintsa gidan tsaff kafin mijinta yazo ya dauke ta suka tafi, saboda gajiya ranar da wuri mama ta wanke Jannat ta Kuma taimaka min Nima na wanke jiki na don yanzu Kai ya waye dukda mama tana da kafiya Amman batamin irin wankan jegon da akeyi da na ruwan azaba ba, Wanda za'a gasa mutum sai yayi laushi,

Ana gamawa nayi feeding dinta dukan mu biyu muka bi lafiyar gado Dan mun nuqu sosai Kuma Jannat Bata da wani fitina ko yawan kuka, daga zaran cikin ta ya cika shikkenan magana ya qare,

**********

Duhu ne ta ko Ina bani Gane Ina ne gaba na Ina ne baya na, tsoro ya Kama ni! Na Shiga rudani! Bansan Ina na shigo ba! Bansan me ya kawo ni ba, ga hawaye dake zuba a idanun na Wanda bansan dalilin shi ba,

Qaran faduwan qarfe naji ta baya na Wanda yasa nayi saurin juyawa Amman duhu ya hana ni gani komai, sai Kuma naji kaman takun mutum ta gefe na, na sake juyawa still bani iya ganin komai, "innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" shine kawai kalmar da harshe na ya lalubo yake maimaitawa don ita tashin hankali na gama Shiga,

Cikin wani hikima na ubangiji Kuma sai naji qara kaman an kunna switch sai haske ya bayyana ta baya na Amman tsoron da ya shige ni lokaci daya na bansan Wanda ya kunna hasken da Kuma me Zan gani cikin hasken ya Hana ni juyawa qirji sai dukan uku_uku yake yi,

"Yusraaahhh" naji muryar Nan daya tilo Mai tasiri a cikin zuciyata ya Kira sunana cikin wani salo Mai dadi da Jan zuciya, lokaci Daya Kika na ya rikide ya koma dariya nayi saurin juyawa don na samu ganin halittar da nayi kewar shi fiye da komai a yanzu Amman me?!"

Sai hango Khamis nayi kwance a cikin jini ga sharbeben Adda a gefen shi shima gaba daya ya dabaibaye da jini,

"Yusraaahhh" ya sake Kiran sunana Yana miqo min hannun shi alamun nazo, wannan karon zafin azaba da daci naji cikin muryan shi da gudu na qarasa wurin da take kwance na durqusa a gaban shi, a rikice nake dudduba jikin shi Yanda akayi mishi Sara na wulaqanci harta kayan jikin shi sun farfashe, jinin dake zuba daga jikin shi Kuma Bai tsaya ba,

Kuka na fashe dashi kaman Allah ne ya Aiko ni ganin Khamis na Shirin rufe idon shi, magana yake son yimin Amman ya gagara da qarfi nake girgiza shi Ina kiran shi on top of my voice,

"Khamis!!! Ka bude idon ka Dan Allah, ka fada min waye yayi maka wannan abun?? Wayene please Mai kayi musu??" Na qarasa hade da saka want marayan kuka,

Da qyar ya iya dago hannun shi ya kawo Kan fuska ta Yana share min hawaye na a hankali ya furta
"Me yasa Kika rabu dani Yusrah? Na fada Miki idan Kika barni mutuwa zanyi, meyasa Kika guje ni Bayan kinsan har yanzu Ina son ki?"

Girgiza kaina nakeyi hawayen fuska na Yana qaruwa
"Aa Khamis, dan Allah ka tashi gani na dawo gareka kada ka tafi ka barni da Jannat Dan Allah"

Ya bude Baki zaiyi magana tari ya sarqafe shi harda gidan jini ke fitowa ta bakin shi, ganin hakan yasa hankali na ya qara tashi Ina jijjiga shi gaba daya jinin dake jikin shi ya Gama bata kayan jiki na, can Kuma sai ya sauqe ajiyar ziluciya Bai sake numfashi ba ko sau daya,

Rungume shi nayi a jiki na Ina kuka Mai ban tausayi, firgigit nayi na farka Ina addu'an neman tsari daga shaidan, saboda irin tashin da nayi a firgice yasa Nasreen farkawa itama ta saka kuka,
Daukan ta nayi Ina rarrashin ta har yanzu Ina cikin firgicin abinda na gani cikin mafarki Kuma Ina roqon Allah yasa mafarki ne kawai ba Wanda ke kamanceceniya da gaskiya ba, Saida na samu nutsuwa na yadan dawo na saka ma Jannat nono a Baki tana Sha Bata dade ba tayi barci don Daman shine a idon ta,

Tun ranar da nayi wancan mafarkin ban sake maimaita irin shi ba hakan yasa na Dan samu nutsuwa a zuciyata hankali na ya kwanta naci gaba da sabgogin gaba na Amman har gobe Khamis da tunanin shi suna mandaqe a birnin zuciyata, Jannat kuwa yarinya Mai haiba yau kwanan ta 50 a duniya sai qara girma takeyi tana qara kyau yanzu ni bani wani juran daukan ta sai Nasreen ne idan ta dawo daga makaranta zasuyi ta karada cikin gidan da ita ko Kuma mama ta goye ta kwata_kwata taqi jinin a kwantar da ita,

Ta bangaren ya Safwan ma shiru kake ji Wai shaho yaci shirwa, tun Ina damuwa a Kan abinda Nasreen ta fada min na dai turo iyayen shi har na daina naci gaba da harqoqin gaba na,

**********
5:02am

Saurin tashi nayi na zauna ga fanka a dakin Amman na hada gumi ta ko Ina, har kayan jiki na yayi sharqaf da zufa, karanto duk wani addu'an da yazo Baki na nake yi, Dan firgici da tashin hankalin da na shiga yafi na ranar,

Sakk irin mafarkin ranar nayi, Khamis na gani a cikin jini Yana maimaita min irin kalaman ranar, Mai hakan yake nufi? Khamis Yana cikin wani hali ko me?..............🤦🏻‍♀️

Don't forget to follow
Vote
Share
And comment as you read 💝

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

18🧛🏽‍♂️
Sauqa nayi daga gadon a hankali Yanda motsi na ba zai tada Jannat ba na Shiga toilet din mama na dauro alwala nayi Sallah raka'a biyu saboda ba'a Kira sallan asuba ba tukunna na zauna ina roqon Allah ya sauya wannan mafarkin da alkhairi, da lokaci ya cika na tashi nayi Sallah na ci gaba da addu'oi na daga inda na tsaya, har gari ya fara haske ina zaune saman darduma hankali na bai kwanta ba ina matuqar son na san halin da khamis yake ciki,+
mafarki iri daya har sau biyu me hakan yake nufi? Idan kuma wani abu ne ya same shi Allah yake min nuni cikin mafarki fa? Yanzu kam koda ban so ba dole yau zan ziyarce shi a psychiatry zanje na gani da idona kuma na tabbatar ko yana lafiya,
Ina zaune mama ta shigo dakin na dago na gaishe ta da "ina kwana mama"

"Lafiya qlau hajiya, yaya kwanan Firdausi"

" Lafiya qlau, mama daman inason tamban ki yau zanje na dubo Khamis a asibiti"

Tsayawa da duba kayan da takeyi a wardrobe tayi ta dago tana kallo na da alaman tambaya tace
"Khamis kuma? Me yasa?"

"Haba mama shifa mahaifin Jannat ne ai ko banje dan komai ba ya kamata musan halin da yake ciki saboda ita"

" To shikkenan hajiya amman ki tambayi izinin mahaifin ki tukunna idan ya amince sai ki tafi"

Gyada Kai kawai nayi na ci gaba da addu'a ta duba jannat har yanzu tana shan barcin ta bata tashi ba, sannan ta dauki kayan da ta ciro ta fita dashi, sai wuraren 7 na tashi daga zaune dan naji motsin jannat ta farka tana kaiwa wani lokaci ba'a daga ta ba zata fara kuka, nayi feeding dinta mama ta karbe ta zatayi mata wanka ni kuma na tafi wurin baban mu,
kafin na isa ƙofar dakin Nasreen ta ƙaraso da gudu kace wani ne ya rako ta, ba don na matsa ba sai ta iya bangaje ni tana dariya kaman zararriya,

"Yau dai Allah yayi aunty Yusrah, buri na ya kusan cika za'a tattare ku keda jannah mai ƙaton kai ku bar mana gida"

Kallon rashin fahimta nake mata dan ban gane inda maganar ta ya dosa ba tace,

"Har yanzu baki harbo jirgin ba?"

Ƙaramin tsaki naja zuciyata bata cikin walwalan da zata jure shirmen Nasreen a yanzu nace mata
"Ke! Ni bani da lokacin ki, idan zaki fadamin abinda ya kawo ki to ina sauraro, idan kuma baki da abin fadi zaki iya bani hanya na wuce"

"Na isa na barki ki tafi baki saurari wannan labari mai daɗi ba? To dai yaya Safwan ya dawo daga tafiyan da yayi kwanaki, kuma da isowar sa ya fada ma iyayen shi qudurin shi a kan ki kuma sun amince zasu nema mishi auren ki, a halin yanzu ma anjima kadan ko da yamma zasu ƙaraso ayi mai kankat daga kin amince sai a saka rana,

sai kije ki fada ma baba ra'ayin ki daman ya tura ni na nimo ki ne shine na kira ya Safwan din a waya muka tattauna yanzu haka wurin ki zanje sai kuma gashi kin fito, oya je ki amsa query"

Tana rufe bakin ta ba tare da ta ankara ba na jawo ta na kifa mata mari kafin na hankade ta gefe ta saki ihu daman a kan tsini nake gashi ta qara takalo ni, Nasreen ta gama dani ta ruguza min duk wani shiri na ko a wani yanayi na tsinci kaina tasan bazan iya musu da baba ba dole idan ya bijiro da buqatar shi na amsa masa balle yanzu da na lura dukkan su ƴan gidan kaman sun gaji da ni ne,

STORY CONTINUES BELOW

Zuciya ta bata shirya cire khamis a cikin ta ta musanya da wata ba, inama zasu qara min lokaci, ba lallai bane idan na auri ya Safwan yaji dadin zama da ni ba don Allah ya gani bani son shi bani ƙaunar shi soyayya ta na khamis ne shi kadai,
ihun Nasreen ne ya dawo dani cikin hayyaci na ya Usman ya qara mata wani marin a kan wanda nayi mata, ban sani ba ashe yana tsaye yana sauraron abinda Nasreen take fada min, yayi saurin toshe bakin ta kada ta jawo hankalin baba ya sake kifa mata ranqwashi yana
"shashasha wawuya ki sake shiga abinda babu ruwanki ki gani sai na zana ki da bulala a tsakar gidan nan, kuma ko a hanya kika sake ganin safwan ko a hanya ne kika gwada kin sanshi sai sauya miki kamanni doluwan banza kawai rufe min baki" ya daka mata tsawa yana sakin ta,

Hadiye kukanta Nasreen tayi sai idanun ta kake gani zuru_zuru hawaye sun taru a ciki amman tsoro ya hana ta kuka yanda tayi kicin_kicin da fuska nima sai da taso bani dariya,

Na juya na wuce dakin baba ba tare da na sake bi ta kanta ba tunda ya Usman ya riga ya gama min da case dinta, sallama nayi baba ya amsa yana zaune a qasa yana breakfast kaman ko wani lokaci na tsuguna har qasa na gaida shi shima fuska a sake ya amsa yana tambayan kwanan amaryar shi Jannat,

"Lafiya qlau baba daman ma ina son tambayar ka zamuje dubo baban ta a asibiti anjima"

"Wani abun ne ya sake faruwa?"

Girgiza kai nayi nace "A'a babu komai kawai dai ina son kai masa Jannah ne ya ganta amman babu wani abu bayan nan"
"To masha Allah, munyi magana da iyayen yaron nan Safwanu yace yana son auren ki shine nace su dakata na tuntube ki tukunna,

Amman ki sani mutuncin ko wace ƴa mace fa shine dakin mijin ta kuma burin ko wani iyaye shine bayan sun tarbyyantar da ƴaƴayen su aurar dasu kuma su zauna lafiya tare da abokan rayuwan su, hajiyata ba zanyi miki dole ba saidai ɗan adam kowa da kalan nashi halin Safwanu ba ɗaya yake da Hamisu ba ko dan albarkacin wahalar da kika sha a auren ki na farko idan Allah yaso zai baki farin ciki da jin dadi a auren ki na biyu dan haka yanzu ra'ayin ki kawai nake son ji nidai na baki zabi"

Wani diff naji lokaci ɗaya wuta ya dauke min da gaske Nasreen ta ida nufin ta a kaina a dole ta shigo da ya Safwan cikin rayuwa ta, dan ko kusa banyi girman da zanyi wa mahaifa na musu ba bani da wannan matsayin, sa'annan idan na qi yayan aminiyita wanda gaba daya familyn su suka dauke ni a matsayin nasu kaman nayi butulci ne,
Gyada kai nayi in affirmation nace "duk abinda ka yanke ni mai biyayya ce a kanshi, na baka zabi baba bani da wani ta cewa a kai"

Murmushi yayi cike da jin dadi yace "Allah yayi miki albarka Yusrah, yanda kike qoqarin faranta mana Allah yasa ƴaƴan ki su ji qanki su faranta miki"

Sauqar da kaina ƙasa nayi ina ƙoqarin tare hawayen da yake shirin sauqo min nace "ameen baba"

"Yanzu idan kun tashi tafiya sai ki fada min zan baki kudin abun hawa"

"Tare ma da ya usman zamu tafi yace zai kaini ya dawo dani"
"Aa ban yarda ba amarya ta ba zata sha sanyin mashin da safiyan nan ba idan na tashi kizo ki karbi kudi ku shiga keke napep ki rufe ta cikin mayafin ki kada ta kwashi mura"

Murmushin yaqe nayi na miqe hade da fadin "to mun gode baba" na juya na fita zuciya ta tana qara min nauyi haka cikin rashin walwala nayi breakfast nayi wanka sannan ya Usman ya dauki Jannat ni kuma na karbo mana 2k wurin baba muka fita,

***********
Tana zaune ta zabga tagumi tana kallon qannen khamis guda biyu mata sai sharban kuka suke yi tana jin inama ace ita ne ta samu damar yin kuka ko zata rage radadin da take ji cikin ranta,

Shigowan mahaifin shi da qannen shi maza 2 da yayan shi 1 yasa sukayi saurin tashi suka nufe shi suna tambayan ko an same shi?, With disappointment on their faces suka samu wuri dukan su suka zauna gaba daya hankalin su a tashe yake,

Numfasawa mahaifin shi yayi yace "wallahi har yanzu ba labari, babu wani ci gaba a cikin binciken a yanda police suka ce sunyi iya bakin qoqarin su amman basu gano inda yake ba"

Sai yanzu ta samu kuka yazo mata, tayi loosing duk wani hope da take dashi na za'a same shi,
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel innalillahi wa inna ilaihirraji'un, yanzu ina khamis ya tafi a cikin halin hauka? Cikin wani hali yake me yake shiryawa? duk bansani ba, shekaran jiyan nan ake sanar damu irin raunukan da yaji saboda tsanantar ciwon shi ba don Allah ya kiyaye ba da ya rasa wani sassa ko bari na jikin shi, amman ace yau ya bar psychiatry a haka?
wannan wace irin ƙasa ce wanda bata da tsaro mahaukaci zai gudu daga asibiti kuma a kasa samun yanzu idan wani abu ya sake samun shi fa yaya zanyi da raina?"

Patting bayan ta yake yi a hankali cikin sigar lallashi ba don shima bayi cikin damuwan ɓatan dan shi ba sai dai tashin hankalin da take ciki yafi nashi,
"Kiyi haquri Firdausi mu duqufa ma addu'a insha Allah duk inda khamis yaje zai dawo gare mu idan Allah ya yarda zamu same shi so ki kwantar da hankali ki kada jinin ki ya hau"

**********

"Kamar yaya babu sunan shi a nan? Ki sake dubawa dan Allah na tabbatar yana ciki Please ko 10 minutes ne ki bamu na ganshi dan Allah sister"

Gyada kai nurse din tayi ta tashi taje wurin wata nurse wanda kaman ita ne in charge tana tambayan ta, dagowa daya nurse din tayi ta kalle mu sannan qasa_qasa tace mata,
"Shine fa mahaukacin da ya gudu ranar Thursday kuma kinsan ance ba'a son kowa ya sani su din su waye me yasa suke son ganin shi?"

"Macen dai tace ita matar shi ne amman namijin bai fadi matsayin shi ba"

Dagowa tayi ta kalle ni ta maida duban ta wurin nurse din tace "wallahi ƙarya takeyi, matar shi ne tun da aka kawo shi wata da watanni bata zo ba sai yau? Kawai kije ki kice musu ba'a samun ganin shi, kindai san case dinshi is confidential idan kika bari wani abu ya fita daga bakin ki to ke kika sani idan kika saka kanki cikin matsala"

Riqe baki tayi tana zare ido tace "rufa min asiri ƴar uwa, ina zan bari aji mutuwan sarki daga baki na? Bari ki gani" ta juyo ta dawo wurin da muke tsaye dake daga ganin ta shahararriyar maqaryaciya ce yasa ko ɗarr a ranta bata ji ba ta dubi cikin idanun mu tace

"Kuyi haquri fa, matsalan shi yayi tsanani ba'a barin kowa ya ganshi yanzu saidai zuwa wani lokaci mai tsawo idan an samu wani ci gaba ya fara samun sauqi zaku ita dawowa ku ganshi............🤦🏻‍♀️

Manage😣

*Ummu Najma ce😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

19🧛🏽‍♂️
Marairaicewa nayi nace mata, "dan Allah sister ki taimaka mana ko daga nesa ne na ganshi Please 10 minutes ya ishe ni"
"Baiwar Allah ki bar nan wurin kafin kema ayi admitting dinki tunda na lura baki da tunani, na fada miki ba'a barin kowa ya ganshi so kike yi na rasa aiki na ne ko kuma me? Wannan ƙasurgumin mahaukacin kika shiga wurin shi saidai a fito dake ba dai ki fito da ƙafafuwan ki ba"+

Ya Usman zaiyi magana firr na hana shi, naci gaba da roqon nurse din nan ina mata magiya ba don ranshi ya so ba amman haka baiwar Allahn nan ta ƙeƙashe ƙasa taƙi yarda daga qarshe ma taruwan dangi sukayi min bayan sunga na tura ya usman waje tare da jannah saboda nasan idan yaci gaba da tsayuwa zai iya musu babu daɗi kunsan saurin zuciya irin na maza,

I tried, i insisted but to no avail haka na fita daga ward din disappointed inaji kaman nayi kuka but I don't want to cry in public, qarasawa wurin shi nayi na karbi jannat daga hannun shi nayi gaba ba tare da nace masa komai ba yayi saurin riqo hannu na ya dawo da ni yana kallon cikin idona da ya tara hawaye qiris yake jira ya sauqa,

"Yaya kinzo zaki wuce baki min wani bayani ba? Kin samu ganin shi ne?"

Girgiza kai nayi kaman zan saki kuka nace "Aa basu barni ba, mu tafi kawai" na fada tare da yin gaba  ya bini a baya har bakin titi muka tsari napep, muna shiga na lalubo wayana na kira mamanshi saida nayi mata 2 missed calls bata daga ba sai a na ukun tayi picking,

Her voice was down amman bansan dalili ba, yanda take amsa min gaisuwa na wani iri kaman tana cikin damuwa, maybe itama a kan halin da khamis din yake ciki ne hankalin ta ya kasa kwantawa,

"Mama yaya jikin abban Jannat?" Na tambaya cikin son tabbatar da halin da yake ciki,

Shiru tayi tana tunanin amsar da zata bani, can tace "da sauƙi sosai Yusrah"

"Da sauƙi amman me yasa da naje suka ce jikin shi ya tsananta?"

Daram! Taji ƙirjin ta ya buga abinda take gudu kenan, bata son kowa ya san da Maganar batan Khamis musamman ma ni, tunda nice na tura shi psychiatry a karo na farko kada yanzu ma na sake saka hukuma ta kamo shi ta maida shi, ta amince Khamis yayi kuskure amman wahalan da yake sha ya isa haka,

Cikin inda_inda tace "k...kinje...kinje Asibitin..ne?"

"Eh naje na nemi ganin shi amman sun hana ni, sunce wai jikin shi ya tsananta dan Allah da gaske ne mama?"

Sauqe ajiyar zuciya tayi tace "toh da sauqin kenan za'a ce, basu son a dinga barin mutane suna ganin shi ne shiyasa suke cewa jikin ya tsananta amman da sauqi kada ki daga hankalin ki kisa damuwa a ranki"

Ji nayi hankali na ya kwanta amman kadan saboda ganin khamis da idanuwa na shine kawai zai sama min cikakkiyar kwanciyar hankali na qaryata mafarkin da nake yawan yi a kanshi, gyada kai nayi kaman tana gaba na nace
"To mama daman na kai masa Jannat ne ya ganta amman yanzu gashi har mun kusa isa gida, dan Allah duk lokacin da aka fara bari ana ganin shi ki sanar dani sai na kai mishi ita"

STORY CONTINUES BELOW

"To Shikkenan insha Allah zan sanar dake, nima zanzo naga kishiyar tawa na kwana biyu ban saka ta a ido na munyi fadan kishiyoyi ba,

"Murmushi mai sauti nayi nace to Shikkenan mama, sai kinzo"

Mukayi sallama ta kashe waya tana salati, can ta sake fashewa da kuka tausayin Khamis da wannan qaramin alhakin Jannat ya shiga ranta, da tana da dama duk abinda zata iya dan ta maido ma khamis iyalin shi zatayi don tasan saboda Yusrah ya gudu daga psychiatry,

Daga labulen dakin nayi na shiga da sallama dauke da jannat a hannu na, Nasreen na gani zaune saman pillow a qasa ta ciro drawern Jannat tana goge kayan ciki, mama kuma tana zaune bakin gado tana linke namu kayan wanda muka wanke jiya aka kwaso su daga shanya,

Zama nayi na fara feeding din Jannat naga tana ɗan qananun mita nasan yunwa ne da bacci tana sha ina tunanin Khamis mafarkin da nayi jiya yana dawo min cikin qwaqwalwa ta,
i don't know why amman lokaci ɗaya maganar da mama ta fada min cewa khamis na lafiya ya goge daga cikin qwaqwalwa ta, har yanzu zuciya ta tana bani Khamis yana cikin Matsala i just feel like nayi ta kuka har sai ya dawo gareni,

Ina gamawa na miqa ta ma Nasreen nace ta fita ta saka ta a kafada su waje tana jijjiga ta na samu tayi gyatsa kada na kwantar da ita tayi min tumbudi, barin gugan Nasreen tayi ta karbi Jannat tana mata wasa suka fita,

Nayi hakan ne dan na samu privacyn da zanyi expressing pains dina wa macen da ita kadai ce zata iya fahimta ta a duniyar nan, mama tana jera kayan cikin wardrobe kaman daga sama taji na rungumeta ta baya na saki kuka mai zafi,

A rikice ta juyo tana kallon fiska ta da lokaci daya ya canza,
"Yusrah lafiyan ki kuwa? Me ya same ki ne?

Sake rungumeta nayi kuka na yana qaruwa da qyar na iya bude baki nace
"Mama Khamis yana cikin wani hali, nayi mafarkin an kashe shi har sau biyu kuma har yanzu hankali na ya kasa kwan...."

Saurin saka yatsan ta saman lebben ta tayi "shhh! Babu kyau fadan mummunan mafarki indai fadan bayi da wani alfanu, kiyi ta mishi addu'a kawai kina neman tsari daga sharrin cikin mafarkin, ina da kuka je asibitin kun samu ganin shi?"

Girgiza kai nayi nace "Aa sun hana mu ganin shi, wai ba'a bari ana shiga wurin shi, amman munyi waya da maman shi tace wai jikin da sauqi, na kasa gaskata hakan ne a cikin zuciyata"

"Yusrahh!!"
Ta kira sunana cikin sigan jan hankali,
"Khamis is Your past, yana cikin rayuwan ki ne lokacin baya kadai yanzu baki da sauran dangantaka dashi bayan Jannat kadai dake tsakanin ku, kada ki manta Khamis ya cutar dake sau da yawa ke da bakin ki kike shaida mana irin azabtuwar da kikayi a hannun shi, meye amfanin damuwa da mutumin da yake cutar dake?" Ta tambaya tana share mun hawayen dake zirya a idanu na,

"Nayi kuskuren barin kulawar ki gaba ɗaya a hannun wani bare wanda bamu sanshi ba ba tare da na bibiye halin da kike ciki ba, ba zan sake kuskuren barin zuciyar ki ya koma wurin khamis ba saboda bai dace da ke ba,

Har yanzu ke yarinya ce qarama ko cika shekaru 22 bakiyi ba, rabuwan ki da khamis ba shi bane qarshen rayuwar ki, na riga na fahimci sauran soyayyar khamis ne yake dawainiya dake amman ya zamo miki kaman dole ki cire shi gaba daya daga cikin ranki ki amince da Safwan muna da yaqinin zai baki farin ciki,

Basai mun tsaya bin wani dogon hanya ana wani kauce_kauce ba, dukkan mu muna son ki sake aure da wuri dan ki kasance cikin farin ciki ki yarda da auren nan Yusrah dan Allah"

Bance komai ba na sake rubguman ta tare da daura kaina saman kafadan ta ko zanji sauqin ciwon dake zuciya ta, yanzu da iyaye na suka nuna basu qaunar Khamis a tare dani ko nima ina son fitar dashi daga zuciya ta amman ba abu mai sauqi bane,

Maganar aure na da ya Safwan ya fara kankama tunda an samu amincewa ta amman ance sai mun fahikci juna sosai kafin manya su shiga ciki dan aure ba qaramin al'amari bane kaman yanda turawa sukayi masa laqani da 'A life time journey' haka yake, babban al'amari ne mai cike da ƙalubale masu rikitarwa,
8:03pm
Zaune nake a gaban mirror ina saka bracelate dina wanda rabo na da saka jewelries ko nayi kwalliya har na manta inaga tun kafin na samu cikin Jannat,

Qarasowa wurin da nake zaune Nasreen tayi da turare a hannun ta tana feshe ni dashi ta ko ina nayi saurin miqewa raina a bace zan qwace turaren ina
"Meye haka ne auta? Baki da hankali ne wurin namiji fa zanje fa, kuma kinsan ratsa tsakanin mazan da ba muharraman ka ba da turare mai qarfi a jikin ka ba yanda har wani yaji yayi mishi dadi to laifin zina ne a kan ki"

"Kai aunty Yusrah, ana taba ki kifara kawo wa mutane sharhi da hadisai, ai ke yanzu ba matan aure bane ko?"

"Hmm Nasreen kenan, haka yawancin mutane auke tunani wannan hukuncin ya rataya a kan 'yammata da matan aure, Allah ya halicci mutane kala_kala wani yana da tsananin buqata 'dan wannan turaren naki zai iya jawo hankalin shi gare ki idan kuma ya ganki yaji wani abu hakan zai iya haddasa mishi fitina"

"Na'am ya shekiya Yusrah ummu Jannat, na yau dai kam ya halalta tunda zancen aure ake, dan Allah kiyi sauri kije kada ya safwan ya gaji da jiran ki na riga na kai mishi ruwa da drinks, kuma baki ga yanda yayi kyau ba wallahi kayan jikin shi ya amshe shi sosai yayi wani haiba da kwarjini gaskiya kinyi Sa'a aunty Yusrah bazawarin ki dai tabarakallah masha Allah ya hadu sosai"

Tsayawa nayi sakare ina kallon Nasreen yanda take zayyano bayani har wani kashe ido takeyi,
"Auta kodai bazawarin nan yayi miki ne na bar miki shi?"

harara Galla min kaman idanun ta zasu fado qasa sannan ta ja tsaki tace "Allah ya sawaƙe wallahi babu abinda zanyi da tsohon mijin wata, miji na sabo yake garr a laida babu sunan yarinyar da aka taba sakawa a jikin kati tare da nashi bayan ni"

Tabe baki nayi nace "sai kuna akace miki bayan ke ba zai sake aure ba ko? Kina nan ke ba ƴar kowa ba sai shegen kishin tsiya ke da kowa ma kishi kikeyi harda wanda ta mutu, Allah idan baki gyara halayen ki ba kina tare da ganin bacin rai auta"

Cuno baki gaba tayi tana ƙunƙuni amman a hakan bata fasa taya ni shiryawa ba, ta rangada min dauri ya zauna daram kaman wata ƴammata ta yafa min medium sized veil na hau takalmi mai tsini, sai nake jina daban kaman bani ba ina tuna lokacin da nake irin wannan hadadden kwalliyar lokacin da nake gidan Khamis kafin ya fara cin uba na,

Sake duba Jannat nayi don tabbatar da tayi barci sannan na fita zuwa parlorn baba yanda nake saka ran ya Safwan yana zaune yana jira na, ina zuwa qofar dakin naja na tsaya inajin bugun zuciyata yana tsananta, murya can qasa nayi sallama amman nasha mamakin yanda yaji har ya amsa,

Cire takalmin nayi a qofa na daga labulen na shiga da wani sallaman dauke a baki na, ina takawa a hankali zuwa 1 sitter dake ɗan nesa kadan da 3sittern da Safwan yake zaune a kai, ina ji a jiki na yanda ya qura min ido har naje na zauna sannan unexpectedly naji ya sauqe ajiyar zuciya,

Saurin dagowa nayi na kalle shi ai kuwa caraf muka hada ido, bazanyi qarya ba Safwan yafi Khamis duk wasu sirrin kyau na ɗa namiji amman ko kusa bai taka matsayin Khamis dina ba, ko yaushe matsayin shi na daban ne a cikin zuciyata, for some seconds muna kallon juna kafin nayi saurin kawar da kaina na gaida shi,

Amsawa yayi with little confidence amman bai manta da tambaya ta yaya Jannat ba, hakan ya gwada min he truly cares about my daughter, bayan mun gama gaisawa ya dan matso gaba cikin gaskiya da gaskiya yace

"Nasan you've been through alot Yusrah but i also have a past, maybe baki taba tsammanin zan zo na nemi auren ki ba nima hakan yake a wuri na, ban taba tsammanin zanyi wani aure da wuri ba bayan aure na da Suhailat amman Allah cikin ikon shi lokaci ɗaya Allah ya dauke ta tare ɗa ɗan cikin ta duk suka koma gareshi, so a gaskiya bani so muyi aure kaman na hadi ko kuma wanda bamu da yanda zamuyi,
Aure ba abin wasa bane kuma ba zama ne na qanqanin lokaci ba, idan za'a samu yanda ake so har qarshen rayuwa ake so aure yayi lasting kuma hakan ba zai taba samuwa ba saida soyayya.............🤦🏻‍♀️

*Sorry 4 d late update please 🙏🏼*

Don't forget to follow
Vote
Share
And comment as you read 💞

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

20🧛🏽‍♂️ *(Marathon)*
*Love* is the foundation of any strong relationship and everlasting marriage, ina so a samu Wannan soyayyar a tsakanin mu tun kafin mu kaiga aure, inason muyi rayuwa mai cike da farin ciki da jin dadi abin kwatance ma ko wani ma'aurata,

Nayi alqawarin zan kula dake Yusrah, zan riqe Jannat kaman ƴar ciki na kuma jini na, ba zan taba bari tayi maraici ko baƙin cikin rashin mahaifi ba kuma ba zan bari kowa ya san cewa ba ni ne na haife ta ba, zanyi ƙoƙarin ganin na goge memories din Khamis daga ƙwaƙwalwar ki, zan mantar dake duk wani cutarwar da yayi ma rayuwan ki a baya, Please ki bani dama sau daya kawai na gwada miki zallan soyayyar da nake miki,

Tsaki naja cikin zuciyata haushin safwan duk ya turnuƙe ni, shi ko iya tsara kalamai baiyi ba shi da yake baran soyayya mai kuma ya kawo Khamis cikin maganar shi? Har yana cewa wai zai fitar dashi daga cikin rayuwata da rayuwar jannat ƴarshi jinin shi, Yasan waye Khamis kuwa? Yasan matsayin shi cikin zuciyata? Tunda nake ban taba yi ma wani ɗa namiji son da nakeyi ma Khamis ba kuma HAR abada ba za'a samu wanda zanyi masa wannan son ba,

Ba don ƙaddara da ya raba ni da khamis ba, ko harara ba zai hada ni da safwan da sunan soyayya ba ballantana maganar aure, daga ido nayi na sake qare mishi kallo yana zaune dunsum ya qura min na mujiya, banga wani abun burgewa a jikin shi ba wallahi no attitude no class no nothing, na yarda yana da kyau da qirar jiki amman ni kama yake min da irin yaran da ake haifan su gaulaye dinnan irin wanda basu da cikakken lafiya,
Murmushi ne ya subuce min ina maimaita last statement dina cikin zuciya ta, ganin haka yasa Safwan shima ya murmusa a tunanin shi ya samu ƙofa ne, yace "ke nake saurare Yusrah, Please just one chance"

Ɗan hade rai nayi saboda kada yaga dama ta da yawa, sannan nace
"I'm sorry ya Safwan amman Jannat bata buƙatar duka wa'innan abubuwan daga gareka har yanzu tana da mahaifi a raye bai mutu ba kuma ina da yaƙinin idan ya samu lafiya zai iya kula da ita so na sauqe maka nauyin Jannat daga kanka ba sai ka takura ba"

"Menene abun takura a ciki Yusrah? Jannat kaman ƴata ce ai tunda jinin ki ne, ina so na maye gurbin ta da yaro na da ya mutu, i want to give her all the fatherly love and care ina son Jannat kaman yanda Khamis yake sonta maybe ma fiye da hak..."

Da sauri na katse shi da "Aa" wannan karon kam raina ya fara ɓaci, safwan yana da hankali kuwa da zai dinga hada soyayyar shi da khamis??

"Jannat mallakin mahaifin ta ne ya Safwan, kaima idan ka ƙara haƙuri Allah zai bamu wasu ƴaƴan wanda zasu zamo mallakin ka amman Khamis yana da complete control na Jannat, idan kayi mana alfarman zaman Jannat tare da mu har zuwa lokacin da mahaifin ta zai warke falillahil hamd amman zan sanar maka saboda kada ka saka rai, da zaran Khamis ya samu lafiya yazo ya nemi da na bashi ƴarshi without second thought zan dauke ta na miqa mishi kayan shi"

Shiru Safwan yayi gaba daya jikin shi yayi sanyi kuma na lura saboda maganganun da na fada mishi ne sunyi masa tsauri da yawa, amman shi bai sani bane zaman lafiya tare da ni shine mutunta Khamis, duk wanda yayi ƙoƙarin sukar khamis ko wanene zamu iya samun sabani dashi idan ba zaka fadi ALKHAIRI a kanshi ba kayi shiru,

STORY CONTINUES BELOW

Tsawon minti 7 muka dauka kowa yayi shiru babu wanda ya sake cewa komai a cikin mu saidai Safwan ya dago ya kalle ni ya maida kanshi gefe yana son magana amman ya rasa ta ina zai fara yana tsoron kada ya sake min magana na disga shi,

Can dai yayi shahada ya danyi gyaran murya sannan yace
"Na manta ban fada miki ba, kinyi kyau sosai"
Murmushi nayi nace "na gode" bani son yaji wani iri yaga kaman I'm rude, arrogant or ina son embracing dinshi ne tun ina waje ya zamo bayi iya controlling dina ballantana ace na shiga gidan shi, shima da yaga haka sai ya ɗan sake jikin shi yana jana da hira har dare ya tsala wurin 10:30pm kafin yayi mun sallama ya tafi bayan yayi mun kyauta mai tsoka,

Nima na tashi na wuce dakin mama dan a wurin nake kwana ni da Jannat na samu tana kwance tana barci an canza mata kayan jikin ta Nasreen kuma na gefen ta tana faman chatting,

Qarasawa gaban mirror nayi na fara cire earrings dina da duk suka bi suke dame ni a kunne saboda nauyi nace
"Auta mai ya samu kayan baby Kuma? Naga bayan magriban nan aka mata wanka aka saka mata shi, bai dade ba kin sake sauya mata wani"

Sauqowa tayi daga gadon still idanun ta a kan waya tayi hanyar fita tana fadin,
"Kema kinsan ko ba'a fada miki ba bayan gida tayi ta bata jikin ta dukda akwai diapers a jikin ta amman saida ya bata kayan ta, kudai je a nima mata maganin kurga, Allah ya tashe mu lafiya"

"Ameen auta, sannu da qoqari"

Bata kula da abinda na shigo dashi ba ta fita gaba daya hankalin ta bayi jikin ta, dan da ace ta sani ko kashe ta zanyi sai taga menene a cikin shopping bag din hannu na,

Shiga toilet nayi na wanke fuska ta nayi alwalan bacci sannan na fito na sauya kayan jiki na zuwa na barci, na dauko shopping bad din da ya Safwan ya bani na koma bakin gado kafin na bude, turaruka ne masu kyau guda biyu sai wani dan babban kwali mai wasu ƙayatattun designs a jiki da qaramin envelope sai boxes manya guda biyu na chocolates, i don't even like chocolates Khamis ya san da haka shiyasa bayi damun kanshi wajen kwaso min tarkacen kayan zaƙi kwata_kwata basu gaba na,

Bude daya box din nayi naci karo da wasu fashion glittery silver earrings da necklace dinshi ga bracelets da wrist watch duka iri daya suna da wasu stones masu sheqi a jiki, tabe baki nayi na bude envelope din shi kuma kudi ne a ciki har 10k, ya Safwan yayi qoqari amman gift din da Khamis ya bani a irin wannan ranan is more precious to me,

I clearly remember that Friday night, inata zumudi har na kasa boyewa tun 7:40 na gama shiryawa kasancewar ranan zai zama haduwata ta farko da saurayin da nake son aure wato Khamis, ban taba jin muryar shi ba, bansan yaya yake magana ba bansan shi wani irin so yake min ba amman ni ya riga ya shige birnin zuciyata,

8:00pm dot, Khamis ya shigo gidan mu tare da jagorancin ɗaya daga cikin yayu na, shima aka yi mishi masauƙi a parlorn baba ko 10 minutes baiyi da zuwa ba na tasa qeyar Nasreen da tray mai dauke da snacks da muka siyo da drinks a kai muka shiga parlorn kaina a qasa,

Zaune yake ya hakince a kan kujera ƙafar shi ɗaya kan ɗaya yana faman latsa wayan shi kaman shine mai gidan gaba ɗaya, ajiye wayar yayi tare da amsa sallamar mu zuciya ta saida ta kusan narkewa da Muryar shi ya doki dodon kunne na it's husky but it's sweet,
Suka gaisa da Nasreen sai zolayar ta yake yi yana jan ta da hira itama dake uwar surutu ne haka ta nemi mazauni a ƙasa ta zauna daram suna zuba zance saida suka kwashe kusan rabin hour kafin da ƙyar ta tashi ta tafi daga nan kuma complete attention dinshi ya dawo gareni daman half na wuri na ne half na kan Nasreen,

Tagumi Khamis yayi ya qura min ido yana qare min kallo ba tare da yace komai ba, jin baiyi magana ba yasa na dago a sace zan kalli ko komawa yayi ya cigaba da danna waya amman caraf sai idanu na a cikin nashi, yayi min kwarjini sosai da bazan iya masa kallon ƙurilla ba,

STORY CONTINUES BELOW

Nanma wani shirun ne ya sake ratsa tsakanin mu ya maida ni kaman TV yana ta aikin kallo na, dakewa nayi na dago na kalle shi cikin ido cikin murya mai sanyi nace
"Mai kake kallo? Ko wani abu ya bata min fuska ne?"

Girgiza kai yayi still yana tagumi yace "No! Kawai ina son na tabbatar gaske ne abunda nake gani ba irin mafarkin da na saba yi ba"

Ƙaramin murmushi na saki na maida kaina ƙasa cike da jin kunya na gaida shi,

"Idan na amsa gaisuwan mafarki na kaman na ƙasƙanta ta ne, ni ya kamata na gaida ta saboda bata matsayi da martabar da ya dace da ita" ya dan zame kadan daga kujeran yace
"Ina wuni my beautiful"

Rufe fuska ta nayi da bakin gyale na ina dariya Khamis is something else, marairaice fuska yayi yace dan Allah ki amsa ki taimake ni mafarki na ta karbi tsananin girmamawa da mutuntawa na nake mata"

Barin dariyan nayi na dake amman still ina murmushi na amsa da "lafiya"

Komawa mazaunin shi yayi ya zauna da kyau yana fadin "alhamdulillah yanzu kam na tabbatar gaskiya ne abin da nake mafarki tana tare da ni a zahiri"

Sauqowa nayi na zuba mishi juice a tumbler sannan na miqa mishi na koma na zauna, ɗan sipping yayi in a stylish way idanun shi ƙyam a kaina sannan ya lumshe idanun shi ya bude su a kaina,
"Tabarakallah masha Allah,
Allah kenan mai iko akan komai mai tsara abubuwa su tafi yanda yaso lallai ya dace wannan halitta ta rusuna ta gode ma Ubangijin ta da yayi mata halitta mai tsananin kyau da burgewa kuma yayi mata babbar kyautan addinin Musulunci kuma ya sanya ta cikin shiryayyu, tabbas ni mai sa'a ne"

Sake washe haqwara nayi tare da jawo bakin gyale na iba rufe fuska ta dashi, wannan bawan Allan son zautar dani yake yi, bayan na riga na daɗe da macewa a kanshi yanzu yana ƙara min illah da kalaman shi, sake tsinkayo muryar shi nayi a sama yana fadin

"Yusrah wallahi ke kyakkyawa ce, murmushin ki yafi mun wata haske, da ace za'a dushashe hasken wata a barni dake kin isa ki haska min darare na har qarshen rayuwata"

So kenan! Makahon abu, da gaske ni ba wata kyakkyawa bace, ba daga dogon hanci ko manyan ido, babu kala mai haske sosai babu cute and pink lips babu irin natural shaved eyebrows kaman yanda ake tsara sauran matan novels🤭 ina dai da kayana dai_dai gwargwado, amman yanda khamis ke gwaɗa ni yasa na fara jin kaina kaman queen of beauty duk sauran mata a ƙarƙashi na suke,

Yusrah idan Allah ya mallaka min ke ba zan bar kowa ya raɓe ki ba, hasken ki da kyan ki dakomai naki mallaki na ne ni kadai i will cherish you till forever duk wasu buƙatun ki na duniya zan biya miki su idan Allah ya yarda, I love you so much,

Kalaman khamis sunyi tasiri sosai a kaina, tun daga lokacin ya samu ya shige jiki na daga qarshe ajiye kunya nayi na dinga zuba mishi surutu kaman Nasreen,

Haka ya zauna ya dinga sauraron shirme na da shiriri ta idan na tiqe ma shike tayar dani I can't imagine someone matured and sensible like khamis will sit and listen to my stupid stories,
Tun daga wannan son shi ya dasu cikin zuciyata ya girma ya fitar da rassa har yanzu kuma na kasa tumbuƙe shi daga ciki,

Sauƙe numfashi nayi na mayar da kayan cikin shopping bag din na bude drawer na saka a ciki, har nayi switching lights off waya na ya fara ringing hakan yasa na kunna wutan na qarasa wurin da na ajiye wayan ina dubawa, da private number ake kira na sake duba time naga 11 har ya wuce

Katsewa kiran yayi a take wani ya sake shigowa banyi wani tunani ba nayi saurin picking na ƙara a kunne na ina jiran naji waye ya kira kuma menene dalilin kiran, shiru akayi ba'ayi magana ba hakan yasa nayi sallama still shiru,

Sake sallama nayi ba'a amsa ba hakan yasa raina ya baci na kashe kiran dan nasan ba network bane tunda inajin numfashin mutum, Kashe wayan nayi gaba daya na kashe wutan dakin na kwanta,

**********
Bayan wani lokaci iyaye na da iyayen Safwan suka hadu aka gama magana an bada sadaki an saka rana 5 months lokacin jannat tayi qwari sosai,

A kwana a tashi asarar mai rai yau aure na da yaya safwan sauran wata guda,

Fitowar mu kenan daga wani store mun shiga zaban dining table bayan mun dawo daga gidan Aisha, na gaji sosai dan babu qarya yau munyi zirga_zirga sosai, Aisha yau ta wahala ni sosai saboda cikin ta ya tsufa shiyasa duk ayyukan gidan ta yau ta jibga min ta miqe ta sha barcin ta shiyasa ko jiran ya safwan ya gama settling bills banyi ba na bar jannat a wurin shi na karbo key din mota zan shiga na zauna a ciki,

Tsaye yake a jikin motan ya nade hannun shi a qirjin shi yana qare min kallo fuskar shi dauke da murmushi,
"Baby, kinyi missing dina ko??" Ya fada yana takowa wurin da nake tsaye...........🤦🏻‍♀️4

_The page doesn't even deserve a marathon ranking🤣 baiyi tsayi ba, amman zanyi real marathon insha Allah😅_

Sorry for the late night post🙈

Don't forget to follow
Vote
Share
And comment as you read😍

*Ummu Najma ce😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

21🧛🏽‍♂️
I was Shocked!!! Stunned!! Khamis ne tsaye a gaba na, ta yaya akayi ya fito daga psychiatry?? Wani kyarma jiki na ya fara yana tsuma purse dina da key din motar ya Safwan dake hannu na duka suka zube,
Ɗan qaramin murmushi yayi ya ɗaga hijab dina yasa hannun shi yana shafa ciki na, "baby ina ciki na? Kin aife shi ko? Yanzu na samu qaramin baby kenan, yana ina? Ko mace ce?+

Duk maganar da yake yi ban samu daman amsa shi ba ko sau daya, jiki na banda ɓari babu abinda yake yi, ɓata rai yayi ya matsa fatan ciki na da qarfi har saida na saki ƙara yana "ba zaki min magana bane?"

A maimakon na bashi amsa kawai na fara convulsion kaman wata mai farfadiya, na fita a cikin hayyaci na gaba daya ina ƙame ina shaking, dariya yayi mai sauti wanda ban ma san yana yi ba yayi min peck a lips yana fadin
"That's my lovely wife, yanzu na tabbatar da kin tuna da ni, so I'm back kuma ɗaukan ki zanyi da baby na mu tafi can nesa mu ci gaba da rayuwa like we used to be before, all...alone"

Sai ya sake bushewa da dariya, just then ya Safwan ya fito daga store din dauke da Jannat a hannun shi idanun shi suka sauƙa a kan khamis, shima saida abin ya firgita shi gani na tare da khamis ina tsaye sai shaking nakeyi kaman wanda aka saka wa shocking, daga murya yayi yana kiran sunana jin haka yasa Khamis daga ido ya kalle shi, ya maido da duban shi wuri na sannan ya nuna shi da yatsa yace "wannan kuma fa?"

Bani da damar da zan iya magana na gama hada zufa ina kallon shi, ya cukumo ni ya manna ni da ƙirjin shi tare da zare min idanuwa cikin ƙaraji yace "me ya hada ki da wancan mutumin Yusrah?? Da auren nawa a kanki wani gardi ya samu daman kiran sunan ki?"

Cikin sassarfa ya safwan ya qaraso gudun kada Khamis ya cutar dani, da ɗaya hannun shi ya bugi kafadan Khamis ya bude baki kenan zaiyi magana Khamis ya kai masa psychiatric punch😅 saida ya kusan zubewa a ƙasa take hancin sa ya balle da jini, Khamis ya sake taƙarƙarewa ze kai mishi lunatic punch a take hankali na ya dawo jiki na nayi saurin qarasa wurin su da ƙarfi nace
"Khamis ka bari dan Allah kada ka cutar da ƴarka"

Tsayawa yayi hannun shi na reto a iska shi bai kai naushi ba kuma bai sauqe ba yana kallo na cike da mamaki har na qarasa na karbi Jannat a hannun Safwan sai zunduma ihu take taga tashin hankalin da tun da na aifota duniya bata taba ganin irin shi ba,

Har wasu hawaye ne suka kwanta a cikin idon shi jijiyoyin jikinshi sun tashi rada_rada, da muryan bacin rai da takaici yace
"Yusrah yanzu har wani ya samu damar dora hannun shi a kan ƴata da sunan kina tare da shi? Ya maye gurbi na fa kenan!!"

"B...ba...ba hak..ka bane fa..kh.."

"To idan ba haka bane menene??" Ya fada cikin tsawan da ya kaɗa hanjin ciki na, harta kukan Jannat saida ya tsaya cakk, ganin kaman fada akeyi a wurin da muke tsaye yasa securities din dake gadin store din suka nufo mu amman kafin su ƙaraso ya Safwan yayi yunƙurin maida ma Khamis raddi amman kashh!! Ya tafka babban kuskure,
STORY CONTINUES BELOW

duka ɗaya Khamis yayi masa ya zube a wurin sumamme ko ƙara shurawa baiyi ba, ya dago yace min
"Ke kuma ina jiran ki gobe kizo tare da ƴata mu tafi sabon gidan mu, idan kuma kikayi taurin kai nasan yanda zanyi ki dawo gare ni dole remember that i can never ever live without you"

Ya juya da gudun tsiya ya shiga wata baqar Honda Accord wanda nidai a iya sani na bansan shi da ita ba ya zuga a guje, securityn kuma sunji tsoron yin harbi ne saboda yarinyar da take hannu na kada ta razana wanda 6 months kawai gareta,

Ganin Khamis ya riga ya tsere sai hankalin mu gaba daya ya koma kan Safwan, suka bude bayan motar shi suka saka shi nima na shiga sannan daya daga cikin su yaja motar sai asibiti,

6:30pm

"Yusrah kin zauna sai kuka kikeyi ki bude baki ki fada mana abinda ya same shi, waye yayi mishi wannan abun?" Cewar A'isha,

Daga jajayen ido na nayi wanda suka rine saboda kuka na kalli maman Aisha na kalli maman ya Safwan da baban su ga nawa iyayen, Nasreen harda sauran ƴan uwan shi kowa ya zuba min ido suna jiran suji daga gareni,

Sake fashewa da wani kukan nayi ina kare fuska ta da tafin hannu na, I don't want to say this amman ya zamo min dole na fada, baki na tana rawa nace
"Kh.. Khamis..ne, shine ya dake...shi"

"Khamis kuma?"

Mama ta tambaya cike da mamaki, sauran kanma kasa magana sukayi, "mama wallahi Khamis ya gudo daga asibitin mahaukata and he is chasing after me"
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" shine kalmar da kowa yake maimatawa cike da jimami,

Zama Aisha tayi a gefe na tare da ɗaura hannun ta saman kafada na tace "ki daina kuka besty wannan ba abin daga hankali bane kada kema ki jawo ma kanki rashin lafiya mu ɓata biyu ɗaya bai gyaru ba, zamu san yanda za'ayi a maidashi psychiatry sai ya kammala jinya a sake shi"

"Idan ya sake tserewa kuma fa? Baku san waye Khamis bane ni da na zauna tare dashi nafi kowa sanin halin shi, he is very dangerous! Ya cutar da yayan ki a karo na farko ba zan bari ya sake cutar dashi ba so kafin muyi abinda zamu zo muna nadama daga baya Please LETS CALL OFF THIS WEDDING, ni na haqura da qara auren bani son daukan hakkin ya Safwan a kaina"

"What? Kina da hankali kuwa? Sai bayan abu ya gama kankama kowa yasan da maganar auren ku saboda wani banzan Khamis kice kin fasa aure? Shi Khamis din waye ne da kike nuna tsoron shi kaman wani mala'ika? Ya isa yayi miki abinda Allah bai miki bane?"

"A'isha Khamis yafi qarfin tunanin ki, maganar shi kaman zane yake a kan dutse bayi taba goguwa, and speaking of an Angel, shi Mala'ika umarnin ubangijin sa yake bi amman Khamis!! Ko zuciyar shi bata isa bashi umarni ba, da abu ɗaya yake amfani shine qwaqwalwar shi wanda sanin kanki ne bayi da cikakken lafiya, idan ba kuna so mu rasa ya Safwan bane dan Allah a fasa auren nan"

Na ƙarashe magana ina kallon sauran mutanen wurin, babu wanda ya iya sake cewa komai dan abun ya zarce tunanin su matuƙa, da ya Safwan ma ya farka ya nemi gani na amman firr naqi shiga dakin da aka kwantar dashi daga ƙarshe ma sulalewa nayi lokacin sun fita sallan magriba na koma gida,

Nasan banyi masa adalci ba amman bani so yaci gaba da saka rai a kaina don indai Khamis yana raye kuma yana yawo ko ina freely like any other person, gwanda ace banyi aure gaba daya ba da ace na auri ya Safwan don babu shakka zai kashe shi tunda laifin da be kai wannan ba ma ya ɗau matakin kisa,

Sai bayan Isha mama da Nasreen suka dawo gida suka sanar ma baba abinda ya faru harda request dina na a fasa aure da kuma hujjojin da na basu, basu yanke hukunci gaba ɗaya zasu yi ko zasu fasa ba amman yace sai an zauna da manyan ya Safwan za'a san yanda za'ayi a kama Khamis tunda yana neman zamo mana fitina,

Wayyo zuciyata, i was hurting deep inside bani son wani abu ya samu khamis kuma bani son wani abu ya sami Jannat ko ya Safwan a dalilin shi, nikam daman sha wuya ce na riga da na horu na saba da azaban Khamis kuma zan iya ci gaba da jurewa, amman ko kadan bazan jure ba idan wani nawa ya shiga cikin yaƙin mu,

Sake kunna screen din waya na nayi na duba lokaci, 12 har da mintuna 37 idanu na sun bushe inason nayi barci amman na kasa tunanin makoma ta kawai nakeyi now that Khamis is back into my life,

Waya na ne ya fara ringing ina dubawa naga private number, kusan sau biyar kenan ana kirana dashi idan na dauka sai ayi shiru ba'a cewa komai har na gaji na kashe amman kusan one month Kenan ba'a sake kirana dashi ba sai yau, picking nayi na saka a kunne na nina bance komai va ina jiran naji yauma za'a min shirun ne ko kuma,

"Baby" naji muryar Khamis ya doki kunne na a firgice na tashi na zauna jikina yana ɓari, kaman yana gani na yayi dariya hade da fadin "relax babe! I know baki san nike kiran ki tun kwanaki bane shiyasa kike kashe min waya, nasan kina sona da yawa ba zaki katse min kira ba, and you know what? I have a lot to tell you amman sai kindawo gareni tukunna tare da little baby na, tomorrow by noon a bye pass express road zan jira ki kina zuwa zamu wuce ba zasu sake ganin mu ba ballantana su takura mana kizo da wuri kinji?"

"Bazan dawo gareka ba Khamis, na riga na haramta maka" nayi qarfin halin fada cikin kasashshiyar murya mai cike da tsoro,
"Dan Allah menene kakeyi haka? Na dauka komai ya ƙare tsakanin mu amman kana maida hannun agogo baya, leave me alone please" na ƙarashe kaman zan fashe da kuka,

"Alhamdulillah! Naji dadi sosai da kika sanar dani da wuri baki bari na ɓata lokaci na ba, daman ba ra'ayin ki na kira naji ba ko kuma shawarar ki nake nema ba, zuwa gareni dole ne ya zama miki tilas ki zo amman ki hanzarta kafin na yi abinda hankali bazai ɗauka ba" kitt ya katse wayan

I was left dumbfounded kalaman shi na ƙarshe sun dasa min mummunan tsoro a zuciyata, nasan idan Khamis ya fada aikatawa tilas ne nidai Allah ya tsare ni daga sharrin shi kawai,

A ranar kam yanda naga rana haka naga dare damuwa goma da ashirin sun dabaibaye zuciya ta, haka na tashi da safe jiki na yayi lagwab da qyar ma na iya wanka ma Jannat amman na kasa komai duk abinda ya hau kan harce na jinshi nake kaman maɗaci,

11:04am
Ina kwance zazzaɓi mai zafi ya rufe ni, ko iya tashi bani yi Nasreen sarauniyar kuka na duniya tazo ta zauna a gefe na fuskar ta sharƙaf da hawaye cikin lallami tace
"Aunty Yusrah dan girman Allah ki tashi ko spoon biyar kici rabon ki da abinci fa tun jiya da rana kada yunwa tayi miki illa ki kamu da wani cutan bayan wanda kike fama dashi"

Ban kulata ba na juya na bata baya bani da aukunin ko kallon abinci ballantana cin shi a halin yanzu, bansan ta ina zan ɓullo ma iyaye na da zancen komawa gidan Khamis ba, nasan ba zasu yarda ba kuma gaba dayan mu zamu uya shiga cikin matsala saboda haka,

Muna cikin wannan yanayin mama ta shigo ta dubi Nasreen tace
"Auta har yanzu bata ci abincin bane?"

Gyada mata kai Nasreen tayi tace
"Wallahi mama ko magana ma taƙi yi gashi zafin jikin ta ya ƙaru"

Dawowa ta gaba na tayi ta saka hannun ta a jikin wuya na tana jin yanda jiki na tayi rau, cikin tausayawa irin na uwa tace "sannu hajiya ko tea ne zaki sha a kawo miki?"

Saboda bani son hayaniya sai kawai na gyada mata kai ta dauki 200 ta bawa Nasreen taje shagon bakin titi ta siyo madara da milo, ta dauki hijab dinta ta fita, saidai fa har 12 Nasreen bata dawo ba har qarfe 1 ya juya zuwa qarfe biyu shiru hankalin mu gaba daya ya tashi yayu na sunyi neman duniyar na shiru ba'a ganta ba har ƙarfe 4,

Zuwa lokacin har police sun shiga cikin zancen, ni da mama kuwa mun bazu a tsakar gida sai kuka mukeyi ana haka sai ga kiran khamis, nasan idan ban dauka ba matsala ne shiyasa kawai nayi picking amman a maimakon naji muryar shi sai naji na Nasreen..........🤦🏻‍♀️
Don't forget to follow
Vote
Share
And comment as you read💖
*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

22🧛🏽‍♂️
"Mama!! Mama! Dan Allah ku taimaka min, Aunty Yusrah ki taimake ni, ku taimaka min dan Allah kada ya kashe ni"

"Nasreen!! kina ina ne? Khamis me kayi ma ƙanwata? Dan Allah ina ka kai..."

Fauce wayan mama tayi daga hannu na ta saka a kunnen ta itama ta saurari ihun da Nasreen take yi amman kafin tayi wani magana Khamis ya amshe wayan daga wurin ta yana dariyan mugunta,+

"Baby hope kin gama shirin tahowa cos yanzu na canza plan zan amshe ki ne in exchange with Nasreen, na riga na gama shirin komai ke kawai nake jira please kada ki bata lokaci da yawa your sister doesn't like staying with me"

"Tsinanne! Allah ya tsine maka albarka Khamis, ka saka mu munqa baƙaƙen dare mun zubar da hawaye mara adadi a dalilin ka insha Allah ba zaka gama da duniya lafiya ba"

Tabe baki yayi shi wannan kalaman nata ko ɗaɗa shi da ƙasa baiyi ba indai zai samu Yusrah ta dawo gare shi ba tsinuwa ba ko menene a fada a kanshi su ya shafa,
"Umm mama wannan kiran ba naki bane balle ace mun tsaya gaisawa so Please idan ba zaki damu ba kidan miƙawa matata Yusrah wayan inaso zanyi magana da ita, Thank you"

"Ya Allah ya isar mana abinda kayi mana, ya sanya kaci karo da fit..." Da sauri Yusrah ta miƙe hade da fauce wayan
"mama me kike fada ne haka? Uban Jannat ne fa kike tsine mishi idan abin ya shafe mu fa"

Kuka ne yaci ƙarfin mama ta rasa me zata ce min sabida takaici, Khamis ya gama hada mata zafi ni kuma nazo ina kawo mata maganar banza, ji tayi kaman ta rufe mu da duka dani dashi,

"Khamis dan Allah ka rabu da Nasreen ba ita kake buƙata ba nice ina? to gani zuwa dan Allah ka saketa ta dawo gida"

"Thanks for understanding my love, sannan kada ki manta ki taho tare da baby Jannat idan kuka shigo hannu na sai na miqa ma su mama Nasreen na basu haƙuri, ina jira sai kunzo" qitt ya katse kiran,

A rude na shige bedroom din mama na dauki Jannat dake shaƙar baccin ta na goya ta a baya na, ban tsaya ɗiban wasu kaya masu yawa ba na saka hijab dina na zari hand bag dina juyowar da zanyi naga mama tsaye a baya na,

kallo na take yi cike da mamaki batayi tsammanin da nace ma Khamis gani zuwa zuwan zanyi da gaske ba,
"Yusrah babu inda zaki je, baki da hankali ne zaki dinga biye ma wannan mahaukacin? Yanzu zaki tafi wurin shi dan ki ƙwato Nasreen kina nufin mun fifita ta a kanki ne da zamu barki ki tafi don ta dawo?"

"Mama Khamis ba zai iya cutar dani ba amman muddin banyi abinda yace ba zai cutar da Nasreen"

"Cutarwa kuma na nawa? Akwai wani cutarwan da zaiyi miki da ya wuce wanda ya riga yayi miki shi a baya ne? Indai nice na haife ki to nace ba zaki tafi wurin mahaukacin nan ba kuma magana ta ya zauna"
Ruƙo hannun ta nayi duka biyu cikin nawa ina kuka na fara mata magiya,
"Dan girman Allah mama ki barni na tafi na ceto rayuwar ƙanwa ta nayi imani da cewa Khamis shine ƙaddara ta kuma zan rungume shi hannu bibbiyu, idan kuma na samu dama zansan yanda zanyi ya koma psychiaric amman yanzu kam kar ki tsayar dani please"

STORY CONTINUES BELOW

Na ja akwatin da sauri na fita daga dakin ba tare da na kula kiran da mama take min ba, har na kai tsakar gida tayi saurin riqo ni ta since goyon baya na tace

"Tunda baki jin magana kije, amman ba zan taba barinki ki tafi da yarinyar da bata san komai ba ta shiga uƙubar mutumin nan ba jika ta ƙwaya ɗaya tall"

Daidai nan baba da sauran yayu na suka shigo gidan tun kafin su ƙaraso mu mama ta zayyane musu abinda ya faru da kuma sharadin da Khamis ya kafa sai an cika kafin ya dawo da Nasreen,

Ya Usman ne ya fara hayagaga yana ƙudunduma ma Khamis ashariya dan ranshi ba ƙaramin baci yayi ba, amman baba na tsaye ya tsare ni a gaba da kallo ba tare da yace komai ba yana karantan yanayi na, umarni kawai yayu na suje jira daga wurin baba suje su nemo wurin da khamis yake su ƙaddamar mishi dan ya zamo mana bala'i amman yace su dakata tukunna,
ya ja hannu na zuwa parlorn shi suma suka rufa mishi baya muka shiga muka zauna sannan ya karbi waya na daga hannun mama ya miƙo min yace
"Gashi ki kira min Khamis din nayi magana dashi"

"Bani da numbern da yake amfani dashi yanzu sai ya boye yake kira na"

"Shikkenan sai mu jira nasan zuwa jimawa idan Allah ya yarda zai kira ki" ai kuwa bamu fi 5 minutes da zama ba sai ga kiran shi ya shigo baba yace na ɗauka na saka a speaker,

"Time is going baby me ya tsayar dake har 5 baki iso ba?"

"Ba babyn bace mahaifin ta ne mahaifin yarinyar da ka ɗauke ka ajiye a wurin ka"

Shiru Khamis yayi baice komai ba yana sauraron baba yaci gaba da cewa,

"Saboda me ko kuma ince a wani dalili ka ɗauke Nasreen bayan a iya sani na babu abinda tayi maka mu ma iyayen ta bamu rage ka da komai ba"

Saida yaja dogon numfashi ya sauƙe sannan yace "baba ni matata nake so ta dawo gare ni ba riƙe Nasreen shine buri na ba"

"Wata matar taka kake nufi? Indai Yusrah ne babu auren ka a kanta don dukan mu shaida ne an raba auren ku a kotu, to me yasa zata dawo gare ka bayan kai ba mijin ta bane a yanzu?"

Kaman zaiyi kuka yace "ai na mayar da auren, igiyoyi uku ne a tsakanin mu ba ɗaya ba, dan Allah ku taimaka min ku dawo min da matata nayi alƙawarin ko ƙuda ba zai taba Nasreen zan dawo da ita har gida lafiya ƙlau"

"Mu ƴan adam ne Khamis, bamu da ikon canza abinda Allah ya tsara ba idan Allah yayi da sauran zama a tsakanin ku bamu isa mu hana hakan faruwa ba saidai sanin kanka ne baka da cikakken lafiya kuma babu uban da zai dauki ƴarsa ya danƙa maka a cikin yanayin da kake, da ka zauna a asibiti anyi maka magani ka fito mun tabbatar ka samu lafiya da da hannu na zan danƙa maka Yusrah"

"Baba basu da niyyan min jinyan da zan warke kullum banda azaba da baƙar wahala babu abinda suke bani, sunce ba zan samu lafiya da wuri ba and i miss Yusrah badly ba zan iya zama na tsawon lokaci ba tare da ita ba dan Allah ku dawo min da ita ina sonta sosai wallahi"

"Mutum bayi cutar da abin da yake so Khamis, ka cutar da Yusrah ba sau daya ba ba sau biyu ba, da ace bamu gane halin da take ciki muka dauki mataki da wuri ba da ita da kake ikirarin kana son da abinda ke cikin ta duk basu raye a yanzu, da mun rasa su duka"

Bani kallon fiskar Khamis amman nasan kuka yake yi yanzu haka shiyasa yayi shiru na tsawon lokaci baiyi magana ba, zuciyar Khamis tana da rauni da kuma taushi sosai shiyasa abu kadan yake affecting dinshi, zuwa lokacin nima kukan yaci ƙarfi na, na cusa kaina a tsakanin cinyoyi na Allah ya gani yanzu haka ji nakeyi kaman na tashi na tafi wurin shi,
Ya dau lokaci mai tsawo kafin cikin ƙarfin hali yace "baba ban taba ganin ta ba fa, ban santa ba, tunda aka aife ta ba'a taba damuwa da a kawo min ita na gani ba, ba don na aminta Yusrah ba zata tsallake magana ta ba da nace ko sunan ta ma ban sani ba,
mahaifi na daman ba wani damuwa dani yayi ba, mahaifiya ta ma ta juya min baya, Yusrah ta juya min baya ta raba ni da gudan jini na yaya zanyi dan Allah ko a kaina aka fara rashin lafiya da ba za'ayi min uzuri ba? Su biyu ne mallaki na a duniyar nan shiyasa zanyi duk abinda zan iya dan ganin sun dawo gareni"

"Naji hujjojin ka Khamis kuma na yarda zan maido maka da Yusrah amman sai ka dawo min da Nasreen munzo mun zauna na kafa maka sharuda dan bazan yarda ka sake cutar da ƴata ba"

Murya a raunane Khamis yace "Baba idan nazo ina ba zaka saka su maida ni psychiatry ba?"
"Bazan saka su maida kai ba zamuyi magana ne na fahimta na baka matar ka da ƴar ka"

"To Shikkenan baba insha Allah zan dawo da ita, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi" da "ameen" baba ya amsa yana kashe wayan ya zurma ta a aljihun gaban rigan shi sannan ya ciro nashi ya danna kiran mahaifin ya safwan,

Muna zaune a wurin ya zayyane masa yanda sukayi da khamis tass sannan yace a kira asibiti a sanar musu su turo doctors din da zasu dauki Khamis a kaishi wani wurin can mai nisa yanda zai samu tsaro sosai ba zai iya guduwa ba, daga baya sai a yanke shawarar ko za'ayi aure na da ya Safwan idan kuma yace ya haƙura sai a fasa,

Hankali na ya tashi matuƙa da jin wannan maganar, sun ɗana ma Khamis tarko ne wanda ba zai iya tsallakewa ba kuma nasan yanda a yanzu ya safwan ya qwallafa rai a kaina da kuma jannat ba zai taba haƙura da aure na ba dole nayi wani abu a kai,

Ƙarfe 6 saura mutanen da baba ya saka a kira suka iso tare da mahaifin ya Safwan da shi kanshi ya Safwan ɗin dan duk yanda sukayi ya zauna a gida saboda raunin shi yaƙi wai shi a dole he care for my safety, saidai har wurin magriba babu Khamis babu alaman shi, koma menene ya hana shi zuwa da wuri hakan yayi mun yanzu zan san yanda zanyi na dakatar dashi kafin ya iso,

Ina goye da Jannat ina ta zagaye tsakar gidan sabida na samu tayi min barci na hango su sai ɗura ruwan allurorin da zasu yi ma Khamis sukeyi a cikin sirinji kaman wani doki, daga ƙarshe suka ga alamun ba zuwan yanzu zaiyi ba sai suka wuce masallaci domin yin Sallah amman sun bar likitan dan shi ba musulmi bane,

Ina ganin haka na sulale na fita daga gidan luckily babu wanda ya lura naje bakin titin layin mu ina jiran zuwan Khamis, ban dade da tsayuwa ba sai gashi yazo cikin motar da na ganshi jiya tare da Nasreen, nayi saurin haska idanun shi da Torchlight din mama wanda yake da haske kaman na kama barawo,

Yana ganewa yayi parking ya fito wurin da nake tsaye yana kallo na sama da ƙasa yanda na fito tajaran majaran ga goyo a baya na,

"Yusrah mai ya fito dake? Me kikeyi a nan wurin?"

"Khamis ka saki Nasreen kawai ta tafi gida amman kada kaje dan Allah"

"Ban gane ba, meyasa? Ba baba yace na maida mishi ita zai maido min da ke ba? Me yasa kuma zaki ce kada naje?"

"Wallahi yaudaran ka baba yakeyi ba zasu gyara auren mu ba, har yanzu suna da ƙudurin aura min ya Safwan kuma sun kira mutanen da zasu maida ka mental asylum, kana shiga gidan nan ba zaka fito da ƙafar ka ba, idan ƴarka ne gata nan a baya na ka ganta ka tafi daga baya zamu hadu mu san abinyi" na fada ina ƙoƙarin sunce Jannat daga baya na,

Dakatar dani yayi yace "kada ki fito da ita tasha sanyi mu shiga mota sai na ganta"

Ban kawo komai a raina ba ya bude front seat yace ma Nasreen ta fito ta bamu wuri zamuyi magana, tana fitowa na duru cikin mota na since Jannat harda aukin kunna haske saboda ya samu daman ganinta da kyau,

Rufe marfin motan yayi ya zaga ya shiga driver seat banyi aune ba naji Khamis ya kunna mota ya zare shi da ɗan iskan gudu.............🤦🏻‍♀️
Love You my fans💖
#team safwan🤕
#team Khamis😈

Naga ma kunyi creating wani team mai suna
*team Yusrah mai abin haushi*😂😂

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

23🧛🏽‍♂️
Nasreen na ganin tafiyar mu ta yi gida da gudu, da shigan ta taci karo da baba yana fitowa tare da ya safwan da ya usman biye dashi a baya zasu fita nimo ni dan sun duba ko ina a ciki kuma har lokacin Khamis bai ƙaraso ba,

Rungume baba tayi tare da sakin kuka a dame ya ɗago fuskar ta yana kallo cikin farin cikin ta dawo gare su lokaci ɗaya kuma damuwa ya lullube zuciyar shi yana taraddadin jin abinda ya saka ta kuka, ko Khamis yayi mata wani abun ne? Ya tambayi zuciyar shi,

"Me ya faru auta? Ina khamis din ko ba tare kuke ba"

Share hawayen idonta tayi tana jan hanci tace
"Tare muke amman ya riga ya tafi, aunty Yusrah ta bishi sun gudu"

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" shine kawai kalmar da yaya Safwan yake maimaitawa,

Ya usman yace "sun dade da tafiya ne auta? Ta ina suka bi?"

Ta bude baki zatayi magana baba ya dakatar da ita ranshi yayi mugun baci amman yana ƙoƙarin dannewa yace
"Ku barta tunda ta zabi abinda ranta yafi so, Allah ya tsare ƴar wannan yarinya da bata ji ba bata gani ba daga uƙubar mahaifin ta Yusrah kuma taje da halinta tunda ta gwada tafi ƙarfin mu bamu kai wanda zamu fadi magana taji ba, Safwanu sai kayi haƙuri Allah ya baka wata natar da tafi Yusrah komai da komai"
Yana gama fadan haka ya ratsa ta tsakanin su ya wuce cikin gidan ya bawa mutanen da aka dauko wanda zasu kama Khamis tare da doctor haƙuri ko minti 1 bai ƙara ba ya fita daga gidan gaba daya, har lokacin muna tsaye da ya Safwan a bakin ƙofa ba tare da munce ma juna komai ba ya sada kanshi ƙasa ni kuma ina tsaye ina ƙare masa kallo i can see disappointment all over his face, kaman an tsikare shi yace

"Yauwa auta dan Allah fada min gaskiya Yusrah da son ranta tabi khamis ko kuma tilasta mata yayi?"

"Ya safwan ka daina yaudaran kanka dan Allah, idan kana tunanin Yusrah abun yarda ce a kan abinda ya shafi Khamis to ka daina, zata iya tunanin ƙaramin ƙwaƙwalwa gare ni ba zan gane abinda suka shirya ba amman tayi kuskure"

"Amman yaya za'ayi ta so mutane biyu a lokaci daya? Bayan ta amince zata aure ni me yasa zata koma wa tsohon mijin ta? Ko son da take min baiyi ƙargon da zata zabe ni a kan wani bane?"

"Aunty Yusrah bata taba son ka ba ya Safwan, tana kula ka ne a sakamakon matsawar mu kuma ta amince zata aure ka ne saboda yin biyayya wa iyayen ta amman ko na second ɗaya Khamis bai taɓa fita daga zuciyar ta har taji zata musanya shi da wani ba, kayi haƙuri dan Allah da ƙarairayin da nayi ta maka na saka kayi tunanin aunty Yusrah tana son ka ,duk shiri na ne saboda bani son ganin ta a gidan da ba gidan auren ta ba, amman gidan auren ba na Khamis ba, sai gashi ita kuwa shi ta zaba ban goyi bayan ta ba amman zanyi ta mata fatan alkhairi a duk inda take, Allah ya tsare ta ya kare ta daga dukkan sharri"

Da ƙyar Safwan ya iya lalubo kalmar "ameen" ya fada yana kallon bayan Nasreen yayin da take shirin shiga dakin su, Yusrah tayi breaking heart dinshi ba zai taba manta da abinda nayi mishi ba, ko tsayawa yin sallan isha da ake kira baiyi ba ya fada motan shi yayi gaba zuciyar shi a dagule,

STORY CONTINUES BELOW

**********
"Khamis meye haka? Ina kuma zaka kaini"

Na fada hankali na a tashe tare da ƙara rungume Jannat a ƙirji na saboda gudun da yake yi ya fita hankali,
bai kula ni ba ya yanki kwana ya sake zura a guje saida na shide ganin titin duhu dulum amman a kanta Khamis yake wannan  gudun gashi babu gidaje sai daidaiku dake wurin ta bayan gari ne,

Bamu tsaya nan ba ya sake yankan wani titi a 360 degrees yanzu kam rufe idanu na kawai nayi ina salati a baki na da zuciya ta Jannat kuwa sai tsilli tsilli take da idanuwa, saida mukayi tafiya na kusan 45 minutes duk a cikin garin Yola kafin muka sauka wani hanyar da babu kwalta sai lokacin Khamis ya daina mahaukacin gudun da yake yi,

A hankali na bude idanuwa na jin yanda yake sauqe ajiyan zuciya na sauqe su a kanshi lokaci daya yana sake min murmushi, yana driving ne amman hankalin shi yana kaina saboda yasan wurin babu kowa ballantana yaci karo da wani abun hawa,

"Kai baby gaskiya ke matsoraciya ce, little baby na ma bata ji tsoro ba sai ke? Idan kina tare da ni na fada miki ki daina jin tsoron komai a ko wani lokaci zan zamo miki kariya"

Dan ɓata rai nayi nace "baka bani amsata ba, ina zaka kaini? Kuma menene dalilin guduwa dani daga gidan mu? Yanzu nasan su baba suna ta nima na"

"Oh come on, a kan mene zasu nime ki bayan sun san cewa tare da mijin ki kike? Kuma ai baba shi yayi min alƙawarin zai bani ke, a bisa sharadin ba zan sake saka ki kuka ba kuma nayi alƙawari ma zuciyata ba zan sake barin ki kiyi kuka ba, shiyasa kawai na sauƙaƙa ma baba aiki na tafi dake ba tare da na sashi dogon surutu ba"

Dai_dai nan muka iso bakin gate din wani gida, yana da ɗan girma amman ta waje babu fenti, da kanshi ya fita ya bude gate sannan ya shiga da motan cikin gidan, umarta na yayi da na dauki Jannat mu shiga ciki zai rufe gate din ya shigo,
Murda handle din ƙofar na shiga, parlorn tsaf_tsaf yake da duk wasu abun buƙata na yau da kullum na rayuwar ɗan Adam ko ina a share a goge daga gani akwai mutane dake rayuwa a ciki yanzu ko kuma basu fi awanni da fita daga gidan ba dan baiyi kama da ajiyayyen wuri ba,

Zama nayi saman kujera tare da cire hijab din jiki na still ina bin parlorn da kallo, na bude zip din riga na da nufin bawa Jannat nono dan naji ta fara ƙananun mita, ina cikin feeding din Jannat Khamis ya shigo hannun shi dauke da manyan shopping bags niƙi_niƙi ya ajiye a saman Centre table dake gaba na,

Daga ido nayi na kalle shi cikin al'ajabi nace
"Khamis a ina ka samo kudi ne? Gidan nan na waye? Sannan sabuwar motan da kake hawa shima na waye?"

Zuba yayi a kujeran gefe na tare da furta "wash", ya lumshe idanun shi tare da bude su a hankali cikin gajiya,
"Baby irin wa'innan jerin tambayoyin da wanne kike so na fara amsawa? Ko ni namiji na gaji ballantana ku amman idan neman bayani kikeyi ki kwantar da hankalin ki kamar kin samu, yanzu ki gama bawa little baby na abincin ta ki ɗibo plates ga abinci a nan ki saka mana muci mu ƙoshi sai kisha labari" ya ƙarasa fada yana gwada laidan kan table,

Ban sake cewa komai ba naci gaba da feeding din Jannat ina mamakin yanda Khamis ya gama shiri kaman yasan abinda zai faru ya riga ya gama tanada komai,

Kaman yanda ya fada ina gamawa da Jannat na zaunar da ita ai kuwa yayi wuff ya dauke ta yana ƙare mata kallo, daman ya gama ƙaguwa ya jita a hannun shi kawai dai bayi son katse mata ƙoshi ne yasa ya danne zuciyar ta ya haƙura ta gama,

Daga ta sama yayi yana ƙare mata kallo she looks partially like him, ƙyalkyalewa tayi da dariya tana wuntsila ƙafafuwar ta that gave him so much joy shima bai san lokacin da ya dara ba, saboda tsananin jin daɗi har wasu ƙwalla ne suka taru a idanun shi,

Juyowa yayi ya kalle ni na zuba musu idanu ina kallon su cike da sha'awa da birgewa yace
"Yusrah yanzu wannan yarinyar tawa ce?"

"Taka ce halas malas"

STORY CONTINUES BELOW

"Allahu akbar, ashe nima ina da rabon riƙe tawa jinin a hannu na, Yusrah ba a ko wani lokaci bane ya kamata kabi dokokin society idan ba haka ba zasu raba ka da jin daɗin ka na duniya gaba ɗaya su ko a jikin su, i never know this is how someone feels when he is called a father, it's indeed a blessing"

Girgiza kai kawai nayi ina dariya ganin kaman Khamis ya zauce, yana ta zuba zance idanuwan shi a kan Jannat ko ƙyaftawa bayi yi, na shige kitchen, na fito da plates biyu da goran ruwa masu sanyi da na same su cikin fridge,

bude takeaways din nayi naga tuwo ne da miyan egusi, na juye ɗaya a plate ɗaya na jawo ɗayan plate din zan juye ɗayan yayi saurin kawar dashi yana harara na
"Yaushe muka fara raba ƙwarya da zaki zuba abincin ki daban"

Hararan wasa na maida mishi nace "Alhaji na har yanzu fa bamu san makomar auren mu ba tukunna, so we have to maintain our distance har zuwa lokacin da zamu samu tabbacin halalcin shi,"

Sauƙe Jannat yayi daga kafadar shi duk ta jiƙa rigan jikin shi da yawu ya zaunar da ita a kan cinyar shi ranshi a bace, baice komai ba ya jawo hannu na ya zaunar dani a gefen shi jikin mu yana gogan juna sannan ya miƙa min cokali ya saka nashi yana ci a nutse, ganin canzawar yanayi shi lokaci ɗaya yasa nasha jinin jiki na har muka gama cin abincin ko tari ban sake yi ba,

Da yazo fita Masallaci ya faɗa min cikin bags din da ya shigo dashi akwai kayan sakawan mu na sauya kayan jiki na nayi wanka ma Jannat gashi nan zuwa, yana fita na duba laidojin kaya ne masu tarin yawa, ban bata lokaci ba na haɗa ma Jannat ruwan wanka nayi mata kafin mu gama ma ta fara barci so ina shirya ta na kwantar da ita nima na shiga wanka,

Saida na gama shiryawa tsaff na tattara kayan farlon na zuba su a wurin da ya dace kafin na nemi wuri na zauna ina jiran Khamis, sai lokacin kuma mama ta fado min a rai, nasan ko baba bai nuna damuwar rashin sanin wurin da nake ba ita zata nuna, ga Nasreen ma bata iya saka damuwa a ranta ba idan Khamis ya shigo zan karbi wayan shi na kira su na kwantar musu da hankali,

Na tsunduma cikin duniyar tunani ya shigo har ya zauna ban sani ba saida ya taba ni sannan nayi saurin matsawa gefe ina kallon shi, shima kallo na yake yi yace
"Lafiya baby? Mai ya razana ki?"

"Babu komai bansan ka shigo bane sannu da dawowa"

Miƙewa tsaye yayi ya riƙo hannu na da nufin miƙar dani yana fadin "muje mu kwanta nasan kin gaji da yawa"

"Tukunna dai, baka amsa min tambayoyin da nayi maka dazu ba, wannan gidan da motan da kake hawa da kuɗaɗen da kake bushasha dasu na waye ne?"

Komawa yayi zauna yace "gida na aboki na ne, sunyi tafiya ne shi da matar shi zuwa ƙauye shine nace ya bani aro na zauna a ciki na kwanaki biyu, mota da kudi kuma nawa ne amman bazan boye miki ba bata hanyar halaliya na same su ba, bayan na gudo daga psychiatry na shiga kasuwancin safaran miyagun kwayoyi wanda a hakan na samu na tara kuɗaɗe masu tsananin yawa cikin ƙanƙanin lokaci amman wannan ba shi bane abun damuwan, nayi alƙawarin zan saka ki farin ciki kuma ko ta wani hanya zanbi na saka ki koda zan ɓata lahira na"

Mummunan bugawa ƙirji na yake yi tunda khamis ya fara magana, na zama speechless gaba daya lallai yau na tabbatar haukan shi gaskiya ne, dan mai hankali ba zai taba fadan irin haka ba, bai damu da yanayi na ba yaci gaba da cewa

"Daman kuma kin tambaye ni mai muka zo yi a nan ko? To akwai wasu mutane da nake son gyara musu zama, yanzu bani kisa don't worry ba zan kashe kowa ba amman na rantse da Allah sai na kwantar a asibiti, da munafikin alƙalin da ya raba aure na dake da kuma likitan da ya azabtar dani ya rikirkita ni lokacin da nake mental asylum, kada ma kice zaki bani haƙuri dan nayi rantsuwa kuma wallahi ba zan fasa ba"

Kallon shi kawai nake cike da jimami har yanzu na kasa furta komai, anya Khamis ya canza kuwa? Anya ba zamu koma gidan jiya ba?"

**********
Yauma irin mafarkin da nakeyi kwanaki shi nake gani, amman yau ban farka ba har saida wasu mutane guda biyu suka ɓanɓare ni daga jikin gawan khamis suka jani tare dashi zuwa gaban wani tafkeken kogi suka jefa shi a ciki nima suka tura ni tare dashi,
ban san me yayi musu ba, ban san su suwaye bane bansan dalilin da yasa suka kashe shi ba, wani ƙara mai ƙarfi ne yasa na farka a firgice, ƙofar dakin da muke aka aka balla sai wasu gardawa guda biyu na gani a kanmu, kafin nayi wani yunƙuri Khamis ya diro ta gaba na ya lullube ni da bedsheet din gadon tun daga kan fuska ta har ƙafa na, ya zamo bani ganin komai sai sautin su kawai nake ji,

"Malam mai ya shigo da kai har cikin ɗakin matar aure? Ko sata dakayi ai sai ka tsaya daga parlor ƙaramin ɗan iska"

Wani dariyan shaƙiyyan ƴan duniya ɗayan yayi yace "idan ka ɗauki cinnaka ƙaramin ɗan iska har ka far mishi to ni kunama ne, ɗan uwan shi na jini kuma ubanshi a ta'addanci, ita matar taka ka tambaye ta tafi kowa sanin waye cinnaka shaƙiyyin da ya addabi mutanen adamawa gaba ɗaya yaro na ne"

Shima Khamis cikin nashi taurin kan na mahaukata yace
"Daman tashi na kayi da tsakar daren nan kawai dan ka bani labarin kanka? Gaskiya ka cutar dani kuma ba zan yafe maka ba, da ace babu sutura a jikin matata fa? Da ace kaga jikin ta da wani rayuwan zaka nemi yafiya ta?"

"Kaine ya kamata na tambaye ka da rayuwan da zaka nemi yafiya ta na kashe ƙani na cinnaka mai shago da kayi, domin yanzu yanzun nan zaka bar duniya"

Ban sake jin komai ba sai ƙaran harbin bindiga har Jannat saida ta razana babu shiri na yaye bedsheet din don ganin abinda yake faruwa sai ganin Khamis nayi kwance a ƙasa warwas.............🤦🏻‍♀️

*I know some of you might say*
_Wannan ta matsa mana da maganar following dinnan, bayan yawancin ku kuna karatu a wattpad kuna voting harda comments ma wasu sunayi_

*Amman yanzu saboda yanayin abubuwa lokacin da nake posting ya canza ba kamar da da nake yi 9:00pm ba nakan yi very early kuma nakan yi shi late, wanda ba ni nake musu sharing da kaina ba ma sai ya kwana ya huce suke samu, so wasun ku suna cewa basu sani idan nayi posting a wattpad amman duk lokacin da nayi nakanyi qoqarin announcement duk wanda take following dina zata gani, kuma ina saka link a kai wanda ba sai kin shiga reading list dinki ko kuma kin hau profile dina kin duba ba, directly link din zai kaiki page din da na sake*

_so keep *following* shima yana ƙara min ƙarfin guiwa💖_
_*voting* yana saka na gane cewa kunji dadin page din_
_*sharing* domin wasu su samu_
_*commenting* oga kwata_kwata kenan😂😂_

Ummu najma ce👻

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

24🧛🏽‍♂️
Ihu mai tsananin ƙara na ƙwalla cikin firgici da tsananin tashin hankali na diro daga kan gadon na ƙarasa jikin gawar khamis ina jijjiga shi da iya ƙarfi na kaman yanda ko wani lokaci nake ganin inayi a cikin mafarki ina kiran sunan shi da ƙarfi ko zan samu ya farka,

Mutumin da ya kira kanshi da kunama ne ya ƙaraso wurin da nake durƙushe ya tsunguna tare da saita min bindigan da ya kashe khamis dashi a ƙirji na, ya saka yatsan shi daya a saman lebben shi yana furta "shhhh" alaman nayi shiru na daina ihun da nake yi,

barin ihun nayi na dawo sai kuka, inayi Jannat tana yi ina kallon kunama da jajaen idanu na zuciya ta fall da tsoro,
Dariyan mugunta yayi mai sauti yana gwada ni ma abokin ta'addancin shi da suka shigo tare shima yana taya shi darawa, ɗan tsagaitawa yayi ya tambaye ni da
"Yusrah sunan ki ko?"+

Shiru nayi ban amsa ba naci gaba da kuka na ina kallon jinin dake kwaranya daga jikin Khamis, da ya daka min wata uwar tsawa ban san lokacin da na gyada mishi kai ba shiri ba,

"Hakan yayi kyau, nasan kina son sanin cikakken bayani akan dalilin da yasa na kashe mijin ki da kuma asalin wanda ya kashe wato ɗan uwa na cinnaka ko?"

Shina gyada kai nayi ba tare da na san nayi hakan ba, yace
"Yayi!!! To shi dai cinnaka ƙani na ne uwa ɗaya uba ɗaya kuma magajin gadon mulki na na daba, kullum buri na bai wuce idan na fadi cinnaka ya hau ya zauna ba ya amshi sunan kunama kuma hakan ne yake faruwa yana iya bakin ƙoƙarin shi wajen ganin sunan shi ya zaga ko ina ya zama abin tsoro,

Saidai kuma daga baya ban san abinda ya faru ba, wani malami yayi wa cinnaka wa'azi kuma ya dauka ya tuba ya canza halayen shi da sunan shi, abokan mu'amalan shi, harma da dabi'un shi, kwata_kwata banji daɗin hakan ba amman babu yanda na iya dole na rungumi cinnaka a duk inda yazo min domin shi kadai ya rage min jini na a duniyar nan, iyayen mu an kashe musu tun kafin su an mu yayi ƙauri lokacin muna saran ka kashe a kashe maka, daga baya ma suka kashe ƙanwar mu mace ɗaya tilo,

Saidai rayuwa bata zo ma cinnaka da sauƙi ba bayan tuban shi a garin adamawa, yana fiskantar tsangwama da kyara ko hada sahu dashi ba'a yi a masallaci duk inda ya ratsa ko kuma ya zauna haka zaki ga mutane suna darewa basu son zama kusa dashi shiyasa ya yanke shawaran canza wurin zama can nesa da garin Yola yanda zai shimfida sabuwar rayuwa,
Ni da kaina na zaba ma cinnaka garin da zai je Kebbi kenan nasa aka kama mishi sana'a aka bashi jari yana ta fafutukar canzawa zuwa cikakken kamilin mutum harda tara gemu da ƙasumba amman rana tsaka, wannan daƙiƙin mijin ki mahaukaci yaje har gidan da yake zama ya farr mishi, haka aka kawo min cinnaka yana ƙaƙarin mutuwa cikin jini kaman yanda mijin ki yake kwance a yanzu,

A hannu na ina kallo cinnaka ya mutu ko damar maganar ƙarshe ban samu yi dashi ba, bai fada min wanda yayi masa wannan aika aikan ba amman na saka yara na su bincika min kuma idan kere na yawo zabo na yawo wata rana dole su hadu, na san dole zan hadu da makashin cinnaka kuma na ɗau mishi fansa,

STORY CONTINUES BELOW

Lokacin da na san wanda yayi mishi wannan aikin nazo farautan rayuwar Khamis amman taimakon da Allah yayi mishi an tsare shi a asibitin mahaukata da na ɗaɗe da maida shi ya zamo labari ba tare da kowa ya sani ba saidai a neme shi a rasa, amman daga baya kuma sai na yanke shawarar ɗanɗana ma iyalin shi abinda naji lokacin da ya kashe cinnaka, shiyasa na bari sai randa kuke tare dan zo na dauki ranshi, Yanzu gashi kin shaida ko babu komai nasan kinji kwatankwacin zafin da naji a raina a wancan lokacin kuma wancan jaririyan zata koma marainiya kinga buƙata ya biya"

Na gama ƙosawa da labarin kunama amman ina sauraren shi zuciya ta yana suya, Khamis is the cause of his own death, saboda irin baƙin kishin shi na hauka, Khamis ya cutar da kanshi ya cuce ni, baisan rashin shi ɗaya da rashin rayuwa ta yake ba?

Ban ƙarasa tunanin takaicin da nake yi ba naji kunama yana kwala kiran wani yaron shi Mintsili, ya shigo suka tattari Khamis ɗaya ya kama hannu ɗaya ya kama ƙafa shi kuma ja ni muka fita daga gidan gaba ɗaya ba tare da ya damu da yanayin da jannat zata kasance a ciki ita kadai ba,

Sunzo da mota amman basu saka mu cikin motan ba saboda wurin da suka da niyyar kaimu bayi da nisa, haka ya dinga jana da ƙarfi gashi pjamas ne a jiki na khamis kuwa daukan mushen kare sukayi mishi muna tafiya cikin duhun dare, munyi tafiyan kusan 30 minutes kafin muka iso gaɓar ruwan da ya tafi ya hadu da River benue suka jefa gawar khamis ciki, nayi tunanin nima zasu jefa ni ciki ne kaman yanda na gani a mafarki amman basuyi hakan ba suka juya suka tafi suka barni a wurin,

Inama ace nima jefa ni ciki sukayi da nayi farin ciki ko babu komai bani raye balle nayi ƙunci da takaicin rashin khamis, ni musulma ce kuma nayi imani da duk wanda ya kashe kansa ya mutu kafiri ba don haka ba i would have committed suicide, ina zaune ni kadai a wurin ruwan dake zuwa yana dawowa yana jiƙa ni, banma san menene zanyi ba kallon ruwan kawai nake ko gawan khamis bani iya ganin saboda ƙarfin gudun sa kuma babu hasken wata,

Just a while ago nake tare da khamis, muna cikin farin ciki da annashuwa tare da gudan jinin mu a tsakiya amman yanzu da ƙarfi an raba ni dashi, ina daɓashe a wurin har aka kira assalatu na farko aka bi aka kira sallan asuba ko motsawa banyi ba, har saida gari ya fara haske kafin masu kamun kifi suka fara zuwa dan gudanar da sana'ar su,

Da farko da suka hango ni sunyi zaton ba mutun bace duk suka tsorata suka kasa ƙarasiwa saida aka kira sarkin ruwa shine kadai mai jarumtar ƙarasowa inda nake, yana zuwa yayi min magana a maimakon na amsa shi sai na saka kuka, shi yaje ya nimo abinda na sakaye jiki na dashi suka dinga lallashi na har na fada musu abinda ya faru,

Babu ɓata lokaci yasa yaran shi suka bazana cikin ruwa nimo gawan khamis kafin su dawo ni kuma ya bani aron wayan shi na kira gida, number baba na fara sakawa na kira shi saboda nasan idan na kira mama ɗaga hankalin ta kawai zata yi,

Yana zaune yana zikirin shi na safiya shiyasa bai samu daman ɗaukan kiran farko ba sai a na biyu yayi picking, yana sallama na fashe masa da kuka,

Shiruu yayi baice komai ba yana sauraron kuka na, saida nayi mai isana sannan da ƙyar na iya buɗe baki nace
"B..baba Khamis, Khamis ya..."

Dajin haka ya katse kiran a tunanin shi khamis ɗin ne yayi min wani abu shi yasa na kira dan na kawo ƙara, duk kiran da nayi wa baba yaƙi picking daga ƙarshe na haƙura na kira numbern ya usman dan na riƙe numbers din mutanen gidan mu baki ɗaya a kaina, bugu biyu ya dauka tare da yin sallama amman yana jin murya ta ya kashe wayan,

Haka ma sauran yayu na duk wanda na kira da nace Yusrah ne zasu kashe mama kanma tun kafin na kira ta suka karbi wayan ta tare da na Nasreen sukayi switching dinshi off basu barta tasan halin da nake ciki ba, daga ƙarshe na hakura nayi nadaman rashin jin maganar iyaye na da duk hakan bata faru ba,
I was left with no option than to call YA SAFWAN, nasan ko dangi na zasu yi fushi dani wa'innan souls guda biyu Ya Safwan da Aisha ba zasu taba fushi dani ba,
Saida kiran ya kusan katsewa kafin Ya Safwan ya dauka da kaji muryan da yayi sallama da ita kasan na masu barci ne,
"Ya Safwan Khamis ya mutu, sun kashe min shi"

Shine kawai abin da na iya fada na saka kuka, wani tsalle ya daka ya diro daga kan gadon a firgice ko tsayawa jin sauran bayanin baiyi ba ya zari jallabiyan shi da keys din motar shi ya fita da gudu ya shiga mota sannan ya ɗau hanya ba tare da ya san inda zai je ya same ni ba,

Saida yayi tafiya kadan kafin ya kira, wannan karon bani da courage din magana sarkin ruwa ne ya karbi wayan yayi mishi kwatance kuma har ya iso ba'a samu gawar khamis ba,

Yana fitowa daga motan ko rufe ƙofa baiyi ba ya nufo wurin da nake tsungune ina risgan kuka, ɗan dafa kafada na yayi ba tare da yasan yayi hakan ba ya kira sunana a hankali, ɗago jajayen idanuwa na nayi na sauƙe su a kanshi ganin shine yasa nayi saurin miƙewa na rungume shi tsamm a jiki na,

Mutuwan tsaye ya Safwan yayi jin jiki na a cakuɗe da nashi ya kasa tabuka komai, yana so yaji kanun labarin daga gare ni gana son sanin mai ya faru saboda ya gano bakin zaren amman na kashe mishi jiki,

Saida na sake shi tukunna na gano ɓarnan da nayi, shima ya daidaita nutsuwar shi kafin tambaye ni abinda ya faru cikin kuka na zayyane mishi komai, dan dai namiji ne ya safwan yasa ya iya controlling kanshi amman zan iya cewa ya fini shiga damuwa a wannan lokacin,

"Ina Jannat? Shine tambayar da ya fara min, sai a lokacin na tuna tun daren jiya na bar Jannat a gida tana kuka, kafin na bashi amsa muka ga ana fito da wani abu kaman gawan mutum daga ruwan, saurin juyar da kaina nayi dan bazan iya gani ba,

Ƙarasawa qurin abun ya Safwan yayi suna magana da sarkin ruwa, sun dauki lokaci mai tsawo kafin ya dawo wuri na with a sad face, da ƙyar ya iya fada min khamis ne aka ciro kuma babu rai tattare da gangar jikin shi,

Duk wani tashin hankali da mai tunani zai iya yi na shige shi, zubewa nayi a kan guiwowina na dinga risgan kuka kaman Allah ne ya aiko ni safwan yayi rarrashin duniyar nan har ya gaji amman naƙi yin shiru, daga ƙarshe a hakan ya tattare ni muka je gidan da Jannat take ciki muka ɗauko ta daga gani kwana itama tayi tana kuka har bacci ya ɗauke ta don sai sauƙe ajiyar zuciya take yi,

Daukar Jannat mukayi ya kira motan daukan gawa aka dauki gawar khamis za'a saka shi a kai gida ai mishi shirin zuwa gidan shi na gaskiya..................🤦🏻‍♀️
Manage please 😁
*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

*Ina miƙa saƙon ta'aziyya ta ta bogi zuwa ga ƴan team khamis, inyi muku na Antimee tace Allah ya ƙara nauyin ƙasa,🤭 ah to nidai bani na fada ba😅*4

*Sannan sauran wa'inda sukayi comment jiya ban amsa ba suyi haƙuri dan Allah ba ƙyaliya nayi muku ba WhatsApp dina yayi expire ne a maimakon nayi updating dinshi sai nayi deleting na sake downloading wani, domin idan nace zan bari yayi restoring messages din suna da yawan da zasu iya kawo min matsala a wayan, afwan Please🙏*+

*Thanks for the love MATAR KULLE fans, ina sonku irin har cikin jini na ɗinnan* ❤️❤️❤

25🧛🏽‍♂️
Daga wurin gida ya Safwan ya maida ni gawar khamis kuma aka kai gidan su, baba da sauran yayu na suna tsaye a bakin ƙofa lokacin da muka isa saboda tun a hanya ya Safwan ya kira su ya fada musu abinda ya faru,3

Saboda Jannat dake hannu na har ya Safwan yayi parking ban motsa ba saida ya fita ya zago ya bude min ƙofa, ɗaga rinannun idanu na nayi na sauƙe su a kan fiskar baba lokaci ɗaya hawayen da nayi ƙarfin halin riƙe su suka sami daman gangarowa saman fuska ta, yaya na wanda yake bin ya usman ya dauke jannat daga kan cinya ta ya riƙe ta a wurin shi,

Baba baice komai ba ya kama hannu na ya jani a hankali har zuwa cikin gida mama da Nasreen kaman jira suke yi ina shiga suka rungume ni suna taya ni kuka,
" A kan ido na suka kashe shi mama sun zalince ni, sun cutar dani" shine kalmar da ya fito daga baki na,

Ƙara ruƙunƙume ni mama tayi tare da runtse idanuwan ta hawayen tausayin ƴarta masu zafi suna sauƙa a saman kuncin ta, innalillahi wa inna ilaihirraji'un take maimaita min cikin kunne na ko zan samu na riƙe amman bani ma ɗa ƙarfin magana,

**********
Maman Khamis firr taƙi ta kalli gawan da aka shigo dashiba matsayin na Khamis, rikicewan da na gani a fuskar mahaifin shi bayan yayi arba da gawan ne ya ruɗa ni amman sai naga Ya safwan ya jashi gefe suna magana ƙasa_ƙasa, daga farko sun fara kaman zasu yi hargowa daga baya kuma ban san me safwan din ya fada mishi ba naga sun daidaita, (to me hakan yake nufi? Oho!)

Shigar da gawan aka yi aka wanke shi aka suturta shi sannan aka saka a kan makara aka fito dashi domin yi mishi Sallah, kada kuso kuga tashin hankali a gurin mahaifiya mai ƙaunar ɗanta wanda bata bari yayi nisa da ita gashi yau za'a raba ta dashi dole, da suka fita haka ta zauna dabas a ƙasa tana kuka mai ban tausayi,

Bayan an gama komai an taru ana zaman makoki sai ga Yusrah yaya safwan ya kawo ta tare da jannat, tana sauƙa daga motan ta tsaya tana ƙare musu kallo an zauna anyi jingum_jingum, safwan ma tsayuwa yayi yana kallon ta don ce mishi tayi ya kawo ta akwai abin da take so ta fada,

Bata ce wa mutanen wurin komai ba da ɗan gudun ta tashiga cikin gidan ta bar Safwan tsaye da yarinya a hannu, tana shiga ciki ta dinga kutsawa tsakanin mutane batabi ta kan masu yi mata ta'aziyya ba ta wuce wurin da ta hango maman Khamis tana risgan kuka ta tsunguna a gaban ta murya can ƙasa yanda babu wanda zai ji tace,

"Mama ki daina kuka Khamis yana raye bai mutu ba, na manta ban fada miki ba gawan nan ba nashi bane"

Ɗagowa tayi a firgice tana kallo na yanda na fada mata maganar cikin qwarin guiwa alamun gaskiyar shi tun daga zuciyata ta fito, lallai ta yarda na zauce firgicin mutuwar Khamis ya shiga jiki na domin idan da cikakken hankali na ba zanyi irin wannan maganar ba"

Riƙe hannu na tayi ta saka kuka tana fadin "Yusrah haƙuri zakiyi dukkan mai rai mamaci ne"
Saurin fisge hannu na nayi raina a bace, ta yaya za'ayi ace mahaifiyar Khamis bata gane gawan ɗanta ba? Duk da cewa nima ba kallon ƙurilla nayi ma gawar da aka ciro ba amman ina da tabbacin ba na Khamis bane,

Wannan karon cikin ɗaga murya nace "wallahi mama na fada miki Khamis bai mutu ba gawan nan ba nashi bane, ba kalan kayan da suka kashe shi dashi ba kenan, Khamis bai cika saka fararen kaya ba bayi ma son farin kala sosai kuma gawan nan da farin kaya a jikin shi, kice ma mutanen nan su tashi su tafi Khamis bai mutu ba"

Tsagaita kukan ta tayi tana ƙoƙarin calming dina na daina hayagagan da nake yi kada na jawo hankalin jama'a zuwa gare ni, amman inaa yanda take taro ni haka nake bauɗewa, daga ƙarshe na dawo ihu kaman anyi ma kirista mutuwa, har maza dake zaune a waje suka shishshigo,

bani son ma jin naji an ambaci sunan Khamis an danganta shi da sunan mutuwa don ina ji a jiki na khamis yana raye bai mutu ba idan ma sunce ya mutun basu da hujjan da zasu gwada na an sami gawan shi tunda ni dai ko wuƙa zasu saka min gawan nan ba na Khamis bane,

Daga ƙarshe yayu na aka kira da taimakon ƙannen shi mata suka kwashe ni a wurin da na duƙufa ina kuka kaman raina zai fita, akan me zan fada musu Khamis bai mutu ba suƙi yarda? Ba ni bace matar shi kuma ko yaushe nake tare dashi, ko siffofin jikin Khamis duk na fisu sani so idan nace musu ba shi bane ya zamo dole su yarda amman sunƙi yarda,

Da muka isa gida ma saida suka rirriƙe ni kafin aka shigar dani gida na gama dawowa kaman ƙaramar mahaukaciya, a daki suka saka ni suka rufe tare da mama tun lokacin Jannat ta koma marainiyar ƙarfi da yaji tayi shiruu tana bin mutane da ido ga yunwa sosai a cikin ta amman ko ta kanta bani bi,

Mama ta kada ta rawa ta fahimtar na gane cewa mutuwa gaskiya ce na rungumi ƙaddara ni kuwa nace fyattt ban san da wannan zancen ba Khamis yana nan da rai,

**********
Shigowa suka yi cikin gidan wanda yake na ƙasa rungume da mutum daga gani bayi cikin hayyacin shi , suka wuce cikin bukkar dake bakin ƙofa suka kwantar dashi saman gadon kara, sannan ɗaya daga cikin su ya fara duba gudun jinin shi ta hanyar amfani da yatsan shi yana matsa wrist dinshi,
Yayi hakan da sauran gwaje gwade na kusan 7 minutes sannan ya ɗago yana duban ɗayan mutumin cikin hausan shi mai rauni yace
"Ɗan nan karbo min jaka ta wurin hinde"

Da "toh baba" ya amsa sannan ya fita, bai dade ba ya dawo da jaka irin na fata ya miƙa mishi, shi kuma ya kunna wuta a aci balbal ya ciro wasu qarafuna ya ajiye, ɗaya daga ciki mai baki kaman kwarashi amman baki biyu yake dashi ya saka a jikin aci balbal din ya ƙona bakin abun sosai sannan ya tsoma a cikin ruwa ya ɗaga rigan mutumin tare da yin bismillah yasa a daidai wurin da harbin bindigan yake ya ciro bullet...........🤦🏻‍♀️

_Kuyi haƙuri da gajercin page ɗin yau, ina ɗan bincike kan wani abu ne ban samu kammalawa ba, amman gobe zanyi posting sau biyu idan Allah yaso_

*Masu fada dani da masu jin haushi na da masu cewa sun daina karatu duk dan saboda mutuwan Khamis sai ku maida wuƙan ku🤭 Khamis is alive🤓*3

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

26🧛🏽‍♂️
*Wurobokki village*

Duk abinda yake yi yana bayani ma yaron shi kuma ya zuba ido da kunne yana kallo yana sauraro, yana cire bullet ɗin ya zuba wani abu tsalalo kaman ruwa ya goge wurin tass sannan ya saka zare da allura ya fara dinke wurin,

Basu dauki lokaci mai tsawo ba ya gama mishi ɗinkin ya saka bandage ya zagaye kunkumin shi dashi yanda zai rufe ciwon sannan suka koma kan raunin shi dake kai, wannan karon ma yaron ya bada aikin yana yi yana masa gyara kuma yana ƙara guiding dinshi har ya gama ya naɗe kanshi yanda germs ba zasu sauƙa kan ciwon ba sannan yaron mai suna Jaɗe ya fita da kayan da sukayi aiki dashi domin tsaftace su,+

Mahaifiyar Jaɗe ne ta shigo da sallama ta ajiye mishi garwashin wuta a cikin kasko mai ɗan girma sannan ta fita ba tare da tayi wani magana ba ko kuma ta tambayi waye mutumin da suka shigo dashi, dan ta saba da hakan aikin mai gidan ta ne jinya ma marasa lafiya,

Wani kullin magani ya dauko ya ɗibi kadan ya zuba a cikin wutan, ya ɗebo wasu itacuwa ƙananu ya zuba, a haka saida ya haɗa magani kusan kala 5 duk hayaƙi ya gauraye dakin, yana zaune yana daɗa duba jinkin shi jaɗe ya dawo da cup din ƙarfe mai dauke da ruwa da kuma wasu mutattun yadi da sun gama yin laushi riga daban wando daban,

Miƙa wa mahaifin shi kayan yayi, sai ya karbi wando zallah yace ya maida rigan babu musu kuwa ya ajiye kofin ruwan ya koma da rigan a hannun shi, mutumin ya saka aska ya farke rigan jikin shi harda singlet ɗin ciki sannan ya sauya masa wandon jikin sa, ya ɗauki ruwan kofin yayi addu'a a ciki sosai sannan ya shafe masa fuskar sa da ƙirjin shi dashi yana gamawa shima ya fita tare da sauƙe asabarin ƙofar dakin,

Sallamar da yaji ana kwaɗawa a kofar gidan ne yasa fuskar shi sauyawa zuwa yanayi mai muni, daga gani baiji daɗin zuwan wanda yake sallamar ba, jaɗe ne ya ƙaraso wurin da yake tsaye ya dauki sandar sa dake jikin ɗakin da suka kwantar da mutumin ɗazu ya ɗaura saman kafadar shi yace
"Baba hara naje nace mata bakki na, nashan gulma ce kawai ta kawo ƴar Laraba"

"A'a ɗan nan, bari naje na shame ta naji yau kuma dame tajo kada kuma aikan mai gari ne, nashan ba jai wucce a kan maganar baƙuwar nan da muka sinto gaɓar ruwa ba"

Da fadan haka ya zura takalmin shi ya fita wurin ɗan Laraba a ƙofar gida, kaman mutumin arziƙi ya bashi hannu suka gaisa sai washe haƙwara yake yi gulma yau tayi kasuwa,

"Malam Arɗo, mai gari taa aiko ni na gaya maki tana shon ganin ki a fada yanjun nan"

"Ƴar Laraba fatan dai laafiya koo?"

"Kin shan dai maganar guda ɗaya ce kullum, boɗɗi ce ya shake racin ɗa'a wa mai gidan shi yarima to shine don kada a koro miki ɗan ki ba tare da kin shan abin da yake faruwa ba mai gari tace a nimo ki, kinga nan ƙafa ta ƙafar ki"

Sauƙe ajiyan zuciya malam Arɗo yayi don baiyi tunanin abin kenan ba, lokacin da suka tsinto baƙon nan a bakin ruwa da suka zo wucewa da shi tabbas ɗan Laraba ya gansu shiyasa yayi tunanin har yaje ya kai rahoto gaba ne,

STORY CONTINUES BELOW

Yafi so shi da kanshi yayi bayani wa mai gari domin munafukan shi basu kai rahoto sai sun ƙara gishiri a miya, kuma kwana biyu manoma sun matsa musu suna biyo makiyayan da suka shiga gonakin su har gida suna kashe su,

Amman matsalar boɗɗi ma ba ƙaramar matsala bace a gare shi, yarinya ƙarama ƴar shekaru 12 a duniya kacal ko mallakan hankalin ta bata gama ba mashayin yarima yana gana mata azaba, kuma ya gama sambadan ta a kawo ƙarar ta gidan uban ta da barazanar saki,

Tasa qeyar shi a gaba ɗan Laraba yayi zuwa fadar me gari...

**********
Ihu na saka na fincike ɗan kwalin kaina na wurgar a gefe, na miƙe da wani ƙarfi da naji yazo min a wannan lokacin kaman na doki nayi hanyar ƙofa da niyyar zuwa naci mutuncin shegiyan da tazo min ta'aziyya, Aisha ta daddage da tsohon cikinta aihuwa yau ko gobe ta jawo ni baya, tasa ƙafar ta ta take babban yatsar ta yanda ta san duk yanda tayi ba zata iya ƙwace wa ba,

"Wai me ya hau kan ki ne Yusrah? A haka zakiyi ta fada da mutanen dake zuwa jajanta miki rashin da kikayi? Nikam a kanki ne aka fara mutuwa ne kam da baza ki rungumi ƙaddara ba?? Khamis is gone! Ya tafi kuma har abada ba zai dawo ba, ki yayyafa ma zuciyar ki ruwan sanyi ki riƙe amanar da Allah ya baku, tun safiya ake abu ɗaya ki tausaya ma Jannat dan Allah"

"Nifa na fada muku gawar nan ba na Khamis bane wallahi tallahi ba nasan bai mutu ba, me yasa ba zaku yarda dani ba? Idan ma kuna ganin kaman ƙarya nake yi kuje ku bude gawan kuga fuskar shi mana! Ba na Khamis bane wallahi"

Ƙaramin tsaki taja gaba daya haushi na ya dabaibaye zuciyar ta ji take kaman ta nada min duka amman ta san hakan ba shi bane mafita,

"A ina kika taɓa jin anje an tono kabari dan kawai a tabbatar da mamaci? Ai idan ma ba Khamis ɗin bane baki da tabbacin ko yana raye tunda ko gawan shi ba'a gani ba, babu yanda za'ayi mutum ya nitse a ruwa kuma yaci gaba da rayuwa"

"Ina da hope cewa Khamis yana raye besty, ina ji a jiki na da akwai rai da ruhi a gangar jikin khamis kawai yayi mana nisa ne, but i believe wata rana zai dawo gare ni"

"Shikkenan tunda kin kafe a kan haka, it's ok ki zauna da yunwa amman ki amshi Jannat ki shayar da ita dan Allah, kinsan bata wani iya cin abinci sosai ba kunun nan idan an bata ba son karba take yi ba, ki fita hakkin baiwar Allan nan"

karban Jannat nayi a hannun Nasreen sarkin kuka, fuskar ta caba_caba da hawaye tana binmu da idanu, banyi musu ba na karbi Jannat na zauna a bakin gado na fara shayar da ita, matar dake waje ta ɗan jiyo hayaniyar mu sama sama amman dan ta tabbatar da abinda taji muna faɗa ta bankado ƙofar dakin ta shigo gaba ɗayan mu muka ɗago muka zuba mata ido dan jin mai ya shigo da ita,

Kame_kame ta fara tana dariyan yaƙe ta juyo ta dube ni tace
"Yusrah yaya haƙuri? Ashe mijin ki sa'i yayi"

Saida na banka mata uban harara sannan nace
"Haƙuri ban ganshi ba kaman yanda munafurcin ki ya jiyo miki Khamis yana raye bai mutu ba idan kin gama kema zaki iya fita ki bar mana gida" na miƙe tsaye ko gyara zaman riga na banyi ba na fita ina ƙunkuni yanda nasan zata jini,

"Magulmaciya, munafukar banza an girma ba'a san an girma ba" na ratsa ta gefen ta na fice daga dakin na koma ɗakinmu da yake mazaunin na Nasreen a yanzu duk da anyi mutuwa tsakar gidan babu kowa duk nayi musu kora da hali,

Matar nan saida ta zubar da ƙolla a wurin dan tabbas kalamai na sun ƙona mata zuciya taji zafin su sosai, ɗan ta na hudu ne sa'a na amman saboda rufewan ido da toshewar ƙwaƙwalwa (inji sweetheart 😂) na rufe ido na zuba mata rashin mutunci son raina,2

Danne zuciyar ta tayi tayi sallama ma su mama sallama ta tafi tasan ko me nayi mata ita ta siya da kudin ta, tana fita mama ta nemi wuri ta zauna sai kuka dan gani suke yi na zauce tunda gashi harda ci ma manya mutunci, tafi kowa sanij rashin kunya ba hali na bane, dama ace Nasreen ne tayi haka zata iya yarda itama sai da wani babban dalili,

***********

Kin dai ji da kunnen ki Ardo, yarima ta fada miki abubuwan da boɗɗi yake mishi sai ki yanke hukunshin da jai mata da kan ki,

Sunkuyar da kanshi Malam Arɗo yayi yace
"Allah ya taimaki mai gari, Allah ya hushi zushiyar ki, boɗɗi yayi laifi ayi mishi hukunshin da ya dace amman kada yarima ya rabu da shi dan Allah"

Gyada kai mai gari yayi alaman gamsuwa shi kuma ɗan iskan yana hakimce yana sakin wani shu'umin murmushi, mai garin ya juya wurin shi yace
"To kinji dai yarima, an bakki wuƙa da nama amman kiyi haƙuri banda shaki kinji ko?"
Gyada kai yayi, mai gari yayi hamdala kaman abin arziƙi sannan yace ma su Malam Arɗo
"Ki tashi ki tafi an sallame ki"

Tattara takalman shi malam ardo yayi yana ta godiya kaman wanda akayi mishi kyau ya bar wurin, a hanya mutane sai sun rusuna suke gaida shi saboda tsananin girmamawa dan shine kaman babban likitan garin wanda ke musu magani,
A ƙauyen ba kowa ne yake zuwa asibiti ba don yayi musu nisa ga kuma kashe kudi, kuma malam Arɗo salo biyu ne wurin bada magani, yana amfani da ayoyin Alkur'ani da kuma ilimin sanin itacuwa da Allah ya bashi gashi yanzu har babban ɗanshi ja'e yana son gadan shi, shiyasa case ɗin boɗɗi a gidan auren ta yake mugun ɗaga mishi hankali saboda yana barazana ne da mutuncin shi,

Duk ranar da boɗɗi tayi kuskuren fitowa daga ɗakin mijinta daga wannan rana mutane zasu daina kallon shi da gashin ido dan haka al'adan garin yake idan sunyi aure duk rashin daɗin dake cikin ta ba'a saki idan kuma akayi to laifin matar ne itane bata riƙe auren ta da kyau ba,

Malam Arɗo na shiga gida ya fara shirin shiga jeji ɗebo magani wanda a da shirin shi na tafiya nan da kwana biyu ne amman yasan tunda aka kawo ƙarar boɗɗi yau sai an jera kwana uku ana saka shi sintiri a hanya gwanda ya tafi yau din kawai,

Saida ya sake duba jikin Khamis ya bar jinyar shi a hannun jaɗe tare da yi masa bayanin duk abubuwan da zai dinga mishi kuma ya tabbatar mishi Khamis zai iya farkawa nan da sati guda ko sama da haka,
**********
Al'amarin Yusrah kullum gaba_gaba yake yi ta gama fita daga hayyacin ta ƙarshe saida suka danganta ta da asibiti aka daura ta a kan magunguna dan sauran ta kaɗan ta zauce,

Iyayen ta harma da iyayen Khamis sun kada sun rawa amman taƙi shiga takaba, tace ita mijinta yana raye babu dalilin da zai saka ta maida shi mamaci, haka zatayi wankan ta da sabulu mai ƙamshi na musamman ta saka kayanta ta feshe jikin nan da turare ta murza ɗauri kuma fa babu inda take zuwa kawai dai ta nuna musu taurin kanta ne,

Labari har ya fara yawo a gari cikin dangi wai na haukace saboda mutuwar miji na wasu har zuwa suke yi da sunan ziyara wai dan suga wani irin hauka nake yi amman basu samun wani cikakken bayani...............🤦🏻‍♀️

*Sorry for the fulani errors😂, i know that I sound weird and horrible but the situation is not like the one in KAMA DA WANE, na iya yaren Spanish kaɗan amman ban iya fulatanci ko cikin cokali ba🤭 so shiyasa ma banyi karambanin fara sako fillanci a ciki ba, bear with me please😅*

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

27🧛🏽‍♂️
Kafin malam Arɗo ya tafi saida ya biya wurin mai gari ya nemi iznin sa domin ba'a shiga garin ba'a fita sai da sanin sa, daga nan ya fada mishi sun tsinci baƙo a bakin ruwa kuma yana halin neman taimako don ceto rayuwar sa shiyasa bai ɓata lokaci ba ya dauke shi ya kaishi gida ya fara mishi jinya,+

Mai gari yaso yayi tawaye amman da aka fada mishi ana kyautata zaton baƙon ɗan birni ne sai ya ja bakin shi yayi shiru yana tsammanin duk ranar da wannan baƙon ya farka zasu samu wani alkhairi daga gare shi,

Jaɗe da mahaifiyar shi hinde da kuma matar shi ba ƙaramin ƙoƙari suke yi ba wajen kula da khamis in malam Arɗo's absence, saidai yau tafiyan Malam Arɗo sati 2 harda ƙarin kwana 3 Khamis bai farka ba, hakan ya ɗan daga hankalin jaɗe dan iya yawan kwanakin da ya dauka bai farka ba iya wahalar yiwuwar farkawar nashi ko kuma ma ya tashi da wani cutar daban,

7:46pm

Sanyin abinda yaji yana ratsa fatar ƙirjin shi yasa shi bude ido a hankali saidai bayi ganin komai sai duhu hakan yasa ya maida idanun shi kirif ya rufe na ɗan wani lokaci, saidai bai daina jin sanyin wannan abun ba, yana cikin haka yaji an saka masa wani abu mai ɗumi a gaban goshin sa amman abun yana taba fatar goshin sa sai yaji zafi sosai a take ya buɗe idanu tare da kai hannun shi zai taɓa wurin da yaji yana yi masa zafi,

Saurin riƙe hannun shi jaɗe yayi yace "alhamdulillahi, shannu kaɗɗo Allah baki lafiya shannu ko?"

Kallon wannan farin bafulatanin dake kanshi Khamis yayi, bai san shi ba! Hasali ma ko taba ganin shi baiyi ba to ma a ina yake?,

Dafa hannun shi yayi yana ƙoƙarin tashi wani zafi da yaji a gefen cikin shi yasa yayi saurin tashi ya zauna da kyau tare da kai hannun shi wurin, ɗago hannun shi da zaiyi sai kawai yayi arba da jini hakan ya firgita shi sosai ya sake maida hannun shi gefen cikin ya danne kan ɗinkin da akayi mishi yana fitar da wani sauti cikin zafi da azaba,

Babu abinda ya fado mishi a rai cikin rayuwar shi na baya sai Yusrah!! Tabbas ya tuna ranar da yayi stabbing Yusrah a gefen cikin ta da screw driver, itama irin wannan zafin taji kenan? Irin wannan raɗaɗin da ko shi namiji ya kasa jurewa amman duk da hakan ya faru Yusrah taci gaba da zama tare dashi??

"Ina Yusrah take?"

Shine tambayar da ya fara yiwa jaɗe, "Ki kwantar da hankalin ki kaɗɗo, kin shake fama raunin dake jikin ki koma ki kwanta", ya faɗa tare da taimaka mishi ya kwanta ya dauko ruwan rubutun da malam Arɗo yace da ya tashi a bashi ya sha ya kai mishi bakin shi yana ɗaga mishi kai alaman yasha,
Khamis dai ya shiga ruɗu, bai san a ina yake kuma tare da suwa yake ba, amman hakan baisa yayi ma jaɗe musu ba ya buɗe bakin shi ya sha maganin Sannan ya mayar da kanshi ya kwanta,
Jaɗe ya warware ciwon shi yanda yayi jini ya sake dubawa kafin ya goge mishi wurin ya rufe da sabon bandage, kafin wani lokaci khamis ya sake komawa barci ba tare da ya sani ba bai sake farkawa ba saida  hasken rana ya bugi fuskar shi,

STORY CONTINUES BELOW

Wannan karon a hankali ya tashi ya zauna don ya san da ciwon jikin sa, ya fara bin ɗakin da kallon da baiyi mishi a daren jiya ba saboda babu wadataccen haske,
Sauƙe ƙafar shi yayi ɗaya bayan ɗaya ya miƙe da dafa bango ya daga sabaran ƙofar ɗakin ya fito yana takawa a sannu a sannu, gidan yayi mishi kama da na ƙauye to shi kuma mai ya kowa shi ƙauye cikin gidan mutanen da bai san su waye ba?
Tuna lokacin da ya gudo da Yusrah ya fara har zuwa lokacin da kunama ya harbe shi duk maganganun da ya faɗa ma Yusrah yana jin shi da kuma lokacin da suka ɗauke shi suka jefa shi a ruwa, yana jin kuka da ihun da Yusrah take yi a wancan lokacin to yanzu ina take?

Yana bala'in son ganin Yusrah a yanzu harma da jannat yana tsoron ace su kunama sun cutar mishi da iyalin shi,

Mahaifiyar su jaɗe ne da ta fito daga kitchen ɗin su na murhu gaba ɗaya hayaƙi ya bule wurin sai ƙoƙarin kunna wuta takeyi itace yaƙi bata haɗin kai,

Da hanzarin ta ta ɗauko ma khamis kujera ƴar tsuguno ta ajiye mishi ya zauna tana mishi sannu, ganin yana yawan kai hannu wurin ciwon yasa ta janyo mayafin ta daga kan igiyar shanya ta fita ƙofar gida sannan ta saka ɗaya daga cikin yaran jaɗe ya kira shi idan ya dawo daga gona saboda ba'a gida ɗaya suke rayuwa ba bukkar su na gaba kaɗan,

Ba'a daɗe ba jaɗe ya shigo ya zo wurin khamis yana kallon shi da murmushi a fuskar shi dan alamu sun nuna sauƙi ya fara samuwa

"Sannu koɗɗo, yayi jikin naki?"

Dago idanun shi khamis yayi ya zuba mishi ba tare da ya amsa tamabayar da yayi mishi ba ya sake jefa mishi wani tambayar

"Ina Yusrah?"

"Washeshe Yushra kuma?"

"matata ce ita, bata zo tare dani bane?"

Girgiza kai yayi yace "A'a kaɗɗo babu wata yushrah da yajo, ke kaɗai muka tsinta a bakin teku, ki fada mana menene shunan ki?"

Shiru khamis yayi bai amsa ba ya kalli Hinde da ta koma can loko ta maƙale taƙi ko kallon yanda yake ga yara ma duk sun zuba mishi idanu sai kuma ya sauƙe kanshi ƙasa yana kallon ciwon cikin shi, sannan yace

"Sunana Khamis"

"To Hamishu daga wani gari kikke?"

Dagowa yayi a hasale jin wannan baƙauyen yana niman ɓata mishi suna yace " ni suna na ba Hamisu ba, and where the hell am i? What brought me here?"

Ɗan shiru jaɗe yayi yana mishi kallon rashin fahimta dan kwata_kwata bai fahimci inda xancen nashi ya dosa ba, saidai kafin yayi wani magana wata ƙanƙanuwan bafulatanan yarinya ta shigo gidan da kuka ɗauke da ƙullin tsummokaran ta,
direct wurin da hinde take tsaye ta ƙarasa ta zuba a ƙasa tare da yin pillow da tsummokin ta tana kuka kaman Allah ne ya aiko ta,

Da ƙyar ta iya buɗe baki cikin siririn muryar ta da harshen fillanci tace
"Inna yarima ya sake ni"

Dafe ƙirji hinde tayi ko salatin ma ta gagara itama sai kuka, abinda yayi matuƙar bawa Khamis mamaki ya ɗaure mishi kai shine harda jaɗe a cikin kukan kuma a gaban yara, amman mai yayi musu zafi haka suke irin wannan kuka? Ko mutuwa akayi musu ai wannan rashi tawakkali ne,

Saidai Khamis bai sani bane, kukan da suke yin nan gwanda mutuwa a kanta don bala'in da suke hasko ma kansu nan gaba abin kwatance ne ma ƴan baya, idan sukayi wasa zaman karkarar sai ta gagari jikokin su ba su kaɗai ba,

**********
Saurin shan gaban ta mama tayi tare da karbe akwatin da take ja, ta tare mata hanya tana kuka tace
"Yusrah yanzu kuma ina zaki je? Dan Allah kiyi haquri ki zauna wallahi babu yanda yafi miki mutunci a halin yanzu kaman gidan iyayen ki, ki taimake mu dan Allah"

Itama yusran kuka take yi gashi saboda ɓacin rai har wani diri jikin ta ke yi, cikin ɗacin murya tace
"Ai na san da hakan ne mama shiyasa a rashin miji na kusa dani na zabi na dawo gare ku amman naga alaman Nasreen da sauran yayu na suna da matsala da zama na a cikin gidan ubana shiyasa zan bar musu gidan na tafi gidan iyayen mijina na zauna, nasan su tunda sun san darajar sa kuma sun san matsayin da yake dashi a zuciya ta ba zasu taɓa takura min a kanshi ba"

Na sake ratsawa ta gefen ta zan wuce mama ta sake maida ni baya,
"Ai gida namu ne ko ba nasu ba, mu mun amince miki ki zauna har ƙarshen rayuwar ki ba zamu taɓa takura miki a kan abinda baki so ba, Yusrah ki rufa ma ƴarki asiri ki raine ta a gidan mutunci don Allah"

"To wai meye damuwar su dani ne? Mai na tare musu? Safwan ɗinnan ko shine namiji ɗaya tol da ya rage a duniya da idan ban aure shi ba zan mutu idan nace bana yi za'ayi min dole ne?"

"Ke ba ƙaramar butulu bace aunty Yusrah" muka ji Muryar Nasreen tana fada ta bayan mu, rufe ido nayi ina sauƙe numfashi a hankali domin idan ban kai zuciya ta nesa ba a kan maganar safwan zan iya jima Nasreen rauni,

"Eh! Nasan kin jini da kyau butulu mai manta alkhairi kawai, wai ke mai taurin kai kinƙi yin takaba an bikin kuma kinƙi yin aure yanzu me kike so ma rayuwar ki? wallahi kinji kunya da har iyayen ki zasu nemi abu daga wurin ki kasa musu sabida namiji shi ɗin ma matacce"

Daga jin kalmar ta na ƙarshe ban san lokacin da na taƙarkare na sharara mata mari ba, Khamis ɗin nawa ta kira matacce?

"Wallahi tallahi ki kiyaye ni auta, ni ba sa'ar wasan ki bane idan kin zage ni kinsha banza ko da wasa harshen ki ya sake tuntuɓen zagin Khamis sai na fitar miki dashi waje, shi Safwan ɗin uban ki ne da kika daddage kike tada jijiyoyin wuya a kansa, me safwan ɗin ya ƙare ki dashi?"
"Mutunci da sanin ya kamata, safwan ɗan halak ne da yayi halacci kuma aka yaudare shi amman still bai fasa taimakon wanda ta yaudare shi ba"

Tafa hannuwa nayi a hasale nace "fiine then ke kije ki aure shi tunda har kin samo wa'innan qualities ɗin daga gare shi, amman nikam soyayyar miji na ya rufe min ido bani ganin su"

Girgiza kai Nasreen tayi cike da takaici mama tana janta baya amman tana tirjewa tafi so sai ta gama zazzage min abinda ke cikin ta tukaunna,

"Bari ki gani aunty Yusrah, sau ɗaya just once ya Safwan ya buɗi baki yace yana so na ba zanyi wani tunani ba kafin na amince mishi, ke kuma daga baya ina tabbatar miki zaki zo kiyi nadama a lokacin da nadamar ki ba zata amfane ki da komai ba don lokaci ya riga ya ƙure miki"

"Indai a kan Safwan ne to kisa ma ranki kaman tunda aka haife ni bansan menene ma'anar nadama ba"

**********
Saida jaɗe ya gama shan kukan shi tare da sauran mutan gidan ya taso yazo wurin Khamis yana share hawaye, taimaka mishi ya tashi ya fara ƙoƙarin yi da nufin maida shi cikin ɗakin ya kwanta don ba'a cika son yana yawan motsa jikin shi ba, ƙi Khamis yayi yace a fara bashi ruwa yayi alwala tukunna,

Buta jaɗe ya dauka ya nufi randan ƙasa zai ɗibo ma Khamis ruwa, sai lokacin boɗɗi taji zata iya tashi daga inda take rashe a turbayan ƙasa ta karkade ƙuran da ya hau mata saman kaya sannan ta ɗaga ƙullin tsummokin ta,
Juyowan da zatayi taci karo da ƙaton gardi yana zaune ya zuba mata idanu ko riga babu a jikin shi..............🤦🏻‍♀️

Don't forget to follow
Vote
Share
And comment as you read 💖

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*´¯)

😈 *MATAR KULLE*  😈

     _(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

         *BY*
        *UMMU NAJMA*

28🧛🏽‍♂️
Wani kaɗawa hanjin cikin ta sukayi suna bada sautin 'ƙulululu' tana zazzare ido kaman wanda akayi ma ƙarya, da azama ta juya ta nufi ɗakin hinde saboda sauri har tana tuntuɓe,

Dogon tsaki Khamis yaja yana rayawa a zuciar shi gidan nan mahaukata kawai aka tara komi nasu a baibai, jaɗe yana kawo mishi ruwan yayi alwala ya taimaka mishi ya miƙar dashi suna shiga ɗaki sannan ya shimfida mishi abin da suke sallah a kai ya zauna ya gabatar da sallar isha da asuba dan a tunanin shi kwana ɗaya kawai yayi bayi cikin hayyacin shi,+

Yana idar da Sallah ya samu sun shigo mishi da abinci a akushi, kallon ɗukamen tuwon yayi wanda ya sha man shanu har wani gangara yake yi a take yaji amai ya taso mishi sai kawai ya saka murfi ya rufe abincin kada ya sake jiƙa musu aiki dan a rayuwan shi ya tsani man shanu,

"Kaɗɗo bakki shon abinshin ne a kawo miki wani?" Jaɗe ya tambaye shi, gyada kai kawai khamis yayi ya ɗauki abincin ya fita dashi ba tare da yasan dabwani abun zai sauya mishi ba, suma abinda suke ci kenan,

Kitchen ya mayar da abincin sannan ya fita zuwa gidan shi ya gani ko matar shi zata sama ma Khamis abin da zai saka a cikin shi, ɗan ɗanwaken da tayi musu zasu ci dududu bai wuce rabin mudu ba haka ya ɗauko kacokan ya kawo mishi, yaci ya rage tukunna ya bawa yaran saura shi kuma da matar shi su rungumi na annabawa su sake cin ɗumamen safe,

Khamis bai sake komawa barci ba sai bayan da yayi sallan azahar, sai da ɓoɗɗi ta daina jin motsin su gaba ɗaya tukunna ta iya fitowa don zagawa banɗaki, gaba ɗaya khamis ya gama tsorata ta ita bata taɓa ganin shi ba kuma bata da kwanciyar hankalin tambayan waye shi a yanzu,

**********
"Auta.." na kira ta a hankali ina taɓa kafadar ta, bata juyo ba ta sake gyara kwanciyar ta yanda zata bani baya da kyau,

"Nasreen please, I'm sorry Allah ba zan sake ɗaura hannu na a jikin ki saboda wannan maganar ba I'm so sorry amman nima ki daina kawo min zancen Safwan don Allah"

Juyowa tayi tana fuskanta na itama cikin muryar nutsuwa tace "meye laifin ya Safwan ne dan Allah? Me zaiyi ya sami lokacin ki aunty Yusrah? Ki faɗamun ko menene zanje na same shi na sanar dashi zai miki"

"Tashi ki zauna" na faɗa ina ɗaga ta, zama tayi ta zuba min idanu tana sauraren bayanai na,
"Nasreen ke yarinya ce har yanzu shiyasa ba zaki fahimci menene soyayya ba, ba'a yi mishi dole, ba'ayi mishi garaje, kuma babu ƙarya a cikin ta domin duk wanda yayi ƙarya a cikin soyayya ba zata taɓa bulle masa ba, zuciyata bata mararin ya Safwan koda ace alal misali na amice dashi zaman mu ba zaiyi mana daɗi ba"

"Aunty Yusrah ki daina cewa ni yarinya ce idan har maganar soyayya ne because I can clearly understand everything, i can understand your situation, you are troubled and depressed amman halin da kike ciki bai kai wanda zai makantar da ke ki kasa gani ba,
na daɗe banga wani namiji irin ya Safwan ba wanda yake soyayya da duka zuciyan shi kuma yake hidima ma wanda yake tare dashi saboda Allah, bai damu da abinda zai ribantu daga gare ki ba har gobe shi yake ɗaukar dawainiyar Jannat kamar mahaifinta wata mace ce zata samu irin wannan namijin taƙi amincewa dashi bayan ke?

STORY CONTINUES BELOW

Bari ma na buɗe miki tsohon sirri na da babu wanda ya sani, na so ya Safwan sosai lokacin da ya rasa aunty Suhailat daga yanda ya koma bayan mutuwar ta kadai zaki gane tsananin son da yake mata da kuma shaƙuwan dake tsakanin su, nayi burin dama ace nice na mutun wallahi indai zai mini irin wanna son, amman ban saka ma raina ba saboda shekaru na sunyi ƙarancin da babu wanda zaiyi tunanin min aure a lokacin shiasa na shafa ma kaina ruwan sanyi nayi haƙuri"

Share hawayen dake ƙoƙarin zubo mata tayi ni kuwa na zuba mata ido cike da al'ajabi wai ƴar Nasreen ɗinnan ne, ƴar wannan abun ko jimawa da cika shekara na 16 bata yi ba amman har take maganan wani soyayya harda aure, lallai zamani ya cika mai juyayi ,

"Lokacin da aka raba auren ki da Ya Khamis dalilin da yasa nayi ta shige masa da maganar ki kenan domin ina so miki abin da nayi muradi ma kaina ban samu ba, yanzu baki da ya Khamis baki da ya Safwan malam Nasir kan ma ba'a maganar shi dan tuntuni ya janye,

Haka kike so ki ƙare rayuwar ki ke kadai? Aunty Yusrah ko dan ana miki kallon mutunci ki tsallake tsangwamar society ba zaki ƙara aure ba?"

Hannun ta na jawo duka biyu na saka cikin tafukan hannaye na na dunƙule su ina ɗan sake mata ƙaramin murmushi wanda iyakacin shi saman leɓe ba don na aminta da zancen ta ba saidai tunda tayi min magana cikin lallami da tausasa harshe nima dole nayi mata da sanyi yanda zata fahimci muradi na,

"Auta kin taba ganin yanda aka yi aure a kan wani auren?" Na tambaye ta ina kallon cikin idanun ta

Girgiza kai tayi alaman A'a, naci gaba da cewa
"To kinga kuwa babu yanda za'ayi da auren Khamis a kaina na auri wani daban idan ba wai saki na yayi ba, kaman yanda kikayi imani da nagartan Ya Safwan har kika iya bayyano kyakkyawan halayen shi da suka saka ya samu matsuguni a zuciyar ki, nima haka nayi imani da cewa mijina wata rana zai dawo gare mu nida ɗiyar shi,

And also me yasa zaki ɓarar da soyayyar ki a kaina? Me yasa zaki nema min abinda zuciar ki take so baki neme shi ma kan ki ba dukda kina da damar yin hakan?"

"Aunty Yusrah ai nasan ko nayi hakan a banza ne tunda ya Safwan ba zai yarda ya jira ni har lokacin da zan isa aure ba" ta fada cike da kunya kanta a ƙasa tana wasa da yatsun ta,

"Wa ya faɗa miki? Waye ma yace miki baki isa aure ba? Tunda kin iya soyayya ai zaki iya zaman aure, wa yaga auta a dakin miji hehehe akwai show ashe" na ƙarasa tare da kwashewa da dariya ina tafa hannu,

Duk rashin ta idon Nasreen a ranar haka ta wuni muna wasan ɓuya, don ina ganin ta sai na saka dariya ina fadin "Auta amaryar dash dash" kan kace me sai kaga ta zara da gudu tayi ɗakin mu ko ɗakin mama,

Mama sam bata gane a kan meye nake tsokanar ta ba amman ko ma meye ne hakan yayi mata daɗi don rabon su da suga nayi dariya a cikin gidan tun ranar da nazo musu da labarin mutuwar Khamis,

**********

5:02 pm
Ya buɗe ido, jaɗe na zaune a ƙasa gefen shi kaɗan yana ta faman rubutu a jikin allo ga kuma ruwan wankewa a cikin ƙwarya a gefe, yana lura da ya farka a jiye abinda yake yi ya taso ya gyara mishi kwanciya tare da ɗan dago kanshi yanda zai zamo balanced yasan idan ba hakan yayi mishi ba yanzu zai iya cewa zai miƙe a kan ƙafafuwan shi,

Jaɗe na gama gyara shi ya dauki ruwa a cup din silver yayi addu'a sosai ya miƙa wa khamis ya sha sannan ya miƙo mishi abinci, wannan karon jallof ne na shinkafa wanda na musamman aka girka mishi kada su sake kawo mishi irin abincin su ya kasa ci,

Yanzu kam abin ya fara ɗaure ma Khamis kai, ga tsananin al'ajabin karamcin wa'innan mutane da basu ma san waye shi ba amman suke ta ɗawainiya dashi ba tare da gajiyawa ba,
"Tun yaushe ne kuka kawo ni nan gidan?" Jaɗe ya tsinkayi muryan Khamis yana faɗin haka,
Dagowa yayi da murmushi a fuskar shi yace "satin ki ukku jiya"

Zare ido Khamis yayi yace "three weeks? Amman me yasa kuka ɗauki nauyi na baku nemi dangi na sun kaini asibiti ba?"

"To ai bamu shanki bane Hamishu, bamu shan shu waye dangin nakki ba ashibitin karkarar nan kuma da nisha gashi suna da chada mu kuma bamu da kudi"
Shiru Khamis yayi don ya rasa abin faɗa ya dauki spoon ya saka cikin abincin da suka bashi yana tsakura a hankali kafin cann kaman wanda aka mintsila yayi saurin cewa
"To yaya za'ayi yau na shiga mota na koma Yola? Iyaye na zasu iya biya min kuɗin asibiti"

"Shiwon ki yayi zurfi Hamishu, va zai yiwu ki shiga motan kashuwa a haka ba"

"To babu yanda za'ayi na samu waya na kira gida sai suzo da motar su su ɗauke ni"

"Ai duk karkarar nan Yarima ne kaɗai take da waya kuma yanzu ita maƙiyin mu ce tunda ta shaki boɗɗi, ko munje ba zata yarda ta bamu ba"

Cike da rashin fahimta Khamis ya tambaye shi "wacece kuma boɗɗi?"

Share shi yayi kaman baiji tambayar ba yaci gaba da rubutun shi har saida Khamis ya sake maimaita tambayar shi, kafin ya amsa
"Boɗɗi ita she Saudatu ƙanwa ta da ya shigo ɗaju da shafe yana kuka"

In shock Khamis ya ƙara zare ido tare da faɗin "what? Kana nufin ƴar wannan tatsitsiyar yarinyar aka yi wa aure da wani yarima?? This little girl? Wannan ai rashin imani ne, dole auren ku ya dinga mutuwa da wuri ai yara basu kai sun kawo ba a dinga ɗaura musu responsibilities da ba iyawa zasuyi ba"

Murmushi jaɗe yayi yace "mu al'adan mu kenan Hamishu, da yarinya ya kai munzalin girma yanda Annabi s.a.w ya fada muke mishi aure saboda jaman shi a gidan iyayen shi a wannan lokacin bashshi da amfani, ban taba juwa birni ba amman anshe matan ku sai sun tsufa suke aure haka ne?"

Tsaki kawai khamis yaja ya maida kanshi gefe yana ƙunƙuni "azzalumai kawai irin ku ne kuke cutar da yara ƙanana idan kaje asibiti ka gansu cikin halin ha'ula'i saboda cututtuka da kuma yoyon fitsari idan suka zo aihuwa, Allah sai ya saka musu wallahi"

Jaɗe yaji shi sarai amman sai ya share maganar dukda ya sosa mishi zuciya, babu abinda suka tsana kaman wani bare ya zagi al'adan su ko kuma ya kushe su amman Khamis ko ba komai zaici darajan baƙunta da kuma rashin lafiya amman da ya nuna mishi ƙabilanci dan ta wurin ma ba'a barsu a baya ba,

Yana gama rubutun ya wanke ya ajiye a gefe matsayin na amfanin anjima sannan ya tashi yayi tafiyar sa ba tare da ya bari wani magana ya sake shiga tsakanin su da Khamis ba, shi kuwa tun lokacin tsananin tausayin boɗɗi ya kama shi matuƙa,

Idan dare ya tsala lokacin da mutane da dabbobi duk suka nemi mafaka dan huta gajiya shi kuma idanuwan shi biyu saboda zafi da raɗaɗin ciwo haka zai dinga jiyo sautin kukan ta, kuma cikin ko wani dare sai tayi bata gajiyawa, daman ba wani walwala yaga ana yi ba a gidan tunda yazo amman dawowar ta cikin gidan yazo musu da wani ƙunci wanda suke kwana kuma su tsahi tare dashi,

Har bayan wasu ƴan kwanaki idan aka ce wa khamis ya zayyano kamannin boɗɗi to an haɗa shi da babban aiki don tun ranar da ta shigo gidan baifi sau ɗaya ya sake ganin ta ba shima ɗin a fisge, lokacin ya fito yin alwala itama tana shirin fitowa daga ɗaki aiko tana ganin shi da gudu ta juya, har yau bata yarda sun sake haɗa ido ba da taji alamun shi a waje to bata fitowa har sai taji alamun ya bar wurin,............🤦🏻‍♀️

*Fans Ayi min haƙuri yau ɗinne nayi busy da yawa sai gobe zamu haɗu insha Allah*

Don't forget to follow
Vote
Share
And comment as you read 💖

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

29🧛🏽‍♂️
Tun Khamis yana ƙoƙarin zama a ɗaki domin barin ta ta sake agidan ubanta har ya fara gundura da zaman ɗakin shima kawai yaci gaba da fitowa kaman ko yaushe, idan dare yayi sai jaɗe ya taimaka mishi ya fito tsakar gida a haɗa wuta suna shan dumi saboda wurin akwai sanyi sosai,+
Satin Khamis 5 da kwanaki 5 a wuroɓokki malam Arɗo ya dawo daga tafiyan da yayi, saidai yana shigowa gari da labarin abinda ya faru da boɗɗi ya fara cin karo bai zarce ko ina ba sai fadan mai gari don jin ba'asi, ba zallan mai gari da mutanen shi ba harda shi yariman yaron da bai wuce shekaru 19 zuwa 20 ba suka zauna suka ci mutuncin malam Arɗo ta uwa ta uba da duk dangin su, basu barshi ba har saida suka tabbatar da ya zubda hawaye sannan hankalin su ya kwanta,

Da ya tashi tafiya suka ƙara mishi da wani kayan haushin, yarima da bakin shi ko kunyar idon shi baiji ba yace idan boɗɗi ta gyara halayen ta a faɗa mata zata iya zuwa ta bashi haƙuri ya maida ta ɗakin ta,

Malam Arɗo ji yayi a zuciyar shi kaman ya kama yarima yayi mishi dukan tsiya amman hakan ba zai yiwu ba, don bala'in da suke ciki yanzu kaɗai ya ishe su ba zai sake jangwano musu wani ba, saidai ya ɗau aniyar duk abinda zai faru boɗɗi ba zata taɓa dawo da kanta ɗakin yarima ba in dai baizo yayi bikon ta ba,

Da baƙin cikin abun a ranshi ya shiga gida, amman yayi iya ƙoƙarin shi ya danne nashi bacin ran saboda ya samu ya kwantar da hankalin boɗɗi, jikokin shi yaran jaɗe da yaron yayar boɗɗi sahura mai shekara 1½ wanda take wurin su saboda laulayin ciki da take fama dashi itama duka duka shekarun ta 16 ne, suna ganin shi suka ruga da gudu suna mishi oyoyo,

Boɗɗi kuwa tunda taji shigowar shi ta koma ɗaki ta rufe tsananin kunyar mahaifin ta ya kamata, itace mace ta farko a dangin su da ta taɓa yin aure ta fito kuma wannan tabon abin kunyan da tayi musu tun yanzu zasu fara ganin sakamakon shi ba tare da ɓata lokaci ba,

Zuwa jikin ƙifar yayi yana kiran ta a hankali da taxo ta buɗe mishi ƙofa bayan ya ajiye kayayyakin da yazo dashi, ya ɗauki tsawon lokaci a wurin yana lallashin ta da ƙyar ta yarda ta bude mishi ƙofar ya shiga ta koma ciki ta haɗa kai da guiwa tana ci gaba da kuka,

Yanda ta rame ta zagwanye gaba ɗaya saida ya bashi tsoro, harta yatsun hannunta saida suka gwada rama ga wasu gashushuwan wuyan ta da suka fito kaman wanda aka ɗaura mata necklace, gashin kanta da yake a bude yanzu ya zube don a yanzu iyakacin shi ƙasan kafaɗun ta kaɗan gashi ya sauya kala saboda datti tayi baƙi ta lalace,

Danne hawayen dake ƙoƙarin zubo mishi yayi ya ƙarasa wurin da take zaune ya durƙusa yana patting bayan ta a hankali tare da maimaita mata wa'innan kalman da yaren fillanci
"Kiyi haƙuri inna ta, shi rayuwa haka yake cike da darussa kala_kala, kuma wanda Allah yafi so shi yafi jarabta idan kin zubar da hawaye yau tilas wata rana zakiyi dariya"

A ko wani lokaci idan wani daga cikin mu yana cikin matsala kalaman da yake faɗa musu kenan, idan sun tambaye shi ma'anar haka sai yace musu wannan saƙo ne a dunƙule ga mai tunani,

STORY CONTINUES BELOW

Share hawayen idanun ta boɗɗi tayi tace
"Baba aradun Allah banyi laihi wa yarima ba, duk abinda tashe inyi mata ina yi amman kullum shai tashe banyi daidai ba kuma ta hukunta ni a kan laihin da ba nawa ba"

"Ba shai ka ranste ba boɗɗi, ni na yarda da irin tarbiyyan da na baka, ba yarima ba koma waye na shan zakayi mishi biyayya, Allah ya sha hakan shi yafi alkhairi"

Ta san mahaifin ta mai sauƙin kai ne da saurin fahimta, koda zata samu matsala da kowa a ƙauyen saboda wannan ta san shi a ko wani lokaci zai goya mata baya fiye ma da mahaifiyar ta, kwanciya tayi a ƙasan ta daura kanta saman cinyar shi wasu hawayen suna ci gaba da sintiri saman fiskarta tace

"kiyi haƙuri bani nashe mata ina so na dawo gida ba kora na tayi amman da bajan dawo ba shaboda bani shon kina jubar da hawayen ki a kaina"

Saurin share fuskar shi yayi da gefen rigan shi yana mamakin dukda ta bashi baya amman har ta iya ganewa yana kuka, ya jingina kanshi a garu yana dhafa gashin kanta a hankali yake maimaita
"Allah heini am boɗɗi"

Suna zaune a haka har bacci ya ɗauki boɗɗi irin wanda ta daɗe bata yi irin shi ba dan yau taji kaman an yaye mata rabin damuwar ta da ta samu ta fitar dashi, mahaifiyar ta bata taɓa bata wannan damar ba kullum saidai tace tayi haƙuri bata taɓa zama ko na minti ɗaya ta tambaye ta koda dalilin da ya saka Yarima ya koro ta ba, shiyasa takan zauna tayi ta kukan baƙin ciki dan ita kadai ta san abinda ke cin ta a zuciya,

Saudat na barcin ta a kan cinyar shi hinde ta kawo mishi abinci yaci yaci gaba da zama, bai daga ta ba saida tayi mai isarta ta tasho don kanta sannan ya fita yayi alwala yayi shirin sallar magriba, kada kuso kuga wulaƙancin da akayi mishi a wurin sallah kowa yaƙi hada sahu dashi duk inda ya ratsa sai kuga mutane suna darewa ko hanya idan yabi suna karo da wani sai ya juya ya da kasan sunga aljani, hakan kwata_kwata bai dame shi ba saboda ba sabon abu bane a garin anyi ma ƴan baya wa'inda suka fishi daraja ma ballantana shi da abun ya rutsa da ɗan mai gari guda kuma tun kafin ya dawo ma jaɗe ya kwashi wulaƙancin da yafi wannan sunci mutuncin shi ba kaɗan ba shiyasa har Khamis saida ya lura da canzawar yanayin shi,

Duk cikin abubuwan da sukayi mishi abu ɗaya da yaji suna faɗane yayi matuƙar ƙona mishi rai ga sosa mishi zuciya, shine laƙanin karuwanci da suke yi ma boɗɗi kuma yana da tabbacin maganar daga wurin yarima da iyayen shi ya samo asali, don a halin yanzu zasu iya yin komai don su ɓata mata suna idan har bata koma gare su ba,

A da malam Arɗo ya saka ma ranshi indai yarima yazo ya nemi yafiyar boɗɗi kuma ya nemi ta koma gidan shi zai haƙura ya barta ta koma, amman a yanzu ya ɗau alwashin ko kashe shi zasu yi aure ya haramta tsakanin boɗɗi da yarima HAR ABADA kuma yayi alƙawari ma kanshi da ikon Allah mijin da boɗɗi zata aura a gaba ba za'a taɓa samun irin shi ba a kaff ƙauyen wuroɓokki, sai ya fisu komai da komai zaiyi ma ƴarshi auren gata kuma auren jin daɗi koda kuwa zai rasa gaba ɗaya abinda ya mallaka,

Saboda wannan bacin ran, bai ko tsaya wani ɓata lokaci a wurin Khamis don ya tambayi asalin shi da kuma dalilin da yasa aka harbe shi aka jefa shi cikin kogi ba ya duba jinyar da jaɗe yake mishi kuma da alama akwai nasara a ciki don yayi ƙoƙari fiye da ganda malam Arɗo yayi tunani hakan sqi ya ɗan rage mishi wani ɓari na cikin damuwar tashi, yanzu ya samu asalin wanda zai gaje shi a likitanci na gargajiya koda bayan ranshi domin a da yayan jaɗe shine yayi asalin kwarewa amman yayi musu nisa saboda wani abu da ya taɓa faruwa da su aka kore shi daga ƙauyen shiyasa har yau bai sake waiwayowa ba,
sauran yaran kuma duk mata ne dukda suma baiyi ƙasa a guiwa ba yayi musu training sosai harta boɗɗi zata iya bada maganin cutar da baiyi tsanani sosai ba kuma a warke da ikon Allah kuma gwana ce wurin yin ruƙiyya don tun kafin tayi aure ta haddace al-qur'ani mai girma,

A daren ranar yayi albishir ma jaɗe na ya tashi daga matsayin mai koyo ya dawo mataimaki, kuma ya bashi damar haɗa maganin da suke amfani ma ko wani majinyaci da yazo gare su wanda aikin shi shine ya ɗago duk wata cuta da yake jikin mutum yanda zasu gano ta suyi mishi maganin ta, shiyasa ko wani lokaci suna alfahari da kalar tasu jinyan yafi na asibiti domin can idan kaje bayan ka kashe kuɗi maganin rashin lafiyar ka kawai zasu baka basu damu da a duba ko da'a kwai wani matsala ba,

Sati guda jaɗe ya dauka kafin ya gama haɗawa shima da taimakon mahaifin shi, zuwa wannan lokacin raunukan shi sun ɗauko warkewa so koda wani abu ya taso ba za'a samu wani matsala babba ba,
A ranar da aka fara yiwa Khamis wannan maganin yaga tashin hankali, gaba ɗaya lissafin shi saida suka birkita ya dinga kuka da idanun shi, shi tunda suka fara mishi jinya ko yaushe samun sauƙi yake yi yana ɗaɗa jin daɗin jikin sa amman a wannan ranar yanda yaga rana haka yaga dare shima bai san takamammen abinda ke damun shi ba,
(Ranar farko kenan)

Tunda suka ga alamun wani ciwo ya baiyana basu yi ƙasa a guiwa ba suka dage wurin mishi amfani da maganin, Sannu a hankali Khamis ya rikide daga cikakken mutum kamili mai tunani da rashi surutu zuwa wani ɓalɓal, duk ya gama sukurkucewa a yanzu kanma abin ya wuce tunanin malam Arɗo da jaɗe dan yaro ɗan shekara 5 ma yafi Khamis nutsuwa da hankali a yanzu,

Bayi duka bayi zagi amman kalli ɗaya zaka mishi ka gane cikakken mahaukaci ne, bayi da wani magana sai taɗin maman shi da kuma Yusrah, harta boɗɗi yanzu ta ƙagu ta san wacece Yusran nan da ko yaushe bakin Khamis bayi rabuwa da ambaton ta,

Kwanaki sun rikiɗe zuwa satuttuka, satuttuka sun rikiɗe zuwa watanni, yanzu haka watannin khamis 11 cus da barin gida yana ta faman jinya ba tare da sanin kowa nashi ba, harta mahaifiyar shi ta cire rai amman har yanzu, har gobe Yusrah bata cire a ranta cewa Khamis yana raye ba, bata fidda tsammani wata rana zai dawo gareta ba tunda har yanzu bata yarda shine ya mutu ba,

Amman tayi ƙoƙarin ganin ta rage damuwar ta ko dan well-being ɗin Jannat dole idan tana son bata kula ta mantar da wani shashin ranta abinda ya faru da Khamis, on the other hand Nasreen ta dage mata a kan idan har tana son ta yarda da auren ya Safwan kuma su juya akalan soyayyar shi zuwa gareta dole sai itama ta yarda ta koma makaranta don ta tabadar ma kanta da ƴarta ingantaccen rayuwa a nan gaba,

Yusran ma taji ɗaɗin hakan don dama tun a baya tana da burin yin karatu mai zurfi kuma tension din makaranta na saka ƙwaƙwalwar ta ya zama busy Kuma tunda ta yaye Jannat lokacin da ta cika shekara guda da wata 3 iyayen Khamis sukan dauke mata ita taje tayi sati kafin a dawo da ita ,yanzu haka ta kusan gama aji ɗaya,

Boɗɗi yanzu itace ta dawo kaman mai kula da khamis saboda yanayi na damina jaɗe ya duƙufa ma aikin gona saboda tun lokacin da aka kori yayan shi daga garin an hallaka musu da yawa daga cikin dabbobin su da suke kiwo ya dawo sai ɗaiɗaiku kuma abinda suke samarwa bai isa ya riƙe gidajen su gaba ɗaya ba,

Alhamdulillah, sauki ya fara samuwa sosai wurin Khamis bayan jinyar ciwon hauka da yayi na tsawon shekara guda harda watanni biyu bayan jinyan harbin da yayi, kuma a yau ne suka tashi da wani sabon fitinan wanda harda shi Khamis da abin bai shafa ba ya shiga cikin tashin hankali,

YARIMA YA MUTU kuma mutane sunyi rantsuwa a kan boɗɗi ce take maita ta cinye shi saboda yayi mummunan jinya sakamakon miyagun ƙwayoyin da yake musu shan hauka wanda sunfi ƙarfin jinin shi,
Tun safiya suka hana kowa kwanciyar hankali, ko masallaci babu wanda ya fita a gidan gashi Khamis har ya fara shirin tafiya gida nan da kwana 10, babu wani abu na cutarwa da basu yi musu ba su burin su kawai a fito da boɗɗi su ƙona ta kowa ma ya huta,
boɗɗi taso ta fitan ko idan sukayi nasaran kashe ta hankalin kiwa zai kwanta wannan tarzoman da suka tada zai lafa amman ƙememe Khamis ya hana ta, a daren ranar ya dauke ta da sanin iyayen ta suka lallaɓa suka bar ƙauyen bayan yayi musu alƙawarin zai riƙe ta amana........🤦🏻‍♀️

*Ummu Najma ce 😘*

(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)

😈 *MATAR KULLE* 😈

_(Thriller)_

_Short story_
©️2020 special

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/+

Blog : prowritersnovels.blogspot.com

Follow me on Wattpad @ayeeshatmuhd

*BY*
*UMMU NAJMA*

Nayi wani kuskure a cikin Wannan littafin 👇🏼

_Allah basira da kwarin ido👏🏼. Murna takoma ck🤦🏼‍♀️ Khamis yamutu yadawo ,nidai gsky bansoba ,naji anacewa Yusra tayi takaba bayan bb takaba akanta, inbamu mantaba alqali yaraba aurenta harta gama idda,kuma koda Khamis yadawo ba'ayi sabon daurin aureba asalima bbnta cewa yayi taje gata ga duniyarnan,ba mutuwa ne yadawo da ita ba bb wani takaba akanta koda mutuwar yy dagaske,Nasreen kikwantarda hankalinki kibar yusra dahalinta gata ga Khamis nan zaishayar da ita mamakinsu namaza kannan aljanu hhh😄 Anayi munajin..... Ummu Najma cigaba dagashi_
*Mmn zarah*

*Hakan ya faru ne a dalilin sauri da mantuwa saboda naso nan gaba na gwada cewa harta ɗaukan ta da yayi suka gudu ya haramta saboda ba matar shi bace, saidai idan mai karatu ya lura a daren bai take ta ba har aka shigo aka harbe shi, so idan ma mutuwa yayi babu takaba a kanta don already an raba auren su, kuma miji bayi taba maida auren da shari'a ta raba har sai idan shari'ar ne ta amince a gyara auren*

_dan Allah duk wanda ya sake ganin kuskure a wani wurin ya sanar dani saboda nayi saurin gyarawa kada mu ɓatar da wanda basu da sani a kai, na gode mmn zarah,_
_love You all so much_💖💖

30🧛🏽‍♂️ *(FINALE)*
Kallon boɗɗi Khamis ya sake yi tunda suka bar ƙauyen su take kuka ya ma rasa da wani kalma zai lallashe ta a yanzu, ba don ta faɗa ma mutanen dake cikin motar da suka zo a ciki cewa tare suke ba da zasu tunanin ko sato ta yayi, murya ƙasa_ƙasa yace

"Saudat don Allah ki share hawayen ki kada ki sake jawo hankalin mutane garemu, insha Allah nayi miki alƙawarin babu abinda zai taɓa samun ki zan kaiki wurin da za'a kula sosai ke dai kawai kiyi ta addu'a Allah yasa kada mai gari da mutanen shi su cutar da iyayen ki, ki bar kukan nan haka Please"

Gefen mayafinta ta saka ta faco majina ta goge shi sannan da same wurin ta share hawayen fuskar ta, Khamis dai kallon gwale kawai yake yi gashi sai warin man shanu take yi wanda take amfani dashi a gashin kanta, yamutsa fuska yayi tare da kawar da kanshi gefe lallai matan ƙauye akwai gyara ba kintsi ba gyara,

Tsara musu a daidaita yayi suka shiga ya faɗa mishi wurin da zasu je suka ɗau hanyar gidan maman shi, dan yafi so ya ajiye boɗɗi kafin yane gidan su Yusrah, tafiya suke yi yayin da ya zurfafa cikin tunani bai son yaya Yusrah zata yi reacting idan ta ganshi ba, bayi ma da tabbacin ko har yanzu yana da damar sake shiga rayuwar ta ko kuma ta sake abokin rayuwa, missing her is killing him, gaba ɗaya fargaba ya mamaye farin cikin da yake ciki na dawowa wurin ahalin shi da iyalin shi, fatar shi kawai Allah yasa Yusrah ta bashi dama ta biyu ya kasance tare da ita da baby Jannat,

A daidai ƙofar gidan mai napep ya ajiye su babu kuɗi a jikin Khamis don wanda suka fito dashi sun biya kuɗin mita shiyasa yace ma mai napep ɗin ya jira ya karɓo masa, dai_dai zai shiga ciki mai gidan yaci karo da wani mutumi yana fitowa, komawa da baya yayi ya bashi dama ya fito sannan sukayi musabaha yana mamakin yanda akayi wani mutumi da ba ɗan uwan shi ba ya fito daga gidan da mahaifiyar shi take zaune,

STORY CONTINUES BELOW

Tambayar shi inda wa'inda suka zaune a gidan suke yayi ya sanar dashi sun daɗe da tashi tun bayan mutuwar ɗansu suka bar gidan don dama gidan na haya ne, godiya yayi masa suka koma cikin napep ɗin yayi mishi kwatancen family house ɗinsu dan yana da tabbacin wurin ta koma,

Da isar shi family house ɗinsu ya samu yayun shi biyu suna tsaye tare da wani mutum da bai san ko waye bane suna magana, da fara'ar shi na ganin ƴan uwan shi ya fita ya ƙarasa wurin su yayi musu sallama nan ne fa suka fahimci waye a gaban su, kallon shi suka yi na tsawon sakwanni 4 kafin babban yayan shi yayi wani gardin ihu ya iba a guje zai shiga gidan, a garin haka ya zame ya fadi ya buga goshin shi a ƙasa,

Bai daddara ba ya sake yunƙurawa zai tashi, timm ya fadi wannan karon kunkumin shi ya buga a jikin ƙofar dake gate ɗin gidan, saida yayi haka yafi sau uku yana faɗuwa daga ƙarshe kawai ya rarrafa ya shiga gidan a haka yana ihun neman taimako,

Ɗayan yayan shi dake tsaye kuwa gwada shi yayi da yatsa jikin shi yana kyarma yace
"Kha...kha.. Khamis, mutum ne kai ko aljani?"

Murmushin ƙeta yayi yace "aljani ne kaima ka gudu"

Kafin ya rufe baki ɗayan mutumin da suke tare dashi shima ya tattara a guje, yayan nashi yazo guduwa caraf ya riƙo hannun shi yana sake mishi murmushi ai sai suma kawai ya faɗi a ƙasa rigijif,
Mai a daidaita yana ganin haka ya hankaɗo boɗɗi waje ya wurga mata kayan ta a 360degrees ya bar wurin,3

Juyowa Khamis yayi yana kallon boɗɗi dake zaune daɓas a ƙasa tana kuka, dafe goshin shi yayi yaja siririn tsaki shi kam an haɗa shi da aiki, ashe haka mata suke da raki? Ya tambayi kanshi, to indai haka ne Yusrah jaruma ce ko lokacin da yake cin uban ta sai ta ɓaci take kuka,

Haɗe fuska yayi yace "ke tashi mu tafi" ganin babu alaman wasa a fuskar shi yasa ta share hawayen ta ta miƙe tare da rungumo jakar ta a ƙirji ta bishi a baya suka shiga ciki, suka bar yayan shi da ya sume a wurin, kishiyoyin maman shi suna zaune a kujera ƴar tsunguno ɗaya tana gyaran shinkafa ɗaya kuma tana daka a tirmi suna ganin shi a saba'in suka zubar da shinkafar gaba ɗaya a ƙasa suka dukan su suka ɗuru daki ɗaya har suna karo da juna,

Shekara guda kenan harda ɗori bai samu nishaɗi irin na yau ba, ya tsaya yana ƙyalƙyala dariya harda riƙe ciki, boɗɗi dai kallon shi kawai take wannan mutumin ga tsoro ga abin tsoro, ita bata taɓa ganin yanda ake gudun mutum kuma yake jin ɗadin haka ba, anya wannan Hamishun ba aljanin bane da gaske kaman yanda ya faɗa??

Muryar shi ne ya katse mata tunani yana faɗin "biyo ni" ya ɗuru ɗakin dake gaban shi, shiga falon sukayi taga ya sake ɗuruwa wani ƙofa sai taja ta tsaya tsoro ya kamata sosai, ganin ya daɗe da shiga bata biyo shi ba yasa ya leƙo parlorn yace
"Ke fullo ba siyar dake fa zanyi ba, an fada miki ke a kasuwa ma tsada zakiyi? Ki shigo wurin mahaifiyata na kawo ki" ya ƙarasa tare da dage labulen ta hango mata kwance a kan gado da alama bata san da shigowar su ba tana barci,

Jan ƙafar ta boɗɗi tayi a kunyace tabi bayan shi suka shiga ɗakin ta nemi position a jikin garu ta ja ta maƙale kaman sabuwa soja, shi kuma ya ƙarasa bakin gadon ya zauna sannan ya fara taɓa ƙafar mama a hankali yana kiran sunan ta, bude idanun ta tayi ta zuba su a kanshi da sauri ta miƙe tana mishi kallon ƙurilla ta dafe ƙirjin ta haɗe da faɗin,

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, allahumma ajirni fi musibati waklifili khairan min ha, ya Allah kasa ko barci nake yi ya siffantu da gaskiya"

"Ba mafarki kike yi ba mama, gaskiya ne ɗanki ne Khamis a gaban ki, ina raye ban mutu ba kawai Allah ya nisanta ni daga gare ku ne amman gani yanzu na dawo"

"Tabbas Yusrah tayi gaskiya, duk cikin mu itace kawai bata yarda da cewa ka mutu ba kuma ta faɗa mana amman munƙi yarda saboda harda gawa an kawo mana da sunan naka amman ban ga fuskar shi ba, ashe ba kai bane wancan"

STORY CONTINUES BELOW

"Gawa kuma? Kina nufin an kawo wani gawa har cikin gidan nan akace nawa ne?"

"Ƙwarai kuwa, kaima ka san ba don munga gawan nan ba da ba zamu taɓa cire rai a kan dawowar ka ba, zanyi ta jira ko tsawon shekaru nawa zaka share baka dawo ba hope ɗin cewa kana raye ba zai fita daga zuciyata ba amman tunda ka dawo yanzun ma an gode ma Allah, Allah ya ƙara tsare min kai"

Da "ameen" ya amsa ta gwada boɗɗi tace "wannan yarinyar kuma daga ina?"

"Mama daga wurin da na fito take, ina so ki riƙe ta a wurin ki naje wurin Yusrah na dawo sai na baki labarin abinda ya faru don bayan ku babu wanda ya san da dawowa ta"

"To Shikkenan Khamis, sai ka dawo ɗin Allah ya tsare"

**********
Yafi 20 minutes tsaye a ƙofar gidan amman ya rasa abinyi, ga yara suna ta wucewa amman ya rasa da wani aika zai tura ɗan aikan, Yusrah zai saka a kira ko kuma mahaifin ta? Idan ya tura a kira ɗaya daga cikin su ace inji waye? Wanda ya mutu ya dawo? Ha'inin mijin ƴarsu mugu azzalumi?

Yana ta saƙe_saƙe a ranshi motar Safwan ya tsaya nesa dashi kaɗan, Nasreen tayi mishi sallama ta tattari kagan da suka zo dashi zata shiga ciki sai zuba ma juna murmushin love suke yi, Khamis bai lura da su ne a cikin mitan ba kuma suma basu gane shi ba har saida Nasreen ta kusa shiga kafin ya kira sunan ta,
tana juyowa sukayi ido huɗu da Khamis wanda ya mutu, ai bata san lokacin da ta saki kayan a ƙasa ba saboda ruɗu a maimakon ta shiga gida sabida tafi kusa da wurin sai ta juya da gudu ta koma motar Safwan wanda ya tsaya yaga shigan ta gida kafin ya wuce ta buɗe ta shiga zuciyar ta yana lugude,
"Lafiya Reen? Me ya baki tsoro haka, waye can kika gani kike gudu?"

Muryar ta na rawa tace "khaa.. Khamis ne, wallahi shine dan Allah kaje ka duba ka gani"

Safwan yasha mamaki da bayanin Nasreen amman ba sosai ba tunda shi ya riga ya san Khamis a wancan ranar bai mutu ba amman bai saka ran zai dawo ba"

Fita yayi daga motar a nitse ya ƙarasa wurin shi ya miƙa mishi hannu suka gaisa sannan yace
"Barka da dawowa Khamis, na san kazo wurin iyalin ka ne amman kana da tabbacin cewa ka shirya dawowa gare su kuwa?"

"Insha Allah, wannan Khamis din dake tsaye a gaban ka halayen shi ba irin na da bane, sannan ina godiya da baka maida iyali na sun zama naka ba"

Murmushi safwan yayi yace "ai ko nayi niyyan hakan Yusrah ba zata taɓa bari ya faru ba, ta duƙufa wurin jiran ka bata taɓa gajiyawa ba ɗan tsaya ina zuwa"

Ya koma mota yace ma Nasreen ta fito ta shiga gida ta nema musu izinin shiga, da ƙyar da suɗin goshi ta yarda ta wuce ta gaban Khamis da gudu ta shiga gida, tana zuwa taci karo da Yusrah tana shanya a kan igiya saboda bata da lectures da safe shiyasa ta kwashi wankin Jannat tana yi ita kuma tana zaune dabas a wurin tana cin sabulu yusran bata sani ba,

Tare Nasreen tayi tana tambayar ta lafiya? Saboda yanda ta shigo sai haki take,
"Aunty Yusrah ya Khamis ne ya dawo, gashi can a waje tare da ya Safwan",
Daukan hijab dinta tayi ko ƙarasa sakawa bata yi ba saida taje ƙofar gida sannan ta bude ƙofa ta tsaya tana kallon shi hawaye na taruwa a idanun ta, murmushi yayi tare da kiran sunan ta ai bata san lokacin da taji wani abu ya fisge ta ba sai jinta tayi a ƙirjin shi ta rungume shi tsamm a jikinta tana kuka mai tsuma zuciya,

Shima Khamis ɗin ji yake kaman yayi mata kuka, he knows that so much is going in her mind now amman yasha mamakin da Yusrah ta amince ta sake amsan shi bayan tsawon lokaci, she is truly a blessing to him, a die hard lover and a saint wife,

Da ƙyar ta sake shi suka shiga gidan wurin mama saboda baba ya fita sai rana zai dawo, har ƙasa Khamis ya durƙusa yana bawa mama haƙuri, da ƙyar da suɗin goshi, saida Safwan, da Nasreen, da Yusrah harda ya usman da ya dawo ya saka baki kafin da ƙyar mama ta yarda ta yafe mishi ya zauna jiran baba dan baiga ta tafiya ba,

*A taƙaice*
Ba'a saku wani matsala da baba ba ya yafe ma Khamis kuma ya amine Yusrah zata koma gidan shi amman bisa sharaɗin sai ya miƙa kanshi a psychiatric hospital an duba lafiyar ƙwaƙwalwar shi sannan an tabbatar da ya samu lafiya kaman yanda ya faɗa anyi mishi jinya, idan har babu wani matsala sai yazo su koma wurin alƙalin da ya raba auren su ya gyara shi, saboda a case ɗin da shari'a ta raba aure ita kaɗai take da ikon maida shi haka yake a musulune,

Daga gidan su Yusrah Khamis bai zarce ko ina ba sai psychiatry bayan ya faɗa musu labarin abin da ya sami boɗɗi da kuma dalilin zaman ta wurin mahaifiyar shi, ƙarshe itama a wurin Safwan ta samu labarin boɗɗin,
kuma shima Safwan ɗin yayi confessing cewa dalilin da yasa yayi ƙaryan gawan Khamis da na wani saboda bayi so a ɗaga hankali ayi ta zaman jiran tsammanin da babu tabbas amman shi da mahaifin Khamis ɗin sun saka a bincika musu gari_garin da kogin da aka jefa shi ya ratsa ko zasu yi sa'a a same shi,

1 month later
Jan numfashi yayi yana shafa fuskar ta da yatsan shi ɗaya cikin salo mai ratsa jiki murya can ƙasa yace,
"Na kusa mutuwa baby, banyi tunanin zan iya ci gaba da rayuwa a haka ba, babu ke a tare dani"

Murmushi Yusrah tayi tana taro numfashin ta dake ƙoƙarin fita daga jikin ta tace
"Ko yaushe kana cikin zuciya ta, baka taɓa fita daga cikin ta ba ko na minti ɗaya, so ka daina cewa bani tare da kai, my soul is always with yours"

Wani jan baki yayi yace "but my body is not with yours, i miss You like hell i just wanna be with you baby"

"Nasan da haka shi yasa ma na var Jannat a gida wurin mama, Yusrah taka ce HAR ABADA sai yanda kaga daman yi da ita, ummu Najma rufe mana labule ki gani"

(Uhhmm toh aunty Yusrah)
*TO BE CONTINUED*
_Sai mun haɗu cikin littafi na gaba mai suna ƘARAMAR BAZAWARA (cigaban wani sashi na matar kulle) a yanda zamuyi karawa ta biyu cikin wani salo mai rikitarwa, abun dai ba'a cewa komai😚 sai wanda ya gani, wanda zan fara rubuta shi kwanannan insha Allah_
*Dumbin godiya da tarin jinjina zuwa ga ƙungiyar PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION da mutanen dake cikin ta, jagorori kuma ja gaba wurin canza rayuwar al'umma*


Post a Comment for "MATAR KULLE COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...