HAUSA ARAB CHAPTER 5 - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

HAUSA ARAB CHAPTER 5

HAUSA ARAB CHAPTER 5

- - Post a Comment

 HAUSA ARAB CHAPTER 5


Anajak Bangkong hotel, Bangkong Thailand.


4

Tafiyarmu zuwa kasar Thailand ba karamun tasiri tayi wajen dawomun da nutsuwata da hankalina ba wadanda na dade rabona da su. Hotel din da muka sauka mai kyawun gaske ne wanda yanayin shi kadai zai sanyaka nishadi. Ya Mahmud bai bari na samu damar samun lokacin tunani mai yawa ba. Gabadaya hankalinsu ya tafi akan bin duka hanyoyin da zasu dawo mun da kuzari da nishadi na. Hakan yasa nake

matukar kokarin ganin na danne duk wani bacin rai da damuwa da ke cikin raina domin na kwantar wa da su Mami hankali ganin irin kokarin da Suke haikan a kaina. Amma deep inside zuciyata wallahi damuwa ce da bakin ciki mara misaltuwa, mintina talatin basa shudewa ba tare da tunanin Aisha ya fado raina ba. Nakan faki ido na shiga toilet nasha kukana na wanke fuska na sa Kwalli na futo. Idan tunanin ya dameni wani lokaci sai na bude veranda na futo ina shakar sassanyar Iskar da ke kadawa ina kallon pool din da ke kasan hotel din.


Tunda muka zo Ya Mahmud yake kaimu wuraren bude ido da museum masu kayatarwa. Bama yini a gida sai can bayan sallar isha'i muke dawowa.

Yammacin alhamis din da tayi dai dai da kwanakinmu sha bakwai da zuwa Thailand Ya Mahmud yace mu shirya muje yin siyayyar tsaraba saboda kwanaki uku ya rage mana mu tafi gida.

Ina futowa daga wanka na shafa mai cikin sauri daman tuni na sallama make up da wahalhalunshi..... daga kwalli shima saboda kodewar da idanuna sukeyi nake sawa sai chapet ko nude lipstick idan Ya Nuratu ta matsa mun kenan.

Shiryawa nayi cikin wata neutral cold shoulder chiffon floral maxi dress wadda ta amsheni sosai.

Triangle dankwali na daure kaina dashi tare da sakin jelunan dankwalin zuwa kafatada ta. Na feshe jikina floral perfume mai dadi sannan na dauki jakata na sakalo chain dinta jikin wuyana. Takalmina sandal ne flat sosai domin nafi jin dadinsu yanzu.

Bayan mun kammala ne Amal ta shigo da gudu tana cewa Uncle yace mu futo ya gama.

Hannunta na rike muka futo su Mami

na biye damu.

Central World mall Ya Mahmud ya kaimu. Tun  daga hango view din wajen Ya Nuratu ta soma doki kamar wata yarinya, sai zuzuta kyan wajen da tsaruwarsa Takeyi. Da muka shiga kuwa babu Wanda wajen bai kayatar da shi ba, ko ni sai da ma tsinci kaina ina murmushi. A level 1 of central world din kawai muka tsaya saboda girman Mall din. Ya Mahmud yace kowa ya shiga inda yake da abun siya saboda kada mu bata lokaci da yawa. Ya Nuratu ta rike hannun Amal suka shiga Marks and Spencer. Mami ma ta bisu, Ya Mahmud ya kalleni yana nazarin yanayina sannan yace "me kike son dubawa?" A Sanyaye nace "ni idan akwai "The body shop" nan zan shiga, kayan shafana sun kare." Wani yaje ya tamabaya sannan ya dawo yace mun a level 2 din mall din yake. Muka tafi. Shi yake turamun trolley din ina zuba dukan abinda nagani ina bukata, harda Karin sabbin turarukansu masu sanyi da na gani. "Na gama Ya Mahmud we can go" na fada ina mikar da hannuna da ya soma tsami. Cewa yayi "Baki siya kayan kwalliya ba toh" nace "it's out of my hobby yanzu Ya Mahmud, bana bukata" gyara tsayuwansa yayi  soma magana cikin serious tone "Ya mukayi da ke jiya Zara? Wanne alkawari kikayi mun?" Nayi shiru. Bai jira amsata ba yace "ina cemun kikayi zaki kokari kiga kin koma old Zaran da na sani, sannan duk lokacin da kika tuno Aisha na gaya miki addu'a zaki mata shine kadai abinda zai amfaneta, shine at

ta San kina mata so na gaskiya! Wannan koke koken da tunani babu abinda zai amfane ku dashi daga ita har ke! I know it's not easy, I know how it feels Zara, I've gone through it, amma dole hakura kake kaci gaba da rayuwa hakan bai nufin ka manta da wanda ka rasa ko ka daina damuwa da shi, no! wannan shi ake kira rungumar kaddara da tawakkali. Please sister ki daure kinji? Idan kikaji kina missing Aisha ki dau waya ki kira Ihsan kuyi hira, ki gaya mata damuwarki, zakiji kin samu relief. Sannan kiyi ta addu'a Allah ya baki juriya da dangana zakiga kin samu sassauci sosai! Zara ina tausayin Mami, you have no idea how she feels idan tana ganinki cikin wannan halin, itama fa irin wannan rashin ya sameta, amma hakuri tayi ta ci gaba da rayuwa ta sadaukar da farin cikinta a kanmu. to me yasa mu ma ba zamu bi duk hanyoyin da muka san zamu faranta ranta ba? Rayuwar duniya ba'a dawwama cikin jindadi.......

...."

Wani ne ya zagayo ta bayan Ya Mahmud ya rufe masa ido! Cikin murmushi yace "who's this?" Mai maganar yace "guess" murmushi ya sake yi sannan yace "mubarak" ana fada gayen ya kwashe da dariya yana zare hannunshi daga fuskar Ya Mahmud! "Ya akai ka ganeni?" Ya fada cikin mamaki! Wani killer smile Ya Mahmud yayi yace "who wears women perfume bayan kai" suka kwashe da dariya suna tafawa. Sannan sukai hugging din juna na yaushe rabo! Nikam tsayawa nayi ina kallonsu da sha'awa. Wai Shi Ya Mahmud shi yake zaban abokai ne? Duka abokanshi kyakyawa ne masu class kamar su sukai kansu. Wannan ma wani handsome giant ne kamar shi yayi kansa. Kana ganinsa kaga cikaken bafulatin Nigeria sai dai baki ne na gaske, wanda hutu da danshin naira yayi wa faskwarima ya mayar unique.

Ina cikin wannan lissafin naji Ya Mahmud yace "meet my sister Zara" cikin murmushi yace "hy sister Zara nice meeting you" cikin jin kunya na risina na gayar da shi. Ya amsa cike da jindadin girman da na bashi, sannan yace "ina Mami?" Ya Mahmud yace tare muke ma.......Kan ya karasa sai ga wata gajeriyar mace fara sol mai kyau tana tura yar kyakkyawan baby cikin push chair. Tana ganinmu ta bude baki da mamaki "wa nake gani kaman Hausa Arab?" Mubarak ya dube ta yace "Kamar a mafarki ko? Jiya muke hirarsa" Ya Mahmud tuni yasa hannu ya sunkuci yar babyn ya rungume kamar zai gudu da ita. Sannan aka shiga gaisawa, "su nawa ne Mubarak?" cewar Ya Mahmud! Mubarak ya Sosa keya yace "su hudu ne, mun bar su Faruk a hotel suna bacci" cewa yayi "masha Allah! Allah ya raya su" matar da Ya Mahmud ya kira Surayya earlier ita tace "wannan madam din ka ce Hausa Arab? yaranku nawa" duk yanda yaso boye yanayin fuskarsa sai da wani  sashen ya bayyana damuwa, a sanyaye yana murmushi yace "No! She is my little sister. Banyi aure ba" da mamaki duka suke kallon shi Mubarak yace "tun bayan rasuwar Jawahir bakayi aure ba? Over 10years" tuni Idanun Ya Mahmud suka rikide suna wani maiko kamar zasu digo da mai. Ganin zasu jefa shi cikin wani hali nayi gyaran murya nace "amma yanzu an kusa auren shi saura 5months" Mubarak ya mika masa hannu a sanyaye yace "congratulations! Allah ya sanya alkhairi friend! Allah yajikan Jawahir" daga masa kai kawai Ya Mahmud yayi bai iya amsawa ba, Mubarak ya ciro card dinsa ya bashi yace sai sunyi waya zaizo ya gaida Mami har hotel dinmu. Mukai sallama da su. Sai dai I'm not comfortable at all da yanda Mubarak yake kallona. Ko bayan sun tafi sau biyu yana waiwayowa yana kallona muna tsaye bin layin biyan kudi.

Ni kuwa wani irin tausayin Ya Mahmud ne ya kamani, ashe yana da abokai masu yaya har hudu, shi baiyi auren ba, wanne irin so shi kuwa yake wa wannan Jawahir da ya kasa mantawa da ita yakejin ciwon rashin ta kamar jiya ta mutu?. Haka muka wuce ya biyamun makuden kudin siyayya ta da katinshi sannan muka futo. Sai gashi ni na ware na koma rarrashin sa ina ta dauke masa hankali domin ya dawo dai dai! Na dora da cewa "Mu shiga "Mango" Ya Mahmud mu siyawa Safna takalma da jaka ko ba zaka kai mata tsaraba ba?" Murmushi yayi yace "bata da size anan customized ne takalmanta sai na koma London zan siya mata" na girgiza kai. Daga nan muka shiga "Zara" muka dan siya abubuwa kafin Mami ta kira shi a waya tace sun kammala suna jiranmu.

Har yayi gaba na kira sunansa, ya tsaya cak yana kallona. a sanyaye nace "Ya Mahmud yanzu fa ka gama yimun nasiha kuma kai gashi kana yi" murmushi yayi ya hadiye hawayen da ke taruwa a idanunshi yace "I'm okay sister mu tafi. Ina wayarki ne?" Pouting nayi nace "wannan dan nacin ne ya dameni, sai ya kira sau hamshin a jere kamar mahaukaci, da na gaji sai na kashe wayar na ajiye!" Cewa yayi "Imam ko? nima diverting dinshi nayi da na gaji!"

************************************

   ABUJA, NIGERIA


Har karfe gomasha biyu na dare tattaunawar Daddy da lauyansa barrister Suraj makarfi bata kare ba. Domin fata suke su kammala komai cikin sirri ba tare da sanin waninsu ba. Bayan Daddy ya gama cike duk wata takarda da ake bukata shima Br. Suraj yayi nasa sannan ya hade su cikin file din da ke table din gabansu yana cewa "yanzu sai idan Mahmud din ya dawo komai zai kammala" Daddy cikin Karfin hali yace "don Allah barrister ka kula, a tafi da komai cikin taka-tsan-tsan.  Barrister yace "kada ka damu Alaji. Ba abinda zai faru da yardar Allah" daga nan sukai musabiha sukai sallama Barrister ya tafi.

Kan kujerar da ya tashi ya dawo ya zauna ransa a jagule, ya dade yana son yin wannan abu amma tunanin irin wadannan abubuwan da zasu shigo da tsoron halin da zasu iya fadawa ya hana shi yin komai akai. Amma lokaci tafiya yake, rayuwa tana gaba, mutuwa kuma na iya daukar mutum a kowanne lokaci, idan yaci gaba da binne wannan al'amari har lokacinsa yazo tabbas zai dana sani mara misali kuma zai bar baya da kura don haka dole ne ya fuskanci wannan matsala ya warwareta kafin hakan ya faru. Daren ranar sam baiyi bacci ba yana saka da warwara ya kulla ya kwance yana tunanin gamuwar su da Dada gobe, hanyar da zai bullo mata ta amince da wannan babban al'amari  saninta da yayi a matsayin jajirtacciyar mace, tsayayyiya mara daukar wargi ko raini mai tsayawa akan maganar. Bata tsoro bata shakka kuma bata lamuntar wani ya shigo mata da wani bakon al'amari cikin zuriyarta. A karshe dai alwala ya daura ya hau kan sallaya kamar yanda ya saba kowanne dare, yau kuwa da niyya ta musamman akan wannan lamari mai matukar muhimmanci a rayuwarsa ya tashi.

Washe gari da safe ya shirya tsab cikin shigarsa ta alfarma kamar yanda ya saba musamman idan zai je wajen Dada. Bai saurari abincin vicky kukun shi ba ya shiga bayan motarsa Abdul Hadi ya dauke shi zuwa gidan Dada zuciyarsa na luguden bugu har suka isa. Duk tarin dukiyar da ya mallaka da girma da matsayin da yake da shi baisa Dada ta ware shi cikin yayanta tana shakkarsa ko gudun zuciyarsa ba, mace ce dakakkiya kuma tsayayyiya akan yayanta mai adalci da gaskiya da amana.

Don haka ko yan koren nasa masu take masa baya bai dauki ko daya ba ya taho shi kadai, don yasan akwai tataburza da cakwakiya a kwance.

Lokacin da ya shiga cikin gidan tuni Baba Rabi ta kammala hada masa shiryayyun traditional dishes irin wanda yake so a katuwar shudiyar tattausar dadduma ta alfarma.

Dada na daga gefe akan sallaya tana walha. Sai ya cire babbar rigar fara sol din shaddar sa ya zauna ya soma serving din kansa da kansa ba tare da neman Baba rabi ba. Duk yanda yaso cin abincin bai iya ciwuwa a wajen sa ba, sai bakin shayi da ya cika cikinsa da shi.

Sai da ya kammala sannan Dada Dada shafa addu'a ta gyara zama ta zubo masa manyan idanunta masu cike da kwarjini da kada yan hanjin Wanda ta rutsa da su. Bayan ya gaishe ta a ladabce tayi gyaran murya ta sake daure fuska tace "wacce irin magana ka zo mun da ita mai kama da ta wanda ya futa daga hayyacinsa jiya? Na tabbatar dai baka shan komai, kuma na shaidi adalcinka da tausayi ga yaranka gabadaya, don haka nayi nazari kaf na kasa gane dalilin da yasa kake son yin wannan danyen aiki wanda zai rusa maka kyakykyawan zumunci da so da kauna da ke tsakanin yayanka?? Ina so na fahimta"

Salaam! We are back!

Hope you all had a wonderful Eid?

May Allah accept our act of worship!

I miss you guys alot.

I'm sorry for dropping this late, I have been super busy, but I just had to squeeze my time and write this chapter for you!

Wacce magana ce tsakanin Dada da Daddy? wanne yunkuri yake niyyar yi haka? Da alama dai akwai wani babban al'amari a boye wanda Daddy yake boyewa?Sai da gaban Daddy ya fadi kafin ya tattara duka dauriyar da yake da ita ya hado kan hankalinsa da tunaninsa ya tara su waje daya. Sannan ya soma magana cikin taushin murya da ladabi.


"Dada cewa nayi na rubuta a rubuce da sa hannuna da na lawyer na da kuma cikakkun shaidu cewa na mallakawa Mahmud kashi sittin bisa dari na abinda na mallaka a dukiya ta. Kuma ko da na mutu ban idda wannan nufi ba toh na rubuta wasiyya akan haka sai an soma cire wannan kason kafin a raba gadon abinda na bari!"


Wani irin kallon (me kasha?) Dada take wa Daddy tunda ya fara magana har ya kai aya, shi kuwa baisan hakan ba don kansa a kasa yake maganar. Cikin kaushin murya tace "saboda kaine shugaban mara sa adalci na duniya ko kuma shugaban mahaukata? Na dauka jiya wani abun ne ya shiga kanka ko kuma wasu magautan ne suka kawo wa kwakwalwarka hari saitin ta ya hargitse, shine na sallameka nace ka dawo yau da niyyar zan kwana inai maka addu'a toh ashe abun naka bai shafi gushewar hankali ko tabin kwakwalwa ba sai tsagwaran rashin adalci da tunani da kuma rainin hankali! Ni za ka fuskanta da wannan magana? Kanka daya?"+


Sake nutsuwa Daddy yayi duk da zafin maganganun Dada a gare shi bai bari ya nuna wata alama akan fuskarsa ba. Sai ma kara ladabta harshen sa da yayi ya dunkufar da kansa ya soma bayani a karo na biyu


"Kuyi hakuri Dada! Tsakanina da ku har abada babu raini ko wasa. Kuma wallahi ban sauya ko kadan daga yanda kika sanni ba, sannan banyi haka don na fifita Mahmud cikin yara ba. Akwai al'amura masu yawa Dada wanda nake rokon ki mun afuwa ba sai na gaya miki ba ki amince da bukata ta.

na kai shekaru goma ina son yin wannan yunkurin amma tsoron abubuwan da zasu biyo bayan haka ya sanya na ke fasawa. Lokaci tafiya yake kuma babu wanda yasan gawar fari shi yasa nake tsoron kada lokacina yazo ban idda wannan nufin ba. Kuyi hakuri Dada ki fahimce ni, wallahi banzo da rainin hankali ko son zuciya ba! wannan wani abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwata Dada ki yi mun wannan alfarmar"


Wani irin shiru ne ya biyo baya kamar babu halitta a wajen! Dada ta tafi wani dogon nazari mai zurfin gaske, ta yarda ta tabbatar da amana da adalci irin na danta, ta yarda da kyawawan dabi'u da tausayi da jin kansa kuma tana alfahari da samun da mai irin zuciyarsa don haka lallai wannan batu da yazo da shi akwai wani babban al'amari a cikinsa mai girma. Toh menene shi? Wanne irin sirri ne wannan da ya boye mata bayan bai taba boye mata wani abu na rayuwarsa ba, cigabansa da gazarwarsa, dadinsa da kuncinsa, bai taba yin wani abu bai shawarce ta ba. Musamman wani abu akan Mahmud wanda tunda ya fuskanci son da take masa ya tattara ya bar mata duk wata ragamar rayuwarsa da jagorancin sa. Meye Wanda ya boye mata tsakaninsa da Mahmud? Wadannan tambayoyin Dada take wa kanta, sai dai kaf ta gama tunani bata da amsa. Hakan ya sake dugunzuma ranta hankalinta ya tashi. A karshe dai kawai cewa Daddy tayi

"Ka bani wani lokaci zanyi tunani akai, zanyi addu'a. Ni da kaina zan neme ka idan na kammala! Sai dai ina so kaima ka kara addu'a akan wadda kake yi kuma kayi tunani mai zurfi kafin lokacin"

Cikin ladabi Daddy yace "toh Dada insha Allahu! Allah ya kaimu! Nagode Allah ya saka da alkhairi Allah ya kara girma"

A sanyaye tace "Ameen" sannan ya dago daga sunkuyen da yake yace "Dada lokacin zuwa Jedda yayi fa, har ma munyi magana da likitan"

Ajiyar zuciya tayi a ranta tace "koma banje jedda don asibiti ba, ai naje Makkah da Madina nayi wa wannan lamarin da kazo mun da shi addu'a" don haka ga mamakin Daddy wannan karon batai musu ba tace "to ai sai a shirya lokacin tafiyar" cikin jindadi yace "ai tafiyar na hannunku, duk saboda kuka shirya jirge yana jiranku"

A nutse tace "to mu bari su Zainab sun dawo tukunna sai a san me za'ayi! Jibi ne dawowar tasu ko?" Yace "eh amma sai gata zasu iso nan Abuja, sai sunyi transit a Dubai kafin su iso" tace "Allah ya kawo su lafiya" daga nan kuma suka shiga hirarraki irin wanda suka saba yi idan sun samu lokacin zama tare. Sai gab da azahar Daddy yayi mata sallama ya koma gida, a yammacin ya wuce America zai halarci wani taro da za'ai akan yanda za'a habbaka tattalin arziki da bunkasa kasuwanci.

------------------------------------------------------------


STORY CONTINUES BELOW

Bangkong, Thailand.


Tashi na daga bacci kenan na tashi daga kan gadon nasa remote na zuge duka labulayen dakin hasken rana ya shigo sannan na shiga toilet nayi brush nayi wanka da alwalar sallar la'asar! Yau yini nayi ina bacci ban bi su Mami kasuwa ba. sai Amal da ke ta baccinta itama.

Bayan na idar da sallah nayi shafa na shirya cikin wata "Valentino floral print long sleeve tiered faille mini dress" Kalarta baki da ja sai na saka bakin pencil Armani trouser daga kasa.

Na taje gashina wanda ya cika sosai a dalilin rashin kula da nake da shi kwanan nan, katon red ribbon na daure gashin da shi daga tsakiya sannan na kwantar da gaban gashin nawa da jan band madaidaici. Ba da niyyar kwalliya nasa kayan ba amma ni kaina sai da na tsurawa kaina ido a jikin mirror saboda yanda kayan suka karbeni fiye da tunanina. Sai na zauna gaban mirrow din nayi skin care routine dina fuskata sai glowing take. sannan na tashi Amal nayi mata wanka. Ina cikin shirya ta su Mami suka dawo. Na kammala muka futa parlour gabadaya!


Ya Mahmud na kwance akan tree seater na kyalkyale da dariya nace "Ya Mahmud in ce kuwa Ya Nuratu ce ta baka wahala haka?"

Ba tare da ya juyo ba yace "ai ni da shopping da Nuratu...... ko kyauta zata siyemun kayan na yafe wallahi" na sake yin dariya. Nace "me tayi maka Ya Mahmud? Sai ta cika trolley da kaya zata mayar tace ta fasa ko?" Da sauri ya tashi zaune yana cewa "awww daman ta saba yin hakan? Tana diban kaya tana calculating kudin, da ta gama ta ga kudin sunyi mata yawa sai ta aje komai tace ya fasa! Ni bansan lokacin da ta koyi wannan son kudin ba"

Ban kalli Ya Nuratu da ke ta faman harara ta ba nace "Ai daman haka take Ya Mahmud, kaine baka sani ba! wataran ma sai ta dawo gida tayi lissafi zata mayar........." pillows Ya Nuratu ta shiga jefomun ina dariya na tashi da gudu zan shiga kitchen na jiyo karar kofa!

A tunanina room service ne na bude da sauri....a sukwane naja baya ganin wani giant din mutum a tsaye sanye cikin fara sol din shadda karamun dinki sai walkiya take, Bazan gano ko waye ba a dalilin mugun tsayin da yake da shi wanda sai na shilla kaina sama sosai zan gani, kafarshi wani lafiyayyen takalmin fata ne brown, duka hannyensa dauke da jakunkunan Chloe da Dior. Kamshin turaren mata na Arabian Oud ya bugi hancina. Take nagano cewa Mubarak ne abokin Ya Mahmud.

Na koma da sauri falon ina haki. Na dubi Ya Mahmud nace "abokinka yazo yana tsaye" da sauri ya mike yana cewa

"Shine kuma kika taho kika barshi a tsaye Zara" ni dai na nemi kujera na zauna ina zare ido!

mintina biyu suka shigo tare. duk tsayin da Ya Mahmud ya mallaka wannan basamuden ya fishi. Bayan sun zauna muka gaishe shi, ya bini da wannan mayen kallon nashi irin na rannan, sai na tashi da niyyar komawa daki, Ya Mahmud ne yace "yauwa Zara gaya wa Mami ga Mubarak yazo, ki kawo masa ruwa kuma" ba'a son raina ba na tafi aiken.

Bayan na gayawa Mami na wuce kitchen na hada lemuka da ruwa da cookies na saka a tray na dauko. Da na iso falon mamaki ya cikani, yanda suke hirar sabo da Mami sosai da alama ba karamun sani tayi mishi ba. Ina aje tray din a gabanshi na juya na koma daki.

Wayata na dauko na kunna da niyyar kiran Ihsan, amma tun kafin na nemo number Ihsan kiran Imam ya shigo. Kamar jira yake na kunna. Cikin haushi nayi rejecting call din na nemo number Ihsan na kira, bugu biyu ta dauka.

"Haba Zara kuma sai ki daukeni ki saka a kwandon shara? Me nayi miki don Allah?" Ajiyar zuciya na sauke nace "kiyi hakuri Ihsan wallahi Imamu ne yake takuramun da waya shiyasa na kashe wayar kawai na hakura da kiran kowa, kiyi hakuri" Cewa tayi "ke! Duniya abun tsoro Zara kinga kuwa yanda mutumin nan ya koma? Kinga lalacewar da yayi kamar dan drug? Sau biyu yana wuni a kofar gidanmu wai yazo na taimaka na baki hakuri, sai da faisal yace zai kira mishi yan sanda ya tafi! Abun tsoron ya isa Zara, wallahi kayan da suke jikinsa zasu baki mamaki, yayi baki ya futa hayyacinsa" share kwallar da suke zubomun nayi ina tuno halin kuncin da ya sanya Aisha ciki da barazanar da ya dinga yi mata gashi tun kafin ayi nisa Allah ya kama shi. Nace

"Hmm Ihsan ita rayuwa idan har zaka mayar da yaudara da zalunci dabi'arka ai karshen ka ba zai dadi ba! Son ranshi ya aure ni ya saka ni cikin wannan kuncin da bala'i, Allah ya kubutar dani."

A nutse Ihsan tace "kai Anya? Zara ba son yaudara Imam yake miki ba wallahi. Sai dai mu bar shi akan cewa Allah ne ya kama shi ya jarabceshi da sonki don ya hukunta shi akan yaudarar da yayi wa yan mata. Amma Imam na tsananin sonki fiye da tunanin ki wallahi" tabe baki nayi nace "sai yaje ya karata da matsalar shi! Ya zancen zuwa shopping din? Yaushe zaku tafi?" Tace "Mummy ta siyo komai a London Zara, daman kinsan Faisal ba son tafiyar yake ba, yana ganin kayan da ta kawo, yace an fasa." Dariya nayi nace "toh Allah ya kawo mana babies lafiya" tace "an tabbatar baby girl ce guda daya, kin daina tsorata ni" nayi dariya. Mun dade muna hira kafin muyi sallama. Daman Imam sai shigowa layi yake nayi maza na murtsike wayar na wulla cikin jaka.2

Saurarawa nayi kadan, sai naji kamar suna maganata a parlour kasa kasa. Na sake matsawa jikin kofa sai na tsinto muryar Ya Mahmud yana cewa "Mami daman tun shekaranjiya nasha jinin jikina, jiya sai ya kirani yana cewa wai don Allah anyi wa Zara miji? Nace masa da tuni anyi bikin ma fasawa akayi! Harda ihun shi, wai in Allah ya yarda rabonsa ce! Bakiga magiyar da ya dinga yimun ba akan na shawo masa kanta. Yana da matsala sosai da matarshi, kuma Mamanshi ta matsa masa akan ya kara aure sai dai shi bai ga wadda yake so da zai iya aure ya hada ta da Surayya ba. Wai yana ganin Zara yaji kamar an amsa mishi addu'ar shi" suka kyalkyale da dariya. Ya Nuratu tace "wallahi naji dadi Ya Mahmud, the guy is soo nice, gashi kunsan komai game da shi da iyayensa, sai dai ita yar rigimar ce bansan ta yanda za'a bullo mata ta amince ba" Ya Mahmud yace "ai babu dole, Zan barshi ya gwada sa'ar shi, idan ta amince shikenan, idan kuma taki sai ya hakura" Ya Nuratu tace "insha Allah ma zasu daidaita ni nayi mata sha'awar shi wallahi!" Ya Mahmud yace "Mami baki ce komai ba?" A sanyaye tace "me zance Mahmud? Ni fatana Allah ya zaba mata abinda yafi alkhairi."

Wani irin gumi naji yana karyomun duk da sanyin Acn dakin na koma gadona na zauna ina maida numfashi! Ko farfadowa daga halin da Imam ya sakani ciki banyi ba za'a kuma jajubo mun wani mutumin?shin auren dole ne?

------------------------------------------------------------

Five days later.


Mun dawo gida lafiya! Sai dai a maimakon kaina yayi sanyi na samu nutsuwa, sai kuma Mubarak ya sake jefani cikin wani tunanin, tunda Ya Mahmud ya bashi number na kullum sai ya kirani, ba wai tsanar shi nayi ba, kawai dai tsoro nake ji domin Imamu ya koyar dani darasin soyayya. Amma maganar gaskiya mutum ne mai kirki da kuma barkwanci, sannan tunda ya fuskanci yanda nake da Aisha sai ya mayar da hirarta topic dinmu. Nikam babu abinda nake so kamar na samu wanda zamu yi hirar Aisha da shi, idan nayi maganarta sai naji na samu wani relief da sanyi a zuciyata, sabanin yanda su Mami suke ganin kamar yawan hirar ta da su zai kara fama mun ciwon rashin ta ne shiyasa basa bari maganar ta tayi tsayi tsakaninmu, Wanda kuma ba haka bane.

Toh sai nace ta wannan hanyar Mubarak yaci lagona, nake saurarar shi sosai!

Drop your comments.

Lots of luv❤

Yuppy! Its another update😀😀 I'm too sweet right?💃😀😀
Ok if you are happy pray for me on this blissful day🥰
Don't forget to recite surat kahf if you are reading this today!
Jumua Kareem!
Ringing din wayar sa ne ya tashe shi daga baccin da ya fizge shi dakyar akan king size bed din dakin da Mami ta mayar mishi nashi! har wayar ta tsinke bai samu kokarin tashi ya dauko ta ba, sai ma sake mirginawa karshen gadon yayi yana ci gaba da tunanin damuwoyin da suka sanya shi gaba, da farko dai a zamanshi a gidan Mami wancan zuwan na bikin Faisal da wannan ya lura da cewa akwai babbar matsala tsakanin Mamin da maigidanta Alh Idriss kuma a dukkan nazari da binciken da yayi ya tabbatar duka matsalolin akan kudi ne, kudin Mami yake ci ita kuma ta rasa ta hanyar da zata bullo masa ta karba ba tare da sun samu baraka ba. Yafi baiwa kansa amsar cewa rantar kudin Alh Idris yayi sanadin tuhumar da EFCC take masa akan mukuden kudaden da ya handame lokacin da yake kan kujerar ministan tsaro na kasa. Rigingimu ne kala kala a kansa musamman da ya kasance wannan sabuwar gwamnatin ta abokan adawar su ce. Shi dai Mami bata bude baki tayi mai bayanin komai ba, kuma bayaso ya tare ta da maganar ba tare da ta yi masa ba. Amma yana tsoron kada Alh Idris ya durkusar da baiwar Allah don yana ganin tana da hakuri ba zata daga masa hankali ba. Amma ya rasa ta ina zai fara, me zaiyi? Lallai yana bukatar yin wani abu akai kafin wata matsalar ta faru. Sam mutumin bashi da kirki, kudin Mami kawai ya hanga yayi amfani da dangantakar yayansa da baban Zara ya auri Mamin ba wai don so ba. Ya tabbatar kuma bata jin dadin zama da shi.+

Matsalar shi ta biyu itace Safna da halin da take son jefa kanta ciki. Gabadaya ta sauya ta chanja sauyi mai ban mamaki, ta daina kiranshi gabadaya sabanin da, da zata kira shi a kalla sau uku a rana ko tana wajen aiki ne kuwa. Sau da yawa shi yake kin daukar wayar don kar ta ishe shi da surutun ta. Amma yanzu Sam ta daina, sai ya kira sau goma bata dauka sau uku ba. Sannan her voice is always very weak, soo weak kamar mai magagin bacci, da ya soma tunanin ko bata da lafiya ne ko kuma wani abun ke damunta sai dai ya san ta a matsayin extrovert wadda bata iya boye feeling dinta ko sirrinta wani abu na rayuwarta. She is outspoken and straightforward, idan tana da matsala shi zata fara tunkara da ita su warware tare. Hankalinsa bai tashi ba sai jiya da ya kira ta dinga bashi amsar shirme, a karshe ya kashe wayar tasa. Zato zunubi ga Musulmi amma gabadaya ya kasa tsaida zuciyarsa ta daina tunanin me Safna take! "DRUG" kalmar da ta fado masa rai kenan! Wani irin dokawa kirjinsa yayi ya mike zaune yana fadin "innalillahi wa inna ilaihi rajiu'un" Allah yasa hasashen shi ba gaskiya bane!
Cikin sauri ya dauko wayarshi, ganin misscall din Daddy yayi amma tsabar rudanin da yake ciki bai fara kiran Daddyn ba ya shiga neman layin Safna. A kulle wayarta ta take. Ya furzar da huci mai zafi kafin ya lalubo lambar engineer babanta. Bugu daya ya dauka suka gaisa cikin mutunta juna, daga nan yake tambayar shi Safna cewa yana ta kiran wayarta a kashe. Cikin nutsuwa Engineer ke masa bayani
"Safna tana Scotland Mahmud taje gidan kawarta joyful" ji yayi makoshinsa ya bushe, dakyar ya sake bude baki yace "me taje yi wajenta har ta aje aikinta saboda shi?" Engineer yace "a yanda tace mun dai wai joyful din sun rabu da saurayinta tana kokarin aikata suicide shine taje ta zauna da ita ta kwantar mata da hankali....amma" kit Mahmud ya latsa madubin wayar ya kashe wayar ya cillar gefe tare da dafe kansa. Yau anyi Uban banza uban hofi. Bakar wahalar da yasha kafin ya samu nasarar raba Safna da Joyful ba ta wasa bace. Joyful shaidaniyar baturiya ce mai hadari, tun ranar da abokin aikinsa Dr.Ahmad mutumin Yemen ya ganshi da Safna ya gaya masa gaskiyar abinda ya sani game da ita, yace masa baisan halin Safna da tarbiyyar ta ba amma yana ganinta da Joyful, ita kuwa Joyful ko turawan tsoron sharrinta suke yi da shaidancinta. Daga nan Mahmud ya soma daukar matakin akan Joyful, Safna ya fara jawa kunne akan ba ita ba Joyful idan kuma bata yarda ba toh sai dai su rabu da shi, wannan barazanar ta sanya Safna shiga taitayinta ta hakura da hulda da Joyful domin tsoron rasa masoyin nata. Shikuma ganin taji maganar sa yasa yaji dadi ya sakankance cewa a Danny a hankali zai iya saita ta ya dawo da ita turbar da yake so tabi, sai akayi dace kuma ta zama kamar rakumi da akala, duk abinda ya sata shi take yi babu musu, wannan ya kara bashi kwarin guiwa wajen neman aurenta. Bai San cewa mata irinsu Safna sun zarce sanin shi da wayonshi da dabararshi ba, bai san san cewa gaula kawai ta mayar da shi ba.
STORY CONTINUES BELOW

Hankalinsa idan yayi dubu ya tashi, ji yayi gabadaya bashi da burin da ya wuce ya ganshi London, kamar yayi tsuntsuwa ya rufe ido ya bude a Scotland gidan Joyful! Kai!! Da yaci ubansu gabadayansu! Ya zama dole ma ya tattara ya koma London a satin nan, yaje ya yaga badakalar da Safna take aikatawa da idanunshi yasan matakin da zai dauka. Ji yayi kirjinshi na mishi wani zafi, wai ace matar da yake shirin aure ke bijiro da irin wadannan miyagun halaye! Take Jawahir ta fado masa rai, yarinyar da ko cikin family dinsu ana kwatance da dabi'arta da kamalarta! Wayyo mutuwa mai yanke Kauna! Me Katse farin ciki, mai raba masoya, da tuni suna zaune cikin kwanciyar hankali da Jawahir kilama da yaransu.

Wasu zafafan kwalla suka taru a idanunshi, lallai duniya akwai rikici kala kala a cikinta! Wayarsa ce ta sake kuwwa ta dawo da shi daga halin da ya fada! yana dubawa yaga Daddy! Da sauri ya zauna sosai yana swiping wayar! "Hello Daddy" ya fada muryasa a sanyaye!
Ta bangaren Daddy ma cikin dauriyar yace "Mahmud kana jina? Ina son ganinka 5pm a Mississippi" ba tare da kawo komai ba Mahmud ya amsa da toh sukai sallama! Time ya duba yaga hudu saura kwata! Cikin hanzari ya Mike ya fada toilet yayi wanka da alwala ya futo a gaggauce ya gyara gashin kansa ya taje sannan ya shirya cikin fara sol din shadda Hilton. An cika ta da dandasheshen dinkin Senegal da coffee din zare! Tana daya daga cikin sabbin kayan da Faisal ya dinko ya kawo masa jiya! ya ciro "La Nuit" ya feshe kwalliyar da shi. Wayoyinsa ya kwasa da katin bankinshi ya saka a aljihu ya iso wajen takalma ya zura lafiyayyen takalmin fata na "Hermes" Kamar daga jikin zaren dinkin aka ciro shi.
Shi kansa duk da halin da yake ciki sai da ya tamabayi kanshi waye ya saka shi wannan kwalliyar haka?ina zaije? Tabe baki yayi ya kashe fitilar dakin ya futo ransa a jagule.

A parlour ya samu Mami tana waya, sai yayi mata alama da hannu ya futa zuwa masallaci sallar la'asar. Ana idarwa ya dawo suka ci lunch tare sannan ya gaya mata cewa Daddy ke nemanshi yayi mata sallama ya futa. Itama tana kammala tayi wanka ta shirya ta tafi office dinta don tana da appointment da wasu mutane.
Karfe biyar saura mintina bakwai ya isa personal gidan Daddy na sirri da ke Abuja. Muhimman abubuwa ke kaishi gidan, kuma amintattun sa kadai suka san akwai gidan, a tunanin Mahmud maganar Mubarak zaiyi masa don jiya mahaifin Mubarak din ya bugawa Daddy waya yace suna son zuwa tambayar auren Zara domin cikin kankanin lokaci suke so ayi komai a gama. Daddyn yace su bashi sati biyu zaiyi shawara zaiji kuma ta bakin ita Zaran.
Sai da ya wuce duka manyan falukan gidan baiga Daddy ba, ya ciro wayarsa ya kira shi, sai yace masa yana bedroom dinsa a sama. Mahmud ya zagaya ya hau benen a ransa yana wasi wasin maganar da Daddy zai masa wadda sai sunje can kololuwar gidan.
Da sallama ya shiga makeken bedroom din mai dauke da formal setting kamar fadar shugaban kasa yana zaune kan lallausan dadduma da takardu a gabansa. A ladabce ya tsuguna yana cewa "Daddy barka da yamma" cikin murmushi Daddyn ya amsa cike da Kulawa. Sai dai suna hada idanu da Daddy gaban Mahmud ya doka, wasu irin feelings ya hango cikin idanun Daddyn a yau masu yawa "TAUSAYI, SO, KARYEWAR ZUCIYA" Ya san irin tsananin son da mahaifinsa yake masa amma bai taba ganin idanunshi cikin wannan yanayin ba sai ranar da yake kwance gadon asibiti a liver pool numfashi nayi mar barazanar yankan kauna. Toh me yake faruwa?
Sai yaji jikinsa yayi sanyi. A hankali ya tsinkayi muryar Daddy cikin tsananin nutsuwa da taushin sauti yana yi masa wasu maganganu masu matukar nauyi da jefa zuciya da kwakwalwa tunani.

"Mahmud!!! A kullum na ganka ina jin farin ciki da alfahari mara misali ina kuma godiya ga Allah ya azurtani da kai! Tabbas kana daya cikin arzikin da Allah yaimun baiwa da su a rayuwa! Tunda ka budi idanu kasan menene matsayin iyaye kake mun tsantsar biyayya da kulawa da riritawa, ban taba saka kaki ba, ban taba hanaka kayi ba! Kaine misalin da zuciyata ke ayyanawa a duk lokacin da naji ana magana akan biyayyun 'yaya masu albarka! Kaine sanyin idanuna Mahmud! Kuma har abada bazan samu wani abu wanda zan iya daidaita kaunar sa da wadda nake maka ba!...kasa a ranka Mahmud ko bayan raina cewa kaine duk wata baiwa da karamci da arziki da farin cikin da na samu a rayuwa a dunkule........"

Kafin Daddy yayi nisa tuni sassanyar zuciyar Mahmud mai rauni ta karye! Hawaye sun soma diga a hankali daga cikin idanunsa suna gangarowa kumatunsa. Idan akace menene weakness dinsa a duniya toh "Daddy da Mami ne" wasu mutane da ko sunansu yaji tsigar jikinsa ke mikewa! Wasu mutane da baisan sikelin da zai iya gwada nauyin dimbin soyayyar da yake musu ya dauka anan duniya. Baisan mahaifiyarsa ba amma bai taba tambayar ta ba, bai taba damuwa ya sani ba a dalilin bude ido da yayi ya ganshi a hannun wata mace wadda za'a tara iyaye mata dubu ba'a samu irinta ba. Wata mace wadda yake jin idan da ransa a hannunsa yake zai iya dauka ya bata ba tare da second thought ba!.. ji yayi Daddy ya dafa kafadarsa a hankali.

"Noo! Mahmud daina kuka! Bana son ganin hawayenka! Inai ma shimfida da wadannan kalaman ne domin na dada jaddada wa zuciyarka cewa no matter what, kai din nawane kuma bazan taba yin wani abu don na cutar da kai ko na bin son raina ba."

A cikin muryar kuka Mahmud yace "Daddy go straight to the point! Idan wani abu kake bukata a wajena ba sai kamun wannan bayanan ba, wallahi ko Dan yatsanka Daddy ba zai fi zuciyata saukin sarrafuwa a wajenka ba, just say a your wish! Zan cika ma ko menene idan har bai ketara dokar Allah ba"

Cikin dauriya Daddy yaja hancinsa ya sake tausasa harshensa sannan yace
"Mahmud hukunci biyu zan zartar akanka masu tsauri sosai! Sannan idan na gaya maka bana son kamun tambayar meyasa! Wannan shine abinda yasa na kirawo ka Mahmud! wadannan abubuwan biyu sune na biyun karshen Burikan da nake da su akanka! Idan na samu wadannan toh wallahi ko gobe na fadi na mutu ban mutu da wani buri ba, sai dai na karshen su shine ganin yayanka na takawa a doron duniya"

Hawaye ne ke futa kamar an balle famfo daga idanun Mahmud lokacin da yake cewa "Daddy ka zartar da duka hukuncin da kake so a kaina kamar yanda zaka juya yan yatsun hannunka, ko su sunyi ma gardama zuciyata zata kasance mai biyayya a gare ka Daddy!"

A tausashe Daddy yace "Na nemar maka auren Amina yar gidan Alhaji Ibrahim mai atamfa da ke Kano! Shekarunta ashirin da biyar ta kammala karatunta na medicine a BUK wannan shekarar! Nasan kasan Alh Ibrahim kuma kasan yanda muke da shi! Na yaba kwarai da tarbiyyar yarinyar tun kafin nayi tunanin hada aurenku! Ina sane da maganar Safna kuma ban janye ba, su biyu zaka hada ka aura lokaci daya! Banyi haka don na hada ma zafi ba, ko na takura maka ko....."
Cikin murmushin karshen karfin hali Mahmud ya dakatar da Daddy ta hanyar cewa
" Daddy ko mutuwa ka aiko wajena ta daukeni zan mika wuya na tafi da tunanin kasan itace tafi dacewa dani a wannan lokacin, babu cutarwa ko takura tsakaninmu Daddy! Idan har kaga ban aure ta ba, toh sai dai bana raye ko kuma Kaine ka dawo kace ka fasa! Meye na biyun?"

Duk dauriyar Daddy sai da ya hawayen sa suka gaza rikuwa ya soma shashsheka a hankali. Ya za'ai ya hada Mahmud da wani abu a zuciyarsa?
A hankali Daddy ya janyo takardun da ke gabansa ya mika masa sannan ya dauko biro ya dora a kai! "Ka saka hannu cikin takardun nan gabadaya ba tare da musu ba"
Da azama ya karba yasa hannu ya fara cikewa daya bayan daya ba tare da karanta abinda takardun suka kunsa ba! ya kammala ya turawa Daddy takardun gabansa!
Murmushi Daddy yayi yana goge hawayen da ke fuskarsa da hannunsa sannan yace "Mahmud na mallaka maka kashi sittin cikin dari na abinda na mallaka a rayuwata! Kuma ko bayan raina sai an cire wannan kason kafin a raba sauran abinda na mallaka! Kar kayi tunanin na kauce Shari'a, da hankalina da ilmina da taimakon babban malamin addini na zartar da wannan hukuncin. Bana son tambaya ko kalubalanta daga gare ka! Idan Allah ya kaimu kayi aure zan tattara komai na mallaka maka a hannunka nabi ka da addu'ar Allah ya taya ka riko! Idan na samu ikon yin wannan abu biyun toh wallahi na gama cika burina, na samu damar sauke hakkin da ke rataye a wuyana tsayin shekaru talatin da tara! Idan da wani burin toh bai wuce kuma na ganin yayan da zaku haifa ba"

Diff! Numfashin Mahmud ya tsaya na dakika! Kansa ya Sara! Kwakwalwar sa tayi cak! Kafin a hankali komai ya dawo masa dai dai! Ji yayi kamar stress din da ya dorawa kwakwalwar tashi ne yayi mata nauyi da yawa ta soma kwancewa don haka sai ya tsaida tunanin baiji da kyau bane, idan ya nutsu zai gane abinda Daddy yake nufi!

Dan! Dan!! Dan!!!
Isn't this scene emotional?😪😫
Wai menene a rufe a cikin karkashin kasa bamu sani ba? Drop your comments🥰Karfe biyar da rabin wannan yammacin Mubarak ya shigo da hancin motar sa cikin harabar gidanmu! Ina dakina a kwance ina tunanin sauyin rayuwa, wai yau babu Aisha, na fasa auren Imamu, Mubarak ya maye gurbin shi! Watanni hudu da suka wuce idan nayi mafarkin da ya hasko mun haka zata faru bazan gasgata ba, gashi komai ya sauya a dan kankanin lokaci! Baba Rabi ce ta bude kofa ta shigo, na dago kai ina kallon yanda take faman washe hakora kamar gonar auduga!

"Uwar dakina ga fa Maigidan namu ya iso! Taso taso ki shirya mana" murmushi nayi kawai na daga mata kai, ta juya tana cewa bari naje na karasa hada masa abincin! Ni dai ban tofa mata ba na tashi jikina a sanyaye na shiga toilet nayo brush na futo!

Riga da wando ne a jikina sai na bude wardrobe na ciro abaya na saka na nade fuskata da mayafin!

In banyi sa'a ba nasan sai munyi fada da Dada akan bakaken kayan nan da nasa! Ta tsani abaya a rayuwarta, nikam kwalliyar ce take ban wahala shiyasa nafi amfani da dogayen riguna da abayar yanzu!

Cikin sa'a kuwa da na futo tana dakinta ita da Ya Nuratu, sai na wuce sadaf sadaf na futa ina tunanin wainar da zamu soya da Mubarak!

Da cikakkiyar sallama na shiga guest room din, ya hakimce akan 2 seater da ke falon cikin shigar sky blue din shadda babbar riga! Sai kamshin 212 falon yake! He looks matured! Babban mutum sosai don zakai tunanin akwai tazarar shekaru tsakaninsa da Ya Mahmud! But he is handsome kuma yana da far'a sosai da barkwanci! He is very simple kuma bashi da jin kansa ko daya!

Bayan mun gaisa ya sake gabatar mun da kanshi cewa shine na biyu a wajen mahaifinsa Alh Ishaq kuma shi kadai ne namiji. Shekarunsa shadaya da aure yana da yara hudu! A Lagos yake zaune yana aiki a hukumar fasa kwauri ta kasa, bayan nan kuma yana harkar shigo da motoci daga America!+

"Bani da matsala da matata Zara kuma ina fatan zaki girmama zaman da Zaku yi tare duk da ba gida daya zaku zauna ba! Sannan idan kina da ra'ayin cigaba da karatu kofa a bude take! Bana son a dau lokaci me tsayi Zara! In 3months a kammala komai ayi biki"


Tunda ya fara maganganun kawai naji baya burgeni, ni fa gaskiya a waya ma nafi son mutumin nan akan a zahiri! Amma na fi danganta hakan da illar da Imamu yayi wa zuciyata wadda bata gama healing ba har yanzu! Beside auren kawai nake bukatar nayi naci gaba da rayuwata! Kila ko zan saitu na fuskanci rayuwa ta gaba! Bayan ya kammala serious maganar ne kuma ya dawo wasa da dariyan da ya saba, yayi ta bani labarin abotar su da Ya Mahmud da zamansu a School wai shi yake tarewa Ya Mahmud fada. A wannan bangaran kam ya samu lamba daya! He knows how to entertain mutum har ma ka manta kana da damuwa.

-‐----------------------------------------------------------------

Wani irin tuki Mahmud yake mai hadarin gaske, Allah dai ya kawo shi gida lafiya! Tun a cikin motar ya soma jin zazzabi don haka da kyar ya isa dakinsa ya fada gado yana rawar sanyi duk da kiran sallar magrib din da yaji ana yi bai iya motsawa ba, sai ma sake shigewa cikin Duvet din da yayi. Sunan Allah ya dinga kira yana kawo duk addu'ar da tazo bakinsa, a hankali bacci mai nauyi ya dauke shi! Bashi ya farka ba sai karfe tara na dare! A hanzarce ya shiga toilet yayi alwala yazo yayi sallarsa shi kadai sannan ya koma ya kwanta!


"Mahmud na mallaka maka kashi sittin cikin dari na abinda na mallaka a rayuwata! Kuma ko bayan raina sai an cire wannan kason kafin a raba sauran abinda na mallaka! Kar kayi tunanin na kauce Shari'a, da hankalina da ilmina da taimakon babban malamin addini na zartar da wannan hukuncin. Bana son tambaya ko kalubalanta daga gare ka! Idan Allah ya kaimu kayi aure zan tattara komai na mallaka maka a hannunka nabi ka da addu'ar Allah ya taya ka riko! Idan na samu ikon yin wannan abu biyun toh wallahi na gama cika burina, na samu damar sauke hakkin da ke rataye a wuyana tsayin shekaru talatin da tara! Idan da wani burin toh bai wuce kuma na ganin yayan da zaku haifa ba"


Abinda kwakwalwar sa ke ta tariyo masa kenan! Kalmomin na kuwwa cikin kansa kamar zasu tarwatsa kwanyar sa! Me Daddy yake nufi da ya mallaka mishi 60% din abinda ya mallaka? Bayan ya san su uku ne a wajen Daddyn! Shi kansa karamun millionaire din kansa ne wanda bai bukatar komai a rayuwa toh me zaiyi da kudin Daddy? Babban tashin hankalin da tunani shine cewar da Daddy yayi wai da ilmi da sharia yayi amfani wajen yanke wannan hukunci!

Duk yanda yaso fassara wannan al'amari ya gaza! A lokacin da Daddy yace yayi masa zabin mata bai dauka akwai wani al'amari wanda za'a sake gaya masa ya doki kansa irin wannan ba, ashe gaba da gabanta, don girman wannan batu na biyu ya shanye fadin duk wata magana da aka taba gaya masa mai nauyi a rayuwarsa!

Babu abinda ya kamace shi irin ya lallaba ya koma London zai fi samun lokaci da nutsuwar yin nazarin komai a tsanake! A kagauce ya janyo laptop dinshi ya shiga yanar gizo ya soma neman booking online! Yana cikin hakan kiran waya ya katse shi, a hankali ya kai hannunsa kan side drower ya dauko ta yayi swiping da sauri ganin sunan Daddy sannan ya daidaita muryarsa yayi sallama! Sai da ya jiyo saukar ajiyar zuciyar Daddy kafin yayi magana "Mahmud are you ok? Kana ina?" Tausayin Daddyn ne ya kama shi tare da sabuwar kaunar shi! A cikin tone mai kwantar da hankali yake cewa "I'm fit and fine Daddyna! Me zai sameni kana tare dani?" Murmushi Daddyn yayi sannan yace "Alhamdulillah! kabi komai a hankali Mahmud, ka sanyaya zuciyarka kaji? Ka mikawa Allah lamuranka Insha Allahu ba zaka tozarta ba har abada" shima murmushin yayi na karfin hali yace "insha Allah Daddy! Kaci gaba da yimun addu'a! Yanzu ma booking nake yi zan koma London in 2 days na bar ayyuka da yawa kuma akwai bukatar nayi wa Safna da babanta bayani tun wuri!" Cikin gamsuwa Daddy yace "hakane! Nima zan kira shi nayi masa bayani na bashi hakuri! Allah yasa komai yazo mana da sauki! Allah ya baka juriya ya dafa maka ya tsaya maka akan dukkan lamuran ka!" Cikin jin dadin addu'ar Mahmud yace "Amin Daddy nagode Allah ya kara girma" dan Jim Daddy yayi yace "amma na zata zaka dan leka wajen Amaryar ku fahimci juna kafin ka koma" kunya ta kama Mahmud! Hakan ya kamata ya soma yi kafin yayi tunanin zuwa rarrashin uwargida! Ganewar da Daddy yayi ya baiwa Mahmud kunya sai yayi dariya yace "Mahmud sarkin kunya! a wayar ma sai anyi halin?" Chukkling yayi yana sosa kai! Daddy yaci gaba da cewa "zan turo ma number ta yanzu! Idan kaga waya zaku yi bayan ka sake dawowa sai kaje" da hanzari Mahmud yace "No Daddy gobe zan tafi Kano insha Allah! Idan na tafi banje ba za suga rashin kulawata! Daman ban kammala booking din ba, sai na chanja date zuwa four days" Cikin matsanancin farin ciki Daddy yace "Allah yayi maka albarka Mahmud! Allah yayi ma tukuici da mafificin alkhairinsa! Allah ya baka yaran da zasu yi ma biyayyar da kayi mun! Nagode......." sai muryar Daddy ta shiga rawa! Ran Mahmud yayi sanyi na jindadin addu'ar Daddy!

"Ohh Daddy c'mon! I'm not ready to cry kada muyi haka! Your baby is forever grateful to have such a darling father like you" Daddy tuni ya fashe da dariya jin yanda Mahmud ya kira kansa baby da yanda yake masa maganar! Shima dariyar yake yi sosai. Cikin farin ciki sukai sallama Mahmud ya sauke wayar a sanyaye yana jin matsananciyar kaunar Daddy na sake mamaye zuciyarsa! Ya tabbatar ba karamun lamari ke kewaye da hukuncin da Daddy ya zartar a kansa ba!

Yana sauke wayar yaji kwankwasa kofa! Shafa kansa yayi yace "ohhh what have I done to deserve this loving parent?" Da kansa ya mike yaje ya bude kofar! Mamin ce a tsaye ko mayafinta bata aje ba! Daman tasan da maganar, domin Daddyn ya gaya mata zai kira Mahmud yayi masa bayani! Tunda ta futa kuma hankalinta na kansa tana addu'ar Allah ya sanyaya masa zuciyarsa.

Cikin kurilla take kallonsa tana nazarin yanayinsa! Gano hakan da yayi ne ya sanya shi wani lallausan murmushi yace "Mami your son has a good news for you! Amma kafin nan yana jin yunwa" itama ya ga lokacin da sauke ajiyar zuciyar kafin tace "daman abincin zan kira ka muci! Ina dinning ina jiranka" a gurguje ya koma dakin ya kammala booking dinsa har da na zuwa Kano gobe sannan ya futo ya same ta a dinnig tana waya! Yana Isowa tayi sallama! Da alama da Daddy suke magana. Kujera yaja sannan ya shiga serving din Mami kafin ya zuba nashi!

Suna cin abincin ya tausasa murya tace "Mami your son has an additional wife! Surukai uku zakiyi lokaci daya"

Murmushi tayi mai kwantar da hankali tace "Daddy yayi mun bayani! Nayi murna sosai, na yaba da yarinyar da hankalinta kuma Mamanta ma mutuniya ta ce! Sai dai nayi fatan Allah ya sanya albarka da alkhairi" ya lura duka iyayen nasa ba don hankalinsu ya kwanta da Safna suka amince da ita ba sai don kawai su faranta masa! Don ko rabin wannan dokin basu yi ba lokacin da akayi maganar auren shi da Safna.

Sai karfe sha biyu na dare suka tashi daga hirar tasu irin ta uwa da 'danta, yana shirin mikewa Faisal ya kira wayar Mamin domin yayi ta kiran wayar Mahmud bai daga ba! Cewa tayi "ya baro ta a daki gashi nan muna parlour" ta mikawa Mahmud wayar! Ko gaisawa bai bari sanyi ba yace "friend muna asibiti da Ihsan tun dazu! Doctor yace ba zata iya haihuwa ba babyn yayi girma" cikin zumudi hade da tausayawa yace "I will be there now" bayan ya gaya mishi asibitin.

"Menene?" Mami ta tambaya rikice! Bayani yayi mata sannan ya shiga daki da sassarfa ya mayar da kayan da cire dazu ya futo. Itama Mamin ta yafa gyalenta suka futa gabadaya.

------------------------------------------------------------

Karfe daya arba'in ina zaune kan gadona ina kallon uban gifts din da Mubarak ya kawo mun! Mayuka, turaruka da kayan kwalliya masu azabar tsada da kuma kudi 200k! Ni nasan bana kin Mubarak ko kadan kuma bashi da makusa amma na gaza gane dalilin da yasa bana dokin auren shi kamar yanda naji akan Imamu.

Tunawa nayi da wayata da na kashe bayan na gaji da kiran da Imamun ya dinga yi mun da number kala kala! Dakyar ne idan bai samu tabin hankali ba. Ina kunnawa kira na shigowa! Ganin sunan Ya Mahmud gabana ya fadi nayi saurin dauka.

Cikin farin ciki yake cewa "The new Aunty in town" a sukwane nace "Ya Sofy ko Ihsan wace ta haiwu?" Dariya yayi yace "Ihsan din dai" cikin daga murya nace "Don Allah Ya Mahmud dagaske?" Yace "Ga babyn a hannuna very cute kaman mamanta" wani uban tsalle na daka ina ihu! Yace "Keee! Dare ne fa! Meye haka?" Ai ban saurare shi ba na yar da wayar na cika gidan da ihu da murna. First time naji genuine farin ciki tun bayan rasuwar Aisha!

Sai da na tashi kowa na gaya masa Ihsan ta haiwu kafin Faisal ya hada mana video call! Sai lokacin nasan Cs akai mata!

Gabadaya ban iya komawa bacci ba ina alla-alla asuba tayi na dau hanyar asibitin! Ana idar da sallah ko na dau key da zumbulelen hijab din sallar na futo nayi wa Dadda sallama zan tafi. Cewa tayi Ya Nuratu ta rakani yayi safiya na futa ni kadai. Na tsaya ta shirya muka dau hanya kamar zan tashi sama saboda zumudi. A reception muka samu Ya Mahmud da Faisal sun dawo daga sallah kenan, muka gaisa nayi wa Faisal barka sannan muka shiga dakin da Ihsan take. A lokacin bacci take yi sai Mummy da mai tayata aiki da kuma step mum din Faisal. Mami na daga gefe ta idar da sallah tana lazimi.

Gaban gadon babyn na soma zuwa na sunkuto ta na rungume! Fara ce sol komai da komai nata irin na Ihsan gata katuwa. An shirya ta tsab cikin kayattatun kayan baby na "Vercasse" sai baccinta take.

Su Mummy na ta tsokana ta suna dariya. Sai da na nutsu tukunna na gayar da su daya bayan daya sannan na baiwa Ya Nuratu babyn dakyar don ji nake kamar na kwace ta na tafi da ita.

Su Mami ne suka soma tafiya mu kam bamu bar asibitin ba sai wajen 9 Ya Nuratu ta jani dakyar muka tafi. Don ji nake kamar nayi ta zama ina kallon babyn. Ihsan har yanzu bacci take don tasha wahala sosai.
Muna dawowa Ya Nuratu ta soma shiri ita da Amal, Dada ce tace lallai ta shirya su tafi Kano tare da Ya Mahmud taga gida. A tsarin Ya Nuratu ba tai niyyar zuwa ba, domin basa jituwa ko kadan da Inna badi'atu, Kamar ba ita ta haife ta ba. Sai da Dada tayi mata nasiha sannan ta yarda ta soma shirin.
Nikam ba karamun farin ciki nayi ba da jin zabin da Daddy yayi wa Ya Mahmud na Amina, Allah yana kallo bana masa sha'awar Safna ko kadan! Bana mishi burin auren mace irinta kuma ina mamakin yanda akayi ya amince da auren nata, inaga hakan bai rasa nasaba da zamansa cikin turawa tsayin shekaru. Amma idan ba sabo da zama cikin turawa ba babu abinda zai kai shi tunanin auren mace mara kamun kai irin Safna. Don haka sai murna ta ta sake karuwa akan ta da.
A lokacin baya na sha addu'ar Allah ya kulla soyayya tsakanin Ya Mahmud da Aisha duk da ban taba furtawa wani ba,amma naso kwarai ace ya samu mace irin Aisha. Ashe akwai abinda Allah ya rufe. Da hakan ya faru sai ana gab da biki zata mutu ya sake fadawa halin da ya shiga a lokacin mutuwar Jawahir kilama a soma Canfa shi ace a dalilin sa matan ke mutuwa. Allah sarki Aisha! A kullum kwanan duniya sai nayi kewarta, babu wani abu da zai faru dani ban tuna Aisha ba. Saboda da ita na saba, ita kadai na saba gayawa damuwata da farin cikina, da ita nake shawara, da ita muke kashewa mu haka rami mu binne babu wanda ya sani. Wata shakuwa ce tsaukaninmu irin ta yan uwan da suka futo ciki daya.
Hakika nayi rashi! Nayi babban rashin da bazan maye gurbin shi ba. Tsakanina da Aisha sai addu'a wadda bana mantawa, duk lokacin da na nisa zanyi mata.+
Wanka nayi na shirya na yafa gyalena na futo! Tuni Baba Rabi ta hada abincin da Dada tace tayi na tafi da shi asibiti!
Amal na kalla wadda take ta faman kumburi tasha kwalliya cikin voile riga da skirt mai kyau da saitin gold dinta wuya da hannaye! Kamo hannunta nayi nace "Amal yaya dai? Ko kayan ne bakyaso kike fushi?" Cikin shashsheka tace "Ni banason naje gidan Inna! Nafi so na zauna anan! Kice wa Maama na zauna anan" a raina Allah wadai nayi da halin Inna. Yar cikinta da yar mitsitsiyar kwallin jikarta na gudun zuwa wajenta saboda mugun hali.
Tsugunawa nayi na kamo hannunta na soma lallashinta "No Amal ba haka ake ba! Ya zaki bar Maama tafi ita kadai wajen Inna? Kinaso Inna tayi fada meyasa bakije kin gaida ta ba?" Shiru tayi tana niyyar soma kuka na sake cewa "And you know what? Amaryar Ya Mahmud tana kano ko bakya so kije ki ganta?" Sai lokacin tace "da Uncle zamu je?" Na girgiza mata kai ina cewa "yes! da shi zaku tafi Amal! Are you happy now?" Tayi murmushi tana daga kai.
Dada ce tace "Allah ya kyauta halin Badi'a Allah ya dawo da ita kan hanyar gaskiya! Wannan bakin hali har ina? Ace naka yana gudunka kiri kiri saboda bakin halinka" Ni dai gum nayi da baki kaina a kasa domin ina kunyar idon Ya Nuratu. Ita kuwa kamar ta fashe da kuka don takaici, a dole za tai wannan tafiyar ba don tana so ba.
Ya Omar ne yayi sallama ya shigo! Cikin murmushi nace "mu futo ne Ya Omar?" Harara ta yayi yace "Wai don Allah gani kike kamar lokaci daya aka haifemu mukai kuruciya tare ne?" Dariya ya bani yanda yayi kicin kicin yana masifa. Dada tace "kaga fara zuwa mu kammala abinda na kira ka sai ku soma fadace fadacen naku idan ma casuwa zaku yi zan baku wuri" murmushi nayi nace "Dada yanzu menene laifina? Daga nace mu futo?mu da muke expecting baby anytime ba dole ana ganin shi a tambaya ba" da sauri ya nufo ni na tashi a guje nayi bayan Dada ina dariya.
Muna cikin haka Ya Mahmud yayi sallama cikin wata kamilalliyar shiga. Babbar riga ta blue din voile wanda ya amshe shi sosai. Ya daidaita wata tsadaddiyar hula akan gyararriyar sumar sa sai walkiya yake. Kamar yau ne daurin auren. Kamshin "La Nuit" ya karade falon.
Futowa nayi daga maboyata ina cewa "wow! Ya Mahmud you look extra-ordinarily handsome!soo Masha Allah" na karashe "Masha Allah" da wani tone na yabawa ina yiwa Ya Omar gwalo domin shima irin kayan ne a jikinsa bambamcin kawai shi nashi karamun dinki ne. Ya Omar da Ya Sadik duka farare ne sol dogaye masu matukar kyau, shikuwa Ya Mahmud yayi duhu duk da ba baki bane, Amma idan ana yi maka maganar kyau zalla mara gauraye toh Ya Mahmud abun misali ne! Zakai matukar mamaki idan aka ce ma bahaushe ne, baiyi kama da fulanin ba, kana ganinsa zaka dauka cikakken balarabe ne duk da farin shi bai yi yawa ba. Yanayin gashin sa da har yau yake a kanannade kamar na sabon jariri, da kuma kalar idanun shi wani irin fari kamar nono, bakin ma baki wuluk babu sirki, an diga wani abu mai maiko da zaka dauka hawaye ne ya taru, idanun marasa juriyar kallo ne, don da kansu suke lumshe kansu kamar masu jin bacci.
Bayan haka kuma wani sinadari da wata baiwa da kwarjini da ilhama Allah ya wadata shi da su wadanda suke futar da shi unique cikin daruruwan mutane. Duk kwalliyar da yayi dacewa take da shi! Duka kalar da yayi amfani da ita kyau take masa both English and traditinal wears.
Sirrin armashin gayun nashi kuma bakomai bane illa tsabar tsafta, wayewa, da sanin abinda ya dace da shi sannan komai nashi mai inganci ne, kuma unique. Wannan guntun handkerchief nashi designer ne da sunan shi balle kuma tufafinsa da takalman sawarshi. He is sure, a designer Guy. Ya amsa wannan sunan!
Bai tsaya anan ba, ya samu karin nagartattun halaye. Yana da far'a sosai musamman ga mutanen da ya saba da su! Yana sanyin rai da raguwar zuciya mai tausayi da jin kan na kasa da shi, yana da kyauta da son farantawa mutane. Sai dai kamar kowanne mutum tara yake bai cika Goma ba.
Cikakke Wanda yafi Goma cika sai Annabin Allah saw. Mahmud na da nashi cikas din irin na kowanne Dan Adam.

STORY CONTINUES BELOW

Mahmud idan har ta kai ga ya bar abu, toh ya barshi kenan har abada. Bazai taba dawowa gare shi ba. Sannan gano weakness dinsa bashi da wuya ko kadan, da wannan ake yawan cutar da shi. Baya iya boye son abinda yake so, kuma yana da saurin yarda da mutum. Don haka da wuya yayi mu'amula da mutane basu cuce shi ba. Sai dai kuma idan yayi fushi kamar kowanne mai hakuri babu sauki. Baya karbar uzuri ko ban baki.
Da wuya kaji ya kushe mutum ko ya yabi mutum, babu ruwanshi da duk abinda ba'a saka shi ciki ba. Kananan abubuwa ke saka shi hawaye, duk fushin da yake idan kayi sa'a ya saurare ka ka yi mishi magiya toh zai hakura ya sauko, sai dai idan kayi wani abu da zai taba mutuncin sa ko darajarsa, anan kam har gaban kuliya zaku iya zuwa. DR. Mahmud Ahmad Lamido kenan!
Jin compliment di na ya sanya shi murmusawa har hakoransa suka bayyana. Dada tai maza tasa hannu cikin aljihun da ake mata jikin  kowacce irin rigarta ta dauko sabbin yar sardauna ba tare da ta irga ba ta miko mun! "Tukuicin kirarin da kikai wa Mahmud" na isa gabanta nasa hannu biyu na karba ina dariya. Ya Omar kamar zai exploding yana harara ta.
Haka muka tarkata muka mukai wa Dada sallama muka futa.
Ya Omar dinne ke driving Ya Mahmud na gefensa, Mu kuma matan a baya. Airport muka kaisu, har sun so suyi latti don haka mu kai sallama cikin sauri, na mikawa Ya Mahmud yar gift bag me kyau nace ya kaiwa Amina. Murmushi yayi kawai ya karba ya wuce gaba. Sai da muka ga tashin jirginsu muka taho.

"Ya Omar yanzu ba zaka gayamun gender din babyn ba? Kafi so na siyo komai unisex na bayar?" Idon shi akan hanya yace "ki bari idan anyi haihuwar sai kije ki siyo" hararar gefen ido nayi masa nace  "sai anyi haihuwa zan tafi yawon neman kaya? Kaga fa A.laila zan saka ta siyo mun akwai friend dinta da zata zo Abuja zata taho mun da kayan"
Kallona yayi ya sake maida hankalinsa kan hanya yace "ita ba ta da kaya zata dauko miki naki" cikin kosawa nace "aunomun zatai na biya! Please mana Ya Omar" na fada making my best puppy face.
Cewa yayi "idan na gaya miki ya zama sirri! Deal?"  Nayi maza nace "deal" yace "twins all boys" wani ihu nayi ina daga zaune Wanda ya sanya shi gangarawa gefen titi yayi parking.
Nutsuwa nayi sosai don ba karamun aikinsa bane ya make mun baki.
Cikin cool voice yace "Zara you know what? Wannan maganar daga ni sai Sofy muka santa! Not even iyayen ta ko nawa. Kema ganin yanda kika damu da haihuwar da son babies dinki yasa nake gaya miki! Please bana so kowa yasani" Murmushi nayi nace "kar ka damu Ya Omar nayi alkawari bazan gayawa kowa ba. Not even A.laila da zatayi siyayyar. Zance mata Ya Anees zan aje ma dayan tunda itama in two months take expecting!" Ya girgiza kai yana murmushi.
Nace "congratulation ya Omar! I'm soo happy for you wallahi! Don Allah zaka bani daya?" Dariya yayi yace "duka zan baki Zara! You know you are my favourite sister right?" Da wani wide smile nace "really Ya Omar? Thank you" haka muka cigaba da hirar mu har muka isa asibiti. Kai ba zaka kace ni da Ya Omar din da muke fada bane dazu.
Irin alakar mu da shi kenan! A gaban mutane bama jituwa bama haduwa ba muyi fada ba, amma hakan bai hana kyakkyawar alaka ta yan uwan jini tsakaninmu ba. Mun shaku sosai kuma mun damu da juna.....Ya Sadik babban wa ne, bama wasa da shi, bai cika son magana da wasa ba don haka ba mu wani sakewa muyi hira idan ba akan wani abu mihimmanci ba. He is nice shima kuma  idan ina son wani abu nakan tambaye shi direct, kuma zai bani ko menene! Idan wani abu nake so Dada ta fahimta shi nake nema ya fahimtar mun da ita.
Duk yayan Daddy ba matsayin cousin suka dauke ni ba, alaka ce da shakuwa a tsakanin mu ta real brothers and sister.
Mun isa asibiti Ihsan har ta wartsake tayi wanka tayi kwalliyarta. Ga babyn ma ta sake wani kyau an sauya mata kaya.
Aje kwandon abincin nayi na sunkuto babyn ina kare mata kallo, sannan na rungume ta a jikina muna hira da Ihsan tana bani labarin yanda haihuwar ta kasance da C-section dinta. Bani na baro asibitin ba sai wajen biyar na yamma da ta hadani da Allah naje gidanta na debo mata kayan sawa duk da skirt ta taho asibitin kuma tafi jin dadin gown saboda stitches din cikinta.
Ina shiga mota Ya Mahmud ya kirani ta Skype! Duk kwalliyar da yayi dazu bata ishe sa ba wata ya sake da irin unique yadikan da yake amfani da su idan yana sha'awar kwalliyar burgewa.
"Ya Mahmud you wanna kill Kano girls with your beauty ko?" Na fada ina dariya! Shima dariyar yake yi sannan yace "guess where I am?" Kafin ma na bashi amsa sai ya juya camera daga front, nan da nan Amina ta bayyana a kujerar da ke saitin shi cikin kayatacciyar kwalliya mai ban sha'awa! Murmushi nayi nace "She is beautiful, Modest and calm!" Cikin murmushin shima yace "you really define her well" daga nan ya mika mata wayar kamilalliyar fuskarta ta bayyana. Fara ce sol ga dimples duka kumatunta! Muka gaisa cikin mutunci da far'a mai yawa sannan na dora da cewa "ki kula fa da shi dakyau naji ance yan matan kano sun iya snatching "
Dariya tayi sannan tace "wannan dai sharri ne! Babu ruwan mu" mun dade muna hira kafin muyi sallama na aje wayar.
Sai naji hankalina ya kwanta sosai da Amina da Ya Mahmud! Sun dace kwarai.....! Mun kusa shan biki!.....sai kuma na tuno cewa ai bikin nashi tare ne da nawa! Na tabe baki ina tuna abinda ya faru jiya, muna cikin waya da Mubarak matar shi ta shigo dakin. Masifa ta fara wai ba zata yarda da wannan rainin wayon ba, idan zaiyi waya dani ya samu wani wajen da zaiyi amma ba dai a gidanta ba. Ni dai na lallaba na kashe wayata bansan yanda suka kwashe ba. Murza key nayi na kunna motar na tafi Mississippi raina cike da tunanin yanda auren mu da Mubarak zai kasance da kuma masifaffiyar matarsa. Ina shiga layin gidan Faisal na hango motar Daddy a gabana,na duba sosai daga bayan seat din motar ma ina hango farar hularsa gefensa kuma wata mace da lullubi bangane ko wacece ba. Mamaki da tashin hankali suka kamani, domin banji Dada tace zai dawo ba. Karin mamakina ganin gidan da ya shiga, Koda ba komai zan sani game da shi ba, nasan abubuwa dayawa na shi kuma nasan ba shi da gida a Mississippi wanda yake zuwa. Sannan ban taba ganin shi da mace ba. Toh meye yake faruwa. Parking nayi a hankali na balle murfin motar na futo.
Tuni har sun shige gidan an mayar da gate din an kulle.
A nutse na dinga tafiya har na isa gidan, na kwankwasa kofar a hankali, sai ga security din ya bude kofar ya futo yana cewa "who are you? What do you want?" Daidaita nutsuwata nayi na bude jakata na ciro wayata nayi yan danne danne na nuna masa! Hotonmu ne da Daddy da Ya Mahmud a London. Sannan nace masa "I'm his daughter" nan da nan ya soma gaishe ni yana washe baki, sannan ya bani hanya na shiga yana ta bani hakuri. Hannu na daga masa kawai naci gaba da tafiya.
Duk takun da nayi kirjina kara gudun bugawarsa yake, tuni na soma danasanin biyo bayansu! Me zance musu? Me zan gani?" Haka dai na daure na isa kofar, a kulle take ta ciki amma ga key nan ta waje alamar yanzu akai amfani da shi aka bude aka shiga ba'a zare ba.
Nayi mintina biyar kafin nayi jarumtar murdawa na bude kofar. Wani tangamemen parlour ne kamar fadar wani hamshakimin sarki. Na soma takowa a sannu sai naji sautin magana na futowa daga wata kofa a hankali. Cikin sanda na isa bakin kofar na tsaya.
Wani mamaki ne ya kamani jin muryar da ke magana. Muryar Mamina ce tana shaking take cewa "yanzu kana ganin wannan hanyar za'a bi a warware komai ba tare da Mahmud ya sani ba? Ba fa yaro bane! A iya sanin da nayi wa Mahmud na tabbatar sai yayi binciken da zai gane komai ba tare da yayi wa dayan mu magana ba." Daddy ne yace "Zainab to ya zanyi? Abinda yasa nace muzo nan mu tattauna kenan! Yanzu ma barrister nake jira akwai wata takarda da ta bata yake kokarin yanda za'ai amfani da photocopy din kafin a ga original din ta wajena. Kaina ya kulle Zainab! Na rasa ta yanda zanyi na futo na kalli idanun Mahmud nace masa BA NINE NA HAIFE SHI BA!!
Tikisa!!!

Ji nayi kalmomin sun rufto mun kamar saukar aradu! Wani mugun jiri ya kwasheni kamar zan kife nayi saurin zama don kar na fadi. Iya abinda kunnena ya nado kenan kwakwalwata kuma shi kadai take juyawa tana sarrafawa tana kokarin daidai ta shi cikinta don yayi mata nauyi da yawa ta karba...."BA NINE NA HAIFE SHI BA??" Me kenan? Me hakan yake nufi? Na shiga uku! Me kunnena yake gaya mun? Wacce azal din ce ta fado mun na biyo su Daddy cikin gidan nan?
Dan! Dan!! Dan!!!

You all know what writers means by 'Dan! Dan!! Dan!!!' Right?🤣 You know that they will be good drama ahead ko?
Toh ku biyo ni!😥
Who is shocked???😣😣😫
Shebi I told you akwai wani katoton surprise ko? Toh gashi nan! 🤐
Allah yasa kar zuciyar Mahmud ta tarwatse idan yaji wannan magana. Toh wai ma da wanne idon Daddy zai masa wannan bayanin? Ku tayani rubutawa😫 I don't wanna break Ya Mahmud's heart. Matsalolin sun masa yawa.

See you guys😁A hankali na sulale na zauna a kasa ina maimaita "innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" cikin zuciyata domin maķogorona ya bushe, lebbana sunyi nauyin da ba zasu iya sarrafuwa ba.

Sannan daga wadannan kalmomin ban sake gane komai ba, ban kuma jin me suke cewa ba illa kuwwar da kalaman Daddy suke mun akaina.

A hankali nutsuwa tazo mun, na samu kwarin mikewa tsaye sannan na salallaba na futo daga falon ba tare da nayi wani motsi mai karfi ba.

Allah ya taimakeni banga maganannen security din dazu ba a wajen nayi maza na futa daga gate din na bar gidan.

Ko daya ban sake tunawa da zancen daukowa Ihsan kaya ba na shiga mota ta na bar layin ina tunanin inda zan dosa.

Da Aisha tana nan gidansu kawai zan wuce na sauke nauyin da zuciyata tayi mun, ita kadai zata fahimceni ta kwantar mun da hankali ta rarrasheni.

Bayan ita ko Ihsan banjin zan iya budewa wannan sirrin balle kuma wani daban. A dalilin haka sai na samu waje nayi parking na kwantar da seat din motar kawai ina tunanin wannan irin gingimemiyar magana mai daga hankali da mamaki da tsoro da fargaba da tunani da razani. Duk yanda Mami da Ya Mahmud suka kai ga shakuwa kowa a family yasan cewa ba itace mahaifiyarsa ba amma da wasa ko tunani babu wata alama da ta taba nuna cewa Mahmud ba dan Daddyy bane. Kai!! Wannan magana ta daki kaina ta fatattaki farin cikina ta sanya ni cikin matsananciyar damuwar da bansan iyakacin ta ba.

Ni dai ina zaune a wajen na dinga jin kiran sallar magrib, amma ban iya motsawa ba, kaina wani irin sarawa yake yi kamar zai rabe gida biyu. Ko motsi bana son yi ga wayata sai ruri take yi amma na kasa samun kuzari da jarumtar da zan daure na dauka.

Haka naci gaba da zama har karfe tara, wani matsanancin zazzabi yayi gaba dani jikina ya soma rawa kamar mazari. Sai lokacin hankalina ya tashi domin wallahi bazan iya driving naje gida ba.

Dakyar na dauko wayata daga jaka, missed calls ne na Ihsan da kuma Ya Nuratu da Mubarak. Ya Omar na kira, tayi ta ringing bai dauka ba, na kira Ya Sadik shima bai dauka ba, dole na kira Mami. Bugu biyu ta dauka tayi sallama.

A sanyaye nace "Mami kina ina?" Cewa tayi "muna nan asibiti da Safiyya menene?" Cikin karfin hali nace "babu komai Mami! Me suka ce?" Cewa tayi "tana can dai tana fama amma sunce babu matsala! Ina Dada?" A tunanin Mami ina gida! Sai nace "tana nan Mami ina daki ne, Allah ya raba lafiya" mukai sallama! Ita kanta na fuskanci tana cikin wani yanayi ne, ba fargabar haihuwa ce kawai take damunta ba, da ba anan tambayoyin ta zasu tsaya ba sai taji me nake yi? Meyasa muryata haka? Ya akai bance zan taho asibiti ba!

Ina cikin wannan tunanin kiran Mubarak ya sake shigowa nayi swiping screen din a hankali na kara a kunnena tare da yin sallama. A maimakon naji muryar Mubarak ya amsa sai naji wata zazzafar masifaffiyar murya tana karaji cikin dodon kunnena.+


"Ke babu sallama tsakanina da ke kina ji? Gargadi na kira nayi miki! Kyakkyawan gargadi ma kuwa kuma idan kunne yaji toh gangar jiki zai tsira!

Wallahi wallahi ki kiyayi shiga gonar mijina! Mijina nawa ne ni kadai bazan yi sharing din shi da kowacce yar iska ba kina ji? Wallahi duk wadda tayi gangancin tsomo kanta cikin rayuwar mijina sai tayi dana sanin zuwanta duniya gabadaya. Tun wuri ki janye kudurin auren Mubarak idan kuwa ba haka ba wallahi na lahira sai ya fiki jindadi sai na mayar da ke abar kwatance da misali l......


Ina zaune da wayar a kunnena ina sauraren duka kalamanta cikin tashin hankali da tsantsar damuwa. Sai da tayi iya masifar ta da barazanar ta ta gaji don kanta sannan ta ajiye.

Wani irin nauyi naji kaina ya sake yi, zuciyata na bugawa da sauri da sauri.

Wayar Ya Sadik ta sake shigowa, amma Sam ba zan iya magana ba domin kalamaina sun yanke! Sai na kashe wayar na bude WhatsApp na tura masa location din da nake na cillar da wayar ina dafe kirjina da ya soma wani irin zugi kamar zai fashe. Tun ina iya gane halin da nake ciki har idanuna suka soma lumshewa.

------------------------------------------------------------------------------------------------------------------------

KANO

A can kano kuwa cikin yammaci daya Mahmud da Amina suka fahimci juna suka kuma gamsu da hadin da iyayen nasu ke da kudurin yi a kansu. Kowanne ya gamsu da dayan dari nisa dari, musamman Mahmud da ya dinga tunanin ashe akwai irin wadannan matan masu tarbiyya da kamun kai har yanzu! Ya dinga tuhumar kansa akan yanda akai ya amince da Safna har yake shirin auren ta. Lallai gaskiyar bahaushe da yace duk Wanda ya bar gida gida ya bar shi. Zaman shi cikin turawa ko bai kowanne tasiri akan addininshi ba toh lallai ya gurbata wani bangare na tunanin shi da hankalin shi. Domin duk cikakken musulmi me tarbiyya musamman hausa fulani ba zai yi fatan ganin Safna ta zama uwar yayan shi ba. Ita kanta bata da tarbiyya da nutsuwa balle ta samu wadda zata baiwa yayan da zata haifa. Rayuwa kawai take yi kara zube kamar ta dabbobi babu kwaba babu gyara babu sanin ya kamata.

Idan kuwa ya tuno halin da take shirin sake jefa kanta sai yaji gabadaya ta sake fice masa a rai.

Washe gari ma da yamma ya sake komawa wajen Amina, har ya shiga cikin gidansu ya gayar da iyayenta mata da yake mata biyu ne a gidan da yan'uwanta. Sannan safiyar da zai taho ma sai da ya je sukai sallama ya aje musu himilin abun arziki kamar bai san darajar kudin ba sannan ya kamo hanyar Abuja ya baro Nuratu a gidansu da baudaddiyar Innarta sai next week zata taho.


STORY CONTINUES BELOW

Lokacin da Ya Sadik suka iso bansan yanda kaina yake ba. Bayan shi motar police ce da ya biya ya dauko don a tunanin sa ko kidnapping dina aka yi ko kuma wani mugun hannun na fada.

Ganin halin da nake ciki ya sanya shi azamar dauka ta zuwa asibiti.

A hanya yayi wa Mami waya tace ya taho dani asibitin da suke da Safiyya tunda acan na kwanta last ciwon da nayi.

Ban tashi bude idanuna ba sai karfe biyu da rabi na daren ranar. Akan fuskar Dr shareef idanuna ya sauka! Kamar kullum yana cikin fara kal din lab coat dinsa wadda ba za kayi tunanin kuda ya taba hawa kai ba. Idanunsa rufe cikin garai garai din medicated glasses yayi wani kwarjini na musamman! Sauri nayi na runtse idanuna na sake bude su, domin gani nake kamar gigin mafarki ne ya debe ni.

A hankali na sake bude idanun nawa wanda suke cike da nauyi, tabbas ba mafarki bane, shine dai a gabana yana nazarin halin da nake ciki. A hankali na bude lebbana zanyi magana sai kuma na fasa! Murmushi yayi garai garai din hakoranshi masu kama da kankara suka bayyana. Sannan ya gyara tsayuwarsa "hello madam are you back?" Ya fada cikin kwararren British ascent din shi. Girgiza kaina nayi sannan nace "where is my mum?" Juyawa yayi ya kalli yar matashiyar nurse din da ke bayan shi yace ta kira mun Mamin. Shikuma yaci gaba da aune aunen shi a kaina yana nazarin yanayin da nake ciki, Mami ta bude kofa ta shigo! Allah sarki! Wani mugun tsufa naga tayi mun a idanuna ba wannan stylish Mamin mai lamushe shekarunta ba. Stress ya mata yawa a kwanakin nan, ko da yake tunda ta taso Mami bata da rayuwar kanta, kullum cikin daukar nauyin damuwar makusantan ta take. Kullum cikin tunanin hanyoyin da zata bi ta warware matsalolin iyalanta ta samar musu farin ciki da kwanciyar hankali take. Bata zama, Daga jikinta har zuciyarta ba'a huce suke ba, ga stress din business dinta. Ga matsalar da take ciki da Maigidanta ga kuma shirin bikin yayanta lokaci daya, kowanne kuma nashi auren na bukatar kulawa da addu'a! Shi Mahmud mata biyu lokaci daya bayan gaurancin sama da shekaru goma! Ita kuma Zahra gidan kishiya! hatsabibiyar kishiya! Kamar yanda mutane da dama suke bata labarin zafin kishi da rashin kirkin Surayya. Idan kuwa ta tuna da tarzomar da ke cikin bayyana maganar da sukai shekara da shekaru suna rairaito a fefe, sai taji baccin ta ya yanke kwakwalwarta ta kulle, musamman sanin cewa Mahmud na da matsalar zuciya mai karfi. To wanne zata fuskanta a cikin wadannan matsaloli ta warware? Ta ina zata fara?

Toh har tsufa bai saukar mata ba sai yaushe?

A sanyaye ta iso gaban gadona tana kallona cike da so da tausayawa da kauna mai tarin yawa. Sai kawai naji wasu kwalla na ziraro min na tausayin wannan baiwar Allah! A rude ta risina gaban kaina tana cewa "menene Zara? Jikin ne? Me yake miki ciwo?" A sanyaye na goge kwallar idanuna nace "babu komai Mami I'm okay! Na samu sauki" ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "Zara daman ba kya gida? Meya sa ki kai mun karya?" Dr. Shareef ne yayi maza yace "No Mama this is not the right time please! Kwantar mata da hankali zaki yi yanzu ba tuhuma ba! The most important thing muga ta samu sauki!" Girgiza kai Mami tayi sannan tace "shikenan Doctor yanzu zata iya cin wani abu?" A hanzarce yace "why not? Idan zata iya!" Hankalinta ta dawo da shi kaina tace "me kike so kici?" Murmushi nayi nace "Mami kar ki damu I'm fine! Sallah zan fara yi sai nasha tea! Ina Ya Sofy? Har yanzu?" Cewa tayi "har yanzu tana labour room! Muna dai ta addu'a" na girgiza kai ina cewa "Allah ya bata lafiya" sannan Dr Shareef ya futa bayan jaddadawa Mami ta hakura da yimun wasu tambayoyi da tuhuma zuwa lokacin da zan samu sauki.

Ta amsa masa da toh! Bayan fitarsa Ya Omar da Ya Sadik suka shigo sukai mun sannu! Har da Maman Ya Sofy da yan'uwanta da suke asibitin. Daga nan nayi alwala nayi sallah da taimakon Mami nasha tea! Ina kwanciya Nurse ta shigo tayi mun allurar bacci....sannan ta hana ayi mun hayaniya sai na tashi don kaina.


Karfe hudu Safiyya ta haiwu bayan bakar wahalar da ta sha. Amma ganin kyawawan yan mazan twins din da ta suntubo babu zato ba tsammani sai murna ta kacame. Cikin kankanin lokaci aka gyara babies cikin baby suit na garari farare iri daya aka turo su tare da uwar zuwa dakin da zata huta.

Nan da aka dinga rige rigen daukan yaran. Ya Omar bakinsa kamar gonar auduga don farin ciki. Da asubahin farko Ya Sadik ya dauko Dada wadda ta matsa lallai tun daren sai tazo. Abun nema fa ya samu wajen dangi musamman mahaifiyar Safiyya da safiyyan kadai ta mallaka.

WASHE GARI

Farin cikin ganin tagwaye ya sanya ni wartsakewa daga zazzabi da ciwon kan da ke damuna. Dr Shareef ya sallameni da sharadin lallai bayan kwana biyu na dawo asibitin. Dakyar Dada ta sakani a gaba muka tafi gida nayi wanka, suma an sallame su gidan zasu tafi.

Bayan na koma gida kwanciya nayi a gado na kasa wankan ina tunanin maganar da tayi sanadin tsayawar numfashina na wasu dakiku. Ban taba magana mai gigitarwa irin wannan ba! Taya za'ai ace Ya Mahmud ba jinin Daddy bane? Toh dan waye? Sannan abun mamakin shine yanda akayi babu wanda yasan da maganar har shi kan shi Ya Mahmud din.

Sai da Dada ta tayar da ni da kanta sannan na shiga toilet nayo wanka na futo nayi sallar azahar. Simple A line gown din voile na saka na fesa turare sannan na futo parlour na taba abincin da Baba Rabi ta girka don ni. Duk abubuwan da nake yi, zuciyata na makale da tunanin wannan babban al'amari mai girma. Wani zuzzurfan tunani kaina ya dauka mai cike da tambayoyi kala kala.


Ji nayi an sauke mun hannu daga tagumin da nayi. Da sauri na farga na dawo daga tunanina ina share hawayen da suke biyo kuncina wanda bansan lokacin da suka zubo ba.

Daga idanun da zanyi naci karo da fuskar Ya Mahmud! Innallilahi!! Wani mugun tausayin sa ne ya kamani.

A nutse ya zauna gefena yana kallona sannan yace a sanyaye "Zahra? What's wrong with you? Menene? I have a good news for you share hawayen ki kiji"

Wani kuka naji ya subuce mun mai bala'in karfi na zallar tausayin Ya Mahmud, halin da yake ciki da kuma boyayyen bakin sirrin da bai sani ba Wanda yafi komai muhimmanci a rayuwarsa. Na tabbatar da zai ji ko da burbushi na abinda kunnena suka jiyo mun jiya, tabbas da anyi gadon asibiti da shi.

Unedited
Tsayawa yayi sororo yana kallona ina zabga kuka kamar wadda aka aikowa da sakon mutuwa. Kuka bil haqqi irin wadda yake tahowa daga karkashin zuciya, irin wanda ba'a iya tsayarwa idan ba shi ya tsaya don kansa ba.
Sai ya shiga rudani! Mikewa yayi ya shiga dakin Dada ya yambayeta abinda akai mun, nan take bashi labarin abinda ya faru dani jiya da kuma gargadin likita akan a hakura da yimun fada ko tuhuma ta akan hakan sai naji sauki.
Cikin tausayawa Mahmud yake cewa "Dada ina tsoron kada depression ya kama yarinyar nan! Akwai strange abubuwa da suke bullowa daga gare ta masu yawa, tun bayan rasuwar Aisha bata koma normal ba" A nutse Dada tace "menene kuma difireshan? Kai dadi na da kai baka iya dogon zance ba sai ka saka yaren nasara" Murmushi yayi yace "ina nufin ciwon damuwa Dada! Shikuwa idan ya kama mutum da akwai matsala, akwai bakar wahala kafin a rabu da shi! Kuma naga alamun ciwon da dama a tattare da ita.
Na farko dai abubuwan da take matukar so ta rage son su ko nace ta daina son su. Kamar kwalliya mai yawa, saka turare, son girke girke. Wadannan duk abubuwan da take so ne amma yanzu sam ba zaki ganta tana abu daya daga cikinsu ba. Na biyu son mutane da Tsokane tsonanen ta ya ragu sosai, haka kawai zaki ga tayi shiru tana tunani, wani lokacin ma tana hawaye bata sani ba, ko da yaushe tafi son kwanciya ita kadai a daki ko kuma kuka. Ta rame sosai! Duk lokacin da zaki ganta murmushin karfin hali take yi bai kai zuciyarta ba........
Haka yaci gaba da yi wa Dada bayani tana girgiza kai cikin gamsuwa domin ta tabbatar da abubuwan da yake fada da idanunta.
"Toh yanzu asibiti za'a kaita? Daman lahadi ta sama zamu tafi Jedda ganin likitan kafata inaga kawai itama idan taje ta ga likitan"
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "Dada zai fi kyau taga therapist! Akwai mahaifiyar abokin aikina Dr.Ahmad tshohuwar therapist ce kuma ko bayan tayi retire akan kai mata cases irin wannan har gida. Mun saba sosai kuma zan mata bayanin da zata fahimta yanda ya kamata. Bana so a soma bata pills da abubuwa a shekarunta.
Dada tace "toh ai kaine ka san komai duk yanda kaga yafi haka za'ayi! Allah ya shige mana gaba!"+
Bayan na gama kuka na na tashi na shiga toilet na wanke fuskata nasa kwalli domin bana son Ya Mahmud ya matsa mun akan lallai sai na gaya mishi me yake damuna. A parlour na futo na same shi yana cin abincin da na rage, zama nayi ina cewa "Ya Mahmud ragowar kake ci? Ga cooler din abincin a dinning" girgiza kai yayi yace "na kin ne ya bani sha'awa a koshe nake" nayi murmushi na zauna ina bashi labarin twins din Ya Omar, ga mamakina bai sake mun maganar kuka na dazu ba don haka na sake sosai muna hira sai da akai kiran sallar la'asar ya futa masallaci.

Tare muka tafi gidan Ya Omar ganin babies! Lokacin da ya dauko su ya rungume wasu hawaye ya dinga yi kamar zai hadiye yaran. Scene din was soo emotional! In dai ka zauna da shi zaka gane yana son yara sosai musamman babies sabbin haihuwa.
Sai da ya gama jin duminsu sannan yayi musu addu'o'i ya kwantar da su akan gadajen su. Wani makeken daki aka mayar nursery. Komai na dakin blue and white ne yayi matukar kyau. Sai sassanyan kamshin turaruka marasa karfi ke tashi da wani dumi na musamman.
Bamu baro gidan ba sai bayan magrib sannan muka tafi har Mami zuwa gidanta. Bayan na shiga ciki ne yake gaya mata yanda suka yi da Dada! Itama Mamin tayi na'am da shawararsa domin ita kanta matsalar rashin walwalata yana damunta.

Kwanaki biyu bayan lokacin aka kawo kudin aurena da Mubarak! Babu Wanda na gaya wa matar shi tayi mun waya balle barazanar da ta zayyana mun har shi kansa Mubarak din! Washegari kuma aka kai na Ya Mahmud gidansu Amina akai fixing date rana daya. Wato watanni uku dai dai. A ranar Ya Mahmud ya wuce London, da dimbin tunanin yanda zai bullowa Safna da kuma yanda zai tunkari shirye shiryen auren sa.
Ranar a gidan Mami na kwana, tun jiya da Ya Mahmud yaje yi wa Dada sallama na biyo shi don na samu raka shi airport da asuba. Mami gabadaya jikinta yayi sanyi, kamar tace ya hakura da tafiyar yayi ta zama tare da ita. Da daddare ina dakin Mami ina duba kayan da nayi order ta hannun A.laila wanda suka zo da yamma. Ware na Ya Sofy nake a akwati na ihsan na barsu cikin wannan akwatin da aka kawo kayan a ciki, kowacce bayan kayan babies na saka mata turmin super guda biyu da laces guda biyu. Babyn Ihsan na hada mata da bangles masu kyau na gold guda uku. Sai da na kammala shirya komai na rufe akwatinan sannan na shiga gyaran dakin don Mami ta hargitsa shi sosai wajen nemo mun laces din da na saka wa su Ihsan a kayan su. Sai da na hada komai cikin wardrobe na gyara sannan na kula da wata drower da ke cikin wardrobe din. Kullum a kulle take  amma yau ga mamakina sai ga mukullin a jiki, ta bude ta manta bata zare mukullin ba.
Zama nayi sosai na murda mukullin na janyo ta na bude. Hotuna ne da littattafai da takardu a shirye reras.
Cikin nutsuwa na soma ciro hotunan ina kallo, dadaddun hotuna ne tun Mami na yarinya na da na kuruciya da kuma na aurenta. Cikin wani envelope na ciro wasu hotunan guda shida, daya Mami ce da ABBA mahaifina kenan, ranar daurin auren su! Na dade ina kallon hoton cikin sanyin jiki da tausayi , kyakykyawan karshe ne ABBA don yafi Daddy kyau sosai! Ko kadan banyi kama da shi ba kamar yanda ban dauko Mamin ba, sai abubuwan da ba'a rasa ba wadanda dangantakar jini ke gadar da su. Kana ganin shi kaga bafulatani usul. Mami an cakare cikin wata atamfa Holland ire iren wadanda ake dawowa da yayinsu yanzu. Duk da hotunan black and white ne bai hanani ganin kyawunsu da dacewar su ba.
Hoto na gaba Mami ce zaune a bakin gado da jariri a hannunta an nade shi cikin shawl.
Daya hoton kuwa Mami  ce da ABBA da Daddy da wata mata wadda babu tantama Mummy ce mahaifiyar su Ya Sadik. Sauri nayi na wuce hoton don sai da gabana ya fadi a sakamakon mugun tsoron da nake wa wannan matar muguwa!
Zan ciro wani hoton kenan wata yar envelope karama ta fado, na tsaya na aje hotunan na dauka na bude. Rubutu ne aka yi da bakin biro wanda ya soma dan cakudewa saboda ajiya. Sai wani karamun hoto na wani dan saurayin da ba zai gaza shekaru sha bakwai zuwa sha takwas ba da baby katotuwa a hannun shi wadda za ta kai kamar shekara daya. Da na duba sosai sai nagane cewa nice, sosai nice ina yarinya.
Takardar na bude na soma karantawa cikin tsoron kar Mami ta shigo ta riskeni ina mata bincike! Nasan tabbas ranta zai baci don bata so ta aje abu ka taba ba ta saka ba balle wannan wannan asirtacciyar drower da ke kullum a kulle. Haka naci gaba da karatun dakyar, Da nazo layi biyun karshen rubutun ne na zaro idanu a sukwane gabana yayi mugun faduwa yayinda wani abu ya soma yawo a jikina kamar kiyashi. "Innalillahi  wa Inna ilaihi raji'un"  na ke furtawa a fili cikin tashin hankali. Babu shiri na hada komai na tarkata su na mayar cikin drower hannuna na bala'in rawa, yayinda kirjina ke bugawa a lambar karshe. Ina ji ina ma abinda na karanta shima zai koma ma'adaninsa ya bar cikin zuciyata.
Sai da na tabbatar na maida komai kamar yanda na same shi sannan na mayar da drower na kulle kamar yanda  na ganta na rufe wardrobe din ina sauke nunfashi. A guje na mike na shiga toilet na sakarwa kaina shower ba tare da na cire kayan jikina ba don tsananin kaduwar da nayi da abinda na karanta wanda Mami ta rubuta da hannunta.
Na dade cikin ruwan sanyin kafin nayi wanka na dauro towel. Har na futo nayi sallah na shirya cikin kayan bacci tunani bai bar kaina ba.
STORY CONTINUES BELOW

Haka na kwana ina sake saken wannan magana mai sa tunani da mintsinin zuciya. Da safe dole na dora mask akan fuskata na farin ciki da nishadi don kada Mami ta fuskanci aika aikar da nayi wa sirrinta musamman yanda naga tasha jinin jikinta lokacin da ta bude wardrobe din taga mukullin drower a jiki. Muna karyawa take ce mun "ina fatan kinsan jiya Dr. Shareef yace ki koma ko?" Hadiye chips din bakina nayi nace "Mami na manta ma gabadaya" cewa tayi "ni ban manta ba! Na kira asibitin ance yayi tafiya sai na karbi number shi na kira shi! Yana Kaduna yau zai dawo don haka gobe ba sai na tuna miki ba da safe zamu je" murmushi kawai nayi nace "toh Mami Allah ya kaimu" ba tare da na kalle ta ba, don abinda na karanta ya sani having wani irin emotional feeling na musamman akan Mami! She has gone through alot! She deserves happiness mara iyaka, ganin kuma bani da ikon cika mata wannan babban buri nata yakan sa naji jikina yayi mugun sanyi komai ya futa a kaina. Sai dai idan na tuna menene burin nata sai naji gabana ya shiga faduwa! It is not something easy! Ko da yake kana take ne Allah na nashi, musamman idan ka kasance bawa mai barwa ubangiji zabin dukkan lamuran rayuwarka, toh harde hannu kake ka zuba idanu ka jiraci nufin Shi akan ka, ka kuma karba da hannu bibiyu idan zabin yazo ko da kuwa babu soyayyar abun ya ranka.

Sai da nayi sallar azahar sannan nayi wanka na shirya cikin sabuwar embellished super mint green mai ratsin pushia pink da gold. Babu kwalliya a dinkin sai dai style din zai tuna maka da irin yan kananun blouses din zamanin 80's din nan da iyayenmu sukai yayi. Saitin gold marasa nauyi nayi amfani da su ba tare da na saka makeup ko daya ba. Na kawo wadataccen gyale pushia pink mai cike da shiryayyun duwatsu gold na yafa. Daga jakata har takalmi sabbi ne fil na ciro su cikin kayana da suke adane a gidan Mami duk yan kamfanin chloe!
Na kawo turarukan Mami na feshe kwalliyar da su. Ba wai a raina nake son yin kwalliyar ba, ba kuma jindadi ko farin ciki ya sanyani tsantsara kwalliyar da nayi watanni banyi ba, so nake na sauke wa Mami nauyin wani bangare na damuwarta a kaina. Kamar yanda Ya Mahmud yayi mun bayani cewa walwalarmu ni da shi na da matukar tasiri wajen farin cikinta da nutsuwar ta da kwanciyar hankalinta.
Aikuwa lokacin da na futo wani irin murmushi ne ya bayyana a fuskarta mai matukar ban sha'awa. Kana ganin shi kasan daga karkashin zuciyarta yake! Da na karaso gefenta cewa tayi "kinyi kyau sosai Zahra! Allah yasa wannan kwalliyar ta dore! Bana son ganinki cikin bakaken abayun nan da dogayen riguna! raina baya mun dadi" Wani dan hawaye ya taru a idona, ashe ba Dada kadai ta tsani ganina da wadannan loose kaftans da abayun ba, don dai ita tana fada ne. Na tabbatar itama Mamin rashin son takuramun ya sanya bata cika magana akan sabbin dabi'un da na tsiro da su bane.
A nutse na zauna a gefenta nace "Mami  na daina sakawa tunda bakya so!" Wani murmushin ta sake yi sannan ta dafa kafadata ta kwanto dani gefen jikinta. Nikuma na gyara kwanciyar tawa ina shakar sassanyar iskar kaunar da take kadawa tsakanin da da mahaifi wadda Allah ya diga a tsakaninsu. Mun dade a haka babu Wanda yace komai, a hankali na zame kaina na gyara zamana sannan na gaya mata cewa zan tafi na kai kayan barkar tawa. Cewa tayi "amma kinsan cewa ke da driving ba yanzu ba ko? Driver ne zai kaiki" da toh kawai na bita don bana fatan jayayya ko musu ya shiga tsakaninmu a irin abinda nake ji game da ita a yanzu.

                     LONDON
------------------------------------------------------------
Tunda ya sauka yake zirga zirga tsakanin gidan Dr.Ahmad da gidan abokiyar aikin Safna Sarah akan yanda zai samu addreshin Joyful. Ko kadan bai nemi kwanciya ya huta gajiyar zaman jirgin da yayi ba duk da a huce yayi shi. Sai da ya tabbatar da ya samu duk wata sassaukar hanya da zata sada shi da Safna sannan ya dawo gida yayi wanka ya shirya cikin bakaken men's wear na " HUGO BOSS" ya kawo farar hoodie samfurin "HILFIGER" ya dora. Ya janyo hular rigar ya rufe kansa ruf kai ba zaka taba cewa shi bane don bai cika irin wannan shigar ba.
Bai saka "La Nuit" ba don baya bukatar a gane shi a inda zai shiga sai ya kawo daya daga cikin turarukan Ralph Lauren ya fesa ya hada yan tarkacen da zai bukata ya saka a karamar trolley sannan ya ratayo jakar laptop dinsa ya futo.

Flight ya sake bi zuwa Glasgow daga Liverpool don bai jin zai iya zaman train da wannan tunanin a zuciyarsa. Ko yanzu ji yake kamar ya zama tsunsu ya ganshi a Glasgow din Scotland ya kutsa royal crescent ya nemo gidan da Joyful ke zama yaga wainar da suke soyawa da Safna.Bayan ya iso taxi ya dauka zuwa Hilton bath city.
Sai da yayi wanka yayi sallah sannan ya nemi abinda zai saka a cikinsa.
Yana kammalawa ya haye gadon dakin ya nutse cikin katifa ya soma ware gajiyar shi.
Assalam! I'm sorry for the late update please! I am very busy.

Kwanakin Mahmud uku kenan cikin garin glascow amma har yau Allah bai sa yayi katari da haduwa da daya daga cikinsu ba. Idan yaje gidan nasu floor din su kullum a kulle yake, kuma babu alamar futa suke suna dawowa wajen yafi kama da ya kwana biyu a kulle ba'a shige shi ba. Hakan ba karamun sake dagula masa lissafi yayi ba har ya shiga tunanin kuma anya lafiyar Safna kuwa? Wayoyinta duka a kulle suke kuma har yau bata waiwaye shi ba, ba ta cika mu'amala da social network ba don haka baiyi mamaki ba da ya duba yaga dadewar da tayi bata hau ba. Sannan yayi mugun fushi da Dr.Garba Galadanci akan gazawa da yayi wajen baiwa Safna tarbiyya mai kyau kamar sauran nashi yayan da yayi wa aure tuni hankalinsu kwance. Bai san cewa hatsabibancin Safna ya girmi kakannin ta bama balle wani Galadanci.
Kwana yayi yana addu'a akan Allah ya kawo masa mafita cikin wannan cakwakiya da yake ciki mai hadarin gaske.
Maganar da Daddy yayi masa tattara ta yayi ya samu wani lungu acan cikin wani loko na zuciyarsa ya adana shi. Fatansa ya kammala da maganar Safna yasan me suke ciki sannan ya fuskanci waccan maganar mai tarin sarkakiya da kulle kulle.
Allah maji roko, a safiyar wannan rana Allah ya hada shi da su Safna. Dawowarsa kenan daga morning walk din shi yazo gidan nasu ya duba ko zai katari! Da ya gaji da tsayuwa gaban kofar shiga gidan Joyful sai ya nemi waje nesa ya zauna yana tunanin kawai gobe zai juya liverpool yasan menene mataki na gaba da zai dauka. Wata farar mota ce tazo tayi parking a gaban gidan, sai ya tsinci kansa da kurawa motar idanu, murfin gefen hagu ne ya bude bayan sakwanni biyu Safna ta futo cikin wata yoluluwar rigar turawa pitch wadda bata rufe mata komai a jikinta ba. Sai wani ubansun hill da ke kafarta wanda igiyoyin sa suka sarkafe gabadaya kaurin ta. Ta saki uban gashi baya wanda ya sha rini kalar brown! Yana cikin wannan mamakin Joyful ta futo da shigar da tafi ta Safna muni suna tafiya suna dariya suka shiga gidan. Shi dai Mahmud kasa katabus yayi, ko hannunsa bai iya motsawa ba saboda madaukakin mamaki da sanyin jikin da ya kama shi. Yana wajen mai motar yaja matarsa bayan sun daga masa hannu.+

------------------------------------------------------------

Lokacin da na isa gidansu Ihsan gidan shake yake da mutane duk da babu taron suna sai bayan ta warware za'ayi.
Acan dakin Mummy na same ta tana sauya kayan da ta saka da safe zuwa wani leshi mai azabar kyau. Ta kara fari akan wanda take da shi. Hannu na saka da dau babyn wadda taci sunan mahaifiyar Faisal Rukayya, za'a dinga kiranta Amani. Wayata ta soma ruri na lalubo jakata na dauko ta! Number Mubarak ce don haka nayi swiping na kara a kunnena tare da cewa "hello"
Da wata mummunar ashariyar da ban taba jin irinta ba Surayya ta soma! Sannan ta dora da cewa "Na fahimci har yanzu baki san wacece Surayya Bala ba! Kasada da ganganci na neman jefa rayuwarki cikin masifar da bata da karshe......
Cikin rawar hannu na ciro wayar daga kunnena na saka a speaker. Jin kalaman Surayya ya sanya Ihsan barin daurin dankwalinta ta dawo kusa dani ta zauna tare da daukar Amani ta mayar da ita karshen gadon ta kwantar ta dawo ta zauna itama jikinta yana bari.
"Zaki gane baki da wayo kuma taurin kai bai miki amfani ba a lokacin da kika shigo gidana! Wallahi Zara gara a yanke miki daurin rai da rai a kaiki prison a kulle akan rayuwar da kike shirin jefa kanki. Ba barazana nake miki ba! Inaso ki gane cewa nayi miki adalci ne a lokacin da kika shigo kika ci karo da abubuwan da zasu faru da ke. Kinga sai dai kiyi kuka da kanki ba dani ba tunda nayi miki gargadi baki ji ba! Bar ganin Mubarak na rawar kafa akanki! Hmmm! Zaki sha mamakin yanda reshe zai juye da mujiya da zarar kin tako kafarki gidansa! Wanda baiji bari ba"..........tai wata irin dariya mai razanarwa kafin tace "na barki lafiya kafin ta gagare ki"
Kit!! Ta kashe wayar, tuni hawaye ya jika mun fuska kamar an balle famfo! Jikina sai mugun rawa yake yi. Yayin da kaina yake sarawa kamar ana datsa shi.
A hankali Ihsan tace "yaushe matar nan ta soma kiran ki?" Cikin shashshekar kuka nace "wannan karo na biyu kenan!" Sannan na zayyane mata wancan kiran da tayi mun a mota wanda ya kaini ga kwanciya asibiti. Shiru tayi tana tunani kafin tace "gaskiya Zara na tsorata na wannan matar matuka! Daga yanayin muryarta da yanda take sarrafa kalaman ta zata iya kowanne irin mugun aiki! Allah yana gani hankalina bai kwanta da ita ba sam! Kuma abinda ya bani mamaki kamar sunan Mubarak nagani a screen din ko idona ne?" Girgiza kai nayi nace "number shi ce! Da wayar shi take kira na! Wancan ma da wayar shi ne" cikin fushi Ihsan tace "kan uban can! Wato ya sani ma kenan? Ko kuwa ba ya wajen take bugowa?" A sanyaye nace "ni ina zan sani Ihsan! Wallahi ni bansan inda zan sa kaina ba! Bana son auren nan gabadaya Ihsan! Na tsani Mubarak din shi kansa, ina tsoron sharrin matarsa ina tsoron halin da zan fada Ihsan idan na aure shi!
Wannan wacce irin rayuwa ce? Haka na hadu da Imamu na saba da shi nayi nisa a son shi a karshe mummunar akidarsa ta bayyana. Ban gama warkewa daga ciwon da ya ji mun ba maganar Mubarak ta taso, ba don ina son sa 100% na amsa ba, kawai don naga Mami ta matsu taga nayi auren ne, kuma nima kewar Aisha na sakani naji inaso na bar garin nan na sauya wajen zama ko zan samu sukuni. Toh kawai sai kuma wannan matsalar Ihsan? Ni wacce irin mara sa'a ce?"
Na fashe da wani kukan mai bayyyanar da tsantsar bakin ciki da damuwar da nake ciki.
Sai da itama ta share nata hawayen sannan ta soma lallashina tana bani hakuri tare da kwantar mun da hankali. Dakyar na tsagaita da kukan ina sauke ajiyar zuciya a hankali.
"Yanzu abinda za'ayi ki tambayi Mubarak kiji da saninsa take bugo miki waya da wayarsa ko kuwa? Sannan kiyi masa bayanin komai. Ki kara da cewa idan har yasan ba zai iya rike mata biyu ba ya gaya miki! Kiyi masa barazana mai kyau akan ba zaki dauki wulakanci daga matarsa ba. Sai muga me zaiyi akai! Sannan kinga ba gida daya zaku zauna da ita ba, bama unguwa daya ba, idan kika so babu abinda zai hadaku in ba lalura ba. Don haka ki cire tunanin da kika fara na tsanar Mubarak! ba shine mai matsala ba auren wannan zamanin ne! Duk auren da kika gani yana da irin tashi matsalar da challenge din sai dai kawai na wani yafi na wani zafi! Kuma kowa da akwai ta fannin da ake jarabtar shi. Ki kalli abubuwan da Hajiyar Faisal take mun? Ko sunan ta da ya saka fa ba'a son ranta bane, cewa tayi bata so idan dagaske yana son saka sunanta ya bari sai ya auro wadda ta dace da shi. Har yau fa bata zo ganin babyn nan ba, idan nayi mishi complain yace nayi hakuri zata sakko ne! Zara kinsan dai it is not easy ko? Jurewa da biyayyar wanda baya kaunarka! Wata rana har ji nake ina dana dana sanin auren Faisal! Amma kullum abinda Mummy take ce mun shine ba Hajiyar Faisal ce mai matsala ba irin sigar matsalar auren nawa kenan kawai, saboda kowanne aure dole yana da tashi matsalar idan ma ban auri Faisal ba zan iya zuwa na auri wanda babanshi baya sona ko Dan shaye shaye ko mara tarbiyya ko matsalar kishiya ko ta rashin haihuwa! Babu ta inda matsalar bata shigowa kuma ba zai taba yiwuwa ka guje mata ba. Sai dai kayi addu'a da hakuri Allah ya baka mai sauki ya kuma baka wuyan dauka. Don haka kiyi hakuri kici gaba da addu'a kawai! Kada ki bari Mami ta sani idan ba abun ne yayi zurfi ba don hankalinta ne zai tashi fiye da naki, kina ga duk yanda ta rame tayi sanyi kuma hakan bai rasa nasaba da halin da kika fada a baya da wanda kike ciki yanzu. Ki karfafa zuciyarki! You are strong Zara! Don't let this brake you don Allah" da tarin maganganun Ihsan masu kwantar da hankali na shiga toilet na wanko fuskata na gyara ta sannan muka shiga cikin mutane ana hidimar suna.
Sai magriba na baro gidan Ihsan na wuce gidansu Ya Sofiy. Twins sunyi girma sosai suna ta shan madarar su. Kowanne kamar shi kadai aka haifa gwanin sha'awa! Anan na tarar da Ya Anis tayi shiru tana kallon mutane! Daman ita ba mai yawan magana bace musamman ma da ba hausar ce ta ishe ta ba. Gefen ta na dawo muna yar hira nan take gaya mun ita fa garin su take son zuwa haihuwa! Cikin rashin fahimta nace "meye dalili?" Ta gyara zama tace "kinsan Abie na shirye shiryen komawa Hurgada saboda jikin Mamanshi yayi zafi kuma su biyu kawai yayanta! Yayar Abie is paralysed tsayin shekaru ashirin kenan itama sai dai a kula da ita don haka hankalinsa yafi karkata ta tattara ya koma gida gabadaya! Nima rabona da Hurgada wajen 3years kenan inaso naje amma sam Sadik yaki amincewa" tausayi ta bani don zama a kasa babu iyaye ba danginka yana da wahala! Amma nasan tunda Ya Sadik yace mata a'a ba zai yarda ba. Magana daya yake yi! Ba'a juya shi don haka nayi ta bata hakuri nima ina lallabarta kamar nima ba yanzu Ihsan ta gama yimun hakan ba.
Nace "kinga ko bai bari kinje can haihuwa ba idan kika haiwu kikai arba'in dole zakije ganin gida nima kinga sai na biki naga garin ku"
wani murmushi tayi tsantsar kyanta ya bayyana, a raina na dinga tasbihi ga ubangijin da ya kagi wannan sura. Kyau kala kala ne! Amma kyawun Ya Anis irin wanda zaka yi misali da shi ne! Ga hutu da kwanciyar hankali da suka sauka a jikinta fatar ta kamar mudubi don kyalli da haske! Wani ruwan sarkar agogo ne gold a damtsen hannunta na hagu, yanda kalar agogo ta dace da fatar ta kawai nake kallo ina kara girmama girman Ubangiji. Da agogon da fatar hannun na ta kowanne walwali yake shi kadai. Da na waiwayo kuma na kalli Inno mai yin aikin twins na kalli yanda fatarta take shinning din wani irin baki ga faffadan hancinta da ya bararraje a katuwar fuskarta sai naji bakina yana cewa "subhallahi wa hamdihi subhanallahil azeem"
Sai da ta tabani na ankare da abinda nakeyi na mayar mata da murmushin ta sannan taci gaba da mun bayani cikin harshen English wanda tafi kwarewa da magana da shi bayan larabci.
"Zanyi murna sosai idan hakan ya faru, duk da nasan ba zuwan zakiyi ba saboda lokacin an kusa koma anyi auren ki" dariya nayi nace "I promise you idan har ba auren akayi ba zan raka ki" rungumeni tayi tana cewa tagode kuma na fara shiri tun yanzu!
A nutse nace "wai Ya Anis duka danginku suna Egypt ku kadai ne a kasar nan?" Cewa tayi "gaskiya kusan 80% suna can! Amma akwai close relatives dinmu a America da South Africa da wasu ma a Dubai! Amma sun fi yawa a America!
Cewa nayi "toh su waye a Canada su Mum dinki suka tafi suka dade wajen su?" Murmushi tayi tace "Auntyna ce sunanta Azeeza! Ita wannan ko abubuwa ne masu yawa marasa kyau suka yi ta faruwa da ita na ban mamaki a rayuwa har ya zama tayi losing mind dinta. She has been under psychotherapy bayan ta dawo daga coma da tayi 15years a ciki!"
Cikin zaro ido nace 15years cikin coma? How?" Tace "hadarin jirgin sama suka yi and she survived it" abun ya ban mamaki kwarai! Haka dai muka ci gaba da hirarmu ta yan'uwanta da al'adarsu da garinsu har Ya Sadik yazo! Tare muka tafi suka saukeni a gidan Mami suka wuce.

-----------------------------------------------------------
Mahmud yana zaune akan dan dakalin wani gida jikinsa a matukar sanyaye yayinda kansa ya dau zafi sosai. Duk da yana tsammanin faruwar wani abu amma bai tunanin muninsa zai kai haka ba! A yanayin da yake ba zai iya tunkarar su ba, sai ya tashi dakyar ya rarrafa zuwa masaukinsa ya kudundune cikin bargo zuciyarsa tana nukurkusar ciwo! Da kiran sunan Allah ya samu ya mike ya dauko maganin sa yasha sannan ya koma ya kwanta yana dafe kirjin sa. Bashi ya samu nutsuwa ba sai bayan sallar azahar sannan yayi wanka yayi sallah yayi order abinci ya dan tsakura ya kuma shan magani ya sake kwanciya.
Karfe biyar na yamma ya kammala shirinsa cikin yanayin kayan da ya saka da zai taho, ya rufe kanshi tsaf da hular rigar ya futo fuskarsa babu walwala ko daya.
Yana futowa aka soma yayyafi amma bai juya dauko umbrella ba duk da yana bukatar ta don jikinsa baya kaunar dukan ruwa ko kadan!
A jike ya karasa gidan Joyful kirjinsa na dauke fargabar abinda zai ci karo da shi.
A hankali ya saka hannu zai danna bell din shiga gidan sai yaga alamar kofar a saye kawai take ba'a hade ta ba. Don haka ya tura a hankali ya shiga. Madaidaicin parlour ya tarar a kintse tsaf sai dai wani irin wari-wari da karni da ya futa daban daga room freshener din da akai amfani da shi a falon ya sanya shi toshe hanci. Scanning din falon ya shiga yi, kofofi uku ne a cikinsa kowacce a rufe, kai tsaye ya nufi wadda take kallon shi ya bude! Wayam babu kowa! Ya dawo gefen hagunsa ya kama handle din ya bude a hankali! Take Safna ta bayyana akan dan karamin gadon da ke tsakiyar dakin ta baza kwalaben magunguna a gabanta tana sha. Bai iya kara ko taku daya daga bakin kofar ba ya tsaya cak yana kallon yanda ta futa hayyacinta ta rame sosai! Ya dade tsaye yana kallonta cikin tsananin bakin ciki kafin ya tuna abinda ya kawo shi don haka Wayarsa ya ciro daga aljihu ya bude camera ya soma daukanta ba tare da ya sanya hasken flash ba cikin dauriya da jarumta mai yawa. Sannan ya mayar da wayar aljihu ya juya zai futa sai kawai sukai karo da Joyful!
Hannunta dauke da robobin cocacola guda biyu. Cikin wani irin shock ya tsaya cak jikinta na rawa tana kallon Mahmud Wanda fuskarsa ta rikide ta koma kamar ta zakin da aka daukowa 'ya'ya don tsananin fushi, fuskar sai digar ruwa take yi wanda yake gangarowa daga cikin kansa da ya jike da dukan ruwa.
Sai lokacin Safna ta dago ta kalli kofa ai kuwa kirif suka hada idanu da Mahmud! A bala'in razane ta jefar da kwalbar hannunta ta mike tsaye cikin tsananin tashin hankali mara iyaka! Ko a mafarki bata tsammanin Mahmud ba balle ido biyu. Kasancewar maganin ya soma sama da ita ya sanya jikinta ya saki sosai don haka da rangaji take take takowa tana nufo shi hankalin ta tashe!
Wata uwar tsawa ya daka mata wadda ta sanya Joyful sakin fitsari a tsaye don tsananin firgita, daman ba karamun tsoron Mahmud take yi ba saboda ita kanta tasan ya tsaneta kuma yanayinsa yake bata babu abinda ba zai iya aikatawa ga wanda ya shiga gonar sa.

"Stay there! Kada ki karaso nan! Kar ki sake ki matso kusa dani, babu ni babu ke babu sauran wata alaka a tsakanin mu!  Daga yau bana fatan sake saka ki cikin idona har abada."

Cikin tsananin razana da kaduwa Safna take kallonsa lebbenta sun kasa motsi! Sama sama take gane abinda yake fada don tuni hankalinta ya soma futa daga jikinta! Gane hakan da yayi ne ya sanya shi juyawa ya futa da sauri ba tare da ya kalli Joyful ba domin yasan idan har ya daka ta zuciyarsa babballata zaiyi ya karairayata a wajen  nan ka ya kashe ta. Don haka yayi matukar kokarin danne zuciyarsa ya futa daga gidan ba tare da ya dora hannunsa a kansu ba. A hanzarce ya isa hotel room din sa yasha magani ya cire jikakkun kayan jikinsa ya kwanta amma sam sai numfashi ya soma yi masa barazanar daukewa! Danne kirjinsa yayi da karfi yana wani irin tari yayinda bakinsa ya soma bulbulo da jini. Tuni ya fado daga gadon yana birgima a kasa kafin hankalinsa ya soma fucewa daga jikinsa...............

Unedited

Ina shiga gidan Mami tace mun na juya Driver ya maida ni gida wai gobe da yamma zamu tafi Jeddah da Dada an kammala komai! Baki na saki galala ina kallon Mami raina a matukar bace.
Cikin muryar kusa da fashewa da kuka nace "Haba Mami yanzu gobe za'ai tafiya sai yau za'a gayamun don Allah! Bayan ina da abubuwa masu yawa a gabana nima, an kama an saka biki wata uku kacal ni dai abubuwan sun yi mun yawa wallahi!"
Banza tayi mun ta mike ta futa daga dakin nikuwa na kwanta a gado na rusa kuka don wallahi tafiya wani yaje shine karshen abinda nake tunani a yanzu. Kuma nasan abinda tafiyar take nufi, a kalla muyi 3weeks idan kuma Daddy yaga dama yace mu wuce Dubai ko London Dada ta huta. Nikam kowanne minti daya a wannan lokacin amfani ne da shi a gareni bana bukatar na bata shi da kowanne abu da ba zai amfanar da rayuwar da nake shirin fadawa ba.
A hankali naji an dafa bayana ana bubbugawa, na dago da sauri don banji shigowar ta ba. Cikin sanyi ta soma magana
"Zara sau nawa kike so na maimaita miki cewa hakuri ake da rayuwa? Ba abinda kake so kake samu ba domin ragamar rayuwarka ba a hannunka yake ba! Allah shine mai komai kuma shine abun dogaro a kowanne yanayi mutum ya tsinci kansa! Ni ya kike so nayi da kaina? Da inada Wanda zanyi wa kukan nima zama zanyi? Abubuwan da suke kaina suna da yawa Zara ciki har da damuwar da kike ciki, bana son ganinki cikin wannan halin ke da Mahmud hankalina tashi yake yi! Sannan wannan tafiyar kin saba da ita kullum da ke akeyi to menene sabo? Dada ce fa Zara? Wa take da shi da zata dauka bayan ke? Ke kina nan kika kukan tafiya ita Badi'a yanzu tana can tana masifar an kare a kanmu kin zama jelar Dada kamar ke kadai ta mallaka ko ta manta ita haifi Nuratu ni ban sani ba. Yanzun ta gama zagina a waya! Toh ina zan sa kaina? Na mutu? So Kuke stress da tashin hankali ya kasheni? Wannan auren kuma da kike ganin kamar na damu lallai kiyi ba don komai bane ina gudun abubuwan da suka faru akan Mahmud su juyo kanki ne, Dada akan aure bata ragayya bata lankwasuwa kuma bata rangwame, tun kafin zama da ita ya zame miki matsala nake son kiyi auren a huta tunda idan kin zauna me zakiyi? Irin wannan tunanin da damuwar har ciwo ya kama ki? Ina sane cewa ba wai kina son Mubarak bane kawai kin amince ne saboda kinga na amince da shi! Addu'a kullum nake miki Allah yasa ya zama mafi alkhairin zabi a gare ki ya kuma baki rayuwa mai albarka. Please ki saki ranki ki kama harkokin ki!"
Ajiyar zuciya na sauke a hankali cikin gamsuwa da kalaman Mami tare da wani irin tausayin ta. Rungume ta nayi kawai ba tare da na iya cewa komai ba.+
Washegari ina tashi na shirya na futa. A super market na tsaya nayi siyayya sannan na dau hanyar gidansu Aisha! Duk yanda zuciyata take karyewa idan na shiga gidansu ban daina zuwa ba, domin ina ganin kamar kulla zumunci da kannenta da iyayenta shine kadai sakayyar da zanyi wa soyayyar mu. Ko yanzu da na iso cikin gate din sai da nayi kuka na na share hawaye sannan na futo ina amsa gaisuwar masu kula da gidan. A nutse na danna bell din shiga cikin gidan. Iky tazo ta bude! Tun rasuwar Aisha bata koma Ulul Albab ba. Babansu yace ta hakura ta samu makaranta a Abuja taci gaba ko don ta rage wa Umma damuwar rashin Aisha!
Tana ganina ta rungumeni tana mun sannu da zuwa! Duka iyalan suna parlour domin ana public holiday ne. Har kasa na durkusa na gayar da su Umma suka dinga amsawa cikin kulawa da kauna mai yawa, duk da suma idan sun ganni jikinsu mugun sanyi yake yi amma suna kokarin boyewa don kar su karya mana zuciya. Dai dai ne lokacin da zanzo mu rabu ba muyi kukan Aisha ba. Bayan mun gaisa nake musu sallama sukai mun fatan alkhairi sannan na futo hannuna cikin na Iky tana bani labarin sabuwar makarantar ta. Sosai take bani matsayin Yayarta, idan tana da damuwa ni take daukar waya ta gayawa, idan abun farin ciki ne ya same ta haka don haka munyi wata irin shakuwa bayan mutuwar Aisha ta ban mamaki. "Ya Zara kar ki manta ki siyo mun turaren don Allah! A Jeddah ake durawa suanshi Marwa!" Murmushi nayi ina mamakin kamanceceniyar halin su da Aisha! Komai nasu iri daya ne, kamanni ne kawai suka bambamta da su don ita Iky fara ce tas kuma bata da tsayin Aisha! Amma tafi Aisha kyau sosai! Sai dai duk wani hali na Aisha itace photocopyn shi! Shiyasa nake jin ta cikin raina sosai. Muna zaune a mota tana gefena muna hira har Daddynsu ya futo. Cikin mamaki yace "aww Zara yanzu daman baki tafi ba ke da kike da tafiya a gaba tazo ta saka ki a gaba da surutun ta ko? To maza futo ki kyaleta parrot kawai!" Dariya nake yi ita kuma tana bubbuga kafa wai ance mata parrot! Jaka na bude na bata kudi sannan ta futa suna daga mun hannu ita da Daddyn har na bar gate din.
Allah sarki rayuwa! Wai yau babu Aisha! An nannade littafin ta an rufe an bude wani sabon babin rayuwa a gidansu! Duk son da suke mata yau da gobe ta mayar musu da rashin ta jiki, sai dai a tuna ta ayi mata addu'a! Haka rayuwa take! Don haka bawa ya tsaya ya gyara dangantakar sa da Ubangiji komai son da ake maka mutuwar ka ba zata tsaida komai na rayuwa ba. wani abun ma sai baka nan zai futo.

STORY CONTINUES BELOW

Karfe Goma sha biyun agogon Sa'udiyya lokacin da muka sauka a King Abdul'azeez airport da ke Jedda.
Dada, Ya Sadik da Ya Anis sai Ya Nuratu da Amal wanda jirgin rana ya kawo daga Kano muka taho gabadaya. Cikin mintina kalilan muka iso gidan Daddy! Tuni Hajiya tayi wa gidan gyara na musamman yana ta kamshin turaren wutar bakhoor. Ga lafiyayyen abinci cikin manyan food warmers yana jiranmu. Nida Ya Nuratu dakinmu daya daya, kowa yayi wanka ya shirya sannan muka futo parlour gabadaya muka zauna cin abinci.
.........................................................................

Room service ne yazo kawo wa Mahmud kayan shi da ya bayar laundry yayi knocking ya gaji ba'a bude ba! Anjima ya sake dawowa shiru, sai a karo na uku yayi amfani da katin hannunshi ya bude dakin. A razane ya dawo da baya ganin breathless figure din Mahmud a kwance cikin jini. Duk tunaninshi ya mutu ne kuma wani ne ya kashe shi don haka ya ruga da gudu yana ihu zuwa reception.
Cikin mintina kalilan motar yan sanda da ambulance ta iso aka dauki Mahmud zuwa asibiti don binciken sanin halin da yake ciki. Anan ne likitocin suka gano dalilin shigar shi wannan hali suka dukufa akan ceto rayuwarshi tare da tabbatar da cewa ba wani ne ya shigo yayi yunkurin kashe shi ba ciwon zuciyar sa ne ya motsa.
Sai da ya kwashe awanni talatin da tara sannan numfashin sa ya daidaitu bacci mai nauyi ya dauke shi. Mami dai tun jiya take tying number shi a kulle, sai tayi zaton ko wani muhimmin aiki yake yi ya kashe wayar.
..................................................................................................................................................
Dawowarmu kenan daga Makkah domin sauke nauyin umrah, Dada da Ya Anis muka bari domin su ba zasu iya da kansu ba don haka sai mun kammala da asibitin Dada munje madina sai mu wuce Makkah suyi tasu. A kitchen muka samu Ya Anis tana Kan kujera da bowl din fruit a hannunta tana sha. Hajiya na ta hidimar girki. Nidai banma tsaya ba saboda fitsarin da na shigo da shi na haye sama da gudu na shiga dakinmu. Sai da nayo wanka na sauya kaya sannan na futo falon na nemi hanyar dakin Dada. Kamar daga sama naga Daddy ya futo daga dakin a matukar zuciye sai wani irin huci yake kamar zai fashe idanunsa sun rine zuwa wani irin ja. Ban taba ganin makamancin wannan yanayi a wajen Daddy ba tunda aka haifeni, mutum ne shi mai hakuri da boye damuwa da kuma tawakkali akan dukkan abinda ya shigo rayuwarsa mai kyau ko mara kyau. Toh yaushe ma yazo? Kuma meye ya bata mishi rai haka? Sai kuma na tuna wacece Dada da yanda ta kware wajen sarrafa yanayin mutum.
Idan ta hado ku da ita tai maka wani abun sai ka manta yanda ake farin ciki wallahi.
A matukar sanyaye na tsuguna na gayar da Daddy amma ga mamakina hannu kawai ya daga mun ya wuce yana goge gefen idanunsa da bakin hannun rigarsa. Wani irin tsoro ne da tashin hankali ne ya tsirga mun nayi baya da sauri na koma dakinmu. A guje naje wajen window na yaye labulen don ganin futar Daddy! Ko minti daya ba'ayi ba kuwa sai gashi ya futo daga gidan Auwal ya bude masa mota ya shiga suka bar kofar gidan.
A ranar kam munga tsuran tashin hankali da masifa! Domin Dada gabadaya bata futo daga dakinta ba, kuma ta hana kowa shiga sai ma order da ta bayar cewa kowa ya hada shirginsa gobe zamu wuce madina muyi 2days muje Makkah suyi umrah mu juyo jeddah. Nan da kwanaki hudu take son ganinta a gida ta fasa ganin likitan.
Wannan bayani da Ya Sadik yayi mana ya sake ruda cikinmu ya saka mana shakku da tunani! Lallai kowanne abu ne ya sanya Dada yin wannan mugun fushin ba dan karami bane. Ba kuma abun wasa bane don ban taba ganin tayi irin wannan fushin me muni ba.
Don haka sai salon tafiyar ya sauya zuwa mara dadi Sam! Safiyar washegari muka dau hanyar Madeena kowa zuciyarsa a tsinke da tsoro da tunani. Dadinta ma garin tsarki da aminci da annashuwa zamu shiga.
Muna isa masaukin mu Dada bata huta ba tayi wanka ta nada lafayanta tace wa Ya Nuratu a tafi masallaci. Mu kam ko wankan bamu samu yi ba ana tsoron saba umarninta muka shige muka tafi.
Gabadaya addu'o'in mu na wannan lokaci akan Allah ya sakko da Dadda daga kan wannan fushi mai muni muka yi tare da fatan komai zai biyo baya yazo da sauki.
Nikam bayan mun dawo ma da nayi wanka naci abinci komawa nayi masallacin na raba dare ina kai kukana  wajen mai share hawaye a cikin Rawda!Waje mafi daraja da tsarki da girma a duniya da lahira, makwancin Annabin da Allah baiyi wa tamka ba SAW.
Ban taso ba sai da naji raina yayi mun sanyi, wani aminci da salama suna ratsani ga wani shaukin begen soyayyar fiyayyen halitta Alahissalam.

A ran kwana na hudu muka taho gida cikin jirgin Emirate! Abinda bai taba faruwa ba tun daga lokacin da Daddy ya mallaki jirgin kansa. Dada bata sake shiga jirgin haya ba, komai rintsi komai wuya sai Daddy ya matse schedules dinsa ya turo wannan jirgi. Toh sai gashi a wannan karon tace batason jirgin nasa ita na haya zata bi.
Babu yanda Ya Sadik ya iya haka yaje ya yanko tikitin first class din emirate a aljihunsa. Yana zuwa kuwa tace yayi mata lissafin nawa ne zai kama kudin ya gaya mata. Babu bata lokaci ta debo kudadensa in dollars ta bashi, zai mata musu ta katse shi da cewa "jirgin ubansa ma bai burge ta ba balle wani kudin siyan tikitin sa" wannan magana tayi wa Ya Sadik ciwo duk da yasan ita ta haifi Daddy ta raini abinta tasha wahalarsa amma ai da bazar sa take rawa a yanzu. Kuma Daddyn na cikin 2% din mutanen da ake samu cikin masu kudi wadanda suke ma iyayensu biyayyar da Daddy yake mata. Amma lokaci daya akan sabani guda daya ta fututtuke ta gurza masa irin wannan rashin adalci saboda son zuciya. Kai halin Dada ma ita kadai àka sani da irinsa.
.........................................................................
Daga can kasar sanyi kuwa bawan Allah Mahmud na kwance magashiyan kan gadon asibiti yana karbar kulawa ta musamman! Sai da yayi kwanaki biyu sannan numfashin sa ya daidaita. Number Dr.Ahmad ya bayar aka nemo shi akai masa bayanin halin da abokin aikina yake ciki. A ranar akai mishi transfer zuwa liverpool hospital domin samun kulawar ainihin likitan shi kwararren cardiology consultant Dr.Abraham!

Sai bayan ya samu ne yayi wa Mami waya ya sanar da ita cewa bashi da lafiya amma bai nuna mata a kwance yake a gadon asibiti ba yace dai yana bukatar hutu ne shiyasa ya kulle wayar. A yammacin ranar Daddy ya sauka a garin liverpool da damarar fuskantar Mahmud da wannan babban al'amarin da yafi komai girma a rayuwar su wanda yake ta rairaiton boyewa shekara da shekaru, toh yanzu kuwa watan bayyanar da komai ne ya kama gashi Dada ta dau abun da wata fahimta daban wadda bai taba kawowa ba idan yayi la'akari da irin son da take wa Mahmud din da kuma goyon bayan gaskiya da karamci da mutuntawa da mayar da alkhairi ga alkhairi da take da shi. Bashi da zabin da ya wuce fuskantar Mahmud ya warware mishi komai da kansa duk da yasan nauyin maganar na iya yi wa raunanniyar zuciyarsa illa amma bashi da choice bashi da zabi.Assalam! I'm sorry for dropping this late. I am super busy wallahi!
Masu korafi kuyi hakuri ku gane cewa muna da uzuri kamar kowanne Dan'Adam ko ku masu karatu wataran uzuri na hanaku zaman karanta chapter guda daya balle kuma mai rubutawa! Ya kamata ku dinga adalci da sanin me zaku gaya wa mutum.
Muna da abubuwan yi ba da rubutu muka ta'allaka ba, muna karatu muna sana'a muna da wadanda zamu kula da su sannan muna harkokin yau da kullum rubutun saboda nishadi kawai muke yinsa ba biyanmu ake ba ba kuma rashin aikin yi ne ya sanya mu yi ba.
Banyi alkawari update kullum ba kafin na fara rubutun don haka ba Jan rai nake ba, idan kunga banyi update ba toh ban samu sararin yi bane. I didn't mean to hang you a waje daya kuna ta jira. Nima nafi so nayi na kammala amma bazaiyu nayi rushing labarin ba don haka nake Baku hakuri dafatan zaku fahimceni.
Back to our story, da alama dai asiri na shirin tonuwa kuma balli na shirin tashi. Ga Dada ga Daddy ga Ya Mahmud! Yakin mai zafi ne gaskiya don kuwa kowa zuciyarsa a tsaye take. Me kuke tunanin zai faru?

Da daddare muka sauka a Abuja cikin sanyin jiki da bacin rai. Wata irin tafiya mukai mara dadi ko kadan. Babu wanda ya siya ko tsinke balle wata tsaraba sai tarin bakin ciki kawai muka lodo. Acan muka baro Ya Nuratu duk da hutun ta bai kare ba gani tayi dawowan nata bashi da amfani tasan cewa tsuran bacin rai ne zai biyo bayan wannan fushin na Dada. Don haka mukai sallama rai duk babu dadi ta tafi gidanta.


Ya Omar ne yazo daukar mu fuskarsa a matukar daure kamar jakadan lahira! Ko me akai masa Oho! Ita kanta Dadan na lura sai da taji shakkarsa don idan Ya Omar ya hade babu sauki.

Su Ya Sadik ya soma saukewa a gidansu sannan ya wuce da mu gidan Dada. Muna futa ya juya motar sa ya bar gate din cikin fushi. Sosai Dada ta tsurawa hayakin da ya tayar ido tana jinjina kai sannan ta wuce cikin gida ina biye da ita hannuna janye da trolley din ta.

Toilet na wuce na watsa ruwa na sauya kaya sannan na futo falon, Baba Rabi na samu a zaune ta rafka tagumi cikin damuwa na zauna gefenta a nutse ina cewa "Baba Rabi lafiya?" Hawayen da take rikewa ne suka gangaro Kan fuskarta tace "ina lafiya uwar dakina tana cikin fushi Zara? Ko amsa gaisuwata bata yi ba ta shiga daki! Na bita da abinci tace na kwashe bata ci kunu kawai ta tsiyaya a Kofi ta kafa kai kwankwade ba tare da ko jin zafin sa ba. Ba dole hankalina ya tashi ba Zara"

Ajiyar zuciya na sauke a hankali sannan nace "Baba Rabi zuwa yanzu ya kamata ki gane halin Dada! Idan tana cikin wannan fushin nata bata dauke kowa ba. Ni yanzu bana damuwa da abubuwan ta irin da. Daga fushin sai me? Sai fada da zage zage sai kuma me? Ba sai tayi ta gama ba! Sai ma ka kula ta!" Ina gama fadar haka na mike a zuciye na shige daki na bar Baba Rabi baki bude don tsananin mamakin maganganun da nayi. A ranta tana cewa "lallai duk yanda ake tsoronka da shakkar ka, masifa da fushi na sawa yau da gobe a soma raina ka"

Kwarai hakane! Don yanzu wallahi babu kashi hamsin cikin kaso darin tsoron da nake wa Dada! Kawai dai sai dai biyayya amma zancen tsoron fadanta yayi matukar raguwa a dalilin sabo. Sai dai idan nasan ni nayi laifi toh a nan fa hankalina yake tashi don Dada karshen karshen ce. Idan kuwa ba laifina bane, nagano takanta da yanda zanyi takatsantsan kada fushin ta ya shafeni. Wannan shi ake kira zaman yau da gobe, duk tsaurin mutum idan ka karanci halinsa ka gane lagonsa toh zaku zauna lafiya, sai abubuwan da ba'a rasa ba Wanda ba'a

Sauya mutum da dashi. Domin ance hali rubutun dutse. Sauya kayana nayi zuwa skirt and blouse din atamfa. Na yane kafada ta da wadataccen gyale na fesa turare na futo. Sai lokacin na tuna motata na bukatar service! Tsaki nayi na koma daki na kira Ihsan! Bayan mun gaisa nace ta turomun driver dinta zan futa tace toh!

Na dade a bakin kofar Dada ina sauraren wayar sirrin da take yi da Malaminta Mallam Safiyanu da ke Adamawa. Karshen maganar naji inda take cewa "tun daga yau za'a fara! Zansa a turo maka gabadaya in anjima. kullum idan an tashi daga karatun a yanka raguna biyu a bayar sadaka. Sannan a duba kauyen da suke da bukatar ruwa a haka borehole a siya musu inji duk da wannan niyyar. Ka hada da wani acikin almajiranka ayi masa passport su tafi tare da su Mai sunan Malam" tayi shiru tana sauraren shi sannan tace "babu komai Malam nima nagode! Allah ya saka da alkhairi. Allah ya bamu nassara!" Daganan sukai sallama ta ajiye wayar.

Wani mugun gumi na share na murda kofar dakin ina sallama. A ciki ta amsamun fuskar nan a matukar daure tana zaune kan sallaya da alkur'ani a gabanga. Tuni na shiga taitayina. A ladabce na durkusa gabanta nace "Dada zanje Office din Mami, tailolin suna nemana akan dinkunan da Mami ta basu" a cushe tace "kayan biki?" Na gyada kai a hankali duk da nasan karya nake yi hanyar futar kawai nake nema. Kuma sai nafi samun dama idan nace mata futar akan harkar biki ce. Ilai kuwa sai ta amince harda cewa wa zai kaini tunda mota ta an dade ba'a hau ba. Nace mata driver din Ihsan! Ta amsa cikin gamsuwa nayi mata sallama na futo ina hamdala da bata balbaleni da masifa ba.

Ko da yawancin fadan Dada akan gaskiya take yin shi, bata fada da fushi sai an tabo ta, inaji a jikina wannan karon kamar akwai wani babban al'amari a cikin kowanne irin abu ne ya taso mata. Don naga kan me uwa da wabi take bi kawai! Tunda gashi har da Daddy cikin maganar.

Driver na isowa na futa muka dau hanyar gidan Mami. Ina zuwa na tarar itama ta taho gidan Dadan don haka nace mu wuce gidan Ihsan na dawo da yamma. Ashe ashe da Mami taje gaida Dada bata ko kalle ta ba. Cewa ma tayi ta tattara tabar mata gidanta kuma kada ta sake zuwa sai ta neme ta. Kuka, roko, magiya Mami ta zube a gaban Dada tana yi amma ta juya mata baya ta shige dakinta tana jaddada mata cewa kar ta sake zuwa sai ta nemeta kuma duk abinda suka kulla Allah ya tona asirinsu don haka tana nan zuwa daukar mataki akansu daga ita har Daddyn. Sai a lokacin Mami ta soma gane inda zancen ya dosa. Gabanta yayi mugun faduwa domin tasan babu wata magana da ta hada su da Daddy sai ta Mahmud wadda take ganin kamar abu me sauki ne su fahimtar da Dada ta aminta dasu sai dai ga madaukakin mamakin su ta dauki maganar da wani irin zafi da rashin fahimtar da kowanne balli zai iya tashi akan ta. Haka Mami ta bar gidan tana kuka, sai bayan ta koma gidanta ta nemo lambar Daddy don taji ba'asin maganar.+


STORY CONTINUES BELOW

A daidai wannan lokacin Daddy na tsaye a gaban gadon da Mahmud ke kwance magashiyan yana numfashi dakyar da taimakon oxygen. Yayi wani fari alamun rashin jini wadatacce a tare da shi. Ya rame sosai kamar ba shi ba. Hawaye Daddy ya share sannan ya zauna a kujerar da ke gefen gadon yana amsa sallamar Mami a waya. Cikin kuka tace "Daddy kunyi maganar Mahmud ne da Dada?" Wani irin huci ya furzar sannan yace "Zainab ina cikin tsaka mai wuya! Ina cikin tashin hankali da tunani! Ba zaki gane irin addu'ar da nayi ba kafin na sanar da Dada yanda akayi na samu Mahmud da alakata da mahaifin shi da kuma kaddarar da ta shigo mana baki daya. Sai da ta gama saurarena gabadaya sannan ta burkice ta soma fada akan lallai munci amanarta. Ya za'ai mu rufe mata wannan sirrin shekaru kusan arba'in tana kallon wanda ba jininta ta ba tana son shi tana fififta shi fiye da jininta? Ta inda ta shiga ba tanan take futa ba. Ban taba ganin tsuran tashin hankali irin wannan ba Zainab. A halin da ake ciki ina bibiyar Ilyas da ne da inda zan samu danginsa. Shekaru ne masu yawa, son Mahmud da kaunar sa suka makantar dani suka kurmantar dani suka toshe mun basirar tsayawa wurin nema masa dangin mahaifinsa don gudun irin wannan ranar! Toh yanzu me zan ce dashi? Tace lallai family meeting zata hada akan wannan maganar don haka naga babu mafita irin na taho London na same shi na warware mishi komai a nutse da kaina, Ina zuwa Zainab a gadon asibiti na samu Mahmud cikin mahuyacin hali mai muni...

Sai Daddy ya fashe da wani irin kuka.

Itama Mamin kukan ta fashe da shi kamar zata shide tana 'inallilahi wa Inna ilaihi raji'un" sun kai minti biyar suna kuka babu me magana kafin Daddy ya lura da yanda numfashin Mahmud yake sarkewa, kirjinsa yana hawa da sauka. A sukwane ya katse wayar ya danna kararrawar kiran nurses. Cikin minti daya nurse din ta shigo, ai tana ganin halin da Mahmud yake ciki ta futa da gudu tayi kiran likita.

Kafin wani lokaci likitoci guda biyar ne akan Mahmud bayan sun kori Daddy! Daga nan ma sai suka futo dashi daga wannan dakin suka maida shi ICU.

Daddy ya fadi kasa yana wani irin kuka mai taba zuciya domin ya saddakar Mahmud ba zai tashi ba.

Dakyar ya iya daga wayar Mami da take ta bugowa tun bayan katse wancan kiran da yayi. A galabaice yace "Zainab sun maida shi ICU! Zainab zamu rasa Mahmud, Mahmud mutuwa zaiyi!"

A sukwane Mami ta mike tsaye tana wani irin haki. Kanta har juyawa yake yi yayinda zuciyarta ke bugawa da sauri kamar zata ballo daga cikin kirjinta. Katse wayar tayi ta nemo layin Faisal, bugu daya ya dauka! Bata saurari gaisuwar sa ba cikin kuka tace masa "Faisal Mahmud na can rai a hannun Allah don Allah ka duba mun idan za'a samu ticket din gobe!" A hanya Faisal yake yayi maza ya gangara gefen titi yayi parking hannunsa na rawa. Amsawa kawai yayi don yasan bata da sukunin da zata amsa masa duka tambayoyin da suke bakinsa........Daga nan ya wuce neman tikitin B.A guda biyu na safiyar gobe.

..................................................................................................................................................

Ina cikin bacci kuwwar wayata ya tashe ni, na mika hannuna kan side drower na dauko wayar ina mamakin wanda yake kirana a wannan lokacin. Ganin sunan Mami akan screen din ya sanyani bude idanuna da sauri ina kara wayar a kunnena. "Hello Mami me ya faru? Waye ba lafiya?" Maganarta a mugun sanyaye tace "calm down Zahra! Muna hanyar airport ne da Faisal zamu tafi London ciwon Mahmud ne ya tashi! A sukwane na tashi zaune ina cewa "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un! Mami me akai mishi? Wani abu ne ya faru?yana ina yanzu?" Cewa tayi "yana asibiti anyi admitting din shi" Kuka na saka mara sauti ina salati, hankalina a matukar tashe. Ajiyar zuciya Mami ta sauke sannan tace "ki kula da kanki Zahra ki kwantar da hankalinki zamu dinga waya. Don Allah kar ki janyo wa kanki abinda Dada zata huce fushinta akanki kinji? Kinyi sallah?" Sai lokacin na duba agogon dakina naga karfe shida, kakkauran labulena ne bai bari ka gane gari yayi haske.

Na girgiza kai kamar tana kallona nace "banyi ba Mami na zata ma asubar bata yi ba." Cikin sanyin murya tace "ok! Tashi kiyi sallah kuma ki daina wannan kukan addu'a yafi bukata. Ina kuma Jan kunnen ki don girman Allah Zara kada ki bari wani abu ya hada ku da Dada"

Nace "Insha Allah Mami! Allah ya kiyaye hanya! Allah ya bashi lafiya." Daga nan mukai sallama.


Kuka na fashe da shi mai cin rai. Gabadaya duniyar ta daina yimun dadi ko kadan, daman dakyar wannan baccin ya daukeni domin Baba Rabi ta labarta mun yanda Dada tayi wa Mami da tazo, a take nagano abinda yake shirin faruwa. Sirrin da suke rufewa ne lokacin bude shi yazo, kuma alamu sun nuna cewa duka abubuwan suna shigo musu ne sabanin yanda suka tsara, sabanin yanda suke hasashen zai faru.

Gefe guda kuma fadan gaske muka yi da Mubarak akan matar shi, domin rufe ido nayi, nayi masa kyakykyawan warning akanta da kirana da take yi da wayarshi sai yace wai nayi masa rashin kunya. Nace koma me zai fada ya fada amma bazan dauki iskanci daga wajen matar shi ba. Haka muka rabu baram-baram kusan awanni arba'in bai neme ni ba. Amma ko a jikina, ni na fuskanci ma gabadaya ba wai son Mubarak nake ba wallahi! I don't give a damn about him! Ko a mutu ko ayi rai, in ba daban Mami da nake tausayi da abinda Dada zatai mata idan na bijirewa wannan auren ba, da sai nace wallahi na shirya daukan duk wani matsi da masifar Dada na barar da wannan auren kowa ya huta. Banason tashin hankali da stress a rayuwata.

Agogo na kalla na tashi a sanyaye na shiga toilet nayi alwala nazo na tada sallar asuba. Na dade akan sallayar ina yi wa Ya Mahmud addu'o'in fatan samun sauki da salama akan wannan mugun ciwon nasa. Kila shima bai san komai ba sai yanzu, ko kuma jin yanda Dada ta dauki maganar ya daga masa hankali. Allah sarki Ya Mahmud, gabadaya tausayin sa ne yayi matukar kamani, yana ganin ibtila'i a rayuwarshi iri iri sai dai Allah ya bashi ikon cinye jarrabawar sa.

Ban iya komawa baccin ba don zuciyata bata da wannan sukunin, gashi babu wanda zan kira naji halin da yake ciki a yanzu. Addu'a naci gaba da yi masa ina kallon agogo da kiyasta time din da su Mami zasu tashi. Na kira ta mukai sallama a lokacin jirgin ya soma tafiya, ta sake jaddada mun maganar na lallaba Dada yafi sau uku sannan ta ajiye.......

Wani kukan na sake cigaba da dashi saboda yanda nake jin zuciyata babu abinda yafi mun kukan sassauci.

Dakyar Baba Rabi ta sani nayi break fast na dawo dakin na kwanta, Dada har lokacin bata bude kofarta ba balle a kai mata nata abincin. Ko gaisawa bamu yi ba, nikuma ina tsoron kwankwasa mata ya zama laifi.

Daki na dawo na kwanta a gadona jikina a mace, gabana sai faduwa yake yi! Ko ya zasu tarar da jikin nashi Allah ne masani. Na soma tunanin ko Daddy zan kira? Sai dai kuma ba lallai yana tare da shi ba kar na daga masa hankali. Sai Safna ta fado mun raina, nayi sauri na nemo lambarta na kira, sau uku tana ringing ta katse bata dauka ba, hankalina ya kara tashi! Kawai sai nayi shahada na bugawa Daddy don hakurina ya kare.

Cikin sa'a bugu biyu ya dauka! Na sauke ajiyar zuciya a hankali na soma gaida shi. Muryarsa ta kara karyamun zuciya domin yana maganar zaka gano tarin bacin rai da tashin hankali a cikin ta. Cikin sanyi nace "Daddy ya jikin Ya Mahmud?" Sai da ya furzar da iska mai zafi sannan yace "Mahmud yana nan cikin radadin ciwo Zara, ko numfashi sai da taimakon oxygen take yi, kiyi tayi masa addu'a Allah ya tashi kafadunsa idan da rabon zai tashi" wani mugun kuka ne ya kufce mun mai dauke da tashin hankali, inaga shima Daddyn ya manta da wa yake magana ne yayi mun wannan bayanin, don haka sai ya dawo rarrashina yana cewa "ba kuka zaki yi ba kinji Zara, addu'a yake bukata! Jikin nasa ma ai yayi sauki comparing to jiya, kuma likitoci na bakin kokarin su akansa, insha Allah zai ji sauki Zara! Stop crying kiyi masa addu'a kawai" dakyar nayi shiru mukai sallama ina jin kamar na zama tsuntsuwa na tashi na ganni a garin London.

Post a Comment for "HAUSA ARAB CHAPTER 5"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...