CIKIN DA BA,A SO CHAPTER A - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

CIKIN DA BA,A SO CHAPTER A

CIKIN DA BA,A SO CHAPTER A

- - Post a Comment

 CIKIN DA BA,A SO CHAPTER A


*CIKIN DA BA'ASO*@HUMAIRAH B MELODY


*Yabo*

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah buwayi gagara misali daya bani ikon fara wannan littafi cikin aminchi da yardarsa Allah don girmanka kasa in kammalashi lafya.


*JINJINA*

GA AUNTY SIS๐Ÿ’ž bana mancewa dake Kamar yadda bawa baya mancewa da sallah matukar shi musulmine Kaunarki tana Jana Allah ya ida miki dukkan nufinki AMIN.


*KAWAYENA*

Akoda yaushe daku nake yawo a sararin zuciyana

MARYAM SOKOTO(granny)

MARDIA

ABEEDA

MIENERH

MRS FAWWAZ

RABI GOMBE

ZAINAB SULYMAN

SALMA JIBRIN

XOXO

ANEESA AR

MJAY

AYSHA WAKILI

dasauran wayanda ban kiraba ba mancewa nayi dakuba ah ah lokacine baxai bani dama ba #Ana tare#๐Ÿค.


IYAYENA ABUNFAHARINA

bana taba mancewa daku a farko da karshen Alkalamina ina sonku ina kaunarku akoda yaushe DR. MB SHEHU & MALAMA DIJE WADA MANZO my love for you will never dies๐Ÿ˜๐Ÿ˜˜.


YARA MANYAN GOBE

AHMAD SM

MUSA SM

DAUDA SM

FATIMA SM

MUSTY SM

JIDDA SM

ABDALLAH SM

SAIF KT

ISMA'IL KT

SAHURA SA

SADIYA S ADAMU


YAN MATA ADON GARI

ENGR MARYAM(UMMI)

DR. ASMA'U KT Allah YA IDA NUFI

HAFSAT MAIDUGURI

AMINA MAIDUGURI

Allah ya rayaku musha biki


_*SADAUKARWA CE GA MATA MASU CIKI DAKE FADIN DUNIYANNAN nayi hasashe a bisa matsalolin da muke samune shiyasa nace Bari in baje basirata don ban yarda in Karu nikadai ba sai daku makaranta muke samum cigaba haka saidamu marubuta ake samum duk wata hanya ta kulle baraka*_.

Banyi wannan littafi don wani koh wata ba Idan har labari yazo daya toh ku Sani ARASHI NE.

_*Goron sallah ne ga daukacin FANS dina dake fadin duniya Allah yasa muna cikin masu saa Allah yayi mana Muwafaka Allah ya maimaita mana*_Amin


1-5


*****

Gari yadau zafi kowa ka gani gumi yake ketawa a wata unguwa dake cikin Zaria Wato *GYALLESU* unguwace wacce takeda dumbin tarihi a fejin mulkin Nigeria inda kowa ya Sani nanne unguwar da shahararran malamin shi'annan yake Wato sheikh ibrahim zazzaky

Bayan gidansa kadan inda ake cewa *layin baba shani* wani shararren mai dukiya ne dayayi tashe Allah ya gafarta masa amin wani mutumina nagani zaune ya zabga uban tagumi da alama yana cikin tsananin tunani komai yasashi irin wannan tunanin? Kubiyoni yar mutan zariya donjin diddigin labarin, Tashi yayi ya kutsa cikin wani gidan k'asa Wanda kai dagani kasan akwai b'urbushin talauci acikin gidan Allah ka rabamu da talaucin duniya dana lahira amin.+


“Atika wannan talauci ya isheni ace Kullun kai kenan tagumi Idan kaci na rana tunaninka na dare gaskiya wannan Abu ya isheni gaskiya aikin soja zan shiga saboda in tsira da sauran mutuncina kiji dadi iyayena suji”

Atika ta kallai cikeda mamaki

“MD FAUZI wannan wane irin magana Kakeyi Mara dadin ji da saurare? Wane irin aikin soja kaikuwa? Nidai gaskiya saidai kanemi wani aikin amma ba aikin soja ba”

Tabe baki tayi tana buga kafa MD ya tsaya baki bude yace

“Atika koh ki yarda koh karki yarda aikin soja Kamar najeshi tunda na aureki shekara daya kenan su Baba ke bamu abinchi gaki da ciki ai Yau da gobe sai Allah yanzu Idan kika haihu su zasuyi mana hidima? Suyimun aure suci dani sannan su cida matata harda da? Haba atika adinga Sara ana duban bakin gatari mana”.


Haba Atika ta rike chan cikin zuciyanta tace “Ina ni ina zamada soja haka kurum wata rana in bata mishi rai ya halbeni badani ba ai gwara in tattara in koma NAGOYI rigarmu inci gaba da tallan nono da fura”kusa da Atika ya matso ya rungumeta sosai a jikinshi yana shafa kwantaccen gashin kanta

“Atee kiyi hkr bada son raina zan shiga soja ba babune tasa haka koda wasa karkiji komai ina sonki matata” shafa cikinta yakeyi yana magana a gajiye alaman sushiga Daga ciki itako tace Sam batasan wannan ba waje yafita yabarta tsaye, tana naxari

“Atee ina sonki sona hakika kyawunki kadai Abun kallone kafin ace akaiga wajen k'wanciya hmm dole insamu Abun duniya kodan kiji dadi Atee danaji muryarki sai inji sanyi amma maiyasa bazaki amince mun shiga aikin soja ba shine a aiki mafi sauki Wanda zakasamu albashi daxaran kagama ka pension ga gratuities duk aciki ka Karin igiya daza'ayi maka wata rana saika zama wani shege”.


Wani matashine kaman MD fauzi yazo yana k'wadamai kira amma ina ya tafi tashi duniyar,

“Mutumina Na Atee bada kanka asare itace dai itace dai daya tamkar dubu Atee tafi mata dari”bacin kirarin da MD bello yayiwa MD fauzi ina gayawa mai karatu daba k'aramin naushi zai kaimai ba don shi gani yake Kamar mafarki yakeyi aka tadashi, yana dagowa yayi dariya

“MD bello kai wani irin bukar ne bacin ka ambaci sunan Atee Wallahi dasainayi sama dakai” dariya suka kwashe dashi suka tafa MD bello yace

“MD lafya naganka cikin yanayin tunani? Kodai wani abunne yafaru ka kasa ka sanar dani?”

“Abokina kenan Damuwa inada ita katayani rarrashin Atee ta Aminche mun in shiga soja kona tseratar da ita daga shiga wani yanayi bayan zuwan danmu duniya Banaso abinda ke cikinta yataso cikin Kuncin Talauci”.*CIKIN DA BA'ASO*


     

@HUMAIRAH B MELODY
6-10


MD bello yayi shuru na Dan dakik'a sannan ya gyara zama

“Mutumina Atee k'aramar yarinya ce sannan inhar ka iya yadda zakayi convincing dinta Wallahi zata aminche karka damu aikin soja Kamar mun samu kaida ma kayi aure kenan ina nikuma da nake hari”

MD fauzi yayi murmushi yace

“Allah yabarmu tare abokina Kai kadai kake iya sharemun kukana tabbas tarayyata dakai Alkhairi ne burinka kaganni cikin farinciki Allah sarki haka duniya ta gada”

Nan suka taba hirar duniya sannan kowa ya wuce gida, Kafin fauzi yashiga sasan sa dayake gidane Dan madaidaici saida yaje wajen baba Wato mahaifiyarsa suka gaisa sannan yazo mata da zancen shiga aikin soja Hankalinta yayi matukar tashi amma saboda yadda MD ya saita natsuwarsa tuni ya gamsar da ita komai haka ta aminche tayi mishi alkawarin zata sanarda Malam shima bazaiki ba, murna ce Kamar MD zai zautu yace

“Yes tunda suka yarda Dole Atee ta yarda ta kuma aminche duk don ita nake wannan killi fadin”sallama yayi gamida fadawa Dakin ganin Atee yayi ta rakube a karshen gado wani irin kallo ya watsa mata Wanda ita tasan kona meye jiki ba laka ta rarrafo tazo inda yake ya rungume MD tace

“Ina kaje shuru shuru haka? Abunka da kishi irinna Atee shikuma MD fauzi yace

“Gurin budurwa ta naje kuma ta aminche mum Dari bisa Dari in shiga aikin soja bakiga irin karfin gwiwan data bani ba hmmm”Idan kaga Atee mai karatu sai kaci dariya gaba daya ta kasa zama illah mutsu mutsu datakeyi idanuwanta sunyi jajir tace

“Kana nufin budurwarka tafi matarka toh kasani baka isaba aikin soja badaniba Wallahi saidai kasan yadda zakayi dani”MD ya daure fuska yayi kaman baisan ma tanayi ba ya janyo farantin abinchi yafara zubawa tuni ta duro daga gado tace “wani salone kake zubawa kanka abinchi dakanka?”.

+

Zata taba plate din abinchin kenan ya riketa ya kalleta ido cikin ido yace “Karki sake ki tabamun gwanon abinchi tunda bakida tausayin kanki dana mijinki inhar kikaki amincewa da kudurina wannan kadan kika gani” abinchin yaci gaba daci yagama yayi shimfida a kasa ya k'wanta daman dare yayi cikin ransa yace

“Lallai Atee bakida kishi akaina sai Yau na tabbata” haka Atee ta tsaya kallonsa Abun duniya ya isheta shurun dayajine yace

“Kuma kisani gobe zanyi komai in gama nanda wata daya ina gidan soja tunda uwata da ubana da budurwa ta suka aminche kada Allah yasa ki aminche ”.

Bacci dai sai barawo ya sace Atee shiko bacci yake harda minshari washe gari Atee tashi tayi taga ba Fauzi ta leka koh ina amma ina bata ganshiba, daki ta koma dayake ta makara tayi sallah tafara share share Kamar yadda ta saba sannan ta daura ruwan wanka tayi tana fitowa taga tire daukeda biredi da fulas din ruwan shayi dauka tayi cik takai daki ta gama shiryawa amma ba MD breakfast dinta tayi takoma ta kwanta kwatsam saiga wata kawarta da sukayi balbelu tare dadi Kamar zai kaita lahira ya dawo da ita tace

“Kai Mima Ashe rai kanga rai amma ba karamin jin dadin zuwanki nayiba koh banza zaki sharemun hawayena dasukaki kafewa”Mima tayi far da ido tace “Lafya daiko koh dai Hawan jinice ta saki gaba?”

Atee tayi saurin rufe mata baki

“rufamun asiri Ai Idan nace ga aibunta nayi karya zamanmu lafya mukeyi da ita Wallahi tun zuwana gidannan ban taba daura sanwa ba sai abunda nakeso kowa keci acikin gidannan  matsalata dayace MD Fauzi narasa yadda zanyi in hanashi shiga aikin soja”

Mima dake gefe tace “Amma ke bakida hankali shine Abun tashin hankali Kawata Idan bakiyi mishi fatan Alkhairi ba da fatan samum sa'a ba me kike tunanin zakiyi? Lallai bakida imane bare tausayi” saboda tsabar haushi Mima ta kasa cewa uffan Atee tace “Kawata abunda yafi batamun rai shine wai budurwarsa ta aminche?”

“K'warai kuwa dole ta aminche saboda me tanasonsa kuma tanason cigabansa koh karya ne ma yaci ace kin dauki darasi ai danice a lokacin zance nima na aminche koh Dan in maidamai da aniyarsa ki tsaya kallon ruwa wata tazo tayimiki kafa”Shuru Atee tayi daga bisani tace

“Kawata maganar ki dutse kin bani shaawara nayarda na aminche”

“Dadai yafi miki Idan yasamu aikin ke xakiji dadi dakeda danki kinga daganan iyayensa sun samu saukin wani dawainiyan kingama saidai ya siyo kaysn abinchin yakawo musu” Atee tace

“K'warai ma kuwa ”nan sukayita hira Itadai Mima mutuniyar Arzikice shawara babu wacce bataba Atee ba anan Mima taci na rana saida yamma sakaliyya ta tafi, harta tafi MD bai dawoba Atee duk tabi ta damu abunka da miji da mata.*CIKIN DA BA'ASO*


     

@HUMAIRAH B MELODY
11-15


_*Godiya ta musamman ga yan'uwa da abokan arzuka Ngd k'warai da nuna damuwarku a kaina Dafatan Anyi sallah lafya ..*_๐Ÿ˜˜


Harta taga take lek'awa amma babu shi babu labarinsa inta kaitawa mai karatu saida Atee tayi bacci kannan MD Fauzi yashigo, yana shigowa shimfida yayi ya kwanta ai washe gari kafin MD ya tashi Atee ta tashi tana jiran ya farkawarsa, juyin daxaiyi yaji yaci karo da k'afa mikewa yayi yana salati, Kafin ya aje hannunsa Atee tace

“Mijina Ina kwana? Dafatsn ka tashi lafya? hamma yakeyi amma tunda yaji tace mijina batace MD fauzi ba ai saiyaji duniya ta dawo mishi Sabo ji yayi Kamar ya dauki Atee ya dagata sama,

“Lafya” kawai yace mata ya tashi zai fice tayi saurin shan gabansa tace

“Haba koh ba komai ni matarka ce kayi hkr ka tsaya ka saurareni Dan Allah kayi hkr inhar na bata maka rai Kaine kwanciyan hankalina Wallahi banida sauran natsuwa Idan ka k'auracemun Mijina na yarda na aminche Ka shiga aikin sojan Allah yasa Hakan shiyafi Alkhairi a gareka” MD cikin sauri ya juyo yace

“Atee kin aminche? Kin aminche inshiga aikin soja oh my God Atee baki taba farantamun rai irin yadda kika farantamun yauba” da sauri ya rungumeta yana sumbatarta takoh ina yana murmushi Abun gwanin ban sha'awa ita kanta sai taji wani sauki acikin ranta, taji son mijinta har cikin ranta,

“Atee tunda Allah yasa nagama Karatun Jami'a banida wani buri illah iyaka inxama soja koh na ruwa kona kasa kona sama, Atee aiki wuya yakeyi a wannan zamanin kiduba kigani Shekarata Hudu da gamawa amma babu aiki aikin force shine aiki mafi wahala mafi sauki gana kammala training kayi pOP abaka aiki da Albashi Wannan aikin sojan taimakona za'ayi Atee Fatana da rokona a gareki Atee kici gaba dayiwa mijinki Adu'a Allah ubangiji yasa yatafi a sa'a”Tuni Atee tace “Amin ya Allah Fatana nima Allah yasa kacimma duk wata nasara dake tattare da wannan Aikin”Amin sukace gaba dayansu sannan sukaci gaba da har kokinsu.

+

*Bayan Wata Daya*

*****

List yafito sunan MD Fauzi shine a farkon list na biyu dadi Kamar zai kasheshi Sojan kasa yasamu haka yafara shirin tafiya dayake course din *SHORT SERVICE* Zaiyi Wata Tara akeyi Atee tayi murna yan'uwa da abokan arzuka sunyi murna ilai MD bello shima yasamu shima kuma sojan kasa murna wajen abokai biyu ba'a magana rananda MD fauzi zai tafi ranan cikin Atee yashiga wata na bakwai, tayi kukan rabuwa da mijinta k'warai dukda yana namiji saida kwalla suka cikamai ido saboda yadda yasaba da matarsa Rungume ta yayi yace “Atee kisa aranki ina sonki koh ba jima ko ba Dade ke matata ce nabarki a hannun Allah sannan a hannun baba Idan Allah yasa kin haifi da namiji nasa mishi suna *KAMAL* Idan kuma mace kika Haifa nasa Mara suna *KUBRA* shafa cikinta yayi acikin daki yayi kissing kannan yafito suka kama hanya sai NDA Kaduna, inda anan zasuyi training dinsu na wata tara, kwanci tashi anyi wata biyu da sati uku da tafiyan MD fauzi Atee ya haifi danta namiji santalele San kowa kin Wanda yarasa, kyakkyawa ajin karshe tabbas Atee saitayi rabon fada da yanmata babu inda yabar MD Fauzi haka baba ta tsaya tsayin daka ganin Atee tasamu cikakken kulawa fatan ta a Kullun shine yadda suka wahala ganin MD yayi karatu Allah yasa yaji Kansu gobe, Yaro yaci suna *KAMAL Muhammad Fauzi* Haka akayi suna aka watse kamal yayi goshi k'warai.

Haka Atee take kara wayewa saboda tana haduwa da mata iri daban daban harta fara Sanin meye kishi dashi so gaba daya MD Idan yasamu dama suna waya da Atee suyita love Abun ba'a magana har MD yadinga tunanin Anya kuwa Atee ce?.

*WAYE MD FAUZI????*

*****

Asalin sunansa Muhammad Fauzi Lawal Asalinsu yan Zaria ne cikin ganuwa a wani unguwa Albarkawa mahaifin Fauzi security ne acikin ABU Fauzi shine da na hudu wajen Malam Lawal saboda kafinshi akwai wasu su uku wayanda mahafiyarsu ta rasu A takaice MD fauzi shine auta amma a wajen Mahaifiyarsa Habiba shine da daya tilo tundaga shi bata sake wata haihuwa ba koh batan wata Hakan baisa hankalinta ya tashiba bayan ya shekara TALATIN yana aiki akayi mishi ritaya shine yasamu yasiyi gida ginanne a cikin  Gyallesu suka bar cikin City amma dangi kowa nachan.*CIKIN DA BA'ASO*


     

@HUMAIRAH B MELODY


21-25

Ta shafa nan ta taba chan yawancin maza abunda sukafiso kenan kulawa da hira mai ratsa jiki da zuciya toh haka Atee ta kasance yiwa MD koda yaushe, misalin karfe Goma MD ya shirya tsaf zuwa kasuwa saida sukayi shawara da Atee yayi rubuce rubuce abunka da Dan boko komai saida ya k'a'ide yayi lissafin abunda zai kashe kasuwa yaje yayimusu siyayya yayiwa yan'uwansa suma saboda sun taimaka masa lokacin dayake Neman taimako yayiwa Atee itama da baby kamal duk Abun nema saida ya siyo musu Ciki harda sutura nagani na fade daman shi MD Dan aji dadi ne, Golf guda aka ciko sai gida haka aka dinga shiga dasu tsaf ya zauna yawarewa kowa amma na iyayensa da matarsa yafi yawa haka suka zauna sukayi magana ta fahimta

“godiya ta tabbata Allah mai kowa mai komai daya nunamun wannan ranan da mukesa Ran munyi bankwana daduk wani wahalar rayuwa anan nakeso inyiwa iyayena godiya bisaga dawainiya dakukayi dani tsawon lokaci, Yau na daukemuku duk wata nauyi Atee xata fara daura tukunyarta daban lokaci yazo da yakamata ku huta kuma”Dariya kowa yayi ciki harda Atee da farinciki duk ya lullubeta tarasa ta ina zata fara itama godiya tayi musu Sannan yabada kayan akaiwa yan'uwansa suma su shaida yafara aiki, sunji dadi k'warai sunji dadi don har godiya sukazo yimushi.

Saida MD fauzi yayi wata biyu cikin jin dadi da kwanciyan hankali tareda harken idaniyansa Atee yashirya tsaf don zuwa UNIT dinshi inda aka turashi don serving haka Atee ke hada mishi kayansa badon ranta yasoba don bataji zafin tafiyansa Training Kamar yadda takeji yanzun ba don acewarta Yanzune tasan meye miji acikin rayuwarta.+


Ya shirya tsaf don wucewa KADUNA Wato inda aka turashi Atee ranta baiso ba har kuka tadingayi Kamar wata k'aramar yarinya MD fauzi yace

“Kiyi hkr Idan na isa nasamu gida cikin bariki saimu koma gaba daya hkr zakiyi ina Kaduna ina Zaria ai zan dinga shigowa inna samu sarari”ina Atee kuka takeyi har saida baba tasa baki “Kaiko Katafi da ita koh daki dayane saiku zauna koh?”MD yace “Baba kenan bakisan bariki ba wata kila daki daya a hada mutum biyu uku har hudu taya zan tafi da ita hakuri zatayi kawai inje in natsu kannan insan abunyi”Haka sukayi sallama har tasha saida Atee ta raka MD ysnata shafa ma baby kamal kai har kiss saida yayiwa Atee mutane sai kallonsu sukeyi suko koh a jikinsu haka Atee ta koma cikeda kewan mijinta Abun faharinta.

*KADUNA*

Tun a kawo MD fauzi ya sauka ya dauki shatan mota zuwa NDA yana sauka yaciro jakar baya ya sallami mai mota juyowan da zaiyi yaci karo da wata matashiya duk ya watsar mata da littafai ciki harda wayarta cikin Ruwa, Zare ido yayi a rude yafara tsamo mata littafanta harda wayarta wacce rakani kashi ce yafara budeta ya hure ya goge itakoh Kallonsa kawai takeyi tarasa mezatace mishi gashi wani Abu takeji akansa jitayi bazata iya rayuwa inbadashi ba, dagowa yayi cikin zazzakar muryarsa yace“Yan mata kiyi hkr abunka da soja komai zafi zafi kiyi hkr kinji Dan Allah banida burin batawa wani Rai koyaya koh da matata ce dake gida” Hannu yasa cikin aljihu yaciro kudi zasukai naira dubu biyar yace

“Gashi kyasai wasu littafan Dan Allah kiyi hkr”

Takasa amsan kudin takuma kasa yimai magana sai kallonsa takeyi cikeda Love, shiko sai waige waige yakeyi nidai narasa me yake kallo, budar bakinta tace

“Karka damu Kaji babu komai babu mahalukin dabaya kuskure nima kila wata rana inyi maka laifi” yaji dadin maganar ta gareshi sai yaji son yayi mu'amala da ita cewa yayi

“Sunana MD fauzi lawal ” koh zan iya Sanin sunanki?

Wani dadi taji tace “Sunanan MASHAHURA Tanko” haka kawai tafadi ta wuce saboda jitake kaman tayi tsalle ta tungumeshi.

*CIKIN DA BA'ASO*

    
@HUMAIRAH B MELODY
26-30

Binta yayi da kallon wata mota yaga ta bude gidan baya ta shiga saida motar tayi nisa kannan ya tuna bai tambayeta lambar wayarta koh adireshi ba wani haushi yaji kutsa kai yayi bakin gate aka tsareshi yakawo ID card dinsa kafin subarshi yashiga amma da mamaki yanemi ID card koh kasa koh sama babu tuni yaji wani zufa na keto mishi yace
“Am LT LAWAL MD fauzi mune aka yaye kwanakin baya Dan Allah Kuyi hak'uri zuwa gobe za'a kawo mun kila gida na barshi kuma gobe zanyi reporting to work” ai koh kallonsa basuyi ba gasu kananan sojoji amma sai wani fizga sukeyi dabaya ya koma yajingina da bango ya dafa kai yana huci chan cikin ransa yace
“lallai ne yarannan kun masifan samoni don banida ID kun dauka nima irinkune wahalallu? Tunda safe yake wajen gate sun hanashi shiga ciki yayi azahar laasar duk waje.
MASHAHURA ce zaune Cikin class sanye da doguwar bak'ar riga ana lectures duk hankalinta baya wajen malamin tuni ya wurgo mata wata dank'waleliyar tambaya amma ina tayi nisa harya tako yazo inda take batasan yanayi ba saida ya buga tebur yace “Mashahura lafya kika zabga uban tagumi? ” firgigit ta dawo Daga tunanin datake tareda ambatan MD fauzi cikin rashin fahimta Saif yace
“waye MD FAUZI? Mashahura?”ai tuni ta daburce don tasan irin sonda saif yake mata da kishi yana iya haukace mata cikin sauri tafito da ID card tace
“Sir kagani wanine ya fadarda Id card dinshi shine na tsinta kuma sojane Nasan baza'a barshi shiga Bariki ba imba wannan shine Abun duk ya dameni kaga na shiga tunani Dan Allah sir pardon me pls inje inkaimai pls sir ka aramun motarka” magaba takeyi amma tuni Saif ya tsareta da idanu gaba daya Mashahura bata cikin hayyacinta taya zan bata mota noo impossible.
+
Kallonta yayi yace “Saidai kiyi hkr Mashahura I can't” kallonsa takeyi tana wani irin naxari gashi lokacin zuwa a dauketa baiyiba normally Karfe shida take fita lectures,
“Ok baxaka bani ba good and fyn (Yayi maka kyau) tashi tayi fuuu tafita yan class sun rasa maganar da akeyi tsawon lokaci, banda Shukra babu Wanda yasan halinda saif da Mashahura suke ciki, binta yayi da kallo saboda yarasa abunda zaice mambari ya hau yaba dalibai hakuri kannan yaci gaba da karatu, waje tafita ta zauna direba takira take sanar dashi tagama yazo ya dauketa haka akayi, Har harabar KADSU Kaduna state university yashiga kafin saif yafito ta shige mota ga uban go slow a hanya dukta kagu su isa gaba daya cikin garin Kaduna traffic ne tun baran kawo, cikin ikon Allah suka kutsa har suka kama hanyan NDA suna isa bakin gate Mashahura ta saurin fitowa da gudu ta isa inda MD yake tace “Alhamdulilla” MD da sauri ya dago cikeda mamaki yaga Mashahura lokaci guda yaji duk wata damuwa ta gushe yace
“Yan mata barka da dawowa kardai ace cikin wannan Barack din kike?” dariya tayi tace
“Kayi hkr nayi maka laifi na tafi maka da ID card saida ina lectures nagani kayi hkr cikin ladabi taikamai” zata juya kenan yace
“idan bazaki damuba pls kibani lambar wayarki kozamu dinga gaisawa?” bata bata lokaci ba ta bashi 090600..... Da sauri tashiga cikin mota suka shige sai lokacin ya dauki jakarsa ya nufi inda kananan sojoji suke yanuna musu kannan yashiga amma MD fauzi ya kullacesu cikin ranshi k'warai tabbas Idan suka shigo tarkonsa sun bani, haka yashiga yaje yayi reporting aka bashi gida guda k'ato anan ya yada zango Atee kawai ya tuno tun safe basuyi wayaba cikin sauri yakirata lokaci guda tace
“My life lafya kake kuwa kodai aikin ne Daga zuwa? MD fauzi
Yarasa Abun cewa nan ya labarta mata komai amma bai sanar da ita zancen mashahura ba, bayan wata daya MD ya mance dawata Mashahura kwata kwata sai shiri yakeyi nadawo da Atee cikin bariki saboda yanaso tayi Azumi tareda shi saboda yagaji da siyan abinchi, haka akayi komai sabo yasanyawa Atee Daga ita sai kayan sawanta dana bb Kamal baba sunyi kewa amma basu damuba saboda irin hidimar da yake musu babu dare babu rana.
Rayuwar Atee a NDA gwanin shaawa MD sai hidimarsa yakeyi amma gaba daya ya shaku da Mashahura Kullun cikin zuciyarsa take wuni gashi baiyi saving lambarta ba, Kullun saiya fita shawagi Koh Allah zaisa ya hadu da ita Kullun Atee burinta kulawa da mijinta bata kin kiran mijinta a kowani yanayi hatta lokacin da batada tsarki saita farantama mijinta rai Amma batada wata magana saina cewa inhar MD fauzi yayi aure zamana dashi yazo karshe abunda yake Daga mishi hankali kenan.

Tirkashi......๐Ÿค”*CIKIN DA BA'ASO*


     

*@HUMAIRAH B MELODY*


_*Comments dinku shizai bani karfin gwiwa Ina saurare kubini a wattpad Aysha2017 don samun novels dina Wanda nakeyi da Wanda na gama kuyi like kuyi comments kuyi sharing kuyi following ngd❤๐Ÿ˜˜๐Ÿ‘๐Ÿป*_


31-35


Akwana a tashi an shafe watan Azumi da sallah Zaria sukaje sallah bayan dawowarsu, MD yakoma aiki amma Kullun burinsa ina zaiga Mashahura? Wata dabara ce tazomai ya dauki BB kamal sai bakin gate yaje ya tsaya k'watsam Koh minti goma baiyiba saiga motar mashahura Cikin sauri yaje wajen yana buga musu glass Tuni ta bude tana dariya ta sauka tace direba yayi gaba yajirata

“Kiyi hkr Mashahura nayi miki laifi na batar da lambarki kitaimaka kibani wata?”dariya tayi tace

“Baby waye wannan” tafadi tareda mika mishi hannu amma BB kamal yaki zuwa saboda baisan kowaba sai mum dinsa, taci gaba dacewa

“Baka daukeni da muhimmanci ba shiyasa ka batar babu komai” wata lambar tabashi Sannan sukayi sallama ta wuce tana zuwa gida kan gado tafada tace “Saif meyasa nakejin son MD fauzi akanka meyasa kadaina burgeni kwata kwata? Meyasa duk abunda kamun bana ganin ka iya lallai zuciyata da ruhi sun canza shek'a”da wannan bacci ya dauketa amma Duk abunda takeyi gida baasan tanayi ba saboda saif shine Wanda aka tsayar mata zata aura, MD kuwa dadi yaji yakoma gida ita kanta Atee taga chanji Daga wajen mijinta saboda yadda yaketa dariya da murmushi yana ajiye BB ta fita waje gindin wata bishiya yasamu bayan yayi sallan magrib wayar Mashahura takira bugu daya zuwa biyu ta dauka

“Hello”

Shima Daga dayan bangaren yace “Hello ranki ya Dade Lafya kike Koh?”

“Lafya lau nake ya kake ta Auntina ya BB?”wani dadi MD fauzi yaji yadda ta girmama Atee harda tambayan BB Wanda yaki zuwa wajenta, nan sukayita waya Kullun saisun gaisa amma MD yakasa sanarda Mashahura cewa sonta yakeyi so kuma da Aure Kullun wanka yakeyi mai Kamar jirwaye ita kuwa dukta damu ta daina kula Saif shikanshi walakancin da Mashakura take masa yafara kaishi mak'ura amma hakanan yake daurewa, saboda sonta dayake  dukda sun gama watsewa amma bayajin zai iya rabuwa da ita,

Dazaran wayar MD fauzi tashigo toh zata katse na Saif batareda tayi mashi sallama ba Koh wata magana mai dadi.

Kwatsam Mashahura tayima MD kwatancen gidansu daya duba sai yaga Ashe ma kusa suke tabbas daganin zubin gidansu mahaifinta babban sojane, haka rana daya MD ya ware don zuwa wajenta cikin garden aka shiga dashi ya zauna aka kawo mishi lemuka da kayan ciye ciye har yan gidansu suna cewa lallai Yau za'ayi ruwan sama Yaya saif akewa wannan hidimar? Itadai dariya tayi Ta shirya cikin kayan alfarma tana tafe tana yauki, sallama tayi ta zauna tace

“Lafya ka kasacin komai? Saikace wani bako?” MD fauzi yace “tabbas ni bakone saboda nanda kika ganni tsoro nakeji kar gobe a kulleni gidanku babu Wanda yasanni kuma banida wani gata sai wannan aikin kinga kuwa dole in zauna da Rabin jiki”dariya tayi tace “Kafiye tsoro ai dahaka kowa na gidannan zai sanka”

“Mashahura na Dade ina dako”....... Jin horn din mota ya katseshi lokaci daya suka juya da mamaki Mashahura taga saif cikin Motarsa kirar Hyundai 4X.+


Gaba daya tarasa natsuwa a gaban MD wanda ya kafeta da ido ganin ta saki baki cikeda mamaki, cikin ranta tace

“Meya kawo saif gidanmu bayan nayi mishi iyaka da zuwa inda nake bare harabar gidanmu?”  amma saida  maganar ta fito fili MD fauzi ya razana yace shima cikin ransa “Allah yasa wannan bashine Rival dina ba da nayi dakon banza” mashahura tayi saurin waigowa tace

“MD bakayi dakon banza ba Dan Allah ka sanar dani sirrin dake ranka kozan samu natsuwa” shima sakin baki yayi don baiyi tunanin maganar zuci zata fito fili ba, Daidai lokacin da saif ya iso cikin garden din MD fauzi ya mike yabashi hannu amma Saif ya daka mishi tsawa yace “Karka sake ka bani hannu don banyi kala damai Neman aure acikin aureba   har ka isa ka bani hannu daka tafka babban kuskuren da saikayi shakaru aru aru kana jimami”

Mashahura tayi saurin shiga gabansu tace

“MD Dan Allah kayi hkr saif kayi hkr kaima wannan da kake gani he deserve some respect from you atleast he is a luetanant”

“Dakata Mara mutunci wacce batasan daraja da kimar soyayya ba karkiyi tunanin yana soja zanji tsoronsa Wallahi Sam ko daya imma karawane muzuba nidashi shege ka fasa sai yanka kisani duk wani mulki da iko irinna soja baya bani tsoro bare ya dagamun hankali kisani Mashahura bakida Wanda zai iya aurenki saini saboda duk wata niiima da Allah yayi miki Nina fara debeta Sannan naci gaba da morarki harya zuwa yanzu don haka tun wuri ki daina wannan banzan tunanin nacewa zaki zama mai mutunci da kima a idon wani da namiji inhar duk maganar danayi Baku gamsu ba koh Baku fahimta ba toh ina nufin Mashahura You are not a VIRGIN”............*CIKIN DA BA'ASO*


     

*@HUMAIRAH B MELODY*


36-40

Cikin rudu Mashahura ta tsaya tana kallon saif cikin ranta tace “Ka tonamun Asiri saif Ashe dakwai ranan kin dillanci? Ashe dakwai ranan da zatazo kayimun gori budurci na bacin Kaine silar komai? Ashe dai mazinaci baya taba rufawa mazinaciya Asiri wata rana saiya watsa mata kasa a ido duk dadin da saif yake cewa yakeji a kaina Ashe dakwai ranan dazai tozartani a fili a bainar jama'a zina batada rufin Asiri nayi dana Sanin Sanin Saif a rayuwata nayi ladama mai tsanani a yau nagane cewa so shine tushena haka tushen kowani Dan Adam”

Kukane yaci karfinta inda Saif ya juya da niyyan tafiya amma akayi rashin sa'a MD fauzi ya taboshi juyowan dazaiyi ya daukeshi da wani gigitaccen mari ya k'ara dagowa yakara kai masa naushi a kan hanci in takaitawa mai karatu saida MD fauzi yaga yana Neman raba saif da rayuwarsa kannan ya kyaleshi yace

“Ka tafka babban kuskure wajen zama silar rugujewar rayuwar Mashahura Sannan yanzu kana Neman kazama silar zubarda hawayenta noo abunda bazai taba yuwuwa ba kenan inason Mashahura inason ta koda karuwa ce bare a gaban iyayenta take ina sonta sona hakika ina kaunarta kasani kaji da kunnuwanka haka ka jini da kyau bazan taba yiwa Mashahura gorin rashin kai budurcinta gidan miji ba” katso gumin dake kwararuwa daka kansa yayi ya watsawa Saif MD fauzi ya juyo yacema mashahura  “nina tafi” ficewa yayi Mashahura takasa motsawa daga inda take ga saif kwance sai numfashi yake sama sama tace

“Saif bana sonka bana kaunarka mai sonka ma banba makiyi nane kuma kayi gaggawan zanje maganar aurena wannan tozarcin dakamun shikadai zaisa in iya kasheka In huta” cikin gida ta shiga ta wuce kowa a falo da gudu tayi cikin daki ta kulle kanta aciki tayi kuka Kamar ranta zai fita tayi kuka har taji babu dadi wannan itace kaddarar Mashahura, Mai gadi ne yashiga cikin garden yaci karo da mutum da mamaki, yayi sauri yakira mutanen gida dasu kawo dauki haka aka taradda Saif baya koh motsi kowa ya rude saboda ganin halinda Saif yake ciki Asibitin MUSULMI aka wuce dashi tuni suka fara yimai taimakon gaggawa saida yayi awa biyu kafin yasan me duniya take ciki, ankira yan'uwansa sunje Sannan kowa ya watse harda mahaifiyar Mashahura.+


Suna isa gida misalin karfe takwas Hajiya Dada ta dinga kwadawa Mashahura kira har kusan sau uku amma shuru kakeji sama ta hau tana buga mata kofa Amma ina koh alaman mutum babu Mashahura naciki baccin dole yayi awon gaba da ita batasan me duniya take ciki ba haka yayyinta maxa suketa bugawa don ita kadai zata iya sanar dasu abunda yafaru da saif amma ina haka sukayi hkr kowa yakama gabansa karfe biyun dare yunwa ya ishe Mashahura ta sakko kasa kitchen tashiga ta kunna gas ta daura ruwan indomie, ta hada komai ta koma ta zabga uban tagumi saida indomie tafara konewa tafara sata tari kannan ta farka daga tunanin datakeyi, ta zuba tayi daki tafara ci saidai abunda yake damunta MD fauzi yaki ya kirata ta kirashi wayarsa akashe tarasa yadda zatayi haka tagama ci bacci yakara awon gaba da ita washe gari Tunda Safe Hajiya Dada tayi sakko zuwa Dakin Mashahura tana murdawa taji a bude tana isa gareta ta d'aka mata duka cikin firgita ta tashi tana murtsika ido tace

“Good morning” ta tabe baki cikin shagwaba hajiya tace

“Wat is good abt the morning (meye Abu mai kyau acikin safiyan?) Bacin ga dan mutane chan a Asibiti kwance baisan Wanda ke kansa ba”

“Wai hajiya wakike magana? Ne nifa ban ganeba”

“kinci uwaki nace kinci ubaki saif din dayaxo wajenki jiya zakice wai wanake magana? Kanwar ubanki nake nufi Rabi”

“Hajiya I have nothing to do with saif a halin yanzu na tsaneshi bana sonsa bana kaunarsa Daidai da minti daya aure dani dashi babu makaranta daga yau na gamata matukar shizai daukeni Chem 301 inko zanci gaba saidai inta samum carry over, hajiya ki fahimci wani Abu Saif bai chanchanci zama mijin yarki MASHAHURA ba bai chan chanta ba kwata kwata hajiya kunyi mun alkawarin cewa Wanda nakeso shizaku auramun koh? Toh banason saif koda sanadiyyan fadin haka zai kaishi ga halaka I don't care”

Hajiya Dada ta shiga rudani wace irin kiyayya ce lokaci guda tashiga tsakanin Saif da Mashahura? Tambayan da tayiwa kanta kenan kuma tarasa amsar dazata bawa kanta.......


Tab๐Ÿค”*CIKIN DA BA'ASO*


     

*@HUMAIRAH B MELODY*
_*Pls need your Prayers๐Ÿ‘๐Ÿป Akan wani Abu dayasani gaba๐Ÿ˜”*_


41-45


Tashi tayi ta fice itakoh Mashahura mik'a tayi tayi salati Sannan ta gaida ubangijinta tayi breakfast ta shirya don tafiya makaranta da isarta tashiga lectures lokacin lectures din saif yayi kowa ita yake tambaya Abun mamaki Mashahura tace batasan inda yakeba shukura ce tayi tsulum tace

“Kai Mashahura ace duk yadda kuke ace bakisan inda yakeba? Bakisan abunda ya hanashi zuwa school ba? Dakwai lauje cikin nadi Wanda kike boye mana”

Tafi kawai sukaji Mashahura ce ta tashi tace

“Nifa bari kuji dashi daku da lectures din kunyi tsururu in tsaya maida muku zance kun Dade nifa bari kuji daga yau na daina shiga class din chem 301 don haka kowa tasa ta fissheshi kowa takai takai gobarar gemu” Jakarta ta dauka ta tafiyarta Shukura sakin baki tayi Abun ya dameta amma sai ta basar wayarta ta Ciro ta dailer lambar Saif amma sai taki shiga takira yafi sau shurin masaki amma bata shiga, haka students sukayi jugum jigum har lokacin tashi yayi Mashahura duk tayi attending sauran lectures din hankali kwance tafito kwaras kwaras tana tafiya direba tagani Tsaye da sauri tace

“Malam sannu da zuwa pls inaso muje Asibitin musulmi don ganin Mara lafya” babu musu chan suka nufa suna isa ta sauka hannu rabbana babu koh lemu bare biredi karan takalminta kawai akeji tana zuwa inda saif yake tayi sa'a shi kadaine kwance idanunsa a rufe, Tsaki tayi Wanda saida ni humairah na gwada amma ina koh secont biyar bai kaiba yadda na Mashahura yakai sakan talatin dana lissafa, tsakinne yasa Saif bude ido da mamaki yaga Mashahura a gefensa tayi kicin kicin da rai tace

“Hmmm maganin Mara ji kenan angaya maka cewa soja wasane aikin banza harara a duhu ai koda koma ta lalace tafi biyar Albarka koh ka manta cewa NAMIJI BAYA KAD'AN? Koh ga mace bare kai namiji ba zuwa nayi in gaidakai ba zuwa nayi inji shin cewa ka janye koh kuwa saina raba maka tsiya a kasuwa?”

Shuru yayi hawaye ke zuba a idanunsa masu dami Wanda suke iya tarwatsa zuciyar mutum yayi karfin halin tashi yace

“Duk abunda kikace Mashahura daidai ne banida zabi amma inasi kisani magana bata a hannuna tana hannun iyayenmu, duk shawarar dasuka yanke akanmu banida Abun cewa amma kisani Mashahura bacin Raine yasanni fadin wayannan maganganun kiyimin rai ki gafarceni kiyafemun Bazan iya rayuwa ba tareda ke ba kece kwanciyan hankalina kece duk wani sassa na jikina Idan baki zan iya rasa Raina kiyi hkr” kasa saif ya fado ya durk'usa yana kuka......

+

Tabbas saif yaba Mashahura tausayi amma saita basar tace

“Kasani koda maza sun k'are bani ba auren ka saif inamai baka shawara kayi gaggawan janyewa saboda ina iya zama silar barinka duniya koh ka manta abunda akace ne

Mazinace sai mazinaciya? Amma matuk'ar ta tuba tana iya auren Wanda ba mazinaci ba ta maida lamuranta ga Allah komai saiya zama labari, bazan iya aurenka ba saif tunda ka tozartani na tuba nakoma ga Allah nabar sabon Allah amma ina gargadinka ka kuji haduwarka ga Allah live in peace” juyawa tayi ta fice koh kara waigensa batayiba wajen fita Mashahura ta bige k'anwar saif  Wato *Amma* wacce itake binsa wajen haihuwa koh juyowa batayiba bare tabata hakuri dayake Amma itama ba kyalle bace babban yadi ce ta janyo Mashahura ta wanka mata mari tace “Tabbas na tabbata gidanku babu manya har kin isa ki bigeni ki wuce free of charge you must be very stupid nonsense kina kara magana saina wanka miki wani Marin” Mashahura ta mutu a tsaye mamaki ya isheta amma tana kallonta tagane kanwar saif ce Mashahura ta fashe da dariya tace

“Amma bakida hankali, amma inajin kinyi gadon hauka, tabbas ke kincika cikin uwarki da ubanki aini bana fada da bora irinki banda abunki mai jinya maida lamuransa yake ga Allah don Allah yaba Wanda yake jinya lafya amma kin tsaya kina haushi toh kiyi maxa kishiga karki rasa tilon Dan uwanki don Nasan yana gargara” ai tana gama magana ta wuce itakoh Amma da gudu tashiga daki inda saif yake kwance taganshi baya motsi wani Ihu ta fasa tareda kiran NURSE!!!!!!!!!!......*CIKIN DA BA'ASO*


     

*@HUMAIRAH B MELODY*46-50


Cikin gaggawa sai gasu allurori akayiwa saif, Amma sai kuka takeyi cikin ranta tace narasa wane irin cutane ke damun yaya saif  gashi Idan an tambayeshi baya iya bude baki bare yayi magana mun and dad have to do something abt it Abun is beyond our expectation, Likita ne ya kira amma yace

“Brother dinki yana cikin wani irin yanayi na damuwa yakamata a kiyaye koh asan meye damuwarsa don musan yadda zamu magance komai ”Amma tace

“likita yaki magana yaki cewa komai basan yadda za'ayi ba amma zamuyi wani Abu akai inajin Likita sallama zaka bamu Idan mukaje gida zamusan ta inda zamu bullowa lamarin” haka akayi aka sallamesu suka wuce gida...

******

“MD fauzi lafya tun jiya naga gaba daya hankalinka baya tareda kai, sai wani fushi Kakeyi Dan Allah mijina ka sanar dani komai kasanar dani bakada wata abokiyar shawara a halin yanzu saini aiki nane Sanin damuwanka Dan Allah ka sanar dani”wani irin kallo yayiwa Atee yace“Ki rabu dani ki kyaleni bakida wata matsala da abunda ke damuna, wani garane ya batamun rai amma na hkr komai Dan hakuri ne”Kallonsa takeyi cikin rashin fahimta tace

“Shikenan ngd ka nunamun cewa niba matarka bace kuma ina maka albishir da cewa naje Asibiti ance ina daukeda juna biyu”+


Cikin gaggawa MD fauzi ya juyo yace “juna me?”

Atee tace

“Nasan kaji abunda nace don haka maimaitawa Kamar bata bakine”Md yayi kicin kicin da rai

“Kina tunanin ciki kikedashi? garin yaya? Nawa kamal din yake da har zakiyi mishi kani? Bakida hankali Atee wannan cikin dole Azubar dashi koh kinaso koh bakiso don nida kike gani banason haihuwa da yawa ok banason yawan haihuwa Saikace wata bera shekara daya har kinyi ciki? Wato duk bayan shekara zaki dinga haihuwa toh bazai yuwuba kisani sai bayan shekara Biyar biyar zakina haihuwa”

Atee ta shiga rudani tuni idanuwanta suka ciko da kwalla tace

“MD ban gane me kake nufiba kana nufin in zubarda wannan cikin? Wanda wasu ke nema ido rufe Allah bai basuba ni kake cewa bera? Allah sarki dadinta ba a ruwa nasha ba Kuma kasani ai kaza bata kwai saida zakara meyasa tuntuni baka sanar dani hakaba? Ai dako kamal ban haifaba matuk'ar Allah ya bani mahaifar haihuwa, haihuwa babu kakkautawa saina haifi iya kwaina a duniya saidai in zamu daina kwanciyan aure dani dakai mtwww” Atee taja uban tsaki ta shige daki ta dauki kamal tana lallashi dayake ya tashi daga bacci,

Tun daga ranan babu mai cewa kowa komai har an shafe wata guda iyakaci Atee ta dafa abinchi ta jera akan dinning table ta shige daki taci nata duk wata hidima tana mishi amma babu wata Kalma mai dadi koh magana dake shiga tsakaninsu,

Soyayya kuwa dashi da Mashahura tayi nisa har yana shirin turawa gidansu Saif kuwa ya hadu da cutar so yakoma Kamar zautacce koh lectures din ya daina zuwa an dakatar dashi har saiya samu sauki,

Wata safiyar litinin ne Atee na kitchen tana kokarin hada breakfast MD fauzi yashigo yace

“Idan kin shirya acire cikin kina iya mun magana in kawo miki magani kisha koh muje Asibiti a cire kafin yayi girma”mai karatu Idan ka tanka Atee ta tanka koh kallonsa batayiba bare tasan yanayi zan iya cewama Atee bata tsinci komai cikin maganar da MD fauzi yayi ba ganin bata tanka shiba yakara da cewa “Koh kinji abunda nafadi? Kin wani kyaleni ga banza yana magana?”

Saboda tsabar haushi Atee batasan lokacin datace

“Hmmm ai banga marabarka da abunda kace ba don wannan maganar banza Kakeyi cikine nawane kuma inason abuna sai a kyaleni jikinka koh nawa? Cikinka koh cikina? Pls kabarni inji magana ”

Rabawa tayi zata wuce MD fauzi ya janyota ya shake mata wuya yace

“Koh kinaso koh bakiso cikinnan Kamar ya zube ”

Ita kuma tace

“Wallahi matuk'ar cikinnan ya zube ta sanadiyyan ka aure dani dakai babushi MD fauzi bazaka taba birgeni ba Idan baka ba BB kamal guba ka kasheshi ba sannan zansan cewa bakason haihuwa waima in tambayeka boko hauka ne? Kanka aka fara boko ne tabbas Idan haka yan boko suke anyi asaran kudin tara? Pls” sai kici kicin Kwace kanta takeyi amma ina ya riketa gam idanunta sunyi jawur Kamar zata mutu kannan ya saketa ta fadi kasa tib, nan MD yabarta ya wuce wajen aiki koh Karin kumallo baiyiba, itakoh Atee wuya ta rike tana kuka mai cin rai Mikewa tayi zata tashi taji Kamar wani Abu nabin kafarta Da dubawa taga jini cikin rudani ta k'walla ihu Wanda saida MD fauzi yajiyo ta dayake baiyi wani nisaba cikin sauri yadawo saboda yana masifar son Atee sai yaji tausayinta ta kamashi kafin yazo ai tuni Atee ta sumeeee don ba marabanta da gawa๐Ÿ˜ญ.........

Allah ya shiryi wasu maxan yawancin maxa basuson haihuwa bacin zakuga wani uwarsa dozen ta haifesu Allah ya daukaki matan duniya Amin.....*CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)

     

*@HUMAIRAH B MELODY*


51-55


Wani irin kara yayi yana kiran Atee! Atee!! Atee!!! amma ina batakoh motsi ga jini sai zuba yakeyi Kamar da bakin kwarya daukanta yayi cik yafito sai gudu yakeyi da ita cikin bariki har cikin Asibiti tuni aka shiga da ita emergency MD fauzi yashiga rudani k'warai sai zufa yakeyi saida Likita yafito yace anason jini leda biyar kannan ya tuna yabar Bb kamal a gida shikadai, dak'yar ya iya amsa Likita dacewa

“likita asiya jinin koh nawane asa mata aceto rayuwarta Dan Allah nabar One year old baby a gida let me go and bring him ” dagudu ya fita yaje ya dubo Bb kamal da mamaki bashi ba alamansa nan Nasan cewa MD fauzi yana masifar son Kamal tuni ya rude gida gida yadinga bi yana tambaya amma babushi babu alamansa, kuka kawai yakeyi wata bishiya yasamu ya zabga uban tagumi Mashahura ce yazo wucewa taganshi tayi saurin tsayawa ta dauki kamal suka fito tare kamal yana ganin dad dinsa yafara cewa

Abba! Abba!! Abba!!! Cikin sauri ya mike ya rungume Kamal sannan yafara kallon Mashahura yace

“Garin yaya kamal yazo hannunki? A ina kika ganshi? Nashiga tashin hankali k'warai”

Dariya Mashahura tayi tace “Waje naganshi yana kiran Abba shine na daukeshi mukaje waccan shopping complex din na siya mishi ice-cream, ina mum dinsa?”

Cikin rudani yace “tana Asibiti inajin tasamu miscarriage ne yanzu ma chan zan koma”

Zare ido Mashahura tayi tace “How comes? Tasamu miscarriage? Oh my God shiga muje Asibitin” tafadi a takaice

Cikin motar yashiga suka shiga Asibitin tuni an gama mata wankin cikin tanata bacci cikin sauri MD fauzi ya shafa kanta yace

“Sannu Atee kiyi hkr kinji bawai bana sonki bane kidauka Hakan kaddara ne Ina sonki Atee sona hakika Dan Allah kitashi” ai tuni ya juyo ya nemi Mashahura ya rasa ai tuni ta fice waje don kishi yana Neman ya tarwatsa mata rayuwa cikin ranta cewa take dama mutuwa tayi duk na huta da wata kishiya ni humairah Nace me kikeci nabaka na zuba Ai MD fauzi nakine sai yadda kikaso dashi zakiyi...+


Waje ya fito yana dube dube Chan ya hango mashahura tsaye tayi tagumi cikin sauri ya doshi inda take yace

“Mash meye hk kinsan cewa inasonki kuma inason matata Atee kiyi hkr da kalaman dana fadi zuwa sukayi batareda sunyi shawara daniba kiyi hkr” waigowa tayi tana kwalla tace

“Ya zanyi tunda badonni guda Allah ya halicceka ba hkr yakamani dole banida yadda zanyi illah in ajiye makamai na saboda Naga son matarka yafi nawa Nasan koda aure mukayi Saika fifita ta akaina amma dolene inyi hkr saboda ina sonka nima”da gudu ta wuce tashiga mota lokacin Atee ta farfado tana ganin komai dake faruwa tsakanin MD da MASH amma batajiyo komai ranta yakara baci yana shigowa Atee tayi saurin sakkowa tace “MD yamukayi dakai? Abu daya zakamun takaddar saki nake nema Dan Allah MD ka sauwake mun bazan iya zama da Wanda bayason haihuwa ba bazan iya zama da Wanda yake gaba da gaba da zancen Allah ba zama dakai babu yakare MD”Takarashe magana tana kunshekin kuka BB kamal dai sai kallon umminsa yakeyi abunka da yaro shima saiya fara kuka....

“Atee saidai ki mutu Wallahi wallahi bazan taba sakinki ba koda zaki konani da ruwan Batir kiji kisani babu saki a tsarin aurena dake don haka kimaida wukarki kube tun wuri kafin tsinuwar Allah ta ziyarceki kafin mala'iku suyi miki tir sannan wannan kukan baxai taba amfana miki da komai ba”

Itadai jinshi takeyi amma gaba daya yadaina bata sha'awa Atee ta cije baki ta matso hawaye tace “Wacece naganka da ita? Koh itace kishiyata?” komawa tayi ta zauna a bakin gado ta kalmashe hannu shiko MD sai duru duru yakeyi alamun bashida gaskiya Atee tace “Idan bakada Abun cewa ni inada shi MD fauzi ada nayi  ikirarin barin gidanka matsawar zan zauna da kishiya amma jazaman ne zaman karuwa a wuta, dole in mike kafa acemun Aunty koh yaya dole in zauna da duwawuna inga drama kaida bakason Haihuwa har wani aure zakayi? Hmmm Idan ankicin biri aci dila ai wannan ba klass tusa gaban siriki”.

“Dakata........!!!!!Atee kar Abun yakaiga zagi mana, amma kibari muje gida I will explain everything to you yadda zaki fahimci komai”

Atee tace

“Bakada Abun cewa aure kuma Allah ya sanya Alkhairi inace ance kuyi aure donku hayayyafa? Sai naga sabanin haka MD kenan wani da kudi yake nema bai samuba amma sai gashi kai Allah ya azurtaka kayi sanadin barewansa”.*CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)

     

*@HUMAIRAH B MELODY*56-60


_*Wannan page din nakine Hauwa Salisu da Ummee gee Ngd k'warai da bibiyan wannan book da kukeyi*_❤๐Ÿ˜˜

Tana gama magana Likita yazo ya sallamesu sukaje gida da isarsu Mashahura takirashi ai kasa daukan wayar yayi Atee kuwa tace

“Malam ka dauka mana walakanci bashida kyau kar wata rana yazo kaina”harararta yayi ya kwantar da kamal dake kwance Kamar ruwa yana bacci saida Mashahura tayi masa miss call Ashirin amma yaki dauka Hk Atee ta tashi jiki ba karfi tayi bayi ta hada ruwa mai zafi tana bikin jikinta, Sannan tafito tayimai umurni daya kira mata gida haka takira gida ta sanar dasu komai sunyi bakin ciki har akace zaa turo kanwarta ta zauna da ita bakaramin dadi tajiba sosai

Soyayyar MD da MASH Abun ba'a magana haka MD ya tura dukda mahaifiyarsa batason auren dazai kara Amma mahaifinsa yace Aure Arzikine yayi babu komai ni humairah bashir melody nace

_*Tabbas aure ni'inma ne dole asoshi aure yana kara daga darajar mutum ta wani fanni Aure yakansa talauci aure yakan hana kwanciyan hankali aure yana haddasa husuma har takaiga rarra buwar kawuna Wanda bamu fata wani aure yakan zama Alkhairi wani aure kuma sai godiyan ubangiji*_

Atee tayi kishi har taji ba dadi abunda yasata ta rame kenan ka wani rawan jiki da MD fauzi yakeyi sai kace zai auro mai gindin gwal, Amma dayake akwai ilimin Arabi haka ta dinga sallah da adu'a tana rokon Allah ya sassauta mata zuciya nikuwa humairah nace tashin hankali ba naki bane Atee kin rigada kin kafa gida sai gani sai hange hakuri shine abunyi kisa musu ido basuci kuma basusha.+


Duk wannan gwagwar mayar da akeyi MD fauzi yana a Lt dinshi Amma ya daukowa kansa rigima koda yake IBADAH ne, a kwana a tashi bikifah sai matsowa yakeyi Duk yabi ya rame Atee kanta taga chanji don rawa ta chanza dole kida ya sauya salo, Jawaheer ce zaune kanwa ga Atee tace

“Yaya aini naga kinfi Abban kamal kiba da kyan gani Aunty kisa hkr komai rintsi karki sake kiyi wasa da hakokin mijinki karkiga wai bakije boko ba kizauna turus toh ki waye Wallahi iya girki kwaliya Aunty har tafiya itama wani kissa ne Sannan salon magana itama wani bangarene,” Atee ta saki baki tana mamaki yadda jawaheer ke koya mata wasu salo Wanda tama mance dasu, ana saura Kwana Ashirin biki Atee sanarda mutanen gida itafa babu taron da zatayi don batada kudin kashewa bare na murnan zuwan Amarya Tuni baba takirata tayi mata Fes tace

“Kina haukane Atee Saikace kina kauye toh koh a kauye an waye biki sai Kinyi so kike ace kina bakin ciki? Haba yannan kiyi shagali kiyi dinkuna kuyi kida kuyi guda shizai nuna cewa ke macece wacce tasan Abunda takeyi amma baki zauna saidai azo a aje amarya a tafiba babu dangi Bakisan zasu kulle a haban zaniba suyita yawo dake?”

Atee dai shuru tayi daga bisani tace “Ngd baba zanyi hk kuma insha Allah zaki sameni mai jin magana”baba tayi mata adu'a dafatan Alkhairi.

Zaune Atee take a falo tayi zugudi tunaninta shine yadda zata raba mijinta da wata sai hawaye motsi taji Abun mamaki akwatina tagani masu tsada Wanda akalla kudinsu yakai kimanin naira dubu Dari biyu MD fauzi ne ya ajiye tana nishi da fara'arsa yace

“Atee” dogowan dazatayi sai hawaye cikin sauri ya ajiye wayar hannunsa yace

“Atee meye wannan kuka fa kikeyi kidaina zubarda hawayenki a banza mijinki yana sonki sosai ni nakine Atee I love you haka yayita tausasa zuciyan Atee Sannan ya bubbude mata akwati tayi murna amma itakadai tasan me takeji a cikin zuciyanta......

Biki sai karatowa yakeyi saiga Mima kawar Atee takirata cewa gata a Barack dinsu tayi mata kwatancen gidanta haka tayi mata sai gata shiko Ango tuni aka fice shirye shiryen *CROSSING OF THE SWORD* Akeyi, tana sallama taci karoda Akwati iri daya dana Aurenta tace

“Kawata mezan gani kardai ace MD Aure zai kara?”

“Mima kenan Ai ga zahiri kingani Yau saura sati biyu ya angonce wai kayan faden kishiya ne wannan akayimun”

Mima ta jinjina kai tace dankari Rana daya da abokinsa kenan nima katin bikina bazo kawo miki

Atika tayi tsuru tace

“Mima kice lokaci yayi MD Bello ba karamin dace yayi da mata mai kirki yayi ba kinji dadi Wallahi ”mima tace

“Wani dadi yayi na kara aure”tafadi tareda zaro ido

Sunyi hira sosai itadai Mima Shawara kawai taba Atika Sannan ta tafi, Atika ce zaune kan center carpet ta dauki waya ta kira number MD kawai sai Mashahura ta dauka ta dakile murya tace

“Hello wacece?” Abunda ya doki Kunnen Atee kanen tace

“Kutuma inaso ki duba wayar Kiga wane sunane ajiki?”

Mashahura ta duba taga *My Wife* tayi murmushi tace

“Naga Ansa kinfiye naci”

Ai tuni Atee ta sulale k'asa daidai da Shikuma MD fauzi yashigo gida .........*CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)

     

*@HUMAIRAH B MELODY*
61-65

Cikin sauri ya kamata yana jijjigawa amma ina Atee ta sume saboda bata taba tunanin cewa matsayinta kenan acikin ran mijinta ba ruwa ya dauko daga fridge ya watsa mata tayi ajiyan zuciya tayi zumbur ta mike sai hawaye dake malala kusa da ita zai matso tayi saurin dauko Kaskon flower vase tace

“Kana matsowa zan buga maka munafiki Wanda baisan darajar matarsa ta gida ba MD kaci manata ka yaudari zuciya na Ashe na fiye naci danake zaune dakai tun babu Allah tsarki kozakama kowa hk ni Atika ban chanchanci haka ba har Wata tafini matsayi harni zan kira wayarka kaba wata mace da bansan matsayinta ba tunda ba aure aka daura ba Haba MD fauzi menayi Wanda na chanchanci haka? Ka gayamun” ta tarwatsa Vase din dake hannunta ta chakume shi da haushi tana kuka

Laluba Aljihunsa yayi yaji babu waya cikin rudani yace

“Subuhanallah Atee kiyi hakuri Wallahi naje wajen mashahura bansan Chan nabar wayan ba amma ki sanardani metayi miki? Niko saina dauki mataki mai tsauri a kanta”

Wata zuciya tace karkice komai wata tace kice Kiga ruwan gudunsa

Atika tayi ajiyan zuciya don tasan mijinta akwai mantuwa tace

“Nakira wayanka aka dauka akace wacece shine nace a duba a gani mana shine akace dani anga suna yafito wai kinfiye naci”MD yace

“WATTTT!!!!!!”ai dagashi bai sake cewa komai ba waje yayi cikin sassarfa bai zarce koh inaba sai gidansu mashahura tun daga bakin gate yake kwala mata kira Kamar daga sama tajiyo tafito a guje sauri kiris ta fadi Tuni ya tarota ta mike yace

“Bani wayata?”cikin sanyin jiki ta bashi ya duba yaga My Wife takira yace

“Inaso kisani akan Atika ina iya rabuwa da kowacce mace Wallahi akanta na rantse koda kece Autar mata zanbarki bari kiji wani Abu mash don inasonki zan aureki haka itama inasonta ne shiyasa na Aureta don haka Matsawar babu girmamawa a tsakaninki da ita Tsaf zan iya fasa aurennan Karkice banasonta ne koh muzgunamun takeyi koh daya sunnah ce nakeso inyi koyi don haka kiyi taking time dinki imba hakaba zan shayar dake ruwan mamaki”Yana gama magana yayi waje sai gida yana shiga ya durkusa har kasa yace

“Kiyi hkr Atee kiyafemun banida masaniya akan abunda yafaru kiyi hkr ni aure zanyi badon kin gaxaba haka babu macen dazan ragawa matukar tayi kokarin cimiki mutunci I love you Atee you are my heart and soul” itadai tajishi takuma hakura saura kwana uku biki MD fauzi ya siya wata shegiyar mota INFINITY 4XL latest version 2017  kowa saida yayi murna gida yacika da mutane dayake muhadu a falone shiya k'awata falon.....+


Kwanci tashi ba wuya Wajen Allah anyi biki anyi shagali anyi budiri Amarya ta tare haka kowa ya watse ciki harda baba wacce aranan da aka daura aure ta wuce Zaria Amarya tayi kyau da sheki Atika kuwa sai wannan shiga akeyi asa wannan asa wannan cikin turmutsutsun bikin saida Atika tasa kaya sunkai kala sha biyar saboda ta Kore ma yan Gaza gani k'ishi, Bayan kowa ya watse ne MD fauzi ya tarasu yayi musu fada mai shiga jiki wacce kowacce saida yayi la'asar saidai kuma dolene hkr aji aki ji a gani a kauda ido saboda hadaka za'ayi tunda gida ba nashiba gidan kwamnati, Bb na zaune sai wasa yakeyi yana tsalle “Sannan zancen kwana Atika keya kamata kifadi koh?”Atika ta yatsina baki tace

“Ah ah mashahura nabaki wuka da nama sai yadda kikace” wani girma kanta yayi tace “A barshi kwana bibbiyu koh?”

Aka Aminche Atee ta tashi tashiga gefenta itama Mash ta tashi shiko ango yayi waje don Neman Abun ciye ciye, yana dawowa ya mikawa Atee nata ya wuce  Dakin Amarya ransa fes sunyi sallah sunyi adu'a sunyi ciye ciye daganan aka fara Aiki Kamar baza'a ci a rage ba duk wani salo mash ta iya shima ba karamin dadi yajiba saidai ana gama wannan shagalin misalin karfe hudu na Asuba Mash ta kike tangaran koda yake Idan mai karatu yana biye yasan cewa Batakai shi gidan mijiba Sannan tukunya tasaba da girki, shiyasa babu alaman galabaita A tattare da ita kettle ta jona ta hada musu ruwan wanka bayan sunyi sallah an gyra MD fauzi yatashi ya bude wardrope ya dauko wani Abu cikin kwali yace

“Mash Nasan zakiyi matukar mamaki ganin wannan Abun a hannuna koh”? Tana juyowa taga Pills tuni ta zare ido cikin rashin fahimta......

Tab aiki gamai yinka tirkashi Allah mai iko amfara karku kaji kubi ni Humairah bashir melody yar mutan zazzau donjin yadda zata kasance shin mashahura zata aminche da  Kudirin MD fauzi nashan Kwayoyin hana daukan ciki koh yaya?.........*CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)

     

*@HUMAIRAH B MELODY*


_*Dedicated to my group members Wato MELODY NOVEL GROUP๐Ÿ˜˜ Tnx for the love and care*_๐Ÿ‘๐Ÿป

66-70
Meye wannan tafadi tareda tunanin abunda zai sanar da ita

“Mash Pills ne na hana daukan ciki saboda mu more amarcinmu koh kinfiso yau kidau ciki gobe kifara laulayi?”

Mashahura ta gyada kai alaman ah ah wata irin murmushi yayi cikin ransa yace

Haka nakeson mace mai saurin fahimta ba irin Atee ba itama Nasan rashin ilimi ne kawai ke damunta, glass cup ya dauko da ruwan EVA ya bata pills din guda biyu Wanda basaina gayawa mai karatu irinsa ba haka MD fauzi yadinga yiwa Mash hudubar shedan akan daukan ciki harta fara dauka.

Akwana a tashi wajen Allah MASH tayi kwana bakwai cikin na takwas Atee ta amsa girki cikin ikon Allah Atee ta maida komai ga Allah saidai tadauki aniyan cewa ciki kam saita dauka don su bakwai iyayenta suka Haifa Pills kuma batasha, A dinning ta shirya komai na abinchi akaci aka sha Mash sai santi takeyi dare nayi Atee tayiwa BB kamal shinfida a gadonsa Sannan ta shirya cikin gaya nagani na fade Atee dai in takaitawa mai karatu tazama sisi Lagos wani ya ganta zaice yar jami'a ce, A Daren sunyi wani Abu wai lalata kowa ya nuna irin kewar Dan uwansa dayake Abun ba'a magana bayan sunyi komai sun kammala MD fauzi ya dauko same pills din dayaba Mash yaba Atee cikin rashin fahimta tace

“meye wannan? Look MD nifa baxan dauka ba shan pills Nada matukar hatsari baxan sha ba ciki ai bakaina farau ba kuma wayace maka ciki koda yaushe yake shiga mace? Look MD fauzi nifa wannan Abun shizaisa komai zai faru yafaru koh ka mance cewa shaye shayen magunguna yana haifar da mummunar illah Ga lafiyar bil adama? Koh ka manta cewa yana lalata hanyoyin jini da jijiya koh ka manta cewa pills yana iya kawo MATSALA ma Al'adar mace? Koh ina kake lokacin da pills ya lalatawa dubban mata mahaifa? Kana ina Cancer yake kashe mata? Look badaniba indai akan wannan ne zan iya hakura da Tarayya dakai na aure shine kawai mafita akan daukan ciki daga haihuwa daya”

Wani gigitaccen mari ya sakarwa Atee abunda bai taba gigin yimata ba ya nunata da yatsa yace

“Ki sani saikin fiskanci hukunci mai tsanani acikin gidannan don aurenki nakeyi yaxama dole kibi umurnina matukar Nike aurenki Sannan haihuwa nace ta isa haka tarbiyansu ma aikine kazo ka Haifa yayan suzama ba nagari ya kashi I will not take it any longer kisani duk Idan kika sake naga ciki a jikinki ina maiyi miki albishir da cewa saidai kisan yadda zakiyi dashi tunda ke bakida hankali Gashi Idan kikaso kisha Idan bakiso ba ki watsar”

Duk wainar da ake toyawa Mash tana labe tanaji duniya tayi mata sugar sai tsalle takeyi daki takoma don taji tafiya bakin gado ta zauna tace

Lallai nasamu dama in taka Atee tunda na lura batabin umurnin MD fauzi Niko inhar rashin daukan *CIKIN DA BA'ASO* Ne baxan tana daukaba muci love dinmu son rai.

+

Sallama ne ya katse mata tunani cikin sauri tazo

“Sweet lafya naga ranka a bace? Meye ke damunka?

Namiji babu sirri tuni ya yayimo komai yasanar da ita sannan koh breakfast baiyiba ya fita

*BAYAN SHEKARA DAYA*

Atee tazama Abun tausayi ta rame ta kanjame saboda masifar MASH da MD kowani kashi aka kwaso itace tunda MD yaga alaman ciki a jikin Atee yasa mata karan tsana koh inda take baya zuwa sai hantara da kyara aikin gidan dukya dawo hannunta hatta wankinsu ita keyi an maidata bola bola, wani Abun ma sai kayi kuka

Mash ce tafe cikin isa da kasaita tasamu Atee zaune tana bawa BB kamal abinci wani tsawa ta dakawa Atee tace

“Ke maza ki tashi ki wanke mun zanin gado kafin rana ta fadi saboda jiya nayi ambaliya Dayawa haka mijinki yi maxa banason bata lokaci”

Atee taji wani bakinciki har cikin ranta ta dago kai tace

“Karki damu zan wanke bari ingama ba BB abinchi bacci ya tashi gashi yunwa yakeji ”Ai mash tuni tasa kafa ta haure Abinchin tace “Har bawa BB abinchi yafi wankina tashi kin wani aje ciki a gaba cikin da ba'a maraba dashi”Atee saboda karfin imani takasa cewa uffan Sannan takasa kuka BB kuwa yana bude baki yace

“Umma abinchi zube Aunty muguwa”Atee tuni ta kwashe da dariya daidaida mash ta juya Atee tace “Allah sarki duniya Yaro kenan wai shima yasan Wanda baiyi masa daidai ba kai BB kamal yau kasa zuciyata tayi fari kal Nasan cewa yarona jarumine”.Comment dinku da like shine karin karfin gwiwa na........*CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)

     

*@HUMAIRAH B MELODY*_*Wannan page din nakune yan group din Ya Hajja (momma) Allah yakara girma da daukaka yabar zumunchi yabar kauna*_❤๐Ÿ˜˜๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


71-75


Haka Atee ta tashi ta fara wanki a tsak'ar gida Tanayi tana wak'a nan ma Ashe ran mashahura bayaso cikin karaji ta fito tace “hehhhh hehhhh lafya kika cikawa mutane kunne da wasu gad'anki da basuda amfani? Pls bacci nakeji kinsan jiya banyi bacci Wanda ya isheni ba pls I need absolute silence ” Atee itadai bata daina wak'aba Abun da yayiwa Atee dadi Jarka ta dauko ta kira BB tace yazo yayi mata rawa

Haka Atee ta maida mashahura mahaukaciya Ta gama wanki tas Sai wayarta tafara k'ara tashige daki ta kulle daman haka takeyi tasaba,

Dauka tayi tace

“Hello baba ina wuni an yini lafya? Yasu Malam da kowa da kowa?

“Lafya Atika ya jiki kuma ansha jiki haka nakeso acikamun gida da jikoki Wanda zanyi alfahari dasu ” shurune ya ratsa baba tace

“Atika Lafya kikayi shuru kohdai dawani abune?” Atika tayi sauri tace

“Babu komai baba”

“Atika inaso insanar dake wani Abu inaso a daukomun BB kamal yadawo wajena da zama tunda nandai nikadaice tunda ga Sabo za'a samu kuma ba rance za'a baniba kyauta ”jikake kirjin Atee yawani buga tace

“Toh baba inajin Idan kika sanarda Abban sa babu MATSALA ai BB nakune tun yana ciki ake dawainiya dashi har zuwa yanzu indon tanine baba nabaki”Wani dadi taji tashi mata albarka sukayi sallama,

Tana kashe waya ta rushe da kuka tace

“Nashiga uku ni duniya yazanyi da raina Idan aka dauki BB kamal gashi MASH da MD sunama wannan cikin nawa barazana wani k'ara tasaki inajin yinin ranan Atee bata sa komai a bakinta ba ga uban ciwon ciki da ciwon kai ga uban aiki Mash itace yar gaban goshi tunda batada ciki anatacin amarci Kamar da bakin k'warya Atee bata taba sawa ya dameta ba illah iyaka Tana adu'a Allah yabar mata wannan cikin,

Bayan sati daya Baba ta shiryo tsaf don daukan BB kamal ranan anyi rashin Sa'a MD bayanan tana isa tajiyo hayaniya Harta shiga babu Wanda yasani MASH ce tsaye tana ta masifa da kumfar baki harda dungurewa Atee kai.

+

Baba taji wani haushi ta bakinciki a ranta

Mash tace

“Maza ki tashi ki dafamun abinchi yunwa nakeji kuma ki shiga dakina ki wankemun kayana ga toilet dina yayi datti ke har kumba zaki yakemun ga kaina ma ya tsufa”

Atee tayi murmushi tace

“Toh karki damu duk abunda kikace zanyi ai durkusawa wada ba gajiyawa bane sannan shi taimako koh a Jerusalem ana cin arziki”Mash na juyowa Baba ta wanke mata fuska da Mari tace

“Sannu yar matsiyata Wato ke harkin samu matsayin dazaki azabtar da Atika acikin gidanta? Don gidanta ne saboda ke koh kashi mai karfi inajin bakiyi ga Matar Bello Mima ta haihu kekoh kin tasa mata kina kisa toh bari kiji Atee ba jaka kuma kisani badaga sama Allah jehota ba tanada iyaye ke Dakin samu muguwar uwar gida kin isa kiyi tusa mai karfi bare tayi wari? Kinci sa'a Atika tanada kunya da kawaici irinna Fulani dake kin lashi tsuliyarki Wallahi, kuma aiki baxatayi ba ke zakiyi shi”Janyo hannun Atee tayi suka shiga falo tace

“Atee Allah yayi miki albarka Allah yasa kici wannan jarabawan Tabbas ana zaman zalunci acikin gidannan tabbas MD fauzi baxai iya adalciba yau zai xaba kohke koh ita acikin gidannan kiyi hkr Atika irinku kadanne acikin mata Allah saka miki”

Mash ce tashigo koh sallama zata wuce Baba tace

“Ke dawonan mun gaisa? ”

Tace

“Ah ah ina wuni” baba ta daka tsalle tace

“Kinci gidanku da ina wuni toh Kisani dole kiyiwa Atika biyayya don bazaki samu miji daga samaba kice zaki nuna iko acikin gidannan don haka kiyi gaggawan maida takubban yakinki kuma fate nakeson sha ayi maxa kuma inanan sai yadawo naji baasin wannan mulkin zaluncin”.


Waya da Ciro ta kirashi cikin kankanin lokaci sai gashi yadda yaga fuskan Baba yasan ba kanta gabansa yafadi MASH ce tafito tana mishi oyoyo harda yimishi Kiss tana kiran sa baby Ai tuni kallo ta koma sama Nan baba taga Bariki ai rike haba tayi itako Atee Sunkuyar da kanta kasa tayi baba ta tashi tace

“Kinci gidanku da Baby kaima kaci uwarka ladin Baure Tirkashi rashin dabi'ar har a gabana za'ayi wai baby toh kisani danane kiyi gaggawan Neman naki baby tun wuri don lokacin danayi nakuda baki riga kinzo duniya ba mtwww”

Guri ya nema ya zauna yayiwa MASH signal da cewa tatafi

“Ina wuni Baba anzo Lafya? Ke tashi muna magana kin wani samana ido”

Atee ta mike baba tace “Koma ki zauna”

Atee tayi wani sululu ta zauna

“baba inata gaisuwa baki amsani ba?”

“Banida lokacin fitsaranka Fauzi albasa batayi halin ruwa ba......

Tabbas kabani kunya ace acikin gidannan ake yiwa Atika rikon sakainar kashi saboda kin Allah da rashin Adalci toh kasani dole kayi Adalci a tsakanin matanka koh kanaso koh bakaso Abun kunya ne wannan ace uwarta tazo gidannan taga halin dana riki Atee wallahi Idan aurennen bai mutuba toh babu makawa saiya Suma don hk kowacce aurenta Kakeyi kowacce tayi hidimar kanta Idan yazo ban yarda da zalunci ba kasani inhar ka kasa adalci ranan gobe kiyama zaka tashi a shagide fadin Allah ne ba fadin habiba ba”Shidai hkr yake bayarwa saboda yagama da duniya Lafya yakuma gama da iyaye Lafya

“Baba kiyi hkr za'a kiyaye za'a gyra Allah ya huci zuciyanki Amma Atika bata bin amurni na koh kadan”

Baba tace

“Dakata tsohon muna fiki Atika haka akayi?”

Atika tayi shuru cikin ranta tace gaskiya baxan iya tozarta shi gaban mahaifiyarsa ba dole in rufe komai

“Baba babu abunda banayi acikin gidannan Wanda Bai sabawa dokar Allah ba Abu daya nasani...... Gaban MD yace Ras!!!!!!!*CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)

     

*@HUMAIRAH B MELODY*_*Comments dinku Shine karfin gwiwana๐Ÿ‘๐Ÿป*_❤๐Ÿ˜˜

76-80Cikin sauri yace

“Baba nidai Nace za'a kiyaye ba shikenan ba”baba ta tsareshi da ido tace “Akwai lokacin da iska zai kada lokacin kowa zaiga takashin kaza meye kakeci na baka na zuba sannan inaso kasani Yau da kamal zan wuce Zaria tunda har yanzu gida ya gagara cika da yaya” Atika tashi tayi tsbarsu a falo tafara hada kayan Kamal tana kwalla abunka da uwa da Da' duk saitaji wani iri akwati biyu Atee tayi da kayan BB haka tafito dashi ta ajiye kanta tsaye,

Mashahura ce daukeda faranti sai huci take Kamar wata zaki sai wani kunci takeyi ta ajiyewa Baba abinchi ta dauko ruwa tace

“Baby pls muje ciki kaci abinchi kayi wanka ka kwanta ka wuta” MD fauzi yarasa abunda zaice mata illah iyaka magana da yakewa baba cewa

Ana zuwa asa bb a makaranta, Mash ta kulu iya kuluwa fuuuu ta wuce sai daki, misalin karfe Uku baba ta shirya ta koma har tasha suka rakata shida Atee Kamal yayi kuka Kamar ransa zai fita amma tafiya dole, Mash kadai ke gida tuni ta samo kwayar zunda ciki tasawa Atee a zobon data ajiye a fridge saida ta zuba over dose aciki kannan ta jijjiga ta ajiye, Tafe suke cikin mota babu mai cewa kowa komai Atika tayi karfin hali tace

“Inacikin damuwa nasaba da kamal Nasan sainayi ciwon rabuwa dashi ”

“Dakata malama wani sabon salone yimun magana yaushe rabon duniya kisani daga BB kamal banason wani haihuwa bari kiji in sanar dake banason Tara yara” Atika tace

“Saikace wani bature ai tunda ka iya kara aure toh kace haihuwa salamu alaikum banda jahilci irinnaka MD har zakace bakason haihuwa toh bari kaji Allah ba axxalumin kowa bane wallahi sai Wanda yaso ya zalunci kansa kuma Allah baya bacci nidai Fatana Allah ya rayamun abunda zan Haifa ai Abun alfaharine ace Yau mutum yanada yaya tunda bakasan maijin kanka ba” tana gama magana MD fauzi ya kuza mota ya tsaya cik yafito ya budewa Atika mota yace

“Fito waje koh inyi waje dake Matukar baxakiyi family planning akan haihuwa ba wulakanci baki gama gani ba nace banason haihuwa banaso koh kin mance Baba ni kadai ta Haifa so get out of my car am filled with your stupid altitude towards my aims”

Atika tayi karfin hali da turancinta itama tace

“Am not coming down MD fauzi kabarni da peace dina Idan ba hakaba I will show you my true color”Md huci yakeyi kowa sai kallonsu yakeyi Abun babu dadi

Ciki yakoma ya figi mota sai gida suna isa Mash na kutso kai wani tsalle tayi ta rungume shi suka shige ciki ai Atika bata sake ganinsu ba saida tasha zobo tayi tatil cikin minti TALATIN ciki yafara murdawa Kamar ana lugude wani kara ta saki Wanda saida suka firgita..+


Da gudu suka fito suna tambayan lafya? Ai jijine ke malala Kamar da bakin kwarya Asibiti suka kaita suka aje suka dawo gida suka cigaba da shekewa Bayan Wasu lokuta Atika ta farfado likita yace

“Madam meyasa kike shan kwayar zubarda ciki?”Atika tayi kasake tace

“Likita wallahi banasha likita karkacemun cikin danake dauke dashi ya zube Likita inason cikina Likita”

“Kiyi hkr cikin ya zube saidai kuma yakamata ki kiyaye saboda Hakan zai iya haifar miki da MATSALA kidaina haihuwa gaba daya saboda shi maganin zubda ciki yanada hadari sosai ina mijinki?”

Atika takasa magana sai hawaye da takeyi tace “Likita kaidai abar kaza cikin gashinta Likita kabarni in tafi gida zanfi samum natsuwa Likita ne ya dauki Atika cikin mota har kofar gidanta da mamaki taga MD fauzi da mash zaune suma tsinkar fure godiya tayiwa Likita tazo zata wuce MASH ta tureta tace

“Sannu harkin dawo daga barbadan? Ke wace irin karyace My love kasan waccan mutumin kuwa? Manemin matane fah shifa ya daukota amota”Atika ta tsaya kallon ikon Allah jingina tayi da bango saboda jiri dake dibanta wani kazafi takeji da rana tsaka, kishiya hmmm zan takaitawa mai karatu MASH batabin boka batabin Malam tsabar iya kisa ne,

Wucewa zatayi MD fauzi ya kwasheta yace badani ba koma wajenshi inda kika fito banida abunda zanyi dake, Atika ta tashi ta dauko adda tayo Kansu tace

“kafin ku kasheni sainayi ajalinku inyaso a yankemun hukunci da hujja saida Atika ta tabbata sunbar gidan tashigewarta ta kulle koh ina tace

“Idan kunsan wata bakusan wataba hkrna ya kare akan cin kashin da akemun Mash tunda kikayi sanadin zubarmun da ciki kema saina yimiki illah, Abinci tayi kokarin dafawa amma dakyar ta gama taci ta kwanta sai Asuba ta tashi tasa ruwa tayi  gashin jikinta , sannan taji karfi ta dafa abinchi Atika saida tayi sati kannan ta bude kofa Mash gidansu ta tafi shima aka bashi daki, ta gyra koh ina tagama taji sallama ta dago tana murmushi tace

“Refugee kun dawo barkanku da shigowa amma ina so insani kun tahoda likafani koh? Inbaku taho dashiba ku koma don yaki an dingashi a gidannan kusani Baku ba kwanciyan hankali tunda ka nuna DAN CIKINA ABUNKINE A WAJENKA, kuma CIKIN DA BA'A SO saiyazo duniya kohba jima kohba Dade Fuuu ta shige ciki ta fara Girkin rana tana gamawa ta zube a kula tafito kenan MD fauzi yace

“Atika ina abinchin mu?”

Atika tace

“Ina zuwa”

saida ta ajiye abinchin a daki ta dawo kitchen ta dauko flacks ta zuba kasa dayan na miya ta zuba ruwa tazo ta ajiye..........*CIKIN DA BA'ASO*

(unwanted pregnancy)

     

*@HUMAIRAH B MELODY*


_*Dis page is for you AISHA MAHE kwanjinki yakoma*_๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜œ81-85

Daki ta shige ta kulle kanta,

MD fauzi ya dauki abinchi yakai daki Abun mamaki yana budewa yaga kasa ai tsorata yayi tashi yayi a fusace yana kiran Atika amma koh ta tankashi, sai buga kofa yakeyi amma taki budewa sai masifa yakeyi

“Atika nagaji da rashin kirkinki acikin gidannan harmu zaki zubawa kasa da ruwa inkawo abincin dakaina amun walakanci? Hmmm lallai toh dassake” saida ta tabbata ya gama itama ta gama cin abinchi tabude tafito saida ta *gama* ** ** ** ** ** ** **  kallonsa tace

“Amma kaji kunya wallahi bansan cewa ina tareda mai tabin hankali ba kafayi hkr dolece tasani gaya maka haka kasan cewa nayi biyayya iya biyayya amma sainaga anamun rikon sakainar kashi shiyasa naga lokaci yayi dazan *tsaida ruwan miya* koh ka mance cewa nima macece inace auromu kayi don kayi adalci amma saika kasa, Md bakada lokacina bakasan halinda nake ciki ba ina zaune ne kawai matsayin matarka amma babu wani hakki nawa da ake saukewa saboda ni cikin haihuwa gareni har kana mafarkin indafa muku abinchi kuci kaida waccan saunar? Ina MD yaci ace ka gane wacece Atika a yanzu inhar kanaso in dafa muku abinchi Inaso insan matsayina acikin gidannan don inhar ba'a muaamala dani yaushe zan zama baiwa nida girki wata Katuwa da miji? Nooo impossible ”

Tana gama magana tayi kitchen nan taci karo da mash daukeda Flasks din Kasa da ruwa mash tuni tayiwa Atee wanka da kasa da ruwa tace

“Kinyi kadan wallahi keda bakibin amurnin miji mai miji zaiyi dake kuma kece sauna shasha sha kawai Mara kima da daraja Daga Yau kowa ta dafa abincinta kuma Duk ranar da kika kara ciki toh daga ranar kinzama baiwa saboda bakida sauran amfani mace Saikace Bera?”mtweee Hmmm Atee dai kasa motsi tayi tace jirani ina zuwa daki tashiga daidai MD fauzi zai fita takirashi yana juyowa ta watsamai miyan manja a jiki gashi sanye da farin kaya, ta juya hankalinta kwance mamaki ya isheshi wata zuciya ta har xuko mai tabita kafin ya isa ta Ciro wuka tace

“Kana tabani zan kashe kaina kuma kasan bazaka taba fitarda kanka ba Ashe kanada zuciya ace matarka tayimun wannan Abun ka kasa magana saida ni nayima? Amma kaji kunya” Tsayawa yayi cik yace

“Atika meyasa kika zamemun annoba?”

Atika ta juyo tace

“Nafi annoba ni cutace ni mai kisa”.+


A ranan MD fauzi yaraba musu kwana kaman gida yayi lafya Ashe aiki na gaba Saida atika ta shekara Biyar babu ciki babu alamansa Wata rana sukaje gidan MD bello mijin Mima kawar Atee Suna shiga suka taradda shi zaune yara sun zagayeshi suna mishi wasa sai nishadi yakeyi lokaci daya Atika tayi shaawarsu MD fauzi kuwa kasa sallama yayi lokaci daya yaji son yara amma ba'a gidan su ba, atika ce gaba sai Mash sai MD sukayi sallama suka kutsa sunyi murnan ganinsu kwarai anyi musu tarba na musamman haka suka koma suna Sha'awan Mima da mijinta tunda suka koma MD fauzi ke tunani yadda za'ayi yafara yarda matansa su samu ciki amma ina tuni ya kauda wannan tunanin.

*BAYAN SHEKARA UKU*

Lokacin BB kamal yanada shekara Goma a duniya tuni ya saba da Baba dake Zaria, K'watsam Wata safiyar juma'a Atika ta tashi tana ta kelaya amai Wanda sai taba duk wani mai imani Tausayi amma Abun mamaki MD fauzi koh a jikinsa shirin tafiya Akure yakeyi inda akai mishi posting mai karatu a kwana a tashi MD fauzi yakai muk'amin Major amma tafiya bata canza zaniba, Kullun Atika ciwon Yau daban na gobe daban Asibiti taje akai mata Test na pt dana malaria cikin minti TALATIN result yafito Atika itadai taga ansa react amma batasan me yake nufiba wajen Likita taje direct yayi mata albishir  da ciki gareta Atika makwan tayi murna amma sai taji gabanta yafadi saboda tasan tsaka mai Wuyan dazata fada, Gida ta wuce kafin taje MD fauzi ya wuce MASH tasamu zaune a falo ta kure Volume tanajin ATEWO tana rawa Atika ta wuce ta batace da ita kala ba, ganin shigowan Atika yasa MASH kara volume hatta Kasa ansawa yakeyi Ga ciwo ga Kara gashin kan Atee  ciwo yakeyi sosai haka ta kwanta ta toshe kunnenta, Kullun Atika ciwo karuwa yakeyi wayarta ta dauko tayi kiran MD fauzi tasanar dashi abunda ke faruwa budar bskinsa sai cewa yayi “Me kikeso inyi miki? Duk yadda za'ayi ki cire cikinnan don ban shirya tarban wani daba”

Tuni Atika taji kanta na juyawa zubewa tayi rijib a k'asa ta dinga rusa kuka Kamar ranta zai fita jawaheer takira a waya tace

“Nashiga uku jawaheer nashiga tsaka mai wuya meyasa MD bayaso in haihu? Dan Allah Idan kinsan abunda zansha cikinnan yafita ki sanar dani Jawaheer ni ama juyamun mahaifata indaina daukan ciki dazaran nasamu ciki sai kyara da hantara menayi ne ni?”

Post a Comment for "CIKIN DA BA,A SO CHAPTER A"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...