CIKIN DA BA,A SO CHAPTER B KARSHE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

CIKIN DA BA,A SO CHAPTER B KARSHE

CIKIN DA BA,A SO CHAPTER B KARSHE

- - Post a Comment

 CIKIN DA BA,A SO CHAPTER B KARSHE


*CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)

     

*@HUMAIRAH B MELODY*

_*ALLAH KAINE GATANA Allah yabarmu damasu sonmu Amin*_❤😘👍🏻
Kukane yaci karfinta jawaheer tace

“Kiyi hkr Atee komai Nada lokaci kuma mai hakuri mawadaci baacewa hakurinka yakare saidai ace k'aryanka ta kare, kuma ciki baza'a zubar dashi ba saikin Haifa duk wani cin kashi kiyi hkr ki dauka Allah ba azzalumin kowa bane sai Wanda yaso ya zalunci kansa Atee jarabawa ne Allah yabaki ikon ci Banida abunda zan baki kuma karki sake Kiyi wannan shirmen” karaf ta kashe wayan ta kara sautin kukanta jin hakane Yasa Mash kara volume tunda batada aiki saina shan disco,

Laulayin Atee saida yakaiga bata iya koda tashine bare kuma cin abinchi gashi daga ita sai mash a gida ga yunwa datake Neman yimata illah saboda tsabar zalunci mash ta dauke wayarta ta kashe karshe taje gidansu tabar Atika Mima ce ta shirya yaranta sukaje gidan Atika suna shiga Mima ta saki jaka a kasa jibis  ta fara jijjiga Atika cikin rudani tafita makota Neman masu taimaka mata haka suka kaita Giwa Hospital Nan akasa mata drip Tuni Mima takoma gida ta ajiye yaranta wajen binto mai aikin ta, sannan ta kara figar mota sai gidan Atee tana zuwa taga MASH wani banzan kallo tayiwa MASH tace

“Amma Allah yayi azzaluma bantaba ganin muguwar kishiya irinki ba, ban taba ganin Matsiya ciyan Kishiya ba sai Yau Tabbas wasu mata banga laifinsu Idan sukace ma kishiya Tinkiya bakida maraba da tinkiyar Ace Atika batada lafya ace kin kasa kaita Asibiti? Saboda haushin rashi koh bari baki taba yiba bare asa ran zaki haihu? Oh I see toh kisani Allah saiya saka mata kuma banga laifinki ba laifin MD fauzi mijin ku nagani dayabarki yasa miki ido kike yadda kikeso amma Allah ya rsbawa aya zaki da dani kike kishi na rantse da tuni mun Dade da kashe kanmu don wallahi sai munyi mutuwar kasko”

mash tana zaune koh kallon Mima batayi ba Saima kara volume datayi tuni wata zuciya ta dibi Mima tayi wajen TV ta katse wayan tace

“Nasan cewa kin fito daga gidan marasa mutunci bare kuma akaiga tarbiya koh da mijinki ke miki magana haka zakiyi mishi wayar Atika zaki bani?”.

+

Mash tace

“Idan kin gama rashin kunyan naki kina iya shiga dakinta kiduba don ni banida lokacin ki bare na wata kwari” saboda zuciya irinna Mima tuni ta shako MASH tace kibini a sannu nifa haifaffiyar tsakiyan tudun wada ce Yar layin makafi duk wani iskanci da rashin kunya kinsan ya kare a kanmu kisani duk wani rashin kunyanki toh ni uwarki ce” sannan ta jefar da ita kan kujera Dakin Atee ta shiga ta dauko wayar tafito ta fice ta shige Motarta sai Asibiti tana isa ta kunna wayar Atika abunda tafarayi shine kiran MD fauzi amma kusan miss call biyar yaki dauka, Mima ta Ciro wayarta takira Mijinta bugu daya ya dauka yace

“My love Lafya naga urgent kira haka ? Yara duk Lafya daiko?” murmushi tayi

“My life So nake ka kiramun azzalumin abokinka MD fauzi bantaba ganin mugun mutum irinsa ba kasan Dear Yau kasan nacema zani wajen Atika Idan kaga condition din dana taradda ita saika tausaya mata kuma ita kadai a gida MASH tafita gani a Asibiti kwance take ana sa mata drip ciki gareta Gashi yadda nakeji Likita yace

cikin baya cikin mahaifa yana wajen mahaifa sai anyi aiki an maida shi cikin mahaifa Nakirashi yaki yayi picking”

MD bello yaba matarsa hakuri yace zai kirashi yanzu

Jingina tayi da bango tana wuci tana jimami wane irin rayuwane wannan daga mace nada ciki shikenan aikinta ya kare? Oh noo wasu mazan azzalumai ne wallahi Allah yasa mudace Amin

wata dabarace tazowa Mima takira Baba tasanar da ita takira jawaheer tace tasanar Atee bata lafya saboda asamu mai zama da ita Saboda ita taje ta kulada yaranta Kafin rana ta fadi baba tazo chan saiga jawaheer babu Wanda yagane Atika saboda tsabar rama,

Baba tayi fada tayi fada Mima tasanar da ita komai ai baba tuni ta hau adaidaita sai bariki gidan MD tana shiga taji disco yana tashi buga kofa takeyi amma ina MASH tayi nisa bataji wani yaro baba tasamo ya kashe mata wutar gidan, Ana kashewa Mash tafito a fusace tace “waye?”

Ai kawai karo taci da Baba ai tuni tayi turus acikin ranta tace Yau na kade da masifar wannan tsohuwar,

Baba tace

“Uwarki ce yar matsiyata Allah yayi wadaranki wallahi inajin saina je gidanku na sanar dasu irin ta'asar dakikeyi Abokiyar zamanki na Asibiti koh kiyi jimami wato murna kikeyi ta tafi tamutu ba matsalarki bace amma Kinyi Asara duniya da lahira saboda baki taba kashin daba koh toh kiyi gaggawan dafa mana abinchi intafi dashi Asibiti kuma kisani inanan gidan sai Atika tasamu sauki girkin safe daban na rsna daban na dare daban bakida sauran hutu matsamun in wuce”

Ciki baba tashiga ta ajiye ledar kayanta MASH kuwa ranta ba karamin baci yayiba amma yazatayi tunda ta Haifa mata abunda takeso?....*CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)

     

*@HUMAIRAH B MELODY*
91-95

Kitchen ta shige ta daura Girki

Shiko MD bello tuni yakira Abokinsa yasanar dashi halinda Atee take ciki amma da mamaki saiya nuna koh a jikinsa MD bello ba karamin haushi yajiba yace

“Mutumina karka tafka babban kuskure kasan cewa amana ce a gareka kuma sai wanda Allah yaso yake azurtawa da haihuwa”

Dakata MD bello banason shiga shara ba shanu don't interfere in my family issues you hv ur house I hv mine so pls let me be I don't have your time for now sai anjima,

Karaf ya kashe waya abunda ya batawa MD bello rai kenan yace tabbas kanada right din gayamun koma meye amma kuma niba azzalumi bane irinka, office yake ga AC amma gumi yakeyi wayarsa yaciro yakira Mima yasanar da ita komai ranta yabaci k'warai amma saita nuna cewa Komai ba komai bane Girki tayi takai musu Asibiti koda taje Atee ta farka babu abunda takeyi sai kuka tace

“Namiji Dan kunama ne Mima Kiga yadda ya maida rayuwana amma har yanada grantee na wulakantani dubi yadda na koma Kamar wata tsumagiya? Amma duk bai isa Abban kamal ya tausayamun ba Allah Kaine Gatana kasa wayannan yara suji kaina bayan sunzo duniya”Kuka takeyi Kamar ranta zai fita takara da cewa

“Mima Likita yace sai anyi Dan karamin aiki saboda cikin yana wajen mahaifa amma duk wannan bai isa namiji ya tausaya maka ba wane irin zamanine wannan yaro da maxa ke gudun haihuwa?”

Taci gaba da kuka har wata mata mai jinya ta matso tace

“Yarinya akan me kike kuka don miji ya wulakantaki kan ciki? Kisani wata rana kece me jin dadi kiyi adu'a Allah ya baki nagari wata rana kukannan dariya zai zame miki ai duk wacce ta haihu ita mai arziki ce wallahi wukanci kuma kici gaba da hkr wata rana sai labari ”

Atika ba karamin dadi tajiba tayi murmushi tace

“Ngd baba Naji dadi k'warai da gaske Allah yaba Wanda kike jinya lafya” Amin sukace Mima abinchi ta ajiye tayiwa Atee sannu sannan ta wuce gida da niyyan zata dawo gobe Mima zata fita Atee tace

“Mima wai MD fauzi yasan halinda nake ciki kuwa kudin Asibiti da komai ya aiko dashi? Ga magani an rubutomun zan siya” Mima kawai sai hawaye dake kwaranya a idanunta tace

“Karki damu duk abune mai sauki Allah ya rufa Asiri” share hawaye takeyi lokacin baba mahaifiyar MD tashigo tace

“Mima lafya kike kuka? Gayamun abunda ke faruwa Atikar lafya take?”

Mima ta kara rushewa da kuka takasa cewa komai Dakyar baba ta lallasheta sannan tabata lbrin komai tun daga farko har karshen abunda ke faruwa tsakanin Atika da MD fauzi akan haihuwa.

+

Baba tayi salati ta gaida ubangiji tace “Au hakane Wato shiyasa waccan juyan tafi mishi ita koh? Hmmm lallai biri yayi kama da mutum zanyi maganin Abun”waya taciro tace “dubomun lambarsa zakiga ansa danda”

Mima ta lalubo ta kira mata bugu daya ya dauka yafara gaisuwa

Baba ta dakamai tsawa tace.

“wallahi karka bari inyi maka baki don duniya sai tayi maka zafi Karka bari ince tir akanka wallahi saiya bika MD har kakai matsayin da Allah zai azurtaka da haihu kace bakaso? Wallahi wallahi da ace Allah ba kai kadai ya azurtani dashi ba Wallahi da sainayi dozen bari kaji naji duk wani Abu da kakeyiwa Atika toh kayi gaggawan zuwa Kaduna inason ganinka Yau dinnan basai gobe ba Wato waccan juyan tafi maka uwar yayanka koh toh kasani bazata taba faranta maka raiba matukar bata Haifa maka yayaba kuma Kamar Malam yaji wannan batu”

Baba kiyi hkr zuwa wani sati insha Allah zanzo

“Habawa yaro umurni nake baka ba shawara ba kaji dakyau” karaf ta kashe wayar Abun duniya ya ishi baba amma batada yadda zatayi yarane ka haifesu baka haifi halinsu ba........

Sallama sukayi da Mima baba ta karasa

“Sannu Atika sannu kinji Allah yayi miki albarka” Jawaheer ta amshi kulan abinchi ta ajiye baba ta mance da Mash suke Abun mamaki taki shigowa Baba tace

“Ina mashahura da ita muke kinga yar tsiya taki shigowa koh?” Jawaheer tace

“Baba kidaina tada hankalinki akanta fatanmu shine Yaya ta samu sauki shine babban burinmu yanzu” Hakane jawaheer yanzu yaushe za'ayi aikin?

“Likita yace gobe da Asuba insha Allah”

Allah yakaimu inji baba A Daren baba suka koma da mash, mash taci zagi da masifa har saida taji ba dadi, washe gari da Asuba Saiga MD fauzi misalin karfe 7:00 am nasafe yana shigowa jiyayi baba tanata masifa sallama yayi jiki ba kwari yace “Baba ina kwana an tashi lafy?

Baba tace

“Dakata in gama da wannan shegiyar matar taka wacce batasan darajar Dan Adam ba juya kawai aci ai kashi kisani cutar ki yakeyi kiyita shan maganin hana daukan ciki Wallahi wata rana koh bari bazakiyi ba bare ciki kitashi tun Asuba kidaura girki kin kwanta ai bakida sauran Hutu kuma daga Yau kai zaga dinga kwana a Asibiti saboda kai kayi mata ciki kai zakayi hidima da ita Niko da wannar juyar muna nan saina gyra mata zama da hankali ”

MD fauzi hkr yake badawa saboda uwarsa ce ta chanchanci duk wata biyayya,

ALHAMDULILLAH anyi nasaran yin aiki Atee tasamu sauki ciki harya girma Haihuwa kadai muke jira.MD fauzi ya Gina musu katafaren gida ya fitar dasu daga cikin bariki kowacce da bangarenta amma falone kato ya rabasu Kowacce abinchinta take dafawa saidai Idan miji yana wajen ki Atee ce zaune Itada kanwarta jawaheer wacce aka bata tun cikin na Dan tayi daga Asibiti kawai akace ta zauna da ita, MASH ce ta kure musu gida da waka gashi jawaheer tsnada miyagun iska Wanda basuson waka Ai tuni idanun jawaheer sukayi jajir tafara runtse ido tana dode kunne ai tashi guda ganin jawaheer nayi tayi inda Mash take tana isa ta shaketa tace

“Ke kinzama shedaniya bakida wani aiki saina jin waka koh? Toh Yau zanyi maganinki ai tun misalin karfe biyu jawaheer ke dukan Mash har misalin karfe Hudu gashi Atee ciki yayi girma sai an taimaka mata take tashi gashi wayarta bata kusa da ita, Mash tanada mai aiki safara'u kuma tayi mata aike kasuwa tana shigowa taga yadda Jawaheer ke dukan hajiyarta ai tuni tayi kanta amma ina jawaheer ta hada da Safa tayi musu shegen duka saida taga basu motsi kannan ta kyalesu ta barsu kwance tana zuwa daidai shiga falo saita fadi itama ranan Atee taga tashin hankali kwarai gata bata iya komai haka nakuda yakamata Jawaheer kuma a kaida sai tayi awa daya kafin tasan me duniya yake ciki, ni humairah nace Kara kaka kaka Haka Atee ta samu dakyar ta dauko waya takira MD fauzi ya dauka yace

“lafya kike kirana Ina meeting kikira anjima, Atee tace Nakuda nakeyi MD ka kiramun nurse tazo ta dubani MD yace

“Mtwww banida time dinki keda kikaji kika gani ki haihu da kanki aiba saina taro mutane ba” karaf ya katse wayar Abun haushi da takaici Atee tuni ta samu ta rarrafa zuwa bayan dinning ta dauko reza tayi rashe rashe tana ta Abun nishi cikin ikon Allah ta haihu nidai bansan meta haifaba har yanzu, chan naji tskara wani kara saiga Na biyu bayan minti Goma sha biyar takara haihuwan wani Niko zare ido nayi nace Allah mai iko, daga bisani cikin niimar Allah saiga Uwa tabiyo baya Ajiyar zuciya tayi yara sai yanka ihu suke haka ta yanke musu cibi ta yunkura ta mike Niko Humairah nace Allah ba azzalumin kowa bane kuma shi Allah mai jinkan bawansa ne,

Wani zani ta janyo ta goge jikinta sannan tashiga daki ta dauko Zannuwa ta nan nade yaran, Daidai lokacin Jawaheer ta tashi tace Aunty bacci nayi Atee tace

“Eh mana bacci kikayi”

J tace

Aunty ina cikin tace

“Gasu a tsumma” zare ido tayi tayi wani irin ihu tace

Aunty kina nufin kice Yara uku? Tab inajin sai MD fauzi yaji tsoro Cikin da bayaso gasu har su uku inajin saidai ya ysnka su ya zubar, Atee tace

“Kiramun yan gida kije kisa ruwa inyi musu wanka kinsan banida kayan daxan sa musu saidai na kamal Donni bansan mena haifaba har yanzu yara koh sunjisu a wata duniya sai tsala kuka sukeyi, Ai cikin sauri Jawaheer tafara kiran gida tana tambarawa harda Mima, Atee tace

“kiramun MD fauzi kisanar dashi *CIKIN DA BA'ASO* Sunzo duniya”

dayake jawaheer batajin magana yadda akace haka tace tabarshi cikin damuwa sunzo duniya? Tambayan daya bige dayiwa kansa kenan Niko humairah da sauran masu karatu mukace kwarai sunzo duniya Allah ya nuna maka ikonsa kai baka isa ka hana mai faruwa yafaru ba.

Jawaheer tabisu daya bayan daya tana dubawa cikin ikon Allah duk matane Atee tace Alhamdulillah Allah na gode maka,

Haka tayi musu wanka ta shiryasu cikin kayan maza Itama tayi wanka kafin mutane yan nesa sufara zuwa Ai Mima tuni ta hallaro tana ganin yan uku tayi wani irin Ihu wanda ya farfado da Mash da Safa yar aikinta,

“Atee kece da yan' uku? Allah yayi gaskiya Allah ya karawa Annabi daraja kigani Cikin da basso suzo duniya ba kinga Abun Allah daman hk Allah yake tsara lamuransa” daukan su tayi tana kallo tace “Atee bakisai kayan baby bane saina kamal?”

Atee tayi dariya tace “Kinfi kowa Sanin halinda nake ciki abunda baa maraba dasu taya kike tunanin zasuyi wannan darajar ta asai musu kaya? Kema kinjiki da wani zance tunda Allah yarabani dasu lafya toh ya gamamum komai a duniya”

Mami ta jinjina kai tayi shuru babace tareda Bb kamal suka doka sallama wani tsalle bb yayi ya rungume Mummy sa yace “Mum ance yan uku kika Haifa hakane kodai Aunty J wasa takeyi gama tasaba yimun haka?”

Atee taji dadi ganin Bb kamal yayi hankali sai wani girma da kyau yake karawa tace

“Kwarai kanni uku nayi maka mata Kaine mahaifinsu baysn Raina karka sake kabari suyi kukan rashina kaji Dan albarka?”Bb kamal yace

“Naji mum amma fatana kiyi tsawon rai saboda inkaiki makka da umrah kije London kije Paris Mum Idan nayi kudi dake da baba England zan kaiku kuci gaba dazama Mum inada buri Dari ba daya a duniya Fatana Allah yayimun arziki”

Kowa saida yayi dariya baba kuwa har saida tayi kwalla saboda Kamal mutum ne mai imani da tausayi tun yana karami yasan meya kamata

“Atee sannu Ashe abunda aka kunso kenan Allah yayi musu albarka yarayasu tafarkin addini yakara miki lafya hakuri da juriya tabbas ke macece kawo yaran”

Haka aka mika mata daya bayan daya nidai naga bakinta na motsi inajin adu'a take musu, Amma tozalin datayi da Kayan yaran ysbata mata rai tace “Atee kina nufin bakusai komai ba? Atee tayi shuru

Magana nakeyi kinkira uban nasu kin sanar dashi kin haihu?”

Atee tace Baba ankirashi Amma baice komai ba, baba tace

“Lallai ”

Wayarta taciro takira takira amma ina Yanata harka da wata budurwarsa Egili daya hadu da ita a Akure ya maidata tamkar matarsa a gidansa take kwana take tashi saida yadawo hayyacinsa kannan yaga miss calls din Baba cikin rudu yace “Oh my God!!!! Baba takirani itako Egili sai wani shafashi takeyi takoh ina abunka da jaraba tuni yakara komawa ruwa saida sukayi round yayi biyar kannan yakira baba yace

“Hello”

Ai kafin yakai ga magana tace

“Dakata Mara mutunci MD wai meka zamane a duniya mekake tunanin ka zama wai aikin soja haukane kanka aka farane? Wai inasu IBB, inasu abacha, inasu buhari? Ince sunyi aikin nan kafin kai? Matarka ta haifi yan uku amma babu kayan sawa MD wane irin zuciyane dakai? Tabbas inagab da in taka maka birki ka basu kakinsu tunda naga fitsararka tayi yawa”

Shuru tayi

Yakasa magana yar uku? Atee ta Haifa Meyasa? Taya zanfara basu tarbiya? A shekaruna yara hudu? ai sunyi yawa meyasa Atee batajin magana?

Duk shi kadai yake wannan zancen da zuciyarsa

“Idan ka gama tunani ka turo kudi inje kasuwa inyo musu siyayya zuwa anjima”

“Baba kiyi hakuri kinji kiyi hkr zaa turo amma Kibari Mashahura taje ta siyo mana kyaje da kanki?”

Baba tace

“yimun shuru Matarda take bakinciki tunda nashigo gidan tazo ta gaidanine? Koh taga yaran nifa zan iya rabaka da ita saboda rashin kunya da rashin kyautatawan da batamun a matsayina na uwarka”.+Baba za'a turo insha Allah

“Yaushe zakazo?”Gaskiya baba inada aiyuka saboda kinsan yadda aikin yake babu Hutu amma zansan yadda za'ayi koh bayan sunane nazo Abokina MD Bello zaizo saiyayi musu huduba Amma inaso daya asa mata sunanki, daya kuma Sunan mashahura, sai Sunan Umman Atika,

Baba tayi salati tace

“Yau naga sanabe meye gamin Kudu da gabas? Wacece mashahura? Dankari Matarka itama tanada hurumin zabawa yayanta suna don haka Kowa ya zauna a banzan sa” Toh yace misalin karfe Biyu saiga alert dubu Dari ta wayar Atee, Tuni akaje aka cire akayo siyayya nagani na fade Sannan aka siyo Dan akuya aka fede a kasuwa aka gyra akazo akayiwa Atee farfesu mai raida lafya cikin hadin harda Origano, Rosemary, White pepper, Duk don karin lafiyarta Mash dai ita da kanta takai kanta Asibiti aka dubata tana dawowa tashiga sasan Atee tace

“Kinyi nasaran sa Kanwarki ta dakeni toh kisani bashi Kikaci saina miki kare jini biri jini cikinnan Wallahi sainasa kin haifai lokaci baiyi ba” agaban mutane babu kunya ba tsoron sarkin gari hmmm Lallai  J ce ta tashi tace

“Ke karamar bora ce ke kin isa inanan kiciwa yar uwata mutunci koh zarafi nooo Idan kinacin kasa toh ki kiyayi na shuri donni uwarki ce a rashin dabi'a”

Jawaheer kul kika sake zaginta a gabana koh ba komai abokiyar zamana ne  MASH gani ki dakeni Wallahi bazance dake komai ba amma kisani ni kadace mai lambon ban tsoro Idan Kinyi Yau saboda darajar mutanen nan gobe kikayi Kinsan Allah shizai ceceki Ciki kuma sainanda shekara biyu Idan na sake wani saikiyi sanadin zuwansa duniya amma kisani Atee bata varin kota kwana saukinki daya na haihu sannan hakurin nan nawa yananan kafin in irga biyu kibar dakinnan kafin Kiga ainihin kalana, Tunda na sauka lafya duka kin dingi shan shi kenan fitaaaaaa!!??!”

Aiba shiri Mash tafita Abun duniya ya isheta gashi tsnason haihuwa gashi bataso MD fauzi yadaina sakar mata kudi tana holewa, gashi ysnzu baya kusa Shiyasa take fita tana kwana da mazan banza amma kidasu bata taba cikiba kuma basu amfani da condom, itakadai ke wannan tunanin Kowa cikin sasan Atika saida yayi Allah wadai da halin mash, baba tafito tace

“Mashahura ce tashigo koh? jawaheer baki burgeni ba Dakin mata duka tunda batada kunya da inanan dasaina dakata ”kowa dariya yakeyi  Ana jibi suna saiga MD bello dashida matarsa yayiwa yara huduba ta karshenne ya tambayi Atika wani suna takeso asa mata tace

Halimatus Sadiya Wato Gimbiya uwar gida a gidan MD bello,

Wani tsalle Mima tayi takasa rufe baki tace

“Atika banida Abun cewa sai godiya Allah ya rayasu musha biki ”

MD fauzi yaturo kudi bansan iyakaba akasai raguna uku aka harda na bayan suna intaji kwadayi Mash ce takama Bbkamal tayi mishi shegen duka Wanda saida tafasa mishi kai da baki Ran baba yayi karshen Baci Atee kuwa tausayi ysbata Jawaheer kuwa tuni ta nufi Dakin Mash amma saitajishi a rufe bugun duniya taki budewa Baba tace

“Tabbas sai Yau na gane cewa keyar bakin ciki ce da jikokina kisani Yau zamanki a gidannan yazo karshe tuni aka kaishi Asibiti ga yan suna kowa ransu a bace Mima tace

“Atika kina hkr da wannan mata danice ai wata rana gobara xamu hada acikin gidannan” Atika tace Babu komai Wallahi Rayuwa ce kuma kinsan *WANI GARIN YAFI GABAN KUNU* Ita kanta tasan cewa Nagaba yayi gaba nabaya sai tsintar kura bakin cikine amma bakomai, Mash kuwa yini akayi a daki tuni jikin bb ya rude da zazzabi baysn yan suna sun watse tuni akayi Asibiti dashi baba kuwa kiran MD fauzi tayi tace tsnason ganinsa gobe gobe batareda bata lokaci ba.

Yara sunci sunayensu sunyi goshi don Mima da mijinta akwati guda sukayi na kayan takwara.

Washe gari Jirgin safe MD fauzi yabiyo misalin karfe 9:00sai gashi yana shigowa yayi ido biyu da Atika sai yaji sonta har cikin ransa Idan ya tunada yaya uku saiya murtuke fuska, Atika tayi saurin ajiye Mima karama tayi mishi sannu da zuwa daga mata hannu kawai yayi ya wuce sashensa.....+*CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)


  

     PART TWO

     Continuetion

      

     

*@HUMAIRAH B MELODY*_*This Humble page goes to my one and only darling AUNTY SIS💞 you are such a Kind woman I ever seen and sighted Loving will always be my portion May Allah continue to Guide and protect you for me😘*_LYSM
6-10

Atika yayi saro Abun duniya zai fara damunta Wata zuciya tace

(Kema dai Idan da Sabo kin saba meye na damun kanki inxaki rungumi yaranki ki runguma yafiye miki) ajiya zuciya tayi Hmmmm

Lokacin baba ta tashi tun Asuba Tace “Naji  Muryan wannan yaron shine koh” Atika tace

“Eh shine”

Ta goya Mima ta saba mother dayake jawaheer ta dauki sabil suka shige daki Baba dai dagajin amsawan da atika tayi mata tasan dakwai wani kullin daya faru BB kamal ne yashigo kansa daure da bandeji Daidai da fitowan MD fauzi yayi tozali da BB yace

“My Boy kaine kayi girma haka? Allah yayi maka albarka waya jimaka wannan raunin a kai?” yafadi batareda yaga baba ba daman kadan take jira tace

“Wacece banda shegiyar matarka tana bakin ciki gida yacika da jikoki na shine takeso tayi ajalin BB kamal dakamashi tayi mishi duka harda fasa mishi kai tunda yazo duniya koda wasa ban taba kaishi chemist ba saigashi waccan kaddararra taja mishi toh kasani Yau dinnan sai Mashahura tabar gidannan matukar Nina tsugunna da haifeka don gaba dàuki daidai zata dinga musu tana kisa”

MD fauzi zufane kawai yake keto mishi cikin ransa ji yake Kamar yasha guba ya mutu saboda anyi mishi zancen rabuwa da MASH tsugunnawa yayi yana share kwalla yace

“Baba kiyimun afuwa kiyafemun inason Mashahura tana kyautatamun ta yadda baki tunani  kiyi mata afuwa bazata sake ba”

Baba ta mike tsnacin goro tace

“Koh gindin gwal gareta zama da ita Yau ya kare littafi ta dauko da biro maxa ka rubuta mata saki uku kin gani babu kome koh biko”

Mashahura tana tsaye tana kallon ikon Allah shin MD xai iya sakinta? Koh kuwa

“Amshi nace”

MD fauzi yace

“Baba Addini ya haramta saki uku a lokaci daya Baba zan iya sakin mashahura saki daya shima a bisa umurninki dakika bayar baba karki manta Allah dakansa yace duk lokacin da akayi saki k'asa da abunda ke cikinta saisun girgiza kiyi mata Afuwa kiyafe mata”

Daka mishi tsawa baba tayi tace nabaka minti biyu kayi abunda yakamata ke kuma ta nuna Mash nabaki minti biyar ki kwashe yanaki atafi gidan tsoho, Haka MD fauzi ya rubuta saki daya yaba Mash, tuni mash tafadi kasa tana kuka wiwi Baba kuwa sai turata takeyi har cikin dadi ta hada kayanta tana kuka tana cewa “Baby yanzu kazabi kasakeni ina sonka inason zama dakai pls ai baba saida takaita gate kannan ta dawo Jawaheer kuwa sai gwalo take mata Baba tashigo tasamu MD fauzi zaune ya zabga uban tagumi tace

“Aure babu taje chan ta karaci tsiyarya Kai kuma Idan zaga rungumi matarka mai mutunci gwara idan koh ba hakaba kadinga haduwa da bakin ciki, tun farko daman ni banso aurennan ba Dubi yadda tajiwa yaro ciwo ka kasa magana toh bari kaji Wallahi wallahi kar inji kar in gani kadawo da ita” fuuuuu ta wuce takira Safara'u tace daga yau atika zakiyiwa Aiki raino da kulada gida kinji koh Safa tace taji

Jawaheer da Saga su sukayi aikin Suya dayake kowa ranan suna aka watse bayan an gama akayi rabo.

Mash tana shiga gida tafara ihu tana tashiga uku mum nabani Na lalace Kinga abunda MD fauzi yayimun yasakeni mahaifiyar sa tasa ya sakeni Mum ce tafito tace “Dakata kiyimun shuru kukan me kikeyi kinsan cewa duk Wanda yasai rariya da kudinsa ai yasan zatayi zuba tun tsawon lokacin da kikayi aure wakike gani a gidanki inba kinzo ba kar wuyanki yayi kauri yanzu kizo kina kuka? Hmm sannunki da zuwa Ga dakinan ki share ki zauna ga duwawunki gana kanninki Stupid, Abunda kikayiwa Saif ne shi Allah yake nuna miki ishara Kuma karki taba tunanin zaki koma ma Saif  don saura wata biyu bikinsa da kanwarki Xarah”

Wani kuka takara saki nida humairah nace Allah shi kara Alhaki ne yake bibiyan Ki.

*BAYAN WATA HUDU*

Akayi bikin Saif da kanwar mash taji haushi da bakin ciki,

mash harta fita iddah ba MD fauzi babu labarinsa Komai yabi yadami Mash tarasa mafita tuni ta tunada wata kawarta Laila ai shiri tayi don zuwa wajenta.

Atika gida yayi mata sanyi dalili kuwa rashin mash MD fauzi yadawo yana kulata amma fa yanakan bakansa na rashin son haihuwa, ita Kuma tayiwa kanta alkawari haihuwa sai Allah ya tsayar mata da ita, Atika ta koma Kamar yarinya life irinna turawa Har jawaheer kunya takeji yadda take kulada MD Idan yazo sometimes sai sunyi gyran murya suke shigewa ciki subarsu da yara saboda Allah yayiwa Atika ni'ima ga MD fauzi Hariji Wanda mace bata isansa kuma Atika itake iya jurewa banda mash biyu tagaji Muna murna Ashe bako na bayan gari Mash dai saida tashiga tafita ta janyo tsohon mijinta don bamace mijiba saboda sai an sake sabon daurin aure,

Mash dai wajen Boka Laila ta kaita Dagani kasan kazami ne haka tafadi bukata shima yafadi tasa bukatan, shidai boka mande kasur gumin Mushiriki ne mazinaci karo na biyu da mash takoma ita kadai takoma tace so take Atika ta wulakanta yace angama saidai da sharadi

“Sai Kinyi tsirara haihuwar uwarki da ubanki kishiga waccan dakin ” Mash tace “Ranka yadade dakin babu haske ”?

Yace “kwarai haka zaki shiga matsawar kinaso bukatarki tabiya”

Haka ta dinga tubewa Nida har kunya naji Shiko mande sai lashe baki yakeyi Sai lashe baki yakeyi chan naga ya zabura Ya damki Dukiyar fulaninta Gasu sunyi tantsan tantsan Ai tuni naga idanun boka sunyi jawur Kamar garwashi, mash kuwa jikinta sai rawa yakeyi don tsoro tuni ya daka mata tsawa yace

“Shiga Shiga shiga!!???” haka mash tashiga Ai boka ya leko yaga bakowa ai tuni ya afka Dakin Niko Humairah don imba mai karatu lbri saidana bisu tunda yashiga yake shafata y koh ina ga wari dayakeyi MASH sai toshe fuska takeyi.


+

Hmmm Allah kayi mana tsari kuma irin wayannan bokayen Aikinsu yafi karbuwa nidai kubiyo yar Mutan zazzau don nidai na tsorata da lamarin mata.Atika dai abun baa cewa komai Baba ita kanta takasa cewa komai illah hkr da take ba atika akan rayuwa babu yadda bata zuwa ma bawa Ta fawwalawa Allah shine buwayi gagara misali, Atika ta share daki ta zauna MD fauzi baisan cinta ba baisan Shanta ba Malam Lawal kuwa shine yaxamewa Atika bango sai kuma yan'uwanshi dasuke iya kokarinsu akan yayanta, Malam Lawal Kullun cikin adu'a yakeyiwa dansa don abun ya girmi kaka da kakanni.

*BAYAN WATA GOMA SHA BIYAR*

Atika ta yaye yaranta amma duk lokacin data kallesu saita zubda kwalla masu zafi har cikin ranta suna bata tausayi, kwatsam Atika na shara taji sallama dagowan da zatayi tayi tozali da MD fauzi Wanda tunda ta kallai sau daya bata sake mar Marin kallonsa ba don a matsayin azzalumi ta daukeshi dukda yana matsayin Uban yayanta,

“Malama sallama nakeyi baki iya ansawa ne?”

Atika tanajinshi tayi barin iska dashi taci gaba da shara yakara cewa

“Magana nake miki Kinyi banza dani kin maidani Dan iska Dan tasha”

Atika ta ajiye tsintsiya ta dauki Mother daketa tsala uban kuka ta dauko kamu ta bata tana cewa yi shuri yaran albarka yi shiru, MD ba karamin hadiya yayiba cikin gidan ya kutsa yasa kai kenan baba tayi tsalle tace

“Koma karka sake ka shigo mana gida saiyau kasan da muna Rayuwa? Hmmm dole kayi mana sakayya irinta yaran zamani tunda munyi kurum mun haifeka kaima kayi fuka fiki ka Haifa toh kasani ba anan gidan ba maza ka fice kabar gidannan”

MD fauzi har kasa ya dukunna yace “Baba kiyi hkr albarkanki nake nema nashiga wani yanayi baba kiyafemun ”baba tayi ture kaga tsiya tace

“Nina Haifeka koh? Toh kasani baka isa ka wulakanta mu akan wata mace ba zaka iya chanza mace amma Wallahi har abada bazaka taba cewa niba uwarka bace don haka kace duniya ce koh alhakin Atika da wayannan yaran bazai barka ba”

“Kiyi hkr baba Nashiga cikin wani yanayi ne Wanda nikaina bansan meke damuna ba kiyi hkr bantaba Sanin Atika bata gidannan ba sai jiya kiyi hkr baba”

Mtwwwww

Tsaki tayi ta shige daki tabarshi tsaye yayansa Musa yashigo taci karo dashi koh kallon MD baiyi ba ya wuce binsa yayi yana gaidashi sai daga mishi hannu yayi yace

“Dakata Muhammad banida wata magana dakai koh bukatar wani zance koh furuci daga bakinka tunda harka fifita mace akan Uwarka toh kasani babu sauran cigaba ga Dan da bashida biyayya”

Yana gama magana ya shige Dakin baba

Yakara juyawa saiga Wansa babba Umar wuce shi yayi koh waige haka ya bishi yana mai magana shima ya daka mishi tsawa yace

“Banida magana dakai kuma nabaka minti uku zuwa biyar kabar gidannan kafin. Ranka ya baci ”

Dayake yasan halin yaya Umar haka ya fita yasamu Atika ta tasa yan biyu da bb kamal tana musu wasa koh kallonsa basuyi ba Bb kamal kuwa yagane mahaifinsa amma yayi kaman bai gansa ba Ya tsugunna yace

“Atika kiyi hakuri ki yafemun Nasan nayi kuskure” Atika ta tashi ta kwashi yaranta tayi daki bb kamal yayi waje har daki yabita Atika ta turoshi waje tace

“Baka isa kabani hakuri in hakura ba kayi kadan Nasan banida wani yanci a cikin zaman auren danayi dakai baka daukeni da kima ba har ka iya cimun mutunci akan mace nabarka da mashahura Itace ta dace da tsarin rayuwarka baniba banida bakin magana a halin yanzu ka gaggauta bace mun don inaji a Raina zan iya ajalinka”

Atika tayi zafi MD fauzi haka yafice amma yakasa koda shiga Motarsa bare ysbar kofar gidansu, Yanaji yayunsa suna hira da baba gashi shi yafita daban.

A kofar gida ya tsaya har Malam  yadawo har kasa ya gaidashi  Malam yace

“Sannu tabbatacce Kaine haka sannu Muhammad kace wani Abu Kasani duk Wanda ya zalunci wani toh tabbas Allah ya sakama Wanda aka zalunta baka cika daba dahar ka iya zuwa inda muke inace kasake wasu iyayen ne inace bamuda sauran daraja matarka fin shekara tana nan saiyau muke ganinka bakasan yadda muke rayuwa ba? Kaico duniya mace mace makira ce inhar kabari taci karfinka toh ka halaka inhar zata rabaka da Iyayenka harda uwar yayanka ”

Koh ina dai ba dadi wajen MD duniya tayi mishi kwatson mage rana zafi inuwa kuna yarasa Abun cewa sai hawaye

“Malam kuyi hkr ku yafemun nayi kuskure amma bazan sake ba kayimun afuwa, Atika ta koma dakinta hakan bazai sake faruwa ba kayi hkr nayi ladama,” Malam yaji Tausayin dansa wani imani ya shigeshi yace

“Bazaka taba tsira ba Muhammad matukar kana tareda shedaniyar matarka saidai Atika ta koma saboda darajar mu datake gani amma badon halinka ba Bari ta shirya ku tafi tare”Atika tayi kuka har saida taji jiri cewa take baba baxan koma ba baba ki taimakeni baba na aminche ina auren Amma abarni a banza na ita abarta a wofinta nikadai Nasan irin Ukuban datake ganamun Malam kaimunrai rai yaya Umar yaya Musa baxan koma gidannan ba na tsani gidan na tsani gidan, Ganin tana kuka yasa Yan uku kuka bb kamal kuwa tsaye yayi yace babu inda uwarsa zata haka akayitaba Atika hkr harta Aminche amma da sharadi saidai Baba ta koma gidansu da zama Malam yace Sam tabi mijinta

“malam daraja daya MD fauzi yaci na girmanku danake gani Wallahi da babu inda zani sannan saidai in tafi da jawaheer don ita kadai zata debemun kewa”

Haka akaje Nagoyi gidansu Atika yan'uwanta sukayiwa MD fauzi cha saura kadan suyi mishi duka saboda takaici su a haukarsu so suke MD fauzi ya sakar musu kanwa....+*CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)

     

   *PART TWO*

    continuetion


*@HUMAIRAH B MELODY*21-25

_*YANCIN KAI*_

Shiko fauzi son matarsa yakeyi itama Kuma haka zuwan Mash ne ya tarwatsa musu soyayyarsu, Haka jawaheer ta shirya abunda yasa nake son iyayen atika mutane ne na Arziki Wanda sukeda kauda ido da hangen nesa basu dogara ga boka koh Malam ba dukda suna asalin filani haka suka wuce Tunda atika ta shiga mota batace komai ba sunshuga garin Kaduna MD fauzi ya biyata wajen saida naman rago yasiya musu sannan suka tsaya a kangiwa Store sukayi shopping Da jawaheer ake wannan aiki itakoh Atika ta tsunduma kogin tunani yadda zata kara kasancewa a gidan da yazame mata Kurkuku, Gida suka wuce suna shiga naji MD fauzi yana waya Dagaji dai Mash tayi balaguro ne batanan farinciki Kamar ya kashe atika sai a time din naga tayi wani kasaitaccen murmushi, Nima na tayata.

Ciki suka shiga yan uku kuwa sai bacci sukeyi Mima karama ce kawai ido biyu tanata gwaranci sunyi aiki sosai Atika tasamu Yancin kai Atika ta samu damar wata yawa abinchi iri iri MD fauzi kuwa sai rawan jiki akeyi an Dade baa Hadu ba duk lokacin daya kusanci Atika shi kadai yasan abunda yakeji shi gaba daya matan rudashi sukeyi harya kasa tantancewa,

Bayan Wata daya Atika ta murmure tayi bulbul abun sai Wanda yagani har shiryawa sukayi tsaf suka bishi Akure Saida tayi wata Uku babu mash babu labarinta, sai Karin farinciki

Mashahura kuwa tana kasar England uwa ba kwaba inda achan tasamu farar fata Wanda ta fake da taje yin masters degree inda sukacin duniyarsu da tsinke Wata shigar Idan mashahura tayi babu marabanta da Tsirara MD fauzi yayi yayi tadawo tace bata gama kammala komai ba karshe tace an kara mata shekara, Gashi ta hadu da kawaye Masu jida naira kyau da iya holewa Abun saiyayi yawa Har madigo takoma yi lalacewar tayi lalacewa, Shiko yana Nigeria yayi bayau da baki wasu mazan ma basu tunani dakwai irin klas din matan daza'a tura waje karatu dakwai wayanda koh kofar gida baka barsu su fita ba bare Kuma ka barsu da maigadin ka ai angama maths.

Mash dai an waiwayo gida wata safiyar Asabar inda tasauka a filin saukan jirgin sama a Kaduna dake mando Dan tasi ta dauka sai unguwarsu tana sauka mai gadi ya bude mata Gate ta shiga tayi bangarenta tabude tashiga tuni tadau waya takira Safa Tace tadawo fah taci gaba da aiki haka Safa ta dawo ba karamin chanji tagani wajen uwar dakinta ba saboda tsarin shigarta ta banbanta dana da, Waya ta dauka takira MD fauzi atika ce taga kiran gabanta yace Ras ai tuni Atika tayi gaggawan blocking din lambar ta goge saida aka Shari wata biyu MD fauzi baiji duriyar Mashahura ba yadauki waya zai kira lamba taki shiga Duk ya damu Atika dake zaune tace

“Yanaga ranka a bace meye matsalanka tanayi tana matsawa kusa dashi ga wani kanshi dake tashi maijan hankali, Pls kadaina damuwa meka nema karasa a wajena? Ka mance duk wani Abu pls tashi muje daga ciki duk wata kissa saida atika tayi amfani dashi wajen samun kwanciyan hankali itada mijinta duk lokacin daya tunada mash saita mantar dashi komai don Atika babu irin gyran dabatayi natural bana chushe chushe ba, Saida suka shafi over Three month a Akure kannan MD fauzi yafara tunanin maida Atika gida saboda tsadar rayuwa a garin na Akure, Kullun sa rana akeyi Atika na dagawa Karshe Atika tace ita yatafi ysbarta tunda gida yakeson komawa. Mash kuwa mezai dameta tasha giya tabi maxa tabi yan mata Nikam nace alhaki kwikwiyone maishi yakeci, Rana guda Atika ta shirya tsaf don dawowa Kaduna tasa Aranta komai yafaru daga Allah ne MD fauzi kuwa aiki yasha mishi kai bai samu biyo Atika ba illah kudi daya tura musu cikin account Wanda za'a sa yara makaranta sai na abinchi kudin mota a hannu yabasu Cikin dàre misalin karfe sha biyu suka isa Kaduna haka suka tari Dan Tasi sai unguwarsu suna isa sukaga motoci Jeri Jeri Atika ta sallami mai tasi ta buga gida mai gadi ya bude suka shiga yadaukan musu kaya Atika kanta kwancewa yayi tace

“Mai gadi kodai makuwa nayi? Ya haka acikin gidan namu ake wannan iskancin an maida mana gida gidan Soho?”mai gadi yace hajiya nima haka nake tunani don tunda hajiya tadawo daga kasar England gidannan yakoma gidan maxa da mata ayi rawa asha giya ban cire miki ba har zina Anayi saboda duk Idan zanyi shara saina samu ko roron roba sunfi hamsin karshe kenan, Atika ta bude kofa suka shiga Ta kwantar da yaranta jawaheer tace Aunty kisa ido kiyi kallo sai mashahura ta wulakanta dakwai wata rana dana Saci wayarta bari in dauko in kira ubsnta yazo yaga tsiyar da yar'sa take shukawa haka jawaheer tayi bugu daya ya dauka yace

“Hello mashahura lafya kira da tsohon darennan?”

Jawaheer ta lake murya tace

“inaso kasani yarka ta maida gidan mijinta club inxaka iya zuwa kazo ka gani don abun ya wuce misali, cikin gaggawa ya taho harda convoy dayake babban sojane yana shigowa yaga yadda ake jin dadin rayuwa chan ya hangi Mash itada wani Katon gardi tana zaune kan cinyarsa tuni yaje kusa da ita yakira sunanta cikin rudu ta tashi tana Neman gudu tuni ya rike mata hannu yafara dukanta irin dukan karfi

“Mashahura Ashe tarbiyan danayi miki kenan irin sakayyar da zakiyiwa mijinki kiyi mana kenan matsayin iyayenki? Tsakanina dake Allah ya isa mashahura kinyi asara duniya da lahira Mashahura matukar na mutu da bakin cikinki kikasa nayiwa kanninki Asara duniya kin lalace babu damuwa kiyi komai duniya tsnada fadi mashahura kin bani kunya” ai tuni tari a tsarkeshi abun mamaki mashahura koh a jikinta illah wucewa cikin gida datayi ana kaishi Asibiti akace jininsa ya hau kusan Dari biyu da sittin ai kafin Asuba Ya rasu.....+

Labarina dagaske yafaru saidai yan kwaskwarima.Tuni gidajen radio suka fara sanarda mutuwarsa gidansu mash ya rude ganin an kawo gawarsa tareda Sojoji tuni mahaifiyar Mash ta sume gida yacika Dan kam itakoh Mashahura tana gidanta kwance tana bacci batasan me duniya take ciki ba, Atika tunda sanyin safe suke aiki jawaheer ce ta kunna radio taji ana sanarwa cikin sauri tace

"Aunty kinji sanarwa akeyi Brigadia TANKO ya rasu"

ai tangaran ne hannun Atika tuni ya watse Tace amma shine mash ta tashi take saka disco bari Kiga inje wajenta insanar da ita abunda ke faruwa"

Aunty kenan Jawaheer ce ke magana cikeda isa Aunty karki sake kije saboda Mashahura bata chan chanci kiyi mata haka ba macenda batada wani buri saina ganin ta rabaki da mijinki pls kadawo yan'uwanta zasuzo su sanar da ita ai koh kina tunanin daga sama ta fado? Kibar wannan kinji.

Atika ta koma tayi saro tana tunani Ji sukayi an banko gate Cikin sauri Jawaheer tafito tace waye yake banko kofa kanwar Mash tagani dagani basai anyi maka bayani ba,

Buga Dakin mash takeyi amma ta kure sauti, Wani hawaye ne yake zuba daga gurbin idanun Xarah Wanda shizai sanarda mai karatu Yadda takeji na mutuwar mahaifinta, jawaheer ce taje tayi this connecting din wutan gidan lokacin ta bude kofan kawai karo tayi da Xarah takoma da baya tace

"Lafya kika dokamun sammako a gida meye yake faruwa? Naganki so worried "?

Xarah tace

"Sister Mash you are a heartless human being I ever see on this earth, Kece silar komai amma kinanan kina shan music saboda bakida Asara lokacin da baba yake bukatan Adu'arki lokacin kike dadada taki duniya lokacin da zakiyi jimamin rashin bango kuma babban jigo lokacin kike Nishadantar da rayuwarki inaso in sanar dake Baba mahaifina mahaifinki Allah yayi masa rasuwa Kuma yamutu da bakin cikinki kisani Allah bazai barki haka ba Am living " Xarah na karasa magana ta juya Mashahura tace da karfi

"Saime donya mutu? Shine tashi ta kare nikuwa yanzu nawa yake farawa daman yaza'ayi yaci duniyarsa yaci ta wasu Allah yaji kansa Yayi masa Rahma nidai babu inda zani Wanda ya mutu ai ya mutu zuwa gobe Dayawa zasu fara dariya mtwww" daki ta koma ta kulle haushi ne ya isheta babu wuta ai da tuni ta ci gaba da more life dinta, duniya kenan bariki alalan gwangwani, Tuni Atika ta sanarda MD ai kafin faduwar rana ya iso mash kuwa bataje ba Mutane sai tir suke mata lokacin da Atika ta isa gidansu kowa sai tambayan ta mash Yakeyi Xarah tace

"Kudaina tambayan ta Dan Allah ni Nasan irin zaman da wannan matar takeyi da mash sannan itada daba mahaifinta bane tazo gaisuwa itakoh da shine silar zuwanta duniya ai batazo ba Baba ya mutu da bakin cikin mash Ya mutu da bakin cikinta Kuka kawai Xarah keyi mahaifiyarsu fah takasa magana kuka kawai takeyi sai dare mash suka koma gida suna isa sukaci karo da mash cikin wando da riga Matsatsu Cikin sauri ta cire glass tace

"Ke yaushe kika dawo? Gidannan?" budar bakin Atika tace "Ana gobe mahaifinki zai Rasu nadawo" jawaheer taja hannun Atika sukayi sasansu Mash ta biyosu da gudu tace

"Bakuda wajen zama a cikin gidannan sannan as you can see kulle gidan zanyi don hatta mai gadi na koreshi"

Atika tace

"kina iya rufewa saboda ba zamanki nakeyi ba zaman mijina nakeyi koh nima zakiyi silar kasheni ne? Banida lokacin ki kinji Banida lokacin batawa tare dake kuma kisani nasha karfinki" mash ta mutu da mamaki sasanta ta koma da gudu tana cizon yatsa garin yaya tayi sake Dan zaki ya girma bacin taso kasheshi tun yana ciki? Ohhhh tana cikin hakane taji horn Jawaheer ce tafito ta bude Gate Mash tayi saurin fitowa ganin MD fauzi yasata zuwa da gudu ta chakumeshi tace

"Macuci munafiki mara mutunci meyasa zaka dawoda waccan boran?"

Mashahura kiyi gaggawan sakin kwalan rigana kafin inyi sanadin barinki duniya yadda kece silar mutuwar ubanki, Kisani babu abunda banjiba akanki kuma you will surely pay for it I will deal with you acikin gidannan, Atika kuma matata ce ta sunnan wacce ke tsaremun kanta akoda yaushe+*CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)


  *PART TWO*

  Continuetion

     

*@HUMAIRAH B MELODY*


_*MARYAM SKT  my love for you is unstoppable😍😘 MAMA SKY I love you the way you love me MARYAM KD Allah ya ida nufi kema kina Raina HUMAIRAH ABUBAKAR YOUNG GRADUATE 2017 I love you to the moon an back I heart you dear❤BILYLN BILYAMINU ganaki I love you so much da duk group members dinki😍*_31-35

Ke kuma kin maida aure na dake zaman dadiro kije England ki mance da rayuwana gaba daya alokacin danake tsaninin bukatuwa look mashahura kinyi kadan in zauna ina miki wani explanation you don't deserve it sannan daga yau kireni daga matsayin mijinki kije kiyi duk abunda zakiyi mash Between you and you serving GOD”

Mangareta yayi ta fadi kasa rijib Jawaheer kuwa mezatayi banda dariya tace

“Kadan kika gani shegiya Mara mutunci”

Mash ta biyo jawaheer da gudu ai tuni j tayi tsalle biyu sai daki, Yana shiga Atika ta yarbeshi tace

“Kasha hanya ya kokari yakuma Karin hakuri?” da godiya ba karamin dadi MD fauzi yajiba ya rungumeta ya dauki yara yana musu wasa suma sunata sashi

Dariya haka Atika ta fada ta hada mishi ruwan wanka yana gamawa j ta gama girki haka yaci ya kwanta saida safe tunda sanyi safiya Mash keta surfa bala'i kaman zata Ari baki Shiko yana fitowa zuwa zaman makoki ya shige warsa mota ai da gudu ta Dauko wani karfe ta fasa mishi glass din mota jikake tas tas, Wani bakin ciki ya kawo ma MD fauzi wuya yafito yafara dukan Mashahura tako ina yadinga dukanta kaman an aikoshi Yace

“,yadda kika fasamun Glass din mota kisani kudin Abinchinki na wata HUDU dashi zanyi amfani in gyra kisani kinyi kanki illah nasiya muku mota Keda Atika amma kisani itama saidata zanyi insiyi Glass din motata amma kafinnan kema saina fasa miki jikinki duka yakeyi tana ihu Atika tace

“Jawaheer bari inje inba MD hkr ysbarta haka”

Aunty kenan kedai bakida dsbara Wallahi Kiga yadda tadinga muzguna miki har kina wani tausayinta? Akanme aini inkasheta zaiyi babu inda zani Saboda haka Aunty ishara ce Allah yafara nuna mata.

Atika dai batada mugun hali saboda Allah yayita mai matuk'ar tausayi dajin kai shiyasa mash take bata tausayi, Saida yayi mata Li's kannan ya ajiye motar yafita da kafa Gidansu yafara zuwa ya shiga ya gaida mahaifiyarsu Mash nan take mishi zancen mashahura fah

“Mum kibar mashahura duniya ce ta ishi kowa riga da wando tabbas mum dakwai ranan ladama tananan zuwa kidaina tada hankalinki atleast mashahura tasan meke mata ciwo tunda haka ta zaba ai kawai ki kyaleta nima ido nasa mata” mummy ta share guntun hawayenta sukayi sallama, Yana fita BB motors ya isa ya ajiye Motarsa ya dauki na Atika yakai mata Mash kuwa tuni tayi mankas ta sheme a Falo tana bacci cutar data samu mash Allah ya yaye mata,

MD ne ya sauka ya shiga sasan Atee yace

“Guest what? ”

Atee tace

“Meye Dan Allah” ta bayanta ya koma ya rufe mata ido yace “albishirinki?”

Atika tace goto

“Fari ko ja”?

Tace fari kal kal tafiya sukeyi harsuka fita jawaheer tana ganin sabuwar mota zatayi ihu yayi mata alaman tayi shuru,

“Me kike tunanin zaki gani” Atika tace me kuwa?

Bude mata idon dazaiyi Taga tsaleliyar mota Toyota Highlander wacce ake cewa inkin isa mijinki ya siya miki irinta Atika tayi ihu tayi tsalle ta rungume MD fauzi sai hawaye yafara kwarara lokaci daya kuma tana Dariya tace

Babu abunda take tunawa sai irin rayuwarta ta baya, ni Humairah nace baa yabon Dan kutturu saiya shekara goma da yatsa, bin motar kawai take tana tabawa Abunka dana Village yashigo birni tace

“Ashe duniya taza kaini inda banyi zato ba? Mijina Kaine Farinciki na Banida bakin yimaka godiya Allah yajikan iyaye Allah yayi maka kyakkyawan masauki a gidan Aljanna Idan nace baka ba talauci ka yarda Allah maiyi ne, MD fauzi Allah yayi maka Arziki duniya da lahira Narasa dawani halshe zan gode maka” har kasa Atika ta durk'usa tana kuka tana gode masa don batayi zaton haka daga gareshi ba koh a mafarki dagata yayi yace

“Amin Atika karkiji komai nidinnan me sonki ne Kiyi hkr bisa ga muzguna miki danayi tayi a baya”cikin sauri Atika tace

“Haba MD fauzi meyasa komai bazai wuce ba Na yafe maka duniya da lahira ”

Dariya akayi akayi shewa Dukkansu ne suka juyo Mash tace

“Wani bariki ne akayi anan wani darene jemage bai gani ba don an siya miki mota shine kike wani murna kisani motarnan tana iya zama ajalinki ki rubuta ki ajiye nidake shege kafasa”Tuni murnar Atika ta koma ciki tuni taci motar ta fice mata  a rai tuni taji kaunar motar ta fice mata

“Kinyi karya Mashahura kisani duk wani threat dinki will not work kuma Idan kika sake hakan t faru you will regret the rest of your miserable like in Dark prison and let me inform you something duk abunda yasamu Atika believe me sainayi Ajalinki kema na yarda na Aminche nima a kasheni” miyaune ya taru a Bakinsa tuni y tofa mata a fuska Mashahura tayi saurin rufe fuska tace

“Whatttt?”

“Yes wannan shine zai sanar dake cewa maganata Zanen Dutse ce”....


+

_*Tirkashi ana murna bako ya tafi Ashe yana bayan gari muje zuwa shin me mashahura zatayi wa atika? Boka zata komawa koh koh motace ajalin Atika? Gadai  sharadin md fauzi kuma baya magana biyuMuje zuwa.......*_😍Cikin sauri Atika ta koma daki tana Huci ai taci alwahin Atika bazata taba jin dadi a gidan Fauzi ba takai gwaro takai mari haka ta dinga Safa da marwa a falo ita guda, Atika kuwa da Jawaheer da MD fauzi ciki suka shiga tuni Atika ta mance da wata mota yanata yan'uku da za'a kaisu Makaranta, Washe gari tunda safe suka tashi suka shirya Yara MD fauzi yadaukesu cikin motar Atika yakaisu makaranta, MD yana fita MASH ta sabi gyale sai gidan Laila nanta tarar batanan fitowa tayi ta miki hanyan zuwa wajen boka mande Tana zuwa ta tarar bakowa ta shige ta zauna

Wani Dariya yakeyi

Hahahahaha Ashe kina tafe nayi tunanin kin daina zuwa wajena ai sannunki da zuwa tun Kafin kixo Nasan abunda ke tafe dake Kishiyarki ta zama Mowa mukuma

Kin zama bora hahahahaha wata dariyar yakara kwashewa mai ban tsoro yace aiki ya ganki Za'ayi aiki mai zafi akanta amma sai kinyi sati daya a wannan gidan, tuni mash ta muskuta tace

“Boka sati guda fa kace nikuwa inzan iya kwana anan ai toh kamar tsirara nake jifa gidan kaman dauji”

Keeeeeh!!!!!!!!!

Ya daka mata tsawa ki iya bakinki Idan ba haka ba reshe zai juya da mijiya tuni MASH ta gimtse baki tana rawan jiki kin shirya kohkuwa?

Mash tace

“Na shirya Wallahi a shirye nake amma inaso inje gida in sanar da mijina zanyi tafiya indan ruko wasu abubuwan”

Aljani Mune bai aminche ba daga yau kwanan yafara maza shiga ciki shiga ciki ai jiki na rawa mash ta shiga sai waige takeyi ikon Allah Yanzu Ace mashahura ubanta ya mutu bataje koda taga gawarsa ba amma tazo wajen boka gashi yau sadakan uku? Allah kasa mufi karfin zuciyanmu tabbas wasu mata shedan ya buga musu ganga tareda yimusu Fitsari aka,

Boka mande ya kutsa ciki Abu kamar al'mara Saida mash ta kwashi kwana biyar a gidan boka mande yana lalata da ita A ranan na shida saida Mash taji kaman zata mutu saboda Azaba Idan ya kama Dukiyar Fulaninta sai yaji kamar zai cire kan  sannan Idan ya matsa Sai taji Kamar tayi fitsari saboda yawan tabawa har bataso tayi motsi, Cikin ranan na bakwai ne MD fauzi yakasa hkr da Rashin ganin MASH har saida ya tambayi Atika itadai tace

“Tun ranan nan bansake ganinta ba kuma bataje gida ba?”

“I don't think so”

Ficewa yayi.

Mash ce zaune cikin dakin boka yace inaso ki tube kayanki don yau zan miki wanka da Ruwan Damo sai yadda kikaso yi da mijinki ke kadai tashi tayi ta tube ai lokaci daya boka mande yafara Kyarma ai tuni ya ajiye ruwa ya raba kansa da kayan jikinta sannan yafara Aiki kamar yadda ya saba, Idan yayi wani abun sai Mash tayi amai donji take Kamar har Wuya yazo mata, saida yayi amfani da ita kusan Awa uku baisan ma yayiba tashi tayi zata gudu ya danki kirjinta ai tuni tafadi ta sume amma saboda Rashin imani wata Dariya ya saki yace

Yoh aini haka nakeso Kullun inta harka kawai a sume ma zafi sakewa, ya kara tubewa abun saida nayi kuka saboda Neman duniya wasu matan su halaka Kansu sukai Kansu wuta? Allah kasa mufi karfin zuciyanmu.

Bayan awa mash ta farfado taga boka tsaye yace

Tashi kiyi wankan ai tana wankan tayi kokari tasa kaya ta wuce gida duk inkaga mash kasan ba kanta sai dàre ta iso gida tana shiga tayi wanka ta zauna zaman jiran tsammani Kamar daga sama saiga MD fauzi jiki na rawa yake

“Gimbiya ykk dafatan dai lafya”idan mai karatu yaga yadda MD fauzi keyi sai yayi Dariya Atika ta kirashi a waya yadaga yace

“Ke dallah karki dameni saida safe gani wajen Gimbiya mashahura ” tunda Atika taji haka ta daura hannu aka tace

“Mash ta kara jefani cikin musiba maiyasa bata bari mota tayi ajalina ba dadai wannan bakin Daren?”Atika tayi kuka Kamar zanta zai fita jawaheer ce tayita nata hkr washe gari MD fauzi ya wuce aiki dayake yadawo Kd abunka da soja,

Yana fita Atika ta shirya saboda ana koya mata mota tafito kenan mash tace

“Bani mukullin Shegiya mai bakin ido kina magana in fasa miki baki wuce ciki Atika ta bata ta juya ciki Kamar batada wayo mash tayi Dariya tayi shewa tace “Muzuba nidake shege kafasa kisani yadda naci duka kema saikin ci na jaki, Atika tana shiga ta rushe da kuka jawaheer tace

“Lafya Aunty kike kuka?”

Atika ta karbi mukullin motar jawaheer tace

“Kuma kika bata look aunty kidaina jin tsoronta shiyasa take samun galaba a kanki is better kuyi damben mutuwa ku kona gidan” jawaheer tafice ta kutsa Dakin Mash ta sheketa tace

“mukullin mota koh in dauke numfashinki kisani daga yau kidaina yida Aunty atika dani zamu kwama Wallahi sai kin gane ban banci tsakanin kasa da tsakuwa haka MASH ta tashi ta dauko bakaramin tsoron Jawaheer mash keyi ba+Jawaheer ta fice takaiwa Atika mukulli tafito zuwa koyan mota tareda tahir mai koya mata Mash ta tashi ta koma wajen boka tace

“boka mande inaso a batarmu da Atika kar a sake ganinta don bana kaunar ganinta acikin gidan so nake dagani saishi muzauna a gidan kaga saiya zama bawana”

Boka yayi Dariya yace za'ayi yadda kikace amma kuma duk ranarda Atika tadawo toh kisani ranan kema zaki shiga duniya kina hauka baza'a sake ganinki ba ni kuma zakiyi ajalina ranan, sannan zan baki wani magani kisa a kofar shigowa na dakinta dana shigowa gida karki sake wani ya ganki don inhar wani koh wata ta ganki jin dadinki na lokaci ne don saita dawo , mash tace taji takuma Aminche daduk wani sharadi haka yabata Kullun kaho kuda biyu, takoma gida tana tunanin yadda zata yi gashi koh ina tiles ne gashi ance kar wani yagani toh yaxanyi?

Nidai tsayawa nayi inga ikon Allah mata halinmu saimu Allah ka shiryi bayinka wata ta gwammace jefa yar' uwarta mace cikin wani hali ita ta zauna kalau Allah kasa mufi karfin zuciya,

Kwatsam Atika ta yanke shaawaran zuwa wajen Mima a barikin Zaria na sojoji dayake nan aka mai dasu Atika ita ta tukasu har Zaria dukda dakwai learner har yanzu, Nan mash ta tashi aiki tuburan don harta mai gadi saida ta aikeshi guri mai nisa, Amma Ashe bai tafiba don yaga alaman Rashin gaskiya a tattare da ita,

Saida ta bude tiles ta hak'a ta birna tasamu wani tiles ta rufe tasa simintin tiles duk Musa mai gadi na kallo, Takoma bakin gate daga inter-lock tasa ta maida Duk akan idon Musa mai gadi tana gamawa ta waiga bataga kowa ma shiko tuni ya dirka yatafi Aiken ransa a bace.

Yana dawowa da Dariya mash tace

“Musa kenan Kanaji da tsawo kamar doron zabi danina dakai sauri” yafa Dade amma dayake tanaso ta wayance shikuma yace

“hajiya kinyiwa kanki dakika zageni kai kayi koma kan mashekiya” Mashahura ta jima tana juya Kalmar Musa a ranta don tasan jirwaye mai kaman wanka yake mata saita maze, Tayi ciki kwansu Atika biyu amma ba karamin ziyara sukayi ba baba taji dadi sosai har bakin mota suka rakata, MD fauzi kuwa tuni an jika an bashi yanasha ranan da Atika ta dawo ranan tafara Hauka tuburan tunda ta fita ga gudu baa sake ganinta ba Anyi nema anyi nema amma ina abun yaci tura Shiko MD fauzi koh a jikinsa don da aka sanar dashi cewa yayi

“Nifa da Atika da bata duk dayane a wajena saboda inada wata matar yara kuma Allah shi raya ga Jawaheer taxauna da yan' biyu tadinga kula dasu” abun yayiwa yan'uwansa ciwo Yan' uwan Atika kuwa zuga sukayi har Kaduna sukayiwa mash kare jini biri jini daga ita har MD fauzi kuma da sharadin su nemo musu kanwa.

*BAYAN WATA DAYA*

Jawaheer tana zaune tana adu'a taji yan'uku na kuka tafita aguje tafito taga mash rikeda Bulala ai tuni idanun j ya juya ta amshi kebul din hannunta ta dunga dukan mash kwatsam saiga MD fauzi shiwai zai ceci mash ai tuni yaji nushi tako ina saida Jawaheer tayiwa mash lubus da jiki sannan ta kwashi yaranta sai daki, MD fauzi yace wai anya yarinyar nan ita kadaice? Kuwa? Mash tace

“Wallahi aljanace nidai ka fitarda ita daga gidannan imba hakaba saita kashemu wata rana” MD fauzi yace “Mashahura kidaina Wannan tunanin yan'uku basuda dama babu mai iya musu sai ita wallahi kibarta kawai” anshafe kwanaki an shafe satika har wata gashi wata Bakwai babu Atika babu labarinta,

*********

Mahaukaciya yi rawa mubaki biyar Wucewa nazoyi cikin garin kano a wata unguwa mai suna Yan'Kaba naga yara sunyi cinchirindo kamar ana sadaka  nidai jin ana mahaukaciya yasa na tsaya Ido biyu nayi da Atika saina ji Wasu hawaye Na zuba ai tana ganina ta sunkuci kayanta gashi dagani Ciki gareta tana Gudu tana cewa

*CIKIN DA BA'ASO* cikin da BA'ASO tundaga ranan nake Neman ta bansake sata a ido ba

Duk wani masoyin Atika yayi mata fatan Alkhairi da sauka Lafya Allah ya hadata dana gari, Anata shirin Hada auren Jawaheer da MD fauzi amma batareda sunsani ba saboda yadda su mother suka saba da ita basu iya rabuwa da ita ba mash tazama wata hamshakiya gashi koh bari bata tabayiba kuma bai damunta tunda tasamu miji da dukiyarsa tana juyashi yadda takeso.+*CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)  *PART TWO*

 

     

*@HUMAIRAH B MELODY*


_*Mai cece kuce akan Wannan novel nawa kiyi hkr saboda majority kari the both KUMA DUK WANDA YA RAINA TSAYUWAR WATA SAIYA HAU SAMA YA GYARA*_46-50


Gashi MD fauzi yakai matsayin COLONEL, girma yazo amma macce ta maidashi tsala mace ta maidashi gaula mata muji tsoron Allah Wallahi namiji ba abun yiwa haka bane ranarda ruwa ya karewa Dan kada har a titi sai an ganki yana miki tijara namiji ai badan a saba bane, kiyi asaran kudinki jikinki hannun ki kafarki wajen zuwa wajen boka koh malamin tsubbu, Mata shiyasa Allah yasa mata masu mallake mazajensu a jerin wayanda bazasuji koda kamshin Aljanna ba, sannan ya tsine musu sannan karshen su babu kyau, Jawaheer dai sai kula dasu takeyi kwanci tashi saboda double promotion da BB kamal yake samu a school har yakai Ss 2 saboda gwazonsa ga tsantsar hadda yaro mai addini, Duk sati saiyayiwa Mahaifiyarsa Wato Atika Saukan Al'qurani dafatan Allah ya baiyanata,

Tafiya takaini kauye a Hadejia ni humairah tafe nake zani Gidan Audu Mani  Wanda mahaifin Kawata ne Iklima cikin gidan nashiga yadda naga wata mata tana ihu alamu hauka take Nidai bance komaiba na koma gefe ni humairah naga Atika da tsohon ciki sai magani ake bata nanna zauna na yada zango nakira iklima nace

“Nasan Wannan matar tabbas Atika ce yar Zaria ce” nidai na zaiyana musu komai nayi musu kwantancen inda take a Kd suka bada umurnin daxaran taji sauki zamu kaita gida,

Allah ka amshi aduarkmu akan Atika Kd na shirya tsaf nadawo saura kwana biyar bikin Jawaheer da MD ni humairah narasa me zanyi fatana da adu'a ta Atika tadawo Kafin kwana biyar.

********

“Bawon Allah daga ina ka dauko ni ina yan'uku? Ta shafa cikinta tace meye Wannan? Cikin da BA'ASO shine a jikina nashiga Uku Ina MD fauzi yake shiya kawoni nan koh saboda bayaso in haihu koh? Dana samu ciki saiya Sani cikin damuwa”magana takeyi babu Wanda yace da ita komai Audu Mani ne yayi mata magana yace

“ki kwantar da hankalinki kinji fatanmu da Allah yabaki Lafya kusan satinki biyu ana miki magani kenan saboda cutar hauka Atika ta mike tana kallon kayan jikinta tace

“Innanallahi wa'inna ilaihir rajiun yanzu hauka nayi?” Nabani sai hawaye dake zuba

“Sharrin Mashahura ne Wannan itace silar komai Allah nagode maka Dan Allah kukaini inga yarana Dan Allah kutaimaka Mother tafisu rigima yatayi da rayuwarta? Dan Allah kukaini kuka Atika takeyi mai lasi saida tayi mai isanta aka bata Abinchi ai Atika takici itadai yaranta da Jawaheer, Haka sukayita lallabata har washe gari akayi shatan mota sai Kaduna ganin tafiya taki karewa Atika tace

“Malam inna wai wani garine Wannan?”

Suka hada baki

Jigawa kenan tarin Allah ai sai Atika ta kara rushewa da kuka Mai tsanani tace

“Allah ka sakama baiwarka Ya Allah ka sakamun da gaggawa tabbas nayi sake da abubuwa da dama na rayuwa nayi sake da *AZUMIN* litinin da laraba lokacin danake cikin tsanani, nayi saka ci da AZKAR na safe dana yamma, nayi sakaci da *SALLAR DARE* lokacin da nake cikin halin ni aysu nayi sakaci da Adu'oi da dama rashinsu ne yasani fadawa Wannan halin” saita kara fashewa da kuka mai cin rai Wanda ni kaina Humairah saida nayi kuka saboda duniya batada tabbas, suna isa Unguwan su suka Dakata a kofar gida Musa mai gadi yafito yana ganin Atika yace

“Hajiya Ashe kina Raye?” Tayi murmushi tace “Musa kenan ka mance cewa cuta ba mutuwa ba sumunta daga Allah ne wata rana sai lbr”

Musa yace gashi yanzu sukaje kasuwa kuma hajiya dake ciki tace kar inbar kowa yashigo saboda a bakin aikina ne,

Atika tayi Dariya ta kalli Malam tace “Kaji malam ”? Dariya yayi Musa yace hajiya nadade ina jiran Wannan rana tazo hajiya zan gayamiki sanadin ciwonki hajiya Mashahura itace silar haukataki saboda natuna wata rana data aikeni Insiyo mata wani Abu na mmance daganinta Nasan batada gaskiya, nan Musa ya kwashe komai suna tsaye saiga MD fauzi da Jawaheer tuni sukayi turus Jawaheer ta murtsuka ido tace

“Aunty kece Koh fatalwanki?”

Atika tayi Dariya tace

“Nice”

MD kuwa sakin kayan hannunsa yayi da wayarsa da komai yace Atika kece Koh spirit dinki? Tace nice mushiga ciki suna shiga Mashahura taga Atika tuni ta mike tace

“Ke ubanme yadawo dake gidannan so kike nima ki haukatani? yadda na haukataki? Kowa sai kallon kallo akeyi.

+

Tirkashi

Jinjina ga duk duk daukacin masoya cikin da BA'ASO godiya ta musamman gaduk masoyana dake Lardin zazzau dama Kaduna baki daya one love.*CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)

     

*@HUMAIRAH B MELODY*
_*Wayannan Page din dazasuzo a karshe nakune manyan mata diban fari Takunku sannu Allah yayi muku baiwa Irin wacce bakowa yakewa ba na rubutu*_


*AUNTY SIS*

*FIRDAUSI SODANGI*

*RASH KARDAM*

*KHALEESAT HYDAR*

*UMMI AISHA*

*MRS UMAR*

*NANA DISO*

*LUBABATU MAITAFSIR*

*BATUUL MAMMAN*

*AYEESH CHUCHU*

*SAFIYA ABDOOL*

*MIEMIE BEE*

*SANAH UMMU BENA*

*SANAH S MATAZU*

*RUFAIDA OMAR*

Allah ya kara baseerah girma da daukaka LYSM❤😍😘


+

51-55


MD fauzi tuni yafadi ya sumamme itakoh Mashahura sai tonawa kanta asiri takeyi tundaga farko har kashe abun gwanin ban haushi tuni tafara kokarin cire kaya tana maganganu harda wani abun Wanda ni Hummy bansan anyi ba, Atika kuwa mezatayi sai kuka shabe shabe Mashahura tace “Kuka kikeyi bake keda kukaba nikeda kuka nikeda kuka boka mande kaiko kaiko kaima Nasan kanan kanajin yadda nakeji hahaha ” ta kece da Dariya Malam Audu Mani da musa mai gadi suka kamata suka daureta MD fauzi kuwa ruwa Jawaheer ta debo aka watsamai tuni ya mike ya tashi yana cewa Allah ya isa tsakanina dake Allah ya tsine miki albarka macuciya a haka zaki kare, Asibiti zani, tashi yayi ya shiga mota Musa ya bude mishi gate Giwa hospital yaje yasamu kwararren Likita Wanda yasan aikinshi yasanar dashi bukatarsa haka aka dibi jininsa da fitsarinsa akace yadawo Nanda kwana biyar Tuni MD ya buga kafa yace baisan Wannan ba hankalinsa bazai taba kwanciya ba matukar baa gama yauba haka MD fauzi yanemi guri ya zauna har saida aka kammala don baxan iya cewa ka yawan awonnin ba, Likita na fitowa MD fauzi ya amshe takardar ya bude yana ansa non active a jikin tskardar test din HIV yace

“Likita kasanar dani meye non-active?”likita yace kabari muje office Wannan maganar bata waje bace lokaci daya MD fauzi yaji kamar an zare ransa cewa yake shikenan rayuwata ta kare rayuwa bata a bakin komai ni Nasan mutuwa kawai nake jira shikenan ya gogamun cuta,

Office suka shiga Likita ya dubi MD yace

“Oga a yadda mukayi kwaji na HIV bakada ita saidai kuma kana daukeda cutar sanyi wacce ake samunta ta hanyar jima'i koh a bandaki Mara tsafta sannan komai Lafya ai tuni MD fauzi yaji wani iska na shiganshi yace

“Likita mace abar tsoro ce komin yarintarta nafada cikin tarkon mace Allah ne ya kubutar dani Allah yaga zuciyana bana nufin kowa da sharri” Likita yayi murmushi yace “Kayi wasa da abubuwa uku a tsarin rayuwarka  Asiri gaskiya ne yaci annabawa bare kai banza mutum Adu'a makami ce ga dukkan mumini kayi watsi da ita baka sallar dare Wanda Allah yake sakkowa Dan amsan aduar bayinsa kayi wasa da Azumi Wanda shina waraka ne daga dukkan bakin ciki koh damuwa kariya ne daga dukkan sharri, baka Wannan taya kake tsammanin Allah zai taimakeka bayan yace tashi in taimakeka don haka Allah y kara tsaremu baki daya ya rubuta mishi magunguna da yadda zaa sha sallama sukayi ya wuce gida yana isa ya taradda Mashahura an daureta ya kalleta yaci wani haushi yacema

“Musa mai gadi meye na daureta Banida buk'atarta saketa tayi waje sakamakonta kenan na cin amanar aure da sabawa Allah da iyaye” haka aka saki Mash tafice a guje tundaga ranar hauka tuburan bata Wannan bolar bata waccan bolar gashi ta gamu da cutar cancer mahaifa koda yaushe jini bin kafarta yakeyi dalilin Kwayoyin data dinga sha ba bisa ka'ida ba mash tayi zuwan banza duniya bada bare gudar tsoka, baba kuwa taji dadin ganin Atika don zuba sukayi daga Zaria Malam Lawal mahaifin MD fauzi kuwa tsufa yakamu da ciwon suga.

*Rayuwa mai dadi*

Tun rabuwar MD fauzi da mash gidansa yazama tamkar makabarta wajen kwanciyan hankali farincikinsu yadawo kamar da amma kuma kamar yadda kuka Sani baa canzawa tuwo suna MD fauzi hali nanan ciki ankusa haihuwansa yanuna bai kaunar cikin har yakaiga MD fauzi yace ciki banasa bane  lokacin datayi hauka ta sameshi Atika Kullun cikin kuka takeyi tace

“Md Tunda nazo duniya ban taba Sanin wani namiji a duniya ba bayan kai Wannan ciki dazaiyi magana tabbas daya fadi koshi Dan waye? Amma ai rana bata karya MD saida uwar diya taji kunya, Ai zamani yazo likitoci zasu tabbatar da komai cikin kankanin lokaci ” Atika dai tana tsumayen haihuwa saida da yakai cikin yayi wata goma sha biyu shekara kannan ta haifeshi ranan wata Laraba kwanansu daya a Asibiti aka sallamesu ta haifi danta namiji yaci Suna Abubakar(Iman), Dayake tsohuwar haihuwa ce baayi wani dauki ba amma tunda aka haifi Wannan da bai taba kuka ba bare kuma ya bude ido numfashi kamar ansammai dakyar ai tuni aka kaishi Asibiti Cikin hanzari akayo Zaria dashi Asibitin Shika don Giwa hospital sunce baxasu iyaba..............Ana zuwa EMERGENCY WARD aka nufa dashi wajen yara Wato PEDIATRIC , Tuni likitoci sukasa mishi OXYGEN abunda zai taimakawa numfashinsa duk Wanda yaga Atika saita bashi tausayi MD fauzi kuwa Daga Ganshi kasan ba Lafya Tuni aka rubuta magani gashi koh nono bai tsotsaba aka akasa Atika matso nono a feeding bottle nonon mai ruwan doruwa Yello Wanda akeso yara sussha saboda yana daukeda VTM A, B and E haka aka cusamai abun abinchi a hanci koh kuka bayayi bare motsi bugun zuciya kwai kake iya gani, kudi a ranan saida aka kashe dubu Hamsin, Cikin kwana biyar saida MD fauzi yaxama abun tausayi Tabbas CIKIN DA BA'ASO yaxama abun kula da shiga rai da rayuwa a wajen MD fauzi bai tabajin son da ba irin na Iman ba gashi yanuna kiyayyarsa yanuna baya kaunar yara gashi Allah ya azurtashi da DA' Mara Lafya Wanda zai zame mishi ishara yazamewa maxa irin MD fauzi ishara,

Gaba daya Zaria suka dawo su yan uku da Jawaheer Mima kuwa tanajin Labarin suna Zaria Kullun saita kai musu abinchi Safe da dàre Atika taba Mima Labarin duk abunda yafaru bayan rabuwarsu Mima tace

“Atika Kina lungu ne shiyasa kike tunanin cewa wai akwai mata irin Mashahura? Toh wallahi akwaisu wasu sunfita ma bari kiji Wata ma cewa za'ayi maniyyin mijinta zata kawo koh gashin gaban mijinta wata ma kashe mijin zatayi da Asiri asamai cuta saboda kar a gane, wata kurciya zatasa ayi mai koh ayiwa kishiyar ki godewa Allah daya baki Lafya yakuma yimiki sakayya kidai duk abunda zaa ce mace zatayi toh zatayi ”

Atika tayi saro abun duniya da mamaki ya isheta atika tayi ajiyan zuciya tace

“Allah yasa mudace yanzu dai kinga halinda muke ciki yau kwana biyar kenan Iman yakiyin kuka yakiyin motsi sai bugun zuciya shima da Taimakon Oxygen” kuka tasaka mai cin rai shiko Md fauzi yana wajen Dakin yayi tagumi gashi aljihu yafara kasa saboda ciwon Iman, sai sukayi sati da kwana biyar ana Abu guda a Asibiti akayi suna ina wani batun suna ciwo yacinye kudi, Daga karshe gida suka koma akafarayin na Hausa ni Hummy nace Wannan shine jarabawan Fauzi Allah shine meyi akowani lokaci a sadda yaga dama Wannan kadai ya ishi MD fauzi ishara, Ranan da suka koma gida Iman yayi wani dogon suma Wanda saida akafara shirin yimasa wanka ana tunanin babu shi gashi yaro baya iya kallon mutane saidai yayi k'asa dakai kamar munafiki daganinsa kaga tsoho nidai nace anya ba Dan ruwa bane? Anya ba sauya mata Dan akayi a ciki ba? Da wayannan tambayoyin washe gari aka isa wajen mai magani yana ganinsa yace Wannan yaron ku kaishi Islamic centers nanne kawai zaku samu Maganinsa saboda daganinsa Aljanune suka shafeshi......

Nan MD fauzi da Atika suka tsorata suna fita basu zarce koh ina ba sai ALFURK'AN ISLAMIC CENTER T\w nan aka ysnke musu kudi naira dubu Ashirin take yanke MD fauzi yabada Akafara yimishi adu'a ana mishi Ruqiya yaro tuni yafara motsi amma babu kuka an basu magani adinga mishi amfani dasu kuma a yawaita sa karatu Al'Qur'ani sai bayan sati daya sudawo, suna hanya aka kira MD fauzi cewa anyi mishi posting zuwa Maiduguri Lokaci daya yaji ransa ya baci saura kiris ya karawa Wani Dan bus mota dakyar suka koma gida Baba dai bakaramin jidasu Atika takeyi ba Jawaheer tasamu miji za'ayi mata aure,

Bayan sun shiga dakine dare yayi sosai MD fauzi ya tashi sai Safa da marwa yakeyi yana tunanin tafiyansa Maiduguri wani Abu yagani kato kamar SA mai kaho ya fita daga jikin Iman salati kawai yakeyi yana Adu'a

“Atika atika tashi tashi” atika cikin bacci tace MD fauzi Lafya kinga abunda nagani ne? Sa mai kaho ai tuni ta mike abunka da jininsu aka suka sunkuceshi suka rungume saiji sukayi yana kuka kadan kadan.+[7/15, 8:27 PM] Humairah Melody: *CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)

     

*@HUMAIRAH B MELODY*


_*Dedicated to*_

AUNTY SIS

FIRDAUDI SODANGI

RASH KARDAM

KHALEESAT HYDAR

UMMI AYSHA

MRS UMAR

NANA DISO

LUBABATU MAITAFSIR

BATUUL MAMMAN

AYEESH CHUCHU

SAFIYA ABDOOL

MIEMIE BEE

SANAH UMMU BENA

SANAH S MATAZU

RUFAIDA OMAR

_*Allah yakara baseerah girma da daukaka LYSM😍❤😍*_

        

         END


61-65


Washe gari Iman yadaina koh motsi yakoma yayi wani jagab sai a lokacin suka kara tabbatar da cewa ciwon Imam Shafar aljanu ne sati biyu amma babu wani improvement, MD fauzi washe gari ya tashi jiki ba k'wari yan'uku suka gaidashi suka fice dayake ba karamin wayo garesu ba

_*Atika inason insanar dake wani abu amma kiyi hkr duk abunda kikaga yasamu bawa daga Allah ne adu'a ita kadai nakeda bukata daga gareki*_ Atika tayi tsaye ta rungume hannu tace

“Kaki ka Sanaar dani sai danwaken zagaye kakemun pls kasanar dani kohdai akan Iman ne?”

_*koh daya Atika Nasan cewa ciwon IMAN daga Allah ne kuma ishara ne Allah ya nunamun koh ince haka Allah yake tsara lamuransa a duk sadda yaga dama Wannan akan aiki nane Inaso in sanar dake an turani MAIDUGURI Aiki*_

Atika tana kan cushions ai sai ta zamo kasa tace

“My love ka tausayawa rayuwata data yarannan karka ce zaka Maiduguri shiyasa tun farko banida bukatan Aikin sojan nan kasani yanzu tafiya zakayi a kasheka? Amaidani mai takaba? Ka maida yaranka Marayu?

Ka tausayawa Wannan yaron dake hannuna Tare dakai kadai zan iya kula dashi Kaine jigo Kaine duk wani bango nawa”

Shuru tayi ya sinna kai a kafa maganganun Atika ne kawai sukasa sa kuka amma tafiya dole ne bashida wani zabi haka ya mike batareda yacewa Atika komai ba, Kaduna ya wuce yasa gidansa a kasuwa ya kammala komai nasa dake Kd yadawo Zaria yamma lis, Yana shigowa yaga Atika ta tasa yaranta sai kuka takeyi Jawaheer kuwa sai lallashi takeyi Yana kutso kai yaji gabansa ya fadi ya shige daki yakira Atika ta sameshi a daki,

_*Atika meyasa kike yimun haka akaina aka fara zuwa Maiduguri look kisani Narigada nasa hannu babu gudu Baja da baya kina tunanin Idan nace nabar aiki baki tunanin a zargeni da wani Abu? Lokacin da ake fafatawa ga Rashin tsaro daya addabemu? Cewa za'ayi inada hadin baki adu'a zakiyi yadda sauran mata sukewa mazajensu Na siyar dakomai nawa dake kaduna, gobe xan nemi gida insiya muku zama a Zaria yakamaku zan ajiye muku komai na rayuwa Zan dinga yimuku aike Idan sararin hakan yasamu*_

Atika tayi saro Abun duniya ya isheta tayi nannauyan ajiyan zuciya tace

“Naji nakuma gamsu Allah ya kareka ya tsareka daga sharrin makiya Allah yakaika Lafya ya dawo dakai lafya”bak'aramin dadi yajiba nan yashiga yasanar da Baba yagayamata komai tayi mishi adu'a Malam kuwa ciwon suga ta tasashi gaba Ss dai muyi fatan Allah ya ba marasa LAFYA lafya baki daya.

[7/16, 7:43 AM] Humairah Melody: *CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)

+

     

*@HUMAIRAH B MELODY*
_*Dedicated to*_

AUNTY SIS

FIRDAUDI SODANGI

RASH KARDAM

KHALEESAT HYDAR

UMMI AYSHA

MRS UMAR

NANA DISO

LUBABATU MAITAFSIR

BATUUL MAMMAN

AYEESH CHUCHU

SAFIYA ABDOOL

MIEMIE BEE

SANAH UMMU BENA

SANAH S MATAZU

RUFAIDA OMAR

_*Allah yakara baseerah girma da daukaka LYSM😍❤😍*_


66-70

*BAYAN SHEKARA GUDA*


MD FAUZI yatafi yana chan Bama wani gari a chan garin Maiduguri anata fafatawa Iman kuwa yananan jiya iyau Allah ya hadasu da Iyawansa babu yadda suka iya sai hkr ansamu yafara zama yana magana kadan kadan Sun samu k'wararren mai magani yace wata rana kamar ba'ayi ba zai warke a Yan ganda suke zaune yasiya musu tankasheshen gida Wanda suke morewa Ansa yara a Takon international school dake kusa dasu Atika tana zaune cikin tsira da Aminche Har Malam Lawal ya rasu MD fauzi baizo ba saboda yaki a fagen daga, amma yayi masa adu'a daga chan.

_*Shekaru sun mika saida MD fauzi yayi shekera HUDU a Maiduguri sune diban farko kafinnan yadawo Atika tayi murna kaman zata cinyeshi gashi tazama uwa yara mata kusan shekara goma sukeda a yanzu A kiyasi Bb kamal kuwa anyi SSCE yayi narasa an kaishi Malaisiya University of kaula Lumpur, yarone Dan karami amma Allah yayi mishi baiwa MD fauzi duk Idan ya kalli imam sai wani imani yazo mishi*_ saboda yayi ladama da dana Sanin cewa yara niiima ne kuma Allah yakanba Wanda yasone a lokacin dayaga dama Yaya rahmane aduk inda suke yau Idan mune gobe bamu bane Lokaci daya ya rungume Iman yana kuka lokacin da Iman yazama big boy saidai daka ganshi kasan miskini ne.

*BAYAN SHEKARA GOMA*

MD fauzi yayi ritire a muk'amin burgedia Abun gwanin ban shaawa yadda suke cikin jin dadi baba itace bango a halin yanzu bayan rasuwar Malam, Wata rana Atika sukaje Kaduna ziyara Kwatsam suka hadu da Mash Atikace ta ganeta Don MD bai ganeta

“tsaya Dan Allah inje wajen mash inbata koda Wannan snacks Dinne” haka ya dubi atika yace tana haukan salon ta cimiki rauni? Tohni babu ruwana ehe

Atika tace taji tagani ta isa wajen mash tana ganinta ta kare mata kallo

“Atika? Kece kuwa? Daga ina kinga yadda na zama koh hauka nakeyi” saita kwashe da Dariya atika sai kuka takeyi mai tada hankali Wanda saida MD fauzi yaji tabashi tausayi yarasa meyasa atika zuciyarta takeda Rauni, Ta ajiye mata suka wuce bayan sun dawone akan hanyan kawo suka tsinkayi mutane anyi cin cirindo mezasu gani gawan Atika kwance bata motsi duniya Atika ta kwarma ihu tace

“Mash!!!!!!!”.

[7/16, 7:59 AM] Humairah Melody: *CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)

     

*@HUMAIRAH B MELODY*_*Dedicated to*_

AUNTY SIS

FIRDAUDI SODANGI

RASH KARDAM

KHALEESAT HYDAR

UMMI AYSHA

MRS UMAR

NANA DISO

LUBABATU MAITAFSIR

BATUUL MAMMAN

AYEESH CHUCHU

SAFIYA ABDOOL

MIEMIE BEE

SANAH UMMU BENA

SANAH S MATAZU

RUFAIDA OMAR

_*Allah yakara baseerah girma da daukaka LYSM😍❤😍*_


71-75


Nan Sukayi kwatancen gidansu ana zuwa aka tarar sun tashi baasan inda suka koma ba haka akayi mata sallah mutane tsiraru suka sallaceta ciki harda tsohon mijinta MD fauzi haka suka koma zuciyansu cikeda Tausayin halinda Atika take ciki sun tuna baya Baba kuwa koh a jikinta wai an tsikari kakkausa koh gexau

Rayuwa MD fauzi da Atika tayi kyau mutuka Allah yabarta dashi badon iyawa koh dabaranta ba saidan ikonsa, Bb kamal yaxama abun alfahari bayan wasu yan shekaru habiba, Zainab, Halima sun girma rana guda akayi aurensu kowacce aka kaita gidan mijinta Bb kamal kuwa Anyi anyi yayi aure yace tabbas shi tsoron mata yakeyi saiya natse tukunna, BB kamal kuwa toh bamace zaiyi kwantai ba saboda laluransa shima zai samu daidai shi.


Alhamdulillah...

_*Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai daya bani ikon kammala Wannan Dan rubutu nawa Idan nayi kuskure Allah ya yafen abunda na fada daidai Allah yasa ya isa ga mutane*_

Post a Comment for "CIKIN DA BA,A SO CHAPTER B KARSHE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...