Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KUSKURE NA CHAPTER B KARSHE

KUSKURE NA CHAPTER B KARSHE

- - Post a Comment

 KUSKURE NA CHAPTER B KARSHETsayawa tayi tana takaikawo a k'ofar gidan, " _Bugawa zanyi azo a bud'e ko kuwa in k'ira a waya azo a bud'e? Amma ai banason masu aikin nan Susan da zuwana_" Sakina tayita Sak'a da war wara a ranta.


 Ta d'au kamar mintuna 10 a tsaye bakin get d'in, iskar safiya sai kad'awa takeyi wata iskace ta taso me k'arfi wanda har sai da k'ofar get d'in ta bud'e ta rufe alamun a bud'e take, Sakina a hankali ta juya ta d'auka wani ne zai bud'e k'ofar ta ciki,  Ga mamakinta sai taga ba kowa a hankali tasa hannu ta tura k'ofar sai taga ta bud'e hakan ya Mata dad'i da sauri ta shige cikin gidan, kai tsaye part d'in Izzatu ta nufa, sai datayi jim a bakin k'ofar tana tunanin mezatace ya kawota da safiyar nan, zuwa can wata dabara ta fad'o Mata sai tayi saurin murd'a k'ofar ta shige falon  kawai

Tana shiga ta maida k'ofar Tasa Mata key sannan ta sauk'e ajiyar zuciya tana farinciki 'yan aikin basu san da zuwantaba, Bakowa a falon tasamu waje ta zauna ta d'au kamar 20 minutes tana zaune sannan ta tashi ta nufi kitchen d'in dake cikin falon.
*******

******

****

**

*

Izzatu ce kwance jikinsa kamar wacce takeyin barci, Ransa yamasa fari tas, Abun daya faru a first night d'insu hakan yasa yake ganin bazai ta6a samun izzatu a cikakkiyar budurwaba shiyasa yake danne feeling d'insa akanta  Amma sai a daren jiya Wanda yakasance shine first night d'insu yasamu izzatunsa a cikakkiyar budurwa yarasa inda zaisa farincikin dake ransa.

 Babyna, safraz ya fad'a yana shafa kan izzatu.


  D'aga masa kai tayi alamun na'am amma idonta a rufe


Murmushi yayi sannan yace, open your eye pls.

 Idonta ta bud'e amma sai ta kalli gefe , yakuma cewa, my sweet see my me  face to face pls.


A hankali ta rad'amasa a kunensa, Besty ina kunyanka allow me pls.


 Dariya yayi sannan yace, okay nagane mekike nufi musakeyin abun dazu da asuba ko? Sai ya Fara yaye bargon dasuka rufa dashi.


Da sauri izzatu ta mik'e ta dira dg kan gadon, amma sai taji kafafuwanta sun kasa takawa tasaki wani k'ara tana k'okarin wincilawa safraz yayi hanzarin tare ta ta fad'o jikinsa, Kuka tasaki tana k'ara k'an k'amesa.


Ganin hawaye a idonta yasa Safraz ya Fara rud'ewa dan yasan bawasa bane serious ne tunda tayi Kuka.

Gyramata kwanciya yayi ajikinsa cikin kulawa yace, Reality banason ganin tears in your checks ya marairaice fuska kamar wanda zaiyi kuka , sannu a hankali yasa harshensa ya Fara lashe hawayen dasuka gangaro kumatunta.


 D'agowa tayi ta kalleshi tace, My sweet kajimin ciwo inajin pain sosai dalilin tsayuwar nan danayi.

Wani bala'in tausayinta yaji dayasan zaiji Mata ciwo daya hakura dan da alamun  bada dare bane da safiyarnan ne daya kuma.........


  Binta yake da kallon k'auna ji yakeyi kaf duniya babu abinda yafiyemasa soyuwa irin Izzatu, Cikin sanyin murya yace, Reality hospital zamuje yana gama fad'in hk ya d'auketa cak yanufi toilet da ita.

Baifi kamar mintuna 23 ba suka fito tana rungume a hannayensa dukkansu d'aure da towel,  A kan gadon ya kwantar da ita, Mayukanta ya d'auko ya fara shafamata da k'yar yake iya daurewa ji yakeyi kamar yayita shafamata man kar ya gm sabida skin d'inta laushi dukda ba Fara amma ba fara bace tas amma skin d'inta yana d'aukar hankali hkm dirinta yana d'aukar hankali domin Allah ya hore mata boobs da body ko tfy take kowannensu yana zuji musamman body d'inta sai kacema tana sane take juyawasu,

K'uramasa ido tayi tana kallonsa ya tafi tunani karemasa kallo tayi safraz! ta furta a ranta jajayen le6ensa ta kalla

K'uramasa ido tayi tana kallonsa ya tafi tunani karemasa kallo tayi safraz! ta furta a ranta jajayen le6ensa ta kalla kamar Wanda yasa jambaki Amma dukda hk sajensa yafi burgeta ya kwanta kasancewar  shid'in farine tas hakan yasa sajen bak'i yayi gwanin sha'awa a farar fatarsa  idanuwan daya k'uramata ta kalla suna lumshe tamkar mejin barci, Ajiyar zuciya yayi sannan ya mik'e ya nufi sif .........

     Sannu a hankali ya fara samata kayan, bra yake k'ok'arin  d'auramata idonta a rufe hakan ya bashi damar karewa boobs d'inta kallo, pant .... Doguwar rigane irin roba me kwanciya ajiki ya bayyana shape d'inta yayi Mata kyau sosai

Cumb yasa yana  taje Mata gashinta Wanda yasauk'o har kafad'unta sai shafa mai, powder ya gogo da soson powder d'in yafara gogawa a fiskanta tana murmushi, sai lips stick daya samata a let6enta.


  Ido d'aya ya kanne Mata yace, yakikaga madam na iya kou?

 Dariya tayi sannan tace,  Kafinima iyawama dear. Safraz yace bari na shirya sai in k'ira doctor Hafsat ko sakina suzo su bamu magani kou?

  Sai daya shirya kansa tsaf sannan ya d'au wayansa ya d'auketa a hannayensa yanufi falo

A dai_ dai lokacin kuma sakina tana jera Abincin data girka a deining table, Safraz yana k'ok'arin zaunar da Izzatu a kan kujera yace, Wa nake gani kamar Likita (sunan da safraz yake fad'awa sakina kenan), ?

Sakina k'arasowa inda suke tayi tazauna a hannun kujera tana dariya tace, Uncle bakama bane nice ( Uncle take cemasa dukda kasancewar cousin d'inta tun tana yarinya idan yaje gidansu gaida momy yana siyamata su biscuits DA sweets shiyasa take cemasa uncle).

Sakina ta kalli Izzatu tace, ka tambayi Aunty kullum Nazo gidannan bana samunka shiyasa yau nayi sammako gashi har na shirya muku breakfast ma kuna bacci.


  Izzatu tace, hkne kam sakina akwai ziyara bakamar shaheda ba, Kice yau zamu yini muna hira abunmu.

  Safraz yace, Likita kinzo a dai dai dama Autynki ba lpy dm.

  Cikin kulawa sakina ta kalli Izzatu tace, Ayyah meyake damunta, Sai kuma kunya ta kama safraz yarasa me zaicemata duk suka Mata shuru.

Sakina tace, Hym wallahi kun bani dry sosai ni kuke kunya wai? Are you pregnant Aunty? a,a bacikine da itaba bari inje  inshirya wasu takardu a library sai ta fad'amiki, yana gama fad'in hk ya tashi ya biwata hanya da zata kaishi library d'insa.

Sakina tace, Aunty meke damunki? Izzatu tace, yayanki yajimin ciwone during sex inna taka inajin ciwone sosai wlh.

Sakina tace, Amma bakisha wani magani daya k'ara matsekiba ko shiyasa hk?

Izzatu tace, No

Sakina tace, to muje d'aki nadubaki sai ingane meza'ayi

Izzatu ba yadda ta iya dan tanajin ciwo sosai Wanda tasan taji ciwone.


Da taimakon sakina suka isa har d'akin,  ......….....


 Tana gm dubata tayi saurin kallon Izzatu tace, Anty?

Izzatu tace, na,am.

Sakina tace, Am um naga  nki a rufe da alama this is the first time you have a sex.


Izzatu batayi mamakiba dan tasan dole duk likitan daya Dubata sai yagane Amma taji dad'ima da yakasance sakinace ba doctor hafsat ba wato likitar familyn su safraz domin tana da tabbacin sakina yarinyace me sirri.

Izzatu ta kalli sakina tace, hkne sakina yesterday is my first night.

Sakina bata kuma cewa komaiba Kawai tayi hanyar toilet duk abinda ya dace tayiwa Izzatu sannan suka dawo falo.

 

Sakina tace, Anty banason 'yan aikinki susan nazo , bari nakira uncle akwai magungunan dazan rubuta yasiyosu yanzu,

 Izzatu tace, tom.

Library inda safraz yake sakina ta tafi, tana zuwa tasamu gu ta zauna bairo da paper ta d'auka tarubuta wasu magunguna sannan tashiga can ciki inda safraz yake yana Neman wani littafi ganin sakina yasa ya dakata.

 Sakina tamik'amasa takardar tace, Uncle wananan magungunan za,asiyosu yanzu tayi amfani dawasu yanzu, tana gama fad'in hk tanufi hanyar fita sai datazo dai dai kofa zata fice tajuyo tace, sannan a d'aga mata k'afa kamar kwana 2 kafin ta warke, murmushi safraz kawai yayi shima yabi bayanta.

Lokacin da sakina ta tafi library wajen safraz alokacin Abu me aiki tazo tana buga  k'ofar falon zata kawo musu breakfast, Izzatu taji d'an sauki sakamakon taimakon da sakina ta yimata dan hk da kanta taje ta bud'ewa Abu kofar  , Izzatu tacewa Abu "barshi zanshigar dakayan" Abu bayan ta gaisheta ta mik'o mata kayan tajuya ta tafi Izzatu ta maida k'ofar ta rufe.

A dai_ dai lokacin sakina ta dawo falon, kayan ta kar6a takai kitchen. Tana cewa yau nawa za,aci kun makara yan aiki Izzatu kuma na dry.

Bayan sun kammala breakfast safraz yaje d'aki ya d'auko jakansa sakina da tattare kan table d'in.


Inda Izzatu take yazo ya tsugunna ya rik'e hannayenta yace, Baby zantafi zanyi missing beauty na kissing d'inta yayi a kumatu sannan yamik'e tsaye itama mik'ewa tayi, tayi hugging d'insa  safraz yace, pls kikulamin da kanki my sweet. Har bakin k'ofa ta rakashi.


Sakina tace, uncle maganin pa naga shirin fita kayi.


Safraz yace, eh Zan aiko za,akawo.


Kamar bazasu rabuba yafita yatafi.

Suna zaune suna kallo suna d'an ta6a hira, Sakina tace , Aunty inason muyi wata mgn.

Izzatu tace, to sakina inajinki.

Sakina tace, Dan Alah aunty ki d'aukeni kamar yar'uwarki kifad'amin gaskiya karkiyi la'akari da mijinki zai auri yayata Dan Allah.

Izzatu tace, Shikenan sakina karkiji komai wlh na yaba da hankalinki nutsuwarki da iliminki Zan fad'amiiki iya gaskiyata.


Sakina tace, Anty meye tsakaninki da mijinki da har tsawon wannan lokacin bakutaba sex ba ? Gaskiya nayi mamaki sosai Dan soyayyah wannan nasan uncle yana sonki iya so, Amma meye matsalar Aunty?

Izzate dama tasan tambayar da sakina zatayimata kenan, Anan ta bata dukkan labarin sharrin da akayimata a Daren farko na aurenta DA irin rayuwar da sukayi ita da safraz.


 Sakina batayi mamakin jin komaiba domin dama taji momy ta fad'a.

Sakina Ranta ya 6aci matuk'a ta kalli Izzatu tace, wannan wasune suka kullamiki Dan cikar burinsu, Allah zaisaka miki kinyi kokari sosai wlh, Wallahi nayi bakincikin jin hk Amma Alhamdulillah Allah ya dai dai ta tsakaninku Sannan inson fad'amiki wata mgn Aunty karki karacin wani Abu da masu aikinnan zasu dafa   ki sallamesu kawai kice bakya bukatar masu aiki koda uncle da mami zasuce miki meyasa, Wlh ban yarda dasuba Aunty Dan Allah ki sallamesu  a yau.

Sun dade suna mgn akan lamarin dg karshe sakina taja ra'ayin Izzatu dacewa a yanzu anayin amfani da 'yankin mutum a cutar dashi tunda aka fara yimata hk gara ta zauna babu wasu 'yan aiki Izzatu ma ta amince da hk.

Zuwa can da Rana suna cikin d'akin Izzatu, sakina tanayimata guga Abu tazo falon tajere mata Abincin Rana wanda duk tasa guba aciiki, Izzatu har dakinsu Abu taje tamusu bayanin ta sallamesu badan sunyimata komai zasu iya tafiyama yanzu ma sannan ta dau dubu Hamsin ta basu.


Izzatu tana shigowa falon ta kwalawa sakina kira amma sai taji shuru bata amsaba, tace, Allah sarki masu aiki shikenan kuntafi sai ta karasa bakin deining table tana bubbud'e girkin da sukayi, lemon kwakwar dasukayine taga yaji marada ya burgeta sai ta tsiyaya a kofi takai bakinta zatasha.

Kamar walk'iya sakina tayi saurin fitowa dg toilet tayo falon, ganin Izzatu na k'ok'arin kai cup d'in lemo bakinta yasa ta arta dawani bala'in gudu tanufi Izzatu.

 Cikin zafin nama sakina tasa hannu ta buge kopin wanda tuni izzatu hartasa sashi bakan    bakinta tana k'ok'arin kur6ar lemon, Tas ! Kakeji k'aran fad'uwar kopin nan ya tarwatse a wajen lemon kuwa yad'an zubarwa izzatu a jikinta.

Sakina kirjinta ta dafe tana maida numfaahi domin hankalinta ya gama tashi, da izzatu tasha da tasan komai yariga yadagule amma sai ta godewa Allah da hkn bai faruba tana maida numfashi ta d'ago ta kalli Izzatu.

 Izzatu kuwa ta tsaya sororo tana kallon abun mamaki, sakina tace, Aunty menace miki d'azu , karki kuma cin duk abunda yafito a hannun wad'annan masu aikin, kiyi tunani sosai akan abunda yafaru dake dole wasuke ne suka shirya kuma wanda sukeda kusanci dakene So ki sallamisu kawai dan kar wani abu yakuma faruwa.  Sakina aranta tace"Bani da damar tona asirin mahaifiyata dana fad'amiki gaskiya aunty amma zan baki kariya iya iyawata kafin Allah ya tona musu asiri dan Allahba azzalumi bane".

Izzatu tana dariya tace, Sakina kin bani dariya wlh sai kace wanda zasu samin kuba acikin abinci, Karki wani damu su sukemin girki koyaushe, abundaya faru kuma yariga yawuce ai dukda cewar wanda yavkullamin sharrin ba hk yasoba so yayi ya raba aurenmu nida safraz amma kinga ikon Allah komai yayi dai_dai, Kizo muci abincin nan kawai babu wani abu dazai faru.


Sakina takalli izzatu tace, hne Aunty amma kije d'aki tun d'azu uncle yanata k'ran wayanki dakika fita, inkin dawo sai muci abinci.


Izzatu tayi hanyar d'akin da sauritana dingisa k'afa.

Tana tafiya sakina ta tashi da sauri ta tattara duk abincin tayi waje dazu duk ta juye a kwandon shara lemukan kuwa suma duk ta zubar, sannan taje kitchen ta wanke kwanukan sosai, Inda cup d'in ya fashe ta share ta goge wajen sannan ta koma kitchen ta fara shirya musu abincin rana julop d'in taliya tayi da kifi da lemon kwakwa, Har tazo deining ta jere kayan Izzatu bata dawo falon ba.Itakuwa uzzatu koda tashiga d'aga ta duba wayar bataga misscalled d'in safraz kamar yadda sakina ta fad'amataba sai tayi tunanin ko sakina ta taga tacemasa bata kusane kawai sai taje toilet tacire rigan jikinta daya 6aci ta watse ruwa,  Bayan tagama shiryawa cikin riga da sikita na atamfa kanta ko d'an kwali babu tayi hanyar falo sai kuma ta tuna, dawowa tayi ta d'au wayanta tayi dialing number safraz wanda tayi saving da suna _MY RIGHT CHOICE_ kan gado ta fad'a suka fara wayarsu wanda babu komai acikinta sai kalmomin k'auna dasuke fad'awa juna da bayyanawa juna yadda sukayi missing junansu.


  Sakina data kammala komai sai tayo d'akin dan taga meyasa izzatu ta dad'e hk, Rungume da fulo ta ganta kan gado tana wani lumshe ido.

  Sakina tace, Aunty nagaji da jira nidai zaje inci abincina nafa jin yunwa, har sakina tayi hanyar fita dg d'akin izzatu ta dakatar da ita.


  Tacan 6angarenne safraz yaji abunda sakina  take cewa shiyasa yacewa izzatu taje taci abinci,  Izzatu ta wani shagwa6e murya tace, My sweet kaima inason kayi lunch yanzu kaji.

Safraz  yace, to my queen kici abinci sosai ki kulamin da kanki, tace, tom realityna tayi mai kiss sannan ta kashe wayan.

A6angaren su Abu masu aiki kuwa, mamaki ya damesu musamman Abu domin ma'u dama tacire hannunta aciki dama shirin tafiya takeyi tabar gidan sai gashi tun kafin ta tafi izzatu tazo ta sallamesu.


Kai tsaye gidan momy su Abu suka tafi Afalo suka sameta a zaune tana kallo, Tayi mamakin ganinsu amma sai tayi tunanin ko aikin datasasune yayi kyau sukazo sanar mata, cikin fara'a ta k'ar6esu suka gaisa.


Tunkafin momy tace komai Abu ta kwashe komai ta fad'a mata, Nan momy tacika da matuk'ar mamaki har tanayin zufa.


   Momy fuska babu annuri ta kalli Su Abu tace, Kun tabbata bata gane wani abuba? Abu tace, wlh hajiya babu wani Abu damuka bari ta fahimta Abincin safema mumuka dafa kuma dashi suka karya, to da ranannan ne dai kawai tazo ta sallamu tace badan munyi mata komaiba hk kawai.


 Momy ta girgiza kai tace , lallai wannan yarinyar tawuce tunanina kodai bokantane yak'irata ya fad'amata kar taci? Hmmm ! Naga ikon Allah, kun tabbata safraz bazai dawo da ranaba kar muje ya dawo yaci abincin musha uku?


 Abu tace, Ah ! hajiya ai sam baya dawowa da rana, Abincinma d'an dai_dai iya cinta muka dafa dan ka taci tarage wani yaci.


Momy tace, To yayi , Allah yasa taci matsiyaciya kawai idan ma bataciba saina 6ullomata   ta wata hanyar, Kutashi kuje Abunku sai na nemeku.


  Nan suka mata sallama suka tafi.

Suna kan hanya ma'u ta kalli Abbu tace, Sai dai ta nemeki wlh dg yau babuni babu lamarinku.


   Abu tace, hmmm kaji dashi kai kad'ai.


 Dama idan baku mantaba, Su Abu mazane na mataba, Kasan cewarsu 'yan daudu shiyasa zaiyi wahala kaganesu idan sukayi shigar mataa

Wata rayuwace me cike da d'umbin soyayyah da kulawa  tashiga tsakanin safraz da izzatu, kullum cikin farantawa juna suke, Koda izzatu ta fad'wa safraz ta sallami masu aiki baice komaiba saima murna da yayi domin yana ganin hkn zaifi yimasa dad'i ya sake shida matarsa.
Momy kuwa tazuba ido taga wani abu yabiyo baya amma shuru har tsawon kwana 3 hkne ya tabbatar mata cewa izzatu bataci abincin da'akasa poison d'inba ba k'aramin 6aci ranta yayiba, Sakina kuwa kwata kwata tadena zama suyi hira ita da momy kullum tana d'akinta hk kawai sai tadinga jin haushin momy tanajin zafi da rad'ad'in abinda taso aikatawa hkm karima idan ta k'ira bata d'agawa ko tayi mata mgn ta social media bata reply.

Akwana atashi ya rage saura kwana 3 kacal d'aurin auren Safraz da Karima, Duk izzatu tashiga damuwa amma duk da hk safraz yafita shiga damuwa kullum cikin rarrashinta yake sam bayason damuwarta da da yadda zaiyi afasa auren da yayi domin shima bayaso ko kad'an tsawon sati 1 kenan baya zuwu office yana manne da izzatu kullum cikin rarrashinta yakeyi har ta manta da duk wata damuwa idan kaga yadda sukeyin rayuwa abun abun sha'awa.

Safraz ne a tsaye gaban madubi daga gani daga wanka yafito yana shiryawa, itakuma izzatu tana kan gado ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya tanata danne dannan waya.


Safraz yace, Baby har yanzu bakiga wayana ba kou? To kodai a waje na 'yarne.

Izzatu ta ajiye wayan hannunta ta kalleshi tace, a'a bayan fitankama daka dawo da wayar a hannunka sai dai ko wani wajen ta fad'a gashikuma a silent take ko ank'ira baza aji ringing ba matsalan.


Safraz yace wallahi kuwa tana silent sai dai kicigaba da dubamin kafin nadawo, Amma kibani aron wayanki idan na fita dole zanyi amfani da waya, My love kidubamin nawa pls kafin nadawo dan nasan anata k'irana.

Har bakin motansa ta rakashi ya shiga yaja yatafi sannan ta dawo ciki , Abun mamaki tana shigowa falon ta hangi wayartasa a k'asan deining table murmushi tayi tace, ko na k'irashine ya dawo ya d'auka har zata k'arashi sai kuma kawai ta fasa.Kai tsaye safraz gidansu ya nufa, a falo ya tarar da maminsa da momy sunata hidimar biki hk kawai yaji ransa yayi masa bak'i sam shi mantawa yakeyima wai jibi za'a d'aura masa aure da wata karima.


Bayan sun gaisane mami ta kalleshi cikin kulawa tace, Ina k'ranka a waya tun safe amma baka d'agawa meyasa?


Safraz yace, Wlh mami wayan nawane muka nemeta muka rasa a falo yanzuma sai wayan izzatu na d'auko dazan fito domin har yanzu ba'a gantaba.


Mami tace, hb ni nasan dama akwai dalili kaje wajen Abbannakune ?


Safraz yace, Yana nema nane? Bari naje 6angarensa.


Mami tace,  yanzu kam yafita sai dai zuwa gobe da safe.


Tunda suka afara magana momy taji cewa wayar izzatuce a hannun safraz taji wani dad'i a ranta dan tayi wani tunani tasamu damar kulla wani sharrin a yanxu.


A dai_dai lokacin karima tashigo tana wani rangwad'a da karairaya ganin safraz a falon, Abunka da mara kunya ganin momynta da mami bai hanaba sai tazo kusa dashi ta zauna.


Big bro barka da fitowa, Karima ta fad'a tana wani wawwara ido ita bata yaddaba tana fari da ido.


Wani haushinta ne ya kama safraz kamar yatashi ya bar wajen amma ganin akwai iyayensu awajen sai kawai ya daure yace, Yauwa karima  sauk'an yaushe ?


Nan takuma narkewa jin yana tambayan yaushe ta dawo tunaninta ai duk acikin damuwa da lamarintane yasashi yayi tambayar, Cikin kinibibi ta shagwa6e murya tace, Am d'azu da safe na iso lokacin da na sauk'a a Nigeria inata k'ranka kazo airport ka d'aukoni amma kak'i kayi receiving call d"ina why dear ?


Safraz da tuni haushinta yacikashi yace, Okay my phone got lose since morning, Wannan ma wayan my choice d'inace not mine yayi nuni dawayan dake hannunsa.


Wani irin haushi taji dataji yacewa Izzatu my choice wato magana yakeson fad'a mata kenan, tace hmm aiko ba yauba inna k'iraka baka d'agawa kuma kai baka k'irana why?


Safraz daya fara gakiya da maganganunta sai yayi k'asa_k'asa da murya ta yadda su mami bazasujiba yace, Wannan kuma bani da lokacinkine you know? Ya d'aga mata kira.

Takaici ne ya kama karima tun kafin takuma cewa komai safraz ya mik'e ya fice dg falon.


Mami ma ta tashi ta shiga d'akinta zata d'auko wani Abu, yarage falon dg karima sai momynta.


K'asa_k'asa momy ta fara cewa karima, ai bazama zakiyiba Tunda wayarta tana hannunshi kitashi kishiga ciki ki rubuta text message na Sharri iri_iri amatsayin kwartontane yaturo mata baisan cewa wayar tana hannun mijintaba  kidinga tura masa Sai momy tazo kusa da karima ta fara rad'a mata maganganu a kunne.


Mgn take rada mata ta yadda ba Wanda zaiji metake cemata, ganin mami ta nufo falon yasa karima ta mike ta nufi  dakin Shahida ta na shiga  ta fada kan bed tana dariya, wani extra sim tasa a wayanta sannu a hankali ta fara Rubuta messages a tsitstsinke tana ruwa zuwa number din Izzatu Driving yakeyi hankalinsa a kwance murmushi dauke a fuskarsa  a hankali ya shafa sumar kansa  I love you my Izzatu ya furta a fili tamkar tana gabansa,   yacigaba dacewa Ni nasan I can't survive without you! If I had lost you, my life would have be in troubled, But now Alhamdulillah you are the rest of my life... A dai dai kofar gidan jafar yayi Horn for a while gateman yazo ya bude masa, parking lot yanufa yayi parking motansa, maimako yafito yashiga cikin gidan sai ya kwantar da kujera yayi lay abunsa wayan Izzatu ya dauko yafara duba  pictures dinta yana yasakin murmushi.


Jafar dake  can upstair yaga shigowar safraz ganin shuru shigoba yasa ya sauko downstair ko zaiganshi.


  Hafsa ce  zaune tana bawa Afra abinci, ganin shi yana saukowa dg  upstair yasa tasaki murmushi tana cewa, Har  kayi baccin kenan?   Hmmm Dariya yayi shima sannan  yace, babu wani bacci dm  danakeji rigiman Afra yasa na gudu muku ya karasa mgnr yana lakutan kumatun Afra, momyn Afra safraz bai shigoba kenan ? Jafar ya tambayi Hafsa.


Kallonsa tayi  tace, eh bai shigoba amma niji budewa gate maybe ko yana wayane.

  Jafar yace, OK let me check yakarasa mgnr yana fita  a falon.

 Still yana kwance yanata kallon pictures dinta yaji shigowar jafar cikin motar,  Um da kyau Ango what are you waiting for you dabaks shiga  inside ba? Jafar ya fada yana kallon safraz.


Jin jafar yace Ango yasa safraz ya daure fuska yace, Ango wa?

Tuni jafar ya gano dalilin dayasa ya daure fuska dariya yayi sannan  yace, All the the world know that you are the groom of Izzatu, ya karasa mgnr yana murmushi shima safraz murmushi yayi tare da gyara kwanciyarsa  ya Dora kafafunsa kan sitiyarin motar sannan  yace, I stayed looking at her pictures.

[

 Dariya jafar yayi yace, Au bakayi satisfied da kallonta dakayi a gd ba ?

Safraz ya lumshe ido yana cewa, I always want to be with her, jafar yace,  that's good, To yanxu what's going on?

Safraz yace, wannan jarababben Aure  nazo  ne to seek your advice, jafar yace, About what?

Safraz yace,   gida daya zan hadasu ko separated?

Jafar ya kallesa yace, To ita  Izzatu ka tambayeta? Safraz ido ya narke kamar zaiyi kuka yace, Banason ina  Mata zancen Sam as I know you can tell what I suppose to do.

Jafar yace, wannan ma yy dai dai in my view you suppose to combine them sbd  bawai son karima kakeyiba da ace kana sontane sai ka raba musu gida but ka hadasu gd dy  is better hakan zaifi.

Safraz yakelleshi yace, Yarinyar bata da tarbiyya baka ganin zata  haddasa matsala?

Jafar yace, no Izzatu is a good lady banajin zata biye mata.


 Ajiyar zuciya safraz yayi sannan  yace, thank you my friend.

  Yana gama fadin  hk  messages suka  fara shigowa a wayar Izzatu dake  kan cinyarsa baida niyyar dubawa jafar ya kallesa yace, sako  sunata shigowa wayanka ka duba mana  kasani ko madam ce  ya karasa mgnr yana daga  masa  gira.

 Safraz yace, No ba wayana bane na Izzatu ne banga nawa  bane na dau  nata duk tunanina zamuyi wy  da Kai sai nagama kawai bari inzo gidan, ya karasa mgnr yana tashi zaune.

 A dai dai lokacin ma sakonnim sai sake shigowa sukeyi.

 Wanne irin  messages ne hk  waye  yake  son takurawa matata wayan ya dauka zai duba number din a boye  messages din ya bude.... Lokacin jafar ya bude motan  yafita yanufi wajen megadi.Walwalar fiskansa ya canza ganin boyayyen number hakannema yasa yashiga inbox din messages din ya fara karantawa:


_Hi my love_


_Sweetheart ina  fatan kina lpy? Ya kewata ko bakya kewata?_


_I really Miss you dear, inatason nakiraki naji muryanki amma kar inkira a gaban  mijinki inkin samu lokaci ki kirani kinji babyna_


_Ya mgnr damukayi ki sallami yan aikinki ina  fata  kin sallamesu domin inna cigaba dazuwa gidanki  watarana zasu ganni  asirinki zai kuma tonuwa kamar na first nigh dinki kuma sannan kicigaba da amfani da magungunan nan Dana kawo miki kullum zai dinga jinki a matse tamkar babu namijin dayake amfani dake_


_Yaushene Auren nasa ? Ina fata ba gd daya zaku zauna da kishiyartaki ba in gd dayane sai dai mudinga haduwa a hotel kenan_


_kullum mafarkina nagama karatu muyi aure  dake,, innayi nasarar kammala karatuna dolene ya sakarmin matata muyi aurenmu kou?_


Hannunsane yake ta rawa amma yakasa sakin  wayar ta fadi nan da nan kwayar idanuwansa suka canza dg  fari  zuwa jajajur gumine yaketa keto masa tamkar an watsa masa ruwa, shuru yayi ya kurawa wayar ido amma ya kasa cigaba da karanta sakon,  zuciyarsa tafarfasa takeyi   ranshi na kuna  kansa  ya kwantar kan sitiyarin motar sannan  wasu zafafan hawaye suka fara fitowa a idonsa.

A lokacin ne jafar ya bar gun me gadin ya nufo inda  safraz yake , shikuma me gadin da sauri  ya bude gate jin anayimasa horn dg  waje, driver din jafar ne yashigo yadawo dg  aiken  da akayi masa.


Kafin megadin yayi yinkurin rufe  gate din tuni safraz ya tada mota ya fita dg  gidan a guje jafar yana masa mgn amma ko kallon inda  yake  baiyiba, Ganin hk  yasa hankalin  jafar yatashi cikin hanzari ya karbi motan da driver dinsa ya dawo da ita yabi bayan safraz.

Gudu yakeyi akan titi reckless driving domin ko gabansa baya  gani sosai, He is driving at high speed jafar dake bayansa hankalinsa yayi matukar tashi ganin irin  gudun da safraz yakeyi duk tunaninsa ko wani Abu yasamu matarsane gashi ya rasa ta yadda zaiyi ya dakatar dashi hk  yacigaba da binsa kawai suna sheka gudu.

Cikin Sa,a suka isa  gidan da sauri  safraz ya fito da nufin ya bude gate ya Shiga nan ya bar motar bakin  gate ko makulli bai cireba balle ya tsaya shigar da ita, kuma batare dayasan jafar yana bayansaba, cikin matsanancin 6acin rai yashige gidan.
 Jafar yakara girgiza sosai ganin yanayin fuskar safraz da barim motar da yayi a waje, Cikin Abun da baifi mintuna ukuba ya shigar da motarsa data safraz tare da rufe  gate din shima cikin part din Izzatu yanufa cikin sauri.


  Izzatu tana zaune a falo  tana kallon hotunan bikinsu a wayar safraz, ko ina  tsaf tsaf sai kyalli yakeyi ga daddadan kanshi dake  tashi tako ina, wedding grown ce black color a jikinta tamkar wata amarya ga makeup data tsara a fiskanta tayi  matukar kyau sosai kallo  daya  kamata sai ka kara domin Izzatu irin  matan nanne masu sirrin kyau tana da diri me daukar hankali gashin ta data sauko dashi kafadanta sai ya kara bayyana tsantsar kyawunta, kasancewar TV a kunne yake  yasa bataji karan bude gate ba.
   Kamar dg  sama taji  anbude kofar tare da bugota da karfi, da sauri  ta kalli kofar shigowar yanayin dataga safraz yasa taji kirjinta ya buga dam!!! Amma duk da hk  nufarsa tayi  in dash ta fada cikinsa tana kokarin yin hugging dinsa, Cikin zafin nama ya hankadata gefe wata irin faduwa tayi ta buga kanta da karfi, take jini  ya fara fita  a goshinta ya wanke mata fiska  inda take ya nufa cak ya shako wuyanta ya mikar da ita,  zafafan maruka ya bata guda biyu left and right sannan  ya shaqe mata wuya ya fara cewa, Why you doing that to me? Cikin kakkausar murya, Izzatu menamiki ne hk  why you hate me too? why you marry me since you don't love me? Sai ya koma mgn cikin tsawa zuciyarsa natafasa , Dama ke mazinaciya ce  Fasika ? You deceived me I hate you wlh Izzatu na tsaneki I must kill you right now, tayi matukar galabaita tunajin abunda  yake  cewa har  hankalinta  yafara gushewa domin ya shaweta iya karfinsa, Dai dai lokacin jafar ya shigo dauke da wayar Izzatu da safraz ya bari a mota da makullayen motocin a hannunsa, Ganin Abinda ya faruwa da sauri  ya watsa abubuwan dake  hannunsa kan kujera ya nufesu cikin tashin hankali, Cikin karaji yake kara mai maita, Izzatu I will kill you kin cuceni kin cuci rayuwata Allah ya isa  bazan yafemikiba dama kasheni kikayi yafimini sauki rather than this thing, jafar dake saurarensa ya rasa gane  me kalamansa suke nufi, Safraz baka da hankaline meya sameka? Jafar ya fada lokacin dayake kokarin kwace  Izzatu dg  shakar dayayi mata, amma ina Sam ya kasa domin ya shaketa iya karfinsa har wani rawa  jikinsa yakeyi Izzatu kuwa nuti tagama fita  a hayyacinta idanuwanta duk sun firfito sun canza launi daga  fari zuwa jajajur ga jini har  zuwa lokacin yaki  dena fita  a goshinta duk jikinsu ya baci  da jini dg  ita har  safraz din, Wani yanayi jafar yashiga na tashin hankali da baitaba shigaba ya kasa kwaceta ganin safraz naneman yin kisa agabansa, Wani irin  mari ya kwashe safraz dashi da duk iya karfinsa yana cewa are you mad safraz? Are you in your sense? Kasaketa nace cikin daga  murya yake mgnr amma safraz kuwa ko ajikinsa tamkar badashi yakeba, Ganin hk  bazatayiba yasa jafar daukar wani kofin  glass dake kan table a tsakiyar falon ya bugawa safraz a kansa  wani firgitaccen zafi yaji yaziyarci kwakwalwarsa hkn yasa ya saki izzatu ya dafe wajen tare da runtse idanuwansa, Kasa tsayawa tayi da kafafuwanta luuuuu ta tafi ta fadi kasa da sauri  jafar yayo  kanta kafin yace wani Abu har  numfashinta ya dauke idanuwanta  sun kakkafe hannunta ya dg  amma yajisa a sake kan kofar hancinta ya kara hannunshi nanma babu fitar numfashi, jiki a sanyaye ya Mike tsaye ya kalli safraz dake tsaye yana maida numfashi hannunsa daya  a kan ciwon da jafar yaji masa akansa, Shikenan you killed her jafar yafada muryansa yana rawa  tear rolling down on his checks. Jin Abunda jafar yafada yasa safraz dawowa cikin hayyacinsa kamar wani me koyan tafiya ya fara dakawa zuwa inda gawar Izzatu take a kwance, a gaban  gawar yayi nail down, I firgice ya fara mgn, Izzatu ! Izzatu ! Izzatu dai tashi kiji wata mgn kinji, wlh zan yafemiki laifin dakikamin wlh da gaske nakeyi tashi kiji, sai ya fara girgizata ya fashe da wani matsanancin kuka mecike da manufofi dayawa shima jafar binsu yake da kallo  yana kuka marar  fidda sauti, Kwantar da kansa  yayi  yana bugawa akan kirjinta, Banso na kasheki da hannunava ba Izzatu I just pretend to kill you but I don't really mean  that,  wlh babu Wanda nakeso kamarki kaf duniyar nan I really love you with all my heart, why you did that to me? I forgive you forever my wife may Almighty Allah forgive you.
  A dai dai lokacin wasu jami'an lpy suka shigo cikin falon kai tsaya inda take kwance suka nufa wasu suka janye safraz suka dorata kan wani gado sukayi hanyar  fita  da ita, ganin hk  yasa safraz kara kidimewa yayi wajensu, Amma jafar ne ya dakatar dashi dacewa  don't you dare to fallow them cikin kakkausar murya, juyowa safraz yayi ya kallesa lokacin dayake goge hawaye sa hannunsa, Waye  ya kira ambulance ni matata bata mutuba pa  safraz ya fada yana shashshekar kuka, wani kallon tsana jafar ya watsa masa sannan  yace, You are in trouble wallahi! I never expect you can kill human being let alone your wife, what lead you to do bad thing like this? A dai dai lokacin sukaji jiniyar motar tafita dg  gidan, cikin sauri  safraz yayi hanyar  fita  a falon, jafar yakuma  cewa you will never reach them  idan ma ka bisu mezaje kace musu? Kaika kashe ko me? Cikin razana safraz yace atop saying I killed her she is alive up to now, Cikin bacin  rai jafar yace, I'm regretting knowing you in life safraz ! Amma dukda hk  I will keep your secret By virtue of your father's position, Mutuncin gidanku zai ragu awajen  al'umma tawani 6angaren km saboda mami zanyi shuru amma bayan hk  wlh zanso a hukuntaka, Safraz durgushewa yayi akan gwuiwowinsa yana matsar  kwalla ya kalli jafar yace, Don't say that jafar nima zanso a hukuntani kamar yadda nayiwa matata rayuwa na bayada wani amfani a yanxu koba a kasheniba nasan bakinci zai kasheni I hate myself nasan kaima yanxu ka tsaneni  duk Wanda yaji suma  zasu tsaneni to why I will stay at this world? I prefer death to life may Allah take my soul now Izzatu forgive me pls Allah ka yafemin na aikata babban *Kuskure* na yadau hukunci cikin fushi wannan shine Babban *KUSKURENA* ya karasa mgnr cikin matsanancin kuka yana buga  kansa  a kan tiles, Take jikin jafar yayi sanyi  zuciyarsa ta karaya ya karaso gunsa ya durkusa ya dafa  kafadunsa cikin sanyin murya yace, Safraz! safraz ya dago suka hada  ido jafar yacigaba dacewa Tell me what happened between you and Izzatu, Hannunsa ya km sukaje kan kujera suka zauna safraz ya sauke  ajiyar zuciya sai dasukeyi shuru na Dan wani lokaci safraz yana cigaba da zubar da hawaye daga  bisani yayi wiping eye dinsa ya fara cewa, Abundaya faru ada naso nayi keeping dinsa secret between Izzatu and me but now I must tell, Duk Abinda ya faru a daren farkonsu na aure  ya zayyanawa jafar bai rage komai ba, Jafar yashiga matukar rudani   da mamaki  safraz ya katseshi dacewa, Ta amsamin ta aika amma nayi hkr hkn yasa nakuma shiga  damuwa matuka  nayi tunanin  nasaketa har  na dau  bairo da paper nafasa saboda ina  matukar son Izzatu, Haka mukayita rayuwa duk tsawon lokacin nan Muna hk  har Allah ya dai dai ta tsakanimmu randa na fara kusantar Izzatu duk wani zarginta yafita a raina domin sai naji kamar nine nafara sex da ita Ashe tana amfani da maganine ba ta yadda zanyi nagane, Izzatu ta sallami masu aikinta wlh ban kawo wani daliline yasaba kasancewar yau banga wayanaba yasa na dau  nata  lokacin damuke tare a gidan naji shigowar messages yy yawa shiyasa na duba, Hannu  yasa ya dauko wayar Izzatu ya bude yabawa jafar Dan ya karanta messages din.

Karantawa yakeyi yana girgiza Kai gumi na keto masa duk AC dake falon, yayi matukar razana daya  karanta messages din wayan ya ajiye gefe ya sunkuyar da kansa kasa sun dade a haka bawanda yacewa wani kala, zuwa can jafar ya kalli safraz yace tashi muje hospital din kou, A sanyaye dukkansu suka nufi harabar gidan jafar yashiga mazaunim driver suka bar gidan zuwa JK HOSPITAL, wani private hospital ne mallakin abokin jafar Mahmud yasan ananne kawai za,a karbi Izzatu batare da jami'an tsaroba kuma muhmud zai rufa musu asiri shiyasa jafar ya rubuta message ya durawa Mahmud cewa yana bukatar ambulance cikin gaggawa, Dan yasan bazasu za,a sallaceta tunda iyayenta bass kasar zaifi kyau susamu Jana izarta  sunada bukatar ajiye gawarta a asibiti.

Doctor Mahmud ne atsaye akan Izzatu dake kwance a gado, wasu nurses biyu a tsaye a bayanshi, Sai daya  gm gwaje gwajensa sannan  yajuyo ya kalli nurses din yace, she has demised, da sauri  nurses din suka karaso bakin  gadon, Dayar ce  tasa hannu ta rufe  mata ido sannan  taja  blanket ta rufeta dashi.

  Dakin da ake  ajiye dead body suka kai Izzatu akasakata acikin bayan suncire mata dukkan kayan dake jikinta sun doshe hanci da hunnenta da audiga  sun samata wata powder, wani dogon akwati aka sakata aciki kamar durowa Sannan suka lullubeta dawani kyalle suka tura akwatin suka rufe,


Doctor Mahmud yana office dinsa a zaune jafar da safraz suka shigo jiki a sanyaye,  bayan sun zauna  jafar ya kalli Muhmud yace, Doctor sannu da aiki, dg  yanayin fuskar jafar doctor Mahmud yasan mutuwar ta jikinsace sosai danshi  Sam baisan safraz ba yana dai jin sunanshi agurin jafar amma baisan shi a fuska ba muhmud shima cikin kulawa da nuna alhini yace, Lpy jafar yakuma  Karin hakuri?


 Wani irin  bugawa kirjin  jafar yayi dammmm! Duk dayaga  a yanayin daka fita  da Izzatu amma bai gama fidda rai ta rasuba sai dayaji abinda abokinsa Mahmud yace anan  ya tabbatar da rasu, Safraz kuwa da darkarewa yayi ya kasa motsawa a inda yake a zaune sai yaji kamar ba dai dai kunansa yaji masa ba kasa wani yunkuri yayi idanuwansa suka kafe  kama bakinsa yakasa furta komai, doctor muhmud ne ya mike tsaye yacewa jafar, let's go. Mikewa jafar yayi yabi bayansa amma har sukaje dai dai kofar fita  Safraz bai biyosuba, Safraz kataso abinda jafar yafada kenan yajuya yabi bayan doctor, Da kyar yamike tsaye ya fara dakawa a hankali yanajin  kamar zai fadi kasa har yakusa isosu, Sun danyi  tpy kadan  suka iso  kofar wani daki da security guda biyu a tsaye a kofar kowanne  dauke da bindiga, dakin suka shiga  akwai mutane ma aikata su biyar  kowa  yana harkar gabansa wani daki suka kuma shiga  again, duk Safraz yana bayansu yana binsu Sannan doctor Mahmud yasa key ya bude wata kofa  ya shiga  jafar nabisa Safraz nabiye masa baya, Dakin duhu sosai muhmud yayi nufi wani waje ya dau  wata babbar fitila ya kuna, Dakin dauke yake dogayen akwatuna nasa  gawa Wanda zasukai guda talatin, numbers din dake jikin akwatunan ya fara dubawa gar tazo 15 a hankali ya jawo  kamar ya bude durowa, juyowa yayi ya kalli inda su jafar da Safraz suke tsaye yace, Bismillah! da murya kasa kasa hannun Safraz jafar ya kama suka karasa gurin sai dasuka karaso Sannan doctor Mahmud yasa hannunsa ya yaye kyallen da aka rufeta dashi yabude iya fuskarta, Idon safraz ne ya kai kan Izzatu dake kwance  idanuwanta a rufe  an toshe hancinta da kunenta da auduga,


Izzatuuuuuuuuu! Safraz ya fada da karfi kuma cikin razine, luuuuu yatafi da baya zai fadi jafar yayi saurin taroshe ya fada jikinsa ya suma.

 Da sauri  doctor Mahmud ya maida  akwatin ya rufe yayo  kansa suka kamashi suka fita a dakin,  Da sauri  sauran ma aikatan sukayo kansu ganin sun kamo Safraz a hannu gadon da ake  Dora gawa idan a fita da ita akai  suka dora  Safraz sukayi emergency dashi cikin sauri.


Sai da doctor Mahmud yabashi kulawa ta musamman sannan  ya auna  Bp Sa jininsa  ya hau  sosai Allurar bacci yayimasa  sannan  suka koma office dinsa shida jafar, Ajiyar zuciya doctor Mahmud yayi Sannan yace, Ai bansan yar,uwarsa bace  sosai hk  dabai kamata yamushiga dashi ba Allah sarki, Kallonsa jafar yayi yace matarsa ce , kamar bayason yin mgn. Allah sarki Allah yaji kanta da Rahama waye  ya aikata mt hk!? Cewar doctor Mahmud, jafar Rasa  abinda zaice masa yayi sai ya fara kame-kame um ah nima dai bansaniba, Doctor Mahmud gazing din jafar yayi Sannan yace, you are laying jafar look ! Kafadamin gaskiya Dan karmusamu matsala da Jami,an tsaron asibitin nan karban gwatan zai iya bamu matsala  ta inda baka tunani  tunda bata da file a asibitin nan kuma anan tayi jinyaba tell me the truth, ya karasa mgnr yana cire  glasses din dake idonsa, Badan  jafar yasoba ya fada masa cewa sun samu yar  matsalane a tsakaninsu Safraz yy zuciya ya daketa shine tsautsayi ya kawo ajali,  Arazane doctor Mahmud yake kallon jafar Sannan yace, Wlh if nasani bazan tabashiba Dana rabu dashi dg  suman ya zarce shima ta mutu ranshi a bace  ya fadi hk, Wato saboda abokinka ne shine zaka goya  mai baya a rufe  zancen ko to badani ammah jafar kabani mamaki wlh zaka iya goyawa zalunci baya kenan?  ya watsa masa wani kallo me kama da harara, A nitse jafar yace, No doctor try to understand me pls bawai abinda kk tunanina abisa *kuskure* ne, da masifa doctor Mahmud yace, Wane laifine zatayi masa hk  har data cancanci dukan mutuwa?   Ni sai yanxu nagane *KUSKURENA* dana karbi gwatar a asibitina duk tunanina accident ne wlh ina  dubata naga kisan hannune sabida  shaqar dayayi mata fatar wuyanta duk sai daya salube wannan za,a kira kuskure??? Ya karasa mgnr yana buga teburin dake gabanshi, innalillahi wa inna,ilaijirraju,,un  shine kawai abinda jafar yake  maimaitawa tare da dafe  kansa bawanda yakuma  cewa komai zuwa can jafar ya dago yace, shine Safraz Best friend dina danake baka blr kaji  nacema wlh to wallahi summa tallahi ba da ganganci hk  ta faruba ko cinnaka bantaba tunanin Safraz zai kasheba abun yazo da tsautsayine wlh Safraz is a moral person he cares about everyone around him moreover he is a very religion ni kai na ina  cikin damuwa over, the reason why I decided to seek your assistant because Dan gidan Alh Hashim Muhammad ne   his father is famous nasan kasanshi shiyasa nake  son rufe  mgn not because of Safraz is my friend you know?


Kai doctor Mahmud ya daga  masa sannan ya yace, Any way kasanar da iyayen yarinyar shima Safraz din ya samu hawan jini kuma yakamata yaga neurosurgeon (likitan kwakwalwa) saboda da alamun indai  kamilin mutum ne as you said lpy qlau bazai akaita hk  ba yafadi  hk  yana mikewa tsaye hanyar fita waje yy yana cewa komai tayi masa inhar yaji bazai jureba sai ya saketa shot and simple ya kara fadin  hk  yana fita a office din.


Jafar ya Dade a zaune a office din shi daya Sannan ya tashi ya fita ya nufi gidan su Safraz.
Mami zaune a falo  ita sa  momy Adama  sai gudanar da harkoki akeyi  a shirya wancan a kulla wancan wannan shu Shiga wadancan su fita  dukdan bikin Safraz da karima, Can dakin Shahida karima ce  ita da babbar aminyarta fauza wacce suke  karatu  tare a England fauza dake sun samu hutun 2weeks yasa fauza ta biyo karima Dan susha shagalin bikinta, Dariya suke suna shewa karima tagama bata dukkan labarin abunuwan dasuka kitsawa Izzatu fauza ce  tace, Ai wlh kina enter kiyo out da ita, ita din wa?  Karki raga mata ina  fadamiki kawata sai kin tsaya da kafarki ita din banza I'm telling you zakiyi nasara, dariya karima tayi tace hehehe ke! Rabu da bakin  halina  idan ya motsa zanyi maganinta jina  nakeyi dai dai da ita ai ita ganin kyantanam takeyi tafi kowa  Ammana nikuma...  Sai tayi shuru ganin sakina  tashigo dakin food is Read shine kawai abinda sakina  ta fadamusu tajuya ta fice , kallo  suka bita dashi fauza tace yanaga tana frown fin face karima tace, himmm hk  take da wannan bakin  halin nata  tare suka mike suka falon dukkan su suna deining  table suma  suka karasa suka zauna.

 

Bayan sun kammala suna zaune dukkansu a falon Jafar yashigo da sallama, cikin fara,a mami ta tare shi  gaisawa sukayi na Dan wani lokaci mami ta kalli inda Shahida take tace, Shahida kawowa yayanki drink mana, ahhh mami tabari nagode dama zuwani sai kuma yayi shuru yarasa ta inda zai fara

Kallonsa mami tayi ta gano  dumbin damuwa tattare  a fuskarsa har zuwa lokacin kansa na sunkuye ya kasa dagowa su hada ido, sakina da Shahida suna harkokin gabansu amma Anty Adama, Fauza, da karima hankalinsu ya kan mami da jafar.

  Cikin tausasa lafazi mami tace, jafar ko akwai wata matsalane?   naga kamar kanason yin mgn amma ka kasa fell Free I'm listening you ta fadi hk  tana cire  siririn glasses din dake idonta, Daurewa jafar yayi ya daugo ya kalli mami face to face har suna hada  ido sai kuma ya dauke idonsa ya kalli gefe,  ya fara mgn yanacewa, Mani Allah yayiwa Izzatu rasuwa  yanzunan safraz yana hospital a kwance ba lafiya, ya fada a takaice.


Duppppp Falon yayi tsit tamkar babu wani Abun mai rai acikinsa, Duk cikinsu babu Wanda baiji abinda jafar yafadaba amma dukkansu kokonto sukeyi anya kunansu ya jiye musu dai dai kuwa.


Sakina  ce  tayi Saurin zabura ta mike tsaye ta nufo inda jafar yake tana cewa, innalillahi wa,inna ilaihirraji,un  ta karasowa ta zube akan gwuiwowinta tace, Yaya jafar mekace? Anty Izzatu kace??  Lokacin idanuwanta na zubda kwalla, daga  mata kai yayi alamun eh shima yana kokarin goge kwallar dake dg  idonsa, wani kuka tasaki me ban tausayi tana kifa kanta akan kujerar da jafar yake zaune, Mami tuni ta nemi ganinta  ta rasa sai data laluba inda tasa glasses dinta ta dauka tasaka Sannan ta fara gani dashi-dashi    kallon jafar tayi tace, ja     far Iz za tu na ta ra    su  kace?? Hawaye nabin fuskarta, kuka takeyi  sosai tamkar ranta  zai fita, Shahida fadawa tayi kan kujera itama tasaki wani kuka da karfi, Aunty Adama wani yanayi ta shiga  Wanda tarasa gane  na farincikine ko tsoro amma sai zufa takeyi, Sakina  kuwa indan  banda dukan uku-uku babu abinda kirjinta yakeyi tsoro yabi ya mamayeta jitakeyi kamar za'agane abunda   sukayi, fauza ma hk  ne anata bangaren tsoro ya cikata sosai.


A dai dai lokacin Abbansu safraz yashigo falon yana rike da hannun Shahid, turus yayi ganin yanayin

Mutanan dk parlour wasu na kuka wasu sunyi jugum jugum, Idonsa ne ya kai kan jafar  dake zaune kan shi a sunkuye takawa yayi yakai izuwa tsakiyan falon izuwa lokacin shima fargaba tab cike da zuciyarsa domin ganin yadda mami take kuka.

A lokacin Anty Adama tasa hannu tawani mutsitstsika idonta zata  kakalo kukan karya  ta fara cewa, Innalillahi Kai duniya ina  zaki damu  ayyah Izzatu yarinyar arziki diyar albarka kwana ya kare sai ta fashe da kuka ta kalli inda Alhaji Hashim yake tsaye tacigaba dacewa,  Ayyah Alhaji yanxu nan mummunan lbr ya riskemu Allah yayiwa Izzatu rasuwa  tacigaba  da yin kuka kamar gaske, Alhj Hashim inda mami take ya kalla cikin rudani yace, Ah ni ah ban ganeba wacce Izzatu kuke nufi? Caraf Anty Adama takuma cewa, Alhj wacce Izzatu ce  damu idan ba matar safraz ba, wayyo mutuwa gamu manya meyasa bazaki daukemuba kibar matasa su muri rayuwa suma  Ayyah rayuwa Izzatu Allah yamiki Rahama Allah yasa can yafimiki nan Allah ya yafe  miki yarinyar arziki duksan da naje  gidanta  ta tareni tamkar mahaifiyarta ta karramani har inajin dadi karima tasamu abokiyar zama ta gari Ashe Ashe zamuyi babban rashi tacigaba  da garzan  kukanta Abu kamar gaske.

Alhj Hashim shima dabaya yaja  yasamu kusa da jafar ya zauna, yanata mai maita innalillahi wa,inna ilaihirraji,un  sai da aka dau tsawon kamar mintuna goma bawanda yacewa wani qala sunata sharar hawaye, zuwa can Alhj Hashim ya dubi mami yace, ya isa  hk mami you have to stop crying the best she needs now is prayer, ya fadi hk  yana goge kwallar dake idonsa da handkerchief din dake hannunsa.


Sakina  ya kallah da Shahida yace, kudena kuka ya isa hk pray for her, shima Shahid sai goge nass  hawaye yake yacigaba dacewa, Indeed we belong to Allah, and indeed to him we will return. Killi  nafsin za'iqatul maut, may Almighty Allah rest her soul, May Allah forgive her jafar dake gefensa yace, Amen.

  Murya a dashe mami ta kalli jafar tace, jafar what happened to her? Nasan lafiyanta qlau da safen nan Dan bayan da Safraz ya bar nan munyi waya  da ita banji  wani alamun rashin lpy a tattare  da itaba hkm  Safraz har ya bar nan baicemin tana rashin lpy ko wani abuba.

  Sai da jafar yaji fafuwar gaba amma cikin dakiya ya kalli mami yace, nima  bansan meya sametaba mami, caraf Anty Adama tace, shi ajali inyayi kira koba ciwo dole aje.

  Alhj Hashim yayi ajiyar zuciya Sannan yace,  Allah ya Mata Rahama wlh na Dade banji  mutuwar data girgizaniba irin  wannan jiyapa muka gama waya da mahaifinta yake cemin yau zasu sauka a Nigeria nake  cemasa indai  Dan Daurin Auren Safraz ne wlh yabari andauke  masa Sam yaki yadda wai yaza ayi daurin aure  babu waliyin ango hk  mukayi sallama akan yau zasu iso, yanxu wannan zasuzo su tarar  nashiga rudani ya karasa mgnr yana yana sauke wata ajiyar zuciyar, Sannan ya kalli jafar yace, ina  Safraz?  A sanyaye jafar yace, yana can hospital din shima ba lpy.
Karfe  4:00pm dai dai suka sauka  a Airport dukkansu fuskokinsu dauke da fara'a musabbin farincikin nasa  bai wuce ayau zasuga 'yarsu daya wato Izzatu, Suna fitowa ta Arrival yazo ya taresu ya karbi wani Dan keke dasuka Dora jakunkunasu akai suna turawa karasa tura keken yayi har inda motarsa take Sannan yasa jakunkunan a boot,  murmushi dauke a fuskarsa yace, Yaya sannunku da hanya Prof Abdullahi yana murmushi ya kalli kanin nasa  yace, Hanya Alhamdulillah Abbas ya muka sameku? Wlh lpy qlau Yaya Abbas ya fada, Hajiya Rukayya ta kalli Abbas tace, naga duk ka kara tsufa Dan wata2 nan da ban gankaba ta karasa mgnr tana dariya, Abbas yace, Ah bawani Anty kawai kedai kice kin saba ganin fararen fata  a America yanxu kuma kinga  baki, dukkansu suka kwashe da dariya Sannan suka shiga  motar suka nufi gida.Abangaren Safraz kuwa shikadaine kwance a side room, Dakin dan medium ne hk  dauke da gado guda daya sai fridge a kusurwar gadon ta dama sai Dan dogon drawer a bangaren hagu sai  AC dake saitin gadon dayake kwance Sannan toilet dake kallon kofar fita, (wannan daki shi akecewa side room a hospital masu kudine ke  kama irin wannan dakin kuma bako a wanne hospital akesamu side room ba sai babban asibiti).


  A hankali ya bude eyes dinsa yunkuri yayi zai mike zaune amma yaji kansa yayi masa nauyi tamkar an Dora masa wani Abu akai,  Dukda zanyi  air conditioning dake dakin hakan bai hana Safraz yin zufaba sai panting yakeyi kamar Wanda yayi gudu, da kyar yasamu tashi zaune Sannan yasa hannu ya cire  Karin ruwan dake daya hannunsa, yunkuri Yayi ya sauka  a kan gadon yaji bazai iyaba komawa yayi ya jingina da gadon yana maida  numfashi.Suna zaune a parlour bayan sun Dan huta  sunci abinci hjy Rukayya ta kalli  Prof tace, Sai kiran number Izzatu nakeyi amma ba,a dagawa, Sighting yayi Sannan yace, maybe bata kusa da wayan ne basuna cikin bikiba ko kin manta, Frowning face dinta tayi Sannan tace, Me zai kaita bikin kishiyarta kaima da son mgn takarasa mgnr tana kuma dialing number din Izzatu, prof ya kalleta yace, kinga  matsalarku Ku mata ai yadan ja  gutun tsaki yasa hannu ya dau wayarsa dake ringing ganin surukinsa ne ke kiransa yasa yayi murmushi yayi accepting din call din,  Assalamu Alaikum Prof ya fada.

Daga  can Alhj Hashim ya amsa  sallamar tare dacewa ina  fata  kun sauka  lafiya.

Prof yace, Lpy Alhamdulillah Alhj yanxu nake shirin in kiraka inshedama munsauka.

Alhj Hashim yace, Masha Allah barka da isowa.

Prof yace, Yauwa barka dai ya shirin taro kuma?

Alhj Hashim yace, Taro gashinan anata shiri, sai kuma yayi shuru na Dan wani lokacin yarasa  me zai cemasa zuwa can yace, gamu ma a asibiti Safraz babu lafiya.

Subhanallah !!! Meyasa mesa? Cewar  professor Abdullahii.

Ahj Hashim yace, gashinan dai muma  zuwanmu kenan asibitin.

Wanne hospital ne? Prof ya tambsya.

JK hospital ne, Alhj Hashim yabashu amsa.

Ganin isowa in sha Allah prof ya fada a takaice,  Sannan sukayi sallama.


Hjy Rukayya taji  dukkan abinda sukace kasancewar wayar a fee take, Shiyasa naketa kiran Izzatu bata daukaba Ashe Allah ya bashi lpy, prof yace Amen shirya muje Mu dubashi tashi tayi tashiga bedroom bata dadeba ta fito suka fice.

 Safraz yana nan zaune  Abbansu da jafar mami momy dama sakina  Shahid da Shahida suka shigo dakin,  Tunda daya kallesu bai kara dagowa Yakuma  kallon kowa  acikinsuba yanayin yadda yaga fiskokinsu yasan sunsan da lbrn mutuwar izzatu, Sunsan Nina kashe Izzatu? Shine tambayar da yayiwa kansa. Abbansu ne ya kaste masa tunani  dacewa sannu Safraz kayi hakuri Allah yayi mata Rahama, wani sabon kukane yaji yazo masa mamima hawaye take zubarwa tana Kallon yadda dannata yafita a hayyacinsa kowa jayayi ya tsaya jugum jugum.


 Ba'a dau wani lokaci ba Prof suka iso  hospital din shida matarsa, dakin da Safraz yake suka nema aka Kai su da sallama suka Shiga, Aunty Adam ce  ta amsa   yanayin dasukaga mutanan dakinne  yasa suka dauka ko Safraz yana shan jikine sosai, koda sukayi masa yaji bai amsaba sai wani fashewa dayayi da kuka, Prof ne yace haba Safraz Kai fa jarumine cuta  ai ba mutuwa bace  be patient my son sannu kaji wish you quick recovery itama Hajiya Rukayya cewa tayi, sannu Safraz Allah yasa kaffarane meyake damunka? Shuru yy Mata baice komai ba hkn bai dametaba  tunaninta jikinnasane yasa bazai

Iya mgn ba, kallon mami tayi tace, Hb  Hajiya meyasa zakina yin hawaye hk  zakina karyar mai da zuciya ai Ayi hakuri Allah zai bashi lpy.

  Hajiya Rukayya kasa hakuri tayi ganin bataga Izzatunta ba yasa ta Dan numfasa tace, izzatu batana nan kenan nakikkira wayanta bata daukaba  nayi tunanin ko zamu sameta dan batasan yau zamu dawoba ban fada mataba Dan nayi mata bazata, Ganin babu Wanda yace Mata uffan yasa tace, Niko kodai akwai wani Abu daya faru bayan rashin lpyr Safraz ne? Ta karasa mgnr tana sauke  idonta akan Safraz da idanuwansa a rufe  amma tears sunta rolling in his checks.

 Dai dai lokacin Doctor Mahmud ya shigo, Har gaban  Ahj Hashim yazo ya tsugunna Dan dama sunsan juna sosai  yace, Ina wuni Alhaji ya hakuri kuma?  Sai dayayi kamar bazai amsaba domin yarasa  tayaya zai tinkarisu ya fada musu rasuwar yarsu, a sanyaye yace lpy doctor hakuri Alhamdulillah. Doctor Mahmud yakuma  cewa, Allah yy mata Rahama Allah yasa ta huta. Alhaji ya amsa da Amen.

Doctor inda Safraz yake yanufa danya cire  masa ruwan daya daura masa.

 Prof ne ya kalli Alhaji Hashim yace, wacece ta rasu? Itama Hajiya Rukayya a matukar firgice  tace wacce ta rasu? ........


Iz za tuuuu.....   Jafar ya fada Mauryarsa na rawa  dasauri suka kallesa Hajiya Rukayya ta Mike tsaye a razane shima Prof mikewa yayi, Allah yayiwa Izzatu rayuwa a yau dinnan sai dai hakuri Alhaji Hashim ya fada yana sunkuyar da Kai kasa.


Innalillahi wa, inna,ilaihirraji,un  shine abinda Prof ya fada yana cire hular dake kansa hawaye ya cika idonsa amma bai bari sun gangaroba yayi sauren sharesu, Itama Hajiya Rukayya bakinta na rawa  tace, inn..lillahi.. Bata karasa ba kuka ya kubce mata me tsananin gaske.


The terrible day !!! The day of sorrow!!! Bad moment !!! The most  Painful day in their life, they missed their only daughter izzatu they are very sad.


Cikin dakiya da dauriya  Prof ya goge idanuwansa ya kalli Safraz dayake ta garzar kuka yace, ya isa hk Safraz you should stop crying, I pity you I know how much you love my daughter izzatu but Allah loves her More then us,  our prayers she needs now pls wipe your eyes. Yajuya ya kalli Hajiya Rukayya ma yace, Rukayya ban yadda ki kara zubar mata da hawaye ba nothing is more painful to me then tears in your checks stop crying this an Oder from me.

 Sai a lokacin doctor Mahmud ya gane  sune  iyayen marigayiyar take yaji wani tausayinsu ya saukar  masa a zuciya ksllonsu yake cike da tausayi Dan ko kadan  baya tausayin Safraz saima haushinsa da yakeji.


Doctor Mahmud ne ya katse shurun dakowa yayi dacewa,  Sai gobe  za,a karbi gawan ko? Alhaji Hashim yace, eh doctor in Allah ya kaimu yanxu yamma  tayi, Doctor meyake damunta Wanda yayi leading to death in haste hk? Take jafar yashiga wani yanayi na rudani Safraz kuwa tuni ya gama saddakarwa kawai shima akashesa.


Shuru doctor Mahmud yayi, Ahj Hashim yakuma cewa, doctor menene ya dameta  jafar yace, bai saniba Safraz kuma nasan bazai iya cemana komai ba wannan mutuwa ta farat daya dukda in lokaci yayi Dole ko babu ciwo dole za,a mutu, dukkansu shuru sukayi suna saurarensa.


Doctor Mahmud ya nisa yace jafar kuyi hakuri I can't hid  the truth, marigayiyar batayi jinya a hannunmu ba ko lokacin da aka kawota tariga ta rasu ko tun acan  gida ko akan hanya, Dana takura jafar yafadamin menene yasameta Danna ciwon dake jikinta tamkar ba accident bane dukane  yacemin sun samu sabani da mijinnatane har ya daketa wannan shine sanadin rasuwarta.


 Tun kafin doctor ya gama fada Safraz ya sauko dg kan gadon ya durkusa akan gwuiwowunsa yana zubda hawaye wani bayan wani.


Kowa da abunda  bakinsa yake furtawa na dg  addua mamice ta rushe da wani irin kuka Hajiya Rukayya kuwa idonta kafewa yayi hawaye suka kasa fitama kawai kallon Safraz take zuciyar ta na bugawa, Prof kasa motsawa  yayi kamar an shukasa awajen  hk  ya tsaya sai kafafunsa dasuka dau rawa, sakina  Shahida Shahid  razanace ta bayyana a fuskokinsu  har Anty Adama sai data razana.

Alhaji Hashim ne ya tako  yazo Gavan Safraz ya tsaya yana Kallonsa sai daya Dade tana yimasa wani irin kallo Sannan ya daukesa da wani gigitaccen  mari ya hau dukansa baji ba gani yana kuka yana cewa, let kill you too I'm regretting get you as my son, Ashe ban saniba kai mahaukacine, are you in youth sane Safraz zaka kashe yar  mutane?  Da kyar Prof ya janye Alhaji Hashim dg  kan Safraz duk kuwa ya fasa  masa baki da hanci jinine kawai ke fita fuskarsa tayi jajawur.


Afusace Alhaji Hashim yayi waje yabar dakin, Cikin abinda baifi mintuna 10  ya dawo da police uku a bayansa,  inda Safraz yake ya nuna musu sukayi kansa suka samasa ankwa a hannayensa, malam tashi daya dg  cikin police din ya daka masa tsawa, da kyar ya iya mikewa tsaya hajijiya na kwasarshi, Abbah !! Safraz ya fada yana kallon mahaifinsa yacigaba dacewa, I know I'm guilty but I beg you for the sake of Allah do me a favor Inason in halacci zana izar matata  ya karasa fadar haka  yana daga  hannunsa alamun yana roko, cikin tsawa Alhaji Hashim yace kufita dashi, Prof zai mgn shima ya dakatar dashi, suka fice  da Safraz Wanda da kyar  yake iya takawa yana tafiya yana tangadi kamar zai fadi.

Ranace ta bakinciki da zubda hawaye, domin both site dukkansu yadda sukaga dare hk  sukaga rana kowa yana juyayin abun azuciyarsa, kowa hankalinsa ya karkata Neman dalilin dayasa Safraz aikata hk  saka  da warwara kowa yakeyi a zuciyarsa summan mutane uku mami, Hajiya Rukayya sai kuma sakina.


Mami tunaninta yaki tsayawa  a waje daya tayi kuka har idanuwanta sudena zubda hawaye headache mai karfi da fever suka rufeta, ta kure iya tunaninta tana son dalilin sanin  meyasa Safraz ya kashe matarsa, tunaninta yafi  karkata akan Karin auren da zaiyi ko shine ya haddasa matsalar wannan shine abinda tunaninta yafi  bata, " ko Izzatu tayi masa wani abune daya fusa  tashi yayi zuciya domin tasan  Dan nata  akwai matukar hakuri amma fushinsa bashi da kyau,   inhar sadin Karin auren nan ne hk  ta faru to tabbas nayi danasani nice sila Keenan? Tunda Nina tilasta shi badasan ranshi ba" sake-saken da mami tadinga yi kenan domin ta Dorawa kanta  alhakin salwantar ran Izzatu da sanya  danta  cikin wani hali, Nan sabo kuka yazomata tayi tayi har asuba.Itama Hajiya Rukayya tunaninta bai wuce akan Karin auren da Safraz zaiyi ne hk  ta faru, tayi kuka kamar ranta  zai fita tun  Prof yana rarrashinta har yafara yimata fada, hk  suka kasance suma  har asuba.Sakina  tashiga matsanancin damuwa domin duk tunaninta ya sauka  akan mahaifiyarta da yayarta sune  abun zargi a zuciyarta duk dataji ance  Safraz ne amma zuciyarta tana bata wani mummunan abu suka sake kulla mata adaren ranar sakina tayi kuka Wanda bata taba  yin irinsaba hk  take ta saka  da warwara har gari ya waye.Safraz daya tsinci kansa arayuwar dako  a mafarki bai taba  tunanin ba wato police station dakin da aka sakashi Dan karamine ko kafarka bazaka iya mikewaba, black T-shirt a jikinsa me karamin hannu hakan yasa sauro suka samu daman cizonsa hannayensa har fuskarsa wani hawari dakin yakeyi hakan yasa baibi ta kan cizon da sauron sukeyi masa ba ya hau  vomiting kamar zai amayar da hanjin cikinsa, Abunka da Dan Hutu tuni yafita a hayyacinsa ya galabaita tamkar Wanda yayi one month bashi da lpy,  sai spiting yakeyi kamar mai ciki duk inda sauro yayi biting dinsa daya itching sai wajen ya kumbura, su biyarne a adan  karamin dakin sauran hudun sunyi barcinsu a tattakure sai snoring sukeyi very soundly, Snoring dinsu yabi ya cika masa kunne yadda yaga rana hk  yaga dare a rakube a zaune yana wiping tears in his eyes.Fauza ce  zaune a gefen gado tayi tagumi tana kallon karima dake kwance on bed tana baccinta hankalinta kwance, Mami da fargabane suka cika mata zuciya ganin abinda kawartata ta aikata har yayi sanadin salwantar rai, A hankali ta sauke sight tana Dana sanin biyota gidansu datayi  anya bazata shirya  gobe  tawuce gombe ba domin a gidansu babu Wanda yasan tazo Nigeria, dama karima ce  ta dauki  duk wani responsibility data akan ana gama bikin su koma bawanda yasan tazo, duk son duniyanta sai take ganin bazata iya aikata abinda karima da mahaifiyarta suke kullawaba da hk  taja blanket itama ta kwanta.Shima Jafar haka take a bangarensa matarsa tana zaune gefensa tana tayashi jimami mutuwar izzatu tayi matukar girgizata Dan dan zaman dasukayi na two months sun saba sosai sun zama cloth friends, ta zubda hawayen rashin izzatu sosai Sam lbrn da mijinta ya bata bata yadda dashi ba tafi dangantashi da sharri bata ji  cewa izzatu zata  iya aikata abinda ake ganin ta aikataba, kaf tunanin ya kare wajen gano shin waye me shiryawa izzatu wannan tuggun? Sam hankalinta kuwa kwallarta tunaninta sun kasa koda hasaso mata wani ko wata da hk  bacci ya dauketa, shikuwa jafar kwannan zaune yayi jimami gami  da tausayin abokinsa ya cika masa zuciya tawani bangaren kuma Haushi da tsanar doctor muhmud sun cika shi.
Tun  sassafe suka nufi hospital din, Alhaji Hashim sai daya riga  Prof isa asibitin, Suna zaune acikin office din doctor Mahmud, Babu Wanda yacewa wani qala shikuma doctor Mahmud yanata rubuce -rubucan yadda zasu karbi dead body na izzatu batare da wani problem ba.

 Alhaji Hashim ne ya kalli Prof yace, Alhaji Abdullahi!! Prof dagowa yayi ya kallesa batare daya amsaba. Alhaji Hashim yacigaba yacewa, Dan Allah kayi hakuri ni yanxu nasan babu Wani Abu dazan fada maka Wanda zai sanyaya zuciyarka amma Dan Allah ina  me baka hakuri Dan Allah, Nine zan shige gaba ganin anyankewa safraz hukuncin daya dace dashi muddi ba,a kashesaba to zansa ayimasa daurin  rai da rai, wlh ban taba tunanin safraz zai aikata hk  ba nasan yarone me nagarta  bansan me yajashiba ya aikata hk  wallahi kasancewar Sa Dana bazai sa  inkasa hukuntasaba inhar nayi hukuncin da baiyimaba ka daukaka kara a kowacce kotu a duniyar nan wallahi zan tayaka.


 Ajiyar zuciya Prof yayi Sannan yace, kadena mgn kamar dani da Kai bamu zama dayaba, kamar izzatu da safraz ba dayane a wajenaba kana mgn ne kamar nafison izzatu akan safraz to wallahi kayi *Kuskure* Alhaji izzatu tariga ta tafi kuma nasan idan an bincika akwai kwakwkwaran dalilin dayasa har yakai hannu ya daketa Allah takawo ajali safraz yazama sanadi Amma ba Dan yaso  hakaba shima safraz bazai aikata hk  da ganganba *KUSKURENE* izzatu ta tafi muyi mata zaton Alkhairi a yanxu nafi jin halin da Safraz yake ciki  banso abun yaje gurin hukuma ba abinda nafi damuwa insani  menene ya hadasu har ta Kai ga hk  na tabbata Safraz is a moral person he have good behavior kamar yadda na tabba izzatu ma hk  take.

  Allah sarki!!! Shine abinda Alhaji Hashim ya fada a zuciyarsa, Babu mai iya yin abinda Prof yayi sai  Adali kuma jurumin mutum Wanda addini da tauhidi suka gm ratsa zuciyarsa.


A dai dai lokacin jafar yashigo da sallama, duk suka amsa  masa Sannan suka gaisa.

An dau kamar awa  biyu da rabi  Sannan doctor yace subi bayansa a dai dai dakin ajiye gawa suka dakata shikuma ya Shiga.


 Kamar mintuna 22 hk suna tsaye suna jiran fitowa  gowar dan har an kawo motar da za,a sakata a ciki Sukaga doctor Mahmud ya fito da gudu wasu ma,aikata biyu na tura gado dauke da mutum a kwance a Kai an lullubesa, da gudu suke tura gadon iyakarfisu kamar zasu tashi sama shima doctor Mahmud yana binsu da gudu, duk inda suka wuce sai jama,a subisu  da kallo har suka isa emergency. Dakin da aka kwantar da Safraz nan suka Shiga suka rufo kafar cikin hanzari suka dorata akan gado har zuwa lokacin tanatayin  hiccup wato shakuwa da sauri daya dg  cikin nurses din ta juya  tafita  a dakin doctor Mahmud nan ya hau  Danna chest dinta in a haste, danna kirjinta yake da sauri da sauri har yanayin zufa ya dau kamar mintuna 5 yana dannawa Sannan nurse din ta dawo dakin dauke dawasu abubu gida 2 kamar dutsen guga sai dai basu kai dutsen guga girma ba da sauri doctor Mahmud ya karba cikin hanzari ya Dan tattaba jikin abubuwan alam ya kuna  Sannan ya rike daya a left hand din shi daya kuma a right. A saman kirjinta ya Dora wani irin firgita tayi ta zabura, yakuma  dorawa takuma  zabura kamar zata  mike zaune, Ana uku yana dorawa ta bude idonta tare da jan numfashi. _Alhamdulillah_ Doctor Mahmud ya fada tare da mikawa nurses abinda ke hannunsa,  tana kwance idonta a lumshe yazo saitin kunnanta yace _Izzatu_ kamar yadda yaji Safraz ya fada sa'ada ya suma, idanuwanta ta kuma budewa tar ta kallesa alamu taji  kiran   dayayi mata.


 Baya doctor Mahmud yaja  ya fada kan kujera ya zauna yana saukar da Ajiyar zuciya yace, _Alhamdulillah saura kadan  mu tabka babban *Kuskure* Allah mun godema daka  tashi wannan baiwarta taka damun aikata kisa cikin *Kuskure*_

Sai daya dau kamar mintuna 15 hk yana ta ajiyar zuciya Sannan ya umarci nurses din dake tsaye a kansa dasu kawo masu wasu abubu daya bukata babu 6ata lokaci suka kawo masa.
  Tana kwance a hankali abubuwan dasuka faru tsakaninta da Safraz suka fara dawomata cikin Brain dinta hawayene suka fara rolling dg  eyes dinta, meyafaru? Shine abinda take ta tambayar kanta duk da batasan menene dalilin dayasa Safraz yayi Mata hk  ba amma is a serious problem jitayi kawai she's eager to know what happened a hankali take yunkurin tashi zaune da sauri doctor Mahmud ya iso  bakin gadon ya dakatar da ita.

Idonta dasuke a kumbure ta daga  ta kalli doctor in a lower voice tace, Pls I want to see my husband, takarasa mgnr wasu guntun hawaye na fitowa from her eyes.
Da mamaki doctor Mahmud yayi saurin Kallonta daga  masa Kai tayi cikin kulawa yace, Calm down !!! You will see him later but not now sorry.
  Yana gama fadin  hk  ya kalli nurses din yafice a dakin,  daf da ita suka karaso suka fara kokarin sakamata wata doguwar Riga me kama da rigan sanyi bayan sunsa mata daya dg  cikinsu ta mika Mata cup dauke da tea mai kauri babu gardama Izzatu ta karba ta fara sha sai data sha fin rabi cup din Sannan ta mika musu, kamar mintuna biyar takuma bata wani cup din me dauke da warn water Izzatu ta karba, Magani ta dinga bata tana sha har ta gama Sannan ta koma ta kwanta  suka wanke mata ciwon dake goshinta tare da daura mata ruwa Sannan suma suka Fice babu bata lokaci itama bacci ya dauketa.

Office dinsa  yakuma kaisu bayan sun zauna doctor Mahmud ya kallesu muryansa a sanyaye yace, ina  me Neman afuwarku bisa  kuskuren Dana aikata na tayar muku da hankali wallahi lokacin da aka kawota nayi duk iya bincikena alamu suka nunamin ta rasu amma Ashe akasin hkne yau muna daukota da zummar Baku ita kawai sai na lura kamar tana hiccup  cikin izinin Allah gashi har ta farfado, Ashe tayi long faint ne.

_Alhamdulillah! Alhamdulillah Alhamdulillah_ shine abinda Alhaji Hashim yake ta maimaitawa , Prof kuma ya sunkuyar da kansa kasa sai ga wasu hawaye masu dumi sun zubo masa.

Basu wani bata lokaci ba doctor ya kaisu har dakin suka ganta tanata barcinta cikin kwanciyar hankali.kafin kace  me tuni labarin farfadowar izzatu ya yada  family masu tahowa asibitin nayi masu kukan farinciki ma nayi hkm masu bakinciki nayi, lokacin da labarin ya isarwa su Anty Adama sai datayi kamar ta hadiyi zuciya ta mutu saboda bakin ciki  abangaren karima ma hkne ranta  yayi mugun baci har sai data kasa dannewa ya bayyana akan fuskarta.

  Wajen karfe daya Izzatu ta farka dg bacci, lokaci yan dubiya  suka samu damar shigowa dakin cika yayi da mutane anatayi mata sannu Hajiya Rukayya bakin ta yaki rufuwa domin ganin tilon diyar tata ta bude ido kamar an mata kyautar aljanna hk  takeji.

Tunda yanxu Alhamdulillah ga yadda ta kasance kabada izini asaki Safraz, Prof ya fada yana kallon Alhaji Hashim.
Hmmm Rabu dashi sai na koya masa darasi tukunna nan gaba bazai kara Kuskuren kai hannu kan matarsa ba, cewar  Alhaji Hashim.
A"a Alhaji ba hk  za ayiba hakuri za,ayi ansan  yayi *Kuskure* sai ayimasa afuwa Allah yanason masu yafiya domin Sam ba halinsa bane.
Jafar dayake zaune agefe yace, Abba Dan Allah kayi hakuri sharrin shaidanne amma suna zamansu lpy Dan Allah Abba ayi masa afuwa in sha Allah wannan shine na farko kuma na karshe.

Alhaji Hashim yaji dadin yadda prof yake nuna kulawa ga dansa Safraz shikanshi kwana yayi baiyi bacci saboda damuwar abinda dayayiwa Safraz din sam bayason damuwar dan  nasa ko kadan Amma girman laifin daya aikata bazaisa yaki hukuntasa ba.

Da kyar suka samu ya yarda, yan sanda  ya kira yace in anzo bailing Safraz subada shi.

Babu bata lokaci Prof da jafar sukaje suka karboshi kasan cewar ko takalmi babu a kafarsa yasa Prof yasa jafar ya tsaya a wata plaza yafita ya sayi takalmi da set din kayan da zaiyiwa Safraz basu tsaya ko inaba sai wani Dan karamin hotel Prof ya umarci Safraz yaje  yayi wanka  ya bashi kayan daya siya, Babu musu Safraz ya karba ya Shiga duk tunaninsa wajen zana  izar Izzatu zasu, dg  jafar har Prof duk tausayinsa ya cikasu Dan jikinsa yayi rudu  rudu  alamun yasha  duka  ga cizon sauro abunka da farin  mutum fatarsa tayi ja  duk ya  kumbura.
Safraz ko daya shiga toilet din bai samu damar yin wanka ba kuka yayi har ya gode Allah ya wanke fuskarsa kawai ya canza kaya  ya fito suka tafi.

Koda sukazo asibitin Safraz bai kawo komai aransaba suna tafe yana binsu har dakin da Izzatu take, zuwa lokacin babu mutane sosai a dakin dg  mami sai Hajiya Rukayya da Hafsa matar jafar sai sakina da Alhaji Hashim.
   Prof ne ya fara shigowa sai jafar saikuma Safraz yana biye  a baya, yana shigowa Izzatu dake zaune takai kallonta kanshi wani bala,in tausayinsane ya bugi zuciyar ta Dan duk Hafsa ta fadamata abun daya faru na kowa yayi zaton ta mutu da dalilin dayasa Safraz ya daketa dakuma yan sanda  da babansa yasa suka kamashi, har text din saida hafsa ta bata ta karanta domin da safe jafar yaje  gidan ya gyara inda ya baci da jini da glass cup din daya tarwatse nan ya dauko wayoyin Izzatu da Safraz ya bawa Hafsa ta ajiye.

Shima Safraz kurawa izzatu ido yayi yana tunanin kodai mafarki yakeyi ne Amma ganin zahirin gaskiya ne ba mafarki ba yasa ya karasa bakin gadon da sauri, kallon juna suka dinga yi hawaye nabin fuskokinsu bawanda ya iya cewa wani Abu.

Alhamdulillah ya furta yanayin murmushi da hawaye nakuma bin fuskarsa zama yayi abikin gadon yana ta dariya shi daya kamar mahaukaci, Alhaji Hashim ne yace, dariyan me kakeyiwa mutane da kana Santa kayimata hk  idan Bacin akwai sauran kwannan a nan gaba da tuni shikenan To wallahi inayimaka last warning kar inkara ganin makamancin hk  kuma yanxu ka tsugunna ka bata hakuri.
Safraz da kansa yake a sunkuye a hankali ya tsugunna har kasa ya kalli Izzatu yace, ina  Neman afuwarki Dan Allah kiyi hakuri.
Duka  dakin sai dayabawa kowa tausayi Izzatu kam  fashewa tayi da kuka.

Kwanan Izzatu biyu a asibitin aka sallameta, taso  ta wuce gidansu  Amma mahaifinta ya hana dole takoma gidan ta, Ranar juma ,a bayan anyi  sallar juma,a   aka daura auren Safraz da karima a inda Prof shine waliyin Safraz wani kanin  mahaifin karima yazama mata waliyinta,  farinciki wajen Karima babu iyaka domin samun cikar burinta Wanda ta kudurce a zuciyar ta muddin tashiga  gidan Safraz sai tayi mai yiwuwa Dan fitar da Izzatu koda kuwa ta hanyar bin malsmai ne. Safraz kuwa babu yabo  babu fallasa bazakace yana farinciki ba hkm  bazskace tana bakinciki ba, damuwarsa duk yana kan Izzatu kullum kara jin Santa yakeyi a zuciyarsa Amma abinda yafaru Sam yayi masa Katanga da ita Dan ko mgn ba sosai Sukeyiba, Izzatu kuwa ta murmure  Masha Allah duk da tana cikin damuwa Amma tabarwa Allah lamarunta tunanin ta bai wuce halin dazata Shiga idan karima ta shigoba babu abinda yake hadata da Safraz gashi ya kara aure hk  zata dinga Kallonsa shida matarsa ita kuma tana gefe wannan shine abinda yafi damunta.


Ajiyar zuciya Izzatu tayi ta kalli  Ramlert da Dan guntun hawayen dake idonta ya karasa fitowa Sannan tace, Ramlert this is end of my story Amma na yakaice miki labarinne because there's no enough time.
Tabbas you're Best among the rest kawata  I pity you I can not define describe how I feel, sorry Izzatu be patient kikara hakuri sosai Amma nima ina cikin rudani me tarin  yawa Allah ya tona  musu asirin kasuwaye, karki dami zuciyarki da tunane-tunane akan wannan auren take it easy don't bother yourself keep praying Allah zai ganar dashi watarana. Cewar  Ramlert.

Hmmmm Ramlert kenan nasan dole zan wulaqanta  idan matarsa ta shigo yanxu ma baya tani inaga yasamu wata, Duk wani abunda  kikaga yafaru a wajen dinner dinnan yanata wani haba-haba dani duk yayi ne Dan kar a gane  har yanxu akwai matsala  a tsakaninmu Dan na Dade banga yayi dariya kamar irin ta ranar ba na fahimci bayason karima ta gane  akwai wata matsalar a tsakaninmu, ina  San Safraz matukar so  Amma zan iya hakura dashi matukar nafuskanci wani wulakanci idan matarsa ta tare.

No Izzatu karkice hk  matsalar dayane wannan tsargin dake tsskaninku Amma wallahi he loves u More than u love him, every a bad beginning has a good ending take patient akwai ranar dazai fahimta gaskiya Zata bayyana, da safe baya miki so mai tsanani da tuni ya sakeki Amma he can't separate with you because he loves you so much ni dai shawara gareki ki kara hakuri inhar abun yaki to sai asan  yadda za,ayi inta  kama arabu din Amma indai kika matsa kuka rabu yanxu babu wani nasara domin har abada bazai daina zargin abinda kikayi masa Amma yanxu inkuna tare maybe the true will appear, ki kara juriya da hakuri me hakuri na dafa  dutse har yasha romonsa.

Izzatu tace, thank for your advice my dear may Allah reward you Amply, Allah ya barmu tare my sister good friend like no another.

Sun Dade sun tattaunawa Sannan Writer Ramlert ta tafi.

A can gidan mami kuwa cike yake da jama'a anata hidima domin duk a gidan aka hade bikin karima da Safraz din, dan babansu Karima ma wani bangare aka basu acikin gidan abata  gudanar da biki  cikin kwanciyar hankali.

Amarya tana ta doki saboda gobe  za,a kaita dakin ta tasha gyara sai walkiya takeyi  fauza babbar kawar amarya suna like da juna  anata gudanar da shagali, Sakina kuwa bayabo ba fallsa tana Dan nuna farin ciki  Amma damuwace fal zuciyar ta. Ango Safraz kuwa yana can gidansa tamkar ba Ango ba domin tun  safe yana daki a kwance yanata tunane tunansa karima kuwa ganin bata ganshiba gashi wasu friends dinta nason  su gaisa dashi yasa tadamesa da kira tsaki yaja  a ransa yace " _malama don't bother me now bakya gabana damuwar datake gabana ma ta isheni, haka kawai a mannamin wahala_" yakuma gyara kwanciyarsa yaja  blanket ya rufa.

Amarya karima events tashiya kala-kala Amma babu Wanda Safraz yaje hakan ba karamin damunta yayi ba karima na zaune gefen gado duk ranta  a matukar bace  Abu kadan  sai taja  tsaki fauza dake shirya kaya cikin wata box ta kalleta tace, Amarya bakya laifi wai kedawa ne hk?

Mmmm fauza wannan mutumin meyake nufi danine?  Ai wulaqancin yayi yawa .

Fauza tace, kema dai wani lokaci kamar bakya fahimta, wannan auren fa kinsan dole akayi masa dole kema baza kiga yadda kike soba Amma idan kikayi hakuri yaune za a kaiki gidansa sai kiyi yadda zakiyi kisamu Shiga zuciyarsa ko kadan  ne Amma kina sawa kanki  damuwa shima kina takura masa duk ba mafita bace wannan.

Karima tace, bazaki gane  bane idan aka bibiya wannan matsiya ciyar matar tasace take hanasa, kowani wadataccen kudi ta hana ya bani  a yadda Safraz yake da kudin nan dannace 10 millions nake bukata daga  events zuwa komai da komai shine zai hanani wai 5 million s kawai ya bani abun nan ya konamin rai matuka.

Fauza tace, hohoho wlh bakida godiyar Allah yanxu miliyan 5 dinne  yamiki kadan? Wlh yayi kokari sosai kema kinsan kudin dakika nema yayi yawa, ni dai wallahi zan Baki shawara ta karshe  kinsan dai mudai yanxu ba yara bane kitsaya ki mai da hankalinki ki natsu kisan me kikeyi, karima ina me shawartarki ki zubda makaman yakinki ki zauna a gidanki lpy  karkibar wannan damar ta subuce miki kidena Ganin Safraz Dan,uwanki ne muddin yasan abunda  kuka aikatawa matarsa Allah zai iya rabuwa dake  yanxu kinsan wajen sau  uku kina zubda ciki ki rufawa kanki  asiri tunda kikasamu kikayi wannan auren ki rikesa da kyau karki bari ya kubce miki ina  fadamiki gaskiya ne a tsayina na aminiyarki kuma wallahi kidena daukan shawarar momynki hanyar datake Dora ki is not good, kiyi tunani sosai ki gani

Tsaki karima taja  sannu tace, ai dole zakice hk tunda kinga ke najib yana sonki Abu kadan  zai kiraki a waya yadamu da lamarinki kuma ke ko kin aureshi baki da kishiya ai wlh sai iya inda karfina ya kare idai akan izzatu ne dole tabarmin Safraz ni daya.

Dariya fauza tayi Sannan tace, hb  karima yanxu bagashi keda Safraz kunyi aureba nifa ko zancen aure  bayamin Amma kina cemin nafiki nifa idan Bacin najib ina  sanshi tuni na rabu dashi babu ruwana da kudinsa ko mulkin babansa domin bata lokacine soyayyah tsawon shekara uku, kedai kiyi amfani da damar ki.


Har suka gama hiransu babu alamun karima ta dau shawaran da fauza ta bata


Tana zaune a falo ita daya tayi tagumi da alamu tayi nisa a tunani,  kare mata kallo ya tsaya yanayi ganin cewa bata kollonsa har yau yanajin wani matsanancin Santa na kara Shiga zuciyarsa takawa yayi ya karasa tsakiyar parlour din amma har zuwa lokaci batasan da mutum kusa da itaba kujera yasamu opposite dinta ya zaune, _izzatu_ ya fada in a silent voice dinsa da sauri tayi firgigi ta dago ta kallesa har sunayin 2eyes, wani critical looking yayi mata for a moment  sai a lokacin yaga wata muguwar ramar  datayi wani mugun tausayin tane ya tsarga zuciyarsa tuni hawaye ya tsatstsafo dg  idonsa kokarin maidasu yayi ya kalleta lokacin kanta na kasa yace, what's wrong with you?


 A halin damuke a yanxu har zaka tambayi  meke damuna ta fada a zuciyarta, shuru tayi batace masa komai ba yakuma cewa,  kiyi hakuri !!!

Ji  tayi zuciyarta karye tuni kuka ya kubce Mata ita kanta tana tausayawa mijinnata tasan ba,a San ransa komai ke faruwa ba ko tayi zataji haushinsa ko tsanarsa sai taji ta kasa, irin kukan datakeyi ne ya tayar masa da hankali domin bai taba ganinta in such situation ba da hanzari ya taso dg inda yake ya dawo kusa da ita ya zauna, shima zuwa lokacin idanuwansa duk sun ciko da kwalla, kuka takeyi  sosai.

Cikin dashash shiryarta da bata fita sosai tace, May Allah show me the day!!  Which day? Safraz ya tambayeta tana gazing dinta.

Bata bashi amsaba tacigaba dacewa, what a terrible life? Pls Allah have mercy on me, don't let me give up  I want to pass the trial you are testing with, don't let me ever turn away from you, no matter how many trial and difficulties you tests me with, let the difficulties make a stronger Muslim and more sincere y you, ta karasa fadar  hk  tana fashewa cikin matsanancin kuka.

 Shima rasa abinda ke masa dadi yayi furucinta sun shigesa sosai har  ya fara tunanin kodai tilasta ta yakeyi su aikata badalar batare da ranta nasoba.


 Hannnayenta duka  biyu ya riko ya rike gam yana jin radadin kukan datakeyi har cikin zuciyarsa, stop crying pls, your cry  hurt me more, don't think I stop loving you I love no one but you up to now wlh izzatu I love u so much kawai dai nakasa rarrashin zuciyana ne game da abinda kikamin but u really love u, I wish muna rayuwa ne cikin farinciki ba irin hk  ba u forgive you izzatu but promise me you will never do that again, ya Karasa mgnr tana dago habarta kura mata ido yayi yana kuma jin Santa na shigarsa.

  Shuru tayi ta kasa koda kallonsa without knowing what to say, sai siraran hawaye dake rolling a checks dinta, I said stop crying ya fada yana Sa harshensa a kan kumatunta ya fara lashe hawayen dake saukowa dg  idonta lumshe idonta tayi bai dena ba har sai dayaji hawayen sun dena zuba.

     Ajiyar zuciya ta dinga saukewa a hankali cak ya dauketa ya Dora kan  lap dinsa yayi hugging dinta sosai a jikinsa yana shafa gashin kanta kasancewar ko dankwali babu akanta dama wani small Vail ne ta yafa Wanda zuwa lokacin ya salube ya fadi kankujerar, sun dau lokacin a haka daga bisani wayansa dake gefe a ajiye ya fara ringing sai dayayi kamar bazai daukaba saboda he is enjoying the moment domin ya manta rabon  daya kasance da matarsa a hk  bayason abinda zai katsemasa jin duminta dakeji kusa dashi, badan  yasoba yasa hannu ya dau wayar ya duba _My mom_ shine sunan daya bayyana akan screen din wayar  zuwa lokacin kiran ya katse yana kokarin kiranta  wani kiran yakuma shigowa, cikin ladabi ya daga  tare dasa wayan a speaker.


 Daga can bangaren mami cikin sauri ko bari bata yi sun gaisaba tace, ka kawomin izzatu yanxu safraz want to see her in hurry.

Mami lpy ? Meyafaru? Ya tambayeta.

Lpy qlau mana just banason tana can gefe daban ne hakan baya min dadi yakamata ace yau ana yini tazo.

 Ahhhh ! Mami bikin kishiryata zata  zo? Hb  mami ni dai gaskiya aa  ya fada a shagwabe.

Zakaci kaniyarka Safraz dalla kayi maza ka kawomin ita.

Wai mami da gaske kike?

Wai ni inayima wasane ? Ina busy kuyi maza kar ka kai karfe 1 baka zomin da itaba, tana gama fadin hk  bata jira me zeceba tayi hang up din wayar.


Message ya turawa jafar kamar hk  _I want to see you pls I'm at house_ _OK_ shine replay din da jafar yayi masa.


Sunkuyowa yayi saitin fuskarta yaga idonta a rufe  a saitin Kennanta in a whisper yace you heard all that Mami said? Nodded din head dinta tayi.

 Like a baby hk  ya dauka ta yakaita bedroom dinta badan  tasoba kawai Dan umarnin mami Amma da bazata jeba, sai data Shiga bathroom Sannan ya fito ya nufi dakinsa.


Wani tsadadde kuma rantsatstsen less pink colour tasaka ya matukar amsar jikinta dankareriyar sarka da dakunne tare da zobbe da abun hannu Wanda suke walkiya daka gansu zaka gane  gold ne ko wanne tasa shi a mazauninsa  simple makeup ne a fuskarta dankwali ta dauka ta dasa wani ashshakakken dauri  Wanda ya bayyanar da yalwataccen gashin  dake kwance a goshinta mayafi ta yafa  a kanta Sannan ta rataya jaka  tare dasa Wani tsadadden flat shoe, daga  mayafin jakar da takalmin duk coffee colour tayi matukar kyau sosai tamkar ita yati  kanta, tana fesa turare Safraz ya shigo dakin turuss yayi ya tsaya yana Kallonta a hankali kuma ya karaso inda take a tsaye a gaban  madubi Kallonta ya ringq  yi Amma bata yadda sun hada idoba, dark Green Shaddace a jikinsa rigar iya gwuiwarsa hannu rigar shima ba dogoba iya gwuiwar hannunsa sai black shoe da black cap dayasa. Bayanta yazo ya tsaya ta yadda zasuna ganin Kansu a Murrow din, dukda takalmin datasa  yana da Dan tudu Amma a iya kafadarsa take rungumrta yayi ta baya yasa hannayensa ya zagayeta dasu, tacikin madubin ta kalleta yace, kinyi kyau sosai matata tamkar zaki gasar kyau, batasan sanda murmushi ya subuce mata ba shima murmushin yayi Sannan yace, are you ready? Daga  masa Kai tayi batare dace komai ba phone dinta dake gaban  madubi ta dauka yaja hannunta suka Fice.


 A compound suka samu jafar zaune Cikin mota, baya yabude Mata tashiga Sannan shima ya Shiga bayan, Lallai kunsamu driver jafar ya fada yana Dan juyowa bayan, Ah mana,    driver  a tuqamu a hankali duka sukeyi dariya Sannan jafar ta tada  motan, suna zuwa get Safraz ya sauka  ya bude Sannan ya rufe  suka dau hanya.


Dayake gidan da Dan tazara tsskaninsu 1:33 dai dai suka isa gidan, parking lot sukayi parked Sannan suka nufi cikin gidan gidan cike yake da mutane duk inda suka ratsa anata Ango Ango har suka isa babban parlour mami mutane basufi gomaba a parlour ciki kuwa hards mami Amarya karima da fauza,  izzatu ce ta fara Shiga da sallama duk mutane suka amsa  tare da dagowa suna kallonta nan jafar da Safraz suka biye mata baya, Wani faduwar gaba karima taji lokacin dataga izzatu wani masifar kyau dataga tayi fauza ma bin Izzatu ta dinga yi da ido da bata ganetaba sai dataga safraz ya shigo da jafar.

    Da fara,a mami ta tari Izzatu ta nuna mata waje kusa da ita ta zauna, su Safraz kuwa basu dau Wani lokaci ba suka bar parlour n,  Sai da aka Dan dau lokaci Sannan mami taja Izzatu bedroom dinta.

Ya jikin naki izzatu? Mami ta tambayeta.

Jiki Alhamdulillah Mami, izzatu ta amsa.

Bai kuma miki wani Abu ba dai kou?

Izzatu tace, eh babu komai mami.

  Sun Dan tattauna wasu batutuwan Sannan suka fito dg  dakin. Hakan ba karamin konawa karima zuciya yayiiba ga Safraz ya shigo ko Kallon inda take bai yiba duk ranta  ya dagule tashi tayi ta Shiga dakin Shahida itama fauza ta bi bayan ta.


Fauza tace, Shiyasa nake cemiki ki dau komai a hankali karkiyi biyu babu, ki duba matarsa kiga kalarta namiji yana da irin wannan matar wallahi babu macen dazata rudeshi, Amma idan kika  kwantar da hankalinki kuka zauna lpy sai kisamu abinda kikeso tunda matarsa bata da tashin hankali nitsatstsiyace wallahi.

    Ni rufemin baki Dalla, Da wannan matar zamu zauna lpy ? Kina ganin data shigo parlour ta min mgn ne.

Fauza tace, wannan ai ba laifinta bane datazo ta mana sallama ke yakamata kiyi mata mgn tunda bikinki tazo Amma bakiyiba ni banga laifinta ba, nidai Ina fadamiki gaskiya  ki ajiye duk Wani tantirancin da mukayi a school ki rungumi rayuwar ayrenki hannu bibbiyu abinda zanyi nima shi nake fadamiki kema kiyi,

 Karima tace, you never understand me pa, if Safraz bai rabu da itaba I never enjoy my married life.

  Fauza tace, I can't force you is just advice, najib yacemin zai biyo plane na karfe 3 yau indan  yazo za muyi ta ta kare kodai ya tsaida lokacin da zai tura iyayensa gun iyayena kokuma kowa ya kama gabansa tunda na gama karatu kuma yanxu babu Wani wasting time dina da zanyi fauza na gama fadin HK ta Shige bathroom.

 Wayan karima ne ya fara ringing number babu suna a ya tsine ta daga kiran, hello waye?

Alhaji suraj  ne taji an amsa mata.

Wai kai baka da hankali ne? Bance ma nayi aure kadena kirana ba, look ! Mlm nifa ko banyi aureba babu abinda zanyi da Kai ka gane ? Kit ta kashe wayan tare dajan tsaki
Biki yayi biki anci ansha kowa yana cikin nishadi, wajejen karfe 5 na yamma anata shirin Kai amarya kowa yanata kintsawa amarya ma tashirya domin yafiya gidan miji,  Anty Adama kuwa baki ya kasa rufuwa sai murna akeyi, fauza kuwa andau kwalliya domin najib yana dab da isowa.


Alhaji Hashim ne zaune a falonsa shida Prof wato mahaifin Izzatu domin wata amintaka ce  tashiga tsakaninsu a yan kwana kinnan, waye ya dauka ya kira mami yace tazo tare da Izzatu da karima, Sannan ya kira Safraz shima yace yanason ganinsa.

   Basu Wani bata lokaci ba mami Izzatu da karima suka shigo cikin parlour din, a dau wani lokaci ba Safraz da jafar suka shigo, suna zama sai ga Anty Adama itama ta shigo, Wani mutum da suke kira da baba bala Yayan marigayi mahaifinsu karima shima ya shigo Sannan jafar ya bude taron da addua.

 Daga bisa Alhaji Hashim ya fara cewa, To Alhamdulillah ala kulli halin,  Dukkanmu musan abinda ya hadamu a nan, Allah ya muku Albarka gaba dayanku safraz Inason ka natsu ka saurareni a yanxu Izzatu da karima dukkansu Matankane suna karkashin kulawarka kayi kokarin yin adalci a tsakaninsu karka bari shaidan yayi tasiri akanka ka ringa  nuna banbanci a tsakaninsu kaji tsoron Allah, kayi kokarin sauke  hakkinsu da Allah ya dorama aringa Kai zuciya nesa banda daukar hukunci Cikin fushi aringa hakuri da iyali aringa Kai zuciya nesa, Ku kuma kuji tsoron Allah Ku zauna lpy a tsakaninku banda tashin hankali, Ku kyautatawa mijiku Ku hade kanku, izzatu karima kanwarkice dukda a girme ta girmeki Amma kece babba a wannan fanin kija girmanki Ku zauna lpy, kema karima Izzatu yayarkice  dukda kin girmeta a ashekaru Amma a wannan fannin kece karama tunda a bayanta kika zo Dan hk kibata girmanta Ku zauna lpy. Wannan shine abinda zan ce  muku Allah ya bada dorarran zaman lpy.

[10/24, 8:46 PM] Ramlert: Prof ya Dora dacewa, That Masha Allah duk wani Abu fada Alhaji yariga daya fada inhar kukabi abinda ya fada to  babu makawa zaku samu farinciki da zaman lpy me dorewa, Ku tsaida gaskiya da amana a zaman takewarku kuyi hakuri da junanku Allah ya muku Albarka Allah yabsku zaman lpy da zuri,a ta gari Amen.


Baba bala yace, Alhamdulillah bani dawani abun cewa domin manyan malamaina duk sun fada Allah ya Sanya muku Albarka a rayuwar Aurenku Ayi hakuri da juna Dan Allah, Anty Adama Dora dacewa, Dan Allah kuyi hakuri da junanku Ku hade kanku waje daya, musamman karima inajan kunnanki kafin zuwanki suna zaune lpy banyadda yanxu kuma inji wata matsalaba ranki zai baci yadda kika samesu kema ki Dora a hk, Izzatu Dan Allah ki dinga hakuri da ita nasan kina da hakuri Allah y...

   Ai bata Karasaba Fauza ta shigo parlourn a hargitse bako sallama tamkar wacce aka hankado ranta a matukar bace, Sai data duba taga  inda karima take Sannan ta nufi wajen tana isa ta cafko ta kaimata wani wawan dundu tare da shaqeta da hannayenta tn cewa, karima nizaki tozarta ? Ni zaki wulaqanta ko to wallahi baki isaba Sai dai Mu tozarta juna ni kenan kar inyi aure  tunda ke kinsamu kinyi ko? Da sauri jafar ya taso ya rabasu.

  Tana kokarin kuma cafkota Prof yayi saurin Dakar da ita, nan ta fashe da kuka tana cewa, wallahi Allah ya isa tsakanina dake muguwa azzaluma mai Bakin hali Ashe muguntar taki nima sai kinmin to wallahi bakiyiwa banzaba wallahi.

 Da sauri karima tace, Hb fauza meye hk bakiga iyayenmu bane a nan zomuje daki tana kokarin Kama hannunta, ke dalla karki Kuskura ki taba min hannu munafuka kawai, Prof yace, ya isa hk ke kiyi hakuri menene ya hadaku hk  kike  jifanta da munaban kalamai hk ?

 Da sauri fauza tazo gabansa ta durkusa tace, baba wannan kawatace for over 10 years dagani har ita kowa yasan halin kowa Amma shine...

   Da sauri Anty Adama ta katseta dacewa, ke tashi kiba  mutane guri  kuje  can Ku karata kunfi kusa, tashi ki Fice a nan nace bazaki tashi ba nan ta nufo kanta, riqe kafafun Prof tayi tana kuka tana, wallahi dady bazan fitaba kace  ta rabu dani. Prof ya dakatar da Anty Adama dacewa, Ah kyaleta aji meya hadasu, Amma fir  Anty Adama taki barinta itama kuma fauza taki fita tariqe kafar  Prof har sai da Mami da Alhaji Hashim suka dakatar da Anty Adama da kyar, fauza tana shashekan kuka tace, Amma shine jiya da daddare zata  turawa saurayin da zan aura text message wai ya rabu dani bani da tarbiya sau  uku ina  zubda cikin shege kuma wallahi karyatake nasan na taba zybdawa sau  daya Amma ita sau  uku tana zubdawa a England, yanxu tayi nasaran rabani dashi Dan taga  ita tayi aure, Duk da munyi rashin tarbiya a baya ta dace tamin HK baba? Fauza ta fada tana kallon Prof tacigaba dacewa,  tun  jiya har zuwa yau nake tayimata nasihar ta zauna lpy a gidanta da abokiyar zaman ta, Amma ni shine ta kabani da mai sona, nima tayaya take tunanin zan rufa nata asirin.

  Sakina da a lokaci taga  shigowar fauza a hargitse ta nufi part din Abbansu Shahida yasa ta biyo bayanta Dan taga  da alamun ba Lpy ba,  jikin karima ya fara rawa kirjinta na dukan uku,uku, zufa tafara keto Mata da rawar murya tace, wlh fauza karya ne nibance masa komai ba yaudararki kawai yake so yayi, look!!!  badai nikikayiwa HK ba? Sai na fadi abinda bakyaso ajidin.

 Ran Alhaji Hashim ne ya baci ya daka musu tsawa dacewa, kuyiwa mutane shuru dallah,  Safraz da Izzatu kuwa yan kallon suka zama Dan cecekuce ne ya barke s falon har gara Mami da jafar sunsa  baki, kutashi Ku bani guri  Alhaji Hashim ya fada, da sauri fauza tace, Dan girman Allah dady ka saurareni kuma ka bani dama akwai abinda zan fada.


 Kuje can kuyi Amma ba,anan  ba cewar Alhaji Hashim, da sauri fauza tace, Abune daya shafeku baki daya Amma idan kukaki saurarata watarana sai kun dau gawar Izzatu a gidan Safraz.

  Ba karamin razana kowa yayi da mgnr taba, mahaifiyar karima zata  iya hanaku Ku saurareni sbd  zan tona  musu asiri dady ku  hanata, jikin Anty Adama da ya dau rawa cikin razani tace, ke kiyiwa mutane shuru iskancin naki  yazo har kaina, a harzuqe Alhaji Hashim yace, Adama dakata inhar karya take zamu gane  kar inkarajin bakin kowa a nan wajen ya juya  ya kalli fauza yace, muna saurarenki.

  Da sauri karima tace,  pls fauza don't do that to me, nan itama Alhaji Hashim ya dakatar da ita.


Fauza ta juya  ta kalli safer tace, Safraz Ku yafemin Kai da matarka wallahi da sanina  da aka kitsanuku dukkan abubuwan nan Amma wallahi babu hannuna aciki, nan fa tafara tone tonen tunda abinda suka vawa mami Tasha tayi doguwar suma, har yan daudun dasuka Kai gidan Izzatu a matsayin masu aiki da sharrin  kwarton dasukayi mata da text message din da karima ta turamasa lokacin dasuka San wayar Izzatu na hannunsa tacigaba dacewa, har poison momy tabawa masu aiki suka saka mata a abinci Amma Allah ya kiyaye bata Ciba maybe kota ganene shiyasa Sai ta koresu.

 Mami da tuni ta gama jiqewa da gumi kunya ta rufeta saboda takaicin abinda yar  uwarta ta aikata mata, daga Izzatu har Safraz jisukeyi tamkar a mafarki Karima kuwa tuni ta fara rawar sanyi,  murya na rawa Anty Adama tace, makaryaciya muzakiwa sharri? Memukayi miki? Kinzo zaki rusa mana zaman lpy.


 Enough Momy sakina ta fada, Momy ki godewa Allah da asirinku ya tonu  kuna  da rai zaku iya Neman yafiyarsu, ni da kaina naji lokacin da ki kasaka su susamata poison a abinci batare dakinsan nasaniba, Nina yi silar  dakatar da daruwar hh domin agidan na yini na hanata  cin abincin kuma nasakata dole ta kori masu aikin, takarasa fadar  hk  tana fashewa da kuka.


Innalillahi wa inna,ilaihirraji,un  shine abinda kowa yake maimaitawa, zumbur Safraz ta Mike tsaye tashin hankali dauke a fuskarsa Momy ya kalla yace, Momy wallahi Allah ya isa bazan yafe mukuba da sauri ya karasa inda karima take sai sharbar kuka yakeyi maruka  yashiga bata da duk iya karfinsa babu Wanda yayi yunkurin hanasa, kije ki auri Wani Safraz din bani ba na datse igiyoyin dake tsakanina dake nasakeki idan kinga  dama gobe a daura miki aure  babu iddata akan ki, yana gama fadin HK ya juyo ya tsugunna a Gavan Izzatu hawayene ke zuba a idonsa, Izzatu ki yafemin wallahi ban taba tunanin wannan abun sharrin akayi mikiva har nayi yunkurin kashe ki Dan Allah kiyi hakuri Dan Allah wallahi wallahi na cutar dake forgive me pls, bata iya cewa komai ba sbd  kukan datakeyi itama.


Tuni fauza ta Fice a falon akwatin ta taje ta dauka tavar gidan, Karima kuwa kuka ta dinga yi tana bawa Safraz hakuri Amma Ko saurarenta baiyibs tajs hannu Izzatu suka bar falon jafar yabi bayansu Kai tsaye gida ya kaisu shima ya wuce nasa gidan Dan kowa zuciyarsa a dagule take babu Wanda zai iya yin wata mgn ta kirki, Mami ma da sakina tuni suma sukabar wajen, baba bala shima kallon Momy yayi yace, tirrr da wannan bakin halin ya bar wajen.


Simi simi Momy itama tabar parlour ko cikin gidan bata komava ta gama hanyar gidan,  karima kuwa falon Mami taje  tana kuka tana bata hakuri tasa Safraz ya maida ita Mami bata saurareta ba HK ta gaji ta dau jakanta ta kama hanyar gidansu


CONCLUSION*_🀚🏻 _*Thanks for reading*_

_*Thanks for your supports*_

_*Thanks for your prayers*_

_*Thank you so much my fans*_πŸ€πŸ»πŸ‘πŸ»


_Wannan shine karshen wannan Dan karamin littsfin, Allah kasa ya zama hujja gareni ba hujja a kainaba, Abun Dana fada na dai dai ba iyawata bace  Wanda nayi ba dai dai ba wannan *KUSKURENA* ne dakuma gazawata_


_Sakonnin danakeson na Isar a wannan Dan karamin littafin_:

_1 Yanke hukunci batare da bincike sosai ba yana kawo Dana sani, ayi bincike sosai kafin yanke hukunci_

_2 Juriya da Hakuri duk inda zaka tsinci kanka a rayuwa ka kasance mai hakuri da juriya musamman a rayuwar Aure, kar ayi gaggawa Dan gudun Dana sani wacce nasan kyeyace_

_3 San dukiya ko kwadayi abune dayake kai mutum ga halaka a nisanta zuciya saga San abin duniya kullum a rayuwa kasowa dan,uwanka abinda kakesowa kanka_

_4 Karka gurbata rayuwar wani Dan inganta taka, Ayi adalci ga juna_

_5 Wanda kake  tunanin bazai cucekaba shine macucinka, Dan hk  sai anyi taka tsantsan a rayuwa koda kuwa da Dan,uwankane_


 _Alhamdulillah_ Haka taron biki ya tashi babu dadi kowa ya Kama gabansa wasu nata zagin Safraz kasancewar basu San dalilin dayasa yayi sakin  ba,  sakina ce  zaune a Gavan mami.

  Mami!! sakina ta kirata.

 Dagowa tayi ta kalleta batare data amsa ba.

Kiyi hakuri Dan Allah kidena tunani haka.

Ajiyar zuciya mami tayi, Sannan tace, Hmmm yau naji kunya a Gavan mijina da surukina sakina, 'yar'uwata fa wacce na dauke tamkar uwa agareni itace da aikata wannan aiki. Yanxu me Anty Adama ta rasa daga gareni ?

 Kiyi hakuri mami wallahi kalli cikin bakinciki hk  nake kwana nk tashi babu irin nasihar da bana  yi musu Amma dg  baya Sai suka dena yin mgnr su a gabana, nayi bakinciki sosai inama ba Momy bace ta haife.....

Ke!! Mami ta daka Mata tsawa, kar inkara jin wannan zancen a bakinki sakina, uwa ko a Yaya take uwace babu mai iya canzata hakuri za kiyi kiyi ta addua Allows ya ganar  da ita.

 Hawaye ne yasuka fara bin idonta tace, hkne mami but.

But what? But tashi kije kiyi sallah, Mami tabata umarni babu musu ta tashi tabar wajen.Mami ta Dade anan zaune tanata  tunane_tunena bakinciki fal zuciyar ta tasaka wannan ta warware wannan.


A6angaren Su Izzatu kuwa Safraz ya rasa inda zaisa kanshi, sai yanxu yake Ganin yayi wauta rashin bincike da baiyiba dukda abubuwan sun faru tamkar a gaske kunya da nauyi gami  da tausayin Izzatu yakeyi matuka, Zaune take a gefen gado kanta a kasa takurawa tiles ido tamkar tana kallon television, yana tsaye abakin kofa  yana Kallonta Wanda yasan tayi nisa a tunani a hankali yashigo da sallama dagowa tayi ya kallesa tare da amsawa Sannan ta maida kanta kasa without saying a word.

Baby!!! Yafada muryansa a kasalance.

Dagowa tayi ta kallesa batare datace komai ba.

Forgive me pls I know you hate me now. I'm seeking your forgiveness pls. Safraz ya fada yana me kuramata ido.

Batace komai ba tacigaba dawasa da yatsun hannunta.

Tashi yayi daga inda yake zaune ya durkusa yasa gwuiwowinsa a kasa, Dan Allah ina  rokonki Izzatu kiyafemin tears suka fara bin idonsa, hawaye sosai suke zuba dg  idonsa tamkar Wanda aka badawa yaji a ido.

Da sauri ta dago ta kallesa cikin hanzari ta Mike tana kokarin mikar dashi tsaye, pls stand up kadena durkusamin is not good, tun jiya nacema babu komai ya wuce pls kamike nace.

 Izzatu in komai ya wuce meyasa kinki sakewa dani, ki fadamin me zanyi Wanda zaisa muma  muzama kamar kowamne ma,aurata ? Dan Allah ki yafemin matata I reality *MY MISTAKE* pls wlh ina  kaunarki Izzatu.

  Ni babu abinda kayi min, what happened is not your fault so kamike tsaye  , you know I must bother about what happened in our married life but it's our destiny amma ni me nayi musu haka? tana zuwa nan ta fashe da kuka me tsuma zuciya.

Mikewa yayi da sauri ya jawota jikinsa ya fara rarrashinta da kyar tayi shuru, Kiyi hakuri kinji ya rada mata a kunne, I love you sarauniyar kyawawa ya fada yana Dan cizon kunanta tare suka saki dariya. Komai ya wuce ko my sweetest? Ya tambayeta lumshe idanuwanta tayi alamun eh, yauwa ya fada yana kara hugging dinta sosai a jikinsa, Allah ya sakamana na bakincikin dasuka samu na tsawon lokaci ya fada yana sauke  ajiyar zuciya.

*AFTER 3 MONTHS*

*BAYAN WATANNI 3*Momy Adama ce  zaune a parlour sakina na can nesa da ita tana rubuce+1 Karima na zaune kan kujera tana danne dannan waya.

 Momy Adama tace, Karima bani hankalinki nan, da sauri karima ta ajiye wayar dake hannunta ta maida hankalinta kan momy, Dan yanxu ta fara hankali bata wani misbehavior.


Momy Adama tace, Kinga yanxu an tsaida ranar auren kanwar ki tsaya kiyi tunanin sosai ki fidda wani kema sai a hadaku.

Momy pls kidena fadar  hk  Dan Allah kisa  baki Safraz ya maidani Dan Allah momy kibawa mami hakuri zata  hakura.

 Wani kallo momy ta Mata me dauke da ma'anoni kala kala, Sannan tace, Wannan lokacin kuma ya wuce karima, waye ya kawo matsalar duk bakeba ce ke me kawa  duk kika kwashe sirrimmu kika fada mata to aikinga kawa  yanxu, ko a waya bazan iya kiran Mami ba a yanxu dai kima fidda rai akan Safraz zaifi miki ki tsaya ki fidda miji  wannan kawun Baku bala wallahi zai iya miki auren dole yanxu ya matsamin akan mgnr ki Dan,uwan mahaifinkine ba yadda na iya dashi.

Sakina bata ce  komai ba sai jinsu datakeyi da kunne
Fauza kenan kina mamakin ganinane a gidanku kou? Safwan ya fada yana Kallonta yana dry.

 Wani kallo ta watsa masa Sannan tace, mekazo yi gidanmu?ko takuma fadama wani abunne kazo ka fadamin fauza ta fada tana galla masa harara.

Dariya ya kyalkyale da ita sannan yace, Haba  my love barinki nayi ki huce na wannan tsawon lokacin amma kinsan I can't life without you.

Cikin mamaki fauza take Kallonsa kamar ba safwan din dayayi mata rashin mutuci ya rabu da itaba. Kaga malam meye HK niban fahimcekaba.

 Gyaran murya yayi Sannan yace, my fauza wannan abun daya faru duk tsarawa mukayi nida  sakina sister din karima, Lokacin dakuke  tsaka da bikin karima sai aka kirani dawata number yarinyar tamin bayani sunanta sakina ita kanwar karima ce  tanason Mu hadu idan akwai wani lamari da zan taimaketa dashi tayi begging dina sosai da har bazan aminceba sai kawai na a mince nayimata alkawarin in sha Allah zan taimaketa inhar zan iya , Ran Dana shigo Abuja ita na fara kira ban kirakiba, Muka  hadu a restaurant na Transicope Hilton hotel ni duk tunani zatacemin tana sona ne, Nan take fadamin a wayanki ta dau number na Sannan taji kina fadawa karima cewa zanzo gobe , Nan ta kwashe duk labarin cousin dinta Safraz da matarsa Izzatu ta fadamin, tasanar dani sister dinta da mamanta ne suke hada musu sharri, naji tausayin ta gaskiya amma sai ng ni wanne taimako zan iya mata , To shine da ta nemi na fadamiki cewa karima cemin ke batacciyace da sauransu tasan  dole inna fadamiki hk nace narabu dake kema zaki tona asiri, nima kuwa na amince domin suna zaluntar Izzatu dayawa maybe in asirinsu ya Tonu zasu dena, kuma ta burgeni yarinyar bata goyon bayan family dinta da aikata zalunci kinji abinda yafaru.Ajiyar zuciya fauza ta sauke tare da goge gumin dake fuskarta dukda air conditioning din dake motar, safwan yace, Kinga laifin Mu acikin wannan lamarin?  Kema banyi tunanin zaki goyi bayan zalunci ba dear amma ki gyara da sauri fauza tace, No safwan ba wai ina  goyon bayanta bane ba yadda na iya tunda sai dasuka kulla abunsy nasani nasiha gwargwadon iyawata inayi mata bazan iya canza taba satuni na canzata, kuma abinda kukayi ko kadan  banji haushi ba sai farinciki danayi ko ba komai nasan kun dakatar da ita dg  aikata barna zata  iya Neman yafiyarsu yanxu Safraz zai samu kwanciyar hankali shida matarsa. Zanje na bata hakuri akan abinda nayi mata

A,a karkije yanxu kibari sai an kwana biyu insan samune sai bayan munyi aure  Dan a yanxu bazata fahimcekiba.

Hiransu suka sha sosai.*AFTER 8 MONTHS*

*BAYAN WATANNI 8*


Fauza tayi aure  da safwan.

Sakina tayi aure  da Dr Nazeef (Wani lecturer ne a school dinsu).

Hakama Karima tayi aure da Alhaji Habib.


Abinda ya faru kuwa shine, lokacin da bikin sakina ya gabato har zuwa lokacin karima bata fidda miji  ba, ran baba bala yayi matukar baci  yayimata rantsuwa zai aura mata wani muddin bata kawo mijiba, Ganin cewa da gaske yake yasa duk hankalin karima ya tashi tarasa inda zatasaka ranta wata rana tafi ta taje  banki wani mutum ya biyota har gida acikin wata rantsatsatsiyar mota shine Alhaji Habib, ta Dan tsaya ta saurareshi ta bayan kamar sati daya tace masa idan da gaske yake ya fito, babu bata lokaci Alhaji Habib ya fito ba laifi ya kashemata kudi dg  lefe har zuwa kudaden daya bata ananfa akasha biki.Mami ta maida komai ba komai ba tare da ita akayi hidimar bikin su sakina, sai dai taro ya watse cikin jimami da da alhini domin sul6in tayals ne ya kwashi momy Adama ta fadi kasa daga nan kuma ta kamu da cutar shanyewar 6arin jiki wato faralais hk  aka kai amare a ranar cikin jimami da koke+1, karima bata kara Shiga tashim  hankali ba sai da aka kaita gidanta Ganin gidan da aka kaita, gidane Dan matsa kaici Wanda bai wuce Rabin fulotiba, mata uku ne a gidan kowacce tana da yara a kalla sunkai 7, 3, babbar matar I tace mai yara 9 kuma duk matan  Alhaji Habib ne Wanda hk yace mata matarsa daya yarsa mace itama daya.


Haka yan kai karima suka watse kowa nafadin albarkacin bakinsa,  karima karewa dakin nata  kallo tayi falle  dayane dg  gado sai durowan Sa kaya da madubi sai Ledan daki da aka shinfida, hawayene kebin  fuskarta tana mamakin itace kuwa a wannan Dan akurkin wai shine dakin ta anya ba mistake akayi ba aka kawota wannan gidan,  tana wannan mamakin har Alhaji Habib ya shigo.

  Zatayi  masa mgn a harzuke ya dakatar da ita dacewa, ki tsaya kiji  batun Inason ki nutsu nidai a farko sunana habibu bawanda yasan ni dawani Alhaji Habib bantaba hajjiba balle  kuma umara, kiyi hakuri da abinda zan sanar miki na miki karya wajen auren ki azuwan inada kudi ni talakane gaskiya wannan motar da kike ganina da ita tame gida nane  yakan akena da ita wajen wanki ko banki da sauransu, har zuwa ranar daya aikeni banki na hadu dake to bawai nazo miki da niyar aurebane nayi mamaki danaji kince  na fito to daga nan nafara fafutuka da karume karume harda Neman rance, naje naciyo bashin  banki na miliyan 2 Wanda bansan taya  zanyi na biyasuba dasu nayi lefe da sauran abubuwa dasu namiki  kayan  daki duk Dan inasanki ban damu  da halin dazan Shiga ba in lokacin bayan kudin yayi, matana dai uku ne kice ta hudu yarana 19 ne in sha Allah kece zaki cikemin na 20, ya karasa mgnr yana Dan dry.

A zabure karima ta mike tsaya, ta nuna shi da Dan yatsa tana cewa, karya kake wallahi ka kalleni namaka kala da wacce zata zauna a wannan gidan? Ka canza tunani wallahi bazan kara mintuna 5 acikin gidan nanba wannan sune  kayan  dakin dakace a barshi kai zakayi.


 Dariya yayi yace karima Keenan idan da banyi HK ba ni na isa na sameki,  lokacin da yan uwanki sukazo ganin gidama gidan maigidana na kaisu ya tafi umara shi da matarsa da yan yaransu biyu aikina shine gadin  gidan sai kuma Dan business danake yi, anyi  Sa,a kuwa basu Dade da canza komai na gidan ba, idai bani nace ki tafi gidan kuba bazaki taba iya tafiyaba domin nariga Dana kafeki a gidannan na mallakeki kinsan abunki da Wanda yayi karatun allo nasan hk  zata  iya faruwa shiyasa na kafeki babu inda zakije sai da izinina matata ta kaina.

 Kasa gane  inda kanta yake tayi kamar zata  zauce  hk  ta dinga ji, duk yunkurin datayi na fita a gidan jitayi ta kasa. HK har gari ya waye.


Haka rayuwar karima yacigaba da tpy, bata iya yiwa habibu musu komai yace sai dai ta tsinci kanta tayi, Da wayo da lallami ya dinga amshe mata kudadenta dan tana da yayi millitan uku a account dinta HK yadinga karba har yasamu ya biya bashin  daya ciyo. Gashi da ice suke girki duk ran girkinta tana shan wahala sosai tayi kuka ta gode Allah, ganin ta fara yin Baki da rama yasa ya raba  musu girki da sauran Mayan take yin nata  ita kadai.

  Dayake suna Dan shiri da matarsa ta ukun wato saratu da karima yasa karima ta bata kudi taje  kasuwa ta siyo mata furniture masu tsada  dasu carpet da sauran kayan datake  bukata, ita da saratu suka fidda kayan dakin suka saka sababbim  kujerunma ukune suka  samu Shiga dakin dakin ya kawatu babu laifi, da sauran daya kujerar  da kayan dakin data cire  duka  ta barwa saratu, saratu tayi ta godiya tana murna babu laifi karima ta nutsu, Koda sakina tazo gidan ba tayi mama ki ba Dan tayi imani sakayya tun DG  duniya ake fara gani, tayi ta bata baki akan ta karbi rayuwa a yadda tazo mata sakayyar abinda suka aikatane, nan sakina tame zata  siyawa karima gida ta koma amma Sam Habibu yaki hk  suka hakura takuma sissiyo mata abubuwan da zata  bukata, nan ta shawarce ta akan taje tanemi yafiyar Izzatu da Safraz.

    Hakama bangaren fauza lokacin datazo gidan karima sai datayi kuka,  Ganin wai karima yar  kwalisace a wannan gidan itama ta nemi siyan gida dan karima ta koma habibu yaki kuma ya hana tanema mata aiki, hk  suka hakura ta bata one million dan taja jari dashi.
Har gida karima taje  ta nemi yafiyar Izzatu da Safraz, hkm  Momy Adama itama tanemi su yafe mata.


Izzatu ce Zaune kan kujera da tsohon ciki Safraz na zaune a kasa kafafuwanta akan cinyarsa yana mata tausa, waiii sweetest kanayi da karfi fa, ta fada tana turo baki.

   Oh!!!!! Sorry Maman twins bazan karaba,

Zansha fresh milk dinnan daka siyo jiya da sauri ya tashi ya nufi fridge ya dauko tare da cup ya zuba yana bata abaki tana sha._*Finally sub hana kalla humma ash hadu alla,ilaha illa anta astagfuruka wa,atubu Alain*_
Post a Comment for "KUSKURE NA CHAPTER B KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...