DAN BABBAN GIDA COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

DAN BABBAN GIDA COMPLETE

DAN BABBAN GIDA COMPLETE

- - Post a Comment

 DAN BABBAN GIDA COMPLETE


Samrah p. o. v

Samrah Ya kamata ki canza kayan

Nan na jikin ki haka kike so mu fita cikin unguwar nan duk jama'a na kallon mu?

Sai da na gama zuge tee din jikina sannan na dube kausar wadda tun dazo idanun ta ke kai na, kallon tsaf nayi mata sanye take da wata duguwar brown din hijabi mai hannu.

Sai da naja wani dan guntun tsaki sannan na ce mata, meye haka kausar kin wani saka wata doguwar hijabi sai kace matar liman, kausar ta kalle ni tayi wani dan murmushi da bai kai ciki ba ta ce Eh!


matan liman din ce kuma wanan shigar ita ce duk wata musulmar kwarai zatayi don kare martabar ta, itace kuma Allah (SwT) Ya umarce mu da muyi, ba irin shigar ki ba irin ta jahilan fark...kee kausar!


Na dakatar da ita cike da tsiwa cikin daga murya nace What are you saying kausar?

Wa'azi kike min ko me? Sai da na matso kusa da fuskar ta sannan na sa dan yatsa na ina mai nuna ta, nace idan wa'azi zakiyi kije masallaci ina jin can za'a fi sauraron ki ba nan ba ina gama fadar haka na figi jakata nayi gaba.. ta biyu ni cikin sassarfa tana bani hakuri.Samrah p. o. v

Samrah,samrah! AMMI ce ta kwada min kira.

Sai da na Dan yi tsayowar minti biyar sannan na koma cikin gidan ina mai yatsinar baki, tsaya mata nayi aka ina taunar cingam.

Ammi ta ajiye tire din da ke hannun ta sannan ta dube ni, ina zaki ne samrah? Baki ga magrib ya kusa ba? Ko so kike baban ki ya dawo yayi ta fada ne? Meyasa ne ke kam bakiji samrah? Eyye!

Shiru nayi mata.

Na turo baki Ammi fa yanxu zan dawo plss na.. na tafi? Wani assignment ne fa aka bamu kuma gobe ne za'ayi submitting dole na gama shi yau.. cikin raina nace (astagfurullah) nayi ma Ammi karya.


Sorry Ammi!

Shigowar safwan kanina ne ya dauke ma Ammi hankali, Anan ne ni kuma na samu damar fita!

Ina fita na tarar kausar bata nan cikin raina nace ko a jikina! Na san gida ta koma abun ta, ita wai a dole uztaziya.


Mtsww wani dan kuntun tsaki na saki na ci gaba da tafiya ta ina wakar india.

Ina shirin tsayar da mai taxi kenan sai naga wata katuwar jeeb prado ta parker gaban neighborhood din mu ,wani saurayine kyakyawan gaske naga ni ya fito daga motar sanye yake da duguwar farar jallabiya irin ta larabawa.

+

Yana fitowa ya zuba man wani kallo wanda yake cike da tsana da kyama, kallon jikina nayi riga ce da lagins a jikina kuma ni dai ban ga abun kyama a tattare da niba,

Murguda masa baki nayi nace mutum sai kallon tsiya sai kace wani maye.

Na jiyo kenan zan shiga taxi kenan, a tsammani na shi din ba bahaushe bane saboda yanayin shi da naga ni irin na larabawan usul ne.

Hannun sa ya sa ya kamu riga ta, ya tsura min kyawawan blue eyes din sa, ya daka man tsawa What do you just say,? Ina jin haka ciki na ya fara motsi saboda tsabar tsoro cikin raina nace ashe dai yana jin hausa?

Ware masa nawa brown eyes din nayi cike da tsiwa nace how dare you touch me! Yayi saurin sakina ya daga murya yace Repeat what you just said to me.

Tsaki na ja masa .mtsww nace I can't! Na shiga taxi cikin sauri ina mai kara kiran sa Maye kawai !

Cikin daga murya ina dariyar mugunta.

Hy guys how is this chapter hop you enjoy itSamrah p. o. v

Misalin karfe 8.00 na dare na dawo gida, pls dont be surprise, as you already know am a party girl!

Cikin sanda na shigo gida hannu na rike da takalmana ina tsoro kar Ammi ta ganni.. har na zo bakin kofa kenan zan shiga sai dai naji muryar ABBA


kee samrah!

Ya fada cikin daga murya daga ina kike! Hey guys am just speechless dont know what to say to Abba!..

Ba day ke nike magana ba samrah kinyi shiru kin kyale ni ko, yi hakuri Alhaji!


A heard a voice 4rm behind. Omg who was this angel that save me from Abba!+

Sai da ta tambaye ni kafin ta tafi.. wani Assignment din makaranta ne taje yi ko samrah?

Daga idanuna nayi sai naga Ammi ta tsura man ido.. kada kaina nayi alamar eh!

Sannan Abba yayi fada kar a sake barin yaran sa fita da magrib.. Ammi tayi saurin amsa masa.

Yana tafiya ta juyo kaina tace samrah! Look at me, na kallo ta da idanuwana da suka canja kalla cikin minti biyu sun koma jajar don kuka, tace haka mukayi da ke? Ba sai da nace maki ki dawo gida kafin magrib?

Ta shi nayi cikin sauri nayi hugging Ammi, Am really sorry Ammi ba zan kara ba ban samu taxi da wuri bane shi yasa.. Ammi ta tashi ta ce kije ki ci abinci kafin Abban ku ya fito yayi maki fada.

Murmushi nayi cikin raina nace Abba sai fada but he still love us.. Ammi ce ta kalle ni tace me kuma kike wa murmushi samrah, saurin tashi nayi nace Ammi ina safwan ya dawo daga tahfiz din daran ne?


Ammi na shirin fita tace eh yana waje tare da Abban ku kiyi sauri ki fito..

Pls comment bellowSamrah p.o.v

Yau bayan na dawo daga makaranta misalin karfe hudu na yamma ,

duk na gaji saboda azumin da nike yi na ranan litinin.

Ina shiga gate din gidan mu naga wata bakar Jeep anyi parking din ta cikin raina nace yau baki aka yi kenan gidan.

Ina shiga cikin palo naji gamm nayi karo da mutum, wata kara na saki


Auuuchh!! Ammi kaina!

Sai a lokacin ya lura da akwai mutum a gaban sa tsaki ya jaa mtswww don't you hav eyes!! Bakya gani ne ya fada cikin daga murya..

Oh.. This arrogant man again? Mtsww na ja tsaki cikin raina nace mutum kullun fuska a daure ba ko fara'a sai shegen girman kai day Jan ajin tsiya.

+

Get out of my way ya fada yana mai saka hannun sa cikin aljihun wando sa.  Da sauri na matsa na shiga cikin gida,

Abba na gani tare da mai martaba suna magana,  cikin sauri na zo zan wuce samrah!


Abba ya kira ni

Baki iya gaisuwa bane?  Ko baki ga baki bane a gidan?

Cikin sauri na duka na gaisar da su ,samrah ce haka ta girma? Naji

Mai mai martaba ya fada.

Ni dai nayi sauri na shiga kicin ina kiran Ammi.

Sorry for the short chapter

Samrah p.o.v
Ina shiga kicin na tarar da Ammi tana wanke wanke.
Nayi sauri na rufe mata ido Ammi ta taba hannu na tace samrah?
Nayi sauri na cire hannu na ina dariya
Ammi yunwa nake ji na fada ina mai shan wani juice da ammi ta hada na kwakwa ina shanyewa nace Ammi tace dama dole kiji yunwa ai kin fita tunda safe ba ko breakfast
1
Ajiye cup din da ke hannu na nayi nace Ammi kin san mene?

Tace a'a sai kin fada nace hmmn
Dr .Arrogant ne ya hana mu fita lectures muke tayi kuma baya son late coming a class din shi.
Ammi na yanka water melon tace shi kuma lecturer din ya sunan sa kenan Dr.arrogant?
Dariya nayi nace Ammi sunan sa Dr. Ahmad zaid, Egyptian ne yana koya mana physics.
Oh God! Kiran sunan sa ma yasa raina ya baci that arrogant jerk na fada ina mai tsaki mtsww
Ammi na shirya drinks a try ta kalle ni samrah! Malamin ki kike zagi ko? Nayi dariya nace Ammi ya cika girman kai ne
Ammai tace toh naji, shiga dakina ki dauko man waya ta ki zo kici abinci
Ina mika ma Ammi wayan ta na bude freezer na dauka chocolate ice cream. Ina sha naji wani sanyi hmm yummy na fada.
Ammi wannan ma ya isa
Ammi na motsa miya face samrah ice cream din safwan ne bakin shanye naki bane jiya?
Na turo baki nace ammi yunwa fa nake ji
Ammi ta kada kai tace kida safwan ne ni dai ba ruwana , nace Ammi pls don't tell him nice na sha tace toh.
Cikin sauri nayi huggin dinta nace thanks Ammi nayi mata peck a cheeks din ta
Har zata fita nace Ammi na ga mai martaba dazo a parlor me ya kawo su?
Ammi na jin na fada haka tace nima ban sani ba, kije kiyi wanka kizo kiyi wanke wanke
Ammi, Ammi! Safwan ya shigo da sauri cikin kicin ina ganin sa na zaro ido OMG! This boy is back am finish na fada cikin raina
Nayi sauri na boye bayan dinning table.
Ammi naga mai martaba sun zo yace ma zai bani doki nayi hawan sallah babba. Cewar safwan.
Ammi tayi murmushi tace Allah?
Safwan!
Safwan yace eh Ammi ai zamu je sallah katsina ko?
Ammi ta dafa kan safwan tace eh safwan ko dan kai ai zamuje yawan sallah fada.
Cikin jin dadi safwan yace yawa Ammi zaki fada wa Abba ko?
Ammi tace eh mana tana murmushi
Safwan naji haka yayi hugging Ammi yace you are the best Ammi in the world
Sorry guys for not posting for so longAmmar p.o.v

Ammar ne kwance dakinsa yana sauraron Qur'ani suratul Rahama.

Amma  zuciyar shi har yau nazarin yarinyar yake da ya hadu da ita kwanakin baya a estate da mai martaba sarki ya aike sa wajan uncle khalid

Gashi sun kuma haduwa da ita yau gidan uncle khalid

Rintse idanon sa yayi yana mai tunanin Al'amarin ko dai yar gidan ce?

Tambayar da yayi wa kan sa kenan

No! Ya ba kansa amsa, koda ban san yaran uncle khalid ba nasan suna da tarbiya.

yana jin kiran sallah ya kashe karatun Qur'anin ya mike

Why am i even thinking about that manner less girl


Tsaki yaja mtsww yana mai tuna haduwar su da shigar da ke jikin ta.. Yayi tir da halaye irin na ta

Ya shiga toilet.

************************************

Bayan na idar da sallah Asuba nayi azkar na dauko Qur'ani ina biya hadda ta, sai kawai naga an bude kofan daki na

Ya samrah!

Rufe ido na nayi ina girgirza kai na, ina idar da ayan na bude ido na,

safwan na gani tsaye yana kallo na, ya samrah ina ice cream dina?+


Na tambayi Ammi tace bata san wa ya dauka ba.

Rufe Qur'ani na nayi, na kalli safwan wanda ya cika pam da fushi kamar zaiyi exploding yana jira na bashi amsa amsa

Safwan nace maka ban san wanda ya sha maka ice cream ba kazo early morning kana tambaya na, kama yi sallah kuwa?

Nayi mana ya samrah ina so nakai ice cream dina school ne.

Mikewa nayi nace kai ka sani , sai ji nayi safwan yace What ya na mai nuna roban ice cream da yatsan sa.

Ya samrah! Ya zaro idanun sa na kalle sa menene?

You drank my ice cream! Ya fada yana daga murya.

Pls vote belowWacece samrah ?

Samrah fara ce kyakyawa, tana da tsayin gashi baki kirin dashi

Samrah na da tsayi , tana da wushirya da digon baki a fuskar ta wanda yake kara ma takyau.


Samrah bata da jiki sosai amma akwai ta da shape mai kyau wanda ake kira coka cola shape.

Samrah na da ibadah sosai da kyawawan halaye wanda ba wanda yasan tana dasu sai Allah.

Wani gyefen kuwa an san ta da wasu bad habits wanda suka sa mutane ke ganin ta kamar marar tarbiya, akwai ta da yin shigar banza da koma zuwa party.

Samrah yarinya ce mai ilimi sosai na boko da kuma addini.

Asalin ta

Asalin su yan katsina ne suna zaune a cairo da iyayanta da kanin ta safwan,

Asalin sunan ta Samrah khalid first daughter of engineer Khalid, shakarun ta 22 a duniya tana karanta medicine a university of Al azhar dake cairo.

Mahaifiyar ta hajiya fatima wato Ammi.

Alhaji khalid wato Abban samrah yan'uwa ne da mai martaba sarki zaid.

Sarki zaid yana da yara biyu, yan biyu maza da kuma mace daya.

Yana da mata biyu hajiya zainab itace matar sa ta biyu tana da diyar ta mace zarah yar shekara 18 wadda ke karatu a baze university Abuja tana karanta law.

Sai matar shi ta farko Neelam wadda aka fi sani da mami, balarabiya ce yar kasar Egypt, tana da yara maza yan biyu Ahmad da Ammar suna da kamanin larabawa gaba dayan su, amma ba identical twins bane.

Ahmad doctor ne yana lecturing a Al Azhar university dake cairo, yayi aure da matar sa daya da babyn su dan wata shidda, sunan shi fou'ad

Auran dangi aka yi masu.

Ammar

Ammar pilot ne yana aiki da emirates airlines. Bashi da aure, mai martaba ya hada shi da cousin din sa amma yaki.


Ammar akwai shi da kasaita, jijida kai da girman kai.

Mutum ne mai son Addini yana son mace mai addini da natsuwa, kunya da kamala.

Dan gatane a wajan sarki, saboda irin sun mulkin sa sarki ya nada shi crown prince.


Samrah bata san su Ammar ba suma haka. Amma tasan zarah saboda suna zuwa wajan mai martaba lokacin sallah.

************************************

Safwan ya kalle ni ya samrah you drank it all?


Sauri nayi na gudu ina dariya, safwan ya biyo ni da guda ya na kokarin saka mun kyankyaso a jikina

Samrah! Abba ya kirani meye haka kuke yi da safen nan?

Cikin shaksheka saboda gudun da nayi nace Abba safwan ne ke so ya saka mun cockroach a jiki na, na fada ina me ya mutsa fuska ewww.

Safwan yace Abba karya ne ta shanye mun ice cream dina ne fa kuma ina so nakai school yau.

Abba yayi kyaran murya sannan yace yi hakuri safwan zan saya maka wani yau inshaAllah.

Ina jin haka na fito daga bayan kofa nace Abba ni ma pls ka saya min. Abba yace a'a ba kin shanye masa nasa ba this is your punishment samrah.

Safwan yayi min gwalo. Na shiga daki ina buga kofan saboda haushi .


Ina shiga daki na kira kausar

Kausar-Hello kawas yau kin tuna da ni ne?

Samrah-Ina jin ta fadi haka na kwashe da dariya.

Lallai kausar tun ranan dai shiru ban sake ganin ki ba ko a school.

Kausar-Samrah ai ke din ce ba'a iya maki.

Samrah-Naji din, yauwa na kira ki ne naji ko zaki shigo school yau?

Kausar -ni diyar wa ai dole na nazo kin man ta muna da Dr. Arrogant ?


Samrah - kedai bari yau ai azumi zan dauka dan nasan hali kila sai mun kai magrib ,bare ma yau chemistry ne zamu dade a lab.

Haka dai muka cigaba da fira har 8:00am.

Pls vote & commentAmmar p.o.v

Mai martaba dan Allah kayi hakuri inshaAllah zan kawo maka ita .


Na baka nan da kwana uku I mean three good days ka kawo matar da zaka aura ko na daura maka aure nan da kwana uku! Kana jina ko!

Ammar na jin haka ya tashi tsayi yana zaro blue eyes din shi , mai martaba ya cigaba da fatan kaji abun da na fada?

Ammar ya Kada kai cikin sauri, yace na ji mai martaba yana fadar haka ya fita fuu kamar iska.

Ranka shi dade, dan sarki jikan sarki, fadawa ne dayawa suka rako Ammar dakin mama wato (hajiya zainab) suna masa kirari .


A kishingide take bisa wani kafet mai zane irin na gargajiya na gidan sarauta, sanye take cikin kaya na Alfarma da wasu kuyangi suna mata fifita gefin ta kuma wasu kayan lambu ne.

Assalamu Alaikum, Dan sarki Ammar zai shigo ,wani bafade ya fada.

Mama na jin haka ta kada kai Alamar eh.

Kuyangi dake gefen ta taba izini suka fita .Ammar na shigowa mama ta lura da yanayin shi kamar yana cikin damuwa.+

Zama yayi yana nade kafafunsa irin zama na isa zaman da yaran sarauta keyi, sannan ya dukar da kansa ya gaishe ta

Mama ta amsa tana kallon sa, Ammar lafiya?

Ammar na dago kansa sai hawaye idanon sa sunyi jajar.

Mama mai martaba ne yace na fito da mata cikin kwana uku kacal ko ya aura mun wanda ransa ke so.

Ajiyar zuciya mama tayi hmmn Ammar! Mama ta cigaba, abun da mai martaba ya fada gaskiya ne Ammar shekarun ka karuwa suke yi ba raguwa ba kaga Dan uwan ka yayi biyayya yayi auran sa gashi yanzu har da yaron su.

Ammar najin haka ya dago da kansa.

Mama kwana uku kacal mai martaba ya bani just three days!


Ya fada yana mai nuna yatsun shi uku, matar da zan aura fa ake magana mama ,cikin kwana uku har zan samu matar aure?

wadda ke da tarbiya da natsuwa kamar yanda nike bukata?

Mama ta saki ajiyar zuciya, maganar ka gaskiya ne Ammar, amma kasan koda kwana kin sun cika mai martaba ba zaiyi maka zabin banza ba.

Kayi hakuri kaji ko?

Mikewa yayi, yana mata sallama.

Pls vote belowAhmad p.o.v

Zaune yake a office yana tattare wasu document dinsa, yana shirin zuwa lab

Sanye yake da wani farin lab coat da farin gilashi wanda ya kara wa grey eyes din sa kyau.

Karan ring tone din iPhone din sa yaji kafin ya saka hannun sa a cikin aljihun wandon sa,

Ahmad - hello

Ammar - (kaifa haluk ya akhi)? Ya kake?

Ahmad -(Ana bikhair) ina lafiya.

Ammar- bro ina cikin matsala (ammar ya fada cikin harshan larabci)

Ahmad- subhanallah, me ya faru??

Ammar- mai martaba ya bani just three days na fito masa da matar da zan aura.

Ahmad - what! (Limaza salasa Ayyam)? Meyasa cikin kwana uku? Da gaggawa haka?

Ammar -(laa aarif wallah) ban sani ba wlh.

Ahmad - do you talk to some one about it?

Ammar- eh nayi magana da mama, buh she supported him, I don't know what to do right now.

Am freaking out right now, bro kasan dream dina i want to marry the girl i love and the girl that love me with all her heart, the girl that have good character.

Damn man! My dream will never come true!

Ahmad -kayi hakuri ba matsala inshaAllah, shawarar da zan baka shine

Kaje Egypt kuyi maganan da mami, I know she will do something about it, coz mai martaba yana respecting decision dinta don't worry much about it ok?

Ammar - I can't go to Egypt in these days bro, because of my work, i will be living to u.s tomorrow.

Ahmad - OK but you need to call her.

Ammar -eh zan kira ta yanxu idan mun gama magana, my regard to my little boy tell him uncle love him so much, I miss his banna and my sister in law khadija I miss her delicious food.

Ahmad -lol. Ok I will tell them bye am having class now.

Ammar -ok bye

Suna gama magana Ahmad ya shiga lab.

************************************

Samrah

Samrah! Ammi ta kira ni, kizo kiyi breakfast, hand bag dina na dauka sannan na sauka kasa,

Ammi yau fa monday ina da lecture bye, na daga mata hannu.

Ina shiga school na duba aguguna OMG! Am late, sauri nayi na shiga lab.

Ina shiga na tarar har sunyi nisa, har zan zauna naji ance you! Get out of my class!


You are always late.

Cikin raina nace this arrogant jerk again.


Sai da nayi addu'a kafin nace am really sorry Dr. I won't be late next time.


Shiru yayi ya cigaba da abun da yake yi.

Bana so na fita yau saboda zaiyi mana test.

Ya Allah help me out.


Pls vote belowAmmar p.o.v

Yana gama waya da Ahmad ya zauna ,meyasa mai martaba zaiyi masa haka, just three days for God sake! 

Ya fada yana mai ture wani glass cup dake side din sa.

Wayar sa ya dauko yayi dialling namban mami, yana ringing sau biyu ta dauka.


Ammar -Assalamu Alaikum mami

Mami -wa'alaikum salam habibi.

Ammar yayi shiru,  sai shakshekan kukan shi mami taji,

Mami - limaza dafali yabky? Meyasa baby na yake kuka?


Ammar ya goge hawayan shi sannan yayi wa mami bayanin matsalar sa.

Mami najin haka tace kar ya damu, yanxu zata kira mai martaba zasu yi magana.

Ammar na aje wayan ya lashe lips din sa na kasa, ya shafa gashin kansa,

Ya Allah! Ya fada

Pls safe me out.


************************************


samrah

Ya samrah! 

Ammi tace kiyi sauri, safwan ya fada, ina saka lagins dina, na yi parking din gashi na in a messy bun sannan na dauka purse dina na sauka kasa.

Ina sauka Ammi tayi min kallon tsaf sannan tace

Samrah wannan shigar kuma da ita zaki fita?

Shiru nayi mata ina kallon wani waje

Nasan wannan bashi ne karo na farko ba da Ammi take yi min nasiha akan shigar da nike yi.

Ammi sorry na fada ina pouting lips dina.

Cikin Sauri nayi ,hugging dinta nace Ammi ba zan kara ba.

Daga kan ta tayi tace naji, kullun dai haka kike fada.

Har mun shiga mota ,na kalla Ammi

Ammi shopping din sallah zamuyi?

Ammi ta girgiza kanta

A'a tsaraba zamuyi gobe zamuje katsina.

What! Na fada Ammi katsina kuma

Why all of a sudden Ammi?


Don't ask me that questions samrah

Ammi ta fada tana kokarin tayar da mota

Ta dube ni haka Abban ko ya fada gobe zamu je Nigeria inshaAllah .


Cairo festival city mall muka nufa

Sayayya sosai muka yi har karfe 5:00 kafin muka dawo gida.

Karfe 8:00 pm bayan na idar da sallah isha'i, Ammi ta kirani samrah kije Abban kuna kiran ki, yana dakin sa.


Ina shiga nayi sallama, Abba ya amsa.

Zama nayi gefen kafet din sa nace Abba gani.

Gyaran murya yayi sannan yace Samrah! Ammin ku ta fada maki gobe zamu je Nigeria?

Daga kaina nayi alamar eh.

Toh Alhamdulilahi, yaushe ne kike gama makaranta ne?

Dago kaina nayi nace Abba cikin shekaran nan ne inshaAllah

Abba yace wane wata kenan?

June Abba,  na fada ina daga kaina

MashaAllah Abba ya fada.

Jeki kwanta gobe morning flight zamu bi. Kin ji ko?

Ina fita daga dakin Abba zan shiga dakina ina tunanin meyasa Abba keyi min wannan tambayoyin.

Auccch! Ammi! Na fada ina sosa kafa na da na fadi.

Ya samrah meye haka ina tafiya kin zo kin fado mun ba kya kallon hanya ne?.

Safwan ya fada yana sosa hannun shi.

Oh God sorry safwan

Daga mun kansa yayi ya shiga dakin shi.

Dakina na koma ina shirya kayana saboda tafiyan gobe.

Pls vote belowSamrah p.o.v

Ya samrah! Ammi tace kiyi sauri,

Safwan pls tell Ammi am coming,

Ina saka jeans dina, nayi parking din gashi na  sannan na dauka akwatina  na sauka kasa.

Ina sauka Ammi tayi min kallon tsaf sannan tace

Samrah wannan shigar kuma fa? Jiya ba sai da na maki magana a kanta ba? Kuma haka zaki airport din?

Misalin karfe 6:00pm jirgin mu ya sauka Nigeria.

Mai martaba ne ya turo driver din sa ya zo ya kai mu fada.

Ina shiga cikin gida wanka,  na shiga

Ina shafa wani lotion sai na ji phone dina na ringing


Duba screen din wayan nayi

Sunan kausar na gani cike da murna na daga wayan

Kausar my bestie na fada ina dariya

Dariya tayi a nata gefen.

Kausar tace na zo gidan ku Samrah naga bakowa lafiya?+

Lafiya lau Kausar tafiya ce ta same mu cikin kwana kin nan wallahi muna Nigeria

Kausar-Nigeria?

Samrah - kwarai kuwa, bamu dade da isowa ba ma.

Kausar -ok muma zamu zo bayan sallah inshaAllah. Ki gaida mun da zarah.

Samrah - ok zata ji bye.

**********************************

Ammar

Mai martaba ayi man hakuri zuwa nx.. Dakata Ammar!

Yau nike so kazo ba ruwana da wani aikin ka! Kana jina ko?

Mai martaba na gama fadar haka ya kashe wayan .


Misalin karfe 6:30pm jirgin Ammar ya iso Nigeria.

Yana shiga fada, side din sa ya nufa yayi wanka yaci Abincin da mama ta sa aka kawo masa

Masallaci ya shiga yayi sallah. Yana nan har a kayi sallar isha'i


Bayan an yi sallah isha'i yana dakin sa kwance rigar bacci ce a jikin sa yana ta tunanin mafita.

Ringing din da wayar sa tayi ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da yake yi.

Yana duba screen din

Mai martaba ya gani a rubuce

Gaban sa ne ya fadi ,bismillah yayi kafin ya daga wayar.

Ammar !mai martaba ya kirashi.

Na'am baba,  ya amsa cike da fargaba.

Da fatan Ka iso lafiya?

Lafiya lau baba .


Kana ina ne? Mai martaba ya cigaba kazo dakina ina son magana dakai.

T.. O. H ba.. Ba Ammar ya fada cikin in'ina.

Tashi yayi ya saka takalman sa ya nufi sashen mai martaba.

Yana shigowa mai martaba ya dube sa da kyau,  tausayin sa yaji ganin yan da Ammar din ya rame sosai cikin yan kwana kin nan.

Mai martaba yayi kyaran murya , Ammar! Ka dawo lafiya?

Lafiya lau baba.

Mai martaba ya ci gaba Am..

ka samu matar da zaka aura din?

Ammar ya kada kai alamar a'a

Mai martaba ya dube sa da kyau yace toh madallah!

Ka shirya nan da kwana biyu zan daura maka aure.


Ba maganar kari ko ragi kwana biyu kacal na zaba. Wannan karon dole kayi min biyayya Ammar!

Zaka iya gayyatar abokanka na kusa.

Ammar ji yayi kamar an sara masa wani karfe akai.

Ji yake yi ina ma ace yau ya mutu da ya huta da wannan tashin hankalin,

Bankwana yayi wa mai martaba kafin ya fita.

Yana shiga daki numban mami ya kira ya saka mata kuka.

Samrah p.o.v
Shirye -shirye naga ana tayi a fada, ko na menene? Oho!
Wata kuyanga na gani cike da kayan fruit salad a hannun ta, tana shirin yankawa.
Matsowa nayi kusa da ita na tambaye ta.
Wannan shirye -shiryan na menene?
Sauke kanta tayi tace.
Ranki shi dade, wannan shirye shirye da kiga anayi duk na auran Yarima ne
Yarima! Na fada sunan ina mai nazarin ko wanene shi.
Kallon ta nayi nace wane yarima kenan?
Tace yarima dane ga mai martaba sarki wanda aka fi sani da crown prince.
Baya zama a wannan kasar sosai dan ko ni sunan sa kadai nake ji amma ban san sa ba a fuska.+
Na dai ji labarin irin kyauwun sa kamar dan larabawa yake.
Kallon kuyangar na kara yi sannan na tambaye ta Ko dan mama ne?
Sun kuyar da kan ta naga ta kara yi sannan tace.
Yarima da ne ga Mami wato uwar gidan mai martaba wadda ita asalin yar kasar masar ce wato Egypt.
Dan kaman nin sa kusan daya ne da mahaifiyar sa wato Mami .

Hannuna na saka na nauka kankana cikin fruit salad din da take yankawa kafin nan na tafi.
Dakin zarah na koma ina karanta wani English novel , ba Dan kwali a kaina.Kai na daure yake in a messy bun .
Zarah ce ta shigo cike da fara'a tana shigowa ta zauna a wani tool dake kusa da side dina.
Amaryar mu! Ta fada tana murmushi. Rufe book din dake hannu na nayi na saki ido ina kallon ta.
Meye haka kuma zarah?
Tana jin na fada haka ta mike tsaye tana murmushi.
Samrah stop pretending, u are not good at it.
Wanda keka yi ma ya isa haka nan.
Mikewa nayi nima ina rike da kugu nace what do u mean zarah?
Ban fa fahimce ki ba Amarya kamar yaya?.
Zama tayi tace haba samrah yanxu kwanan ku har biyu a gidan nan amma baki fada min kice matar da mai martaba zaya Aura wa ya Ammar ba?
What! Aure!
Na fada cike da tsiwa, ban gane me kike fada ba zarah.
Who is the Ammar you are talking about?
Ba zaiyo ba, nasan su Abba suna sona ba zasu min auran dole ba zarah, may be dai wata samrah din ce bani ba inajin baki ji da kyau bane zarah.
Zarah ta kalle ni , idanu na cike da hawaye sun jajir don kuka, mikewa tayi ta dawo kusa da ni ta dafa kafadata tace, ba komai samrah inajin I miss understood the conversation inajin ba ke din bace.
Goge hawaye na nayi nace zarah!
Nasan su Abba ba zasu taba min aure da mutumin da ban sani ba.
Zarah ta dube ni tace kar ki damu samrah idan ma da gasken kece toh baki da wata damuwa saboda ya Ammar mutunin kirki ne, bashi da wata matsala inshaAllah.
Pls vote belowDaurin Aure

Manya manyan sarakunan Arewa da yayan sarakuna da dama na gani.

Cikin shiga ta alfarma tare da manyan mutane wanda sun taka matakai da dama a gwamnati a kofar gidan sarki zaid

Duk sun zo halartar daurin Auran dan babban gida wato the crown prince.


Mai martaba sarki zaid, shi da kansa ya zama waliyin samrah.

Taro yayi taro wanda ba'a taba kamarsa ba a garin katsina wanda tarihi ma yayi nuna shine na farko.

Taro da ya halarci manyan sarakunan kasashe da dama.

Misalin karfe 2:00pm na rana aka daura auran Ammar & samrah

Akan sadaki 500,000.


************************************

Samrah

Ina fitowa wanka daga toilet din dakin mama, ina ta kokarin goge gashin kaina da wani karamin towel, zama nayi kusa da side drawer ina wakar India (hamari adhuri kahani)

Gashin kaina nayi combing wanda ya zuba har gadon bayana wata wakar na shiga yi ta ( Nancy)

Na mike ina rawar Arab na belly dance.

Hips dina na ta twisting sosai kamar yanda Arabs din keyi.+

Muryar zarah naji tana magana.

Prince! Mama tace idan kun gaisa ka fito mai martaba yana jiran ka zaku tafi kilisa.

Ji nayi kamar na nutse cikin kasa don kunya.

Ya salam na furta cikin raina, does that mean tun dazu akwai mutum a dakin nan?

What the..! Na fada cike da tsiwa.

Juyowa nayi cikin sauri na ga mutum tsaye a baya na kyakyawan gaske.

Sanye yake cikin wata farar shadda.

MashaAllah! Na fada a raina

Ya hadu karshe, kai kace balarabe ne

Fuskar shi cike take da annuri.. Sai dai me?

Idan ka kare masa kallo zaka fahimci yana yin sa yana cikin kunci da bacin rai.

Blue eyes din sa na kalla wanda ya so ya jefani cikin wani yanayi. Wata zuciya ce tace min.

Focus samrah!

Kar kyawon sa ya rude ki.

Dan yatsana na sa, ina nuna sa cike da tsiwa nace, malam baka iya sallama bane? Kuma me ma ya kawo ka nan? Wane rashin hankali ne zai saka shigowa dakin mutane ba neman izini?

Dan yatsana ya ture daga fuskar sa yace kee!

What the hell! Ya fada cikin daga murya har ina firgita

Hannun sa ya daga yana shirin zuba man mari zarah tazo ta tsaya.

Kayi hakuri prince don Allah, ta fada tana rike da hannun sa.

Get out zarah!

Ya fada cike da isa, cikin sauri zarah ta fita don tasa halin Ammar akwai fushi.

Ta san da wa take magana, wannan bashi ne karo na farko da wannan manner less girl din take min rashin kunya ba ya kamata tasan ko ni waye.

Yatsan shi ya sa yana nuna kansa yace nine Ammar ,dan babban gida the crown prince.

Mace bata isa ta takani ba wlh. Sai dai ni nayi abun da nike so da ita

How dare you ya fada yana mai zuwa kusa da samrah.

Hannun ta ya jawo tayi dan kara kadan.

How dare you touch me? Ta fada cike da tsiwa.

Yatsanta Ammar ya rike ya matsi iya karfin shi.

Samrah ta saki wata irin kara har sai da tayi hawaye don azaba.

Sakin hannun yayi sannan yayi wata dariyar mugunta yace

Idan kina cin kasa ki kiyayi ta suri.

Samrah na jin haka ta ture shi tace Allah ya isa mugu kawai.

I hate you!


Yana jin haka ya kara matso ta ya janyo ta jikin shi da karfe sannan ya rada mata a kunne.

I hate you too! Gashi kanta ya sunsuna wani kamshi yaji mai dadi har yaso ya fita haiyacin sa.

Kukan ta ne ya dawo da shi daga duniyar da ya shiga.

Jan gashin kanta yayi , kara ta kara saki. Wayyo Ammi !

Murmushi ya dayi sannan yace wannan tsiwar take duk ina ta tafi?

Kadan kika gani yarinya.

Zaki gane kinyi da dan babban gida.

Hop dai kinyi shirin zaman har abada dani? Saboda Auran mu ba saki, ba yaji. Kina jina ko?

Ya fada yan mai shafar hips dita matsowa yayi wanjan Kunne ta ya ce by the way nice dance.


Ture sa nayi da karfi ina kokarin saka hijabi ido na cike da hawaye nace .

How dare you touch me! I hate you, I hate you!.

Kuma ka daina cewa auran mu ba saki don yau din nan zaka sake ni mugu kawai.

Murshin mugunta yayi mata yace good night wify!

Yana fadar haka ya fita fuu kamar iska..


Pls vote below.Samrah p.o.v

Zarah ce ta shigo cikin sauri ta dube ni. Samrah prince bai dai yi maki komai ba ko?

Hawaye ne suka kara fitowa daga idona , ina gogewa nace zarah meye ma baiyi man ba.

Zarah ta dube ni cike da tausayi hannu na ta rike tace kiye hakuri samrah kiyi biyayya, ki rungumi kaddara.

Mikewa nayi ina duban ta, me kike nufi zarah?

Zarah tace samrah ina so ki gane komai ya samu bawa yayi hakuri dashi ya kuma yi tawakali.+

Mintina talatin da suka wuce aka daura maki aure da prince.

Amma har kun fara samun sabani dashi.

Ki tuna fa samrah shima fa auran nan ba a son ranshi bane aka daura. Biyayya kawai yake yi don ya farantawa mai martaba.

Ina ma ace kema kiyi biyayya ki sace zuciyar mijin ki. A hankali saiki ga komai yayi daidai tsakanin ku.

Tab di! Lallai ma zarah! Na fada ina shirin fita nace zarah ni da yayanki zaman lafiya har abada in dai ba sakina yayi ba.

Ba wani zaman aure da zan yi dashi, shima fa ba sona yake yi ba.

Har in zubar da ajina don na sace zuciyar sa?

Tab di! Ai kuwa badai ni samrah ba don ko yayi kadan.

zarah ta dan yi murmushi tace ba komai samrah mu nan dake zaki zo kina bani labarin irin son da kike masa.

Ba zaki gane bane samrah prince yana da kirki amma sai kin zauna dashi zaki gane halayan shi.

Tabe baki na nayi nace shi ya sani dai waya ta na dauko na Kira kausar ina fada mata labarin abun da ya faro, ta tausaya min sosai, daga bisani take fada mun ita ma next month za'ayi nata bikin da Fahad wani cousin din ta.

Muna gama magana da ita Ammi ta shigo tayi min nasiha sosai akan nayi hakuri.

Tashi nayi hugging din ta, ta share min hawaye na.

Abba ne ya shigo ya kara min nasiha yace na shirya gobe zamu koma gida saboda karatuna, ba zan tare ba har sai na gama tukunna.

Cike da murna nayi hugging Abba. Suna ta samun Albarka.

************************************

Ammar

Ammar ne kwance daga shi sai wani short . Ya kwanta fuskar sa na kallon sama.

Wannan bakar rana ce, Ammar ya fada yana mai jin wani bakin ciki a zuciyar sa.

Ji yake yi ina ma ace hakan bata faruba, ina ma ace matsalolin shi zasu tafi daran yau.

Amma ina matsalar sa na nan tare dashi .


Duk da yasan bakin ciki baya dauwama, haka ma farin ciki.. Tuna wa yayi da Allah yace inna ma'al usri yusrah..

Juyawa yayi daga kwancen da yake yana kokarin yin bacci, amma ina baccin ya gagara.

Tashi yayi ya dauko ruwa yasha, yana jin ina ma ace ya manta da duk wata matsalar sa da damuwar da ya shiga.

Yana cikin fushi, rudu da damuwa.

Yana fushi da kansa nakin bin umarnin mahaifinsa da yayi na zama a Nigeria tsawon sati daya.

Ya shiga rudu akan meyasa sai wannan yarinyar? Upon all people

Meyasa sai ita? Why, why ! YA fada yana mai fasa cup din da ke hannun sa.

Tunawa yayi da rashi kunyar da ta masa dazu. Zuciyar shi ta shiga ruwaino masa surar ta tun daga fitowar ta daga toilet har zuwa lokacin da take rawa yanda hips din ta ke juyawa ya tuno.

Yarr.. Tsikar jikin shi ce ta tashi.

Tsaki yayi ya ce why! Meyasa kyawon ta ya zama na banza!

Meyasa ba zata zama macen da yake so ya mallaka ba, meyasa bata zama kamanmiya ba?


Wayarsa ya dauko ya danna layin Ahmad sun sha fira har yana kwantar masa da hankali akan yayi hakuri, yayi tawakali.

Kayan sa ya saka ya dauki key din sport car din shi ya fita ganin garin New York ko ya samu saukin abun da yake ji a zuciyar sa.

Pls vote belowBayan sati daya

samrah p.o.v

Muna fitowa daga test din Genetic na zauna kusa da wani shop.

Kausar na gani ta nufo wajan da nike, ina zaune anan har ta iso wajan da nike ta zauna tana murmushi.

Kallon ta nayi nima ina nawa murmushin nace kausar yau kinga MR. Arrogant ko?

Kausar tayi daria tace kedai bari ae test din sa tayi dadi sosai wlh.

Kallon ta nayi nace Allah yasa haka exams din sa suyi mana dadi.

Kausar na aje bottle din coke dake hannun ta tace, munyi karatu ne ai sosai ma test din nan .


Kallon ta nayi nace, wai ni kam kaus.. Wayar tace tayi ringing ta dube ni tana murmushi fahad ne ya kira ta fada, picking tayi suka sha soyayyar su, daga bisani ta bani wayan muka gaisa da shi.

Ina mika mata wayan na dafe kaina ina tunanin rayuwata, wato ni haka zan kare? Ba wani farin ciki? My dreams has been shattered!

Kausar ta dube ni lafiya? Ta fada tana dafa hannu na kallon ta nayi, wani murmushin takaici nayi mata nace kausar kin san matsala ta, wannan kaddararran auran da aka yi mun be kare ni da komai ba sai takaici.+

Kausar ta matso kusa dani ta zauna, kallona tayi cikin ido kafin tace samrah ki fada mun gaskiya , tunbayan bikin ku prince ya kira ki kuwa?

Tsaki nayi, mstww that wicked jeck! I hate him kausar.

Bana bukatar jin muryar sa, kuda zamu zauna a haka ne har abada ban damu ba.

Matsala ta igiyar auran sa da ke kaina, shi ne kawai damuwata,

Ina ma ace ya sake ni!

Sun kuyar da kaina nayi ina hawaye.

Kausar ce ta bani hakuri har nayi shiru. Tace kar ki sa kan ki damuwa da yawa kinga mun kusa fara final exams kiyi hakuri kinji, ki samu ki fito da grade mai kyau.

Murmushi na mata nace hakane kawata thanks for being here with me.


Hannun ta na ruko nace tashi mutafi gida an kusa shan ruwa ga azumi ina yi.

Murmushi tayi tace wlh samrah kina burge ni saboda azumin nafila baya wuce ki. Murmushi na mata nace kema fa zaki iya yi ae akwai lada fa sosai. Toh tace min kafin muka fita daga gate din school.

************************************

Ammar

Kwance yake yana wasa da fou'ad (babyn Ahmad) khadija ce tashi ita da Ahmad suna ta kallon sa.

Ahmad na zama saman kujera fou'ad ya fara kuka.

Ammar ya bata rai cikin wasa yace kaji yaro daga ganin baban ka har ka fara kuka kaje wajan sa ko?

Khadija na jin haka ta fara dariya, ta mika hannu ta dauka fou'ad tace fou'ad kana ma uncle kiwoya ko?

Ammar yace kyale shi ba zan kara saya masa sweet ba.

Ahmad na jin haka yace ku bani baby na, khadija ta dauko ma Ahmad feeder din fou'ad ana bashi yayi shiru.

Khadija na zama ta dube Ammar tace prince wai nikam yaushe zaka kawo mana Amaryar mu ne mu ganta? Ko sai ta haihu zamu je suna?

Tsaki ya danyi, yace wlh ko khadija ni fa har na manta da ina da wani aure ma .


Idonta ta zaro tana kallon shi, kafin nan ta maida dubanta ga Ahmad tace lafiyar ka kuwa prince?

Ya za'a daura maka aure ka manta da yar mutane? Kana ganin hakan ka kyauta kenan?

Nasiha suka shiga yi masa ita da Ahmad .

Sun bashi shawara akan yaje ya ganta tunda yana cairo ko ya kira number din ta ya rinka jin halin da take.

Tashi yayi tsaye, hannun sa na cikin aljihun sa yace nifa ko number dinta bani dashi.

Khadija da Ahmad suka tsura masa ido cike da mamaki.

Ammar kana tsoron Allah kuwa?

Kasan aure kuwa? Ahmad ya cigaba akwai hakkin ta a kanka haka itama akwai hakkin ka a kanta.

Ina baka shawara da ka nemi number dinta ka kirata ko ka je gidan su ka ganta kafin ka bar cairo.

Naji ma mai martaba yace medicine take yi ko? Ammar ya daga kafada oho! Ni ban san ni ba.

Zan kira zarah ta bani namban ta, amma ba zan iya zuwa gidan su ba gaskiya!

***********************************


Samrah

kwance nike saman gado da rigar bacci a jikina kai na ba dan kwali, gashin kaina duk ya zubo a baya na

Gaba na laptop dina ce ina wani Assignment.

Video call naga ya shigo ina dubawa naga bakuwar namba ce.

Daga wa nayi

Ya salam! Na furta gabana ne ya fadi , ganin fuskar shi wadda ba zan taba mantawa ba har abada.

The wicked jeck!


Hello.. ya fada fuskar nan tashi a daure tam ba alamar fara'a

Baki iya gaisuwa bane?

Murguda masa baki na nayi cike da tsiwa nace eh din!

Idan ka isa kuma ka zo nan kayi abun da zaka yi.

Ina fadar haka na masa kwalo, fuskar nan tashi ya hade ba alamar dariya, hakan dayayi bai hana shi yin kyau ba lips din sa na kalla,

Am I that handsome? Ya fada yana smiling ganin irin kallon da nake masa. Kunya ce ta kama ni kashe call din nayi na kwanta ina nadamar yin hakan da nayi.

Wani bangare na zuciya ta kuwa bai gaji da kallon kyakyawon fuskar sa ba.

Ina ma ace mu din masoya ne? Na fada ina murmushi da kuwa na dace miji mai aji na shiga tsara.

Meyasa ba zai zamo min my dream man, ina ma ace ya zama my prince charming!

Ina fadar haka nayi murmshi .

What is wrong with me? I can't fall for that arrogant man.

Tashi nayi na shiga toilet nayi alwala nayi sallah dare. Na ruki Allah ya zaba mun abunda yafi zama Alheri.

Ina idar wa na kwanta.

Pls vote & commentBayan wata daya

Samrah p.o.v

Ina dawowa daga school bayan mun gama exams.

Motocin mai martaba na gani a kofan gidan mu,  gabana ne ya shiga fadowa.

Ina shiga palor naga Abba da mai martaba, zuwa nayi gefen su na tsuguna na gaisar da mai martaba ya amsa cike da fara'a.

Ya taya ni murnar kammala karatuna da nayi.+

Gyara zama na nayi nace Abba akwai wani graduation party da za'a hada mana da anjima ina so naje .

Ko zan iya zuwa Abba?

Gyara muryar sa yayi ya ce samrah ai ga mijin ki nan shi ya kamata ki tambaya don hakkin sa ne ya barki ko ya hana ki.

Saga kaina nayi na kalle sa ya kara kyau sosai.

Tashi nayi,  mai martaba naga ya masa magana da ya biyo ni.

Muna tafiya daga palor na shiga canja salon tafiya ta.. Buri na ya dawo tafin hannuna,  sai ya gane dawa yake zancen!

Mace yar boko dani, namiji bai isa ya juyani ba kamar yadda yake tunani.

Inajin yanda idanon sa ke bina da kallo har muka isa daki na.

Muna isa ya rufe kofan.

Kallon sa nayi cike da tsoro nace

Meye haka?

Murmushi naga yayi wanda ya kara masa kyau yace.

Me kuwa nayi?

Ina needing privacy saboda ina tare da matata, ya fada yana daga gira.

Tabe bakina nayi sannan na dube sa,  wannan akwatin fa?

Daga gira yayi yace me kike tunani umm?

Matsowa yayi kuwa da ita ya matse ta jikin shi sosai yace kin san dai na fi karfin nayi sharing wannan karamin dakin dake ko?

Ammar ne fa!  Dan babban gida.

Ajina ya wuce nan kin gane ko?

Ki ma cire wannan bad thought din daga ranki.

Matse hannun ta yayi , sannan yace kina jina ko?

Ture sa ta yi tace Allah ya isa.

Murmushin mugunta ya mata sannan ya ce. Ki bude akwatin can akwai gifts din da mai martaba da mami suka ce a baki.

Akwai wani kaya a ciki ki fito min da su, sai ki dauki na ki.

Kallon sa nayi na tabe baki nace ni fa bana bukatar komai naka, so ka tattara su ka tafi dasu bana so, kuma bazan saka ba.

Tashi nayi na dauka sakon da mai martaba ya bani da na mami na bar masa nasa anan.

Toilet dina naga ya shiga, yana fitowa na zuba ma six pack din sa ido, gyaran murya yayi kafin yace do you like what you see?

Cike da kunya na kauda kaina nace, meyasa baka daura towel ba, daga kafadon sa yayi yace ba towel dina a toilet din.. what do you expect me to do humm?


But my towel is inside na fada cikin sauri. Kallo na yayi yace like seriously, u expect me to wear dat pink towel hmmn?

Matsowa yayi kusa da inda nike yace karki damu, bana sharing ok.

Matsawa nayi from his side nace kai dai ka sani.

Waya ta ce tayi kara,  kausar ce ta kirani tana tuna mun time din partyn ya kusa.

Ce mata nayi na fasa zuwa.

Ammar na jin haka ya karbe wayan yace tana zuwa, kar ki damu tare zamu zo da ita ok?

Kausar na jin haka tace waye ke magana?

Ammar yace mijinta ne.

Yana fadar haka ji yayi kalmar ta masa wani iri a baki.

Kausar na jin haka ta gaisa da shi kafin ta kashe wayan.

Saka kayan sa yayi wanda na lura kalan wanda ya saya mun ne.

Wato nufin sa muyi anko kenan?

Lallai yana da aiki kuwa na fada a raina.

Tashi nayi ina neman saka wasu kaya dake wall drop dina, sai dai naji an riko ni ta baya.

Ga kayan da nike so ki saka a nan ya fada.

Tsaki na masa cike da tsiwa nace wai me kake nufi ne eyye! Kana nufin har ka isa ka saka ni yin abun da banyi niya ba?

Toh  baka isa ba kayi kadan wlh.

Matse ni yayi sosai har muna shakar nufashin juna.

Matse mun baki yayi sosai sannan ya shiga kissing dina da karfi.

Sai da ya gaji kafin ya bari, 

Rike lips dina nayi ina hawaye nace mugu kawai ban yafe ba.

Murmushin mugunta yayi yace ni mace bata isa tayi min rashin kunya ba kin gane?

Ba'a haifi macen da zata gaya man magana ba kina jina ko?

Da Dan babban gida kike magana kin gane!

So mind your language woman!

Ya fada cikin babbar murya.

Hararar sa nayi ina shirin kwace kaina.

Rike ni yayi gam.

Yace ko ki saka rigar nan ko kuma na saka maki su da kaina.

Kallon sa nayi cikin mamaki kafin na nace idan ka isa ka saka mun din.

Banyi tunanin rashin kunyar sa takai nan ba sai da na ga yasaka hannun sa yana zage zip din rigata.

Yana niyar ya cire kayan jikina.

Hannun sa na rike gam.

Nace zan saka da kaina.

Toilet na shiga na saka kayan.

Ina fitowa ya zuba min ido yana kallo na.

Wajan mirror na nufa naga yadda rigar tayi bala'in yi min kyau.

Kaina na shiga kyarawa ,kallon gashi na ya shiga yi,  koda bai yi comment ba nasan gashin ya burge shi sosai, ganin irin kallon da yake min.

Kayan kwaliyata na dauko nayi, sannan na feshe jikina duka da wani Arabian turare mai kamshi.

Jakata na dauko kafin muka sauka kasa.

Muna sauka Ammi tace har an shirya ? Ammar naga ya duka kai yana gaishe ta .


Cikin zuciyata nace kalli mutum kamar mutunin kwarai.

Safwan na shigowa ya rike Ammar yana bashi labarin son dokin shi.

Ammi tayi dariya tace Ammar rabu dashi kaji, indai safwan ne baya gajiya da labarin doki.

Murmushi yayi yace ma safwan ya shirya gobe zai kaisa wajan hawan duki na larabawa.

Muna fita muka ga har mai martaba ya tafi,  wayar Ammar ya kira yace masa shi ya koma gida.

Motarsa muka hau wata latest Ferrari baka mai kyaun gaske.

Hall din muka nufa wanda ya cika da mutane sosai,  waya ta nasa na kira kausar.

Kausar na zuwa ta gaida Ammar.

Yana amsawa ya fita amsa waya .

tace kawata kinga yanda kukayi kyau.

Kice yau dai ku zakuyi winning best couples na medical department.

Hannuna na sa na dan buge ta nace ke kika sani.

Muna fita hannun sa rike da nawa. Kallo duk ya dawo kanmu.

Hall din muka shiga.

Kai kace wasu masoya ne.

Muna shiga aka fara kirin sunayan graduate students .

Ana gama kirin sunayan mu.

Wani lecturer din mu yayi speech.

Ina cikin tunani nane naji an tabo ni kamar a mafarki naji yace tunanin me kike yi?

Hannun sa na ture, gyaran murya yayi sannan yace baki ji ana kirin sunan ki ba?

Sunana naji an kara kira kafin na tashi na hau stage.

Speech nayi da larabci, kafin na koma English.

Ina gamawa aka fara clapping.

Komawa nayi na zauna, ina zama yace nice speech(har cikin ransa ya ji dadin yanda tayi speech dinta), kauda kaina nayi nace thanks.

Bayan an gama aka kira sunana,

V. C din mu da kansa ya bani award na most calm.

Award da dama na karba har abun ya bani mamaki.

Kausar ma ta karba nata.

Ana gama bayar da awards aka fara casu.

Rawa sosai nayi saboda wannan babbar rana ce a wajena.

Ammar na ganina ya bata rai. Ko bai fada ba ranshi ya bace sosai.

Hannu na ya kama muka shiga mota.

Kwacewa nayi nace

Meye haka? Zaka kamani kamar wata baiwar ka?

Kallo na yayi idon nasa yayi ja sosai, har sai da naji tsoro gannin yanda ransa ya bace .


Kina matar aure zaki je kina rawa a gaban maza? Ya fada cikin daga murya. Kallon sa nayi nace ina ruwan ka? Kuma da kake maganar ni matar aure ce haka ake aure? Kauda kai na nayi nace, nifa bana so ana takura ni

Auran da ba na soyyayya ba.

Ba abunda yace man sai dai naga mun iso gida. Yana sauke ni ko shiga baiyi ba ya ja mota ya bar wajan.

Binsa bayi da kallo har motar ta bace.

The picture up dere is samrah and Ammar outfit.1Bayan kwana biyu

Ina gama breakfast na kai dining table,  yau  ina cikin farin ciki sosai saboda yau ne zarah zata zo.

daki na koma nayi wanka, wata English gown na saka tana da hannu karami, blue color ce.

Gashina na gyara ,sakin gashin nayi har gadon baya na.

Make up kit dina na dauko na yi simple make up .


Ina sauka naga prince har ya sauna a dining table yayi wanka shima cikin riga da wando na English wears.


Zama yayi yana latsa wayar sa, da alama ni yake jira na sauko, don ko abincin be ci ba.

Ina zuwa zama nayi opposite kujeran shi, murmushi na masa kafin na gaishe shi.

Ya amsa , serving abincin na mana na tura masa nasa.

Ina cin abincin amma ina kallon sa da gefen ido, yan da naga yana kallo na ko abincin be taba ba.

Gyaran murya nayi nace abincin ya maka yaji ne?

Kada kansa yayi alamar a'a.+

Sai kuma naga ya fara cin abincin, toasted bread ne da papper soup din naman kaza, sai kuma tea.

Muna gama breakfast ya fita, ni kuma na koma palor ina jiran zuwan zarah.

Ina kallon wani hausa film mai suna Abdallah, sai naji wayata tayi ringing

Ina dagawa naji muryar sa, zarah tace min ta kiraki wayar ki bata shiga, zata shigo wajan karfe biyar na yamma

.

Toh nace masa, zan kashe wayar kenan yace Samrah!

Yanda ya fada sunan naji sunan ya min dadi, Na'am,

Na fada.


Ina so ki gyara min dakina ,a wanke toilet din idan ba zaki damu ba.

Ok, na fada ya kashe wayar.

Tashi nayi na haura saman dakin shi na shiga, gyara dakin nayi na saka turaran wuta.

Toilet din na shiga na wanke, kayan dattin shi duka na kai laundry room.

Rufe dakin nayi na kuma kitchen nayi abincin rana.

Misalin karfe biyar sai ga zarah ta shigo da karamin akwatin ta.

Hugging din ta nayi cike da murna muka shiga palor ta ajiye kayan ta.

Har zan shiga da ita daki naji ta kira ni.

Samrah!  Ina tare da su khadija ne, sallamar su ce ta katse ta.

Zuwa nayi na tare ta.

Mace ce kyakyawa da wani cute baby a hannun ta.


Gabana ne ya fadi ganin yanda yaron yake kama da Ammar.

Suna zama na shiga kitchen na kawo masu juice da snacks.

Matar wadda naji zarah ta kira ta da khadija naji ta cemin.

Amaryar mu cike da zolaya tace gashi mu mun zo tunda Ango na boye mana ke. Murmushi na mata na dauka babyn ina kara kallon sa da kyau.

Oh my world, why am i feeling jealous.

Kodai Ammar ya na da wata matar ne?

It can't happen.


Ajiye babyn nayi na dube maman sa nace ya sunan shi?

Murmushi tayi tace sunan sa fou'ad.

Ni ma murmushin na mata na jawo hannun zarah muka shiga kitchen.

Muna shiga nace zarah pls wacece ban gane ta ba?

Ammar na da wata matar ne?

Naga babyn ta na kama da Ammar .


Zarah na jin haka ta hau yimin dariya, please ki ansa ni mana, shiro tayi ta cigaba da dariya

Palor na koma, ina shiga naga Ammar zaune suna magana da khadija hannun sa rike da fou'ad.

Hararar sa na shiga yi, shi kuma yana nema ya rike dariyar da ke bakin sa.

Da Alama Zarah ta fada masa.

Ina zama naji salamar mutum.

I know this voice na fada a raina.

STORY CONTINUES BELOW

Yana shigowa naga, Mr. Arrogant ne tashi nayi tsaye ina zazzare ido.

Miss Khalid! Naji ya kira ni

You, ya fada yana kallo na.  Kece matar brother dina?

Kallon Ammar nayi cikin sauri kafin na kalle Mr. Arrogant.

So they are brothers na fada a raina.

Yes sir na fada. Ammar ya dube Ahmad yace dama kasan ta ne?

Zama yayi yana murmushi yes i know her she's my student.


Not only student but my most brilliant student you are lucky Ammar.


Fou'ad na kuka naji khadija tace go to your dad duk ka ishe ni da kuka.


Oh dama matar Mr. Arrogant ce kenan?

Murmushi nayi, naga Ammar na kallo na.

Da sauri na bar wajan cike da kunya.

Zama nayi daki saboda kunya na kasa zama palor, zarah ce ta shigo tana mun tsiya.

Ashe dai ana so ake kaiwa kasuwa tunda har kishin yayan nawa ake yi, cewar zarah, tashi nayi na koma kitchen kedai kika sani na fada ina hararar ta.

Ina kitchen ina wanke wanke naji ringing din wayata.

Ina dagawa naji muryar Ammi, Ammi na ,I miss you soo much.


Na fada cike da shagwaba.

I miss you too my baby girl,  ina Dan babban gida ne?

Kwana biyu bamu gaisa ba.

Yana palor Ammi bara na kaimasa,  no barshi kawai yanxu zamu fita da Abban ku ne.


Ok Ammi my regards to safwan and Abba.

Muna gama magana na kashe wayan ina tunanin gida.

I really miss home


Ina zaune a kitchen bayan na gama wanke plates da fou'ad a hannu na ina wasa dashi, sai dai na juyo naga mutum na kallo na ganin irin kallon da ya bini dashi yasa na tashi tsaye .


Matsowa prince yayi yazo dab da inda nike yana kallon brown  eyes dina yace.

Eyye Ashe dai  ta iya raino 

Murmushi nayi masa sometimes indan na kalle sa sai naga kamar ba arrogant prince din da na sani ba, ya karba yaron .


Har yazo zai fita yace kizo kuyi sallama da khadija yanzo zasu tafi.

Ina zuwa na rike hannun khadija nace please mana ku kwana mana anan.

Idon ta naga ta zaro tace rufa man asiri ga Ahmad can ki tambaye shi, idan ya yarda toh

Zuwa nayi palor na iske Ahmad da Prince a tsaye da alama suna jeran fitowar mu ne.

Ban san lokacin da na je kusa da prince ba, hannun sa na rike gam nace

Please ka ruka min Ya Ahmad mana ya bar su khadija su kwana.

Jawo ni yayi zuwa kitchen ya matse ni jikin bango kissing dina ya shiga yi, har ban san lokacin da na maida masa martani ba.3

Daga bisani ya kyale ni, goshin sa ya dura bisa nawa yana nunfashi sama sama.

Meyasa kike so su kwana?

Ya tambaya yana kallon cikin ido na.

Saboda...

Muryar zarah muka ji tana kiran sunan mu.

Kafin ta shigo nayi saurin ture shi daga jikina na fito palor.

Ahmad ya dube ni ya yi min sallama har mun fito raka su.

Naji Ammar na magana da Ahmad akan su kwana a gidan mu.

Ahmad yayi murmushi ayi mana hakuri Amarya next time sai mu kwana yau akwai meeting din da zan je.

Murmushi na masa nace ok ba komai sai next time din sir.

Juyowa yayi yace please call me Ahmad.

Daga kaina nayi alamar eh.

Suka shiga mota .


Suna tafiya Ammar ya tafi masallaci gida ya rage daga ni sai zarah.

Daki muka koma muka sha fira.

Bayan sati biyu

Samrah

Alhamdulilah cikin satika biyu da suka wuce mun fara shiri da prince sosai har zarah na mana tsiya.

Naji dadi kwarai da prince ya barni na tafi bikin kausar kafin shima ya tafi nasa aikin a Abu dhabi.

A maiduguri aka daura mata aure,tare damu aka kawo amarya kaduna

Muka barta gidan angon ta fahad.

Bayan mun dawo daga bikin kausar, zarah ta tafi gida katsina, gida ya rage daga ni sai ni.

Bayan sati daya prince ya kira ni maganan aiki na.

Zan fara zuwa nan da kwana daya.

Tunda na fara aiki bani da hutu, yau ma ina ta yin kokari naga na dawo gida saboda, yau ne prince zai dawo.

Bayan na dawo wanka na shiga,  ina fitowa nayi kwaliya ta na saka riga da wando.

Kitchen na shiga na dafa pasta da miyar naman shanu, ko ci banyi ba na zauna ina jiran prince.

Har mamakin kaina nike yanda na kosa ya dawo, wata zuciya tana fada man na fara son shine amma ina karyata hakan ne saboda ganin shi be damu dani ba kamar yanda na damu dashi.

Wayata naji tayi ringing, ina dauka naji ana nemana emergency an kawo wani patient ,yayi hatsarin mota.

Cikin sauri na canja kayan jikina na nufi hospital.

Ina zuwa na shiga office na dauka abun da nike bukata na shiga theater room ,Dr Hammad na gani a bakin kofa yana jira na mufara aikin ,man dai ya shiga yimin  bayanin irin critical condition din da patient din yake ciki da sauri na shiga ina mai son ceto ran wannan bawan Allah..

Fuskar wanda na gani a kwance yasa ni ganin wani duhu daga nan ban san wane hali na shiga ba.

Pls Vote belowSamrah p.o.v

Misalin karfe 2:00pm muka isa garin katsina.

Muna isa wasu motoci daga fada suka zo tarban mu.

Muna isa cikin fada ni dashi kowa yayi hanyar sa.

Side din sa ya nufa ni kuma na nufi side din mama,  ina shiga dakin ta ta tarbe ni cike da murna, hugging dinta nayi kafin nan na gaisar da ita.+

Kunyangin da ke gefenta taba umarni su kai ni side din zarah don ita bata nan tana school.

Ina shiga naga dakin a gyare, abinci kala-kala na gani saman kafet.


Toilet na shiga na watsa ruwa ina fitowa naga ga akwatina baya nan.

Jakadiya na sa aka kira min

Tana shigowa na zauna saman kujera ina duban ta.

Tsugunnawa tayi gefe na tace ranki shi dade akwai matsala ne?

Kallon ta nayi nace ba matsala sai dai akwati na ne ban gani ba.

A ina kuka ajiye min?

Ranki shi dade, ai a can side din Yarima aka umarce mu da mukai, jakadiya ta fada tana sunkuyar da kanta.

What! Maza-maza aje a dauko man shi! Na fada ina daga murya.

Shiru tayi min.

Kallon ta nayi nace ko baki jini bane?

Sunkuyar da kanta naga tayi, tace ayi hakuri ranki shi dade.

Amma mu ta nuna kanta, bama shiga side din Yarima Ammar.

Babu wanda yake shiga daga mama sai zarah sai Ahmad da khadija idan sun zo Amma ni da sauran kuyangin gidan nan iyakar mu kofar side din bama shiga.

Ya akayi toh kuka kai kayan cikin gidan? Na tambaye ta cike da tsiwa har tana firgita.

Da sauri naji tace, ranki shi dade ai store muke kaiwa .

Akwai lifter dake shigar da su ciki.

Get out! Na fada ina huci.

Rai na yayi mugun baci ko abinci na kasa ci.

Kiyi hakuri ranki shi dade .. naji ta fada.

Ina ne dakin nasa?

Na tambaye ta, side din sa na opposite side da na mai martaba.

Akwai mutane?

Kada kanta tayi alamar a'a.

Tashi nayi daga ni sai towel cike da sauri na nufi side din nasa.

Ina shiga kamshin sa ya duki hanci na.

Dube -dube na shaga yi ina neman inda zanga akwatina.

Wata kofa na gani bude ,ina shiga naga wani daki .


Komai na dakin black and white ne.

Wani haddadan gado na gani, royal bed ne an shinfida masa zanin gado me farar fulawa da baki.

Kallon dakin na shiga yi ina mamakin irin dukiyar da aka kashe a dakin,

Girman sa kuwa zai kai girman daki na sau biyar.

Motsin ruwa naji a toilet, hakan ya bani daman duba ko wane lungu da sako na dakin amma ban ga akwati na ba.

Zama nayi kan tool ina jiran sa ya fito daga wankan.

Sai da najira tsawan minti talatin kafin nan ya fito.

Ina ganin fitowar sa,  hannun sa rike yake da wani karamin towel yana goge kansa dashi.

Kauda kai na nayi daga kallon sa.

Nace ina akwatina ?

Yana jin haka ya juyo cikin sauri ya ganni tsayi

Kee! Meya kawo ki nan?

Kina da hankali kuwa?

Ba'a fada maki ba'a shigowa side dina ba?.

Dakata malam na fada ina daga hannu na.

Bani da lokacin amsa maka wadanan tambayoyin naka,  akwatina nake nema kuma jakadiya tace side dinka aka kawo su.

Tsaki yayi yace woman get out!

Kar ki dame ni. As you can see ba wani akwati a dakin nan.

Zama nayi nace ni ba inda zani har sai ya nemo man akwati na,  don ni bani da kayan sawa.

Fita yayi ya bar dakin yana dawowa ya dube ni.

STORY CONTINUES BELOW

Na tambayi security sunce yana store kuma ba wuta. Sai ki jira sai gobe don baza ki samu akwatin ki yanxu ba.

Get out! Ina so nayi bacci.

Tashi nayi na tsaya gaban sa rike da kugu, kallo na naga yana yi

Hakan ya bani damar hararar sa ina shirin yin kuka.

Matsowa yayi kusa dani da alama na bashi tausayi. rike hannuna yayi yace ki saka na zarah mana.

Kallon sa nayi ina hawaye nace kayan ta duka suna store ita ma.

Zama yayi Yace yanxu ya kenan ..?

Wayar sa ce tayi kara mai martaba ya kira shi yana so ya ganmu.

Yana kashe wayan ya dube ni mai martaba na kiran mu.

Ido na na zare ina kallon sa nace yanxu? Daga kansa yayi alamar eh.

Fashe wa nayi da kuka nace ni ban san yanda zanyi ba fa.

Wayar sa ya dauka ya kira mama yace ta fada wa mai martaba ya kira number na ance nayi bacci.

Tashi yayi ya dauko man wata rigar baccin sa. Karba nayi zan fita ya kira ni da sauri.

Kee!  na juyo ina kallon sa, ni sunana ba kee ba ka gane ko?

Tsaki yayi yace what ever! Koma dai ya sunan yake.


Kar ki fita haka!

Akwai security,  kallon sa nayi nace sai me?

Daga hannun sa yayi yana shirin mari na, komai ya tuna sai ya bari. Are you questioning my order?


How dare you say that to me!


Matsowa yayi kusa dani yana shafar jikina yace ,wannan jikin nawa ne ni daya, ko kin manta ne  bana sharing so don haka sai ki rufe shi.

Murmushin takaici yayi yace koda  dai  nasan  kedin baki da kamun kai. Shiyasa har zaki iya fita a haka kina matar aure.

Kinsan darajar aure kuwa?

Kar kiga kamar ina kishi ne  no  bakishi bane

Darajar aure na dakikayi

Shiyasa zaki rufe jikin ki don ni bana sharing  ok!


Ture hannun sa nayi  ina mai jin zafin abun da ya fada a raina  "ko da yake baki da kamun kai " maganar  ta  bata mun  rai sosai


Matsawa nayi nesa dashi nace baka isa ka bani wata  order naka ba nabi kayi kadan

Matsowa yayi ya matse mun baki  yace nidai na fada maki karki fita haka idan kin fita kuma zaki san sauran ko kin manta ne?


Dan babban gida ne fa!


Bana tolerating raini ko kadan.

Tsaki na yi na shiga toilet din sa na saka kayan wata jallabiya ce ta maza ta dan yi mun yawa saboda yafi ni tsawo.

Ina fitowa ya bini  da kallo yana murmushi

Nice pj ya fada yana daga gira, kallon sa nayi na tabe baki ,what! Kar ki kara ya fada yana kara matsowa

What have i done?

Oh baki ma sani bako?

Bana ce maki  bana son rashin  kunya  ba?

Matse bakin yayi yace bakin nan baya ya ji ko?  Sai rashin kunya da ya iya.


Cikin sauri na kwace kaina nace mugu kawai!

ina  folding  towel dina .

fita nayi na barsa yana shirin fita zuwa side din mai martaba.


Ammar P. O. V


Yana isa dakin mai martaba ,bayan sun gama gaisawa .


Zama Ammar yayi irin zaman yayan sarauta. Mai marataba na a shingide yace Ammar!

Abun da nike so da kai, shine ka rike Amanar da aka baka na auran yarinyar nan, kasan aure ba a wasa dashi kana jina ko?

Daga kansa yayi yace inshaAllah zanyi kokarin rike Amanar da kuka bani.

Murmushi mai martaba yayi yace to madallah! Allah yayi maku Albarka.

Gobe da safe sai ku shirya tafiya Abujan ko? Tun da can ne gidan ka yake.

Toh mai martaba. Har ya tashi zai fita mai martaba ya kira shi Ammar!

Dawowa yayi ya zauna kasa.

Yana zama mai martaba yace yauwa!  Maganar motar da na bata.

Kasa wani yaje ya dauko ta a kaimata ita Abuja.

Kuma nayi magana da mahaifin ta akan aikin ta, tunda ta gama karatun ta na medicine zata fara aiki a asibintin mu na Royal hospital.

Ammar yace to ba damuwa zanyi wa  Ahmad magana tunda shine ke kula da asibitin sai tafara.

To h toh madallah sai ka kirashi ko?

Mai martaba ya fada.

Suna bankwana ya koma dakin shi ya kwanta.

Gari na waye wa suka yi bankwana da su mama da mai martaba.

Misalin karfe 8:00am suka hau hanyan abuja.

Kallonta yayi fuskar ta na kallon window ear piece a kunnan ta, tayi shiru.


Wayar sa ya dauko ya kira nambar waziri ya bashi umarni da yasa wani ya taho da motar samrah zuwa abj Suna gama magana ya kashen wayar ya kalle ta.

Akwai abunda zaki yi ne? Mu tsaya travelers mosque?

Shiru tayi  alamar bata ji ba, hannu sa ya cire ear piece din da ke kunnan ta.


Maimaita mata tambayar ya kara yi.

Kanta ta kada alamar eh saboda fitsari take ji sosai kuma ga yunwa tana ji.

Suna isa ya nuna mata bangaran mata shi kuma ya nufi masallaci yayi sallah, suna gama sallah suka hau hanya kunya sam ta hana ta fada masa tana jin yunwa don ko break fast bata yi ba.

Suna hawa hanya, ya dan saci kallon ta yaga har ma ta fara bacci ,murmushi yayi ya dan gyara mata kanta don ta ji dadin baccin.

Kallon kyakyawan fuskarta  ya kara yi yaga tana baccin ta hankali kwance kamar wadda bata da damuwa,

Kare mata kallo yayi na sakan guda yaga irin kyauwon ta.

Samrah kyakyawa ce sosai koda baya son ta ya sani ita din kyakyawace.

Surar jikin ta ya kalla irin wanda yake fatan ya mallakane.

Abu daya ne ya raggu a jikinta, shine tarbiyarta.

Ya fada yana yamutsa fuska.

Daidai nan ya isa gate din gidan sa dake maitama.

Pls vote below

Samrah p.o.v
Ina cikin bacci naji ana kiran sunana. Firgigit nayi na farka.

Dariya yayi ya kalle ni kee nine. Matsoracciya kawai. Ki fito mun isa, yana fadar haka ya fita daga motar
Bin shi nayi da ido ina murmushi,
I love when i make him laugh.
Gidan babba ne sosai yana da garden da kuma parking garage.
MashaAllah yayi kyau sosai, koda ban fada masa ba yasan gidan yayi min yanda yaga ina kallon ko ina.
Muna shiga cikin gidan wow kawai na iya fada don komai na parlon ya min, Ammar has a good test na fada cikin raina.
Matsowa yayi kusa dani yace yadai! Sai a nan ne na dawo daga duniyar tunanin da na shiga.
Ki duba duk room din da ya maki ki shiga naki ne.
But not my room! Ya fada yana daga gira.

Kallon sa nayi kafin na fara duba dakunan gidan gaba daya.+
Ina hawa stairs naga wani daki awesome na fada komai na dakin milk ne, da wani hadaddan gado royal bed.

Hawa gadon nayi nace wow am in love with this room already.

Wanka na shiga nayi sallah, riga da three quarter na saka gashin kaina na gyara ya zubo zuwa bayana,
Zama nayi ina kallon dakin, ciki na naji yayi wani kara saboda yunwa .

Fitowa nayi daga dakina ina neman kitchen.
Gam! Naji na buge da wani hard abu, ina daga kaina naga prince cikin kananan kaya yayi kyau sosai.
Where do you think your going?
Bakya gani ne?
Am, ina so ne naje kitchen.
Me zakiyi a kitchen din?
Shiru na masa.
Ko bakya jina ne! Ya fada yana mai daga murya har sai da na firgita.
Yunwa nake ji na fada kasa-kasa.
Hmmn meyasa baki fada man ba?
Je ki shirya muje restaurant daga nan muje kasuwa ki sawo kayan abinci.
Saboda kitchen din babu kayan abinci
Toh na fada kafin na nufi dakina, ina zuwa na canja kayana zuwa riga da wando jeans.
Ina fita palor na same shi kallo daya na ga yayi min ya kauda kansa.

Go and change that dressing of yours
Yana fadar haka ya fita waje ko juyo wa baiyi ba.
Da naga dai fuskar shi ba alamar wasa yasa ko gardama ban masa ba kuma ga yunwa ina ji.
Dakina na koma na saka riga da skirt na atamfa.
Ina fita a mota na iske shi yana waya, ina shiga ya kalle ni ya yace saka seat belt dinki.
Hannuna na saka amma na kasa saka seat belt din saboda nisan da yayi min.
Da Ammar yaga dai na kasa sakawa ya matso har jikin shi na shafar nawa kamshin shi na shaka ,wani sanyi naji cikin raina.
Yana gama sakawa ya cigaba da driving.
Ko magana bai kara yi min ba har muka isa restaurant din.
Muna gama cin abinci muka nufi jabi lake mall sayyaya sosai nayi.
Muna gamawa ya kaini wuse market nayi sayyayan Atamfofi.
Wai baya so ina saka kananan kaya, gashi kuma kaya na duk kananan kaya ne sai kadan.
Muna gamawa gida muka nufa, muna isa yayi parking garage ,ya shiga cikin gida, ina fitowa naga butt din motan a bode ga kuma kaya da yawa a ciki ,wato shiyasa kenan ya banni ina ta kwaso kayan da nike so yaki ya hana ni ko.
STORY CONTINUES BELOW

Sauri nayi na bisa dakin sa, ina shiga naga har ya tube rigar sa yana sanye da wata karamar riga marar hannu.
Hannuna nasa na kama kuguna nace
Prince, kazo mu kwashe kayan nan kasan fa suna da yawa ba zan iya shigo da su ni kadai ba fa .
Kwantawa naga yayi ya juya man bayan sa.
Zuwa nayi kusa da shi nace ko baka jina ne wai!
Mikewa yayi yace kee! Yana mai nuna ni da dan yatsa. Are you commanding me! How dare you! Ya fada in his husky voice.
Ba'a koya maki cewa please! ba
Ya fada yana mai daga yatsun shi biyu,
Get out of my room, ki je ki koya yanda ake magana.
Kafin ki zo nan kin gane ko?
Kallon sa nayi, naga ba alamar wasa a fuskar sa .
Fita nayi fuu, na bar masa dakin raina a bace saboda maganar tayi mun zafi a rai.
Security na sa suka shigo min da kayan cikin gida.
Suna gamawa nace su tafi, kayana na cire na shiga wanka nayi sallah.
Wayata naji tayi kara ina duba naga Ammi ce, kuka na sakar mata, daga bisani ta bani hakuri da nasiha sosai tayi min, nayi magana da Abba shima haka nasihar yayi min, bayan na gama magana da safwan na kashe wayan.
Kayan bacci na saka na kwanta cikin bacci na ne naji waya ta na ringing, ina dagawa muryarsa naji, mai cike da isa, coffee yace na hada masa.
Shiru nayi masa na kashe wayan, tunawa da nasihar su Abba da nayi shi yasa ni tashi.
Ina zuwa kitchen na dudduba naga coffee maker din na hada masa.
Bansa sugar ba don bana son rigima ban sani ba ko baya so,
Kwankwasa masa nayi
Come in, naji ya fada ina shiga kamshin sa ne naji ya bugi hanci na oh my world, I love this scent !

Saman gado na ganshi yana aiki a laptop dinsa ya saka riga da wando na bacci.
Zuwa nayi kusa dashi na dura coffee din bisa wani tool na gefen gadon sa.
Ina kallon sa ta gefen idona yanda ya bi jikina da kallo.
Riga ce fara tas ta bacci jikina iya gwiwa, hannu ta siriri ne ,kana iya gani jikina baki daya saboda rigar fara ce kuma bata da nauyi ,transparent ce sosai.gashi na daure yake in a tight bun.
Ina ajewa na fita na bar masa dakin, komawa nayi dakina nayi Alwala na kai wa Allah kukana don shi ne kadai me share min hawaye na.
In the morning
Misalin karfe tara na tashi ko wanka banyi ba na shiga kitchen saboda wata yunwa da ta tashe ni.
Ina shiga na gyara kitchen din tsaf na shiga yin breakfast .

Pan cake da oath nayi na zauna ina ci, sai da na koshi kafin nan na tashi, nazo zan fita daga kitchen din naga prince ya shigo cikin manyan kaya sun yi masa kyau sosai
Ina so na bashi nasa break din amma me?
Ina tsoron rigimar sa, abincin na dauko na aje saman dinning table, na hada coffe na aje masa, na koma dakina.
Ina shiga daki wanka nayi na kwanta bacci.
Misalin karfe biyu zarah ta kira ni.
Zarah - Dr. Samrah Amaryar mu, zara ta fada cike da zolaya.
Samrah - barister ina fushi, na fada ina dariya.
Zarah - bari kidai kar kisa a daure ni, ina neman afuwa matar dan babban gida.
Samrah - haba zarah yau kwana na har biyu garin abuja amma ace baki zo ba duk kewar gida ta kamani.
Zarah - kai doctor ga prince kusa me kuwa zai saki ka daici.
Samrah - kinji ki, kamar baki san halin yayan naki ba da rigima sai kace dan goye, jiya ma sai da makuyi rigima da shi.
Zarah - cikin dariya tace haba dai, har yau baku daidai ta kan ku ba?
STORY CONTINUES BELOW

Samrah - me za'a fasa ae har gobe ma don kiji.

A bar ma wannan maganar yanxu dai yaushe zaki zo ne ya kamata mu je yawo na gaji da zaman gidan nan so boring wlh.
Zarah - kar ki damu ina gama last paper ta zan shigo.
Samrah - yaushe kenan?
Zarah -nan da two days inshaAllah.
Samrah Allah ya kaimu lfy.
Muna sallama na kashe wayar.
Wanka na shiga na sake kayan jikina zuwa three quarter da vest na fito ,banji motsin sa ba, hakan ya nuna ya fita.
Ina shiga kitchen na duba dinning table naga ya ci breakfast din da na masa.
Murmushi na danyi, na shiga hada lunch.
Fried rice nayi da soyayyar kaza da lemun kwakwa.
Ina gamawa na aje masa a dinning table ta tafi da nawa palor naci.
Ina gamawa na wanke plates din na koma palor na kunna tv ina kallon wani American film.
Misalin karfe hudu ya shigo gida, yana shigowa dakin sa ya nufa yayi wanka, yana saukowa na ganshi da wani three quarter irin kalan sojoji da wata farar riga, sun masa kyau sosai.

Kitchen ya shiga, ya dan jima a ciki ina jin abincin da na ajiye masa ya ci.
Nazo zan leka kenan muka yi karo dashi.
Dafe kaina nayi nace Auchhhh! Na danyi kara kadan.
Meke damun ki ne?
Ya fada yana kallon idona, bakya gani ne? Ko sai an kai ki asibiti?
Ammm ina gani na fada cikin sauri na bar wajan.
Palor na ga ya koma yana kallon ball.
Ina ganin haka na koma dakina na shiga karatun wani English novel.
Ina ganin karfe biyar na yamma yayi , na tashi na tafi kitchen.
Ammar p.o.v

Zaune yaka a palor yana kallon football match, gefen shi jug ne na coconut milk juice din da samrah ta hada masa.
Yaji dadin abincin sosai, ga mamakin shi abincin ya masa test din na mami, ko dan itama samrah da larabawa ta zauna, the food test Arabian, his favorite food.

Be taba shan coconut milk juice ba, amma yaji nata ya masa dadi sosai.
Tuno ta yayi jiya da ta shigo dakin sa, yana kallon komai na jikinta wanda idan ba dan yayi ta maza ba, da ya fita haiyacinsa.
Daga kansa yayi saboda motsin da yaji ya ganta cikin kicin.
Sanye ta ke da bomshot kallar fari da black top his favorite colors.
Hips din ta ya kalla, yaga wandon ya kamata sosai, kuma shape din ta ya fito.
Kallon ta ya shiga yi tana aikin ta tana rawa ,tana juya hips dinta.
Murmushi yayi cikin zuciyar shi yace yarinyar nan na neman rikita masa lissafi.
Wayar sa ce tayi ringing, yana dagawa yaga abokin sa ne.
Prince Samir Dan sarkin egypt.
Sun sha fira na dan lokaci kafin ya fita yayi sallah magriba.
Yana dawowa ya tarar da har ta gama abincin dare.
Yana dubawa yaga bata nan abincin ne kawai, saman dinning table.
Wayar sa ya dauko ya kira.
Tana sauko wa yace yana da magana da ita.
Zama tayi tana jiran ya gama cin abincin.
Yana gamawa ya kalle ta.
Ina so daga yau idan kin gama abinci ki jira na dawo mu ci tare, kallon sa tayi cike da mamaki.
Daga mata gira yayi, yace hakan ba yana nufin mun fara son juna bane but at list we can try to know each other better.
Yana gama shan pineapple juice din da ta zuba masa yace, motar ki da mai martaba ya baki tana nan an kawo maki day fatan dai kin iya driving? Ya tambaya yana mai kallon brown eyes din ta, yana fadar haka ya yaga tana murmushi.
Koda bata fada masa ba yasan taji dadi sosai.
Eh na iya driving ta fada tana kallon nashi blue eyes din.
And! Ya fada yana duban ta maganar aikin ki, nayi magana da Ahmad yace ba damuwa.
Zaki iya farawa in the next 2 to 3 months.
Saboda akwai wasu surgeons yanxu, amma yasan zuwa next month zasu yi retire sai a fara daukan sababbi.
Kallon ta yayi yaga tana murmushi har sai da wushiryar ta ta fito.
Sosai yaji dadi da yaga tana cikin farin ciki.
Kallon sa tayi cikin ido.
Tace na gode sosai. Kada kansa yayi yace ki gode wa Allah.
Harta tashi zata fita ko mai ta tuna, dawowa tayi ta kalle sa.
Amm, kuma sai ta fasa fada.
Menene?
Am dama zarah zata zo gobe ina so ta kaini wajan tellan ta,
Ok ya ce mata yana shirin tashi, cikin sauri koma tace masa.
Akwai bikin kawata on Saturday a kaduna ina so naje.
Tashi yayi yace wannan kuma ki bari sai lokacin yayi sai na gani ko zan iya bari ki tafi.
Yana ganin yanda ta bata ranta cikin shagwaba ta ce.. Kawata fa ce sosai gaskiya sai naje.
Kallon dan bakin ta yayi yanda tayi pouting dinsa yasa yana jin kamar ya sumbace ta.
Don't cross ur limit, ya fada ya wuce dakin sa.
Yana tafiya ta kwashe plates din dinning table ta wanke tas kafin ta ,kwanta ko coffee din ma bata hada masa ba saboda fushi.
I need your comments and vote below.Bayan kwana biyu

Ina gama breakfast na kai dining table,  yau  ina cikin farin ciki sosai saboda yau ne zarah zata zo.

daki na koma nayi wanka, wata English gown na saka tana da hannu karami, blue color ce.

Gashina na gyara ,sakin gashin nayi har gadon baya na.

Make up kit dina na dauko na yi simple make up .


Ina sauka naga prince har ya sauna a dining table yayi wanka shima cikin riga da wando na English wears.


Zama yayi yana latsa wayar sa, da alama ni yake jira na sauko, don ko abincin be ci ba.

Ina zuwa zama nayi opposite kujeran shi, murmushi na masa kafin na gaishe shi.

Ya amsa , serving abincin na mana na tura masa nasa.

Ina cin abincin amma ina kallon sa da gefen ido, yan da naga yana kallo na ko abincin be taba ba.

Gyaran murya nayi nace abincin ya maka yaji ne?

Kada kansa yayi alamar a'a.+

Sai kuma naga ya fara cin abincin, toasted bread ne da papper soup din naman kaza, sai kuma tea.

Muna gama breakfast ya fita, ni kuma na koma palor ina jiran zuwan zarah.

Ina kallon wani hausa film mai suna Abdallah, sai naji wayata tayi ringing

Ina dagawa naji muryar sa, zarah tace min ta kiraki wayar ki bata shiga, zata shigo wajan karfe biyar na yamma

.

Toh nace masa, zan kashe wayar kenan yace Samrah!

Yanda ya fada sunan naji sunan ya min dadi, Na'am,

Na fada.


Ina so ki gyara min dakina ,a wanke toilet din idan ba zaki damu ba.

Ok, na fada ya kashe wayar.

Tashi nayi na haura saman dakin shi na shiga, gyara dakin nayi na saka turaran wuta.

Toilet din na shiga na wanke, kayan dattin shi duka na kai laundry room.

Rufe dakin nayi na kuma kitchen nayi abincin rana.

Misalin karfe biyar sai ga zarah ta shigo da karamin akwatin ta.

Hugging din ta nayi cike da murna muka shiga palor ta ajiye kayan ta.

Har zan shiga da ita daki naji ta kira ni.

Samrah!  Ina tare da su khadija ne, sallamar su ce ta katse ta.

Zuwa nayi na tare ta.

Mace ce kyakyawa da wani cute baby a hannun ta.


Gabana ne ya fadi ganin yanda yaron yake kama da Ammar.

Suna zama na shiga kitchen na kawo masu juice da snacks.

Matar wadda naji zarah ta kira ta da khadija naji ta cemin.

Amaryar mu cike da zolaya tace gashi mu mun zo tunda Ango na boye mana ke. Murmushi na mata na dauka babyn ina kara kallon sa da kyau.

Oh my world, why am i feeling jealous.

Kodai Ammar ya na da wata matar ne?

It can't happen.


Ajiye babyn nayi na dube maman sa nace ya sunan shi?

Murmushi tayi tace sunan sa fou'ad.

Ni ma murmushin na mata na jawo hannun zarah muka shiga kitchen.

Muna shiga nace zarah pls wacece ban gane ta ba?

Ammar na da wata matar ne?

Naga babyn ta na kama da Ammar .


Zarah na jin haka ta hau yimin dariya, please ki ansa ni mana, shiro tayi ta cigaba da dariya

Palor na koma, ina shiga naga Ammar zaune suna magana da khadija hannun sa rike da fou'ad.

Hararar sa na shiga yi, shi kuma yana nema ya rike dariyar da ke bakin sa.

Da Alama Zarah ta fada masa.

Ina zama naji salamar mutum.

I know this voice na fada a raina.

STORY CONTINUES BELOW

Yana shigowa naga, Mr. Arrogant ne tashi nayi tsaye ina zazzare ido.

Miss Khalid! Naji ya kira ni

You, ya fada yana kallo na.  Kece matar brother dina?

Kallon Ammar nayi cikin sauri kafin na kalle Mr. Arrogant.

So they are brothers na fada a raina.

Yes sir na fada. Ammar ya dube Ahmad yace dama kasan ta ne?

Zama yayi yana murmushi yes i know her she's my student.


Not only student but my most brilliant student you are lucky Ammar.


Fou'ad na kuka naji khadija tace go to your dad duk ka ishe ni da kuka.


Oh dama matar Mr. Arrogant ce kenan?

Murmushi nayi, naga Ammar na kallo na.

Da sauri na bar wajan cike da kunya.

Zama nayi daki saboda kunya na kasa zama palor, zarah ce ta shigo tana mun tsiya.

Ashe dai ana so ake kaiwa kasuwa tunda har kishin yayan nawa ake yi, cewar zarah, tashi nayi na koma kitchen kedai kika sani na fada ina hararar ta.

Ina kitchen ina wanke wanke naji ringing din wayata.

Ina dagawa naji muryar Ammi, Ammi na ,I miss you soo much.


Na fada cike da shagwaba.

I miss you too my baby girl,  ina Dan babban gida ne?

Kwana biyu bamu gaisa ba.

Yana palor Ammi bara na kaimasa,  no barshi kawai yanxu zamu fita da Abban ku ne.


Ok Ammi my regards to safwan and Abba.

Muna gama magana na kashe wayan ina tunanin gida.

I really miss home


Ina zaune a kitchen bayan na gama wanke plates da fou'ad a hannu na ina wasa dashi, sai dai na juyo naga mutum na kallo na ganin irin kallon da ya bini dashi yasa na tashi tsaye .


Matsowa prince yayi yazo dab da inda nike yana kallon brown  eyes dina yace.

Eyye Ashe dai  ta iya raino 

Murmushi nayi masa sometimes indan na kalle sa sai naga kamar ba arrogant prince din da na sani ba, ya karba yaron .


Har yazo zai fita yace kizo kuyi sallama da khadija yanzo zasu tafi.

Ina zuwa na rike hannun khadija nace please mana ku kwana mana anan.

Idon ta naga ta zaro tace rufa man asiri ga Ahmad can ki tambaye shi, idan ya yarda toh

Zuwa nayi palor na iske Ahmad da Prince a tsaye da alama suna jeran fitowar mu ne.

Ban san lokacin da na je kusa da prince ba, hannun sa na rike gam nace

Please ka ruka min Ya Ahmad mana ya bar su khadija su kwana.

Jawo ni yayi zuwa kitchen ya matse ni jikin bango kissing dina ya shiga yi, har ban san lokacin da na maida masa martani ba.3

Daga bisani ya kyale ni, goshin sa ya dura bisa nawa yana nunfashi sama sama.

Meyasa kike so su kwana?

Ya tambaya yana kallon cikin ido na.

Saboda...

Muryar zarah muka ji tana kiran sunan mu.

Kafin ta shigo nayi saurin ture shi daga jikina na fito palor.

Ahmad ya dube ni ya yi min sallama har mun fito raka su.

Naji Ammar na magana da Ahmad akan su kwana a gidan mu.

Ahmad yayi murmushi ayi mana hakuri Amarya next time sai mu kwana yau akwai meeting din da zan je.

Murmushi na masa nace ok ba komai sai next time din sir.

Juyowa yayi yace please call me Ahmad.

Daga kaina nayi alamar eh.

Suka shiga mota .


Suna tafiya Ammar ya tafi masallaci gida ya rage daga ni sai zarah.

Daki muka koma muka sha fira.

Bayan sati biyu

Samrah

Alhamdulilah cikin satika biyu da suka wuce mun fara shiri da prince sosai har zarah na mana tsiya.

Naji dadi kwarai da prince ya barni na tafi bikin kausar kafin shima ya tafi nasa aikin a Abu dhabi.

A maiduguri aka daura mata aure,tare damu aka kawo amarya kaduna

Muka barta gidan angon ta fahad.

Bayan mun dawo daga bikin kausar, zarah ta tafi gida katsina, gida ya rage daga ni sai ni.

Bayan sati daya prince ya kira ni maganan aiki na.

Zan fara zuwa nan da kwana daya.

Tunda na fara aiki bani da hutu, yau ma ina ta yin kokari naga na dawo gida saboda, yau ne prince zai dawo.

Bayan na dawo wanka na shiga,  ina fitowa nayi kwaliya ta na saka riga da wando.

Kitchen na shiga na dafa pasta da miyar naman shanu, ko ci banyi ba na zauna ina jiran prince.

Har mamakin kaina nike yanda na kosa ya dawo, wata zuciya tana fada man na fara son shine amma ina karyata hakan ne saboda ganin shi be damu dani ba kamar yanda na damu dashi.

Wayata naji tayi ringing, ina dauka naji ana nemana emergency an kawo wani patient ,yayi hatsarin mota.

Cikin sauri na canja kayan jikina na nufi hospital.

Ina zuwa na shiga office na dauka abun da nike bukata na shiga theater room ,Dr Hammad na gani a bakin kofa yana jira na mufara aikin ,man dai ya shiga yimin  bayanin irin critical condition din da patient din yake ciki da sauri na shiga ina mai son ceto ran wannan bawan Allah..

Fuskar wanda na gani a kwance yasa ni ganin wani duhu daga nan ban san wane hali na shiga ba.

Pls Vote belowAmmar p.o.v

Bayan Ammar ya iso Nigeria,  misalin karfe hudu.

Mota ya hau ta company daga Airport yana shirin dawowa gidan sa.

Murna ya shiga yi na son ganin fuskar samrah, be san meyasa zuciyar shi ta kasa hakuri ba.

Yaki yake da zuciyar shi don kar taso samrah Amma ina!

Kamar yana kara mata wutar son samrah ne. Wani gefe na zuciyar sa tana tsoro kar yarinyar ta raina sa.

A ganin sa duk ranar da samrah ta lura da son ta da yake yi toh fa raini sai ya shigo.

Samrah ba irin matan da yake so ya aura bace amma tana da wasu suffofi da idan suna tare sukan sa ya fita haiyacinsa.

Sha'awarta da sonta sun dame shi, tunowa yayi da ranan da hakurin shi ya kare har yakai da kissing dinta a kitchen, sosai yaji dadi da ta mayar masa but he was disappointed ture san da tayi.


Shedan ne ya shiga zuga shi yake jin ina ma ace yanxu tana gaban shi da tagane kuran ta.+

How can shi just push him away?

Ya fada yana buga hannun shi, gudu ya shiga yi da motar  sosai

kiiiyyyyy


ya fada wani rami tayar motar shi ce ta fashe tayi daji dashi salati kawai ya iya yi daganan be san ina kansa yake ba .


Wata Ambulance ce tazo tayi rushing dinsa zuwa hospital.

Samrah p.o.v

Bude idona nayi na ganni saman gadon asibiti,

Tuno da fuskar Ammar da nayi cikin jini yasa kai na sarawa, wani irin kara na saki.

Wata nurse naga ta shigo tana ririkeni da sauri na ture ta ina neman tashi.

Dr. Hammad ne ya shigo ,

Dr. Hammad cousin din Ammar ne ta wajan mami, wanda yake zama a Abuja shima kwararan surgeon ne tare muka fara aiki dashi a Royal hospital.

Nurse what happen to her?

I don't know Dr. I had her screaming load.

Matsowa naga yayi daidai fuska ta, kuka nike yi da karfi.

Tashi nayi ina kallon sa da idanuna duk hawaye.

Rike sa nayi cikin daga murya nace.

What happen to him Dr.?

What happen to my husband Dr.?

I need to see him now Dr.

Is my husband alive Dr.?

Please show me were he is .


Calm down Dr. Samrah. Mijinki na nan lafiya .


mun shiga yi masa aiki cikin sauri, Allah ya bamu ikon cito rayuwar shi but he is in a critical condition now.

Mun aje shi a comma, we hope he will be better soon, saboda he is badly injured.

Ina jin haka kuka na ya karu, show me were he is i need to see him now please Dr..

Ya kamata ki samu hutu Dr. Samrah you are still weak, anjima sai ki ganshi ok?.

No Dr. Please show me were my husband is! Ba zan iya kara minti biyu ba a nan ,take me their pls.

Hmmn OK.  Since kin damu ki ganshi, Mun kaishe V. I. P room, nurse din da ke dakin yasa ta kaini room din.

Ina shiga naga yanda jikin sa yake  be San ma wanda ke kansa ba .


Dr. Hammad na shigowa na ce Dr. When is he waking up?

I need to talk to him.


Zuwa nayi wajan da aka kwantar da Ammar na shafa gefen fuskar shi.

Wasu hawaye naji sun kara zubawa ganin ko ina bandage ne a fuskar sa, I love you Ammar please don't leave me I need you in my life Ammar, I promise ba zan kara maka rashin kunya ba kaji pls wake up, we need to go home.

STORY CONTINUES BELOW

Dr. Hammad naji yace,  samrah ! Plus calm down. Ammar baya jinki kiyi hakuri  ki cigaba da Addu'a inshaAllah zai samu sauki.

Smiling nayi ina cigaba da shafa fuskar Ammar peck na masa a goshi nace, Ammar kana jina ko?

Zaka bini mu tafi gida ko?

Kana sona ko Ammar?

Gani nayi jikin sa baya motsi, shiro be bani amsa ba.

Bude wani bed sheet nayi wanda aka rufe masa jiki.

Wani irin firgita nayi ganin raunikan jikin shi.

No!  Na fada da karfi ina hawaye hannuna nasa na tushe bakina ina kuka iya karfi na.

Fita nayi daga hospital din ina kuka, daga bisani na dauki wayata na kira su mai martaba da Abba na fada masu halin da ake ciki.

Misalin karfe 8:30pm.  Dakin ciki yake da mutane, mai martaba da kansa yazo da mama da su zarah.

Abba ma yace zasu zo gobe haka ma Ahmad da mami.

Mama ce gabana saman kafet, ta sani gaba sai naci abinci Amma , ko ruwa na sha baya zama cikina.

Kuka ma da kyar ya tsaya daga idona.

Karfe sha daya daidai suka bar asibitin, ni da zarah kadai aka bari muka kwana.

The next day

Da safe su mai martaba suka kawo mana abinci, da kayan sawa.

Muna nan dai zaman jinya har su Abba suka iso naji dadin ganin Abba da Ammi ,safwan be samu zuwa ba saboda makaranta.

Su Ahmad da mami sun zo da yamma kowa dai ya taro, mutanan wajan aikin sa da dama sun zo, har yayan sarakuna da dama sun zo gani


dan babban gida.


Mami sosai taji dadin ganin irin kulawar da nike ba dan ta, tana ta shimin Albarka.


Ana watsewa da daddare na shiga kaiwa Allah kuka na.

Aikina ma dole sai da na dauka hutu saboda kula da mijina.

Yanxu ne na yarda da na kamu da son Dan babban gida.


Why ! Why will I be inlove with that heartless man wanda bansan matsayina ba a zuciyar sa.

Kuka sosai na shiga yi,

Samrah ya kamata kiyi hakuri hakanan wannan abu da ya faru kaddara ce,  inshaAllah prince zai samu lafiya. Cewar zarah.

Kallon ta nayi, zarah! Ina kiran sunan ta na fara kuka, hugging dinta nayi nace, zarah I really want him to get better, duba ki gani fa zarah. Ko fa motsi bayayi har yanxu his unconscious.

Zarah ta rike min hannu, ta zaunar dani gefenta tana goge min hawayan da ke ta zuba daga idona, kallo na tayi da kyau tace.

Samrah kinga yada kika zama kuwa, duk kin rame bakya ko cin abincin kirki. Ya kamata ki kula da kanki don ko shi prince idan ya ganki haka bazai ji dadi ba.


Ko kina so kema ki kwanta ciwo ne?. Don Allah ki rika cin abinci

Addu'a kawai zaki rika masa.

Addu'a na shiga yi Allah yasa wa prince sona koda rabin wanda nike masa ne, ya kuma bashi lafiya.


Ina mamakin kaina yanda na kasa ci ko sha duk na rame saboda damuwar da nike ciki ta son Ammar, da kuma ciwon da ke damun sa.

A daran nan ko runtsawa bacci banyi ba. Qur'ani na dauko na cigaba da karatu ko naji saukin radadin da ke zuciya ta.

Assuba nayi na tashi zarah mukayi sallah, muna idarwa, mami ta zo hospital da ita dasu mai martaba.

Su Abba sun koma cairo saboda safwan .


Ranar kowa zama yayi shiru ganin yanda jikin Ammar yayi tsanani tsawan sati daya Amma ba wani canji.

Duk wani magani da za'a bashi ni ke bashi , ni ke kuma yi masa duk wani allura da za'a kawo.

Zama nayi gefen gadon da yake kwance , karami towel nasa ina goge masa jikin sa.

Kallon fuskar sa nayi, hawaye naji sun fito daga idanuna, sunkuyawa nayi na yi masa peck a goshin sa da lips din sa.

Pls wake up Ammar I love you.


Lips dina na shafa ina tuna ranan da prince ya fara kissing dina a cairo in my room.


Murmushi nayi,  I remember every thing that happen. It was on my graduation day.


Fuskar sa na shafa nace you stole my first kiss Ammar.


Wajan kunnan sa na koma nace don't worry Ammar,  I have forgive you, for everything you did to me.


I need you alife, ka manta, kai ka fada mun auran mu na har abada ne mutuwa kadai zata rabamu.

We have to see our grandchildren before living this world Ammar.

Don't live me now.

Kifa kaina nayi jikin shi ina kuka.

Pls  vote below.Bayan wata shida

Samrah p.o.v

Bayan na gama sallah magriba, zama nayi ina addu'a. Shafawa nayi na mike na nada kafet din na ajiye gefe guda.

Qur'ani na dauko, zama nayi gefen da Ammar yake kwance  ina karantawa har zuwa karshen suratul yasin.

Ina idarwa na ji ringing din waya ta dubawa nayi naga number din kausar ce. Cike da farinciki na daga call din.

Kausar - hello matar dan babban gida. Ba fada me ya kawo gaba kin wani manta dani.

Samrah - hmmn kawata kenan, ba zaki gane ba. Ina cike da damuwa Allah kadai nike kaiwa kuka na.

Yau wata shidda kenan da kwantawar mu Asibiti, kausar bana da wata natsuwa nayin wani abu ke ko waya rabun da nayi da wani har na manta.

Kausar - subhanallahi! Waye bashi da lafiya? Samrah!

Samrah - Ammar ne, (cikin kuka samrah ta fara magana),  kausar tunda aka kwantar da shi ko motsi baya yi, kullun ana magani amma kamar bayi ake yi ba, sai kin ganshi be san ma wanda ke kanshi ba.+

Ni kaina duk na rame na shiga damuwa kowa yazo sai ya min fadan kin cin abinci, abincin kona ci baya zama cikina.

Kullon saidai naci kukana.

Kausar - ya salam!  Addu'a zakiyi samrah cuta ba mutuwa bace inshaAllah Allah zaya bashi lafiya.


Ki kulan mun da kanki don Allah. Su Abba sun zo ne?

Samrah - eh sun Kara zuwa kwana uku da suka wuce amma sun koma cairo, kausar addu'a kullun cikin yinta nike sai dai fatan Allah yasa a dace.

Ya fahad?

Kausar - fahad lafiya lau yana gombe wajan aiki amma jibi zai dawo, inshaAllah zamu zo ganin jikin Ammar. 


Dan ma jikina din ba dadi kullun cikin laulayi da munzo jibin.

Samrah - cike da jindadi nace kawata kardai? Mun kusa samun baby?

Kausar - cike da zolaya tace, kima fara tara kudi, na kayan babies don ko cikin ne dani watan shi biyar ma kuwa.


Samrah - wow, mashaAllah. Allah ya kawo mana shi ko ita lafiya sai kun zo din.

Kausar - toh sai anjima.

Kashe wayar nayi na zauna ina kallon fuskar Ammar, sai naita tuna lokacin da muke fadan mu da lokacin da yake mun dariyar sa mai sa na mance komai da kowa sai shi.

Shafa gefen fuskar sa nayi nace Allah ya baka lafiya mijina. I don't want our love to be incomplete.

Murmushi nayi wanda be kai ciki ba nace,  Ammar kausar is having a baby za mu je suna ko da kai?

Shiro nayi ina kallon fuskar sa, magana nike yi amma baya ko motsawa infact baya jina,wasu hawaye naji sun zubo mun.

Kwankwasa kofa naji anyi da sauri  na share hawaye na.

Zarah, mami da mama suka shigo da kulolin abinci da fruits kalakala da drinks.

Tashi nayi hugging dinsu.

Zarah ta kura min ido, tace mama kinga har yanxu samrah kuka take yi.

Murmushi na kakaro nace mama Allah ba kuka nike ba.

Mami naga ta tashi ta zaunar dani kusa da ita tace.

Habibty samrah!

Cikin harshen larabci tace Meyasa ba zaki yi hakuri ki bar ma Allah ikon sa ba, cuta fa ba mutuwa bace, ni na haifi Ammar amma ina daurewa da damuwata na barwa Allah ikon sa.

Kwantawa nayi saman cinyarta nace mami kullun cikin roka masa lafiya nike, kuma nayarda da ubangijina zaya karba mun addu'ata ko ba yau ba.

Mami tayi murmushi tana shafar kaina, mama da kanta tasa mun abinci, zarah ta zuba mun juice.

STORY CONTINUES BELOW

Kadan nace na ajiye cukalin ina kallon gadon da Ammar ke kwance sai wasu hawayan suka zubo min.

Mami na ganin haka ta share min tace kici abincin samrah kinji ko?

Kallon ta nayi nace mami, kullun idan naga halin da Ammar yake ciki sai naji zuciyata ta karaya kamar ba zai rayuba.

Shish mama ta katseni kul! Samrah

Kar ki kara fadar haka kinji ko?

Cuta ba mutuwa bace. Allah zai bashi lafiya, zauna kici abincin ki.

Gobe inshaAllah mai martaba yace Za'a kawo maki wata kuyanga wadda zata tayaki kula da Ammar don ki samu ki koma aikin ki kinji ko?

Kada kaina nayi,  nace mama

Dama akwai aikin da zanyi da yafi wannan?

Akwai aikin da yafi na kula da  mijina?

kullun ina samun lada marar kirguwa saboda kula da marar lafiya yana da lada sosai, bare kuma mijina?

Ba sai an kawo kowa ba zan cigaba da kula dashi .


Ba aikin da ya kai mata ta kula da lafiyar mijin ta alokacin da yake bukatar kulawarta.

Ko na koma aiki bani da natsuwar da zan iya yin wani abu.

Su mama sun dan jima sai da daddare suka tafi suka barni, nida zarah.

Bayan kwana uku

Ina zaune saman kujera ta gefen gadon da Ammar yake,  kwankwasa kofa naji. Ina budewa naga kausar.

Tsalle nayi na hugging dinta cike da murna, muna shiga suka zauna na basu juice.

Muna gaisawa da fahad yayi min ya mai jiki ya fita.

Yana fita na kalli kausar tayi kiba ta kara fari, tayi kyau.

Lallai kausar kice fahad na kula mana dake kinga yanda kika yi kyau kuwa?

Ko cikin ne yasa ki haskawa haka?.


Kallon ta nayi naga tayi shiru tana kallona.

Hawaye naga ni suna fita daga idonta. Matsowa naga tayi, hugging dina tayi ta fara kuka.

Haba samrah kinga yanda kika rame kin yi baki, duk kin bushe gabadaya.

Murmushi nayi wanda yake na takaici ne, hannun ta na rike naja ta har wajan gadon da Ammar yake wance nace, duba ki gani kausar kinga halin da Ammar yake ciki?

Ya bazan rame ba?

Kina tsammanin zan iya cin abinci, ina ganin sa cikin wannan halin da yake ciki? Rai hannun Allah.


Kada kaina nayi hawaye na zuba daga idanuna nace kausar!

Ki taya ni da Addu'a, saboda wannan ciwo na Ammar kullun tsorata ni yake, kullun natashi sai naga kamar zai farka amma ina!

Kausar ta rike mun hannu ta zaunar da ni kusa ita, tace ba komai Allah zai bashi lafiya inshaAllah.


Wata leda ta miko min wanda yake cike da fruits. Karba nayi na aje .muka cigaba da firan yaushe rabo.

Kausar na tafiya Ahmad yazo shida khadija, sun dade suma har sai dare kafin suka tafi.

Yau safiyar wata litinin ina karatun Qur'ani, kamar yadda na saba every morning sai na karanta masa Qur'ani. Ina idarwa na tufa masa addu'a na zauna kusa dashi.

Motsi naga hannun sa ya fara yi, cike da murna na tashi tsaye ina kallon yanda idanun shi ke kokarin budewa, Ahankali naga sun bude.

Alhamdulilah  na furta baki na har yaki rufuwa saboda murnar da ke raina.

Blue eyes dinsa ya zuba min yana kallo na bakin sa na kokarin yin magana, matsowa nayi kusa dashi don naji ko me yake son fada.

Ruwa!

Sauri nayi na kawo masa ruwa yasha. Me kake so kuma?  Ba komai ya fada.

Gyara masa kwanciyar nayi ya dan kishingida da bango.

Ina jin salamar su zarah da guduna naje nayi hugging mami nace mami ya farka yayi min magana mami.


Tace mashaAllah, Alhamdulilah

Allah min gode maka.

Rike min hannu tayi muka je kusa dashi ya gaishe da mami. Zarah ta gaishe shi itama ya amsa.

A ranar yini nayi fara'a har su mami na mun tsiya.

Shidai Ammar baya cewa komai sai dai idan anyi abun dariya yayi murmushi. 

Duk inda nayi sai naga yana bina da kallo. Murmushi na masa na raka su mai martaba waje shida mama suka zo da yamma.

Dare nayi kowa ya watse

Dr. Hammad ya shigo, yace lallai Ammar ka gode wa Allah kayi dacen mace ta gari. Don tunda ka kwanta ciwo ita ke ta kula dakai.

Murmushi Ammar yayi ya cube in yace Allah shine abun godiya

Allah saida ya saukar da magani kafin ya saukar da cuta don haka shine abun godiya.

Dr. Hammad ya kirani na fita zuwa office dinsa, kallona yayi dakyau yace well done

Dr. Samrah!

A gaskiya kinyi kokari Allah ya saka maki da Alkhairi, ke  macen kwarai ce a zamanin nan da kamar wuya a samu mata irin ki.

Murmushi nayi Nace komai nayi don samun aljannata ne Dr.

Ba kamai, yanzu ya maganan salaman mu ne?

Well zan baku salama lokacin da muka ga jikin nasa ya kara kwari sosai ok ?

Ki daina sa damuwa a ranki inshaAllah ba damuwa.

Ok doctor, godiya na masa na koma dakin da aka kwantar da Ammar.

Ina shiga na tarar har yayi bacci, zuwa nayi na gyara masa bargon nayi masa addu'a na tufa masa, kafin nima na yi wanka na kwanta.

In the morning

Saboda yau ina fashin sallah, ban samu tashi da wuri ba, sai wajan six na farka ,ina tashi naga Ammar na kokarin mikewa.

Zuwa nayi na kamashi, ina zaka je ne? Toilet ya fada yana mai rike kanshi.

Zaunar dashi nayi nace kanka na maka ciwo ne?

No, am feeling dizzy ya fada yana kokarin tashi.

Ina kai sa toilet din nace zaka iya kai kan ka ciki? Ko sai na shigar da kai.

Zan iya ya fada yana dafa bango.

Yana gama alwala ya fito na shinfida masa kafet yayi sallah.

Gadon shi na gyara, nace ko zaka koma gadon ne? Kada kansa yayi alamar a'a.

Murmushi nayi na koma kusa dashi na zauna, nace yau Friday ko zaka karanta suratul kahf .


Qur'ani na dauko masa ya fara karatu ni kuma ina binsa da hardar surar da nayi.

Muna idarwa mukayi addu'a muka shafa tare.


Kallon sa nayi nace prince I love your recitation.


Murmushi yayi, yace Jazakallahu khairan.


Muna nan zaune sai ga zarah ta shigo da flasks din ruwan zafi ,da kula da jug.

Zama tayi ta gaishe da Ammar ya amsa yana murmushi tace Prince gaskiya jikin ka mashaAllah da sauki sosai.

Yace Alhamdulilah, Allah shine abun godiya.

Plate na dauko na zuba masa chips din da zarah ta kawo da coconut milk juice din da ta hada.

Hannuna ya rike yace kema sai kin ci.

Kinga yanda kika rame kuwa?

Zarah naji tace prince wlh tunda ka fara ciwo samrah bata cin abinci sosai sai kuka kawai.

Jawoni yayi jikin sa yace, idan kina so naci abincin toh kema fa sai kin ci shi. Hannun sa ya sa ya dauka spoon din yana bani da kansa, ni ma na fara bashi yana ci.

Zarah dai kallon mu takeyi amma tausayin mu take ji cikin ranta.

Muna gama ci ,na kaisa toilet yayi wanka na saka masa kayan da kaina.

Su mami ma sun shigo sunga jikin Ammar Alhamdulilah da sauki sosai.

Don yana zama ayi fira dashi.

Plus vote belowBayan wata hudu

Ammar p.o.v

Ammar ya samun sauki ya koma wajan aikin sa.

Ya dawo Nigeria bayan ya samu Hutu ne ya dauki matar sa samrah suka tafi yawon honeymoon din su a paris.


Kwance yake da wata farar vest, kansa na saman cinyar samrah idanun shi a lumshe tana shafa masa kai tana waya da mami.+

Tana gama wayar ta, cike da shagwaba tace prince !


Bude idanun sa yayi ya kalla fuskar samrah wadda ita ma idanun ta na kansa, suna hada ido tayi murmushi tace,

My Prince charming! Har ka fara bacci ne?

Shima murmushin ya mayar mata yace yes my Queen.

Murmushi ta kara masa har wushiryarta ta fito kadan tace kasan mene?

Hannun sa yasa yana shafa gefen fuskar ta.

Tashi yayi ya zauna yana fuskantar ta yace my Queen sai kin fada.

Kallon blue eyes dinsa tayi tace, prince I really like it when you call me ur Queen.


Murmushi ya mata ,ya matso wajan kunnan ta yace you are my Queen samrah.


Hawaye yaga suna fita daga idanun ta, yatsan shi yasa yana share mata, yace. Subhanallah what happen?


Kallon sa tayi cikin idon sa, ta hada hannun ta da nashi na matse gam.

A jiyar zuciya tayi, tace prince ayau ka cika mun buri na kullun mafarkina koda bamu zama masoya ba, ya zama na muna zaman lafiya.

Peck Ammar ya mata a goshi yace, kiyi hakuri samrah nasan, a matsayina na mijin ki,


auran mu shekara daya kenan amma bamu taba samun zaman lafiya irin na yau ba, bana kula da ke kamar yanda na dauka Alkawari,

amma still kin rufa mun asiri.


Ba wanda yasan halin da muke ciki .

Hakika samrah kin kasan ce mace ta gari, ba yanda nike tsammanin ki ba, sai naga akasin haka.

A lokacin da nayi jinya, koda bana cikin haiyacina abokaina da dama sun fada mun yanda kika yi kokari wajan samun lafiya ta, wanda ba kowace mace bace zata iya haka.

Kara matse hannun ta yayi yace samrah! Kallon idanun sa tayi wanda suke nuna mata irin son ta daya kiyi koda be fada mata ba.

Mikewa yayi yace my queen tashi ki rakani wani waje.


Garden suk nufa suka dan zagaya sai da yamma likis suka shigo cikin gida.

Suna shiga samrah ta yi wanka ta canja kayan jikinta zuwa English wear, ta fito palor ta tarar da Ammar shima har ya shirya zuwa wando da riga na English wears.

Zama suka yi suna dan fira tana bashi labarin school din su da Ahmad brother dinsa, wanda suka sama suna Mr. Arrogant.

Ammar na ta dariya.

Kallon sa samrah tayi tace my King!

Ammar na jin ta kirashi da king ya kalle ta, murmushi tayi tace daga yau kai sarkine, amma na zuciya ta.


I can't hide it anymore Ammar, son ka ya min yawa, I have to confess to you.

Koda kai din baka sona, ta fada tana goge kwalla da ta sauko daga idonta.

Farin ciki ne ya baiyana a fuskar Ammar daya ji wannan kalaman daga bakin samrah .


Matse ta yayi jikin shi har suna shakar nufashi junan su.

Kallon cikin idanun samrah yayi yace kin yadda nine Ammar?

Samrah ta kada kai alamar eh.

Kara matse ta yayi yace yasuna na?

Samrah ta kalle sa cikin ido tace Dan babban gida, yarima Ammar the king of my heart !


Tana fadar haka ya hada bakin sa da nata yashiga sumbatar ta in a passionate way.


Ya mantar da ita komai da duk wata damuwa da ta taba shiga a baya.

Hannun ta tasa tana shafar suman kansa, Ammar najin haka ya kara matso ta jikin shi, harshen sa yasa yana lasan gefen wuyanta.

Wani yarr samrah taji a jikin ta, shafa kansa samrah ta cigaba dayi tana nishi samasama

Hannunsa yasa yana shafar hips dinta ,rike hannun sa samrah tayi gam, kallon ta yayi cikin rashin fahimta yace what happen?

Am really scared prince.


Murmushi yayi ya kara manna bakin shi cikin nata, harshen sa yasa yana wasa dashi cikin bakinta .


stay calm my Queen, I won't hurt you.


Janye jikin ta samrah tayi daga nashi tana nishi sama-sama.

No prince!

Samrah ta fada,

Me kike nufi my queen? Ammar ya fada yana kara zuwa wajan da samrah take tsaye hannun sa yasa yana sage rigarta ta baya, cire rigar yayi daidai shoulder dinta ya fara kissing din ta.

Ture sa tayi tana hawaye

Kana sona? Samrah ta fada tana kallon shi.

Rike hannun ta yayi yace baki yarda dani bane?

Don't you trust me?

Shafan gefen fuskar shi tayi tace no my king. Na yarda da kai dari bisa dari.

Amma bazan iya mallaka maka kaina ba.

What! Nifa mijin ki ne ,my queen ina da hakki na a kanki .


No MY KING!

Samrah ta fada tana me kada kanta tana murmshi.

Ba zan iya mallakama ka kaina ba, har sai ka fada mun kana sona.

Murmushi Ammar yayi har dimple dinsa ya lotsa.

Sumbatar samrah ya shiga yi, sai da yaga hankalin ta gabadaya baya tare da ita, sannan ya kyale ta.

Matsawa yayi wajan kunnan ta ya dan ciza kadan, har sai da tayi kara.

I love you my Queen!


Yana fadar haka samrah tayi hugging din sa ta fara sumbatar sa ta ko ina.

Daga ta sama Ammar yayi yana juyata. Dariya sosai samrah tayi, saboda wannan rana, wannan dare bazata taba manta su a rayuwar ta ba.

Is a moment that she will cherish for ever.


Ammar na ajiye ta a kan gado yace.

Let go and perform ablution my queen. Tashi tayi ta bishi sukayi alwalan tare.


Sallah suka yi raka'ah biyu.

Ammar ya dafa kan Amaryar sa abun kaunar sa, Sarauniyar sa samrah addu'ah yayi.

Suka shafa gabadayan su.

Daga bisani yayi mata tambayoyi da suka shafi addini.

Kwarai yayi mamaki dayaga samrah ta amsa masa tambayoyin sa gaba dayansu.

Yayi farincikin sannin samrah me addini ce, ba yanda yake tsamanin ta ba.

Suna gamawa Ammar ya dauke ta ya kaita saman gado.

A wannan daren ne, Ammar da samrah suka zama daya. Suka raya daren cikin so da kaunar junan su.

Daren da kowannan su ba zaya taba mantawa ba.

Is a moment that they will not be able to forget in their entire life time.

Moment of love and trust .


Assuba

Tare suka tashi suka yi sallah assuba, da karatun Qur'ani.

Suna gamawa suka kwanta rama baccin jiya da basuyi ba.

Wayar da aka kira ce ta tashe su daga bacci.


Samrah na dagawa fahad ya fada mata kawarta kausar ta haihu baby girl. Cike da murna ta tashi tana rawa.

Ammar ya dube ta yana dariya yace kee lafiya?

Hugging dinsa tayi tace kausar ta haihu baby girl.

Pls vote belowBayan wata biyu

Samrah p.o.v

Yau tunda na dawo daga hospital taliya kawai na iya girkawa saboda duk jikina yayi weak sosai.

Ina gama girkawa na kai dining table na aje

Dakina na koma na yi wanka na canja kayana zuwa wata short gown marar nauyi, gashin kaina na gyara na daure shi da ribbon.

Wani Arabian turare na dauko wanda Mami ta aiko min shi daga Egypt kamshin turaren nada dadi sosai.

Feshe jikina nayi da turaren kafin na tashi na koma dakin Ammar.

Saboda yau da asuba na fita ban samu gyara masa dakinsa ba. Ina shiga na gyara dakin ,na wanke masa toilet na saka turaren wuta.

Komawa nayi palor na share na yi mopping floors din.

Ina gamawa naji kaina ya fada min ciwo dama dauriya kawai nike yi saboda kwata kwata bana jin dadin jikina .


Zama nayi palor ina jiran Ammar ya dawo.

Karfe 7:00 pm daidai ya dawo, lokacin na shiga daki ina sallah.

Yana shigowa dakin sa ya shiga yayi wanka, ya fita sallah.+

Sai bayan isha'i  ya dawo daga masallaci.

Yana bude kofa lokacin ni kuma ina fitowa daga kitchen.

Hugging dinsa nayi da sauri.

Nace my king I miss you soo much, ina ta jiran ka since.


Na fada ina pouting lips dina.

Hannun sa yasa yana shafar bayana yace am sorry my queen for keeping you waiting.


Hannun sa na rike nace zo muje muci abinci, rike ni yayi gam yana shakar kamshin jikina.

I love diz scent. Murmushi nayi nace thank you.

Peck ya min a goshina yace ok lets go and eat.

Muna zama saman dining table, yace hmmn i love diz aroma.

Kallo na yayi ya daga gira.

My queen me kika dafa mana yau ne?

Ina ta jin kamshi.


Tashi naga yayi da sauri, minti biyu please ina zuwa.


Ya fada, da sauri naga ya fita ya dawo da wata bakar leda.


Yana bani na karba, ina tambayan sa ko menene a ciki?


Budewa nayi naga kaza ce gasassa ,  kamshin kazan ne da yashiga hancina naji zuciya ta na tashi.

Da gudu na shiga toilet, ina ta Amai kamar wadda zata amayar da yan cikin ta gaba daya.

Ammar ne yashigo da sauri cike da damuwa a fuskar sa yace lafiya?

Wanke fuskata nayi, kafin na fito daga toilet din.

Rike min hannu na yayi, ya zaunar da ni kan gado ,kaina ya dora saman cinyar shi yana shafawa a hankali.

My queen!

Ammar ya kirani, me ke damun ki ne?

Rike cikina nayi ina hawaye nace, prince cikina ke ciwo kuma tun last month, sai inji jikina yayi weak kuma bana son warin abubuwa.

Yau ma dakyal na dawo daga aiki.

What! Tun last month baki da lafiya kuma baki fada mun ba!


Ya kamata ki fada mun ae samrah sai muje asibiti ko?

Girgiza kai na nayi.

Cike da shagwaba nace no no dai bana son alura fa.

Ammar na jin haka ya fara dariya har yana rike ciki.

Doctors na tsoron allura?

Hannu na nasa ,na dauko wani karamin pillow ina bugun shi yana ta dariya.

Kuka na sakar masa, wanda nasan na shagwaba ne kawai.

Yana ganin haka ya bar dariyar ,daki ya kaini ya dauko min wasu kaya yace na saka saboda na bata jikina da aman da nayi dazo.

STORY CONTINUES BELOW

Ina canza kayan, ya matsa min naci abinci kadan.

Daukata yayi ya dorani saman gadon shi.

Zama nayi saman gadon na matso wajan da yake kwance yana chatting da wayar sa.

Nace prince, please ina so ka kaini hospital gobe.

Aje wayar yayi yace ba kince kinji sauki ba.

Kada kaina nayi na rike hannun sa nace.  I want to confirm something.

Kallo na yayi cikin ido.

Yace me kenan?


Prince ina so nayi pregnancy test, na fada a lokaci daya.


I think am pregnant na fada.


Murmushi naga Ammar yayi ,hugging dina yayi sosai har bana iya nufashi.

I can't breath na fada ina dariya.

Peck ya min a lips dina yace I will be very happy if is true.


Ya fada cike da farin ciki.

I love you my queen.


Kwantawa nayi a kafadar sa,  Murmushi na masa, nace I love you more my king.

Kallon jikina yayi yace haba,  shiyasa naga kin kara kyau kinyi fresh.

Ashe akwai ajiyata.

Rigar ta ya daga,yana shafar cikinta yace dady love you.

Dariya na shiga yi masa, nace ban fa tabbatar ba saboda banyi test ba.

Murmushi Ammar yayi yace oho dai ni dai nasan akwai ajiyata a wanan cikin naki.


Dariya muka yi gaba dayan mu.

Kallon na yayi ya shafi gefen fuskar ta yace.

Ina son babies samrah fiye da yanda kike tsammani.

Hannun ta tasa tana shafar fuskar sa tace Allah ya bamu masu Albarka.

Amin, Ammar ya fada.

Bayan kwana biyu

Third person p.o.v

Ammar da samrah sun je hospital, an tambatar masu da samrah na dauke da juna biyu .


Ammar yayi farin ciki sosai, su mai martaba ma sun zo kowa dai yayi murna da jin wannan cikin.

Ammar ya hana samrah zuwa aiki, har sai ta samu sauki saboda laulayin da take yi.

Kausar da zarah sunyi farin ciki sosai. Don zarah ma tare wa tayi a gidan su samrah tana kula da jikin samrah.

Safwan da Ammi sun zo suma sunyi kwana biyu kafin suka koma cairo.

Samrah tayi murna kwarai da taga Ammin ta da safwan .


Kyauta  sosai Ammar ya bata .

Yau ma kwance take saman kafet ita da zarah suna fira.

Ammar suka gani ya shigo da kayan wasa da yawa a hannun sa.

Tashi samrah tayi tana masa dariya ita da zarah.

Zarah ce tace prince kenan babyn wata biyu ,wanda yake cikin ciki har an fara saya masa kayan wasa?

Lallai babyn nan dadyn sa na ji dashi ko ita.

Murmushi yayi har dimple dinsa ya lotsa , Sosa keyasa yayi ,yace su kyale shi, ba kudin su bane ae.

Shiga dakin sa yayi, shida samrah.

Suna shiga tace prince kenan Allah ya kawo mana babyn nan lafiya, kila ma kafi son sa,

Naga yanxu ba tani kake ba.

Ta fada tana pouting lips dinta.

Ammar najin ta fada haka, sunbatar ta ya shiga yi.

Yace kar ki kara fadar haka. I love you all. Cikin ta ya shafa yace

Karki damu kinji ko?

Murmushi tayi tace I love you too.

Fitowa suka yi suka ci abinci kafin ya dauke ta suka koma daki.

Tunda samrah ta samu ciki, Ammar yake kokarin kula da ita sosai, ko aikin sa ma ya dauki hutu har sai bayan sati daya.


Samrah tayi wa Allah godiya da yasa mijinta ya fara son ta kuma ya ke kula da ita sosai.

Wanda a da can bata taba tunanin faruwar hakan ba.

Bayan kwana biyu, samrah ta samu sauki.

Ammar na ganin ta samu sauki ya kwashe ta suka tafi da ita wajan aikin sa a Abu dhabi.

Ammar ya cigaba da kula da ita duk ranar da yake free.

Lokacin da cikin ta ya shiga wata biyar,  Ammar ya kaita taga gida, sosai taji dadin ganin Ammin ta da Abba.

Har gidan Ahmad ya kaita tayi wa khadija kwana biyu .


Sati biyu tayi a cairo,  har Egypt ya kaita wajan  mamin sa tayi sati daya

kafin suka dawo Nigeria.

Suna dawowa ta matsa sai da ya kaita kaduna gidan kausar, taga diyar kausar wadda yanxu tayi wata bakwai ,sunan maman fahad aka sa mata wato Amina..

Kausar taji dadin ganin samrah sosai, sun sha fira sosai har sai karfe hudu Ammar ya dauke ta suka koma Abuja.

Ammar ne kwance saman cinyar samrah tana wasa da gashin kansa tace.


Hmmn my king, Ammar ya daga kai yana kallon ta, wane baby kafi so?

A boy or a girl?

Tashi Ammar yayi ya zauna yana fuskantar ta ,hannun sa yasa yana shafar cikin ta.

Yace duk wanda Allah ya bamu ina so. Murmushi samrah ta masa tace Allah ya kawo masu albarka.

Zama yayi kusa da ita yace Amin ya rabbi. Rike hannun ta yayi yace zo kiga wani surprise, binsa samrah tayi tana dariya.

Pls vote and comment below

This will be the last chapter, I will be writing the epilogue very soon inshaAllah.Epilogue 1

Samrah pov

Zaune nike da katon cikina ,ina yanka fruits, saboda yau monday Ammar na azumin lada.

Ina cikin yankawa naji marata ta fara ciwo, rintse idanuna nayi ina salati.

Dakyar na samu na mike tsaye ina kiran sunan Ammar,+

Da saurin sa naga ya shigo, yana shigowa ya rike ni lafiya?

Me ke damun ki ne?

My Queen what is wrong with you?

Ya fada cike da damuwa .


Hannun sa na kama na rike gam, ina salati marata Ammar , na fada ina me kara rike hannun sa.

Ammar na jin haka ,ya dauke ni muka nufi hospital, muna zuwa aka kaini labour room.

Cikin ikon Allah nakudar tazo min da sauki.

Allah ya Albarkace mu da twins mata,

Ammar pov

Ammar na waje ,bayan ya kira su mai martaba da su Ammi ya fada masu halin da samrah ke ciki.

Wata nurse ce ta fito ta fada masa samrah ta haihu lafiy... Kafin ta karasa har Ammar ya shigo dakin.

Yana shiga ya dubi samrah a kwance duk sai ta bashi tausayi saboda ganin walahar da ta sha .

Don yaji ance nakuda akwai wahala, cike da saurin sa ya matsa wajan da take kwance,

Peck ya mata a goshin ta har zuwa lips dinta.

Hannun sa yasa yana shafar fuskar ta yana murmushi.

Bude idon ta tayi taga Ammar a gefen ta, murmushi tayi masa tace my king ina babies dina?

Babies?

Ammar ya fada yana kallon ta. Murmushi samrah tayi tace eh!

Twins na haifa.

What! Dagaske! Cike da farin ciki Ammar yayi hugging dinta yana sumbatar ta tako ina.

Tashi yayi yaje wajan da yaran suke a kwance, dubawa yayi yaga duk mata ne. Murmushi yayi ya dauko su ya mikawa samrah daya ya rike daya.

Addu'ah yayi masu, kafin ya masu huduba da kiran sallah.

Kallon samrah yayi yace Allah ya maki albarka, kin min kyautar da tafi komai a duniya, kin sani cikin farin cikin da ban taba shiga ba a duniya.

Murmushi samrah tayi tace Amin my king Allah ya raya mana su .


Samrah na kallon babyn hannun ta tace, my king kaga wannan tana kama da kai.


Kallon babyn Ammar yayi yaga tana bacci so innocent.

Kamar yanda samrah ta fada din kamanninsa twins din ke dashi, har da kalar fatar sa.

Duba ta hannun sa yayi yaga ita ma kamar sak tasa ce, sai dai ya hannun sa, ta gado digon bakin fuskar samrah (wanda hausawa ke cema, tawadar Allah).

Babyn hannun sa na kuka, ya fara lallashin ta samrah ta dube shi tana murmushi kallon ta yayi yace what happen?


Dariya ta shiga yi masa, tace well i think zaka yi kyau da raino!

You are going to be a good father my king.


Dariya Ammar yayi yace ke ko! Zaki gane. Miko mata babyn yayi yace give her her food.


Samrah na jin Ammar ya fada haka ta kalle shi, tace my king bana so na saba masu da shan nono fa!

What! Me kike nufi?

Ammar ya fada ranshi bace, my queen karkisa raina ya bace ok?

Are you kidding or what?


Calm down my king, samrah ta fada tana matsowa kusa dashi tace, abunda yasa na fada haka saboda yanayin aikina.


Kasan ba koda yaushe zan na samun zama tare dasu b..

STORY CONTINUES BELOW

Dakata samrah! Ammar ya fada ranshi bace, dole ne ki kulan min da yarana ok?

Aiki kuma ba zaki kara zuwa ba har sai kin yaye twins ok?

Kallon samrah yayi yaga tana hawaye matsowa yayi ya zauna gefen ta aje bbyn yayi saman cinyar ta,

Hannun sa yasa yana shafa bayan ta, goge mata hawayan ta yayi yace.

My queen am sorry, i don't mean to make you cry at all. Am sorry if i over reacted.


Kifa kanta tayi jikin shi tana kuka sosai, a hankali Ammar ya shawo kanta har ta fara breast feeding babyn din duka.

Tana gamawa yayi murmushi yace I love you samrah, murmushi ta mayar masa ta hada bakin ta da nashi ta shiga sumbatar shi.


I love you more sweetheart!


Aje babies din tayi saman cinyar ta tace my king wane suna zamu saka masu.


Ammar yace a sa sunan mami da Ammi ,Neelam and fatima.

Cike da farin ciki samrah tayi hugging dinsa tace nice choice, sai mu rika kiransu safa and marwa ko?

Ammar ya daga kai alamar eh.

Waya samrah ta dauko, Ammar ya dube ta, wa zaki kira?

Nafa kira kowa, murmushi samrah tayi tace nasan ka manta da kawalli, kausar zan kira na fada mata.

Kausar - kawata meye duniya? An manta dani ko?

Samrah - ke dallah can na sauka!

Kausar - garin kaduna koko ina!?

Samrah - kefa banza ce wlh, toh na haihu!

Kausar - haba dai! Alhamdulilahi Allah ya raya ,me aka samu ne? Ni ina ta ganin kamar sai next month ne ae, har ina fada ma fahad ya tara kudin super kawalli ta kusa haihuwa.

Samrah - (cikin dariya) aiko dai sai ku kara wata super din saboda twins ne na haifa.

Kausar -mashaAllah,besty Allah ya raya mana su, ina Ammar ne? Hop ya maki kyautar Abuja baki dayan ta. Nasan bakin nan nasa ya kasa rufuwa saboda farin ciki.

Samrah - ( cikin dariya) aiko dai ya kasa ya tsare.

Kausar - toh sai mun zo.

Samrah - toh a gaida fahad da baby girl.

Samrah na gama wayar Ammar ya dube ta,


lafiya yau kana ta kallona?

Dariya yayi ya matso kusa da samrah hannun ta ya rike yace gulmana kuka yi ko?

Ya fada yana murmushi, dariya samrah tayi tace ba ruwana ba gulman ka mukayi ba fa! Aje babyn hannun sa yayi.

yace wane kyauta kike so na baki?

Hannu samrah tasa ta kama kugu tace well ni Ammar na ke so, hop zaka saya mun shi ni dayana?


Dariya Ammar yayi sosai har sai da fararan hakuransa suka fito yace indai ni kike so already ni naki ne.


Wane abu kuma kike so bayan wannan?

Samrah ta daga kai alamar tunani can dai tace. Ina so ka so ni, so na har abada!


Next? Ammar ya fada yana daga mata gira, sona already na baki zuciyata,

Wane abu kuma kike so?

Ina so ka kaini umarah! An gama sai me? Ammar ya fada.

Aikin hajji samrah ta fada tana dariya.

Sai me kuma? Ammar ya fada.

Twins! Samrah ta fada tana dariya sosai.

No! Ammar ya fada yana kallon ta, shima dariyar yake yi.


STORY CONTINUES BELOW

Kukan babyn ne ya dawo dasu daga shirmen su.

Ammar ya dauketa yana jijjigata, miko wa samrah yayi.

Samrah ta kalle shi cike da shagwaba tace.

Ba yanzu na basu bane? Akwai fa zafi! Sorry Ammar ya fada kadan zata sha.

Samrah ta dauketa, tace chop chop kawai.

Sai babyn ta fara dariya, suma suka fara dariyar.

Samrah

Misalin karfe 8:00 pm sai ga su mama da mai martaba sun zo .


Mai martaba sosai yayi farin cikin ganin jikokin sa, kyautoka da dama dai na samu haihuwar twins din nan.

Ana gobe suna sai ga su Ahmad da su mami, da Ammi na da Abba kowa yazo suna, gidan mai martaba aka rada suna, mukayi shagalin suna Abuja.

Kausar ta zo, har saida tayi kwana biyu kafin fahad yazo ya tafi da su.

Khadija da zarah kam sati daya suka min kafin suka tafi. Ammi kwana biyu tayi ta koma cairo.

Bayan suna da sati biyu aka yi baikon Zarah da Dan sarkin zazzau.

Lokacin tana level 3,sai ta karasa karatun ta za'a yi biki.

Hutun Ammar na karewa ya kwashe ni muka je Egypt gidan mami, shi kuma ya koma Abu dhabi wajan aikin sa.

Yau ina kwance dakin Ammar na gidan mami, har bacci ma ya suma kwasa ta, sai naji kamar magana sama sama.

Tashi nayi na saka hijab, saboda vest ce da laggins a jikina. Ina fita naji muryar Ammar da Ahmad a palorn mami, sauri nayi na koma daki na shiga wanka, riga da skirt na atamfa na saka dinkin ya hadu sosai don yabi shape din jikina.

Gyele na yafa kalar milk na fashe jikana da wani Arabian turare da mami ta bani.

Ina shiga palor nayi sallama, ina shiga Ammar ya zuba min ido, gaishe su nayi, Ahmad ya dauki safa ,Ammar kuma ya dauki marwa suna masu wasa.

Dukawa nayi na gaishe da Ahmad ,na tambaye shi yasu khadija da fou'ad.

Samrah!

Mami naji ta kirani ,Na'am mami na fada kaina a duke, Abinci zaki kawo masu.

toh mami na fada ina shirin tashi.

A daki zanci naji Ammar ya fada blue eyes dinsa a kaina.

Tashi nayi na kawo wa Ahmad nasa dakin mami, na nufi side din Ammar da nasa. Ina shiga dakin na iske ya shiga wanka, ya ajiye safa a gadon yara marwa kuma a gadon mu.

Zama nayi na gyara masu kwanciya, kafin na shirya masa abincin sa saman kafet.

Yana fitowa daga toilet na tashi da towel a hannuna, na fara goge masa jikin sa.

Rike hannuna yayi ya zaunar dani cinyar sa yace I miss you!

Cike da shagwaba nace I miss you more habibi!


Tashi nayi ina shirin tashi daga jikin sa ya time ni gam, yana shakar kamshin jikina.


Please na fada ina kallon idon sa wanda yake cike da so da kauna just two minutes na fada ina shirin tashi, dauko masa kayan sa nayi, yana sakawa yace nayi kyau?

Ya fada yana murmushi, sosai ma kuwa na fada ina fesa masa turare.

Zama yayi gefen da nike yace my queen naga kin kara kyau kinyi fresh kodai bakya tunani na ne?


Ni duk na rame ina tunanin ku amma kuna nan kun manta dani ko?

Hannun sa na rike ina wasa dashi, nace haba my king kasan ba zamu manta da kai ba, kullun fa sai munyi waya dakai.

Peck Ammar yayi min a checks dina yayi murmushi yace ,da ku zan koma ,kallon sa nayi cike da shagwaba nace bafa haka mukayi da kai ba my king.

Wata biyu kace zamuyi, yanzo kuma kace tare zamu koma?

Dariya Ammar yayi yace uhumm dama nasani ae bakuyi missing dina ba. Kin fi son zama da mami ko?

Dariya nayi nace ni dai ba ruwa na. Safa ce ta fara kuka, Ammar ya dauketa yana wasa da ita, zama yayi kusa dani yace my queen me kike ba yaran nan ne?

Sai kiba sukeyi? Naji sun Kara nauyi.

Dariya nayi nace me kuwa nake basu, kasan su din chop chop ne.

Dariya Ammar yayi.

Na karbi babyn hannun sa, nace my king food is ready.


Yana gama cin abincin ,yasa na shirya su safa da marwa muka tafi outing cikin gari.

Sai yamma likis, muka dawo.

Sayayya sosai mukayi na kayan babies.


6


Pls vote below

Due to the coming of Ramadan ,I decided to shorting the story, but i decided to write epilogue for u guys. D epilogue will be two or three, it depends if am free.3rd person P. O. V

Bayan shekara biyu

Yallah habibties kuyi sauri ku gama cin abincin nan.


Samrah ce tsaye a kitchen a dining  tana kwashe plates din da aka gama cin abinci.

Safa! Ce ta mike tsaye tana magana cikin gwaran cinta ,tace momma zamu je school ko momma?+

Shafa kanta samrah tayi tace yes habibti! Hurry up.

Sweetheart! Ammar ne ya fito daga dakin shi cikin shiga ta Alfarma yayi kyau sosai, kai kace saurayi ne dan shekara 28.


Yana saukowa ya rungume samrah ta baya yace my queen i miss you soo much.


Peck samrah ta masa a lips dinsa ta dura hannuwanta saman kafadunsa ,

Murmushi Ammar yayi yana shafa cikinta Dan wata biyar yace .


How are you sweetheart umm.

Ya baby na? hope baya baki wahala?

Dariya samrah tayi tace sai kicking yake, like father like son.

Murmushi Ammar yayi ya rike hannun samrah yace come feed me babe am hungry Kin manta dani ko sai twins kawai kika sani ko? Ya fada yana pouting lips din sa.

Dariya samrah tayi, ta kama checks din sa, ta masa peck a lips, tace sorry my husband na barka da yunwa ko?


Momma momma!

Marwa ce ta fito da sauri daga kitchen bakinta duk chocolate .


Samrah na kallonta taga duk jikinta ya baci da chocolate ta kalli Ammar,

Ammar ya daure fuska ya ce what's wrong with you marwa habibti?


Tsogunnawa yayi daidai level din ta yace, ba na hana ki shan chocolate ba ?

Shunkuyar da kai marwa tayi tace zo kaji Abba, zuwa tayi daidai kunnan Ammar tace sowie Abba! 

Safa ma Tasha dayawa pls don't tell momma marwa ta fada tana me saka yatsanta tana lashe chocolate din hannun ta. Murmushi Ammar yayi ya daga ta sama yace.

Kar ki kara kinji ko?


Daga kanta marwa tayi tana dariya.


Abba mee too. Safa ta fada tana turo baki.

Ammar na jin haka ya daga su su biyun yana masu wasa.

Sweethearts come on.. Ku sauka ku bar daddy ya ci abinci ko?


Ammar na gama cin abincin sa ya, ya kalli samrah yana murmushi yace guess what?

Kallon sa samrah tayi cikin rashin fahimta tace what ?


Ammar ya ce wane kyauta zaki bani, idan na fada maki?

Promise me ba zaki yi tsalle ba, saboda baby na.

Hararar sa samrah tayi cikin wasa tace babyn ka ko babyn mu. Ammar na jin haka ya fara dariya yace sorry habibti.

Dariya sosai samrah tayi tace 😘 lot of love tana me Sara masa irin na sojoji.

Murmushi Ammar yayi yace.

Zarah ta haihu baby girl!

Da gaske! Oh my world ,tsale sosai samrah ta shigayi tana ma Ammar gwalo 😜


Binta Ammar yayi suka shiga zagaya palor din suna dariya.

Ammar na rike samrah. Ta kama cikin ta, ta saki wani kara.

My king cikina! Ammar na jin haka ya rude yana ta fada.

I told you habibti ki daina gudu kin gani kin sa cikin ki na ciwo ko?.


Ganin irin rudewar da Ammar yayi yasa samrah dariya, tace am just kidding my king.


Dariya Ammar yayi ,yana shirin fita da twins.

My king!

STORY CONTINUES BELOW

Samrah ta kira shi amm. Tayi shiru tana tunanin yanda zata fada masa mahaifin sa bashi da lafiya.

Matsowa tayi kusa dashi ta kama hannun sa tace wa su twins su zauna a palor ta dawo.

Kallon samrah Ammar ya shiga yi cikin rashin fahimta, what's wrong babe?

Murmushi ta masa kafin ta kama hannun sa suka shiga daki.

Ammar ina so yau zamu je katsina.

What !katsina!

To do what!  Todays ago fa muka dawo samrah.

Zaunar dashi tayi tace, jikin mai martaba ne yayi tsanani Ammar.

Dafe kanshi yayi yace why!  Why samrah!

Mahaifina bashi da lafiya ki kasa fada mun?

For what! Ammar ya fada cikin daga murya har jijiyoyin kanshi suna fita. Kallon sa samrah tayi cike da tsoro, gani tayi ya dawo mata old Ammar sak dan babban gida !

Tashi samrah tayi ta rike shi tana kwantar masa da hankali, har ya sauko daga fushin da yake yi.

Hannun samrah Ammar ya rike, ya ce, my queen ki hada mana kaya yanzu nan.

****************;*****************

Misalin karfe 10:00am na safe su Ammar suka shiga garin katsina, fada suka sauka, gida duk a cike jikin mai martaba yayi tsanin sosai gaba daya family an taro.

Zarah ta zo itama da baby girl dinta.

Abban samrah da Ammin ta sun zo ganin jikin mai martaba.

Side din mamin Ammar samrah ta kai twins ,wajan fou'ad yaron Ahmad.

Bayan wata shida

Ammar ne kwance a gado yana wasa da baby boy din su da ya ci sunan marigayi sarki zaid, mai martaba da ya rasu .

Samrah ta shigo dakin da jug a hannun ta.

Tana shiga ta zauna bisa gado tana kallon Ammar da babyn ta zaid.

Hawaye taji na zuba daga idanun ta, what happen to you my queen?

Murmushi samrah tayi har dimple dinta ya lotsa.

Goge hawayen ta tayi tace thankz for everything my king, thanks for the love and....

Ammar ne ya rufe mata baki da kiss din sa me rikitar da ita.

I love you samrah, so much babe, I can't live with out you dear you are my hayati.

Thankz for giving me dix wonderful family.

Momma momma!!

Twins ne suka shigo da gudun su.

Momma uncle safwan ya zo cewar safah.

Samrah na fita da saurin ta tayi hugging safwan.

Ya kara girma ya zama big boy.

Suna gaisawa, Ammar ya shigo palon suka gaisa.

Safwan yace amm ya Ammar ina so zanje kilisa da dukin ka.. Safwan ya fada yana sosa keya.

Murmushi Ammar yayi, ya ce safwan kenan har yanxu kana nan da son doki kaje ka fada wa malam bello ya gyara dokunan sai mu fita tare.

Cike da murna safwan ya tashi tsaye ya kama hannun twin suka fita.

Ranan juma'a suka koma katsina aka nada sabon sarki, Ammar shine wanda ya gaji mahaifin sa.

Saboda Ahmad bashi da ra'ayin mulki. An sha bikin nadin sarautar Ammar kai kace wanin bikin sallah ne. Manyan sarakuna da dama sun halarta taron.

Murna sosai samrah tayi.

Ammar dinta ya zama sarki.

My queen!

Ammar ya shigo dakin yana kallon samrah, tunanin me kike yi?

Ya fada yana karban zaid daga hannun ta yace my boy what happen to momma? Ya fada cikin muryar yara, har abun ya ba samrah dariya.

Hugging dinta yayi ta baya, sai ga su twins sun shigo da gudu.

Abba yau na hau doki marwa ta fada tana hugging Ammar ta baya.

Tsugunawa yayi daidai level din su ya masu peck a check.

Kafin yayi hugging family dinsa yana me cike da farin ciki.

I love you dan babban gida

Samrah ta fada tana murmushi, hanunta Ammar ya rike gam. Yace I love you too my queen.1

Bayan nadin sarautar da aka da sati biyu. Suka tafi ummarah tare da yaran su.

Alhamdulilah this is the end of my novel hop you enjoy it.

Post a Comment for "DAN BABBAN GIDA COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...