BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 4 by sumayyah Abdulkadir - HAUSA NOVELS
Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Top Widget Posting

BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 4  by sumayyah Abdulkadir

BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 4 by sumayyah Abdulkadir

- - Post a Comment

 BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 4

by sumayyah Abdulkadirdinkin Mohammed. Da yake suna da shaidar residence permit (takardar shaidar mallakar muhalli a kasar Birtaniya) basa neman bisa. Booking din jirgi kawai suke yl. 


Mami ta gaya musu su hada kayansu, gobe zasu wuce UK yaye su Yayansu. 


Safah ta yi kicin-kicin da fuska ta ce, “Ni dai Mami ba zan samu zuwa ba, akwai assignment din da nake yi”. 


Hajiya Zainab ta dan zuba mata ido tana nazarin ta, akwai wani boyayyen bacin rai a idanunta wanda ba ta fahimci ko na mene ne ba. Don bata ga abin bacin rai cikin kalaman da ta yi ba. 


Ta ce, “Ba sai ki tafi da assignment din ba in munje can sai ki yi?” 


Kamar za ta yi kuka ta ce, “Don Allah Mami ki yi hakuri ni kawai bana son zuwa’. 


Hajiya Zainab ta rike baki cikin mamaki ta ce, “Ke kadai za ki zauna a gida kenan?” Ta ce, “Ba ga su Dije ba duk suna nan babu abinda zai dame ni”. 

Da Daddy ya shigo Haj. Zainab take gaya masa sakon Safah. Ya yi mamaki sosai, domin ya yi zaton kafin kowa ya ce zai je ita Safan ce za ta fara cewa za ta. 


Ya ce, “Kirawo min ita”. 


Ta shigo cikin doguwar riga kirar Bahrain ruwan gwaiduwar kwai (beig) a jikinta. Ta daure gashinta da wani tafkeken bakin ribbons. Can kusa da Daddyn ta zauna fuskarta ba walwala. 


Cikin hikima da tausasawa ya ce, “Safah yaya ne? Na ji an ce kin ce ba za ki je graduation ceremony din Yayanki ba?” Yadda ya yi mata maganar a tausashe, sai ta ji ya tausasa zuciyarta, ta yi shiru bata bashi amsa ba har sai da ya _ sake maimaitawa. 


Cikin sanyin murya ta ce, 


“Dama inada assignment ne, amma zan tafi da shi na yi a can Daddy tunda kana so in je”. 


Ya ce, “To ko ke fa? Assignment din da har sai an koma hutu sannan a karba? Amma in baki je ba ai ba zai ji dadi ba, mu 

duka ma ba zai yi murna da zuwan mu ba, kinsan Imam dav’. 


Saukar sassafe suka yi a London, daga ‘national-rail’ suka bi jirgin kasa zuwa Loughborough. 


Safah tana ta kumburi na babu gaira babu dalili tun saukarsu a ‘Gatwick’. Sanye take da tafkekiyar rigar leda baka har gwiwarta asabili da ‘snow’ dake sauka_ yaf-yaf kamar yayyafi har a jikinsu, daga cikin rigar ledar bakin wando ne ‘cherokee jeans’ a jikinta da farar ‘shirt’ mai dauke da bakin rubutun = ‘dolce&gabbana’, hannayenta cikin bakaken ‘hand-socks’ haka takalmin dake kafarta (snow resistant) ne, da safar kafa din suma bakake. Fuskarta kawai kake gani data zagayeta da dan karamin farin mayafin pashmina.idan ka ganta a lokacin saika tuna da fitacciyar jarumar _fina-finan kudancin Najeriya Geneibiebe Nnaji. 


Hatta kwayar idonta cikin bakin gilashin da aka fi sani da ‘FF’ (fitnessfirst) take. 

Shigar da tayi haka Marwa tayi, sai banbancin kala amma duka ‘design’ daya ne, ita Marwa tayi amfani da ‘red & white’ ne maimakon baki da farin da Safah tayi amfani. Ita kuma saita tuna maka da jarumar finafinan kasar Hindu (Diya Mirza). 


Sabanin Safah dake kumburi mai nuni da an takura mata tafiyar da ranta baya so, ita Marwa cike take da dokin son ganin Yayan nasu. 


Tana son ganin wanne irin ci gaba ya samu a shekarun da ta yi ba ta ganshi ba? Tun fil’azal Imam na da wasu ilhamomi da bata taba ganin kowa dasu ba. Ko addu’a take a kan miji na gari, cewa take “Ya Allah kamar Ya Imam!”’. 


Cikakken matashi dan shekaru ashirin da tara. Ya zama katon gaske. Kai ka ce dan shekaru talatin da biyar ne. Yana da wata irin halitta da kalar fata mai daukar hankali da fizgo zuciya zuwa gare shi. Musamman daga fitinannun matan da suka san kirar 

namijin duniya. Girman da ya kara ya basu mamaki dukkannin su matuka; dogo sosai, mai ginannen jikin da babu kiba, babu rama a jikinsa. Ba kamar yadda yake a da ba. 


A yanzun idan ka kalle shi mayuwaci ne ka bambance nationality dinsa, kasancewar Hajiya Kaltume Shuwa, yayin da mahaifinsa yake cikakken Bahaushe. A da yanada kala irin ta Alh. Aliko da mahaifinsa, amma a yanzu ya fisu haske ya su murjewa, kalar shuwa ta fito sosai a jikinsa, duk da duhun hausawan bai barshi yayi tasiri sosai ba. Sai maida shi kamar Egyptian bakaken cikin su. 


Kamannin Uwa da Uba ne suka cakude suka bada surar wannan giant mai sanya Zuciyar diya mace cikin soyayya ta babu gaira babu dalili. Idanunshi kadai sun narkar da zuciyar Marwah, cikin wata irin masifaffiyar soyayya ba Imam din baki dayansa ba. 


Ita kanta Safan da ta kalle shi ta ji yayi mata kwarjini ainun, ya kuma burge ta, 

burgewa ba kadan ba. Irin wadannan mazan da Allah Ya hadawa komai na rayuwa, tsiraru ne a cikin al’ummah. Tace cikin ranta 


“ashe haka Ya Imam ke da kyau?” 


Sai dai hakan bai sa ta ji soyayyar shi ta aure ba, ko wani abu makamancin haka, ko kadan bata bari zuciyarta ta raya hakan ba, bata ji wani abu daban da na baya ba, wato kafin ya tafi. Tunda ta riga ta sawa ranta hakan. 


Marwah ba ta taba ganin wanda hular ilmi ta yiwa kyau, ta tsaya kyam a kansa, ta dace da zubin halittarsa, ta fiddo haiba da kamalarsa, ta maida shi ‘choculatebature’ irin Ya Imam ba. Da da ne, rungume su yake yi, amma a yau baki kawai ya rike cike da mamakin girmansu, yana satar kallon kwayar idon Safah, a lokacin da Daddy ya rungume shi. 


Fuskar Safah ba yabo ba fallasa ta ce, “Congratulations Yaya Imam!” Kwayar idon shi ta yi nauyi a cikin 

kallonta ya ce (idanunshi a lumshe) “Godiya nake Safahn Mami!”’. 


Marwah dake rabe a bayan Safah, tana lekensa, yana ta hira da Daddy, a lokacin da zuciyarta ke ragaita. Ragaita cikin soyayyar da ba’a san tana yi ba. Ta lalubi hannun Safah ta sanya mata wata leda da aka sunke wani abu a ciki cikin ‘wrappingsheet’, (cikin abin nade kyauta) mai kyan gaske. Ta rada mata cewa ta bashi, (a zuwan ita Safahn ce ta bashi). 


Kallon rashin fahimta Safah ta yi mata, ta kada mata kai ta rausayar, kana ta langabar, cikin kallon lallashi, alamar kada ta watsa mata kasa a ido ta bashi. 


Ta gatsina baki ta ce, “Ke kin fiye fi’ili wallahi”’. 


Sannan ta mikawa Aunty Shahida dake gefensu tana waya ta ce, “Ki bawa Ya Imam in ji Marwah’’. 


Shahida sai ta dauka kunya ce da kara, don haka ta yi murmushi ta ce, “In ji ki dai’. Ta murguda mata baki tace “sai kuyi kuma”. 

Shahidah ta kama baki “ni kike zobarawa baki Safah?”’ Kamar tace “an zobara mikin” sai kuma tayi tafiyarta wajen su Mami ta barta anan. Abin sai ya bata dariya ta girgiza kai tace 


“Biyu Kyautar Allah!!! 


Ta karasa inda suke shi da Daddy ta bashi. Ya jujjuya, ya yi mata kallon tambaya. 


Ta ce, “Sakon Safah ne!”’. 


Bayan Daddy ya kammala duk cikeciken takardun da suka kamata da sanya hannu (clearance), Almustapha ya karbi kwalinsa na zama cikakken ‘Auto-MobileEngineer’ (makerin motoci) da tayin aiki tare da kamfanin ‘General-Motors’ din Amurka, a ranar suka juyo Bournmouth. Gidan Alh. Aliko na garin Bournmouth akwai dalibai da suke zaman haya a ciki, alokacin kuma ana hutun karshen shekara kowa ya tafi hutu kasarsa, don haka gidan fes yake, kamar da mutane a ciki, ‘yan share-sharen da Shahidah tayi ba masu 

yawa bane. Kowa ya nemi makwanci domin ya shimfide hakarkarinsa ya huta gajiyar tafiyar jirgin kasa. 


Bai bude sakon Safah ba sai da ya zo kwanciya. Katin gaisuwa ne mai bala’in kyau da tsada (greeting card) na fatan alheri, ga abinda tace; 


“as you stribe hard 2 achiebe your goal... ... here’s hoping that you edcel in ebery way,... with faith in yourself and strong determination.... I strongly beliebed that success will surely come your way! A kasa ta rubuta sunanta -Safah Dan Kasa. 


Ya yiwa wannan kati karatu fiye da sau hamsin yana murmushi. A daren bai iya ya yi barci ba, sai karatun katin Safah. A little gift that means a lot 2 him.... Wannan ne abu na farko da ya taba fitowa daga hannun Safah zuwa gareshi da sunan kyauta ta soyayyah. Don _ haka muhimmancin wannan kati, yafi kyautar gida da mota a gun Imam. Ya kwana yana 

hasaso fuskar Safah ne, tana karanta masa wannan sakon, suna fita daga siririyar fatar bakin ta. 


Allah kadai ya san adadin kaunar Safah cikin zuciyarshi. Sai dai ta yi kankanta kwarai da ya tsaya yana bayyana mata dimbin soyayyar dake dankare cikin zuciyarshi a yanzu. Yana da yakinin Allah Ya halicci zuciyarshi tun fil’azal da soyayyar SAFAH, ta yadda har ba zai iya cewa ga adadinta ba. 


At 29, yana ganin lokaci ya zo da ya kamata ya yi aure, to amma da wace ‘yar mitsilar Safahn? Da ko sakandire bata gama ba? Yana ganin har yanzu da sauran lokaci, kwata-kwata bana ne suka cika shekaru goma sha shida da haihuwa. 


Ba shi da damuwa, don ya san Safah zaman shi take. Iyaye da kakanni sun san da al’amarinsu tun ranar da aka haifeta. Babu macen da ke burge shi duk fadin duniyar nan sai ‘yar uwarshi jinin jikinshi Safah. 


Ita kadai ce zai iya baiwa gurbin uwar 

‘ya’yansa. Mata kala-kala ya gani a rayuwarshi, daga namu na bakar fata mazauna Britain har zuwa na jajayen kunnen asali, Arab, Asians, Indians, Pakistani, Iranian, Moroccons, Portuguese, Somalis harda Jamaicans, sun so shi sun kaunace shi, da aure ne ko da gurbatacciyar mu’amala. 


Amma Safahn nan ita kadai ke da mulkin zuciyarshi, ta yarda har bai iya daga ido yayiwa wata mace kallon kima. Saidai ayi mu’amala kawai (dating). Mulkin Safah a zuciyar _ Imam, mulkine da ya tabbatar har 


abada babu mai ture shi. 2K ok 


Washegari misalin karfe tara na safe, ya yi wanka ya shirya cikin bakin jeans da farar riga mai ratsin baki samfurin (Calbin Klein). Ya fesa turare a gurguje ya janyo kofar falonshi ya rufe, ya shigo falon duk jama’ar gidan suna falo suna kalaci, amma babu Safah a cikin su. 


Marwah da Aunty Shahida suka gayar da 

shi, shi kuma ya gaida su Daddy, ya ja kujera gefen Hajiya Mama ya zauna. Yace, “Ya ya uwargida me zan samu ne?” Ta ce, “Kai tafi can, maigidan da babu awo babu cefane”’. 


Ya ce, “Ai kema kin san don bana nan ne, amma tunda gani na dawo, cefane sai kin ture, kin rasa yadda zaki yi da shi’. 


Sannan ya yi zagaye da kwayar idanunshi masu sheki kan kowa dake bisa tebirin ya ce (yana kallon Marwah). 


“‘Ta-robar, ina ta-karfen ne?” 


Ta yi murmushi, wani kishi ya turniketa, amma ta sadda kanta kasa, idanunta suka kawo kwalla ta ce, ““Tana dakinmu, tana da assignment ne”’. 


Ya ce, “Assignment ne zai hana cin abinci? Bari in gano ta”. 


Babu wanda ya tanka musu. Ya mike tsam ya doshi dakin nasu. Duk suka bishi da kallo. Gabadayansu kallon tausayin yadda ya damu da murdaddiyar matar da yake so, ita bata san ma yana yi ba. Don ta kai ta kawo kowa ya fara ganewa. 

Zaune take a kan study-table da manyamanyan littafan sakandire a gabanta, da gilashin karatu a idonta mai kara karfin idanu ga wanda ke yawan mu’amala da takarda, tana ta rubutu. 


Daga bakin kofa ya tsaya yana kallon ta, duk wani motsinta a kan idanunsa. Ba ta san da tsayuwar shi ba, shi kansa bai san adadin lokutan da ya bata yana kallon nata ba. 


Watakila jikinta ne ya bata akwai mutum a tsaye a kanta, ta dago a hankali ta dube shi, kana ta maida kanta ta ci gaba da abinda take yi. 


Ya ce, “Sorry to interrupt... ki taso ki yi kalaci’. 


Ta yamutsa fuska ta ce, “Bana jin yunwa”. Ya ja kujera kusa da ita ya zauna, ya ce, “To nima ba zan ci ba, kawo rubutun in taya ki’. 


Ba ta yi musu ba ta mika masa biro, sai ya hada komai ya rufe ya ture gefe, ya fuskance ta sosai a yayin da ta sunkuyar da kanta. 

Ya ce, “Na kasa gane inda kika dosa Safah, na kasa gane abinda ke karkashin zuciyarki game dani. Safah idan har yau bakisan matsayina a gareki ba sai yaushe ne?” Yayi dan shiru sannan yace “abinda kike bani a rubuce, ba shi nake gani a kan fuskarki ba. 


Ina so mu yi magana ta sosal, mene ne matsayin alkawarin iyayenmu a kanmu? Aure nake so Safah, ba kuma da kowa ba sai ke kanwata da na rayu shekaru masu yawa cikin son ki da kaunarki, sannan cikin dan lokaci in Allah Ya nufa, a kalla bayan kammala karatun sakandirennan, kin ga na girma har nafara_tsufa. Taimakeni ki gaya min matsayin da kika bani a zuciyar ki, domin attitudes’ (halayenki) sun fi yimin kama dana wahainiya mai canza launi a sarari’” 


Kanta ta sunkuyar ba tare da ta ce da shi komai ba. Tana so ta ce da shi ai ba ni nake rubuta maka ba, don ni bani da lokacin ta (soyayyar). Amma kimarshi da darajar shi da take gani na Yaya agareta 

kuma dan uwan da babu kamarshi garesu a yanzu, ya hana. Ita har gobe kallon Imam take kawai a matsayin dan uwa na jini, amma babu birbishin soyayyah, ko kadan babu. Ita kuma bazata iya bude baki ta gaya mishi hakan ba. Al ya zama cin fuska! 


Duk da bata san yaya soyayya take a Zuciyar mutum ba, zata iya dorar da cewa ita kam bata jin komi sai kauna ta ‘yan uwantaka akan Yaya Imam, kwatankwacin wadda take ji, a kan Marwah da aunty Shahidah. 


Ya yi maganar duniya ta ki ko dagowa ta dube shi, ranshi yai mugun baci, don nan duniya babu mai yi masa wulakancin da Safah take masa, bai san lokacin da ya kai hannu ya fizgo nata ba, tace “....... za ka ballani......???7” Shima ya ce “zaki kashe ni ke, idan ni ban ballaki ba. Gara in ballakin, in huta da wahalar da kike baiwa zuciyata Safah”’. 


Allah Sarki! Fita ya yi kuma ya debo kayan karin kumallon da ‘tea’ a kankanin 

kofi ya kawo mata har teburinta, ya tsugunna a gaban ta, ya dora hannu akan gwiwoyinta, ya kwantar da kai a masangalin kujerar da take zaune sabida ya ga tana hawaye, hawayen da yake ganin shi ya kamata ya zubar dasu ba ita ba. Ita hawaye take don ya takura mata, da tunanin zamansa a gida yanzu wanda ke nufin a tursasa ta. Cikin murya mai rauni yace 


“ki sha ba don ni ba, ba don ki so ni ba, ko don na isa in saki abu ki yi, sai don damuwar da nake ciki akan ki sha din, kiyi mini wannan alfarmar, zan samu Safah?” Ta dago ta dube shi, duk sai ya bata tausayi. Amma ba ta ce da shi komai ba. Sai ta mika hannu ta dauki kofin ta kai bakinta, ya juya ya fita zuciyarshi cike da tunani mai yawa. Bai fuskanci inda ta dosa ba. Wata irin mutum ce mai wahalar karantuwa da mugun zurfin ciki. Hakan ke boyewa mutane zahirin abinda_ ke karkashin zuciyar ta. 

Kwanansu uku a Bournmouth suka juyo gida Najeriya. A kwanaki ukun nan da ya yi yana bin Safah agindi-agindi, ko kalmar sannu bai ji daga bakinta ba. 


Flat guda Daddy ya ware mishi cikin gidan da ma’aikatan da za su dinga tsaftace masa muhalli. Amma Marwa ta dakatar dasu, ita ke gyaran sashen Yayan da gyara masa daki tsaf-tsaf. 


Shi kansa ya kula da edtra-care da ta-robar (Marwa) ke bashi tun dawowar shi, kuma yana jin dadi da kulawar da take nunawa a kanshi, wadda Shahida bata yi, shima yake dan tsokanar ta jefi-jefi da (ta-robar) ba kamar da ba. 


Tun kuma dawowar su Safah ba ta kara bari sun hadu ba, buya take a dakin baki tana ta karatun ta. Domin duk sanda yake binta da marairaita da wadannan dadadan kalaman nasa, jikin ta mutuwa yakeyi tayi masa abinda yake so din ba tare da musu ba. Koda ranta baya so. 


Shi ma bai matsa mata ba, har kullum yana mata uzuri da cewa yarinta ke damun ta, 

duka-duka nawa take? Shekaru dai-dai har goma sha hudu ya bata. 


A karshen watan takardar daukar shi aiki ta fito, har da zabi na kasashe har biyu, karkashin kamfanin kera motoci na ‘General-Motors’ din Amurka, reshen (U.K) a garin ‘Glasgow’ ko babban reshensu a ‘Detroit’ (U.S). 


Suka yi shawara shi da Daddy da ya zabi reshen kasar Birtaniyan, kasancewar kamar gida take a garesu. ‘GeneralMotors,’ kamfanine fitacce a Amurka, dake kera motoci masu ban mamaki, sune suka yi ‘bolt (motar nan mai aiki da batir), GMC. Terrain, camero, Cadillac _ srd, Baudhall, opel-astra’ da wasu da dama. Suna biyan albashi da yawa. Tareda daukar nauyin rayuwar ma’aikatansu har ma da iyalin su in akwai, musamman ga wadanda ba ‘yan kasa ba irin sa. 


Kowa ya taya Almustapha murna, wannan karon ma Marwa ta tura mishi mail na taya murna da sunan Safah. 


Tare da Daddy suka je har ‘Glasgow’, inda 

Almustapha ya shiga ofishinsa cike da dimbin nasara. Da fatan alkhairi daga bakin iyayensa da ‘yan uwansa, da duk mai kaunarshi. Shi kadai ne dan Najeriya a kamfanin gaba daya. 


Wannan ba karamin abin alfaharin Daddy bane, kuma abin alfaharin kasarmu baki daya. In da za a ci gaba da samun irin su Almustapha a kasar nan, da kila wata rana muma mun samu kamfanin kera motoci a Nigeria daga hazikan matasan mu kamar sauran kasashen da suka ci_ gaba. Almustapha ya soma_ aikinsa_ cikin kwarewa da himma. Daddy ya dawo gida 


cike da kewarsa. R anar wata juma’a Daddy (Alh. Aliko) da Mami Hajiya Zainab suna falo suna hira aka hasko tashar Aljazeera, inda ake nuna sababbin motocin buick da cadillac da kamfanin kera motoci na ‘General Motors’ ya sanya a kasuwa; karkashin jagorancin Engineer Imam Zubair Dan Kasa. Aka hasko shi cikin bakaken ‘suit’ yana bayanin nasarori da matsalolin da suka gamu dasu wajen kera motocin, da dalilan da suka sanya farashinsu ya ninka sauran motocin da kamfanin ya kera a baya. Cikin turancinshi (British accent) dake fita

Post a Comment for "BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 4 by sumayyah Abdulkadir"

Please chat with our team Admin will respond in a few minutes
Hello, is there anything we can help you with?
Type message...