Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

KASUWANCI NA COMPLETE

KASUWANCI NA COMPLETE

- - Post a Comment

 KASUWANCI NA COMPLETE


Kudin cinikin awarata nake irgawa duk da ba kudin arziki bane amma dukkansu daga yan goma sai yan biyar sai ko ashirin,kanwata na shiga kwalawa kira MEENAT wai baza ki fito ba sai na shigo na mareki,Maganar AMMA naji tana daga gefena a kwance saman yar tabarma tace Haba MUFEEDA ta wannan wacce masifa ce haka dan Allah ki dinga dagawa yaran nan kafa kannenki ne fa,Amma kina dai jin tun dazu nake jiransu su fito su tafi Islamiyya amma sai nauyi sukeyi kuma sun San cewar anjima zan soya Awara,gashi gobe zasu zo suna takura mana a basu kudin Break, to ai sai bisu a hankali dan Allah kinga ni ba lafiya ce dani ba kece komai nasu kece uwarsu kece Ubansu Mufeeda kece komai dinmu,Zuciyata ce tayi rauni nace to Amma ba komai na Dena kiyi hakuri Allah zai baki lafiya kinji,ga kudin nan Amman mu bari na gyara gidan na daura mana tuwo naga muna da ragowar garin masara,Murmushi Amma tayi tare da kallona tace Mufeeda Allah ya miki albarka Allah ya baku miji na gari,ya baku yara su rama muku abinda kukayi mana na alkhairi,Mufeeda yau shekarar babanku Sha uku da   bacewa,har yau ina Sa ran watarana zai bayyana da Zanfi kowa murna ya ganku Ku uku kun Zama yan mata gaku kyawawan gaske kamar indiyawa,musamman ke Mufeeda kunfi kama da Shuwa sosai mahaifinku kika biyo domin shine fari kamar balarabe haka yake har kin fishi Hasken fata ma,su kuma su Meenat sune masu kalata wato su ba farare ba su kuma ba wanda zai kira su bakake duk gaku Allah ya bani Ku kyawawa farare daku amma duk kyan nan sabo da talauci ko Sallama ban taba ji ance ana sanku ba,wanda na tabbata da masu kudi ne komai muni auruwa sukeyi,musamman ke Mufeeda kin kai har 16yrs amma nafi so na aurar dake tunda ba makaranta kike zuwa ba,Baki na turo gaba tare da sakin shagwaba ina shure shure kamar yarinya ina kukan sangarta Allah Nidai Amma bana son aure kuma ma nawa nake,hmmm Mufeena Mufee tawa ai gashi nan kin fara girma har da Irgan dangi,Ammah mene Irgan dangi? tace gasu nan a kirjinki Kin fara Nono Mufeeda akwai maganar da za muyi anjima idan yaran nan sunyi bacci,kunya ce ta kamani nace to Ammah Allah ya kaimu bari na gama aikin ko kina da bukatar shiga bayi na taimaka miki? Ae rikeni muje Mufeedata Allah ya miki albarka,
DOWNLOAD HERE👈

Post a Comment for "KASUWANCI NA COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...