BUGUN ZUCIYA COMPLETE - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BUGUN ZUCIYA COMPLETE

BUGUN ZUCIYA COMPLETE

- - Post a Comment

BUGUN ZUCIYA COMPLETE


📙 Dada! Dada!! Wata matashiyar yariya ce ke rangadawa tsohuwar kakanta kira"

    Fitowa tsohowar tayi tana kokarin gyara daurin zaninta take fadin, nashige su nikam wannan irin kira haka?"

    Turbune fuska yariyar tayi lokacin da sukayi ido biyu da kakar tata tana fadin ayya dada danma kinsamu ina murnan ganinki shine zakice wani kin shigesu?, juyawa tayi da nufin komawa, cikin sauri dada ta jawota cikin fara'a tace dawo2 ai ban dauki murya ba, maraba lale lale takwara, karashewa tayi tare da jawota jikinta ta rungume"

     Daidai lokacin wani farin dattiju ya shigo tare da sallama, yana ganin su haka yasaki murmushi"

    Cikin sauri yariyar ta kwace daga rukon dada ta nufi cikin dakin, tabarma ta dauko ta shinfida wa mahaifinta ya zauna tana jin sun shiga gaisawa da dada ta koma dakin dada"

    Gyarawa tashigayi duk da cewa dakin agyare yake dan dada macece me matukar tsafta, gadon ta lokuikuye yayi tsaf kaman baza ahauba sannan ta dau tsintsiya tahau shara"

    Bayan ta gama ne ta dauko dan kaskon turaren wuta ta nufin dan karamin kitchen din dada dake tsakar gida"

     Tagabansu dada tazo zata wuce dan haka duk suka juyo suna kallonta harta kusa isa kitchen din dada tace"

    Aiko takwara bazaki samu rushi a kitchen dinnan ba, dan yanzun baban ninki sun hanani amfani da murhu"

    Juyowa tayi ahankali tace to yanzun baki kunne turaran rushi kenan?

    Gurin tabawa nake samowa"

    Cikin rawar jiki ta nufi kofar gida tana fadin bari naje na samo"

   Lokacin da dada ta komar da kallonta ga dannata gani tayi yayi shiru kanshi akasa, gyaran murya tayi sannan tace girman dan mutum babu wuya yanzun dan Allah kalli yadda takwara ta girma ko yanzun aka mata aure saita xauna"

    Da sauri ya dago kai, yace dada kin sosamin inda ke min kyaikayi, hankalina ya fara tashi ayau tum muna hanya zuciyata ta fara tsinkewa"

   Cikin kulawa tace kakwatar da hankalin ka insha Allahu Allah zai tsare babu abin da zai faru, kuma ma ai takwarar tawa Allahamdulillahi natse take tsaf ga kunya ga tsafta"


     Hmmm dada akwai wani hali dana kula tanashi wadda har yanzun banji kowa ya furta ba, ban saniba koni kadai nake gani?

   Kaga, banason jajibe2 karkace komai tunda ta gama secondary data same miji amata aure, idan ma kana da burin tayi karatu ne idan tayi aure tayishi can dakin mijinta"

   Nisawa yayi daidai lokacin ta shigo da sauri tashige dakin dada cikin kankanin lokaci kamshi ya cikka gidan"

    Dada ko hira sukaci gaba da danta zuwa can ya dauki mukullin motar sa dake kan tabarma yayiwa dada sallama ya fice"

    Mikewa dada tayi ta nufi daki tana fadin takwara maza ki fito kutafi kisan abbanki besan jira"

    Aguje ta fito ranta bace ta kalli kakar tata tace kai dada memakon kice mishi yabarni anan, ninafi son zamagurin ki kuma, shiru tayi kawai ta nufu kofa cikin zubura baki"

    Binta da kallo dada tayi harta kule, sannan ta sauke idananunta tare da fadin duk sanki da gidan nan *Asma'u* dole ki hakura dan babanninki ba yadda zasuyi ba"

    Ko da suka kama hanya babu abinda take banda zunbura baki, abbanta na kula da ita saidai ya dauke idon daga kallon ta dan ya fahimce manufarta"

    Suna isa gida ta nufin dakin mahaifiyarta ranta bace, tare da matso hawaye"

    *Ma'u* ya, kin fita da farinciki kuma kin dawo min da kuka, menene ya faru?

    Turo baki ta karayi cikin kuka tace mama nifah banason gidan nan nafison gidan dada, kuma aidama keda abba kuncemin idan na kare secondary zan koma can"

    Shiru mama tayi tana nazari kafin ta dago kai abba yayi sallama ya shigo ganin su haka yasashi hade fuska tare da fadin yaya ne?

   Mikewa mama tayi tare da fadin alhaji ai kafi kowa sanin halinta gatanan wai ita gidan hajiya takeson zama"

   Bazaiyuwu ba mamana, idan kikayi wasa konan da kofar gida zan hanaki fita, kinga yau kika dawo daga makaranta karki yadda wani abu ya hadani dake ban ce bazaki koma gurin dada ba, amman sai naga yanayin natsuwar ki, yana gama fadin haka ya fice abinsa ko waiwaye babu"

   Washegari 
DOWNLOAD HERE

Post a Comment for "BUGUN ZUCIYA COMPLETE"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...